← Book details Alkawarin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 24

Sashe 16

Alkawarin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Garden din takarasa tun daga nesa kawayenta dasuka hangota suka kwalamata kira hakan yasa takarasa zuwa inda suke zama tayi sanan tadauki bottle na ruwan dake gaban Farida tabude takai bakinta ta kwalkwale duk kallo suka bita dashi, saida ta shanye goran ruwan tass sanan ta ijiye tana sauke ijiyan zuciya, Farida tace “daga ina kike haka duk kinyi zufa kaman kin fito daga yaki” dan yatsine fuska tayi kaman bazatai magana ba ganin yanda suke kallonta yasa tace “Ahmad na mara shine yabiyoni and someone…..” tadanyi shiru kafin ahankali tace “wani mutumi yataimakeni” atare dukansu all the 5 friends sukace “wani mutumi” shiru tayi sai chan tace “oho nima ban sanshi ba” dukansu dariya sukahau yi dasauri takallesu tace “me” hada baki sukayi sukace bakomi, sharesu tayi kawai cus she doesn’t even feel okay batasan mesa ba, duk suna zaune wata kawarsu tashigo eatery dagudunta tana haki tace “kufito kugani yan sanda sun shigo school dinan anzo ana kwashe su Ahmad da Gang dinsu” dasauri Farida tace “ke haba let’s go video it musashi a internet” dukansu tashi sukayi itama ta tashi tabisu suka fice daga cikin garden din, van suka gani na police gaban wani eatry dake kusada garden din dasuke ciki, dasauri suka karasa gaban eatry din student sun cika wajen suna kallon Van din police, suna tsaye wajen dayay cha da mutane sukaga an fito da Ahmad da akasamai handcuff a hannu an sashi a van din sai abokanen shi na dazsu dasuka biyota guda biyu saikuma wasu guda biyu daban yan sandan sun fito dasu ana sakasu a van din saiga police man dinan shima yafito daga eatry har lokacin yana sanye da kayan dazu farin shadda waya a kunenshi still, hada idanu sukayi batasan mesaba jitayi gabanta yafadi dasauri ta sauke kanta kasa tareda juyawa ahankali tamabar wajen bata kara juyowa ba kawai tai hanyar class nasu, daidai lokacin ana shirin fara wani lecture kujera tasamu atsakiyan ajin ta zauna sanan tabude jakanta taciro note nata da pen aka fara lecture ko kadan takasa concentrating batasan mesa ba she just keep seeing police man face din da what happen today, gabaki daya all through da day har yamma ita kanta tasan yau ba school tazo ba takasa natsuwa tunanin shi da komi yacika mata kai, wuraren 5 na Yamma Adamu direba yazo daukan ta shiga motan tayi ahankali tace “Adamu please kafara kaini Coldstone nasayi ice cream nasha saimu wuce gida” cikeda girmamawa yace “to Miss Khairy” daura kanta tayi akan kujeran tajuyar da kanta tana kallon hanya tareda fuzar da ijiyan zuciya, she just hope tanashan ice cream dinan sanyin shi zaisa brain nata yay sanyi tadena all tunane tunanin datakeyi tun safe.

