PART 2
Abdul Jalal Part 2 Complete Hausa Novel · about 447 min read
_PAGE 1
/54_
Bismillahirrahmanirrahim, da sunan Allah me rahama me jinkai, Allah yakara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi muhammadu salallahu alaihi wassalam.
Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki, da suka bibiyeni a littafi na farko, Alhamdilillah yanzuma gani na dawo domin kawo muku kashi na biyu, nagode da kulawarku, ku biyoni domin jin yadda zata kaya a cikin wannan littafi naku me farin jini.
Banyarda a juyamin littafi ba ko amfani da wani bangare ba tareda izinina ba.
Domin gyara, shawara ko sharhi, za a iya tuntubata akan what's app number dina
07063065680
Gmail @ [email protected] Facebook @ real humaira
_MY FIRST NOVEL _
Jeje bude baki yayi yana kallon Hannah, dan yarasa meze ce mata, Hannah takuma kallon Jeje, ta nunashi da key din motarta
"wannan itace magana ta karshe dazanyi da kai, nidaku dan halak ka fasa, kome zefaru sena mallaki Jalal, indai na amsa sunana Hannah" daga nan ta dauki Jakarta tai gaba abunta. Dukan tabur jeje yayi da karfi, yasa kafa yai ball da tebur din "Why, ya haka ya za a yi abubuwa su lalacemin haka, akwai matsala muddin Hannah tace zata aikata abunda ta fada. Mukullin tasa motar ya dauka shima ya bar gurin.
Jalal yana gama cin Abincin sa ya mike yana hutawa, anata kiransa ana masa bangajiya, wayarsa yadakko, IG yashiga yana shiga yaci karo da hotunan birthday dinsa, abunda ya bashi mamaki, hotunan shida Jalila yafi yawa, shi akafi yadawa, fitowa yayi yakoma what's app still status din mutane hotunan ne suke yawo, shiru yayi ya kurawa hotunan ido, wani hotonsu ya tsaya akai yana kallo, yanda ta dan zumbura baki tana kallonsa, shikuma yana dariya, tsaki yayi "kalleta dan Allah se tsabar iya rashin kunya, shi mamaki yake yadda akayi tai mugun rainashi sam bata shakkarsa, kaman ba yarinyar dasuka dinga wasa da ita a zanin goyo ba, yan uwan sa mazama tsoronsa sukeji amma banda wannaan yarinyar, zuwa wani dan lokaci ya kashe wayar, ze ajiye kiran Jeje ya shigo wayarsa, kaman kar ya daga, seda ta kusa katsewa sannan ya daga
"hey man kana inane?"
"me zakayi min kake nemana?"
"ina wajene ina jiranka" "wajen ina kenan?" "kofar gidanku mana" "ok ina zuwa" Jalal ya duba yaga Jawwad yana toilet dan haka kawai ya fito, yana fita yaga motar Jeje a kofar gidansu, karasawa yayi ya tsaya bece komai ba, jeje ya fito yana wata shu'umar dariya da wannan katuwar muryartasa yace "man of the day, our celebrity yane?"
"Normal, mukarasa cikin gida" Jalal ya fada a takaice, yaiwa Jeje jagora zuwa part dinsa, suna zuwa Jeje yanemi guri ya zauna, Jalal yaje fridge ya dakko wa Jeje ruwa da lemo, ya hada da giya ya aje masa, Jeje ya dan kalli Jalal yace "J man, ya gajiyar jiya"
"gajiya tabi lafiya" "good wai ya akayi ka bar gurin nan jiya, ban san ka tafi ba?" Jalal ya danyi shiru yana tunani sannan yace "gaskiya i can't recall, Hannah tabani wayne jiya, bansan meyakuma faruwa ba, ban san ya akayi na dawo gidaba, na tambayi Jawwad ma yace min ba shi yakawoni gida ba, i think ansamun wani abu a giyar nan. Dan zare ido Jeje yayi, dayaji statement din Jalal na karshe amma ya maze yace "anyway but J man, akwai wata cute baby da pictures dinku suke yawo social media, tagama haduwa babyn nan, nifa tayimin wallahi, inaso insata a harka"
"wace yarinya kenan?" Jalal ya tambayeshi a takaice, Jeje ya zaro wayarsa ya nunawa Jalal hoton Jalila, tareda fadin "wallahi Jalal komai yaji ajikin yarinyar nan, zanso tayi joining insata a layi, zata kawo harka, maganar tama kawai abar sha'awa ce komai nata na birgewa ne, gaskiya ta hadu"
Wani mugun hade rai Jalal yayi, ya kalli Jeje a fusace yace "Are you out of your sense, wai kai bunsurun inane da duk inda kaga mace jikinka har rawa yake, let me warn you, Wallahi3 na rantse maka, muddin wani abu yasameta sena daureka, kasan wacece? Kanwar Jawwad ce, yarinyar da yakeso, danme zaka dinga wannan kazamin maganar akanta, karka kuma fadin wani magana akanta kota arziki kota sharri akanta, wannan yarinyar ba irin jakan matan dazaka iya nasarar lalatawa bane, kaji na gaya maka take your leave now "ya nunawa Jeje hanyar fita, wani irin kallo Jeje yaiwa Jalal, amma seya daidaita nutsuwarsa yace" is ok j man bansan abunda ke tsakaninku bane, ashe kanwar kace, na dena bazan kuma ba kayi hakuri "
" Naji amma for now tashi kabani guri, raina yagama baci, tashi ka tafi" ba musu jeje ya mike ya fita.
Da Jawwad yafito yaga Jalal ya tafi, kawai se shima yafito, yaga Jalila cikin flours dinta tana gyarawa, ya fuskanci tanason furanni, a hankali ya karasa inda take ya zauna, ta waigo ta kalleshi, tai murmushi "Allah yatemaki yayana na kaina" Jawwad yai murmushi yace "Ameen yar baby, ya meyasa kikeson furanni ne?" "nima ban saniba, kawai dai ina sonsu ne, na gidanmu a kaduna nasan sunyi missing dina, in bana nan ummi ke kularmun dasu" sekuma tai shiru idonta yacika da kwalla, Jawwad ya nisa sannan yace "am sorry, nagane kidena damuwa kinji kicigaba da addu a muna kan nemanta har yanzu" gyada masa kai tayi tareda murmushi, yace "Yawwa babyn Yayanta" yasa hannu a aljihunsa ya dakko chocolate yabata, hannu tasa ta karba tana murmushi, tareda kokarin maida hawayenta, tai murmushi tace "Nagode Ustaz" "yaukuma nine ustaz" "Eh mana" sukayi dariya gaba daya, Jawwad yace "yawwa baby, nace wai me yafarune jiya? Ya akayi manu ya kawo Jalal gida, dazu yake tambayata ya akayi ya dawo gida" Jalila tai ajiyar zuciya tace "Hannah ce ta kaishi wani guri suka bashi wani abu, naga yafita hayyacinsa, tasaka wani yaimata gadinsa ta tafi tana waya, kawai naji ban yadda da itaba, shine na dauke hankalin wanda tasa gadinsa nasa Manu ya daukeshi ya kaishi gida" shiru Jawwad yai na dan lokaci sannan yace "thank you for your contribution my dear, hakika kintemake shi, maybe akwai abunda sukeson yi masa, narasa meyasa Jalal yakasa gane basa kaunarsa, anyway mungode sosai Baby Amma ya akayi kikasan Hannah"?
"A a, ban santa ba agurin naji ana fadar sunanta, Yaya Jawwad no need kaimin godiya fa, manta kawai, amma akwai wani abu da nagani yabani mamaki"
"Mekika gani?"
"Wannan mutumin na rannan, da ya dinga zagin Jalal, dan kun gaisa da dansa, shima fa yaje gurin nan, abunda yakara bani mamaki shida wannan Jejen naga suna magana, shiyasa nace maka shima yana kama da yan shaye2"
"Anya kuwa shi kika gani, maybe kamace kawai, bana zaton baban Faruk a irin wannan gurin, saboda yanada tsatstsauran ra'ayi, kece dai kike masa kallon ba mutumin kirki ba "
"Yaya kenan shikenan tunda baka yadda ba, magariba tayi bari inje inyi salla"
"to shikenan, dan Allah anjima ki dafo mana wannan tea din naki me dadi"
"Hmmm yayana kwadayayye kawai" "ke kika koyamin kwadayin ai" tai murmushi ta mike ta tafi cikin gida, Jawwad kuma ya fita masallaci.
Tunda Jeje yafita yake zancen zuci "lallai tunda Jalal yaketa masifa akan yarinyar nan to ba karamin matsayi take dashi a gurinsu ba, lallai dama tazomin akan wannan fitsararriyar yarinyar zan jefi tsuntsu biyu da dutse daya" Jeje ya kyalkyale da dariya, sekuma ya hade rai daya tuno da maganganun Hannah, dakuma abunda Jalila ta gaya masa ranar birthday din Jalal, "muje zuwa yan mata mu daku zanga wazeyi nasara"
Bayan sallar isha'i Jawwad yasa Jalal a gaba yayi salla suka zauna suna hira, Jalal yace "Jawwad ina jin bacci, bari in tafi gida" "No karka tafi yanzu ka tsaya baby zata kawo mana tea, ka tsaya kasha seka tafi" "ok bari in jira, ina son sha, kasan wani abu"
Jawwad yace "A a seka fada" "har yanzu ina mamakin me aka zubamin a giya wanda ya bugar dani haka tsawon lokaci"
Jawwad yai ajiyar zuciya "Jalal shiyasa nake gaya maka tun ba yauba, hulda da mutane irin wannan be kamata ba, kasan wani abu? Jalila ce tasa aka dawo da kai gida, tunda kafita daga gurin nan, ni bansan meyafaru ba, bayan ka bugu tasa manu ya daukeka yakawoka gida" kallon Jawwad ya danyi, ya dan tabe baki irin he don't care din nan, wayar Jawwad tafara ringing, ya kalli Jalal yace masa "excuse me please" ya daga wayar
"Hello My Jawwad ya kake?"
Muryar Hanan ce, Jalal ya kafe Jawwad da ido, Jawwad yace "ina lafiya Hanan, ya mutan gidan"
"Nifa fushi nake, ashe Jalal yayi birthday bako gayyata ko my Jawwad"
"A a Hanan ba haka bane, Jalila ce ta gayamiki ko?" "A a, wannan ce zata gayamin, bata gayamin ba, hotuna nagani suna yawo a social media, kunyi kyau bama hotonta da Jalal, best couples of the year, kyanta ace wedding pictures ne"
Ba Jawwad ba hatta Jalal dayake gefe yana jinsu seda gabansa ya fadi, amma yarinyar nan ta cuceshi, tarasa dawa zata hadashi se wannan fitsararriyar yarinyar Allah ya kiyaye,
Hanan tace "My Jawwad ya kayi shiru ne" "bakomai Hanan, ni banga hotuna nan ba" "bari in turomaka, zaka gani sunyi kyau, idan birthday na yazo, irinsu zamuyi" Jalal yawani hade rai, Jawwad ya kashe wayar, ya dafe kai "wallahi wannan yarinyar tafi Jalila rigima" Jalal ya dan kalleshi, wa din? Kafadi son ranka dai" "ba son rai bane Jalal, hanan tafi baby rigima, banason Jalila ta gane, zataji ba dadi" dariya Jalal yayi "ganewa ta nawa sedai kar akuma, ai gara Hanan din akan wannan fitsararriyar, gara ta gane din" wani irin kallo Jawwad yai masa, ya cigaba da latsa wayarsa, hotunan da Hanan ta turo masa yake gani, wanda mafi yawa Jalila ce a jiki da Jalal, nan take yaji wani abu yazo ya tsaya masa a rai, Hanan ta turomasa "ya ka gansu, sunyi kyau sosai, sun kuma dace da juna" da sauri Jawwad ya rufe data, ya kashe wayar gaba daya yayi shiru, shikuma Jalal ya nuna ko a jikinsa, kuma yasan shima Jawwad din kishi yake, dan yasan zeji ba dadi, Jalal yai kaman besan wasu hotuna bane, ba a dadeba sega baby Jalila ta kawo musu tea, amma taga Jawwad wani iri, kaman yana cikin damuwa, ta dan kura masa ido tace
"Yaya lafiya dai, yanaganka a haka, kowane abu ne yafaru" girgiza mata kai yayi "Bakomai Jalila" gyda kai tayi, ta tashi ta tafi, Jalal ya zauna ya sha tea dinsa yayinda wanda aka hada tea din dominsa yakasa sha. Bayan Jalal yagama, ya mike abunsa ya tafi gida. Daren ranar da kyar Jawwad yayi bacci, yana matukar son Jalila, meyasa hanan takeson rikita komai ne tana kokarin hada Jalila da Jalal itakuma ta maye gurbin Jalila, sam hakan ba me yuwuwa bane haka ya kwana wannan tunanin. Bangaren Jalila kuma, ta takura kwakwalwarta gun tunanin meye alakar, baban faruk da Jeje, idan har shi yana hulda da mutumin banza kaman Jeje, to mezesa yayiwa Jalal wannan muguwar tsanar haka? Waima yanzu a gurin wa zataji waye Jalal, waze gayamata tarihinsa, Jawwad sam yaki gayamata,sannan meye burin Ilham akansa, meyasa hanna ta bugar dashi haka ranar birthday dinsa? Tarasa me bata amsar wannan tulin tambayoyin, ji tayi kanta yana neman yafara ciwo, dan haka ta hakura da tunanin tayi bacci.
Ya zuba mata ido yana ta kallonta tana shiryawa a gaban mudubi, dan waigowa tayi, ta kalleshi tai masa murmushi "ka dena kallona" "ta yaya zan iya dena kallon ki, kowa yana son abu me kyau, ni kekadaice abu me kyan da idanuna ke iya gani, kinga babu batun dena kallonki" murmushi takumayi masa "hmmm my cwt kenan, to nagama yi maka kwalliyar zo ka daukeni" ba musu ya mike yazo gaban mirror ya tsaya ta miko masa hannu, ya dauketa kaman wata yar baby, ta makalkaleshi tana dariya, ya nufi kan gado da ita, yayinda take kallonsa tana murmushi.
A hankali JALAL ya bude idonsa, yana kallon dakinsa, idonsa ya sauka akan agogo, karfe takwas dai2, se yanzu yagane mafarki yake, wani dogon tsaki yayi, ya tashi zaune "wannan wace irin masifa ce, shikenan kullum babu mafarkin wadda zeyi se wannan yarinyar, shi a yanayin dayake ganinsu ne shida ita yake bashi haushi" tsaki Jalal ya kumayi ya sakko daga kan gadon ya tafi toilet, domin yin wanka yai salla "
Karfe tara da rabi, Jalila tana ajinsu, an fara lectures, amma sam hankalinta baya kan malamin, tayi zurfi a cikin tunanin ta, gata a aji amma hankalinta yayi wani gurin, lecturer ya kalleta, cikin tsawa yace mata" Ke! Tunanin me kike haka ina lectures " a hankali ta dago ido ta kalleshi, ta maida idonta kasa, ba tareda tace masa uffan ba," ni kikewa wannan kallon ina miki magana, tashi tsaye, seda taja wasu seconds sannan ta mike, "bayanin me nagamayi yanzu?" ta daga ido, suka kalli juna itada malamin, ta dauke kanta tai masa shiru "wai ba magana nake miki ba" still dai shirun takumayi "ok get out from my class" ba musu balle bada hakuri ta dau jakarta, da wayarta ta nufi hanyar fita wasu suna kibashi hakuri, banza tayi musu, malamin yacigaba da mita "irin wannan sune jakan aji, irinsu ke kwasar carry over, se tsabar iskanci waisu yaran masu kudi" "tunda ka koreni kuma gashi na fita kacigaba da yimusu lectures din mana karka shiga lokacin su" tsit ajin yayi ana kallonta, tai ficewarta abunta" mamaki ne yacika daliban, dama tana magana haka, amma Allah yayi mata baiwar murya me dadi, sedai ana tsoron lecturer saboda masifaffe ne, da kyar in bata jawa kanta carry over ba a gurinsa, dan masifaffe ne gashi baya uzuri, yan ajin suka fara gulma, ji yadda take magana da izza, lallai wannan muguwar yar rainin hankali ce, itakam tana fita tasamu guri ta zauna ta cigaba da tunaninta
Siyama ce tafado mata a rai, kwana biyu basuyi waya ba, dan haka ta dakko wayarta ta kirata, bugu biyu Siyama ta dauka
"hajiya Jalila manyan kasa talaka najinku dama"
Jalila tai murmushi "ke banason wulakanci fa, yakike yasu umma?" "duk muna lpy Alhamdilillah, yauba lectures ne naga kin kirani yanzu" "akwai lectures koroni akayi" Siyama tace "hali zanen dutse, har yanzu biki canza ba ko? To university ba secondary school bace, ko islamiyya, Allah sarki malam babba yanata tambayata ke"
"Allah sarki malam, kice masa ina lafiya, ke ba ruwana da wata university, wani hakuri zan bashi ya riga ya koreni, hada wani wai irinmu ne dakikai" "hnm adinga hakuri dai sisy, nace ya mutuminki kuwa?
" waye mutumina kuma? "
" Jalal mana" siyama tabata amsa
Tsaki Jalila tayi "ta yaya yazama mutumina?" "knfi kowa sani, nace yafara shiryuwa kuwa? " "tab shiriya se ta Allah, dan banga alamaba, abun se addu a, niba wannan ba ma kinsan wani abu" "a a sekin fada" "Siyama hanan ce takeson Yaya Jawwad dina, kuma fa da gaske take" "to meye a ciki, ai abun farincikine" "haba Siyama ya kike fadin haka, da wanine ba yaya Jawwad ba, se in hakura in barmata, amman kaman baki san abunda ke tsakanina da yaya Jawwad ba"
"da kenan abunda ke tsakaninki da Yaya Jawwad, amma yanzu naga kin canza sheka zuwa Jalal" "mtseww, kinfiye wasa Siyama, wannan bugaggen uban me zanyi dashi"
"karki rainamin hankali mana, in bahakaba me yakaiki gurin birthday dinsa kukayi hotuna, hada kallon soyayya" zare ido Jalila tayi "nidin, nasan naje gurin birthday dinsa, amma wani irin kallon soyayya" siyama tai dariya tace "kai Jalila ansan madarar gogewa mutane hadda, to a status din mutane na ganku"
lecturer da yakori Jalila ne ya taho, da wasu dalibai su hudu suna binsa, Jalila tace "hmm ke se anjima, zamuyi waya" ta kashe wayarta, lecturer yazo saitin Jalila ya tsaya ya kalli daliban "kun ganiko, na koreta daga aji, memakon tabani hakuri tazo nan tayi zamanta tana waya da samari, se karshen semester yazo tasamu carry over ace bani da mutunci" ita dai shiru tayi masa, yagama masifarsa yai gaba, wani daga cikin daliban ya dawo da baya yace" yan mata meyasa baki bashi hakuri ba ai ba a haka tunda gaba yake dake seki lallaba a rabu lafiya "
"akan me zan bashi hakuri, yayi kama da wanda za abawa hakuri ya hakura ne? Kuma fa dagani hakurin kuke bashi kowata alfarma kuke nema a gurinsa amma ga yadda yake wani shareku"
"eh to kinsan Jami' a se hakuri, kowane lecturer da irinsa, kuma ko dan kar ya kadake, ai da kin bashi hakuri " Jalila ta kalleshi tace
" Yaya na nagode da shawararka amma bazan bashi hakuri ba, kuma koda ban taba zama a lectures dinsa ba banida test banida assignment indai zan shiga exams dinsa sena ci" tana gama fadin haka ta mike, tai tafiyarta. Ji tayi yau makarantar ta isheta dan haka ta kira manu, tace yazo ya maida ita gida , befi minti shabiyar ba sega manu yazo, ya dauketa don tafiya gida, Jalila tace "Manu wai yana ganka haka, kaman mara lafiya" manu yace "ke dai bari Mamace ba lafiya an rubuta mata maganin dubu hudu, kuma ni bani dako sisi, gashi ba adade da biyana albashi ba"
"Allah sarki amma meyasa baka tambayi Abba ba"? "haba Jalila, idan na tambayeshi ai ban kyauta ba, kullum cinkin yimin hidima yake, sedai inkina dashi ki aramin" "Bakomai akwai kudi a account dina muje banki, se mu tsaya in ciro in baka" "kai godiya nake uwar dakina, Allah yasa kifi haka, Allah yabaki miji nagari, ya jikan magabata, Allah ya...
" Ameen nagode, godiyar ta isa haka, yi sauri muje"suna zuwa banki Jalila ta sauka ba layi sosai, dan haka bata wani dade ba ta ciro kudin ta nufo hanyar fita taji ana fadin
" Yan mata adon gari, in baku babu gari, inkunyi yawa gari ya baci, amma kyawawa irinki dazasu cika garin nan, dayakara kawatuwa, barka da wannan lokaci" daga kai tai ta kall
i me maganar, koda tai tozali dame maganar, take gabanta ya fadi.
More Comments More typing.............................
_ABDUL JALAL (2020)_
_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)
PART
_PAGE
/ 55_

Follow the group of ABDUL JALAL NOVEL FANS through this link
https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL
Follow me on watpad @Ayshercool7724
_MY FIRST NOVEL _
A hankali ta daga idonta, tasa a cikin nasa bata manta fuskarba dukda gani biyu ta taba yimasa, baban faruk ne, bako shakka shine, wani shu'umin murmushi yayi mata irin nasu na yan duniya "ko baki gane ni bane"? wani kallon rainin hankali tayi masa" sannan tace "dukda kasancewar kwakwalwata tana rike, tareda tuno abubuwa masu mahimmanci da suka shafeni ne, amma hakan besa na manta wannan fuskar ba"
"Kenan nima inada mahimmanci a gurinki tunda har kika tunoni? " "sosai makuwa kanada mahimmanci, shiyasa na iya tunaka" wani murmushi ya kumayi "Amma naji dadin zama daya daga cikin masu mahimmanci a gurin wannan kyakyawar halittar, amma meyasa nazama me mahimmanci a gurinki" Jalila a zuciyarta tace saboda ka shigo cikin suspect dina amma a zahiri tace
"saboda kasancewar ka uba nagari, me kokarin kare mutuncin dansa daga hulda da mutanen dabana kwarai ba" "kinji haushin abunda nayiwa Jalal kenan, amma inkika duba ya cancanci hakan, duba da yanayin wani irin mutum neshi" Jalila ta dan kuramasa ido, kai da ganin mutumin nan kaga rikakken dan duniya, tsabar iya barikine yasashi yake acting kaman mutumin kirki, "excuse me please komai nawa a ka'ida nakeyinsa ina da abubuwan yi yanzu se anjima" yai saurin dakatar da ita ta hanyar cewa "yi hakuri dan tsaya mana dan Allah, ina so mudinga haduwa muna gaisawa ne, in bazaki damuba ga complementary card dina seki kirani, dakuma adress dina, mutane na musamman nake bawa wannan adress din" hannu tasa ta karba ta kalli katin ta juyashi, ta dan kalleshi na wasu seconds, tsaf ta haddace lambarsa da adress din jiki, sakin katin tayi a kasa tai masa wani kallo da yakasa gane me take nufi, kawai ta juya tai tafiyarta, tsayawa yayi ya zuba mata ido, "gaskiya wannan yarinyar yar rainin hankali ce, amma kota halin yaya, seya gane wacece din Jalal, kuma se yayi yadda yakeso da ita
Itakam tana fitowa ta kalli manu tace " yi hakuri manu na dan dade, muje nagama"ta shiga mota suka tafi, ta dakko kudin tabawa manu tace gashi nan, aiwa maman sannu, kuma ita kyauta ta bashi ba rance ba" manu kaman ya yi kuka dan murna se godiya yake mata.
Jalila na zuwa gida, ta tarar gidan ba kowa dan haka ta tafi dakinsu ta haye gado ta sha baccinta, alhalin school ana can ana lectures, se bayan azahar ta tashi, tana tashi da baban faruk ta tashi a ranta, ras take kuma ganin katin daya bata a idonta,
kabiru Idris, shine sunan dayake jikin katin, wayarta ta dakko tayi saving sunansa da lambar sa, da adress din dayabata a jiki, duk tayi saving a wayarta, sannan ta aje wayar a hankali, sannan tace kaima ban yadda da kai ba. Ta tashi ta tafi kitchen ta hado cornflakes dan tana jin yunwa, maimakon ta koma daki seta fito harabar gidan tai zamanta a kujerun harabar gidan, ta gefen Jawwad dayake gurin akwai bishiya, ta zauna tana shan cornflakes dinta, tanayi tana karanta qura'ani a hankali, tana dan ka
a kafarta, Jalal ne ya shigo yazo ya wuce ta gabanta bata kulashi ba be kulata ba, ya wuce part din Jawwad, yana zuwa ya dau laptop dinsa da yabari a dakin ya samu guri ya zauna ya fara video call da daddynsa
"My Man ka girma, naga hotuna na birthday kunyi kyau Allah yakaro tsawon rai da lafiya me inganci" "to Ameen amma ni fushi nake da kai"
Daddy yai dariya "to menayi?" "Kaje ka makale a England kaki dawowa, bakayi attending birthday na ba" daddy yai murmushi "to ai nace ka daga birthday din indawo kaki, kuma abubuwa sunyimin yawa anan gakuma aikin daka sani, koka manta ne?" "ban manta ba daddy, ina fatan ana samun cigaba" "eh anasamu Alhamdilillah" "to hakan yayi kyau, yaushe zaka dawo?"
"ina nan tafe next week Insha Allah"
"To dan Allah ka dawo haka, inaso indinga ganinka" daddy ya dan girgiza kai "Allah sarki yarona, karka damu, nace kazo nan mu zauna tare kaki" Jalal cikin damuwa yace "Haba daddy, in taho nan in bar aminina dan uwana, kasan bazan iyaba" "Hakane Jalal, ina Dan nawane, ko yau bakwa tare?" "Yana makaranta" "that's good, Allah ya nunamin ranar da zaka koma makaranta, yanzu ka zama mutum Jalal ina fatan Allah ya shiryamin kai inmaka aure" ya mutsa fuska yayi ya kalli system din "Aure kuma? Habaa daddy yaushe aka haifeni, ni banason gayyatowa kaina matsala, mata matsalane daddy kaima kasani" ya karashe maganar kaman zeyu kuka,
"ABDUL JALAL, bakowace mace ce matsala ba, in har kayi dace da samun mace ta gari, kaga hotunan birthday dinka danagani, dana ganka tareda Takwararka abun yamin da
i, senaji dama matarka ce, yarinyar tanada nutsuwa ga tarbiyya " wani mugun hade rai Jalal yayi "What matata kuma, Allah ya kiyaye, wannan kwailar, mara kunyar, na auri wannaan sedai kuzo ku tarar na kakkaryata"
A gigice Ilham ta tashi zaune, ganin hotunan da aka turomata ta what's app, ba tareda tasan waye ya turoba, hotunan dasu Jalila sukayine, a kasa aka rubutamata "Yakika gansu, perfect match, ina musu fatan Alkhairi, da fatan kasancewa tare har abada, wannan itace matar data dace da Jalal bake ba" mikewa tsaye tayi akan gadon, "What ni za ayiwa wannan rashin hankalin, lallai Jalila tayi bal'in rainamin hankali. Ba tunanin komai, taja gyalenta tai waje, Mummy tana yimata magana amma taimata banza, ta fita se gidansu Jawwad, tana zuwa taga mutuniyar tata a hakimce a farfajiyar gidan, kusada part din Jawwad, a inuwa se kada kafa take, tana ciye2 hankali kwance, bazar2 Ilham ta tunkari Jalila taje kanta ta tsaya tana huci, Jalila kam kaman ba kowa a gurin, tacigaba da abunda take. Cikin masifa Ilham tace
"Wato gargadin danayi miki bakiji ba ko? Saboda kin rainamin hankali, abunda kukayi keda JALAL a gurin birthday dinsa be isheki ba ko? Hakan be miki ba seda kika hadani da wannan tsinanniyar yarinyar Hannah a gurin nan, Shine duk be miki ba sekin hada da turomin hotunanku, sau nawa ina gaya miki kifita harkata, ina tausayawa rayuwarki idan na tashi hukunta ki" Ita Jalila abun mamaki yake bata wai wace jarabar hotuna na ake damunta haka akai, ba tareda ta kalli Ilham ba tace
" tunda kekika halicceni dole ki tausayawa hukuncin dazaki yimin mana, ki kasheni ki huta mana, seki tabattarmin dake kanwar Jalal ce, hakan se ya tabbatar da cewar bashi kadai yake shan giya ba"
Takarasa maganar cikin ko in kula, tacigaba da watsa cornflakes dinta a baki, Ilham ta kawo iya wuya, wato Jalila takai karshe gurin raina mata hankali, idonta taf hawaye tace "Wallahi Jalila in baki fita hanyata data Jalal ba, kina daf da fadawa rijiyar sharrina, idan nasakoki gaba ruwa seya gagareki sha, Inakuma yimiki kashedi kinfara kaini bango, idan turn dina yazo bazaki ji dadi ba, ki kiyaye.
Jalal ne yake tajin hayaniya, har ya basar ze kwanta seyaji hayaniyar yana kara yawa, dan haka ya yanke shawarar fitowa dan ganin meke faruwa, yana fitowa ya tsaya a kofar part din Jawwad yana kallon dramar da ake.
Ilham tacigaba da cewa
"waike wace irin mayyace? Mara zuciya, meye hadinki da mune, baki da alaka ta kusa ta nesa damu why do you involve yourself in our family matters, nagaya miki nakuma gaya miki Jalal nawane, wace irin mara zuciya ce ke, kishiga hankalinki harni zaki turawa hotuna, kina kece kika dace da Jalal, zakiga wacece Ilham, na daga miki kafa amma baki ganeba, zakiga me zanyi" Kamshin turaren JALAL Jalila taji, hakan ya tabbatar mata da fitowa yayi, dan haka bata kula Ilham ba ta mike tsaye, ta taka a hankali, cikin takunta na isa, kunsan fa Ummi jinin sarauta ce dan haka akwai abun
a jinin Jalila, taje gaban Jalal ta tsaya, ta kalli Jalal sannan ta kalli Ilham, ta nuna Jalal sannan tace "Wannan shine mara zuciya, mara tarbiyya shiyakamata, kigayawa bakaken maganganu bani Jalila ba, shi duk abunda yake meyasa baki ja kunnensa ba dan kina tsoronsa, kokuwa dan abunda yake ranki wanda kike boyewa, to ni bana tsoron kowa se mahalicci na, aike karamar mara kunya ce, ni idan zanyi sedai aga na aikata, bana fada, idan akabari nafadi abunda zanyi komaj muninsa sena aikata, ke alwashi nawa kika dauka kika kasa cika ko daya, Tunda ABDUL JALAL yashiga rayuwar Yaya Jawwad to a cikin rayuwata yake, shi zaki Jawa kunne ya rabu da Jawwad, in har ya rabu da Jawwad, ba ruwana da shi, bari kiji in gaya miki za ayi dayan biyune ko Jalal ya fita daga rayuwar Jawwad kokuma kudirina....
Sekuma tai murmushi ta kalli Jalal
"Kagayawa wannan sokuwar yarinyar, niba abunda zanyi da kai, baka da abunda ze birgeni insoka bana cikin jerin banzayen matan da zasu zubar kimarsu da ajinsu akan namiji mara daraja irinka, wanda besan ciwon kansa ba balle yasan na wani, namijin da besan darajar iyayensa ba, namijin dabaya girmama alaka, dan da kanayi da zuwa yanzu ka tausayawa Jawwad kadena abunda kake, namijin dabe maida sabon Allah komai ba, baya kunyar sabawa mahaliccinsa agaban kowa, shikike tunanin ya cika siffa da kamalar dazan soshi a matsayin uban y'ay'a na, shi kike tunanin zan zubar da kimata ina hayagaga dake akansa "ta nuna Jalal sama da kasa da hannunta
" Ilham ki canza tunani, Jalila ba irin sauran matan da kike tunani bane, duk abunda kikaga inayi i have a mission, kawai ina kokarin rama Alkhairi ne da Alkhairi, karki manta da maganar dana yimiki abaya muddin kudirina yaci karo da na wani zan rusa kudirin ko uban waye dan cikar burina" ta waiga ta kalli Jalal, da idonsa tuni yayi ja, gashi ya kasa matsawa daga inda yake kaman an dasa shi, Ilham rasa bakin magana tayi, Jalila ta kalleshi a wulakance, kaikuma ka gayamata ta kiyayeni dan muddin takuma cin mutuncina saboda kai akanka zan rama, har sena gamsar da ita cewa bawata alaka me ma'ana tsakanina da kai" tana gama fadin haka takoma ta dau Cup dinta tai cikin gida ta barsu nan a tsaye.
A hankali ya lumshe ido, ya tako a hankali ya nufi hanyar fita, Ilham tai sauri tace "Yaya Jalal dan Allah...
Daga mata hannu yayi alamar baya son jin mezata ce, yai gaba abunsa, maganganun Jalila na cigaba da tafarfasa zuciyar sa. Yana shiga gida ya nufi part dinsa ya samu guri ya zauna ya dafe kai yai shiru, Ilham ta biyo shi tazo ta zauna a kusa dashi, "Dan Allah yay Jalal kayi hakuri, nibani da laifi anan, kawai ina kokarin kare alakar dake tsakanina da kaine, meyasa bazaka yadda dani a in zama wani bangare na rayuwarka ba"? Tashi tsaye yayi ya tafi bedroom dinsa ya kulle kofa ya barta a palour.
Jalila koda ta koma dakinsu, kwanciyarta tayi ta dakko wayarta, tafara chatting, ta bude pages da take advertising kayan da Maama dakuma Mummy Jalal suke siyarwa, tana kawo musu customers sosai, daga gurare daban2, wasu suzo da kansu, wasu kuma a aika musu har garin da suke, gashi Jalila ma tana harkar catering ta iya girke2, wani lokacin ta kanyi snacks ta siyar, gashi duk karshen wata Abba yana basu kudi, wani lokacin dubu Ashirin zuwa talatin, inda me bukata tayi amfani dasu, Jalila bata da wata matsala se na kewar Ummi da har yanzu yake damunta, dan har yanzu takan kulle kanta tayi kuka me isarta, tana naan tanawa Ummi Addu"ar Inda rabo Allah ya kuma hadasu.
Chats dinsu da siyama ta bude taga ta turomata hotuna tana dubawa taga hotunanta ne da Jalal, wani dogon tsaki taja yanzu watakila saboda wannan hotunan Ilham tazo kanta tanamata hauka, har zata rufe data dinta taga wani sako ya shigo, tana budewa taga an mata sallama, ta duba profile din taga basuda group in Common dame maganar, amma an rubuta unique zarah, batayi reply ba ta rufe data. Da Nana ta dawo tayi mamakin ganin Jalila a gida, Manu yagaya mata ai tun goma da rabi ya dawo da Jalila gida, Nana ta kalli Jalila
"Jalila ya akayi naganki a gida, manu yacemin tun safe kika dawo, kobaki da lafiya ne?" "lafiyata kalau zaman makarantar ne ya isheni, na dawo gida" dan zare ido Nana tayi to lectures dinfa? "
" Kinga ki manta kawai"
"Bangane in manta ba kefa al amuranki se a hankali" "A a nagaya miki gaskiya to meye na tuhumata" Nana tace "tabdijan, A haka zakiyi karatun sekin gadama zakiyi attending class in kika fadi fa" "Nana kidenamin fatan faduwa, ba abunda zekadani Insha Allah" "to Allah ya yadda amma dai banga ta yadda za aci jarrabawa a haka ba" Jalila ta dan tabe baki tace "ke kika ga haka"
Tunda Ilham takoma gida takewa Mummy kuka, "Mummy dan Allah ki gaggauta auramin Jalal, wallahi zuciyata daf take datayi bindiga in har ban mallakeshi ba, Mummy nagaji da wulakancin Yaya" Mummy ta dafata
"Kiyi hakuri mana Ilham kefa macece yakamata kija ajinki, kuma ni namiki alkawarin auren Jalal" "Mummy babu wani batun aji a fagen soyayya, Mummy dan Allah kiyi wani abu"
"Haba Ilham wai meye hakane, kibari daddynsa ze dawo next week Insha Allah, in ya dawo semu san yadda za'yi, tashi ki tafi dakinki ki dena wannan kukan" mikewa Ilham tayi ta tafi dakinta, tana zuwa ta rufo kofa, sannan tai kwafa "Mummy kicigaba da jamin rai akan auren danki, koki sabaki ya aureni ko karkiyi sena aureshi, sena cika burin mahaifiya ta, sekin wulakanta kin dandani bakin cikin da uwata tayi, ko zan tafi tsirara bazan bari A banza Jalal ya auri wataba bayan ni, wasan ze fara nakusa kawo karshen wannan dramar, indai na haifu se nasa bakin cikin ABDUL JALAL ya kusa kasheki, sekuma ya aureni dan zan iya halaka duk wadda tai nufin aurensa ko wacece!!!!!
Share please
More Comments More typing..............................
_ABDUL JALAL (2020)_
_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)
PART
_PAGE
/ 56_

Gmail @ [email protected]
Facebook real humaira
_MY FIRST NOVEL _
Daga nan Ilham tai kwafa, ta nufi kan gadonta, tai shiru tana sake2 a ranta.
Jalal kwata2 yarasa abunda yake masa dadi, meyasa Jalila tai masa wannan muguwar tsanar haka, bata da burin da yawuce taci mutuncin sa, tabbas maganganun da take gaya masa sun fara isarsa, dole ya hukunta ta hukuncin da suka hadu seta canza hanya, hukuncin da zata dandani abunda yakeji idan taci zarafinsa, gata kanwar kanwarsa, amma ko Ilham dasuke gida
aya bata isa tayi masa haka ba, jiyayi zuciyarsa na wani irin zafi mussaman idan ya tuna yadda Jalila take kiransa da namiji mara daraja. Dole ya hukunta ta dai2 da abunda tayi masa, Ilham ma ze gamu da ita, duk yadda yaso ya manta abunda tayi masa kasawa yayi, karshe ma yaji zuciyarsa tayi masa wani irin nauyi haka yaita juyi akan gado.
Jawwad kam be dawoba se bayan la'asar ya gaji matuka, dan haka benemi Jalal ba se bayan, sallar magariba, yaje gidansu ya duba dakinsa yaga baya nan ya duba bedroom dinsa se yaji shi a rufe, be kawo komai a ransa ba yakoma gida, yai trying lambar Jalal amma shiru baya dagawa, haka ya hakura ya nemi abunda zesawa cikinsa, dan yasan maybe Jalal ya tafi nasa yawon, amma ya damu da rashin daga wayarsa da Jalal beyiba.
Nana tana kwance tana waya da saurayinta, Maama ta shigo dakinsu tace dan Allah in tayi salla taje ta karbo mata laces a wajen Mummy dan in anjima hajiya Jamila zata turo yaranta su karba, dan bata fuska Nana tayi "Maama dan Allah ki aiki Jalila baby ne zezo fa, Maama ta dan bude baki" Lallai Nana, wato saurayinki yafi aikena ko? "" murmushi Jalila tayi tace "Allah ya shiryeki Nana, bari inyi sallar magariba ni se in karbo miki Maama" dan gyada kai Maama tayi ta fice
Jalal kam yanajin wayarsa na ringing yai banza dan tunda ya kulle kansa a daki be fito ba, banda jujjuya kalaman Jalila ba abunda yake, ga yunwa yakeji yanzu yana fita Jawwad ya ganshi a haka ze dameshi da tambayoyin me yake damunsa danhaka ya yanke shawarar ya shiga cikin gida yasamu abinda zeci base yaje gurin Jawwad ba. Ya mike daga kan gadon ya fara yin alwala dan sallar asuba kawai yai, gashi yanzu magariba akeyi, yayo alwala yazo yai sallar azahar da isha'i, seyaji ya gaji dan haka ya mike yace yayi magariba da isha'i anjima kokuma gobe da safe, ya bude dakinsa ya fito, cikin gida ya nufa yana shiga palour Mummy suna kallo itada Ilham bebi takansu ba ya nufi kitchen ya zubo Abinci, ya dakko madara ya fito, abun mamaki yabawa Mummy dan kwanan nan yadena cin Abincin su, Mummy ta kalleshi tace "Jalal zo mana" waigowa yai ya kalleta kaman kar yaje kome ya tuna, kawai se yadawo yasamu guri ya zauna a palourn, yafara cin Abincin sa ba tareda yace komai ba, Mummy takuma tattara hankalinta ta kalleshi "yanaga kana cin Abincin mu yau?" Jalal be dago ya kalleta ba yace
"Dame gidan yakawo Abincin yace banda nine? Yabata amsa ba tareda ya kalleta ba ajiyar zuciya Mummy tayi
" A a ni banceba kokunyi fa
a da Jawwad ne? "
" No, yau abincin gidan mahaifina nakeson ci" "Hmm hakan yayi kyau dan nima bana jin dadin kauracewa abincin mu dakayi dukda tarin dukiyar mahaifinka amma ace sedai kaci Abinci a wani guri. shi Jalal mamakin yadda taketa lallabashi yakeyi, ya sha madarar sa sannan yace "Serious ashe bakya san hakan, hmm amma kinsan wani lokacin abun hannun Jawwad ya fiyemin abun cikin gidan mahaifina" Mummy tace "kaga ba wannan ba, daddynka ze dawo next week" "munyi waya, yagayamin" yabata amsa a takaice "Yawwa dama sonake in yadawo ayi maganar aurenka, tunda lokaci yayi dayakamata ace daga kai har Jawwad din kunyi aure, aure shine cikar mutum"
Bayan Jalila ta idar da sallar magariba ta fito karbowa Maama aikenta, kaitsaye gidansu Jalal ta nufa ta tsaya suka gaisa dame gadinsu sannan ta wuce, tana zuwa ta tura kofar palourn ta jiyo hargagin Jalal yana masifa
" wakike tunanin ze auri mutum irina, wakike tunanin yabani 'yarsa, ko sokike in auri wadda zata soni dan dukiyata? Ta aureni dan ta kasheni ta mallaki abunda nake dashi, Wace yar mutuncin ce zata auri
an da kikayi sanadiyar lalacewarsa da kanki, lalatacce dan giya kamarni Mummy kozanyi aure a rayuwata se wadda zata soni dan Allah badan wani abu nawaba, wadda bazata kyamaci rayuwar da nake ba, meye damuwarki da dole senayi aure, ai aure ba dole bane"
Da sauri Mummy ta katseshi ta hanyar cewa "A a Jalal abun duk be kai haka ba, baga Ilham nan ba, itace me sonka tsakani da Allah meze hana ka aureta ai kanwarka ce" wani mugun kallo yayiwa Mummy "Au Ashe kinada wani
an da kika haifa bayanni ai ban saniba se yanzu" Mummy ta kalleshi cikin rashin fahimta tace "kamar yaya?" "inba wani
an ne dake bayanni ba ai kinsan ba amin dole ko? Ya kalli Ilham" Ke! A tsorace Ilham ta waigo ta kalleshi "tunda muke na tabacewa ina sonki" shiru tayi ba tace komaiba, ya kalli Mummy cikin masifa da tsawa yafara mata magana
"wai dan Allah yaushe zaki fara playing role dinki na uwa, kimin adalci a matsayinki na mahaifiyata, ba kya tunanin in shiryu, se kokarin kuma rusa rayuwata domin wanke laifinki a idon wanda kikayiwa, yakamata ki tausayamin ko sau dayane yakamata ki barni na huta haka, please Mummy ki tausayawa rayuwata haka, a matsayina na tilon danki" karo na farko da Jalila taji ya kira mahaifiyarsa da Mummy, itakam tana son sanin tarihin Jalal da mahaifiyarsa, amma waze gaya mata. Jalal kam yana gama fadin haka ya tashi ya bar palourn ya fito fuuuu kaman guguwa, yana fitowa be kula da Jalila ba a gurin ya wuceta, a hankali tabi bayansa, yana zuwa motarsa ya nufa, yana zuwa ya shiga motarsa yana kokarin kunnata,
seya fasa kunna motar ya jingina da kujera yayi shiruu, gefen motarsa taje ta tsaya tai knocking glass din, a hankali ya sauke glass din motar kawai yai tozali da fuskar Jalila. Kokarin kunna motar yake, saboda yasan in har ya tsaya ze iya illata yarinyar nan, dan yasan yanzunma ci masa mutunci zatayi, hannu tasa ta dafa window din motar saitin Jalal tana kallonsa, tana iya juyo yadda yake numfashi,
"ABDUL JALAL kaji tsoron Allah kaji, karka mutu mahaifiyarka tana jin haushinka, kome tayi maka kabata matsayinta na uwa, Annabi salallahu alaihi wassalam se da yafadeta sau uku yace abita sannan yace uba, kaji tsoron Allah kadinga yafiya mana, ka tausaya mata kaimata biyayya, kaji dan gidan daddyn sa, ba daddy kawai keda hakki akanka ba, nasan yanzu mashaya zaka tafi, dan ba kunya ce da kaiba naga baka da alamar zaka dena shan giya, kayi a hankali da duniya, sannan ka kiyayi miyagun abokai, u have to focus, ka kiyayi JeJe da Hannah da sauran miyagun abokanka, basa komai banda rusa maka rayuwa, basa nufinka da alkhairi ka kiyaye, jeka Allah ya shiryeka" manyan idanunsa da suka sauya zuwa launin ja ya zuba mata, cikin idonta ya saka nasa, dukda akwai duhu se hasken fitilu be hanashi ganin fararen idanuwan taba masu kama da tana jin bacci, ji tayi kaman an daureta takasa motsawa tabar gurin, itama ta kura masa ido, ji tayi idonta yayi nauyi, ga Jalal yamata wani irin kwarjini, kamshin turarenta duk yacika masa hanci, daurewa yayi, yai mata wani mugun kallo me wuyar fassara, sannaan ya dauke kansa yace
"ki kiyayi haduwata dake, zanyi maganin wannan shishshigin naki, sekinyi dana sanin shigowa rayuwata, zan baki mamaki, bari in tuna miki alkawarin dana taba yimiki, zan maida ke abun kwatance irina, matsa ki bani guri ko in takeki da mota. A hankali ta motsa bakinta, tafara magana a hankali cike da rainin hankali tace
"zaka iya ai, inbaka takeni da mota ba ba sunanka ABDUL JALAL ba, ni bazan fasa fadan gaskiya ba, kome za kayimin, Kuma bazan taba zama abun kwatance irinka ba, dama kwatancen kirki ne da sauki, Allah ya tsareni zama abar kwatance kamar dan giya"
"Haka kikace?" "baka da kunne ne?" Ajiyar zuciya Jalal yayi, ya kunna motarsa, Jalila ta ja dabaya ya ja motarsa da gudun tsiya, Jalila ta juya zata shiga gidansu Jalal, taga Ilham a tsaye a bakin kofa tana mata wani irin kallo na tuhuma, fuskarta na dauke da tsantsar bacin rai, dakuma tsanar Jalila, dan tana hangen abunda yafaru, tsakanin Jalal da Jalila, a hankali Jalila ta karaso, kota kan Ilham bata biba, ta tureta gefe ta wuce cikin palourn, ta tarar da Mummy a palour ta fada mata sakon da aka aikota, Ilham ta shigo palourn taji zuciyarta tana raya mata taje ta dakko
wuka ta kashe Jalila ta huta, itako Jalila ko kallon Ilham batayi ba, tacigaba da abunda take.
Jalal kam kaman yadda Jalila ta fada, mashayar sa ya tafi, amma yana tafe tunani kawai yakeyi, yana ta nazarin mezeyiwa Jalila wanda ze bata mata rai, soyake ya bata mata rai yadda zataji zafi sosai fiye da yadda take masa, manyan mutane ma suna shakkarsa, saboda kwarjinin sa, amma yarinya karama tana caza masa kai, wani abun takaicin jinsa yake duk jikinsa ya mutu, kamshin turarenta kawai yakeji, yai kwafa zeyi maganinta ne. Yasamu guri yai parking Ya fito daga mota
Guri yasamu ya zauna, yai shiru dayake ansan abunda yake bukata customer ne sosai, aka kawo masa giyar dayake sha, befi minti shabiyar da zuwansa ba, sega Hannah tazo , dan an kirta a waya an sanar da ita Jalal yazo, guri ta samu ta zauna tana fuskantar Jalal, "Jalal ina kashiga haka, babu ko waya nadena ganinka kwata2 tun a gurin birthday din ka bankuma ganinka ba gashi inason ganinka, nayi niyyar zuwa gidanku amma bani da lafiya ne" kallonta ya danyi yayi shiru ya cigaba da shan giyarsa. Kallonsa Hannah ta kumayi "Jalal ya kayi shiru, kayi magana mana" "mezance miki, inajinki" ta numfasa tace "Jalal dan Allah menene alakarka da wannan yarinyar me iyayin tsiya, ta fadamin sunan ta amma na manta, a zatona itace Ilham amma ranar ta nunamin Ilham tace ita ba itace Ilham ba" ajiye cup din hannunsaa yayi ya kalleta "meyasa kike tambayata wacece?" "ta damu dakai sosai" "hmm ya akayi kikasan hakan?"
"Alamu nagani" "yayi kyau" shine amsan da Jalal yabata, "Jalal dan Allah wacece ita a gurinka" a fusace ya kalli Hannah yace "ke kin isheni, ki kyaleni dan Allah" "meyasa zakace in kyaleka bayan saboda kai nazo gurin nan, Jalal wata alfarma nake nema a gurinka" kura mata ido yayi sannan yace "ina jinki" "Jalal tuba nakeso nayi, na dena abunda nakeyi, dan Allah so nake ka aureni, aurenka ne kawai ze iya cetoni daga halakar danake ciki please Jalal.
" Aurena ze cetoki daga halakar dakike ciki, nikuma ze janyomin halaka, ke kina tunanin zan zabi mace kamarki a matsayin matar aure, Hannah banason yarana suyi irin rayuwar danayi, dan haka uwa tagari zan zaba musu, ina miki murnar shiryuwa da kikayi, naso dan Allah kika shiryu, amma ina miki fatan alkhairi Allah yabaki miji nagari "yana gama fadan haka ya tashi ya tafi. Hanna ji tayi kaman ta fasa ihu, duk tsawon lokacin nan dasuka dauka tare ammaa ace babau soyayyarta a zuciyarsa, anya JALAL mutum ne kuwa? Aikuwa ko karfene a zuciyarsa seya soni sena aure shi, tana cikin wannan tunanin Jeje yazo, yasamu guri ya zauna a kusa da ita ya kalleta "Hannah manyan kasa, mekuma kikazo yi nan?"
"meya dameka dame nazoyi, oppression na fito, na fito farautar abunda zuciyata ke so, kuma zanyi iyayina inga nasamu" "Hannah kenan dazaki zubar da makamanki ki dawo mucigaba da aiki tare gurin ganin munyi nasara akan Jalal"
"Jeje meyasa kanka baya jane, ban gayamaka cewar bazan kara maka aiki ba, kaina nakewa aiki yanzu, kafita daga harkata ko inyi maganinka wallahi" ta dau Jakarta tai tafiyarta, bayanta Jeje yabi da kallon mamaki, gaskiya Hannah ba karamar mara mutunci bace, betaba zaton zata juya masa baya ba, dole yai taka tsan2 da ita dan yasan halin Hannah sarai, inta sawa ranta samun abu setayi duk yadda zatayi ta sameshi, dole yai wani abu akanta.
Koda Jalal ya dawo gida, Gaba daya yau angama dagula masa lissafi, mussaman Jalila, yau an hada masa zafi sosai duk ransa a bace yake, yarasa me zeyi ya huce, kalmar namij mara daraja da Jalila takira shi dashi se yaji wani mugun bacin rai ya kamashi, yayi tunani sosai mezeyiwa Jalila ya huce haushinsa, gani yai yana kara batawa kansa lokaci, dan haka zuwa yayi ya kuma daukan giya
Ya sha me isarsa, seda fita hayyacinsa ya fadi a gurin yana bacci.
Share please
More Comments
more typing..........................
_ABDUL JALAL (2020)_
_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)
PART
_PAGE
57_ 4

Bayan haka bazan gajiba da mika gaisuwata da godiya ga yan uwa da abokan arziki ba, bayan haka

Yauma Jalila seda sukayi fada da wani lecturer dinsu, saboda dalibai biyu sunyi laifi ya kori daya yabar daya, dayake wadda yabari din sameera wata muguwar fitsararriya ce, ba dalibai ba har malamai tsoronta sukeji, babban abunda yake bakantawa Jalila be wuce, yadda wasu daga cikin yaran talakawan nan kemata shishshigi ba don samun gurin zama, itakuma taita hantararsu tana musu tsawa, tana zaginsu ko haushi basaji kusan duk ajin suna shakkarta, kaf ajin nan aminiyarta dayace wadda batayiwa wannan rashin mutuncin wato saleema, tun zuwan Jalila ta lura da halin kowa, ita saleema itama babanta yana da rufin asiri yanada kudi amma ba kaman Samira ba, sedai yadda Jalila ta kula saleema ba karamar yar iska bace ba kowa ke gane hakan ba saboda ta iya takunta.
Yanzuma samira ce takewa, wata yar gefen seat dinta magana zahra, zahra ta bada attention dinta sosai akan lectures dinta, koda lecturer ya juyo, samira ya gani tana magana amma ya kori zahra sannan yace bata da attendance dinsa na wannan semester gaba daya, ya kyale samira be koreta ba, har ya juya ze cigaba da lectures Jalila tace
"Excuse me sir" ya waigo yana kallon Jalila, yace mata "Ya dai?" "Sir meyasa ka kori zahra, ba ita tayi magana ba, bakaga ba ita take magana ba, kamata yayi ka koresu su biyun, koka kyalesu duka, amma bekamata a kori wata abar wata ba, amma am sorry idan na fadi ba daidai ba" juyowa yan ajin sukayi suna kallon ta, zuwa yanzu sunfara gane halin Jalila, ba karamar kwalluwar mara mutunci bace, yayinda take birge wasu, saboda iyayinta, da fadar gaskiya, malamin yai saroro yana kallonta ya hade rai yace
"waye lecturer tsakanin nidake?" kanta tsaye tace "Sir wannan ai amsace a bayyane kaine lecturer, nikuma daliba"
"dan me zan yanke hukunci kiyi challenging dina? Ke wacece? Ido kika fini banga abunda yake faruwa bane, ke har kin isa inyi magana ki kalubalanceni a gaban students dina, are u out of your sense" nan fa ya dau zafi ze farayiwa Jalila masifa ta inda ya shiga bata nan yake fita ba, yace ta tashi ta barmasa ajinsa, yauma babu batun ta bada hakuri ta dau jakarta zata kara gaba, shikuma yacigaba da zage2 hardace mata mara tarbiyya aikuwa a take tace "Excuse me sir, daga fadan gaskiya zaka fara min fada hada cemin mara tarbiyya, am just your student not your daughter, am sorry for what i did, kayi hakuri in har na bata maka rai, amma karka manta fadar Manzon Allah ne salallahu alaihi wassalam, duk wanda yaga ana aikata abunda be dace ba, ya kawar da hannunsa, in ba ze iyaba yayi da harshensa, in baze iyaba yaki abun da zuciyarsa wanda shine mafi raunin imani, sir be kamata aji tsoronka aki fada maka gaskiya ba, tunda Allah ne kadai abun tsoro, dan kana shugaba ko malaminmu baze hana a fada maka gaskiya ba, duk wanda ya shigo aji ba dan me kudi dana talaka, kayi treating dinsu equally, yazakaji in zahra yarka ce aka hukunta ta akan laifin wani, kasani wannan hukuncin dakayi mata ranar alkiyama sekun tsaya a gaban Allah, wannan abunda kayi mata ya isa ya toshe maka hanyar arziki a rayuwarka, kudena raina daukar hakkin dalibanku ku dinga ganin ba wani abubane ba dan Allah yabaku dama, bekamata kace gaba daya batada attendence din wannan semester dinba, but with do respect sir this is against our Islamic teachings, da na kowame" daga nan ta juya taana wannan takunnata na kasaita tafita waje, koda Jalila ta fito ta tarar da zahra tasamu guri ta zauna tana kuka, kusada ita Jalila taje ta durkusa ta dafata, "Kidena kuka kinji, Insha Allah komai zezama dai2, kidena zama inda wannan yarinyar take kinga ta cazami ki an koreki" zahra ta kalli Jalila dan ko sannu bata taba hadata da Jalila ba a hankali zahra tace "kema ya koreki ne" "Eh korata yayi" nan Jalila tagaya mata abunda yafaru, zahra tace meyasa kikayi masa magana, rannan ma an koreki daga aji, karki jawa kanki matsala "Jalila ta danyi murmushi tace" babu wata matsala, indai ka dogara da Allah ta ya isar maka, be kamata ya kyaleta keya hukuntaki ba akan laifinta, waima tukuna me kikayi mata naga alamun ta takuramiki"
tsit ajin yayi, aka rasa me cewa wani abu, shiru lecturer yayi na wani dan lokaci, sannan ya kalli wani dalibi yace yaje waje ya kirasu Jalila, aikam ya kirasu sukazo, yace sunemi guri su zauna, sukakoma gurin zamansu, bekuma cewa komai ba yacigaba da gabatar da lectures dinsa, koda yafita haka wasu suka cigaba da surutai akan Jalila, samira ce da yan group dinta tace "ina son sanin waye uban yarinyar nan da take wannan gadarar, harni zata kalla tace a hukunta, tasan waye uabana a kasar nan" saleema tace "kedai bari, amma dagani ba yar talaka bace yanayinta kawai zaki kalla kisan hakan, kuma motar da akekawosu ma babba ce, da alama itama babanta wanine, babyn tama hutawa" tsaki samira tayi "duk kudinta tayi na ubanane, saleema inaso ayiwa yarinyar nan warning, sannan kota halin yaya ina bukatar zahra" sameera tai murmushi "yadda kika dama haka za a sha yar masu kasa, sanan kizuba ido kiga wannan yarinyar carry overs din dazata kwasa a school din nan" suka kwashe sa dariya, Jalila ta kalli zahra, "Zahrah baki gayamin ba, meye hadinki da samira ta takura miki haka, kekuma kinkasa daukar mataki" ajiyar zuciya zahra tayi tace "Jalila ina cikin matsala, ni kinga babana bakowa bane ba a garin nan, ni yar talakawa ce, kinga samira da salima yaran masu kudine sannan kuma... Setayi shiru" inajinki cigaba mana wata ajiya zuciya Zahrah takumayi "Jalila samira da saleema, ba kawayene kawai ba yan iska ne, tun suna yara suke tare, daga maza har mata ba wanda basa nema, wannan yan group din nata dayawansu yaran talakawa ne, amma tasasu a wannan harkar tana basu kudi masu yawa, dayawa lectures sun santa, ba wanda ya isa tasa kara ya tsallake, saboda babanta dan siyasa ne suna da kudi, koda anyi niyyar yimata wani abu a makaranta se tayi amfani da alfarmar mahaifinta, in bata gadamaba setasa a kori mutum, da kike ganin ta haka hatta a hukumomin tsaro taana da mutane, kuma harkar da takeyi har wajen kasar nan, mu amalarta hada manyan masu kudi, itada saleema suke wannan abubuwan, shine tace wai tana sona" zahra ta karashe maganar da hawaye, kallonta Jalila tayi labarin ya daki zuciyarta, amma ta dake tace "to kekuma kikace mata me?" "shine nace mata a'a shine taketa bibiyata take takuramin, tace setasa an koreni a makarantar nan, nikuma inajin tsoro saboda, inason inyi karatu" ta karasa maganar tana zubar da hawaye, Jalila tayi tsaki "kekuma saboda wannan shashancin naki dole ta takuramiki, kin nuna kina tsoron ta, tashi muje muyi salla, semuga ya za ayi" suka tashi suka nufi masallaci, a hanya suka ci karo dasu Samira amma, ba wanda ya kula wani, Samira ta kalli saleema tace "sweet heart, bi yaran can, bana son ta shiga tsakanina da zahra, dan haka ki kiramin ita kice ina kiranta" "bakida wata damuwa, bari inje" kafin saleema taje su Jalila har sun kai masallaci, tana zuwa masallacin taga Jalila ta cire hijjabinta tana alwala, tsayawa saleema tayi tana kallon Jalila, yanzu takekuma ganin kyawun Jalila, parkistan ne a jikinta wando da riga, se dogon gashinta irin na fulani, tana tsugune tana alwala, tubarakallahu komai yaji a jikin Jalila,
koda Jalila ta idar tai ido hudu da sameera, tsaki tayi tasaka hijjabinta, suka shige masallaci, haka samira tacigaba da jiranta seda ta idar, saleema ta karaso gaban Jalila ta zauna ta kalleta taimata wani murmushi irin na rikakkun yan isaka tace "baiwar Allah dukda kasancewar, ajinmu daya amma bansan sunanki ba, aikoni akayi gurin ki, samira ce takeson ganinki" shiru Jalila taimata ta dauki jakarta tana saka wayarta, ta kalli kalli zahra tace "zahra taso muje department dinsu Nana, muje capteria muci abinci, saleema tace tab lallai wannan yar rainin hankali ce, saleema tace" baiwar Allah, magana nake fa, samira tace tana son ganinki " Jalila ta kalli samira tace " bani da lokacin kowace kucaka a school din nan amma zuciyata zata iya canza ra'ayi "
Daga nan taja hannun zahra suka fita daga masallacin, koda sukaje gurin cin abinci zahra tana ta bawa Jalila labarin halin su saleema. Koda suka gama cin Abinci suka koma aji, lecturer be shigo ba, samira ce ta shigo da mukarrabanta, se wani shan kamshi take, tazo seat din Jalila ta zauna a kusa da ita, ta kalleta tace "dukda bansan wace ce keba, hakan baze hana kisan wacece niba, kuma yar wace niba, kisani ba amin shishshigi, baki isa inyi wani abu kice zakisa a hukunta niba, tunda na shigo makarantar nan, naga yadda kanki yake rawa, to kitsaya a iya matsayinki, nan fada tace duk wanda yake ajin nan a karkashina yake, dan haka kitsaya a matsayinki" samira ta mike zata tafi Jalila batace komai ba, sema murmushi da tayi "yaro be san wuta ba seya taka, baki sanni ba ne, amma muje zuwa"
Ana haka lecturer ya shigo wanda yasa kowa nutsuwa, tunda lectures suke shigowa sau dubu inzakayiwa Jalila tambaya shiru zatayi tace bata saniba, hakan yasa aka fara gulmar ko dakikiyace se tsabar fitsara da izza a cikinta, dasuka fito daga lectures, tay8 sallama da zahra tai tafiyarta gida saboda Manu direba bezoba, Nana kuma basu gama lectures ba, Jalila ta tafi gida tanata tunanin labarin da zahra tagaya mata akan su saleema, lallai dole wasu iyayen su hana yara mata neman ilimi, katura yarinya makaranta amma ta lalace saboda abun duniya.
Haka Jalila taje gida a gajiye, tanata tunani daban2 kanta har yafara ciwo, gida ta shiga, tana tura kofar palour taci karo da yaya mairo da Naja da Maama a palour suna hira, seda jikin Jalila yayi sanyi ganinsu a gidan nan, dan ta san bacin rai zata sha yau, sallama tayi ta shiga, ba wanda ya amsamata se Maama itama a ciki ta amsa, Jalila ta ce "ina wuninku" yaya mairo tai saurin cewa "ke dan Allah ki wuce ni banason kinibibin gaisuwarki, wuce kibani guri" Naja tai saurin cewa "tsabar kinibibine wai ita dole ace ta Allah" Jalila batace komai ba ta wuce dakinsu, tana shiga nan ma ta tarar da sa'ada kwance akan gadonsu tana danna waya gefe ga kwanon abincin dataci da jarkokin lemo da ruwa akan gadon duk ta bata gadon, ta zubar da abinci akai, kallo daya Jalila taiwa sa'ada, ta dauke kanta kaman bata ganta ba, ta ajiye jakarta da hijjabinta, ta dau towel ta shiga wanka, tagama ta fito ta zauna a gaban dressing mirror tana shafa mai, sa'ada ta dago kai ta kalli Jalila ta tabe baki "tabdijan anzo an samu guri, se murjewa ake ana yadda aka gadama, Allah ya rufa asiri ba a girma a cikin arna ba da yanzu ko ana gona hakan doya da goyon shege kokuma anayiwa
coci hidima"
Ware gashinta tayi tana tajewa, ba tareda da tayiwa sa'ada magana ba, Naja ce itama ta shigo, ta haye kan gadon gefen sa'ada tana tauna cingam, ta kalli Jalila tace "Allah sarki, mukam mungode Allah da yayimu a musulmai, ba arna ba" haka suka ding a yiwa Jalila rashin mutunci suce wannan suce wancan, amma taki kulasu, ta dauki doguwar riga tasaka, halima ta shigo dakin da sauri ta Rungume Jalila, Jalila ta kalleta "leemart saukar yaushe?" halima tace "dazun nan na dawo akace kina makaranta, Aikena akayine se yanzu na dawo" "Allah sarki ya kika baro mutan garinnaku" "kowa lpy kalau Alhamdilillah, nayi kewarki sayyada Jalila" murmushi Jalila tayi "nima nayi missing dinki da hirarki me ban dariya" Naja tace "Ke halima meye haka kike wani rungumeta, kokema kin hada iri da arnan ne, ko kyamarta ba kyaji" saroro halima tayi tana kallon Naja, Jalila tace "leemart dan Allah hadomin madara da sugar a cup ki hadomin da spoon ina son zansha goldenmorn" halima ta gyada kai ta fita, sa'ada tace "tabdijan wayaga basa banba ansamu guri se abunda akeso a keci sekace a gidan ubanki, lallai Allah ya temakeki wai, da yanzu ana can anacin teba a kauyen su tsohuwa, ko ana gona ana bauta" Jalila kam gaban mirror takoma ta shafa turarurrukanta, ta dau mayafin rigarta ta daura akanta, halima ta kawo mata madara, ta karba tayi godiya, seda tagama shirinta tsaf, sa'ada da naja suna gayamata bakaken maganganu, a hankali Jalila tazo gaban su ta tsaya sannan tace
"nan gidan ubanane, inada ikon yin abunda nakeso inci abunda nagadama inyi yadda nakeso, kufa meye matsayinku a gidan, se abunda yakawo ake diba a baku, kokuma ayi amfani da abunda aka farauto a bariki" da sauri Sa ada ta kalli Jalila, Jalila tacigaba da cewa "kukiyayi cimin zarafi kyaleku kawai nakeyi, ranar dana tashi nuna muku ainihin kalata, zakuji babu dadi, a kiyaye" tanagama fadin haka ta tashi ta fito takoma harabar gidan tai zamanta, a inuwar data saba zama, amma me tunani ya addabi zuciyarta, ga tunanin yadda zata sami tarihin waye Jalal, taya ya zata samu mafita akan
al amuransa, ga tunanin labarin da zahra tabata akansu saleema, jikinta yana bata wani abu akan su, amma takasa gane menene? Kai ita wace kaddarar ta kawota kano, tana zamanta cikin kwanciyar hankali da umminta, kaddara ta kawota kano tunani kaman ze haukata ta, ga jarabar dangin mamansu Jawwad dabasa kaunar ganina"Allah sarki Ummi na, Allah ya bayyanamin ke" a hankali ya rike hannunta
"Yar babyna, tunanin me kikeyi hakane, da alama kin gaji sosai kuma akwai damuwa a tareda ke, kinkasa cin abincin naki, kuma ga hawaye a kwance a idonki, abunda nafi tsana ganin hawaye a idonki, gayamin tunanin me kikeyi? " Jawwad ne a durkushe a gaban Jalila ya hada hannunta da kofin ya rike a nasa, a hankali kwallar dake idonta ta gangaro, Jalila ta dake tareda kakaro murmushi taimasa " Yaya kadawo ashe? " " naki wayon gayamin meyake damunki?
"bakomai fa nagajine kawai" "amma kika kasa cin abinci" ya karbi cup din hannunta ya debo goldenmorn din ya nufi bakinta dashi "bude bakinki" dauke kanta tayi, ta rike hannunsa "A'a yaya Jawwad, karkashiga matsala, kasan su Yaya mairo suna gidan nan, kar ayimaka fada"
Kallonta yayi "Baby, ni ban damu da hakan ba, bana fargabar kome ze faru indai akanki ne, nasan maybe zuwansune ma yasa sukayi miki wani abu daya bata miki rai"
"A a basuyi min komai ba" "Baby hakan be kamata ya dinga damunki ba, kome za ayimin zan iya jureshi indai akankine, komai tsanani ina tareda ke Jalila, bazan iya rabuwa dake ba, nasan Abba ze bamu goyon baya, ina sonki Jalila " dan tsura masa ido Jalila tayi a ranta tace "Allah sarki yayana, goyon bayan uwa shine, nasan indai dasu yaya mairo to bazasu barmu tareba" murmushi tayi masa "yaya ka tashi ka zauna akan kujera mana" "A a sekin gayamin kema kina sona tukuna" rufe idonta tayi tana dariya
Jalal ne ya turo gate ya shigo ya tunkaro inda su jalila suke
Share please
More Comments More Typing.............................
[09/04, 12:29 PM] Ayshercool:
_ABDUL JALAL (2020)_
_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)
PART
_PAGE
/58_

