← Book details Abin Tsoro Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 3

Gabatarwa

Abin Tsoro Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 14 min read

UMBU.
na
Benaxir Omar
(Based on a True Life Story)
Dedicated to Aisha nd Sakeena Dansabo
Benaxiratuuuuuu******
Hankalina yana kan sakonni na whatsapp da
suke shigomin alokacin da naga Aisha tamin
magana
“Adda ya gida da makaranta?”
“lafiya kalao Alhamdulilah mun gode Allah
yakike?” na amsa mata.
“Nazo da wani labarin Al’ajabi ne wanda
nake so ki rubuta min duniya su gani kuma
su amfana dashi tunda naga kina karban
labari irin haka ki kuma rubuta da fatan ban
takura ki ba”
“ko kadan Aisha, amma ina jarabawa don
haka ina kammalawa zan neme ki sai ki isar
mini da wannan sako da kike son isarwa,
insha Allahu ni kuma zan rubuta kowa ya
karanta ya kuma amfana”
“bakomi Allah ya kaimu ina jira”.
Kamar yadda muka yi da ita na kuma yi
mata alkawari, yau ina kammala jarabawa ta
na yiwa Aisha magana domin ta fada mini
labarin da take son kowa yaji, labarin da
yake cike da Abun Al’ajabi, takaici, haushi da
kuma darussa aciki wanda zai saka duk mai
karatu sanin cewa duniyan ma ba wata abun
daga hankali bace, tabbas Duniya makaranta
ce.
Wannan labari ba daga bakin mutum daya
yake ba, sai da aka hado kan dukkan wani
wanda yakeda hannu acikin rayuwar baiwar
Allah muka gamsu sannan nake rubutawa,
Ubangiji Allah ya sa nafaraa sa’a na kuma
gama a sa’a, kuskurenmu Allah ya
gafarcemu, Allah ya shiryi duk iyaye irin na
Kaulat, masu rayuwa irin Kaulat.watakila mai
karatu zai ga abunda bai gamshe sa ba, ku
sani cewa KALMA DAYA ban kara acikin
labarin ba, ya faru ne dagaske. kuma wacce
zanbada labarinnan akanta ta rasu, Ubangiji
Allah ya jikanta, ya mata rahama ya kuma
kai haske kabarinta, sannan burin
marigayiyar ce a rubuta wannan labarin a
fadakar wa duniya da kuma dukkan iyaye.
Bismillahi Rahmani Rahim
Sunanta Kaulat Adams, wacce aka fi sani da
kaule,Haifaffiyar garin illorin, Mahaifinta
Alhaji Adams ya kasance mai arziki sosai sai
dai babu wadatan zuci ma’ana baya
taimakawa iyalinsa, irin masu kudin da zaka
ga arziki a tattare dasu ga gida ga mota
amma iyali a tsiyace, kowacce matarsa ita
take yiwa kanta da kuma yaranta hidima.
Mahaifiyarta yar garin niger ce, sannan
Kaulee ce yar farinta sannan shi Alhaji
Adams shi ya musuluntar da ita ya kuma
aureta .
Kaulee ta girma agun iyayenta har Allah
yasa ta shiga FGC billiri dake garin gombe,
tayi junior class dinta har ta kammala
sannan ta shigo ss1 inda aka kawo wata
malama mai suna Hajiya fadila, Hajiya Fadila
ta zamo tamkar mataimakiya ko ince uwa
agun kaule, wacce take da ilmi ga kuma iya
zama da mutum, sabawansu takai ta kawo
har kwana kaule tana yi agidan Hajiya Fadila
anan staff quarters,ta zamo yar gida, sun
saba sosai da mijinta tana mishi kallon
mahaifi yayinda shikuwa ba haka yake mata
kallo ba. Kusan rabin kayanta agidan ta
ajiye shi tamkar ba yar makarantan kwana
ba, kasancewar kuma ana tsoron Hajiya
Fadila yasa aka gagara tayar da maganan
balle ta dawo hostel.
