← Book details Abin Tsoro Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 2 OF 3

kashi wannan yaro ba danka bane! ka fice

Abin Tsoro Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 20 min read

ka barni ko na nemo ubansa ku kwashi dan
kallo dashi” shiru yayi don alokacin ji yake
kamar ya saceta ya gudu har da hadiye
yawunsa gashi ta kara kyau duk da
ramewan da tayi, wani mummunan kishi ya
gulle shi tsaki yaja ya juya ya fita amma can
cikin ransa jikinshi na bashi cewa lallai
wannan yaronsa ne, zai bar mata amma zai
sa musu ido, yasan Kaule sarai duk da bai
sameta a ‘ya mace ba yasan tsautsayi ce ta
gifta, shima don makarantan da ya sakata
ne ya sa ta amince dashi amma akan
mutuwanshi yasan Kaule kamilalliya ce.
Kwanansu uku aka sallamesu a asibiti, Maria
har ta kira oganta ta fada mishi wanda tuni
ya fara fadawa yanuwa da abokan arziki
adole ta dawo mai jego, sai mata wankan
jego ake dangin miji kaman su bauta mata
kowa na marhaban da yaro, kunsan haihuwa
baya buya, nonon Maria yaki cikowa don
haka sai Kaule ta fara shayar dashi da
mutane suka zo sai Maria take ce musu ai
Kaule yaranta biyu, kowa na mamakin
wannan abun al’ajabi amma dai suka yi
shiru tunda damuwansu a haifi yaronne
kuma an haifa, ran suna aka yiwa Baban
Mijin Maria takwara Usman, yaro yana girma
kammanin Bala na kara fitowa, amma
haskensa da idonsa sak Kaule,ana haka mijin
Maria ya dawo murna agunsa kaman me,
yana ganin yaro yace “anya yaronki ne?”
gabanta na fadi ta zaro ido sannan tace
“kaman me fa bangane ba?” yayi dariya
sannan yace “yaronnan bai da kirki sai ya
dauko kammanin Kaule anya ba danta ba?”
kayan cikinta tuni suka kada, idonta yayi
jajur ta tsorata sosai.
mar
(Based on a True Life Story)
Nwa
Dedicated to Aisha nd Sakeena Dansabo
www.Benaxiromar.com
Dariya yayi sannan yace “meye na tsorata?
kama suke yi sosai, i guess kinji jiki gurin
haihuwa Allah ya raya yaushe za kije paris
din? kin san banda lokaci sosai zaki iya
zuwa ke kadai?”
” a’a zanje da Kaule kaga tamin kokari,
abunda tamin ba wanda zai iya min”
” gaskiya ta katse hidimominta ta zauna
dake tayi kokari sosai donhaka zan biya
muku ku tafi tare, sai taje tayi epassport
afara shiryawa ko? tunda ke kina dashi”
rungumoshi tayi don taji dadi sosai, “rufe
idonki” ya fada mata hakan yasa ta rufe
idonta, tana ji ya makala mata awuya
sannan yace “bude” tana budewa tayi
mamaki sosai domin kuwa sarkan diamond
ce awuyanta
“yeeeeeeeeeehhhh hubbby!” ta rungumeshi
tana murna, daya daga cikin dalilan da take
kara sonshi kenan, akwai shi akwai kyauta
da iya farantawa mace rai, matsalanshi daya
baya zama agida amma duk lokacin da ya
dawo gida yakan yi kokarinsa ganin ya
faranta mata rai fiye da duk wata mace
atunaninta.
Tuni suka fara shirye shiryensu, yaron na
wata takwas aka yayeshi sannan suka kama
hanya, satinsu biyu a paris daga nan suka
wuce umrah a dawowa suka tsaya dubai ba
shakka sun bude ido, Maria tayi hakan duk a
matsayin godiya wa Kaule akan kyautar da
ta mata, dawowansu gida suka cigaba da
zama tare sun shaku sosai.
