← Book details Akan Pre Weeding Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 5

Sashe 4

Akan Pre Weeding Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

```MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUMMM WANI ABU SAI ROYAL STAR WRITER'S ✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) 💪💪💪💪
UP-UP-UP```

_🍂"ALƘALAMINMU🖋️ ƳANCINMU"🍂_

*GAJEREN LABARI*

*🅿️85&90*

_Wannan page ɗin sadaukar wane gareka Muhammad <MAIDUGURI> (MAIYALO DA DADDAWA😜) Naji daɗin goyon bayanka da yabawarka Akan wannan littafin nawa maitaken AKAN PRE_WEEDING PICTUR'S INAYINKA ADIK INDA NAKE KUMA KAKE ALLAH YAƘARA KAUDA MUGUN IDO KANKA NAWAN M.D💃💃💃💃_

```INASANE DAKU MASU KUSHE DA ZAGI SAIDAI ZAGINKU BA ABUNDA ZAIMUN KUMA BAZAI HANANI ƘARASA WANNAN LITTAFIN BA IDAN KINJI HAUSHI TO KIDAINA PRE_WEEDING PICTURE'S BA KYAU KAWAI LALACEWAR ZAMANI NE DA HUƊUBAR SHEƊAR HAƊIDA ƘARSHEN ZAMANI FATANA MUJI TSORON ALLAH MUGYARA KABARURRUKANMU TINKAN MUSHIGESU TINATARWACE KAWAI DAGA MUJAHEEDAH MATAR MLM.. AMMIEYN KHAUSAR DAMA MUHAMMAD <MAIDUGURI> AKODA YAUSHE MUNA FATAN AL'UMMARMU TAZAMA TSALKAKKIYA NAGODE ALLAH YASA MUDACE KUMA ALLAH YASA MU AMFANA```

_A KWAI YUWAR NADAINA TYPING GABA ƊAYA IN ALLAH YAƘADDARA FARUWAR HAKAN_

Aɗan razane Naxla tamiƙe "Whats? Daddy kasan me kake faɗa kuwa? Alhaji habib ɗin ne zaimun irin wannan sakin na walaƙanci kuma Abainar jama'a kotarewa banyi ba yamun saki Uku,? kai haba ina!! inagadai bakaji da kyau ba ko banice hakan tafaru da itaba gaskiya,"

Haushi ne yasa Daddy baiƙara magana ba Yakunna t.v ɗin nakin yana faɗin "saiku kalla nan kuga"

Aikuwa har Anwatsa kan medi'a dama masu vide'o sunzo wurin da ƴanjarida sun fara aikinsu kasancewar Alhaji Habib babban mutum ne mai ƙuɗi kuma ɗan siyasa,

Angama komai har AnÉ—aura Auren naxla da habib Akan sadaki million 3 ras, Saiga kira yashigo wayarsa, YaÉ—aga yanata faman washe baki Dan Aganinsa yayi babban kamun tagaban Office,

"Kasan waka Aura kuwa Habibu? to kashiga medi'a kagani,"

Kit Aka katse kiran, da kallo yabi wayar dan tintasowarsa baitaɓa jin Mahaifiyarsa takira sunansa ba amma yau gashi takira kuma yanayin muryarta dakwai damuwa, danha cikin sauri yahau medi'a..

Aikuwa take yafara cin karo da hotunan naxla haɗida vide'o birjik wai pre_weeding pictures Abun bashawa dik jikinta waje hutunan gashi maza saimata comments da laking Ake itakuwa saiƙara barbaza photunanta take,

Ransane yayi mugun ɓaci baisan hakan take da rawar kaiba da wallh baiyi wannan ganganjin ba, Miƙewa tsaye yayi cikin fusata Yafurta," Ni Alhaji habib Mainera nasaki matata wadda kuka ɗaura Auran yanzu wato naxla nasaketa Saki ɗaya! biyu!! Uku!!! ras ba gyara kuma dalilin wannan sakin shine *AKAN PRE_WEEDING PUCTURE'S*.,"

Yana gama faÉ—in hakan yabar wurin cikin takaici da tsanar dik wata mai É—ora pic A medi'a da biyewa shairin shaiÉ—an gun wannan la'anan nan Abun wai *PRE_WEEDING PICTURE'S*.....

Daddy kam kasa Aikata komai yayi yabar wurin cikin ƙunar zuci, Aiko ƴanjarida tin nan suka sami kanun labarai yazamana ko ina shi Ake hasakawa da photunan ta na *PRE_WEEDING PICTURES*...

Zama tayi ƙasa dirshan wata zufa na mata tsiyaya bata taɓa tunanin zata samu mummunan sakamako irin wannan ba, nafarko tanason Habib gashi yanzu ya haramta gareta na biyu gashi nata Hutunan sune suka Zaga duniya shikenan tabar mugun record ba wanda zai Aureta na uku taɓata sunan iyayenta,

"nashiga uku ni naxla wannan wace irin ƙaddarace mai nauyi haka,"?