Or email address @ [email protected]
Or Facebook on real humaira
_MY FIRST NOVEL _
Ransa a hade ya tunkarosu, yana zuwa ya kalli Jalal yai murmushi, seda hakoransa suka bayyana, Jalal be fiye fara'a ba seda dalili dan kullum fuskarsa a hade, hakan ya tabbatatwa da Jalila, Jalal yana cikin farinciki
"Kasan wani abu Jawwad?" Jawwad yace "A a seka fada mutumina" Jalal se ya juya harshe yaiwa Jawwad magana da wani yare wanda Jalila bata iya fuskanta, dan zare ido Jawwad yayi tareda yin murmushi "dagaske kake?"
"kwarai dagaske nake, daddy ze dawo gobe Insha Allah, amma kasan meyafi sani farinciki"? "A'a seka fada"
"daddy ya tabbatar min da cewa 'yan maiduguri zasu kawo mana ziyara, zasuzo kano Jawwad, kaga hakan na nuna komai ya wuce" yakarasa maganar da kwalla a idonsa mikewa tsaye Jawwad yayi, "Dagaske zasuzo Jalal" "hakane daddy ne ya gayamin, zasu kawomana ziyar" "Alhamdilillah Jalal nafika murnar hakan, naji dadi, Allah ya kaimu suzo, hakan na nuna komai ya wuce a gurin su"
"Hakane gobe insha Allah zamuje dakko daddy karfe hudu ze dawo" "to Allah ya kaimu" ita dai Jalila ba tace komaiba sema wata cakwakiyar tunanin dasuka kuma sata, dama Jalal yanada yan uwa a maiduguri amma basa zuwa, ita bata taba ganin baki sunzo gidansu bama, se abokan kasuwancin Mummy dakuma wasu tsirari daga danginta, dan ko a gurin birthday din Jalal wadanda tagani, sunfi kama da Mummy, Jawwad ya kalleta yace "sarkin tunani, mekuma kike tunawa? Zamu wuce nida Jalal zamu fita"
"Hmm sekun dawo" Jawwad yai murmushi suka fita shida Jalal.
Yaya mairo ce take korawa Maama jawabi
"Zainab yakamata mu karfafa zumuncinmu ta hanyar hada auratayya a tsakanin yaranmu, kinga yaron gurina Nura tun Nana tana yarinya yakesonta, yakamata kubashi Nana, sannan Jawwad mu hadashi aure da Naja, kinga haulat kuma dan gidan baba habu Dini shize aureta, tunda Nana kanwar Nura ce kinga duk se a hada su koya kikagani?" seda Maama tai Jimmm, dan gara batun hada auren Jawwad da Naja akan auren Nana da Nura, dan tasan Nana bazata yadda ba, balle Abba tasan baze mata auren dole ba, dan sam Nana ta tsani Nura basa jituwa balle data girma gashi duk wanda yasan Nura yasan ba mutumin kirki bane, dan zuwansa prison sau uku
"Yanaga kinyi shiru ne? Ko baki yadda bane?" tab tasan a yanzu idan ta nuna mata rashin amincewarta zasu samu sabanine dan haka tace
"gaskiya Yaya mairo, wannan tunanine me kyau Allah ya tabbatar mana da Alkhairi saura kuma amincewar yaran"
"to meye inma basu yaddaba ai dole subi umarninmu" "A'a Yaya mairo in har basu amince ba Abbansu baze yadda ba, har gara Jawwad amma kinga Nana kinsanta da taurin kai"
"Ki barni dasu kawai, kinga Jawwad in aka hada shi da Naja kinga zamu dauke hankalinsa daga kan wannan makirar yarinyar, bari Nanan ta dawo" Maama dai ta amsamata ne amma badan ta yaddda da abunba har cikin zuciyarta.
Jalila tana nan inda su Jawwad suka barta halima tazo ta zauna sukai ta hira, har la'asar, Jalila na shirin komawa cikin gidane manu direba ya kawo Nana gida daga school, ta gaji sosai
Ta kalli Jalila "sarkin gudun makaranta kin gudunne tun azahar"
"wayagaya miki, mungama lectures ne da wuri kawai, sannu"
"Yawwa, au halima kindawo ashe" "eh na dawo" "yayi kyau"
Suka dunguma zuwa cikin gida, suna zuwa suka tarar su Mama duk suna palour, Jalila tai wucewarta dakinsu, tanaji Yaya mairo tanawa Maama mita
"Zainab ashe har yanzu baki janye yaranki daga jikin wannan kinibabbiyar yarinyar ba ko, saboda munafunci data dawo seta koma waje ta zauna, amma Nana tana dawowa kinga tabiyota ta dawo"
Sa'ada tace "hmm kema dai kyafada, muna funci a gurin kabilu bama dai ita tana wa mutane gadara sekace a gidan ubanta" dogon tsaki Nana tayi, ta wuce dakinsu
Binta sukayi da kallo, Naja tace "Tabdijan zama da madaukin kanwa, Ace kina magana Nana tayi miki tsaki, lallai abun ya girmam
Nana tana shiga daki ta tarar da dakinsu kaca2, kan gadonsu hada kwanukan abinci "Jalila meye haka? Yanaga dakinmu a haka, sekace makwanci mahaukata, dakin dayake tas amma hada kwano akan gado"
"Ke karki saukemin gajiyar makarantarki, ni kin taba ganin ina cin abinci akan gado, kuma in tashi in bar kwano, nima haka na dawo naga dakin, bakinku ne sukayi masa haka"
"Kutmelesi, waisu Naja aikuwa sena musu rashin mutunci sun dauka kowa kazamine irinsu, suna abu kaman sakarkaru" fuuu Nana tai waje tana zuwa palour tafar zazzaga masifa "Ke sa'ada akanme zaku shigar mana daki kuci abinci akan gado, wannan wane irin shirme ne? Muda a haka muka bar dakin zakuyi marmarin shigane," Maama ta daka mata tsawa "Nana meye haka? Sa ada ba gaba take da keba? Kuma ya akayi kikasan sune sukayi hakan? " cikin shagwaba kaman zatayi kuka tace
"Maama dan tana gaba dani sesuyi
mana haka a daki, kuma koba a gayamin ba ai nasan Jalila tafini gyara dakin nan tunda bata son kazanta bata tabcin abinci a guri ta barshi ba, amma daga zuwansu zasu bata mana daki, wallahi karku kara shigar mana daki, tunda baku da hankali, kazamai kawai" bude baki sukayi da mamaki Naja zatayi magana Yaya mairo ta hanata tace "rabu dasu yi hakuri bazasu karaba, sannan inason in kin samu lokaci kije gida kisameni ina son ganinki" seda Nana ta yamutsa fuska, sekuma tayi shiru
takoma daki tana kunkuni tana mita, seda tafara gyara gurin sannan ta shiga wanka, dan Jalila tace wallahi kartin banza bazasu bata daki ta gyara ba. Koda Nana ta wuce daki Yaya Mairo tace "kingani ko zainab yaranki na neman sufi karfinki ace har kina fada tana mayarwa saboda waccan yar karuwar, kinsansu arna ba ruwansu yayansune suke juyasu shiyasa take so ta mayar miki dasu irinta ki tashi tsayefa wallahi aikine babba agabanki"
Koda su Yaya mairo suka tashi tafiya seda aka bude store aka jido musu kayan abinci, banda wanda Abba yakesawa a diba a basu, banda kudi da take bawa yaya mairo, se anbi kayan abincinsa na gida bada saninsa ba anbasu banda sitira da sauran kayan more rayuwa, dayake Yaya mairo akwai mugun sonn abun duniya, duk an kwashi kaya an kai boot Manu direba ze maidasu gida. Nana ta fito daga wanka zata shafa turare, amma ta lura babu wasu abubuwan akan mirror dinnasu, tsaki tayi "Allah ya kyauta wannan masifar, Jalila kallifa hada kayan mu suka sata, wallahi senaje se sun bamu" da sauri Jalila ta dakatar da ita "bari Nana ai yan uwankune inkikayi haka kaman kin tozartasune, ai arzikine sekinada abun sata za a sata, bakomai semu sayi wasu" haka Jalila ta lallabata ta hakura badan tasoba. Jin alamun fitarsu daga palourn yasa Jalila ta fito palour, hakan yai dai2 da dawowar
sa ada zata dauki wasu kaya data bari a palour wanda na Nana ne da Jalila ta dauka bada izininsuba, hada kayan man shafe2 da turaruka da Nana take mita, Jalila ta kalleta tai murmushi "Allah sarki bariki batayi rana ba, ace duk iskancin da ake a bariki ba a tara abunda za a rike tsofaffi ba se an hada da maula a dangi, bayan haka kuma se an hada dana sata to Allah ya kyauta" a fusace ta kalli Jalila ta nunata da yatsa "Karki kara dangantani da bariki" "Ke sauke yatsanki karki kuma nunani
karki rainamin hankali mana nasan komai kallonku kawai nake daga ke har mahaifiyarku, kuma wallahi kigayamata ta kiyayeni inasane da abunda takemin da cin mutuncin uwata datakeyi, idan na tashi yimata rashin mutunci se tagane bata da wayo, har yanzu ban taba gwada muku wace Jalila ba, ta kiyayi haduwata da ita" Jalila tai gaba tabar sa ada da bude bakin mamaki. Bayan tafiyar su Naja da daddare Nana se mita take "nikome yaya mairo zata gayamin wani wai senaje gidanta, Allah yasa wani abun Arzikin nanba rainamin hankali zatayiba, nibana son zuwa gidanta saboda wannan Jarabar tata"
"To ai hakuri zakiyi, maybe abunda take son gayamikin yanada mahimmanci ne"
"Anya Jalila bana tunanin hakan amma bansaniba"
"Yawwa Nana dan Allah in tambayeki mana?"
"to Allah yasa nasani" "dama Jalal suna da wani yarene naji sunayi shida Yaya Jawwad" murmushi Nana tayi tace "Eh sunadashi, ta bangaren daddynsa, kakanin Jalal kanuri ne" Jalila ta gyada kai tace "Amma ya akayi Yaya Jawwad ya iya"
"Lallai Jalila har yanzu kina daukar amintarsu da wasa, tare suke kwana su tashifa, yanzune suka dena kwana guri daya, saboda Yaya Jalal yana fita yawonsa, da har maiduguri suke zuwa suyi kwanaki" jinjina kai Jalila tayi tace "lallai kam dole ya iya yaren" daga nan suka bar wannan zancen, Jalila ta kwanta bacci Nana kuma tafara waya da saurayinta.
Yau lecturer su Jalila ya kudiri aniyar yimusu test, unexpected saboda ya hukunta Jalila sir Hafiz kenan, matashin mutum me matukar izza da jin kansa, bashi da mutnci kokadan, kayadda dalibai a course dinsa shiyafi komai sauki a gurinsa, ga kwauron maki shiyafara korar Jalila daga class, sau biyu yana korarta daga class, na farko yana lectures tana tunani na biyu kuma kullum ya shigo class yamata tambaya bata sani ba, gashi ya lura seta gadama take attending class ya fuskanci dakikiya ce amma tana da izza da jin kanta dan haka, bayan anfito daga lectures karfe biyu, unexpected ya kira captain dinsu yace, ze musu test bayan sallar azahar, students din sun shiga damuwa saboda basu shirya ba, kowa yakama littafin sa, zahra ma ba abarta abayaba ta dage tanata dudduba littafinta, yayinda hajiya Jalila bayan ta idar da salla, ta janyo abincinta tanaci tana chatting da yaya Jawwad yana dariya , zahra ta kalleta "Jalila ke bazakiyi karatun ba? Test fa zeyi kuma ance yanada kwauran maki" "don't mind me, yi karatunki kawai, ni yunwa ce ta dameni" "to amma ai gara...." "shhh ya shiru kicigaba da karatunki kar haddarki ta zube" zahra ba karamin mamaki Jalila take bataba, ga dukkan alamu dai ba wani ja take ba saboda ba ataba tambaya ta bada amsaba amma za ayi test ko a jikinta, se tsabar iya tsiwa fal cikinta,
Karfe biyu da rabi suka shiga test din nan, wadda duration din test din 30minutes ne kawai, ga tsaro a hall din dan duk ya rarrabasu, bame iya ko kyakykyawan motsi, sannan Jalila ita kadai aka ajiye agaba bakowa a kusa da ita bayanta ko gefenta, gashi ya dakko wasu malaman department din su tayashi invigilation, Jalila ta lura yasamata ido sosai, ya dinga safa da marwa yana kallonta, kowa ya dukufa amma ita tana zaune tana kalle kallenta karewa ma ta tafi tunanin abunda yake gabanta na rayuwar Jalal, sir hafiz yazo kanta ya duba paper dinta ammma empty, ya kalleta yai kasa da muryarsa ya dan sunkuyo da fuskarsa yace "dakikiya kawai ba abunda kika rubuta, dama ba kyaja se tsabar iya shege ko? Rashin mutunci kawai shine a kwakwalwarki, bakomai se shirme, sokuwa kawai barikiji in gayamiki wannan shine last chance dinki idankika fadi test din nan kin fadi exams dina" wani irin kasaitaccen murmushi Jalila tayi masa alamar sam bataji zafin maganganunsa ba ta dauke kanta, seda yayi gaba ta bude paper dinta ta amsa tambayoyin, nanma itace karshen bayarwa, yauma batajira manu ba ta tafi gida.
Tana tsaye tana jiran mota, amma bata samuba dan haka ta yanke shawarar fara trecking, tana cikin tafiya taga wata katuwar mota range rover baka wuluk se sheki take, ga wasu mota biyu gaba da bayan motar, range rover tazo ta tsaya agabanta, kokari take ta wuce motar, amma se kokarin rufemata hanya me motar yake, "wai wani tsabar wulakanci ne haka? Bana son wulakanci fa. Wasu yan sanda ne biyu, suka fito daga motar " Yan mata kinsan waye a cikin motar nan kuwa, ki iya bakinki fa, kinsan matsayinsa kuwa? yanzu dai yace yana son magana dake kishiga motar semu ajiyeki" cewar daya daga cikin yansandan, wani mugun kallon banza Jalila tayiwa yan sandan, "ai mutum ne a motar ba aljan bako, to duk matsayinsa ace masa bazanzoba, malam bani hanya zan wuce" kuma shan gabanta sukayi "Ke waime kike takama dashi haka kike mana wulakanci kinsan suwaye mu, kinsan dawa muke tare?" "matsalarkuce koku suwaye kodawa kuke tare ba damuwata bace, kuban hanya kawai in wuce tunkafin in taramana jama'a" motar aka bude, wani hamshakin mutum ne yafito daganinsa yaci ya koshi, sanye yake da kakin yan sanda, nan suka dinga sara masa, babban mutum ne ba yaro bane, dan ze haifi Jalila, gabanta yazo ya tsaya "Am sorry mun tsareki a hanya, kizo mu saukeki a gida kinga da rana sosai" Jalila da rashin kunya taso tayi masa amma ganin babban mutum yasa tafasa "A a bakomai nagode, inada kudin mota, amma kace subani hanya in tafi" "zasu baki hanyane, amma kitemakeni da lambarki inaso zamuyi magana" dan zare ido Jalila tayi "laifin menayi maka?"
'laifine babba kam tsakaninki da hukuma , amma tsakaninki da hukumar zuciyata"a ranta tace "ji tsohon kawai, tab wallahi wrong number zanbashi"
"yakikayi shiru, kitemakamin mana"
"kawo abu inrubuta maka" ya mikomata galleliyar wayarsa, dazata samasa wrong number kawai wata zuciyar tahanata "ze iya zama garkuwa gareki daga sharrin su Jeje" ajiyar zuciya tayi tasaka masa lambarta
"Nagode sosai beauty, muryarki kawai ta isa sani bacci cikin nishadi, bankiba muyita tsayuwa anan kinamin magana, gayamin sunanki"
"Kaga ni nagaji, tafiya zanyi rana ta dameni" "hmm se anjamin aji kenan, to shikenan tunda bazaki bari inkaiki gidaba i will call you Insha Allah" bata kuma cewa komai ba ta wuce.
Tana zuwa gida tai wanka tai salla taci Abinci, Mummy takira Maama awaya tace dan Allah ta turamata Jalila ko Nana,su karbi sakon Ilham tana bacci, Dayake Nana bata dawo ba seta tura Jalila, wani tea flask ne me kyau a kwali Mummy tabawa Jalila tace ta kaiwa Maama, wata coustomer zata siya, ta karba ta fito, Jalila na fitowa harabar gidan motarsu Jawwad ta shigo sun dakko Daddy daga airport, tsayawa Jalila tayi daddy ya fito daga motar dauke da brief case dinsa, kana kallonsa kaga mahaifin Jalal, amma yafi Jalal kyau, sedai wannan dogon hancin Jalal ya dakkoshi, shaye2 ne yabata Jalal amma yana da kyau irinnasa, har kasa Jalila ta zube tana gaisheshi, da fara'a ya amsamata
"Takwarar Jalal, ashe kina kanon har yanzu ya kike ya karatu" cikin tsantsan ladabi Jalila tace "Karatu Alhamdilillah daddy" "Masha Allah, Allah ya temaka yayiwa rayuwarku albarka" "Ameen daddy" Jawwad ya dakko trolley da traveling bag na daddy sukayi gaba yayinda Jalal ya tsaya rufe mota, ta taka ta karasa gurin Jalal yana juyowa yaci karo da ita hade fuska yayi kaaman yaga kashi, dan da yaganta yake tuno cin mutuncin datayi masa, seyaji kaman yaimata shakar da seta kusa zuwa lahira
"Kalleka a haka sewani zumudi kake wai kai kafi son mahaifinka, sekace gaske, abunda inka ga dama shima daga masa murya kake, kokagaya masa maganar daka gadama, kana nuna kana sonsa amma baka hakan a aikace, ka girmamashi, tausasa lafazi a gareshi, in gari ya waye kaje ka gaisheshi, in yana maka fada ka nutsu ka danne zuciyarka, kayi hakuri dashi a duk lokacin daya bukaci taimakonka ko alfarmarka zama taredashi da gudun bacin ransa wanda hakan zesa yaji dadi yayi alfahari dayana da
a me kaunarsa, duk fa bazaka iya wannan ba, ta yaya zaka nunawa duniya cewa kana son mahaifinka, hmmm bazaka iyaba banda zafin zuciya da raina iyaye baka iya komai ba kodayake ba abun mamaki bane no need to expect anything good from you, giya ba karya bace, a canza hali abokin Yaya.
Ta danyi murmushi tai gaba, tana addu'ar Allah yasa abunda tafada yai tasiri a zuciyar Jalal, Jalal karasa rufe motar yai ya nufi cikin gida jikinsa a sanyaye, Jalila tazame masa karfen kafa ta uzzuramasa dayawa, gashi har yanzu yakasa samun mafita akanta. Cikin gida yanufa jikinsa a sanyaye yana zuwa ya tarar dasu a palour a zazzaune, daddy ya kalli Jalal yace "Ya dai naganka a haka? Meya faru" dan girgigiza kai yayi "bakomai daddy" haka dai akayi hira sama2 aka watse domin bawa daddy damar ya huta.
Hannah ta na kwance juyi kawai takeyi, zuciyarta fal tunani da damuwa, dagaske son Jalal ne yake damunta, gashi har yanzu takasa samawa kanta wata mafita sam Babu alamar Jalal ze amince ya aureta, a da aikin datakewa Jeje na son Jalal ya amince da ita, sudinga shedanci hakan ya gagara, amma ita yanzu babban burinta ya aureta in har ya aureta tagama karuwanci har abada, to amma tayaya? Yazata samo kan Jalal ya yadda da ita ya karbeta ya aureta, abaya tasan ta taka rawa gurin kara ingiza shi akan shaye2 amma yanzu tayi nadama, son gaskiya takewa Jalal yanzu ita meye abunyi meyakamata tayi, shiru tayi daga can kuma tayi wani guntun murmushi.
Koda dare yayi, Jalal rasa abunda yake masa da
i yayi, tunani ya dameshi, ransa yagama baci Jalila ta dameshi, to amma dagaske take baya son daddy? Shidai yasan yana son daddynsa to amma fa wataran shima yanamasa masifa kaman yanda yakewa Mummy, to hakan yana nufin hakan danakeyi daddy bayajin dadinsa? , to meyasa nake hakane? Gaskiya ina son daddy na, dan bani da takamarsa, jiyayi kirjinsa yafarayi masa nauyi dan haka yatashi yakunna sigari, yana gamawa ya dora da giyarsa seda yafita hayyacinsa sannan ya kwanta bacci
Share please
More Comments............
_ABDUL JALAL (2020)_
_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)
PART
_PAGE
/59_

Abun takaicin, ya kwanta da bacin ran Jalila, zuciyarsa har wani tafasa take dan bacin rai, amma abun takaicin yauma kwana yayi yana mafarkin Jalila, cike da shaukin soyayya da kauna, a yanayi irin na ma'aurata, mafarkinsa na karshene me ban tsoro, ya firgita kwarai ganinshi yayi wasu mutane sun daureshi akan dutse, maza da mata suna saransa da wasu dogayen wukake, Jalila ta bullo daga wani guri ta taho da sauri ta rungumeshi, tana tare masa saran, yayinda sukuma mutanen suka dinga saranta jikinta yana zubar da jini, ta rungumeshi gam itakuma jini na zuba a jikinta a hankali take kiran sunansa a cikin kunnensa ABDUL JALAL. Juyi ya dingayi yana kokarin ya tashi, A firgice ya tashi daga baccin dayakeyi, yana haki, a hankali ya daga kai ya kalli agogo karfe takwas da rabi na safe, tashi yayi zaune yai shiruu yana nazarin mafarkin dayayi na karshe, jujjuya abun ya dingayi a ransa yana tuno yadda take furta sunansa, tunani yake meye alakarsa da wannan mutanen haka suke saransa, dan gutun tsaki yayi, "komeyema na bata lokacina akan wannan shirmen mafarkin" mikewa yayi ya sakko daga kan gadon ya tafi toilet don yayi brush yai alwala kawai ya tuna se yayi wanka, sannan zeyi salla wani dogon tsaki yayi "Jarababbiyar yarinya ta addabawa rayuwata, tazomin a farke ta dameni, dan jaraba har cikin baccina ma seta biyoni, ji yanzu ga rana tayi amma senayi wanka zan salla komeye hakan oho" haka yaita mita yai wanka yafito yai sallar asuba.
Bayan ya idar da sallar ya tafi cikin gida, kai tsaye part din daddy ya nufa, ya tarar daddy ya tashi har yana breakfast Shida Mummy suna hira, sallama Jalal yayi, daddy yadago yana kallonsa yafara murmushi, Jalal yaje kusa dashi ya zauna, cikin girmamawa yace " good morning daddy" ba Mummy ba har Daddy seda ya kalli Jalal, rabon da ya gaida daddy haka da safe cikin girmamawa tun kafin ya lalace dan sedai daddy ya gaida Jalal amma badai ya gaisheshi ba, dama Mummy ba a maganarta itadama baya ta tata, amma abun mamaki yau hada sallama, daddy ya fadada murmushinsa yana shafa kan Jalal yace "Morning yarona katashi lafiya?" "Lafiya kalau daddy, ya gajiyar ka?" "Ba gajiya Jalal, kayi breakfast ne? Ko Jawwad din kake jira?" "No daddy Jawwad nasan ya tafi makaranta" "taho muci nawa to" girgigiza kai Jalal yayi, "kaci Abincin ka daddy, ni zanci nawa daga baya, dama zuwa nayi in gaisheka, sannan in kalleka inajin dadi, kasan na dade ban ganka ba nayi kewarka daddy"
Mummy tace "Hmm wannan soyayya haka, lallai Jalal" daddy yai murmushi yace "to ya ranki, nima kllonka yana sani farinciki yarona, idan na kalleka ina jin da
i, wannan gudan jini nane, babbar kyauta daga Allah, ina alfahari da godewa Allah dayabani kai" dan shiru Jalal yayi cike da damuwa yace "daddy yanzu har farinciki kake da kasancewata danka, kalleni fa daddy kalli rayuwar danake yi, mutane dayawa na kyamar halayena, yayinda wasu suke gudun a dangantani dasu a matsayin danginsu saboda munin halayyata, mutane kalilan ke kaunata suke son farincikina daddy kai da Jawwad bansan wani irin so kukeminba, kai mahaifina ne amma Jawwad da rana
aya be taba kyamata ba"
"Jalal ko a yaya kake kai Allah yabani, kaine nawa ko halinka yafi haka muni inamaka fatan shiriya, amma ni a haka nake sonka, sannan lamarinka da Jawwad soyayyace daga Allah wanda samunta a wannan zamanin abune me wahala, shiyasa nake maka fatan samun mace tagari, Jalal ba abunda yafi zama da wanda yake kaunarka da
"hakane daddy, Jawwad na musamman ne, naso a ce ciki daya muka fito dashi, amma daddy dagaske bana sauke nauyin dayake kaina a matsayin danka ko? Yadda nake treating dinka bahaka ya dace
a nagari yayiwa mahaifinsa bako? Kayi hakuri daddy zan dena Insha Allah"
"waya gaya maka haka kai yaron kirkine, kana kokarin farantamin karka damu lokacine wataran se Labari, Allah ya shirya min kai" "Ameen daddy"
"Jalal ta mahifinka kawai kake, a tunaninka shikadai yake da hakki akanka, ni ko oho ko, da inyi farinciki dakar inyi baka damu bako?" hade rai Jalal yayi, yaiwa Mummy wani kallo me cike da ma'anoni, ya tashi ya fita ya bar dakin gaba daya, daddy ya dan dubeta " Hadiza sam bahaka yakamata ki dinga treating Jalal ba, ko kina manta kece me laifi a gurinsa, yakamata kiyi tunanin hakan. "haba daddy Jalal, shikenan shi abu baze wuceba a gurinsa, kullum da laifina zetamin hukunci" "hadiza ke kike ganin laifinki karamine, banga laifin Jalal ba lokacin danake jan hankalinki, baki saurareniba se yanzu data kwabe miki, seki nemi daidaito da
anki".
Jalila tana tafe akan varander na class dinsu ta ga captain dinsu da takaddu a hannunsa, yanata sauri da alama class zeje, wanda tayi Imanin takaddun hannunsa tests dinsu ne, sauri takara ta hada da dan gudu ta tana kiran sa, tsayawa yayi ya waigo, mamakine ya kamashi yaukumashi wannan yar kwalisar takewa magana ya tsaya suka gaisa da ita "Captain wannan tests dinmune ko?" "Eh sune, me yafaru" "yawwa dan Allah alfarma nake nema, sonake kabani tawa anan" "amma meyasa?" "bakomai kawai inason kabani tawa anan ne, banaso sekaje aji" yadda ta kafeshi da ido yaga tayi masa kwarjini matuka dan haka yace
"to shikenan ya sunan naki, se in duba miki" "A a bani in duba tawa da kaina, karka damu ba ta wanda zan duba tawa kawai zan dauka" ba musu ya mika mata takaddun an fa
i test din nan sosai, kuma gashi over 40 ce duk an fa
i tunda test din be fadi zeyita ba, Jalila tana ganin tata ta zare, tana kokarin mika masa takaddun taga wani suna Samira Kabir Idris, Tunawa tayi Kabir Idris shine sunan dake dauke ajikin katin da baban faruk yabata a banki, mika masa takaddun tayi tace" Thank you very much "
" You are welcome " tunani ta dingayi waye me irin wannan sunan a ajinsu, maybe ma kawai sunane yazo
aya, da sauri ta tafi class taje gurinta ta zauna, Captain yana raba takaddu tanajin ya ambaci sunan Samira Kabir Idris, ta juya dan ganin kowace, wadda tai tsammanice Samira kawar saleema, se yanzu taga tsananin kamaninta da Alhaji Kabiru, kenan 'yarsa ce, ajiyar zuciya Jalila tayi, barewa bata gudu danta yayi rarrafe, ba a banza ba Allah yabashi irin wannan yar, Alhamdilillah bincikena zezo da sauki, sena gane alakarsa da Jeje, tana cikin tunanine taji captain yana cewa
"Yan class kunga munyi test, ga a yadda tazo dan haka se mudage a exams, sannan muyita addu'a dan banga wanda ya ci talatin bama, amma yace yanason ganin Jalila Aliyu Imam, in taji tasan kanta taje yana neman ta, danni ban santaba" zahra ta kalli Jalila," bake ake nema ba? "
"nice"
"Naga ba abaki naki test dinba, ni dai kinga wai 19 na samu" "kigode Allah ai kinyi kokari, yawwa zahra dan Allah samira sunawane yan gidansu" "Su biyune kawai yayanta faruk, sekuma ita sukenan" "Kuma a gidansu ansan me takeyi? "
"Gaskiya bansaniba babansu dai yana da zafi, wataran yana kawota makaranta, mamansuce dai ance ba ruwanta da tsanani akan tarbiyya"
"Mene sana'ar babansu?" "Kai Jalila sekace wata lawyer wannan tambayoyi haka" "yi hakuri akwai abunda nakeson ganewa ne" "gaskiya ban saniba, amma naji kaman ance dan kasuwa ne" "shikenan nagode sosai".
Bayan antashi daga school Jalila tai tafiyarta gida bataje kiran sir hafiz ba, tanata tunanin yazata bullowa lamarin Alhaji Kabiru, dan tana zargin mutumin nan sam bata yadda dashiba, wayarta ta dakko ta duba what's app dinta, taga lambarsa tayi appearing a contact dinta na wats app, dan bayan dawowarta gida ranar tasaka lambarsa a wayarta hotonsa ne akan dp dinsa tayi sa'a yana online, dan haka tayi masa sallama, seconds kadan ya amsamata, suka gaisa yace mata be gane me maganaba, rasa me zatace tayi, kawai ta kashe datarta ta ajiye wayar tai shiru tana tunanin anya haka yakamata tayi, ko kawance zata kulla da samira, amma in tayi haka itama za adingayimata kallon 'yar iska, lambar hanan ta kira amma taki shiga dan haka ta hakura.
Hanan kam tana kwance, tana trying lambar Jawwad amma a kashe, ta ajiye wayar ta dafe kanta, turo kofar dakinta, dan dago kai tayi da mamakinta setaga Siyama, zumbur Hanan ta mike tana murmushi "oyoyo Siyama matar Yaya yauke kika kawomin ziyara" murmushi Siyama tayi "yau nina kawomiki tunda kin mance dani nace bari inyi surprising dinki" "amma naji dadi" Siyama ta zauna, Hanan taje ta kawomata ruwa da lemo da snacks suka zauna sunata hira, Hanan ta kalleta "ta Yaya Abdallah gaskiya Siyama, kin rike wuyan yayana over, komai ke ni ya manta dani gayamin meye sirrine" "haba Hanan waceni rike wuyan Yaya, shiya rike nawa wuyan, wallahi Hanan Abdallah ya iya soyayya shiyake tabarani, bana tunanin akwai namijin daya kai yaya Abdallah iya soyayya da kula da mace" dariya sukayi gaba daya "Siyama ya bakyacin snacks dinne?" "A a ni snacks be dameniba dama chocolate ne" "Ahh sekace queen J, kinsan inkinaso ki birgeta kibata chocolate, gaskiya ina missing Jalila ina kaunarta har cikin raina, amma alakarmu na shirin samun matsala wanda hakan bazemin da
i ba, amma nakasa samun mafita, dama kobakizoba ina son zuwa siyama" hanan ta karasa maganar cikin damuwa,
"Amma Hanan bangane mekike nufiba, kamarya alakarku na shirin samun matsala kamar yaya?"
"Siyama Jawwad nakeso, da farko na dau abun wasa, inayine domin Jalila ta maida hankali akan Jalal, saboda sunfi dacewa amma yanzu nagane wallahi son gaskiya nake masa kota ina yaya Jawwad ya hadu" zare ido Siyama tayi "Hanan kin san irin soyayyar datakewa Jawwad kuwa?" "Siyama soyayyar dake tsakanin Jawwad da Jalila na yan uwantaka ne, amma da Jalal ta dace shike bukatar taimakonta, ina kaunar Jalila amma bazan iya rabuwa da Jawwad ba" Hanan ta riko hannun Siyama, idonta taf hawaye tace "Siyama babu wasa a zancena, wallahi dagaske nake inason Aliyu Jawwad, so na gaskiya, sannan ina kaunar Jalila ina jinta kaman wani tsagi na rayuwata, amma bazan iya rabuwa da Jawwad ba" Ajiyar zuciya Siyama tayi, ta gogewa Hanan hawaye "For now kiyi hakuri ki dan bani lokaci, zanyi tunanin mene mafita, amma kidena kuka" gyada kai Hanan tayi kaman karamar yarinya, daga nan suka shiga wata hirar
Seda aka kwana biyu, Jalila bataje kiran sir hafiz ba, captain ne yazo yana kuma shela a aji, danshi besan wace me sunan ba, tashi tayi ta fita tatafi offers dinsa, tana zuwa ta shiga da sallama ta tarar da shi da wasu lecturers a office din ammasu dattawane ba kamanshi matashiba, amsamata sallamar sukayi, kaman yadda yake
abi'ar Jalila har kasa ta zube cikin girmamawa ta gaishesu, suka amsamata cikin mutunci, shi sir hafiz mamaki ma ta bashi, ya kalleta a fusace "uban mekikazo yimin office, kin fadiko? Ba abunda zanyi miki aidama seda nagaya miki fita kibani guri, dakikiya kawai kisawa ranki kin gama faduwa exams dina" batace komai ba ta juya tai tafiyarta
Malaman nan suka dinga jinjina tarbiyyarta, saboda a wannan zamanin a yan matan jami a asamu me durkusawa har kasa ta gaida malamai abunda wuyar samu "hmm bakusan halinta bane, tsabar iya makircine dakikiyace gata fitsararriya, nayi test ta fa
i shine takamo hanya tazo".
Bayan kwana
aya sir hafiz yakuma sawa a kira Jalila Aliyu Imam, tareda kashedin in batazoba zesakamata zero a test dinsa, kuma zuwa office dinsa Jalila
tayi, yau wasu yan matane a ciki se iyayi suke suna yauki, gani tayi bashida niyyar saurarta dan haka tazo gaban tebur dinsa tace "Sir tunda baka da lokacina karka kara turawa kace inzo, zuwana nawa office din nan kaki saurarata, bayan kaikace inzo" daga kai yayi ya kalleta, yayinda yan matan suka bita da kallo "ni nace kizo? Kizo in miki me" "bakai kace inzoba karka kara tura captain yana shelar wacece Jalila Aliyu Imam dan bazan kuma zuwa ba, kaitasamin zeron inka ga dama kasamin abscent se wani wulakanci kakemin menayi maka hakane? , in akwai abunda be kai zeroba kasamin" da sauri ya kalleta "What kece Jalilan?" zumbura baki tayi "Eh nice" "karya kikeyi" ba tace komai ba ID card dinta ta dakko ta diremasa a gabansa, dauka yayi ya karanta ya kalleta tabbas itace
"Ya akayi kikacinye test dina gaba daya alhalin wani abunma banmuku ba, kaf ajinku ba wanda yaci ko 30,ko satar amsa kikayi? Kallon yan matan dake office din tayi tai ta kalleshi tace
" Sir Hafiz , Never Judge book according to it's cover, bana satar amsa kuma bantabayiba, kana muzantani agaban yan aji kana cemin dakikiya, abun ba anan takeba, kayi alkalanci, idan baka yadda da wannan test dinba ka canzamin wata, amma karkayi tunanin zaka tambayeni a gaban yan aji in baka amsa" shiru ya danyi, ya kalleta yafarayi mata tambayoyi, a nutse take bashi amsa, gashi ta iya turanci matuka, ga mamakinsa har abunda be koya musuba inya tambayeta seta bashi idea dinta, ajiyar zuciya yayi "shikenan zaki iya tafiya zan nemeki" Jalila ta juya ta fita. Sir Hafiz ya dade yana mamakin kwakwalwarta, gata gentle, amma meyasa tsarin rayuwar ta daban da saura ko maganarta ma daki daki kuma a tsare, kuma ba ruwanta maganar kozatiwa wanda ta fadawa dadi ko a a seta fada kuma ko
a gaban waye. haka yaita mamakinta.
Yau weekends dan haka tun sassafe Jalila taketa gyaran wardrobe dinta, tagama tsaf seta ga qura'nin da daddyn Jalal ya taba bata, ta jujjuya qura'nin yana nan kar dashi a cover dinsa "Yakamata in dinga tilawa da qura'nin nan, Allah ya bawa daddyn Jalal ladan" tagama gyaran drower dinta, ta tafi kitchen, wainar masa suka tsiriyi itada halima, a matsayin abincin rana, seda suka gama Jalila taje tai wanka ta dawo
aki ta zauna tana kwalliya wayarta tafara ringing, tana dubawa taga bakuwar lamba ce, bata san wayeba dan haka ta saka wayar a silent.
Tunda daddy yazo garin nan Ilham take kasa kunne taji, anyi batun aurensu da Jalal amma shiru yau kwanan daddy uku da dawowa amma bataji Mummy tace komai ba, dan haka ta yanke shawarar zuwa tasamu Mummy, dakin Mummy taje bata nan, dan haka ta tafi kitchen, aikuwa Mummy na can tana hadawa daddy fruit salad
"Mummy sannu da aiki"
"Yawwa daughter, kin tashi daga baccin ne?" "ina wani Bacci Mummy alhalin duk ina cikin zullumi da damuwa" "akan mefa?" "Mummy maganata da Jalal mana, har yanzu naga Daddy ya dawo amma bakice komai ba fa"
"Ilham kenan akwai gajen hakuri, ina nan zan gayamasa insha Allah kafin yakoma za asa ranar aurenku" Murmushi Ilham tayi "Allah yasa Mummy, dan na kagu inganni na mallaki yayana" "hmm daughter ba kunya ko" Ilham ta dan rufe ido tana dariya.
Jalila tagama kwalliyarta tasaka turare, ta mike taje ta dauki Abincin Jawwad ta nufi part dinsa dashi, tana zuwa ta tarar bakowa a palour, ta ajiye abincin tasamu guri a palourn ta zauna, tana jiransa koyana wanka ne, ta dora kafa
aya kan
aya tana danna wayarta, hankalinta yana kan wayar sosai, tana game tanayi tana murmushi, warin sigari taji ya daki hancinta, da sauri ta
aga kanta, tai tozali da Jalal ne ya fito daga bedroom din Jawwad, kallo
aya tayi masa ta
auke kanta taji tsigar jikinta ta tashi, dagashi se gajeren wando, kana ganinsa kasan yana cin karfe, a mur
e jikinsa yake, ga ko ina na jikinsa lullube yake da gashi, fatarsa se sheki take, babu alamun wahala a tareda shi, ya nufo inda Jalila gadan2
zazzare ido Jalila tayi, kirjinta ya shiga dukan uku2 tanaso tayi magana amma takasa.
More Comments
More Typing.....................
Koda yaushe bazan manta da gudunmuwarku ba ABDUL JALAL NOVEL FANS GROUP
inajin dadin comments dinku, sauran masoya wanda nasani da wanda bansaniba ina godiya
If you want Join the what's app group via this link
@https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL
Or contact me via my number, i mentioned at the above page
If you are not reading the novel please don't join.
[09/04, 12:29 PM] Ayshercool:
_ABDUL JALAL (2020)_
_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)
PART
_PAGE7
60_

Jalila da kyar take fizgo numfashi, nufota yacigaba dayi, yana zuwa seya wuceta yatafi gurin Tv yanata shan tabarsa, yaje yasaka wayarsa a caji, Jalila kuwa se binsa take da kallo, yagama sa cajin ya taso yakuma dawowa harya wuceta ya dawo ya zauna a gabanta ya kura mata ido, dauke nata idon tayi, "naga kina son kallona ne shiyasa na zauna kigama karemin kallo" ya busamata hayakin sigari a fuskarta, da sauri ta dago tareda toshe hanci, ta dan fara tari, "wai meye haka, Allah ya sawwake inzauna ina kallonka, kato da kai kazomana gida tube sekace dakinka" "dakin Jawwad dakina ne, dan haka ko tsirara naga dama zanyi yawo" yunkurawa tayi zata mike, ya maida ita kan kujerar ya kafeta da ido, yasa kafarsa daya a gefenta, ta kalli inda yasa kafarsa aranta tace kalli jikinsa duk gashi kaman wani dan biri, lighter ya jefomata yasa wata sigari a bakinsa, yaimata alama ta kunna masa, wani mugun kallo tayi masa ta dauke kanta "Allah ya kiyaye ya rufamin asiri, nikabani hanya in wuce, kalleka dan Allah" hannunta daya yakama cikin mugunta ya murde mata yatsu, ihu tayi saboda zafi, take tafara zufa cikin tsawa yace "Kunnamin ko tarihi ya maimaita kansa, inkuma duramiki sigari yanzun nan" jiki na bari ta kunna lighter ta mika hannunta ta kunna masa, "dan Allah ka sakarmin hannuna, yatsuna zasu cire" a hankali yasakar mata hannu, idonta har yayi ja, yacigaba da busa mata hayaki, gashi ya tareta da kafa bazata iya guduwa ba, hannu ta kai zata toshe hancinta, "wallahi kika toshe hancinki sena wanka miki mari, sena baki mamaki da hannunki zaki shata" bashiri ta ajiye hannunta yana busa mata hayaki, se tari takeyi tana dauke numfashi "gaskiya Jalal dan iskane bashida mutunci, yanzu inna matsa da rashin kunya ze iyayimin akuya" seda ya shanye tabarsa tsaf sannan yadubeta "nine Namiji mara daraja ko? Ni Jalal nikike zagi ko?" shiru tayi tana kallonsa, daka mata tsawa yayi "ba dake nake ba kike wani kallona mara kunya" cikin dakewa tace "karya nayi, aiba kadyanayi ba namiji me daraja baze abunda kake ba" "hakane Amma kin bar kari tun ran tubani, kinyi sake namiji mara daraja yamiki Illa, wadda bazaki ganetaba a yanzu, idonki kawai ya nuna a tsorace kike kar in miki wani abu, ba abunda zan miki a yanzu, amma kisani bana yafiya, bana mantuwa, sena hukunta ki akan cin mutuncin dakikemin bazan kyaleki ba, sena gwada miki abunda nakeji idan kika ci zarafina, kidena shishshigi akan abunda baki saniba" Yayi ajiyar zuciya "tashi ki tafi kibani guri kuma kar inkuma ganinki a part din Jawwad dai 2 wannan lokacin, dan kinsan baya nan inkuma kika kuma zuwa to nasan abunda kikazo gani"
Sumi2 ta tashi, taje bakin kofa ta tsaya ta kalleshi "to me zanzo gani, kaikanada abun kallone jiki duk gashi ba kyan gani sekace ji
kin biri, kokuma wannan jijiyoyin zanzo kallo, jiki kamar dan wrestling aikai ko kyan gani baka dashi, kasa wannan katon hannunka ka matsemin yatsuna Allah yasakamin dan ban yafeba kuma duk barazanar ka bazan dena fadan gaskiya ba, sannan kayi kadan kayimin Illa ko a yanzu ko a gaba, mugu kawai "tai ficewarta, Jalal kam yana jinta tana banbaminta ko dago kansa beba balle ya kalleta.
Ta wuce cikin gida tana yarfa hannu saboda zafi, tana zuwa daki taga Nana ta shirya da alama fita zatayi
" Ya dai naganki kin hade rai, me akayi miki ne? " Jalila ta yamutsa fuska "Bakomai" "Shikenan dama kenake jira kizo ki rakani gidan, Yaya mairo, tace tana son ganina"
"Tab amma badani Jalilan bako?"
"Kamar yaya?" "kamar yadda nagaya miki mana, haka kurum ketace tana son gani baniba, dan haka ba inda zani, banje gidanta ba ma cimin mutunci take, inaga innaje mata gida, kitafi kawai, ba inda zani" "Shikenan tunda bazakiba, dama banason tafiya nikadai ne" "sauka lafiya ki gaishesu"
Bayan Jawwad ya dawo daga school suka zauna domin cin Abinci rana shida Jalal, Jalal ba karamin dadi yajiba ganin wainar shinkafa ce, sunci Abincin nan sosai, Jalal yace "Jawwad dan Allah in da sauran Abincin nan ka zubamin in kaiwa daddy, kasan yana son wainar shinkafa" "Hakane Allah yasa akwai, bari inje cikin gida in duba" Jawwad ya tafi domin dubawa koda Abincin, Jawwad na fita aka kirashi waya, Jalal ya daga wayar ya duba, seyaga sunan Hanan, Murmushi yayi ya daga wayar
"Jawwad ka manta dani ko? Baka daga wayata, nashiga wani hali banajin dadin abunda kakemin" gyara murya Jalal yayi
"ba Jawwad bane, Jalal ne" "Jalal kaine yakake ya gida" "lafiya kalau ya Abdallah, kodayake muna waya dashi" "Yana lafiya, Jalal kaga abunda Jawwad yakemin ko? Banajin dadin hakan, dan Allah kasa baki, Jalal inason abokin ka da wasa na dau abun amma yanzu serious nake sonshi, Jalal help me, so masifa ne, da ban yadda da hakanba se yanzu" "kinaji Hanan, kiyi hakuri Jawwad inyace baya Sonki karya yake, kawai yana duba alkar dake tsakaninki da kanwarsa, amma karkidamu zamuyi magana dashi" (
nikam nace su Jalal dama an iya rarrashi haka) Ajiyar zuciya Hanan tayi "to nagode sosai Jalal, agaida su Ilham"
Jawwad ya shigo da food flask a hannunsa, ya ajiye ya kalli Jalal, "gashi nan Abincin Baby ne tace abawa daddy, amma dawa kake waya haka a wayata"
"Jawwad" "Na'am ina jinka" "Meyasa kakewa yarinyar nan hakane" "Wace yarinyar kenan?" "Hanan mana, ta damu da kai, kamanta kaikake min fada akan Ilham segashi kaima kanayi, meye marabar Hanan da waccan fitsararriyar banzan, ba gara Hanan din bama tafita nutsuwa da saukin kai" "Haba Jalal, Jalila da soyayyar ta na tashi, banason yin abunda zan bata mata rai, tarayyata da Hanan baze haifar da da me idoba, kuma Hanan da kake ganinta itama rigimammiyace, kaikewa Jalila wani kallo dan bakwa jituwa"
"Jawwad yakamata kakoma hankalinka, kayi wani abu akan yarinyar nan mana, kana ganinta so classic nasan da wanine ba kaiba zata sauke ajinta tace tana sonsa ne? Kayi wani abu mana" tsaki Jawwad yayi
"Ina tsawon shekaru Ilham ta dauka tana nuna maka so, kai mekayi akai"
"Jawwad kasani nasani, nida Ilham bamu dace ba, kuma kasan dalili, kuma bari in sake jadadda maka, kokuma in tunamaka wani abu, mahaifiyarka bazata taba bari ka auri Jalila ba, musamman in wannan magananniyar matar tana nan, kaima kasani, kayi tunani Jawwad kafin al'amura su kwabe maka" yana gama fadin haka ya kwashi food flask din yai ficewarsa, yabar Jawwad a zaune yana tunani.
Jalal yana zuwa gida ya tafi part din daddy da fara'arsa, "daddy ina fatan bakaci Abincin rana ba? " "banciba ina shirin ci dai" "Abincin daka fiso nakawo maka" Jalal ya turawa daddy flask din ba karamin murna daddy yayi ba daganin Abincin da Jalal ya kawo masa, "Jalal inaka samo wannan Abincin?" "a gidansu Jawwad" "yaushe rabon da inci masa" daddy ya dan kalli Mummy "Madam kindenamin Abincin gargajiya, mussaman favorites dina" "hmm ba gashi danka yakawo maka ba sekaci ai" daddy yai murmushi "Jalal wayayi girkin nan yayi dadi" "nima bansaniba" Mummy tace "nasan baze wuce Jalila ce tayishiba, dan Maama bata fiye yin girki ba Nana kam dama ba a maganarta akwai son jiki" daddy yace "Jalal inka koma ka turomin takwararka, kafin inkoma England inason inkuma cin irin Abincin nan" hade rai Jalal yayi "daddy waibaka san sunanta bane zaka dinga cemata takwarata" murmushi daddy yayi irin na manya "hmmm to ko in tunamaka tarihin yadda aka samata sunan ne? Dan naga kaman ka manta" "Wai daddy meyasa kake son yimin haka, abune yafaru shekaru da suka wuce kuma kuruciyace baya wuce ba" murmushi daddy yayi "kaji tsoro kenan" "niba wani tsoro danaji" "hmm Jalal kenan, a shikenan tunda kaki yadda" ganin daddy yana neman takura masa yasa yatashi ya fice, bayan fitar Jalal ne Mummy ta kalli daddy "daddyn Jalal, inason muyi magana da kaine" "to ai gani ina jinki"
"Dama gani nayi lokaci yayi daya kamata mucika muradin yaran nan, ina ganin Jalal idan akayi masa aure ze samu nutsuwa, ze rage abubuwan dayakeyi" Ajiyar zuciya daddy yayi
"to yanzu wace yarinyar kike gani zata auri Jalal a wannan halin dayake ciki?" "to ai Jalal yanada wadda yakeso, ga Ilham nan suna son junansu, yakamata kawai ayi magana asaka rana" "kin tabbatar da duk su biyu
suna son junansu" "Eh mana sun son junansu, yakamata ayi magana kaje kasamu baban Ilham ayi maganar auren nan" "Kina ganin ba matsala a yin hakan, sunada banbancin halayya, kaman zamansu bazeyi dadi ba" "kaga tunda dai suna son junansu a haka ai shikenan" "Amma ni Jalal be taba yimin wannan zancen ba" "to aini gana nagaya maka" daddy yayi Ajiyar zuciya, be kuma cewa komai ba".
Jalila kwance akan gadonsu ta dakko wayarta ta kira Alhaji Kabiru amma be daga ba, dan haka ta sauka tafara chatting, tana what's app tana hira da zahra, setaga Alhaji Kabiru yakirata, ta daga wayar amma batace komai ba, setaji yana cewa
"Jabir Nakiraka bata shiga, se yanzu tashiga, kayan sun taho daga kudu, munyi waya sunkusa karasowa kano za a sauke a gidan gonata, kaje ka karba se ka rarraba musu cikin dare, kayiwa Jeje magana shima yazo ya karbi nasu" shiru Jalila tayi, wane irin kayane wannan? ta kashe wayar , ta maimaita "Kaya a rarraba cikin dare, kuma hada Jeje" what's app ta koma da sauri tai masa sallama, amma beyi reply ba, ajiye wayar tayi tanata tunani, besan lambar waya kiraba kenan, "Allah nagode maka nafara samun hint akan mutumin nan, Allah kabani mafita" wayarta takuma dubawa setaga ya amsa mata sallamar
"barka da rana, ranka ya dade yakake ya harkoki"
"lafiya kalau, wake magana?" shiru Jalila tayi tana tunanin wani suna zata gayamasa, kawai setace masa "Halima ce" "Wace haliman?"
"hmm duniya da gaskiya kuwa? Wadda kabawa complementary card a banki" "ohhh am so sorry, kuma seda na kawo kece dan na dau muryarki, sedai dan bansan sunanki bane, ina fatan kina cikin koshin lafiya, Gimbiya Halima" "Ina lpy" "Amma nayi mamaki, dakika nemeni, danaga kin yaga card din banzaci zaki nemeni ba, nayi farinciki gaskiya" Jalila ta biye masa suka dinga chatting, daga baya ta sauka ta rufe data dinta,
Jinjina kai tayi, "lallai wannan mutumin zakayi saurin fadawa tarkona, Kuma abun mamaki, wani kayane ake rabawa cikin dare, ga sunan Jeje ya ambata, to me hakan ke nufi, wannan ya tabbatar da yana hulda da Jeje, to wace irin hulda Alhaji Kabiru yakeyi da JeJe haka, wanda yasashi zuwa gurin birthday din Jalal a boye, kai akwai lauje cikin nadi" tana tsaka da wannan tunanin still aka kuma kiranta a waya, koda ta duba tagane lambar Dan sandan nan ne, tsaki tayi harta ajiye wayar sekuma ta yi wani tunani ta daga
"Salamu alaikum" amsamata yayi sanna yace "beauty barka da wannan lokacin ya kike seda ta dan tura baki gaba "Lafiya kalau" "dama cewa nayi bari inkiraki inji lafiyar ki, sannan inaso inzo gidanku in ganki"
"What gidanmu kuma mezakayimin" "Meye abun tashin hankali, inasonki ne aurenki nakeso inyi, please" ture wayar gefe tayi takama dariya sannan ta maida wayar kunenta "Ni wallahi kabani kunya yar baby dani yaushe na isa aure, kuma ya za'a yi Abbana ya aura maka ni, ni gaskiya yarinya ce" yadda take shagwabar ba karamin birgeshi takeba
"Haba yar baby wayace miki baki isa aure ba sannan kuma babu kunya a soyayya" "Babana bazemin aure yanzu ba kuma yariga yabadani, amma nima bansan wayabawa ba" Ajiyar zuciya yayi "bayarwa ba aure bane dan haka zancigaba da neman aurenki"
"Hmm shikenan se anjima, zanyi karatu yanzu" "To Baby tunda kinki gayamin sunanki, ayi karatu da kyau, inkinki mu hadu zannemo gidanku inzo gurin Abbanki da kaina" "Sekazo" daga nan ta kashe wayarta "tab ina zan kai wannaan mutumin"
Bayan sallar la'asar, Jalal yakoma gurin Jawwad, koda yaje ya tarar dashi wani iri kaman mara lafiya, Jalal bebi takan tambayar meyake damunsa ba, saboda yasan akan maganar dazu ne,
"Jawwad daddy yace yana son ganin kanwarka"
"wacce daga ciki?" "wadda ta yi Abincin yau"
"Jalila ce tayi, Allah yasa ba laifi tayiwa daddy ba" "nima bansaniba yace dai taje yanason ganinta"
"zangaya mata Insha Allah" "yayi kyau bari in tafi in kyaleka naga kana cikin damuwa tunda mukayi magana dazu, karka bata lokacinka gurin dogon tunani, maganata itace gaskiyar lamari, duk inda zaka juya kayi tunani kasani maganar dayace mahaifiyarka da yan uwanta basa som wadda kakeso kuma bazasu bari ka aureta ba, dan haka mafita kacireta a ranka ka maye gurbinta da Hanan"
"Jalal tayaya wannan abun ze yuwu, ni Jalila nakeso, Kuma maganar Maama nasan zata amince ne in na lallabata" murmushi Jalal yayi "Shikenan Allah yabada sa'a, amma karka manta da batun kiran daddy" yana gama fadin haka ya fice.
Tunda Jalal yafuta tunani ya damu Jawwad, wayarsa ya dauka ya kira Jalila suka dinga hira, har ya manta da abunda yake damunsa, daga nana yagaya mata daddyn Jalal yace taje yanason ganinta.
Jalal yana komawa gida, kozama beyiba kiran Hannah yafara shigowa wayarsa, tsaki yayi ya ajiye wayar ya shiga sabgoginsa amma tacigaba da kiransa, takirashi yafi sau goma, a fusace Jalal ya dau wayar
"Hannah kina bina bashine? Wannan kiran haka meya faru?"
"Niko nake binka bashi Jalal, meyasa kake wahalar dani hakane? So seya koma kiyayya bana sukuni idan banganka ba, Jalal dan Allah ka tausayawa zuciyata, Jalal kasan Masifar So kuwa? Na tabbatar dakasani dabakaimin haka ba, Jalal ka dubi girman Allah ka tausayawa zuciyata" murmushi Jalal yai kaman Hannah naganinsa
"Hannah kenan, ina mamakin sanda soyayyar da kikemin ta rikide zuwa ta gaskiya abun akwai mamaki gaskiya, but don't mind me akan abunda na fada kinji, nagaya miki gaskiya tun farko, baze yuwu ace nayi yawon club sannan ace matata ma tsohuwar yar club bace, dukda zuwa club dinmu yanada banbanci, kiduba a samarin club dinnaki kisamu wani ku daidaita amma ba Jalal ba"
"Amma Jalal ai nace maka na tuba wallahi inka aureni zandena"
"Ni ABDUL JALAL nafi karfin ragowar garorin bariki, ki kiyayeni" yana gama maganar ya kashe wayarsa.
Daddy sam yakasa yadda da batun Mummy gameda Jalal, shidai yasan Jalal ko zancen mata bayaso ayi masa, amma ya akayi haryake soyayya da Ilham besaniba dukda yana dadewa baya nan, amma yasan da zeyi masa zancen, dan haka ya yanke shawarar kiran Jalal yaji tabakinsa.
Hanan na kwance akan katafaren gadonta, tayi zurfi a tunanin ta, taji an turo kofar dakinta, dan daga kai tayi taga mum dintace, batace uffan ba tai shiruu tacigaba da tunani, gefenta Mum tazo ta zauna ta dafata "Auta meyake damunkine, yan kwanakin nan kullum cikin damuwa kike meyake damunkine" a hankali Hanan ta tashi zaune "Mummy na ba wata damuwa, damuwar school ne kawai kinsan akwai tension na makaranta"
"Hakane Hanan, amma yusuf yakawomin kararki fa" dan ya mutsa fuska Hanan tayi "Meyace miki?"
"gaba daya kin canza masa yakasa gane kanki, meyake faruwa ne?"
"mummy kinsan tun farko dama ni bawani yimin yaya
ba kinsani, Mummy kinsan wani abu kuwa"
"A 'a sekin fada"
"tun farko kinsan ba son Yusuf nakeyiba, Mum zuwana kano naga Yayan Jalila cousin dinta wanda takeso, da saboda in tsokaneta nace ina sonshi, amma daga baya abun yakomamin Gaske, Mum ina son Abunda Jalila takeso ne, kuma yazama dole tabarmin dan basu dace ba".

Daga Alkalamin Aysher cool
Comments dinku yana sani nishadi ABDUL JALAL NOVEL FANS GROUP ina yinku irin sosai din nan Allah yabar zumunci yabar kauna
Join the what's app group via this link ABDUL JALAL NOVEL FANS GROUP :https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL
Don't join in ka/kinsan baka karanta novel din
07063065680
_ABDUL JALAL (2020)_
_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)
PART
_PAGE
/61_

Wani irin Kallo Mum tayiwa Hanan
"I don't think you are in your senses, Hanan, kawartaki dukda yarinyar ba wani yimin tayiba, amma son da kike mata yasa na kyaleku tare, amma hakan bazesa inkasa gayamiki gaskiya ba, Hanan inkikayi haka baki kyautaba, hakan ba daidai bane, Jalila taana kaunarki meyasa zakiyi mata haka" kwalla ce ta taru a idon Hanan
"Mummy ki fuskanceni banyi haka dan cin amanar Jalila ba, Mum wallahi makauniyar soyayya nakewa Jawwad, Mummy he is very nice and gentle, gashi salihi, Mum soyayyata da Jawwad mafita ce kuma ceton Jalila ne, inajinta a zuciyata kamar yar uwata ta jini, dan haka bazan iya cutar da itaba all i know is that inason Jawwad "
"Kamar yaya kenan, tayaya kike son maida karya gaskiya"
Labarin abunda ke tsakanin Jalal da Jalila tabawa Mummy, ta nisa tace
"Mum ko bankuma cewa komai ba kinsan Jalal is her e destiny, ita kadaice zata iya sadaukarwa domin ceton sa, Mum mahimmanci Jalal a rayuwarta ne yasa ake mata nuni da halin dayake ciki a mafarki, Mum kibani karfin gwiwa, zanyi meyuwuwa in dauke hankalinta daga kan Jawwad, sannan zan temaketa akan rayuwar Jalal" Jikin Mum ba karamin sanyi yayiba dajin labarin da Hanan tabata,
"Shikenan Auta, zancigaba dayimuku Addu'a Allah ya zaba abunda yafi Alkhairi".
Jalal cikin gida ya tafi domin samun yin hira da daddy, yana zuwa ya tarar da Ilham a babban palour da waya a hanunta tana waya, kotakanta bebi ba yanufi part din daddy, bayansa Ilham tabi da kallo "muje zuwa Jalal zakaga tsiya" Jalal yana zuwa ya tarar da daddy a
palour dinsa suna hira da mummy, daddy na ganinsa yai murmushi "dan halak kaki ambato, zancenka nakeyi a a raina karaso Dama inason ganinka dan gidan daddy"
"to gani mezaka bani, Jalal yafada yana zama akan kusa da daddy"
"Jalal magana nakeso muyi da kai, Mum dinka tazomin da magana nayi murna da jin hakan shine nakeson ji bakinka" Mummy tai farat tace
"Ba dai maganar da mukayi dazu bane, ai mungama magana dakai, meye kuma na tada wannan zancen, kayi abunda yakamata kawai" daddy yace
"A a Madam karmuyi gaggawa, dole mubi komai a sannu sannan inji ta bakin kowannensu" "A'a fa ai mungama magana wannan kawai maida hannun agogo baya zakayi"
Jalila da sallama ta shigo palourn, Ilham na palourn amma tai mirsisi taki amsawa, "Aminiya Ilham amsa sallamar ma seyazamo miki aiki, amsa sallama dabi ace ta kyakkyawan musulmi, karki zama irin yayanki nan mana" tsaki Ilham tayi tareda fadin
"meye hakane wai? Ke kullum in baki shiga sabgata
ba bakyajin dadi ko? Ina ruwanki da nida danuwanane mayya"
"Aini indai a irin sha'anin nan ne to nafi uwar mayya naci, mayya in akayi magani ana samun nasara nikuwa babu abunda zakiyi kiyi nasara akaina, sannan duk abunda ba'aso ni shinakeyi dan aji haushi, and the most craziest part of me is that bana riko, yanzu zamuyi fada yanzu zan manta, duk abunda na rike a zuciyata nake fushi akansa to yanada mahimmanci a gurina, dan haka nibana gaba dake Ilham dan bakikai inyi hakan ba dake, sannan kuma bazan fasa bata miki raiba in har kikayi abunda yaci karo da Ra'ayina sedai kiyi hakuri "
Lallai Jalila tacika yar rainin hankali, wulakanci goma da ashirin.
Duk yada Mummy tayi a wayance kar Jalal yaji zancen nemamasa auren Ilham daddy yaki, karshe a fusace Jalal yace" waini meye hakane daddy, afadamin komene mana, inbaza ayiba meye na dakko maganar agabana, nibanason irin haka fa"
"Ohh ka kwantar da hankalinka yaron kirki, aiba abun tashin hankali bane, maganane me dadi akanka, maganane nacika maka burin rayuwarka, Mummy dinka tagama yimin bayani akan komai, nagame da abunda ke tsakaninka da Kanwarka Ilham, dan haka zanje muyi magana da mahaifinta asa rana, nayi farinciki da har kafara tunanin aure Jalal, cigaba yafara zuwa a rayuwarka kaga......
"Enough daddy" Jalal yai maganar a fusace, "Wannan maganar daga ina? Duk matan duniya in rasa wadda zan aura se wannan, in har farinciki kake nafara maganar aure, to da saurana, wait wai wama yagaya maka wannan maganar, kodayake base ka gayamin ba nasani," ya kalli mummy "Ke kika gaya masa nasan haka, nidake na taba cemiki ina son wannan yarinyar ne? Meyasa kikemin hakane, meyasa kikeson kuma rusa al'amuran rayuwata, ke a ganinki Ilham ta dace da zama matata, kimin adalci kiyiwa kanki mana, akoda yaushe kidena duba maslahar kanki kawai, kuma Ilham tunda Ubanta na raye se ta bar gidan nan, ai ba gidan ubanta bane ba, akanme za a dinga batamin rai haka, wallahi sena kakkarya yarinyar nan inga uban da ze tsayamata" daddy yai gaggawar mikewa da nufin tare Jalal amma Jalal ya kauce ya nufo hanyar fita,
Ilham taiwa Jalila wani mummunar kallo "ai dama da ganinki base an fada ba ke mayyace, bari inkuma jadadda miki, duk maitarki kurwata data Jalal tafi karfinki haka kika ganmu haka zaki kyalemu, nidashi mutu ka raba" "to dan kincemin mayya ai ba haushi zanji ba, ko ina cin kurwa bazanci taki data Jalal ba saboda bazanci kazamar kurwa ba, kuma kina bani mamaki, dakikancinki yayi yawa Ilham bansan lokacin dazaki gane cewa niba abunda zanyi da wannan dan giyar ba, kuma kema dakike ta wahala akan se ya aureki don cikar burinki, ABDUL JALAL baze taba aurenki ba Ilham, tunda yace baya sonki baze sokiba, kuma kinsan daddyn sa yana goyon bayansa, nasan hanya dayace dake dazakibi ki aureshi hanyar sihiri kuma wannan hanyar bata bullewa" da sauri Ilham ta kalli Jalila tanaso tayi magana amma takasa,
"Karya kikeyi, Yaya Jalal yana sona kuma bani da wani mugun nufi akansa, ubanwa yagaya miki saboda wani dalili nakesonshi, munafuka duk masifarki wallahi haka zaki kyalemu, dan banga uban daya isa ya hanani auren Jalal ba"
"Eh kinyi mamaki ko? Ya akayi nasani, da bakinki kika fada, ba a gurin wani naji ba sannan.....
" A gidan ubanwa na taba gayamiki ina sonki meyasa ba kya ganewa, sa'anki neni, mahaukaciyar inace ke dakike tunanin zan aureki? Yau zaki tattara kibar gidan nan tunda bana ubanki bane, akanme zaki dage cewar nikikeso nace bana sonki bana sonki meye haka wai, mekike nema a gurina ne Ilham" Jalal ne yakewa Ilham magana cikin fada, da sauri daddy ya fito tareda Mummy, daddy ya karaso inda Jalal yake "haba Jalal ai duk abun be kai hakaba, koba komai kanwarkace, kayi hakuri"
"Daddy wace irin magana kakeyi hakane, seta bar gidan nan koni inbar muku gidan, akan me za a takurawa rayuwata, for what reason dad, ace kullum mahaifiyata batada buri se ganin bacin raina" Jalila rasa abun cewa tayi, ta kalli wannan ta kalli wannan,
"Haba Jalal ya ina matsayin mahaifiyarka zakace bana son cigabanka, Aurenka da Ilham alherine ni banga aibun Ilham ba, a tunanina komai ya wuce" wani mugun kallo Jalal yaiwa Mummy duk ya birkice idonsa yai jawur "Kikace komai yawuce, karki yaudari kanki mana, kodayake son zuciya baze barki kidinga ganin gaskiya ba, nayi dana sanin kasancewarki mahaifiyata, kullum bakida burin daya wuce gayyato matsala cikin rayuwar dan dakika haifa, haka sauran iyaye sukeyi" Jalila kasa jure abunda Jalal yake tayi , wanda hakan yasa ta mike ta fice daga palourn jikinta a sanyaye, tafito ta jingina da bango tai shiru tana tunani "meyake damun Jalal ne? Dole nasan dalilinsa na cin zarafin iyayensa musamman mahaifiyarsa, ina tausayawa Jalal ya mutu yana sabawa iyayensa, zanso inji dalilin hakan kozan iya temakamasa, wulakanta iyaye ba abune me sauki ba"
Ilham se kuka take, duk yadda daddy yaso ya shawo kan Jalal ya kasa, seda yai me isarsa sannan ya bude palourn ya fito a fusace, yana fitowa Jalila tana gurin a tsaye akan hanyar daze wuce, hannu yasa ya hankadeta gefe yai gaba abunsa ya nufi part dinsa, mamakine yacikata, kodayake ba abun mamaki bane kadan daga aikin giya. Jiki a sanyaye ta baro gidan, sedai me tana fitowa taga motar
Hannah a kofar gidan, ta fito tana ta kiran lambar Jalal amma yaki dagawa. Jalila a ranta tace "lallai Jalal kana cikin iftila'i" dayake duhun magariba yafara yi, Hannah bata gane wacece ba, dan haka tace "Dan Allah baiwar Allah naga kaman daga gidan kika fito Jalal na ciki ne?"
Karasawa Jalila tayi gabanta "kalli da kyau baki gane wacece bane?" se yanzu Hannah taganeta "dama kece?
" Eh nice, meyasa bakyajin kunyar zuwa neman Jalal ne? Mace da aji akasanta abunda kike zubarda mata kike" "Ke kome nakeyi beshafeki ba kingane bana son surutu, Jalal yana nan ne?"
"Eh Jalal yana nan, amma kaman yanda nagaya miki kwanaki yauma hakanne baze zoba, huwaila kike kowa, ni mamaki kike bani meyasa bakida kunya ne, me yayi miki haka kika uzzurawa rayuwarsa"
"Ke dakata, ba abunda yadameki, Ko agaban uban waye zan fada son Jalal nake, nan da kankanin lokaci ze aureni" murmushi Jalila tayi "to Ilham dinfa? Kokina tunanin zuba miki ido zatayi ki aureshi, naga kaman tafiki sonshi dan tafiki himma ina tunanin za'asa sa ranar aurensu" zare ido Hannah tayi "dagaske kike?" "nasankine dazan tsaya ina miki wasa"
"Ni Jalal zewa haka wallahi basu isaba dagashi har kanwar tasa, Nikadai zan aure Jalal in rayu dashi sena lalata komai, in bahakaba sena masa sharrin da nan duniya babu wanda ya isa ya fiddashi, nayi wannan alkawarin" "kaman ba yanzu kika gama cewa kina son aurensa ba, kin dade kina cutar da rayuwarsa, ranar birthday dinsa kun shirya yimasa wani abu, ni nasaka aka dauke shi daga gurin bayan kin bashi kwaya kin bugar dashi, a wannan lokacin nakara tabattar da bakinku daya da da wannan dan iskan, sannan kisani babu wani sharri dazakiyi masa yayi tasiri akansa Allah yana tareda shi, dan haka wannan ba soyayya bace, ba kyasonsa dan Allah, ku saurari yadda karshenku ze kasance " Jalila ta juya tai gaba, da sauri Hanna tabi bayan Jalila tana mata magana akan dan Allah ta tsaya, amma Jalila taimata banza tai wucewarta zuciyarta cike da tunani. Ba karamin mamaki Hannah tayiba, gaskiya Jalila tabata mamaki ya akayi haka, dama ita tasaka aka dauke Jalal, ita ta turasa wannan shirin da suka dade sunayi, to meye manufar Jalila akan Jalal.
Jalila kam Tana zuwa gida
ta tarar da Nana ta dawo daga gidan Yaya mairo, ta tarar dasu a palour Nana tana kuka, Maama tana rarrashinta, kaman ta wuce seta fasa ta tsaya "Nana lafiya kuwa"
"ke bana son gulma ina ruwanki, wuce kitafi inda zaki, uwar tsegumi kawai" ba Jalila ba hatta Nana seda taji babu dadi abunda Maama tayi.
Dakinsu ta wuce taje tai alwala tai sallar magariba, tafara tilawar al'qur'ani, wayarta se ringing takeyi amma bata dauka ba harseda ta idar da karatunta, tana duba wayar bakuwar lamba ce da akayi ta kiranta da ita ranan, dan haka ta ajiye tacigaba da sabgoginta, har bayan sallar isha'i Nana bata shigo dakin ba Jalila kuma bata nemeta ba, wayarta ce takuma daukar ringing, a fusace Jalila ta dauka "Wai ya hakane ankira ban daga ba kuma se kuma kira ake, haba inkuma ina wani uzurinne fa?"
"Tuba nake, adon gari, nakasa samun sukuni ne amin afuwa"
"waima wake magana?"
"Suleman ne" "waye kuma Sulaiman ni bansan wani suleiman ba" "yi hakuri, wanda kuka hadu shekaran jiya kika bashi lambarki" seda Jalila ta dan yamutsa fuska dan ita ta manta dashi,
"ohh nagane sannu yakake?" "lafiya amma ba lauba, nakira nakira baki daga ba, inata kewar muryar nan taki" "Hmm to ai yanzu gashi kaji" "Hakane nayi farinciki fatan kina lafiya" "eh lafiyata kalau" haka sukayi waya da Jalila kaman ammata dole, ita kunya ma yake bata da haushi inyayi wani abun tsoho dashi se wani tabara yake mata.
Nana ce ta shigo jikinta a sanyaye, Jalila bata kulata ba taje tazubo abincin dare tanaci, bayan tagama tai shirin bacci ta haye gado tana chatting dinta, Hanan tana online, suka fara hira kaman abun arziki, har Jalila take bata labarin Alhaji Kabiru, dakuma wannan dansandan, Hanan tabata shawarwari, Jalila tagaya mata abunda yafaru yau agidansu Jalal, Hanan ta fara kunna Jalila "queen gaskiya Jalal is destined to be in your life, dan haka ki kauda wata Ilham da Hannah gefe kisa kai dan kun dace sosai, ke kadaice zakiso shi tsakani da Allah ki temaki rayuwarsa"
"Ke bana son shirme Allah ya kiyaye meye abunso a gurinsa, meye abun birgewa a gurin mashayin giya"
"A'a adena zakewa dai, kar nan gaba azo a gigice akan sa ehee dan bazan bawa mutum shawara ba"
"Narasa meyasa kike likamin wannan sakaran, inada Yaya Jawwad ba abunda zanyi da wani Jalal"
"Ke dakata, Jawwad nawane kuma ni kadai, gara ki rungumi Jalal tun lokaci be kuremiki ba, Jawwad baze aureki ba nina gayamiki" rufe data Jalila tayi, dan hartaji wani bacin rai yana tasomata" Nana ta kalli Jalila tace
"Jalila bazaki tambayi meyasameni bako? Kina kallo ina cikin wani yanayi" tashi Jalila tayi takoma kusada Nana "Nana hawayen nan naki jinake kaman ni nake zubar dashi, kinji abunda Maama tace dazu, shiyasa ban takuramiki inji meyasaki kuka ba bansaniba kobe shafeniba"
"haba Jalila har akwai abunda ze sameni dabe shafekiba?" "to yanzu kiyi hakuri gayamin meya faru?" Nana ta share hawayenta sannan tace
"Jalila wai kiran da yaya mairo tayimin, waiso take ta hadani da Nura waiya aureni"
"Waye kuma Nura" "babban danta ne, wallahi Jalila inda abunda natsani na bude ido ingani be wuce wannan Jakinba" "Amma Nana meyasa?"
Wasu hawayen ne suka kuma zubowa Nana "Jalila dan dabane fa, mugun tantirine har prison yayi, ga shaye shaye na masifa, ba ilimin addini bokon ma secondary ya tsaya, wai dan zalunci shi takeso ta hadani aure dashi, wallahi akace sena aureshi sena kashe kaina, inkuwa aka kaini gidansa sena ksheshi na kashe kaina"
Da sauri Jalila ta rufemata baki tareda fadi "subhanallah, Nana karki kara fadin hakan, wannan maganar tayi tsauri, amma me Maama tace?" "cewa tayi inyi hakuri, zatasan matakin dazata dauka, nikam hakan beminba kawai ajanye wannan maganar, inbahakaba gara in bar gidan nan" "Nana nace kidena irin wannan zantukan mana, kiyi amfani da kwakwalwarki, kina tunanin Abba ze yaddane, baze yadda ba dan haka kiyi hakuri, ba abunda zesa ki aureshi Insha Allah mutumin kirki zaki aura, zan tayaki addu'a kinji My Nana kidena kuka, banaso" gyada kai Nana tayi sannan tace "Saboda tsabar son zuciya irin na matar nan waishi kuma Yaya Jawwad da Naja za'a hadasu, wallahi inshi ya yadda nibazan yadda da auren dan daba ba, gara in kashe tsinanne in huta"
Comments nakeso ba sticker ba, kokuma just thanks,
A kullum ina alfahari daku masoya wannan novel
Daga alkalamin Aysher cool
07063065680
_ABDUL JALAL (2020)_
_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)
PART
_PAGE
/62_

