PART 2
Abdul Jalal Part 2 Complete Hausa Novel · about 125 min read
_PAGE 4
Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Or email address @ [email protected]
Watpad @Ayshercool7724
_MY FIRST NOVEL _
Shiru Jalila tayi ta kalli kayan daya ajiye mata sannan tabi bayansa da kallo har ya fice daga gate, din shiru tayi ta tafi tunani, Ahmad yace
"my queen, meya farune?"
Da sauri ta dawo hayyacinta tace "bakomai fa"
"Amma waye wanan?" ya tambayeta yana me kureta da ido, ta dan sauke numfashi tace "Yaya na ne"
"Yayanki queen, ba Jawwad ne kawai Yayanki ba?"
"Abokin Yaya Jawwad ne, dan haka Yayana ne kawai"
"Amma babu wani abu a tsakanin ku kuwa?"
"Meyasa kake min wannan tambayar? Ko baka yadda dani bane?"
"Ahh haba waneni ince ban yadda da gimbiyata ba, ina so ne in tabattar da abunda ke tsakaninku, dan da idonsa yana shaye2"
Ba karamin haushi maganar Ahmad ta bata ba, kenan shima yanayi, in ba yanayi ba, ba abunda idon Jalal yayi dayake nuna yana shaye2, dan haka tace
"baya shan komai, kawai bashi da son magana ne, baya kula mutane"
Kyaleta Ahmad yayi yaga alamar bata son zancen suka cigaba da hira, Jawwad ne ya fito ze wuce su Jalila ya tsaya suka kuma gaisawa da Ahmad dayake dazu sun gaisa, Jawwad yace "to sirikina zan iya ce maka se anjima, ni zan tafi kai Jalal airport ne"
Da sauri Jalila tace "Ina zashi?"
Jawwad yayi murmushi yace "Aiki mana, an tura shi Lagos, se lokacin biki inaga ze dawo, bari inje karyai ta jirana, kin san baya son jira, se anjimanku" Sukayi sallama da Ahmad ya fita.
Ahmad ya maida idonsa kan Jalila yace "Gimbiya naso a ha
a bikin nan hada namu, na kagu in mallakeki"
Murmushi kawai tayi amma hankalinta baya kansa, tanata zancen zuci ne, dayaga haka yace "queen naga kaman Akwai abunda yake damunki, bari in tafi semunyi waya"
Ta mike ta rakashi har bakin gate sannan ta dawo ta zauna akan kujerun tana nazari
"At least yakamata ace sunyi sallama da Jalal, tayi masa nasiha, Amma bata tunanin zata iya kuma rabarsa ba saboda mahaifiyarsa.
Jawwad ya ga sam fuskar Jalal a daure take, babu alamar walwala ko fara'a, Jawwad yai masa magana yafi a kirga, amma ko daya be bashi amsa ba, dan haka ya kyleshi suka cigaba da tafiya a haka kaman kurame.
Gajiya Jalila tayi da zaman tunanin ta mike ta tafi cikin gida, Nana tana zaune a palour suna waya da Mahmud,
"Nana waike dan Allah ba kya gajiya da wannan wayar ne? Kuyita surutu tun ana fadar gaskiya se an koma fadan karya"
Nana taki kula ta seda ta gama wayarta sannnan tace
"waike Baby an gaya miki kowa irin kine me tsarin tsiya, ke yadda ba kya son yawan waya kowa ma hakane, ai a rana inji muryar Mahmud sau hamsin bazan gajiba, musamman mu da muke distance relationship, ai Ahmad din nan ma ban wani yadda kina sonsa ba"
"Inasonshi sosai, amma hakan bashi ke nufin a dinga uzzuramin da surutu ba"
"Hajiya Jalila, kyaji da shi dai"
Hanan ca ta kira Jalila a waya, ta daga tasa a kunnenta
"hello Baby, 'yar uwata rabin jikina ashe Family dinmu daya Baby? Narasa inda zan sa kaina dan farinciki, dazu Abba yake gayamin kuma wai an kawo kudin Aurena da Haidar, Baby na rasa me zanyi dan farinciki"
Murmushi Jalila tayi tace "na riga ki ji ai, kiyi Azumi ki godewa Allah"
"queen na rasa inda zan saka raina dan farinciki, daddy yace zasuzo karbar kudin Nana, narasa yadda zanyi dan murna"
"haka Al'amarin ubangiji yake Hanan, yana juya komai yadda ya so"
"Hakane Queen, amma naji haushi da baza'a hada da nakiba, ni ina Jalal ne ma?"
"yaje interview din nan ai, an turashi lagos zeyi wata uku"
"Allah sarki bawan Allah, wallahi Jalila bana kaunar Aurenki da Abokin Yaya Yusuf din nan, in duniya da gaskiya Jalal ya kamata ki Aura"
Wani dogon tsaki Jalila tayi ta kashe wayarta, dan bata son Hanan ta bata mata rai.
Jalila ta mike har zata bar palourn taga Maama tazo ta wuce kitchen, gaba daya Jalila bata jin dadin yadda kowa ya fita harkar Maama, dukda abubuwan da Maaman tayi mata, Akwai lokutan da ta kyautata mata, dan haka taga be dace ta mata hukunci da laifin da take mata ba, dan haka tabita kitchen din, Maama na kokarin kunna gas Jalila tayi maza taje ta karbi lighter tace "Maama kawo in kunna miki, me zaki dafa?"
"barmin Abina zanyi"
"A'a Maama, tunda ba abunda nake ki barshi in dora miki"
Jalila ta karbi lighter ta kunna gas, dan jimm Maama tayi tana Kallon Jalila, yadda Jalilan ke Acting kaman Maama bata taba yi mata wani abu na bacin rai ba.
Jawwad suka isa airport yayiwa Jalal Sallama amma ya amsa masa a ciki, sam baya walwala, yasan halin Jalal baya son takura, tunda be niyyar gaya masa meke damunsa ba, ya ja Akwatinsa yayi gaba yabar Jawwad.
Haka Jawwad ya taho yanata tunanin me akayiwa Jalal yake wannan bacin ran haka?
Bayan Jalila ta gana yiwa Maama girki, ta koma daki, ta dauki Alqur'anin nan tana ta jujjuyawa, Kamshin turaren Jalal yakeyi, hakama dan teddyn ta, tasa hannu ta ta dinga duba Alqur'anin nan page by page, amma sam bata ga komai a ciki ba, kodai Jalal dama yana son raina mata hankali ne kawai?
Shiru tayi ta tuna yadda taga yana yinsa bayan ya gansu tareda Ahmad, Fuskar nan tasa a daure babu alamun sassauci, tayi shiru ta cigaba da zancen zuci, ;yanzu ze tafi lagos bashi da kowa a can, babu me kula dashi, Allah kadai yasan meze aikata,
"kinfi so in cigaba da shaye2 na ko? Ke Garkuwa ce a gareni" ire iren wannan maganganun nasa da Maganganun Antynsa da take gaya mata tabata amanar Jalal ne yasa take tunanin Anya hukuncin data yanke yayi dai2 kuwa?
To Amma nikuma mutuncina fa? " gaba daya ta rasa me yakamata tayi? Yanzu tana gaya Hanan, tasan Hanan zata canza mata magana tafara kawo wani abu daban, dan haka tabar Abun a ranta ta cigaba da Yiwa Jalal Addu'a.
'yan kwanakin nan sam Abba ya dena shiga harkar Maama, har gara Jawwad ma yana zuwa gaisheta, Nana kuwa seda Jalila tasata a gaba ta nuna mata be dace ba abunda take yiwa Maama, wannan abunda yafaru tsakanin ta da Abba ne da kuma' yan uwan ta, sannan ta samu Nana ma take shiga sabgar Maaman, Abba ya gayawa Maama ranar Lahadi zasuyi baki, za'a kawo kudin Auren Nana, abakin su Nana taji batun haduwa da 'yan uwan Abba a Bauchi, ba tayi mamaki sosai ba jin ance su Hanan' yan uwansu Abba ne ba, sakamakon matukar kamannin dake tsakanin Jalila da Hanan, sedai taji haushin rashin sanar da ita da Abba beba.
Tun ranar Juma'a suke shirye2 domin bakin daza'ayi, Jalila ce jagorar girke2 da shirin yadda za'a karbi baki.
Gefe guda Jawwad yana ta shirye2 Ranar litinin shima ze tafi gurin nasa Aikin, ba karamin kulawa Hanan take bashi ba, da soyayya da kuma shagwabarta, yanayin yadda take nuna yarinta a wasu bangaren ba karamin birge shi yake ba.
Kamar yadda aka saka ranar lahadi daddyn Hanan yazo Kano aka karbi kudin Auren Nana, itama lokaci dayane dana Jawwad dakuma Abdallah Yayan Hanan, ranar har mutan bauchi seda sukazo garin kano karbar kudin, da kuma kara taya juna murnar haduwar su a matsayin 'yan uwa. Jalila taji dadi da akazo hadda Hanan da Mummynta, Maama seda ta sha jinin jikinta ta raina kanta ganin manyan mutanen da sukazo gidan, Abun Arziki ya hadu dana Arziki, dangin Su Jawwad dana Su Jalal, Ranar anci ansha, kai ka dauka bikin Aure akeyi rana ce me matukar tarihi da wannan Ahali bazasu manta ba. Jalila sam bata samu kebewa da Hanan ba, saboda Hanan na manne da Jawwad, sam bata jin kunyar kowa take nuna masa soyayya.
Mummyn Hanan se mita take tace "Ni gaskiya naso a hada abun nan hada na Jalila, in aurar da 'ya' ya uku, amma in shirya da kyau, amma bakomai anata se nafi shiri ko Jalila?"
Ita dai Jalila sedai tayi murmushi ta sunkuyar da kai.
Duk yadda Maama take jin kanta take kuma jin haushin Auren Hanan da Jawwad boyewa tayi, Saboda sam bata da makusa, 'yar dangi ce, kuma' yar uwar dan tace, tana da kyau dai2 gwargwado kuma tana da Ilimi, yanayin kyau da gayun mahaifiyar Hanan ya isa ya nuna maka 'yar ta ma hakan take. Koda ta hasko Naja seta ga abun se A hankali, kuma tun abun nan da sukayi mata ta tabattar da Ko Auren akayi Naja zata iya wulakanta ta.
Da ire iren wannan tunanin yasa ta ajiye duk wani bacin rai aka shiga hada2. Tareda tsara yadda suke ganin bikin ze kasance, Ba laifi Mummyn Hanan ta saki jiki Maama, Sunyi hira sosai kaman sun saba, sannan suka tattauna akan yadda harkar bikin yaran nasu ze kasance. Se la'asar Suka tafi, mutanen Bauchi suka tafi, Su Hanan ma a ranar suka juya kaduna saboda Su Hanan suna jarrabawa, su kuwa danginsu Mahmud, suna kawowa Mahmud kudin Aure sukaci Abinci suka juya Borno.
Wasa2 sosai tunanin Jalila ya hana Jalal sukuni, da yafara aiki in ya tuna da ita gaba daya se yaji duniyar tayi masa zafi, yarasa inda zesa kansa, meyasa Mummy tayi masa haka? Idan yaji abun ya dameshi se ya tafi club yaje ya cika cikinsabda giya, dukda wasu lokutan yana bawa aikin da yaje yi mahimmanci, Sam Jalal bashi da sakewa da mutane, dan haka be saba da kowa ba, sedai yana girmama shugabanninsa na gurin aiki, girmamasun da yake besa sunga alamar ze bari su taka shi ba, inda yake burgesu yana maida hankali akan aikinsa sosai.
Duk lokacin da yaje Club mata da suke damun sa ne ga kuma shigar tsirara da suke yasa shi dakatar da kansa ga zuwa Club, idan yaji ba yadda zeyi se yayi shaye2 se yayi abunsa a dakinsa na hotel da yake ciki.
Amma duk da haka yarasa dalilin da yasa mata ke binsa, sedai in baze fito ba.
Hannah ce zaune akan kujera tana kwalliya, Sa'ada na kwance akan gado tana danna waya, dan dakatawa da kwalliyar Hannah tayi ta dan kurawa madubi ido, sekuma can ta daki kan mirror tace "Impossible baze yuwu ba wallahi"
Sa'adah ta waigo ta Kalle ta tace "lafiya kuwa?"
"Akwai matsala Sa'ada" Hannah ta bata amsa
"matsalar me fa?"
"Sa'ada ki kalleni ki kara, kimin kallon tsaf tun daga sama har kasa, ki kalli yadda nake gara kan maza, in taka wanda naso in wanke wanda naso, amma a hakan har rububina wasu suke, in sauke Ajina in cewa Jalal idan ya Aureni zan dena bariki, Amma ya watsa min kasa a ido"
Wani dogon tsaki Sa'ada tayi tareda fadin "Nina dauka ma wani mutumin kirkin ne, A she akan wannan mashayin ne, ni ba wannaan ya dameni ba a yanzu"
Hannah tace "Mutumin kirki ne mana, ki kalleshi kallon tsaf Sa'ada Namiji ne irin wanda duk wata mace zatayi burin Aure, shaye2 ne kawai matsalar sa, da farko da nakewa su Jeje aiki, nna zata zan samo kansa ta sauki ya yadda dani, Amma duk wata dabara da kisisina ta matan bariki nayi amma yaki amincewa dani"
"to kibi wani mana, ko shine kawai namiji?"
"bazaki gane ba Sa'ada, bakiga irin kirar da Allah yayi masa bane, kuma da kike ganinsa a haka, dukiya ce dashi kaman abun banza"
"Ya akayi kika sani, nasan dai babansa yana da kudi, amma shikam ko aikinyi ba shida shi" Sa'ada tayi maganar tana yatsina fuska
"Hmm to wallahi har ki mutu in ba wani ikon Allah ba, kaf danginku daku da abunda kuka mallaka, bazaku kaishi dukiya ba, yana da kudi da mahaifinsa yasa ake juya masa, Jeje yaso ganin bayan dukiyar nan shida mai gidansa amma abun be yuwu ba suka kare a prison"
Sa'ada ta tashi zaune tace "to ke yanzu meye abunyi, ni ban taba sani ba, kin san ya taba kusa tonamin Asiri ina zuwa club agaban babarmu"
Dariya Hannah tayi tace "Abune mawuyaci ya tona miki Asiri, bar ganinsa a haka, yasan abunda yakeyi, naje har gidansu na dana masa tarko, amma ga dukkan alamu ya tsallake shi, wannan karon zan masa tarkon da zan rike shi a wuya, be isa ya kuma subuce min ba"
"Yakamata kam, Amma ni nan tunanin yadda zan huce abunda abokinsa Jawwad yayiwa Naja nake, kiri2 yafasa Auren ta, yarinyar nan duk ta shiga damuwa"
"Allah sarki, to wai ya'akayi aka fasa Auren? Waye yaje yai mata gulma a gurin baban nasa?"
"ya za'ayi in sani, Amma da nafi kyautata zaton wannan munafukar kanwar tasa ce"
"Wace kanwar tasa ya'akayi tasan abunda Naja take? Ko dai itama tana ta bawa?"
"Ke bari, wata yarinyace yadda kika san boka haka take, ni dai ban san tana wani biye biye ba, Amma kina zaune in taso seta nemo waye ubanki koda ke baki sani ba, wai ita Jalila makirace ta bala'i, idan tace bata san abu seta ga bayansa, tasa Jawwad ya fasa auren Naja se kawarta"
Jin an ambaci Jalila yasa Hannah zare ido tace
"Kan bala'i ai nasan wannan yarinyar, tabdijan ni zan gaya miki makira ce, ke wallahi keda kike bariki tafi ki iya rashin mutunci, ke zata iya yuwu wa ita tasa aka hana, bari in gayamiki yarinyar nan tafiki bala'i, dan koni tasa min ido akan Jalal, ita take rusa min komai "
Cikin mamaki Sa'ada ta kalli Hannah tace" wai kin santa ne? "
" Nikuwa na santa, kuma nasan illar ta, munyi Arranging da Jeje mun gama komai, zamu sace Jalal ranar birthday din sa, idonta na kanmu, muka bugar da shi da giya ta shammace mu tasa aka dauke shi daga gurin, ke ina jin kishin cewa ita tasa aka kama Oga KB"
Zaro ido Sa'ada tayi cike da mamaki tace "Ke haba dai? Shikuwa oga KB yana me,duk iya kuri da gadarar rashin mutuncin nasa, yarinya ce fa karama"
Hannah tace "hmm ke dai bari, mace kenan, kaidin wata yafi wata, irinsu kuma sa'a ce dasu a rayuwa, kibi a sannu kawai"
"Tabdijan amma babu kama, dan bakiga cin mutuncin da muke mata ba mu da babarmu, kin san uwarta tsohuwar arniya ce, bakiga cin mutuncin da muke mata ba"
Hannah tace "Yawwa kuma ga cin mutuncin da tayi muku nan, kuma ta gama daku ba"
"Sosai makuwa ta gama damu"
"shiyasa wannan karon shirina ita da Jalal ne, dan bana ta wannan Ilham din dan wannan ba mace bace, wannan tafi hatsari, baze tsallake wannan tarkon ba a yanzu, na duba mashayar da yake zuwa ba adadi amma ance ya dena zuwa, duk da haka zan nemoshi"
Yauma duk da tarin farinciki da Jalila ta tsinci kanta a ciki yau, amma bacci ya kauracewa idanuwanta, jikinta na bata Jalal yakoma shan giya, da kyar ta samu bacci ya dauke ta, amma mafarkin Jalal a cikin wani yanayi na shaye2, yasata farkawa, gabanta na wata irin mummunar faduwa, wayarta ta dakko ta duba karfe biyu da rabi na dare, ga shi ita ba lambar Jalal ce da ita ba, tarasa mema zatayi gallery dinta ta shiga tana dubawa, tsofaffin ajiyayyun hotunan ta take dubawa, hotunan da sukayi da Jalal tun wani zuwa da Hanan sukayi, haka taita kallon hotunan, a haka har ta kawo kan hotunan birthday dinsa, cin karo tayi da wani hoto da'akayi harda Hannah a ciki, take gaban Jalila ya fadi, dan sam ta manta da Hannah, kuma barin Hanna ba tareda daukar wani mataji ba tamkar kashe maciji ne ba'a sare kansa ba a rayuwar Jalal.
A hankali ta ajiye wayar, ta sakko daga kan gadon ta shiga toilet tayi alwala tazo ta tada salla.
Ranar litinin Jawwad shima yayi nasa shirin tsaf domin tafiya Gurin nasa aikin dake birnin tarayya, Abba yayi masa Nasiha sosai tareda sa masa Albarka, haka ma bangaren Maama, tayi masa Addu'a da sa Albarka, dukda marin da Maama tayi masa akan Naja, hakan besa ya nuna mata har yanzu yana fushi ba, Bangaren Jalila kuwa har kuka tayi, saboda zatayi kewar Yayan nata sosai
Abba yace "Jalila kina kuka dan zeyi tafiya, kuda kwanan nan zeyi Aure gaba daya zasu bar gidan, su barki seke kadai"
Kara fashewa da Kuka Jalila tayi, Nana tace "Abba ka gani ko? Wannan yar taka ta fiye shagwaba wallahi"
Jawwad yace "haba babyn Abba, sekace ba jaruma ba, zan dawo ai kidena kuka"
Sukayi ta tsokanarta ita kuwa dagaske take kukanta.
Haka sukayi sallama da Jawwad shima yakama hanyar tafiyar sa.
Jalal yana waya da daddyn sa sosai, sannan suna waya ds Jawwad, suna shirye2 yadda biki ze kasance a tsakanin su.
Abban su Jawwad yana kasuwanci ne a tsakanin Kano da lagos, dan haka in yaje suka haduwa da Jalal.
Jalila Nason sanin halin da Jalal yake ciki, amma babu wata hanya da zata san hakan, dan haka taketa kokarin boye damuwarta.
Maama Allah ya temaketa Abba ya sakko daga fushin dayake da ita, sannan tunda abun nan ya faru Su Yaya mairo ko a waya basu kara neman Maama ba, abun ya dameta sosai dan haka ta shirya da kanta taje gidan su.
Tunda tayi sallama suka amsa suka shareta suka ki kulata, ita tayiwa kanta gurin zama, ta gaida Yaya mairo amma taki kulata, seda ta bata 'yan kayan data saba kaimusu, shine Yaya mairo ta dan saki rai suka gaisa, Naja ta gani a lullube tana bacci, Maama tace "Yaya, Naja ba lafiya ne?"
Kafin Yaya mairo ta amsa Naja ta fara magana cikin maye "Ni... Ni.. Ba... Wallahi baaaaani da.... Da lafiya, Shiyasa naiwa kaina caaajiii, baaaa danki yaki Aure na baaaaaa, wallahi....
Cikin tsawa Yaya mairo tace" yimin shiru dan ubanki, ciwon mara take, shine ta sh
a magani fiye da ka'ida"
Gaba daya jikin Maama yayi sanyi saboda babu tantama Naja maye takeyi. Shiru tayi takasa cewa komai, Naja ta cigaba da surutai, can kuma ta kwalla uwar kar, sega jini na gudu a tsakar dakin daga karkashin Naja.
Se bayan la'asar su Jalila suka gama lectures ta gaji matuka, haka kurum tun suna lectures takejin gabanta yana faduwa, da kyar ta tsaya aka gama lectures ta fito, danma manu direba ne yaje dakko ta daga school, abunda yabata mamaki be wuce ganin motar Hannah a gabansu ba, tana tsala gudun wuce sa'a, kuma da alama layinsu zata shiga, Jalila tasa Manu direba yayi parking a farkon layinsu, ta sauka ta shiga layin da kafarta, aikuwa tana zuwa taga Hannah tayi parking din motarta ta shiga gidansu Jalal, Jalila batayi shawarar komai ba ko tunani tabi bayan Hannah zuwa cikin gidan.
Masu kirana a waya please am sorry, ku dinga min magana ta what's App, ina kokarin duba messages, amma kira musamman idan ina aiki, bana samun daga bakuwar lamba am sorry.
Ina godiya da kulawa.
Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
What's app only 07063065680.
Watpad @Ayshercool7724
*ABDUL JALAL*
_Story, writing and edited _
AISHA HUMAIRA
( _Daddy's girl_)
*PERFECT WRITER'S*
*ASSOCIATION*
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A*
PART
_PAGE

Hannah gaba daya kanta ya kwance bata taba tsammanin abubuwa zasu kwabe mata haka ba, wai me yakawo Jalila a gabar da takeso kulla wannan gadar Zaren, da komai ya tafi dai2, Jalal baze taba tsallake shirinta ba, wayarta ce ta fara ringing amma Hannah tayi biris da ita, an kirata ya kai sau shida sannan ta dauka a fusace tace
"dalla waye haka?"
"ke dalla zizo ne, za'a miki abun Arziki amma kina wa mutane hauka, ki tattara kayanki tun wuri kisan inda dare yayi miki wallahi"
"kamar yaya? Saboda me?"