Kaulee kamar yadda nace yar illorin duk
wanda yasan yan illorin yasan akwai fulanin
cikinsu, baka ce amma doguwa siririya tana
da matukar kirar kalangu tamkar cikakkiyar
bafulatana, macece mai fara’a son mutane,
da kuma girmama na gaba da ita, ga kokarin
addini iya gwargwado, tana da farin jinin
maza domin kuwa kowa harinta yake a
kankancin shekarunta, sai dai hidimar
gabanta kadai takeyi bata damuwa da kowa
balle soyayya ya shiga ranta ko abun da ya
shafi haka.
Ranar da bakin cikin rayuwanta ya auku
kuma ya fara dinkin saka shine randa Mijin
Hajiya fadila ya dawo gida alokacin bata nan
sunje wani excursion da dalibai, Kaulee ce
kadai acikin gidan sanye da dogon riganta
tana gyran daki, wanda aiki ya zamo
dabi’anta bata iya zama shiru ba sai ta
nemo abun yi, lekowa yayi sannan yace
“Fadila fa?”
“ina wuni uncle? sun tafi excursion” ta amsa
Bai amsa gaisuwan ba ya juya, wanka yaje
yayi sannan yasa jallabiya ya fito, tana
zaune a falo tana kokarin goge kasan DVD
da yayi kura tana mamaki domin jiya da safe
ta goge shi, ji tayi ya taba bayanta yana jan
gashinta, a razane ta juya don ganin mai
mata wannan barna, mamaki kaman ya
cinyeta
“un-uncle!”
“shhhhh” yasa hannu a bakinsa yana mata
nuni da tayi shiru sannan ya fuzgeta ya jata
sai dakinsu, akan gadon matarsa ya ketawa
Kaulee hakkinta, ya yaga mata rigan budurci
cikin izza da mulki irinta mugayen maza.
ar
(Based on a True Life Story)
Dedicated to Aisha nd Sakeena Dansabo
Kuka tayi sosai, tana tunanin makomar
rayuwanta domin tabbas tasan cewa Hajiya
Fadila ba zata barta ta zauna mata a gida
bayan cin amananta da tayi ba.
“ina so kiyi shiru, kar ki gwada mata wani
abu ya same ki sannan hakanne zai sa na
rufa miki asiri, domin zan iya ce mata ke
kika janyo komi kuma kinsan zata yarda har
gidanku za taje ta tozartaki” ya fada mata
alokacin da yake kokarin saka wando. Kuka
tayi sosai ta tattara dakin da bedsheet din ta
kintsa gadon sannan taje bandaki ta kimtsa
jikinta duk ya ji mata ciwo yayi mata rauni,
Hajiya Fadila bata dawo ba sai wuraren karfe
goma don haka bata fahimci halin da gidan
nata yake ciki ba washegari da sassafe ta
kara fita, wannan ya kara bashi daman
dawowa alokacin ta shirya cikin uniform
zata shiga makaranta, har ta isa bakin kofa
taji an rike hannunta jikinta na bari ta fizge
muryanta na rawa tana cewa “uncle kayi
hakuri, un-uncle!” rufe bakinta yayi ya nufi
daki da ita ya fama mata ciwon da yaji
mata, uniform dinta duk ya baci tana kuka
ta koma daki ta canja sannan ta fito, idonta
duk a kumbure gashi ta shiga makaranta aka
mata dukkan latti dama daliban suna jin
haushinta yadda take fita da shige cikin
makarantan yadda takeso.
Hajiya Fadila bata gane halin da mijinta da
kuma Kaule suke ciki ba, wacce daga baya
ita Kaule yabi jikinta bawan Allah ya mayar
da ita injin aduk lokacin da yake bukatanta
zai nemo ta tun ba taso har ta fara zama da
kanta,ahaka ta kammala har ss3 tayi waec
da neco suka rabu tabar gidanshi, Hajiya
Fadila ba tasan wannan wainan da aka toya
agidanta ba.
Dawowanta gida bayan farin ciki da murna
daga yan’uwa kowa na farin cikin Kaulee an
gama sakandiri saura jami’a ta huta har na
watanni kadan lokacin da jarabawansu yafito
da komi ta tattari kafa ta nufi gun
mahaifinta ta gaisheshi ya amsa sannan
tace ” Batun cigaba da karatuna ne, ga
jarabawa na naci kuma na sami admission
anan B.U.K ”
“Wani karatu kuma Kaule? ai kina mace kam
yanzu sai aure, babu batun karatu, kibar
karatu wa maza yan’uwanki kuma ki jirani
zan nema miki mijin aure insha Allahu”
Ta kalleshi ta tabbatar da gaske yayi babu
wasa don ba yau tasan shi ba, mutum ne
mai taurin kai da kaffafiyar ra’ayi inya fadi
abu toh sai yayi ta rokeshi taga yana kan
bakansa don haka ta gyada kai tace “bakomi
Allah ya kaimu” . Ta sami mahaifiyarta ta
roketa itama hakuri ta bata “kibi mahaifinki
kawai ya miki auren kinji?”