************
Usman yakai na shiga makaranta don haka
Kaule da kanta ta nemo makarantan da zata
sakashi a matsayinta na Aminiyar
Mahaifiyarshi a tunanin mutane, Bala kuma
kusan kullum yana hanyan siya wa yaro
kayan kwalama, haka kawai yake son yaron
sun saba sosai dashi, bata hanashi ba
sannan kuma bata bashi fuskan da zai kara
cewa danshi bane, an saka shi a makaranta
mai tsada duk da cewa ya shaku da Kaule
fiye da Maria tabbas uwa ba wasa bace,
sannan ikon Allah ma ba wasa bane, hakan
ya kawo surutu gun mutane yan’uwan da
suke zuwa gidan sun fara surutun zaman da
Kaule take agidan jin haka cikin mutunci ta
tattare ya nata sai Abuja, birnin bariki, a
mararaba aka sauketa ta kalli gabas da
yamma kudu da arewa, duk da bata da gurin
zuwa tasan tabbas zata samu gurin zama,
ta kalli jikinta rigan atamfa da zani ne dole
ne ta nemi inda zata canja kaya, cikin
kasuwan ta shiga tana dube dube har taga
bandaki ta nemi shago ta ajiye akwatinta ta
ciro kayan da zata sanya sannan ta shiga
ciki, doguwar riga ce ya fitar da shape dinta,
ta saka sannan ta cire dankwalinta ya
kumbushi kanta, ta ciro wayanta mai tsada
sannan ta janyo akwatin nata ta nemi taxi
drop tace “Maitama” ya mata bayanin
kudinta ta bude baki “malam maitama hour
nawa ne zuwa can?” yayi murmushi “madam
na minutes drive ooo mek we na dey go”
mamaki ya isheta ko daga illorin zuwa abuja
bata kashe kudin da yake gaya mata tabiya
ba ” na so it be o, and madam na drop you
say, kokoma enta mek we go” ta ja numfashi
sannan ta shiga yayinda yasa akwatin a
motan suka tafi duk da ita kanta jin kanta
take motan corolla ce kuma yake taxi da ita
abun mamaki, suna isa ita kanta tasan sunje
Maitama, gidaje ne manya manya na
alfarma ‘lalle akwai kudi a habuja’ ta fada
aranta duk da bata san inda zata sauka ba,
mutumin yace ” wey for maitama?” ta kalli
inda take sannan tace “here” yaja yayi
parking ita kuma ta ciro akwatinta ta mika
mishi kudinshi har zai tafi tace ” where is
this place please?” kallonta yayi cikin
mamaki sannan yace “Ministers hill nah, u
neva no wey u dey go?” bai kulata ba ya
shiga motansa ya tafi, gyra kayanta tayi
tana tafiya cikin takun isa da kasaita tana
jan akwatinta, ta sanya wayanta a kunnenta
kamar mai waya duk wanda ya ganta
alokacin idan yacire abun hawan da bata
dashi yasan ba karamin kifi bace.
Tayi tafiya yakai na minti goma kafin taji
horn abayanta, bata juya ba taci gaba da
karyan wayanta, hakan yasa yasha gabanta
sannan ya fito, gabanta yayi mummunan
fadi ‘wayyoni Allah yayi halittan kyau anan’
ta fada a zuciyarta yayinda a zahiri ta juya
kai tare da cewa “beb ki dauka min jakan na
120k, sai ki tura min account numbern
matan zan tura mata kudinta yanzunnan” sai
ta kashe sannan ta kallesa alokacin ya
nannade hannunsa yana kallonta, dogo ne
bugun farko tasan shuwa ne , manyan yaran
maiduguri,
“Naga kina tafiya ne nace barin rage miki
hanya”
“ah no kar ka damu, ina neman hotel ne
nearby, dake nazo wani conference”
“karki damu muje na kama miki”.