Seda gaban Jalila ya fadi, kirjinta ya buga da karfi, amma ta dake ta maze, ta lallaba Nana suka kwanta, amma bacci ya gagari Jalila, gaba daya abubuwa sun cunkushe mata ta rasa menene mafita, dan haka ta tashi taje tayo alwala ta tada salla.
Washegari da safe seda Jalila takusa sasu su makara sannan suka tafi makaranta, yauma sir hafiz yashiga ajinsu Jalila, har yayi lectures yagama hankalinsa yana kanta, ita kam ko a jikinta, abubuwan dasuka dameta kawai take lissafawa, na farko damuwar Jalal, ga abunda Hanna tace, Hanan ma ta dage akan son datakewa Jawwad tana lika mata Jalal, ga abunda Nana tagaya mata jiya da daddare, gaba daya zuciyarta a cunkushe take tanason sanin waye Alhaji Kabiru ta hanyar yarsa dake ajinsu wato saleema, kallo daya zakayi mata kasan tana cikin damuwa, sir hafiz yana monitoring din duk moves dinta sam attention dinta baya kansa, dan haka yace ta tashi tsaye, ba musu ta mike, ya dinga yimata tambayoyi amma taki kulashi tayi masa shiru, lamarin yarinyar nan ba karamin daure masa kai yake ba, daya dameta ma kawai seyaga idonta ya cika da kwalla, tana nema tafara kuka. Dan haka ya kyaleta yacigaba da lectures dinsa ba tareda yace ta zauna ba, yagama tsaf sannan yace ta biyoshi office, banza tayi masa, tanemi guri tai zamanta ta kifa kai, tarasa meyake mata dadi, hawaye tafarayi tanayi tana gogewa, zahra ta dafata tace "Kiyi hakuri kidena kuka, nikaina banajin dadin abunda lecturer din nan yake miki, nasan ba dadi amma dan Allah kidena kuka kinji" sam zahra batasan meye damuwar Jalila ba dan haka tabita a haka, zahra tace "bari inje in siyo miki ruwa kisha ki wanke fusakarki" Jalila ba tace komai ba, zahra tafita taje siyo ruwa, a hanyarta ta dawowa, Su Samira suka datseta, suka sha gabanta, samira ta kalleta sama da kasa sannan tace "A tunaninki tarayyarki da wannan dakikiyar yarinyar zesa in fasa bibiyarki ne, wallahi yazama dole ki amince da bukatata, komai kike bukata na more rayuwa zanbaki shi, amma muddin kika cigaba dabin yarinyar nan, ina tausaya miki abunda ze biyo baya, saboda rayuwar taki dakike takama da ita, ita zansa a tarwatsa yadda sekin wulakanta a idon duniya " a firgice Zahra ta kallesu, Saleema tace "Zahra dama ce a gareki kina ganin su zee da salma duk asirinsu a rufe sunata hutawa, keme yasa bazaki yadda ba, waike ta Allah ko, wallahi duk matakin data dauka akanki kekika jawa kanki, sannan yazama dole kiyi gaggawar rabuwa da wannaan dakikiyar yarinyar. Daga nan suka wuce suka batta a gurin, a hankali ta furta" Nashiga uku, Allah ka tsareni daga sharrin wadannan mugayen" jiki a sanyaye tafara motsa kafarta
"Ke! Ke!!" taji ana mata magana a baya, tsayawa tayi ta waigo, setaga sir Hafiz, "kigayawa kawarki kice mata bataji kiran danayi nata bane" jinjina kai kawai tayi, ta tafi aji ta kaiwa Jalila ruwa ta sha ta wanke, fuskarta Jalila ta kalleta, a sanyaye zahra tace "sir hafiz yace meyasa bakije kiran da yayi miki ba" jin maganar zahra a sanyaye yasa tace "lafiya naganki wani iri, me yafaru" zahra bata boye mata komai ba tagaya mata, "Jalila inaga dole mudena hulda tunda suka sakoni gaba, inacikin tashin hankali" ran Jalila ba karamin baci yayi, ta kalli zahra "har yanzu babu uwar datayi nakuda ta durkusa ta haifi wata shegiya dazata sa inyi wani abu ku indena wani abu dan ina tsoronta, dan haka nasiyi wannan rigimar koni kosu, musamman Saleema, bada ita zanyiba sa makyankyashinta zanyi" mamakine yacika zahra kaman ba Jalilan da take kuka ba yanzu abun tausayi amma yanzu itake masifa haka "Jalila meye kuma makyankyashi?" "ba ruwanki, kuma bazan dena hulda dakeba sedai kibar department din nan, in yaso ba tarwatsawa ba in sunga dama susakawa rayuwartaki bom, ba abunda ya shafeni bane tunda kedai bakida wayo bakusan yancinkiba, seki zauna wasu yan kwaya suna raina miki hankali saboda bukatarsu" tanagama fadin haka tatashi ta dau Jakarta tabar ajin, tabar zahra baki bude.
Office din sir hafiz ta tafi, tana zuwa su samira na fitowa, kallon Samira tayi ido cikin ido tace mata "Kiki yayi shiga hurumina, karki yadda kisanni a ainihin kalata" ta juya ta nufi office din, tayi knocking yace ta shiga, yana zaune yana breakfast yana shan tea, dan kuramata ido yayi ya dauke kai yacigaba da abunda yake, har kasa ta durkusa ta gaisheshi dan dagowa yayi ya amsa mata, bata jira izininsa ba ta haye kujerar dake fuskantarsa ta maze hada jujjuyaw
a, aransa yace "Ikon Allah wanna yarinyar ba dai mulkiba" seda yagama abunda yake yayinda still yanzuma tunani take tanayi tana kokarin maida kwallar data taru a idonta, ya dan dubeta yai nazarinta nawasu seconds sannaan yace "Wayabaki damar ki zauna?" bata kalleshiba tace "bana son tsaiwa dazu ma daka tsayar dani a
aji kafata ciwo take" "Kodayake bakiyi kakar wahala ba, amma Meyasa kike kokarin boye baiwar da Allah yayi miki, meyasa kika zabi kidinga dizga kanki agaban yan ajinku? Kika fi maida kai akan tunani kullum?" shiru ta danyi idonta taf hawaye tace "ai kai ka janyomin, nagaya maka kadena tambayata agaban yan aji amma kullum seka tambayeni danka wulakantani, ni bazan bada amsa agaban yan ajiba, bana son sa ido"
"Wayece miki dan in wulakantaki nake tambayarki?" "Zuciyatace tagayamin" murmushi yayi "tagayamiki ba dai dai ba, amma meyasa kike boye baiwar da Allah yayi miki, ga yawan tunani a class, you are too young ace kina tunani dayawa?"
"Akan me zan nuna ni watace? A hakanma wasu sun tsaneni a ajinmu nibansan menayi musu ba,"
"Suwaye suka tsaneki?"
"Samira da gangs dinta mana, kuma wallahi in basu fita sabgata ba senayu maganin yarinya "
Kallonta yayi "I like your confidence, amma kidena wannaan maganar, yarinyar nan tanada manya karki sa kanki a matsala kinada kwakwalwa me ban mamaki, ba ruwanki dasu kiyi karatunki kawai" Jalila a zuciyarta tai murmushi "tab aikuwa bazan bar gurin nan ba senaji Labari sosai akansu, bari inbi da mutumin nan a sannu"
Dan zumbura baki tayi "ni ina ruwana da wasu manyanta akan me zata takuramin, nima inada Allah kuma babana yana sona dan haka ba wanda zemin komai"
"No bahaka bane, yarinyar tasan manyan yan siyasa, gata fitinaniya har yan daba ne da ita karkije tasa a miki Illa" Zare ido Jalila tayi ta lura yanajin dadin hirar dasuke dan haka tace "to sir amma aka kyaleta a cikin school din nan haka kawar nan tata tafi tsanata taana cemin dakikiya fa,
They are terrorist in har mace za'ace tanada yan daba tazama hatsari a society" "Hakane amma ya zamuyi, hukumar makaranta bata dau mataki ba ance babu kwakwkwarar hujjar data tabattar dahakan kinga se hakuri, dan haka ba ruwanki dasu kiyi karatunki kawai kidena wannan tunanin"
"To nagode sosai Insha Allah zan kiyaye, amma tunani yazamemin dole, anyway am very grateful with your advice nagode, Allah ya jikan mahaifa" murmushi yayi yace "Nima nagode Allah ya wuce mana gaba" ta dakko Jakarta ta fito.
Jalal jiyake kaman inyayi kykyawan yunkuri zuciyarsa zata fasa kirjinsa dan bakinciki da bacin rai, daren ranar kasa bacci yayi, yasha giyar amma batayi masa komai ba, haka Jawwad yazo yasameshi da safe, juyin duniya yaki kula Jawwad balle yagaya masa meyake damunsa, haka Jawwad ya hakura ya kyaleshi ya tafi makaranta, yana nan zaune a palour yaji bacci ya sace shi, kira'ar Karatun Jalila ya dingaji a mafarki, wadda yagani a gidan telabijin shekarun baya koda ya farka daga baccin se yaji babu damuwar a taredashi, yai ajiyar zuciya yai shiru yana tunani wayarsa ce take ringing, kallon wayar yayi, sunan Hannah yagani, tsaki yayi yaki daukar wayar.
Ilham hankalinta yagama tashi jin abunda Jalal yace jiya, kwana tayi batayi bacci ba, aiko sama da kasa zata hade bazata bar gidan nanba ba tareda ta samu abunda take soba, dan haka da sassafe ta tafi dakin Mummy,
Kuka sosai tasakawa Mummy, "Mummy kingani ko, baya sona kinga wulakancin dayayumin, betabamin goriba se jiya dan kawai ance asa ranar aurenmu nikam nashiga uku Mummy, wallahi inban aureshi ba mutuwa zanyi"
"Ilham meye hakane, kibi komai a sannu mana, kiyi hakuri bazaki bar gidan nan ba shima bacin raine yasashi fadin abunda yafada amma kiyi hakuri zan shawo kan matsalar"
"Mummy nan da yaushe to? Nifa gaskiya na damu, bantaba tunanin Yaya Jalal zemin haka ba, anya kuwa ze yadda da aurena"?
"Nace kiyi hakuri nasan abunda zanyi, aure keda Jalal ba fashi, kigoge hawayenki kidena kukan haka ya isa, tashi muje palour"
Ilham ta goge hawayenta suka fito itada Mummy.
Hannah tarasa meyakemata dadi, dagaske Jalal za'asamasa ranar aure da Ilham, aikuwa da Ilham ta tafka mafi girman kuskure a ratuwarta, to amma Jalila fa meye nata manufar, amma yakamata in gayawa Jeje wadda ta rusa masa shiri, amma yakamata inyi magana da Wannan yarinyar yana da kyau insan meye manufarta, wayarta ta dauka tayiwa Jalal message
Jalal ya shiga yai wanka, message ne ya shigo wayarsa, ya dauka ya duba
"Wallahi Jalal inbaka amince da aurena ba, narantse maka sena nuna maka ni cikakkiyar yar bariki ce, wallahi sena maka sharrin da harka mutu ba wanda ze yadda bakai kayi ba, ka rubuta ka ajiye gara tun wuri kanemamana mafita karka kuskura kayi ganganci auren wata, dan wallahi bakai ba kwanciyar hankali
"Hmm bakida hankali" Jalal ya furta a hankali, yafito ya tafi cikin gida dan yunwa yakeji, a palour yaga Mummy da Ilham, be kulasu ba yaje ya dakko abunda ze dakko ya nufi part din daddy, Ilham ta zata yanzuma zemata masifar yace tabar gidan amma taga be kulata ba, yaje part din daddy ya zauna yaci Abincinsa suka sha hira, a haka daddy yaita masa nasiha akan hakuri dakuma yadena kyamar Ilham, se Jalal yaji kaman yai masifa danshi baya son adinga dangantashi da Ilham wai ya aureta, se ya tuno abunda Jalila tagaya masa akan baya yiwa mahaifinsa biyayya, haka yayi shiru daddy yaitai masa nasiha, Jalal yana gama cin Abincin sa ya kalli daddy "daddy kaga naji nadena, yanzu inason in dan fita ne"
Daddy yace "ba dai kasaon fadan danake maka Seka dawo Allah ya kiyaye" "Ameen" ya tashi yabarwa daddy kwanukan Abincin a palour, Ilham tanata fargaba da Jalal yafito amma taga still be kulata ba ya fice daga palour, dakinta ta koma ta dauki wayarta takira yaseera, bugu biyu ta dauka
"Hello yaseera kinajina?"
"ina jinki Ilham lafiya naji muryarki a haka"
"Yaseera ina cikin matsala" "matsalar me kuma?"
Nana Ilham ta gayamata dukkan abunda yafaru jiya akan ance za'ayi maganr aurensu da Jalal.
"tabdijan lallai Ilham akwai katuwar matsala, gaskiya yayan nannaki akwai taurin kai, dole musake shiri amma kunyi waya da ummane?"
"A'a yaseera amma zanje anjima, wallahi banaso ingaya mata ne hankalinta ya tashi banaso ta karaya akan bazan iya cika mata burinta ba, gani nake bazam gayamata ba, gara mubari ranar Sunday muje gurin malam"
"to shikenan yadda kika gani, amma abun da damuwa wallahi, ace duk wani kissa taki tasiri akansa sekace ba namiji ba, anya ba mata maza bane ba
Ace mutum zuciya kaman karfe"
"Hmm kema dai kyafada yaseera, bari ranar ki shirya da wuri muje"
"to shikenan Allah ya kaimu" "Ameen yaseera nagode sosai".
Y'an kwanakin nan, Jalila ta dan sakewa Sulaiman suna gaisawa saboda tasamu damar daze temakamata, amma sam taki yadda yazo gidansu ko susake haduwa, dama ba koyaushe yake zama a kano ba se lokaci2 yake zuwa, aikinsa yafi a Lagos, anan yake gayamata shi kakakin rundanar yansanda ne na jihar Lagos, amma iyalalinsa suna kano, suna hira sosai da Jalila yana bata labarin nasarori da hatsarin ayyukansu, amma daya dakko batun daya shafi soyayya seta kashe wayarta, hakama Alhaji Kabiru Jalila ta sakar masa sosai gani yake kaman sonshi takeyi, a nan takara tabattar da Saleema yarsace ta cikinsa itada faruk.
Yanzuma waya suke da Alhaji Kabiru
"sweet heart wai yaushe zaki farantawa masoyin kine, kinki yadda mu hadu"
"tab waikai bakajin kunyane yarka fa daka nunamin hotonta zata girmeni kawai sesuga ka auri yar yarinya?"
"to meye a ciki gidanki daban zan ware miki, ita Saleema tanacan karatunta tanagama karatu zan aurar da ita, Faruk yana ABU, sukenan yarannawa fa, kuma basuda damuwa da aurena, please my sweet kibari mu hadu mana, yakamata kinunamin soyayya ina Sonki fa" shi sam besan Jalila tasan Saleema department dinsu dayaba, Jalila aranta tace me mutumin nan yake nufine? Amma ta maze tace
"yaushe zakazo ku gaisa da Abba na?"
"Ai wannan ba wani abun damuwa bane, kibari mugama fahimtar juna mana kinki bari inzo gidanku balle mudan dinga fita chilling din nan, bakya wani nunamin soyayya"
"Banda wannan danake maka wacce kakeso kuma?"
"yakamata ace kinkawomin ziyara gidana mu gaisa mana" "haka kurum matarka ta zaneni" "wayace miki nan zakije, gidana danake ganin special guest dina zakizo" murmushi Jalila tayi "hmmm special guest, ashe nima special ce" "sosai makuwa please my sweet yaushe zakizo?"
"karka damu kabari in mungama exams zanzo, ba dai zuwa kawai zanyi shize tabattar maka da inasonkaba karka damu"
"Kai amma naji dadi sweet, Allah ya kaimu kugama"
"Ameen se anjima" koda sukayi sallama Jalila ta kalli wayar ta takunna recording gaba daya wayar datakeyi tana recording dinta, tana saving a Gmail dinta "Azzalumi kawai, shiyasa abunda kakeyine yasa yarka take can take watsewa a makaranta bakasaniba Jaki kawai, zakuga abunda zan muku kaida yartaka sena kunyataka agabanta in nuna mata nafita iya rashin mutunci".
Sosai Zahra ke gudun cigaba da mu'amala da Jalila sedai ta waya saboda kashedin dasu sameera sukayimata, gashi suncigaba da uzzuramata akan lallai ta amince da bukatar sameera, tarasa inda zatasa kanta abun ya isheta, dan haka ta samu Jalila tagayamata halin da take ciki, "Zahra yazama dole ki amince da batun su Sameera"
"haba Jalila so kike rayuwata ta tarwatse ne yazakice haka?"
"basonake rayuwarki ta tarwatse bane, taimakonki zanyi"
"to tayaya Jalila, kinsani nasani dukkansu ba mutanen arziki bane da sharri suke nufina"
"Nasani ai tarko zamuyi musu nasan yadda zanyi dasu" Saleema ce tazo har inda su Jalila ke zaune ta kalli zahra "wato zahra bakiji kashedin da Sameera ta miki bako? Har yanzu kina biyewa wannan yarinyar ko"
"Ke wai dakata, suwaye dinta ku, ana dolene ko angaya muku kowa sakaraine dabba irinku" "Ke shiga hankalinki, bana son shishshigi muna daf dasawa amana maganinki yadda ko hanya muka hada sekin kauce"
"Allah ko? Dama waze hada hanya da kazamai jakuna marasa tsoron Allah, aini base kunsa anyi maganina ba, nizanyi maganinku daga ke har kawartaki ba sameera ba ko langa ce kukiyayeni musamman ke" ta nuna Saleema,
"Asararu ko kunya bakwaji kaf school din nan kowa yasan mekukeyi" kafin Saleema tayi magana Jalila ta dau jakarta tayi gaba tabarsu Zahra a gurin.
Kwanci tashi ba wuya a gurin Allah su Jalila suka fara exams din first semester, kowa yana abunda yaga ze fisheshi, wasu sun dukufa karatu, wasu ko sharholiyarsu kawai sukeyi, itakam Jalila ta maida kaine akan lissafin yadda zata bullowa al'amuran ta dasuka dameta,
Yau karfe tara zasu shiga exams, ita Nana sun gama tasu Jarrabawar dan hutu ma sukeyi, gashi Manu direba baya nan Maama ta aikeshi, da karambani Jalila tasaka Manu yakoya mata mota, da mukulli na nan da dakanta zata tafi yau, dan haka ta yanke shawarar tafiya ta hau napep,
Tana fitowa daga gidataga Daddy da dansa Jalal a jikin motar Jalal, durkusawa Jalila tayi "daddy ina kwana?" "Lafiya kalau Jalila makaranta za'atafi ina direban naku?"
"daddy baya nan, napep zanje in hau karfe tara zamu shiga exams"
"kai Masha Allah, Allah yabada sa'a, takwarar Jalal, Allah ya temaka" Jalal ya tsani yaji ance takwarar nan tasa, yawani hade rai, "Ameen daddy nagode sosai Allah yasaka da alkhairi bari in tafi kar in makara" "A'a tsaya, dama Jalal fita zeyi, Jalal kuje seka ajiyeta a makarantar tunda duk hanyace" kallon daddy yayi, ya kalli Jalila ya dauke kansa
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool
What's app only 07063065680
_ABDUL JALAL (2020)_
_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)
PART
_PAGE
/63_

Ita kanta Jalila setaji kaman tace A'a amma taji nauyin yin hakan, daddy yakuma cewa "Jalal maza kunna motar ku tafi karta makara" Jalal kaman yace bazashi ba amma yasan yana fadan hakan tasamu abunyi, bece komai ba ya bude motar ya kunna, Jalila ta tafi ta bude gaba ta shiga, "yawwa Allah yayi muku albarka sekun dawo" Jalila ce kawai tace Ameen, Jalal ya kunna motar yajata da gudun tsiya, yadda yake gudu yasa Jalila ta kalleshi "ni gaskiya in wannan ganganci za'ayi da rayuwata ka saukeni, akanme inkasaba kasada da rayuwarka to badaniba" banza yamata yacigaba da tukinsa, yadda yake ratsa tsakanin manyan motoci yasata runtse ido tana ambaton Allah, kallo daya yayi mata ya dauke kansa, "dan Allah ka tafi a hankali koka tsaya in sauka" jitayi an tsaya hakan yasata bude idonta, gani tayi yayi parking, yasa hannu ya yana dakko taba yana kokarin kunnawa, "kutmelesi meye haka ne?" banza yayi mata ya kunna tabarsa, sakin hayakin yayi fuuu a cikin motar, juyawa tayi zata bude kofar motar amma taji a kulle gam, yasa lock ta kalli agogon hannunta ta makara sosai ana daf da shiga exams,
"wai meye haka dan Allah nika budeni in tafi zan makara, ga warin hayaki ya isheni" Shiru yakumayi ya kwanta sosai a jikin kujerar yana busa hayakinsa, ji tayi kaman ta wanka masa mari, yanajinta amma yayi banza da ita kamar wani itace, dafe kanta tayi, wayarsa tafara vibration ya dauka yaduba message din Hanna ne danhaka ya ajiye wayar tareda fadin "wasu matan are just useless" Jalila ta dago ta kalleshi, "ai Useless din ba iya mata bane hada maza, dan gara mata da wasu mazan dabasa jin magana" wani dan guntun murmushi yayi, wanda shikadai yasan yayi shi, gani tayi ya shanye sigari kusan uku yakuma kunna wata, hannu tasa ta fizgeta ta jefa waje "wallahi baka isaba, akanme ina zaune zaka dinga shan taba ka cikani da hayaki salon inje aji a dauka ninasha tabar, ka budeni in tafi in yaso kaima kazama tabar, batareda ya kalleta ba yace
" warin taba ai kin dade kinayinsa, ba iya taba ba harda na giyama kinayi, kece baki saniba amma nakusa dake sun san hakan" kallonsa tayi alamar bata fahimta ba
"ya za'ayi nida bana shaye2 indinga warin giya, Allah ya kiyaye" "bakiyi addu'ar a inda ya daceba, dan kinriga kin makara, kuma ba lallai sekina sha zakidinga warinsu ba" hannunta ya kamo, ya nunamata "a jininki abun yake, akwai jinin yan giya a jikinki dan haka sekidena cika baki" ita Jalila sam batagane inda maganganunsa suka dosa ba, wayartace taketa ringing tasa hannu ta dakkota Alhaji Kabiru ne akan screen din wayarta, screen din Jalal ya tsurawa ido yai shiru kaman me nazari, ya kalleta ya kalli wayar, kashe wayar tayi ta mayar cikin jakarta, kallon tuhuma yayi mata na wani dan lokaci, sannan ya dauke kansa, "hmm Jawwad za aci amana, hakan yafi ai, dan baki dace dashiba gara ya auri mutuniyar kirki, dan duk jarabarki bazaki auri dan uwana ba, Jawwad da salihar mace ya dace ba irinkiba" kallonsa tayi sannaan tace "nice ma kai, aigarani da kai, kaima kasan hakan kuma duk bakin cikinka sedai kayi, dan nafi karfin ace za'a kyamaceni a matsayin mata, dan nasan nafi wannan doluwar kanwartaka"
"Hmmm meye kuma nasakota a wannaan zancen? "
"kaika sani, nikawai ka budemin in fita" banza yayi mata yacigaba abunda yake, wasa2 kusan mintunansu talatin a tsaye Jalal yaki tafiya, hannu takuma sawa zata fizge tabar bakinsa cikin zafin nama ya hada da hannunta ya rike, ya juyo yana kallonta, wani mugun kwarjini yayi mata ta kasa magana ta sunkuyar da kanta kasa, "karki kuskura, bar ganin na kyaleki dazu" sakar mata hannu yayi, yacigaba da abunda yake, karfe tara hada rabi, amma Jalal yaki kaita makaranta, tarasa mezatayi kawai tafara kuka, seda Jalal yaga dama sannan yaja motar yacigaba da tafiya, wannan karon kuma a hankali yake tafiya kaman bayaso, hannu yasa ya kunna radio motar inda karatun Al qur'ani yake tashi, Jalila aranta tace "Tab dama yanajin karatun qur'ani" bata gama tunanin ba taji Jalal yanabin karatun a hankali, juyowa tayi tana kallonsa, danta tabattar anya kuwa shine yakeyi, sosai yakebin karatun cikin suratul Ibrahim, dan tabe baki tayi tana jinjina lamarin dama Jalal ya iya karatu haka, amma koda wasa bata tunanin ko bismillah ta tabajin yayi, se masifa da wake2, tana cikin tunanin taji yayi parking, "inkin gama kallon nawa seki fita"
" Baka da abunda zan tsaya ina kallo, ko Meye amfanin zuwanama, tunda dai na makara nasan ba lallai inyi jarrabawar ba, kaida Allah in abunda kayimin dai2 ne, kodayake baka san darajar jarabbawa ba shiyasa kamin haka kuma Insha Allah se" "Ke!!!!" ya dakamata tsawar data tilasta mata yin shiru
"wallahi duk randa bakinki yai kuskuren yimin muguwar Addu'a akanki zata kare, gobe in ankuma cewa kibi namiji mara daraja irina sekikuma biyoni, fitarmin daga mota, inbahakaba na kunna motar nan senaje gida zan tsaya, kyasan yadda zakiyi" bude motar tayi tanata kunkuni gashi ta hade rai sosai, ta fice tabar motar a bude tai tafiyarta, ankai ruwa rana sosai kafin abar Jalila tashiga hall din exams saboda ta makara, Jalila ji take kaman tana komawa gida takama Jalal ta shakeshi seya suma, haka tai exams din ta fito cike da takaici,
Tasamu guri ta zauna a karkashin wata bishiya, ta zauna babu dadewa Zahra ma tazo gurin "Jalila ya akayi kika makara haka yau?" dan tsaki Jalila tayi "kedai bari, wani ne yajamin wallahi, kuma ze gauraya dani" "hmm Jalila kenan me jama'a, Amma ke sir Hafiz fa yace ince miki kije, nifa nakasa gane meke shirin faruwa tsakanin ku" Jalila ta kalleta ta dauke "ki goge zuciyarki tsaf kidena bari tana kawomiki wani tunani" zahrah ta jinjina kai "ke ba wannan ba Jalila, ina mafita anawa lamarin? Ina cikin damuwa wallahi"
"Nasani Zahrah, amma abubuwan dasuke kaina dayawa ga wannan jarrabawar ga sauran abubuwa"
"to nidai kitemaka Jalila, karsuyi nasara akaina"
"Ai yazama dole in temaka miki, sabida indai nayi nasara kikayi yadda nace to nikeda riba, zangaya miki yadda zamuyi, amma banason gaddama da taurin kai, duk abunda nace kiyi, bazan bari kiyi abunda zaki cutu ba"
"to shikenan inajinki" Jalila ta gyara zama "zaki Amince da bukatar su Sameera" zaro ido Zahra tayi "Amma meyasa?"
Nan Jalila ta tsarawa zahra yadda abun ze kasance, zahra ta yadda da abunda Jalila tagaya mata.
Zahra ta tashi ta dau wayarta zata tafi, Jalila ta dakatar da ita, ta dakko wayarta tasaka ta a tsakanin litattafan Zahrah daga sama, sannan ta kalli zahra" harkije ki dawo karki sake ki tabamin waya, jeki dawo ina nan ina jiranki"zahrah ta gyada
kai ta tafi, inda tasan zata samu su Sameera, tai sa'a kuwa suna gurin, tana zuwa tasamu guri ta zauna a kujerar opposite din su Sameera ta kalli Sameera tace "Sameera gurinki nazo" Sameera tamata wani mugun kallo sannan tace "fatan kinzo ki sanar dani kin Amince da bukata tane?" "A'a zuwa nayi in rokeki alfarma dan Allah dan annabi kirabu dani kiyi hakuri wallahi iyayena zasu shiga damuwa insuka gane gurbatacciyar hanyar dana fada" Saleema ce ta katseta "Ke saurar bama son shirme , kekinfiso aita nanata magana ko? To bari kiji bata sauya zaniba, koki yadda kokarki yadda bazaki kubucemana ba sannan sekinso iyayenki zasu san abunda kikeyi, abunda kezaki amfana kudi fa zaki dinga samu" Sameera ta dagawa Saleema hannu alamar tayi shiru, ta kalli Zahra "idan baki amince da bukata ta ba, wallahi kartin yan daba zansaka suyi miki fyade" A razane Zahra ta kalli Sameera "yes and i mean it, fyade na wulakanci na tozartawa kuma duk garin nan babu wanda ya isa yayi wani abu, inada yan daban dabakowa ke iya hayarsu ba, sannan inada manyan dasuka tsaya min, babu wanda ze gane ninasaka akayi miki haka balle adau mataki, bakida gatan da za'a iya kwato miki hakkin ki, kinga tarwatsewar rayuwa tagama, karatu ya kare se zaman gida jiran ajali danko waje baki isa ki fitoba saboda gudun kyamar da mutane zasuyi miki" da kyar zahra ta hadiye mugun yawu "shikenan dan Allah kar abun ya kai haka na yadda, na amince amma bana son mutane su gane" Saleema ta kyalkyale da dariya, "ashe bari ba shegiya bace yarinya da wata garan gara wata" Murmushi Sameera tayi, "kin temaki kanki" zahra ta share hawayenta "A ina zamu hadu?" nan Sameera taimata kwatancen wani gida, zahra tace "zanzo Insha Allah, sannan kibani lambarki incase ko zan bata" ba tunanin komai Sameera tabawa Zahrah lambarta, sannan ta karbi ta Saleema ma" har zahra ta mike zata tafi ta dawo ta zauna tace
"Amma dan Allah kujawa yar seat dina kunne, nayi2 tadena shiga harkata taki" Saleema tace "banni da ita zanyi maganinta" zahra ta jinjina kai ta wuce yayinda sukuma suka kyalkyale da dariya, zahra takoma inda tabar Jalila, tana zuwa tana niyyar labartawa Jalila abunda yafaru, Jalila tasa hannu ta zare wayarta, sannan ta kalli zahra "shikenan semunyi waya ina sauri zan koma gida" "Amma baki tsaya nagaya miki yadda mukayi dasu ba" "karki damu mu hade ta what's app" cikin mamaki Zahrah ta kalli Jalila "to amma meye amfanin.....
" Shhhhh semun hade "Jalila tayi gaba abunta.
Tana zuwa gida yaya Jawwad yana tsaye shida Abba, karasawa gurinsu tayi" Abba yana ganka a gida iyanzu? "yan makaranta ya jarrabwa" "Alhamdilillah Abba harka dawone?"
"A'a tafiya ce takamani, zanje Lagos" dan hade rai Jalila tayi "Abba da tafiya zakayi ba sallama" "to ai gashi munyi sallamar" Jawwad yace "Abba muje karka makara, wannan babyn taka bazata bari ka tafi ba"
"Nima zan biku Abba" Jawwad yace karatun fa? Naga kuna exams "
" Eh ai bakomai dan Allah ni zan biku" Jawwad yace "rigimammiya yanzufa kika dawo baki gajiba" "bangajiba Allah" Abba yai murmushi "taho mutafi shalelena, ai rakiya zakiyi min" da murnarta ta hau motar suka tafi raka Abba airport, suna tafe suna hira itakuma ta dakko wayarta tasaka earpiece tana kallon video, dazu wayarta data saka a agaban jakar zahra video ta saita ta kashe flash din wayar, duk wani magana dasukayi yayi recording, wanda ita kanta zahra bata Sani ba, aciki Jalila taji kwatancen gidan da akayiwa zahrah a dan bare, ita Jalila bata san ma inane dan bare a kanoba, hiding video din tayi a wani app ta ajiye wayar, suka raka Abba airport, seda Jawwad yabiya ya saimata ice-cream da tarkacen chocolate suna tafe suna hira har sukazo gida. Suna zuwa suka tarar da Maama a harabar gidan, kallon tuhuma takeyiwa Jalila da Jawwad "daga ina kuke?" Jawwad yace "dama Tafiyace takama Abba zeje Lagos kuma bakyanan shine muka rakashi airport" "in kayi salla kazo ina son ganinka" "to Maama insha Allah zanzo" Maama ta juya takoma cikin gida, Jawwad yajuya ya kulle mota, yaga Jalila a tsaye abayansa bata tafiba "ya dai?" "bangaji da ganinka bane" murmushi yayi mata "Babyna kenan, aini nakine zakita kallona sekin gaji" "bazan taba gajiya da kallonka ba, jekayi salla kazo kiran Maama" "to shikenan see u later" daga nan yafita ita kuma ta shige gida, a cikin gida bataga Nana a dakinsu ba, san haka tashiga tayi wanka tai salla. Tana ninke sallayar taji wayarta na ringing Alhaji Kabiru ne wani uban tsaki taja
Ta daga wayar suka gaisa, haka ta dake ta boye damuwarta suka sha hira kamar gaske, Alhaji Kabiru ya matsa matuka akan se Jalila taje gidansa, taita lallabashi tana bashi hakuri daga baya ta kashe wayarta, fiowa tayi palour domin taje kitchen tasamu Abinda zataci, gani tayi anyi bakuwa a palour da alama gurin Maama tazo, suka gaisa da Jalila tace "bari inje in kira miki ita inaga tana daki" Jalila ta tafi dakin Maama danyimata magana Jalila ta jiyo kukan Nana tana cewa "Wallahi Maama gara in mutu da in auri Nura, wallahi yaya mairo kozata kasheni bazan aureshi ba" "nima ban goyi bayan hakanba, bazaki Auri Nura ba, amma yazama dole Jawwad ya auri Naja, intaga Jawwad ya auri Naja zata hakura inyaso kesekice ba kya sonsa" "Maama saboda me shima yayan ze auri Naja yakamata ayi masa adalci abarshi ya zabi wadda yakeso" "ke rufamin baki, dole ya auri Naja saboda bazan bari ya auri wannan yarinyar ba, indai ina raye baze auri Jalila ba saboda bana kaunar uwatta itama bana sonta dana baze auri yar Arniyaba karuwa" Jalila ji tayi kaman ansoka mata mashi a zuciyarta, tura kofar dakin tayi kaman bataji komaiba tace "Maama kinada bakuwa" hade rai Maama tayi "to naji jeki ina magana da yata" juyawa Jalila tayi ta fice tafasa cin Abincin, tafasar da zuciyarta take tasa takasa komai, ga hawayen yaki zubowa balle taji sanyi aranta, a hankali taketa karanto addu'oi domin zuciyarta tayi sanyi, gani tayi inta cigaba da zama bacin raine ze dameta gara ta fita ta rage wasu abubuwan dan haka ta dau hijabinta tasaka ta dau nikab da Jakarta ta fito palour, Maama tana gaisawa da bakuwarta "Maama dan Allah zan dan fita bazan dade ba zanje siyo kayan cake" "sekin dawo" shine kawai abunda Maama tace mata, tana fitowa harabar gidan Manu ya taso "A'a uwadakina ina zuwa haka daga dawowarki yamma tayi sosai" "Manu key zakabani na mota zanfita" "Ahh ai yayi wuri kifara tuki da kanki bakigama kwarewa ba kinsan tuki a kano se kwararren direba" "karka damu ba nisa zanyiba" Manu direba yabata key din mota, ta fita sannu a hankali take tukin da tambaya hartaje unguwar danbare inda su Saleema suka kwatantawa zahra sukace acan zasu hadu, abakin layin tayi parking ta fito sanye da nikab ta shiga layin, layin shiru ba mutane sosai, har kofar gidan taje ta tsaya daga baya, tana nan tsaye sega wata mata tazo wucewa, Jalila ta tare matar suka gaisa sannan Jalila tace "baiwar Allah dan Allah tambaya nake?" "ina jinki Allah yasa nasani"
"Dan Allah ke yar anguwar nance" "meyasa kika tambayeni?" Jalila tace "kinga ba cutar dake zanba wasu yan tambayoyi kawai zanyi miki" matar tace "ina jinki"
"dan Allah waye me wancan gidan" Jalila ta nuno mata gidan "hmm wanna gidan da kike gani wai yan makaranta ne a ciki, kuma bawani yan makaranta taron yan iskane maza da mata bawanda basa zuwa gidan, ke kawaima gidan karuwai ne da yan shaye2 " "Amma kuke zaune dasu a anguwar ina hukuma" "wace hukuma aiko ankamasu se an sakosu saboda ita ainihin me gidan wata yarinya ce, tanada manya a sama ba wanda ya isa yayi mata komai samfirin yan mata samari da yan daba babu wanda babu, har wasu manyan mutanen ma suna zuwa nan"
"Nagode sosai yar uwa, da amsamin tambayoyina" matar tace "bakomai amma fa koda wasa karki sake kice nina gayamiki danba ruwana" "karki damu babu mejin wannan zancen". Daga nan Jalila tayi godiya ta nufo gida, anata kiraye kirayen sallar magariba, tana komawa gida ta nufi cikin gida
"wallahi Jawwad da raina bazaka auri yar arna ba, ko ka auri Naja kokasamu wata ka aura amma ba wannan yarinyar ba, Naana dai zanyi yadda zanyi bazata auri nuraba amma kai kam sedai kayi hakuri bazaka aureta ba wallahi"
"Maama dan girman Allah kiyi hakuri Jalila batayi miki laifin komai ba, wallahi Maama ina sonta dan Allah karki rabani da ita, ina sonta dan Allah wallahi bazan iya auren Naja ba"
"Au har ina fada kana fada Jawwad, nagama yanke hukunci, sedai ka mutu dan bana kaunarka da yarinyar nan baze yuwu jikokina su fito daga tsatson arna ba, wannan fitsararriyar yarinya mara tarbiyya to baka isaba ni na haifeka dan haka na isa da kai, bazaka aureta ba, tun kuna kanan akan uwatta ba irin wulakancin da ban fuskanta ba, ubanku yayi min shi Aliyun yayi min rashin mutunci akan uwatta dama shiba mutunci yacika ba, dan halinsa ta dakko, ga kakarku kowa ya hademin kai Allah ka dai yasan me tayi ta shiga ta fita ta rabani da dangin mahaifinku, suka tsaneni se yanzu kakuma jawomin jaraba baze yuwuba, zamanta a gidan nan ma ba yadda zanyi ne, amma bana kaunar ganinta kusada ku" sunkuyar da kai Jawwad yayi ya dafe kansa da karfi Jalila ta bude kofar palourn gaba daya suka juyo suna kallonta
Daga Alkalamin
Aysher cool
I don't want stickers or just thanks, comments nakeso, dan shike bani karfin gwiwa, ina Alfahari daku
ABDUL JALAL NOVEL FANS GROUP
_ABDUL JALAL (2020)_
_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)
PART
_PAGE
64_

Kallo daya tayi musu ta dauke kanta ta wuce cikin dakinsu, itakanta Maama seda tasha jinin jikinta dan gani take kaman Jalila taji abunda tace, tashi Jawwad yayi ya fice, yayinda Nana da sauri itama ta mike da nufin bin bayan Jalila amma Maama ta hanata, "Ina zaki? Karki sake Kibi ta mayya" haka Nana ta hakura tafasa bin Jalila, Jalila tana shiga dakin tai jifa da jakarta da hijabinta akan gado ta zauna ta fashe da kuka me tsuma zuciya, dama tsanar da Maama take mata harta kai taci mutuncin mahaifinta haka shida baya doron kasar tsawon shekaru, ga kazafi datakeyi wa uwata, menayiwa wannan matar hakane meyasa ta tsaneni, banda albarkacin Abba dasu Nana da matar nan itada zuri'arta suka ganni se sun canza hanya, "zamana a gidan nan baze yuwu ba, bazan cigaba da jure cin zarafin iyayena ba musamman uwata ba dan kawai tubabbiya ce gara inshiga duniya, to amma inna tafi Jalal fa? Tabdijan wallahi matar nan tahana Jawwad aurena bata isa ya auri wata Naja ba, in ita Maaman bata san wacece Najaba to nina sani, Jawwad kuma dan uwana ne, intace baze aureniba baze auri Naja ba wallahi, bazan zauna a kasheni da bakin ciki a biyeba, ta karkashin kasa zan fara ramawa nagaji" "Enough!!!!" Jalila tafada da karfi idonta duk hawaye, guri ta nema ta kwanta hawaye na cigaba da bin gefen idonta to Jalal dinme ma? Nagaji tafiya zanyi sena bar gidan nan wallahi nagaji da wannan abun da akemin, hijab dinta tasaka ta mike. Nasihar ummi ta dinga tunowa wanda take yawan yi mata akan hakuri da rayuwa dakuma karbar kaddara, komawa tayi ta zauna ta fashe da kuka me ban tausayi.
Jiki a sanyaye Jawwad yayi sallar magariba, gaba daya yarasa abunda yake masa dadi, Jalal ne ya shigo dakin da sallama, amma sam Jawwad bejiba hankalinsa baya jikinsa, dafa shi Jalal yayi cikin damuwa yace "Jawwad lafiya kuwa? Meyake damunka kake tunani haka?" Ajiyar zuciya Jawwad yayi, ya danyi shiru na wani lokaci sannan yace "Jalal ina cikin damuwa, narasa meyakamata inyi" "gayamin meya farune?"
Nan Jawwad yagaya masa komai sanna ya dora da cewa "Jalal babban damuwana shine cin zarafin da Maama tayiwa iyayen Jalila ina kyautata zaton Jalila taji abunda Maama tace, amma ban tabbatar ba, data shigo ba wanda ta kula a cikinmu, wallahi bana zaton zan iya auren Naja bazan iyaba wallahi"
Shiruu Jalal yayi, "Jawwad a duk lokacin da aka ci zarafin Ummi, har cikin zuciyata nakeji, raina yana baci, bana manta Alkhairi Jawwad, idan har a matsayinmu na hausawa zamu cugaba da aibata wanda suka karbi Addinin musulinci daga baya to tabbas wanda ba musulmi ba zasu dinga kyamatarmu da addininmu, Jawwad kayi hakuri, amma mahaifiyarka da yan uwanta basa kyautatawa, dukda ina gefe ina fadar rashin kunyar yarinyar nan bazan mata sharri ba tanada matukar biyayya wadda wanda dayawa aka haifa a musulincin basuda ita, kuma itama ai a musulinci aka haifeta, Ummi mace ce me karamci da ilimi riko da Addininta yasa ta baro iyayenta gidan jin dadi dau shekaru ba tareda ta waiwayesu ba, soyayyar datakewa mijinta da yan uwansa ce tasa nima naci Albarkacinku, Jawwad mahaifiyarka bata kyauta ba, kuma zigata akeyi amma kasani gara wanda ya tuba daga baya akan abunda yar mahaifiyarka take aikatawa"da sauri Jawwad ya kalleshi yana kokarin yayi magana, Jalal yace "karka tsananta tambaya dan bazan gayamaka komai ba amma lokaci zenuna komai, mahaifiyarka zatayi nadamar abunda tayi, kayi kokarin ganar da ita, tun kafin tasamu kanta a halin datawa mahaifiyar take ciki, nima da datawa damuwar nazo maka amma bari in kyaleka ka huta, kacigaba dayaimana addu'a kaji dan uwana, banason damuwar ka ina kaunarka dan uwana kadena damuwa" Jalal ya dan daddaki bayan Jalal alamun rarrashi, daga nan ya tashi ya fice.
Jalila yadda taga rana haka taga dare, se tufka da warwara kawai takeyi, gashi tunda ta dawo Nana ko dakin bata shigaba, Maama ta hanata Nana bata kwana a dakin ba a can gurin Maama ta kwanta.
Bangaren Jawwad ma hakane, juyi kawai yakeyi, ya daga waya zs kira Jalika yaga inya kirata ma mezece mata, tunda be ta
bbatar Jalila taji abunda Maama taceba.
Washegari Sam Jalila bata nuna da wani abu a ranta ba, sedai ko karyawa batayiba ta fita domin tafiya makaranta, a kofar gida tasamu Manu yanata goggoge mota, suka gaisa takoma gefe tana jiransa yagama su tafi, Jalal yana cikin motarsa a kofar gida, zeje wani guri, daga cikin motarsa yana ganin yadda ta rame, da ganin idonta kaman bata samu bacciba ta kwana cikin damuwa, lokaci2 tana goge idonta da handkerchief, Jalila tanada yawan fara'a bata fiye hade raiba, musamman in ta samu abun tsokana, amma yau fuskarta sam babu annuri, setayi kaman wadda ta dade tana jinya, har cikin ranaa seyaji babu dadi ganinta a haka, haka manu ya dauketa ya kaita makaranta.
Hannah abun duniya ya dameta tarasa ta ina zata bullowa lamarin Jalal, amma tanason sanin matsayin Jalila a gurinsa, yazama dole taga Jalila, amma kafin taga Jalila kokuma bari in bari tukuna, amma bari inje gurin wannan garan sena hadu da Jeje, Hannah ta shirya tsaf ta dau mota, ta tafi inda tasan Zata hadu da Jeje, Jeje na ganin Hannah yafara murmushi yana tafa hannun sa "barka da dawowa Gimbiya Hannah" daga masa hannu tayi alamar bata son surutu, guri ta nema ta zauna tana facing din Jeje, Jeje ya rigata magana ta hanyar cewa "dama nasani Hannah zaki dawo, zaki cigaba da aiki damu kin temaki kanki da kika gane hakan, don Jalal baze taba aurenki ba, ni kaina yau rabon da Jalal yazo mashaya ya dade, shiyasa wani shirin muke sakeyi akansa zuwanki a yanzu kinzo akan gaba" "kaga dan Allah kayi shiru kaji meyake tafe dani se surutu kake, kai ka isa inyi magana in janye saboda wani banzan me gidanka baku isaba wallahi ka tsaya ka saurareni, nazone in gaya maka wanda yasa aka dauke Jalal ranar birthday dinsa ba kowa bane face wannan yarinyar data
kawo cake" a razane ya kalleta "are you serious?" "sekaje kayi bincike, da bakinta tagayamin haka, sannan kasani in har tana raye to baka isa kuyi nasara akansa ba, seku sake shiri sannan nima bazan bari kuyi nasara akansa ba saboda aurensa zanyi, mataki ya rage ku dauka akan wannan yarinyar, danni nafi karfinku kasani" "Amma hannah........" kaga ni na riga nagama magana" ta mike ta bar gurin, jinjina kai Jeje ya dingayi yana tuna abunda Jalila tagaya masa daren da yafara ganinta akan Jalal, tabdijan yazama dole ya dau mataki akan yarinyar nan. Yazama dole anjima inje gidansu Jalal da kaina, inbahakaba akwai yuwar wannan yarinyar tamayar mana da aiki baya, bazan bari oga KB yaji wannna zancen ba mara dadi"
Anfito daga exams Jalila tana tafiya kaman wadda kwai ya fashewa a ciki, daka ganta kasan bata cikin walwala, gani tayi an sha gabanta tana daga ido taga saleema, matsawa tayi da niyyar wucewa, takuma shan gabanta "Ke magana zanyi dake" Jalila ta kalleta "ina jinki" "Kashedi na karshe zanmiki akan Zahrah, ta kawo mana kararki dan haka ba ruwanki da rayuwar da takeso tayi, dan haka kidena mana shishshigi, bake ba zahra" Jalila ta dakko wayarta tana dannawa sannan tacewa Saleema "tsakanin nida zahra wakika haifa da kikemin wannan kashedin?" "haka kikace to kicigaba karki fasa zakiga abunda ze biyo baya"
"bazan dena ba, mekika isa kiyumin meze biyo bayan?" cikeda da gadara saleema tace "Abunda ze biyo bayan abune mafi muni da bakinciki a rayuwarki abu mafi kunya da asara" murmushi Jalila tayi
"shikenan ina jira, nabaki nan da yan kwanaki in har abun da kika fada be faru daniba to ke ze faru akanki, sha3 kawai" binta da kallo Saleema tayi, yayinda itakuma ta wuce, office din sir Hafiz taje, yanata marking, ya kalleta "hmm Gimbiya yar senaga dama se yau kikazo kiran danayi miki" shiru tayi batace komai ba "well ya exams din" "lafiya kalau Alhamdilillah"
"meyake damunkine? Naganki kaman bakida lafiya" "lafiya ta kalau" ta bashi amsa a takaice
Mikewa yayi ya tattare takardun gabansa yasaka a drower yace mata "biyoni" ba musu tabi bayansa, sun danyi tafiya me nisa sannan sukazo bakin wani office, Sir hafiz ya bude kofar yamata alama yace "bisimillah" Jalila ta kalleshi "fara shiga zanbiyoka abaya" murmushi yayi "kina zaton zan cutar dakene anyway biyoni a baya" suka shiga office din, office din babbane sosai ya hadu matuka, se kamshi da sanyin Ac ne ke ratsa ko'ina a cikin office din, kallo daya tayiwa mamallakin office din yana kashingide yana dannan laptop dinsa, sallama sir hafiz yayi, da fara'a wanda ke danna laptop ya dago tareda amsa sallamar, musabiha sukayi da sir hafiz suka gaisa, ita dai Jalila kallonsu kawai takeyi Sir hafiz yace "kalleta ina fatan ita kake nufi" mutumin ya kalleta "eh itace Hafiz nagode sosai Allah yasaka da alkhairi" suka kuma gaisawa sir hafiz ya kalli Jalila yace "to game son ganin naki nan" batace komai ba sir hafiz ya juya ya fice, mutumin ya kalleta "bisimillah ga kujera nan kizauna mana" ya mike ya yaje fridge ya dakko mata ruwa da lemo ya ajiye a gabanta, "wai meyasa kake nemana, ni dai ban sankaba menayi maka" murmushi yayi ki kwantar da hankalinki dolece tasa na nemeki saboda naganki da abunda na dade ina nema " kallonsa tayi irin ban fahimta ba
"dan Allah a ina kikasan ABDUL JALAL, meye alakarki dashi?" kallonsa tayi cikeda mamaki sannan tace "waye kuma hakan?"
"Naganki a motarsa jiya yakawoki school shiyasa na tambayeki"
"kai mene alakarka dashi?" "Abokina ne, mun dade bamu hadu ba sena ganku tare, shiyasa na tambayeki saboda akwai wani muhimmin abuna a tare da shi?"
"shiya kamata ka tambaya alakar dake tsakanina dashi tunda abokinka ne, kokuma inbaka lambarsa seka tambayeshi" "to shikenan bani lambar tasa" mikewa tsaye Jalila tayi sannan tace "Sena tambayi izininsa tukuna" ta juya tai ficewarta daga office din tana zancen zuci "wannan wane irin abune kawai kawani fara tambayata waimeye alakata dashi mtseww" wata Jalila ta tsayar ta tambayeta sunan me office din, tagaya mata sunanshi malam Sagir Ahmad, Jalila taimata godiya ta tafi,
Koda ta fita tsaki yayi, ya dauki wayarsa, ya dan daddana sannan yasa a kunnensa "hello, ke gaskiya yarinyar nan tanada matukar wayo, taki yadda tacemin komai a game da alakarta Da yayanki" Ajiyar zuciya Ilham tayi "kai duk dabarar naka da iya maganar amma ka kasa" "lallai Ilham, yarinyar tana da lissafi batacemin komai ba akan alakarsu" "shikenan nagode sosai" "yawwa to se anjima" Ilham ta aje wayar ta jinjina kai "shikenan tunda kinki fada, bari in je gurin malam inji meze cemana, Allah ya kaimu goben"
yauma seda Jalila tasa nikab taje dan bare gidan dasu Saleema suke sheke ayarsu, ta tsaya daga waje, maza da mata ba wanda baya zuwa gidan nan, seda ta tabbatar su Saleema suna zuwa gidan nan kuma babu kalar yan iskan da babu. Ta dau lokaci a labe tana kallon masu shiga da fitaa a gidan sannan ta tari abun hawa takoma gida.
Ko a gida ma tunani taitayi, ko Jalal zatayiwa zancen wannan Sageer din cab toma tayaya zan tari wannan jarabbabben da wannan maganar ko ina, tana cikin tunanin ne Nana ta shigo dakin da fara'arta tace "kindawo ashe?" "Eh na dawo Nana" "yaya Jarrabawar" "Alhamdilillah"
"Jalila taso zomuje ankawo sabon order na laces da turaruka, zomuje mu zaba"
"kai Nana wane irin lace kuma? Duk kayan damuke dashi" "to Ai Abba ne yayo waya yace muje" "to bari indakko hijjabina" "kai Jalila ingo mayafin nan dora, banaso wasu su rigamu zuwane a zabe abarmu" Jalila ta karbi mayafin hannun Nana ta yafa, ta kalli Nana "Nana gaskiya mayafin nan yai kadan dubi kayan jikina fa?" "wallahi watakila har muje mu dawo bazamu hadu da kowaba taho kawai" Nana taja hannunta suka tafi gidansu Jalal, Mummy bata babban palour dan haka sukaje part dinta, tana palourn ta tana kallo, Ilham tana kwance tana gyara dogayem faratan ta cikin girmamawa suka gaisheta ta amsa, Ilham bata kulasu ba, Nanace taitayiwa Ilham korafin ta dena nemanta yanzu zumuncinsu ba kamar da ba, nanma Ilham batayi wani responding ba a zuciyarta tace "kina tareda babba makiyata zan dinga sauraranki, taanar danake mata yanzu ai harda ke" Nana tace "Mummy anuna mana kayan mu zaba tun kafin azo a kwashesu" murmushi tayi tace "to hajiya Nana, dankuwa kinsan akwai costumer da Jalila ta hadani dasu sunce zasuzo da sun rigaku zuwa da sun kwashe" Jalila tai murmushi "Mummy ashe har yanzu suna zuwa" "muna hulda sosai suna siyayya a gurina, Jalila maza shiga bedroom dina ki dakkomin mukullaye acikin wardrobe dina, se muje a bude store ku gani" Jalila tana mamakin yadda Mummy batajin komai take turata kan kayanta, Ilham seda ta dago ta kalli Mummy, Mummy ta dauke kai, meyasa Mummy bata yadda da ita akan irin wannan lamuran nata, tsabar haushi Ilham ta tashi takoma baban palour, Jalila taje ta dakko keys, sukaje store suka gama ruwan idonsu suka dauki kaya" Mummy tabiyosu sun fito babban palour sega Daddy ya shigo shima suka gaisa daddy yace "Jalila na kuwa tura Jalal nace masa yace inason ganinki sega faduwa tazo dai2 da zama" murmushi tayi "ai bansaniba Daddy dana zo" yace hakane ya kalli Mummy yace "yan borno zasuzo next weekend Insha Allah"
A razane Mummy ta kalleshi, Ilham ma seda ta tashi zaune, Mummy tace "yan barno kuma? Meza suzo suyi?" "Zumunci mana, dan haka Jalila naga kin iya wannan kayan dadin Abincin naku na yan zamani da irin namu na yan da, dan Allah inban takuramiki ba inaso za'ayimin zamuyi baki ne nasan Madam bazata iya ba ita kadai" Jalila ta dan rusuna "bakomai Daddy Insha Allah ba damuwa za'ayi"
Nana tace "daddy dama Abincin hada wani na kwadayi" murmushi yayi "Eh mana Nana irin naku na zamani ba" Jalila tace "amma wani irin Abincin kakeso ayi musu sannan su nawane"? "Yawwa takwarar son, nagode sosai, yanzu kije gida kiyomin list din Abunda za'a bukata, kiyi musu kawai Abinci me dadi, nasan zasuzo da dan yawa ina jiranki kiyo list din, wanda muke dashi shikenan in babu se a siyo, inkin tashi kizo kiyi anan karki bata muku gida "
"to Daddy bari inje yanzu zan kawo maka Insha Allah"
Su Jalila suna futa Mummy tace "dan Allah dagaske kakeyi koda wasa!"
"daga snake shiyasa ban takuraki nace kiyi musu girkin dazaki karbesu ba gara nasa na waje suyimin tunda ke ba lallai kiyi ba, bayan shekaru yan uwana zasuzo sukawomin ziyara" daga haka ya wuce part dinsa, dafe kai Mummy tayi tanemi guri ta zauna ita kanta Ilham kanta ya kulle,
Jalila tana zuwa gida, ta zauna tayi list din abunda take bukata ta fito domin kaiwa Daddy, amma tundaga kofar gida taci karo da motar Jeje, "Wannan annamimin mayen yazo kenan" tana shiga taga Jalal da Jeje a harabar gidan, suna zaune akan fararen kujeru suna hira, suna shan wata irin taba me girma sosai dan tafi wadda Jalal yake sha girma, zuwa tayi ta wucesu cikin gida, Jeje da kyar ya iya dauke idonsa akan Jalila, saboda karamin mayafine ajikinta gashi doguwar rigarta cif jikinta
Share please
Daga Alkalamin Aysher cool
I want Comments not stickers or just thanks what's app only
07063065680
_ABDUL JALAL (2020)_
_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)
PART
_PAGE
65_

"Waime kake kallo hakane?" Jalal yaima Jeje tsawa cikin inda2 Jeje yace "ohhh am sorry J, nothing, dan samomana kayan washi mana, tunda kwana biyu bamu hadu ba" Jalal yace "to jirani ina zuwa" Jalal ya mike yaje part dinsa ya kawo musu kwalaban giya da wayne cups ya ajiye akan table din"Jeje yace "yauwwa nace meyasa kadena zuwa club, friends nata tambayarka yane? Ga beb dinka Hannah duk tana cikin damuwa irin sosai kagane eh"
"kai bari kawai, haka nan bana son zuwa club din nan, a gida nake dura duk abunda nakeso normal ne ai nan da can" "A'a akwai banbanci, nan
ba wasu zafafan mata, bawani sauti me ratsa kunnuwa, kodayake bebs din dake ratsawa a gidan nan naku ma sun isheka kallo, especially wannan zazzafar baby girl din, komai nata me kyaune," hade rai Jalal yayi, a fusace yace"kamanta kashedin danayi maka abaya ko" Jeje ya sauri yace "ohh No am sorry bazan karaba Insha Allah, yanzu kaga dakkomin wani product din wannan ta isheni, kusan kullum ita nake sha, nasan bazaka rasa na manyan kai ba, dan Allah kabani wani product din" "bazanje ba sedai karka sha" "please am sorry nasan kanada masu tsada dan Allah ka dakkomin" banza Jalal yaiwa Jeje, sekuma can jumawa ya tashi ya tafi dakko masa wata giyar
Jalila ta shiga palour bakowa, Seta jiyo sautin maganar Mummy a bangaren daddy, kaman sa'insa sukeyi, dan girgiza kai Jalila tayi, be kamata taje musu a yanzuba, tana jiyo muryar daddy yana "yan uwanane gurina zasuzo ba gurinki
ba, insunzo sedai kibar gidan"
"Amma kamanta abunda yafaru ne? Har kake wannan tunanin?"
"ni ba abunda ya faru tsakanina dasu sedai tsakaninki dasu" Jalila juyawa tayi tafito da sauri dan karma su fito su ganta su gane taji sa'insar da sukeyi. Koda ta fito harzata tafi, ta juyo Jeje cikin wannan muryar tasa mara dadin ji
yana cewa "hi beb i like your confidence, akwaiki da fada da cikawa, " tsayawa tayi cak ba tareda ta juyo ba, yacigaba da cewa "kin fada kuma kincika, kinyi nasarar batamin aikina na wannan rana wanda na dora raina akaki, amma ki saurari hukuncin dakuma abunda ze biyo baya" juyowa tayi ta kalleshi, kawai taga kwalaben giya akan tebur, take taji ranta yabaci koya daddy zeji in yafito yaga dansa yana shan giya a cikin gidansa, shida wani dan iska ta kalli Jeje "ai fada da cikawa baka ga komai ba, se randa sharrin ka yakoma kanka, se ranar dana ga karshenka, asararrae dan wahala, kalle ka sekace karen arna tir da kai da halinka, kuma shi zalunci in abunyine kacigaba, nima bazan gajiba"
"Jalal, shike kama da kare amma ba dainiba shike kama da karnuka, kuma kisa ido, zakiga yadda ze koma ke, zakiga yanda zan maida shi, senacika alkawarin da na daukarwa me gidana, se Jalal ya lalace fiye da tunaninki seya kare rayuwarsa a prison a wulakantacce, ke asuwa naganin bayana karya kikeyi, dukda bangane meye nufinki akansa ba amma zanyi maganinki wallahi, senamiki tabon da harkibar duniya bazaki manta ba"
"Shikenan naji nakuma yadda, koni ko kai duk wanda yasamu dama yaga bayan dan uwansa, sena wulakantaka daga kai har megidannaka, ainasan waye megidannaka zaka gani, banda ai sam Jalal be dace da tarayya da tababbe irinka ba tunda kaikayi sanadiyar yazama haka, ka cutar da rayuwar sa, sannan kacigaba da wargaza masa rayuwa, nikuma zancigaba da bashi kariya dayi masa addu'a har zuwa numfashina na karshe kuma insha Allah seka wulakanta kafin in bar duniya, sanna kasani........ Shiru tayi ganin Jalal yafito da wata katuwar kwalbar, yaje ya zauna, tana tsaye tana kallonsa ta gefen flours Jeje yaimata wani shu'umin murmushi, Jalal sam be kula da itaba, saboda tana bayan inda yake a zaune, Jeje ya bude giyar ya zuba, sannan ya zubawa Jalal a cup ya mika masa, Jalal ya karba ya kai bakinsa ze sha, Jeje kuma idonsa na kan Jalila, yanaso yaga yadda zatayi da hanzari ta kaaraso inda suke, Jalal ji kawai yayi an kwace kofin hannunsa ta kalli fuskar Jeje ta watsa masa ruwan giyar nan a fuskarshi , gaba daya suka bita da kallo, ta kalli Jeje cikin zafin rai tace "Asararre tababbe mara zuciya, wallahi inbaka ji tsoron Allah ba, mushen jaki seyafi karshenka kyan gani, saboda rashin mutunci a cikin gidan mahaifinsa zaka biyo shi kuyi shaye2" ta kalli Jalal tuni idonta yacika da hawaye "kaima saboda rashin zuciya Jalal mahaifinka na cikin gidan nan kana nan kana sha masa giya a gida, kowane lokaci ze iya fitowa yazeji in yaganka a haka? Memakon ma kuyi a dakinka amma kake shan giya a bainar jama'a ko kunya bakaji, kodayake bakaji kunyar Allah ba sena mutane, bakaji dadin halinka ba wallahi"
Jalal sam ba abunda Jalila tayi bane ya bata masa rai illa irin kallon maitar da Jeje yakemata, ta juya ta hankade tabur din da giyar take kai, suka fadi kwalaben suka fashe, tana kuka tana fadin "Jalal kaji tsoron Allah, Allah ya tsinewa me shanta, da duk me ta'amali da ita, amma giya a cikin gidanku, gidan mahaifinka"
ta kalli Jeje "kafita kabar gidan nan, wallahi bantaba tsanar mutum a rayuwataba kamarka, idan na ganka jinake kaman naga shedan natsaneka wallahi, kallon nan danake maka kaman zuciyata ta fashe haka nakeji, in baka bar gurin nan ba sena maka illa da kwalba" ta durkusa tana kuma fasa kwalaben dabasu fashe yadda takeso ba, Jeje ya kalli Jalal "J man, anya yarinyar nan ba mahaukaciya bace ba, kalli fa abunda takeyi" kafin ya rufe bakinsa tafasa hannu da kwalba, da sauri Jeje ya durkusa ze tabata, cikin zafin nama Jalal ya janyeshi, "meye haka kake kokarin yi" Jalila gaba daya ta hargitse kaman mahaukaciyar, Jeje yace "haba J kalli yadda beb din nan takeyi inta illata kanta ba karamar asara za'ayi ba, kallon Jeje yayi,"get out from here" da mamaki ya kalli Jalal "me kake nufi?"
"kafita ka tafi yanzu ka bar gidan nan" "Amma Jalal......
" kafita nace bakaji menaceba ne, kosokake seta illata kanta" Jeje ji yayi gaba daya duniyar tamasa zafi jiyake kaman ya mutu ya huta yau shi Jalal yakewa wannan tsawar saboda mace, ya juya ya fice daga cikin gidan, da sauri Jalal yasa hannu dago Jalila daga durkushen da take, ya jinginata a jikin bango sannan yasa hannunsa ya dafe gefe da gefe, ya kalleta yace "baki da hankali ko?, sekinyiwa kanki Illa tukuna, ji yadda kika yanke hannu meye amfanin hakan da kikeyi ne? Ina ruwanki dani dolene sekin shiga shirgin rayuwata" idonta duk hawaye tai masa wani irin kallo, shima kallonta yayi daga sama har kasa, ya karewa rigar jikinta kallo sannaan ya kalleta
"Idan kika kuma bari naganki da kaya irin wannan sena bata miki rai, sena yaga kayan ko agaban uban waye, sena miki rashin mutincin da bakya tunani" idonta duk yayi ja tace "au yanzun meya hanaka yagamin rigar, tunda baka da hankali, Jalal baka da hankali na fada kuma zan fada ko agaban waye baka da hankali, ai daka sani ga yagamin riga seka tabbatar min lallai giyar daka sha tafara aiki, yanzu kagama cemin ina ruwana da rayuwar ka, nima ina ruwanka datawa rayuwar, kanwarka wace irin shigar ce batayi seni zaka dingayiwa shouting haka, ko tsirara zan tafi ba ruwanka dani, in kafasa yagamin kaya baka kaunar Allah, sannan ka gayawa abokinka zan gauraya dashi, dagani kabani guri in wuce ko in hankadeka akan kwalaban nan, koka mutu banda asara" banza yayi mata ya cigaba da kallonta, "Nine banida hankali ko? "eh baka da hankali, ka matsa in wuce nace ka tsaya kana karemin kallo, duk ka cikani da warin giya, da kaurin hayaki, kaman zanyi amai. Jitayi kaman wani abu yana shanshana mata kafa, dubawatayi taga menene, ihu tayi, ta rungume Jalal tana" wayyo Allah na mene wannan" dubawa Jalal yayi seyaga ashe dan karensa dayake cewa bobby ne
kiwata shiyake
a part dinsa ya bar kofa a bude shine yafito, karen dan guntune da kadan yafi mage tsayi, ga jikinsa buzu2 da gashi gashi kato sosai amma ba tsawo, daga England daddy yakawo masa shi, Jalila bata taba ganin kare irin wannan ba, kuma batasan dashi a gidan ba.
Ilham se kiran layin Maminta takeyi ta labarta mata abunda yake faruwa a gidan, amma wayar taki shiga ba network, dan haka ta yanke shawarar bari ta fito waje kozata samu network.
Koda bobby yaga Jalila ta tsorata sekara zuwa kusada ita yakeyi, yana shanshana mata kafa, sosai take ihu tana kara shigewa Jalal, hmm dariya ma tabashi tagama zaginsa kuma yanzu abun tsoro yazo ta rirrikeshi, dan haka ya kyaleta Bobby se zagaye mata kafa yake,
"Nashiga uku, Dan Allah a temakeni, wani abu ze cinyemin kafa, waimeye haka bazaka hanashi ba banaso, dan Allah banason mage fa" duk ta yamutsa masa kaya gashi ta goge masa jinin hannunta duk a rigarsa, janyota yayi ya tsayar da ita "meye haka? Kare ne fa kalli" itadai bata taba ganin Kare a haka ba, Jalal ya dago bobby a hannunsa yana nuna mata, aikuwa Bobby yai tsalle yakoma jikinta, ihu takumayi tana nema fita a hayyacinta, tana kokarin cire Bobby a jikinta, dan tsoro yakebata, sosai takuma rike Jalal tana ihu, Jalal ya riketa ya dauke Bobby a jikinta,
Abunda Ilham tagani ne yai matukar tayar mata da hankali, tarasa idonta biyune kokuma mafarki takeyi, Jalila ajikin Jalal, abunda bata taba ganin yayi ba, nan take taji kirjinta ya buga da karfi, tama rasa me zatayi, ta juya takoma cikin gida da gudu. A hankali yacewa Jalila "Nutsu mana is just a dog, ba abunda ze miki, kalli yadda kike nema ki firgita kanki, duk tsiwar taki kalli yadda kika rikice akan kare, seki dagani ai, tunda ba jikin Jawwad bane, jikin makakke ne mara daraja, kokindena kyankyamin gashin jikin nawa" tsaki Jalila tayi ta juya, girgiza kai Jalal yayi, Jalila tai tafiyarta gida.
Nana tazo ta zauna a kusada Jalila tace "Jalila kamshin wani turare kikeyifa" "kamar ya?" "kamar yadda nagaya miki, kamshin me dadi" "turare na dai dayane kuma kinsanshi sekuma me?" "hmmm bakomai, yaushe zamu kai dinkine?" "ko yaushe ne kikaimana, ni har yanzu bamu gama jarrabawa bane" "to shikenan"
Daren ranar Ilham ko na minti daya bata rintsa ba ta dau wayarta ta kira malaminta
"hello malam ina cikin damuwa fa, yarinyar nan da alamun soyayya suke da Jalal, tashin hankali na ma kar inje Aikin da akayi masa ya karye" "Aikin da akayi masa har yanzu yana jikinsa, amma kibari zuwa gobe kizo" "to shikenan nagode zanzo goben" sukayi sallama, saboda tunani da bacin rai, tarasa meyake mata dadi, sabida abunda idanunta suka gane mata yau amma gaskiya Jalila tacika yar rainin hankali taita nuna ita batason Jalal dan munafunci ashe soyayya da suke harta kai ta rungumeshi, taita nuna ita ta Allah ce amma abun bahaka yake ba, Allah2 kawai take gari yawaye ta tafi gurin malamin nan ayi duk me yuwuwa ayita ta kare!.
Jawwad har ya shirya ze kwanta, Hanan ta kirashi, kamar ya share ta sekuma ya dauka
"barka da dare abun kaunata fatan kana lafiya" "lafiya kalau hanan yaya mutanen gidan?" "duk suna lafiya kalau Alhamdilillah, kwana biyu ko nemana bakayi meyasa" "bakomai Hanan abubuwa ne sunmin yawa kawai, gashi muna daf dagama school" "Allah sarki nayi murna sannan inamaka fatan Alkhairi, Allah ya sanya Albarka a ilimin ka yasa al'umma su amfana"
"Ameen Hanan naji dadin Addu'arki nagode sosai" "No bekamata kayimin godiya ba, tunda ina sonka zanso duk wata karuwarka Jawwad, amma na lura kaman ina takuramaka ni kadai nakesonka nasan kana guduna saboda Jalila, amma nima yakamata ka tausayamin Jawwad, Abunda kakeji game da Jalila shinakeji game da kai, bazanso incigaba da takurawa rayuwarka ba, bazan so saka ka a cikin damuwa ba, zanso ka kasance a cikin farinciki koda zezama ni narasa nawa"
"Hanan yakamata ki......" "A'a Jawwad base ka gayamin komai ba, karka damu, amma kasani bazan dena sonka ba har karshen rayuwata, inasonka Jawwad, amma Insha Allah wannan shine kira na karshe da zanyu maka, bana son rusa maka farinciki, tunda na fuskanci ina takuramaka, ka gaishemin da masoyita kuma yar uwata" kafin yayi magana ta kashe wayarta, jiyayi daga karshe kaman kuka take, seyaji sam beji dadin hakan ba, dan haka yai kokarin bin layinta amma a kashe haka yaita trying har ya hakura.
Da wuri Jalila ta shirya dan tafiya makaranta, sam bata jin dadin jikinta, ta kwana da ciwon kai wadda tasan damuwa ce datayi mata yawa, kallo daya zakayi mata kasan tana cikin damuwa dan duk ta rame, tana fitowa ta tarar manu yana goge mota, suka gaisa ta shige gaban mota ta kifa kanta, tana jiran manu yazo su tafi, har ya shigo ya kunna motar bata dago kanta ba, seda taji gudun yayi yawa ba tareda ta dagoba tace "Manu mutafi a hankali mana, kaina ciwo yake sosai, wannan gudun kaman zamu bar gari" shiru be amsaba kuma be dena gudun ba, dagowa tayi kawai taga Jalal ke tuka motar ba manu ba
"kaiii meye haka kuma? Ina manun?" shiru yayi yacigaba da tuki "magana fa nake maka, yauma ka dakkonine don kamin wulakanci, inkuma makara wallahi baka isaba ka ajiyeni kawai in sauka" still bekuma cewa komai ba
"wai baka jinane? Nika ajiyeni, bana son adinga gani tareda kai kar wannan shashan yan matan naka su dinga min hauka, gashi har wani yafara titsiyeni sena gaya masa alakar dake tsakanina da kai ni ka ajiyeni" "Ke!!!" seda ta tsorata, saboda yanayin da yayi maganar "idan na ajiyeki duk abunda yasameki kika sani, ba cewa kikayi kanki yana ciwo ba, amma se surutu kikeyi, wallahi kika kuma magana sena baki mamaki, in an ganmu tare duk wanda ya tambayeki kigayamasa abunda kika gadama" ba shiri taja bakinta tayi tsit, ko minti biyar beyi, da wannan maganar da Jalal yayi ba, wata mota tasha gaban tasu motar a guje, wanda ya tilastawa Jalal yin parking.