“Bakomi Allah ya kawo mijin”. ta tashi ta
nufi daki.
Washegari da Sassafe ta tattara kayanta ta
koma gidan kawarta anan Illorin din, Maria,
maria na da aure sai dai mijin baya zama
kuma asalinta yar kano ce shima haka, aiki
ya kawosu illorin basa tare da kowa kuma
basu cika zuwa gida ba, mijin yakan yi wata
bakwai ko takwas bai zo gida ba irin wannan
aikin dai yasa Maria take rayuwanta ita
kadai komi ita kadai, zuwan Kaulee yasa
suka fara zama tare tace mata tayi zamanta
har sai randa ta gaji.
Kaule ta fara rayuwanta domin addini kam
anfara watsar dashi ko ince an watsar dashi,
samari kuwa sai zuwa suke daga koina, ita a
tunaninta jira take mahaifinta ya sauko daga
fushin da yayi sai ya kaita makaranta bata
cika kula mazan da suke addabanta ba sai
dai idon Kaulee ya bude.
Wata rana sun fito daga gidan Maria zasu je
kasuwa wata mota sai binsu take, tun baya
damunsu har maria ta tsaya da motan don
ya wuce su, tsayawa yayi ya fito Babban
mutum ne akalla yakai shekara 40-45 a
duniya ya kalli Kaulee yana murmushi
tamkar wanda aka bashi kyautan gonan
auduga ita kuwa kamar ta kasheshi don
bakin ciki,
” ina wuninku ina gajiya”
Maria ce ta amsa yayinda Kaule ke mika
sakon harara “lafiya malam zamu tafi ne ka
tare mana hanya” ta fada tana yatsina baki,
lafayanta yana fadi tana mayarwa tsansan
matsifa
“Kuyi hakuri, kuna tafiya ne kika ja hankali
na don Allah kiyi hakuri ki kula ni kinji?”
Maria ce ta jata gefe ” jeki ki me zai fada
miki daga gani wannan babban Alhaji ne
akwai arziki jeki diba na diba mu ware”
sannan suka dawo alokacin tace masa ” me
kake so yanzu?”
“muje motan nawa sai mu bita abaya ko? in
yaso zan yi miki bayani akan hanya” ta bishi
cikin kissa wacce zan iya cewa halittanta ce,
tana shiga taji wani kamshi ga kuma kanta
na juyawa, ta rasa meke mata dadi har wani
jiri taji can kuma ta fara murmushi
“me kakeso?” yayi dariyan muguntansa da
ya saba sannan yace “ke”
“muje” ta fada masa,
Aikuwa bin Maria da ba’ayi ba kenan aka tafi
hotel room, sai da yayi mai isansa yaji
tabbas wannan bata bari bace, macece
wacce ta amsa sunanta mace. Suna
gamawa yace mata ” me kike so kuma na
miki?”
“Makaranta nake so nayi, shine kadai burina”
“Na miki alkawari zan saki a makaranta har
sai randa kika ce kin hakura amma zaki na
bani kanki aduk lokacin da nake so, Sunana
Bala Kutur, Ko me kikeso a duniyannan zan
miki inhar ba zaki hanani kanki ba” tayi
murmushi aranta tace ‘ wani ya samu na
bati na shekara uku ba ci ba sha balle kai’
Ya mayar da ita Gidan Maria kuwa inda tayi
mata bayanin cewa zai sata a makaranta
nan ma sai daya sallemata da bandir din
dari biyar guda uku.