Agaban wani Babban joint na coldstone Adamu yay parking hakan yasa tabude motan tafito ta shiga ciki, daidai wani Babban Jeep na shigowa wajen parking yayi kusa da Benz da Adamu ke ciki, bude gaban motan yayi yafito ahankali wanan karan yana sanye da kayan yan sanda Rolex din dake daure a hannunshi yakalla shidda saura, sanan yazaga zuwa boot din jeep din yabude keken guragu yaciro ya ijiye ya maida boot din yarufe sanan yadawo bangaren baya yabude motan wata kyakkyawan tsohuwa ce fara sol kaman balarabiya zaune abayan tasaka Riga da zani irin na tsofaffi anmai dinkin Bubu kafafunta da hannayenta sunsha lalli, hannunshi yamikamata batare dayace mata uppan ba hararanshi tayi tana kama hannun nashi tamike tsaye da kyar tana masifa tace “idan kaga dama kai gaba dani dagayau har jibi Ice cream dai saika kaini nasaiwa jikoki na ja’irin yaro kawai” ko kala baice mata ba da taimakonshi ya daurata akan keken sanan yamaida kofan bayan yarufe da karfi tace “kama balla motan baban karfi, ubanka zai sayamin wata Alhamdulilah Allah yamai arziki rufin asiri danasha takaici” cikeda masifa yace “wlh Goggo in baki shiru ba anan zan barki na shiga ciki nasayo” wani kalan murmushi tayi tamaka bakinta tace “yo ai nadauka gaba kake dani to muje nadena” dan murmushi kadan kawai yayi sanan yashiga turata zuwa gaban entrace din dakenan divided into 3, staircase ne gefe da gefe sai tsakiya a bit sloppy floor dazaka haura ka shiga cikin shagon, daidai lokacin security na budewa Khairy kofa tana fitowa rikeda paper bag na ice cream din dakuma handbag dinta rataye a shoulder dinta, saiga wasu yara su biyu maza dabazasu wuce 8yrs ba suna guje guje kowanne rikeda ice cream dinshi dayan kawai ya mamayi brother shi ya fizge ice cream din hakan yasa brother yay ihu yabi dan uwanshi da gudu Khairy dabude mata kofa kenan tasa kafa tafito zata fara sauka daga staircase din kawai yaran suka fito suka mugun bangajeta dayasa ita kanta tasaki wani irin ihu kafanta ya gicce abunku da tiles kawai ta kifo zata fadi da mugun sauri Gwaggo tace “Subhanallahi” dawani irin sauri yasaki wheelchair Gwaggo daidai kanta zai daki dakaIUlin stairs din…
2️⃣1️⃣

Free page
Saida tai sallan isha’i sanan tacire hijabi kayan bacci taciro tasaka tana tunanin abinda yafaru dazu itada Aliyu, dan murmushi tayi sanan ta kashe wutan dakin ta kwanta.
Batasan mesaba tadade kwance rikeda wayanta tana kallon wayan every minute deep down she wish to hear his voice amman kuma bamataso tana tunanin what she wish for din akanshi abin is so so new for her she’s not just use to it, ahaka bacci yay awon gaba da ita wayan nakan kirjinta this is the first ever time in her life da waya ke bacci akan kirjinta.