"Allah ne yake sonki da rahama, Wallahi Jiya na raka wani me gidana Unguwa, ya tsaya gurin wani me gidansa dan sanda ne babba, naji me gidannan sa yana waya, bayan ya gama yake gayawa maigidana, wai wani yabada izinin a kamo masa wata yarinya a ajiye masa ita har seta haihu, ta yaye yaron ya shekara biyar sannan a saketa, idan kuma ba tada ciki aita ajiye ta kar a saketa, kuma yadda mutumin nan yake kwatantawa na gano kaman kece, ban gasgata hakan ba se jiya da naje palace, wallahi cikin dare 'yan sada sukazo nemanki, dan haka in kin san da wata cakwakiyar da kika kulla tun wuri ki kama gabanki wallahi "
Hannah ta hadiyi wani mugun miyau ta ce
"Shikenan nagode sosai zizo"
Ta katse wayarta ta mike tsaye tareda fadin
"kan bala'i banga ta zama ba, ni Jalal zewa haka? Wallahi yadda ya fada din nan aka kamani kashina ya bushe, Amma wallahi in yasan besan wata besan wata ba, ni zesa akama, nizewa hauka? Banga ta zama ba"
Ta mike da sauri ta
janyo Akwati tafara zuba kayanta tanayi tanayin surutai.
Jalila tattar komai ta ajiye a gefe ta maida hankali akan karatunta, dan yadda takeji in bata dena yawan damuwar nan ba zuciyarta zata iya bugawa, sosai Maama ta rage wannan gabar da takeyi da Jalila, tana dan sakewa da Jalila har suyi hira, suna shirye shiryen yadda biki ze kasance, Jalila bata taba nuna mata tana fushi da ita akan abubuwan da tayi mata a baya ba, Maama har mamaki takeyi, wani lokacin yanayin halinta daya da Jawwad, ka musu laifi amma su nuna basu san kanayi ba, ita kanta Nana tayi mamakin yadda Maama tayi saurin karaya da Al'amarin da yafaru.
Jalila tana kitchen tana aiki Nana ta sameta
"sannu da aiki Jalila, har tausayi kike bani, ke ba kya gajiya da aiki, da ke zaki rigani Aure ai ban san ya zanyi da aikin gidan nan ba, dan ma su Yaya Jawwad basa nan, aikinsu sam baya karewa"
Jalila tai murmushi tace "Nana uwar son jiki, keda zakiyi Aure ai son jiki banaki bane, madam get ready to face the challenge, Ba sauki a Aure"
"Nasani amma gaskiya bazan iya yadda kikeyi din nan ba, tabdijan shikenan kai bawa baka da hutu"
"Aikuwa mukayi miki aure kikaje kikayi shirme, in yace ze kar Aure Addu'a zamu taya shi, mu fidda anko mu sha biki"
"Kan bala'i ji muguwa, to ta Allah bataki ba"
"Kai Nana sarkin kishi"
"ke ba dole inyi kishin sa ba, ke har mamaki kike bani, ainaga kokarin ki da zaki auri Ahmad din nan, inajinki Hanan tana gaya miki matarsa bata da kirki"
Jalila ta murmusa tace
"Nana kenan, macen da ta amsa Sunanta mace, wadda ta yadda da kanta bata batawa kanta lokaci akan wani kishi, duk rashin kirkin matarsa ai ba akanta zan zauna ba, zan maida hankalina ne akan mijina, zanyi kishine da matar da nasan ta fini Ilimi, kyau, dukiya da asali, se matar data hada wannan abubuwan lokaci daya itace watakila zan kalleta a matsayin kishiya"
jinjina kai Nana tayi tace
"Sannu Jalila, Aini ko Kaza za'a aajiye ace kishiya ta ce to hankalina baze kwanta ba, yaushe zan kashe kaina, ke masu irin wannan zuciyar taki bau da yawa"
A tare sukayi dariya, Sannan Nana tace
"Yawwa Jalila nikam nace ya akayi kika amso qur'anin nan daga hannun Ilham? Na ganshi a karamin drwower"
Dan murmushi Jalila tayi tace "Nawane ai ba nata ba, dan haka tunda ya tafi dole ya dawo"
"Amma dagaske yaya Jalal ne ya baki shi? Kamar yadda Ilham ta fada?"
"watakila shi yabani dan bani da tabbas" Jalila ta fada ba tareda ta kalli Nana ba
"Kamar Yaya baki da tabbas?" Nana ta tambayeta cike da mamaki
Jalila ta juya ta cigaba da aikinta sannan tace
"Kamar yadda nagaya miki mana, bani da tabbas na shi yabani koba shi bane ba"
Nana tace "Kai Jalila kin fiye rainin hankali, mutum yayi miki magana ki raina masa hankali, in tai wari dai maji, Ke Jalila ban gaya miki ba"
"Ina jinki hajiya Nana jarida"
Nana ta dan hade rai tace "kefa 'yar wulakanci ce, wace irin Jarida kuma?"
Jalila tayi murmushi tace "Allah yabaki hakuri"
Nana Ta dan saki fuskarta tace "Wai bakiga kwana biyun nan Maama duk tayi sanyi bane"
Cikin ko in kula Jalila tace "Ban lura da hakan ba, tana komai nata kaman yadda take a baya"
"Shikenan tunda haka kika ce amma Anjima zaki rakani wani guri"
"Ina kenan?"
"In munje zaki gani, saura daga baya kice min bazaki ba"
Jalila tace
"zan raka ki Insha Allah, Amrya ba kya laifi"
"kai Jalila har kinsa naji dadi" Nana takarasa fadar hakan tareda fita daga kitchen din.
Koda Jalila ta kammala aikinta ta koma daki, ta tarar da missed calls a wayarta, ta dauka ta bude don duba waye ya kirata haka? Kiran na Jawwad ne da kuma Ahmad, tana kokarin kiran Jawwad ne kiran Ahmad ya shigo wayarta, dan haka ta fasa kiran Jawwad ta amsa kiran Ahmad, Jalila ta shafe lokaci me tsawo suna waya da Ahmad, Sosai Ahmad yake bawa Jalila kulawa, dan tana iya shafe lokaci me tsawo suna waya ba tareda ta kosa ba, sukanyi kwanaki basuyi waya ba, saboda yanayin Aikinsa, dan haka duk lokacin da suka samu dama suna daukar dogon lokaci suna tare a waya, tana cikin wayar ne kiran wayar Jawwad ya dinga shigowa, dan haka sukayi sallama da Ahmad, ta kira Jawwad, tana bugawa ya daga
Jawwad yace "Baby dawa kike ta waya hakane? Da farko na kira baki daga ba, Nakuma kiranki busy busy, for more than hour"
"Am sorry Yaya Jawwad , Ahmad ne ya kirani, shine.. sekuma tayi shiru
Jawwad yace
"Hmmm to shikenan nagane, dama munyi magana da Hanan tace; zasuyi magana da Nana irin kayan da zasu saka na dinner, za'a turawa Abba, A dakko musu, kayan sun iso, ta kira layin Nana baya shiga"
Dan zumbura baki Jalila tayi kaman yana ganinta tace
"suka dai za'a siyawa nikuma fa? Ko tun yanzu anfara ware ni"
"Waya isa ya wareki babyn Abba, A sekin zaba sannan za'a basu su zaba suma"
"to shikenan zan musu magana Insha Allah, ya Aikin kuma?"
"Aiki Alhamdilillah gashi muna ta fama"
"To Allah yabada sa'a"
"Ameen Babyn Abba"
"Ina Jalal? Ya nasa Aikin?" Jalila taji tayi maganar ba tareda ta shirya yinta ba.
Jawwad yace "Kinfara missing dinsa ne?"
Sekuma taji gaba daya ta dirirce tarasa me zatace
"Amm a'a kawai na tambaya ne, don't mind me, yaushe zakazo"
Jawwad yace
"A'a tsaya, naji dadi da kike tambayarsa, dama be kamata ya samu aiki ta hanyarki, yakama hanya ya tafi nesa da gida kuma ace bakya bincikar ya yakeba, Jalal dai yana nan lafiya, kuma yadda yake nunamin yana jin dadin Aikin nasa, Alhamdilillah ana samun cigaba a rayuwarsa, muna godiya kanwar mu, Allah yabiya ki ladan wannan dawainiya damu da kike"
"Ameen Yaya, to shikenan,
naji kaman Maama tana kirana"
Jawwad yace "to shikenan munyi waya da Maaman dazu da safe, Amma in cewa Jalal kina gaisheshi?" ya tambayet cikin zolaya
Da sauri tace
"A'a karka fada, ni bana gaisheshi"
Jawwad yai murmushi yace "Shikenan se anjima"
sukayi sallama, ta danyi Ajiyar zuciya, sannan ta mike, ta tafi bandaki dan daura Alwala anata kiran sallar Azahar.
Da la'asar Nana ta uzzurawa Jalila suka dau mota fita, seda suka tsaya a kasuwa sukayi siyayya, Sannan Nana tace ta rakata Asibiti dubiya, Sam Jalila bata kawo komai a ranta ba ta raka Nana Asibiti, suka shiga female ward, Nana ta tambayi wani daki, aka nuna musu, Seda suka shiga
dakin sannan Jalila ta lura da suwaye a dakin, Su Yaya mairo ne a dakin, se Naja dake kwance kaman gawa, ana samata ruwa,
da Jalila tasan gurinsu Nana zata janyo ta, da bata biyota ba, Amma me sukeyi a Asibiti? Ta tambayi kanta, Sallamar dasu Jalila sukayi ne yasa su juyowa suga su waye, Ganin Nana da Jalila yasa su hade rai, Jalila ta samu guri ta tsaya, Nana ta karasa ta zauna, tace
"Yaya Mairo ina wuni"
Rai a hade yaya mairo tace "lafiya"
"Yame jiki kuma?" Nana ta kuma tambaya
A fusace Yaya mairo tace
"ban sani ba gulayya, uwarki ta gaya miki shine kikazo ganin kwaf, hadda dakko wannan annamimiyar shedaniyar, to da dan uwanki ya fasa Auren Naja bata mutu ba tana da rai, sannan ki gaggauta dauke wannan tsinanniyar yarinyar ku bar gurin nan, dan na tsani yarinyar nan bana kaunar ta, Yarinya sekace mayya, wayasani ko bayan Kafirci ta gaji maita, kila ta sha a Nono, kiri2 tana kokarin rabani da 'yar uwata, za' ayi Auren nan amma ta shiga ta fita ta hana, makira sedai kici kanki wallahi, kurwarmu tafi karfinki"
Jalila dake gefe tace "kinga nifa ban san nan zamuzo ba, dana san nan zamuzo da bazan biyota ba, ni ban san Naja bata da lafiya ba, dan haka kidena zagina, wallahi kika kuma zagarmin uwa sena rama, ko ina maita zanci naman kune? Me zan ci ajikinku jikin matsiyata, Azzalumai"
Sa'adah ta taso a fusace tazo gaban Jalila ta nuna ta
tace "ke karki kuskura ki zagarmin uwa"
"in aka zagetan me zakiyi?"
Jalila ta tambayeta tareda sauke hannun sa'adah tace
"uwata da aka haifa a cikin Arna, da ita nake Alfahari, dan haka duk wanda ya kuma Yunkurin zaginta se inda karfina ya kare"
Nana ta mike da sauri taje tsakaninsu ta tsaya tace
"haba dan Allah, nifa ban kawo Jalila gurin nan dan kuyi rigima ba, nazo in duba Naja ne nace ta rakoni, me yakawo zancen maita,
yaya Jalila tayi hakuri a lokuta da dama da kuke cin mutuncin ta, Yaya mairo a rayuwa mussaman idan kanada 'ya' ya bakayi wa dan wani gori, kokuma mummunan baki, ......
"rufemin baki ko in gaureki da mari, kema ta shanye ki, shine zakizo kimin rashin kunya, na rufe kofa in muku dukan tsiya a gurin nan"
Jalila tace
"Wallahi babu matar da ta isa in tsaya ta dakeni, wallahi Nana dana san nan zaki kawoni bazan biyoki ba, kuma ki kyalesu karsu fasa zagina, bacin ranki akan an fasa aurar 'yarkine, badan anyi yunkurin likawa Yaya Jawwad ita ba ba abunda zesa in fadi wani abu a kanta, tunda tun ba yauba nasan halin yaranki kaf, nasan Naja tana shaye2, an gayamin Sa'adah na bin maza kuma kowanne inada tabattaciyar hujja akan hakan, kuma bari kiji ni ce nan nagayawa Abba yayi bincike akan Naja, kuma bincike ya tabattar masa da ba mutuniyar kirki bace, nan gaba in zakiwa dan wani gori ki duba gaba da bayanki ki tabattar bakida abun gorin tukuna, Allah ne ya sa kamin cin mutuncin da kikemin nida uwata, kuma kadan kika gani wallahi, kekuma Nana ingo key din motar kya taho, ni zan hau ta haya in koma gida"
Jalila tayi ficewarta, da sauri Nana ta biyo bayan ta, da kyar ta lallaba Jalila ta hau motar suka nufi gida, harsuka je gida Jalila bata kula Nana ba ta cika tayi fam, suka shiga da kayan siyayyar da sukayi daki, Jalila ta hade rai sosai Nana ta nisa ta zauna a kusada ita
tace
"Jalila nasan zakiji ba dadi abunda nayi miki, na kawoki anci mutuncinki, Jalila nasa ki rakoni ne dan kiga sakayyar hakurin da kikeyi, Jalila me hakuri ba a taba ganin bayansa, duk takurar da sukayi miki abaya zagi da cin mutuci, Amma abun Allah agaban Maama cikin jikin Naja ya zube, Jalila sadaukarwarki da jajircewarki akan samarwa wasu farinciki, Allah baze taba barinki ki wulakanta ba, Jalila duk lokacin da naga hawayenki ina shiga matukar damuwa, amma dayawa kikanyi kukane idan kika kasa samarwa wani farinciki, kokuma wani yayi hurting dinki, amma hakan baya hanaki kokarin ganin kinsa nakusa dake farinciki, shiyasa na kaiki kiga sakayyar da Allah yayi miki akan makiyanki, masu saki zubda hawaye, Jalila ina sarawa kokarin ki, masu irin zuciyarki kadan ne a cikin al'umma, Allah ya dawwamar da haske a cikin rayuwarki"
Jalila ta rungume Nana, tana zubda hawayen da bata da tabbacin na farinciki ne kona bacin rai, tace "Nana nagode da addu'ar da kikayi min, dukda kasancewar su yan uwan mahaifiyarki baki juyamin baya ba, Amma Nana har cikin zuciya ta bana murna da abunda yasamu Naja, duk abunda yafaru da mace daya a society makamancin wannan, gurba cewa ce ta al'umma, da Yaya mairo tayi musu tarbiyya me kyau, Allah ka dai yasan mutanen dazasu amfana dasu, kuma da bazan taba adawa da Aurenta da Yaya ba, Amma ina fatan Allah ya shiryesu, yabasu mafita "
"Ameen Jalila "
Tunda Jalal yayi wannan tafiyar be kara dawowa ba, sedai suyi waya da daddyn sa ko Jawwad, Amma Jawwad yaje sau biyu lagos gurin Jalal, dukkan wani shirye2 suna yinsa ne ta waya shida Jawwad, tunda sukayi wannan rabuwar da Jalila basu kara haduwa ba.
Jalal yayi kalau dashi, bashi da tension sosai, sena tunanin irin missing din Jalila da yayi, 'yan kwanakin da yayi tareda ita, suna shiri ya tsaye masa, amma da zarar ya tuna maganar ta na babu shi babu ita gaba daya se yaji abun duniya ya dame shi, shi kansa yasan Jalila halitta ce me matukar mahimmanci a rayuwarsa, a yanzu yana kokarin yin salloli biyar a rana, dukda ba kowane lokaci yake yinsu akan lokaci ba, yana kokarin yaki da zuciyarsa yaga yayi salla. Amma duk lokacin da yaji abubuwa sun da meshi, yana zama yayiwa kansa caji da giya yadda yakamata.
Sannan Jalal yasaka a nemo masa Hannah duk inda take, se yaga waye gatanta, dan yayiwa kansa alkawarin se yasa an ladabtar da ita, seta gane shiba sa'anta bane da zatayi masa hauka.
Bangaren Jalila ma tana son sanin halin da Jalal din yake ciki, tana son sanin ko har yanzu yana shaye2? Wace irin rayuwa yakeyi zamansa a lagos? Tana tausayin Jalal sosai, musamman idan ta tuna da labarin rayuwarsa da kuma amanar da Antynsa ta bata, ko ba komai dukda fadan da sukeyu takan tuna Alkhairan sa, Amma da ta tuna abunda Mummy da Ilham sukayi mata, gaba daya se ranta ya baci, se taji bata sha'awar kuma shiga shirgin rayuwar Jalal, dama saboda Jawwad suke haduwa, in Jawwad yayi Aure ko ganinta baze kara yiba balle mahaifiyarsa ta zargi wani abu.
Rana bata karya, sedai uwar diya taji kunya inji hausawa, Duk abunda aka sama sa rana inda rai da lafiya zezo, Shirye2 sunyi nisa game da wannan bukukuwa da wadannan iyalai ke tun kara, Jawwad yayiwa Hanan saiti uku na kayan lefe, be cika mata tarkace ba, sedai yazuba mata kaya masu matukar tsada da kyau, haka Nana ita set hudu mahmud yayi mata, itama an zuba mata dukiya (kunsan family su Jalal akwai masu gidan rana) gaba daya kayan lefen bauchi aka kaisu, a can aka karba kayan, na Abdallah ma aka kai kaduna gidansu siyama, gaba daya Basa zama, koda yaushe Hanan tana yawan zuwa kano saboda siyayyar biki.
Duk wani shirye2 Jalila ce kan gaba gurin tsara yadda abubuwa zasu gudana, An shirya gaba daya bikin zasuyi shi a garin bauchi ne.
Saura sati daya a fara biki, su Nana suka tafi garin bauchi inda acan za'ayi dukkan wata hada2 ta biki,
Jawwad da Jalal tare suka je har maiduguri suka kai musu katin bikin Jawwad, dama ga abun dai2 da bikin Nana, rabon da Jalal ya taka kafarsa garin maiduguri har ya manta, Amma bisa ga mamakinsu sega Jalal, dangin Daddy sunyi matukar farincikin ganin Jalal, ya nutsu ba kamar da ba, yasa manyan kaya hada hula, gashi suka samu labarin har aiki yake, sunyi farincikin ganin sa, sun samu kyakyawar karba daga dangin Jalal, dama Jawwad ma dan gida ne, seda suka kwana biyu a garin maiduguri suka wuce bauchi shida Jawwad, sam Mummy bata san batun Jalal yaje maiduguri ba.
Ayi hakuri yau typing babu yawa, nayi busy sosai ne

Shirye2 sunyi nisa sosai ana ta hada2, za'a shiga satin biki, Jawwad da Jalal sun kwana biyu a bauchi suka koma kano domin rabon invitation ga abokan Jawwad, Amma har suka tafi Jalila basu hadu da Jalal ba, duk inda amare suka shiga Jalila na biye dasu, tare sukaje gyaran kai, da kunshi na amare, hatta gyaran jiki da Jalila ake, se sheki take kamar itace Amaryar, in kaga yadda take zakewa kai kace itace amaryar, Ana gobe za'a fara bikin 'yan uwansu Jalal daga maiduguri suka zo (dangin su Mahmud) lokacin da suka zo su Jalila sun tafi gurin kunshi, tunda suka zo Antyn Jalal ke cigiyar Jalila, Amma aka sanar da ita sun tafi gurin kunshi, guri na mussaman aka tanadarwa dangin mijin Nana. Ana gobe a fara bikin su Jawwad suma suka dawo shida Jalal, duk inda zashi kafarsa kafar Jalal.
'yan uwa wanda sukazo daga wasu garuruwan, Inna ta dinga nuna musu Su Jalila Da Nana, tana gaya musu ga' ya'yan da jikokin kanwarta.
Yaya mairo kam da zuri'ar ta kaf babu
wanda yazo taron nan, sedai sauran 'yan uwa da abokan Arziki.
Se dare su Jalila suka dawo daga gurin kunshi, kallo daya zakayiwa fuskar amaren zaka gane yadda suke cikin farinciki, gashi sun dau kyau Masha Allah, suka tafi part din Anty fido a can suke kwana saboda estate din ya fara daukar harami da baki, kasancewar daddyn Hanan babban mutum ne asanshi sosai. Hakama Abba yanada mutane sosai, ga dangin su Jalal, dan haka estate din cike yake da mutane.
Koda su Jalila sukayi sallar magariba, Hanan tace
"gaskiya sena kira Haidar yazo ya ga kunshin nan"
Jalila tace
"ke zumudin me kikeyi? Kwana nawa ya rage?"
"dan kwana nawa ya rage, se indena kula dashi? Se yaga kunshin nan, in yamasa ayi biki da shi, in yace be kyau ba a dirje shi a daren nan"
Gaba daya sukayi dariya, Nana tace
"ni dama muna gurin kunshi Mahmud yacemin; sunzo dazu suna tareda su Yaya Abdallah, ina son mu hadu da shi, inji ko yaci Abinci?"
Jalila kallonsu kawai take tana murmushi, tana mamakin ya sukeji a ransu game da soyayya haka? Ita dai tasan tana son Ahmad, Amma bata tunanin zata iya wannan rawar kafar akansa kamar yadda su Hanan sukeyi, ko lokacin da take son Yaya Jawwad bata tunanin zata iya abunda su Nana sukeyi, tana kallonsu suka canza kaya, sukayi waya da su Yaya Jawwad suka fice babban palourn part din.
Itama sallolinta tayi, tai wanka ta canza kaya, ta samu ta nutsu tana cin Abinci, ta nayi tana chatting da Ahmad, yana ta mata magiya akan ta fito yana son su hadu amma taki, se wasa take masa da hankali.
Maama ta kira Jalila a waya tace taje main part ana neman ta, haka ta tashi ta tafi, da ita so take ta samu ta kwanta ta dan huta, ta fita ta kofar kitchen yadda su Hanan bazasu ganta ba.
Koda taje, da kyar ta gano Maama saboda cikar da akayi a gidan, Maama tace
"dangin mijin Nana ke nemanki, Antyn Jalal tunda sukazo take cigiyar ki fa"
Jalila tace "Ai ban san sunzo ba, suna ina?"
Maama tayi mata Jagora har masaukin da aka basu, Jalila na shiga Antyn Jalal ta fadada murmushinta tace " 'yar halak taki ambato, tun dazu nake cigiyarki"
Cikin fara' a Jalila tace
"Anty sannunku da zuwa, munje gurin kunshi ne shiyasa, ya kukazo? Ya hanya?"
"Alhamdilillah Jalila, Allah yasanya Alkhairi, ya kaimu lokacin naki Auren, kalli yadda kike sheki kamar Amarya"
Sunkuyar da kai Jalila tayi, alamun kunya, ta gefen Antyn ce tace
"Masha Allah itace Jalila kenan, kai Jalila Allah yasaka miki da Alkhairi, muna godiya da nuna kulawarki ga danmu, last week sega Jalal a maiduguri, babban farinciki danayi, wai aikin dayake ta silarki aka same shi, mungode Jalila"
Gaba daya Attention din sauran da suke dakin ya dawo kanta, wasu suna magana da hausa wasu nayi da yare, suka dinga yi mata Addu'a, tarasa Addu'a mema suke mata haka? Kamar wadda ta basu wata gagarumar kyauta.