KURA A RUMBU.
na
Benaxir Omar
(Based on a True Life Story)
Nwa
Dedicated to Aisha nd Sakeena Dansabo
Gani take yi kakarta ta yanke saka, bata yi
bacci ba tsantsan farin ciki domin kuwa ba’a
taba mata irin wannan kyautan ba a
rayuwanta. Washegari da sassafe ta hada
kan kayanta suka nufi kano don ganin ko
za’a karbeta duk da cewa anyi post jamb, da
karfin mulki irin na Bala kutur aka mata nata
daban akayi sa’a taci don haka ta fara batun
jiran registration da sauransu, gida ya kama
mata one bedroom flat mai kyau, ba abunda
bai saka mata wanda ‘ya mace zata bukata,
sannan yaje da ita kasuwa ya siya mata
kayan sawa da atamfofi suka sami tailor ya
mata express.
********
Tana kwance a daki alokacin ya fita, ta
janyo wayanta ta kira layin Ma” kasancewar
ta gane muryanta yasa tace “ina kika shiga?
kowa na nemanki?”
“Inna na sami wanda ya sakani a makaranta,
ya biya komi yanzu har gida ya bani, ina nan
garin kano”
jin haka da sauri Inna tace “kudi fa? ya
baki? in ya baki kudi ki turo, kinga ni da
kannenki sai wahala muke sha babanku yaki
sake kudin” ba tayi mamakin kalamun inna
ba domin kuwa idan da sabo ta saba ta
kuma santa da son abun duniya don haka
sai tace “akwai, turomin account number
yanzu na turo” aikuwa tana kashewa taga
alert mikewa tayi ta fito don taje tasa kudin
sai ga Bala kutur cikin maganansa ta yan
maye da izza yace “inaaaaaaa zakijee
suga?”
“zan je bank ne”
“toh ki tsaya mana na ci kadan ko?”
kalamun sun mata nauyi haka ta koma
aranta tana cewa ‘lallai wannan yaji bariki’
sai da ya idda bukatarsa yaga bai gamsu ba
ya mike ya janyota sannan yace “kin—gane—
ne? bana gane komi, barin gwada miki
yadda zakiyi, ya ciro wani dorina yana
dukanta kukan da take yi shi kuma ita take
sanyaya masa zuciya “yauwa haka nake so”
sai da ya zaneta tana kuka yana biyan
bukatarsa sannan a kuka yana biyan
bukatarsa sannan ya barta ta tafi bank da
kudin da ya batan ta turawa mahaifiyarta ta
dawo.
Rayuwa ta ci gaba da tafiya mata haka, idan
yaga bai gamsu ba zai nemo dorinansa ya
daketa kuma ya bata kudi a wadace duk
jikinta ciwo. Wata rana da safe yafita aiki ta
ji yunkurin amai da gudu taje tayi, hankalinta
ya tashi ganin cewa tabbas ciki gareta
domin kuwa sai alokacin ta tuna tayi batan
wata
“innalilahi wainna ilaihi rajiun” sai data
zauna ta tika kukanta yadda ya isheta
sannan ta mike zata sa kaya taga waya na
kara ta duba taga Innarta ce daukan da zata
yi tace “Kaule kudi dai ya kare ki kara mana
kinji” tayi murmushin bakin ciki hawaye na
bin gefen idonta sannan tace “toh” Inna ta
kashe wayanta, kayanta ta tattara tabar
gidan sai illorin, don ta mugun tsorata da
batun ciki, gidan Maria ta nufa wacce taje ta
sameta itama cikin tashin hankali da matsifa
dangin miji sun sa ta agaba batun haihuwa,
sai waya da batun damun mijinta ya karo
aure, Kaule na jin haka tace “kirashi kice
masa kina da cikin wata uku” ta juyo ta
kalleta ” baki da hankali ne? ai na zan samu
yaro?”
” Zan baki nawa” zaro ido Maria tayi,
“ae, Bala yamin2Ba damuwa to, kin duba
wata nawa ne kike batun wata uku? muje
asibiti tukunna ko? amma anya babu
matsala? ba za’a gane ba?”
“ke meyasa kike da tsoro? mijinki baya
zama, danginsa babu mai zuwa daurewa
zakiyi har na haihu kafin ki bari ya dawo”
aikuwa Maria taji dadin wannan shawara
“tsaya nayi wanka muje mu gwada”.