Dariyar takaici Daddy Yayi Kafin Yace,"Da saura yanzu baki shiga ukun ba dan ina tabbatar mikihar 100 saiki shiga bawai 3 ba tinda kika biye shiɗan ke wayayya ba wai *PRE_WEEDING PICTURES* To gashi Auren ki yatarwatse kuma kinrasa miji kenan saidai kita zama haka, ke kam kinga illarsa yau kuma harda ƙawarki naji Ance Ansaketa itama Dik *AKAN PRE_WEEDING PICTURE'S*..........

Yana gama faɗin hakan yabar ɗakin, Abokan natama watsewa sukayi kowacce tawuce tana dariya haɗida faɗin Alaƙara suna ƙara bada labaran ...

Surayya na hanga zaune saifaman share hawaye take tana nadamar yin ƙawance da Naxla dan da baisameta gidansa Aɗakinsa hakan ba da bazai saketa ba,

Ameera ce dake da tsohon cikinta take lallashinta...

Shigowa Abba yayi Palourn da sallama yaÉ—an kallesu, Tabashi tausayi Amma hakan baihana yafaÉ—a mata gaskiya ba,

Zama yayi kusa dasu yana fuskantarsu haɗida kunna t.v ɗin Yace," Kinga Abunda yafaru da sheɗaniyar ƙawar taki,"

dik kansu suka kalle t.v Sosai Surayya tatsorata da lamarin duniya nadamar biyewa zuciya da naxla take nazuwa *PRE_WEEDING PICTURE'S* Sosai Abba yamata faÉ—ada nisaha haÉ—ida nuna mata illar wannan shegen photunan..........

_BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_

WhatsApp number 07064904617 or call 07031012948

Abba yayi gyaran murya sannn Yace "Sahir kafa É—amuna dalilin sakin matarka,"

"Abba katanbayeta kaji," yana sunkuyar da kansa yayi maganar...

"Dungure masa kai Umma tayi "Saboda muna Abokan wasanka Aidole katsaya ɓatamuna lokaci na mutanbayeta, Munganta mukace kuma ai kaine babba koba Aure dan haka ko kafaɗa muna wllh ko naɓata ranka sahir dama inafushi dakai bawai na sauka bane," taƙare maganar cikin hasala..

Malam Yace,"A'a kada Ayi haka ita tafaÉ—a muna meye sila,"

Surayya dake matso hawaye Tace," Wllh Abba bansani ba banmasa komai ba harma yafita ne kawai yaturomun wannan text ɗin wllh bansan komai ba Abba," taƙarasa maganar tana ɗan matsawa baya,..

"Sahir kayi magana kona saɓa maka wllh," cewar Mahaifinsa cikin fushi......

Tabbas yalura iyayen nasa sunɗau zafi dan haka yafara bada haƙuri," Abba kuyi haƙuri wllh inason Matata yanzuma namaidata ɗakinta dan Allah kada kuyi fushi dani dama dan kawai tayi....,"

Saikuma yayi shuru yakasa ida faÉ—a...

Muba Yace," Bafa ranar ɓoye ɓoye bace wannan Sahir kafaɗe gaskiya kawai,"

Shuru yayi na ƴanwasu mintuna kafin yafara bada labarin sanda Akaturo masa text da zuwansa ɗaurin Auren dama haryanzu Anan yawan matsanta masa da text kuma idan yakira bata shiga,, Amma wllh inasonta nakasa faɗin wannan ne saboda banason Sunanta yaɓaci idan narabu da ita haka saƙat zata iya Auren wani record ɗinta baiɓaci ba, amma wllh inasonta Abba kumun Afuwa dan Allah," Yaƙarasa zancen yana nuna nadamar Hukuncin da yaɗauka....

"Nuna muna photon" Mlm Yace mahaifin Surayya....

Badon yasoba yabada wayarsa take Photunan surayya guda 3 suka bayyana kowanne É—inkin yaÉ—ameta kuma gawani saurayin kusa da ita suna murmushi wajunansu.
Haka kowa na É—akin ya kalle pic É—in, Mlm
Harzuwa kanta Hannunta narawa taduba Hawaye kezuba daga idanuwata tana girgiza kai Sam takasa magana dan batasan mezatace su yarda da ita ba..

Ajiyar Zuciya Mlm Yasauke "Wannan ko bantanbaya ba Nasan kunsan waÉ—annan photuna na *PRE_WEEDING PICTURE'S* É—insu ne,"

" to amma ina tahaÉ—u da wannan"
Cewar Ameera dake zubda hawaye...