Aysha cool
_ABDUL JALAL (2020)_
_Story and written by_
AISHA HUMAIRA (daddy's girl)
PART
_PAGE
66_

Jalal bai fita daga motar ba,
dayake motar tint glass ne, da mamakin Jalila motar data sha gaban tasu, Jeje ne a ciki da wasu manyan karti suka fito, suka tinkaro inda tasu motar take, knocking sukayi a side din direba, a hankali Jalal ya sauke glass sukayi ido hudu da Jeje, rikicewa Jeje yayi, cikin inda inda da mamaki yace
"J man kaine da kanka, huh ya gida amm...
"shut up please" Jalal ya katseshi, "nasan za'ayi haka ai, shiyasa na shirya hakan, Jeje baka da amana, baka da mutunci, kobataci darajar kowaba taci darajar yayanta amininane, amma saboda baka da mutunci shine ka shirya cutar da ita, kuma duk abubuwan data fada akanka karyane? Ba karya bane ba, Jeje inaso in maka kashedi, koda makamancin wasa ba kai babu ita, idan nakuma fuskantar ka shirya wani abu akanta na cutarwa, you know what am capable of doing, ka kiyaye "
" haba Jalal kai ka dauki abun a haka amma ni banyi niyyar yimata wani abuba... "Enough malam, kayimin blocking way, ku janye motarku zan wuce" cike da bakinciki Jeje yasa aka janye motar, ya shirya ya dauke Jalila yaketa mata haddi, saboda abunda tayi masa, ya dauki fansa akan abubuwan datayi masa, ya akayi Jalal ya gane shirina haka, dukan motarsa yayi da karfi, yayiwa kartin umarnin su shiga mota.
"kinga Abunda shishshiginki ya nemi ya janyomiki ko? Da kin bari kin taho ke kadai da wani zancen ake ba wannan ba" ya karasa maganar cikin fada, kallon Jalal tayi, ta dauke kanta
"waman yatawwakallu alallahi fahuwa hasbuh, dan haka be isa yayi min wani abu ba, kuma kaima baka isa ka kareni daga komai ba, ba gudu ba ja da baya wallahi koze kasheni seyayi nadamar niyyar dayayi akaina, kar ya fasa, zan nuna masa wacece ni duk Abunda nasa gaba Allah yana bani sa'a kansa, bana alwashi in kasa cikawa, duk wanda ya takaleni da sharri senaga bayansa, kodame yake takama, dan haka ba kaika kareni ba Allah ne, kuma ka gaya masa zamu gauraya dashi dan haka kadenamin tsawa"
Jalal yakara jinjinawa Jalila akan taurin kai, betaba ganin mace me taurin kai kamanta ba, bata da tsoro bata son raini, kuma abun mamakin she has a luck, kota gangamo rigima se Allah ya kwaceta. Kallonta kawai yayi yai shiru bekuma cewa komai ba yacigaba da tukinsa, suna zuwa kofar gate yayi parking, "Fita" "aiko bakace in fitaba zan fita, komeye nayimin gadara aiba motarka bace, kuma bani nace ka kawoni ba dan haka karka kara yimin tsawa" harzata bude motar, setaga wannan lecturer da Sir Hafiz ya kaita gurinsa wato Sir sagir yazo wucewa, da sauri ta kalli Jalal
"Yawwa kasan wancan mutumin?"
Kallo daya yayiwa sagir yagane shi, cousin din baban Ilham ne, shikuma meye hadinsa da ita oho, amma yace "ban saniba kifita nace"
"to kayiwa kanka dama sako yabani in baka, tunda kace haka shikenan" ta fice abunta Jalal ya girgiza kai yatafi.
Karfe tara na safe Ilham tana kofar gidansu Yaseera ta kirata awaya ta fito suka tafi gidan malamin nan. Suna zaune agabansa kaman masu neman gafara, ya kalli Ilham yace "kunyi sake gaskiya, saboda aikin baya tasiri akansa yanzu sosai kaman a baya, amma yanzu mekikeso ayi" Ilham kaman ta fashe da kuka tace "Malam har za'ayi maganar aure bawan Allah nan yaki yaita min wulakanci, amma katsam naganshi da wannan yarinyar da nake gayamaka rungume a kirjinsa, hankalina ya tashi matuka" "to aina gayamiki Asiri baze tasiri a jikinta ba, yarinyar bahaka take zaune ba tayiwa Al'qur'ani kyakyawan riko, tanada ibada danhaka sedai ayi Amfani da kissa, da dabarunku na mata akanta badai sihiri ba" ya dakko wata kwalba da ruwa a ciki ya mikawa Ilham, yace "gashi nan ki tabbatar kinzuba mai wannan ruwan a Abinci ko Abun sha kin bashi da hannunki yaci, daga nan kome za'ayi baze kuma yinkurin hana Aurenku ba"
Yakuma dakko wani turare, ya mika mata tasa hannu ta karba sannan yace "shikuma wannan ki tabbatar kinyi amfani da wannan turaren, kinshafa kafin kibashi Abinda kika zuba wannan maganin" Ilham ta gyda kai, yaseera tace "to amma malam kana ganin auren nasu ze yuwu kuwa?" "in har tayi yadda nace, komai zewuce ze aureta, kiyi a hankali, kikula da kyau muddin aka samu kuskure to komai ze iya lalacewa, danba karamin hadi nayi ba, karki bari wannan damar ta wuce" sukayi godiya Ilham ta bude jaka ta debo kudi fal ta bashi, sannan suka fito suka tafi,
"Yaseera wallahi bansan ya zanyi inbashi Abu yaciba, haushina yakeji sosai, ko kallona bayayi balle yaci abun hannuna" "aikuwa haka zaki dage ki kokarta har bukatarmu ta biya, kiyi iya kokarinki kiga kin aiwatar, sannan yazakiyi da wannan yarinyar" "banni da shedaniya aini harnaga abunda zan mata kyaleta kawai" akazo inda yaseera zata sauka sukayi salkama. Ilham tana karasawa gida taga mota a bakin layinsu, rabawa tayi da niyyar ta wuce aka kuma biyota da motar, ta ja ta tsaya, Hannah ce tafito daga cikin motar, tasha gaban Ilham, kallo daya Ilham tayi mata ta ganeta, Ilham ta hade rai sosai, Hannah tacire glass din fuskarta tace "nasan kin ganeni, babu bukatar inmiki bayanin waceceni, kashedi ne nazo miki dashi, wanda sabawa kashedina daidai yake da rusa duk wani farincikin ki" "inajinki fadi abunda kikeso"
"Naji labarin za'ayi miki baiko da Jalal, dan haka nazo miki da kashedin kiyi gaggawar janye batun ayimuku baiko, inbahakaba banki in salwantar da rai ba, dan haka kishiga hankalinki, kiyi tunani" mamakine yakama Ilham, wannan maganar kuma daga ina amma ta dake tace
"Kinyi kadan wallahi, sedai muyi asarar rayuwarmu gaba daya amma kome zakiyi, wallahi indai ina numfashi baki isaba, aurena da Jalal se anyi shi" "haka kikace ko?" "bakida kunne ne, dalla matsa ni kibani guri in wuce" Ilham ta bangaje Hanna ta wuce, Hanna tace "zaki gani kuwa"
Ilham tai tafiyarta gida, Hannah ta shige motarta, itama ta bar gurin.
Yausu Jalila suka kamalla first semester exams dinsu, su sameera se kuma bibiyan zahra suke akan su tabattar data amince da bukatansu, yayinda gefe daya suke tayiwa Jalila barazana kala kala. Da Jalila takoma gida ma sabgoginta ta shiga yi, Suleman ne yakirata, ita mutumin nan yafara isarta, ta daga wayar suka gaisa, yaita mata magiya tabarshi yazo gidansu,
"dan Allah kayi hakuri babana ya bawa wani, inkazo gidanmu zega kaman ina kokarin bijirewa umarninsa ne"
"subhanallah kiyi hakuri, baki gayamin da wuri ba, bazanso kisamu sabani da mahifinki ba, amma naso ace na sameki a matsayin matar aure ina sonki sosai, a tarayyata dake ya nunamin kinada nutsuwa da ilimi, dan haka ina son mudinga gaisawa kafin kiyi aure" murmushi Jalila tayi aranta tace "gaskiya mutumin nan akwai saukin kai" a fili tace "karka damu insha Allah zamu dinga gaisawa" sukayi hirarsu sannan sukayi sallama. Yana kashe wayar taga tests din Alhaji Kabiru akan wai tana wulakantashi tsawon lokaci yanzuma ya kirata wayarta busy tama waya da wani, in bazata yadda dashiba ze hakura" murmushi tayi sannan tace
"hmm kiris ya rage zaka gane baka da wayo" ta kirashi a waya ta dinga lallabashi tana bashi hakuri tayi masa alkawarin zasu hadu r
anar juma'a, haka ya yadda yaita murna. Takira Zahrah a waya tace mata tacewa su sameera zatazo gurinsu ranar juma'a, zahra ta yadda. Jalila tace "Allah yasa abunda na shirya yatafi dai2".
A yammacin ranar ta shirya tasa nikabinta ta tafi hisba, taje takai report akan wannan gida da su sameera suke sheke ayarsu a ciki, sukayi mata alkawarin insha Allah zasu kaiwa gurin sumame, Jalila tace tanason ganin mataimakin commnder personally, yace bakomai sukaje wani office din Jalila tace "ranka ya dade gurin nan sonake kuje ranar juma'a misalin karfe hudu na yamma"
"Amma meyasa?" "saboda a lokacinne manyan lalatattun suke zuwa, abun haushin hada manyan mutane" "karki damu Insha Allah zamuje" "to shikenan nagode sosai ranka ya dade" Jalila ta taho gida cike da farinciki tareda fatan Allah yasa su afka tarkonta, sesun kunyata tun a duniya, daga nan ta taho gida, tana zuwa gida Jalila tasamu Nana tace "Nana kece me sauraran radio, dan Allah inaso kibani lambar wani gidan radio inkina da ita wanda kikasan in Labari yajemusu se duniya taji"
Nana tace "ikon Allah yaukuma me za'ayi da lambar radio, Allah yasa dai ba wata rigimar kika kwaso mana ba" "ke haba dai, nima sonake indinga jin radio yadda nima zan dinga kira inji muryata a radio" Nana tai murmushi "to shikenan na dauka wata rigimar za'a kwaso mana ne" Jalila Allah 2 take asabar tazo taga yazata kaya. Ta kaiwa daddy Jalal list din abunda take bukata na girkim da zatayiwa bakinsu.
Jalila tagayawa zahra cewar tacewa su Sameera karfe hudu na yamma zatazo gidansu.
Ilham duk wata hanya data san zatabi domin janyo hankalin Jalal hartasamu damar bashi wannan maganin amma yaki, dan wani mugun kwarjini ya kema ta gashi ko san ganinta bayayi, gefe guda tsanar Jalila na karuwa a zuciyarta, kiris take jira tasamu damar dazata yiwa Jalila abunda se kowa ya tsaneta.
Haka nan Jawwad yakejin tausayin hanan a ransa, yana ganin kaman be kyauta ba, amma duk yadda za'ayi shi Jalila yakeso, kuma yana fatan ze aureta. Yayinda bangare
Jalila tana kokarin yin baya2 da Jawwad musamman idan Maama tana nan, sabida batason tashin hankali sam, dan zuciyarta na rayamata yiwa Maama rashin mutunci wataran, shiyasa ko Abinci ta dena kai masa sedai halima ta kaimusu, iyakacinta da shi ta waya, sekuma in anyi sa'a ya shigo cikin gida kokuma sun hadu a harabar gidan.
Ranar Alhamis Jalila taje gidansu zahra, Zahra tayi murna sosai da ganin Jalila, tayi wa ummanta introducing din Jalila suka gaisa daga nan suka wuce daki, Jalila tace "ke ba zama nazo yiba, ya ake ciki kingaya musu gobe in Allah ya kaimu zakije?"
"Eh nagaya musu, zanzo karfe hudu"
"yawwa zahra to yanzuma wani abu nakeso kiyimin" "me kenan?" Jalila ta dakko wayarta tasaka wani sim din a ciki, sannan ta kalli zahra, lamba zankira yanzu, inason kicewa mutumin nan kinaso ku hadu a wannan gidan ranar juma'a, kinuna masa kaman kinsanshi a baya amma bazaki gaya masa wacece ba" Jalila taima zahra bayanin abunda takeso tayi, zahra tace "Amma Jalila..." kinga babu batun amma kawai kiyi hakan" "to shikenan" Jalila tai hiding lamba takira Alhaji kabiru tabawa Zahra, bugu biyu ya dauka sannaan yace
"Hello wake magana" zahra tace wata baiwar Allah ce, kadai kacemin baka dau murya ba"
"gaskiya bangane ba, wacece dan Allah?" "nikuma kaga naganeka ba amma in duniya da gaskiya be kamata ka kasa gane wace ba, a cikin yan matanka ne" "to aikinsan abunne dayawa" "hakane kam, amma in ka ganni zakaji kunya akan cewar baka ganeniba" "ko? To nidai ki gayamin" "bazan gayamaka ba sedai in munhadu a gidana zaka gane" washe baki yayi, "gidanki wanne kenan" ta kwatanta masa gidan dasu Sameera suke zuwa, "kazo ranar juma'a karfe hudu, semu hadu ko?" "aikuwa zaki ganni dan zanso sanin wacece?" zahra tai murmushi "to shikenan nagode se anjima" zahra ta kashe wayar, ta kalli Jalila, Jalila ta jinjina mata "weldone dear kinyi yadda nakeso, zan barmiki sim din nan a gurinki, kucigaba da waya har Allah ya kaimu gobe juma'a, komai yazo karshe"
"Amma Jalila shi waye wannan?" "ba ruwanki kedai kawai kiyi abunda nace inkuma akasamu kuskure kece a ruwa baniba" Jalila taimata sallama tai tafiyarta.
Yau juma'a shine ranar da Jalila take sa ran su Sameera su fada trap dinta, kuma gobe ranar asabar bakinsu Jalal zasuzo dan haka ta rarraba hankalin ta kashi2, tun sassafe take up and down, taje kasuwa tayo siyayyar abubuwan dazata bukata na aikace2 da zatayi, karfe uku da rabi ta shirya tasa hijjabinta da nikab ta dau jakarta, Nana ta kalleta "Jalila ina zaki hakane kiketa sauri?"
"banisa zanyiba yanzu zan dawo" amsar da Jalila tabata kenan tafito, tanata sauri a harabar gidan taci karo da Jawwad, "Baby ina zuwa haka da ranar nan? " "Yaya zan dan fitane gidansu wata kawata"
"in hanya ne muje se in kaiki" "Aa kayi tafiyarka kawai, yanzu znadawo bazan bata ba kaji sweetheart" ta kashe masa ido tai waje murmushi yayi ya girgiza kai,
Jalila ta tafi layin gidan, can karshe tasamu guri ta zauna, tana nan zaune motarsu Sameera tazo suka shiga itada Saleema, sunyi wata irin shiga ta fitsara abun babu kyan gani, ga wasu manyan karti
maza suna shiga suna fita daka gansu kaga manyan yan duniya, dan basu da maraba da yan daba. Jalila takira zahra a waya "ke ya akeciki kunyi waya yatahone?" "Eh ya taho, yacemin yana hanya, yanzu su Saleema suka kirani, wai ina inane, nace musu nakusa zuwa" Jalila tace "good kice masa ya hanzarta inbahakaba zaki fita" "to shikenan"
Ba'ayi minti goma ba da waya dasukayi da Zahra sega Motar Alhaji kabiru a layin gidan yayi parking dai2 kofar gidan da su
Saleema suke ciki, yana zaune a cikin mota be fitoba, zahra takira Jalila, "Jalila yacemin waigashi a kofar gidan" "kice masa yashiga kansa tsaye" Jalila ta katse wayar tanata addu'a Allah yakawo yan hisaban nan da gaggawa, tana kallo Alhaji Kabiru yafito daga mota ya doshi gidan nan, Jalila tana ganin ya shiga gidan, takira gidan radio ta sanardasu cewar hisaba sunzo kame a
unguwar dan bare kuma akwai wani gagarumin abun kunya dake shirin faruwa,
"Innalillahi wa inna ilaihi raji un" shine abunda Alhaji ya dinga maimaitawa ganin yarsa ta cikinsa Saleema da shiga rabin tsirara akan cinyar wani kato, suna shan shisha, gefe ga wasu sunata aikata badala ciki hada Sameera, a takaice dai gidane na manyan karuwai da yandaudu

Koda Saleema ta dago tai ido hudu da mahaifinta a gigice ta mike daga cinyar wanda take zaune, tana zazzare ido, gaba daya sukayi cirko2 suna kallonsa, koda ya duba yaga waye Saleema take kan cinyarsa ba kowabane illa Jeje, a gigice Alhaji Kabir yace "Saleema abunda kike aikatawa kenan, kin cuceni kin cuci kanki Allah ya isa tsakanina da ke" ya maida idonsa kan Jeje "nizaka ciwa amana, karasa da wadda zakayi lalata se yar cikina, duk halaccin danayi maka a rayuwa wallahi seka ga karshenka sekaga abunda zanyi maka, sena dau mummunan mataki akanka" Jeje rasa mezece yayi gaba daya ya rude, daga gefe wani tsageran matashi yace "wai dan Allah meyakawo ka nan gurin, kake wannan maganganun ne, nina dauka harka kazo, kaima fa ana kaimaka matan nan guest house dinka to meye dan anyiwa yarka, abunda kakewa yayan wasu nefa" seda Alhaji Kabiru ya duba sosai sannan ya gane matashin, tabass suna kaimasa karuwai yana biyansu kudi. A fusace Alhaji Kabiru ya dau wata kwalba ya nufi inda matashin yake, Saleema se kuka takeyi, jin ance itama ga abunda mahaifinta yakeyi, yana zuwa ya bugawa matashin a ka, sauran matasan sukayo kansa, duk wanda yazo seya kaimasa suka da fashashiyar kwalba.
Itako Jalila koda taga Alhaji Kabiru ya shiga cikin gidan nan ta kuma kiran yan jarida, tana gama wayar sega motar "yan hisba, tareda yan sanda, sukayiwa gidan dirar mikiya, suka kewaye shi, sannan wasu suka shiga cikin gidan, babban abun kunya da asara shine kama uba da 'ya a gidan karuwai, nan aka tarkata kansu tsaf, Alhaji Kabiru se rantse2 yake, ga wadanda yajiwa ciwo da kwalba, Saleema banda aikin kuka ba abunda takeyi, kan Jeje se zubarda jini yakeyi,'yan sanda suka caje gidan inda akasamu miyagun kwayoyi, da kayan shaye2 kala2, kafin a tafi dasu yan jarida suma suka karaso, suka rufawa motar yansanda baya dan zuwa daukar rahoto, ba karamin farinciki Jalila tayiba, rasa inda zatasa kanta tayi dan murna, batasan lokacin dataji hawaye farinciki nabin fuskarta ba "Allah kai kabani wannan dama, Allah kaikabani nasara ba dabarata da wayona ba, Allah nagode maka, nagode da ni'imarka da kariyarka, Allah kasa sanadiyar shiryuwar bawanka ce tazo" hanyar titi ta nufo tana sauri, yamma tayi sosai, ta tafi gida gida cike da murna da farinciki.
Takoma gida tanata murna, tana zuwa ta tarar da sa'ada tazo itada Naja wai a gidan zasu kwana biyu, Jalila ko takansu bata biba, murnarta kawai takeyi,
Nana tace "Baby meye sirrin wannan fara'ar da murmushinne haka?"
"Nana nima ban saniba ina murna ne kawai" "Hmm kyama fadi gaskiya" "gaskiyar kenan Nana" sukayi dariya gaba daya. Kan kace me Labari yafara yada duniya cewar an kai sumame gidan karuwai, inda aka kamo hada wani uba da 'yarsa tareda yaronsa a gidan" nan da nan zance yafara zaga social media, da sauran kafafan watsa labarai, inda ake ta tir da Allah wadaran akan Alhaji Kabiru.
Nana takira Jalila a waya "Jalila Allah yasaki a Aljannah, kinceci rayuwata da sauran rayukan dasu Saleema sukaso lalatawa, Allah yabiyaki da mafificin Alkhairi, Allah yabaki miji nagari me kaunarki" "ba komai Zahra, Nagode sosai nima Allah ya amsa mana bukatunmu"
Alhaji Kabiru yashiga cikin matsanancin bakin ciki, yarasa msyake masa dadi, wai yarsa yakama da wanda ya amincewa wato jeje, abun bakincikin ankamoshi da yarsa a gidan karuwai, gashi ba'asan ainihin me yafaru ba amma zance yanata yada duniya, nan yashiga tunanin waima wacece wadda takirashi tace yaje gidanta ne, in akajima ya tuna yadda yaga yarsa da jeje, se ransa yakara baci, ya kalli Jeje yace "Jabir (shine ainihin sunan jeje) Allah ya isa tsakanina da kai, duk halaccin danayi maka a rayuwa amma ka lalata min yarinya" "dama can lalatacciyace, kuma halaccin dakayimin aiba kyauta kaimin ba aiki nake maka, shekaru nawa nayi inamaka bauta" "Au hakama zakace ko, zamu fita ai zakaga abunda zanyi maka, kasanni kasan halina" Jeje ya kalleshi "kabari kaga munfita lafiya tukuna, aisena bari munfita lafiya zaka samu damar yimin wani abu, dan haka sena fadi komai" zazzaro ido Alhaji Kabiru yayi, "me kake nufine wai?" inbaka ganeba seka bari sena aiwatar zaka gane".
Duk yadda su Sa'ada sukaso bakantawa Jalila rai bata kulasu ba dan karma su bata mata farincikinta, tabar musu dakin takoma na halima ta kwana a can, tun sassafe tai salla, sukayi aikace2 dazasuyi itada halima a cikin gidan, sannan ta tafi gidansu Jalal itada Halima, tunda Ilham tai arba da Jalila takejin kaman ta dau wuka ta kasheta, suka gaisa da Mummy ta nuna mata kitchen Jalila suka shiga suka fara abunda yakamata, aka jima Nana itama tabaro wasu sa'ada gidan ta tabiyosu Jalila a ranar suka hada snacks din dayakamata, sukabar aikin dabasu gama ba zuwa gobe, kafin bakin suzo sesu karasa, Nana da halima suka koma gida, Jalila ta tsaya tana jarasa gyara kitchen din, Jalal ya shigo da katon kwando cike da fruit ya ajiye yai waje abunsa, ta zauna ta shiryasu a fridge sannan ta tafi. Wahsegari da safe Jalila ta dawo, bata tashi halima ba daga bacci saboda taga alamar tagaji sosai jiya, ta dama kunun gyada, ta dibi nata a dan karamin flask ta tafi dashi.
Jalila tayi busy sosai a kitchen, dan bata samu ko karyawa tayi ba, dogon wandone a jikinta da rigarta har gwiwa me dogon hannu, ta daure kanta da dankwali, amma karshen gashin ta yafito, taji alamun ana kallonta, bata waigaba ta basar tacigaba da abunda take, cikin kitchen din ya karaso ba sallama ba komai yakama dube2, bata kulashiba tacigaba da aikinta ya jijjiga tea flask bakomai a ciki, tsaki yayi ya bude fridge yana kallon arrangement din datayiwa fruits din, still ya rufe fridge din, Jalila ta fuskanci yunwa yakeji, ta kalleshi "wai meyene?" "bansaniba"
"karka sani din" yaje ya duba kettle yaga akwai ruwan zafi a ciki, ya dakko ya zuba bako lipton, ya dakko madara da sugar yana kokarin antayawa, ita Jalila ma dariya yabata, ta dakko flask ta zuba masa kunun gyada a cup, ta zubamasa samosa, ta mika masa, bako kunya ya karbe, yanemi guri kan kujera a kitchen din yai zamansa yafara ci, itakuma tacigaba da aikinta, wayarta tafara ringing, sunan sweet hanny shine akan screen din wayar, tadaga wayar tasa a kunnenta "Hello sisyna ya kike" hanan tace "Hmm ba fada meyakawo gaba Baby, kin yadani, kin manta dani ko?" "A'a hanan ban manta dake ba, ko zan manta komai bazan manta da yar uwata ba"
"Anya kuwa Jalila? Kina guduna saboda inason Jawwad ko? Karki damu hakan baze shafi zumuncinmu ba, amma yakamata kikawomin ziyara, in duni6da gaskiya bekamata ace tunda kikabar kaduna baki kuma zuwa ba"
Kwalla ce ta taru a idon Jalila, cikin muryar kuka Jalila tace "Hanan bazan iya zuwa kaduna, bazan iya zuwa anguwarmu ba, Hanan hakan ze tayarmin da hankali, inzo unguwarmu ummi bata nan, bansan inda take ba, kiyi hakuri Hanan, amma kina raina daks da sauran mutane masu mahimmanci danake dasu a garin" takarasa maganar hawaye nabin idonta, "Jalila na fuskanci abunda yake damunki, inajin damuwarki a zuciyata, kiyi hakuri mucigaba da addu'a kinji, kidena kuka" gyada kai Jalila tayi kaman tana gaban Hanan, sannan tace "Nagode Hanan, kigaida kowa da kowa mussaman babana" "zasuji Insha Allah yar baba" ta kashe wayar, duk kokarin da Jalila tayi ta cigaba da aikinta amma takasa, tanata kokarin daurewa ta hadiye kukanta amma takasa hawaye ketabin idanunta, sosai Jalal yaji tausayinta ya kamashi, yaji inama ace shima zeji wannan kaunar da shaukin da y'aya sukeji game da iyayensu mata, har fuskar Jalila tayi ja. Tasowa yayi yazo bayanta ya tsaya yana kallon ta, dagowa tayi ta kalleshi suka hada ido, "Meyasa bazaki karbi kaddara a duk yadda tazo miki ba, memakon kiyi addu'a amma kike kuka, hakan bekamata ba, kizama jaruma mana" dauke kai tayi takuma fashewa da kuka wannaan karon hada sheshsheka, sunkuyowa yayi daf da ita a hankali yace, "Ummi tana raye, kuma zaki ganta very soon, jikina yana bani" da sauri ta kalleshi ya jinjina mata kai, yai mata alama
tasa hannu ta goge hawayenta, "da mutum yana da ikon sauya kaddararsa, kokuma kuka yana canza wani abu, da mutane dayawa sun fita daga matsalolin dasuke ciki, wani lokacin mukanyi kuka ne don samun sassauci a cikin damuwar da take damunmu, amma ta wata fuskar kukan yana karamana matsala ne da damuwa, ummi tayi rayuwa me tsayi ba tareda yan uwanta ba, kuma hakan besa wani abu yafaru da itaba, dan haka kema addu'a zakiyi kicigaba da hakuri " yana gama fadin hakan ya mike ya kai hannu ya juye sauran kunun gyadan nan ya juya ya fice, Jalila tabi bayansa da kallo, tai ajiyar zuciya tacigaba da aikinta jikinta a sanyaye.
Wajen karfe shadaya na rana mummy ta shigo tanayiwa Jalila sannu da aiki, Jalila tace yawwa" Mummy barka da safiya"
"Yawwa barka ya aikin?" "lafiya kalau Mummy nakusa kammalawa ma" "to masha Allah" Bayan Mummy tafita ba dadewa Jalila taje gida ta dakko wasu spices ta dawo, ta windowa kitchen dake harabar gidan taga Ilham tana zukar wani abu a kwalba da syringe tana tsirawa ruwan a jikin wani jan Apple, Jalila ta tsaya tana kallonta, tana gamawa ta maida shi cikin fridge ta rufe ta fita ba tareda ta lura Jalila ta ganta ba.
Se wajen karfen daya Jalila ta karasa girkin Abincin tareda taimakon Nana data biyota daga baya. Sun kammala komai sun gyara kitchen din kaman ba'ayi amfani dashi ba, suka fito itada Nana, daddy yana palour "Sannu da aiki yaran kirki, nasaku wahala ko?" Jalila tai murmushi "ba wani wahala daddy mun kammala komai ma" "Masha Allah, Allah yayi Albarka" Nana tace "Ameen daddy, amma ni gaskiya nagaji" "Aidama ke lazy ce Nana" sukayi dariya, daddy yace "Jalila amma in sunzo aizakizo kiga yan uwan yayanki ko?" murmushi tayi ta jinjina kai, daga nan suka fita suka tafi gida. Jalila ta gaji dan haka wanka tayi, Naja tana kan gadon ta baje, Jalila ta haye gadon ta kwanta itama, Naja ta kalli Jalila "malama meye haka? Bakiga nice a kwance agurin ba" "Eh banganiba, babu a house ko?"
A fusace Naja tace "amma kinsan karyane kicemin babau a house ko" "in akwai a house ai dabakiyi wannan shirmen ba, kodayake aiba mamaki a sha rashin hankalin nono" "kut me kike nufi?"
"inkika bari, nakuma bude baki da nufin mayar miki da martani sekinyi kuka, dan haka kiyi abunda ya dameki bacci zanyi" Jalila ta kwanta abunta, tabar Naja tana kallonta, can cikin bacci Jalila taji Nana tana cewa "Ke Jalila ki tashi, bakinku sunzo fa?" A hankali Jalila ta bude ido "wane bakin kuma?"
"Bakinsu Jalal mana, ki tashi yau zakiga yan uwansu, masu irin hancinsa"
Jalila takuma juyawa akan gadon tace "ni dan Allah ki kyaleni mana" "Ke Jalila kinada matsala wallahi, dan Allah ki tashi muje, akwai wanda nakeson gani a cikinsu, inajin kunya inje ni kadai" Jalila ta bude ido ta kalli Nana, "ikon Allah, Nana kinda damuwa, wallahi nikam ki kyaleni"
Nana tace "kar Allah yasa kije" "eh bazaniba" har Jalila tafara bacci, ta tuno Apple din nan, kartaje Ilham takuma zuba wani abu, zumbur ta mike, ta bude drower tasaka kayanta, tafito da sauri ta tafi gidansu Jalal, harabar gidan duk motoci, tundaga varrender take jiyo hayaniyar mutane, ta bude kofar palour a hankali, dayawansu kamansu daya da Daddy Jalal, duk haka suke da dogon hanci sosai aranta tace "tab wannan ko bata sukayi da wannan hancin nasu za'a ganesu" se yare sukeyi, ga Jawwad ma a cikinsu, shima se yaren ake dashi, tanaji daya yana tsokanar Nana, da wata irin hausarsa yace "gaskiya Nana kin girma kin ganki kuwa, waike yan mata tunoki nake lokacin kina dan karamarki" Nana ta dan zumbura baki "kajika Kaima ai da bahaka kake ba, ji yadda ka wani tara gemu, waikai dole ka girma" dariya sukayi gaba daya, daddy yai murmushi yace "Nana yaushe zaki dena surutu ne, bakinki baya mutuwa" kallo daya zakayiwa Jalal kasan yana cikin farinciki, fara'a yake sosai, 'yan uwansa duk nutsatstsu, amma shi yafita daban a cikinsu dan gashin kansa ba kyan gani, ga kallo daya zakayi masa kasan lips dinsa yana shaye2, setaji hakan ba dadi, a hankali ta sulale ta shiga kitchen ba wanda ya ganta, Tana tsaye a kitchen din Ilham ta shigo taci kwalliya sosai, gashi tasa wani turare me karfi, wanda sam bashida dadi, wani banzan kallo taiwa Jalila sama da kasa a wulakance, "Aikin banza jaraba da maita, tunda kingama abunda akasaki aisekikoma inda kika fito ko, ko yanzunma wani munafuncin zakiyi, shine kika dawo"
"Aini bana munafunci kaina tsaye nake abunda nakeso, Aikinne ban gama ba, nazo nakarasa wanda aikin da nakarasa yafi kowanne mahimmanci, na bata aikin wasu dan gyara nawa, kamar yadda nasha fada muddin aikin wani yashigo nawa, sena bata shi" kallon Jalila tayi cike da mamaki wannan karon kuma me take nufine, kwafa Ilham tayi tawuce ta
fara daukar kayan Abinci tana fita dasu, alhalin lokacin da Jalila take aikinta ko dauraye spoon Ilham bata tayata ba, Jalila ta tsaya tana kallonta tagama fita da kayam Abincin, ta dawo ta bude fridge tafara jera fruit a tray, tana kallon Ilham ta dakko Apple din nan tai masa guri na musamman akan tray din, tayi waje, Jalila tabiyo bayanta ta tsaya a window tana kallonsu, Ilham sewani iyayi take tana kwarkwasa, Jalila tayi mamaki da bataga Mummy ta fito ba, bakin su biyar ne maza hudu se mata uku, duk daka gansu kasan yan uwan daddy ne,
Ilham cikin iyayi tace
"bari kufara da fruits kafin kuci Abincin ko" cikin bakin daya shima me matukar kama da Jalal yace "Eh hakane gaskiyanki Ilham" tafara binsu daya bayan daya tana basu Apple, Jalila tana kallonta ta dauki Apple din nan ta mikawa Jalal, ya mika hannu ya karba shima kamar kowa dayake Apple yana daga cikin favorite fruit din Jalal. Jalila tana ganin irin kallon da Ilham kewa Jalal, Ilham na ganin Jalal yaci Apple din nan tafara murmushi. dawowa Ilham tayi da tray din ta ajiye a kitchen, har zata fita Jalila tace "bar murna karenki yakama zaki kinyi mantuwa" waigowa Ilham tayi tana kallonta, kawai taga Jalila tana jefa Apple sama tana cafewa
"Ilham kinsaba lamba, saboda na canza Apple din" a razane ta kalli Jalila, Jalila ta karaso gaban Ilham, ta kamo hannunta ta doramata Apple din, duba da kyau wannan shine Apple din dakika zubawa magani ba wanda yaci ba, ko baki gayamin ba nasan abunda kika zubawa Apple din nan na asiri ne akan Jalal, Ilham shi so ba'asiyan sa kuma sihiri be isa yabaki soyayya ba koya soki na lokaci kadanne, in abun ya barshi shikenan, yanzu meye ribarki a cikin cutar da dan uwanki? "

"Bakinsu Jalal mana, ki tashi yau zakiga yan uwansu, masu irin hanci
nsa"

68_

A razane Ilham ta cewa Jalila
" Ubanwa ya gayamiki wani abu na zuba a ciki, ke bayan munafunci hada sharri a lamarin naki, ai na dade da gano sonshi kikeyi, kalleki a haka kaman ta Allah amma tsabar rashin tsoron Allah da idona na ganki kina rungume Jalal, se anyi magana kice aike basanshi kike ba, in ba sonshi kike ba uban me ya kaiki jikinsa, meye naki nasamun ido iyee, munafuka kawai" Jalila tai murmushi tace "inkika daga murya kanki zaki tonawa Asiri baniba, danni ba ruwana, sannan dan na rungume Jalal, damace nasamu kema kije ya rungumeki mana inkincika mace" Jalila takarasa maganar tana dariya, tacigaba da cewa
"Ilham tsabar mugun abunkine yasa kullum idonki yake ganemiki abunda ze hanaki sukuni tsakanina da dan uwanki, amma ko makamancin so na wancan abun babu araina fatan kin gane, for now Jalal beci wannan tsafin ba sekije kiyi wani shirin kuma" tana gama fadin haka bata jira me Ilham zatace ba ta juya zata fita, Ilham tasa hannu ta janyota, ta waigo sukayi ido hudu, Ilham kaman ta fashe da kuka tace "wannan karon kinyi Nasara, amma ki saurari abunda ze biyo baya nan gaba"
"Idan har Allah shine abun dogaron mutum to a koda yaushe nasara tasace, dan haka inaji ranki, sannan kisani bani kadai yakamata kigabaya ba, Hanna ma tana nan tana target akanki, sekin kara tunani kin rarraba hankalinki, dan hanna bazata barki ba," Jalila ta fizge hannunta tai gaba abunta.
Ilham taji wasu hawaye na bacin rai suna bin idonta Allah yahadata da Jaraba, mezatayiwa Jalila ta huce ne? Gani take da za'abata wuka seta kasheta, ita hannah ba barazanace a gurinta ba Jalila tafi tsayamata a rai, da Jalal yaci abun nan da yanzu anmawo karshen komai, amma Jalila ta wargaza komai, ajiyar zuciya Ilham tayi "dole in sanar da umma abunda ke faruwa, na dauka zan iya shawo kan lamarin nan amma abun yafi karfina"
Jalila kam takuma silalewa ta fice ba tareda kowa ya ganta ba ta tafi gida. Koda Jalila takoma gida, sabgoginta ta shigayi, amma takan tuna nasihar da Jalal yaimata dazu, babban abunda yabata mamaki yace jikinsa yana bashi ummi tana raye fatanta Allah yasa hakane ummi tana raye, har akayi sallar isha'i sannan Nana ta dawo gida, da fara'arta ta tafi gurin Jalila ta zauna, Jalila ta kalleta "se yanzu kika dawoko? Dan kinga Abba bayanan" "Aiko yana nan baze hananiba, Allah sarki Yaya Jalal se murna yake yaga yan uwansa"
"Hmm Nana ai dan uwa dadi ne dashi, sedai abun tausayin naga yan uwannasa duk nutsatsu amma banda shi"
"ya akayi kika gansu bayan kina gida?" "naje naga palourn a cike bazan iya wucewa ba dan haka na dawo" Nana ta dan girgigiza kai "bari kawai Jalila, Jalal abun tausayi ne, Allah ya kyauta kawai" daga nan Nana bata kuma cewa komai ba ta tashi, ta bar dakin
Jalila ta dauki wayarta ta hau internet, batun abunda yafaru da Alhaji Kabiru ya zaga duniya, hada masu kara abunda ba'ayiba, yan makarantarsu Jalila kuwa se murna suke da kama su Sameera da akayi suke, dama dayawa suna jin haushin su Saleema, sabida yadda suka gallabi makarantar, ga bata yaran mutane dasuke, se zancen ake tareda Allah wadaran da suu saleema ace ankamaka kaida mahifinka a gidan karuwai,
Jalila tace dole taje station din da aka kai su Alhaji Kabiru, kuma yanzu amfanin Yallabai Sulaiman yazo. Don kuwa setayi me yuwuwa ta tabattar da ta kawo karshen Jeje da Alhaji Kabiru, taji dadi da Allah yasa aka kama da jeje a wannan kamen, Dagashi har Alhaji Kabiru sesunyi danasanin shiga gonarta, Tagama abunda takeyi tana shirin kwanciya, sa'ada tace "ya haja? Ba dakin halima zakije ki kwana ba ai dakin zaki barmana malama, mu a ina zamu kwanta" shiru Jalila taimata tana kokarin jan bargo, Naja tasa hannu ta rike bargon "malama maganafa ake miki, ki tashi ki bamu guri kitafi dakin yan aiki ku kwana a can dan bazamu kwana dake a daki daya ba" mikewa Jalila tayi a zaune, ta kalli su Naja "da Abba yake gina gidan nan gudunmuwar nawa ubanku ya bayar" bude baki sa'ada tayi "ke karki sake ki zagarmana uba wallahi, dan kika zagi ubanmu semunyi kasa2 dake"
"inna zage shi mekuka isa kuyi, aiba karya nayiba, in ya kawo gudunmuwa lokacin da ake gina gidan nan ku fadi nawane a biyaku, kudena min gori, inkuma bebada ko sisi ba, kar shashar data kara cewa inje in kwana a dakin me aiki, tunda ba da gudunmuwar tsoho a gina gidan alfarma akemuku, koni nawa iyayen ba mutane bane da kuke zaginsu ? Inkun ji haushi a daren nan kukoma gidan naku iyayen, kuma wallahi duk wadda takuma yimin maganar banza sena gayamata maganar dabazata iya bacci ba" ta juya ta kwanta akan pillow tana murmushi. Haka suka hakura suka tafi dakin Maama suka kwana a can, dan Jalila ba karamin taurin kai gareta ba.
Hannah duk ta rame sabida dorawa kanta masifar son Jalal dakuma kishinsa, tayiwa kanta alkawarin muddin bata aureshiba sedai ayi biyu babu, dan in har tana raye bazata bari ya auri wata mace ya zauna da ita ba, kodai ya aureta cikin dadin rai, kokuma ya aureta kota tsiya, yanzu yazma dole ta hada kai da jeje, ta yaudareshi su hada kai taga bayan Ilham, Ita Jalila nata me saukine, Ilham ce tafi tsayamata a rai, ta dakko wayarta taita kiran lambar Jeje, amma taki shiga, tayi2 harta gaji ta hakura, da niyyar gobe taje ta sameshi, (bata san ankama shi ba)
Da sassafe wayar Jalila tafara ringing, cikin magagin bacci ta kai hannu ta daga wayar, muryar Jawwad taji "Am sorry baby na tasheki ko?" ya fada a hankali
"bakomai Yayana, fatan ka tashi lafiya"
"Lafiya kalau, hope kinyi bacci me dadi?"
"Alhamdilillah yayana" "yawwa baby wata alfarma nake nema a gurinki"
"fadi kanka tsaye komenene indai zan iya dole ayi shi"
"Yawwa baby, kinga a gidansu Jalal na kwana muna tareda su mahmud, gari ya waye babu alamar Mummy zata basu breakfast, na shiga cikin gidan yanzun naga ta kulle kitchen dinta, daddy kuma ya fita kiran gaggawa da akayi masa da asuba ya tafi Abuja, to banason Jalal yasani, dan Allah ki dafa abunda yasamu abawa bakin nan" mamakine ya cika Jalila to meyasa Mummy zatayi haka, meye ma'anar hakan datayi, ajiyar zuciya Jalila tayi
"bakomai karka damu, zan hada abunda ya sawwaka inkawo"
"Yawwa Baby, Allah yayi miki Albarka"
"Ameen bloody" gajiyar jiya bata saki Jalila ba. ta tashi ta tafi kitchen ta dora girki, ba a dade ba Nana ta fito taji karar kwanuka a kitchen ta leka setaga Jalila nata fama a kitchen "Jalila kekam meyasa ba kyason hutawa rankine, da sassafen nan kowa na bacci kekina kokawa da kwanuka, gashi gajiyar jiyama bata sakeki ba"
Jalila ta gayamata duk abunda yafaru, Jinjina kai Nana tayi tace "Tabdijan itakam har yanzu Mummy abu baya wucewa a gurinta, to Allah ya kyauta"
Da mamaki Jalila tace "meye baya wucewa a gurinta? " Nana tace
"manta kawai, bari inzo in tayaki, bekamata kiyi aikin keka dai ba" Nana ta tayata suka karasa aikin, duk yadda Jalila taso Nana tagayamata wani abu, amma Nana taki ta basar da zancen. Maama tafito kitchen zata dauki plate,
Jalila tace "Maama ina kwana" "lafiya" shine amsar data bawa Jalila, ta kallesu "wai wane irin girkine da har yanzu ba'a gama breakfast ba"
Nana tace "Yaya Jawwad ne yasamu aiki, mummy tahana bakinsu Abincin safe" dan zare ido Maama tayi
"Are you serious, ita har yanzu bata dena wannan abunba? Itama dai Mummy by now yakamata ace komai ya wuce, kodan danta, amma Ai shikenan"
Se Karfe tara na safe Suka gama aikin Abincin, suka dauka suka kai gidansu Jalal, a palour suka tarar da wata mata me fara'a, tana kama da daddyn Jalal sosai, zatayi shekara talatin da biyu,
Jalila bata santa ba amma dagani tasan yar uwar daddy ce, Nana ta santa, suka gaisheta, ta amsa musu cikin fara'a, suka tsaya suna hira da Nana,
Jalila bata da saurin sabo, gashi bakomai take ganewa a hausar matar ba, dan haka Jalila ta mike takoma gida ta dakko sauran kayan, tana dawowa tundaga harabar gidan tafara jiyo hargowar Jalal kaman a filin yaki, a ranta tace "jarababbe Allah yayi dare gari ya waye a gaban mutanen ma baze dena wannan jarabar ba" tana shiga palourn ta ganshi a tsaye a gaban Mummy idonsa jawur yana surfa masifa, wata mekama da wadda suka tarar a palour dazu tana rikeshi tana masa magana da yarensu, cikin fushi yake kallon Mummya yana cewa
"Wace irin macece ke mara Adalci, ai Abincin banakibane ba dazaki hana 'yan uwan babana ci, kodaga gidanku aka kawoshi, amma kinsan ki diba har kibawa wanda basu kamata ba, akanme dan uwansu ne yake nema yakawo zaki hanasu Abinci, ke wace irin mara adalcicene meyasa kika fiye sonkanki, su basuyi fushi dakeba seke zakiyi dasu, why? Mummy why? Wace irin zuciya ce dake haka"
Mummy tace "Jalal nikake ciwa mutunci agaban mutane, kake zagina a gaban mutanen daba kaunata suke ba, nikake gayawa wannan miyagun maganganun, uwarkace nifa nikake ciwa mutunci haka" takarasa maganar tana hawaye, jiyo hargowane yasa Ilham ta fito da sauri daga dakinta, don ganin meyake faruwa, ta tarar Jalal yanata baka'i
"Eh nayi din, dan sunfiye minke a matsayin uwata, haifata kawai kikayi amma sam bakisauke hakkinki na uwaba meyasa kikazamo uwa a gareni, a rayuwata sam banyi dacen uwaba, kowani da yana farinciki yana murna in aka ambaci uwassa amma bandani Jalal, baruwanki da ya rayuwata zata kkasance se cikar miyagun burikanki sukikasa a gaba, har yau kinkasa yin nadama akan rayuwar da nakeyi saboda rashin kulawa irin taki, dakuma laifukan dakika aikata a rayuwarki, wallahi mahaifina da danginsa sun fiyemin ke wallahi" cike da masifa da bacin rai Jalila tafara magana
"ABDUL JALAL Kaji kunya wallahi, agaban mutane kake gayawa mamanka wannan maganar, ba ladabi babu da'a ba komai, kome tayi maka tunda tariga takawoka duniya tagama yimaka komai, kalli 'yan uwanka dasukazo kowa a nutse tunda ga fuskarsu shigarsu da kamalarsu amma banda kai, ta yaya kake tunanin zaka cigaba a rayuwa da wannan wulakancin da kakewa mahaifiyarka,kana tozartata kana nunawa duniya kai baka da tarbiyya, tirr da hali irin naka Jalal, Allah ya shiryeka inme shiryuwa ne, ba yadda za'ayi kaga haske ko cigaba a rayuwarka alhalin kana tozarta mahifiyarka, tir da halinka wallahi"
A mugun fusace ya juyo, ya kalleta ido cikin ido, kan Jalila yayo gadan2, itakuma taki motsawa balle ta gudu, kafin ya karaso gurinta, matar dazu dasuka tarar a palour tashiga tsakaninsa da Jalila, tana girgizamasa kai "Allah ya huci zuciyarka, kayi hakuri, ka kyaleta"
Yare ya canza yana magana,ya cigaba da tunkaro su idonsa jawur cike da masifa, tareda kwalla, ya nuna Jalila yanawa matar magana da yarensu, a cikin maganar da Jalal yake taji ya ambaci sunanta, JALILA!!!
Abunda tunda take bata tabajiba, sedai yace mata ke, koyace wannan yarinyar kokuma yacewa Jawwad kanwarka,
Matar tacigaba da bashi hakuri da yarensu, ta kalli dayan tace "mahmud jashi kufita, kabashi hakuri" Mummy tuni tabar palourn yayinda Ilham agabanta akayi komai, Nana ma rasa bakin magana tayi,
Matar nan taja hannun Jalila suka fita daga palourn, bayan gidan taja Jalila ta zaunar da ita akan wasu fararen kujeru, sannan itama ta zauna ta kalli Jalila tace
"Dama kece Jalila?" Cike da mamaki Jalila ta kalleta "Eh nice, ya akayi kika sanni?" Ajiyar zuciya matar tayi tareda murmushi, "kece baki sammu ba, amma mu duk munsanki ai"
"Amma naga bamu taba haduwa ba, ya akayi kuka sanni"
"ba abun mamaki baneba Takwararmu, duk family dinmu munsanki, amma meyasa kikewa Jalal hakane?" da mamaki Jalila ta kalleta
"me nayi masa kuma?"
"duk lokacin dakika bata masa rai seya gayamun, kina yawan sakashi fushi meyasa?" dan dauke kanta Jalila tayi tace
"Anty Jalal baya kyautawa abunda yakeyi, kullum yana jefa rayuwarsa a cikin hatsari, ace mutum yakai munzali kaman Jalal amma ace kullum cikin sa'insa yake da mahifiyarsa bekamata ace yana daga mata murya haka ba? Banda sauran abubuwa dayake dabasu dace ba, kema kinsani, amma meyasa bakwa zuwa inda yake maybe dakuna zuwa da ganinku zesa yarage wasu abubuwan da yakeyi, rayuwarsa ta gurbace dayawa, baya ganin girman kowa, shaye2 shine babban abokin rayuwar Jalal, be damu da ibada ba sam, ko abokan kirki bashida su sena banza, yayi shaye2 a club yayi a gida, kuma ko a gaban waye, baya ubangiji, da sauran abubuwa marasa dadi dayake aikatawa"
Ajiyar zuciya matar tayi
"Jalila tabbas maganarki gaskiyane, Jalal baya kyautawa duk rayuwarsa ta gurbace, amma meyasa kika damu akansa haka?" Jalila tace
"nima bansaniba, kawai dai soyayyar da Jawwad yakemasa ne, dakuma kokarin dayake dan ganin Jalal ya shiryu yasa banajin dadin abunda Jakal yakeyi"?
"kin taba tunanin meyasa babu soyayya da tausayi na da da uwa a tsakanin Jalal da mahifiyarsa?"
"eh nayi wannan tunanin, amma nakasa samun amsa, nayi2 Jawwad yagaymin amma yaki"
"meyasa baki tambayi Jalal dinba?" zare ido Jalila tayi "taya zan tambayeshi nida muke fada, ya shakeni a banza" murmushi tayi "baze shakeki ba Jalila" Jalila ta kalleta
"tab lallai wallahi ze iya shakeni, har dukana yakeyi" matar tayi murmushi "Jawwad yacika dan uwa nagari, daya boye sirrin Jalal, dukda a yau zamu bar kano, zamu koma garinmu, tunda matar gidan bata son zuwanmu, amma yanzu a takaice zan baki labarin waye Jalal, sannan ya ingaya miki ya akayi muka sanki, idan nabaki labarin sekiyi masa alkalanci"
Please pray for me zanfara exams, dana kammala zan cigaba da posting insha Allah
Comments nakeso ba sticker ba kokuma just thanks

69_

WANENE ABDUL JALAL???!!!!!
Khadija munir shine cikakken sunan mahaifiyar Jalal, malam munir shine mahaifinta suna zaune a unguwar dorayi dake cikin garin kano, malam munir malamin makarantar secondary ne, sannan yana yan sana'oinsa domin rufawa Iyalansa asiri, yanada mata uku, hauwa itace uwargida, se sadiya itace matarsa ta biyu, da zulaihat itace matarsa ta uku, yanada yara goma sha uku, khadija 'yace ga sadiya matar malam munir ta biyu, khadija su ukune agurin mahaifiyarsu, itada yayyenta maza biyu, Abubakar da Aliyu, itace yarinya ta tara a gurin mahaifinsu, khadija tana da kyau daidai gwargwado, wanda har wasu suke cewa duk tafi yaran gidan kyau, dukda kasancewar ta ba fara tas ba amma tanada kyau, khadija yarinyace mara kunya, bata dagawa kowa kafa, duk wanda yayi mata duk yarintarsa duk tsufansa zeta cimasa zarafi babu ruwanta, tun yayyenta na kamata su daka intayi rashin kunya harsuka gaji suka kyaleta, saboda rashin mutuncin ta bata bar kowaba ciki harda matan babanta da yayyenta, mahaifiyarta ta sangarta ta kasancewarta ita kadaice yarinyarta mace, duk wanda ya daki khadija ranar se anyi tashin hankali da mahaifiyarta, har kirari takewa khadija cewa "ni 'yata matar manyace, se wanda yaci yatada kai zan bawa, dan khadija na ba kalar talakawa bace" hakan yasa abun yafara tasiri a zuciyar khadija tun tana yarinya, takejin cewa kota isa aure seta samu me kudi zatayi aure idan kuwa bata samu me kudiba, gara ta tsunduma ita tanemi kudin dan bazata iya auren talaka ba, kuma batason rayuwar wahala.
indai khadija nason abu, kaya kona uban waye koda kudi ko a bashi, mahaifiyar khadija zata siyamata su.
Saudat kanwace ga khadija sakuwarta ce khadija tabata shekara daya da rabi, ita saudat 'yace ga zulaihat amaryar malam munir, itace ta biyu a dakinsu, wani lokacin suna matukar shiri ita da khadija saboda halinsu yazo daya dukkaninsu tsagerune, Sedai Khadija tadama saudat ta shanye a tsageranci, dukda wannan shiri dasukeyi baya hana in tsiyar khadija ta motsa tayiwa babar saudat rashin mutunci a hadu aita masifa a gidan nan, makaranta da yan unguwa babu wanda besan halinta ba, karamin aikintane ta zagi malami agaban dalibai, in an koreta mamanta seta canza mata makaranta, dama islamiyya tuni ta dena zuwa, a cewarta tunda tasamu na salla shikenan, dan bazata jure wannan masu gemun kaman brush suna dukan kyakyawar fatarta da fatar bunsuru ba, abun dukan doki, malam munir yayi iyayinsa gurin ganin khadija ta nutsu amma abu yaki yuwuwa,
Abinci se wanda taga dama zataci, sutura se wadda takeso zata saka, wani wanki da guga almajiri uwatta take biya yayiwa khadija, haka dai rayuwar khadija ta tashi a mugun sangarce, ga rashin tarbiyya.
Tun tana jss2 tafara samari, inda a nan ne ta hadu da saurayinta Kabir, Kabir yana matukar sonta kaman yayi hauka, Kabir marayane, mahaifinsa ya rasu, dagashi se mamansa da kannensa mata biyu, shikadaine namiji gashi mahaifinsa bebarmusu wani abun kirkiba se gidan dasuke ciki, seyaje yayi aikin wahala yake samo abunda zasuci yake biyan kudin makarantarsu, tunda yafara soyayya da khadija abubuwa suka fara tabarbarewa saboda yawan bani2, yazamana da kyar yake iya morawa mahaifiyarsa da kannensa wani abu sedai yayiwa khadija haka yadinga dawainiya harta shiga sss, nan manyan mutane suka dinga fitowa suna sonta, duk cikin manemanta babu wanda yayi mata saboda ita burinta ta auri, namiji kyakyawan gaske sannan wanda ya tada kai da naira, sannan tanada burin tazaga duniya, tayi ilimi me zurfi a kasashen waje, yadda zata goga kafada da manyan mata a kasar Nigeria dama nahiyar Africa gaba daya, shiyasa duk wanda yazo indai yanada kudi zata wankeshi son ranta sannan ta sallemeshi, dan har yanzu bataga dai dai da itaba, malam munir yayi iya yinsa dayimata nasiha itada yar uwatta saudat amma abu ya gagara, ana cikin wannan haline Allah yayiwa malam munir rasuwa, mutane sunji mutuwarsa saboda mutumin kirki ne kwarai dagaske, bayan an gama makoki khadija tacigaba da tsiyarta daga inda ta tsaya, ganinda Kabir yayi masu kudi na neman aurenta yasa kara zage damtse, dayasamu kudi ko anmusu albashi dayake yasamu aiki a wani kamfani, seyaje ya kashewa khadija su, har rawar jiki yake wasu kudin sushigo yakuma kaimata, alhalin gidansu wataran se a kwana biyu ba a dora tukunya ba, se ayi term biyu ana korar kannensa saboda kudin PTA, amma baze iya basu ba sedai khadija.
Mahifiyar Kabir ta zubda hawaye ba'adadi amma bayadda ta iya da wannan hali na ko inkula da danta Kabir yake musu itada kannensa, sam takasa gane kansa.
In khadija ta dau wanka ta taho seka dauka wata yar hamshakin Attajiri ce, saboda 'yar kwalisa ce ga karya data dorawa kanta, khadija tayi candy amma taki cigaba da makaranta tace seta auri mekudi zataje abroad tacigaba da karatu, sabida abun kunyane a ce nan gaba intazama wata a Nigeria ace za' ayi interview da ita tace a Nigeria tayi karatu.
Yauma yammace taci uban ado tana taku kamar tana taka kwai, taji anamata horn da babur amma tayi banza taki matsawa, mutumin yadinga horn amma taki ko daga kai balle tabashi hanya ya wuce, parking yayi ya kalleta yace "baiwar Allah kokurma ce ne? Inata horn kibani hanya zan wuce amma kinyi banza" wani mugun kallo tayi masa, "idanni kurma ce kaikuma mara hankali ba" zaro ido mutumin yayi saboda yasan a haife ya haifi wannaan yarinyar
"nine mara hankalin yarinya?"
"kwarai kaine mara hankali, ya za'ayi ina tafiya zaka isheni da horn da wannan rubabben gwangwanin naka, kana nema ka kashemin dodon kunnena, aida seka tsaya in wuce, kokuma ka canza hanya, tunda bakai ka gina hanyar ba ai"
"Amma kina ganin ya dace ki kirani mara hankali da girmana da komai"
Cikin tsiwa tace "to semenene? Ai abun rashin hankalin kayi"
"shikenan in abunda kikayimin dai2 ne za'ayiwa mahaifinki kiji inda dadi"
"to ya mutu wata uku dasuka wuce, inkuma kabarin za'abishi ayi masa se inji, aikin banza mutane suyita abu kaman wasu yan kwaya"
Cikin rawar murya yace "nine kaman dan kwayan"?
"kaimana da dawani nake, wayasanima ko ita kaje kasha, kake nema kayimin akuya nonsense" tayi gaba abunta, mutumin nan seda ya zubda hawaye, ya kunna babur dinsa yazo daidai saitin khadija ya tsaya ya kalleta yace "Insha Allah sekin haifi dan kwaya, sekuma ya miki abunda kikayimin"
"kai kasani, koma kwayar zan haifa, shirmen banza kawai, adai dinga kula, da irin kwayar daza'asha in bahakaba a kare a gidan mahaukata" bataji mezece ba tayi tafiyarta.
A fusace ta shiga gida tana ta mita, saudat na tsakar gida tana danna waya, ta dago ta kalli khadija tace "Ahh kaga manyan mata a gidan Kabir ya akayine, waya taboki kike mita?"
A wulakance khadija ta kalli saudat, "waye kuma kabir, karki kara hadani da wannam matsiyacin, a tunaninki mace mai daraja kamarni zan iya auren wani Kabir, tausayinsa kawai nakeji wanke dan banza zangama, da zarar nasamu my dream hubby inyi dumping sha3 aside inyi aurena, idan na auri wannan fakirin ta ina burina ze cika" murmushi saudat tayi, "angaisheki matar manya, banga laifinkiba, nima ina bayanki wayakeso
talauci ai kudi kawai alaji, amma meya bata miki rai haka?"
Nan khadija ta gayamata abunda yahadata da wannan mutumin, saudat tace "ke manta dashi, kinsan irin wannan mutanen, basa raina abun magana"
"aikuwa yajawa kansa dan sedana masa rashin mutunci naji dadi a raina" sukayi shewa gaba daya, uwar gidan malam munir tana jinsu tace
"khadija baki kyauta ba abunda kikayi"
Khadija ta murguda baki "ai dama banyi dan in kyauta ba, kinganni ba ruwana, da kusanci, ko girman mutum ana mun nake ramawa ehee"
"to Allah ya shirya"
"Ameen ya shirya abunda yafi hakama".
Haka rayuwa tacigaba da tafiya, khadija tana gwara kan samari, yau ta wanke wannan gobe ta wanke wancan, ba wanda yake da ikon yin Magana, gefe dan wahalarta wato kabeer yanata faman wahalta mata, uwarsa da kannensa kuma ko oho.
Yau ake sa ran za'a kawo kudin auren kanwarsu khadija, wato surayya babbar yayarsu maryam tanatayiwa khadija da saudat fada akan su tsaida miji sudena wannan shiriritar, zumbura baki khadija tayi "waike Anty Maryam akanki muke zaune ne? Duk kinbi kin ishi mutane, itakanta surayya guda nawa take za'ayi mata aure, yarinya da kuruciyarta shekara iyanzu ta haihu, ga mijin shiba kudi ba, gaba wani ilimi me zurfi duk tabi ta tsofe da wuri" bude baki Anty Maryam tayi "lallai sannu khadija, surayya ce tayi yarinta da aure, kuma shi arziki na Allah ne ai, sannan ita ya mace darajarta shine dakin mijinta, ba gararamba a layi tana tara samari ba"
"eh ansan arziki na Allah ne amma ba wanda yakeson talauci ai, tara samari yanzu muka fara semun wankesu munci rabonmu mayi auren"
Saudat ta kwabe baki sannan tace "batta ai ita na fuskanci so take kowama yayi rayuwar wahala kaman yadda tayi, kuma babu wannan zancen"
Anty Maryam dataga abun nasu dagaske suke tace "to Allah ya baku hakuri matan masu kudi"
Khadija tace "Ameen Anty Maryam, Allah yabamu mutemakamuku tunda ku baku da rabo" suka kyalkyale da dariya itada saudat. Ana haka sega surayya ta shigo dakin goye da yarinyar Anty Maryam tace "Anty kinga
humaira tayi bacci a bayana gaskiya na iya raino" Anty Maryam tace "Aikuwa dai kin iya raino, badi iyanzu in Allah ya kaimu Insha Allah kinkusa haifar naki" rufe ido surayya tai tace "gaskiya inajin kunyarki Anty maryam amma dai Ameen" dan zaro ido khadija tayi "au kekinayin auren zaki zage kiyita barin yara sekace kazar hausa"
Saudat da sauri tace "ganemin hanya dai"
Surayya tace "to meye a ciki yaya khadija, yara rahama ne bakasan wanda zaka huta dashi ba"
"Ai seki zage kibada himma, ga auren talaka ga haihuwa, nan da nan ki ragwabe akasa banbance tsakaninki da mamanki, kinga bari in tashi in je in abunda yake gabana wannan batamin rai zatayi" khadija ta fice daga dakin, Anty maryam ta girgigiza kai "Surayya kyale wadannan sunyi nisa basajin kira, se fatan Allah ya shirya". Haka rayuwa tacigaba har akayi bikin surayya, yayinda su saudat duka dorawa ransu dogon buri musamman khadija, bata saurarawa duk wani saurayi da yashigo hannunta, duk tsiyarka duk arzikinka seta wankeka sannan ta sallemaka, amma duk da haka tana tare da Kabir, sha wuyanta kuma yana cigaba dayimata hidima iyakar yinshi, ya wofantar da mahaifiyarsa da kannensa.
Kawayen saudat sun san khadija sosai, duk da kasancewarta me izza da jin kanta, ko kawayen kirki khadija bata da su se yaran manyan masu kudi, yaran masu kudin ma se yarinyar da akasan ubanta wanda ya tara dukiya sannan tayi kawance dake.
Ranar wata laraba suna zaune, saudat tayi bakuwa, kai daganin yarinyar kasan kudi sun zauna, saboda ba tayi kalar wahala ba, motar da aka kawota ma a ciki ba karamar mota bace, kawar saudat din me suna Salma ABDUL JALAL Tajudden, kawar saudat ce sosai tasanta da dadewa dasuka hadu a gurin wani biki, khadija tanajin sunan salma a gurin Saudat, tana bata labarin kudin da familyn su salma ke dashi, bayan Salma sun gaisa da mutan gidan, taciro iv card a Jakarta ta bawa Saudat tace "ga iv din nan, saudat dan Allah kizo gurin bikina saura three weeks" saudat tace "Insha Allah zanzo, ashe abun yazo yama za'ayi kice bazanzo ba bayan nayi duk ankon bikinki"
Salma tayi murmushi tace "Ainasan halinkine saudat, yanzu in bakiga dama ba sekice bazaki ba"
"zanzo Insha Allah"
"kinga bari inyi sauri, akwai guraren danake son zuwa, se anjima" har Salma ta mike zata tafi, khadija tace "Salma ni baza'a gayyaceni ba, anyway ina miki murna Allah yasanya Alkhairi" murmushi salma tayi "ni na isa, kema ga naki, ina gayyatarki yaya khadija" ta mikawa khadija iv, tasa hannu ta karba, bayan fitar Salma suka duba iv din nan, kwana bakwai cif za'ayi ana bikin nan, khadija tace "Saudat wai ita kam wannan wazata aura haka"
"mhmm yaza'ayi insani khadija? Najidai ance dan uwanta ne, boyeshi take kaman ciwo batason aganshi, iya sanina da ita tana son gayen nan kaman ranta, ko sunansa bata fada, kinga jikin iv dinma sunan tane kawai, Allah ya kaimu bikin dai muje muga wazata aura haka"
"Ainima dole inje bikin nan, dan naga alamar irin bikin da nake sone, dan haka dole a kece raini, muyi wanka kaman yaran senetes, inje inyi sababbin kamu" dariya sukayi gaba daya suka tafa. Kafin lokacin bikin Khadija tasa Kabir a gaba, seda yasamomata kudi kusan dubu arba'in ta sai less din dinner, ta dinga bin samarin ta, tana karbar kudi a gurinsu da haka seda ta sai komai sabo, tayi anko kafin lokacin bikin nan
Ranar da'aka fara biki, khadija da saudat sun dau wanka, kaikace sune dangin amaryar, khadija takira wani saurayinta yazo ya daukesu a tsaleleliyar motarsa, ranar kamu da bridal shower, da mother's evening duk ango bezoba, amma anci an sha, anyi barin kudade, kai dagani kasan wannan family sunci sun tada kai, naira ta koka a wannan bikin, gasu kyawawa kaman su sukayi kansu, daga mazansu har mata, gasu dayawansu ba farare baneba amma sunada matukar kyau, sunada dogayen hanci mazansu da matansu, wanda hakan ze tabattar maka family dayane, saboda suna kama da juna, khadija tayi samari a gurin bikin nan, saboda tayi kwalliya tayi kyau harta gaji, kaman uwa daya uba daya suke da amaryar, bangaren saudat ma hakane tasamu samari a gurin bikin.
Ranar dinner hall ya cika taro yayi taro, manyan mutane maza da mata daga bangarorin Nigeria sun halarci bikin, Mc yabada announcement cewar ango da amarya zasu shigo, nan aka shiga yimusu kirari "Ango Alhaji Habib kamal tajudden, matashin Attajiri me ji da kansa, me gwalagwalai da zinare, Ango kayi dacen amarya hajiya salma ABDUL JALAL Tajudden, me kyautar zinare da dama hagu bata saniba, me ado da
sarkar zinare, abu naku maganin a kwabeku" haka aka cigaba da yimusu kirari tareda saka musu kida flower girls ne suka fara shigowa, se wasu kyawawan 'yan mata sannan ango da amarya a tsakiya.
Amarya da ango sun hadu, sunyi kyau harsun gaji, tunda khadija tayi tozali da angon nan tarasa nutsuwarta, ya
hadu karshen haduwa bata taba zaton akwai kyakywa a maza irinsa ba, da farine toda tabbas zaka iya rantsewa kace bayajin hausa, wannan shine irin mijin datake tsarawa zuciyarta tana son aure, wanda bata taba zaton ganinsa a gaske ba, Habib ta maimaita sunansa a hankali kaman yadda taji Mc yafada dazu, gumi taji yana tsatstsafo mata a goshi. Shikam ango se fara'a yakeyi cameras kota ina se hotuna akeyimusu, Saudat ta janyo hanun khadija sukaje suka dinga hotuna da ango da amarya, bayan sun dawo gurin zamansu ne saudat tace "khadija kinga wannaan bawan Allah kaman shi yakera kansa, dan Allah ga kyau, wallahi yafita kyau sosai" da kyar khadija tace
"mhmm aikam dai yana da kyau" duk bata cikin hayyacinta, haka aka gama dinner din nan aka watse, a hanya khadija tacewa saudat "Sauda amma Salma ba hausawa baneba ko?"
"eh to rabinsu hausa rabinsu kanuri, yan borno ne, kasuwanci yakawo wasunsu kano"
"lallai kam, gasu da kyau gasu da kudi" haka suka cigaba da hira har sukaje gida,ranar khadija kwana tayi tana tunanin habib, tareda mafarkinsa.
Suncigaba dazuwa gurin bikin nan har akayi akagama. yayinda kullum khadija insukaje suka dawo, soyyaya da tunanin habib ya cigaba da ninkuwa a zuciyarta.
Ranar daza akai amarya, juyin duniya saudat tayiwa khadija akan suje kai amarya tace bazata ba, tun tana lallabata har itama ta hakura tace tafasa zuwa gurin kai amaryar, taje daga baya, in Salma ta tare. Ranar Khadija ta kwana da matsanancin kishin Salma, kasa bacci tayi daren ranar dan tayi mamaki yadda kaunar habib ta mamaye zuciyarta lokaci daya haka, haka ta kwana sake2 da tunani har gari ya waye. Koda gari ya wayema bata fito tsakar gida ba tana tana kan gado tana juyi Saudat ta shigo dakin tazauna gefen gadon ta kalli khadija tace "yar uwa tashi muyi wata magana kibani shawara dan Allah" khadija ta kalli saudat idonta duk yayi ja alamar rashin bacci, ta mike zaune ta dan yatsina fuska ta kalli saudat "fadi inajinki?" Saudat ta gyra zama tareda kallon khadija sannan tace "Khadija nifa tunda mukaje bikin salma, nayi ido hudu da mijinta naji wallahi inasonshi, shiyasa nazo kibani shawara yazanyi, Dan gaskiya bazan iya hakuri ba, bazan iya auren kowa ba seshi, dan Allah sister bani shawara ta ina yakamata in fara?"
Gaban khadija ne yafadi, zuciyarta ta shiga bugawa da karfi, ga wani gumi dayake tsatstsafo mata a iya goshinta, taiwa Saudat wani irin kallo, sekuma tayi murmushi seda hakoranta suka fito, ta kalli saudat" Kin tabatta kinason Habib? " da sauri Saudat tace" Wallahi khadija so bana wasa bama, wallahi ina sonshi, aurensa nakesonyi" khadija ta gyada kai takuma yin wani murmushi

70_

Ta dafa kafadar saudat "bakida damuwa zanyi meyuwuwa inga burinmu yacika, amma kisani dole abu daya yafaru, ko kiyi nasara, kokuma akasin haka" "hakane amma ni nafi sa ran nasara dan kome zefaru sedai yafaru"
"gara kidinga sawa ranki nasara da akasin haka, yanzu dai macigaba anjima, inada abunyi yanzu"
"to shikenan bari zan dan fita dama, sena dawo"
Saudat nafita khadija tabi bayan saudat dawani mugun kallo, sannan tayi kwafa "gaskiya Saudat bakida hankali, kekin isa inso abu kema kice kinaso, zakiga tsiya dake zanyi tarkon cikar burina, ita kanta Salma seta barmin Habib" ta sakeyin kwafa ta nemi guri ta kwanta.
Sati daya da kai Salma gidan habib, Saudat ta shirya taje gidan Salma, ba karamin tsinkewa Saudat tayi ba da ganin aljannar duniyar dake gidan Salma, gidane na alfarma kaman ba a Nigeria ba, ga shi an kashe masa kudi da kayan alatu, haka Saudat ta sake taita kallo tana video gidan dan ta nunawa Khadija, bangaren kayan Abinci ba a magana, tasamu kyakyawar tarba daga salma, ta karramata da kayan Abinci sukayita hira Saudat tace "Salma kawo in turamiki hotunan da nadingayi miki lokacin biki" ba musu Salma tabawa Saudat wayarta, tana cikin yimata turi ta faki idonta ta dauki lambar Mijin Salma wato Habib, haka suka dinga hira se la'asar sannan saudat ta tafi, saudat taso taga habib amma bata ganshiba salma tagaya mata baya gari.
Tunda saudat taje gida tana rawar jiki taje tasamu khadija tadinga nuna mata video gidan salma, gaba daya khadija ta rikice da ganin aljannar duniya, tabbas habib shine mijin daya dace da ita,
Daga nan ta nuna mata ta samo lambar Habib "khadija ga lambarsa na samo ta ina yakamata in fara"
Hanzarin me kike ne, ba tace miki baya gari ba, kibari se kaman
nan da sati daya mana maybe lokacin ya dawo"
"anya zan iya jira har sati kuwa, nifa banki ace ko a satin nan a daura aure ba dan ba karamim so nakeyiwa gayen ba, kokuma ince nakewa dukiyarsa ba"
Khadija ta jinjina kai tace "to wai yazakiyi da kawarkine, in ta gane zaki aurar mata miji" tsaki saudat tayi "wayake tawani matarsa, ai ranar biyan bukata rai ba a bakin komai yakeba, indai buri zecika, to babu batun kunya da cin amana, inma ta gane ita tasani nidai fatana in ganni a cikin wannan daukar" "hmm Gaskiyar ki yar uwata, Allah ya ida nufi"
"Ameen khadija, ammafa in Salma tagane ba karamin hauka zatayu ba, dan tana masifar son gayen nan, gata da kishi kamar bala'i, amma tasamu dai dai da ita indai nice" murmushi khadija tayi
"gaskiya zata taro match kishi da hajiya Saudat" sukayi shewa gaba daya.
Kwana biyu da zuwan saudat gidan Salma, khadija ta shirya tun safe ta fita ashe wayar saudat ta dauka tun dare ba wanda yasani, ta fita ta cire sim din saudat tasa a wayarta ta dauki lambar Habib, sannan ta kakkarya layikan saudat ta zuba a kwata, sannan ta jefar da wayar tai tafiyarta, bata koma gida ba se bayan magariba yaje ta tarar anata jimamin wai barawo yashigo gida jiya da daddare yasace wayar saudat, ta shiga sahu akaita jajantawa saudat, saudat tabiyo khadija dakinta kaman tai kuka tace "wallahi khadija ba batan wayatane yabani haushi ba, rasa lambar habib itace ta konamin rai"
"don't panic dear, karki damu, inkika canza waya seki kuma samo lambartasa, aibawani abu a ciki"
"haba khadija kinsan da yadda nasamo lambar nan kuwa idan nakoma mezance mata inkuma karbar wayarta, kuma kwata2 yaushe naje gidanta dazan koma" ta karasa maganar kaman zatayi kuka
"haba saudat kefa kikace ranar biyan bukata raiba abakin komai yake ba, amma kibari kaman in akayi sati biyu sekikuma zuwa, kinga ba wanda ze zargin wani abu"
Saudat ta kalleta "haba khadija har sati biyu, anya kuwa zan iya jurewa"
"Saudat idan kikabari matarsa ta gane zaki aurar mata miji to tabbas bazata kyaleki ba, gara kibi komai a sannu in lokaci yayi taji"
Saudat tayi nannauyar ajiyar zuciya tace "kuma kinyi gaskiya khadija, shiyasa nakeson shawarwarinki nagode sosai, bari anjima Mukhtar zezo se in sashi yakawomin wata wayar"
"eh hakan ma yayi kyau"
"hakane nagode bari inje inyi salla" tana fita khadija tai murmushin mugunta.
Khadija tasa kabir yasiyo mata sabon waya, me madannai tayi saving lambar habib a ciki, kullum safiya da dare seta tura masa zazzafan text messages da addu'oi , hakama da daddare zata tura masa
bata taba kiransa a waya ba, shima kuma betaba biyowaba balle yaji waye. Amma habib yana mamaki wacece take turomasa wannan messages haka, shidai yasan ba Salma bace bata da wannan lambar, kuma tunda sukayi aure bata yimasa tex kamana yadda take masa kafin suyi aure, amma bari ya tambayeta ko itace take turo masa, salma na gaban mirror tana taje kai, habib yana kan gado a kwance ya kalleta yace
"my sweet lambobinki nawane?" kallonsa tayi "meya farune??"
'No bakomai na tambayeki ne dai"
"fadamin gaskiya ko watace take kiranka ka zata nice" gabansa ne ya fadi ya kalleta, amma yakasa magana a hankali ta tako tazo ta zauna a kusa dashi tace
"yanaga ka tsorata, nafada dai2 kenan"
"A' a kam kinbani mamakine kawai, daga tambaya kin canzamin magana, kaman kina zargina"
Tayi Ajiyar zuciya "Habib kada Allah ya nunamin ranar da wata mace zata dinga kiranka, amatsayin budurwarka, inaga a wannan ranar se zuciyata tayi bindinga, bazan iya jure ranar dazanyi sharing dinka da wata mace, inasonka habibi da'iman" seda cikin habib ya duri ruwa, amma ya dake yace
"I love you too hibbaty, karki damu zuciyata kekadai ce a ciki, zan rayu dake har zuwa karshen rayuwata" yai mata murmushi tareda yin kissing dinta a goshi, ta dora kanta akan kirjinsa tanata ajiyar zuciya, message ne yashigo wayarsa, yasa hannu ya dauka ya bude message ne na nuna tsantsar soyayya da kauna da khadija ke turomasa, sauri yayi yasa lambar a blacklist, ba tareda salma ta dago ba tace "habiby waye ya turomaka message?"
"Alert ne, kayan dana siyar aka turomin kudin" har cikin ranta ta yadda da abunda yace.
Haka khadija takuma canza layi tacigaba da turawa habib messages baji ba gani, abunne yafara damun habib kar by mistake Saudat tagani, gashi layinsa ne dayakeso wanda huldodunsa na kasuwanci duk akai suke da se ya cire layin ya yar, besan mezece ma Salma idan taga wannan messages dinba, dan Yasan halinta da mugun kishi, yanzu se cibi yazama kari, ba dan haka ranar ya yanke shawarar yakira yaji kowacece, da safe wajen karfe goma khadija tana kwance tanata tunanin habib tana kallon hotunansa, karamar wayarta datake kiran habib da itane tafara ringing, ga mamakinta taga Habib ne nannauyar ajiyar zuciya tayi tareda yin murmushi ta rungume wayar a kirjinta tanajin ringing din wayar harcikin zuciyarta, wayar tayita ringin harta katse bata daga ba taitajira koze kuma kiranta amma be kirata ba. Kusan kwana uku bekuma kiranta ba itamuma tacigaba da turamasa, rana ta ukun da daddare yakuma kiran wayar khadija seda ta kusa tsinkewa, sannan khadija ta tattara duk wata nutsuwarta ta daga wayar, tana dagawa kafin tayi magana a fusace yace "wai dan Allah wacece haka, kina nema ki hadani fada da matata meye hakane, karki kara turomin wannan rubbish din nagaya miki" maganganunsa sunyimata zafi, amma ta dake tace "ohhh masha Allah, zanyi bacci irin wanda bantabayiba yau habib, naji muryarka Ina sonka, kayi bacci me dadi kaman yanda zanyi cike da farinciki" tunda tafara magana gaba daya jikinsa ya mutu yakasa cewa komai, itama bata jira meze ce ba ta kashe wayarta, tace "Lallai Habib bakasan wacece khadija ba bazaka taba kufcemin ba tunda kayi gangancin kirana" khadija bata taba gajiyawa ba gurin yi masa aiken zafafan kalaman soyayya.
Yau sati biyu cif tacika da zuwan saudat gidan Salma, tun karfe goma na safe ta shirya, tazo tayiwa khadija sallama cewar zataje gidan Salma, ita khadija ta manta ma cewar sunyi da khadija yau zata koma gidan Salma, khadija ta dake taimata fatan nasara, bayan ta fitane ta dinga mata dariya. Koda saudat taje gidan me gadi yasanar da ita cewa masu gidan basanan sun tafi Abuja karfe 2narana zasu bar Nigeria zasu wuce Dubai, Saudat jitayi kaman ta dora hannu akai tayi ihu, tacewa me gadin "dan Allah yayana kozaka temakamin da lambar me gidan?" zare ido yayi "lallai da alamu kina da tabin hankali yadda tsaro yayi karanci zakice abaki lambar megida, to ni kaina bani da lambarsa, seta PA dinsa, se in abun me mahimmanci ne sannan ya hadaki dashi kuyi magana, inkuma bame mahimmanci bane ba yakamaki yace bakida gaskiya, indai baya gari tokomenene hakura nake"dafe kai saudat tayi takuma cewa" dan Allah kabani lambar P. A dinnasa mana" "waike wace irin mayyace ne, bar kofar gidan nan ko inyi waya azo a tafi dake wallahi" "No yi hakuri zan tafi, insun dawo senazo" daga nan ta juya ta taho gida, tareda tsinewa barawon dayasaci wayarta albarka, tasamo lamba a bagas an sace wayara haka ta dawo gida jiki a sanyaye, kallo daya khadija tamata tagane babu alamun nasara, nan Saudat tabawa khadija labarin abunda yafaru taita rarrashinta tareda bata karfin gwiwa kaman gaske. Khadija takoma daki ta tsarawa Habib text
"Hayateee ashe zakabar kasarnan ba labari, masoyi masoyine ai at least yakamata in sani ai, Allah yakaika lafiya, yatsaremin kai yakareka ya kare dukiyarka, Allah ya albarkaci neman ka, ya doraka akan makiyanka, dukda ni baka damu daniba amma ni kullum soyayyarka ninkuwa take a zuciyata, gangar jikina tana Nigeria, zaka tafi da rayuwata Dubai, kaine rayuwata habib ka kulamin da rayuwata, zanyi kewarka rayuwata, Ina sonka Hayateee" Habib yana harabar hotel din dasuka sauka yaji message din yashigo koba a gayamasa ba yasan na wannan mayyar ne, yana budewa yakaranta sakon yana kuma karantawa, to ya akayi tasan zebar kasar, kiranta yayi seda taja aji sannan ta dauka
"barka da wannan lokaci Rayuwata"
"ke wai aina kika samu lambata kike takuramin haka, sannan wayagaya miki zan bar garine yau"
"haba hayatee, kaifa rayuwata ne, yaya za'ayi inkasa sani, dukda nibani da mahimmanci a gurinka, kai kanada mahimmanci a gurina, Habib yakamata ka girmama kalmar so" tayi ajiyar zuciya, cikin kissa kaman zatayi kuka tacigaba da cewa "Habib bansan da wani kalman za gwada maka yadda nakeji a zuciyata ba"
"kinga dakata, wai bakisan inada aure ba kwata 2 wata biyu kenan da yin aurena, yazaki dinga turomin messages na soyayya in matata tagani fa?" "shiyasa bana kiranka nakemaka message, kuma mata hudu Allah ya halatta maka, karkayi garkuwa da aurenka ka wulakanta bukatata"
"Ke inkece a matsayin matata yazakiji idan akayi miki haka, inason matata kuma ni bazan kara aure ba mace daya Salmana ta isheni"
"Habib da kaine a halin danakeciki nake maka abunda kakemin yazakaji, nafara sonka tun kafin infara ganinka" tayi ajiyar zuciya sannan tace, "shikenan Habib ka dawo lafiya Allah ya dawwamar da farinciki a rayuwar aurenka, nikuma zan dawwama cikin bakinciki har karshen rayuwa ta, zancigaba da rayuwa da soyayyar ka" takarasa maganar tana hawaye "kakula da kanka rayuwata ina sonka rayuwata Habib, i will miss you, zanshiga yanayi mara dadi habibina" kafin yayi magana ta kashe wayarta, habib yacigaba da jujjuya kalaman yarinyar, dan tabe baki yayi yakoma masaukinsu.
Seda habib ya shafe wata shida bezo Nigeria ba shida Salma, suna dubai yana business dinsa suna cin aamarcinsu, sam khadija bata samun habib a waya saboda bata da lambarsa ta Nigeria, ta turamasa message harta gaji, ta bibiyi har gidansa taje tabawa megadinsa makudan kudi da zimmar duk randa habib ya dawo zekirata a waya ya sanar da ita, sannan tace masa idan har Saudat takuma zuwa gidan ya hadata da 'yan sanda, yace musu su tuhimeta, sannan ayi mata iyaka da zuwa gidan habib, ganin kudi yasashi amsawa yace yadda takeso haka za' ayi. Wannan kudin databawa megadin gidan Habib Adashin da kabir yayi ne a gurin aiki yakawo mata fiye da rabin kudin yace ta sai kayan kwalliya, shine ta dauki kusan dubu tamanin tabawa megadi dan yayi mata aiki.
tsawon watanni shidan nan haka tayisu kaman mara lafiya, zazzafar soyayya da takewa habib ta wuce misali, har rashin lafiya tayi, gaba daya yan gidansu sun kasa gane kanta, juyin duniya taki gayawa kowa abunda yake damunta, ta rame sosai. Haka bangaren Saudat tayi zarya gidan habib harta gaji, kamar yadda khadija tagayawa megadi haka ya hada Saudat da yansanda, yace musu be yadda da itaba da alama, irinsune wanda yanfashi ke hada kai dasu, haka yan sanda suka kama Saudat, ranar wuni tayi a cell, yayyensu maza sukace ba ruwansu bazasu belinta ba, dama bata da kunya gara a koyamata hankali. Maman Saudat ta dinga hadasu da Allah suje sufito da Saudat sukaki, sukace "aibasu suka aiketa yawon gidan masu kudiba" Khadija da kanta takira kabir a waya tace yazo yanata rakiya, tasa Kabir agaba sukaje police station sukayi belin Saudat, yadda khadija tasaki jiki da yansanda suka dinga hira hada exchange na number ba karamin batawa Kabir rai yayi ba, tunda suka fito yake mita "haba khadija kinsan bana sonki da irin wanan abun, danmene zaki saki jiki da wasu mazan a gabana hada basu lambar wayarki"
"kai dakata malam, aurena kake dazaka dinga takuramin, inbahaka nayiba kana ganin zasu sakarmin kanwata ne? Nifa banason wanan shirmen naka wallahi, inka gama mitar ka iya tafiya" tai shigewarta gida tabarshi a nan a tsaye. Tunda suka koma gida Saudat tayi wanka takasa ko cin Abinci, khadija taje kusada ita ta zauna "Saudat wai meye na damun kanki, bagashi naje nafito dake ba?"
"mtsee khadija ba wanan ya dameniba, ni yanzu tashin hankali na rasa habib, wallahi khadija inason habib, zanyi duk meyuwuwa nima inshiga wannan daular in dama, kome zafaru dani a gaba sedai ya faru amma sena auri habib"
"Saudat kibi komai a sannu, karkiyi gaggawa, se komai yazo miki da sauki, inkikace zakiyi garaje to zaki lalata komai ne"
"hakane amma ni yazanyi zuciyata kaman ta fashene khadija, ni kawai burina inganni a wannan daular" khadija aranta tace "yarinya man kaza, niba dukiyarsa kawai nakeso ba, har shi kanshi habib din nakeso, dan haka zan cigaba da wasa da hankalinki yarinya" ta riko hannun Saudat
"yar uwa, duk macen dataga habib taga dukiyar daya tara dole tasoshi amma kibi komai a sannu, in baki iya takunki ba garin wannan rawar jikin naki wataran prison za'a kaiki, yanzu abunda ze faru kidanyi hakuri kibari su dawo kasar nan semuga ya zamuyi tunda ba abunda zamu iya a yanzu tunda baya kasa"
"shiyasa nake sonki khadija, kin damu da damuwata, zan bari se ya dawo kasar nan"
"idan ya dawo dinma karki sake kikuma zuwa layin gidansu, kibari zansa aje a dan dinga survey din anguwar tasu da anga ya dawo za'asanar damu, Nikaina zanyi alfahari inganki a cikin wannan daular, inkika samu aina samu" rungume khadija tayi da sauri "nagode sosai, inaji dake yar uwa"
"zakigane baki da wayo, bazan taba bari kikuma rabar inda habib yakeba"