Duk da tayi farinciki sosai a zahiri ta gwada
masa ya bari yayinda shikuma ya dage
akarshe ya karbi akwatinta ya saka a bayan
aura dinsa,motan ta kasheta , tana shiga
wani sanyi da kamshi ya bugi hancinta taji
dadi sosai ko ba komi ta yanki sa’a daga
shigowanta,
“akwai hotel din da na saba zuwa a central
area haka, hankalina yafi kwanciya dasu in
kaiki can ko kuma akwai wanda kika fi so?”
“a’a muje kawai”.
Haka ya kaisu har Reiz continental ya mata
booking ya biya ya karbi access card din
sannan suka wuce, hotel din na da kyau
sosai, tana shiga ya ajiye akwatinta sannan
yace “barinje na dawo kafinnan kin huta” ta
gyada kai ta shiga toilet shi kuma ya fice,
wanka tayi ta sanya riga da wando wanda
ya matseta ta tattaro gashinta sannan ta
zauna jiransa, sunyi waya da Maria take ce
mata ta sami wani yanzu komi zai yi sauki,
bata idda magananta ba ya shigo da ledoji a
hannunsa, ta karba zata ajiye ledan ya
kubuce zai fadi riko ta yayi da sauri suka
hada ido tana jikinsa, basu san lokacin da
suka afka wa juna ba, hannunsa ya sanya
ya kashe wuta.
URA A RUMBU.
na
Benaxir Omar
(Based on a True Life Story)
Nwa
Dedicated to Aisha nd Sakeena Dansabo
www.Benaxiromar.com
Sun aikata abunda suke ganin ya fi musu,
don kuwa Kaule ta kure masa tunani taso fin
karfinshi, gefe daya ya juya ya kwanta yana
jan numfashi ta tashi ta shiga bandaki ta
kimtsa tana fitowa ta samu baya nan , zama
tayi agefen gadon tana gyra ribbon din
gashinta don atunaninta yadan fitane, ganin
takarda tayi da envelope, ta bude takardan
tana kokarin karantawa
” it was nyc having fun with you” murmushi
tayi ta bude envelope din bandir din dubu
daya guda uku abin ya bata mamaki sai dai
ba abun mamaki bane, ta fito masa a
babban yarinya, bariki sai da kudi ake
samun kudi, mikewa tayi ta fita cin abinci
bayan ta bude ledojin da ya kawo dazun
sabulun wanka ne su soso, chocolates,
turare da dai sauran tarkacen mata, bayan
ta gama cin abinci ne ta nemi drop yakaita
yawo, ce mishi tayi ya zaga da ita gari
kawai suna kan tafiya motar ta buge wata
motar mata da take tuki tana waya, drivern
ya fita ya nata mita matan ta fito daga
range rovernta ta bashi hakuri wanda hakan
ya burge Kaule, dubi mata da saukin kai,
gaisawa suka yi da matan tace “wallahi kin
burgeni sosai” matan tayi dariya ” kema
haka, kamar ba yar gari ba ko?”
