← Book details Abdul Jalal Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 7 OF 14

PART 2

Abdul Jalal Part 2 Complete Hausa Novel · about 14 min read

_PAGE 5
Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ [email protected]
Watpad @Ayshercool7724
Happy marriage
lyf to you sister Amina, may yours be among the best.
_MY FIRST NOVEL _
Mmurmushi Jalila tayi tace
"Masha Allah naji dadi gaskiya, dama bana zuwa ko'ina daga makaranta se gida, gashi an gayyaceni biki 'yar class dinmu bansaniba ko zaka barni inje?"
Dan hade rai yayi yai mata shiru,
Tace "Kace wani abu mana"
"gaskiya bazaki ba" yaba ta amsa
A shagwabe tac
e "meyasa?"
Jalal yace
"har yanzu baki kama da me Aure ba, kawai kifita wani ya biyoki no gaskiya ki hakura"
Kara marairacewa tayi tace
"please, Allah tunda nazo gidan nan school kawai nake zuwa, dan Allah ka barni inje"
Makale kafada yayi "yace ni dai A'a"
Ya kalli cikin idonta yace
"Allah me yadda yaso, Baby da dane nace karki fita ko kallona bazakiyi ba, ko baki niyya ba sekin fita dan ki ban haushi ko?"
Shiru tayi ba tace komai ba
Jalal yace
"naji zakije, amma ni zan rakaki kiyi minti goma mu dawo, dan bazaki dade ba, kar inje wani ya kalleki koma wani ya biyoki yace yana so, tunda har yanzu baki gama amsa sunan matar Aure ba"
Dan kallonsa tayi tace
"saboda me? A gaban mutane fa aka daura min Aure"
"eh nasani mana an daura miki Aure, har kikace ba kya son mijin da'aka baki, Amma ai bakiyi daya karatun ba daze maida ke matar Aure, ina da dauriya ko Jalila? Akwai dalilina dayasa na kyaleki kike cin karenki ba babbaka, ina jiran time ne"
Yai maganar yana kashe mata ido daya, sarai Jalila ta gane meyake nufi Amma ta maze tace
"karatu kuma? Wane irin karatu ne kuma haka?"
Jalal yace
"Au baki gane karatun da nake nufi ba?"
Mikewa yayi zaune yace
"bari in fara karanta miki kozaki gane"
Ai zumbur ta mike tsaye ta fice daga dakin, Ba karamin dariya Jalal yayi ba yana son ya zolayeta a irin haka yaga yadda fuskarta ke bayyanar da tsoro"
A zaman su Jalila ta gama fuskantar waye Jalal, mutum ne me matukar son a damu da shi, kulawa take bashi ba ta musamman dan kamar karamin yaro haka yake wani lokacin, ko Abinci ta kawo masa indai bata zauna ta bashi ba, ko ta zauna yana ci suna hira ba baze ci Abincin ba, sannan cikin hikima take canza masa wasu munanan dabi'un nasa zuwa kyawawa, ta tsaya tsayin daka akan kula da ibadar sa da kuma Adduo'i, kulawar da yarasa ce a baya ta taimaka gurin kara dulmiyashi harkar shaye2, Mummy harkar kasuwancinta da son zuciya tasaka a gaba, yayinda Daddy ba mazauni bane, Jawwad kuma ga makaranta ga sauran hidimominsa dukda ya taka mahimmiyar rawa a gurin Jalal, ga kyama da al'umma suke nuna masa saboda yanayi na shaye2 da sauran dabi'unsa, shiyasa abun yayi masa yawa, babu me jansa a jiki yaji matsalolinsa kome yake damun shi, wata shakuwa ce ta musamman ke kara shiga tsakaninsu.
Bangaren Jalal ma babu Abunda ze cewa Allah se godiya, dan ya fidda ran yin kyakywar rayuwa kaman kowa, Amma ba zato ba tsammani dawowar Jalila karo na biyu a cikin Rayuwarsa tazo masa da Haske da tausayawa, a cikin rayuwar Auren nan nasu, dukda kasancewar a baya basa jituwa, Amma ta ajiye wannan a gefe tana ta iya kokarinta a kansa, tana masa biyayya dai2 iyawarta, duk wanda yasan irin rayuwar takun sakar da sukayi a baya, babu me cewa zata iyayiwa Jalal biyayya haka, musamman wanda yasan halinta a bangaren tsiwa da rashin daukar raini, tana zama tayi hira da shi, tai masa nasiha, idan abu ya dameshi ta rarrasheshi hakan ya mantar da Jalal duk wata mummunar rayuwar da yayi a baya.