_MY FIRST NOVEL_
Haka khadija tacigaba da wasa da hankalin Saudat ba tareda ita Saudat din tasan me khadija take shiryawa ba.
Khadija ta karbi kudade dayawa agurin Kabir da sauran kudaden data damfara a gurin samarinta tafara business na atamfofi da kayan sawa, gurin manyan masu kudi, saboda tace in Allah yasa lokacin bikinta kece raini zatayi bazata barima azo ayi wani abu
a wannan gidan nasuba, biki za'ayi kaman na diyar sarakuna, dan jikinta yana bata zatayi galaba akan Habib saboda alamun sun nuna yanada saukin kai da tausayi.
Ranar da habib yadawo Nigeria me gadinsa yakira khadija a waya yasanar mata, taimasa godiya take ta turamasa katin 5k saboda albishir din dayayi mata, shi habib har yamanta da batun me turomasa messages, se bayan kwana biyu yamaida layinsa na Nigeria messages din khadija yafara cin karodasu ba adadi, tsaki yayi ya aje wayar yashiga sabgoginsa, kwanan sa uku da dawowa yakoma gurin aikinsa, yana zaune a office aka kirashi a waya, bakuwar lamba ne dan haka beyi tunanin komai ba ya daga wayar, tana sallama ya gane wacece, amma yarasa meyasa duk lokacin dazata kirashi baya iyayimata rashin mutunci. Yana cikin wannan tunanin yaji muryarta tana cewa "Rayuwata, barka da dawowa kasa Nigeria, ina maka barka da zuwa nayi kewarka matuka, nayi rashin lafiya sosai bayan tafiyarka, ina fatan kundawo lafiya" Abun mamaki taji yace "ya jikin naki?" seda tayi murmushi ta wani lumshe ido "Jiki ina samun sauki Alhamdilillah"
"me yake damunki?" takuma kashe murya "hayatee komaima yana damuna, nikaina narasa meke damuna, amma jigon rashin lafiyata soyayya ce, at least zansamu relief tunda ka dawo, bari in barka ka huta, I love you hayatee" ta kashe wayarta, tunda habib ya dawo Nigeria tafara shawo kansa saboda koyace katta kara kiransa bata fushi, kullum cikin nuna masa soyayya take, ta lura ya dan damu akan maganar rashin lafiyarta, hakan yasa tafara ji ajikinta burinta yana daf da cika. Tacigaba da kokari tana dauke hankalin Saudat daga kokarin zuwa gidan habib.
Seda khadija ta lura habib yafara bata kulawa, seta dena tura masa message ta kashe wayar da take kiransa da ita domin ta tabattar da ko yafara sonta, haka ta danne zuciyarta tsawon sati biyu bata kirashi ba kuma bata turamasa message ba.
Ranar da sati biyu ta cika khadija ta kunna wayarta, messages ne suka shigo wayarta, data bude duk na habib ne sekuma kamfanin layi, dayake shikadai take kira da layin, duk messages din yana tambayarta ina tashigane layinta baya shiga Allah yasa lafiya, bata san lokacin datayi wani tsalle ba tayi ihu a daki, mamanta ta shigo dakin da sauri "ke lafiya meyasameki?"
"bakomai mama bansan nayibane"
"to Allah ya shiryeki auta" mama ta fice khadija ta mike tsaye hada rawa a cikin daki. Bayan sallar magariba kabir ya tura yaro yace yayi masa sallama da khadija, tace yaron yace tana zuwa, ta shirya zata fita gurin kabir sega kiran Habib. Nan da nan ta tashi ta kulle kofa tazo tanemi guri ta zauna akan gado ta daga wayar cikin sanyin murya tai masa sallama, kafin ya amsa sallamar yace "ina kikashiga haka tsayin wannan lokacin?"
"hayatee bani da lafiya ne fa"
Cikin sauri yace "subhanallah jikinne har yanzu? Yanzu kina inane?"
"ina gida naji sauki"
"dagaske kinji sauki kokuma wasa kike?"
"Am serious, yau naci Abinci sosai nayi wanka nayi kwalliya, i wish kaga kwalliya nan hayatee" murmushi yayi yace "dagaske?" "Eh mana nayi kyau sosai, sedai ciwon so duk ya ramar dani"
"yaushe zan ganki?"
"Duk sanda kakeso, a shiryenake"
"kiyi fixing time, seki gayamin zanzo mugaisa"
"masha Allah, hayateee harnaji na warke gaba daya"
"to Allah yakara afuwa, bari zan shiga gida" cikin sauri cikin shagwaba khadija tace "haba hayatee ni wallahi bangaji dajin muryarka ba, kalli tsayin lokacin daka dauka bana jin muryarka fa" haka khadija ta dinga hilartasa suka shantake suna waya, tana masa hira me dadi har gurin goma da rabi na dare sannan sukayi sallama, Kabir yagaji da jira gashi lokacin sanyi amma khadija taki fitowa maganar duniya tayi banza taki bude kofa tacigaba da wayarta, daga baya tace ace masa yacigaba da jira inyaga ze iya tana da abunyi me mahimmanci datakeyi.
Seda ta gama wayarta tace ace masa ya tafi bazatazoba. Saudat ta shigo dakinta tace "khadija wai dan Allah wani zazzafan kika samune haka kusan awa uku kina waya, naga duk saurayin dakikayi bakya yiwa Kabir wulakanci amma yau kin shuka masa dayawa fa" khadija tayi wani shu'umin murmushi tace "ai ke bar gara kawai, najefa fatsata a ruwa kuma da alamu nakamo kifi me nauyin gaske, ba kama kifinne matsalar ba, sedai zanyi gwagwarmaya kafin kifin yazama mallakina saboda akwai masu farautar wannna kifin dayawa abakin ruwan" ta kuma kallon Saudat tace "kodayake kince ranar biyan bukata rai ba abakin komai yakeba yar uwa, dan haka zan jure gwagwarmaya da kubale in mallaki kifin nan"
Saudat tace "kinga ni kiyimin hausar dazan gane, se wani kwana2 kikemin, nibangane mekike nufi ba"
"karki damu zaki gane very soon yar uwa"
Bangaren habib kuwa, Salma ta damu matuka baya kaiwa tsawon wannan lokacin a waje, amma yau ya kai, tayi2 yagayamata dalili yace bakomai wani abune ya rikeshi haka ta hakura.
Wasa2 taga ya maida hakan dabi'arsa baya shigowa gida se bayan goma, dataga bashida niyyar denawa itama ta watsar dashi tacigaba da sha'aninta, seta ajiye masa abincin sa akan dining tayi kwanciyar ta, hakan yakara bashi damar sakewa suyi waya da khadija.
Ranar juma'a da yamma suka shirya zasu hadu a wani gurin shakatawa, saboda khadija bataso yazo da rana gidansu Saudat ta ganshi, yarigata zuwa gurin yana zaune yanata duba agogo har yafara fidda ran kozatazo, yana kokarin kiran layinta ne, yaji kamshi me dadi yacika masa hanci, dukda yajuya baya, amma tana kallonsa tabaya tasan shine, a hankali ta tako tazo bayan kujerar dayake ta tsaya, ta durkuso da kanta a hankali tace "Hayateee barka da zuwa" ya dago kai ya kalleta daga sama har kasa, doguwar mace ce, sannan tana da dan kiba kadan, baza akirata da fara tas ba amma tanada hasken fata sosai, tabbas khadija tana da kyau dai dai2 gwargwado, murmushi yayi mata "sannu da zuwa masoyiyar boye" murmushi tayi ta zagaya ta zauna akan kujerar datake facing dinsa, suka gaisa sun sha hira sosai sannan ya dauketa ya kaita har bakin layinsu shikuma ya tafi.
Khadija tayi nasara samun zuciyar habib tana nunamasa soyayya iyayinta, haka habib yasake da khadija suke soyayya ba tareda Salma tasani ba, yakanzo gurin khadija tadi, Saudat ta fusakanci yan kwanakin nan khadija tana cikin farinciki. Bayan sun gama cin Abinci khadija ta tafi daki ta shafe kusan awa uku tana waya, a iya sanin Saudat datayiwa khadija tasan bata son doguwar waya, amma ya akayi kwanan nan take waya haka, mikewa tayi tabi khadija daki, taje ta tarar da ita tanata zuba shagwaba a waya, tana ganin Saudat ta shigo dakin tai maza tayiwa habib sallama ta mike zaune
"Saudat lafiya kuwa na ganki haka ba zato babu tsammani"
"hmm dole kice haka mana almost 3hrs kina waya, ba'a kojin mekike fada, shikam wani me nasarar ne haka? Kodai kin hadu da dream hubbyn nakine" wani kasaitaccen murmushi khadija tayi "kwarai kuwa kedai kiyitamin Addu'a"
"shine babu ko Labari balle a gabatarmin dashi"
'mekikeci na baka na zuba, shida zezama sirinkinku sekin gaji da ganinsa "Saudat tace" Allah sarki Kabir yanata tsuma ze aureki "
Tsaki khadija tayi
" ke dalla kidenamin zancen wannan wawan, nifa badan ina tausayinsa ba da tuni na dade masa wulakanci, kodayake wulakanci na nawa, bashida zuciya ne"
"Mhmmm nikam nace khadija waime ake ciki game danawa damuwar ne, wallahi khadija ko baccin kirki bana iyayi" Ajiyar zuciya khadija tayi tace
"gaskiya Saudat ina tausaya miki, abun nada matukar tausayi, nikaina na kagu inga kinshiga wannan daula amma semunbi komai a sannu, bakisan iya kokarin danakeyi miki ba, yanzu haka nabada cigiyar in yadawo a sanar dani, naje har layin gidansa dakaina, amma ance an hana shiga layin ba tareda wanda zakaje gurinsa yasaniba, amma inata miki kokari "
" to khadija Allah yasa adace"
"zama adace kakri damu Saudat".
Duk ranar da Habib zezo gurin khadija tadi sedai su hadu a gidan kanin mahaifiyarta acan suke zancen, soyayya ce me karfi tashiga tsakanunsu, duk kasar dayatafi A gaggauce yake ya dawo domin ya hadu da ita, baya jure dogon lokaci basu hadu ba.
Habib da kansa yacewa khadija ze turo iyayensa ayi maganar aure, amma zeje maiduguri tukuna in yadawo seya turo, tayi murna ranar kamar ta zauce bata taba zaton a abubuwa zasu mata da sauki haka ba.
Gefe guda habib yanata tunanin, yadsa ze sanarwa da Salma batun auren dayakeso yayi, dan yasanta da matukar kishi, dan haka ya yanke shawarar zefara zuwa maiduguri in magana tayi nisa yagayawa Salma.
Koda Habib yajewa mahifiyarsa da zancem Aure bata bashi goyon bayaba hasalima faada takama yimasa "haba habib, yaushe kayi auren fari da har zakace zaka kara aure, yarinyar nan yar uwarkace fa, mahifinka da mahifiyarta uwa daya uba daya, hakan ze iya shafar zumuncinku, gaskiya ka hakura kozakayi aure ba yanzu ba" yakada yaraya amma mahaifiyarsa taki yarda, Habib tunda yake betaba yiwa mahaifiyarsa musuba se wannan karon, yaita mata magiya, karshe seda yaje yagayawa yayanta yazo yasa baki, badan tasoba haka ta amince, amma tace kafin aje neman auren se anyi bincike, akayi bincike amma bincike ya nuna khadija ba mutuniyar kirki bace, batada aibu, sedai rashin kunyarta da iya fitsara, yan uwan mahifin habib suka gayawa mahaifiyarsa nan ma ta dage tace baze yuwi ayi auren nan ba.
Khadija yagayawa khadija halin da akeciki ta damu sosai nan ta shiga addu'a ba dare ba rana, ta sanarda mahifiyarta komai sukacigaba da addu'a habib yanakin baze iya rabuwa da itaba dan haka yacigaba da lallaba mahaifiyarsa.
Habib ya canza gida, yakoma wani dankareren gida daya Gina a gadon kaya, gidane na alfarma matuka, anan ya tsara inya auri khadija ze hadasu da Salma. Bayan khadija ta tabattar da Habib ya tashi daga gidansa, taje ta samu dansandan dayake gadin rukunin quaters din dasu Habib suka tashi, tabashi kudi, ta shiryamasa abunda takeso yayi mata, sannan ta dauki Saudat sukaje tsohuwar unguwarsu Habib da nufin suje sugani yadda zasuyi kozasu samu Habib, suna zuwa dansanda dayake gadin rukunin quaters din yace musu "wakuke nemane?" khadija tace "gidan Habib kamal mukazo"
Nan yagaya musu "Ai yabar quaters din nan, tunda yadawo daga Dubai bezoba"
Da sauri Saudat tace "ina suka koma?"
"kamarya ina sukakoma dokace, da sun yadda daku dakunsan inda suka koma dan haka kubar nan gurin" khadija tai kokarin yagaya musu amma yai musu korar kare tare da barazanar ze kullesu, khadija ta kashe masa ido alamar aikinsa yayi kyau.
Habib yasha wahala sosai sannan mahaifiyarsa ta amince da maganar Aurensa da khadija, dangin mahifinsa ciki harda mahifin Salma, sukazo nema masa auren khadija gurin wan mahaifinta, sannan mahifin Salma yajawa mahifiyarta kunne kan be yadda wani yagayawa Salma Habib zekara Aure ba shida kansa ze gaya mata, dangin mahifin Habib suka kai kudin Auren Habib akasaka wata shida.
Khadija jitake kaman ba itaba, habib yagaya mata ansaka wata shida ji take yamata nisa wata shidan nan, se murna take ta tafi dakinsu Saudat cikin zumudi tana kiran sunan Saudat, tana zuwa ta tarar da Saudat tana kuka, da sauri ta karasa inda take tadafata "Saudat meyasameki haka?" Saudat ta share hawayenta ta girgigiza kai tace "bakomai khadija"
"A'a da komai gayamin menene?" Saudat ta dan gyara zama tace "khadija har yanzu burina becikaba, gashi ke zakiyi aurenki amma ni se gararamba nake, ba wani tsayayye wanda nake hangen yakasa samuwa, yanzu zakiyi aurenki ki barni" khadija ta riko hanun Saudat sannaan tace "Saudat dan adam be isa yasamu abunda ba rabonsa ba, indai habib rabonkime sekin aureshi, inba rabonkibane ba ba yadda zakiyi, shawarata agareki shine karki tsaya jiran Habib, ki bata lokacin ki, tun wuri kinemawa kanki mafita"
"khadija kina nufin in hakura gaskiya bazan iyaba kome zefaru, kedai kiyi aurenki ni zancigaba da fafatukata, sena auri Habib wallahi" murmushi khadija tayi "to shikenan Allah yabawa me rabo sa'a" daga nan ta tashi ta fice.
Habib da kansa ya shirya ya dauki Salma suka je maiduguri, yakaita gidansu da nufin tayi musu yan kwanaki, mahaifin salma yasa aka kiramasa ita dakinsa, ya zaunar da ita yayi mata nasiha sosai sannan ya sanarmata Habib ze kara Aure, ji tayi kaman mahifinnata ya watsa mata wuta, take idonta yayi jawur ta kalleshi "Aabba kan nufin Habib dinane zeyimin kishiya, kuma kake gayamin innalillahi wa inna ilaihi raji un, dan Allah Abba kacemin da wasa kake, wallahi bazan iyazamabda wata a matsayin kishiyata ba"
"Ke meye hakane? Akanki aka fara, to ki nutsu, akanme mijinki yanada halin daze auri mata hudu ya kuma iya rike su danme zakice baze aure ba, karki kuskura inji kin daga masa hankali shiyasa nace nizan gaya miki da kaina, dan haka kiyi hakuri, daba a aure dakema baze aureki ba, yakamata kija girmanki tunda kece uwargida, dan haka kiyi hakuri tashi kije Allah yayi miki Albarka " da kyar ta mike tsaye tana tafe tana hada hanya ta tafi dakin mahaifiyarsu, tana zuwa ta zube a jikin mamansu takama kuka
" mama dama habib ze iya yimin kishiya, ko shekara biyu bamuyi da aure ba shine ze auri wata, mama anyimin adalci kenan" ajiyar zuciya mama tayi tana dan dukan bayan Salma alamun rarrashi
"kiyi hakuri Salma kinji, kuma bazamu kira abunda habib yayi da rashin kyautatawa ba tunda shima danmune, ni macece salma masan meye kishi abune me ciwo amma kiyi hakuri zakiga ribar hakurin, kiyi masa fatan alkhairi sannan karki nuna masa kin damu"
"A'a Mama bazan iyaba, wallahi zuciy
ata zata fashe, mama bakisan menakeji ba, bantaba mafarkin Habib zemun kishiya ba, in hakanema yabari sena kwana biyu a gidansa mana, amma yaushe mukayi auren zemun haka, toni na hakura da aurennasa yaje ya zauna da wadda yakeso" nan mama taita rarrashinta tana nunamata illar cewa zata kashe aurenta. Kwanan salma biyu a gida sannan habib yazo daukar ta, iyayen salma sam basu canza masa ba, sedai Salma fuskarta sam babu walwala zakayi zaton jinya takeyi, harsukazo kano batace masa uffan ba.
Bayan sunkoma gidama ta tattara tayi watsi dashi, bata cin Abinci sosai kullum cikin kuka take abun yafara damun habib sosai dan haka yaje ya sameta a dakinta yanzuma idonta jawur da alama tasha kuka sosai. A hankali ya karasa ya zauna kusa da ita yayi kokarin janyo ta jikinsa amma ta kwace, ya kalleta "habibty dan Allah kiyi hakuri, bazanyi Auren nan dan in wulakanta kiba, matsayinki yana nan a zuciyata kaman yadda kika sani, dan Allah badanniba kidena azabtarmin da kanki, kidinga cin Abinci kin rame sosai kindena bani kulawar da duk kike bani, please my Salma calm down" kuka takuma saki me ban tausayi, ya rungumeta ya dinga mata nasiha yana rarrashinta a irin kishi na salma be taba tunanin ze iya rarrashinta ta hakura ba, kusan kullum se iyayenta sun kirata a waya anmata nasiha da addu'oi hakan yasa tasamu raguwar radadin da take ji a zuciyarta.
Biki nata karatowa anata shirye2 amma har yanzu yan gidansu khadija basu taba ganin Habib ba, sunyi mitar sunyi harsun gaji amma taki yadda aganshi, yayyenta sunyi fada sosai dasukaji cewar ba Kabir ne yakawo kudin auren khadija ba, amma aka barshi yana wahala, amma mahaifiyarta ta goyamata baya, hatta yan anguwa bakowa yasan khadija zatayi aure ba saboda tace ba kowane garane zezo mata gurin biki ba, mussaman ma yan unguwarsu yan bakin ciki, Habib yana sakarwa khadija kudi yadda yakamata anata shirin biki. Babban abun mamakin yadda haryanzu kabir besan khadija zatayi Aure ba yana zuwa gurinta tadi, kuma yanabata abu takarba, yauma suna tsaye tagama hira da Kabir wani makocinsu yagansu, sungama tadi ya dakko uwar leda cike da kaya yabata, nan ya jinjina kai lallai wannan yarinyar tacika yar banza, aikuwa sena gayawa yaron nan, kokuma inje har gida ina sanarwa da uwarsa dan watakila idan nagaya masa wannan makirar yarinyar tace karya nake babarsa zanje ingayawa
Tirkashi

Washegari da yamma makwabcin su khadija yatafi gidansu Kabir, dayake abokin baban kabir ne kafin ya rasu, yaje gidansu kabir yai sallama mahaifiyar kabir tayi masa iso, bakowa a gidan se ita suka gaisa da mutumin, tunda mahaifinsu kabir ya rasu jefi jefi yakanzo su gaisa shima se a shafe shekara bezo ba, suna ciki gaisawa ne kannen kabir suka shigo suka gaisheshi ya amsa yana su karimane suka girma haka masha Allah, yana nan zaune yaga suna gaganiyar fita da murhu da ice waje, seda suka gama ya kalli mahaifiyar kabir yace "suwai ba waime yaran nan suke da murhu a waje" mahaifiyar kabir tace
"kasan yanayin rayuwar ne se godiyar Allah, suna dam soye soyene a waje suna siyarwa, in sun siyar muke samun biyan bukatun yau da kullum da nauyin karatunsu, ga kuma batun aure na kokarin tasowa, ba mai yimana komai se Allah"
"Amma ina kabir, naji ance yasamu aikin kamfani kwanakin baya, ga kuma nakan ganshi wataran a kasuwa yana neman kudi, ya akayi yake barinku har se kannensa sunfita waje suna siyarda abu" Ajiyar zuciya mahaifiyar kabir tayi
"hmm lamarin kabir se addu'a inzaka yankani bansan inda yake kai kudi ba, kullum na tambayeshi se yace bashida kudi, semu shafe wata uku ko gawayin girki be saimin ba balle Insaran kayan Abinci, ficika kabir baya moramin a kudin dayake samu, haka kannensa zasu shafe tsawon likaci a gida ba makaranta saboda ba abiya kudin makaranta ba amma baze iya biyaba, tun ina magana harna hakura na zuba masa ido"
"Tirkashi anya kabir nason yagama da duniya lafiya kuwa?"
"to yazanyi, na hakura na kyale shi yaje in abunda yakemin ya kyauta yaje shima ze gani"
"to bari in gayamiki wani abu, kimanin shekaru shida kenan kabir yake zuwa gurin wata yarinya a kusa da gidana, ita yake kashewa kudadensa, yarana suna shiga gidan suna gayawa mahaifiyarsu irin hidimar dayake mata, yanzu haka yarinyar bikinta saura sati shida, shi kabir ne saniba kuma ko jiya akan idona yabata katuwar leda cike da kaya"
Zaro ido mahaifiyar kabir tayi "kana nufin dama dagaske ne kabir yana neman yarinya, a gayamin amma ban yadda ba"
"Aiko yakamata ki yadda, dan yarinyar ba karamar hatsabibiyabacce ba, ya dade yanamata wahala duk abunda yasamu ita yake bawa, yanzu kuma zatayi aurenta ta barashi, gara tun wuri kisan halinda kike ciki, ni zan tafi Allah ya kyauta gaba" haka mutumin nan yatashi yabar maman kabir da bacin rai batasan lokacin data fashe da kuka ba "yanzu duk wahalar danayi daku amma sakamakona kenan agurinka kabir, ka fifita budirwa sama dani" haka ta cigaba da kuka, da magariba kannen Kabir suka dawo daga gurin sana'arsu amma suka tarar da mahaifiyarsu ranta a bace, na suka shiga jero mata tambayoyi, bata boye musu komai ba tagaya musu, karima tace "aini na dade da sanin zancen nan, banason ranki yabacine, amma yaya kabir har adashi yake yaje ya kaimata, komai yasamu ita yake kaiwa"
"Amma karima shine baki taba gayamin ba" karima tace "to mama meye amfanin fadar, yanzu da kika sani meyakara inba bacin rai ba, ai ga sakayya nan, zatayi aure tabarshi kuma itama zata gani, dan Allah kidena kuka" haka suka cigaba da rarrashin mahaifiyarsu daren ranar mahaifiyar kabir kasa bacci tayi, mussaman inta tuna matsin rayuwar dasuke shiga amma Kabir baya musu komai yana can yanayiwa budurwa bauta.
Yau khadija ta shirya ta tafi kasuwa bata nan, mahaifiyar kabir kasa jurewa tayi ta shirya ta tafi gidansu khadija, da taje khadija bata nan se mahaifiyar khadija ta tarar suka gaisa sannan maman Kabir tace "dama nice mahaifiyar Kabir" umman khadija tace "Allah sarki sannu dazuwa, kabir yaron kirki ya kuke ya yan uwansa"
"muna lafiya kece mahaifiyar khadija?"
"eh nice ya akayi ne?"
"yanzu dama bazaku bashi auren yarinyar ba amma kuka dinga sawa yana kashemata kudi har tsawon shekara shida, ni ina can ina fama da maratun kannensa, kukuma ya tare a gurinku, ga wahala gashi yarinyar zatayi aurenta kunyi mana adalci kenan" takarasa maganara idon taf kwalla, umman khadija tace "to baiwar Allah ai se hakuri dama indai ka haifi namiji ai wata ka haifawa, kuma ita mace allura ce a cikin ruwa me rabo ka dauka, kuma kinsan halin yarn zamani ba'a iya musu dan haka se hakuri"
"Yanzu hakan yayai daidai kenan"?
"to inma beyi daidai ba aisedai kiyi hakuri" ana haka sega khadija ta dawo, batabi takan mamanta da bakuwar dasuke tareba ta shige daki abunta, mamanta ta kirata ta nunamata maman kabir tace "ke ga babar kabir nan tabiyo jin kadin ya akayi kinsan bazaki auri danta ba kika dinga ci masa kudi, itakuma baya kulada ita" kallon mahaifiyar kabir tayi tace "banda abunki aiba nina rikeshi nahanashi tafiya ba, kuma ni bance karya kulaldake ba, abunda nasani niba sa'ar aurensa bace dannafi karfin auren matsiyaci irin danki m, kidubeni da kyau
banyi kalarsa ba dan haka yaje yanemi daidai da shi baniba, sannam ze iya lissafa abunda ya kashe a biyashi konawane, zan auri miji daidaidani danki shine matsiyaci se abiyashi kudinsa sekuma me? "
Bude baki mahaifiyar kabir tayi cikin mamaki "Au hakama zakice" ta juya ta kalli mahaifiyar khadija "yanzu kun kyautamin, kina kallon yarki abunda kukayi adalci ne? Shikenan kuda Allah kuma wallahi ke sekinga sakayya a rayuwarki, se Allah yabaki dan dazemiki fiye da abunda kikasa dana yaimin, kirikiri insha wahala da yayana, tun suna kanana har suka girma, amma kika kanainayemin yaro, kin hanashi ya amfanamin komai, alhalin kinsan ba aurenshi zakiyi ba, wallahi na barki da Allah" kuka sosai mahaifiyar kabir takeyi, wanda hakan ya janyo hankalin mutan gidan suka fifito tsakar gida, ita kuwa khadija tace "ai kokinki ko kinso dole kibarni da Allah dama, kabir ne naci rabona dama rayuwa ta gaji haka, kinzo se hayagaga kike mana kin taramin mutane sekace namiki sata aikin banza kawai" khadija tai tafiyarta ta shige daki haka mahaifiyar kabir ta baro gidan gwiwa a sabule tanata kuka, tana zagin khadija.
Koda mahaifiyar kabir takoma gida inta tuno abunda yafaru se tayi ta kuka, da magariba kabir ya shigo gidan, yazo ya gaisheta a fusace tace "ka tashi bana bukatar gaisuwarka kabir, kaje na yafewa diniya kai na sallamaka ga yarinyar daka fifita fiye da uwarka, kabir ashe tsawon shekaru shida kanayiwa yarinya bauta itada iyayenta, amma ni wani lokacin abunda zamuci da kannenka gagararmu yakeyi kana kallo ko a jikinka, kaje idan abunda kayimin ka kyauta kaje ga duniya nan"
"haba mama wacee irin maganace wanan wane munafikin ne yagaya miki haka?"
"dalla rufemin baki nice munafukar, har gidansu yarinyar naje yau, suncimin mutunci ita da uwatta, kuma suka tabattar min da wani zata aura, kayi asara kabir, bazanma bakiba amma hakkina ya isheka wallahi" a sukwane kabir ya mike tsaye "bangane khadija zatayi aure ba wayagaya miki?" wani takaici ne ya tokare mata a kirji wato shi ta batun auren ne ya daga masa hankali, shiru tayi ta sunkuyar da kai tanata sharbar kuka, a sukwane ya fice yabar gidan. Be tsaya ko ina ba se gidansu khadija akayi masa sallama da ita, yau yaci sa'a ta fito, ko gaisawa basuyi ba a gigice yace "khadija wai dagaske aure zakiyi"?
"injiwa?
" mama tacemin tazo gidan nan, an tabattar mata aure zakiyi, khadija ki gayamin gaskiya "
" nifa bana son wannan abun ds kakeyi ka nutsu mana, nibawani aure da zanyi da auren zanyi da bakasani ba, ka dinga bincike ka tabattar da abu kafin kazo kanamin surutu"
"Alhamdilillah har naji dadi, khadija inna rasaki bansan ya zanyi ba" dariyar mugunta tayi masa tace "kaga zankoma gida ina aikine, adinga hakuri dan ba kullum ake kwana a gado ba, kaga dama A'ayi bikin kawata ne zanturomaka 100k a account dinka inaso asamomin sababbin dari biyar biyar"
"100k dijena ai sunyi yawa, yazaki lika har hundred thousand"
"bacewa nayi kabani kyauta ba, zanturomaka ne kamin canjinsu kawai"
"dija samun sabon kudi yana dan wahala, amma zan duba miki insha Allah zan kawomiki karki damu"
"shikenan yayi kyau, ka gaida gida" daga nan ta shige cikin gida abunta.
Lokacin biki nata kuma karatowa, Salma ta rame sosai, duk tayi duhu saboda damuwa, mahaifiyar Habib da kanta tazo kano, taitayiwa Salma nasiha tanabata hakuri, sannaan tajawa Habib kunne akan ya kulada Salma, Ta hadasu tayi musu fada sosai sannan takoma maiduguri.
Saura sati biyu biki Habib tafiya takamashi, akai sa'a a ranar akakawo iv din biki, yaje dakin Salma ya sameta a kwance ya zauna a kusada ita yace "Habibty anjima zan tafi, ga katin biki an bugo ko da wanda zaki gayyata"
"Allah ya sanya Alkhairi" shine abunda tace masa kawai
"Habibty banajin dadin yadda kike shareni, nasan namiki laifi amma horon yayimin tsanani"
"dan Allah habib ka kyaleni, ka tafi karka makara"
"kina korata kenan?"
"niban koreka ba amma ka kyaleni"
"shikenan amma kimin Addu'a mana"
"Adawo lafiya Allah ya kiyaye hanya" haka ya juya ya tafi jiki ba kwari, bayan fitarsa ta dakko wayarta tana kallon hotunan bikinta da Habib tana kuka, hotunan Sauda data ganine yasataga bata kyauta ba yaushe rabon dasuyi ko waya, dan haka tasaka tshohon layinta ta kira Saudat. Ba karamin mamaki Saudat tayi ba dataga kiran Salma dan haka cikin sauri ta daga wayar
"salamu alaikum" Saudat tafada,
"wa'alaikum salam, Saudat yakike ya gida"
"lafiya kalau Salma, Salma naje gidanki ba adadi bana samunki, daga baya aka cemin kuntashi bansan inda kikakoma ba"
"eyya kiyi hakuri Saudat, kinga mun dade bama Nigeria ne, kuma damuka dawo ba dadewa munkoma gadon kaya"
"Allah sarki yanzu kina gari kenan, aiko insha Allah cikin satin nan zanzo dukda munata shirin biki" Salma tace
"Masha Allah, bikin waza'ayi? Amma ba gayyata"
"Khadija ce zatayi Aure saura 3 weeks"
"Kai kice na bugo waya a dai dai, da yanzu se ayi babuni ai yakamata inzo bikin khadija, dukda nima Habib ne zeyi Aure kusan lokaci dayane ma dana khadija" seda gaban Saudat ya fadi
"A.... Au... Aure kuma, wai wani Habib din kike nufine?"
"Hmm Saudat kenan, wane Habib kuwa, mijina mana, abun yabaki mamaki ko? Aure zeyi Saudat, amma Insha Allah zanzo bikin khadija ban manta dawainiyar da kukayi a bikina ba" cikin Saudat tace "to shikenan Salma se anjima, semun sake waya" ta kashw wayarta, mikewa tayi a sukwane ta tafi dakin khadija tana kwala mata kira
"lafiya kikemin wannan kiran, kaman wadda kikebi bashi meye haka?"
Saudat ta karaso cikin dakin tana haki ta zauna sanna tace "Khadija na shiga uku"
"Kamar ta kinshiga uku, meyasameki?"
"Ni narasa ta ina zanfara, Salma sun dawo Nigeria yanzu haka mukayi waya da ita tagayamin unguwar dasuka koma, wai amma Habib Aure zeyi saura 3 weeks, Khadija Aure zeyi nikam na kade, wallahi ko wacece bata isaba wallahi "
"to shine kika daga hankalinki haka, kemafa mijin watane kike kokarin sekin Aura, har gara ke baki Aureshin ba, ita matarsa ma bata daga hankalinta ba seke, Saudat abun nan naki yafara yawa, you better find another solution, kidena bawa kanki wahala, inbahakaba ki mutu bakiyi Aure ba"
Mamakine yacika Saudat ta kalli khadija "Au hakama zakice, dole ki gayamin haka tunda ke zakiyi Aure, to bari kiji ingayamiki wallahi kowa ze aura inze auri mata hudu seyasaki daya ya aureni, duk bala'in daza'ayi sedai ayi wallahi, matsalata tawace zanyi kokarin shawo kan matsalata inci ka burina, zanje gidan Salma sedai ai duk wacce za'ayi "
Murmushi khadija tayi" To Allah yabawa me rabo sa'a, fada da aljani ba wasa ba, kije Allah yabawa me rabo sa'a" tsaki Saudat tayi ta fice daga dakin, sosai khadija take dariya tace "sha3 zakigane bakida wayo, keda Habib har abada"
Duk yadda mutan gidan su khadija sukaso suga mijin dazata aura ki tayi , kome za'ayi sedai a gidan yan uwan babansu, amma taki yadda sam yazo gidan, invitation din daurin Aure ma hanawa tayi agani, saboda kar Saudat tagano, tayi mata hauka.
Yau khadija ta yanke shawarar zata gayawa kabir Aure zatayi zata sallame shi, yadena zuwa gurinta yaje shuma Allah ya hadashi da rabonsa, da magariba kabir yakawowa khadija wannan kudin, lokacin saura kwana takwas biki, ta karbi kudin tayi masa godiya suka gama hira zetafi tace "dan jirani ina zuwa" ta shiga cikin gida ta dakko iv ta fito, yana nan tsaye inda ta barshi ta miko masa kati. Yasa hannu ya karba yace "wannan fa?"
ba fargabar komai tace "duba kagani mana?"
Kafin kabir yagama karanta katin, yaji kafarsa na rawa, fitsari yacika masa mara
"khadija wannan invitation din na waye?"
"bangane ba bagashi a hannunka ba kana gani, sunan waye kuwa, katin Aurena ne, saura kwana takwas dama ita duniya haka ta gada, dan haka iname baka hakuri Kabir Allah yahada kowa da rabonsa, nasamu irin mijin danake mafarkin Aure dan haka
Cikin tsawa Kabir yace "Dalla malama dakata, kina nufin zaki Auri wani baniba wallahi khadija karya kikeyi, shekara shida ina wahala dake, amma kice bazaki Aureniba wallahi karya kikeyi"
"dalla dakata, kai namaka kalar auren matsiyaci kamarka, wanda se ya samo da kyar, nasamu hamshakin attajiri daidai dani kaima seka samo yar talakawa wadsa zata iya da talaucinka ku daidaita, inkana ganin bazaka hakura ba, ka lissafa nawa ka kashemin kobo bayan kobo za'a biyaka hada Riba "
" Wallahi baki isaba, kece babbar matsiyaciya kwadayayyiya, kije k Auri wani khadija, kin kyauta amma wallahi yadda nasa uwata kuka saboda ke, kema se kinyi wanda yafi na uwata, zan nuna miki ni dan halak ne, amma ki saurari matakin dazan dauka akanki, anta gayamin zakiyi Aure amma ban yadda ba yau kin gayamin da bakinki, wallahi sena wulakantaki a idon duniya, sena turamiki bakinciki mafi muni da zeyi ajalinki"
Kare masa kallo tayi tsaff sannan tace "kai kana ganin har akwai wani bakinciki, zanyi Aure a gidan Naira, zan rayu da wanda nakeso, jeka kayi abunda kaga zaka iya, khadija ce kafi kowa sanina sha3 kawai, idan nayi Aure bazaka kara ganina bama dan wahala" ta shige ta barshi a kofar gidan
Zubewa kabir yayi a gurin, yanajin kaman zuciyarsa zatayi bindiga wai yaushi khadija tabawa katin Aurenta.
Salma tana gabaan dressing mirror tana shafa mai, ta kalli envelope din invitations da Habib ya ajiye mata tsaki tayi ta ture envelope din invitations din suka zube kasa, a hankali ta kai hannu ta dakko na daurin Aure tana dubawa
Duf! Duf!! Duf!!! Taji kirjinta yana bugawa
Khadija Munir yakasai tunani take ina tasan wannan sunan, take sunan Saudat ya fado mata Saudat Munir Yakasai, taduba inda za'ayi daurin Aure unguwar su Saudat ne layinsa
Ji tayi kaman numfashinta ze dauke, wayarta ta laluba ta nemo lambar Saudat, jikinta na bari, Saudat ta daga sama2 Salma take jawo Numfashi tace
"Saudat waye
ze Auri khadija?"
Cikin rashin fahimta Saudat tace "lafiya kuwa Salma?"
"ki gayamin wa khadija zata Aura?"
Takuma tambayar cikin karaji
Saudat tace "nima bansaniba amma naji tace sunanshi Habib"
"INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI UN!!!!!! "
Salma ta furta da karfi
A ko yaushe ina alfahari daku masoya wannan Novel ina godiya da addu 'oinku
Sannaan masu rokon adinga posting a Facebook insha Allah za' a fara posting din Littafin ABDUL JALAL
Facebook tundaga farko
Insha Allah, za'afara posting a group din
AISHA HUMAIRA NOVEL FANS (Daddy's girl) dakuma sauran groups nagode sosai

Da sauri Saudat tace "Salma lafiya kuwa? Wai meya faru ne?"
Cikin kuka tace "dole kicemin meyafaru Saudat, kuncuceni ina zaman lafiya da mijina, amma ku yaudareni keda yar uwakki wallahi bazan yafe muku ba Saudat, kije da Allah nabarku da Allah daga ke har khadija" cikin rashin fahimta Saudat tace "bangane me kike nufiba Salma, dan Allah kimin bayani"
"Au saboda baki da kunya har bayani kike nema inmiki, Azzalumai kawai, wallahi bazan yafe muku ba na yadda dake kun hada kai da yar uwakki kun cutar dani cuta mafi muni kuda Allah" ta kashe wayarta, ta dora hannu akai ta fashe da wani irin matsanancin kuka me tsuma zuciya
"Na shiga uku ni Salma, menamuku kuka kwacemin miji, mijina mafi soyuwa a gareni shi zaku auremun Habibin nawa, shi zaku auremun na shiga uku ni Salma, meyasa nasanki Saudat" haka tacigaba da kuka tana surutai.
A salube Saudat ta sauke wayar, takasa gane inda maganganun Salma suka dosa, meye alakarsu da Auren mijin Salma. Tana cikin wannan tunanine taji ana shelar ankai lefen khadija gidan kanin babansu, akwati ashirin da hudu, gida ya dau sowa da hayaniya
"Akwati ashirin da hudu"? , Saudat ta maimaita, "itakuwa khadija ina tasamo Attajirin mutum haka? Waye wannan ze Auri khadija haka, shiyasa take boye shi, to tabbas idan har bansamu Auren Habib ba, sena shiga na fita naraba khadija da Auren nan koda tayishi, dan bazeyuwu tayi Aure tasamu Attajiri haka, nikuma ina gararanba ba"
Tafito tsakar gida yan gida nata surutu, wasu na san barka wasu na kushewa, suna agarin kwashe2 kil dan yankan kaine, inbahakaba akwati ashirin da hudu sekace wata yar gwal, yayinda bakin mahaifiyar khadija yaki rufuwa dan murna.
Khadija bata gida dan sedare ta dawo, yauma Saudat gurin khadija ta tafi
"Khadija nikam dan Allah ki gayamin waye mijin nan ko a hoto ki nunamin shi, akwati ashirin da hudu dozen biyu fa, sana'ar meyake haka"
"mekike ci na baka na zuba, har gidan nan zezo ranar daurin Aure kijira zaki ganshi ai, koma sana'ar meyake ni ina ruwana"
"sewani Boyeshi kike kaman ciwo, zamu ganshi dai muga meye ake boye mana, nace wai yazakiyi da kabir ne"?
Tsaki khadija tayi "Kabir din banza, nabashi katin daurin Aurena, yagama zage zagensa da kumfar baki, uwassa ma tayi tagama, nace yaje yai duk abunda yaga ze iya"
"hmm khadija manya, amma Kabir be cancanci haka daga gareki ba, ya miki wahala be kamata ku rabu baran baran ba"
"to ko zaku daidaitane keda shi?"
"Allah ya kiyaye ke ki auri me kudi nikuma ki hadani da matsiyaci Allah ya kiyaye"
"yo kuma ni sekiga laifina"
"to abar wannan zancen dazu tela ya aiko miki da dinkinki"
"Aiko ya kyauta, dama nagama biyansa kudinsa"
"Khadija munyi waya fa da Salma dazu" wani mummunar faduwar gaba ta ziyarci khadija amma ta dake tace "Allah sarki"
"Amma wasu magamganu ta dingayi da bangane musu ba"
"kamar ya kenan"
"ni kaina ban gane me take nufiba, Amma zankuma kiranta, yadda take maganar tana cikin damuwa"
"Saudat duk wanda za'ayiwa kishiya ai dole yashiga damuwa, mussaman bw san da wacce kishiyar zata shigo ba, kibata shawara cewa ta mike tayi tsaye, dan duk wata mace a yanzu musamman wadda zata shiga gidan me mata toda shirinta take zuwa"
"bata tsaya ta saurareniba balle in bata wata shawara, bari dai ayi bikinki agama, nikuma zan mike inyi fafatuka nima inshiga a ta uku" dariya sosai khadija ta dingayi mata "lallai Saudat yakamata kema seki dage Allah yabawa me rabo sa'a"
Yau Habib yadawo daga tafiyar da yayi, dan satin biki yakama, dan gidansu khadija har sunfara wasu events din da mamakinsa koda yadawo Salma bata gida, yakira wayarta amma taki dagawa. Yasan bata da wasu kawaye ko gurin zuwa a kano dan haka a ranar ya shirya ya nufi maiduguri, aikuwa yanazuwa tana can gidansu gaba daya bata hayyacinta banda aikin kuka babu abunda takeyi, dayake shima gidansu ne be jira amma sa isoba ya shiga gidan ba kowa se ita kadai a palour a kwance akan doguwar kujera idonta duk ya kumbura saboda kuka
"Salma meyasa kika taho kekadai baki gayamin ba, inata kiran wayarki kinki ki dauka hankalina ya tashifa"
Banza tayi masa ta dauke kanta, "haba Salam meyake faruwa ne?"
"dan Allah ka rabu dani Habib karshen wulakanci kayimin shi, karasa wadda zaka Aura se yayar kawata duk matan dake garin nan, bakasan wacece khadija ba, amma ka rubuta ka ajiye sekayi danasanin wannan auren kuma bazan koma gidanka ba nagama Aurenka Habib, am really disappointed on you " mikewa tayi zata bar palourn ya riko hannunta amma ta fizge ta wuce dakinta ta kulle kofa, jiki
a sanyaye yanemi guri ya zauna ya dafe kansa a gurin, Salma tanada mahimmanci a rayuwarsa baze taba bari kishinta ya rufemata ido ta rabu dashi ba, amma me take nufi daze auri yayar kawatta dama tasan khadija ne? Mikewa yayi ya nufi part din mahaifin Salma.
Amma yana zuwa ya tarar yanada baki dan haka yajira ya gama sannan yashiga, mahaifin Salma na ganinshi yafara murmushi "Ango kasha kanshi, saukar yaushe haka ba Labari" dan sosa kai Habib yayi ya samu guri ya zauna yace "Abba dan Allah ka tayani bawa Salma hakuri, duk na rasa gane kanta, munyi sallama lafiya na tafi na dawo na tarar bata gida ta taho nan, nace tazo mukoma tace bazata koma gidana ba" Ajiyar zuciya mahaifin Salma yayi sannan yace "Mata se addu'a, ni na dauka kasani kai ka batta tazo ai, kuma mahaifiyarta batacemin yaji tayo ba, tashi muje yaudin nan zaku koma kano tare Insha Allah"
Suka mike suka tafi dakin Salma, Abba yace ta bude masa shine, haka ta taso ta bude,
Nan ya dirar mata da fada ta inda yashiga bata nan yake fita ba, yaimata kaca2
Cikin kuka tace "Abba kayi hakuri amma yayar kawatace fa, meyasa yaya Habib zemun haka"
"ko kawartaki ce aiba haramun bane ba, kuma daba'a Aure daba a Aureki ba" daga nan ya yakoma yimata nasiha da rarrashi, ya hadasu gaba daya yai musu nasiha yai musu Addu'a, Abba be bari maman Salma ta dawo ba yace ta shirya tabi Habib sukoma Kano.
Da magariba Saudat tanata safa da marwa a daki, tarasa meyake mata dadi, khadija zatayi Aure ta batta, gashi khadija tasamu me kudi itakuwa ko oho, ga Salma na wasu maganganu da bata gane kansu ba, "gaskiya yakamata inyi wani Abu, bari inji in Salma na gida gara tamin kwatancen gidanta inje inji komai, sannan inyi fafutukar haduwa da Habib"
Wayarta ta dakko da sauri ta dannan lambar Salma, aiko a fusace Salma ta daga wayar "me kike nema a gurina kuma, kun kwacemin miji, hakan yayi sanadiyar samun sabani da iyayena, kun rabani da farinciki na, shine kika bugo kiji kona mutu ko? To ban mutu ba da raina"
Cikeda mamaki Saudat tace "dan Allah Salma kiyi hakuri bangane mekike nufi ba"
"dole kice baki ganeba, maciya Amana kin hada kai keda yayarki zata Auremin miji, Saudat kurasa wanda zaku cuta seni Habib dina yayarki zata Aura, nagode Saudat karki kara kirana a waya, kuma ko a lahira bana fatan Allah ya hadani da ireiren zuri'arku" Saudat bata karasa gane me Salma take nufi ba, dan kojinta bata gamayi ba, dan tuni ta saki wayar a kasa, kokari take ta tabattar da bacci take kokuma idonta biyu, kaman wadda aka tsinkula tayo waje da sauri daga dakin.
Khadija tana kwance tana wayada Habib
"Hayatee dan Allah kazo inganka mana, tunda satin biki yakama banaganka ba kuma kacenin kadawo daga tafiyar"
"kiyi hakuri Dijart, wallahi Salmace duk ta birkicemin, kuma bata da lafiya dole ina tareda ita kiyi hakuri, Tana bukatar kulawa ta mussaman"
"nibana bukatar kulawarka kenan?
" bahakabane ba deejart, ita daza'ayiwa abokiyar zama tana bukatar rarrashi da kulawa, yawwa nace dama kinsan Salma ne? "
" Meyasa ka tambayeni"
Saudat ce ta fado dakin bako Sallama tayo kan Khadija, da sauri khadija ta tashi zaune ta kashe wayar
"Khadija wane Habib din zaki Aura?
Waye Habib din?" dama khadija tasan wannan ranar zatazo, dan haka ta mike da sauri ta rufe kofar dakin, saboda yan biki sunfara zuwa gidan da mutane, ta dawo ta kalli Saudat tace
"ina jinki, mekike cewa?"
Cikin fada tace "tambayata ma kikeyi? Waye Habib din dazaki aura?"
Cikin dakewa tace "Habib Kamal me Gwal, mijin Salma kawarki shi zan aura" A razane Saudat ta kalleta "ke yanzu khadija bakji kunyar gayamin haka ba, macuciya Azzaluma, na yadda dake kici amanata, mijin kawata, wanda nakeso nazo nagaya miki matsalata, kikace zaki temakamin ashe cuta ta zakiyi khadija, na yadda dake amma kimin haka"
"ke dalla dakata, mekikace mijin kawarki, aigara ace nina aureshi akanki abun kunyar seyafi sauki, ni abun kunya gaba na bashi ba bayaba, kekikace ranar biyan bukata rai ba abakin komai yakeba, kema Auren cin amana kikaso kiyi ai, Saudat na dade ina mafarkin Auren miji irin Habib tun ranar da naganshi naji nakamu da sonsa amma abun mamaki, kika rigani gayamin kema kina sonshi, a lokacin nan dana gayamiki ina sonsa nima toda biyu babu za'ayi, shiyasa namiki shiru, na gargadeki da kinemi wani karki tsaya jiran Habib amma kimayi bris dani, kisani mutuwa ce kadai zata iya hana Auren nan, duk wani shige da fice dazakiyi a yanzu aikin gama ya gama baki isa kiyi komai ba, dan ba karamin shiri nayi ba"
Fashewa da kuka Saudat tayi tace "khadija da tun farko kin sanardani kina son Habib, dazan iya barmiki shi, da ban wahal da kaina haka ba, amma kika bari na dinga lalube kina rainamin hankali, tun tasowarmu kaf cikin yan uwana uwa daya uba daya dake na yadda, amma kinmin cutarwa mafi muni khadija!!!! Kinsa na zubda hawaye kin bakantamin rai kinmin tabo me muni da bazan manta ba, kin kwace abunda na kallafa raina aki, shikenan ki shirya ki rubuta ki Ajiye idan harni Saudat yar halak ce haihuwar uwa da uba, wallahi senamiki mummunan tabo kema ki Auri Habib ga daula nan kinsamu, amma ki saurar zakiga nima abunda zan iya" ta juya da sauri fuskarta duk hawaye zatayi waje khadija ta rikota, karo na farko dataji tausayin Saudat amma ta basar tace
"Saudat ki fawwalawa Allah lamarinki, kiyi wanka da fetur, sannan ki hau risho da wandon leda yafimiki sauki akan hana Auren nan, kisawa zuciyarki salama kibi a sannu kema sekiga kin samu ko wanda be karasa Habib bane, kinfi kowa sanin hatsarina karkije garin daukar fansa kikuma ruftawa wani tarkon wanda bazanso hakan ba, har yanzu ina kaunarki yar uwata, kar abunda nayu miki ya shafi zumunci da kaunar dake tsakaninmu"
Fizge hanunta tayi da karfi ta bude dakin ta fice, Ajiyar zuciya khadija tayi ta koma ta zauna tayi murmushi tace "Saudat kenan, na dade ina ankarar dake amma baki gane ba, naciki wasa se hakuri"
Tundaga lokacin nan Saudat tafara rashin lafiya har akayi gama bikin khadija, tarasa nutsuwarta gaba daya, banda tunani babu abunda take, so take ta samu hanyar dazata turawa khadija bacin rai dan ta huce, tarasa mezatayi danta huce, kasa samun mafitane yasata takara shiga damuwa da halin rashin lafiya, yayinda khadija ko a jikinta hidimar bikinta kawai takeyi, anyi hidima sosai a bikin khadija anci an sha, anyi watsi da nera yadda yakamata.
Kabir yashiga matsanciyar damuwa gameda Auren khadija, yayi kuka, yayi kukaba adadi, ga fushi da mahifiyarsa keyi dashi, ga basussukan mutane saboda yadda yakecin bashi yana kashewa khadija, gaba daya duniya tayimasa zafi, yarasa meyake masa dadi.
Tunda Allah yasa khadija ta shiga gidan Habib komai yafara rushewa, gaba daya hankalin Habib yakoma kanta, Salma dama bata da surutu, khadija tafita baki, dan haka ta shiga hadasu fada, dama khadija bata kaunar dangin Habib tunda taji labarin basa son Aurenta, da Habib baya wata guda cikakke beje maiduguri ba amma tunda ya auri khadija seyayi watanni bejeba, Salma sedai ta zauna tasha kuka, ya shirya musu tafiyar wata daya Dubai shida Salma da khadija, Salma tace bazataba, ya dauki khadija suka tafi basu dawoba seda sukayi wata uku, gaba daya Salma ta zubawa sarautar Allah ido.
Idan yan uwan Habib sukazo gidan ta dinga rashin mutunci kenan tana habaici
Tunda taje dakin miji Saudat bata taba zuwa gidanta ba balle takirata a waya, hakazalika seda ta shekara guda cif sannan ta yadda tabi Habib maiduguri ta gaida mahaifiyarsa, tunda mahaifiyar Habib taga khadija taji sam bata kwanta mata ba dan sam babu alamar kunya ko kara a tareda ita, tunda ya aureta shekara guda sannan tazo ta gaishesu. Ta lura khadija a tsaye take ga Salma ta rame matuka tayi duhu, dan bata gayawa kowa meyake damunta, kota fada ba a goya mata baya sedai ace tayi hakuri kishine ke damunta.
Maman Habib ta kirashi dakinta, ta dinga masa fada, akan yadinga adalci tsakanin matansa, in bahakaba seyayu danasani, dan taga alamun wannan tsagerar daya aura kamar suna cutarda Salma, dan ita sam wannan yarinyar batayi mata ba, banda rashin mutunci shekara guda da aure sannan sukazo yakawota gida sugaisheta shi kansa ya canza gaba daya,
Haka yaita bata hakuri, yace insha Allah ze gyara amna yana kokarin yimusu adalci.
da kyar khadija ta hakura ta kwana biyu a garin tace ita ya maida ita gida ta fuskanci danginsa basa kaunarta.
Watan khadija biyar a gidan ta fuskanci tanada ciki, koda tagayawa Habib yayi murna matuka, tunda ya auri Salma shekara biyu kan na uku amma bata taba ko batan wata ba, sunje Asibiti ance lafiyarta kalau, dan haka yayi murna da wannan cikin
"Habib kadena murna da wannan cikin zubar dashi zanyi wallahi!"
Cike da mamaki ya dubeta "kamarya ya? Ina neman abu in samu kice zaki zubar khadija why?"
"ban shirya haihuwa yanzu ba wallahi, da kuruciyata bazan tsufa ba wahalar yaya ta kasheni ba, tun kafin muyi Aure kasan burina inason yin karatu me zurfi a kasar waje, tayaya zanyi karatu da ciki, kwata2 yaushe nayi Auren zanyi ciki, wallahi sena zubar"
khadija kiyimin rai dan girman Allah kiyi hakuri, kibari ki haifamin cikin nan seki tafi karatun"
"sekuma kayi, in kanason cikinka seka dauka ka maida shi jikinka ka haifa, amma indai a jikinane bazezo duniya ba gara ka hakura inkun matsu kaje kaimata cikin ta haifa maka"
Saroro yayi yana kallonta, ba kunya take gasa masa wannna maganganun.

"haba khadija, yanzu dan sunnan zakice zaki zubarmin, ina son yara sosai, ki haifamin ko dayane seki tafi karatunki bazan hanakiba, mama tana matukar son yara, tanason jikoki, dan Allah kibari ki haifamin"
Mikewa tayi ta shige toilet tabarshi a gurin a zaune. Tana shiga bandaki tayi tsaki tace "in maman nason yara, se itama ta haifa aiba abun kunya bane, aikin banza nibahakane yakawoni ba"
"ikon Allah Salma nata nema ido rufe tana Addu'a, itakuma Allah yabata zata zubar"
Haka Habib yaita fama da Khadija, a haka har yakoma Dubai, ta shirya ta tafi gidansu sunyi murna sosai da ganinta, khadija tanada kyauta tanayu musu aike sosai, kama daga Abinci sutura da kudi, amma idan Habib yayi niyyar yiwa yan uwansa kona Salma wani abu, indai tasani seta hanashi, amma itakuma ta nayiwa yan gidansu.
Ranar dataje gida seda ta tsorata dataga Saudat tayi rama matuka, tayu duhu duk wannan kwalisar babu, har cikin ranta taji babu dadi yanayin dataga Saudat, dan haka ta dan damu, daki tabi Saudat tacewa sauran kanensu sufita subasu guri, b musu kowa ya watse, tazo kusada Saudat ta zauna ta kalleta tace "yar uwata, meyake damunki haka? Saudat kinga yadda kikakoma kuwa?"
Tsaki Saudat tayi, ta juya mata baya
"Saudat nasan ban kyauta mikiba, amma rayuwa bazata tafi a hakaba, kisani dama can Allah be rubuta Habib mijinki baneba, idan kika cigaba da wannan rayuwar tozaki kashe kanki a banza ne, tunda kinsan Bazaki samu Habib ba, Saudat inaso mucigaba da zumuncinmu, kimanta da abunda yafaru ki karbi kaddararki, Allah yafito miki da miji, indai kudine Saudat duk abunda kikeso zanmikishi Insha Allah" mikewa zaune Saudat tayi ta kalli Khadija
"Zumunci nidake har abada wallahi, kin riga kin rusa alakar dake tsakanina dake, ke kinama yaudarar kanki ne da kike cewa wai mukoma kaman da, naji tawa kaddarar kenan da tasameni a sanadinki, kema ki saurari taki kaddarar, malama ki tashi kibaani guri, ficemin a daki"
"Saudat nikike kora haka?"
"na korekin ko uwata ce tamin abunda kikayi min sena rama, dalla malama fita munafuka"
"shikenan tunda haka kika ce, inkika dawo hayyacinki zaki gane me nake nufi" khadija ta mike ta bar dakin.
Bayan tafiyar Habib da yan kwanaki khadija Taje chemist tace subata maganin abortion, me chemist din yace shi gaskiya baya irin wannan harkar, take ta zube masa uwar kudi, take jiki na rawa yabata magani da yadda zata bi cikin ya zube, ta dauki maganinta ta tafi gida, yadda yace mata haka tayi amfani dashi, aikuwa ba adau wani lokaci ba mararta ta dinga ciwo wuni tayi tana murkususu a haka har seda cikin nan ya fita, tasha wahala matuka, gashi ba wanda tagayawa, ko Salma da suke zaune gida daya bata mata magana, haka tai wahalarta ita kadai ta gama.
Saboda daukin cikin da Habib yakeyi, sati uku yayi ya dawo gida, gurin khadija yafara sauka, se wani sabon kalan soyayya yake nuna mata sabida duk zatonsa cikin yana nan.
Da daddare yana cin Abinci shida khadija, ya kalleta yace "cwt Deejah, Wani suna kikeso musakawa babynmu inkin haihu, ina son in sanarwa su yaya hajjo, cewar munsamu rabo, ko baby" dan ya tsina baki tayi
"mhmm kaga dakabar wannan batun gayawa mutane ansamu rabo, bayan tafiyarka na fadi a toilet cikin ya zube, ban gayamaka bane saboda kar hankalinka ya tashi"
Abincin daya hadiya ne yaji ya makale masa a makogwaro yaki wucewa,
"kin zubarmin da ciki ko khadija?"
"niba zubarwa nayi ba zu.....
" Shut up!!! "
Yafada cikin tsawa da sedata razana
" saboda kin rainamin hankali kike cewa zubewa yayi, wato baki hakura ba shine kika zubarmin da ciki, dan kinga ina lallaba ki ko? Nikikayiwa haka ko? Har innuna miki abunda nakeso amma ki shure kiyi son ranki, kin zubar Minda ciki nagode "
"Ahhh Hayatee wallahi.....
" yimin shiru"
Ya katseta, ya tashi ya dau wayoyinsa yabar palourn, dafe kai tayi bata taba tunanin Habib ya iya fada haka ba, saboda gaba dayansa silent ne, bashida hayaniya sam. Amma fushinsa baze hanata cinma burinta na rayuwa ba.
Wasa2 tunda yabar part dinta seda yai sati guda bata ganshi ba, ko ta waya, dan haka ta shirya ta nufi part din Salma, tana zuwa ta tarar Salma na kitchen tana girki batabi takan Salma ba ta nufi palour na biyu,
"lafiya zaki shigomin ba sallama ki wucemin daki?"
"ba ruwanki ba gurinki nazo ba" ta shige tabar Salma a gurin, tana shiga kuwa ta tarar da Habib a palourn yana karanta jarida, karasawa tayi ta zauna kusada shi
"Hayatee kwana bakwai banganka ba, meyasa dana gayamaka abunda yafaru baka yadda daniba" shiru yayi yaki dagowa ya kalleta, hannunsa ta riko ya dago
a fusace
Amma seyaga fuskarta sharkaf da hawaye, nan take jikinsa yayi sanyi
"Hayatee, duk lokacin danakiraka Hayatee i mean it har cikin raina kai rayuwata ne, meyasa ka karyatani baka yadda bani na zubar maka da ciki ba, inason abunda kakeso tsautsayine ya gifta cikin ya zube dan Allah kayi hakuri" ta zube akan gwiwoyinta tana kuka, hannu yasa ya dagota ya rungumeta yana share mata hawaye
"is ok am sorry my deejat, ya wuce kidena kuka" a hankali tace "I miss you Hayatee, dan Allah karka kara fushi dani haka"
"I miss you too baby, bazan kuma ba"
Khadija yar duniya ce yanzu kana zaune zata siyeka.
ganin shirun yayi yawa yasa a fusace Salma tanufo palourn, Amma abunda idonta ya gane mata yasata ja da baya da sauri, jitayi kaman andoramata dutse a zuciyarta, kitchen takoma ta toshe bakinta tana kuka, tanaji tana gani anzo har cikin gidanta an kwace mata miji.
Antyn Jalal ta kalli Jalila data tattara duk wata nutsuwarta kaman tana daukar karatu tace
"kinga rana tayi, shabiyu takusa, kuma da azahar zamu koma maiduguri, zan kara takaita miki labarin nan dannima bakomai nasani ba, Amma kinsan meyasa khadija tayi nasara ta kwace mijin Salma?"
Girgigiza kai Jalila tayi
"Salma ta zurawa Habib ido tana ganin kaman yadena sontane, maimakon ta tashi tsaye tayi fighting ta gwada masa soyayya, ta kwaci mijinta, seta karaya da wuri tana ganin kaman bazata iya kishi da khadija ba tafi karfinta, ta zuba musu ido"
Haka rayuwa tacigaba, seda Khadija ta zubar da ciki kusan hudu Habib be saniba, data fuskanci tasamu ciki setaje ta zubar, daga karshema taje tai planing hankalinta kwance ba wanda yasani, tacigaba da cin amarcinta, yau suna wannna kasar gobe suna waccan kasar, khadija tayi duk me yuwuwa takara farraka tsakanin Habib da Salma baya Jin maganar kowa se khadija, khadija yar kwalisa ce yar gayu, ta iya gayu ga girki da iya magana, yanzu zatayi laifi amma take zata mantar dashi duk wani laifi datayi, seda khadija ta shekara uku tana cin duniyarta da tsinke ta taka wanda takeso duk meson wani abu a hannun Habib seya biyo ta gurinta, Salma kam yau da lafiya gobe babu saboda bacin rai kullum cikin guma mata khadija take, duk wani abu datasan zatayi ta bata mata shi takeyi.
Sedai ta shiga daki tayi kuka.
A yan shekarun nan Saudat haka takeyinsu ba walwala tayi iya tunaninta taga hanyar dazata rama abunda Khadija tayi mata amma takasa samu, kuma tayiwa kanta Alkawarin kozata mutu wajen daukar fansa setayi, zata nunawa khadija ba ita kadai ta iya makirci ba, zata rama inda babu wanda ze gani balle ya tausayawa khadija. Saudat haka tasamu FCE ta shiga take zuwa makaranta dan ta ragewa kanta zafi. Tsawon shekarun nan uku zazzafar gaba Saudat tajeyi da khadija duk abunda tasan ya shafi khadija nuna masa kiyayya take muraran, har mutane suka fara fuskantar hakan, yan gidansu sunyi mamakin dama akwai abunda ze hada khadija da Saudat dazesa sununawa juna kiyayya kasancewar ba'ajin kansu.
Khadija ta hurawa Habib wuta kan lallai ita seyasamo mata Admission a Dubai ko Egypt tafara karatu, ya nunamata yan uwansa bazasu yadda da hakaba, tayi hakuri duk makarantar datakeso a Nigeria ze kaita amma banda kasar waje, amma fafur ta badawa idonta toka taki, haka yafara nema mata Admission a Dubai ba wanda yasani seshi da ita, Allah ya temaketa tasamu, yasamu Salma yace itama ze nema mata se sukoma can gaba daya, Salma tace bazata ba sedai su barta anan duk sanda yayi niyya in yasamu lokaci yazo yaganta, ya kada ya raya amma Salma tace itafa bazata ba suje se sun dawo.
Haka Habib da khadija sukaje suka tare a Dubai, ita tana karatu shikuma yana kasuwancinsa, seyafi wata uku bezo Nigeria ba gurin Salma ba inma yazo bayafin kwana goma ze juya, hatta mahaifiyarsa ta zuramasa ido, tana masa Addu'ar Allah ya shiryeshi, yana daga cikin kaddararsa Auren hatsabibiyar mace.
Wani zuwa da mahifiyar Habib tayi itada kannensa mata nida yayata,
Gidan bakowa se Salma kawai mama ta tambayeta ina Habib ina khadija nan ta fashe da kuka tagaya mama duk abunda yake faruwa, Mama hankalinta ba karamin tashi yayi ba, ta dinga yiwa Salma fada, danme bata gayamata irin rayuwar da takeyi agidanba kenan, nan da nan ta kira Habib tace kome yakeyi ya yanke su dawo Nigeria tana nan tana jiransa. Yagaywa khadija tace wallahi bazat bar karatunta ta taho ba, shidai ya tafi shikadai, haka Habib ya taho yabarota a can.
Ba karamin bacin rai mama ta nunawa Habib ba tace masa yazama wajibi yadawo da Khadija Nigeria bata yadda da batun karatu a kasar waje ba tunda bashida hankali, ya tare a gindin mace yana zaluntar yar uwassa, yaita bata hakuri, gefe yana fargabar yadda ze sanar da Khadija batun fasa karatunta.
Yaita bawa mama hakuri amma fafur taki yadda tace se khadija ta dawo kasa Nigeria, hankalin Habib ya tashi yarasa ya zeyi da wannan batuna A
Mama, haka ya shirya ya koma dubai yasanarwa khadija hukuncin mama, amma tace ita bazata dawo ba, yasan yadda zewa mama ta hakura amma ita karatunta yafara nisa dan haka yayi hakuri.
Mama tanata matsa masa lamba akan ya dawo da khadija gida, ana cikin wannna halinne khadija ta fuskanci tana dauke da juna biyu abun ba karamin mamaki yabawa khadija ba, yaza'ayi ace tana planing amma tasamu ciki, nan da nan ta shiga damuwa. Tabass barin cikin nan shize hanata da ciigaba da karatunta, gashi bata san kowa ba a Dubai balle tanemi maganin zubar da ciki, dan haka ta samu Habib tace masa ta yadda sukoma Nigeria, ba karamin mamaki yayi ba yadda akayi ta yadda ta dawo Nigeria.
Bayan sun dawo ne, taje inda tasaba samun maganin zubarda ciki tazo ta sha, seda ta kwana biyar tana zubarda jini ba wanda yasan me yafaru, da kyar tasamu jinin ya tsaya amma ba karamin galabaita tayi ba.
Ammame bayan jinin ya dauke haka tacigaba da rashin lafiya, kullum ba lafiya tana kwance kusa
wata biyu taki zuwa asibiti seda taji tana neman ta mutu sannan ta shirya ta tafi Asibiti lokacin Habib baya nan, Asibitin dasuke zuwa taje sukayi mata gwaje2 suka tabattar mata tanada cikin wata uku da sati biyu, abun yabata mamaki dama cikin nan yana nan be fitaba, suka dubata suka bata magunguna, tana barin Asibitin bata zame ko inaba se chemist din da take karbar magani, tai masa bayani yabata wani maganin dayafi
wancan karfi, sannna ta tafi gida.
Khadija na barin Asibitin, doctor Hisham yakira Habib ya sanar masa yanzu amaryarsa tabar Asibitinsu kuma tana dauke da juna biyu na wata uku da sati biyu. Habib yayi murna a take yaiwa Hisham transfer na kudi, tukuicin Albishir, yana katse wayar ya kira khadija
"Madam sannu ya jikin naki"
"Wayace maka banida lafiya?" *"Hisham ya sanarmin kina dauke da babyna, na wata uku Ashe shike wahalar min dake, Allah maji rokon bawa abunda nake ta nema tunda kikayi bari se yanzu Allah yasa aka kuma samu, Masha Allah, Allah yarabku lafiya my deeja" hade rai tayi kaman tana gabansa amma ta maze
"Hmm Hayatee ka kyaleni, nasha magani duk jikina ya mutu"
"Eyya sannu, i wish ina kusa danamiki tausa, amma a satin nan zan dawo Insha Allah"
"shikenan se anjima" ta kashe wayarta, lallai doctor Hisham munafikine shine har ya kira yagayawa Habib, to gara ma yadena rawar kafa dan "kafin kadawo na zubar dashi ta rariya sedai kai yadda zakayi se burina yacika, senayi karatu me zurfi a abroad "
Haka takuma shan maganin zubar da ciki ta dinga malalar da jini, ta kira Habib tagaya masa hankalin sa ya tashi sosai, amma bata gayamasa wani abu ta shaba, yakira doctor Hisham ya sanar dashi, har gida sukazo don duba khadija, dole suka dauketa zuwa Asibiti, da kyar aka ceto ta saboda tasha wahala sosai, a satin Habib ya dawo an rike Khadija a Asibiti ana bata kulawa ta musamman still akayi scanning still cikin yana nan be fitaba, doctor Hisham ya gano tayi Amfani da Abortion pills amma be gayawa Habib ba.
Ya sameta ya dinga mata nasiha, sannan yace idan makamancin haka yakuma faruwa ze sanarda Habib gaskiya, ze gayamasa tana shan Abortion pills ne.
Sannan doctor Hisham ya sanar da Habib cewa zata samu sauki ya kwantar da hankalinsa.
Tunda Habib yasamu labarin cikin nan yakuna tattare a gurin khadija, yake matukar lallabata, itakuwa khadija batun cikin nan ya tsaye mata a rai, sam bata kaunar cikin nan, ga cikin ya hanata sakat saboda laulayi yauda lafiya gobe ba lafiya Habib yana bata kulawa iyayinsa amma ita kawai yadda zata zubar da cikin nan takeyi, takuma shiryawa ta tafi tasamu me chemist din nan tace masa ita so take inba ze iyaba ya hadata da wanda zasu ciremata cikin nan.
Me chemist din nan ya nuna mata illar yin hakan zata iya rasa ranta kokuma tajawa kanta mummunan ciwon daba lallai ta warke ba. Haka khadija takoma gida, duk yadda zatayi cikin nan ya zube wannan karon kin fita yayi, dukda basa jituwa da dangin Habib amma sunyi murna da cikin nan nata,
Abun duniya yakara hadewa Salma, tarasa meyake mata dadi, gaba daya Habib ya canza kaman ba Habib dinta dasuka sha soyayya a bayaba, ga sharri da khadija take mata taita hadasu rigima da Habib, ga rashin lafiya data ketayi, tana zuwa
Asibiti Akai mata gwaje2, aka sanarmata mata jininta ya hau sam hankalin Habib da nutsuwarsa ya tattarasu akan Khadija.
Salma ta shirya taje maiduguri tasami mahaifiyar Habib tace mata dan Allah tasa baki Habib ya saketa bazata iya zama dashi ba ta gaji, mahaifiyar Habib tai kokarin bata hakuri amma ta fashe da kuka "mama wallahi in Habib be sakeni ba zan iya rasa raina, dan Allah ki amince ya a raba Aurenmu" mahaifiyar Salma ma ta yadda tace a sakar mata yarinyar ta baze yuwu a kashe mata ya da bakinciki ba. Mama takira Habib tace tanason ganinshi ya shirya ya tafi.
Koda yaje maiduguri mama tagaya masa abunda Salma ta bukataHabib kuma yace besan zance ba, mama tace yadda Salma takeson Habib harta bude baki tace ya saketa lallai abun ya kai makura dan haka ta goyi bayan ya saketa ta huta haka,
Salma taje ta samu Habib tace
"Habib nasoka tun bansan meye soba, ka koyaddani sonka, Habib ina maka sona gaske shiyasa banason ka kasance cikin wanda Allah ze hukunta ranar Alkiyama, Habib banason Allah yakamaka da laifin rashin adalci a tsakanin matanka, shiyasa nakeso ka sakeni dan Allah Habib, sakina shize kara tabattarmin har yanzu akwai tausayina da kaunata a zuciyarka ka sakeni Habib " tana zuwa nan a maganarta ta sume a gigice Habib ya dakko ruwa ya zuba mata amma bata tashiba haka aka kaita Asibiti jininta ya hau sosai, kwanam ta guda da wuni a asibiti sannan ta farfado, koda ta farfado da kuka ta farfado akan dan Allah Habib ya saketa,
Mama ta titsiye Habib tace seya saki Salma,
"Mama wallahi bazan iya sakin Salma ba ina sonta"
"Kana sonta ka hada kai da makirar matarka kuke neman kasheta, Ka Saketa kokuma in maka baki"
Jiki a sanyaye ya furta ya saketa saki daya. Take Salma tayi ajiyar zuciya tareda murmushi tace "Nagode Habib ina maka fatan rayuwar Aure managarciya da matarka, Allah yabani mesona har abada"
Habib yayi zarya maiduguri akan Salma ta dawo amma fafur aka rasa me goya masa baya, Salma kuma tace itada gidansa har gaban Abada!!!
Khadija kam ko a jikinta, Murna ma tayi tace zata cigaba da rayuwarta yadda takeso, dama kishi da ita se wadda tayi gagarumin shiri, ganin yadda Habib yatada hankalinsa yasata tayi duk yadda tayi ya manta da babin Salma suka cigaba da Rayuwarsu.
Ba karamin kaduwa Saudat tayi ba dataji labarin Salma ta bar gidan Habib, bata taba tunanin hatsabibancin khadija ya kai taraba Salma da Habib ba. Dan haka abun yakara yiwa Saudat ciwo, yanzu duk wannan uban gidan da uwar dukiyar ita kadai ce matar gidan. Nan take taji Ranata yakara baci, "zaki gane baki da wayo khadija wallahi sena miki Abunda ga dukiya amma seta gagareki ci cikin kwanciyar hankali"
Haka khadija tacigaba da rainon cikin da tayi kokarin yafita amma yaki.
Wata tara labour yazo amma bazata iya haihuwa da kanta ba se cs akai mata aka ciro mata da namiji kato kaman Habib yayi kaki ya tofar saboda kama.
Seda akayi sati biyu ta warke saboda cs din da aka mata sannan akayi gagarumin shagalin suna, sam be gayawa khadija sunan dazesawa jaririn ba se ranar suna, ya sanar da sunan yaron ABDUL JALAL, sunan mahaifin Salma kenan!!!!
Tabdijan da alama Habib ya debota da zafi sunan baban Salma fa yasakawa dan khadija.