Dangin Jalal suna da matukar kirki da karamci, nan Antyn Jalal ta dinga nuna mata dangin Jalal, tana gaya mata kowacce mecece a gurin Jalal, 'yan gayune, kuma kallo daya zakayi musu kasan suna hutawa, gasu kyawawa abunda ta lura da shi shine, gaba dayansu babbar shedar da zaka gane family dinsu da shi, shine wannan dogon hancin irin na Jalal, mazansu da matansu haka suke kayan dogon hanci, Kamar sun saba da Jalila suka dinga yi mata hira, gaba daya Jalila jinta take a takure, Anty ta lura da hakan dan haka tayiwa Jalila sallama, tace seda safe.
Jalila na fitowa tana sauri takoma part dinsu ta hadu da Yusuf a hanyar shiga babban parlour, yace
"Yawwa Alhamdilillah, naji dadin ganinki a yanzu, zomuje kimin wani dan aiki"
Jalila tace
"to Yaya" yana tafe tana binsa a baya, ya shiga inda ake ta hada2 dafa Abinci, ya dakko wani kwando da manyan warmers akai da plates, da spoons da serving spoons, yabawa Jalila ta karba ta rike, shikuma ya dakko cartons na ruwa da lemuka, yace
"muje Bakinmu nasa akayiwa girki, dare yayi Abinci ya kare
" Jalila ba tace komai ba ya shiga gaba ta biyo bayansa, wani part din suka nufa, ita
bata taba sanin da gurin bama, saboda parts din da suke bangare daya na estate din ma dayawa, tundaga waje harabar part din ake iya juyo hayaniya na tashi da dariya na 'yan maza, Yusuf ya shige gaba yasa hannu ya bude kofar ya shiga, ya juyo ya ce mata
"Shigo Jalila"
ba musu ta bishi da kayna a hannunta, kallo daya tayi musu ta sauke kanta, mazane sun kai su bakwai a cikin palourn, inma basu fiba, dan haka duk taji ta takura, kanta a sunkuye ta dan risina ta gaishesu, suka amsa mata gaba daya, dayan yace "A'a wannan kaman Hanan"
Taji muryar Abdallah yace
"Ba Hanan bace, sister dinta ce, Amaryar Ahmad to be"
Ahmad yace
"Tun dazu nake magiya ki fito in ganki kika ki, cikin sa'a sega Yusuf ya kawomin ke, amma dan mugunta ya hadaki da wannan kayan nauyin, memakon shi ya dakko"
Sunkuyar da kai Jalila tayi tana sauke kwandon hannunta, Yusuf yace
"Au ban maka abun Arziki bako? Nida yakamata ka godemin"
Ahmad yace
"nina isa in fadi haka, ince bakayi min abun Arziki ba, Kamin abun Arziki sirikina, wallahi Yusuf ji nake kaman a daura namu auren nida Jalila" ya dan kalli Jalila yace
My Queen yakamata muyiwa Daddy magana, yadda kikayi shar dake haka kamata yayi kawai muma ayi namu"
Jalila ta sunkuyar da kai cike da jin matsananciyar kunya.
Daya daga cikin Matasan yace
"dan banza uban zumudi, dole kayi zaman jiran shekara guda, kacigaba da lallabawa da Ameera, kokuma kayi biyu babu"
Gaba daya kunya suke bawa Jalila, tayi kokarin mikewa domin tabar dakin, ta mike kenan kawai idonta ya sauka ana Jalal da tunda ta shigo bata kula da shi ba, farar Jallabiya ce a jikinsa fara kal, sumar kansa ta sha gyara se sheki take, watanni hudu kenan bata ganshi ba, amma ya kara kiba, gaba daya ya tattara hankalinsa akan danna waya da yakeyi amma gaba daya idonsa akan Jalila yake, yana mata wani irin kallo da takasa gane na menene? Tuhumace, kokuwa meyake nufi?
Muryar Abdallah taji yace
"Queen kin san kuwa ranar dinner, Siyama zasuzo ayi dinner anan, ranar daurin aure in angama da nan, zamuje kaduna a can gidansu za'a daura namu"
Cikin sakin fuska ta juyo tace "Dagaske Yaya Abdallah, zanga Siyama? Rabon da in ganta tun ranar dana bar kaduna"
Ahmad yace "tasan Amaryar taka ne?"
Abdallah yace
"tabdijan Aminiyarta ce ta kuruciya, wadda take Jawa duka, kai Jalila ai an girma an dena neman magana, Siyama tana bani labarin wahalar da ta sha saboda ke, gaskiya badan badan ba sena rama mata"
Jalila ta dan zumbura baki sannan tace "Seku rama din ai"
Ahmad yace "Ka rama me? Munci bulus ko queen?" ta dan jinjina kai tana murmushi.
Koda aka bude warmers din nan, jallof couscous ne, ya sha nama da kayan vegetables, ta dan kalli Jalal ta kalli Abincin tasan Jalal baya cin Couscous kome zeci oho?
Kai bazakace Jalal yayi existing a dakin nan ba, duk hayaniyar nan da'ake yi, kala bece ba, shida kujerun gurin kusan daya, dan ko uffan baya cewa, ko abun dariya sukayi fuskar nan tasa murtuk take babu alamar wasa.
Kallon da yake wa Jalila gaba daya yasa ta tsargu har taso ta diricice, dan haka tace "seda safenku"
Ahmad yayi farat yace
"tsaya in rakaki
zamuyi magana"
Yusuf yace
"Sena gayawa Amira, wannan rawar kan da kake yi"
"Karka fasa gaya matan"
Jalila ta nufi hanyar fita, dan gani take kaman Jalal ze iya tashi ya dizgata agaban mutane, tana kokarin wucewa tayi tuntube da kafar Jalal kasancewar ya mike kafafunsa kuma takusa da kafafunsa zata wuce, ga shi a rude take dan haka ta kusa faduwa, Allah ya temaketa bata fadi ba tace "Subhanallah" shikam Jalal ko a jikinsa dan ko kallon inda take beyiba, Ahmad yace
"Haba ya haka? Kana kokarin nakasa min mata, ka baje kafafunka akan hanya, at least yakamata ka bata hakuri"
Wani irin kallon baka isaba Jalal yayi masa ya maida kansa kan wayarsa ya cigaba da abunda yakeyi, ba tare da ya furta koda harafi daya ba Jalila tace
"No karka damu, base yabani hakuri ba, wannan ai besan yayi laifi yabada hakuri ba, da na fadi kafar zan take inga ta tsiya"
Kallon da Jalal yayiwa Ahmad ba karamin batawa Yusuf rai yayi ba, dan da'a waje ne wani civilian din yayi musu haka, seya gane shayi ruwane, shibe ma san daga Ina wannan mugun dan jiji da kan yake ba.
Abdallah yace
"Yusuf kabi a hankali, wannan da kake yabata hakuri, in yaso se ya hana abaka Auren nan, sirikin kane ka bishi a sannu, yayan Mahmud ne daze Auri kanwarku Nana, kuma babban Aminin Jawwad"
Yusuf yace
"wannan din"?
"Kwarai Shidin"
Jalila dai ta fice waje, Ahmad ya biyo bayan ta,
"Jalila wai me wannan mutumin yake takama da shine da yakewa mutane kallon basu isa ba??"
Jalila tace
"ba kallon mutane basu isa bane, haka yake, haka halayarsa take, ka lura ko Mahmud da yake kaninsa baya kulashi sosai, Yaya Jawwad da Abdallah kawai yake shiga shirginsu"
"Amma meye hadinki dashi da ze dinga kallonki haka?"
"Ba wani kallona da yake, kaika ga hakan, bani da Abunda Jalal ze tsaya kallo, A lissafin Rayuwarsa baya shiga shirgin mata, koda 'yan uwansa ne, muna gaisawane kawai saboda Aminin Yaya Jawwad ne"
"Kai queen, duk taurin kai da dagiyar namiji, baze iya dauke kai akanki ba, Amma me ya kai Jawwad abota da wannan bahagon mutumin". "Amintarsu hadin Allah ce"
"to shikenan, abar maganar ya gajiya,? naga kunshi ki yayi kyau, kamar in saceki in gudu"
Murmushi tayi tace
"Tabdijan kaida Daddy kuwa, inka gudar masa da 'ya"
Haka suka cigaba da hira, ya rakata har kofar part din Anty fido, sannan ya koma.
Tana shiga part din tabi ta babban parlour, bakowa a ciki ta nufi makwancinsu, tana shiga Hanan ta kalleta tace "daga ina haka?"
"Naje cikin gida ne, Yaya Yusuf yasakani aiki" Hanan bata kuma cewa komai ba, Maimakon su kwanta suka zauna sukayi ta hira, seda suka raba dare sannan kowacce ta nemi guri ta kwanta.
Washegari yakama ranar daza'a fara biki, ranar ne za'ayi kamu, iya mata da yamma, ko Angwaye bazasu gurin ba, iya mata ne a gurin kamun, , a wani katafaren dakin taro,
karfe biyar na Yamma, Amare suka iso dakin taron sanye da shiga irin ta fulani, Suka fito a ainihin usulinsu na fulani, 'yan matan ma, duk kayan fulani suka sa, se manyan iyaye da suka saka Atamfar anko na kamu, karshen haduwa kam sunyita ba' a magana, Sunyi kyau, Amara kirjin biki ma wato Jalila tayi kyau, ammata simple make up, gashi anmata ado da gashin kanta, sosai kayan suka karbeta, Anyi raye raye, anci an sha, an lika kudi, anyi hotuna da 'yan uwa da abokan Arziki, anyiwa Amare kamu, ba' a tashi daga gurin ba se karfe goma na dare, motoci sukazo suka kwashesu zuwa gida. A motar Ahmad Jalila ta koma gida, Jalila banda motar Jalal bata taba hawa motar wani ba se Ahmad, suna tafe yana yaba irin kyawun da tayi. Da suka koma gida ma a idon Jalal suka dawo, Jalila tayi kyau se hirarsu suke ita da Ahmad.
Tunda suka koma, Jalila bata tsaya tabi takan kowa ba, ta tafi part dinsu, Mummyn Hanan ce tazo ta samesu a dakin da suke zama, tace "Kuyi maza kuzo, Uwar mijin Nana tazo, kuzo muje ku gaisa"
(wato Salma uwargidan daddyn Hanan)
Jalila najin haka tace "nima bari in biku"
Ko kayan basu canza ba, suka bi bayan Mummy.
Koda suka shiga masaukin da'aka bawa Maman Mahmud kamshin turare ne ya gauraye dakin, tana zaune akan kujera, Jalal na zaune a kusa da ita, se wasu 'yan mata, da kuma Antyn Jalal tana salla, da alama hira sukeyi da Jalal, kamarta daya da dan nata Mahmud, haka kuma tana dan yanayi da Jalal din, suka shiga da Sallama, ta dago cikin fara' a ta amsa, Mummy Hanan tace "to Hajiya Salma ga yaran naki nan, sune Amaren"
Ta kallesu daya bayan daya, ta kalli Nana tace "ga sirikar tawa nan, ita nasan ta ai"
Sukayi murmushi suka durkusa suna gaisheta.
Jalal ya kalli Jalila tayi kyau sosai, Se murmushi takeyi, Hajiya Salma tace "Jalila baki sanni ba ko?"
Jalila ta Kalle ta ta jinjina mata kai, Hajiya Salma tace
"ni na sanki ai, kamar ki daya da mamanki, Amma kuma kusan duk kamaninku daya keda Amaren"
Jalal ya juya harshe sukayi magana da Hajiya Salma.
Nan ta shiga yi musu Nasiha akan Aure, da mahinmancin biyayyar Aure. Tana cikin yi musu ne Maama ta shigo, ta kawowa Hajiya Salma Abinci, nan suka hadu aka cigaba da yiwa Amare nasiha, Jalila kam ta kame tana sunkuyar da kai sekace itace Amarya. Jalal ma yana kusada Hajiya Salma ake musu wannan fadan, ko a jikinsa, be kula Jalila ba haka itama bata kulashi ba, tsakanin ta da shi se kallo.
Jin da Jalila tayi Hajiya Salma tana bayani da manyan bakake, Mummy Hanan ba ruwanta suka dinga yiwa amare fada, da koyar dasu zaman takewar Aure, ba shiri Jalila ta mike zata fice, Maama tace "Ina zaki kuma?"
"Amm... Zanje inci Abinci yunwa nakeji"
Sosai Jalila ta bawa Hajiya Salma dariya,
Tace
"dawo ki zauna, ina da magana dake dama" shiko gogan har akayi aka gama ba inda yaje yana zaune, daga karshe ma Abincin da aka kawowa Hajiya Salma ya zuba yafara cin Abunsa.
Yadda
Jalal yake wa Hajiya Salma kamar irin dan Autan nan nata, kuma ga dukkan alamu tanaji dashi.
Seda aka gama yiwa su Nana fada, Aka sallamesu amma tace Jalila ta tsaya, suka tafi Maama ma komawa tayi, dan Akwai Ayyuka sosai a gidan, Maama na fita Jalal yabi bayanta, yace dan Allah yanaso a bashi tea.
Ya rage daga Jalal se Mummyn Hanan, Jalal da Hajiya Salma.
Hajiya Salma tace "Jalila me dana yayi miki ne?"
Jalila ta kalleta da alamar bata gane ba.
Hajiya Salma tace
"ABDUL JALAL mana babban dana kuma
an Auta, kince bake ba shi, me yayi miki ne? Ba laifinsa bane, nasani laifin Mummyn sa ne, Amma kiyi Hakuri, Daughter Jalal yana jin maganar ki fiye da yadda kike tunani, Jalila Taimakon Rayuwar Jalal kike, Jihadi kikeyi, Allah ne kadai ze biyaki, karki duba abunda mutane zasu fada, kedai kiyi dan Allah, duk yadda muke da Jalal bana masa fada, idan nayi masa fada se yafara gaba dani ko wayarsa na kira baze daga ba, Amma da yake Allah ba yadda baya lamarin sa, kinga dake da Jawwad, musamman ke yanajin maganar ki, ban san me kikayi masa haka yake jin maganar ki ba" tai maganar cikin zolaya, sannaan tace
"Naji dadin ganin cigaban da aka samu a rayuwarsa ta bangarenki, ko danginsa babu wata wadda yake sakewa da ita kamar ke, yana jin maganar ki dukda shirin naku na Tom and Jerry ne"
Jalila ta sunkuyar da kai, Mummyn Hanan tace
"gaskiya nima yadda na lura da shi, baya son. Mutane sam, mussaman ranar da suka je mana can Kaduna, Amma dukda haka a nutse yake". Hajiya Salma tace
"Wallahi sister badan kaddarar Rayuwa da ta faru da shi ba, yarona mutumin kirki ne, ki tambayi Jawwad kiji, Wallahi banga abunda bazan iya mallakawa Jawwad ba saboda dawainiyar da yayi dashi ba"
Mummy tace
"ke kika haife shine?"
Hajiya Salma tai murmushi tace
"Dan ex-husband dina ne?"
Zare ido Mummy tayi "Haba dai, duk abun nan bake kika haifeshi ba?" sukayiwa Jalila nasiha sannan, Hajiya Salma ta sallami Jalila, sannan suka cigaba da hira ita da Mummyn Hanan.
Tunda Hajiya Salma tazo, duk abunda take bukata sedai ta kira Jalila, duk inda zatayi kuma seta kira Jalila, kamar dama can sun san juna, Mafi yawan tattaunawarsu akan yanayi na Rayuwar Jalal ne, Sosai Hajiya Salma taji kaunar Jalila a ranta, Jalila tanada biyayya, da girmama mutane, ga kuma namijin kokarin da take akan yaransu Jalal.
Washegari yakama ranar daza'ayi dinner, tun safe ake shiga ana fita a gidan nan, gida yacika da mutane,
Shabiyun Rana Siyama ta iso itads 'yan uwanta, Labari na ishe Jalila Siyama ta karaso aids gudu ta nufi cikin gidan tana zuwa suka Rungume juna, Maama tace
"Jalila kiyi a hankali, karki ji mata ciwo mana"
Jalila tace "Siyama ta, dama zan kuma ganinki?"
Siyama tace "gani kuwa kin ganni" Jalila ta janye Siyama, Zuwa bangaren Anty fiddo, Hanan Ma na ganin Siyama ta rungumeta itama tace "Na dauka tun ranar kamu zakizo, Amma shine baku zoba se yau"
Siyama tace "Ai muma munyi kamu da party a can ne, saboda wanda bazasu samu damar zuwa nan ba"
Suka gabatar da Siyama ga Nana, dan
basu san Juna a zahiri ba, Amma sukanyi waya saboda Jalila,
"Nana tace, Sannu da zuwa Siyama, ya hanya?"
"lafiya kalau Nana, ya taro?"
"Alhamdilillah"
Suka zauna suka dinga hira, suka shantake a gurin, suka dinga hira suna tuna kuruciya da shiritar da sukayi, Nan Jalila ta dinga basu labarin Artabun fadanta da Jalal, har lokacin daya taba yi mata duren hayakin taba. Sunsha dariya, Nana sam bata san rashin jituwarsu ta kai haka ba, Amma bata gaya musu fadi tashin da ta dinga da kokarin ganin ya shiryu ba, har labarin su Hannah da Jeje bata gaya musu ba. Suka shantake suna ta dariya.
Anty Fiddo ta shigo ta samesu a zaune suna hirarsu suna ciye2, kaman karsu rabu, Anty fiddo tace
"waikuna nan a zaune, kamata yayi ku hanzarta ku fara shiri, ku tafi gurin kwalliyar nan, kar a bata lokaci" seda ta kai aya ta lura da Nana, taana ganin Siyama
"Tace Amryarmu, gaskiya Abdallah ya iya zabe, Jalila ke Alkhairi sanadiyar kawancenki da Hanan, mun gano 'yan uwanmu, kuma sanadiyar ki Abdallah yayi mata shima, Allah ya kaimu Aurenki da Ahmad"
Hanan tayi farat tace
"ba Ameen ba"
Anty fiddo tace
"Saboda me?"
"nifa bana son Auren ta da wannan Yaya Ahmad din wallahi, matarsa bata da mutunci, wannan Ameeran tab, ni wallahi bana son Auren su"
"ina ruwana da rashin mutuncin matarsa, dai dai da ita nake, ai dani ze zauna ba dake ba"
Siyama tace
"Nikam Jalila ina Jalal, ina son in ganshi"
Tsaki Jalila tayi tace "ina nasan inda wani Jalal yake"
Hanan tace "Karya takeyi, yana nan Haidar ya gayamin, suna tare"
Nana tace "Too Siyama kema kin san Jalal, ai dole ki ganshi, nasan watakila anjima yaje gurin dinner zaki ganshi"
Anty fiddo tace "kunga abar surutun nan haka, ku tashi ku fara shiri"
Haka su fara shirye2, karfe hudu suka tafi gurin kwalliya.
Karfe tara na dare Jalila tana tareda Amare an musu kwalliya me daukar hankali, kayansu iri daya, sea green din material, da takalmi da purse, Jalila kuma tasaka blue-black na material kaman yadda shine yazama ankon dinner, Tasaka bakin takalmi da jaka, jikinta babu mayafi, Su Jalila ne 'yan shigo da Amare, masu shigo da amare kowacce gefenta da namiji da, Amare da Angwaye, Jalila Ahmad ne a gefenta, suka shigo da Angwaye, ana musu hotuna tareda likin kudi, suka kai su har kan high table, nan aka tsaya aka fara hotuna, Ba zato ba tsammani Jalila taga Jalal, sanye da shaddarsa coffee colour, me tsadar gaske, ta sha aiki da bakar hula da takalmi sau ciki, tsinstiyar hannunsa dauke da wani dankareren Agogo, fuskarsa ba yabo ba fallasa, ya durkusa gefen Jawwad yana masa magana a Kunne, nan aka shiga hotuna 'yan uwa da abokan Arziki, Jalila anyi hotuna da ita ba Adadi, nan Hanan ta nunawa Siyama Jalal,
Siyama tace "Yadda Jalila ke masa rashin mutunci bazakace haka yake ba, hadadde dashi" sukayi dariya
ba karamin kyau Jalila tayi a idon Jalal ba, Amma ganinta ba mayafi yasa duk yaji ransa ya baci.
Nan aka fara gudanar da taro kaman yadda aka tsara, dukkan bangarorin sunyi bajinta gurin lika dukiya kaman ba'a san dadinta ba, Hajiya Salma ba'a barta a baya ba gurin yin wannaan hidimar, tunda ta hau kan stage Jalal ya fito ya dinga lika mata kudi, kamar be san ciwonsu ba. Aka dinga mata kirari, ko Mahmud da ta haifa bata masa likin da tayiwa Jalal ba, ta koma gefe, takira Jalila tasa me hoto ya dinga daukarsu hoto itada Jalila da Jalal.
Hakama Sunsha hotuna Jalila da Maama, Jalila tayiwa Maama likin kudi sosai ta dinga rungumeta suna hoto a wayar Jalila, kamar ba Maaman da take gallaza mata ba.
Lallai halayar Jalila daban take, sam bata riko.
Aka jima M. C ya kira Amare da Angwaye kan stage, suna dan takawa, yasaka wakar da Jalila ke matukar so, dan haka stage din nan ba kowa se Amare da Angwaye, Jalila ta fito, tafara Rawa itada
Su Hanan Jalila Rawa take me cikeda daukar Hankali, ba wani girgiza jikinta take ba, Amma ta dau hankalin mutane, Ahmad ya fito ya dinga mata barin kudi, ana musu hotuna.
Jalal ya kai karshe a bacin rai, Ga jikinta ba mayafi, ga dinkin yayi fitting dinta, gata tubarakallahu tana da diri me daukar hankali bawata rawa take ba, juyi kawai take Amma Jalal ya kule musamman yadda Ahmad ke mata barin kudi, yana mata wani irin kallo, wayar Jalila ce tafara ringing dan haka ta sakko daga kan stage din ta fita daga hall din domin amsa wayar, tana fita Jalal yabi bayan ta.
Tofa Fans Oga Jalal ya dau Zafi, A tunanin ku mezeyiwa Jalila?
Nayi muku dogon typing dan haka ina bukatar Comments
ABDUL JALAL NOVEL FANS GROUP
My Love for you is endless, daku da masu bina pvt da masu karanta littafin duk ina godiya Allah yabar kauna, ina sonku kaman yadda kuke nunamin kauna

Follow me onWatpad @Ayshercool7724

Daddyn Jalal ne a tsaye da yana rataye da 'yar karamar Jaka, da alamu zeyi tafiya ne, Mummy na kan three seater ta kalmashe kafa tana danna remote. Daddy yace
"wai dagaske deeja bazaki bikin nan ba?"
Ya tsina fuska tayi tace
"Nifa bana son yin doguwar tafiya inba a jirgi ba kasani, kuma me zanje inyi musu, banda jaraba ayi biki a inda suke sun kwasa sun tafi wata uwa bauchi biki, ko meye amfanin hakan oho?"