Tun Yaya mairo tana sintirin zuwa gidansu Jalal akan maganar sa'adah harta gaji ta hakura saboda korar wulakancin da Mummy tayi mata a cewarta
"ta gaji da zaryar da take mata a gida suje can su daidaita"
Ba yadda ta iya haka ta tafi gidan Maama kozata sa baki a sakar mata sa'adah, dan yanzu ko zuwa tayi police station ba'a bari ta ganta, ta kwashe duk yadda akayi ta fadawa Maama,
Maama tace
"to ni Yaya mairo ya kike so inyi?"
Yaya mairo tace
"Dan Allah zainab kisa baki, yarinyar nan Jalila ta gaya masa yasa a sakarmin 'ya ta dan Allah"
Maama tace
"Yaya mairo idan mukayi haka ai bamu da kunya kenan, ko kin manta irin cin zarafin da kikasa muka hadu muka dingayi mata? Se yanzu zamu nemi Alfarma a gurinta?"
Yaya mairo tace
"Dan Allah zainab ni dai ki roketa a sakarmin sa'adah, wallahi yaron
nan da yake ba dan mutunci bane, mahaifiyarsa tana rokonsa a sakarmin sa'adah se cewa yayi, se nayi hawaye fiye da wanda matarsa tayi"
Maama tace
"gaskiya Yaya bazan iya tunkarar Jalila da wannan maganar ba"
Abba ne ya shigo gidan ya tarar da yaya mairo a parlour suna hira, Yaya mairo na gaisheshi be amsa ba yace
"zainab ban gaya miki bana bukatar sake ganin yayarki a gidana ba? Ban hanaku zumunci ba, amma ku hadu a wani gurin, dan bazata dinga zuwa tana rarrabamin kan iyalai ba"
Abba ya dubi Yaya mairo yace
"dan Allah karki kara zuwarmin gida, in bahaka ba zan dau mummunana mataki akanki, ki tashi ki tafi"
Yaya mairo tace "zainab kina kallo mijinki na cimin mutunci?"
Maama tace
"ba cimiki mutunci yake ba, maganar gaskiya ne ai, tunda yace ki bar masa gida kawai ki tafi"
Haka Yaya mairo ta fito tana rusa kuka, ta koma gida ta rasa abunda yake mata dadi, ga Naja ma kwanan ta uku bata gida, ta kirata a waya tace mata
"karta kara kiranta tana cikin koshin lafiya"
Sa'adah kam da taji uwar bari tuni ta fadi inda za'a samu Hannah, akayi nasara kuwa 'yan sanda sukaje itama suka kamota amma ba' a saki sa'adah ba ma.
Jalila ta gama shirinta tsaf na zuwa gurin biki, ta dakko Jakarta ta fito, tana fitowa Jalal ma ya fito, ya sanya shadda coffee color, kansa ba hula, ya taje sumarsa ta sha mai, se kyalli take, ga kamshin turarensa ya cika gurin yana kokarin daura wrist watch, Jalila ta kare masa kallo tace
"wow looking so masha Allah" dagowa yayi ya kalleta yana murmushi, karasowa tayi ta karbi agogon ta saka masa, ta shiga daki ta dakko masa hula, tasaka masa sannan tace
"kafi kyau da hula, bari inyi maka hoto"
Jalal yace
"gaskiya sekin biya zakimin hoton"
Jalila tace
"danma zan saka a wayata shine sena biya? To an fasa"
Dariya yayi yace
"hmm ni hotonki a wayata sunkusa dubu, nikuma ko daya nasan baki da shi, bakomai nidai ina sonki my wife"
Jalila ta dan harareshi tace
"ina ka samu hotona har kusan dubun?"
"kina mamaki ne? In mun dawo zan nuna miki"
"to shikenan Allah ya kaimu mu da wo din"
Ta dinga daukarsa hoto, seda sukaci lokaci suna wannan hotunan, sannan sukayi nufin fita, Jalila ta kuma kare masa kallo daga sama har kasa, ta tuna lokacin da yake kan ganiyar shaye2, irin shigar daya keyi, yadda yake magana ga rashin fara'a, ta kalleshi yanzu a hankali ta furata "Alhamdilillah '
Jalal yace
"lafiya kuwa kike min kallon kurilla, kinsan fa bana son kallo?"