What's app only 07063065680.

Saudat ta danyi shiru sannan tace "kumafa hakane amma tayaya kenan?"
"bari muje gida zan gayamiki meyakamata kiyi"
Watarana Khadija ta shirya da dauki Jalal taje gidansu, suka wuni acan se magariba suka koma gida a hanyarsu takomawa ta hadu da Kabir, amma ta dauke kanta kaman bata sanshiba ta zuge glass din motarta tai tafiyarta, Kabir yayi mamakin girman motar da khadija take ja, kana ganinta zaka san tana cikin daula da jin dadi, gefe ga danta kaman ba dan hausawa ba kyakyawa dashi. Taja motarta tabar gurin ya dubi shikuma irin rayuwar dayakeyi ta wahala, ya gyada kai yace "wallahi khadija senayi silar kin fito daga wannan daular dan bazaki yaudareni a banza ba"
Haka Rayuwa tacigaba da gara Kabir wanda hakan yasa yafara shaye2 miyagun kwayoyi.
Bayan Rabuwar Salma da Habib an takuramata a gida akan lallai setayi Aure, wani Ambassador yafito yana sonta, akayi bikinsu, abun Allah ko wata guda batayi a gidansa ba Allah yasa ta samu ciki, Masoya da yan uwa sun tayata murna sosai har Allah yasa ta sauke lafiya ta haifi namiji akasamasa Mahmud, bayan mahmud ta haifi Yusuf da Yasmin, Mahmud shine wanda mukazo dashi, zakiga yana kama da Jalal. Amma Allah yayiwa Ambassador Ahmad Rasuwa shekaru biyar dasuka wuce. Dan haka tai zamanta a England.
Khadija ta karbi makudan kudi a hannun Habib tafara kasuwanci, tana zuwa kasashe daban2 tayi sarin kaya ta sayar, tana da manyan shaguna a fadin kasar nan, wanda dukkansu mallakinta ne.
Saudat ta haifi diya mace, bayan danta munir, wadda itace Ilham, khadija taita zaryar Asibiti akan tanason takuma samun ciki, amma abu ya gagara har wasu kasashen sukaje da Habib amma aka sanar matada bazata kara samun ciki ba, Mahaifarta tasamu matsala sakamakon rauni datayi saboda yawan shan abortion pills datai tayi, khadija ta damu sosai har tagaji ta hakura.
Saudat ta nunawa khadija komai ya wuce, Khadija ta dinga mata barin kudi baji ba gani, Khadija tagayawa Saudat halin da take ciki
"Saudat naso ace nakuma samun haihuwa, ko mace in haifa, Jalal yasamu dan uwa"
"tunda Allah yabaki Jalal dinma ai ki gode masa, dan wani har ya mutu bazega kwansa a duniya ba"
Gefe guda Saudat tayi farinciki jin cewa khadija bazata kuma haihuwa ba, hakan yasa takara kudurcewa ranta seta Rama abunda Khadija tayi mata akan Jalal.
Ummi ta dade bata haihu ba, sunyi girma lokacin da Allah yabata haihuwa, Tunda Allah yasa Ummi ta haifi yarinya mace, hakan yakara saka Jalal zaunewa a gidansu Jawwad, kullum suna tare suna Rainon Kanwarsu, Jalal yaitabin Uncle Aliyu kanin mahaifin Jawwad yana cemasa dan Allah asakawa jaririyar nan sunansa wato Jalal. Aliyu yabiye masa yace Jalal sunan mazane amma insha Allah zanmaka takwara, karka damu, Ranar Suna yasamata Jalila, yace yayiwa Jalal takwara, Habib yaji dadin karar da Aliyu yai masa, yadda suke nunawa dansa soda kauna, duk rikicin da Jalila takeyi intaji muryar Jalal yanzu zata fara murna, gaba daya Jalal jiyake Jawwad da danginsa sune komai nasa.
Fafur khadija tahana adinga kai Jalal dangin mahaifinsa, acewarta tunda basa kaunarta danta ma basonshi suke ba, Amma a haka Habib yake zuwa yakaishi ko a ranar ne su juyo, duk dangin Habib sunsan Jawwad, Jawwad yanajin yaren kanuri kaman yadda Jalal ma yafara jin fulatanci saboda kauna da shakuwa.
Jalila na karama sosai Mahaifinta yanemi Aiki a garin kaduna yatafi da Ummi da Jalila, saboda yawan tsangwama da iyalannasa ke fuskanta, dukda lokacin Jalal da girmansa yashiga secondary, amma haka ya dinga rikici yana kuka, Shi be yadda a tafi da Jalila ba ya saba da ita. Tare yake cin Abinci da ita, komai yagani na wasa se yace ita ze kaiwa, komai yaci seya ajiye nata. Jalal ya dade yana damuwa akan barin gari da uncle Aliyu sukayi, Abun har yafara bawa khadija haushi, yadda ya tashi hankalinsa akan wanda ba dangin iya ba na baba sun bar gari. Ummin Jalila seda tayi kuka lokacin dazata bar kano, saboda ta riga ta shaku da yaranta Jalal da Jawwad
Bisa ga Shawarar zulaiha, Saudat seta dakko Ilham tace ga Ilham nan tabawa khadija ta dinga debewa Jalal kewa ze manta da waccan yarinyar, khadija tayi murna da wannan kyauta da Saudat tayi mata, lokacin Ilham nada shekara takwas khadija ta karbeta, amma sam Ilham basa shiri da Jalal dan sam bata da kunya shikuma ga son girma, dan haka har dukanta yake, Jawwad yaita masa fada yace Ilham kaman Jalila takefa itama kanwarmuce, Jalal yace "Jalila ba mara kunya bace, ni Jalila ce kawai kanwata ba wannan ba"
Har yanzu khadija bata fasa yawace2 kasuwanci ba, Jalal ya tashine a tsakanin kwararo ba bu shakuwar uwa a tareda shi, Allah ne ya dubi Jalal ya hadashi da mutanene kirki irin dangin Jawwad.
Jalal yanada matukar kwakwalwa, sarrafa abu da haddace shi baya masa wahala, dan suna Jss2 suka Sauke Al'qur'ani, suka juya hadda, wanda wannan nasara tasu da taimakon Allah da taimakon Ummine da mijinta, Saboda itake tsayawa taga sun iya dukkan wani karatu dasuka koyo a makaranta, sunyi nisa sosai a haddarsu dan sunkai izufi Arba'in Rayuwar Jalal tafara samun matsala, Jalal yana SS2 a secondary komai nasa yafara lalacewa, sakamakon haduwa da miyagun abokai dayafarayi, Jalal yanada kyauta ga faran faran da mutane, ba babba ba yaro kowa nasane, duk wanda yakeda bukata Jalal ze dauka yai masa, hakan yasa har manya suka fara girmama shi suna gaisheshi.
Jalal lokaci daya ya canza watarana khadija bata kasa tana can harkar kasuwancinta daga Daddy se Jawwad da Jalal a gidan Ilham kuma tana gidansu, 'yan fashi suka shigo cikin dare, suka kama masu gadi suka kullesu, suka shiga cikin gidan, Habib yace su dauki duk abunda sukeso a gidan amma karsu taba masa yaransa, suka sakasu kneel down, sannan tattara abunda suka samu a gidan har zasu tafi dayan ya juyo ya saita Habib da bindiga, gaba daya yaran suka fara kuka, dan fashin ya musu tsawa amma suka ki yin shiru, dan fashin ya saita Jawwad yace "bari in kashe tilon dannaka dan yafiye maka komai a duniya kuma da alama yana sonka sosai" zatonsu shine Jalal, dan haka ya saita Jawwad da bindiga, Habib yace dan Allah karku kashemin shi, gaba daya yaranane, tunda kun samu abunda kuke so dan Allah ku kyalesu garani kukasheni, dan fashin nan yamasa banza ya dan kunamar bindigarsa, kawai Jalal ya mike tsaye, bullet din ya shigeshi a gefen kirjinsa, yan fashin na ganin haka, suka kwashi abunda suka kwasa suka gudu. A gigice Habib da Jawwad sukayi kan Jalal amma yana kwance kaman ba rai jini nata malala a kirjinsa, hakan ya firgita Jawwad kwarai shima ya suma a gurin, misalin karfe uku na dare haka ya daukesu ya tafi dasu Asibiti.
Da kyar aka cire bullet din a kirjin Jalal, ya galabaita saboda a gefem zuciyarsa bullet din yasameshi, shima Jawwad da kyar aka samu ya farka. Wannan fashi ana kyautata zaton dasa Hannun Kabir a ciki, amma ba'a tabattar da hakan ba. Seda Habib ya kai su Jawwad Dubai aka dubasu acam sannan hankalinsa ya kwanta, seda akayi kwanaki sannan khadija tasan meyafaru.
Akaita zuwa duba Jalal, Allah yatemakshi ba'a dadeba ya warke suka koma makaranta.
Mahaifin Jalal ya hada mahaifin Jawwad da manyan mutane akan harkar kasuwancinsa, wanda silar hakan Allah yasawa mahaifin Jawwad nasibi a kasuwancinsa, yasai gida a Sharada NNDC, suka koma, Jalal yasamu daddynsa yace masa dan Allah yanaso yasaimusu gidan dayake makawabtaka danasu Jawwad sukoma, haka kuwa akayi suka tattara suka koma kusada juna, ga gida ga gida.
Har yanzu babu jituwar Arziki tsakanin Jalal da Ilham, ba Ilham bama kawai hatta mamanta Saudat basa shiri saboda hakanan Allah be hada jininsuba, wataran Saudat tazo gidan, tabawa Jalal kyautar turare, da yanuna baze karba ba, Amma Jawwad yasashi ya karba, yace masa ba a haka mutum yamaka kyauta ka gwaleshi, Tunda Saudat uwace a gurinsa, Ranar suna kwance cikin Dare, Jawwad yaji kaman ana jijjiga gadon dasuke kwance dan haka ya tashi da sauri ya kunna fitila, yaga Jikin Jalal yanata Kakkarwa, abun yabashi tsoro sosai, ya tattaba Jalal yace "Dan uwa meyasameka kobaka da lafiya ne" Jalal ya masa shiru, koda Jawwad ya cigaba da magana se Jalal ya bude idonsa seda Jawwad ya firgita wani irin Green yaga kwallarsa tayi, ga jijiyoyin kansa sun tashi sunfito sosai har goshinsa, Jalal ya rike Jawwad yace "Jawwad wani hayaki ya shiga jikina, kamin Addu'a amma karka gayawa kowa, ka dauki turarenda Maman Ilham tabani ka jefar dashi, daga ciki hayakin yake fitowa" Jawwad yadinga karanto masa duk abunda yazo bakinsa a haka har bacci ya dauke Jalal, sannan Jawwad ya dauke turaren ya boyeshi, Jawwad beggayawa kowa ba kaman yadda Jalal ya bukata.
Tundaga nan Jalal yafara zama wani iri, Suna SS2 Jalal yafara haduwa da miyagun abokai, ciki hada wani hatsabibi waishi Jabir Junaid, suna ce masa Jeje, gaban Jalila seda yafadi jin an ambaci Jeje,
"tunda Jeje ya shiga Rayuwar Jalal komai nasa yafara lalacewa, ya koya masa shaye2, Jawwad yai kokarin ya raba Jalal da Jeje amma abu ya gagara, Jawwad be gayawa kowa Jalal yafara shaye2 ba, yayai2 amma Abun na Jalal kullum gaba yakeyi, a haka har mutane suka fara ganewa. Habib yashiga tashin hankali daya fuskanci Jalal yafara shaye2, ya shiga dakin Jalal ya tarar dashi a kwance ga kayan shaye2 Jawwad na gefensa yayi tagumi, hankalin daddy ya tashi, ya tambayi Jawwad me yake faruwa haka, nan Jawwad yaiwa daddy bayanin komai, amma be gayamasa tun asalin meya faruba, ya dai ce masa shima kawai gani yayi Jalal yana shaye2, yayi2 ya dena yaki Habib yashiga tashin hankali jin tilon dansa yafada mummunar Rayuwa, A lokacin khadija kusan watanta guda bata Nigeria, Bayan Jalal yadena maye ya zaunar dashi yaita masa nasiha yana masa fada, amma Jalal fadan nan ko a jikinsa.
Bayan dawowar Mummy Habib ya dinga yi mata fada yana cewa "Khadija a sanadin rashin kulawarki, da sakacinki Rayuwar dana ta tasamma rugujewa, Jalal yakama hanyar lalacewa, wace irin uwace ke"
A fusace tace "Nifa baangane inda maganganunka suka dosa ba, da can bakasan inada sakacin ba se yanzu?"
"ABDUL JALAL yafara shaye2, shaye2 yakeyi" Zare ido tayi "Kamar ya shaye, ni dana baya shaye2, Jalal baze hakaba"
"koki yadda kokarki yadda yarage naki, sekije ki bincika" a gigice ta fita tanufi dakin Jalal, aikuwa tana shiga ta tarar dashi yanata busa hayaki, cikin tashin hankali ta karasa cikin dakin
"Jalal mekakeyi haka? Shaye2 fa kakeyi"
Banza yamata yacigaba da abunda yakeyi, ta karaso ta nufo inda yake amma ya dakamata tsawa "Karki sake kizo inda nake tunda ba kyason bakya kaunata, bakida wata magana dazaki gayamin lokaci yariga ya kure, Mummy da hannunki kika rusa Rayuwata, kin fifita son zuciyarki akan Rayuwar danki, kifita ki barmin dakina, bana kaunar ganinki"
"Amma Jalal........
Jifa yafarayi da duk abunda yaci karo dashi cikin tsawa yake cewa" Kifita Nace bana son ganinki, kije kudi su baki farincikin da duk kike bukata, kifita kibani guri, Jawwad ne yashigo dakin da Sauri yaga abunda Jalal yake da sauri yaje ya rikeshi, Mummy ta juya cike da damuwa tabar dakin.
Tundaga wannan lokacin Rayuwar Jalal tashiga rudani, yadena jin magana ibada ma baya iyayi, yadena ganin girman kowa, yadena ganin mutuncin kowa, kowa ya janye dansa daga shiga huldar Jalal, Jawwad ne kawai be barshiba, da mahaifiyar Jawwad ta fuskanci Halin da Jalal yafada setayi kokarin ta rabasu, saboda kar itama nata dan ya lalace. Amma abu ya gagara mahaifin Jawwad yace indai tai kokarin raba Jawwad da Jalal batayi adalci ba Addu'a yakamata tayi musu gaba daya, wasa2 abu yafara shafar kwakwalwar Jalal ya manta abubuwa saboda shaye2, a haka suka gama secondary suka shiga jami'a, Jawwad na mechanical engineering, shikuma Jalal yana karanta civil engineering, shima a university din haka yakara lalacewa da shaye2, kullum Jawwad kokari yake yaga Jawwad yadena abunda yakeyi amma abu ya gagara.
Suna level 1 kakar Jalal mahaifiyar khadija ta rasu, Jalal yazama rikakken dan shaye2, yazamana in har Jawwad bega Jalal ba to a Club ze tsintoshi. Dukdahaka lokaci zuwa lokaci Jawwad yana raka Jalal maiduguri su gaida dangin mahaifinsa Khadija tacewa Jalal bata yadda yakuma zuwa maiduguri ba, inyakuma bata yafe ba tunda dangin mahifin sa basa sonta shikuma Jalal yace sedai katta yafe, ita mutum nawane sukace basu yafe mataba, Jawwad yace masa be kamata yadinga zuwaba tunda tace bazata yafeba hakkinta ze iya kamashi, dama dangin Habib tuni suka dena zuwa saboda wulakancin Khadija.
Jalal yana shekararsa ta karshe a Jami'a abun nasa yakara ta'azzara, da yana iya karatu dukda yana shaye2, yana da kwakwalwar sosai dan yana daga cikin wanda ake ji dasu ga barin kudi dayakeyi, amma a final year kwakwalwar Jalal takara birkicewa, yakasa karatun ga mantuwa, makarantarma gaba daya yadena zuwa, se yawon club, abokansa yan iska suka kara like masa saboda yadda yake sakar musu kudi, gaba daya iyaye suka hana yaransu shiga harkarsa, suka shiga tsangwamarsa da an ganshi se a tashi abar guri yazama abun kyama, kowa ya gujeshi se Jawwad, hakan yakara tunzurashi yafara rashin mutunci yadena ganin girman kowa, memakon amasa nasiha ko Addu'a se akaita Allah wadaran
da halinsa, hatta dangin Khadija basason yaje inda suke bayan abaya harsosuke yaje saboda sunsan indai yaje seya musu barin kudi, ana cikin wannan halinne Ilham ta nuna tanason Jalal a haka, hakan ya tabattar da akwai abunda Ilham suke shiryawa dan daukar fansa akan Khadija da danta, Amma hankalin khadija be kaiba itama ta goyi bayan hakan tana ganin tahaka ne zata wanke zuciyar Saudat akan abunda taimata, har zuwa wannan lokaci ake wannan turka turkar.
Kakar Jalal mahaifiyar Habib tayi kuka lokacin data samu labarin yanda jikanta yakoma, gashi kiri kiri an hanashi zuwa inda take da wannan bakincikin takoma ga Allah, tanawa jikanta fatan shiriya, amma ranar dasukazo gaisuwa suka juya, Mummy tahana Jalal kwana, wannan abun yakara bakantawa danginmu Rai, muka dauke kafarmu daga gidan Habib tsawon shekaru. Babban abun godiya ga Allah shine Jalal baya neman mata ba ruwansa da mata, ko a makaranta ko a club ba ruwanshi dasu, ze sha giya yayi askin banza, yayi rashin mutunci, baya ganin girman kowa musamman Mummynsa dayake ganin sam batayi masa adalci ba a matsayinsa na danta, tunda ta goyi bayan ya auri Ilham, da nufin ta wanke laifinta na baya yakara jin haushin mahaifiyarsa.
Antin Jalal ta kamo Hannun Jalila da fuskarta ta jikebda hawaye tace "Jalila nagaymiki iya abunda nasani gameda rayuwar Jalal, wani abun nima har yanzu ban saniba, nasan zanbarki cikin dunbin tunani, amma Jalila bantaba zaton Akwai wanda ze iya karkata hankalin Jalal ba, duk lokacin daka dakko yimasa Nasiha ko ransa yabaci sekaga yafita hayyacinsa idonsa ya canza kala yafara jifa da abubuwa, kin dakko hanyar daidaita Rayuwar Jalal amma bata sigar dakika fara ba, duk lokacin dakika batawa Jalal rai seya gayamin, Jalila akwai abubuwa da bangayamiki ba saboda ba'a bakina yakamata kijiba, wannan tarihin danabaki nagaya mikine bisa Amincewar Jalal, yanzu mu tashi kinga azahar tayi wanka zanyi inyi Salla zamu juya.
Jiki a sanyaye Jalila ta mike suka nufi cikin
gidan, Jalila kam waje tayi, ta tafi gida, tana zuwa gida ta tarar da Nana a harabar Gidan, Nana tana ganinta tace "Jalila ina kika shiga ne? Tun dazu nake nemanki nakira layinki amma wayar na daki"
Jalila batace uffan ba ta wuce daki, tana zuwa ta zube akan Gado, ta fashe da kuka
"ban kyautaba, Mummy meyasa? Meyasa kikayi haka, Ashe shiyasa Jalal yake cewa Kinfiye sonkanki, Saboda kudi da son zuciya kin bata farincikin mutane da dama, kinyi sanadin Rayuwar danki, Jalal ka yafemin bansaniba" takara fashewa da kuka

Sosai Jalila take Hawaye, tareda surutai a hankali, Nana ce ta shigo dakin, da sauri Jalila ta goge hawayenta, zuwa tayi ta zauna ta kalli Jalila
"Jalila lafiya kuwa, meyasameki? Meyasaki kuka kuma ina kika shiga tun dazu nake nemanki" Jalila bata san wace tambayar yakamata ta fara amsawa Nana ba, Jalila ta dan girgigiza kai tace "Bakomai karki damu"
"Yazakicemin ba komai, kuka fa kikeyi"
"Nana bakomai"
"Shikenan tashi muje, Bakin su Jalal zasu tafi, taso Anty Amina tace inkiramata ke" se yanzu Jalila tasan sunan Antin Jalal dinma, ba musu ta mike suka fito tare, suna shiga gidan suka tarar dasu sunfito zasu tafi, Mahmud ya kalli Nana yace "Nana gashi zan tafi bangama ganinki ba" murmushi Nana tayi "Nima bangama ganinka ba, kaje kayi zamanka a England, memakon kadawo Nigeria muma mu amfana da iliminnaka, kaje se wani uban kumatu kakeyi"
"Allah hajiya Nana, ke bakiga yadda kikakoma bane, kinzama wata madam, yanzuma Anti Amina mukayi waya, zasu zo nan kano, shiyasa nadawo nace nima suzo dani zan dade a Maiduguri kafin inkoma England" ya kalli Nana yayi kasa da muryarsa yace "Nana wannan ce Jalila ne?"
"itace kasanta ne?"
"A'a na tambayekine kawai, naga tana kama da wata ne, just forget, bani lambarki"
"Seka biya tukuna" murmushi Mahmud yayi, "Yimata kudi ko nawane imbiya" Nana tai dariya ta karbi wayarsa tasamasa lambarta, Suna tsaye suna jira Jalal yafito suyi Sallama amma tunda Jalila taimasa abun nan da safe, ya shige daki yaki fitowa ko sallama suyi, Jawwad yanata masa magiya amma yaki bude kofar nan.
Anti Amina takamo hannun Jalila tayi gefe da ita, ta kalleta tace "Jalila kuka kuma? Meyasa? Munasa ran samun nasarar daidaita rayuwar Jalal ta hanyarki amma muga karaya a taredake, karkimana haka Jalila, banbaki labarin Jalal dan isaki damuwa ba" kaman ta ziga Jalila takuma fashewa da kuka, Rungumeta Anti Amina tayi tana sharemata Hawaye cikin kuka Jalila tace
"Anty dana san haka Rayuwar Jalal take daban zama daya daga cikin masu kara rusa farincikinsa ba nasan na dade ina bata masa Rai amma.......
" Jalila kina yimasa hakane dan inyaji haushi ya dena abunda yake nasani karki damu kinji kidena kuka"
Jalila ta jinjina kai, suka musu rakiya har mota suka daga suka tafi.
Jalila jikinta a sanyaye takoma gida, daki takuma komawa ta kule akan gado tayi shiru nan ta shiga tunani daban2,
"Kenan Kabir shine Oga Kb? , Jeje yataka Rawa gurin lalacewar Jalal, menen alakar Kabir da Jeje?" dafe kanta tayi tai tagumi hannu bibiyu tai shiru sekuma wani abu yakuma fadomata a rai
"Saudat tabawa Jalal turare, aranar yadinga karkarwa cikin dare yana firgita, kenan Saudat ma wani abun tayi masa kokuma mene? To wa zangayawa? Mema yakamata inyi ne? "
"Yasalam" Jalila ta furta da karfi tareda dafe kanta, da Hanzari Nana ta shigo dakin ta tarar Jalila ta dafe kai tana kuka
"Jalila lafiyarki kuwa? Tun dazu nake tambayarki meyasameki amma kinki gayamin se kuka kike kinga yadda idonki yayi Ja kuwa?"
Murmushin dole Jalila ta kakalo, "Karki damu kaina namin ciwo sosai, allow me to rest" ta ture Nana ta kwanta, Nana ta dade tana mamakin meyake damun Jalila haka?
Yadda Jalila taga Rana haka taga dare, banda zunzurutun tunani da tambayoyi ba abunda ke kai komo a zuciyarta, ga wani irin tausayin Jalal dake ratsa zuciyarta, antarwatsa Rayuwarsa akan abunda lokacin da ake laifin baya duniyar, gaskiya Mummy bata cancanci zama uwa ba, ta fifita duniya akan Rayuwar danta. Har gari ya waye Jalila idonta biyu,
Halima da Nana ne suka hada breakfast, nanma sukayi sukayi taci Abinci takici, Abun yafara bawa Nana tsoro, dan haka taje tagayawa Maama halin da'ake ciki
"Nono kikeso inkamota in bata ko goyata zanyi inta jijjigata?"
"Maama bahakaba, at least yakamata musan meyake damunta, kartayiwa kanta illa, tun jiyafa bataci Abinci ba tanata kuka, kinsan batada cikakkiyar lafiya fa?"
A fusace Maama tace "fita kibarmin daki, kar Allah yasa taci, inta kashe kanta aita huta"
"Amma Maama....
" Bazaki fita ba sena makeki" ba shiri Nana ta fito, ta nufi part din Jawwad amma bayanan, takira wayarsa harta katse be dauka ba, daki takoma tazubawa Jalila ido data kwanta ta rufe ido, amma hawaye nabin gefen idonta
"Jalila dan Allah kitashi kici Abinci, wallahi gaba daya zuciya ta babu dadi, na damu matuka, dan Allah kici wallahi inbaki ciba nima bazanci ba" A hankali Jalila ta bude ido, ta mike zaune ta kalli Nana tace "zubo muci, banason kizauna da yunwa"
Nana ta zuba Abinci amma Jalila ta dan cakala ta barshi.
Wunin Ranar Haka Jalila tayi duk surutun nan amma yau tsit kakeji, Nana tayi tambayar harta gaji ta samata ido.
Da daddare Jawwad ya shigo yasamu Maama a palour yake gaya mata Ankai Jalal Asibiti. Da sauri Jalila ta mike ta fito palour ta labe
Maama tace "meysameshi haka?"
"kinsam jiya yan maiduguri sunzo, kuma dai kinsam babu jituwa tsakaninsu da Mummy, andai bata masa rai yaje ya kulle kansa a daki, yafasa abubuwa sosai sannan cikinsa da yunwa ya sha wani abun bansan meyasha ba, da kyar na bude dakin dazu, naganshi a sume shine muka kaishi Asibiti, yanzu can zantafi zan kwana dashi"
Maama ta kalleshi "ohhh Jawwad Allah yayemaka wannna Jaraba, wannan yaron Jalal kullum seyajanyo abun daze hanaka hutawa, sekayi tayi ai wahalalle"
Murmushi Jawwad yayi yace "Maama kenan, ai duk dan halak baya manta alkhairi, bari in tafi seda safe" ko kallonsa bata kumayiba, har ya juya ze fita Nana tace "Yaya Jawwad amasa sannu dan Allah, kuma wallahi Baby ma inaga wani abu na damunta tunjiya kuka takeyi, taki cin Abinci da kyar nasata taci kadan"
"Haba dai? Kuma kin tambayeta meyake damunta?"
A fusace Maama tace "fita katafi inda zaka, bazasu hadu sukasheka ba kowa
ya kwaso iskancinka akanka ze sauke, kaidabaka san ciwon kanka ba"
Jiki a sanyaye Jawwad ya juaya yafita, Jalila takoma daki ta kwanta tai shiru tamarasa tausayin wa yakamata taji.
Jin batun Jalal na gadon Asibiti abun yadameta.
Har gari yawaye Jalila nata kasa kunne taji wanda zeyi zancen halin da Jalal yake ciki, har wajen azahar shiru, Jalila tace "Nana naji kaman yaya Jawwad yace an kai Abokinsa Asibiti?"
"Eh acanma ya kwana, har yanzu kowaya beyoba, dazu Maama takirashi a waya amma bata shiga"
"to ya jikinnasa?"
"Nima bansaniba wallahi, amma bari mujira zuwa anjima"
Jalila ta gyada kai, ta dakko wayarta tana dubawa taga missed calls rututu
Call logs dinta tashiga tatarar da missed calls na Zahrah, Jalila ta kirata a waya bugu biyu ta dauka
"Salam alaikum, Jalila ina kika shiga tun jiya nake kiran wayarki amma ba kya dagawa"
"Am sorry ina wani mahimmin abune, se yau na dakko wayar, ya akayine?"
"Hmm Jalila sarkin Sabga, dama gayamiki zanyi anbada belin Baban Samir Fa shida duk wanda aka kamasu, shine nace kina ganin ba abunda ze faru kuwa insuka ganomu"
"Zahrah karki damu babu abunda ze faru, koda anganomu muka shirya wannan abun, to ki zame kibanni ba ruwanki balle baza'a gane ba, Burina ya cika na tonawa duniya asirin ya da Uba, duk wani cin zarafi da wulakanci dasu Saleema sukeyi dole sudena, saboda wannan mummunan abu. Kunya dasuka aikata, Amma tabbas zankuma gauraya dasu, Alhaji Kabir da Jeje, Nagode kigaida Umma" Jalila ta kashe wayarta, tacigaba da duba kiran da akayi mata takuma cin karo dana Hanan, da sauri ta kira Hanan, seda takusa tsinkewa sannan Hanan ta dauka, tace "Se yanzu zaki kirnaiko? Tun jiya nake kiranki amma kinki dagawa yar wulakanci kawai"
"Yi hakuri Hanan, lokacin bana tareda wayar se yanzu na duba nagani"
"To na hakura Allah ya temakeki, dama zamuje Bauchi nan da 2 weeks, Daddy yace zamuzo mu tambayi Abba inya yadda mutafi dake Inna taganki"
Jalila tace "Hanan zanyi murna da zuwanki, ina cikin matsala inason inganki"
"Matsala kuma Jalila? Meyafaru?"
"Hanan na dade ina tafka kuskure, yanzu ina nadamar abunda nayi, abun baze yuwu ta waya ba, nafison mu hadu"
"Subhanallah Jalila nadamar mekuma? Zaki banni cikin damuwa da tunani, ki gayamin menene?"
Jalila ta dan share Hawaye tace "Hanan for all this time i have hurting Jalal, calling him with different bad names, he is innocent, Hanan an gayamin tarihinsa, Jalal abun a tausaya masane, inajin kunyar hada ido dashi, Hanan ban kyauta ba"
"Is ok kidena kuka, ai duk dan adam baya wuce aikata kuskure, Calm down, abunda na dinga nunamiki kenan a baya amma baki ganeba, baka yankewa mutum hukunci kai tsaye akan abunda kaga yana aikatawa, idan nazo zamuyi maganar, amma ya akayi kikasan ba laifinsa bane?"
" Ai baze yuwu a waya ba, se mun hadu"
"Amma yakamata ki wanke lefinki"
"Hanan tayaya, tunda na riga nayi"
"Hakuri zaki bashi mana"
"Hakuri kuma?"
"Eh mana, yakamata kinemi ya yafe miki"
"mhmm Inasu Yaya Abdallah? Inason ganinsa ma ina neman yamin wata Alfarma inze iya"
"Wace Alfarma kenan?"
"Ina ruwanki semun hadu nida shi, ki gaida Baba"
"Hmm shikenan zeji Insha Allah" sukayi Sallama
Jalila kasa jurewa tayi ta dau waya takira Jawwad amma baya dauka, haka ta hakura.
Washegari shiru2 Jawwad be dawo ba. Har bayan Azahar gashi baya daga waya, hakan yasa Jalila ta kara shiga damuwa, ta fito harabar gidan, dan tasamu ta kadaice tayi tunani, tana nan Zaune tayi nisa sosai a tunanin tarasa ta ina yakamata ta fara, gaba daya abubuwa sun hargitse mata.
Motsi taji abayanta yasatayi saurin waigawa, Jawwad ta gani a tsaye tai sauri ta mike tsaye.
"Baby meke damunki hakane? Tun dazu nake magana amma kinyi shiru, gayamin meke faruwa?"
Murmushi Jalila ta kakalo, "Yaya Jawwad bakomai kawai dai banji bane, ina ka shiga bana ganinka nakiraka a waye baka dagawa"
"Jalal ne ba lafiya, na kaishi Asibiti na manta wayata a gida"
"Meyasameshi?"
Ajiyar Zuciya Jawwad yayi sannnan yace "jininsa ya hau, yana damun kansa dayawa, Jalal baya iya controlling bacin Ransa, yanada saka abu a ransa, ga kinsan shan taba yana kara saka hawan jini, amma Alhamdilillah jikinsa da sauki an sallameshi tare muka dawo gida" jinjina kai Jalila tayi "Allah yabashi lafiya"
"Ameen Baby, meyasamin ke kuka kika kasa cin Abinci Nana ta gayamin"
"Nikuma ai kaina ke ciwo kawai itakuma tabi ta damu, amma na warke ai"
"Anya kuwa, karya ba halinki bane, fuskarki ta nunamin kina cikin damuwa"
"bana cikin wani damuwa ni, kako ci Abinci naga kaman a gajiye kake"
"Hmm wato ba kyason incigaba da tambayarki ko?"
"bahaka bane, banaso ka zauna da yunwa ne"
Murmushi Jawwad yayi, "Ina jin yunwa kam, samomana wani abun, Jalal ma beci Abinci ba, yaki cin Abinci wallahi, nayi2 amma yaki, Yana cikin damuwa sosai, anyway samo mana abunda yasamu in lallabashi koze ci" gyada kai Jalila tayi ta juya da sauri ta tafi cikin gida.
Tana shiga palour ta tarar da Maama tana mata wani irin mugun kallon banza, Jalila ta dauke kai kaman bata san meke faruwa ba tai kitchen abunta. Ta dafa masa jallof spaghetti, ta hada da juice bayan tagaama take tunani yanda Maama ta zauna a palou
tana mata kallon banza, yanzu in tace zata kaimasa Abinci wani bacin ran zata jawa kanta dan haka ta kirashi a waya tace yazo ya dauka, befi minyi bakwai ba sega Jawwad yaje kitchen ya dauki Abincin. Har yazo ze fita Maama takirashi, yadawo ya zauna a gabanta yace "Maama gani, Allah yasa ba laifi nayi miki ba"
"laifi kuma tun yaushe kake sabawa umarnina, minyi magana akan muna son hada Aurenka Naja amma har yanzu baka kumabi takan zancen ba, sekara shigewa wannan algungumar yarinyar kakeyi, ban isa ingayamaka magana kajiba ko?"
"Maama dan Allah kiyi hakuri, na yadda in Auri duk wadda kikeso, amma bazan iya Auren Naja ba"
"Jawwad kake kallon tsabar idona kake cemin bazaka iya Auren Naja ba"
"Maaama Naja yar uwata ce bazankita haka kurum ba amma...
" Yimin shiru badai akan waccan hatsabibiyar kake rawar kaiba, idan ina raye ayi ingani, tashi kabani guri"
Jiki a sanyaye cike da damuwa Jawwad ya mike yabar palourn.
Tunda yan maiduguri suka tafi Jalila bata kara saka Jalal a idonta ba dan sam yadena zuwa gidansu, ga Jawwad yanata complain akan Jalal bayacin Abinci yana damun kansa sosai, ga matsalar da Jawwad yake ciki shima Maama nata tursasa shi tace se ya Auri Naja, amma ita Nana ta tirje tace bazata Auri faruk ba an kyaleta, Jalila tarasa yadda zatayi taga Jalal, duk abun yafara damunta. Ga yaya Jawwad dinma ta dena ganinsa ko waya basa yi, yadena shigowa cikin gida. Zaman cikin gida ya isheta dan haka ta fito danta sha iska, ta fito ba dadewa Jawwad ya shigo yayi parking, duk taga ya dan rame, yafito ya kulle motar, takarasa inda yake "Yaya Jawwad wai meyake damunka hakane, ka rame kuma tun shekaranjiya ban kuma ganinka ba" cike da damuwa yace mata "Baby Jalal, yana nema ya kashe kansa"
"Kamar yaya?"
"Ankuma kwantar dashi a Asibiti, tun shekaranjiya ina can, banason inkira Daddy kar adaga masa hankali, idan Mummy taje gurinsa, seyace seta tafi bayason ganinta yanzu haka jikinsa yakuma rikicewa, yanzu haka tun jiya yana ICU, maybe yau zasu fito dashi" nan da nan jikinta ya hau rawa, cikin rawar murya tace
"Subhanallah Allah yabashi lafiya, if you don't mind zan rakaka in dubashi"
"Shikenan naji amma kibari seda safe in Allah ya kaimu zanzo muje" ta jinjina masa kai takoma cikin gida
Yau Hannah har gidan Jeje taje nemansa tayi sa'a kuwa yana nan, Jeje yayi mamakin ganinta sosai "yau kece da kanki a gidana"
"Eh nice amma kasan duk lokacin daka ganni bukatace ta kawoni, almost one week ina nemanka, bana ganinka layinka baya shiga, amma naji ana rumors ankamaka kai da megidanka a gidan karuwai meye gaskiyar lamari" shiru Jeje ya danyi ya kalli Hanna
"Ni ina zargin dasa Hannunki akan abunda yafaru dani, shekara da shekaru inawa Oga Kb aiki inasamun rufin Asiri a gurinsa, ina hutawa da 'yarsa ba tareda yasani ba lokaci daya aka masa cunen gidan danake zuwa yakamamu, yanzu ya sallameni tareda cin alwashin seyaga bayana, wallahi Hannah indai dasa hannunki a wanna cin zarafin da' akamin bazaki tsira daga sharri na ba"
Murmushi Hanna tayi sannan tace "Aidama karshen alwa kasa, kuma ramin mugunta kurarrene, Jeje idan har zanmaka wannan manakisar yan sanda suka maka kaida uban gidanka to wallahi da duk yadda zanyi bazaka fita daga hannun yan sanda ba daga kai harshi, dara ce taci gida kawai, kakoma kayi tunani ka sake nazari waze iya aikata maka haka, kasan innice nayi maka wannan aikin bazanji tsoron gayamaka bako? tunda irin tarbar danasamu daga gurinka kenan shikenan nagode ni na tafi, amma kakiyaye shiga hanyata, kasanni ban da kyau"
tanagama fadin haka ta juya tanufi motarta, yayi Yunkurin ya biyota amma ta tashi motar tabar gurin.
Yauma Jalila ba bacci, saboda tashin hankali da damuwa, se addu'a da takeyi, Nana kam ta gaji da tambayar ta meyake damunta. Da Asuba Jalila tai wanka tai salla ta shiga kitchen ta dama kunun gyda da dankalin turawa, karfe bakwai tagama shiryawa tsaf tana jiran Jawwad, Nana tai juyi akan gado ta kalli Jalila
"wai shirin mekikeyi hakane?"
"Asibiti zan raka Yaya Jawwad muduba Yaya Jalal" dan zaro ido Nana tayi, sannan tai murmushi
"Yaukuma da kanki kike cewa Yaya Jalal" takuma murmushi tace "Zanso inje nima induba shi, amma wallahi bacci nakeji, kuyi masa sannu in an sallamoshi naje in duba shi, kokuma in Maama zata semuje tare" Nana ta juya tashige bargo, Jalila na nan zaune, wajejen karfe takwas Jawwad yakirata a waya yace tafito su tafi, da sauri ta dakko kwandon kayan Abincin ta fito, Jawwad ya kalleta yace "Baby hada hidima haka, Abinci kika mana"
"Eh Yaya, koba kwaso?"
"haba mu mun isa, taho mutafi" ta shiga mota suka tafi, suna zuwa Jawwad yaimata jagora har dakin da Jalal yake, suka tura kofa suka shiga ta tsorata da ganin Jalal, yana kwance akan gado dagashi se dogon wando da singlet, yanata sauke numfashi a hankali, ya rame matuka gashi yayi duhu se dogon hancinsa yakara fitowa sosai, drip yana shiga jikinsa a hankali, hawaye yafara bin idon Jalila a ranta tace "idan har Jalal ya mutu ina da alhaki, ninakara assasa bata masa rai"
Jawwad ya dora hannunsa akan gadon da Jalal yake ya sunkuyar da kai, Yana dago ido Jalila taga kwalla a kwance a idonsa
"Yaya karka karaya mana, zeji sauki" Jawwad yai murmushi yace "Baby Jalal wani bangarene na rayuwata, inajinsa a raina kaman wani bangare na rayuwata, banason rasashi, banason wani abu yasameshi da inada yadda zanyi in kawar masa da damuwarsa, danayi amma ba yadda na iya kaddara tariga fata, haka Allah ya kaddara masa, ina fatan Allah ya musanya masa da kyakyawar kaddara " Jawwad yai ajiyar zuciya yace "Bari inje gurin doctor inji meze ce, kizauna anan anjima su Ilham zasuzo nima yanzu zan dawo, inkuma ya tashi kafin in dawo kikirani beci Abinci ba" ta jinjina kai, Jawwad yafita yabar dakin guri ta samu ta zauna akan kujerar gaban gadon Jalal, Hawaye tacigaba da sharewa lokaci zuwa lokaci tana dorawa kanta alhakin wannan rashin lafiyar da yake,
A hankali Jalal yai juyi, da sauri ta goge idonta ta tsaya tana kallonsa bude idonsa yayi a hankali ya saukesu akan Jalila dake goge hawaye, kura mata ido yayi ko kyaftawa ba yayi.

Ya dau lokaci yana kallon ta, cikin rawar murya Jalila tace "Sannu ya jiki?" shiru yayi bece komai ba ya lumshe idonsa, "Ko inkira maka Jawwad" still shiru yayi bece mata komaiba tamarasa mezatayi, idonsa a lumshe taga hawaye nabin gefen idon Jalal, hankalinta yakara tashi "Inkira maka likitane" takarasa maganar tana hawaye, bude idonsa yayi ya juyo yana kallonta "Kukan mekikeyi? Nakumamiki wani laifinne? Nasan bazakiyi kuka dan halin danake ciki ba, zakifiso in mutu saboda yayanki ya huta ba?"
Girgigiza masa kai Jalila ta shigayi amma takasa magana
Ya hade rai yace "kidenamin kuka, nagaya miki kincikamin kunne"
"Yi hakuri na dena" tasa hannu ta share hawayenta, Jawwad yashigo da likita suna zuwa kan Jalal ya bude ido, Jawwad ya zauna kusada shi yace "Sannu ya jikin naka?"
"Alhamdilillah naji sauki azo a sallameni" murmushi likitan yayi sannan yace "kai Jalal da wuri haka, bazamu sallameka yau ba, se mun tabattar dakabi dokokin dazamu saka maka, bamaso se mun Sallameka akuma
dawo da kai Rai a hannun Allah"
Jawwad yace "rabu dashi doctor yi masa abunda yakamata, baza'a sallameshi ba seya warke gaba daya"
Jalal ya tashi zaune, Likita yakara duddubashi, sannan yayi rubuce2 a file din Jalal, ya rubuta wata takadda yace "Ga wannan Jawwad bamu dasu a pharmacy sekaje cikin sabon gari zaka samoshi" Sannan likitan ya kalli Jalal yace "Man yakamata ka cire abunda yake ranka, karka kashe kanka da kuruciyarka kana matashinka, kana da kudi kana cikin Ni"'imar ubangiji meze daga maka hankali haka? " kallonsa Jalal yai ya dauke kai likitan yacigaba da cewa " Jininka ya hau sosai, dole kadena damuwa sannan u must reduce the amount of cigarette and shisha you take every day (PEOPLE WHO SMOKE ARE ABLE TO DIE YOUNG!!!) so you should be careful, akwai sinadarin dayake saka hawan jini a cikin taba, shanta yana kawo lung cancer ko tuberculosis, and you should reduce Alcohol intake, ka rage shan giya shima, tana saka cututtuka da dama, kaman Ciwon Hanta, ciwon koda, tana kara asassa ciwon sugar akwai kuma nauo'in ciwon ido dake sakawa, dan haka a hankali yakamata ka rage, sannan kadinga cin Abinci kaga Ulcer yana nema yazeme maka chronic " shiru Jalal yayi ya sunkuyar da kai, Jawwad yace "Shikenan doctor za'a kiyaye Insha Allah"
"Yawwa masha Allah, Allah yakara sauki" doctor ya juya ya fita, Jawwad ya zagayo ya zauna kusada Jalal yace "Kaji abunda doctor yace ko? Please and please kakiyaye dokokin da aka samaka kaji Dan uwa" Jalal dai bece komai ba, ya sunkuyar da kansa, Jawwad ya juya ya kalli Jalila yace "Baby miko kwandon Abincin nan a hada masa yaci se inje siyo masa maganin"
Ta dakko kwandon, ta zuba kunun gyada cikin
wani katon kofi ta zuba dankali ta mikawa Jawwad, Jawwad ya zare ido yace "Kai Baby yazeyi da wannan kunun yayi yawa ai, bakiga bashida lafiya ba, aibaze iya shanye wannan ba"
Jalila tace "Au haba, ka tuna lokacin dana kwanta a Asibiti cikin katon kofin nan yazare min ido sena shanye, shima ka zare masa ido ya shanye" takarasa maganar tana dan tura baki, Bakinta Jalal ya tsaya yana kallo shikuwa Dariya Jawwad yai yace "itaku kedashi, kema seki zare masa ido ya shanye, bari inje in siyo maganin" Jawwad ya mike ya fita, Jawwad na fita Jalal yai kokarin komawa ya kwanta beci Abincin ba da sauri Jalila tace "Ai bakaci Abincin ba" ya kalleta "Bazanci ba" yakuma kokarin kwanciya Abincin ta dauka ta dora a inda ze kwanta tace "wai meyasa kafiye taurin kaine? Cewa fa akayi kaci Abinci"
"Ke har na kaiki taurin kaine? Waima ina ruwanki danine? Dan giya, mara tarbiyya, zan lalata miki dan uwa, me kike nema a gurina, dauke Abincin ki bazan ciba, kintaba gayamin idan na mutu bakida Asara to meye naki na damuwa da banci Abinci ba?" yasa hannu ya dauke Abincin ya dora akan drower na kusa da gadon sannan yace "Dama a duniya daga daddy se Jawwad ne suke sona se yan uwan daddy, nan duniya idan na mutu ba wanda yakeda Asara, sesu"
kura masa ido tayi "Meye kuma kike kwalalamin idanuwa haka, kidena kallona" yai kwanciyar sa.
Kawai Jalila ta mike ta fice daga dakin, Ajiyar zuciya Jalal yayi dayaga ta fita ya dakko Abincin data zuba ya ci ya aje sauran. Jalila na fita tasamu guri ta zauna a waje ta dakko wayarta tafara chatting tana daga kai ta hango Ilham da mahaifiyarta a harabar Asibitin kallo daya tayiwa Saudat tagane itace mahaifiyar Ilham,
da sauri Jalila ta tashi ta koma dakin Jalal, tana zuwa taga yaci Abincin yana kashingide ya lumshe ido, yana jin motsinta ya bude ido,
"Ke meya dawo dake, ko dama bakida zuciya?" cikin tsiwa tace
"dama ina naga zuciya, tunda kaima bakada ita"
Dan zare ido yayi, ashe halin nata yana nan
Ta fara hada kan kwanuka, Ilham ce da Mamanta suka shigo da sallama yanajin muryarsu yai Sauri ya rufe idonsa. Kai kace bacci yake, Tunda Ilham taga Jalila a gurin Jalal ta hade rai kaman taga kashi
Jalila ta maze tace "Sannunku da zuwa" yawwa maman Ilham ta amsamata, tabasu guri suka zauna Ilham se harar Jalila take, ita kam Jalila data kalli Ilham seta mata murmushi Maman Ilham tace "Yame jiki?"
"da sauki Mama"
"naga alamar kaman yana bacci ne ko?"
Jalila ta waiga ta kalleshi yawani rufe ido kaman gaske amma idonsa biyu, se Jalila ta kudurce wani abu a ranta dan haka Jalila tace "
eh likita yamasa Allurai yasamu bacci, likita yace baze farka ba se bayan Awa biyar, yanzu besan me ake ba"
Maman Ilham ta kalli Jalila tace
" Sedai bangane wannan ba, bakowa a gurinsa seke? ko itama a dangin babanasa take?"
Ilham tai farat tace "Inafa," yar shishshigi yar wahala dai, me hana ruwa gudu, me cusa kanta inda Allah be kaita ba" Jalila tace "haba Ilham, wani ma se yazata banida kirki, menamiki haka ina laifin kice, Sauro me hana giwa bacci, Raina kama kaga Gayya" Jalila ta karasa maganar tana murmushi tace "Mama bari in saka wayata a caji, in karbo muku ruwa a waje" Jalila ta mike ta dau wayarta ta dan daddana sannan tasaka ta a caji ta fita. Ba'a wani dade ba, Jalila ta turo kofa ta shigo da ruwan roba ta ajiye musu ko sha basuyi ba suka tashi sukace tafiya zasuyi. Tai musu sallama suka mata banza Ilham nata gaya mata bakaken maganganu
bata damu ba suna fita taje ta dauki wayarta ta bude, maganganun dasukayi tsaf tayi recording dinsa tai Saving tajuya ta hada kan kwanukan da Jalal yaci Abinci,
bude idonsa yayi yana kallon ta tana dagowa suka hada ido
"Akwai matsala ne?" Jalila ta tambayeshi
"Wani Apple kika hanani ci kika musanya ranar da mukayi baki?" tambayar tazo mata a bazata, ta dan tabe baki sannan tace "Apple kuma ni ban san zancen ba"
"Karya kikeyi" Hade rai tayi sosai
"Eh kasan na saba" tacigaba da abunda take, ko ina yasan wannam maganar oho masa, ta mike tsaye taji ya janyo ta da karfi kan gadon, take jikinta ya hau rawa ta tsorata sosai ta ware ido tana kallon sa
"Ina tambayar ki kina rainamin hankali wani Apple kika hanani ci, kuma meyasa?"
"ni nace maka ban san zancen ba, ka tambayi wanda suka gayamaka mana, ni kacikani"
kara karfin rikon yayi taji kaman ze karya ta, sannan yace "ke bana son karya, for the last time ki gayamin" kawai ta fashe da kuka, mamakine yakama shi, in wani ya shigo se a zata wani abun yayi mata, dan haka a hankali ya sake ta ta mike da sauri ta koma waje, tana fita ta dakko wayarta kunna maganganun Ilham da mamanta. Kawai taji maganar Ilham tana cewa
"Umma wannan itace munafukar da nake gayamiki duk lokacin danayi wani yunkuri zanyi wani aiki akansa itake lalatawa, na dade da gane take takenta sonshi take, amma taki yadda tana rainamin hankali, tasamun Ido ta hanani sakewa, duk lokacin danayi Yunkurin wani abu idonta na kaina, seta wargaza gashi ta hadani dawata tsinanniyar karuwa wai budurwar Jalal ce, hatsabibancin yarinyar nan ya wuce tunaninki, harda wani alwashin indai tana Raye
seta rusa shirina akan Jalal" mamanta tace
"Ke sokuwar inace? Kika kasa gayamin tuntuni mu dau mataki akan shegiya"
"Umm har gurin Malam na kaita amma yace baze iya komai akanta ba, dakike ganinta ita ta musanya Apple din dana sawa maganin ranar, makira tsinanniya" umma ta girgigiza kai tace
"Tab aikuwa da sake, dole muyi wani abu karta bata mana aikinmu, amma Khadija kuwa tazo taga halin dayake ciki?" Ilham tace "Ai ingayamiki baya son ganin ta, kinga abunda ya dinga yi kuwa sekace ya haukace, dakinsa na nan kaman kantin mahaukaciya ya fasa komai a dakin, sangartacce ubansa na dawowa za'a canza masa komai" suka cigaba da maganganun su a zatonsu duk Jalal bacci yake besan mesuke ba, ita kuwa Jalila tana sane tayi haka.
Shiru Jalila tayi tana tunani "Kenan Jalal yaji duk maganganun da sukayi shine yake tambayata? Kafin kuga bayana zanga naku"
Jawwad ta hango ya taho da leda a hannunsa, yana zuwa inda take yace "Am sorry na tafi nabarki ko? Na dade bansamu maganin bane, bari inzo in maida kw gida nasan kin gaji"
"To Yaya sannu da zuwa"
"Yawwa babyn Yaya" yai mata murmushi ya wuce, yakai minti goma sha biyar sannan ya fito ya dauki Jalila suka tafi gida. Suna zuwa gida gaban Jawwad yafara faduwa, sakamakon tarar da Maama a harabar gidan da sukayi a tsaye da alamu a zuciye take, Jalila ta fito daga mota, Maama ta dinga jefamata wani irin mugun kallo, Jalila ta basar tace "Maama sannu da gida" tafada tana kokarin wucewa cikin gida "Dakata algunguma" ta dakatar da Jalila, Jalila ta tsaya ta sunkuyar da kai, Jawwad yafito ya rufe mota yakaraso gurin Maama yace "Maama, meyafaru ne?"
"Ubanka ne yafaru, daga gidan ubanwa kuke? Da kuka fita tun farar safiya se yanzu kuke dawowa?" Jawwad ya dan girgigiza kai yace "Kiyi Hakuri, ta rakani gurin Jalal ne, muna Asibiti tun dazu"
"Yimin shiru makaryaci banza da na wofi, kai ko kunya bakaji ka dingamin karya, Asibitinne se yanzu zaku dawo, tafara janka gantali ko, wallahi ka biye mata kafara aikata wani abu dayasaba da al'adunmu se ranka yabaci, tun yaushe Nake maka magana akan Naja, fafur kaki kaje ko inda take, tunda abun naka hakane Naja ta dawo gidan nan, kuma kobakabso seka Aure ta" ta juya ta kalli Jalila tace "Kekuma ko mayyace sekin kyalemin dana, akan me ke baki da zuciya ne? Wallahi kifita daga idona, shegiya mayya" ba Jalila ba hatta Jawwad seda ya dago Ido suka kalli Maama a tare, Jalila ta juya ta shige cikin gida ta barsu a gurin, tana shiga palour ta fara kicibisa da yaya mairo da Naja, a ranta tace "Ashe wannan ibilishiyar matar ce tazo shiyasa yau akemun saukalen Rashin mutunci, tun daga harabar gida ai shikenan"
Aibata gama zancen zucin ba ta tsinto muryar Yaya mairo tana fadin "Ga shedaniyar nan makira, wallahi kozaki mutu gidan nan ma se ya gagareki zama, kuma seya Auri Naja, danbazamu Aura masa Arniya ba, wadda uwatta ta gudu tazabi barbadanci ta battaba, Nutsatsiya zamu aura masa yar musulmi" Jalila ta tsaya ta waiga taga daga ita se su a palourn Maama tana waje tana cigaba da saukewa Jawwad kwandon jaraba, Jalila tace "To ayi mugani mana, karewar nutsatsiya masallaci Zaku Aura masa, sannan kika kuma zagarmin uwa wallahi sena kira taki uwar na zaga dan uwa bata fi Uwa ba" Naja ta mike a fusace tace "Ke dan uwarki uwatawa zaki zaga"
"badai uwata ba, wannan tsohuwar banzar kika zaga, kinbiyata ladar haihuwarki
datayi, kuma Na zageta ita wacece? Ko fin tawa uwar tayi? Kuma wallahi takuma zagarmin uwa sena fasa mata kai da wannan flask din" Jalila ta nuna tea flask din da takaiwa Jalal Abinci a ciki, hangame baki Yaya mairo tayi Jalila tace "Yanzu nasan ciwon kaina, ina zubarda hawayena ne a inda yakamata, nadena asararsu akan maganganun ku, iyakaci duk tsufan mace ta zagarmin uwa sena rama wallahi, Sannan ke Naja naji ance kindawo gidan nan da zama, kinyi kwantai ana cusa masa ragowa yana baya so amma, saboda ansan baki da mamora, se cusaki akeyu, to kinkawo kanki, bacin ran da uwarki ta dinga kunsamin tsawon shekaru sena ramasu akanki wallahi, kuma kafin inbar gidan nan sena sena tabattar da kin barshi tukuna" Jalila ta juya tai wucewarta daki yayinda Naja da yaya mairo suka rasa abun cewa, Naja tai karfin halin cewa "Lallai yarinyar nan rashin mutuncin ta yakara yawa, amma karki damu, ni zan saita mata zama namiki alkawarin, setabar gidan nan da kafarta, kuma sena Auri Jawwad, kiyi hakuri zan ramamiki" Naja na rufe bakinta, sega Maama sun shigo ta sako Jawwad a gaba tanata masa masifa shikam ya sunkuyar da kansa kasa har suka shigo cikin palourn
Nan Maama da yayarta, Yaya mairo suka saka Jawwad agaba da fada, shikam yayi shiru yakasa cewa komai babban abunda yake kona masa rai be wuce yadda suke cin mutuncin Ummi ba, matar da basuda tabaccin tana raye ko bata raye, seda sukayi suka gama sannan ya mike ya bar palourn, Yaya mairo tacigaba ds zuga Maama tana kara cusa mata tsanar Jalila a ranta. Yaya mairo ta tafi tabar Naja a gidan, koda Nana ta dawo gida ta tarar da Naja a gidan ba karamin haushi taji ba, dan sam Allah be hada jininta dasu ba.
Jalila takira Hanan a waya, tagayamata abunda ke faruwa, Naja ta dawo gidan da zama ita ake so Jawwad ya aure. A fusace Hanan tace "Kan bala'i, wallahi ba'a isa ba" cikin mamaki Jalila tace "Kamar yaya kenan?"
"kamar yadda nagaya miki, ai wannan fadan banaki bane Jalila nawane, ai muna nan zuwa Kanon very soon, ina baze yuwu ba, ai gara in barmiki Jawwad da ina gani ya Auri wannan yarinyar, gentle man like Jawwad, be dace da Auran ballagaza kaman wannan yarinyar ba dukda kasancewar ta yar uwassa" Hanan ta dinga masifa karshema ta kashe wayarta. Mamaki duk yakama Jalila dama dagaske Har yanzu Hanan bata hakura da Jawwad ba? Haka Jalila taita tunani.
Washegari aka sallamo Jalal daga Asibiti ba laifi jikinsa yaji sauki sedai rashin kwarin jiki, Jawwad ne ya dawo dashi daga Asibiti, Dakin Jalal sam yayi kaca2 da kwalabe da abubuwa dan haka suka wuce dakin Jawwad.
Jalal ya kula da yanayin Jawwad kaman ransa
a bace yake, dukda Jalal dinma nasa ran ba dadi amma yace
"Jawwad meyake damunka ne? Saura kacemin bakomai dan fuskarka ta nuna"
Jawwad yace "Jalal duk na rasa meyakamata inyi" nan ya kwashe komai yagayawa Jalal"
"Bazaka Auri wata Naja ba"
"Wallahi Jalal nima bana sonta amma Maama ta dage na rasa ya zanyi"
"Karka damu zamu samu mafita amma wannan yarinyar ba matar Aure bace, dan sam baku dace ba" Jalal yaita kokarin kwantar wa Jawwad hankali yayin da shikuma gefe guda tasa damuwar nakuma sassakar zuciyarsa, musamman idan ya tuna maganganun dayaji Ilham tanayi da mamanta akansa.
A ranar da yamma daddynsa ya dawo, bagan magariba Jawwad yaiwa Jalal rakiya zuwa gidansu, har palourn daddy sedai daddy beji dadin yadda ya tarar Jalal yai rashin lafiya be Sani ba, Jawwad yace "Ai yaji sauki daddy ya warke, bekamata kana can mu tayar maka da hankali ba gashi yaji sauki" daddy yace "Hakane ya jikin naka?"
Jalal yai ajiyar zuciya sannan yace "Naji sauki" Mummy ce ta shigo palourn da cup din tea a hannunta, tazo ta samu guri kusada daddy ta zauna sannan tace "Ya jikin naka?"
Banza yayi yaki kulata, sema dauke kai da yayi, Jawwad yace "Jalal Mummy namaka magana fa" wani uban tsaki yakuma yi ya dauke kai, daddy yace "Haba Son Mum cefa, at least kagaya mata how you feel zataji dadi" mikewa Jalal yayi ya nufi hanyar fita Jalal yabishi yana cewa "wai Jalal wani irin mutum ne kai? Baka kyauta ba meyasa kake hakane, mahaifiyarka cefa?" tsayawa yayi ya kalli Jawwad yace "Ta haifeni ne kawai, amma bata amsa sunan uwata ba, ka gayamin ya dace abunda taiwa dangin mahaifina, shikenan ni haka zan kasance bawanda ze dinga rabata, ba soyayyar uwa, ba dangi ba abokai, haka zan kare Rayuwata, kaikadaine ka iya jure halin mahaifiyata kae taredani har zuwa wannan lokaci, Jawwad yaushe zan samu sassauci akan kaddarorin Rayuwata why me? Mahaifiyata amma kullum itake kokarin rusani itafa ta haifeni, bata tausayamin kodan irin Rayuwar dana shiga saboda ita? Kowa ya gujeni nazama abun kyama, shikenan nasan matakin dazan dauka" yana zuwa nan a zancensa kawai ya juya ya fice da Sauri, Jawwad ya mike ze bishi daddy yace "Son kyaleshi, inka bishi maybe ya sauke maka yabata maka Rai karkaje inda yake a yanzu, zoka zauna nan ina so zamuyi magana da kai, Jawwad ya dawo ya zauna, Daddy ya kalli Mummy yace" Khadija dan kina mahaifiyar Jalal, dole kicire girman kai ki nemi Afuwarsa dan tabbas kin cutar dashi,
Mummy tace "Nifa ina mamakin cewa dakuke nice sila, wace uwace zata sa hannu danta ya lalace, menayi dayazama nice silar lalacewar sa, Jalal ne yakamaga yanemi yafiyata batamin randa yakeyi"
Ta mike a fusace tabar palourn, Jalal kam yana fita yacikaro da Ilham a harabar gidan yabita da wani mugun kallo na tsantsar tsana, seda tasha jinin jikinta, yasa kai ya fice a fusace, Jalila na kan step din palour taga Jalal ya shigo gidan ya nufi part din Jawwad, se hada hanya yake kaman baya ganin gabansa sosai daga inda take ta hango kaman da hawaye a idonsa, da Sauri yakarasa part din Jawwad ya tura kofa ya shiga aiko itama da sauri ta sakko tabi bayansa.
Amma tana zuwa kofar dakin seta tsaya tafara tunani "to idan naje mezan ce masa? Inkuma ya makeni fa?" juyowa tayi zata koma, kawai taji kaman Jalal yana fidda numfashi da Sauri.