Wuraren 12 nadare wayan nata yahau ringing afirgice tafarka tana daukan wayan daga kan kirjinta tana danna gefe dan yadena ringing yay silent, sanan takalli screen din da kyau ganin Aliyu Hydar batasan mesaba faduwa gabanta yayi, ahankali takai yatsanta dake dan rawa ta danna wayan na gab da katsewa takai kunnenta, murya chan kasa dake nuna alamun bacci tace “Hello” shiru yayi yana sauraron muryanta da bazaiyi karyaba tunda yake baitabajin macen da muryanta yamai dadi kaman nata ba, dan gyaran murya kadan yayi cikin wata kalan murya dashi kanshi baisan yanada itaba yace “Khairy” ahankali kaman wata Yar karaman baby tace “Uhm yajiki? Kasha magani?” dan murmushi yayi jikinshi namai wani iri jin muryanta like that so naked sabida baccin data fara, sanan har ranshi yaji dadin yanda ta tambayeshi yajiki koyasha magani, ahankali yace “yeah, Abba yamin allura” kaman zatai kuka dan ita harga Allah tanada tausayin mara lafiya tace “auuch that must have hurts, I hate niddles, sorry ko!” murmushi yayi ya gyadamata kai yace “thanks, you are sleepy”? Gyadamai kai tayi tace “Uhm” ahankali yace “alright good night, make sure you plug in your phone sabida yasami chaji, and say your prayer before sleeping okay” gyadamai kai tayi ahankali tanajin wani iri azuciyanta kaman tacemai sucigaba da magana karya tafi tadenajin baccin tace “okay night” tai maganan batare data cire wayan daga kunnenta ba shima bai katse wayanba sunkai kusan 10min ahaka sanan murya chan kasan kasan makoshi yace “I love you Ummulkhair okay” gyadamai kai tayi ahankali tanaji hawaye nazuwan mata dabama tasan na meyeba but ko Allah yasani she just feel damn connected to him and vulnerable around him kaman ba itaba, katse wayan yayi hakan yasa taciro wayan daga kunnenta tarungume wayan hawayen na gangaro mata daga idanu, karan message dataji yasa taciro wayan daga kirjinta dasauri tabude wayan ganin message from Aliyu Hydar, bude messege din tayi da sauri. “Maisa nake sonki Ummulkhair? Well who am I to question faith? All I feel right now is I wanna spend my eternity with you, gud night Khairy”
Takaranta message din kusan sau biyar sanan ta danna reply tai shiru tana kallon blank space din bamatasan mezata rubuta maiba, saikuma chan tashiga typing .
“I feel vulnerable and free around you, my heart beat whenever I hear your voice, duk sanda na rufe idanuna kai kadai nake gani, is that love?“
Yana ganin message din yay mata reply.
“time will tell Khairy na❤️”
Wani kalan murmushi tayi ganin yakirata da Khairy na sanan ta tashi zaune USB takamo dake jone da wall socket ta saka wayan nata kaman yanda yace tayi sanan takoma ta kwanta tadade kafin bacci yay awon gaba da ita.

Da asuba Baba yashigo yatadata saida yaga tashinta dan Khairy nada nauyin bacci sanan yawuce yatafi, bayi tashiga tadauro alawala tazo tai salla, koda tagama karatun Al Qur’ani tayi yau sosai wuraren 6 ta tashi, hijabi tacire yau ita keson yimusu breakfast tunda bazata school ba hakan yasa ta tashi tafice daga dakin tasauka kasa kitchen tashiga tana murmushi tace “idan matarchan tazo yau zataga na hutashe ta” lafiyayyen breakfsat tahada musu dan sinasir tayi da farfesu sai kunun Gyada dasu fried chips, saida tagama tsaf sanan tashiga fito da komi falo ganin Mama zaune afalo kusada Baba yauma sanye da kayan sanyi yasa ta ijiye kulan a tsakiyan falo ta tashi tana kallon Mama dataga tamata haske sosai Mama datake nan baka but tai wani irin haske, kafinma Mama tai magana Baba yace “ke wuce ki kawo mana abinci ga yayyinki nan zuwa” dasauri tajuya tana murmushi tace “Baba naga Mama tai haske ne takara kyau” kitchen tashiga takarasa fito dakomi takawo lokacin su Manaf sun shigo suma zama duk sukayi Baba da kanshi yadebo ma Mama Sinasir yana bata abaki, murmushi tayi tana kallonsu tana taba Ya Manaf, hararanta yayi yace “dalla kauyus” cigaba dacin abinci duk sukayi kowa yay shiru Baba da Mama ne suka fara gamawa sanan yakalli Khairy yace “Maman ki tace zaki saloon ko” gyadama Baba kai tayi tace “eh Baba, gyadamata kai shima yayi yace “yau rabonki da gidan Baffan ki kwana nawa” dan ajiyan zuciya tayi ganin yanda Baba ke kallonta sanan ahankali tace “an dade Baba” jinjina kai yayi yace “kije ki shirya kitafi saloon yanzu ana gamawa kije gidan Baffan ki ki gaidasu sanan kije gaida Matar Hafiz” ahankali tace “to Baba” “tashi kije” tashi tayi tai sama Baba yacigaba dayima Mama hira yau yanaso yakaita asibiti kotaki kotaso dan kwata kwata this days bata iya baccin dare ga kurajen nan kara fesowa suke ajikinta bana wasaba.
Chapter 16 · 0% Book details