Daddy ya samu guri ya zauna yace
"deeja, in duniya da gaskiya be kamata kiyi haka ba, duk gudunmuwar da Jawwad ya bawa Rayuwar danki, ga tsawon lokacin da kika dauka kuna makotaka, ga harkar kasuwanci da kikeyi da mahifiyar yaron nan, sannan koba komai kema Mahmud danki ne, shima kodan shi bazaki ba? "
"daddy a dawo lafiya, ka musu Allah ya sanya Alkhairi in sun dawo na musu Allah ya sanya Alkhairi, bani da lafiya bazan iya zuwa ba, ka tabattar sakona ya isa gurin Jawwad"
Ta juya ta cigaba da danna remote, haka ya mike ya fice daga palourn tabi bayansa da harara.
Ya fita ba dadewa sega Ilham ta fito daga dakinta, tazo ta samu guri kusa da Mummy ta zauna. Ji tayi Mummy tana tsaki ta dan kalleta tace
"Mummy lafiya kuwa?"
"barni da abun haushi, daddy ze batamin rai, wai se in bishi bauchi gurin bikin nan, ta yaya zanje gurin da Salma zata, ana Auren danta inje, ai na gama zubewa, ba dan ita ba da kodan Jawwad senaje bikin nan, Amma saboda Salma da wannan banzar yarinyar bazani gurin nan ba, Amma bayan biki har can Abujan zanje gidan Jawwad in masa Allah ya sanya Alkhairi, yanzuma na bawa Daddy sako ya bashi, Amma ai naga ke kawar Nana ce, meyasa baki bisu ba? "
Ya mutsa fuska Ilham tayi tace
"Tabdijan akan me zanje, Ai daga baya na gane da hadin bakin ta Wannan banzar take son janye hankalin Yaya Jalal daga kaina, dan haka ba abunda zanje in musu, suje can su karata"
Haka suka cigaba da hirarsu, Ilham na kara kushe Jalila a gurin Mummy.
Jalila Tana fitowa daga hall din ta samu jikin wata mota ta tsaya tana waya, Ahmad ya kirata, tasa wayar a kunnenta tace
"Hello my, ina jinka" ba"a iya jin me ake cewa amma tace "Shikenan in an nagama zan maka magana se mutafi tare" ta dan kumayin shiru tace "A'a idan na koma gida zanci Abinci, bazan iya cin Abinci yanzu ba, in aka tashi zan maka magana"
Ta kashe wayar, tana juyowa taji gabanta ya fadi, Jalal ne a tsaya a bayan ta, ya kura mata ido ko kyaftawa ba yayi
Dan tsayawa tayi itama tana kallonsa, tunda yazo ko sannu bata hadasu ba, ba karamin kyau manyan kaya sukeyi masa ba, gashi gaba daya ya cika gurin da kamshin turarensa, tayi kokarin bin ta gefensa ta wuce, ya kara tare mata hanya, dagowa tayi tana kallonsa ya hade rai kamar be san meye dariya ba yace
" Zoki wuce mu tafi"
Tai masa kallon ban gane nufinka ba tace "Kamar ya, mu tafi ina?"
"ban sani ba, ki wuce mu tafi nace" yayi maganar cikin fushi"
Zumbura baki tayi, tace
"Wallahi ba inda zani ba'a gama ba" yasan halinta da taurin kai, dan haka yasa hannu ya janyo ta har tana kokarin faduwa saboda takalmin ta me tsinine, ba shiri tabi shi be tsaya da ita ko'ina ba se gaban motarsa, ya bude motar yace
"Shiga"
ta kalleshi, cikin muryarta me sigar shagwaba tace
"meyasa zan shiga? Ina zaka kaini kowa yana can ana abun Arziki"
"Wallahi in baki shiga ba zan sakaki da kaina"
Zare ido tayi ta kalli idonsa, babu alamun wasa a abunda ya fada tabbas ze aikata, ba shiri ta shiga motar, ya za gaya ya shiga ya kunna motar, yafara tuki cikin nutsuwa ya bar harabar gurin, yafara tukin kenan aka kirashi a waya, ya daga wayar yasa a hands free, da'alama abunda ya shafi aikin suke tattaunawa shida wanda ya kira shin, dukda zuciyarta a kule take da haushi, Amma bayan ya gama wayar tace
"Ya Aikin kuwa?"
Kamar jira yake tayi magana yace
"ban sani ba, bakida kunya, saboda ke na tafi aikin nan for almost four months baki nemeni ba, Rayuwa ta kaman wanda yake cikin rijiya ne yake neman taimako, kin mikomin abu ina kokarin fitowa kin saki nakoma ruwa, dan kinga ina lallabaki kikemin wulakanci ko? "
" ni wani wulakancin nayi maka? Mekake so in maka kuma? In cigaba da bibiyar ka mahaifiyarka tana min kallon mazinaciya? Da kazo garin nan kana kallona shekaran jiya, har kusa faduwa nayi saboda dalilinka, ko kallona bakayi ba, so kake inta binka, kokuma goyaka zanyi? Ni kawai ana can ana Ta shagali nikuma ka dakko ni, duk gurin nan nika dai na tsole maka ido, ga Ahmad ma yama jirana, yanzu se yayi ta jirana, idan ya tarar bana nan bazeji dadi ba"
ya lura gaba daya a fusace take, yai mata shiru taita mita, yadda Jalila ke kuma fadar Ahmad yafi komai bata masa rai, dan haka yaja wani uban birki a kan titi da seda ta firgita, ya juyo yana kallon ta, ya matso da fuskarsa daf da tata, har suna jin numfashin juna, Jalila najin saukar numfashinsa a fuskarta, gaba daya Jikin Jalila ya hau rawa, taji numfashinta na kokarin tsayawa, gaba daya kamshin turarensa ya cika mata hanci, ga kuma wani mugun kwarjini da yayi mata, cigaba da matso da fuskarsa yake daidai tata, har dogon hancinsa na shirin taba nata, rintse ido tayi sosai jikinta na cigaba da rawa.
A hankali ya dauke fuskarsa, yace mata
"stop shivering, kina tunanin wani abun zan miki? Ba abunda zan miki, sedai ina kokarin nuna miki illar shigar da kikayi ne, look at yourself,"
Jin abunda ya fada, Yasa A hankali ta bude idonta tana cigaba da sauke numfashi.
Ya kuma kallon ta yace
"kalli jikinki babu mayafi, kin hau stage kina Rawa, kowa ya zubo miki ido kina rawa, kalli jikinki, kalli yadda kayan nan suka matse ki, hakan ya dace? "
Kallon kanta tayi, taga yadda rigar ta zauna a jikinta, taga irin yadda Jalal yasata a gaba da kallo, gaba daya seta ji kunya ta kamata, Amma ta maze ta dake, takuma hade rai tareda dauke kanta tace
"Ai dai bahaka na keyi ba, dan dai yau daya, ana biki zaka wani takuramin, naga kai da gajeren wando kake yawo a layi, waye ya dameka?"
Jalala seyayi kamar besan dashi take ba, ya fuskanci rigima takeji, idan ya biye mata fada za suyi a titi, banzan da yayi da ita, hakan ba karamin batawa Jalila rai yayi ba, wayarta ta fara ringing, tasa hannu ta ciro wayar daga jakarta, ta daga wayar tasa a kunnenta, beji me aka ce ba, sedai Jalila cikin shagwaba tace
"please my, na dan fitane yanzun zan dawo Insha Allah, ka jirani semu tafi tare"
Cigaba da wayarta tayi hankali kwance, ta gama tana kokarin ajiye wayar, Jalal yasa hannu ya fizge wayar daga hannunta yace
"Wallahi bazaki koma gurin nan ba"
"Saboda me? Ni gaskiya ka maida ni, wai meye haka?"
"Wallahi kika kuma yi min gaddama, Kano zamu nufa a daren nan, daga nan zuwa a Asuba ma isa kanon, babu abunda yayi min zafi da wani zargi ko wani abu daza'a ce akan hakan, kinsan ni bana gudun magana"
A firgice ta kalleshi, babu alamun wasa a idonsa, he mean what he said, yadda fuskarsa take murtuk din nan, ta tabattar ze aikata abunda yace dan haka taja bakinta tayi tsit, tana kallon wayarta tanata ringing, Amma Jalal ya share, ga shi tana tsoron abunda ya fada, dan ze aikata.
Tanaji tana gani ya maida ita gida, yayinda ana can ana rakashewa, gaskiya Jalal ya kwafsa mata, suna zuwa harabar gidan taga motar daddy, da sauri tace "laa motar daddy yazo"
Nan ma shiru Jalal yayi mata, yana parking ta bude motar ta fice, cikin Sauri ta nufi wata kofa, da ya kasance bangarene da Daddyn Hanan yake saukar manyan baki idan suzo, kamar yadda aka nuna mata.
Tana zuwa ta bude kofar ta shiga da sallama, Daddyn Jalal ne, da Daddyn Hanan sekuma Abba, da wani babban mutum wanda Hanan tace mata baban Yaya Yusuf ne, suka amsa mata cikin sakin fuska.
Tana zuwa ta zauna a gefen Abba, ta kalli daddyn Jalal tace "Daddy sannu da zuwa ya hanya?"
"lafiya kalau Jalila ya taro?"
"lafiya kalau Daddy"
"to Masha Allah, Allah yasanya Alkhairi, Allah ya kaimu naki da rai da lafiya"
Suka amsa da Ameen amma banda Jalila da ta sunkuyar da kai.
Daddyn Hanan yace " 'yar baba, keko ganinki bana yi tunda aka fara bikin nan, ina kika shiga haka?"
"Baba ayyuka ne dayawa, kuma naga baka dawowa se dare"
"Hakane kam, sannun da aiki, Allah ya kaimu naki auren ' yar Baba"
Abba yace
"Baby ya akayi kika dawo ke? Naji ance kuna gurin walima, ina Kika baro Amaren?"
"Suna can ba' a tashi ba, ba Yaya Jalal ne... Bata karasa ba Jalal ya turo kofar dakin ya shigo da sallama"
Shikan sa daddyn sa rabon da ya ganshi wata hudun kenan, ya sha manyan kaya yayi kyau, babban abunda ya daurewa daddyn sa kai be wuce yadda yayi sallama ba kuma ya risina yana gaishesu, suka amsa
Daddyn Hanan yace "ABDUL JALAL ashe kazo, Amma ban ganka ba, bamu hadu ba sam"
Jalal yayi murmushi yace "banfiye fitowa ba shiyasa baka ganni ba"
"Masha Allah, Yaya gurin Aikin na ka?
" Lafiya kalau, ina jin dadin Aikin, Amma nafison zama na a kano, gashi sunce sena kara watanni, bana son zaman lagos din nan"
Daddyn Hanan yace "Nayi farinciki ganinka ABDUL, kayi kalau da kai, me yasa baka son zaman lagos din?"
Daddyn sa yayi murmushi yace "baya son sabga da Mata, kasan kuma lagos babu ruwansu da Addini ko Al'ada, in munyi waya yana gayamin ;shi baya son Abunda matan kabilun nan sukeyi" suka kwashe da dariya, Abba yace "Karka damu Kaji Jalal, kana da gaskiya"
Daddyn Hanan ya kalli baban Yusuf yace
"Kaga yaron dana ce ka samarwa Aiki, Ansamu improvement kwarai a tattare da shi, gaskiya 'yar Baba tana da kai sosai, ita tayi wannan tunanin a samo masa aiki, tace min in aka samo masa aikinyi hakan ze dauke masa hankali da ga barna da yake kuma ya rage masa damuwa da kadaici, a haka gata kaman bata iya komai ba se shagwaba da tsokana amma tafi Hanan kai"
Baban Yusuf yace "ABDUL JALAL karka damu kaji, haka sha' anin Aiki yake, ba inda baya kai mutum, kai dai kayi gaskiya ka rike Addininka kuma kaji tsoron Allah"
Sukace hakane, daddyn Hanan yace
"Karka damu Jalal, za'a san abunyi, babban farincikin danayi, daga can lagos din sun kirani suna yaba maka, naji dadi sosai wallahi, Abunda yake kara shashi shaye2 da wannan phobia din na rashin son mutane,
hadda psychological issues, yana bukatar me jansa a jiki, be kamata saboda halin da yake ciki na shaye2 ayi watsi da shi da lamarin sa ba, kokuma a dinga yi masa mummunan furuci ba, ko mutane su kyamace shi gaba daya ba, kuma wannan yana daya daga cikin matsalar society dinmu, wallahi wanima ko masallaci yaje baza'a hada sahun salla da shi ba, daga haka suke fara janye jikinsu daga mutanen kirki, se na banza su janye su, maimakon a jasu a jiki da nasiha da rarrashi"
Daddyn Jalal ya dan girgiza kai yace
"Wallahi you said it all sir, Jalal gaba daya gudun mutane yake se tsirari, musamman mata, saboda yarasa wani babban jigo a rayuwarsa da duk wanda yarasa dole yayi kuka, shiyasa da Wannan 'yar tawa Jalila da Jawwad banida abunda zan biya su da shi, ko iya haka aka tsaya sun kawo gagarumin sauyi ga rayuwar
ana, bani da bakin godiya, ban taba tsammanin za' a samu sauyi kwatankwacin haka akansa ba"
ya karasa maganar yana kokarin hadiye kwalla da ta taru a idonsa, gaba daya sukayi tsit cike da tausayin Jalal da mahifinsa, Jalal ya sunkuyar da kai, yana tuna Abubuwan da suka shude na rayuwarsa, Ya fuskanci kaddara daban2, gaba daya tausayin kansa dana daddy ya lullube shi.
Jalila kam cikin sanyi jiki, tace
"Haba Daddy, ni me nayiwa rayuwarsa dana cancanci wannan godiyar da kuke tayimin, wallahi banga abunda nayi masa dana cancanci hakaba, ni yakamata in baku hakurin cin zarafin sa dana dingayi a gabanku, nake kiransa da kalamai marasa dadi Amma....
Sekuma maganar ta kasa fitowa saboda kuka, dan Haka ta mike, da sauri tabar dakin.
Shikam baban Yusuf mamaki ne ya cika shi, ace kamar wannan yarinyar ta sauya akalar Rayuwar matashi da ya riga ya dilmiya a gurbatacciyar rayuwa, itakuwa wace irin baiwa ce da ita, ko dayake ance mata 'yan baiwa ne, sedai kowacce akwai sigar da take Amfani da tata.
Jalal yace "daddy seda safenku, zanje in kwanta"
Abba yayi karfin halin cewa "to shikenan Allah ya tashemu lafiya"
Ya amsa da "Ameen" ya mike ya fito kaman wanda kwai ya fashewa a ciki.
Jalila takoma part dinsu ta canza kaya, tayi wanka, har tayi ta fito tausayin Jalal da daddy ne fal a ranta, se goge Hawaye take lokaci zuwa lokaci.
su Hanan suka dawo, suna zuwa suka tarar har tayi bacci.
Nana tasa hannu tasheta, Jalila ta mike zaune tana kallonsu tace "meye kuma na tashi na?"
Nana tace
"ya akayi kika taho ne? Tun a can Maama take nemanki, Ahmad se kiranki yake a waya baki daga ba"
Se yanzu ta tuna wayar tana gurin Jalal.
"Su Abba ne sukazo shiyasa na dawo gida" ta basu amsa
Hanan tace "keda wa kuka dawo, dan nasan baki san hanya ba"
"ban sani ba, uwar kwakwakwafi a isak na dawo"
Hanan tace "daga tambaya? Allah yabaki hakuri"
Siyama tace "Jalila wallahi Jalal ya hadu, kinata masa wulakanci, wani kallo da yake miki kamar ze cinye ki"
Sukasa Jalila a gaba da tsokana tayi musu banza ta kyalesu.
Jalal yana zaune yana ta tunanin abubuwan da suka faru dashi a baya, shi kansa yana sarawa namijin kokarin Jalila, ta iya lissafi gata da himma da kokari, duk rashin kunyarta da taurin kai, akwai kawaici da tausayi, duk zamansa da Jeje besan Cutar shi yake ba, Amma ita a ranar da suka fara haduwa ta gane hakan, ta saka rayuwarta a hatsari da dama saboda shi, besan mezeyi ya saka mata ba" kallon wayarta data ke faman ringing yayi, sunan My yana yawo akan screen din wayar, har wayar ta gaji ta katse, hotonta ne akan screen lock dinta tana murmushi, ya kurawa hoton idon na dan lokaci, ya sa hannu ya shara screen din, wayar ta babu key a kai, wallpaper dinma hotonta ne da Nana, kanta babu dan kwali, ta dan turo baki Nana kuma tana dariya, ya dade yana kallon wallpaper, yayinda kiran Ahmad ya shigo ba'a dadi, ya gaji sa wayar a silent ya ajiyeta ya cigaba da tunani,
Yana cikin tunanin ne, Angwaye suka dawo.
Jawwad beyi mamakin ganin Jalal a gida ba, dan ba karamin aikinsa ne gurin dinner din ma yaki zuwa gaba daya ba.
Gaba daya Ahmad ransa a bace yake yana ta tunanin ina Jalila ta shiga haka? Ya kira har ya gaji amma bata dagawa, kuma ya duba hall din nan be ganta ba, sukayo wa Angwaye rakiya yana shirin fita daga dakin yace
"Jawwad zan tafi seda safe, Dan Allah ko Jalila ta dawo ne ? Nakirata har nagaji bata dagawa"
Jawwad yace
"Aini tunda ta sauka akan stage din nan ban kuma ganinta ba, Amma ka kira wayarta mana"
"Aina kira wayarta ta bata dagawa"
Jawwad yace
"Idan ma ta dawo yanzu nasan tayi bacci, Amma bari in kira wayar ta ta"
Jalal yana jinsu amma be tanka musu ba, Jawwad na kiran wayar Jalila yaji ringing dinta a dakin, da yake yasan tone din wayarta, Jawwad ya kalli inda ringing din wayar ke tashi, tana kan teburin dake gaban Jalal tareda wayoyinsa,
Jawwad ya tafi gaban tebur din, yaga tabbas wayar Jalila ce, Jawwad ya kai hannu ze dau wayar, yace "ya akayi kuma wayarta tazo nan?"
Jalal ya sa hannu ya dauke wayar ya kashe wayar gaba daya yace
"wayar tana gurina, tare muka taho"
A fusace Ahmad yace
"Amma dan wulakanci kanaji ana maganar kayi banza? Meyasa zaka dakko ta? Na lura tunda kazo kake wani jin kai da nunawa mutane gadara, ubanwa kafi? Zaka dinga nunawa mutane jin kai, meye naka na shiga sabgarta? Waye dinta kai? Dama ana fadin kana shaye2 wallahi kamin hauka kurata zansa sumaka duka"
Jawwad da sauri yace
"yi hakuri Ahmad, baka fahimci Jalal bane, shima yayanta ne yana da iko akanta, Bekamata ka dinga wannan maganganun ba, an riga an zama daya"
Zuciyar Jalal wata irin tafasa take, ba dan Dalilin Jawwad ba wannan banzan ya isa ya tsaya gabansa yana zaginsa, dan takamarsa yanada kaki, idan takamar Ahmad kakin soja, shikuma yana da abunda ze siye shi da kakin nasa yasa Aljihunsa
Kawai Jalal ya jingina da kujera ya zaro karan sigarinsa ya kunna yana kada kafa.
Karshen kuluwa Ahmad yayi, wai uban me Jalal ya taka yake wannan gadarar.
Abdallah ne ya shigo dakin da sauri yana fadin "Jawwad ana nemanku a part din daddy, kaida Ahmad"
Jawwad yace "Allah yasa ba wani abun mukayi ba?"
"ba abunda kukayi ance dai in kiraku"
Jawwad yace "Amma a daren nan haka?
" kuzo dai muje, ko menene kwaji a can"
Seda Ahmad yayiwa Jalal wani banzan kallo, yayinda shikuma Jalal yakara yawan hayakin da yake fesarwa a iska, yana lumshe ido Ahmad ji yake da da bindiga se ya harbe Jalal, haka suka fita suka tafi.
Su Jalila kam, babu alamar zasu kwanta yanzu, hira kawai suke suna shewa, Maama ta shigo dakin tace "har yanzu baku kwanta ba?"
Hanan tace
"Wallahi Maama, mun kasa baccin ne, shiyasa muke ta hira"
Maama tace
"lallai kam, ke Nana magana fa ta canza, da mun zata nan da sati biyu zaki tafi, Hajiya Salma tace; dake zasu tafi maiduguri, visar ki ta samu, in aka daura Aure gobe in Allah ya kaimu ranar Asabar zaku tafi maiduguri, litinin zaku tafi can England keda Mahmud, dan haka za'a kawo miki kayanki da zaki tafi dasu, bayan kun tafi"
Take jikin Nana ya hau rawa, cikin rawar murya tace
"Maama litinin fa, yayi kusa da yawa"
Jalila tace "dan Allah Maama a barmin ita se nan da sati daya"
Gaba daya suka fashe da kuka daga Nana har Jalila, Maama taga bazata iya zaman rarrashi ba ta tafi ta kyalesu, Ai Jalila har tafi Nana shiga damuwa, Hanan da Anty fiddo ba yadda basuyi ba amma suka ki yin shiru musamman Jalila, kwana tayi tana kuka, bata taba tunanin zataji haka ba in Nana ta tashi Aure,
Kamar wasa har wayewar gari ranar daurin Aure kuka take, hakan ya saukar mata da ciwon kai da zazzabi me zafi.
Hajiya Salma ta samu labarin halin da Jalila ke ciki, tazo ta dinga rarrashin Jalila, aka nemo likita yabata magunguna, aka samu tayi wanka.
Daddyn Hanan yace akai Jalila bangaren sa ta samu ta huta saboda hayaniya.
Haka kuwa akayi, wunin ranar bata fito ba daga bacci se salla, ta sha kuka shikenan Yaya Jawwad ya tafi da Hanan lagos, Nana ta tafi England, shikenan se ita kadai.
Har aka gama wunin ranar tana kwance saboda zazzabi ga ciwon kai, ita kanta Nana wunin ranar da kuka ta yi shi, se bayan magariba, Mummyn Hanan ta shigo dakin da Jalila take dauke da Akwatin Jalila tace "Jalila maza tashi ki wanke fuskarki, ki sa hijjabinki ki biyoni ana san ganinki"
Jalila tace "Nikuma? Amma me za'ayi da trolley dina anan"
"in munje zakiji, tashi maza" jiki a sanyaye ta mike ta saka hijjabi, har yanzu kanta ciwo yake, dukda zazzabin ya sauka.
Tabi bayan Maama har wani katafaren parlour da yake wani bangare na gidan, suna shiga taga Angwayen nan gaba daya da Amare, sekuma iyayensu maza. Jalal na gefen Jawwad a zaune.
Ta samu guri kusa da Mummyn Hanan ta kwanta a jikin Maama saboda dikinta ba kwari. Sukai tai mata sannu.
Da alamu an dade ana tattaunawa ita kadai ake jira, Maama ta rage murya ta radawa Jalila Daddyn Jalal ya gabatar da kyautar da Mummy ta bayar abawa Jawwad, kyautar gida a Kano, sannan ita ta bayar da sadakin da'aka biyawa Jawwad naira dubu dari.
Jalila tayi mamakin hakan kwarai
Kowacce aka mika mata sadakinta a hannunta, akayi musu nasiha da fada sosai tareda Addu'oi, aka sallami su Hanan, da Nana, Siyama bayan daurin Aure suka koma Kaduna, daddy yace Jalila ta tsaya, Jalal ma yana zaune a gurin.