"Inako tahaɗu da shi inaba gun photunan ba, Sahir kamun daidai kuma Ayanzu nakeson kamata saki 3 taharamta gareta tazauna taɗan ɗane Abunda tashuka ba tazaɓe yin pre_weeding pics ba to itama inason Amata saki 3 Kamar yarda yafaru da ƙawarta ita kanta taɗan ɗana *AKAN PRE_WEEDING PICTURE'S* ɗin,"

Dasauri Saurin Yace,"A'a kada Ayi haka malam wllh batasan najikin photon ba kawai Azal tafaɗa matane kuma hakan tasameta ne *AKAN PRE_WEEDING PICTURE'S*,"..…………………………………………………………………

_BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_

WhatsApp number 07064904617 or 07031012948

*AKAN PRE_WEEDING PICTURE'S* _FREE BOOK_

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MALAM, AMMIEYN KHAUSAR... HEEDAH HYDAR OSTHMAN.... TAURARUWAR ROYAL STAR WRITER'S_

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

```MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUMMM WANI ABU SAI ROYAL STAR WRITER'S ✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) 💪💪💪💪
UP-UP-UP```

_🍂"ALƘALAMINMU🖋️ ƳANCINMU"🍂_

*GAJEREN LABARI*

*🅿️99&100*

FINAL!
FINAL!!
FINAL!!!

FINAL PAGE INSHA ALLAH....

*FRIDAY 17/6/2022*

_Ina godiya ga Allah dayaban ikon kammala wannan littafin nawa mautaken *AKAN PRE_WEEDING PICTURE'S* Wanda nasamu fans Akansa kuma nasami maƙiya dama wanda ke ƙoƙarin kawo gyara Acikin Al'umma Akan wani Aiki maikyau wanda yakasance gaskiya ne to dole ya fuskance ƙalubalai da dama, dan haka najajirce harnaga nakammala littafin dik da saƙwannin ɓatancin ku inasamu Amma bakomai ni dan Allah nake typing ɗina kuma da Aɗau darasi inafatan muɗauke maikyau mara kyau kuma muwatsar Allh yakaremu da imaninmu_

*AKWAI YUWAR WANNAN YAZAMA LITTAFINA NA ƘARSHE SAI WASU BAYAN SHEKARU NACIGABA INNA SAMI DAMAR HAKAN AMMA INKO BANSAMU BA TO SHIKENAN.. INAROƘON DIK WANDA NATAƁA ƁATAMA SILAR RUBUTUNA DAN ALLH YAMUN AFUWA YAYAFEMUN ALLAH YAƘARA SADAMU DA ALKHAIRI...*

"Ni sunana Sani kuma ina aiki Agidan photon da sukaje, Wata ƙawarta danaga Anfasa Auranta yanzu itace tasani Aikin tabani kuɗi masu yawa Akan na aikata wannan aikin, Ana gobe zasuzo photon naxla tazo taban dubu 10,000 Akan namata aikin idan kunzo photuna na saka wani namiji cikin photon naɗauka batare da ke ko saurayin da zaki Aura yagano ba, da farko naƙi yarda Amma ganin yawan ƙuɗin kuma nasan koban Ansaba wani zai Ansa kawai saina Amince, bayan sunzo Anamusu pic ɗin ne sai Aka kirashi bayan yafita kafin yazo natura wanda muka haɗa plan ɗin dashi danufin yazo bata style ne sai yayi Abunda yasata dariya daga nan nayi Amfani da damar nikuwa nadinga ɗaukar photunan batare datasani ba, bayan tawuce na wanko kamar 50 nabata Amma wllh bansan komai game da itaba, dan Allah kuyafemun wllh shairin shaiɗan ne,"
Yaƙarasa maganar yana kuka……

"Ga kanan babban sheɗan! Ai kaine shaiɗan nin mugu wllh ka kassara rayuwata da Ace ta Aure wani narasata ne wllh dasai nakasheka Azzalumi kawai," Yamiƙe haryana shaƙo wuyansa dan yaji zafin lamarin sosai..

Da ƙyar Akasamu ya sakeshi yakoma yazauna yana huci, Shikuwa dik ya tsorata ne..

Naxla da tajima da shigowa taji komai dama tazone dan tafaɗe iya nata laifin kuma taba da haƙuri saita same sani yazo yafaɗa Ashe..

Ƙarasow ciki tayi Cikin tazauna kusa da Surayya takama hannunta Tace," dan Allah kiyafemun wllh naga sakayya tinkan Aje ko ina, kuma wllh ba laifina bane nima Tsohon saurayinki T.j tijjani shiyasani dan yahuce haushin fasa Aurensa dakikayi, kuma dika hakan tasamu ne *AKAN PRE_WEEDING PICTURES'* Domun dabakije yinsaba wllh hakan bazata faru dake ba,"

Jinjina kai Malam yayi "To Alhamdullah tinda komai yazama haka saiku yafe juna domun idan kunduba dika hakan tasamu ne saboda wannan banzar Al'adar wai *PRE_WEEDING PICTURE'S*,".....

"Hakane Abba Amma dan Allah Kayi haƙuri, kawai tatashi mukoma yanzu," cewar Sahir cikin magiya yaƙarasa maganar
Chapter 4 · 0% Book details