“ae” ta fada tana sosa keya, don ta lura
yadda hajiyan ke kallon suturanta
“ina zakije?” ta tambayeta
“wallahi nima ban sani ba, kawai cewa nayi
yayi yawo da ni” fitar da jakanta tayi ta ciro
kudi ta bashi sannan tace ta shiga mota su
tafi, duk da hankalinta akwance yake da
matan amma ta dan tsorata kadan har gida
ta kaisu, gidanta na Asokoro babban gida
daga gani kuma gidan dan siyasa, masu aiki
sai kai da kawowa suke suna gaida hajiyar
yayinda ta haura da ita sama, taje daki ta
rage kayan jikinta sannan ta dawo ta zauna
“kina kama da kamilallun mata, sai dai
shiganki ya fita daban da haka, idan akwai
damuwan da kike dashi ki fada, wannan
shigan ba naki bane,” ta kara kallon jikinta
sai taji kunya rigan ya matseta sosai ga
cibin ta awaje, wandon jeans dinma ya
matse iya dunduniya ga huji kala kala
kaman yadda wandunan yanzu suke zuwa
da yayi,
“bakomi Allah hajiya”
“shikenan” ta mika mata wasu kaya ” jeki
sanya wannan” ta karba aka kaita wani daki,
daga gani dakin budurwa ne ta saka
atamfar, super ce doguwar riga bubu don
haka ya shigeta sannan ta dawo falon ta
zauna, an bata abinci taci ta koshi tayi
sallah wanda ita kanta ta manta yaushe
rabonta da tayi sallah, ganin yadda rayuwar
Hajiyar ke tafiya ya bata sha’awa ga kudi,
ga komi ga kuma addini, hakan yasa data
idar da sallahn taje gefenta tace ” zan baki
tarihina, inaso ki taimaka min kuma ki nema
min mafita” tun daga farko ta bada labarin
har karshe, Hajiya Atika ta tsorata sosai don
wannan labari abun dubawa ne abun alajabi
ne,
“ki zauna anan gidan, yanzu kije ki tattaro
kayanki daga hotel din can, kizo nan ki
zauna zanyi tunani akan matsalarki” cikin
ikon Allah ta bada driver yakaita central area
ta kwaso kayanta daga Reiz sannan suka
dawo Asokoro, wannan dakin aka kaita
sannan Hajiyan tace tayi amfani da duk
abunda ta gani take so acikin gun.
*******
Satinta daya cif tana samun kulawa daga
gun Hajiya Atika har take jin ina ma itace
mahaifiyarta da duk bata sha wannan
wahalan ba, sun saba sosai su kan yi hira
ahankali ta fahimci ashe Hajiyan na da Yara
hudu dukka suna kasar waje suna karatu,
hakan yasa take nan daga ita sai
ma’aikata,da rana tana zaune Hajiya Atika
ta shigo falon sannan tace ” munyi bakuwa
ki fito kiga wacecece” fitanta cikin farin cikin
da ta samu acikin gidan ta hango fuskar
innarta, gaba daya taga garin ya mata duhu,
komi nata ya toshe,sallati tayi sannan ta
dafe bango domin idan akwai abunda take
tsoro yanzu shine taga Inna, zama tayi ta
gaisheta ba yabo ba fallasa, Inna kuwa sai
kalle kalle take taga gida na yan gayu, ‘Ashe
Kaule kam dadi take sha muna can muna
shan wahala’ ta fada aranta.
Hajiya Atika ta shigo suka gaisa sannan tace
” nagode kwarai da kika amshi gayyata ta
kika zo, ina zaune ne da yarki naga ya dace
na sanar dake abunda ake ciki, duk da ta
fada mun damuwanta da kuma tarihinta
inaso ne ayau ta koma gida gurinki” Inna
tayi yake ba tace komi ba sannan Hajiyan ta
cigaba da cewa ” meye daya damuwanki?”
“Kudi hajiya” ta fada kanta akasa, wanda
Kaule taji kaman an caka mata wuka don
bakin ciki,
“zan baki kudi amma da sharadin Kaulat
zata zauna agida, kuma ba zaki kara bari ta
fita ko kice ta nemo miki kudi ba, zan na
baki kudi wata wata na miki wannan
alkawarin, kinada yarinya mace tarbiyanta na
hannunki ko kina so Allah ya kamaki da laifi
ne? hakkin yaranki suna kanki haka zalika
duk abunda ya samesu”.