(Based on a True Life Story)
Nwa
Dedicated to Aisha nd Sakeena Dansabo
Tana fitowa a wanka ta shirya tsaf, ta kira
driver sannan suka fice, sun samu sun ga
likita inda aka auna Kaule aka ga wata hudu
ne ciki kam, ahanyan dawowansu ma Maria
ta kira mijinta wanda sun tafi senegal wani
aiki
“Hubby ya kake?”
“Baby na lafiya lao ya gajiya?” ya amsa
daga gunsa
“zan maka albishir mai zaka bani?”
“me kike so?”
“Vacation to paris, sai kuma ka canja min
mota”
“anyi angama”
“inada ciki, congratulations”
Shiru yayi can yace “me kika ce?”
“inada juna Biyu”
“Oh my! Oh my God!! My baybay!! ohhh
Alhamdulilah dole na dawo, zanyi cancelling
komi gobe na dawo na ganki”
“Nooo! ka bari kayi hakuri ka gama kaji?”
“anya? bazan iyaba gaskiya kinsan sai nan
da wata shida fa zamu taho”
da sauri ta kirga sannan tace “bakomi kar ka
damu zan raine cikin har na haihu sai kazo
kaga babynka ko?”
“a’a zaki wahala ke kadai, barin kira wani
agida azo atayaki zama”
“ka manta Kaule tana nan? zamu zauna
kawai, hubby kasan danginka yadda suke
min inaso nayi surprising dinsu suji kawai na
haihu ne” har da saka kukanta kuwa, hakan
yasa yaji tausayinta sanin cewa tasha jiki
agun danginsa batun haihuwa amma tunda
yanzu akwai cikin zai barta harta haihun, da
haka dai suka yi sallama.
Maria tana tsantsan kulawa da Kaule da
cikinta, duk da cikin yazo da laulayi sosai
tana jin jiki, bata iya cin abinci sai amai da
tofar da yawu, ga tsantsan wahala da take
sha gurin bacci duk ciwon jiki, haka kawai
zata je ta tsoma kanta a shadda don taji
warin shadda wanda ita shi take so kuma
yake sanyaya mata rai take ji a matsayin
kamshi, Inna kuwa kullum acikin tambayan
kudi take Kaule ta kan tura mata amma bata
taba sanar da ita cewa tana da ciki ba,
makaranta kuwa tuni ta ajiye batun shi
agefe, babu yanda Bala baiyi ba su hadu
taki, har hakuri yake bata in yazo gidan
Maria takan ce Kaule ba tazo ba babu yadda
ya iya, gashi dai suna waya in taga dama
shi rokonta yake ta yarda ta aureshi don
ayadda ya saba da jikinta zai iya komi
akanta, ganin zai dameta yasa ta canja layi
taci gaba da rainon cikinta har watan
haihuwa.
Ranar da EDD dinta ya cika aranar ta fara
nakuda, asibiti suka nufa, tasha jiki ga
haihuwa yazo ganin dadewan da tayi tana
nakuda na kusa kwana uku yasa likitotin
suka yanke shawaran yi mata CS aka ciro
dankareren baby boy, tana farfadowa da aka
miko mata ‘Dan ta karba ta mikawa Maria
“Na baki halak malak, ki rike amana”
Maria tana murna tana goge hawaye ta
rungume ‘Dan can ta mayar dashi inda aka
kwantar dashi, tana zaune taga anbude
kofan dakin Bala ne yashigo ba karamin
tsorata tayi ba ganinsa amma ta danne tare
da hada girar sama da kasa
“nace maka Kaule bata nan meyasa kake da
naci?”
“karki damu na riga nasan tana gidanki, na
kuma san kun zo asibiti na kuma san ta
haihu sai dai nazo ne nayi magana da ita,
shin ‘Dan waye ne?”
ko kallonsa ba tayiba ya nufi dakin da aka
kwantar da Kaule, Maria ta bishi da sauri
don kar yaje ya bata musu aiki
“Kaule ‘Da nane ina?”
“ta ina ya zama Danka?” ta fada tana bata
fuska kamar ta kurbi kashi
“saboda ni na saba kwana da ke”
“wai tsaya in tambayeka? ran da ka fara
kwanciya dani budurwa ka sameni? kar ka
manta ba akanka na fara ba kuma ba akanka
zan tsaya ba haka zalika ba kai kadai nake
da ba, na kwanta da maza kala kala kashi
Chapter 1 · 0% Book details