← Book details Alkawarin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 24

Sashe 14

Alkawarin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Wajajen 3:00 na rana tafarka, dakin tabi da kallo kafin ahankali tafara yunkurin tashi dasauri Manaf da Mu’az suka dagota, ahankali Mu’az yace “kinajin yunwa Mama mezakici” dakin asibitin tabi da kallo kafin ahankali tasauke ijiyan zuciya tadanyi murmushi ganin duk sun damu tace “ya akayi bakuje aiki ba yau, laaaa is that Hafiz” tai maganan tana kallon Hafiz dake zaune kan kujeran gaban gadon yana kallonta cikeda tausayi, cikeda murna tace “zonan zoka nunamin hoton jikata nagani” dan murmushi yayi yataso yazo, wayanshi yaciro yafito da picture cute baby girl dinshi yabata karba tayi tace “Masha Allah tubarkallah, Allah ya rayamana kaga yarinya kaman Babanta Yan biyu” tai maganan tana nunamusu hoton kafin idanunta ya sauka kan time din wayan ganin karfe uku har da minti goma yasa dasauri tamikamai wayan takalli Mu’az tace “kiramin Dr yasallameni inkoma gida, Khairi takusan dawowa daga school” tana maganan saiga Baba da Baffa da Dr sun shigo tare, Baffa na ganinta yace “ya jiki Maryam” murmushi tayi tace “Alhamdulillah Baffa, ya ji kalle inasu Hajiya Asiya” kafinma taji amsanshi tace “Dr zokai discharging dina natafi gida” ahankali Dr yakaraso wajen yace “Hajiya kibari mu dubaki na kwanaki tukunna saimu sallameki” kallon Baba tayi sanan takalli Dr rai Adan bace tace “sallameni yarana banaso su dawo Bana gida Dan Allah” kallon Baba tayi sanan ahankali tace “daman Wanan ne shirinka idan ka kawomi asibitin arikeni” dasauri Baffa yazo wajen anatse yace “Maryam kalleni nan” ahankali tajanye idanunta dagakan Baba dake kallonta kuri takalli Baffa, anatse Baffa yace “Maryam kiyakuri ki zauna likitocin nan su cigaba da baki gudunmawa, zamanki agida zai karasa ciwon yazama worst ne, dan Allah maryam inhar kinajin magana ta” lumshe idanunta tayi sanan tabudesu ahankali tace “Baffa tun ina yarinya kasanni ban taba cemaka no ba, kome kacemin inayi dan haka yau Baffa dukanku anan zan rokeku alfarma, dagayau dan girman Allah kome zai sameni karku sake dawodani asibiti, Baffa nasan kalan chutan danake dashi, nasan metake nufi, da inzauna anan allurai da maganinsu yakarasa cinyeni gwara in koma dakina, I want to die adakina tareda yarana dakowa, I hate hospital and zaman asibiti shizaifi kasheni dawuri sama da komi, please Baffa dan Allah, idan baka yarda ba naji zan zauna, amman rokonka nake please Baffa” kowa na dakin saida jikinshi yay sanyi har Baffa, ahankali Manaf yakalli Baffa yace “Baffa please grant Mama wish, let’s just take her back home ko Hafiz” gyadamai kai Hafiz yayi da idanunshi sukai jajir, hakama Mu’az, ganin Baffa da Baba sunyi shiru dan su sunfiso tazauna a asibiti tasami lafiya yasa ahankali Dr yace “Alhaji kubarta takoma gida, idan anything come up ku kirani ni zandinga zuwa nadauki Wanan nauyin” ahankali Baffa yakalli Baba dakokadan baisoba, kallon kayakuri takoma gidan, hakan yasa ahankali Baba yace “shikenan” murmushi Mama tayi sosai nan da nan aka zaremata drop din sanan Dr yarubuta mata magunguna suka saya sanan suka dawo gida gabIaki dayansu.
💫 ALKAWARIN ZUCIYA 💫

✍🏻M SHAKUR

1️⃣4️⃣
Chapter 14 · 0% Book details