Godiya sosai Inna tayi ko ince ta kwana
tana yi, washegari aka hada su da driver ya
mayar dasu illorin, cike da goma na arziki.
e Life Story)
Nwa
Dedicated to Aisha nd Sakeena Dansabo
www.Benaxiromar.com
*********
Tana zaune a daki tayi tagumi, tunaninta
duk yana kan danta gun Maria, duk da cewa
tana da tabbacin cewa Maria zata gwada
masa SO fiye da yadda ita zata masa, haka
zalika gatan da zata masa, duk takaicin
gidansu ya dameta gida ya zama kaman
gidan bariki, hatta omo mutum shi zai cire
kudinsa yasiya kayansa, haka abun karyawa,
abincin rana da dare ne kawai mutum keda
guarantee samu, tayi nadama ma meyasa
take turawa mahaifiyarta kudi domin ta rasa
me Inna takeyi da kudin, fanninta babu
kimtsi haka zalika ba kashewa kannenta take
ba, ba sutura take sawa ba Kai!! Allah wadai
da irin wannan rayuwa, duk jinta take
atakure ba gurin zuwa haka dai take lallaba
zaman, mahaifinta kam da zamanta da
rashinsa duk ya dauka daya agunsa, ko da
ta dawo da taje ta masa gaisuwa bai amsa
ba harta fita, haka dai kullum zata je ta
gaisheshi amma bazai amsa ba,shi adole
fushi yake da ita. Bai dameta ba balle ta
nemi gafara wanda zai sanyaya ranshi
agareta.
Ta manta cewa duk kankantar fushin Mahaifi
akan yaronsa ubangiji yana tuhuman yaro,
sannan babban hanyan hallaka shine fushin
iyaye, Annabi muhammad SAW da kansa
yace Mafi alherin cikinku, Mafi rabo cikunku
shine wanda ya so Allah da manzonsa,
sannan yayi biyayya ga iyayensa,sannan ya
fadi alheri ko yayi shiru, sannan akwai ayoyi
da dama da suka zo mana da muhimmancin
biyayya wa iyaye wanda duk wanda zai
bauta wa Allah yayi biyayya ga manzo abu
na gaba shine biyayya wa iyaye, akwai
suratul ankaboot aya ta 8, akwai suratul
Nisai aya ta 36, suratul israae aya ta 23,24,
duk wadannan kadan daga cikin yadda suka
fito a qur’ani ne ashe kuwa biyayya wa
iyaye na da falala sannan hatsari ne saba
musu.
Mikewa tayi ta shiga daki ta dauko wallet
dinta ta kirga sauran kudin ciki dubu uku,
dubu uku in har ta kuskura kudinnan ya kare
sunanta Sorry don haka dole ta tashi ta
nemi kudi, dari biyar ta cire aciki ta kira
kanninta “siyomin masa da miya agurin baba
tilo” ya karbi kudin yaje kicin ya dauko
kwanan sannan yafita, duk kallonsa take
haka kawai take tausayinsa duk cikin yaran
gidansu ya fita daban, domin kuwa zata iya
cewa daga mahaifinta yayi kan iyaye mata
har yara wanda akalla sun kai goma sha
shida babu mai rikon addininsa da ilmin
addini irinsa, da zata samu kudi mai yawa
zata kaisa ko madina ne yaje yayi jami’arsa
tana so ya zama babban malami domin
ayanzu ma ba wanda zai zauna dashi kuma
ya tashi bai karu dashi ba,tunani dai kala
kala har ya dawo ya mika mata kwanon
sannan ya nemi guri ya zauna yana karanta
wani littafi ta karanta bayan “cure of all
worries” cin masan tayi sai dai tana koshi ta
ture kwanan da kafa ya kalleta sannan yace
“Adda babu kyau abunda kika yi?”
“me kuma nayi malam dalhatu?”
