← Book details Alkawarin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 24

Sashe 19

Alkawarin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wuraren 8:00 na safe tabude idanunta ganinta adakin yayyinta saida abin yabata mamaki, murmushi tayi ta tashi zaune sanan ahankali ta sauko daga gadon lallai tagaji ko lace din jikinta bata chanza ba tai bacci, jakanta tadauka tawuce tafita daga dakin tana tafiya ahankali, flat dinsu tashiga babu kowa a falo sama tayi dakinta tashiga alwala tayi tai salla tukunna sanan tacire kayan wata doguwan rigan bacci ta tasaka sanan tafito direct hanyar dakin Mama tayi bude kofan tayi tace “Mama tun jiya nan ganki ba adakin su Ya Manaf na kwana” akan gado taga Mama ta jingina da hango ta sanya sweater tai fayau da ita da hulan sanyi akanta batasan mesa ba but gani tayi Mama tamata wani iri a idanu, karasowa tayi gaban gadon saikuma ta tsugunna takai hannunta tai tagumi tana kallon Mama, hararanta Mama tayi da kyar ta iya dagewa tabude bakinta tace “me haka”? Ahankali tana kallonta still tace “Mama wlh kin chanza, lips dinki are so dry, Mama wai bakida lafiyane kike boyemin kinyi wani iri eh sabida kinsan zan damu, bazan damu bafa Mama ai yanzu na girma saima na kula dake” dan shiru tayi tana kallon Maman dake kallonta tanaso tai magana amman azaban datakeji awuyanta yasa takasa, dasauri Khairy tace “zan damu kadan but zan kulada ke bakid lafiyane Mama” tai maganan idanunta na rau rau dan she’s really believing Mama bata da lafiya, ganin haka yasa Mama tamikamata hannu sanan tahadiye duk wani azaban datakeji tace “lafiyana kalau kawai gani nayi my little Khairy has grown so sooo big, yarinya na tai girma she can even take care of her Mama come here” dasauri ta tashi hannun Mama takama sai kawai tasaki hannun tafada jikin Mama ta kankameta sosai ahankali tace “Mama wlh ina bala’in sonki, without you bansan ya zan kasance ba, Mama ko idan na kalli wasu yaran ko sai inga they are not lucky sabida bakene Maman su ba, Mama u are the best Mama I the world, u are the coolest Mom, the softest, the sweetest, bakida fada, gashi kina sonmu, we are ur everything Mama, Mama kinsan menene” girgiza mata kai Mamantayi, Khairy tace “all mothers are mothers, but not all mothers are like Mamana, cus Mamana tafi takowa dadi, Mama kinga duk girman dazanyi I will always be ur baby, Yar autan ki, kinga na gama school nafara aiki zan dinga miki komi, Mama nasan kinje makka but zan kaiki makka da kudina da aka biyani albashi wajen aiki” dariya Mama tahauyi sosai dayasa Khairy wani kalan murna, sanan tace “Mama yauma ni zan miki breakfast mezaki ci na dafa miki” ahankali tace “fate nakeso” wani tashi tayi tasauka daga gadon sanan tai juyi tace “then fate it is bari naje” tajuya dasauri tai hanyar kofa hartasa hannu zata bude kofan ahankali Mama tace “Ummulkhair” faduwa taji gabanta yayi hakan yasa ahankali tajuyo takalli Mama tace “naam” dakai Mama tamata alamu tazo dasauri taje gaban gadon, hannu biyu Mama tasa tai cupping face nata tana kallonta kafin ahankali takai goshinta saitin bakinta sanan ahankali ta manna mata kiss a goshin, murya chan kasa tace “I love you Ummulkhairy, Allah yamiki Albarka, Allah ya haskaka rayuwanki, Allah ya tsaremin ke” ahankali tana kallon fuskan Mama tace “Ameen Mama” takasa tashi, ganin kaman she’s trying to read something from Mamas face yasa Mama tace “Oya tashi kije kimin fate na yunwa nikeji Madam kokin fasane tunda kin tasani gaba kaman kin sami talavijin” da sauri ta tashi tana dariya tafice daga dakin.

Bana tagani agaban dakin murmushi tayi tace “good morning Bana natafi yima MaUma fate”.