Dan murguda masa baki tayi tace
"Sena kalla din in yaso a dau mataki"
"haka kikace ko? Zan dau mataki kuwa"
Ta dan laankwasar da kai tace
"kayi kyau sosai, kaman karmu fita a ganka"
Da sauri ya kalleta yace
"do you really mean what you said? kina kishina kenan?"
Dan tabe baki tayi tace "hmm to maybe, Amma kaman ba yau nafara kishinka ba, To ban saniba ko kishin ne koba shi bane"
Wata ajiyar zuciya ya sauke yai murmushi yace
"shikenan muje karki makara, dan 10 minutes kawai zamuyi kuma zamu dan tsaya a wani guri"
Haka suka jera gwanin sha'awa, ya bude mata gaban mota ta shiga sannan ya kunna motar suka fice.
Befi mintuna shabiyar da tafiyarsu ba Ilham tazo gidan, amma me gadi ya sheda mata cewar
"masu gidan yanzun nan suka fita"
Ilham Tace
"megidan shi dawa suka fita"?
Megadi yace
"shida matarsa mana, da alama wani gurin zasu je"
Ilham tace "basu gaya maka ina suka tafi ba?"
A fusace yace
"ke ko dai 'yar leken asiri ce ke? Nace miki sunfita ubansu ne ni da se sun gayamin ina zasu"
Haka Ilham ta koma gida gwiwa ba kwari.
Koda sukaje gurin biki kallo yakoma kansu, sunyi kyau sosai, a table daya suka zauna itads Jalal,' yan makarantarsu sukazo suka gaisa, dayake a cikin kawayen Jalila Jalal yafi sanin Zahra ya dan fi sakin jiki da ita, tunda yanzuma kokari yake yana gaisawa da kawayen nata dan kar yayiwa Jalila laifi, bayason taro kuma befiye sakewa da mutane ba, Zahra tace
"Jalila gaskiya ya kamata ayi muku hotuna kaman a saceku a gudu" zahra taita zolayarsu, nan ma hotunan suka sha, maman amaryar tazo wucewa ta tsaya suka gaisa, Jalal yai mata alheri, Jalal kenan zuma ga zaki ga harbi. Seda sukayi kusan awa biyu a gurin, ya bar Jalila ta sake a cikin kawayenta, dan kanta tace ya tashi su tafi gida.
Seda Jalal yafara biyawa ta police station tukuna, suna zuwa suka tarar da Yaya mairo a gurin tana magiyar a barta taga Sa'adah, Jalal kota kanta bebi ba, yayinda Jalila ta gaisheta
Yaya mairo cikin kuka tace
"na gamaki da girman rabbil izzati ki cewa mijinki ko ganin Sa'adah a barni inyi, ina cikin damuwa wallahi"
Jalila ta dafa Yaya mairo tace
"kiyi hakuri Yaya mairo, insha Allah za'a saketa yau din nan ki dena kuka, zesa a saketa"
Jalal daya ga yadda Jalila ke rarrashin Yaya mairo ji yayi kaman ya maketa, wani lokacin halinta daya da Jawwad, komai girman laifin da kayi musu basa riko, ya tuna cin mutuncin da Yaya mairo tai mata a baya, Amma yanzu se lallabata take yi.
Jalal ya gaisa da 'yan sanda cikin girmamawa sannnan D. P. O yai umarnin a kawo masa su Sa'adah,
Sa' adah tayi baki kirin ga waga muguwar rama da tayi se uban hakora, Ga Hannah itama har dan gwara Hannah akan sa'adah, seda Jalila ta tsorata da ganin ta.