Abba ya mikowa Jalila bandir din kudi, Mummyn Hanan ta mika mata, ta sa hannu ta karba cike da mamaki
"Abba wannan na menene?" ta tambayeshi tana juya kudin
"Sadakin ki ne" a tsorace ta zare ido ta kalli kudin
"Sadakina kuma? Waye mijin?" ta fada a firgice
Daddyn Hanan yace
"kwantar da hankalinki gashi nan a gefenki ABDUL JALAL ne ba wani ba!!!!
Ai a zabure ta zubar da kudin ta ja da baya tana kallon Jalal da ya sunkuyar da kai tana zazzare ido.
In ba'ayi Comments yadda nake so ba, in na tafi se bayan sati zanyi posting
Ina son jin comments dinku, predictions, and your opinions thank you

Jalal ya dago yana kallon Jalila, cikin kuka Jalila tace
"Innalillahi wa inna ilaihi raji un, Abba me yasa? Laifin me nayi a kayimin haka?"
Abba yace
"kwantar da hankalinki, nasan bazaki watsa min kasa a ido ba, ba laifin da kikayi, ganin da cewar hakan mukayi shiyasa muka yanke wannan hukuncin"
Girgiza kai ta shiga yi tana kuka, daddyn Hanan yace
"Calm down my daughter, kinga bakida lafiya, meye abun damuwa? Jalal ne kin sanshi ba wani aka Aura miki wanda baki sani ba, bakomai kiyi hakuri, Allah yabaku zaman lafiya, Kuma nasan kina sonshi ai ko?"
Girgiza kai tayi da sauri tace
"Ni wallahi bana sonshi, Allah bana sonshi haba daddy, duk 'yan uwana ba wanda akayiwa haka seni, daddy Why? Wallahi ni ba son Jalal nake ba tausayin sa kawai nakeji"
Abba yace
"ba cinya ba kafar baya"
Daddy yace
"to wa kike so"?
"Ni Ahmad nakeso" ta fada kanta tsaye tana kuka.
Jalal yasan za' a rina, yasan setayi daru, Amma be taba zaton Jalila zata iya furta bata sonsa ba agabansa haka"
Mummy tace
"Ke rufewa mutane baki, kaunar da'ake miki yasa aka zaba miki Jalal din, in kun zauna zakiji son, kar in kara jin wannan maganar a bakinki, Ahmad yana da mata, ko yanzu yaga dama ze iya neman wadda yakeso a bashi, kamar yadda kikace tausayin Jalal kike, to kiyi hakuri kicigaba da tausayin sa"
Maama kanta jikinta yayi sanyi, seda ta bada shawarar a ji ta bakin Jalila kafin a yanke wannan hukuncin amma basu bi shawarar ta ba.
Jalila ta mike da sauri ta fice daga palourn tana kuka.
Baban Hanan yace
"Jalal sekayi hakuri, kasan yarinya ce karama, kuma an shammace ta, ba zato ba tsammani aka daura mata Aure, kuma tana ganin duk 'yan uwanta su suka kawo wanda suke so, kayi hakuri da abubuwan dazata yi maka ze wuce kamar ba'ayi ba, gata nan Amana ka rike ta da amana"
Sallamar Hajiya Salma, da kannen Mahifin Jalal, da shi kansa daddyn Jalal, ya katse wa Daddyn Hanan maganar da yakeyi, suka amsa musu sallamar.
Suka karaso suka zauna, daddy yafara magana
"Dukkan yabo da godiya da jinjina da kirari sun tabatta ga ubangiji ma daukakin sarki, me kowa komai, Alhamdilillah anyi taro lafiya an gama lafiya, muna fatan Allah yasa anyi kenan, Allah yabasu zaman lafiya, sannan Alhaji Usman, bazan gaza gurin kuma nuna godiya ga dawainiyar da iyalanka suka dingayi da
ana ba har kawo wannan lokacin da kukayi masa ko ince kuka yimana wannan karamcin, iyalanka sun Rungumeshi lokacin da mutane kowa ke gudun sa, Mungode mungode Allah yasaka da alkhairi, Allah yabiya ku da gidan Aljannah ya jikan magabata, Kuma Insha Allah bazamu baku kunya ba"
Abba yace
"Masha Allah, Alhaji Habib duk abunda nayiwa Jalal tamkar Jawwad nayi wa ne, ABDUL JA
LAL tun tasowarsu da Jawwad yake kaunar sa, kusan kaso mafi yawa na Rayuwarsa a gidana yayi ta, dan haka yiwa kaine Allah yabasu zaman lafiya"
Itama Hajiya Salma godiya takuma yi da nuna farincikinta akan wannan lamarin.
Jalila kam tana zuwa ta zube a jikin Hanan tana wani irin kuka me sauti, Hanan ta kalli Nana suka hada ido ta dan jinjina kai, sannan tace
"Wai Jalila lafiya kuwa? Meyafaru ne haka?"
Jalila ta dago idonta da tuni yayi Ja tace
"Hanan wai an daura min Aure nima"
Nana tace
"Aure, dawa aka daura?"
"Nana wai Jalal aka auramin, meyasa a kayimin haka? Takuma fashewa da kuka
Hanan tace
" kece baki sani ba, mu mun riga munsan za'a daura muku Aure"
Zumbur Jalila ta tashi zaune ta kalli Hanan
"Amma meyasa baku gayamin ba?"
"Saboda ana gudun wannan shirmen dazaki yi, aka gargade mu karmu sake mu gaya miki, kuma ni banga aibun abunda akayi ba, hakan shine dai2"
"Haba Hanan meyasa zakimin haka? Ko dan na tsaya tsayin daka kin samu wanda kikeso, shine ni zakimin haka?"
"Jalila abunda ya dace akayi, nasan abunda akayi miki babu dadi, Amma iyaye basa zabawa yaransu abunda ze cutar dasu, wallahi Jalila sekin fi kowa Alfahari da shi nan gaba, Yana sonki, kuma kema kina sonshi, sann......
" Dan Allah dakata Hanan "
Jalila ta katseta
" dan bake akayiwa ba ko? Ina da wanda nakeso amma an Auramin wani daban, shine ya gaya miki yana sona, babu wani abu makamancin soyayya a tsakanin mu, ta yaya zan fara rayuwar Aure da Jalal, bahagon mutum me wani irin murdaden hali,
Mahaifiyarsa bata kauna ta, ko kinsam tana zargina da
anta, Mahaifiyarsa tana da wanda takeso ya Aura, ta yaya zanyi zaman Aure da wanda mahaifiyarsa bata sona, Hanan nasha wahalar Rayuwa, yakamata ace lokaci yayi da zan huta, wannnan Auren tamkar kara jefa Rayuwa ta cikin wata wahalar ne, nasha wuya Ina bukatar zuciyata ta huta Nashiga uku ni Jalila "
" Subhanallah ke Jalila meye hakane kikeyi? "
Muryar Mummyn Hanan ce take magana, da suka shigo ita da Maama, tace
"duk Nasihar da'akayi miki baki jiba kenan? Meyasa bazaki dauki kaddara ba, ko ba'ayi haka ba dama Allah ya rubuta shine mijinki"
Kuka Jalila takuna fashewa da shi maama tace
"Jalila kidena kukan nan haka, batun mahaifiyarsa bata sonki ze wuce, musamman idan ta gane mahinmancin ki ga danta, Jalila tunda kika iya jure rayuwar gidana duk taren kalubalen da kika fuskanta daga gareni da 'yan uwana, bana tunanin akwai wani kalubale daze tsoratar dake, Anmiki ba dai2 ba tabbas, Amma kiyi hakuri ki rungumi kaddara ki riki mijinki, ki masa biyayya, idan kikayi hakuri kikayi biyayya se Allah yayi miki Rahama saboda hakan"
Mummy tace
"wannan gaskiyane, kuma shi Ahmad da kike magana, ai Daddy ne yace ya bashi da farko, yanzu kuma ya bashi hakuri, Jalila na tabattar nan gaba sekin fi kowa jin dadin zama da shi"
Jalila sam bataji nasiharsu na shigarta ba, ita kawai an gama da ita basu san waye Jalal bane shiyasa suke fadar hakan.
Maama tace
"Nana ki shirya kayanku, gobe in Allah ya kaimu hadda ita zaku tafi maiduguri"
Jalila na jin haka ta kuma rusheewa da kuka.
Yusuf ne ya shigo dakin shima a fusace yana fada
"haba Mummy, meyasa daddy zeyi haka dan Allah? Yaza'ayi a Aurawa yarinya wanda bata so, kuma bayan yasan
an shaye2 ne, a family din nan ba wanda aka taba yiwa Auren dole meyasa za'a fara akanta?ga shi sam wannan yaron bashi da mutuci, ga gadara da girman kai"
Mummy tace
"Sannu jagoran marasa kunya, meyasa bakayiwa daddyn ba seni? Kafi su sanin abunda yakamata ne?"
Hanan Kallon yaya Yusuf kawai take yadda yake zakewa yana masifa
Jawwad nai yai sallama a dakin shima fuskarsa dauke da damuwa, ya hango Jalila ta takure a gefe idon nan kaman gaita saboda ja, ga fuskarta duk ta kumbura. Bebi takansu Maama ba gaje gabanta ya tsuguna yace
"Baby why? Meyasa kike kuka haka? Gashi baki da lafiya? "
"ba dole yarinya tayi kuka ba, an mata Auren dole, an Aura mata
an shaye2 wanda bata so"
Jawwad yace
"Yusuf meye haka? Ana kokarin hankalin ta ya kwanta kana son ka kunna wata wutar, koma dai meye an riga an daura Auren nan, ayi musu Addu'a da fatan Alkhairi mana" Jawwad ya kalli Jalila yace
"We are sorry Baby, kaddara ta riga fata, dana san ba kya son Jalal bazan bari ayi Auren nan ba, saboda nasan Jalal baze ban kunya ba shiyasa na amince"
"Yaya Jawwad ni bana sonshi"
"Jalila kulawar da kike bashi da babu so bazaki yi ba, na miki Alkawarin Jalal baze bada kunya ba, kuma shi Alkhairi ne
a rayuwarki, dan Allah Jalila ki kula da rayuwar Jalal kamar yadda kike yi abaya, Nabaki amanar
an uwana please Jalila" ya karasa maganar kamar zeyi kuka.
Girgiza kai Jalila ta shiga yi
"Yaya Jawwad....
"Shhhh kiyi shiru, ki karbi Amana ta kidena wannan kukan"
Hanan tace
"Jalila son da Haidar yake miki baze bari a baki abunda ze cutar dake ba kiyi hakuri da kaddara Queen"
Jalila shiru ta musu ba tace komai ba, ita ka dai tasan me takeji a ranta.
Jawwad ya mike yace
"Mummy seda safenku" sukayi sallama.
Yusuf dai ya cigaba da banbami da mita.
Su Maama suka cigaba da rarrashin ta tareda Nasiha.
Hanan kuma ta shiga hadawa Jalila kayanta dukda tarin gajiyar biki dake tare da ita.
Jawwad yakoma masaukin Jalal, ya tarar Jalal yana shirin kwanciya, Jawwad yace
"Ango ka sha kamshi"
Jawwad ya lura kaman Jalal baya walwala
"Jalal Lafiya kuwa? Naga kaman baka walwala, ko baka son Auren"?
"Jawwad ba wai bana son Auren bane, idan inason Auren itafa?"
Jawwad ya dafa kafadarsa yace
"brother karka damu, nasan zataji babu dadi da farko, saboda an mata bazata ba tareda masaniyarta ba an daura mata Aure, Amma nasan tana sonka, kuma a hankali zaku daidaita cikin kankanin lokaci"
Jalal yace
"Hmm haka dai kake gani"
"Hakane ze kasance, ni dai gata nan Amana Jalal, kayi hakuri da ita"
Jalal bece komai ba ya danyi murmushi, daga nan suka shiga wata hirar.
Hatta Inna ba'a barta a baya ba gurin rarrashin Jalila da yi mata nasiha, dan ita Inna har cikin ranta Jalal yayi mata, dan seda ta zage Yusuf tsaf saboda masifar da yakeyi akan anyiwa Jalila auren dole.
Jalila dai yau tayi kwanan bakinciki, dan sam bacci ko na minti goma batayi ba, Ga Jalal ya kwace mata waya balle ta kira Ahmad, gaba daya tausayin Ahmad takeji, yasaka rai akan Aurenta, yana da matukar kirki ya nuna mata soyayya, shiko wannan Jalal din da magana se ya ga dama ta ina ze nuna mata wata soyayya. Har akayi kiran sallar Asubah batayi bacci ba se sakawa da kwancewa, bayan tayi salla ta koma ta kwanta tana jin yadda kanta ke sarawa, ga kirjinta da yayi mata nauyi, se karanto Addu'oi take daban2 ko zuciyarta tayi sanyi.
Wajejen karfe bakwai da rabi, Mummy tazo ta kira Jalila suka tafi cikin gida, dakin da'aka sauki hajiya Salma ta kaita, mutane sun ragu sosai duk an watse, se tsirarin mutane da zasu raka Hanan Abuja, sekuma ma'aikata da suke ta kokarin gyara gidan.
Bayan sun shiga Jalila kanta a sunkuye ta gaida Hajiya Salma da Antin Jalal, Suka Amsa mata Antyn Jalal tace
"Sannu Amaryar mu, Kin tashi lafiya?"
Take Jalila ta kuma jin wasu hawayen suna zubowa daga idon ta, Mummy tace
"Ikon Allah, har yanzu baki gaji da kukan nan ba?"
hajiya Salma tace
"haba Jalila, banyi zaton haka daga gareki ba, mun san an miki laifi amma kiyi hakuri, Jalila zakiyi Alfahari da mijinki, yana sonki fiye da yadda kike tunani, gaba daya hope dinmu yana gurin Allah kuma yana gurinki, dan Allah ki kwantar da hankalinki ku zauna lafiya, ki gode Allah, Jalal baya kule kulen mata, ke kadai ce macen dana san yana saurara, kiyi hakuri Jalila "
Cikin kuka Jalila tace
"Mummynsa fa bata sona, tace in rabu da shi, kuma ba irin maganganun da ban gayawa Ilham akan sa ba, na kirashi da sunaye marasa dadi, kuma kawai ace shi na aura"
Hajiya Salma tace
"to shine me? Mahaifiyarsa bata sonki ni ba'a gaya miki abunda tayi min ba, ita da Saudat, gidan mijina abun kaunata seda ta rabani da gidan hankalin ta ya kwanta, ko
kin fison a ya auri Ilham din ne? Jalila kece zakisa zaman gidan Aurenki yayi dadi in kin so, ki manta da abunda ya riga ya wuce kinji yarinya ta, Allah ya Albarkaci rayuwar Aurenku, kije ki shirya anjima kadan zamu tafi"
"wai a maidugurin zanta zama? Makaranta fa?"
Antyn Jalal tace "A'a ba'acan zaki zauna ba, Se a inda yakeso zaku zauna, amma akwai dalilin zuwanki can
in"
Jalila dai ba tace komai ba suka cigaba da rarrashin ta. Haka Maama tazo ta ja hannunta domin fara shirin tafiya.
Daddy ya samu Hajiya Salma a masaukinta, shar da ita bakace ita haifi Mahmud ba, sekace kaninta, har yanzu tana tare da Gayunta,
Daddy yace "To Salma kinga abun Allah ko ba zato ba tsammani danki ya samu matar Aure, kodayake na dade ina burin Jalal ya Auri yarinyar nan"
Hajiya Salma tace
"Hakane, yarinyar tana da nutsuwa da kirki, dangin yarinyar nan sun gama yimana komai, Amma daddy wai ya'akayi abun nan ya kasance"
"hmm ai shekaranjiya dana zo, yazo ya ganni muna tare da iyayen Jalila, shine suke tambayarsa ya aikinsa? yace bayason zaman lagos, nake ce musu yanayin sabanin Addini da al'adun mutanen garin ne yasa baya son zaman garin, bayan ya tafi ne, kawai Captain Abdurrasheed yace ; inyana da wadda yake so ai masa Aure ya tafi da matar can lagos, se nake ce musu bana tunanin yana da budurwa, saboda yace yasan babu me bashi 'yarsa yana wannan halin, se captain Rasheed yace; indai yana son Jalila ya bashi ita, shine aka kira Jawwad da yaron daza' a bawa ita da, aka tambayi Jawwad yana ganin in aka Aurawa Jalal ita ze zauna da ita? Jawwad yace "ai Jalal yana sonta, dan haka suka kira shi wancan yaron suka bashi hakuri, shikansa Jalal be saniba se jiya a gurin daurin Auren"
Hajiya Salma tayi ajiyar zuciya tace
"Allah me yadda yaso, kaga Al'amarin ubangiji, ba zato babu tsammani my Son yasamu mace ta gari"
"Hakane amma yaushe zaku bashi ita? Naji kince da ita zaku tafi maiduguri"
Tai murmushi tace
"Daddy kenan, yadda aka daura aure a bagas ba tareda ya sha wata wahala ba, bazan bashi yarinyar nan a bagas ba, bazamu bashi ita ba se mun tabattar da irin Son da yake mata, dagaske yana sonta kokuwa? Zata zauna damu tasanmu, sannan muyi mata shiri irin namu na 'yan barno"
Daddy yai murmushi yace "haba Salma, a takaice dai ta wani bangaren kuna son ku wahalar min da yarone kawai"
Tayi murmushi tace
"Zamu temake shi dai, yawwa sannan Jalila tana kukan matarka Khadija bata sonta har tana zarginta da Jalal, wannan karon bazan lamunci duk wani nau'i na rashin mutunci daga gareta ba, idan baka dau mataki akan wannan lamarin ba, Zeyi wuya mu bawa Jalal matarsa anan kusa, saboda nafi kowa sanin khadija nasan abunda zata iyayi, a wannan karon bazan bari ta cutar da 'yar mutane ba kamar yadda ni tayimin ba"
Ta mike tsaye tace
"daddy bari inje in karasa shiryawa, da wuri zamu tafi"
Ta wuce cikin dakin, Daddy yabi bayanta da kallo, har yanzu Salma tana nan da gayunta da iya kwalliya, nan ya dinga tuna abubuwa da dama da suka wuce a baya.
Wanda zasu yiwa Hanan rakiya tuni sun shirya dan yiwa Hanan rakiya can gidan Jawwad dake babban birnin tarayya, Hanan tasha kuka, da kyar aka banbare Hanan daga jikin Mummyn ta, daddy yayi mata nasiha Sosai, suka hau motoci sukayi gaba.
Da kyar Maama ta takura Jalila ta ci Abinci aka bata magani, Karfe dayan rana Aka gama kintsa Jalila da Nana, suka fito domin tafiya, Jalila ko ganin gabanta batayi saboda kuka.
Tunda su Jalila suka fito Jalal ya sauke idonsa akanta ta rame sosai ga idanuwanta sunyi Jawur, gaba daya tausayinta ya kama shi, ko ya takeji a ranta oho? Sosai yake jin tausayinta a ransa.
Yadda Jalila da Nana suke kukane yasa jikin Maama yayi sanyi, shikenan Nana zata bar kasar se lokaci2 zata dinga ganinta, duk kiyayyar da tayiwa Jalila a baya, bata taba zaton zataji babu dadi haka ba, Zatayi missing din yarinya me kara da kawaici, ga Jawwad shima ze tafi, zasu bar mata gidan se ita kadai, yadda Jalila ta rirrike Maama tana kuka kamar mahaifiyarta yasa Maama ta kamu da matsananciyar kunyar muzgunawaa Jalila data dinga yi, ba tayi aune ba taji itama Hawaye na bin idonta ta kuma rungume Jalila a hankali tace "ki yafemin Jalila" . Jalila ta kankame Mama tana cigaba da kuka
Abba yace
"haba in kina kuka zaki karya musu gwiwa ne, kiyi hakuri, ki gode Allah da ya nuna miki Aurensu kuka rabu lafiya"
Antyn Jalal tace
"Ai dole tayi kuka, kowace uwa haka takeji a lokacin da take bankwana da 'ya' yanta, yaranta uku zasu tafi su batta lokaci daya, maman Hanan ma tana can ta nayi"
Daddy yace
"ya za'ayi se hakuri"
Haka aka sa su Jalila a mota, ana musu fatan Alkhairi.
Mota daya Jalila, Nana da hajiya Salma suka hau, kanin Mahmud ne ze jasu, sekuma tawagar Angwaye da sauran 'yan uwansu dazasu biyo bayansu, Hajiya Salma tace Jalal ya biyosu a tasa motar, Jalila naji na gani suka
aga suka nufi borno.
Tunda aka kira Ahmad aka bashi hakuri akam Aurensa yarasa ina zesa ransa yana matukar kaunar Jalila, sannan duk yadda zeyi yaga Jalila be samu damar yin hakan ba har suka tafi.
Yusuf kam ko sallama beyi musu ba saboda bacin ran abunda akayiwa Aminin nasa, haka kurum an hana mutumin kirki an bawa wannaan sakaran.
Daddy ma ya shirya kayansa tsaf, yayi musu Sallama ya koma kano, yayinda Abdallah ma da tawagar abokansa suka tafi yi masa rakiya kaduna kasancewar a can ze zauna.
Tuni Labari yafara karade unguwar su Nana cewar an
aura Auren Jalal da Jalila, da yake Akwai wanda sukayiwa Maama kara sukaje mata biki 'yan anguwarsu, Labari ya zaga unguwa inda wasu suke ganin an kwari Jalila da aka Aura mata wannan mara tarbiyar dan shaye2, bayan ita kamila ce, me kirki da faran faran ga kowa, Amma duk abun nan ba wanda yaje ya Tari Mummy ya gaya mata.
Bayan la' asar Daddy ya je gida, da ya koma gida be gaya mata ba, seda yaci Abinci yayi wanka yai salla.
Suna zaune da Mummy tana ce masa "ya hanya? Ya kabaro su?
" lafiya kalau Alhamdilillah, Jawwad da iyayensa suna godiya "
Ya mike ya debo goro da alawowi dayawa ya zube a gabanta.
Ta kalleshi tace
"wannan kuma na menene? "
" Na Auren
anki ne"
ana kuma? Wanne
an nawa, daza'a abani wannan kayan haka?"
"Aike yaran naki ukune, ga Jawwad, ga Mahmud, ABDUL JALAL"
"Jawwad din dai, Mahmud ba
ana bane, sannan ba wanda ya isa yayiwa Jalal Aure ba da izinina ba, idan ma anyi ko 'yar uban waye se an fasa shi, kodayake wace mace ce zata yadda ta Auri wannan
an naka?"
Daddy yace "to shikenan tunda baki yarda ba"
Ya dau remote ya kunna tv abunsa. Ta shi tayi tabar masa palourn ta koma dakinta, tunani ta fara yi, tasan daddy da zolaya wani lokacin, Amma kamar in serious tone yayi maganar, tana cikin tunanin ne wayarta ta fara ringing, seda ta kusa tsinkewa hankalin Mummy ya kai kan wayar taje ta
"Salamu Alaikum"
Mummy tace "wa'alaikum salam, hajiya Rahama barka da yamma"
"yawwa Mummy ya gida ya taro?"
"taro kuma?"