Da sauri ta bude kofar ta shiga, yana tsaye yana kaiwa yana komowa, idonsa yazama abun tsoro saboda ja, ga jijiyoyin kansa duk sunfito sun mimmike, gashi da kyar yake sauke numfashi, se faman runtse ido yake, da Sauri Jalila takarasa tace "Jalal meya sameka? Wani abun yafarune? Ko jikinne?"
Banza yai mata ya juya mata baya, da sauri ta zagaya gabansa tana kokarin kallon fuskar sa, amma yasa hannu ya hankade ta, bige hannu tayi ajikin center ta rike gurin tana dan cije lebe tareda ya mutsa fuska alamun taji zafi, ta bugu sosai a hannun, mikewa tayi takuma komawa inda yake, a hankali ta ga ya sulale ya zauna yana motsa bakinsa alamun yanaso yai magana amma yakasa, kawai ya lumshe ido hawaye na fitaa a gefen idonsa, gaba daya yanzu Jalila tausayinsa takeji, tabbas Jalal na cikin kaddarar rayuwa amma hanyar daya dauka ba itace mafita ba. Taje gabansa ta zauna ta dan kura masa ido na wasu mintuna sannan tafara magana cikin nutsuwa da kwantar da harshe
"dukkan dan adam ba abarinsa ba tareda jarabbawa ba, Kowa da kalar tasa kaddarar, inkaji ta wani sekaga taka ba komai bace, Annabi Ibrahim alaihi salam, Annabin Allah ne, ya kira mutanensa akan bautar Allah shikadai, amma Mahaifinsa be musulinta ba, hakan besa ya saba masa a matsayinsa na mahaifinsa ba, karshe ma har wuta aka hada domin a kasheshi amma Allah ya tsallakar dashi.
Annabi Yusuf alaihi salam, Mahaifinsa na matukar Kaunarsa amma se aka Jarrabeshi akan Yan uwansa, suna masa hassada da kaunar da mahifinsu kemasa kaga matsayin sa na Annabin Allah amma har kurkuku yayi, amma daga karshe kaga daukakar daya samu.
Annabi musa alaihi salam shima yayi gwagwar maya, bayan Allah ya tsalakka dashi daga sharrin fir'auna, kalli butulcin da mutanensa sukayi masa, kowane Annabi da kalar jarrabawar da Allah yai masa. Annabawa kenan ina gamu daba kowan kowa ba, wasu na Kabari, wasu na Asibiti se an kwantar an tayar, wasu na prison basu ba kara shakar iskar yanci, wasu na gidan masu rangwamen hankali, wasu na gidan marayu ana musu kallon shegu, wasu guragu ne, suna maula a gefen hanya, wasu yaki yasa sun rabu da iyalansu da yan uwansu, duk cikin wannan ba wanda Allah ya jarabceka dashi, karka zama me butulci da Ni'imomin ubangiji no matter how worst the situation is kazama me gode masa, kanada dama, kanada lokaci kayi kokari ka gyara barnar dakayi a baya, ka yafewa mahaifiyarka inka yafe mata se Allah ya shiga cikin lamarin ka. Anyway for now don't try to kill yourself without changing your life style. Yai shiru idonsa a lumshe amma nasihar Jalila yaji tana tasirir a zuciyarsa a zuciyarsa ya shiga Fadin Astagfirullah wa atubu ilaihi, amma deep into his heart in ya tuna yadda take masa rashin mutunci se haushinta yakama shi, a fili ya bude idonsa yace
"Tashi kibani guri bana son ganinki a inda nake, kinadaga cikin mutanen dasuka kara saka zuciyata cikin garari, da tashin hankali, kinsan yadda nakeji inkika jefeni da kalmar mara tarbiyya, kin dade kina gayamin maganganu masu kona zuciya, a maimakon kalaman kwarin gwiwa, ki tashi kibani guri karki kara zuwa inda nake, nasan da Umminki tana nan nasan komai munin halina bazata taba kyamata ko tagayamin bakar magana ba, bazata taba zama cikin masu kyamata ba, ta nunamin so da kauna, kuma batun yafiya tsakanina da mahaifiyata wannan abunda ya shafeni ne, i never expect such type of behavior from you, why? Why do you hate me before, baki taba tunanin me ya jawomin nake irin wannan rayuwar ba, Never judge book by it's cover, please dismiss from here, in ina ganinki kina kara batamin rai" Idon Jalila kyar akansa bata ko kyaftawa har yayi gama yana huci,
"Naji zan tashi, Nagode sosai, karka manta da kashedin likita, kaci Abinci kasha magani, sannan ka rage shaye2"
"bazan ba uwatace ke dazaki dinga min kashedi haka? Wai ina ruwanki dani ne, meya shafeki da inyi lafiya ko kar inyi"
"A'a ba daya, in kayi inma bakayi ba kanka kayiwa ba Jalila ba, Amma kaji tsoron Allah, kakiyaye dokokinsa sannan ka kulada ibada" ta mike jiki a sanyaye ta fito waje, maganganun da Jalal ya gayamata babkaramin bata mata rai sukayi ba, dukda taji zafin maganganun da Jalal yagaya mata, amma idan ta tuna itama abubuwan data dinga masa abaya setaga bata kyauta ba.
Daddy ya kalli Jawwad yace "Jawwad Abbanka kuwa yana gari ina son ganinsa" Jawwad yace "A'a Daddy be dawo ba tukuna yana lagos amma a satin nan ze dawo Insha Allah" daddy yace "Allah yadawo da shi lafiya, Yaww Jawwad naji Jalal yacemin ka kamalla Masters dinka last Couple of months ko?" Jawwad yace "Eh Daddy Alhamdilillah na kamalla, ina jiran sakamakone, atayamu da Addu'a" daddy yai murmushi yace "Kullum cikin yi muku nake? Kuma nasan da sakamako me kyau zaka fita Insha Allah, nasan yarona
akwai himma ai, dama vacancy na samu, federal zata dauki ma'aikata a farkon sabon shekara anbani vacancy na mutum daya a babban branch din NNPC na Abuja, shine nace ka turomin CV dinka ta Email dina, inkuma zaka karo karatune kuma to, semuga yadda za'ayi kaje ko England ne can wajensu Mahmud ka karasa" shiru Jawwad yayi ya sunkuyar da kai yakasa cewa uffan daddy yace "Jawwad kona bata maka raine?" Jawwad ya girgigiza kai yace "Daddy banida bakin yi maka godiya, tun ina karami kake dawainiya dani, amma ina tunanin dan uwana, daddy Jalal shifa me za'ayi wands za'a tallafawa Rayuwarsa" daddy yai ajiyar Zuciya yace "Jawwad bana tunanin koda Jalal yanada dan uwa ciki daya ze nuna masa kaunar da kake masa, Amma Jawwad ba yadda zanyi ina za'adauki Jalal aiki a wannan halin da yake ciki, yana shaye2 baya son mutane, ga zafin zuciya kana gani ko mahaifiyarsa baya raga mata, anyi2 yakoma makaranta yaki " Inda na godewa Allah ko bayan raina Jalal yanada kadarorin da in ya tattala ze iya rike kansa, inkuma yabarnatar shikenan" Jawwad yace "Daddy bazanyi musu da hukuncin ka ba, amma inaso Jalal ya samu makoma shima, koya koma karatu koya samu aiki, amma idan na tafi Aiki na barshi a wannan halin senake ga kaman banyi masa halacci ba, kuma shaye2 munmasa addu'a muna fatan ze dena very soon, tunda ya rage ba kaman da ba" shiru daddy yayi yana kallon Jawwad dayake magana idonsa taf Hawaye dake nuna hakikanin gaskiyar abunda yake fada har zuciyarsa.
"Jawwad kenan Allah ya dawwamar da haske a cikin Rayuwarka, gwagwarmaya da kaunar dakake wa dana banida abun biyanka, Allah yatemakeka ya baka abunda kake nema duniya da lahira"
"Ameen daddy" daga haka ya tashi ya fita.
Oga KB yana zaune yatasa Samira da wata katuwar bulala, da alamu jibgarta yagama yi, jikinta duk a kumbure dan fuskarta a kumbure gefen idonta yana zubar da jini, Oga KB yace "Tun tsawon wani lokaci kike tareda Jeje?"
Cikin kuka tace "Ranar muka fara haduwa da shi" kafin ta rufe baki yakuma zuba mata bulala tareda fadin "Karya kikeyi, munafuka zaki gayamin ko sena takeki na kasheki, matsiyaciya yanzu shikenan Sunana yagama lalacewa a idon duniya, nida 'yata a gidan karuwai, dana san irinki za' a haifamin da tun a ciki sena zubar dake, Wallahi idan Nagano wanda ya shirya min wannan manakisar sena kasheshi kowaye, ki gayamin tun yaushe kuke tare?"kokuma yanzu inkasheki da poison na kashe banza shedaniya"
"Shekararmu biyar Tare dashi" zaro ido yayi "Shekara biyar amma bansaniba, Cigaba ina jinki se akayi yaya?"
"tun ina secondary muke tareda shi, bayan haduwa ta da Saleema, nasanshi ne ta hanyarta, daga baya yake nunamin yasanka, Yaronka ne akwai aikin dayake maka, duk lokacin danazo maka da bukata baka damuwa da bukatuna, kafi son faruk dani, kana cewa bazaka kara yadda da mace ba koda yar cikinka ce, nikuma bukatuna bakamin, umma ma bayimata kake ba, balle nima ina sa rai, shine Jeje yajani a jiki shine ya koyamin bin maza, yana baani kudi masu yawa sannan ya hadani da masu kudi Shida Saleema, Sau biyar ina zubar da ciki biyu duk nasane" Wata irin zuface ta shiga tsatstsafowa Alhaji Kabiru mikewa yayi ya shake Samira yana fadin
"Samira anya kuwa nine Ubanki, kodayake a rina barewa bata gudu danta yai rarrrafe uwarkima karuwanci tayi ta tuba na Aureta, watakila bayan na Auretanma bata tuba ba" Mahaifiyar Samira ta fito a fusace tace "Sakarmin 'yata wallahi bazaka kasheta ba, tun dazu inamaka kawaici shiru kawai nake, tunda abun naka yazoda cin fuska bari in tunamaka, kana tunanin hakkin uwarka ze kyaleka ne,? kokuma shi yaron dakasa aka lalata ba dan wasu bane? Yaronne yai maka laifi? Kokuwa uban me ya kaika gidan karuwai? Duk nasan abunda ka keyi kyaleka kawai nakeyi dan haka sakarmin yarinya ni Addu'a nake Allah ya shirya yaran musulmi amma wannan bakar zuciyarta ka me cike da sharri dole kaima kaga sharri akan yaranka", A fusace yayo kan mahaifiyar Samira, amma Samira ta rike rigarsa cikin ihu da kuka take cewa "Wallahi karka sake ka tabamin uwa, nidin dai ko kasheni kayi nasam baka da asara, ai a ranar da aka kamamu
a gabaana zizo yace kaima ana kaimaka karuwai gidan hutawarka, tunda na taso katsaneni saboda kawai ni macece ka fifita soyayyar danka namiji akaina, gaka da kudi amma baka moramin komai danme yasa bazan nemawa kaina mafita ba" jin hayaniya yasa tuni mutane suka fara shigowa dan ganin meyake faruwa, Alhaji Kabiru yasa hannu yai wurgi da Samira, take ta fafi bata ko motsi, nan da nan mutane sukayi kanta amma ana dagata sega Jina nata zuba daga jikinta. Shikam Alhaji Kabiru motarsa ya dauka ya fice daga gidan be zame ko ina ba se gidan Jeje, Yana zuwa Jeje baya nan, dan haka ya tafi Club din dayasan lallai zs same shi a can Jeje yana nan, yanata shaye2 shida wasu mata, tareda wasu abokansu.
A fusace ya daka musu tsawa yace su basu guri, daya ta kalleshi cike da maye tace "Wollah ba inda zamuje, ji mutum kazo kasamemu sannan kace mufita
"Jeje yace "Am sorry Guys don't mind him" Jeje ya dawo da dubansa kan Alhaji Kabiru yace "I thinks you said it's over between me and you ba, bayan tsawon lokaci dana dauka inamaka aiki, inamaka bauta dan ka kamani da 'yarka,' yan sanda sunkamamu, shine kacimin mutunci kamanta halaccin danayi maka"
"Shut up!!!"
yayi wa Jeje tsawa
"Duk wahalar danayi maka A rayuwa, tun kana karamin dan isaka na daukeka naimaka gata, na dinga yimaka wahala tsawon shekaru, baka cikamin burina na ganin ankai Jalal kurku a kasksance uwarsa da ubansa na kuka ba, memakon ka maida hankali akan aikin dana saka, sema komawa da kai kana cin amanata, yar cikina kake lalata da ita, kakoya mata bin maza, ga shaye2 ta tabattarmin da sau biyar tana zubar da ciki biyu daga ciki kuma nakane, Ka saurari abunda ze biyo baya, hukuma ce zata rabani da kai"
"Kafin ka kaini gaban hukuma yakamata ka amsawa kanka wannan tambayoyin? Kai yara mata nawa ka lalata?
Ko agaban Allah wace hujja zaka bayar na bada kwangilar lalata Rayuwar ABDUL JALAL da sunan daukar fansa?
Uwa uba karka manta da babbar haramtacciyar harkallar da mukeyi na saida makamai da miyagun kwayoyi" cak Oga KB ya tsaya yayinda Jeje ya kyakyake da dariya yace "Ramin mugunta kenan inzaka gina, gina shi gajere dan kila kai zaka fada"
Wani mugun bakin ciki da bacin raine yakama Oga KB ya juya ya shako wuyan Jeje yafara bugashi akan tebur, dayake a buge yake sam jikinsa babu kwari, nan take matasan dake gurin su taso sukayi kan Oga KB, dan har jini yafara fita daga hancin Jeje, Oga KB na juyawa ya rarumo wata kwalbar giya ya bugawa Jeje a goshi nan take Jeje yafara zubar da jini hakan be isheshi ba seda yakuma soka masa kwalbar nan a kafada, Jini ya dinga fita a jikinsa nan take jiri ya kwashe Jeje ya fadi kasa, da kyar security din gurin suka rike Oga KB suka tafi dashi suka kuma mikawa 'yan sanda shi. Sannan aka dauki Jeje zuwa Asibiti rai a hannun Allah.
Ita kuwa Samira da aka kaita Asibiti ta galabaita ashe wani cikinne a jikinta bata saniba, da kyar aka ceto ranta sedai an tabattar da mahifarta ta lalace bazata kara daukar ciki ba har abada.
Jawwad yakoma gida ya tarar da Jalal a part dinsa, a zaune a akan kujera, Jawwad yaje kusada shi ya zauna, ya dinga masa nasiha tareda rarrashi akan abubuwan dayakewa mahaifiyarsa, Jalal yai shiru yaki kula Jawwad har yai surutansa yagama dan babu alamar Jalal ya dau Nasihar Jawwad, seda ya bari Jawwad yagama tsaf sannan yace "inka gama bani aron key din motarka"
"ina zakaje?"
"In tuhumata zakayi bar abunka"
"A'a ni na isa, gashi amma kabi a hankali kasan bakada lafiya kayi driving a hankali" Jalal bece komai ba yasa hannu ya karbi key yafita.
Jawwad ya nemi guri ya kwanta ya dan huta yana tunanin karamcin da daddy yake nuna masa. Jawwad yasamu yayi bacci, se bayan la'asar ya farka, yaje yai wanka yai salla yana kokarin neman Abunda zeci ya tuna
dakin Jalal yana nan kaca2 yasan inba'asa an gyara ba Jalal baze gyaraba ko dakin ze shekara ahaka, kuma ze iya zuwa yayi shaye shayensa yace ze shiga ya kwanta ga kwalabe da ya farfasa a zube a dakin, Jawwad ya mike ya fita, yana fitowa kafin ya kaiga bakin gate yaji muryar Naja ta kashe murya tana masa magana "Yayana dan Allah inbazaka damuba sonake ka rakani unguwa" Jawwad ya kakalo murmushin dole yace"
"Eyya am very sorry, kinga aiki zanyi ne yanzu na gaggawa dan Allah kiyi hakuri" yana gamawa bejira mezatace ba ya fice daga gidan, tsayawa tayi turus tarasa me zatace. Haka ta juya takoma cikin gida tana cizon yatsa, tana komawa daki ta tararda Jalila tana gyara gashin ta agaban mudubi, ta dinga tsaki tana aikin banza, ita dai Jalila bata kulata ba, seda tagama tsaf ta dauki mayafi ta daure kanta ta dau wayarta ta fice, tana bukatar yin waya domin jin inda harkalarta ta kwana.
Jawwad yana zuwa yafara tattarre Kwalaben dakin yana sakasu a dustbin yana bawa megadi yana fita dashi, Jawwad ya duba bega tsintsiya ba dan haka yakoma gida don ya dakko, yana zuwa ya hangota tana waya, kallo daya tayi masa tai murmushi ta sauke wayar tace "Ya dai naga kayi gumi haka? Meyafaru?"
Murmushi yayi yace "Wallahi Jalal nake gyarawa daki, yayi fata2 da komai, kuma in ban gyara masa ba a haka ze barshi, kar inje ya bugu yace ze shiga dakin ya kwanta a haka" Jalila tai murmushi tace "Allah yasadaka da dukkanin wani alkhairi na duniya da lahira hakika ka cancanci yabo, Yaya Aliyu Jawwad sha gwagwarmaya, amma meyasa sekai zaka gyara masa?"
"Kinsan halin dan uwan nawa, bakowa yake so yashigar masa daki ba, baya son sa ido"
"Hakane muje in tayaka"
"Anya kar in takura miki fa"
"Bawani takura gyaran gida aina matane" ta rakashi suka dakko tsintsiya suka fito akan idon Naja suka fita tare aikuwa tasaki Ashar, Da sauri Nana ta kalleta "Lafiya kike mana Ashar haka sekace ba musulma ba"
"Dalla rabu dani yanzu nacewa Jawwad ya rakani unguwa yace bazashi ba yanada abunyi, amma kalli sunfi ta tare da wannan jakar yarinyar, zasu gane kurensu bari Maaman ta dawo" Nana ta tabe baki tace "Wallahi Naja duk inda kikaje sekinja masifa, muna zamanmu lafiya amma kinzo zaki tayar mana da hankali Aikin banza kawai" Nana ta mike ta fice tabar mata dakin.
Jalila ta dinga taya Jawwad suna kwashe kayan daya fasa suna fita dashi a hankali dakin yafara hankali kula tayi kaman Jawwad yagaji sosai tace "Yayan Baby what's wrong" yace "Baby yunwa nakeji sosai, ga Jalal yafice ban san inda ya tafiba koya ci Abinci oho"
"Allah sarki jekaci kadawo ina jiranka, Abincin yana nan a kitchen"
"God bless you my dear, yanzu zan dawo Insha Allah"
Sosai Jalila tacigaba da aikin dakin, bedroom din zuwa palour ta gyara komai, taje tana goge kan fridge kawai ta bude, kwalabene manya da kanana, tanagani tasan giyace ga kwalayen sigari nan duk ya shiryasu a
ciki sekuma kwalayen madara da Apple a ciki amma kwalaban giya sunfi yawa, fito dasu ta dingayi daya bayan daya ta taresu agabanta ta girgigiza kai, ta tattaresu guri daya tadinga bude kwalbar tana tsiyaye giyar a cikin
dustbin, ta zazzage tabar nan a cikin shara, tacewa megadi yafita da ita. Ta koma dakin ta juya baya tanata mopping taji an rikota ta baya..

Da sauri ta waiwayo don ganin waye ya cukumota haka, tozali tayi da Ilham ido cikin ido, a fusace Jalila tace "Malama lafiya? Meye haka sekace wata mara hankali"
"Nikike cewa mara Hankali? Uban me kikeyi a dakin nan?"
wani irin kallon rainin hankali Jalila tayi mata
"Uban da kikeyi shina keyi, Dan Cikani mana" kara rikon Ilham tayi "Bazan sakekiba, munafuka ranar kinje gurinsa kin zauna a Asibiti dan shishshigi, yau kuma uban me yakawoki dakinsa? Makira Annamimiya"
"Ilham ba ina binki a sannu bane dan ina tsoronki, uban dayake kawoki dakinsa shiyake kawoni kicikani"
"Bazan cikaki ba se kin gayamin uban meye hadinki dashi da har zakizo dakinsa wai kina gyarawa, akan me wayasaki, ke nifa ban yadda dake bama wallahi" hankade ta Jalila tayi ta nunata da yatsa, kikakuma gigin tabani wallahi sena baki mamaki, inkin isa in yazo shikije ki titsiye shimana kokuma kema ki dinga shige masa in zaki samu gindin zama, wallahi Ilham ki kiyayi shiga sabgata inbahakaba sekin gane bakida wayo, bar yimin kallon haka, sakarya kawai"
A Fusace Ilham tayi kan Jalila ta riko hannun da Jalila ta fadi akai sanda Jalal ya tureta fadi, "Wallahi sekin gayamin meye hadinki da Jalal, sannan meyasa kike shishshigi a lamuransa, bazaki bar gurin nan ba sekin fadamin uban da kukeyi"
"Dalla cikani, ubankine Jalal din ko dan kekadai aka halliceshi, sha3 mutumin dabata taki yake ba, inma wani abun mukeyi kema kizo kuyi"
Jalila ta fizge hannunta aikuwa Ilham ta dauka mopper tayo kan
Jalila, tana cewa "Wallahi sekin gayamin yau senaga uban da yatsaya miki koni koke, matsiyaci ya kawai, wallahi sena miki dukan dabazaki sake shigowa gidan nan ba.
Jalila tai sauri ta dauki Ruwan mopping ta shekawa Ilham shi gaba daya a jikinta, sannan ta bita tana kwala mata bokitin. Seda yafara fashewa a jikin Ilham, inda Allah ya temaketa bokitin robane, Jawwad ne yakawo kai yaga
ana wrestling, Ilham ta durkusa tanata ihu Jalila tana bugamata bokiti tana huci, da sauri yaje ya riketa yana fadin "Subhanallah lafiya kuwa? Jalila meye haka?" A fusace Ilham tace
"Dole ka tsaya kana tambaya mana kaima munafuki, wallahi tun wuri kajamata kunne inbata kiyayeni ba sena illata ta wallahi, nikika jika da ruwan datti kika dakeni ko? Wallahi sena sa kinyi danasanin zuwanki duniya"
"Karki fasa, nikuma bazan gaji da lakada miki dukaba tunda bakya gane yaren mutane sena jakuna in an dakeki" Jawwad yace "Jalila yimin shiru, Ilham dan Allah kiyi hakuri komene nasan Jalila ce bata da Gaskiya, rigimanmiya ce tun asalinta dan Allah kiyi hakuri"
"wallahi ni inada gaskiya, akanme zatazo tana zagi....... Jawwad yace" yimin shiru ko in zane miki jikinki yanzun nan, bata hakuri sannan ki wuce kitafi gida sarkin fada kawai" Jalila tai murmushi tace "Ilham dan Allah kiyi hakuri, sharrin shedanne, Insha Allah inkika dena shiga harkata bazan kuma tabaki ba, amma kika cigaba da rainamin hankali zaki gane bakida wayo" Jalila ta juya tai ficewarta, Ilham tacigaba da zazzaga bala'i Jawwad yana ta bata hakuri. Seda Ilham tagama zazzagewa Jawwad rashin mutunci sannan ta bar dakin, Jalila tagama gyara dakin fes, sedai ruwan mopping data zubawa Ilham duk ya kwantaa a gurin, Jawwad yasa abu yai mopping din gurin, har kusan goma na dare sannan Jalal ya dawo, koda ya dawo gidansu ya wuce, yaje ya siyo kayan shaye2, yana shiga dakinsa ya ganshi fes kaman ba dakin ba koba a fada ba yasan Jawwad ne ya gyara, ya danyi Murmushi ya karasa inda fridge dinsa yake amma me yaga an kwashe komai na ciki se madara, iya saninsa Jawwad baya taba masa kayan shaye2 tunda suka taba fada akan haka, a fusace ya mike ya fita harabar gidan yana kwalawa Me gadi kira, a sukwane me gadin yazo dan Jalal baya shiga harkarsa indai yaji yamasa wannan kiram to akwai matsala Jalal yace "Bayan Jawwad waya shigarmin daki? Seda gabansa ya fadi take ya rikice yace yace "Ammm Ilham ce yallabai" a fusace Jalal ya juya ya shiga cikin gida, dakin Ilham ya nufa yana zuwa ya tarar ta fito daga wanka tana sanye da rigar wanka, tana duba goshinta inda Jalila ta daketa da bucket cike da tsana yace "Ke ubanwa yabaki izinin zuwarmin daki?"
"Nikuma?" "tambaya ta ma kike zan tattakaki, ina kayana da kika kwashe a fridge?, nakine koke kika ajiyemin, ina kayana"? Yafada cikin shouting
"Ni ban taba maka kaya ba, kaje dai ka duba" fizgota yayi ya dauke ta da mari, "nizaki Rainawa hankali kinsan nawane kudin kayan nan kuwa, ki gayamin ina kayana ko in shakeki, inkuma kinfara shane kema se inji" dafe kunci tayi tana kuka "Ban saniba, niban daukarma komai ba, meyasa kai Azzalumi ne wallahi se Allah yasaka....... Tas! Yakuma wanka mata mari wallahi sekin fitomin da kayana, gobe in ance kikuma shigarmin daki bazaki ba yai kanta, da sauri ta haye gado tana ihu sosai
"Nashiga uku, atemakeni wallahi ya haukace ze kasheni, bashida hankali " kalmar hauka data kirashi yakara bata masa rai, kan gadon yabita ya shaketa dama kuma a buge yake,
Da sauri Mummy ta nufo dakin a gigice, tana zuwa ta tarar ya shake Ilham idonsa yayi Jawur, Daddy ma da sauri ya fito ya nufo dakin, a gigice Mummy tace
" Jalal meye haka inka kasheta fa?"
" Na kashe banza, ubanwa ya kaiki dakina kika tabamin kaya"
Da kyar daddy ya kwace Ilham a hannun Jalal, Daddy ya kalli Ilham yace "Ilham meya kaiki dakinsa mekika taba masa?"
"ni wallahi bani bace ba, Jawwad ne ya shiga, kuma nida naje Jalila na tarar tana gyra dakin, ni ban taba masa komai ba" takarasa fada tana kuka
"Jalila tabbas itace" ya fada a ransa juyawa yayi ya fice daga dakin da sauri. Daddy yaita bawa Ilham hakuri, suka fita suka bata guri, Ilham fashewa tayi da kuka "lallai Jalila bata da mutunci, bayan dukan datayi min shine taje ta kitsamin sharri, wannan wce irin Jarabace" haka Ilham taita kuka. Shikuwa Jalal yana komawa dakinsa yarasa mezeyi ya huce, Jalila ba karamin Asara tai masa ba, yasan itace ba wani ba, giyace me matukar tsada da wuyar samu, ga kwalayen sigari duk ta kwashe masa haka ya kwanta yana tunanin mezeyiwa Jalila ya huce ne.
Nana tanata waya da Mahmud, abun nasu ya rikide yakoma Soyayya, Jalila ta kule a cikin bargo tana chatting, Zahra take sanarmata ankuma kama baban Samira, ya zaneta ashe tanada karamin ciki, sannan yaje Club yakama Saurayin Samira ya sossoka masa Kwalba, A sukwane Jalila ta tashi zaune, takira Zahra, Zahra na dagawa tace "Jalila kinga sakona ko?"
"Eh nagani Zahra dan Allah dagaske kike koda wasa?"
"Haba Jalila yazan miki wasa a wannan maganar wallahi gaskene, har wasu sunje dubata tana Asibiti"
"Thank you for the Update dear, nagode sosai Zahra Allah ya biyaki" ta kashe wayarta, ta shiga tunanin mezatyi wanda zata sa A rike Alhaji Kabiru wannan karon kar asakeshi a gurfanar dashi a kotu.
Take Suleiman ya fado mata a rai, wani dan guntun murmushi tayi, tamike ta shige toilet ta rufe kofa sannaan ta kira suleiman, sun dade suna waya, tagaya masa komai, tace dan Allah inda wani taimako daze mata yayi, a karbi case din abawa wanda zasu jajirce a gurfanar dashi a kotu, yamata Alkawarin zeyi iyayinsa, sannam intanada wani sheda ta tura masa, ta turawa suleiman dukkan waya da chat dasukayi da Alhaji Kabiru, ta tiramsa har recording din maganar su Samira da barazanar da suka dingayiwa Zahra, Suleiman yace insha Allah zeyi kokari yaga me ze iyayi, yace zesa amasa bincike, kafin yazo kano tai masa godiya sukayi sallama sannaam ta fito daga toilet din, tana fitowa Nana ta dan tsuramata ido sannan tace "Jalila kekam me kike a bayi haka, kinkusa awa daya fa, murmushi Jalila tayi tace
" Ke Awa nawa kikayi kina waya, kai Nana Allah ya shiryeki da sa'ido wallahi" sukayi murmushi gaaba daya banda Naja, data ketawani hura hanci tana shan kanshi, Jalila ta kalli Inda Naja take sannan tace "Bari inzo inkira Yaya Jawwad inji in yayi bacci, in beba ya tayani hira, Tunda ke Nana naga hankalinki nakan wannan Mahmud din" Nana tai murmushi tace "Jalila bazaki gane ba Mahmud ya hadu, he is so romantic"
"Aifa gashi nan gaba daya kin Afka soyayya ba kyaji ba kya gani" suka kuma dariya, Naja ta tsurwa Jalila ido, jira take taga Jalila ta kira Jawwad tai mata rashin mutunci amma taga Jalila tayi kwanciyar ta. Can cikin bacci Jalila ta farka, take jin surutu kasa2, tai shiri setaji Naja ce take waya da Saurayi kusan karfe ukun dare, ga wayar tasu batsace kawai sukeyi, Jikin Jalila yai sanyi, "Yanzu wannan ake kokarin a hada salihin bawa kaman Jawwad da ita, bazan taba bari hakan ta faruba, ai gara Hanan da wannan" Naja tacigaba da wayarta dan tunanin ta gaba daya bacci sukeyi, haka Jalila takasa komawa Bacci har Asuba.
An samu Jeje ya farko da kyar, ya zubarda jini sosai, dan haka ana bukatar akara masa wani, duk abokan shaye shayensa suka zame sukece bazasu iya ba, suma jinin be wadace su ba, balle su bashi, Jeje yace dan Allah agayawa Jalal yasan ko kowa ya hanashi Jalal ze bashi Jini, sukace dan dai sako zasu gayawa Jalal.
Kusan kwana hudu Jalal be kara ganin Jalila ba, Jalal yarasa yadda zeyi ya ga Jalila, ko gidansu yaje ya dena ganinta, sannan kuma ta dena zuwa gidansu, gaba daya ransa a bace yake, saboda wannan mummunar Asara datayi masa, shiba kudinne damuwarsa ba se wahalar samu da irin wannan giyar take dashi, kuma ita kadaice in yasha yake ji
n yaji yadda yakeso. Yana zaune yaji karar mota, ya leka ta window palourn sa yaga Daddy ne yafita shida Mummy, jinjina kai yayi, Wayarsa ya dauka ya kira Jawwad, tana fara ringing Jawwad ya dauka, Jalal yace "Kana inane?"
"Maama ta dan aike nine, ya akayi?"
"Kagayawa kanwarka Mummy na nemanta"
Jawwad yace "to bari in kirata zatazo" ya kashe wayar, Jawwad ya kira Jalila a waya yagaya mata, bata kawo komai a ranta ba tace zataje.
Jalila ta dauki gyalen doguwar rigarta ta saka, ta fito ta tafi gidansu Jalal, sam ta manta da tasaka an fita da kayan giyar Jalal.
Koda taje gidan ba kowa, abun yabata mamaki, ta hangi Ilham a kitchen tana hada Abinci, dan haka ta dan Jira Ilham tafito, tana fitowa Jalila tace "Yawwa Ilham, ina Mummy kuwa? Ance tana nemana" A fusace Ilham ta kalleta "Ban saniba matsiyaciya jarababbiya, wallahi senasaki kuka kaman yadda kikemin, saboda kin iya makirci, kikayi min sharri gurin Jalal bayan dukan da kikamin, shima yazo ya shakeni ya kusa kasheni, wallahi in sharri ne gidan kika tarar, sekin gane bakida wayo, ina nan ina shirya miki trape kuma wallahi sekin fada" cikin mamaki Jalila tace "Ke ni ban gane wani makirci na miki ba, shi makircin ba kekika sanshi, dan Allah ina Mummy"?
"Ninake nemanki ba itaba" waigowa tayi ta kalli Inda Jalal ke tun karo ta, tsayawa tayi kaman wata gunki tana kallonsa har ya karaso inda take, A fusace yakamo hannunta yai waje da ita yana janta, Ilham na ganin haka tace "Allah yasa yamata dukan mutuwa" cikin san
a ta biyo bayansu. Be tsaya da ita ko ina ba se part dinsa a gaban fridge, ya bude fridge din ya kalleta a fusace yace "Ina abubuwan da kika kwashemun a fridge?" kallonsa tayi ido cikin ido, ta dauke kanta tai masa shiru "Magana nake miki ina kayaana?"
"Meye kayan naka?"
"Tambayata ma kike?"
"Eh, ai bansan wani kayan bane gara ka gayamin, idan nina dauka, se ince maka nina dauka inbani bace ba zance bani bace"
"Ke meyasa a rayuwarki, kikeson rainamin hankali ne? Kekika dauka ko kaffara bazanyi ba, ina kayana ko in kakkaryaki yanzun nan" ta kalleshi cike da tsiwa da gadara tace
"Na dauka na zubar a shara, nabayar an fita dashi ansaka a bola" ta kare maganar tana kallonsa up and down, wani mugun takaici ne ya kama Jalal, shi takewa wannan gadarar haka, hannunta ya janyo, sukazo daf suna iya jin numfashin juna sannan yace "Ubanwa yasa ki daukarmin kaya, kekika ajiyemin?"
"ba uban daya sani, nina sa kaina, kaga sakarmin hannu, last week ka hankade ni kakusa karyani yanzu kuma kana kokarin karasamin hannu, cikani" lallai Jalila ta kai makura wajen iya rainin hankali, ta masa laifi kuma tana masa gadara
"Ka cikani nace kobaka jinane, kaikam Allah ya shiryeka, kota lafiyarka bakayi, se tsabar masifa da taurin kai ni cikani....
Wanka mata mari yayi, wanda yasa Jalila dena gani na wani dan lokaci,
"bansan a dadin lokutan dana dauka ba ina miki kashedi akan kifita daga harkata, ke wace irin mara zuciya ce, wace irin uwar shishshigi ce ke? Darajar Ummi da Jawwad kikeci da tuni na kakkaryaki na karya banza, ina ruwanki da mara tarbiya wanda baya ganin darajar iyayensa, ina ruwanki dani? Ke kullum burinki kiyi abunda zaki bata min rai ko?" tuni Hawaye ya wanke mata ido, dan sau daya aka taba marinta shima Hanan ce, kuma seda ta koyawa Hanan din darasi, idonta na kwararar da hawaye, cikin nutsuwa tace
" Hakane na fiye shishshigi, kuma inka karyani ka karya banza, amma da ina cin darajar Ummi da Jawwad koda wasa bazaka mareni ba, dan nasan Jawwad baze taba marin wanda yafito daga ahalinka ba, Nagode sosai da wannan marin da kaimin, bazan taba mantawa ba, Allah yabaka Hakuri, Allah ya huci zuciyarka nadena maka shishshigi Insha Allah, Kacigaba da shan giyarka Jalal da dukkan wani nau'i na shaye2 karka dena, bazan kuma takura rayuwata akanka ba, na tafiyar da lokuta masu tarin yawa akan tunani dan ganin kazama mutum kamar kowa, sannan mutane sudena kyamatarka, nashiga damuwa da gwargwamaya saboda kai, but this is what I deserve from you, dana san abunda naimaka ze bata maka rai ta kai gaka mareni da banyi ba, ina me baka hakuri, Insha Allah dana kammala abunda nake zan dena maka shishshigi, balle incigaba da bata maka rai" gaba daya jikin Jalal yayi sanyi, be gama gane inda magamganun Jalila suka dosaba
"Cikani in tafi" yana kokarin yin magana, cikim Zafin Rai tace "Kacikani Jalal tun kafin in rama marin dakayimin, kaine mutum na biyu daya mareni a rayuwata, wadda taimin na farko seda na tabbatar da na koya mata darasi, kaima wasu dalilaine zasu hanani ramawa ka cikani nace maka" tai maganar tana Hawaye, gaba daya Jalal ya rikirkice, ta fizge hannuta ta fito waje ta tafi gida, seda ta tsaya a waje ta gyra fuskarta ta maze sannan ta shiga gida.
Ilham da take labe kuwa gida ta koma tana murna tareda yiwa Jalila Allah yakara.
Shikam Jalal guri yasamu ya zauna yai shiruu yana tunani, danasanine ya lullube shi, meyasa ya mareta ya akayi har ya mareta, "Jalila ce fa ya akayi na mareta ne? Mtseww yarinyar nan ta fiye shishshigi da taurin kai" magamganun Ilham da mamanta da sukayi a Asibiti ne suka dinga dawo masa. Mikewa yai da sauri yabi bayan Jalila amma kodayaje gidansu ma tariga ta shige cikin gida, dakin Jawwad ya tafi ya zauna yai shiru duk abun duniya ya dameshi musamman inya tuna Hawayen daya gani a fuskarta. Wayarsa ce tafara ringing, lambace ba suna ya daga yasa a kunensa, anan aka sanar da Jalal Jeje yana kwance a Asibiti rai a hannun Allah yana bukatar jini amma an rasa me bashi, bill din Asibitin dana magani ma ba'a biyaba, Jalal yace Insha Allah gobe zezo Asibitin aduba jininsa in yayi daidai asawa Jeje, sannan ze biya bill din Asibiti.
Jalila bata taba zaton Jalal ze iya marinta ba, yau taki kula kowa har dare ba wanda ta kula, duk yadda Naja taso ta tsokane ta suyi rigima Jalila taki yadda.
Washegari karfe sha daya na safe Jalal ya shirya ya tafi Asibitin da Jeje yake, ya tausaya masa ganin halin dayake ciki, bakowa a gurin Jeje se shikadai gashi ba'a wani kula dashi saboda ba'a biya kudin Asibiti ba, Jalal yana zuwa yabiya kudin Asibiti, sannan yasa aka canzawa Jeje daki, Jalal yana zaune agaban gadon Jeje, yana jira likitocin suzo aje lab a duba in jininsa zewa Jeje, 'Yan sanda biyu suka shigo dakin suda wani babban mutum sekuma Jalila mamakine yakama Jalal ya tsaya yana kallonsu, Kokusa Jalila bata nuna tasan Jalal ba sukaje gaban gadon Jeje, y'ansandan suka mikawa Jalal hannu suka gaisa, amma hankalin sa yana kan Jalila, ta kalli babban mutumin ta nuna Jeje tace "Yallabai wannan ne, shine wannan" mutumin ya gyada kai yace "aidaganinsa kaga criminal, ni kaman na taba ganinsa a wani guri, amma wannan fa, dan uwansa ne kokuwa? Shima wannan da gani drunker ne" kalmar drunker da Suleiman yafadawa Jalal, Jalila taji bataji dadi ba, amma ba yadda zatayi tunda Jalal yana shaye2
Jalila tace "Yallabai yanzu zakaji komai daga bakinsa" ta taka a hankali ta tafi gaban gadon Jeje ta tsaya ta kalleshi ya kalleta tace "Yau nacika maka alkawarin dana dade inayi maka, senaga bayanka, inaga kusan sau hudu ina gayamaka wannan kalmar, bari inbaka wani sako kagayawa ubangidan ka Oga KB, kokuma ince Alhaji Kabiru, kagaya masa Ni Jalila Aliyu Imam, ni nasaka aka kamaka da shi da 'yarsa a gidan karuwai" gaba daya suka juyo suna kallon ta.
ABDUL JALAL NOVEL FANS GROUP
inayinku irin sosai din nan comments dinku nasani nishadi da bani karfin gwiwa inayinku ina kaunarku nima Allah ya barmin ku

Gaba daya sukayi shiru suna sauraranta, tareda kallon mamaki, tacigaba da cewa "Sannan kuma zan tabattar maka da zarginka Nice kuma nasaka aka dauke Jalal ranar birthday dinsa" ta juya ta kalli Suleiman tace "Yallabai gashi nan, ku tambayeshi"
Suleiman ya janyo kujera gaban gadon Jeje ya zauna, ya kalli Jeje yace "Ya jikin naka dan uwa" da kyar Jeje ya motsa baki yace
"Da sauki"
suleiman ya gyra zama yace "Inbazaka damu ba, zamuyi maka tambayoyine gaskiya muke bukatar ka gayamana in kayi karya, zamu daukeka a haka mutafi da kai office ka warke a can, mecece Alakarka da mutumin daya yi maka wannan raunukan?"
Jeje yace "Ubangida nane, ni yaronsa ne"
"Ubangidanka kamar yaya? Aikin me kake masa, A ina kuka hadu? Yaushe kafara masa Aiki?" Jeje ya juya ya kalli Jalal ya sunkuyar da kai kasa, a fusace Suleiman yace "magana fa nakeyi maka, kabani Amsa kuma in kayimin karya seka gane kuskuren ka" Jeje ya juya ya kalli Jalal yace
"Jalal ina fatan zakamin Afuwa jin abunda ze fito daga bakina, Asalina nidan garin Azare ne, a cikin wani kauye, mahifina ya dakkoni yakawoni Almajiranci lokacin inada kananun shekaru dabasu fi takwas ba, tunda aka kawoni bawanda yakuma zuwa inda nake, balle susan halin danake ciki, sedana shekara goma shahudu sannan naje gida, kodanaje gida mahaifiyata ta rasu, nayi bakin ciki me tarin yawa nadawo kano, Rayuwar Almajiranci Rayuwace me matukar matsi da wahala, ba kula ba Abinci sabulun wanka wanki, balle magani komai kai zakayiwa kanka Rayuwa tayimin Zafi nafara shiga kasuwa domin neman na kaina, na gudu daga makaranta a haka na shiga makarantar boko, a kasuwar nan nasamu aiki a gidan karuwai nake musu aiki, a haka nakoyi shaye2, neman mata tunda kananun shekaruna, Jagaliya da bangar siyasa ba wadda ba'adamawa dani, mun hadu da Alhaji Kabiru a gurin campaign din wani ubangidansa, ninake jagorantar group din jagaliya da 'yan daba, Alhaji Kabiru ya gayyaceni gidansa da zummar yanaso inmasa wani Aiki zena biyana, na yadda na Amince, ya nunamin hoton Jalal yace akansa yakeso inmasa Aiki, nace kamar yaya, yace soyake Jalal yazama mugun dan shaye2 dan Jagaliya kamar ni, nace masa amma tayaya hakan ze faru yacemin inyi duk yadda zanyi zena biyana duk wata dubu Ashirin, idan har burinsa yacika Jalal ya lalace ze bani wasu kudi masu yawa, Na amince na karbi Adress din Jalal nafara zuwa unguwar su, na lura yanada saukin Kai dayawan kyauta, dukda na girmeshi haka na dinga kokari ina shiga jikinsa, ina turamasa Akidar shaye2, dabe amince ba har sabani muka samu, amma daga baya bansan ya akayi ba ya Amince da kansa, Abokinsa Jawwad yayi kokari yaga ya rabamu amma abu yaki, haka nakoya masa zuwa clubs daban2 kasancewar yanada kudi kayan maye se wanda mukeso zamu sha, Nayi kokarin in koyamasa bin mata amma yaki, sam hankalinsa baya kan wannan shidai kawai yayi shaye2 Alhaji Kabiru yacigaba da biyana makudan kudade kafin daga baya ya nunamin sana'ar dayakeyi ta saida miyagun kwayoyi da makamai ta barauniyar Hanya, idan Jarinsa yai kasa senazo nasan yadda nayi na karbo masa kudi masu yawa a gurin Jalal seyaraba yabani kasona, nazama babban Aminin Jalal, Alhaji Kabiru yasa nadinga Jan ra'ayin Jalal akan mutafi Dubai semunfi holewa acan bame samana ido, mussaman shi da mahaifiyarsa take takuramasa aikuwa ya yadda, shikuma Alhaji Kabiru yahada baki da wasu ma'aikata za'asaka kwayoyi a kayan Jalal, yadda semunje dubai za'a kamashi, idan mukaje dubai aka kamashi da wannan kayan hukuncin kisa ne, Amma abun mamaki se a Airport Jalal yace yafasa tafiyar nan, Saboda Jawwad. Ba karamin fushi Alhaji Kabiru yayi dani ba, yana ganin sakacina ne, da wannnan ya wuce se muka shigo da Hanna wata karuwa cikin tafiyar tamu, Saboda tasirin mace ga da namiji, Amma duk yadda taso ta janyo hankalinsa kanta yaki, Idan yayi shaye2nsa yayi bacci A gurin wataran Jawwad ne yake zuwa ya dauke shi, muka hada baki aka shirya masa birthday party, da nufin cewa za'ayi party ne imu imu abokan shaye2nsa, Amma abun mamaki muka ganshi shida yan uwansa dasu Jawwad, muka shirya idan aka bashi kayan maye a gurin zamu faki idon mutane mu daukeshi, za'a kaishi wani gida da aka kama Hayarsa na wasu yan awanni, Zamu kai Jalal can, a gidan Akwai manyan makamai, Akwai yara kanana da aka hayo aka saka a gidan, Alhaji Kabiru ya saye wasu manyan "yan sanda da kudi, cewar za'azo akama Jalal a wannan gidan, da wannan kayan za'ace an kamashi da miyagun kwayoyi, da Makamai sannam yana safarar yara mata, Amma shima se akasa aka Sace Jalal a gurin party muka nemeshi muka rasa, shima Alhaji Kabiru yai fushi dani da kyar ya hakura, Sekuma karon karshe da Alhaji Kabiru yakamani da 'yarsa a gidan Karuwai, da muka dau tsawon lokaci tareda ita, Yallabai wannan shine Abunda ke tsakanina Da Alhaji Kabiru " gaba daya dakin yayi shiru, Jalal cikin Rawar murya da sanyin jiki yace
" Jeje waye Alhaji Kabiru, Menayi masa haka A rayuwa? Laifin menayi masa yazabi ganina a wannan Kazamar Rayuwar?" Jeje yace" Alhaji Kabiru shine mahaifin wannan Abokin naka Faruk, da mahaifinsa ke yawan yimasa kashedi akanka, sannan kuma shine tsohon Saurayin mahaifiyarka data Yaudara, Yasha alwashin daukar fansa"
"Shine ya zabi Ramawa akaina? Ina ina lokacin dahaka tafaru tsakaninsu? Meye Nawa a ciki? Meyasa kowa akaina yakeson daukar fansa? Meyasa? Jeje nikayiwa haka ko? Kashiga Rayuwata ka lalatamin komai, harda kokarin Rabani da Aminina Jawwad na yadda da kai amma aka hada kai da kai ana hadamin wannan miyagun tarkunan, Yanzu badan Allah ya kiyayeni ba.... Kasa karasa maganar yayi, Hawaye yafara fita a idonsa ya mike yanufi hanyar fita da Sauri, bayansa Jalila itama tabi da Sauri, tana kiran Sunansa amma kafin ta cinmmasa tuni ya hau motarsa ya kunna, ya tasheta da gudu yabar Asibitin.
Haka ta dawo dakin data bar Suleiman, suleiman ya kammala tambayoyinsa.
Jeje ya kalli Jalila yace "Kin shammaceni fiye da tunanninki, ban taba zaton karamar yarinya kamarki zata iya aikata wannan abunba, kin kassaramin Rayuwa, kisani Babu wanda ze iya daukar mataki akan Oga KB, saboda za'a sakeshi ki Saurari abunda ze biyo baya idan aka sake shi" wani mugun kallo tayiwa Jeje "Duk wani zalunci da kassara Rayuwa yabiyo bayan wanda kukayiwa Jalal, Azzalumi daga kai har uban gidan naka, Kaike min kallon karamar yarinya, duk abunda nasa gaba sena ga bayansa, zamu gani nagama da babinku har gaban Abada, kuma ka saurara kagani ko ansakeku zalincin dakukayi baze barku ba" Ganin Jalila ta dau zafi sosai yasa suleiman yace "Kwantar da hankalinki, ki share hawayenki wanda zan dankawa case din shima wanine, za'adau matakin daya dace, kaikuma ina gurin kake wannan maganganun ko? Ka kara daure kanka zaka gane bakada wayo" sannan ya kalli Jalila yace "Shi waye wannan din? (JALAL) Jalila tace" Yaya nane"
"Gaskiya an cutar dashi Sosai, and he needs counseling, kusa ido sosai akansa sannan ku kuladashi, ajashi a Jiki a dage da Addu'a har Allah yasa a raba shi da shaye shayen nan"
"Hakane Insha Allah za'ayi kokarin hakan,
" Yawwa yanzu dai muje in ajiyeki a gida ko? "
" A'a ka ajiyeni a hanya dai" Yai murmushi yace to muje.
Jalila ta koma gida cike da farinciki jin
kamshin Nasara tana saka ran tunda aka kama Jeje to ko Jalal be dena shaye2 ba ze rage sosai, tunowa tayi a halin da yabar Asibitin
"ko yana ina yanzu?, Allah yasa yazo gida lafiya" ta shige cikin gida abunta, tana shiga Nana tace "Jalila ina kika tafine?"
"Hmm kedai bari kawai, gidansu Zahra naje, amma ai gani na dawo"
"Kinci sa'a Abba baya nan, shiyasa kika samu sake" Murmushi Jalila tayi tace "Aiko yana nan ma baze ce komai ba"
"kyaji dashi dai, anjima ze dawo yayo waya ya tambayeni kina ina? Nace masa kindan fita"
"Dagaske anjima ze dawo? Bari inzo inshiga kitchen dole in kintsa cikin Abbana, wannan karon ya dade a lagos" Nana tai murmushi "'Yar gidan Abba, dama yafi sonki akanmu" Jalila dariya tayi ta wuce cikin daki, ta shiga da Sallama amma Naja bata amsaba sema wani dogon tsaki data ja, Jalila ko a jikinta bata damu ba, dan ita nasarar data samu ta fiye mata duk wani neman magana da Naja takeyi, Jalila tanemi guri ta ajiye jakarta da hijjabinta, Wayar Jalila ce tafara ringing ta duba taga Hanan ce, Murmushi Jalila tayi ta daga wayar, tace "Hanan wai yaushe zaku zone?"
"ke ba gaisuwa ba tambayar ya nake se yaushe zamuzo, idan munzo mezaki bani?"
"Ba'abunda bazan baki ba, yau ina cikin farinciki, nasamu Nasarar daban taba zaton samunta ba"
"Wannan wace irin Nasarace kekuwa kike ta murna haka?"
"Bazaki gane ba, bakina akwai magana sosai, kedai kawai sekunzo"
"Gaskiya kifara gayamin yanzu dan zaki barni da tunani"
"Gaskiya bazan gayamiki yanzu ba, innafara bazan iya gamamiki ba, kuma zakiso kiji komai, kawai se kinzo dai"
"Amma naso kifara gayamin yau, daddy ya kira Abba, amma yace yana Lagos kifara hada kayanki zebamu ke, tare zamu tafi Bauchi"
"Eh dama yau ze dawo Abban, Wayaga Jalila a Bauchi, zanga gari inci waina inture"
"Ji kwadayayyiya, ke burinki kici waina, to bazakici wainar ba" sukayi dariya gaba daya, Hanan tace "Baby, ina Abun kaunata" dan jimm Jalila tayi sannan tace "kinada lambarsa ai, meya hana ki kirashi"
"Ban niyya ba, ke nakeso ki amsamin"
"Yana lafiya" Jalila tafada a takaice
"Kimikamin sakon soyayya, kigaya masa kullum yana kawwame a cikin wani bigire me girma a zuciyata, I Love Him, Kaunar Jawwad a jinina take, kigaya masa ina nan zuwa sati me zuwa, in ganshi"
"Kan bala'i wane Jawwad din, ke banason karamin karauwanci, kobaki San anmasa mata bane?" NaJa ce take masifa daga gefe jin an ambaci Jawwad, dayake duk wayar da suke tana ji, Hanan tace "Jalila se anjima ki isarmin da sakona gurin abun kaunata, ba ruwana da kowace mace ko mata hudu aka masa Wallahi seya saki daya ya Aureni, sannan kigayawa me maganar nan Hanan tafi karfin tayi karamin Karuwanci se babban Karuwanci me lasisi, sati me zuwa Insha Allah zan shigo kano, zan gwada mata nawa salon karauwancin, ki gaida mutan gidan" Hanan ta kashe wayarta. Naja ta hau bala'i ta inda ta shiga bata nan take fita ba, yayinda Jalila ta samu guri ta zauna ta dinga kyalkyala dariya, tace "Allah ya kaimu my Hanan tazo, za'a sha drama, zanga yadda zata kaya, agama mu fece Bauchi in garin dadi in zamana se ankuma ganina" Hakan yakara bakantawa Naja rai, ta tashi fuuuu tabar dakin, Seda Jalila tagama dariyarta sannan ta mike lokaci2 Jalal yana fado mata a rai. Kitchen ta tashi ta tafi, ta tarar an Aiki Nana, ta shiga tafara Kokarin dora sanwa musamman dataji batun Abba ze dawo, tana tsaka da Aiki Jawwad ya shigo ya sameta
"Sannu kukunmu, kullum cikin adanamana cikinmu kike, weldone baby" ta juyo ta kalleshi tana murmushi
"Allah yatemaki babban Yaya, da girman kujerarka, Nace Yaushe za'a dakkomin Abban, na dade ban ganshi ba fa" takarasa cikin shagwaba, karasowa yayi gabanta yace "Autar Abba saekin rikici anjima kadan zanje dakko shi ai"
"Yawwa naji dadi sosai, Ina dan uwanka ne?"
"daga gurinsa nake, bayajin dadi ya kwanta bacci"
"Meyasameshi haka?"
"Jalal ba a rabashi da damuwa, be gayamin ba, yace yana bukatar hutu ne kawai" dan jinjina kai, har cikin ranta takejin tausayin Jalal, hawayen dataga yanayi dazu a Asibiti ya tsaye mata a rai, basarwa tayi tace "Yaya Su Hanan zasuzo a cikin next week Insha Allah, zamuje Bauchi in Abba ya yadda"
"Bauchi kuma? Zasu daukemin ke?"
"Ai bazan dade ba ai, nima zanga gari sosai"
"Bawani nan nidai bansoba gaskiya, banason kiyi nisa dani" tai murmushi tace "Hanan tace inmiko mata gaisuwa, tace in gaisheka"
"nifa nayiwa Hanan laifi Jalila, da tana kirana mu gaisa amma yanzu ta dena"
"Karka damu Yaya Jawwad, nasan halin kayaya don't mind her"
"Kinsan banason in batawa kowa rai ni"
"Ni zanbada wannan shedar akanka, kai abun sone ga kowa Yaya Jawwad, Irinka basu dayawa ko a cikin mutane shiyasa........
" To maye bita zaizai" gaba daya suka juyo, Maama ce itada Naja a kofar kitchen din, suka karasa shigowa
"Jawwad ban isa in gayamaka magana kaji ba saboda wannan shegiyar yarinyar ko? Sam kaki saurarar Naja kaki kulata, ka tare a gindin wannan 'yar macen, to wallahi baka isaba Jawwad, Akan yarinyar nan idan na juya maka Baya sedai kanemi wata uwar baniba" da Sauri Jalila ta kalli Maama, Naja se kara zigata takeyi, Maama tace
"Eh kalleni da kyau, munafuka Mayya za' a mallakemin da kaman yadda uwarki ta mallake ubanki aka dinga wulakanta ni a lokacin, wallahi baki isaba kinyi kadan, kuma dan uwarka dan ubanka Naja zaka Aura, kekuma kije kinemi mara mutunci mara Asali irinki, ba dana ba dan dangi gaba da baya"
Jawwad yace "Maama dan Allah kiyi hakuri, kidenai gaya mata haka"
"Wato bakason bacin Ranta, gara batamin Rai akanta ko? Nikae gayawa abunda zanyi, ka kiyayi bakina Jawwad" A hankali Jalila ta tako ta rabe gefen Maama zata wuce, Naja ta kamayi mata Gwalo, bata kulata ba ta wuce daki.
Tana zuwa daki tasamu gado ta Haye, ta sunkuyar da kanta se Hawaye wani nabin wani, Jalila ba karamin dagawa Maama kafa take ba amma sam ita bata gani, amma lokaci yana zuwa da zata gane kuskuren abunda take mata, amma tayiwa kanta Alkawarin seta koyawa Naja hankali. Koda Nama ta dawo tayi mamakin ganin Ran Jalila a bace, tabarta da fara'arta amma ta dawo ta tarar da ita rantaa a bace, Nana tace "Jalila nasan wasu lokutan zaman gidan nan baya miki dsdi, mussaman da Naja ta dawo gidan nan, amma kiyi hakuri komai me wuce ne, dukkan tsanani yana tareda sauki"
Murmushi Jalila tayi tace "Ni nace miki ammin wani abunne? Bana jin dadine kawai"
"Amma ai idonki ya nuna kuka kikayi"
"Baki yadda dame ma fada ba kenan"
Nana tace "shikenan Tashi muje, tunda kin kafe, amma idonki ya nuna akwai damuwa, muje mukarasa girkin" Jalila tai kokarin ta danne damuwarta sucigaba da aiki amma abun yaki yuwuwa, ko yaya Nana ta kauce se Jalila zubda Hawaye, ita kanta tasan tana Hakuri da kauda kai akan wasu abubuwan.
Da la'asar sun kammala komai Jalila tayi wanka ta canza kaya, amma duk ranta ba dadi, tasan Jawwad ma yana nan ransa babu dadi, da sunci karoda Naja seta dinga yar mata da miyagun maganganu, ga Maama agurin babu damar ta rama,
"Ai wallahi Maama mungode Allah, danginmu a tsarkake muke, ai karshen masifa a hada maka zuri'a da Arna" Maama tace
"Godewa Allah kam yarinya, dukkanmu musulmi ne, babu shegu babu Arna" Naja tace
"Maama 'ya' yan halak dinma im aka bincika wasunsu shegune, dan Arna da Auren suma bin maza suke"
A fusace Nana tace "Naja waike dabbar dajin inace? Wani irin hauka... Maama ta katseta ta hanyar cewa
"Rufemin baki ko make miki baki, aiba karya tayi ba kudinma babu tabbas kun hada jini da ita"
ficewa Jalila tayi gaba daya daga cikin gidan tafito harabar gidan. Nanna ta yunkura zata bi bayan Jalila Maama tace "wallahi kika bita sena baki mamaki, wuce ki zauna daga nan inta tafi karta dawo, haka Nana ta koma ta zauna"
Koda Jalila tafito harabar gidan, taga Manu driver da abokansa, a harabar gidan suna gyran flowers, ta duba taga bataga motar Jawwad ba, dan haka ta wuce part din Jawwad, ko ganin gabanta batayi, ta samu gefen kujera ta zauna ta toshe bakinta tafara kuka, bata son kowa yaganta balle a rarrasheta ta zauna tana kukanta, tanajin yadda ranta yake mata zafi. Tana tunanin meyakamata tayi ta huce yadda Maama ke wulakanta ta, bata son gayawa Abba halin da'ake ciki, tasan hakan ba karamin matsala ze jawowa Maaman ba, tana bukatar wanda zata gayawa damuwarta koba komai ta rage damuwa, tasan Hanan zigata zatayi tayi rashin mutunci, gashi ita bada kowa ta yadda ba, balle tagayawa wani abunda ke damunta,,
tana cikin tunani tareda kuka taji magana
"Meyasaki kuka haka?" bata san da mutum a dakin ba, dan haka ta juya da sauri da doguwar sumarsa ta ganeshi, sam bataga kowa a dakin ba, shiru tayi tacigaba da kukanta, karasowa yayi gabanta ya zauna ya zuba mata ido, ji tayi duk ya takurata a hankali yace
"Meyasaki kuka haka?"
"dan Allah nika kyaleni, ina ruwanka da kuka na"
"Inada ruwa da kukanki, kamar yadda kike da ruwa da Rayuwata, now talle me what happens?"

Banza tai masa ta dauke kanta, yakuma kallonta yace
"Gayamin mana"
A fusace tace "bazan fada ba, meye hadinka da damuwa ta?"
"Nasan kinajin haushina saboda kuskuren da'aka samu, amma...
" kace kuskure? Ba wannan ne karo na farko daka mareni ba, kace na fiye maka shishshigi, nakuma yi Alkawarin na dena yimaka kaikuma meye naka nayi min shishshigi, dalla matsa kabani guri in wuce"
"zan baki guri ki wuce, amma meyasa kika damu dani haka, kike bani wannan kariyar bansaniba, dukda irin halayena? Kinyi kokarin kareni a lokuta daban2 bansaniba meyasa? Gashi kinsan abubuwa dayawa dani ban saniba, at least kin haska wani bangare a Rayuwata da yakasance me tsananin duhu, nesanta Jeje dani hakika haskene me yawa a rayuwata, bansan ya akayi na yadda da Jeje nafara wannan muguwar rayuwar ba, kawai na tsinci kaina a wani yanayi dani ka dai nasan menakeji, amma meyasa kika temakeni, kike kokarin ganin kin canza akalar Rayuwata?" yai tambayar yana kara tsareta da ido,
itama kallonsa takeyi dan bata san mezatace masa ba, wani uban tsaki taja ta wuce ta gefensa ta fice daga dakin.
A hankali ya koma ya zauna yana tunanin abubuwa da dama, abubuwa dayawa ya dinga tunawa, Jalila tayi Rawar gani a Rayuwarsa, yanzu ya gane abubuwa dayawa da a da sam besan dasu ba.
Itakam guri tasamu tai zamanta taki komawa cikin gidan tanata zancen zuci, karar motar Jawwad ne ya dawo da ita hayyacinta, shida
Abba ne ya dakko shi a Airport, da fara'a Jalila ta tashi ta nufi inda suke, Abba yace "Jalila bakida lafiya ne? Naga kin rame haka" murmushi tayi "Haba Abba duk wannan kibar danayi kayana sunmin kadan fa"
"Anya kuwa in yadda? Idonki kaman kinyi kuka fa"
"Abba nikam meze sani kuka yau zanganka? Bacci nayi kawai, kawo jakan in rike maka" tasa hannu ta karbi jakarsa, Jawwad yana ganin dakiyar Jalila daka ganta kasan tana cikin damuwa, amma ta maze tanata kokarin boye damuwar.
Ba karamin murna sukayi ba dawowar Abban nasu, Jalila tasan koba komai zata samu saukin wani Abun,
bayan sallar magariba suka gabatar masa da Abinci yaci, nan suka sake aka shiga hira da Abba, Maama tanata dan dari2 kar Jalila tagaya masa wani abu, dan ta lura tun dazu Abba yake tambayar Jalila koda matsala amma tace ita ba komai. Sekusan goma na dare suka watse suka tafi dakunansu.
Ilham tagaji da azabtarwar da Jalal yake mata, yakamata sunemi wata mafitar, tsawon shekarun datayi a gidansu Jalal bataga alamar zasu cinma burinsu ba, Jalal mugun baudadden mutum ne, ga tsabar jaraba da masifa, gashi da rashin yadda, kwanan nan ta lura kaman yakara tsanarta batasan metayi masa ba, ta lura yanzu har uwassa ma yakara fita harkarta, ko cikin gidan baya shigowa, mikewa tayi ta tafi palourn mummy, ta tura kofa bako sallama ta shiga ta samu guri ta zauna
Mummy ta kalleta tace "Ke lafiya kika shigomin bako sallama meye haka?"
"Mummy yaushe zaki cikamin alkawari na ne?"
"Wanne kenan?"
"Mummy har yanzu banga alamar Yaya Jalal ze yadda ya Aureni ba, lokaci fa kuremin yake ni macece yakamata zuwa yanzu kiyi wani abu akai, ina sonshi, banajin zan iya Auren wani bashiba, kitemaka Mummy dan Allah kiyi wani abu" Ajiyar zuciya Mummy tayi "Ilham yakikeso inyine? Yaron naan kullum wutar kiyayyata ruruwa take a ransa, kiduba rashin lafiya nayi amma da naje kansa ga yadda ya rikice gana sambatu infita baya son ganina, ya zanyi Ilham? Kaina ya kulle al'amarin Jalal sunfara bani tsoro"
"Kina nufin in hakura dashi kenan?"
"Bahaka nake nufi ba, amma kidan karamin lokaci, nina miki alkawari ai, bakuma zan saba ba"
"Shikenan Mummy seda safe" Ilham ta tashi ta fita ranta a bace, ji take kaman ta shake Mummy, takoma dakinta ta kulle kofa, ta dau waya takira ummanta tagaya mata abunda ke faruwa, tace mata ta kwantar da hankalinta, in tasamu lokaci taje gida, zasu san yadda zasu bullowa lamarin Jalal da Mummy.
Da sassafe Jalila suka shiga kitchen hada Abinci, bayan sun kammala kowa ya hallara a palour don karyawa, bayan an gama breakfast suka shiga hira, anan Maama ta sanarda Abba ai Naja tazomusu hutune, sannan akwai maganar datakaeso zasuyi da Abba amma ba yanzuba, ba karamin faduwar gaba Jalila taji ba dan tasan be wuce zancem Auren Jawwad da Naja ba.
Abba nan yashiga rarraba musu tsaraba kamar yadda ya saba in yayi tafiya, Abba yabada zuma a gwangwani yace akai gidansu Jalal, A ajiyewa daddyn Jalal, ya daga waya ya kira Jawwad yace yana son ganinsa, bayan yagama waya da Jawwad ya kalli Jalila yace
"Baby Babanki yayo waya daga Kaduna (baban Hanan) yace nan da kwana uku zasuzo, yanaso zasuje dake Bauchi yana neman Izinina, nace masa inkin amince ba damuwa amma bana so ki dade a can" Jalila tai murmushi tace "Na yadda Abba, zanje" Nana kam ta hade rai tace "Ni gaskiya ban yadda ba" Abba yace "Jalila nayi mamakin saurin Amincewarki da batun tafiyar nan, iya sanina dake ba kyason barin gida, amma ya'akayi haka, ko akwai wani abu bakyason gayamin ne?"
"Haba dai Abba, ba wani abu ni kawai inason inzaga inje garuruwan dabantaba zuwa ba"
"Eh hakan yana da kyau, amma bazan bari ki dade ba kinga ga komawa makaranta"
Jawwad yai Sallama ya shigo palourn, ya durkusa ya gaida Abba sannan ya gaida Maama, aciki ta amsa masa dan tanajin haushinsa, yakoma gefen Abba ya zauna yace
"Abbana gani, Allah yasa ba laifi nayi ba"
"Aini baka laifi a gurina, da dai wannan ce tafi kowa iya laifi" Abba ya fada yana nuna Nana, dariya sukayi, yayinda Nana ta dan hade fuska da sigar shagwaba tace "Abba niko? Aikam bana wani laifi ni" Abba yace "Anya kuwa a tambayi Jalila?" haka Abba yasake ya dinga wasa da dariya dasu, banda Maama da take ta cika tana batsewa, Naja kam dama tuni tabar gurin, Abba ya kalli Jawwad yace "Babban mutum, daddynka yamin magana yace yasamo maka aiki a NNPC amma kace kai A'a, yace in rarrasheka ka karba, meyasa bakason Aikin"
"Abba ba banaso bane ba, banason tafiyane saboda Jalal, bansan wani hali ze shiga ba, dukda Alhamdilillah ana samun cigaba a daidaituwar lamuransa, amma banason in tafi yacigaba da mummunar Rayuwa tunda......... Ai kafin yakarasa a fusace Maama tace" Jalal din ubanka ne? Kai meyasa bakada tunani ne? Ana nema amaka gata amma kana maganar wani, baka isaba seka karba ka tafi, tunda kagama karatun zaman jiranwa zakayi? Shiru Jawwad yai bece komai ba, a hankali Nana da Jalila suka zame suka bar palourn ya rage saura Maama, Jawwad da Abba, Abba yace "Jawwad tashi kaje zamu karasa maganar" Jawwad ya tashi ya tafi, Abba yace
"Waime yasa mata wasunku bakuda halaccine? Haba Maman yara, Abunda Jawwad yayi, yai dai2 shine halacci irin kaunar da yaron nan yake masa bekamata kice hakaba, ki kyale shi zuwa wani lokaci tukuna mugani, kinsan kowane dan adam baya wuce rabonsa"
"Naji, Amma Jawwad ya kai munzalin da a yanzu yadace ya fuskanci Rayuwarsa, ya nemi Aikinyi sannan ya mallaki iyali"
"Eh gaskiyane, samun Aiki ba wani babban Abu baneba, kuma bacewa yayi bazeyi Aikin daza'a samomasa ba sedai yace abashi lokacine saboda Jalal, Amma kuma aini har yanzu becemin ga wata wadda yakeso ba tukuna, kinsan mutumin nawa da kunya Akwai fulatancin sosai a tareda shi, Allah yasa ko budurwa ma yanada ita" Abba ya karasa zancen cikin murmushi, Maama tace "inma bashida ita se asmomasa, bazan cigaba da zura masa ido se ya tsofe ba Aure ba, dama maganar danakeson yimaka kenan,
ga Naja nan 'yar gidan Yaya mairo da ita nakeso in hadashi, tunda yarinyar itama ba laifi akwai hankali" Abba ya danyi shiru sannan yace
"To banki ta takiba, Amma banason ayi abunda ze zamana an cutar da dayansu, yakamata muji ta bakinsu tukuna"
"Kamarya semunji ta bakinsu, muba iyayensu bane ba dole subi abunda mukeso, hakan ze kara karfin zumuncin dake tsakaninmu"
"To Allah ya tabattar mana da alkhairi, ni bari in wuce daki zan dan kwanta, kar amanta akaiwa Baban Jalal wannan zumar"
"Za'akai" Abba ya wuce daki.
Jalila tanata tunanin yazata bullowa wannan lamarin, dan in aka hada Jawwad Aure da Naja an zalunceshi, gashi tasan Maama bazata taba barin Jawwad ya Aureta ba, nan duniya tasan inta Auri Jawwad tayi sa'ar miji, salihin bawa da baruwansa da hayaniya"da taga tarasa mafita taje ta janyo trolley dinta ta fara shirya kayan dazatayi Amfani dasu dan tafiya bauchi, taji gara ta dan bar garin tayi nisa maybe ta huta da wannan abubuwan daga wannan se wannan.
"Kayan me kike hadawa haka?"
"Kayan da zan tafi dasu Bauchi mana"
"Jalila bana son kitafi, badan hutunmu next week ze kareba da binki zanyi"
"Allah sarki my Nana, nikaina zanyi missing dinki da kiriniyarki"
"Mtseww Allah raka taki gona, inkin tafi karki dawo bakar kaya kawai, daga nan kema kitafi inda uwarki ta tafi"
Nana ta juyo ta kalli Naja a fusace tace
"Wai Naja ke wace irin mahaukaciya ce" da sauri Jalila ta dakatar da ita ta hanyar cewa "Ke Nana wayagaya miki in kare yana Haushi ana kulashi, kyaleta dan Allah, innaje Bauchi me kike so in kawo miki" Naja tace "Ke kin isa kice min Karya, uwarki ce Karya baniba" Jalila tai sauri tace
"Nana naji kaman muryar Maama tana kiranki yi Sauri kije" Jalila ta tura Nana waje ta dawo ta zauna ta kalli Naja tace
"Uwata batada katon baki da zako zakon fika kuma bata haushi kaman uwar wata, ki kiyayi ranar da bomb dina ze tashi dake, Naja har inda Yayarki Sa'adah ke zuwa a zubar mata da ciki nasani, tsohuwar karuwar Alhaji Kabiru ce dayanzu yake can ana shirin gurfanar da shi a kotu ko karya nayi? "
zaro Ido Naja tayi
"Karya kike ubanwa yagaya miki haka? Waye yayiwa Sa'adah sharri "
"Kinga bana son wani borin kunya, ganina kawai kike amma bakisan waceni ba, bana zama da mutum ba tareda nasan wayeshi ba, karkiyi mamakin kema nasan komai akanki Jalila ta wuce tunaninki Naja, kibini a sannu im bahakaba zanmiki tonon sililin da sekin kasa hada ido da mutane, tun ranar dana ji kina waya cikin dare da Saurayi kema na fara bin diddigin ki dan haka ki kiyayeni"
Gaba daya jikin Naja ya sanyi, yayinda gumi ya shiga tsatstsafo mata ta goshi, tunani tafarayi ya akayi Jalila ta san wani abu akansu haka, bakowa yasan wannan abubuwan da Jalila ta fada ba amma ita ya akayi tasani, Jalila ta tashi tabar inda Naja take tacigaba da hada kayanta. Tundaga Ranar Naja takejin tsoron yiwa Jalila rashin mutunci dan ta tsorata da kashedin datayi mata.
Shikam Jalal yakara takure kansa, tun ranar bekuma haduwa da Jalila ba, yana son ya ganta amma baya samun damar hakan, dan ko a waje baya ganinta, Jalal baya son kowa yaje inda yake, baya iya cin Abinci idan ya tuna abunda Jeje da uban gidansa yayi masa saboda laifin da banashiba seyaji duniyar takara yimasa Zafi, ga abunda yaji Da kunnensa Ilham na fada akansa itada mahaifiyarta, Gakuma Jarumatar da Jalila ta gwada saboda shi abun ya dade yana bashi mamaki ya akayi Jalila ta gano Jeje da uban gidansa akansa suke Aiki harta hada wannan gwaramar, yana son jin wasu abubuwan daga gareta, idan yaji duniyar tayi masa zafi, seya sha giya ya bugu sannan yake jin dadi.
Jalila tashirya kayanta tsaf tun dare, ji take kaman za'acireta daga prison zata tafi kwana biyu ta huta da tension din da suke kanta.
Tun safe Jalila tayi wanka, tai waya da Hanan tace mata zasu karaso da wuri.
Jawwad yaje ya takura Jalal yaci Abinci ya dinga yi masa Nasiha akan wannan takura Rayuwarsa da yayi, Jalal yace "Dan uwa, Nayiwa Kanwar ka laifi fa, nikuma tayimin Abunda har in bar duniya bazan manta ba"
Jawwad yasan Jalila yake nufi yace
"Allah yasa ba wani laifin tayi maka ba? Nasan Halin Baby sarai in wani abun tayi maka Allah yabaka hakuri"
Jalal yai murmushi yace "Ba laifi tayimin ba, Amma tayimin abunda banida abun biyanta, inajin kunyarta abubuwan danayi mata abaya" Jalal ya karasa maganar idonsa fal kwalla
"Subhanallah haba Jalal, haba 'yan mazan daddy, hawaye a idonka, kadena damuwa kaji, komai ze wuce banason ganin ka cikin damuwa muje kaci Abinci, Yau Jalilanma zata tafi bauchi"
"Bauchi kuma?"
"Eh Jalal, nima ban soba amma tasamu ta huta, zaman gidanmu sam baya mata dadi, Maama tana takuramata kuma Yaya mairo ce take zigata, banajin dadin abunda suke mata, inta tafi ta huta kwana biyu, tashi muje ka karya"
Jalal be kuma cewa komai ba yabi bayan Jawwad suka fita. Da kyar Jawwad ya takura Jalal yaci Abinci shima kadan yaci yace ya koshi. Jawwad yaita tunanin me Jalila tayiwa Jalal haka har yake cewa baze manta ba?.
She kusan karfe daya na Rana su Hanan suka karaso kano gidansu Jalila, a guje Jalila ta fito daga cikin gida ta rungume Hanan cikin farinciki, Hanan tace "Nayi missing dinki 'yat Baba" suka kuma rungume juna suna murna, Jalila ta kalli Abdallah tace "Babban Yaya sannunku da zuwa ya hanya?"
"Hanya Alhamdilillah, da tuni munzo amma Hanan tasa muka makara"
"Aina sani ita tahana kuyi sammako" Hanan tace "to mukoma kenan?"
"A'a ni bance ba, ina Baban yake?"
Hanan tace "Daddy shida Mummy zasuje su tarar da mu acan, dama zamuyi biki, yarinya har Anko daddy ya dinka mana nida ke"
Jalila tai musu jagora har cikin gida a palour tabasu gurin zama, taje ta sanarda Abba su Hanam sunzo, dukda wulakancin da Maama takewa Jalila, amma ta sakarwa su Hanan fuska ba laifi, Jalila taje tagayawa Nana su Hanan sun karaso. Naja najin haka ta biyo su dan ganin wai wacece Hanan din nan ne tana zuwa palourn tayi turus, se yanzu ta tuna suntaba haduwa a gidan kamarta daya da Jalila, Amma Hanan takara kyau sosai seda Gaban Naja ya fadi, Hanan tanada kyau sosai gata ta iya gayu, Nana ta fito palour suka gaisa dasu Hanan nan aka shiga hira a palourn, Abdallah yace "Nifa banga Jawwad ba da mutumina Jalal" Nana tace bari inje in kiramaka shi, nasan besan kunzo ba tashi tayi ta fice a palourn Maama da kanta ta kawo musu Abinci, Abba ba ruwansa ya zauna suka dinga hira da Abdallah, Jalila ta janye hannuna Hanan zuwa dakinsu, Nana ta dawo itada Jawwad, Jawwad yashigo da fara'a ya zauna kusada Abdallah suka gaisa daga nan sukayita hira.
Naja ta babbake a daki, dan haka Jalila bata samu damar yiwa Hanan hirar datake so ba sukayita hirarsu ta rayuwa, Hanan taji muryar Jawwad a palour tacewa Jalila zanje wanke Hannu"
"baga toilet ba kishiga mana ki wanke"
"Ba wanke Hannu zanba Jawwad nakeson gani"
Naja tace "Ke mekikace meye hadinki da shi dazaki ganshi?"
Ko tsayawa Hanan batayi ba tayi waje, amma kafin takarasa palourn ta tsaya ta daidaita nutsuwarta sannan ta fito palour,
Da sauri Naja ta fito itama, unexpected Jawwad ya daga ido yasauke akan Hanan, takara kyau dressing dinta ma yayi ba karya, gaba daya besan lokacin dayake kallonta ba, tabass Hanan kamarta daya da Jalila a ransa yace "tsarki ya tabatta ga Allah, ba dangin iya bana Baba, amma ya halicci masu kama daya kuma ba twinsa ba, sedai sunada dan banbanci"
Cikin kasaita ta wuce shi a palour ta nufi kitchen.