Hannah seda ta sandare dan mamaki, Jalal ne a cikin wannan shigar manyan kaya na alfarma, yazama wannan kamilin haka? Gefensa ga matarsa Jalila, yarinyar da tafi tsana, lallai Jalila kwararriya ce gurin makirci, tai musu makirci itada Ilham ta aure Jalal
Jalal yace
"Yallabai wannan itace Hannah, ina son a auna ta a tabattar da tanada ciki? Idan tana da shi seta haifeshi ta shayar da shi ta raineshi inya shekara biyar ta bani shi, idan kuma ba ta dashi zanyi kararta a kotu ta nemomin cikina da ta zubar"
Kallonsa Jalila tayi tasan rainin hankali na Jalal zatayi magana ya daga mata hannu, kuka Hannah ta farayi tace
"wallahi Jalal karya nakeyi, bani da komai nayi hakane danka aureni, dan Allah karka yi min haka, zaka tozartani inkamin haka"
Jalal yace "kina gudun tozarci ni kika tozartani a gurin iyayena, idan har karya kike alfarma daya zanmiki, kije dubai gurin mahaifina ki bashi hakuri ki karyata kanki"
Cikin kuka tace
"na shiga uku Jalal, ina naga kudin zuwa Dubai, kayi min rai dan girman Allah"
Jalila ta kalli wani dan sanda tace
"yallabai Sa'adah bata da lafiya ne naga ta rame sosai? Dan Allah Jalal a saki sa'adah tunda ta nuna inda Hannah take kaman bata da lafiya"
Wani dan sanda yace
"to kusan hakan, tana nan a tsare bata samun shan magungunan ta, ankira likita ya dubata maganinta na kanajamau da bata shane yasa yafara nunawa, amma an bata wani, sannan bazamu saketa ba saboda ta hada kai da wannan kawar tata Hannah sun damfari wani Alhaji makudan kudade, dan haka zamu gurfanar da su a kotu"
Ba Jalila ba hatta Jalal da Yaya mairo seda suka sandare a gurin, Yaya mairo ta dora hannu aka tace
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, sa'adah maganin da kike sha tsawon shekaru kikecemin na gyaran jikine dama na wannan cutar ne, Allah ya wadaranki Sa'adah ni Allah yasa baki gogamin ba bansaniba, abun naki hada damfara kai Allah ya wadaranku wallahi banyu dace ba nikam, daga ke har kanwarki da dan uwanku bana zabe, dan uwanku na prison saboda sata, ke karuwanci da damfara, kanwarki shaye2 da karuwanci nashiga uku ni mairo, Allah ya tsinemuku gaba dayanku 'ya' yan jaraba"
Jalila tuni fuskarata ta jike da hawaye tace
"kidena wannan maganar Yaya mairo, sannan kai kuma officer, this is confidential you don't need to expose her like this baka kyauta ba"
Jalal ba kunya ya rungumo matarsa a gaban mutane yana goge mata hawaye yace
"Haba Jalila kidena kuka mana, Allah ne ya saka miki, ke da'akewa gori Ana cewa tubabbiya ce mahaifiyarki ke gashi Allah yayi ki shiryayiya, SU da suke ikrarin an haifesu a musulinci, kalli yadda suka kare, musulincin nasu a bakine, mu tafi gida kidena kuka "
Jalal yace" Yallabai zan dawo Insha Allah "
Sa'adah ta sunkuyar da kanta tana zubda hawaye, aka tasa keyarsu aka mayar dasu ceil
Sukayi sallama yasa Jalila a mota se gida.
Da sukaje gidan ma taki walwalwala, duk abun duniya ya dameta, wayarta ta dauka ta hau online aikuwa tai sa'a Nana ma tana online suka dinga chatting Jalila ta Gaya mata abunda ya faru
Nana tace "Alhamdilillah ai dama sharri dan aikene, tayi ya kuma koma kanta"
Jalila tace
"A'a Nana, a duk lokacin da musiba ta fada kan wani be kamata muyi murna ba musamman mata, duk abunda yasamu mace raguwar muce"
Nana tace
"rayuwar su dai dan bandani, Allah ne yakamasu wallahi naji dadi kuma, dan sun dade suna zige Maama, yanzu naga ta bakin zagin 'ya' yan wasu"
Jalal na zuwa ya karbe wayarta yaga da Nana take chatting voice message ya turawa Nana yace
"Nana ki kyaleta ta zauna ta damu kanta akan wannan mutanen, ki mata fada kema, ki gaida su Mahmud da Anty Salma"
Ita dai Jalila kallonsa kawai takeyi
Ya ajiye wayar ya zauna kusa da ita ya bude system dinshi, ya shiga wata folder ya mika mata system din, dan zare ido tayi, dan kuwa hotunan tane kawai a folder sun kusa dubu kaman yadda ya fada tun daga na jariran taka har iyanzu, mamakine ya kamata, dan wasu hotunan nata bata taba tunanin sunfita daga wayarta ba tace
"Jalal ya'akayi ka tara wannan hotunan nawa haka?"