"Au tambayata ma kikeyi? Baban su yacemin ;yaje
aurin Auren
an gidan Alhaji Usman a bauchi, ashe bayan na Mahmud har dana Jalal amma baki gaya mana ba, na miki magana ta what's App bakiyi responding ba"
Ai Mummy bata jira me zata karasa cewa ba ta kashe wayar ta kunna data aikuwa messages suka dinga shigowa ana mata Allah ya sanya Alkhairi, wasu na mata mitar bata gayyacesu ba, jifa tayi da wayar kan gado ta nufi part din daddy
"dama dagaske kayiwa Jalal Aure ba da izinina ba? Akan me? Saboda me?"
"haba Deejah, kefa kikace Jalal ya isa Aure, to menen laifi a ciki dan namasa Auren? Kuma ma yana son matar da'aka Aura masan"
"Sekuma nace kayi masa Aure ban saniba, wane irin wulakanci ne wannan? Wallahi baku isa ba daga kai har munafukan da kuka hada kai aka masa Auren"
Sintiri tafara yi a dakin, wani irin gumi yana tsatstsafo mata ita Daddy ze yiwa haka?
A fusace Tace
"Tukuna ma 'yar gidan ubanwa aka Aurawa masa ba tareda masaniyata ba? Kowace' ya ce wannan ta tarowa kanta abunda bazata iya ba, dan sena ga bayan Auren nan Wallahi, sena murkusheshi, bazan taba bari Jalal ya zauna da matar da bani na zaba masa ba, dan babu yarinyar da zan yadda ta juya min
a, nasan baya son Ilham shiyasa na dage ya Aureta, Amma yanzu Ace an min bazata an rusamin shirina baze yuwu ba wallahi "
" Shikenan deeja abunda kike gudu akan
anki fa se ya faru, Sannan koma wacece zatazo har nan ta gaisheki seki ganta.

103

Da Sauri Mummy ta sha gaban Daddy tace
"Wallahi Habib seka gayamin dan me zaka yiwa Jalal Aure ba tareda nasani ba? Sannan kuma 'yar ubanwa aka Aura masa? Wato kaje kun ha
a kai da wannan munafukan' yan uwan naka aka Aurawa
ana yarinya ban sani ba, to wallahi baze yuwu ba,
a dai nawane nina haifi abuna, dan haka ba'a isa a yanke masa hukunci game da rayuwarsa ba tareda sani na ba"
"sekuma kiyi, naga yadda zaki raba Auren ai, indai Jalal ne gaki nan gashi, dai dai yake dake, Akan kira bashi da yarinyar nan zaki kuma lalata alakarki da shine kawai, dan nagaya miki yana sonta"
"karyane Wallahi, Jalal bashi da wata yarinya da yake so, Yarinyar dana zaba masa ita ze Aura"
Dama daddy yasan ze fuskanci wannan kalubalen daga matar tasa, dan haka ya ture ta daga gabansa yabar mata palourn.
Se magariba Su Jalila suka isa garin maiduguri, koda sukaje sun gaji sosai, musamman su Jalila, su da suka sha hidimar biki, basu huta ba akayo wannaan uwar tafiyar.
Gaba daya Jalila ji take jikinta kaman ba nata ba saboda gajiya, har suka je maiduguri kanta a kasa yake, se dai ta jimgina da jikin Nana, ko mota tayi bacci, in aka jima ta shige cikin mayafinta tayi kuka, har sukaje Jalila bata kula kowa ba seda taji an tsaya ance sufito.
Gidan da akayi parking din motar ne yayi awon gaba da tunanin ta, sekace ba a duniya ba, kallo daya zakayiwa gidan kasan mamallaka gidan sunyi hannun riga da talauci, ko da suka fito daga motar Se gu
a akeyi, Jalal idonsa gaba daya yana kan Jalila da take a takure, Suka nufi cikin gidan, tun daga harabar gidan wani irin sassanyan kamshi ke tashi, har zuwa cikin gidan, cikin gidan da'a akwai mutane a gidan da sukazo domin karbar Amaren.
Cikin gidan ma kamshin da yake na musamman ne, fiye da na harabar gidan.
Aka basu
aki, suka gabatar da sallolin da suke kansu, Sannan aka kawo musu Abinci, Jalila da Nana ne kawai a dakin dan haka Nana tace
"Jalila ki daure kici Abincin mana"
Girgiza kai Jalila tayi tace
"Na koshi, ke dai kici kawai, ni kaina kemin ciwo"
"to ko inyi musu magana a nemo miki magani?"
"A'a base kinyi hakan ba, A yanzu dai babu wani magani daze warkar min da wannan ciwon kan"
Suna cikin wannan mujadalar ne Anty ta shigo da tray din fruit a hannunta tace
"Jalila kuci Abincin mana, ga dangin baban Jalal can suna son ganinku kafin su tafi"
Nana tace
"Anty Jalila taki cin Abincin, wai kanta ke ciwo"
"Subhanallah har yanzu kan ke miki ciwo? To daure kici Abincin se a kira likita ya dubaki"
Da kyar Jalila ta cakali Abincin nan ta barshi.
Suka fito parlour inda dangin Daddy keson ganin Amare, se hausa suke suna hadawa da yarensu, sunga fuskar Nana yayinda Jalila ta dukunkune
a mayafi taki bari su ganta, dare ya farayi sukayi musu nasiha da Addu'oi, tareda jadadda godiyarsu ga Jalila sannan suka watse a hankali.
Dakin da'aka bawa Su Jalila yana da kyau da matukar girma, suka koma suka canza kaya, Hajiya Salma da kanta ta kawowa Jalila magani ta sha, tana shan maganin ta nemi guri ta kwanta tayi lamoo akan gado, tana missing din wayarta, tun randa Jalal ya kwace be kuma bata ba, tana son tayi amfani da wayarta amma ya rike
a gurinsa sekace shi ya saimata.
Nana na kwanciya Mahmud ya kirata a waya, Suka dinga hira suna soyewa, kaman ba gobe zasu tafi ba, suna ta soyayya gwanin sha'awa, Jalila ta tuna kowacce ta samu zabinta, ta auri wanda take so suna cikin farinciki amma banda ita, an ha
a ta da wanda be damu da kansa ba ma balle wani, take taji wasu hawayen na zubo mata, ta tabatta Auren Jalal wani sabon shafi ne na kaddarar Rayuwarta.
Hanan kam gidanta yana da girma amma ba can ba, Amma ya tsaru anyi masa gini na zamani, dauke da wadataccen gini, an kashewa gidan kudi sosai, Sannan daddy ya zuba mata kaya yadda yakamata. Wanda sukayi wa Hanan rakiya suna zuwa a ranar suka juyo gida, suka barota tanata rikici, Seda kowa ya watse bayan sallar magariba sannan Jawwad ya shigo gidan, ya sameta tayi zaman dirshan a kasa ta jingina da gado, ta takure kanta sosai, tayi kuka harta gaji, dan girgiza kai yayi ya karaso gabanta ya tsuguna se kamshin turare yake, A hankali yace
"Haba Hanan, kukan ya isa haka, i know you miss home, Amma ba gani ba, sekace wadda akayiwa auren dole, ko kin dena sona ne?"
Girgiza masa kai tayi alamar A'a
"Yawwa my love
, kukan ya isa haka, yau ranar daza muyi farinciki ne, kar kanki yayi ciwo, ko nima kina so ki sani kukan ne?" ya fada yana goge mata hawayen fuskarta.
A hankali tace "A'a ni karkayi kuma
nadena kukan" tai maganar cikin shagwaba
Murmushi yayi mata yace "Yawwa ai nasan baza kiso ki ganni ina kuka ba, shiyasa nima bana son ganin kukanki"
Haka ya cigaba da rarrashin ta har ta dan saki jiki tana hira, Jawwad da kansa yaje kitchen ya dakko plate da cups, ya bude musu kazar da ya shigo da ita, ya cika mata kofi da youghut me sanyi, yace "Bismillah"
Ta kalli kazar ta kalleshi tace "Ni na koshi"
"me kika ci da kika koshi?"
"bakomai" ta bashi amsa, ya lura gaba daya a firgice take, har hakan yaso ya bashi dariya amma ya maze ya
an bata fuska yace
"in baki ci ba, zan kwana da yunwa ne, kuma ni inajin yunwa sosai, tunda aka fara biki bana samun cin Abinci fa, se Ulcer ta kamani ko?"
Yai maganar a
an shagwabe, dariya ya bata tace
"in Ulcer ta kamaka ba rabin zamce ai, Dama haka ka iya shagwaba, wallahi tayi maka kyau"
tai maganar tana dariya, cikin hikima yanayi ya namata hira ya dinga bata kazar tana ci, seda suka kammala, Jawwad ya jagorance su sukayi Sallar nafila, domin nuna godiyarsu ga Allah da kuma fatan zaman lafiya me dorewa a cikin Rayuwar Aurensu.
Se Hamma take tana lumshe ido, da alamun gajiya da kuma bacci a tareda ita, Jawwad ya kalleta yace
"Wannan hammar da kike karki hadiyeni mana"
Tayi dariya ta Mike, tana cewa "gara in hadiyaka in huta ai"
fita Jawwad yayi domin rufe kofofin gidan, da kuma tabattar da komai lafiya.
Hanan ta canza kaya, ta nemi guri ta kwanta, wani nannauyan bacci yayi awon gaba da ita.
Cikin baccin nata ne tana kokarin yin juyi ta jita a jikin mutum, a hankali ta bude ido tace "Haidar"
"My love" ya amsa mata
"bakayi bacci ba?"
"Banyi ba"
"meyasa?"
"ina tunani ne"
"Nasan me kake tunani, be wuce su Jalila ba, ni na gaya maka komai ze wuce, zasu koma normal, Jalila tana son Jalal, kawai dai kasan ta da taurin kai"
A jiyar zuciya yayi, ya kuma kwantar da kansa a jikin ta yace "Naikaina na san Jalal yana sonta sosai, daga baya na yadda da maganar ki soyayyar 'yan uwatanka ne tsakanina da ita, hankalinta akan rayuwar Jalal take, a tunanin ta tausayinsa take ji, amma da haka sonshi yayi mata illa bata sani ba, kaman yadda ban fargaba naki son yakusa karasani"
Ya kai bakinsa kunnenta ya rada mata
"I Love you my Hanan"
Makalkale shi tayi tace "I love you too Haidar"
Daga nan hirar kuma ta canza salo zuwa wani abu na daban, tun Hanan tana daurewa tana biye masa, taji abun ya wuce tunanin ta, ta fara neman taimako, 'yan gidan su ba wanda be sha kira ba dama an hadu da uwar shagwaba, A wanna daren Jawwad ya saukewa Hanan wannan rawan kan nata.
(nima me rahoto naga abun yafi karfina dan haka na dawo da baya, na fito
Gaba daya Nana ta takurawa Jalila da waya, har sha biyun dare tana manne a waya seka ce wata mara aikinyi, haushi duk ya ishi Jalila tana ganin ta fiye zakewa, ji ta ke kaman suna karama ta takaicin da take ciki, ta ja bargo ta rufe har kanta dan ta dena jin abunda Nana take fada.
Washegari tunda safe Su Nana suka fara haramar tafiya.
Wayar Nana Jalila ta karba sukayi waya da Maama, har daki aka kawowa su Jalila breakfast, Nana kanta ba ta sake taci ba, saboda gaba daya ji take ba dadi, zata daga tabar kasarta ta haihuwa Aure kenan.
Karfe sha dayan safe su Nana suka gama shirinsu, suka shirya domin tafiya airport, nan ma seda aka sha daru Da Jalila saboda kuka, haka sukayi Sallama Nana da Mahmud suka tafi.
Hajiya Salma bata bisu ba ita seda ga baya zata koma.
Bayan tafiyar Nana Jalila dakin ta koma ta kwanta gaba daya ji take duniyar tayi mata fadi, ba abokin hira an kawota inda ba wanda ta sani. Ta lura nan gidan Antyn Jalal ne, tana da yara 'yan mata guda biyu, daya zata girmi Jalila, Husnah da Amal, Amma sam basa san mutane basa shiga harkar mutane, dan haka ko sannu bata hadasu da Jalila, sedai sukan gaishe ta.
Hajiya Salma ta shigo ta samu Jalila a kwance tace "Jalila har yanzu jikin ne?"
Jalila tace "A' a naji sauki kaina ne kawai be dena ciwon ba"
"ko dai likita za'a kira"
"A'a Anty naji sauki"
"to shikenan, Amma Jalila ki kwantar da hankalinki, ki cire duk wata damuwa a ranki, Kicigaba da raguwarki kaman yadda kike yi a da kinji"
Jinjina mata kai kawai Jalila tayi.
Koda Hajiya Salma ta fita dakin da Jalal yake taje, yana zaune yana kallon labarai a tashar CNN.
"Sannu Jalal kana nan kana kallo, kai ko tambaya matarka bakayi, ka sameta a sauki, dan haka baka damu da ita ba ko?"
"to me zance? Kokuma me zanyi? Nima ai bata nemana"
"Au hakama zakace ai shikenan, yaushe zaka koma?"
"gobe insha Allah"
"zakaje kano ne kokuwa?"
Jalal ya dan yamutsa fuska yace "daga nan gurin aiki zan koma, bazanje Mummy ta hargitsa min kai ba, lagos zan wuce"
"Shikenan Allah ya kaimu goben" Jalal yace "Ameen Amma, se yaushe Zaku bani ita mu koma kano"?
Hajiya Salma tace
"ita wa kenan?"
"Matata mana" ya bata amsa
Hajiya Salma tace "au ashe matarka ce, baka da kunya Jalal, se lokacin dana shirya yayi tukuna, ashe dai ka damu da ita"
Dan dage kafada yayi irin i don't care din nan.
Jalal idan ya tuna yadda Jalila ta ce bata sonsa a gaban kowa da kowa, yana tunanin wani irin zaman Aure zasuyi? Tsawon lokacin nan dama bata taba sonsa ba kenan? To meze sa ya cigaba da bibiyar ta tunda tace bata sonsa.
Bayan Hanan tayi sallar Asuba komawa tayi kan gado, wani wahalallen bacci ya kuma dauketa. Koda Jawwad ya dawo ya tarar ta koma bacci, ya hau kan gadon ya
an tsira mata ido, baccin ta take hankali kwance, tuno darun da tayi jiya yayi, ya danyi murmushi ya janyo ta jikinsa ya kwanta shima baccin ya dauke shi.
Wajen karfe tara Jawwad ya tashi, Amma Hanan bata farka ba, ya je ya dafa musu tea ya fita, ya fita ba dadewa Hanan ta tashi daga baccin, taje tai brush tai wanka ta saka wata doguwar riga mara nauyi, ta fito parlour amma bata ga Jawwad ba, ta nemi guri ta zauna a kan kujera, befi mintuna goma da fitowarta ba se gashi ya dawo hannunsa dauke da kaya, yayi sallama ta juyo ta amsa suna hada ido ya kashe mata ido, hakan yasata sunkuyar da kai tana murmushi, ya karaso ya ajiye kayan yace
"good morning dear, kin tashi lafiya?"
"lafiya kalau, kaima ka tashi lafiya?" tai maganar tana kokarin kaucewa hada ido da shi
"lafiya kalau na tashi lafiya, How was your night?" ya kuma jefo mata tambayar.
Pillow ta dauka ta rufe fuska tana murmushi haka Jawwad ya cigaba tsokanarta yana bata kunya.
Ya dakko cups yana kokarin hada musu tea tace "Haidar waye ya dafa tea din nan?"
"ni na dafa" ya bata amsa
"Allah yasa dai baka bari yayi kanzo ba, dan na san baka iya girki ba"
Dariya ta bashi sosai
"Ai nafi ki iya girki in gaya miki, zaki kuma gani"
"to ai shikenan hada min yunwa nakeji"
"Ai wannan tea din nawane ni kadai, bazaki sha ba ke kazarki zaki warming a oven ki cinye"
Zare ido tayi tace
"gaskiya bazan ciba na koshi"
Jawwad yayi dariya yace
"se kin cinye ta kuwa"
"aikuwa bazan ci ba, tsaya in baka a baki" ta dinga bawa Jawwad Abinci a baka, yana bata haka sukayi breakfast cike da kulawa da kaunar juna.
Wunin ranar yau Jalila ji tayi duniyar ta kara mata fadi, ga har yanzu Bata kuma sa Jalal a idonta ba balle ta sa ran karbar wayarta.
Bangaren Jalila ma tunanin ta yaza'ayi tayi zaman Aure da Jalal be damu da kansa ba balle ita, tana ganin shima an cusa masa ita ne kawai baya sonta, banda haka kwanan su nawa da zuwa be nemeta ba ga rashin lafiya tanayi amma ko keyarsa bata gani ba balle tasa ran ze mata sannu.
Ko parlour bata fita tana
aki, Hajiya Salma da Antyn Jalal suna monitoring din Jalal da Jalila domin ganin actions dinsu, Amma abun mamaki kowannensu yana nuna be damu da
an uwansa ba, tunda sukazo kwana uku ba wanda ya nemi wani a cikinsu.
Antyn Jalal tana zaune suna hira a parlour su Husnah suna cin Abinci Jalal ya shigo, su Amal suka gaisheshi a ciki ya amsa, dan sun fidda ran ze amsa musu, suka cigaba da cin Abincin su.
Anty tace "Jalal ina zuwa haka?"
"Zan koma lagos ne"
Anty sukayi ido hudu da Hajiya Salma.
Hajiya Salma tace "to wannaan tafiya haka kaman wanda ake kora? Ka gayawa matarka yau zaka koma?"
Cikin ko in kula yace "in kun ganta ku gaya mata"
Anty tace "dan kaniyarka mu zamu gaya mata ka tafi, Anya Jalal ka shirya rike yarinyar nan?"
A ransa yace "ita zaku tambaya in ta shirya zaman Aure dani?"
Hajiya Salma tace "nima dai haka nagani, tunda muka taho bata da lafiya, Amma yaron na ko ta kanta bebi ba, balle in sa ran ya duba ta, ya mata sannu" da sauri yace "bata da lafiya kuma? Me yasa me ta?"
Hajiya Salma tace "ban sani ba" mikewa yayi ya kalli Husna yace
"ina ne dakinta"?
"tana upstairs kusa da
akina" ta bashi amsa, be kuma bi takansu Anty ba ya haura saman.
Kai tsaye ya bude dakin ya shiga, ya sameta ta dukunkune a cikin bargo, a hankali ya karasa gaban gadon nata ya kai hannu ya janye bargon.
Wata sleeping dress a jikinta blue me matukar kyau, kanta babu dan kwali, dukda tayi parking din gashin nata amma gashin ya hargitse, bacci takeyi sosai, Amma tayi rama a baccin ma se ajiyar zuciya take.
Ya kura mata ido fatarta se sheki take, a hankali ta motsa ta mike hannyen ta wajen kirjinsa, hannayenta sun sha ado da jan lalle, hannunsa yasa a nataa ya rike yana kuma kallon fuskarta, bacci take amma tayi kyau sosai. Ya bata lokaci sosai yana kallon ta. A hankali ya saki hannunta
Ya dakko wata 'yar takarda a Aljihinsa da biro yayi rubutu ya ajiye mata akar kashin pillow dinta, ya mayar mata da hannun ta kan gado ya lullube ta ya fice.
Koda ya sakko bekuma ce musu uffan ba yayi waje abunsa.
Anty tace "kinga danki ko?"
Hajiya Salma tace "ai bari kawai, Jalal Akwai taurin kai, suna son juna amma taurin kai neke damun su, se nunawa suke kaman basu damu da juna ba, Allah shi yabarwa kansa sanin dalilin dayasa ya hadasu, Amma wannan zaman Auren nasu da kallo"
"hakane amma zamu cigaba da yi musu Addu'a, zasu dai daita, bari kiga sukoma gidansu da zama, bazaki sake jin kansu ba"
"hakane Allah ya tabattar da alkhairi, Amma bazata koma kano yanzu ba, sonake hankalin ta ya kwanta ta sake nustuwa, daga nan ma waccan jarababbiyar watakila ta sakko"
Anty tace "tab haba sister Salma, kin manta wacece khadija kenan, ai babu batun ta sakko yanzu, kawai dai mu tayasu da Addu'a" haka suka cigaba da hirarakin su.
Koda Jalila ta tashi ji tayi gaba daya dakin ya gauraye da kamshin Jalal, dan tabe baki tayi ta shiga toilet tayi wanka ta sa kaya, tazo tana kokarin gyara gadon tana cire bedsheet din taga takadda ta fado, ta dauka ta bude, wani tsararren handwriting tagani a jiki.
Am going back to lagos, get well soon
ABDUL JALAL se signing dinsa da date
Juya takaddar tayi ta jefar da ita a gurin tayi tsaki, "kwana nawa bani da lafiya, tunda aka daura auren ko ta kaina
bebi ba, se yanzu ze wani rubuta min wata banzar takadda, ya tafi abunda yafi lagos ma ni be shafe ni ba, kuma maimakon ya ajiyemin wayata amma yakuma tafiya da ita sekace tasa.
Haka Jalila ta cigaba da mita, har ta gama gyaran gadon.
Parlour ta fito dan ta gaji da zaman dakin ga shi ba waya a hannunta balle ta debe mata kewa.
Anty na ganin Jalila tayi murmushi tace "Jalila kin fito? Ya jikin naki kuwa?"
"naji sauki Anty"
"to Allah yakara sauki, dazu Mijinki ya shiga dubaki ai"
Dan tabe baki Jalila tayi tai shiru.
Tundaga Ranar kullum cikin turara Jalila suke da samfurin turaruka daban2, a rana se ayiwa kayan sawa turare kusan sau hudu, banda wanda ake tuarar mata jikinta, hatta ruwan wankan Jalila akwai turaren da'ake zubawa, sabulun wankan ta ma na musamman ne aka hada mata, ga mayukan shafawa dana kai, nan da nan Jalila jikin Jalila yara canzawa, duk inda ta gifta kamshi take, duk rashin son kitson Jalila wani na tsufa me kitso take zuwa tayi mata wani, hakama lalle, gaba
aya wannan gidan sun maida Amfani da turaruka kamar ibada, babu wani aiki da takeyi sedai taci ta kwanta, ko ta yunkura zatayi aiki se a hanata, ga kyan gyra da'ake bata dan haka har wani kiba tayi abunta tai kalau da ita. Jalila idan tana son yin waya sedai ta ari ta Anty tayi, ta mata magana akan wayarta tace tabari Jalal yazo.
Tunda Jalal yazo ko a waya be kuma neman inda Jalila take ba itama ba ta nemi jin inda yake ba.
Mummy ta cigaba da tayarwa da Daddy hankali akan maganar Auren Jalal, amma sam yaki saurararta, ya tattara ya koma Dubai, duk abun nan da ake Ilham bata sani ba.
Daddare Ilham na kwance tana chatting, ta shiga Twitter kamar wadda aka saka ta shiga profile din Jalal Alhamdilillah got married to Jalila Aliyu Imam shine abunda Ilham ta gani zumbur ta tashi Zaune tana kuma mutsukke ido, Amma still taga ba mafarki take ba.
Da sauri ta kira layin Nana, Amma bata shiga, se lokacin ta tuna ai Nana Mahmud ta aura, a England zasu zauna.
Fitowa tayi da sauri ta tafi
akin Mummy tana kwala mata kira
"ke lafiya kuwa kike min wannan kiram, meya faru ne?"