2️⃣4️⃣

Free page
This book is 1k to join my group pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461

Chat me up directly by clicking on this link
wa.me/+2347012181461

Wuraren 11 tagama faten daya cika gidan da kamshi, fito da kulan falo tayi Mama tagani da Baba zaune afalo saisu Ya Manaf sunama Mama hira, tashi Maheer yayi yatayata suka fito da komi tsakar falo sanan suka zazzauna karban na Mama Baba yayi da kanshi yadinga bama Mama faten bashi kadai ba harsu Manaf sunyi mamakin yanda tasha faten dan tadena cin abinci, tass ta shanye sai dadi Khairy keji saida kowa yagama sanan ta kwashe komi itada Maheer sukakai kitchen tarema sukai wanke wanken tace “lallai yau mutanen mutuncin ka na nan kusa Maheer” hararanta yayi yawuce yafita daga kitchen din itama tabiyoshi tafito, Baba dake kallonsu yace “go and get ready Khairy malamin ki zaizo by 12” sama tawuce agurguje ta shirya tafito falo lokacin ba kowa Baba yakai Mama dakinshi, by 4 malamin yatafi su Manaf suka fita da ita basu dawo gidan ba sai around 10 tana zuwa lafiyan gado tabi.

Gabaki dayan gidan yau basuyi bacci ba sabida yanda jikin Mama yay tsanani, amai tadingayi na jini both tabaki da hanci, jikinta yay zafi sai maganganu take dabama sa ganewa, saida safen nan bacci ya dauketa.

6 ta tashi tana kallon agogo mamaki ma take ya akayi take lattin tashi late this days, wayanta dataga yay haske yamika hannu tadauka 2miss calls tagani na Aliyu saikuma message dayamata bude message din tayi. “I miss you” murmushi tayi ta ijiye wayan sanan ta tashi tawuce bayi wanka tayo tareda alwala Dan yau tanada morning lectures, tana fitowa tasa kaya tai salla sanan tabude kofa tafito su Ya Manaf tagani a falon sama kwakkwance kan kujera suna bacci, mamaki tayi amman ta tabe baki tai hanyar dakin Mama bude kofan tayi zaune taga Baba kan kujeran dakin yabude Al Qur’ani yana karantawa itakuma Mama na kwance kan gado tana bacci yarufa mata bargo, saida yakai ayar sanan ya kalleta tace “Good morning Baba” murmushi yamata yace “morning daughter, Mama is sleeping jiya dukanmu bamuyi bacci dawuri ba munata hira yayyinki na nan falo suna bacci suma” gyadamai kai tayi tace “eh nagansu” Gyadamata kai yayi yace “jeki breakfast yau Monday 8 kikeda lectures i want you to be serious kigama da good grade” gyadama Baba kai tayi sanan tajuya tafita tana kallon fuskan Mama dake bacci peacefully sanan tasauka falo ahankali, kitchen taje tea tadafa musu duka sanan ta soya chips zama tayi dinning zataci amman hakanan taji takasaci jikinta yamata wani irin sanyi kodan ita kadai ke yin breakfast dinne oho, tashi tayi tawuce sama tana kallon su Manaf da still ke bacci ta shiga dakinta dan shiryawa.

Shiryawa tayi tsaf cikin wani black abaya mai bala’in kyau tai rolling gyalen akanta ko kadan batai kwalliya ba but she looks kaman wata Somalian queen, jakanta tadauka sanan tafito, dakin Mama tabude takalli Baba dake karatu har lokacin tace “Baba natafi” saida ya idasa Ayan sanan yadago kudi yaciro yamika mata karba tayi tana murmushi tace “thank u Baba, kacema Mama natafi idan ta tashi bye” murmushi Baba yayi yace “to yarinyar Mama” maida kofan tayi tarufe yasauke ijiyan zuciya Noo yagaji Khairy deserve to know Maman ta is sick, he’s tired of hiding it from her, bari Maryam ta tashi zai gayamata is time sufadi ma Khairy, Khairy is grown up she can handle it.

Fitowa tsakar gida tayi tana tafiya ahankali hakanan jikinta kawai yamata sanyi yasaki tarasa mesa kawai she’s feeling sad and week ma yanzun nan, karasawa wajen motanta tayi Adamu na shiga itama tana shiga baya daidai sunajin horn mai gadinsu na budewa, motar Baffan ne ke shigowa gidan Hafiz ke tuki, sai motar Ammi biyeda su da driver ke parking sai kuma motan Mom, bude kofan motar tayi tafito tana murmushi da saurin ta tai wajen motan Baffa, daidai lokacin Baffa na bude baya yana fitowa yana mata murmushi yace “yan makarantan bokoko” dariya tadanyi tace “Baffa ina kwana, Ya Hafiz Baban Baby ina kwana, Laaaa Ya Hassan da Ya Hussain harda ku akazo yau” kafinma suyi magana Baba yace “wuce tafi school karki latti” yanuna mata motarta da Adamu yatada yana jiranta shiga motan tayi tana waving Mom dake saukowa daga motanta dan har yanzu motan Ammi bama abude ba kuma bamata iya ganin cikin banda driver shima ta glass din gaba taganshi dan motan tinted ne, jan motan Adamu yayi suka tafi nai gadi yamaida gate din gidan yarufe daidai lokacin Baba da Manaf suka fito.
Chapter 19 · 0% Book details