Dan hade rai yayi yace "Jalal ko?"
"ohh sorry Zaujeee" ta fada tana murmushi
Ya dan gyara zama yace
"wasu hotunan naki tun kina gurin Ummi, wanda na nunamiki ne a gadon kaya, wasu hotunan kuma Hanan ce take turomin, Hanan ta dade tana supporting dina akanki, wasu a wayar Jawwad nake turawa be sani ba, ta saki ta turamata hotuna nikuma tana turomin"
Bude baki Jalila tayi tace
"Amma gaskiya Hanan bata da kunya, ashe an dade ana yaudara ta, inta antaya mata hotuna na tana tura maka, wayace ka kalleni ba mayafi a lokacin?"
Tai maganar tana yamutse masa fuska kaman yarinya karama.
Jalal yace
"Abunda yasa nake kallonki yanzu ba mayafi shine yasani ake turomin hotunanki ba mayafi nake kalla"
"mekenan?" ta tambayeshi
"So mana" ya bata amsa, ya dora da cewa
"Jalila kaman kina tantama akan son da nake mikine, tun a wancan lokacin da nayi kokarin in cire sonki daga raina ganin hankalinki yana kan Jawwad, Amma duk sanda nayi yunkurin yin hakan se inji ina kara azabtar da zuciya tane, Jalila so mugun ciwone, haduwar da mukayi sanda kikazo kano, nasaka miki wasika a cikin cover Al'qur"ani, amma bana tunanin kin gani, Jalila lokacin dana ganki da Ahmad seda naji kaman in kashe kaina saboda kishi, ko yan kwanaki nayi ban ganki ba sena shiga damuwa, dukda in muka hadu bawani abun arziki da ke hadamu"
Ya kalleta ya dan murmusa yace
"kinsan wataran Jawwad ya sha kamani ina kallon hotunan ki? Na maze na hade rai sedai ya kalleni ya kyaleni kawai, kwana biyu na hanashi taba wayata, abunda banayi a baya, ya dau wayar yaga na saka password yana saka sunaki ta bude, wallpaper na hotonki ne da mukayi a gurin birthday dina, aikuwa ya ritsani da tambayoyi, seda na tabattar masa dani har yanzu wannan soyayya da nake miki a baya tana nan, Amma kar ya gayawa kowa, shine yace ze shigemin gaba Indai Aurenki ze sani farinciki, Jalila na dade ina azabtuwa da soyayyarki "
Ya kwanta a jikinta yace
" please Jalila karki rabu dani, ko da ba kyasona ki cigaba da jin tausayi na dan Allah, ko iya tausayinne, nasan watakila watarn tausayin yakoma soyayya, nikam Soyayyar da Umminki tayimin da sadaukarwa da kikayimin, bazata taba bari in cutar dake ba Jalila, Ina sonki my wife ko baki soni ba dan Allah kiyi hakuri zama dani, kinfi kowa sanin halina da fuskantar abunda nake so ciki harda mahaifiyata, ina sonki"
Hannu tasa tana shafa gashin kansa, tausayinsa duk ya mamaye jinkinta, ta kasa magana, shi kuma yayi lamo a jikinta kaman maraya
Jalal Yace
"Gobe in Allah ya kaimu zaki tafi da kayanki, Munyi magana da Abba yace zakuje bauchi da Maama tunda kunyi hutun makaranta, nima zan koma lagos zan cigaba da aikina Insha Allah, amma sati biyu zanyi kawai in dawo, sannan in kun tafi bauchi karki kirani a waya, sedai in nina kiraki"
"But why?"
"haka nan kawai, zakiji dalilin hakan amma, zanyi missing dinki sosai Baby gaskiya transfer zan nema, in ba hakaba damuwa zata min yawa"
Jalila tace
"kanemi zabin Allah kafin ka nemi transfer din nan Allah ya zaba abunda yafi Alkhairi"
"zamana a kusa dake shine mafi Alkhairin ai"
Tacigaba da shafa kansa a hankali tana tunani daban daban a ranta.
Vote, Comment and
Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
What's app only 07063065680.
Follow me onWatpad @Ayshercool7724
*ABDUL JALAL*
_Story, writing and edited _
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girl_)
*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*
Chapter 7 · 0% Book details