Nunawa Mummy wayar tayi, mummy tace "me zan gani?"
"Mummy wai dagaske ne Jalal yayi Aure"
Ajiyar zuciya Mummy tayi tace "tun satin da Daddy yaje daurin auren Jawwad, ya hada baki da 'yan uwansa suka masa Aure, nayi2 ya gayamin wacece yaki"
Innalillahi wa inna ilaihi raji un, Mummy kin san wacece kuwa? Jalila ce fa, kalli Abunda ya rubuta ita ya aura Mummy, na shiga uku, Mummy ki kashe Auren nan kafin sun tare, Wallahi idan suka tare na kade, zan rasa komai, komai nawa ya rushe"
Gaba
aya Mummy tsayawa tayi tana kallon Ilham
"dolene in kashe Auren nan, baze yuwu ba, wallahi ko yana so koba ya so sena kashe auren nan, ni Hajiya zainab zata munafunta, a hada kai da ita a Aurawa
ana wannan makirar yarinyar, in abun gaskiyane ta aurawa nata
an mana, indai nina haifi Jalal seya saketa, a
aura masa Aure ko ya nemi inda nake, rabona da shi wata biyar kenan, baze yuwu ba wallahi"

104

Tunda aka gama biki Maama bata dawo ba, seda takuma kwana goma a Bauchi, taji dadin zaman garin sosai, gashi mutane ne masu karamci da son 'yan uwa, Abba ne yazo ya dauketa suka koma gida kanon dabo.
Bangaren Angwaye da Amare da sukayi Auren soyayya Se shan soyayya da kauna suke, tsakanin su banda Jalila da Jalal da babu wanda yake neman wani
a tsakanin su,
Jalila ita wannan zaman hutun ya isheta, ita dama kano suka batta tayi zamanta a gurin Maama ya fiye mata wanna zaman.
Tana ta zancen zuci ne Husna 'yar gidan Anty ta shigo da waya ta mikowa Jalila, Jalila tasa hannu ta karba, video Call ne ta
aga wayar tana
agawa taga fuskar Jawwad cikin sauri ta mike zaune
"Yaya Jawwad kaine?"
"Nine Baby, yaya borno yasu Anty?"
"lafiya kalau Yaya Jawwad, kayi kiba sosai kaman ba kaiba, ina Hanan?"
"tana kitchen tana girki, kema gaki nan kinyi kibar ai, ya mijin naki?"
Tabe baki Jalila tayi tace "yana can lagos" Hanan ce ta taho da gudu ta haye kan cinyar Jawwad tace
"Hi queen, ya kike?"
"Wow Hanan, wannan kwalliya haka, masha Allah, naji dadin ganinku wallahi nayi farinciki, Allah ya albarkaci rayuwar aurenku, yara muku kaunar juna"
Tausayinta yakama su Jawwad, Hanan tace "Jalila kunyi waya da Nana kuwa?"
"Eh munyi waya da su, ya Abuja ya zaman kadaici?"
Jawwad yace
"muba ma zaman kadaici ko My sugar, masu zaman kadaici suna Azabtar da zukatansu sun san kansu" yai maganar yana kallon Hanan, Hanan tace "Sosai makuwa, ba wani kadaici, kullum muna tare, kema kice akaiki gidan mijinki kigani in zakiji wani kadaici"
"Allah ya kiyaye" Jalila ta fada tana harar Hanan. Wayar Jawwad ta fara ringing, Jalal ne yake kiransa, Jawwad yace
"Baby mijinki ke kirana, bari inje in amsa" Hanan ta zauna akan kujera tace "Jalila wai yaushe zaku sauke wannan taurin kan ke dashi ku fuskanci juna?"
"Hanan ya kikeso inyi ne? Nagaya muku Jalal ba sona yake ba, kawai an lika masa ni ne, tun lokacin biki nake rashin lafiya be nemeni ba, ko ta kaina bayabi, se ranar da ze tafiya ya ajiyemin takadda, sam be damu dani ba, Hanan ku kukayi dacen Auren soyayya amma bani ba, nasan da Ahmad na Aura baze watsi da lamarina ba" kan Jalila ta gama maganar har hawaye ya wanke mata fuska. Cikin taushin murya Hanan tace
"Jalila, kina da Aure yanzu be kamata kidinga ambaton wani namijin ba, Sannan Jalila kinsan halin mijinki tun kafin kuyi Aure, bashida shiga sabagar mutane, dukda ke matarsa ce yanzu, Amma kiyi hakuri, komai ze wuce Jalila, kalli yadda kikayi kyau kamar a saceki a gudu, i wish yana nan yaga wannan kwalliyar taki se ya rude, waima me suke bakine kikayi wannan kyan"
Murmushin takaici Jalila tayi tace
"Hanan kenan, kina tunanin zanyi wani abu daze gani ya yabane? Ko ya burgeshi, shi ba sona yake ba kawai an aura masa ni, be damu da yasan a halin da nake ba balle ya yaba kwalliya ta, se an jima ki gaida Yaya Jawwad.
Jalila ta ajiye wayar ta dora sabon kuka me sauti.
ji tayi an dafata, ta dago ta kalli wanda ya dafata Husna ce fuskarta dauke da damuwa tace
"Sorry dear, please stop crying, kidena kuka ko tunanin broz Jalal baya sonki, is not like that, ina kula da yadda kuke share juna kedashi, which is total bad, an riga an daura Aurenku, kamata yayi ku manta da abunda ya wuce, Jalal has a social disabilities at times, tun lokacin da yakoma drunker, mutane suke kyamarsa he decided to isolate himself from the people, he dint interact with people as before, believe me he loves you bazaki gane hakan ba sekin zauna da shi, yanada kirki sosai, ki dena yawan kukan nan please "
Jinjina mata kai Jalila tayi Husna tace
" Yawwa mrs Jalal, Jalal bashi da matsala bayan ta shaye2, zaki maida shi yadda kikeso, yana sonki ne shiyasa yakeyin abunda kike so, ba dan haka ba a duniya akwai abunda ba wanda ya isa Jalal yayi wani abun yayi. Husnah ta cigaba da rarrashin Jalila, a lokacin take gayawa Jalila Tanada Aure, mijinta baya gari ne, shiyasa itama tazo tayi zamanta a gida.
Ilham takasa zaune takasa tsaye, kwanata kusan shida a gidansu suna sakawa da warwara akan yadda zasu bullowa lamarin ita da umanta, yanzunma zancen da suke kenan
"Umma kin san kashinmu ya bushe idan yarinyar nan ta tare da Jalal, aikin ze lalace ne fa, zamu rasa komai, jiran da mukayi tsawon shekaru mu dauki fansa ze tashi a banza ne, indai yana tareda yarinyar nanmun rasa komai, daular da muke hange bazamu sameta ba"
Umman Ilham taja numfashi ta hura hanci tace
"Bazan taba yadda tsawon wannan lokacin daukar fansa ta ya tsaya akan lalacewar Jalal ba, dole in wulakanta khadija in mallake dukiyar da take takama da ita, sena ga ta wulakanta daga ita har Habib din"
Ilham tace "Umma to tayaya?"
"ki kylaeni kawai, nasan abunda zanyi, tunda ke kinkasa abunda ya kaiki gidan tsawon lokaci"
"Umma kenan, ba kasawa nayi ba, nayi iya yina, ba daban wannan Jalilan ba da tuni an wuce gurin, Amma ni hankalina a tashe yake umma, kin san abunda Aure ga Jalal yake nufi fa a shirin mu, so soyayya da wata mace bayanni ga Jalal kim san barazana ce a garemu, wallahi ko bacci bana iyayi"
"ni nace ki bar komai a hannuna, nasan me zanyi"
"Shikenan Umma"
Mummy har gidansu Jawwad taje da kanta, ta tarar da Maama tana ta fama da aikin gida. Cikin fara'a Maama ta tareta tana mata sannu da zuwa
Aikuwa a fusace mummy tace
"kinga niba yashe bakinki nazo gani ba, ba hakoranki nazo ki nunamin ba, baban su Jawwad na nan ne?
" A'a baya nan lafiya kuwa? "
" ina fa lafiya, saboda tsabar munafunci a ha
a kai da ke a cuceni, a Aurawa Jalal wannan yarinyar dake kanki kinsam bata da cikakken Asali, meyasa baki yadda an
An aurawa
anki ba se nawa
an, wannan yarinyar mara mutunci akan me?
Sumi2 da ita kamar ta Allah amma tana bin
ana"
Maama tace
"Subhanallah
ni kaina ban san da batun
aurin aurensu ba se ana i gobe
aurin Aure, kuma iyayensu mazane suka yanke wannan hukuncin baniba, da amincewar mahaifinsa aka aura masa ita"
"ke kikasani koma suwaye suka amince, saboda tayi kwantai tarasa miji se abawa
ana, Allah kadai yasan abunda aka dukunkune aka bashi"
"Mummy Jalila ba kwantai tayi ba, tanada masoya, Allah ne yayi matarsa, Sannan be kamata kidinga wannan maganganun ba karkizo kiji kunya wataran kamar yadda naji kunya nima, Ni data zauna taredani tayi zaman hakuri dani na tabattar Alkhairi ce ga rayuwar Jalal, a irin zamanbda tayi a hannuna nasan halinta"
"kinga dan Allah ki sauraramin bana bukatar jin wa'azinki, tunda baya nan, ki gaya masa ya shirya karbar karamar bazawara, dan sena kashe Auren nan, ban ga dacewar Jalal da wannan yarinyar ba"
Maama tace "Shikenan duk yadda kika gani, komai ya samu bawa mukaddarine, dadinta ma
an naki ba wani kintsatse bane balle aji haushi dan an rabu da shi, naga ke kanki baki isa da shi ba, temaka masa akayi aka bashi yarinyar nan, kuma duniya da gaskiya baki isa ki biya Jalila da mahifiyarta abunda tayiwa
anki ba"
Maama takarasa maganar tareda shigewa ta bar Mummy a gurin.
Mummy ta dawo gida tana cizon ya tsa, tana tunani iri2 a ranta.
Jalila hankalin ta ya
an kwanta, Husna na debe mata kewa suna hira lokaci zuwa lokaci, sannan duk lokacin da ta keso zata ari waya takira wanda takeso, Mijin Antyn Jalal professor Aliyu Ishaq
yana koyar da darasin turanci a saudiyya, be fiye zama ba, yana da tarin Ilimi, gashi mutumin kirki ne, yana da barkwanci da raha, Girmama shin da Jalila da take da yadda yaga tana gudanar da Al'amuranta yasa take burgeshi, yayiwa Jalal murnanr samun yarinya me kwazo da tarbiyya kamar Jalila. Be kara sarewa da lamarin Jalila ba seda Antyn ta bashi labarin irin Abubuwan da Jalila ta dingayi da kokarinta akan rayuwar Jalal, ya zamana Jalila tana sakewa da shi fiye da kowa a gidan, kamar yadda Ake kiransa Abee haka take kiransa, Jalila tana son mu'amala da mutane masu ilimi dazata Amfana dasu, indai Abee ze fito parlour Jalila zata zauna Suyita hira tana masa tambayoyi akan abubuwa da dama, shikansa duk lokacin da be ganta ba ya dinga tambaya tana ina kenan, yana mamakin kaifin hankalin ta da basirarta, gata da ilimin Addini "
Yauma na gama dinner, Amma Jalila tanata hira da Abee tana bashi labarin irin fituntunun data dingayi lokacin kuruciya suna ta mata dariya, Hajiya Salma tace
"Nikam Alhaji Aliyu me kayiwa Jalila haka take sakewa da kai hada hira, mu kaman tsoronmu ma takeji"
Jalila tayi murmushi tace "Bahaka bane ba, Jalila Aliyu Imam, shine cikakken sunana, kuma Kafin Babana ya rasu Abee nake ce masa"
Anty tace "Haba shiyasa wannan shakuwa haka, Ashe ya da uba ne"
Abee yace "Eh ya ranku, yata kuma sirikata kuma malamata"
Zare ido Jalila tayi tace "Wace ni, se dai in durkusa a koyamin, Seda safenku" Jalila ta fada tana mikewa tsaye, sukayi Sallama ta tafi dakinta.
Bayan tafiyarta Abee yace "Kuna ganin raba yaran nan yanada wata fa'ida ne? Yana can matar tana nan"
Anty tace "Eh mana, muna so mugane dagaske yana sonta ne kokuwa?"
Abee yayi murmushi yace "Lallai kun manta waye
an naku ne, shikenan Allah ya tabattar da alkhairi, Amma nayiwa Jalal murna samun yarinyar kirki kamar ta, tanada hankali sosai"
Haka dai suka cigaba da tattaunawa.
Jalalila kamar kullum ta gama wannan wankan turaren, ta shirya a cikin wata doguwar riga, dayake Anty sunyiwa Jalila sayayyar kayan sawa dana kwalliya tana kan wani karamin kujera tana gyara gashin ta.
Husnah ce ta shigo dakin tana murmushi tace
"Maigidanki yana hanya, broz Jalal zezo ba sanarwa ba komai, kuma nasan badan ke ba bazamu ganshi ba, tashi muje ayi masa girki, Anyiwa me kitso waya tana hanya, ki taso muje"
Hade rai Jalila tayi tace "ba wani girki da zanyi, kuma ni ku kyalemin kaina a haka"
Husnah tace
"Haba Sister meyasa haka ne?" (nikam nace baki san halin Jalila da taurin kai ba)
Jalila tace "wai meye Amfanin inta bawa kaina wahala akan wanda be damu dani ba? Watana daya da kwana Goma a gidan nan ko ta waya baya kira balle yaji ya nake, seni zan ta faman wahala akansa"
Ajiyar Zuciya Husnah tayi tace
"Kina da gaskiya Jalila Amma hakurin dazakiyi yanzu baze kai na baya ba, ki bari ki kama shi a hannu, daga nan seki rama, taso muje su Mummy suna parlour"
Jalila bata da zabi sena ta mike tabi bayan Husnah, suna zuwa parlour Hajiya Salma tace
"Yawwa Jalila, Jalal yayi waya yakusa isowa maiduguri, me kitso tana hanya, dama lallanki jiya akayi shi, in an gama kitson kafin ya karaso ayi masa girkin.
Jalila ta samu guri ta zauna ba tareda tace komai ba, Husnah ta zauna a kusa da ita tana mata magana kasa2
"please sister idan yazo karki hade masa rai haka, karki biye masa dan Allah, ki bawa mara
a kunya"
Ita dai Jalila jinsu kawai take.
Tunda Daddy ya tafi be kara dawowa Nigeria ba, Mummy tarasa me yake mata da
i, in dai Jalal ya zauna da yarinyar nan to zata kwace mata shine gaba daya, dan tun kafin ya aureta ma yana sonta tunda yanajin maganar ta, tarasa ta inda zata bullowa lamarin, gashi a yanzu tasan bata isa taje maiduguri tayi musu tijara ba.
Kafin Jalal ya karaso har angama yiwa Jalila kitso, kitso akayi mata kanana sosai, gashi hannunta ya sha lalle, duk inda ta gifta kamshi take, ga fatarta ta kara kyau se sheki take.
Anty tace " Jalila me yakamata ki girkawa Jalal ne? Mara nauyi sosai tunda naga alamar shigowar dare zeyi"
Dan zumbura baki Jalila tayi tace "befiye cin Abinci da daddare ba yafi shan tea ko fruit, wani lokacin koya ci Abinci seya sha tea da daddare" ta fada tana dan tura baki cikin ko in kula
Boye dairiyar su sukayi, banda Husna da seda ta dara, tace "Ya akayi kika san haka?"
"Nike musu girki shida Yaya Jawwad a gida" tabata amsa
Anty tace "Ke Husnah ina ruwanki ne? Jalila ki dafa masa abunda kika ga ya dace kawai"
Jinjina kai tayi ta tafi
akinta.
Seda ta tafi sukayi dariya, Hajiya Salma tace "Kai lamarin yaran nan sesu, ni ban san wanda yafi wani taurin kai a cikin su ba, ana so ana kaiwa kasuwa"
Anty tace "Jalal yafita taurin kai, bafa yanzu yafara sonta ba shi, Jalal ya dade yana sonta, nasan komai, Dan yaga ya samu yanzu shine yake basarwa kaman be damu da ita ba"
Hajiya Salma tace
"Aike ta hannun damansa ce kinsan komai akansa, Allah ya daidaita tsakani"
Suka Amsa da Ameen
Lokacin sallar magariba Jalal ya iso gidan, ya sha tafiya dan a mota yazo ya gaji sosai, Jalila bata san ya karaso ba, har bayan sallar isha'i tana palourn Abee yana mata bayani akan wani littafi da yake son wallafawa, Husnah tana gefe tana dan tsoma musu baki lokaci zuwa lokaci, zaman da Jalila
tayi da su tafara gane yarensu kadan2, kaman gaisuwa da yaren.
Suna hira kai kace 'ya da ubane, Anty ta shigo palourn tace
"Jalila kina nan, tun dazu Jalal ya iso fa, nazata kina can kina shiryawa ne, kije ki shirya ki kaimasa Abincin"
Jalila ta dan langabe kai tana kallon Anty. A ranta tace "Sekace wani mijin kirki ko wadda zata biki anata in shirya, bayan nasan ko kallo ban isheshi ba"
Abee ya kalli Anty yace "Madam jeki zamuyi magana da' yar auta ta"
"to shikenan nidai ayi Sauri, in ba sokuke yayi zuciya ba ya tafi" ta fada tana shirin barin palourn tareda yin murmushi, Ameera tana zaune bata fita ba.
Abee yace
"Jalila tambayar ki zanyi, ki gayamin tsakani da Allah, in dai kin baban dani ki gayamin kina kuwa son Jalal?"
Taji ya mata tambayar ba tareda ta shirya jin hakan ba.
Hade fuska ta danyi tace "Ni dai ban sani ba ko ina sonshi, shima fa baya sona" ta karasa maganar kaman tana shagwaba
Fuskarta ya kalla, Akwai alamar kuruciya sosai a tareda ita, yarinya ce me tunani irin na manya, Amm lokuta da dama kuruciya tana dawainiya da ita.
Yace "Shikenan daughter Allah ya daidaita ku, ki cigaba da hakuri zaki fara sonsa, Mijin kine yanzu, ki manta da halinsa kinemi Aljannar ki, kuma insha Allah komai ze wuce"
Jalila tace "to Abee nagode" harzata fita Husnah tace "Jirani muje in miki kwalliya, nasan idan na kyaleki ba zakiyi ba"
Ta tasa Jalila a gaba zuwa
aki, ta
akko mata wani material baki da adon jan flowers, riga da skirt ta mikawa Jalila ta karba tana zumbura baki ta saka, tayi kyau sosai, Husnah ta bata turaruka ta shafa, kamshi dai kam ya riga yagama kama jikin Jalila a gidan nan, Husnah tace
"bari in miki kwalliya"
"ni ba wata kwalliya daza'a yimin"
"Jalila ya hakane? To sa kwalli da jan baki mana"
Jalila ta saka kwalli se jan baki Ja, tasaka kwalli, tayi kyau sosai, Husnah ta bata karamin gyale Ja akanta, Jalila ta kalli kanta a mudubi, kayan nan sun kamata sosai ta kalli Husnah tace "Nikam gyalen nan yayi min karami gaskiya, ki bari in saka babba"
"Haba Jalila, gurin mijinki zaki fa, Mijinki ne ba wani ba, in kuma kinki in barki da su Mummy"
Husnah tasata gaba zuwa Kitchen ta shirya mata kayan Abincin a tray ta rakata har kofar palourn da Jalal yake tace
"please Jalila don't mess up, karki bani kunya dan Allah"
Jalila ba tace komai ba ta shiga gabanta se faduwa yake yi, Sallama tayi sannan ta shiga, bata tabaccin ya amsa sallamar nan tata. da farko dakin kamshin turarensa yakeyi, Jalila na shigowa kuwa temperature dakin ta canza zuwa kamshin turaren jikinta, kallo daya tayi masa ta dauke kanta, kanan kayane a jikinsa amma yayi kyau sosai sumarsa se kyalli take, duk ya dena saka wannan kalar dayake wa gashinsa, ya dora kafarsa akan center table, ko a ina zata ajiye tray din oho, ta gefen ido ya dan saci kallonta, tana zuwa bata kula shi ba ta ajiye tray din a kasa, ta juya zataje ta zauna hakan ya bashi damar kare mata kallo, tubarkallah she has a very beautiful heart and body structure, Jalila tana da kyau ga kyakywan surar jiki, ga zuciyarta me matukar tausayi, matsalarta taurin kai da Izza wani lokacin.
Taje ta nemi guri ta zauna a kujerar da take kallonsa ta dora kafa daya kan daya tana kada kafa tareda dauke kanta gefe tana wasa da yatsun hannunta.
Jalal a ransa yace 'Tsabar wulakanci ko ta gaisheni kota ce min ya hanya ba ruwan ta dani, hakan na nufin dagaske bata sona ne? Ko kuma tsabar rigima da taurin kaine? " Jalal ya gaza gano amsoshin tambayoyin sa, to bata kulashi da sannu da zuwa ba ma balle yasa ran zata zuba masa Abincin.
Kallon ta ya kumayi, kayanta cif jikinta ga mayafin iyakarsa wuyanta, hanun nan yayi kyau da lalle, kanta ba dan kwali dan haka yana iya ganin tsagar kanan kitso dake kanta.
Itama Jalila a ranta mita take "tsabar wulakanci koma ya tambayeni ya nake, bayan tafiyar sa ya na karke, ya tafi ya barni ba lafiya koya bugo waya yaji ya jikina, ya sani a gaba da kallo yaki cin Abincin in baze ci ba ni in tafi, mtseww ta danyi tsaki, tsakin ya fito fili ba tareda sanin ta ba.
Saurin dagowa yayi suka ha
a ido ta basar.
Mikewa yayi ba tareda ya kalli inda Abincin yake ba ya mike ze fice, itama ta mike da sauri tasha gabansa suka tsaya suna kallon Juna, lokaci na farko da suka kasance tare tun bayan daura Auren su
"lafiya meye haka?" ya tambayeta
"ya zan kawo Abinci ka tashi baka ciba? Salon in koma ayita tuhuma ta"
"in sun tuhumeki kice su koya miki yadda ake kula da miji, dan baki iya ba" Ta dan yatsina fuska ta kalleshi
"Waye mijin? Aini banga miji anan ba, kaima yakamata a koya maka yadda ake kula da mace dan..... Se kuma tayi shiru ganin yadda ya kura mata ido, Ashe fa yanzu mijinta ne, ba kowace magana yakamata ta gaya masa ba
"Ni kike cewa bakiga Miji anan ba ko?, Nagode sosai, matsa kibani guri in wuce"
Hanya ta bashi ya fice daga dakin, bata bi ta kan kayan ba itama tayi waje abunta.
Washegari ma da Safe Aka sa Jalila ta kai masa Abinci, haushin taki kulashi jiya yasa beci Abincin ba yakuma barinsa.
Yana fita ya tafi gurin Abee, bayan sun gaisa Abee yanata tsokanarsa, Jalal yace
"Abee so nake kasa baki su kaimin matata, ko in dauketa mu tafi basu sani ba"
Abee yace "A'a baza'ayi haka ba ai, kwantar da hankalinka, ko gobe kake so za'a kaimaka ita zan saka baki suba ka ita, na goyi bayanka tunda Daddynka yana jin nauyinsu, ina dalili kanada Aure amma sun barka kana ta fama sun rike maka mata" haka Abee ya lallaba Jalal ya tafi.