“da farko ji yadda kika goge hannunki da
tissue bayan Ibn Abbas, yardan Allah ya
tabbata agareshi yace Manzon Allah SAW
yace ‘Idan dayanku ya gama cin abinci kar
ya goge yatsunsa har sai ya lashe da kansa
ko yabawa wani ya lashe masa’ hadisi ce
ingantancce Bukhari da muslim suka rawaito
shi zaki iya dubawa a riyadul salihin babi ta
109”
“toh naji zan gyra”
“na biyu duk da ke kadai kike cin abincin ta
tsakiya fa kika cakular abincin, shima babu
kyau manzon Allah SAW yace ‘albarka tana
sauka akan tsakiyan abinci don haka kuci
daga gefen kwanukan ku kar kuci daga
tsakiya’Tirmidhi da Abu dawuud ne suka
ruwaito shi”
“naji zan gyra, ba sai ka fadi dayan ba
nasani na ture abinci da kafana shima babu
kyau” murmushi yayi sannan yace “yauwa
Adda ki daina” taji dadi sosai yawo da irinsu
zata canja rayuwan mutum, wanka ta tashi
tayi don yau kam neman kudi tasa aranta,
tana gama kimtsawa ta nemi taxi ya kaita
jamiar Al HIKMA, daga bakin gate ta tsaya
ta ciro wayanta don kiran kawarta Naja tazo
ta shiga da ita, sai taji wayan ba kudi,wani
ne yake tsaye shima a bakin gate din sai dai
ajikin mota yake alamun shima zai shigane,
taje gefensa sannan tace ” malam don Allah
aron wayanka zaka bani nayi waya” ta fadi
hakan don ganin yana kama da hausawa
“lol, ni ne malam? toh malama barin baki”
ya mika mata ta saka lambar Najan sannan
ta kira anan ta mata bayanin inda take
sannan ta kashe ta mika masa, hannunta ya
riko arazane ta kalleshi sannan yace ” shiga
muyi magana” fizge hannunta tayi ” na maka
kama da wacce zaka fadawa doka ta bi cikin
sauki?”
“yi hakuri sauke ki nake son yi”
“kaje zata zo ta dauken”
bai ce komi ba ya shiga ya wuce, Naja za
tazo yau ne ko gobe shiru, ta kai awa abakin
gate tana jira gashi ba kudi awayantan, can
sai gashi ya fito Najan ce agefensa suka
tsaya agabanta alokacin ta kulu kaman zata
mutu ta bude bayan motan ta shiga,
“kawata yi hakuri don Allah nasan kinyi
fushi, ga abokina Shun ku gaisa” wani kallo
da ya juyo ya mata sai da ya tayar mata da
hankali, gaban hostel suka koma inda Naja
karfi da yaji ta hada Kaule da Shun acewarta
ba Dalibi bane daga abuja ma yazo, kuma
yace yana son Kaulen,ita dai taki kulashi
amma sai shige mata yake, tare suka fito
akan zai sauketa agida
“kiyi hakuri in nine na bata miki rai am sorry
babyna” aranta dariya ya bata wato har ta
zama baby,
“kiyi dariya mana kinga jibi zan tafi abuja
kar na tafi kina fushi dani”
“nace maka ba komi ya wuce” hannunta ya
riko bata kwace ba wannan karon haka
yayita murza hannun har suka isa gida, ya
ciro bandir din dari biyar ya bata “kiyi hakuri
kinji kafin na dawo” ta karba tare da cewa
“nagode” ya dauki lambar wayanta sannan
ya tafi, tana shiga gidan wayan Naja ya
shigo “kawata ya Shun kun shirya ko?”
“ae meya faru”
“toh dama zan sanar dake ne, in kudi ne
zaki ci kawata, duk da shi bamusan aikin da
yake ba amma yana da matsifaffen kudi ni
dai damuwana kar kice zaki so shi domin
zaki wahala, kici kudi ki ware, kuma kar ki
yadda wani abu ya shiga tsakaninku”
“bakomi nagode” tana kashewa taja tsaki ‘ji
wannan matan an gaya mata ni zata yiwa
wayo? ina ganin yaro ga kyau ga kudi
meyasa ba zan so shi ba, tsabar keta irinta
mata’.