Yaje yasamu Anty yace mata "kinga tun wuri kubawa yaron nan matarsa yana son abarsa, yamuku kawaici amma kunki ganewa"
Anty tace "Abee Akwai dalilin da yasa muka riketa anan ne"
"A'a Ku bashi matarsa kawai, in baso kike kiga tafara miki laulayi a gidan nan ba, sannan ku kwasheta ku kaita"
Zare ido Anty tayi "Haba dai"
"Eh mana, yanzu da muka rabu da shi yake gayamin insa baki ku bashi matarsa"
Aimin hakuri fa rashin posting akan lokaci, abubuwa sunyimin yawa, adinga min uzuri nagode da kulawarku
Vote and

105

Zare ido Anty tayi tace "gaskiyane Abee, tunda ya iya budar baki yace a bashi matarsa he mean it, zanyiwa Anty Salma magana gaskiya, a bashi iga suje can su karata, tunda be san abun Arziki ba"
Abee yace "gara dai kuyi tunani, wannan ba mafita bace ku bashi matarsa kawai"
Tunda Abee ya bashi goyon baya A ranar Jalal ya shirya ya tafi kano ko sallama basuyi da Jalila ba, dan in dai suka hadu fada zasuyi.
Yayi waya da Daddy ya gaya masa yana son zeyi magana dashi, Daddy yayi masa Alkawarin zezo Nigeria su hadu a kano.
Ba zato ba tsammani Ilham ta dawo taga motar Jalal a harabar gidan, ai a guje takarasa cikin gidan ta nufi dakin
Mummy tana kwala mata kira,
"Mummy Kinsan Jalal ya dawo kuwa?"
Mikewa Mummy tayi "dagaske ko wasa"?
"Wallahi dagaske nake, ga motarsa can"
Jinjina kai Mummy tayi tace "Shikenan rabu dashi, nasan tunda yazo Akwai abunda ya kawo shi, kyleni da shi kawai"
Ilham ta koma dakinta tana cigaba da tunanin wani mataki Ummanta ke shirin dauka akan wannan lamarin, Itakuma me yakamata tayi?
Wasa2 kwanan Jalal uku da dawowa amma sam Mummy bata sa Jalal a idonta ba, da kanta taje dakin Jalal amma baya nan.
Ilham ma duk yadda taso taga Jalal bata ganshi ba, ko ina yake tafiya oho?.
Bangaren Jalila kuwa sekuma shan gyara takeyi, basu gaya mata Jalal yace zasu koma kano ba.
Kwanan Jalal hudu a kano sannan Daddy ya dawo, koda ya dawo babu wata tarbar Arziki daya samu daga Mummy se mita da masifa, Bebi takanta ba ya cigaba da sha'anin sa, babban abunda yake kular da ita kenan, tasa shi agaba taita masifa Amma ya kyaleta yaki kulata.
Ranar da Daddy ya dawo da daddare Jalal ya shigo, ba kowa a palourn dan haka ya wuce part din Daddy, shikansa Daddy yaji dadin ganin Jalal,
Daddy yace "Ango, Ango se wani kyau ka keyi, alamu hankalin ka a kwance"
Jalal ya dan bata fuska yace
"Ina wani hankalina a kwance yake, Kawai su Anty sunje sun rike ta a can gurinsu ko mene amfanin hakan oho?"
Daddy yai murmushi yace "Tunda sukayi haka Akwai dalili"
Jalal ya dan hade fuska yace
"koma meye dalilin nasu ni munyi magana da Abee zan dakkota tazo ta tare"
"Jalal meyasa kai haka? Zasu ga kaman bakayi musu kara ba"
"Daddy sati guda da komawa makaranta yakamata ace ta koma itama, sannan kasan in dai da Auren nan idan nazo kano bani da masauki, bani kwanciyar hankali saboda masifar Mummy indai nazo gidan nan, nasan bata son Auren nan, nikuma inason abuna, kaga ko nazo Kano a gidana zan sauka baseta ganni ba bazan zo mata gida ba"
Murmushi Daddy yayi yace "koma dai meye she's your Mum, yakamata ka dinga mata uzuri sannan ka dinga hakuri da ita"
Jalal yace
"Daddy maganar gidan da zan zauna ne yasa nazo Kano fa"
"to wane gidan zaka zauna, gadon kayan zaka koma kokuma yaya?"
"No bazan koma gadon kaya ba, zamana a gidan nan zena tunamin abubuwan da suka wuce masu batamin rai"
"to ya kake so ayi?" daddy ya tambayar yana bawa Jalal attention dinsa
"gida zan siya a tarauni, a can zan zauna in danyi nesa daku, bana son yawan fitina ko hayaniya, Gobe in Allah ya kaimu se muje ka tayani zaban gidan"
"hmm Jalal kenan, to ai tunda bani zan zauna ba, kai da ita matar taka yakamata ku zabi gidan da kuke so"
"Kyaleta kawai duk gidan dana zaba baza tace beyi ba"
"to shikenan ina fatan kun daidai ta kanku babu matsala"
"karka damu Daddy, in Allah ya kaimu gobe muje a siyi gidan, ka gayawa Abba, next week Insha Allah in basu kawo ta ba, zanje in dakko ta"
Daddy kallon Jalal kawai yake, jalal din maganar sa yake kansa tsaye kuma hankali kwance ba wata kunya ko makamancin haka a tare da shi.
Suna ta hirarsu ba zato ba tsammani sega Mummy ta shigo
akin, seda ta danyi turus ta tsaya, ganin Jalal da tayi kanan kayane a jikin Jalal kaman yadda yasaba sakawa, Amma abun mamaki dogon wandone har kasa a jikinsa, da riga me dogon hannu, wuyansa babu sarka, sannan babu wannan askin banzan da yakeyi kuma ya sawa kan color duk babu, yayi kiba abunsa kuma fuskarsa ba laifi a sake yana murmushi, sabanin da da kullum fusakarsa a murtuke.
Idan lissafinta dai2 ne kimanin watanni shida bata ganshi ba ko a waya baya kiranta, dama ina ta kai matsayin da Jalal ze aje lambarta balle ya kirata.
Jalal yace "Daddy in aka siyi gidan se a sai furnitures ma in saka, kayan kitchen ban san kansu ba maybe su Anty sa saimata, kokuma muje da ita ta siya"
Wannan statement din data ji yafi kowanne bata mata rai, su Jalal basu san ta shigo ba, dan sun bawa kofar baya, nan Take ta shakunu ta karasa shigowa dakin fuskarta babu walwala ta zo ta tsaya.
Jalal na ganinta ya maze ya jingina da jikin kujera ya dora kafa daya kan daya
Ta kalli Jalal tace
"Sannu mara mutunci wanda be san ciwon kansa ba, Jalal saboda ba ka maidani komai ba tsawon watanni shida ban saka a idona ba, kuma saboda kai ba dan mutunci bane har a hada kai ai maka Aire ba tareda izinina ba, saboda munafunci baka tuntubeni ba tunda akayi Auren nan ka hada kai da dangin ubanka kayi tafiyarka inda ta zaba maka, se yau ka dawo kana zaka saimata gida da furnitures, kudin na ubanta ne? Ko shi ya tara maka? Wallahi Jalal se an kashe Auren nan, ban yadda ka zauna da yarinyar nan ba, seka saketa kuma seka baro wannan tsinan nan aikin data samo maka a lagosa, tunda ba ita ta haifamin kai ba"
cikin masifa Mummy take wannan hakilon Masifar, har Daddy ya fusata zeyi magana Jalal yace
"No Daddy yi hakuri, ban sanka da fada ba, kayi shiru kawai, bari zanje in dawo" Jalal ya mike ze fita, Mummy ta kuma fusata tace
"Nizaka mayar 'yar Iska ina maka magana, Wallahi Jalal in baka saki yarinyar nan ba sena maka baki" cak Jalal ya tsaya ya waigo yana kallonta.
Daddy dafe kai yayi, dan shi a rayuwarsa sam baya son tashin hankali.
Jalal yazo gaban Mummy ya kalleta yace
"Mummy idan kikamin baki akan na wasu zaki
ora, inkin min baki baze dameni ba, tunda wanda yake dawainiya dani be ishekiba, baki da wata cikakkiyar hujja na kin Aure na, bazan saki Jalila ba saboda ina sonta, kema soyayya ce tasaki zama da mahaifina, nima na Auri wadda na rayu da sonta, baze yuwu amin Auren dole ba, tunda kema bashi aka miki ba"
"Jalal ni kake gayawa haka?"
Kai tsaye yace
"Yau na fara gaya miki gaskiya? Bazan Auri macen da bana so ba saboda san zuciyarki, da in saki mata ta gara kimin bakin, dama can a lalace nake, in kika min baki kinga dorawa zanyi"
Yana gama maganar ya fice.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji un, nashiga uku, dan dana haifa ya tsaya a gabana yana gaya min wannan maganganun, Habib Jalal ua zabi mace akaina da na haifeshi, ban taba zaton haka ba, tunanina Jalal shaye2 kawai yake, yaushe Jalal ya fara son Jalila da har yake gayamin wannan maganar akanta, tun yanzu, wallahi na tsani yarinyar nan"
Daddy yace "Khadija be kamata kiyi wannan maganar ba, bari in tuna miki wani abu, Soyayyar da nake miki tasa na zauna dake tsawon shekaru, na fifita ki fiye da Ahalina, kika rabani da kowa nawa, Ashe ba dadi, na fuskanci Soyayya bazata yiwa Jalal da wasa ba, dan haka ki shirya sa hannu ki karbi irin abunda kika aikata kema"
Mummy cigaba da rusa kuka tayi tama fadin
"Wallahi baze yuwu ba, ni na haifi dana ba'a isa amin iko da shiba, babu wadda ta isa ta juyamin yaro, nasan wannan makircin Salma ne, zata
au fansa a kan
ana, tana tunanin zata mallake min
a saboda wannan banzan shirin nata? Wallahi bata isa ba" tuni Idon Mummy yayi jawur tana kuka tana masifa, Daddy ba shi da zabin da ya wuce yabar mata
akin, dukda yadda yakejin kukan nata a zuciyarsa, Amma wannan fa
an rashin gaskiyane kawai take yi.
Ilham kuwa tana kitchen tana hada abunda zata ci, sama bata san Jalal ya shigo part din ba, tana daga kai ta window taga shigar Jalal part dinsa, gabanta ne ya fadi, ya wani kara kiba, wani tunani ne yazo mata, hakan yasa ta fito da sauri ta tafi part din nasa, tana zuwa ta tarar baya palourn dan haka kai tsaye itama ta bishi bedroom din nasa, Amma tana zuwa ta tarar har ya shiga toilet, gefen gadonsa ta samu ta zauna ba tare da fargabar komai ba, tayi a kalla mintuna Ashirin sannan ya fito sanye da gajeren wando jikinsa babu riga se karamin towel yana goge ruwan jikinsa, Sam Jalal be kula da Ilham ba, yayinda Ilham ta daskare a zaune tana karewa surar Jikin Jalal kallo,
Gaskiya Jalal ya kai a so shi koba dan dukiyar sa ba, ko ina na jikinsa kwance yake da gashi tun daga kansa har kafafunsa, dogone jikin sa a murde yake, dama ga jikinsa yana cin karfe, kallo daya zaka masa kasan namiji ne me matukar kwarjini, yana
aga kai yayi ido hudu da Ilham zaune akan gadonsa, a fusace yace "Ke meye haka? Uban me yakawo ki dakina a daren nan? Ta shi kifita ki barmin d
aki"
Mikewa Ilham tayi ta tako gaban sa ta tsaya tana kuma kare masa kallo, "Jalal dagaske kayi Aure ko?"
"Tambayata ma kike? Ban sani ba, fita ki barmin daki"
Towel din hannunsa ta karba, ta ajiye ta zuba masa ido, Hawaye ne ya fara bin idonta
"Jalal namaka son da ban taba yiwa wani namiji makamancin sa ba, Jalal why? Ina sonka Jalal, meyasa zaka Auri wata bani ba, Wallahi ina sonka, Jalal ka shmmace ni, ka Auri yarinyar da nafi tsana a rayuwata, Haba Jalal meyasa kamin hakan?"
"kina son Jalal ko kina son cutar da shi? Kina sona nikuma na rayu da son yarinyar da kika fi tsana, saboda a duniya a yanzu babu wanda ya gwada min so kamar yadda tayi, I love Jalila with all my heart, ba abunda bazan sadaukar akanta ba, i am sorry, kema Allah yabaki me sonki"
Wani kululun takaici ne ya tokare kirjin Ilham, Amma ta maze, hannu ta mika kirjin Jalal zata shafa kirjinsa amma ya rike hannunta, ya girgiza mata kai,
Ya dan lumshe ido ya bude yace
"Abunda yasa nake kara Son Jalila kenan, ba ruwanta da abunda ba nata ba, karki tsallake iyakar ki, karki taba mata miji kin san halin ta dai base na gaya miki ba, Abunda kike hari tsawon lokaci ya zama nata, a gaskiya ta miki ba dadi, ta rusa shirinki gaba
ay" ya karasa maganar yana
anyin murmushin mugunta, sekuma ya ha
e rai yace
"malama get out from my room"
Ilham tace "Amma Jalal"
"ki fitar min daga
aki malama, ko ba kya banbance abunda ya dace da wanda be dace ba? Kifita bana son ganinki" Jalal ya katseta
"Yaya Jalal..."
"kifita nace ko in miki Illa, natsaneki bama son ganinki, ki fita ki bar min daki ko in kakkarya ki"
Yadda yakoma yana maganar a fusace ya sa Ilham ta fita da sauri ta bar dakin. Wani dogon tsaki Jalal ya ja ya saka doguwar Jallabiya ya kwanta.
Ilham kwana tayi tana juyi ta kasa bacci, Jalal da ba ruwansa da mata yaushe ya fara Soyayya? Har yake gaya mata yana son Jalila fiye da komai, yadda taga rana haka taga dare zuciyarta kamar zata fito,tana karajin tsanar Jalila a ranta.
Kamar yadda suka tsara, Jalal da Daddy sukaje suka sai gida a tarauni, gidan yayi matukar kyau da tsaruwa, yanada girma sosai gidan, palour biyu, bedroom uku kowanne da toilet se kitchen biyi da store da katuwar harabar gida.
Daddy ya samu Abba akan, an sai gidan dasu Jalal zasu zauna, Jalal ze sai furnitures, Abba yace be yadda ba shi zewa Jalila kayan daki, Jalal ba dan yaso ba ya hakura, Abba da Maama sukaje suka ga gidan sun yaba gidan sosai, Abba seda ya cikawa Jalila ko ina da kaya, gidan ta yayi kyau ya tsaru matuka.
Sam Jalila bata san abunda ake ba, ita dai taga su Hajiya Salma sunata kara shiryata, Hajiya Salma taje ta samu Jalila a daki tace "Jalila ki ware gashinki, me kitso zatazo ayi miki kunshi da kitso, ranar Asabar zaki tare"
Zare ido Jalila tayi tace "Wai Asabar me zuwa?"
"Eh mana, mijinki yace; se kin tare ya gaji da wannan sintirin"
Shiru Jalila tayi ta sunkuyar da kai, Hajiya Salma tace
"Haba Jalila meye kuma na damuwa? Allah ya baku zaman lafiya, karki damu kinji" jinjina mata kai kawai Jalila tayi ba tareda tace komai ba.
Yau weekends ne, Hanan sun gama cin Abincin Rana da Jawwad, tana ta zuba shagwabarta yana biye mata, dan ba karamin birge shi wannan shagwabar take ba, yace
" Habibty Inaga ranar Saturday fa sister dinki zata tare"
"Wai Jalila?"
Jawwad yace
"eh ita, munyi waya da shi dazu da safe kina bacci, ya gayamin ya sai gida, an gama zuba komai ranar Saturday zata tare, inkuma sunki zeje ya dauketa ne kawai"
Dariya Hanan ta kama yi, Jawwad yace
"ya dai, ya naga kina dariya?"
"Akwai kura ne"
"Kura kuma? Meyasa kikace haka?"
"Hmm bakomai, gaskiya yakamata muje kano, zanso inyi kallon yadda wannan rayuwar masoyan zata kasance"
Jawwad yai murmushi yace "lafiya kalau zasu zauna"
"Hakane wuyatta su zauna guri daya, bari a jima in kirata, naga har yanzu bata da waya, se dai kabani taka in kirata"
Jawwad yace "Shikenan naga be bata wayarba har yanzu"
"nasan ze bata insha Allah"
Hanan ta mike ta tafi bedroom dinta.
Jalila tarasa meya kema ta dadi, wai ita ce zata tare a gidan Jalal, a matsayin matarsa, tanata tunane2, Amal tayi sallama, Jalila ta amsa, Amal tace "Anty Jalila, Mummy tace in kawomiki phone, your sister wants to talk to you"
Jalila a ranta tace ;kai yaran gidan nan sunfiye iyayi, ji yadda take magana kamar me koyon hausa
Jalila tasa hannu ta karbi wayar tareda cewa "Nagode"
Wayar aka sake kira Jalila ta daga wayar tareda fadin
"Salamu Alaikum"
Yanayin muryarta ze gaya maka tana cikin damuwa, Hanan tace
"Amaryar Yaya Jalal, ke ko kirana ba kyayi se idan nina kiraki ko?"
Cikin sanyin jiki Jalila tace
" kinsan bani da waya tun ranar dinner da ya karba be baniba, bana son yawan takura musu da karbar waya"
Hanan tace "hakane ya kike ya shirye2"
"shirye2 me?" Jalila ta tambaya
Hanan tace
"Ahhh Haidar yacemin ranar Saturday In Allah ya kaimu zaki tare"
Dan karamin tsaki Jalila tayi
"shine wani ya shirye2, ba wani shirye2 ni abun duniya ya dameni, ina tunanin irin zaman da zanyi a gidan nan"
"meye wani abun damuwa kuma? Karki dorawa kanki ciwo mana, Allah yabaku zaman lafiya yasa kina zuwa kiyi karo da shi"
Jalila tace "inyi karo dame?"
an baba mana, nan da wata tara muzo suna" hanan ta bata amsa
Wani uban tsaki Jalila tayi "Ke kinfiye shirme wallahi"
"bawani shirme, Addu'a nai miki tagari"
"rike addu'ar ki bana so, ni ba haka naje yi ba"
Dariya Hanan ta dinga yi "Wallahi karya kike, abunda kikaje yi kenan, sekin cika masa gida da 'ya' ya duk shekara zaki dinga haihuwa"
Kashe wayar Jalila tayi, tareda yin dogon tsaki, inta biyewa Hanan bata mata rai zata cigaba da yi.
Shirye2 sunyi nisa, Hajiya Salma da Anty sun tsaya an gyara Jalila yadda yakamata, sun hada mata kayan turaruka daban2, Suka shirya mata kayanta a trolley. Ta wani bangaren Jalila tanata murna zata koma garinsu, ta cigaba da zuwa makaranta,
Anty tace "Jalila na cika alkawarin dana taba yi miki, ga turaruka nan, in sun kare ma kiyi magana se in hado miki wasu"
"to Anty na gode"
Abee yayiwa Jalila nasiha sosai, tareda yi mata fatan Alkhairi, yabata kyautuka na litattafan Addini dana zamani, sekuma kyautar system yace taje taita karatu. Jalila tai tayi masa godiya.
Hajiya Salma sunyi waya da Jalal, cewar zasu taho da Jalila gobe zasu tsaya a gidan su Jalila, sannan su kaita gurin Mummy daga nan akaita gidanta.
Jalal yace "gaskiya bana son ku kaita gidan Mummy, dan seta bata muku rai, kawai ku kyale ta"
"A'a Jalal baza'ayi haka ba, Mahaifiyarka ce akwai bukatar a sauke hakkinta na uwa, yakamata ta sawa Aurenka Albarka"
Jalal yace "Shikenan yadda kuka gani, Amma ni a gurina babu bukatar hakan.
Ilham bata taba sanin tana kaunar Jalal ba kamar yanzu, gaba daya kishi ya hanata sukuni ko Abinci bata iya ci, ita a tunanin ta tana so tayi soyayya da Jalal ne dan cika burin mahaifiyarta, Amma yanzu ta gane kaunar Jalal tayi mata illa, bata bacci sam, yadda taga rana haka taga dare, wai Jalal ke gaya mata shidin mallakin Wata mace ne, macen da ta dade tana cusa masa miyagun maganganu da cin mutunci amma saboda bashi da zuciya yake fadin shi mallakin ta ne, hawaye ne ya gangaro daga idon Ilham tace "Wallahi Jalal muddin baka Aureni ba sena fitini rayuwar Auren ka, sena uzzurawa rayuwarku, se Gidan Auren ka yazama kurku ta fishi 'yanci, idan har kuka ji dadin Aure ba Saudatu ce ta haifeni" ta cigaba da kuka da surutai a daki.
Jalila se murna take zata koma Kano, koba komai zata dinga zuwa makaranta ta rage kadaici, karfe goma sha daya na safe suka shirya, Anty, Hajiya Salma, Husna, da wasu daga danginsu Jalal suka taho yiwa Jalila rakiya Kano,
Se kusan karfe hudu na yamma suka iso, Maama ta san da zuwansu dan haka ta riga ta shirya komai, har 'yan uwanta da makwabta ta sanar, bayan sallar magariba za'a raka Jalila gidanta.
Jalila tayi murna ganinta a gida, Abba yayi murna yadda yaga Jalila tayi kalau da ita tayi fes kaman wata matar hamshaki. Dakinsu taje komai yana nan yadda ta barshi, kewar Nana ta dinga ji a ranta, tana tuno abubuwa da dama da ya faru a wannan dakin, wasu ma farinciki wasu na bakinciki. Maama tazo ta sameta tace
"Jalila ki debi duka abunda kike so akayanki, wanda zakiyi Amfani da shi nan kusa se a tafi miki dashi"
"to Maama zan diba Insha Allah"
Sukaci Abinci sukayi Sallolin da ake binsu.
Anty tace "Jalila yakamata ki shirya muje a kaiki gurin uwar mijinki, kar dare yayi sosai"
Ras gaban Jalila ya fadi! Jikinta yafara Rawa, ta shiga duniyar tunanin wace irin karba Mummy zatayi mata.
Kamar wadda kwai ya fashewa a ciki ta Amsa, seda takuma wanka ta canza kaya, suka nadeta a cikin lafaya, se kamshi takeyi Maama ta kama hannunta ta kaita gurin Abba, ya dinga mata nasiha da Addu'a, Jalila se kuka take, yadda Abba yaji rabuwa da Jalila beji haka akan Nana da Jawwad ba, yana matukar tausayinta. Bayan ya gama ne Maama tayi mata 'yan nasihohi da Addu'a, dan sosai take jin kunyar abubuwan da ta aikatawa Jalila.
Wasu daga cikin' yan rakiyar amarya sunyi gaba dan suje suga
aki, Yayinda Hajiya Salma da Antyn Jalal suka nufi gidan su Jalal Da Amarya Jalila.
Vote, Comment and

......