Benaxir Omar
(Based on a True Life Story)
Nwa
Dedicated to Aisha nd Sakeena Dansabo
www.Benaxiromar.com
*********
Kaule ta fada tarkon SO da Kaunar Shun
haka zalika shima ya na sonta domin kuwa
tunda ya tafi hankalinsa yana kan Kaule,
wacce kullum suke waya ta nannade adaki
tana bin kudin da yabata daya bayan daya,
randa zai dawo illorin ya kirata, abun
mamaki Kaule ce har da girke-girke don
tarban Shun wanda yan gidansu kowa
mamaki yake, yana tahowa ya gaida Inna
itama ya zuba mata ‘ya’yan banki kafin ya
tafi tuni ya siya zuciyan yan gidansu Kaule
kowa na marhaban dashi, tare suke wuni
don kuwa Sallah ke rabasu shima don lokaci
nayi Shun zai mike ya wuce masallaci, duk
wani mummunan abu da Naja tace mata
game dashi duk ta karyata domin taga ba
haka bane, Kaule ta koma ga Allah, ibada
kan ibada ga suturce jiki kullum tana gefen
kaninta domin karin ilmin addini, ta gama
fayyace wa ranta cewa Shun zata aura kuma
dashi zata zauna, iyakacinsa taba hannunta
baya wuce nan, shima sai adade kafin ya
mika hannu hakan da yakeyi ba karamin
shiga ranta yayi ba,
“nazo miki sallama zan koma abuja amma
gaskiya zan dan kai wata daya ban zo ba,
kiyi hakuri ki jirani ko babyna” ta kalleshi
narai da ido randa yazo mata da batun zai yi
tafiya
“bakomi Allah ya kaimu, amma dama zanje
abuja gidan kawata idan nazo zan nemeka
sai kazo mu gaisa” murmushi yayi wanda ita
kanta sai da taji dadi haka dai suka yi
sallama ya tafi.
Wata daya shiru babu Shun babu labarinsa
sai dai waya wataran ma sai yaga dama
yake daukan wayan ba shiri ta hada kayanta
tace itakama zata tafi abuja gidan kawarta
azahiri kuwa gurin Shun take son zuwa,
isanta abuja ta kama daki a Reiz domin taji
dadin yadda suke karbeta zuwanta kwanaki
sannan takira Shun cikin ikon Allah sai gashi
yazo, ya dauketa yace ta rakashi gidanshi ya
dauko sako, tafiya suke yi har suka isa wani
guri daga tambarin taga an saka TAFA local
government ne na niger state, amma
hakarkarinta tana garin abuja, bata damu ba
ita dai tayi murna sosai kamar ta
rungumeshi ya kalleta amma babu alaman
sakewa a tattare dashi,
“baby akwai matsala ne? ko bakada lafiya
ne?”
“kiyi hakuri, banda zabi ne akanki, amma ina
sonki kuma zanci gaba da sonki” yana fadan
haka ya bude kofan motan, itama ta bude
nata suka fito suna tsaye wani baki, dogooo
kallon halittarshi kadai zai iya sanya dan
Adam jimamin makomar rayuwarsa ya iso
gaban Shun tare da mika masa check yana
dariyan keta
“kiyi hakuri fa, wannan saurayi naki no get
power na so i come c your picshure for him
phone, i come tell am say i wan sleep with
you i go give am 2million , you see yourself
now you are here” ya kwashe da dariyan
mugunta, hawaye suka ciko idonta ta goge
sannan tace “Shun dama ba sona kake ba?”
“ina sonki wallahi, amma Kaule mahaifiyata
tana asibiti, i need money” ya fada cike da
damuwa a fuskansa, ta gyada kanta cikin
tsananin bakin ciki takaici fal aranta hade da
nadama
“Shun i hate youuu, i so much hate you that
i feel like to squeeze your bones like an
orange” kamota mutanen sukayi Shun ya
shiga motarsa da cheque dinsa yayinda aka
mikata Dandalin Karuwan Tafa, shiganta
gurin ma sai data raina kanta, mashaya, yan
caca, karuwai babu kalan mutanen da babu
acikin gurin, wani daki ya wurgata tana
kokarin faucewa da ya wanka mata wani
mari walkiya ta fara gani a fuskanta, jiri ya
kwasheta ta koma sannan ya riko wuyanta
“fool, get hold of yourself this is just the
begining.”
URA A RUMBU.
na
Benaxir Omar
(Based on a True Life Story)
Nwa
Dedicated to Aisha nd Sakeena Dansabo
www.Benaxiromar.com
*********
Yawun bakinta ta tofa masa cikin takaici, ya
damko gashin kanta wanda dankwalin ya
dade da fadi kasa tsantsan wahalan da take
sha, murda kanta yayi ta saka wani kara “in
kin bukaci mu zauna lafiya shikenan, in
kuma kika ce mugunta kike so na miki shima
zan miki” ya dauki hannunsa ya wanka mata
mari don aganinshi raini ne mace ta tofa
masa yawu yabarta, tsantsan zafin marin
gigicewa tayi ta koma ta buge da kasa,
karfen bayanta da ya coketa tsantsar azaba
suma tayi. A take ya gigice “call the doctor!”
yana dagota yana jijigata shi dai yasan yana
sonta amma yana da mummunan zuciya ba
yason raini duk son da yake miki zai iya
kaiki ga hallaka idan baki yi masa biyayya
ba.
likita yazo ya duddubata ya kuma tabbatar
da suma tayi sannan yayi dabarunsu ta
likitoci dama sun gama kwara mata ruwa
kafin ya iso nan dai ta tashi tana jan
numfashi, tankado kanta yayi ya rungumeta
yana jan numfashi likitan yasa suka kaita
daki.Dakin babba ne yaji duk wani kaya
daya dace asa a dakin mace, hatta suturan
sawa, ya ajiyeta akan gadon sannan ya
rufeta da bargo, zura mata ido yayi, Bai kai
wata biyu da fara sonta ba asali ma a waya
yaga hotonta lokacin Shun da ya fara zuwa
wurinta, ya tambayeshi budurwarshi ne?
Shun yace masa ae amma na shan minti
abunda zai kai shi kenan, shi ya roki Shun
kar ya tabata ya kuma bashi dukiya na gani
na fada akan ya mata dabara hakan yasa
har suka samu kan Kaule ba karamin farin
ciki yayi ba da yaji suna zuwa, amma yaji
takaicin dukanta da yayi daga zuwanta.
Idonta ta bude ahankali tana kokarin juyi
tsantsan dadin gadon kawai suka hado, a
razane ta farka domin halittansa razana ta
yake, hannunta ya koma tsoron cire hannun
ya kamata kar takara shan mari, murmushi
yayi ya rungumota jikinsa kamshin turarensa
ya bugi hancinta ta ja wani numfashi sannan
ta lumshe ido,
“na miki alkawari zan wadata ki da komi, ko
me kike so aduniyannan damuwana kawai ki
soni” da sauri ta dago idonta suna hada ido
ta mayar ta sauke da sauri domin ta rasa
gane meye a fuskarsa baki ne haka yake ko
kuma shafawa yayi, duk da idonshi fari ne
bai hana ta ji tsoronshi ba jikinta na kyarma
bakinta na rawa ta gyada kai alamun toh,
murmushi yayi sannan ya mike ya bar dakin,
abinci aka kawo mata sai dai yadda take
ganin abincin ko shaawa bai bata ba haka ta
zauna agefe tana tunanin rayuwarta yadda
yake bugawa kamar kwallo yau tana nan
gobe tana can, shin laifinta ne ko na
iyayenta? idan ta tuna yadda rayuwanta ta
fara sai taga tabbas iyayenta suna da laifi
Chapter 2 · 0% Book details