Hanan takuma dawowa zata wuce
Abdallah yace "Auta bakiga Jawwad din naki bane" dan kallon Jawwad tayi, tayi murmushi tace "Naganshi mana" Naja kamewa tayi a gurin musamman dataga Jawwad yana kallon Hanan, da alama beji dadin yadda Hanan taki kulashi ba.
Abdallah yace "Wallahi Hanan totally dinta se a hankali, duk ta takuramin wai muyi Sauri muzo taganka amma ta ganka ta wani basar" Jawwad yai murmushi yace "Kyaleta Abdallah zamu shirya ne, maybe gajiyar Hanya ne ya hanata yimin magana"
"Bawani gajiya tsabar wulakanci ne kawai" Hanan ta murgudawa Abdallah baki, suna hada ido da Jawwad ta kashe masa ido daya, gaba daya ya rikice, gani yake kaman kowa yaga Abunda Hanan tayi gaba daya yakasa sukuni,
ita kam Hanan ta wuce Naja takoma inda tabar Jalila a daki, ba kunya Naja takuma biyota dakin, Hanan tana shiga tace "Ohh God, Jalila Haidar yakara kyau yakuma zama babban mutum, wayyo dadi kasheni, naga farincikin zuciya ta" Jalila tace "Waye kuma Haidar?"
"So kike indinga kiransa da sunan da kike kiranshi ne, kowa yace Yaya Jawwad nima ince Yaya Jawwad, Haidar dai kaman in sace shi in gudu haaka nakeji, yawwa Queen ranar muna waya dake naji wata namin kashedi akan abunda yake mallakina, wacece dan Allah?"
"Nice nan, kuma wallahi duk maitarki iyayenmu sun tsaida magana, bashida wata mata in baniba, mayun banza dana wofi marasa zuciya" Naja ce taketa fiffika tana fadan maganganu Hanan taja wani dan tsaki tace
"Jalila aina dauka wadda take cewa zata auri Jawwad din mace ce, ashe mata maza ce mata ta rako duniya, ke cewa akayi ya Aureki, nikuma Jawwad yana sona ne" , dan saurin kallonta Jalila tayi, lokaci da dama Jalila tana daukar abunda Hanan take a matsayin wasa, dukda tana ganin tsagwaron gaskiyar abunda Hanan din ke nufi a idonta Jalila na cikin wannan tunanin Hanan tace "zan tabattar da hakan anan kusa ba a nesa ba, ke Queen ina mutuminne tunda nazo ban ganshi ba"
"Wakenan?"
"kinfini sani, Jalal mana" tsaki Jalila tayi tace "Nifa bana son maganar wannan shirmammen"
"Jalal dinne shirmamme?"
"Eh shidin, ke Akwai Labari amma semun je bauchi Lafiya insha Allah"
"To Allah ya kaimu lafiya"
Abdallah yace "Jawwad nikam ina Jalal ne naganka kai kadai?" Jawwad yace
"Yana part dina baya jin dadi"
"Allah sarki, muje inganshi, muyi salla Azahar sannan mu wuce"
Suka tashi suka tafi part din Jawwad, suka tarar da Jalal zaune akan kujera, yana kallon TV amma sam hankalin sa baya kan Tv, shigowarsu yasa ya daga kai, murmushi yayiwa Abdallah, ya mika masa hannu suka gaisa
"Jalal ashe bakaji dadi ba? Sannu gaskiya ka rame, Allah ya sawwake"
"Abdallah aini na warke tuntuni, Jawwad ne da zuzuta abu"
Jawwad yace "Au ni nake zuzuta abu, dadinta kallo daya za'ayi maka asan baka da lafiya" sukayi Salla, suka zauna sukayi ta hira, Jalal ya sake sosai.
Can aka jima Abdallah ya kira Hanan a waya yace su fito yanzu zezo su tafi, Hanan tace masa to, Jalila ta nunawa Hanan akwatinta tace "Hanan kaimin mota, bari in sa kaya" Nana tace
"bari inje ingayawa Abba zaku tafi" Hanan ta ja trolley Jalila ta kai bakin mota, amma motar a rufe, tasan Abdallah suna part din Jawwad kanta tsaye ta tafi part din, tundaga waje take iya jiyo hayaniyarsu, shiga tayi da sallama duk suka amsa mata, ta fadada murmushin fuskarta ta Kalli Jalal tace "Yaya Jalal kwana dayawa, Yakake ya gida amma naga ka rame sosai" shima murmushi yayi mata yace "lafiya kalau Hanan, amma aini hakanake dama can ban rame ba, yagida ya hanya?"
"Alhamdilillah, ina wannan kanwar taka, yama sunanta?"
Abdallah yace "Kai Aku me magana, daga zuwanki kinfara zuba kaman kanya"
Dan hade rai tayi "kace mufito kuma ka kulle mota, ga kayan queen can na fito dasu, kazo ka bude in samata a mota"
"Sedai kizo ki karba kibude, bari mugama hira"
"Gaskiya Abdallah ka dinga jin tsoron Allah muka katse namu hirar kace mu fito kaikuma ka zauna"
Taki kallon inda Jawwad yake, balle yasaka ran zata kulashi, Jawwad ya karbi key din motar a hannun Abdallah yace
"muje in bude miki motar, Abdallah bashida niyyar tashi yanzu"
Dan murmushi tayi ta juya, Abdallah yace "tasamu abunda takeso, dama ba dan Allah tazo nan dinba, sarkin gulma wani inzo in bude mata mota, kawai kice Jawwad yataso gurinsa kikazo, sewani Iyayi kike"
Hanan taji kaman kasa ta bude ta shige, Abdallah mugun dan rainin hankali ne Jalal yace "Ahha kai Abdallah ina ruwankane? Yada shishshigi haka?"
"Auto nayi shiru, tunda ka goyi bayanta"
Suna fitowa Hanan ta nufi hanyar komawa cikin gida, Jawwad ya kira sunan ta, ta tsaya amma bata juyo ba, ya karasa gabanta yana kallon ta amma ta sunkuyar da kai,
"Hanan, menayi mikine? Tunda kikazo kin kula kowa amma ni kin shareni"
"Bakomai"
"Ban yadda ba komai ba, laifin menayi miki?"
"Haidar dan Allah ka kyaleni, banason matsala, kace baka sona, gaa nazo na tarar da wata tana gayamin ita zaka Aura ya zanyi? Ina kokarin in cireka a raina amma nakasa, ganinka din nan ma yana karamin pressure ne, na damu da kai sosai kaikuma ka nuna baka sona, base in hakura ba, mezesa incigaba da shishshige maka?" Abun mamaki hawaye ke kokarin fita a idon Hanan, hakan na nuna maganganun da take fada har cikin ranta, Jawwad yace
"Zannemi wata alfarma daya a gurinki, zakiyi min? "
"Alfarma kuma? Wace iri"
"Sekinyi min Alkawari zakimin Alfarmar"
"Inkuma bazan iya bafa?"
"Bazan tambayi abunda bazaki iyaba ai, abune me sauki"
"To fadi in zan iya" yai murmushi yace
"Sonake inkuma jin sunan dakika kirani dashi please, yanamin dadi"
Dan zumbura baki tayi ta noke kafada, "Niba wani suna"
"Kince fa zakiyi min Alfarma" cikin shagwaba tace
"ni banyi Alkawari ba ai"
"Please, ko inyi kuka ne sannan ki fada"
"Eh to yi kukan in gani tukuna" sukayi dariya a tare, yanayin irin tsokanar Jalila haka Hanan takeyi, amma Hanan bata iya komai ba akan Jalila, Jawwad yace
"Hanan da bakina ban taba cewa bana sonki ba, ban taba soyayya ba, amma nasan ina son Jalila so ba na wasa ba, kinga akwai alaka me girma tsakanin ki da ita, sannan batun Naja da kikeyi Wallahi Hanan yanzu haka ina dauriya ne kawai, Naja zabin Maama ce, tanason in Aure ta ni inason yiwa Maama biyayya amma bana tunanin zan iya Auren Naja,
Hanan nasan kinshiga damuwa saboda ni but am very sorry, banason kowani rai ya shiga damuwa saboda ni, ta mussaman ke ce a gurina" Hanan tai murmushin da seda hakoranta suka fito, ta jingina da motar tace
"Kasan meyake kara burgeni da kai Haidar?"
"A'a sekin fada"
"A dukkanin maganganun ka kana kokarin fadar gaskiyane, sannan kanada tausayi shiyasa nake kara sonka, Amma bari ingaya maka wani abu, alakar dake tsakanina da Jalila bazan so ta baci ba, saboda ina mata so na gaskiya, bazanyi wani abu in cutar da ita ba, Amma maganar gaskiya kanawa Jalila so ne irin na 'yan uwantaka ba soyayya ta Aure ba, haka ma zuciyar Jalila tana maka sone na' yan uwan taka, nasan zakayi mamaki, Jalila bata taba soyayya da wani ba, tanada Samari Amma har yanzu taki yadda zuciyarta akwai wanda takeso saboda taurin kanta, kaima zan baka lokaci zaka gazgata abunda nake nufi"
Gaba daya zuciyar Naja ta gaama tsinkewa, Ganin Hanan taki dawowa yasa ta fito harabar gidan, amma tayi tozali da Hanan da Jawwad se murmushi yake, tunda take da Jawwad maganar minti goma bata hadasu balle yaita wannan murmushin, Nana ma befiye shiga harkarta ba, a da tayi tunanin ko Jalila yake so, wato wannan yarinyar me girman kan bala'i ita yakeso, koma dai duka yake sonsu ne tana tsaye tana kallonsu
Jawwad yafara magana "Hmm Hanan ina kika samo wannan ideology din, yazakice Baby Akwai wanda takeso, kuma munayiwa juna son 'yan uwan taka?"
"Ban fada domin in shiga tsakanin ku ba fa, nawa hasashen ne haka, Ita kanta Jalila bata son wa take so ba, bakowane lokaci take yadda da zuciyarta ba tana karbar abubuwane da lissafin kwakwalwarta"
"Hanan ya akayi duk kika san Jalila haka ne?"
"Haidar a zaman danayi da Jalila motsi tayi nasan abunda take nufi, nasanta fiye da yunwar cikina"
kyar yake kallon Hanan ko kyaftawa bayayi yana juya maganganun ta a ransa, ganin yanata kallonta yasa tace "ya dai kona bata maka raine?"
"Ina so kicigaba da magana ne, komai kikayi kyau yake miki" murmushi tayi tana rufe fusaka,
yace "masha Allah yanzuma bakiga yadda kika kara kyau ba"
Abdallah da Jalal suka fito daga part din Jawwad, ba karamin matching Jawwad da Hanan sukayi ba, suka nufosu Abdallah na shirin sukarasa ya tsokane su, shikuma Jalal Jawwad kawai yakson ya titsiye yau, amma kafin su karasa Naja ta rigasu dan Naja ba karamin kulewa tayi ba, dan haka ta taho kaman wata kura, ta nufo su Jawwad, tana zuwa ta rike kugu tace "ke wace irin matsiyaci ya ce haka? Nace miki Jawwad shine wanda zan Aura na meye zakizo kina wani shige masa, kina wani salon karuwanci meye haka?"
Hanan kaman tayi magana, sekuma ta fasa tace bari inga matakin daze dauka
Aikuwa Jawwad yace "Naja meye hakane wai? Yazaki kirata da karuwa me tayi miki? Wannan wace irin magana ce"
"Eh dole kace wace irin magana ce mana, kasan ni zaka Aura amma kazo kunfi minti Ashirin a nan gurin alhalin niko hirar minti goma bakayi dani"
Jalal yace "wai dan Allah meyake damun wasu matanne, yanzu meye hakan kuma?"
Abdallah yace mata se Addu'a ai, se yanzu Naja ta lura da shi, wancan zuwan ma tare sukazo, ita da Abdallah ze Aureta aida ta hakura da Jawwad
Abdallah yace "kinga baiwar Allah kiyi hakuri dan Allah, Kekuma Auta, Jawwad fa Ustaz ne, kinzo kin wani kanainaye shi tun dazu, kina kashe masa murya kina fari, Ashe ma ankusa Aurar dashi, ai seki hakura" gaba daya sukayi dariya suka maida Naja kaman wata mahaukaciya,
Hanan tayi murmushi cikin kasaita tace "Macen data kai mace, itace idan tace tanason take samu, ba ragowar muna mata ba" shikam Jawwad ba karamin kunya Abdallah yabashi ba
Sannan Hanan tace "gaskiya Abdallah kai dan hana ruwa gudune, Yaya Jalal ka shiga tsakanina da Abdallah, My Haidar karka damu da Abdallah haka yake da wannan takurar"
Jalal yace "Inyee ashe har suna aka canza maka abun masoya kai Jawwad, se anyi magana ya dinga sunkuyar da kai waishi kunya, bayan yagama zuba kalamai shima"
Da sauri Naja ta shige cikin gida, tanata kumfar baki a palour ta tarar da Nana sun fito
Jalila daga part din Abba
"Ni za'ayiwa hauka, ni wannan
yarinya zatayi wa karuwanci, wallahi yau duk bala'in da za'ayi se anyi, shegiyar yarinya a gabana kaman zata hadiye Jawwad kan bala'i, a fusace Nana tace
"Ubanwa ya hana kiyimusu
can sekinzo mana nan, inkina yiwa Jalila tana kyaleki, ita wannan a yanzu intaga dama wallahi zata saka sojoji sumiki dukan mutuwa, dan ko a ina take a a fadin kasar
nan akwai yaran babanta"
Jalila tace "Nana, bari inje waje inga meke faruwa, Nasan halin Hanan sarai, ba kanwar lasa bace, dukan sojoji yafiye maka dukan wannan bakin nata, koba komai yau na huta, Anamin maganin karya me remote"
Aikuwa Jalila takara angizo Naja, "ke dan abu ta kazakazanki, nikike cewa karya?" Ai Jalila bata jira taji metake cewa ba ta fito.
Jawwad duk yarasa ya zeyi dasu Jalal, se tsokanar sa sukeyi shida Abdallah yana sunkuyar da kai, itakuwa Hanan ko a jikinta data fuskanci sun takura masa, se tace
"cwt Haidar don't mind them, kaga Abdallah aiba a magana shima haka yake zuwa ana kashe masa murya, idan ana masa wannan kashe muryar seka sace shi ka gudu be saniba" seda ta danyi murmushi sannan tace "Kaga yaya Jalal Allah kadai yasan shime ake masa, shima nasan yana zagayewa yaje akashe masa muryar dayake takura maka, kaima ka dinga ramawa amma zanso inga budurwar Yaya Jalal inga in an kashe masa muryar shi ya yakeyi, sweet Haidar sena koya maka magana, adena takuramana"
Jalal yai dariya yace "Ni Hanan aibana soyayya, ban santa bama balle inje a yimin wasu kalamai,, in aka fara yimin kalaman zan kiraki kizo kigani, sedai fatan Allah ya hadamu da masoyanmu
na gaski..... Jalila ya hango tana sakkowa daga steps, tayi kyau sosai, amma abunda yabashi mamaki ta rame, "ko bata da lafiya ne? Tayi rama sosai, itama tana daga ido sukayi ido hudu, taji gabanta ya fadi "kaddai ace har yanzu Jalal bashida lafiya, wace irin rama yayi haka?" kallonta yake yadda take tafiya step by step, Hanan kam tuni taga abunda yake faruwa tai murmushi a ranta
Jalila ta karaso tace "Yaya Jawwad ina fatan komai lafiya, naji Naja tanata masifa, Hanan me kikayi mata ne?"
"meko zanmata? Dan kawai ta ganni da Haidar ne"
Abdallah yace "karya takeyi tun dazu ta tsareshi anan tana zuba masa kalamai, tun yana jinkunya naga alamar kalaman sun fara shigarsa, murmushin yake Jalila tayi tace" nikam ki lallaba ku rabu lafiya"
"karma a rabu lafiyan ba abunda ya dameni bane, haidar dina ne agabana"
Abdallah yace "ke Hanan kinfiye zakewa, ance miki anbadashi amma kin nace" Hanan ta lura yadda Jalal ke kallon Jalila, itama Jalila tana satar kallonsa amma bata bari su hada ido, Hanan ta gyar murya tace
"Queen kinga Yayyenki nan biyu sun takuramana, shi Abdallah nasan yadda Siyama ke kasheshi da kalaman soyayya, amma shi Yaya Jalal ban saniba, da nasani da na ramawa Haidar, amma gayamin ko kin san budurwarsa?" hararar Hanan tayi tace "Aiba tare muke yawo ba balle in san budurwarsa, seki tambayeshi ai"
Hanan ta tintsire da dariya dama tana sane tayi hakan?
Jawwad yace "Baby ina Abba ne?"
"Yana cikin gida, yaya Abdallah ku shiga sekuyi sallama da Abban"
"ok bari muje"
Jawwad ya musu rakiya suka nufi cikim gida
Jalila tayi mamaki yadda Jalal yake hira bazakece shine ba, Jalila tafara kokarin saka jakarta a mota
Jalal ya dan kara kurawa Jalila ido, yazo kusada ita ya tsaya, ya danyi kasa da muryarsa yace
"meyake damunki kika rame haka?" bata dago ba tace
"ni ban wani rame ba, dama haka nake"
"hmm, shikenan tunda kince haka, amma yaushe zaki dawo?"
"Ka Aike nine, wai ina ruwanka danine?"
"Aiba abun zafi bane, meye nayin fushin kuma?"
"idan na tafi bazan dawo ba, idan na tafi zan hutawa raina indena ganin masu ba kanta min rai, kaima ka huta dame yi maka shishshigi, kaci karenka babu babbaka, inka gadama kaima ka gina club din shna giya"
"meyasa ba kya mantuwane? Abu baya wucewa a gurinki kenan?" Su Hanan ya gani suna fitowa dan haka yace mata
"zaki iya zuwa ki zauna a wani garin, kibar Jawwad din naki da Nana tsawon lokaci?, idan ina ganin ki inajin kwarin gwiwar dena wani abun, dama zan miki sallama ne dan inaga kafin ki dawo, zan koma Dubai da zama, bazan kara dawowa Nigeria ba, har abada, ina fatan kiyafemin kura kuran danayi miki, Sannan Nagode da kokarinki a kaina, keda Ummi bazan tabawa mantawa daku ba, sannan A shekarun baya, wani zuwa da kikayi, Su daddy sun baki kyaututtuka, ciki hada wani Jan Alqur'ani me red din box, nina baki kyautar wannan Alqur'ani sannan Akwai Ajiya ta a ciki.

Kallonsa Jalila take kaman wata sokuwa, ya daga kai yaga su Jawwad da Abba suna tahowa, yakuma durkusowa yace mata "Allah ya kaiku lafiya"
Hanan tana kallon abunda yake faruwa harsuka karaso inda motar take, Abba yayi musu nasiha tareda fatan suje lafiya, Abdallah ya shiga ya kunna mota, yafito da ita daga cikin gidan, Nana tace "Jalila dan Allah inkin tafi karki dade, zanyi missing dinki sosai"
"Bazan dadeba Nana, nima zanyi missing dinki" suka rungume juna sannan Jalila ta karbi jakarta a hannun Nana.
Hanan tazo bayan Jawwad ta wajen kunnensa tace "I love you Haidar, i wish to see you soon" ta juya ta shiga mota, murmushi kawai Jawwad yayi, Jalila ta bude mota ta shiga amma hankalin ta yana kan Maganganun Jalal.
Jalal yazaga sukayi musabiha da Abdallah yace "Allah ya saukeku lafiya, ya kiyaye hanya"
Suka amsa da Ameen banda Jalila da taketa zancen zuci. Abdallah ya kunna mota yafara ja a hankali Jalila tanata waigawa tana kallon Jalal harsuka bar layin, Hanan ta daki cinyarta tace "To ai seki dena kallon nasa haka"
dan hade rai Jalila tai tace "kamarya indena kallonsa? Wakenan?"
"Jalal mana, aishi kike kallo tukuna ma meya gaya miki ne naga jikinki yayi sanyi?"
"Bansaniba, niba shinake kallo ba"
Hanan tai dariya tace "Queen ba dai taurin kai ba, bakyason gazgata zuciyarki, ga abu a zahiri amma kinata wani basarwa"
"Ke dan Allah ki kyaleni Hanan"
Hanan tace "Na kyaleki"
Abdallah yana jinsu yai murmushi yace "Hanan kokece sirikar tamu ne? Keda Jalal kuke boyewa"
"Tab Allah ya kiyaye, bawani sirika, wadda ze Aura tana gidansu cousin dinsa ce Ilham"
Hanan tace "karya kikeyi, kefa kikace bazaki bari ya Auri Ilham ba"
"to dan ban bari ya auri Ilham ba kuma ni seya Aureni?.
Abunnasu na nema yakoma fada dan haka Abdallah ya shiga yimusu hira aka manta da wannan zancen, Jalila ta rarraba hankalinta me Jalal ya ajiye mata a cikin Al'qur'ani tsawon wannan lokacin bata taba ganiba? Sannan mezesa yace ze bar kasar nan haka taita zancen zuci, Hanan ta fuskanci Jalila nacikin damuwa, Amma taurin kai ya hanata yadda.
Nana taji babu dadi sosai da Jalila ta tafi jinta take kaman marainiya, Naja taje ta samu Maama ta gayamata abunda yafaru, Maama taimata alkawarin tasan matakin dazata dauka, zata kawo dukkan karshen wannan yaran, zatayi wa Abbansu Jawwad magana.
Jalila se kusan takwas na dare suka isa garin bauchi, wani irin katon estate ne, dake dauke da gidaje dayawa a ciki, kuma kusan duk irinsu daya, tundaga farkon estate din suke cin karo da sojoji, da sunzo wucewa Abdallah yake daga musu Hannu, wani gida suka nufa, duk gidajen da Jalila ta gani a estate din wannan gidan yafi shi girma, shima akwai sojoji abakin gate din, bude musu akai Abdallah yashiga sunata daga masa hannu, Abdallah ya tsaya suna gaisawa, suna masa sannu da hanya, daya sojan cikin gurbatacciyar hausar sa yacewa Hanan "Madam ba magana? Ko gajiyar ce?"
Hannaan tace "kai ba'a magana nagaji kam" dubawa yayi yaga Jalila a motar, kafin yayi magana Abdallah yaja motar zuwa makekiyar harabar dake cikin gidan, Abun yabawa Jalila mamaki bayan sojojin dake bakin gate akwai wasu a cikin gidan, Hanan tafara fita sannan Jalila dukda magariba tayi, amma ko ina hasken fitulu ne, Jalila ta bude motar ta sakko, ga mamakin ta gaba daya idan mutanen dake harabar gurin yadawo kansu, harta dan fara tsarguwa, Abdallah ya bude motar yana janyo kayansu.
Abdallah ina kasamo wannan kuma? Ko dama Hanan tanada sister ne? Suka dinga jerowa Abdallah tambayoyi, Hanan ta kalli wani soja tace Phillips ga kaya nan shigo dasu upstairs taja hannun Jalila suka shige cikin gidan. Gidan shiru se kamshin turare da Abinci dake tashi, gidan shiruu wani tangamemen palour suka shiga, tundaga palourn Hanan take kiran "Anty fiddo, kina inane?" wata matashiyar mace ce wadda bazatafi shekaru Ashirin da biyar ba ta fito tana cewa "Hanan wane irin kirane haka, Salla nakeyi ai yau kinzo kowa se san kin iso wannan ba.... Bata karasa maganar ba tayi shiru, ganin Hanan tareda Jalila, matar tace
"Hanan menake gani haka, ina kika samo wannan me matukar kama dake?"
Jalila tai murmushi tace "ina wuni Anty"
Hanan tace "daga zuwanmu kin isheni da tambaya, ina mutan gidanne?"
"suntafi shirye shiryen biki, anjima maybe kiga sun shigo" ta kalli Jalila tace "Sannu da zuwa baiwar Allah, shigo"
Hanan tace "aiba gurinki tazo ba, innancy tana dakinta ne?"
"Hanan ko kara babu, tana daki tana salla" Hanan taja hannun Jalila zuwa wata kofa, dakine me dauke da katuwar katifa da tv da bandaki da komai a ciki, gefe wata dattijuwace sanye da hijjabinta tana salla, daga imda Jalila take tana iya ganin dattijuwar fara ce tas daganinta kasan tana hutawa amma Jalila gani take kaman ta taba ganinta amma ta manta a inane.
Hanan tace "Shugabaa Inna salla ake tayi ne? Jalila ga toilet nasan zakiyi Alwala bari in dawo" Jalila tace to, koda Jalila ta shiga cikin toilet din shima ya hadu, kaman ba na tsohuwa ba, Jalila tai alwala ta fito harta tada salla tsohuwar bata idar ba.
Koda Hanan ta fito se tambayoyi suke mata ina suka samo Jalila, Hanan tace "Anty fiddo kimfiye tambaya wallahi"
Abdallah yace "kusan shekarunsu takwas kenan a tare, yarinyar da daddy yake gaya muku ce yayi ya mekama da Hanan, itace yace zekawow Inna taganta"
Wadda suke cewa Anty fiddo tace "Masha Allah, sekace wadda taimana maganin Hanan ce, kai amma Abdallah bantaba ganin wanda ba yan uwa ba masu kama kaman Hanan da wannan yarinyar ba, bari in kaimata Abinci masha Allah ashe itace 'yar daddy"
Jalila ta idar da salallolinta a lokacin tsohuwar ta kammala nata lazimin, kurii ta zurawa Jalila ido, Jalila ta idar tazo kusada tsohuwar ta zauna tace "inna barka da yamma" kasa amsawa tayi sedai kallon Jalila da takeyi, Anty fiddo ce tashigo tareda su Abdallah, Inna ta daga kai ta kalli Hanan ta kalli Jalila tace "Haba nifa imce, nasan Hanan bata da wannan nutsuwar, amma ko idona neke ganin ba daidai ba, kamar duk Hanan dince?" tsohuwar kana jin yadda take magana kasan bafulatana ce, hausarta bata fita sosai
Anty fiddo tace "daidai idonki ke gani, kinga me kama da
Hanan ko? Ita daddy yake cewa ze kawo miki ki ganta ai"
Inna tariko Hannun Jalila tace "mairo ashe dama kina raye zankuma ganinki, baki ganeniba, hafsatunki cefa? Allah sarki mairo ina kika shiga tsawon lokaci bamganki ba" sosai tsohuwar ta rike Jalila tana kuka, saroro Jalila tayi tana kallon Inna, Hanan tace "kekam Inna wai har yanzu bazaki dena wannan abun ba dan Allah?"
Abdallah yace "Inna idan mairon takice haka zakiganta bata tsufa kamarki ba, wannan fa yarinya ce sosai, bakuwarmuce kamar da takeyi da Hanan dinki yasa Daddy yace ze kawo miki ita ya nemi alfarmar mahaifinta alfarmar mahaifinta ankawomiki ita amma kina kuka"
Goge hawayenta tayi tace "yi hakuri yarinyata, daga zuwanki zanmiki shirme, zauna kusada ni"
Anty fiddo tacewa "Inna bari muje taci Abinci se adawo miki da ita" inna tace "ita ya sunanta ne? Ko itama Hanan din ce" Abdallah yace "sunanta Jalila"
"Kai wannan sunan da wahalar fada, na dauka itama Hanan dince ko mairo" Anty fiddo tace "Jalila taho muje" Jalila ta mike suka fito,
Anty fiddo tace "Kiyi hakuri haka takeyi wani lokacin haka takewa Hanan ma, wani lokacin setayi ta kuka wai Hanan tana abu kaman kanwatta, kumafa mu bamu san kanwartata ba, bawanda yasan inda take wata kilama ta mutu, amma har yanzu inta tuna setaita kuka"
Jalila tace "Allah sarki, kinsan babu abunda yafi dan uwa dadi duk tsufansa duk yarintarsa"
"Hakane kam"
Sun karrama Jalila sosai sukayi dinner sannan Hanan takai Jalila masauki, Jalila tace "Hanan bari inwa Inna seda safe ko?"
Hanan tace "inkikaje bazatayi bacci ba kuka zata cigaba, ki kyaleta seda safe"
"to shikenan, amma Hanan meyasa duk gidan nan naku sojojine, koduk saboda babanane?"
"Aiba daddy ne kadai soja a estate din nan ba, sannan duk wanda kika gani a estate din duk family dinmune, kaso uku bisa biyu na mazan dake estate din naan sojoji ne shiyasa kikaga sojoji ko ina, yanzu gobe in Allah ya kaimu zan kaiki kigansu akwai yan mata kamanmu, amma basu san munzoba, da yanzu an cika part din nan, Inna itace tushen family din nan, duk yarantane da jikoki da yaran jikokinta, sekuma kanin mijinta shima ya rasu amma akwai yaransa shima da jikoki a cikin estate din nan, mijin inna ya rasu shekaru bakwai baya, amma bata tunanin sa kaman kanwar nan tata tanabamu labarin kanwar ta, babban dantane kawai ya san kanwartata, shima bashida wayo sosai lokacin amma haka wataran take birkicewa ta w
uni kuka"
Jalila tai ajiyar zuciya tace "Allah sarki, tunda kika ga haka ba karamin shakuwa ne tsakanin ta da kanwar tata ba" sukayi ta hira sannan suka kwanta bacci, amma Jalila tana tunanin meyasa bata dakko Al'qur'anin nan ta taho dashi ba, tana son sanin me Jalal ya ajiye a ciki, ita tsawon lokacin da qur'ani yayi tareda ita bata tab ganin komai a ciki ba, to me Jalal yake nufi.
Nana duk gidan yamata ba dadi, se yanzu takejin akwai shakuwa sosai tsakanin ta da Jalila, Naja kam haushin kowa takeji musamman Nana, Nana tarasa mema zatayi taji dadi, ta dakko waya ta kira Jalila suka sha hira, bayan sungama waya da Jalila, wajen karfe shadaya Nana ta fara kwalemar dakinsu kaman yadda Jalila takanyi wani lokacin, ta hargitsa komai tana gyarawa, Ilham ce ta shigo dakin babu ko sallama Nana ta daga kai ta kalli Ilham tace "Ilham anya ba batan hanya kikayi ba yaukece a gidanmu haka, yaushe rabonki da gidan nan"
Ilham ta tabe baki tace "ba dole indena zuwa gidan nan ba na fuskaci anamin zagon kasa, dama mummy ce ta aikoni, tace ace tanason ganin Jawwad, naga bayanan, kuma bakowa a palour, kuma naji ance wannan yarinyar bata nan shiyasa nazo nan dakin, badan hakaba bazan shigoba"
Nana tace "nifa bangane mekike nufiba Ilham, wani irin zagon kasa akemiki hakane a gidan nan"?
"Haba Nana karki rainamin hankali mana, kema haushinki nakeji kun hada kai za'akwacemin Jalal"
"wai dawa kike ne haka kimin bayani dalla2, dawana hada kai za'a kwace miki Jalal din?"
"wannan tsinanniyar 'yar uwar taki mana, Kun hade kai zata kwace min miji"
"Wai kina nufin Jalila ce takeson Jalal kokuma yaya"
A fusace Ilham tace
"Nana nifa wannan maganganun nan naki batamin rai suke karayi, ta yaya zakidinga rainamin hankali ne Nana, kina nufin bakisan kulla2 datakeyi na kokarin rabani da Jalal ba, son Jalal takeyi kuma nida ita tace seta rabamu akanme zan kaunaceta"
Naja ce ta shigo dakin ta kalli Ilham tace "to yanzu tsakanin nidake watake rainawa hankali, waini narasa wannan shedaniyar yarinya ya take? Ba'agane gabanta ba'a gane bayanta, kekince tanason yayanki, ni daza'ayiwa baiko da Jawwad yace ita yakeso, katsam sega wata jarabbabbiyar tazo wai itama shi take so, nibana gane kan wannan yarinyar sekace dan wake Allah kadai yasan gabanta"
Nana tace "Allah me iko, Allah gatan bawa, kowa ya kwaso tarkacen tsiyarsa seta jibge akan marainiyar Allah, yanzu ke Ilham keda Jalila tace miki tanason JALAL iya sanina ko shiri basayi dashi, tayay zakizo da wannan maganar kuma yanzu?"
"Nana ke kanki yanzu haushin ki nakje kina rainamin hankali, ninaga abunda baki ganiba, sonshi takeyi kuma wallahi bata isaba"
Naja tace "Ai daga ita har Nanan bakinsu daya, kedai kiyi iyayinki ki kwaci Saurayinki dan wallahi bata isa ta auri Jawwad ba daga ita har wannan kodaddiyar yarinyar, banda zalama ki hada maza kice kina so duk jarabarta ai daya zata Aura"
Ilham tace "Aikuwa ba dai Jalal ba sedai ta Auri Jawwad dan bata isaba"
Nana zuba musu ido tayi, dan tarasa mema zatayi kotace
Naja tace "Ayi mu gani ai tafi dacewa da wanann dan shaye2, ba Jawwad ba kema banda jaraba mezakiyi da mashayi, ki kyalesu taje ta aureshi suta haukan tare"
"ke gyara kalamanki ni dan shaye2 nakeso, kika fadi bakar magana akan Jalal zanmiki ba dadi wallahi"
Abu yanemi yakoma fada tsakanin Naja da Ilham, Har Ilham ta juya zata fita, ta dawo ta nufi gaban drower da Nana ta fito da komai amma banda wani Dan karamin redbox, gaban drower taje tasa hannu ta dakko Al'quranin ta kalli Nana tace "Nana ya akayi wannan Al'quranin yazo gidan nan?"
Nana tace "Na Jalila ne lafiya?"
"Wallahi Nana ke makaryaciya ce, to wannan Al'quranin Jalal ne, kakrsa ce ta fanso masa a saudiyya, yanzu gashi a gurin ta, nace miki suna soyayya amma kin karyatani"
Nana tace "kinga Ilham wannan Al'quranin fa tun wani zuwa datayi akabata shi daga gidanku, kekika kawo kayan amma kina wani zance daban"
Ilham tace "to tunda kince nina kawoshi, to yanzu zan dauka, bekamata Abunda yake na Jalal yaje hannunta ba, kinsan son dayakewa Al'quranin nan kuwa?"
"Ilham karmu yi haka dake, ki bani inta dawo sekuyi da ita"
"Inta dawo kice meshi tazo ta dauka, inta matsu ta biyoni ta karba"
Bayan Jalila tagama waya da Nana, sunyi waya da Jawwad yagaya mata yakira Abdallah yace masa sun sauka lafiya sukayi waya, ta kira Abba ma ta gasheshi, Hanan taja Jalila suka koma gurin Inna,
Suna zuwa takuma rungume Jalila ta shiga yimata hira da labarai irin nasu na tsofaffi, Inna tanada abun dariya sun dade auna hira, zuwa jimawa 'yan mata da samarin gidan suka ding shigowa duk wanda yaga Jalila seyayi mamakin kamaninsu da Hanan kaman yan biyu, Hanan ta dinga zagawa da Jalila cikin estate din nan, suna da karamci kaman dama can sunsan Jalila tasamu kyakyawar karba, kwanan Jalila uku a garin daddyn su Hanan ya iso shida Mummynta, yaji dadin ganin irin karbar da'akayi wa Jalila, wannan karon sam Mummy bata nunawa Jalila tsana ba sema mamakin girman da Jalila tayi take.
Inna tacewa daddy "dan Allah dan nan kacewa baban yarinyar nan yabarmin ita, wallahi kamar mairona haka take, musamman intana dariya ko tafiya"
Daddy yace "haba inna, yazasu barmiki diyarsu, yanzunma sunyi kokari dasuka bari tazo nan" haka yaita lallaba Inna ta hakura.
Dukda kulawar dasuke bawa Jalila hankalin ta yana kan Jalal tanason sanin hali dayake ciki, amma bata san wazata tambaya ba.
Yau daddare Har sunyi shirin kwanciya Hanan tace "Jalila kina fama da damuwa a ranki, kuma nasan akan Jalal ne meyasa kika damu dashi haka, in ance kina sonsa kice karyane?"
"niba damu dashi ba, ni bantaba jin son Jalal a raina ba, ina tausayinsane kawai"
"karya kikeyi Jalila, kina son Jalal"
"Hanan keba wadda zan boyewa wani abubace ba, bantaba jin son Jalal ba"
"Naji bakyason Jalal, amma mekikeji akansa?"
"Ina tausayinsa ne kawai, dakuma kasancewarsa da Abu mafi soyiwa a gurina wato Jawwad, ina tausayinsa ne da son ganin yazama mutumin kirki saboda Jawwad Hanan koke kikaji labarin rayuwar Jalal zaki tausaya masa"
Nana Jalila tagayawa Hanan komai na labarin Jalal, har kokarin da tayi na ganin an kama oga KB da Jeje, dakuma abunda Jalal yagaya mata lokacin dazata taho
Hanan jikinta yayi sanyi matuka sannan takara jinjinawa Jalila da wannan namijin kokari datayi da sa kanta a hatsari a boye ba tareda kowa yasani ba
Hanan tace "gaskiya Jalal ya cancanci a tausaya masa, Amma kina ganin kowane ze iyayiwa Jalal abunda kikayi masa, Amma tsaya kinason sanin me Jalal ya ajiye miki a Alqur'ani"
"tunda muka taho nakeson Sani"
"yakamata musani, kira Nana a waya kiji in Alqur'anin yana nan ta duba mana"
"Ai in banda ke seshi Jalal ba wanda yasan me nayi"
"eh ai bazata gane ba"
Jalila ta amince ta kira Nana, seda suka gama hira da Nana, kafin Jalila ta tambaya Nana tace "Baby
Ilham fa taga Alqur'anin ki wannan Jan, yau inayimana gyaran daki tazo, tace wai na Jalal ne, kakarsa ce tabashi ya akayi yazo gurinki tace inkin dawo kisameta ki karba"
A fusace Jalila tace "What!!!?

Jalila tace "Yasalam, Nana kiname Ilham zata shigo har cikin gidan nan ta daukarmin abu natane? Meya kai hannunta kayanmu harta daukarmin abu"
"Jalila Al'qurani fa ba Novel bane ko littafin hausa da zan kamata da kokawa in karba, gyaran daki nakemana tashigo ta ganshi ta dauka"
"Nana kingama dani dakika bari ta tafi dashi, amma tunda tace idan na dawo na je karba ki gayamata ta saurari dawowarta wa, tasan karona da ita ba dadi, zanzo in karba idan bata bayar dan Allah ba zata bayar dan dole, karma kikuma tada maganar tabaki zan dawo in karba, banda Jahilace me zatayi da Al'qurani metasani aciki? Inma tasani bashida amfani a gurinta ai"
"To nidai Allah yabaki hakuri, ni bayan haka wasu maganganu tazomin dasu dasam ban gane inda ta dosa ba?"
"Kamar yaya?" Jalila ta fada a kagauce
"Nikam Baby meye hadinki da Jalal ne?"
"Wane irin tambaya ne wannan Nana?"
"Jalila inkinga rashin mutuncin da Ilham ta dingayi a dakinmu sekinsha mamaki, tana gayamin wai na hada kaidake zaki kwace mata Jalal, wai taga abunda ban ganiba, Kina son Jalal ne, Naja tazo suka hadu sukayi tayi, ni abun yabani mamaki iya sanina ko shiri bakwayi dashi amma maganganunta sun ban mamaki "
Jalila tayi ajiyar zuciya tace
"Nana kyale ta aikinyi ne bata dashi, kinsan tun asalina yarinyar nan batayi min ba, shiyasa take neman masifa, nime zanyi da wani Jalal, ai Jalal se ita makakkiya itama din ba Auren ta zeyiba, ki manta da ita zan dawo ai daidai nake da ita ai"
Nana tace "Hmm Jalila kenan, inaji kaman kina boyemin wani abune, amma inba rami meyakawo rami? Shikenan dai sekin dawo din, ki gaida min Hanan dan Allah
Nana ta kashe wayarta, Jalila ta kalli Hanan a salube,
"me Nana take nufi?" dan daga mata gira Hanan tayi tace
"Queen kenan, naga kin damu da abunda Ilham tayi, amma keda bakyasonsa meyasa kike son abunda yafito daga hannunsa haka har kikejin babu dadi?"
"Hanan bansan mezan gaya miki ki yadda dani ba wallahi, Hanan Al'qurani abune me girma, sannan inason sanin meye Jalal ya ajiye tsawon lokaci ni banganiba, sannan muddin ina raye Wallahi sena nunawa Ilham iyakar ta"
"to meye na wannan tada jijiyoyin wuya haka easy queen i know you can do it, amma meye next plan dinki akan Jalal, kina ganin tafiyarsa Dubai akwai Alkhairi kuwa?"
"To yatafi uwar Dubai mana, daga nan yatafi bangon duniya idan yanaso? Ke nagama abunda zan iya akansa kowa tasa ta fishsheshi, dama yace ina takuramasa kinga se yaje yayi abunda ya gadama, nima takaina nake, yatafi bayan duniyama yaje ya bude gidan giya in yanaso"
takarasa fadin haka tana kokarin kwanciya
Hanan tace "karya kike tawajena, nasan halinki kaf Jalila yanzu kina jin wani abu ze sameshi zaki kuma tashin hankalinki, kya gama zagaye zagayenki ne"
Banza Jalila tai mata ta ja bargo ta shige, Hanan tai murmushi itama ta kwanta.
Jawwad yaje kiran da Mummy take masa, amma ya lurada wani kallon banza da Ilham take masa bebi takanta ba ya durkusa ya gaida Mummy dake zaune a palour,
Har kasa ya durkusa suka gaisa, Mummy tace "yawwa Jawwad dama nace kazone saboda Jalal, inason ganinsa amma nasan nidashi bazezo kiran danake masa ba, dan Allah Jawwad ka dinga yimasa fada, sati me zuwa daddynsa zezo akwai maganar danake so muyi nida shi da babansa, dan Allah idan daddynsa ya dawo zanmaka magana inaso ka kawomin shi "
Jawwad yace
"insha Allah Mummy zan masa magana, acigaba da hakuri ana masa Addu'a Insha Allah komai ze wuce, Alhamdilillah yanzu yafara rage wasu abubuwan"
"Hakane Allah yasa hakan nima ina masa addu'a"
Yatashi yai sallama yafita, Ilham tayi tsaki tace "Nifa Mummy gani nake wannaan Jawwad din ke kara ziga Jalal yake wani rashin mutuncin yake kara kina"
"Kinga nidai ba wannan ba, kokarina kawai inga abunda na shirya ya tabatta akan auren nan naku, idan kika matsa kika nuna bakyason Jawwad kinsan baze taba aurenkiba ko? Dan haka kishiga hankalinki"
Ilham ta zumbura baki ta tashi tabar palourn.
Zaman bauchi ya karbi Jalila, tayi kalau da ita, kusan koda yaushe tana tareda Anty fiddo kokuma gurin inna, susha hira taci dariya, gashi cousins din Hanan suma 'yan shaftane mazansu da matansu, haka ake zuwa a cika babban palourn gidan aita wasa da dariya, samarin gidan da yawansu suna suna son Jalila amma fafur Hanan tace, ai Jalila tanada miji. akwai wani cousin din Hanan yusuf akayi bikinsa, komai da Jalila akeyi, kaikace 'yar gidance dama can sunsanta, sunajin tsoron yusuf sosai saboda baya wasa ma sosai, anan gurin babban abokin ango ya like yace shi nan duniya Jalila yakeso, Yusuf yaji dadin hakan, dan haka yace "Aitunda daddy yace da Hanan da Jalila duk' ya'yan sane, shima da Jalila da Hanan duk kannensa ne, ya yaba da halin Jalila dantafi Hanan nutsuwa"
Bayan biki yusuf yasamu daddyn Hanan, yagaya masa Abokinsa Ahmad yana rikon 'yar baba
Daddy yai murmushi yace "indai' yar baba ce inta amince sannan kun cika ka'idojinmu ai semu duba inkun cancanta abaku semu baku"
Yusuf yace "daddy kenan indai ana sanmu ai zamucika dukkan sharudanka" daga nan sukayi ta hira daddy agaban Mummy akayi tace "Amma danayi murna, dan Ahmad mutumin kirki ne zataji dadin zama dashi, amma ina tunanin yadda zata zauna da matar Ahmad, kasan 'yar taka bata da hakuri' ya'yannak ban san wadda tafi wata hakuri ba"
Daddy yace "Ai indai tana sonshi lafiya kalau zasu zauna, inmuka koma zanyiwa Abbanta maganar, indai basuyiwa wani Alkawari ba, Zanbawa Ahmad"
Yusuf yaita godiya kaman shi za'a bawa.
Daga Jalila har Hanan basu san me akeyiba Yauma, an taru a palour ana hira da daddare Daddy yake cewa abashi list din sunayen wanda ze samawa aiki, Jalila ba karamin birgeta family din nan suke ba, kansu a hade yake haka aka gama hira aka watse.
Jalila kullum tana tareda Inna, sannan Mummy Hanan duk ta dena mata wannan wulakanci datake mata abaya.
Jalila suna chatting da suleiman yake gaya mata, an tabattar da Alhaji Kabiru yana saida makamai da kwayoyi shida Jeje, ranar litinin za'a kaisu kotu, Jalila ba karamin farinciki tayi ba, taitayi masa godiya. Ta zauna tayi shiru tayi wani tunani, amma bata gayawa Hanan ba tasan damunta zatayi da tsokana dan haka tabar abun a ranta
Da safe Jalila bayan sungama breakfast taje tasamu Mummyn Hanan tace "Mummy dan
Allah kan daddy ya fita inason inganshi"
Mummy tace "to shikenan zan masa magana" Hanan tace "queen me zakicewa daddy ne? Ina fatan bawata matsala?"
"Ba wata matsala inason inganshiine"
"to shikenan"
Mummy taiwa Jalila iso, taje palourn daddy , ta shiga suka gaisa yanata tsokanarta tana murmushi, se bayan sun gaisa tace
"babana gurinka nazo kamin wata Alfarma"
"Ina jinki 'yar Baba fadi komene? Insha Allah in zan iya sena miki shi"
Jalila ta kwashi kusan Awa guda a gurin daddy sannan ta fito, ko Hanan bata gayawa Abunda ta tattauna da daddy ba.
Har yanzu Jalal baya walwala sosai, daddynsa yadawo Nigeria, yakan shiga cikin gida gurin daddynsa, amma babu ruwansa da Mummy balle wata Ilham, Iyakar Jalal dakinsa, sedai wani lokacin yakan fito amma baya nisa sosai, Jawwad ne ke takuramasa yadan fita dashi suzaga gari, Jalal yadena zuwa club amma yana shaye shayensa a dakinsa be denaba.
Hannah duk yadda zatayi taga Jalal abu ya gagara, dan haka ta yankewa kanta shawara ta karshe, ta shirya tsaf ta tafi gidansu Jalal, Jalal na cikin dakinsa a kwance besan me akeba, daddy yana gaggawa ze fita da yamma motar Hanna tai parking a kofar gidan, ta fito daga motar da wata irin shiga da bata kamaci dan musulmi ba, da sauri takaraso gaban daddy tace "barka da yamma"
Yace mata "yawwa barka" ya dauke kansa yana kokarin bude motarsa tace "Amma dan Allah Jalal fa?" seda gaban daddy ya fadi, kaddai ace Jalal yafara neman matane ya dake yace mata "lafiya me Jalal din yayi miki?"
"meyema bemin ba? Amma dan Allah yana cikine gurinsa nazo, inason ganinsa" kaidajin yadda Hannah ke magana kasan babu Alamun tarbiyya a tareda ita daddy yace
"Meye alakarki dashi dakike nemansa, baki bani amsa ba"
"Akwai alaka me girma tsakanina da Jalal, sanin Alakar bata da amfani a gareka, babu abunda sanin Alakar ze kara maka banda bacin rai da tashin hankali, dan haka bekamata ayi tone tone ba, amma ina neman Alfarmar ka dan girman Allah kasaka baki Danka ya Aureni, hakan ne kadai hanyar tsira da mutuncina"
Mummunar faduwar gabace takama daddy, hasashensa yazama gaskiya kenan, yanzu lalacewar ta Jalal harta kai ga fara neman mata Innalillahi wa inna ilaihi raji un juyawa daddy yayi da sauri ya rike kansa ya shige cikin gida yana hada hanya.
Hannah kam murmushi tayi tace "koda banganka ba Jalal, nayi abunda nasan dole ka nemeni, na fuskanci bakajin rarrashi kafiye taurin kai, gara in fito maka a Hannah ta.
Ilham na palour tana harabar gidan tana waya daddy yazo ya wuce rike da kansa, mamakine yakamata, yanzun nan fa yake sauri ze fita to shida waye, sauri tayi ta nufi gate ta leka, amma taga anja mota batagane waye ba.
Gida ta dawo taje tagayawa Mummy, da sauri Mummy ta fito ta nufi part dinsa yana zaune ya dafe kai akan kujera, zama tayi kusada shi tace
"meyasameka hakane? Habibi lafiya kuwa yanzufa kake cikin walwala kafita meke damunka ne?"
Dagowa yayi idonsa jawur yace "Khadija Jalal"
"meyasami Jalal din? Bashida lafiya ne?"
"ba wannan ba, ina kyautata zaton Jalal yafara neman matan banza" dan zaro ido tayi "Kamarya ya'akayi kasan haka? Kodayake ba abun mamaki bane ba, tunda duk wanda yake shan giya koya kwana a club ba abun mamaki bane amma gaskiya bana zaton Jalal yana neman mata amma"
"Enough!!! Baze yuwu ba khadija, iya sanina
ana ba manemin mata bane ba, ban san ya'akayi haka zata faruba, kinga yarinyar datazo gurinsa yanzu kuwa? Kinsan metace min ne? No baze yuwuba dole in dau mataki, Zina bala'i ce, dole inyiwa tufkar hanci"
Ilham dake labe a kofar dakin sedata kusa rusa ihu, da gudu ta tafi dakinta ta rufe kofa tana sintiri, nashiga uku idan Dagaske Jalal yafara neman mata ina na kama, menene makomata? Kan bala'i hakan na nufin lalacewar komai fa? Amma wacece tazo gurin nasa? Ina baze yuwu ba, idan har Jalal yafara neman mata bazamu samu komai ba gaba daya shirinmu ze lalace ne, dole inje inga umma a yau din nan jakarta ta dauka ta zuba kudi tayi waje da sauri tafita ta tari napep ta nufi gidansu.
A sukwane Ilham taje gidansu, ta tarar da mamanta a tsakar gida tana tankade, "Umma akwai matsala ajiye tankaden nan ki tashi"
A sukwane tace "ke lafiya kike wannan rawar jikin?"
"nikam ki ajiye tankaden nan kitaso akwai matsala"
Jan hannun mamanta tayi sukayi daki ta zauna a gefen gado tace "Umma akwai gagarumar matsala, mahaifin Jalal yace yafara neman mata, wai wata yarinya tazo neman Jalal, be fadi me tace masa ba, amma yace yana zargin yafara neman mata, idan haka ta faru mu menene makomarmu?"
"ki kwantar da hankalinki kitashi kikoma tun kafin su gane wani abu, ki bar komai a hannuna gobe da kaina zanje gidan malam, ya bincikamin tsawon shekaru mutumin nan yana mana aiki, bamu taba samun matsala ba dan haka bana tunanin za'a samu wannan matsalar "
" gara dai kije da gaggawa kar asamu matsalar wannan karon, dan ina cikin matukar tashin hankali "
" bakomai ki tashi ki tafi"
Sukayi sallama Ilham ta taho.
Gaba daya hankalin daddy yagama tashi, yarasa nutsuwa gaba daya, yana murna yana ganin Jalal yafara rage wasu abubuwan amma kawai ace wannan mummunan tashin hankali da abun kunya na gabato family dinsu. Ganin duk ya tashi hankalinsa yasa Mummy tasame shi tace
"Hayatee wannan damuwar ba iyace mafita ba, nasha gaya maka abaya Yakamata ayiwa Jalal Aure, Namiji ne me cikakkiyar lafiya dole ya bukaci abokiyar rayuwa, amma wakake tunanin zebawa Jalal Auren 'yarsa a wannan halin nasa, shiyasa nace tunda Ilham ta nuna tana sonshi a haka kima' yar uwassa ce, kayadda a hada Auren nan, shine rufin Asirin mu, kila ma kaga ya dena abunda yake"
Daddy yai ajiyar zuciya yace "bakin Auren Ilham da Jalal nake ba, ina gudun abunda ze biyo baya ne, kinsan halinsa inbayason abu, yace baya son yarinyar nan, tunda yace bayaso ko anyi Auren nan wahala zata sha"
"Haba Hayatee kafison yadakko maka magana atukuna, a wajene yake cewa bayaso, da anyi abun zakaji shiru sun zauna lafiya amma kayi tunani, ina tunanin ayiwa Jalal Aure shine mafita, tunda banajin ma yanada wata wadda yakeso giyarsa ce kawai ta dameshi, inaga yiwa Jalal Aure shine mafita"
"to shikenan zanga abunda Yakamata nayi, Amma hankalina tashi sosai".
Bayan sallar magariba Jawwad yasa Jalal agaba da mita
"Gaskiya Jalal bana son wannan zaman gidan da kakeyi kadena walwala, kadena farinciki kullum a daki, bana son hakan, inaga zan duba mana wani business mufara kadena wannan zaman, dan haka zanyi tunani business zamu fara"
Jalal yai murmushi yace "Dama ina son yimaka magana, Daddy yacemin yasamomaka aiki amma kaki yadda katafi, karka damu dani Jawwad ka karbi aikinka ka tafi senafi kowa murna, Saura kuma muzo musha bikinka da Hanan, ko angon Hanan?"
Ajiyar zuciya Jawwad yayi yace "Jalal nina rasa mekemin dadi ma, Maama ta matsamin akan Auren Naja, kullum yarinyar nan setayi abunda zatajamin fada a gurin Maama, narasa yadda zanyi da ita"
"Kaine bakayi maganinta ba"
"Kamar yaya kenan?"
"Keje kasamu Abba ka gayamasa yanema maka Auren Hanan mana"
"Taya Jalal? Jalila tana sona idan na Auri Hanan ban kyauta ba Jalal"
"kana maganar kana son ta tana sonka amma meye makomarta agurin mahaifiyarka da danginta?"
Jawwad yai ajiyar zuciya yace
"Kasan wani abu makuwa?"
"A'a seka fada"
"Hanan tace min wai soyayyar 'yan uwantaka ce tsakanina da Jalila, Akwai wani a zuciyar Jalila, amma kana ganin hakan ze iya yuwa?"
Jalal ya dan kalli Jawwad yace
"Hmm Maybe, nidai fatana kaje ka karbi aikin nan kawai da daddy yasamo maka in bahakaba nida kaine"
Jawwad yai murmushi yace "Jalal kenan sedai mutafi tare".
Abbaa ya kira Jawwad dakinsa, gashi ga Mummy Jawwad ya shiga ya zauna yana fatan Allah yasa ba wani laifi yayi ba.
Abba yace
"Yayana na kaina, Maamanka tazomin da wani batu, shine nace yakamata ingaya maka kafin in aiwatar"
Jawwad yace
"to Abba na ina jinka"
"Yawwa Jawwad, Maamanka tace tanason hada Aurenka da Kanwarka Naja, kuma nan da sati biyu takeso akai kudin Auren, sannan ka karbi aikin da'aka sama maka, in anyi Auren se ku tafi can tare"
Duk wata jijiya ta jikin Jawwad seda ta dan tsaya na wucin gadi, gaba daya jikinsa yayi shock, cikin dakiya yace
"To Abbana, Allah ya tabattar mana da Abunda yafi Alkhairi gaba daya"
Maama tayi murmushi tace
"in ankai kudin banason asa fiye da wata shida"
Jawwad yace "to Maama Allah ya temakemu"
Abba yace "ina fatan dai ba'a matsa maka ba, inkana da magana ka fito kayi"
Jawwad yace "A'a Abba babu wata damuwa"
"to shikenan Allah yamaka Albarka"
Haka Jawwad yafito daga dakin jiki ba kwari ya tafi dakinsa ya kwanta
Jalal yayi mamaki jin shiru Jawwad bezoba yau, dan haka ya mike domin yaduba Jawwad, daddy ya kirashi a waya yace yana son ganinsa a cikin gida.
Cikin gidan ya nufa, ya nufi palourn daddy amma yana zuwa ya tarar da
Daddy, Mummy, dakuma Ilham turus yayi ya tsaya yana kallonsu daya bayan daya, yasan akwai wata kulalliya
Ina yinku ABDUL JALAL group irin sosai din nan fa
inajin dadin Comments dinku, kuna Comments kana karamin kaimi typing duk bayan kwana biyu, kuna bari ina lalaci posting duk sati

Kara hade rai yayi ya shiga palourn ya zauna becewa kowa komai ba ya zauna, daddy ya kalleshi yace "son ka tashi lafiya"
"Alhamdilillah" daddy yai murmushi yace "Masha Allah, kayi breakfast ne?"
"A'a ina jiran Jawwad ne kuma bezoba"
"bari a hada maka anan kaci" daddy ya kalli Ilham yace "Ilham hadawa yayanki Abinci mana"
Jiki na rawa ta mike ta nufi dining din daddy ta hado masa kayan breakfast ta kawo ta ajiye, shidai be kulata ba ya zauna yafara cin Abincin sa, daddy suka cigaba da hirarsu shidasu Mummy, shidai Jalal bece musu uffan ba, yana kammala cin Abincin sa ya mike ze fita, daddy ya dakatar dashi ta hanyar cewa "Ina kuma zakaje? Zamuyi magana ne ai"
Dawowa yayi ya zauna yana kallon daddy, daddy yace "Jalal kaga zamanka haka baze yuwu ba, tunda ansamu degree daya da kyar, kaga shekarunka sun fara Ja daga kai har Jawwad zuwa yanzu yakamata ace ansama maka abokiyar rayuwa a matsayinka na namiji, amma bantaba jin kacemin ga budurwarka ba, ko akwai wata bansaniba "
Wani irin kallo Jalal yayiwa daddy sannan yace" dan Allah adena wannan zancen, in lokacin Auren yazo za'ayi, amma dan Allah for now a kyaleni"
"A'a Jalal babu batun a kyaleka, banason cigaba da ganinka a haka ba Aure, bakasan Aure shine cikar mutum ba, inma baka da budurwa ne ga Ilham tace taji ta gani tana sonka a haka, meye laifin Ilham? Dan haka nakiraka tunda kaida Ilham duk dayane"
"A zato na a baya munyi wannan Maganar ta wuce? Wannan tamkar maida hannun agogo bayane, nace bana sonta, bana sonta akan me za'a takuramin, kuma ai naga Aure ba wajibi bane, balle ace in banyiba nayi laifi, dan haka a kyaleni bana sonta bazan Aureta ba"
A fusace Mummy tace "Baka isa ba wallahi, da abun kunyar da kake shirin jawomana gara aimaka Aure, kokana so kobakaso Aure se anyi shi"
"Abun kunya na nawa kuma? Koke har yanzu abubuwan da nakeyi basu isheki kunya ba? Nagama magana ba wanda ya isa yamin Auren dole wallahi, duk duniya natasani wannan yarinyar natsani duk wani abu da yashafeta, Aurene bazan Aureta ba"
Ilham ta rushe da kuka tace "Nashiga uku Mummy, menayiwa Yaya Jalal haka?"
Mummy tace "rabu dashi, Aurene babu fashi, tunda yasan yafara biye biyen mata, har karuwai sufara biyoshi gida, rashin mutuncin sa ya wuce yaje ya samesu a can, se yafara kawosu gida, ai dole a dau mataki akansa"
daddyn Jalal yaso ya hana Mummy karasa maganar amma seda ta karasa, Jalal dake shirin fita ya tsaya cak ya juyo
"Niza kiyiwa sharri dan nace bana son wannan shashashar, Nine nakebin mata, kirasa dame zaki alakanta ni se wannan mummunan Aiki, to wallahi da in Auri Ilham gara a dauramin Aure da Akuya, Nagode da sharrin da kika yimin a matsayinki na uwata"
"Ba sharri tayi maka ba Jalal, gaskiyane" juyowa yayi inda daddy ke magana, nan da nan idonsa ya canza ya harzuka matuka yace
"daddy da bakinka? Kaima ka yadda zannemi matan banza? Ka yadda ni Jalal zan kawo karuwa cikin gidan nan? Ka yadda ni Jalal ina neman matan banza, lalacewata bata kai haka ba" daddy yace
"Ya isa Jalal, ba sharri akayi maka ba, ni yarinyar tasamu a waje tace gurinka tazo, ita tacemin Akwai alakar dake tsakaninku wadda bata kamata inji ba, kuma lallai insaka Aureta shine kawai hanyar tsira da mutuncinta da naka, ka gayamin meye hakan inba neman mata kake ba?"
Shiruu Jalal yayi ya marasa meze ce, mamaki gaba daya ya kamashi, a iya tunaninsa babu wadda zatayi masa haka, su Jeje ne kuma zuwa yanzu suna hannu kodai duk shirin Mummy ne haka? Amma a tunanin sa be cancanci daddy yayi masa wannan mummunan zargin ba, ba tareda yayi bincike ba ana alakanta shi da dabi'ar dayafi tsana a rayuwarsa wato zina.
"Shikenan daddy naji na gode, Jalal danka mashayi kuma manemin mata,
Daddy da ina neman matan banza da lalacewar da zanyi tafi haka, da ba tun yanzu ba matan banza sun dade suna zarya a gidan nan, dukda Jawwad yana rufamin asiri a abubuwa da dama bana tunanin ze yadda ya zauna da mazinaci, shikenan nagode amma kusani Wallahi bazan Auri wannaan shedaniyar yarinyar ba"
Mummy tace "dalla rufemin baki, kai har kanada bakin dazakace bakason Ilham? Ba rufamaka asiri zatayi ba, kanada bakin kiranta shedaniya ka.....
"Enough Mummy!!! Karki kara zagina waye silar komai, natsani Ilham natsani me sonta" yakarasa yana Zazzare ido, daddy yace "Jalal ya isheka haka, danme zaka dinga cewa ka tasani yarinya metayi maka haka? Lokaci yayi dayakamata kadinga dagawa mahaifiyarka kafa"
"Daddy kayanke min hukunci bakayi bincike ba, kasan bana maka karya, nidai fatana kayi bincike kadena zargina, daddy kanamin uzuri a abubuwa da dama ban taba zaton haka daga gareka ba, sannan maganar Ilham wani abune daba lallai in gaya maka meyasa nace bana sonta ba, duk ku kwantar da hankalinku Insha Allah a satin nan zanbar muku gidanku, in bar muku kasarma gaba daya ku huta"
Ya juya a mugun fusace yafito daga part din daddy, gaba daya jikin daddy yayi sanyi tausayin Jalal ya kamashi, ya juya ya kalli Ilham yace "Ilham mekika yiwa Jalal ne yake miki haka?"
Ilham cikin kuka tace "daddy ni bansan menayi masa ba, yakemin wannan muguwar kiyayya"
Mummy ta dinga rarrashin Ilham.
Jalal kam tunda yafito yaji wani abu ya tokare masa kirji, dakin Jawwad ya tafi yana zuwa yatarar da Jawwad kwance akan gado ido a rufe, Jawwad yana kwancene zuciyarsa ba dadi yarasa yadda zeyi da matsalar ke damunsa, jin Jalal ya shigo ne yasa Jawwad ya bude ido, ya tashi zaune ya dake ya boye tasa damuwar ya kalli Jalal yace "Lafiya kuwa naganka haka meya farune?"
Kasa magana Jalal yayi, sedai jijiyoyin kansa da suka mimmike idonsa jawur, se huci yakeyi kai dagani kasan akwai damuwa sosai.
Jawwad yace "ka gayamin mana meke faruwa?"
"Jawwad zan nemi visa, dole zan bar Nigeria a satin nan, kuma wallahi na tafi bazasu kara ganina ba"
"meyasa Jalal, meyasa zakace haka?"
"Jawwad nagama yanke hukunci, wannan karon karka cemin komai dan mutuwa ce kawai zata hanani tafiyar nan, zan bar Nigeria idan na tafi wallahi bazan kuma dawowa
ba".
A kwanakin nan sam Jawwad be gayawa Jalal shikuma tasa damuwar ba, sedai kokarin lallaba Jalal dayake yayi hakuri ammma fafur yaki se shirinsa yakeyi, sannan sam yadena shiga gidansu ya kashe wayoyinsa dan karma anemeshi.
Hanan da Jalila suna zaune suna hira da Inna a dakinta, Hanan tanata chatting ta dan dago ta kalli Jalila tace
"queen Haidar baya daga waya lafiya kuwa?" tai maganar a shagwabe
Jalila tace "kunfi kusa ai, nima bamuyi waya ba"
"nifa duk na damu a satin nan sam banji muryarsa "
Inna tace "waye kuma haidar, da kike kula dashi haka"?
"Sirikinki ne, kwanan nan zezo kiganshi kyakyawa dashi in gayamiki yafi mijinki Alhaji kyau, kai kaf family dinku babu me kyansa"
Inna tace "ke tafi can, anya akwai me kyan mijina, ai Imamu mijin Mairona ce kawai na yadda yafi mijina kyau"
Jalila da sauri tace "Imamu kuma, shine mijin kanwartaki?"
"Eh shine shima dan uwanane, dan Autan su Imamu shine baban Hanan"
Jalila tace "Inna to wai ina suke yanzu ita kanwartaki"
Inna ta danyi shiru tace "bari yarinya ta, Mu ukune a gurin babanmu nida mairo da yayanmu magaji, ni na Auri Alhaji dan yayar Innarmune, itakuma mairo ta Auri Imamu, dan kanin babanmu ne, yana son mairo sosai, 'yan fashine suka addabi garinmu, watarana suka shigo suka harbi wasu, sukayi Garkuwa da wasu, akayiwa wasu daga cikin matan fyade aka kora dabbobinmu sannan aka sakawa bukkokinmu wuta, kafin hakan tafaru yayanmu magaji ya saida
wasu daga dabbobin gadonmu nida mairo yarabamana kudin, to lokacin da 'yan fashi suka shigo garin mairo da mijinta basu dawo daga kiwo ba, A wannan harin aka kashe yaya magaji, nida Alhaji da matar Yaya magaji, da yaranta da nawa yaran muka gudu abun be ritsa damu ba, haka muka baro garinmu muka taho nan bauchi, lokacin duniya na kwance akabamu masauki, muka cigaba da rainon yaranmu, bayan wasu shekaru A hankali bayan wasu shekaru muka dinga haduwa da wasu daga cikin
'yan uwanmu, duk inda mukaa hadu sesu sedawo nan gurin mu su zauna, a haka har mukayi wannan yawan, Amma har yanzu danake miki wannan zancen bansan inda mairo da imamu suke ba, ni ko bangansu ba inga zuri'arsu, Hanan tana matukar kama da ita, amma dana ganki senaga kunfi kama da ita, komai naki irin natane, Allah yasa ke irin zuri'arta ce" Inna ta fashe da kuka,
Jalila tace "Allah sarki inna, kiyi hakuri kinji Insha Allah zaki ganta ko 'ya' yanta, amma ni ban san kakannina ba inada kanan shekaru suka rasu, maybe da Yaya Jawwad ne ze iya sanin wani abun amma ni bansan komai akansu ba"
Suna cikin maganar Yusuf yayi sallama ya shigo, su Jalila suka gaiaheshi ya amsa, ya nemi guri ya zauna ya kalli Jalila yace "'yar Baba kije palourn kasa, second floor kinada bako" gaban Jalila ne yai mummunar faduwa da sauri Hanan ta mike zaune tace "Bako kuma?"
"Kece Jalila?" Yusuf ya tambayeta shiru Hanan tayi tan
a tunanin waye wannan kuma, ya biyo takan Yaya Yusuf, jiki a sanyaye Jalila ta mike, Hanan ma mikewa tayi zata biyo Jalila, Yusuf yace
"ke dawo nan ki zauna, koke nace kije?"
Hanan tadawo ta zauna ta zumbura baki, tana nazarin waye kuwa wannan"
Jalila taje daki ta dakko hijjabinta har kasa tasaka, ta tafi a hankali ta tura kofar palourn ta shiga kanta a sunkuye tayi sallama.
"wa'alaikum salam warahmatullah" dan daga kai tayi ta kalleshi ido hudu sukayi tai sauri sunkuyar da kanta
Yace "karaso mana queen" Jalila a ranta too queen kuma iyayi, ta karaso ta zauna a kujerar da take facing dinsa,
"barka da dare"
"yawwa barkanki dai my queen fatan kina lafiya?"
"Am not queen Jalila sunana"
Murmushi yayi yace "to ai duk daya, koba haka Hanan take ce miki ba, kuma aini ya cancanta in fadi wannan sunan koba hakaba?"
Shiru Jalila tayi, "to ya gajiyar biki?"
"Gajiya tabi lafiya Alhamdilillah"
"Masha Allah, ni sunana Ahmad nasan kinganni a bikin Yusuf, kobaki ganni ba nina ganki kuma kinyimin Jalila, nagayawa Yusuf ya nemamin izinin zuwa gurin ki a gurin daddy, daddy yabani damar inzo, sannan yace inmuka cika wasu sharuda sannan kin amince ze bani ke" ya danyi shiru sannan yace "Jalila harga Allah kinyimin inasonki Aurenki nakeson yi tsakanina da Allah, amma bazan miki doleba se abunda kikace"
Shiru Jalila tayi tana wasa da yatsun hannunta
"queen kice wani abu mana" still ahiru tayi
"ko banyi miki bane? Ki gayamin ba komai, bazan miki dole ba"
Girgiza kai tayi alamar A'a yace "to gayamin abunda ke ranki"
Fafur Jalila taki magana yai murmushi yace "dago ki kalleni"
Noke masa kafada tayi kaman yanda yara sukeyi sannan tace "to ni me zance?"
"wow muryar ki da dadi Jalila, gaki shagwababbiya" murmushi ta danyi
Wayartace tafara ringing, ya kalleta yace "daga wayar mana"
Ta daga wayar tasaka a kunne Nanace tace "Baby ya kike dan Allah yaushe zaki dawo"?
"kai Nana wai yaushe zan dawo ba rana sena gama hutawa" Nana tace
"department dinku sukoma tun last week, nai shiru ban fadawa Abba kun koma ba, karyayi miki fada, sannan an kafe exams dinku yau"
"dagaske menasamu?"
"nidai nasamu upper credit, but Baby wallahi you are the most luckiest girl i ever seen in my life, kaf department dinku babu me points dinki, se zancenki ake, wasu sun sanki wasu basu sanki ba, lectures sunata a nuna musu ke"
"Alhamdilillah yanzu ina Yaya Jawwad kwana biyu baya daga waya?"
"Baby da banyi niyyar gayamiki ba, shiyasa naketa damunki ki dawo, Abba ya yadda Naja ta Auri yaya Jawwad, memakon yaya Jawwad yace masa bayasonta amma yayi shiru kinsan halinsa nan da kwana tara za'a kai kudin Auren sa gidansu Naja"
Jalila ta manta da wani Ahmad a gurin a razane tace "What, Nana dagaske kike dan Allah"
"Wallahi Baby dagaske nake, gashi yanata fama da Yaya Jalal shima wai ranar Asabar ze bar kasar nan, da se wani satin ze tafi, amma wani abun akayi masa a gidansu, yace wallahi inya tafi bazasu kuma ganinsa ba, ke yaya Jawwad yana cikin damuwa, gashi kusan kullum se Naja tasa anyi masa fada"
Mikewa Jalila tayi ta dafe goshinta tace "Nana am coming back this week Insha Allah, Idan har Abba yabari akayi Auren nan an rusa Rayuwar Yaya Jawwad gaba daya, kuma ina tausayin Hanan, zan dawo a satin nan Insha Allah, dole afasa Auren nan"
Sukayi sallama da Nana ta mike zata koma cikin gida Ahmad yace "Jalila lafiya kuwa? Naga kin shiga wani yanayi ko akwai damuwa ne?"
"A'a bakomai"
"Bari in kyaleki, nadawo na karbi lambarki zamuyi waya" gyada masa kai tayi ta fice da sauri.
Jalila na zuwa Hanan tafara yimata tambayoyi "Jalila wai waye Yaya Yusuf yace kinyi bako?"
"ke kyaleni dan Allah wani ne nina manta sunansa ma, Hanan satin nan, maybe nan da kwana uku zankoma Kano"
"Jalila meyasa? Saboda Yaya Yusuf?"
"A'a Hanan Akwai matsala ne, dole inkoma"
"Matsalar mene haka? Jalila kar mutan gidan nan su zargi ko wani lefi sukayi miki"
"bahaka baneba Hanan, Ankoma makaranta sannan ina bukatar zuwa gida"
Hanan tace "hmm ko dai saboda Jalal ne? Gayamin wani abune yafaru dashi ne?"
Cikin damuwa Jalila tace "Hanan dagaske Jalal yake in yabar kasar nan baze dawo ba, wai anyi masa wani abu a gidansu, fitarsa kasar waje hatsari ne" Jalila ta boyewa Hanan batun kai kudin Auren Jawwad kar Hanan ta damu.
Hanan taso ta tsokani Jalila amma ganin ta in serious mood yasa ta fasa tace "gaskiya yakamata kikoma bari daddy ya dawo se muyi masa magana"
Yusuf ne yayi knocking kofar dakin nasu sannan ya shigo da sallama ya kalli Jalila yace "Jalila yaya kun gaisa da Captain Ahmad?"
"Eh yaya Mungaisa"
"to bazamuyi miki dole ba, kigaya masa abunda ke ranki, inkinada wanda kikeso kigaya masa tun wuri"
"tana da wanda takeso fa, tana jin nauyin kane bata fada ba"
Yusuf yace "inkika kuma magana sekinyi tsallen kwado sau sittin a gurin nan, dake nake magana?"
Shiru Hanan tayi yacigaba da cewa "Jalila banason mu cutar dake gidan nan ba'ayi wa kowa dole, nayiwa daddy maganar, in ba kyasonsa ki gaya masa kinji"
Jalila ta gyada kai, yace to seda safenku.
Yusuf na fita Hanan tace "ke Jalila captain Ahmad ne dama, to tun wuri kice masa bakya sansa, har sunkai magana gurin daddy Yaya Yusuf baya wasa, wallahi dagaske suke, in Baba ya tambayeki kice be mikiba ba kya sonsa, kinada wanda kike so"
"Haka nace miki bana sonsa? Wanake dashi a yanzu danake so? To ni yayi min"
"karya kikeyi wallahi, Jalal shine kike so, ba wani aranki seshi"

Tsaki Jalila tayi, taje ta dakko trolley tafara zuba kayanta, A daren Jalila taje tasamu dadyn Hanan tace masa zata koma gida jibi saboda sunkoma makaranta, daddy beji dadi ba yacewa Jalila da kansa ze maida ita gida.
'yan gidansu Hanan sunji babu dadi batun tafiyar Jalila, sun mata Alheri sosai, Inna ma taji babu dadi, tace itama wataran zatasa akaita kano gurin Jalila, ranar da Jalila zata koma tun safe tagama shirinta tsaf, karfe goma na safe daddyn Hanan da kansa yasa Jalila a mota ya tafi kai Jalila gida, suna tafe suna hira.
Jawwad yayi duk yadda zeyi ya hana Jalal tafiya amma wannan karon Jalal ya dage, yayi rantsuwa yace seya tafi sannan yaki gayawa Jawwad hakikanin abunda akayi masa a gida, Jawwad ya tafi gidansu Jalal yasamu daddy bayan sun gaisa yace
"daddy me akayiwa Jalal ne yace in yatafi baze sake dawowa ba, bansan me akayi masa ba"
Nan daddy yagayawa Jawwad abunda yafaru. Jawwad yace
"Amma daddy meyasa kake zargin Jalal akan wannan, daddy zan iya rantsuwa da Alqur'ani Jalal baya neman mata, koma wacece sharri take masa daddy"
"Jawwad se daga baya naga
nima ban kyauta masa ba, ka bashi hakuri, yadena fushi da daddyn sa, amma kokana da masaniyar dalilin dayasa Jalal ya tsani Ilham, ko tayi masa wani abun ne?"
Jawwad yayi Jim sannan yace "A'a daddy nima bansaniba, ban san metayi masa ba"
"Anya kuwa Jawwad zan yadda bakasan komai ba?"
"daddy dagaske nake bansan komai ba"
"to shikenan, amma Jawwad dan Allah kahana Jalal tafiyar nan, nasan yana fushi dani, amma karya tafi ya bar daddyn sa"
"Insha Allah daddy zanyi kokarin yin hakan"
Jawwad ya tashi ya fita, tun lokacin da Abba yayiwa Jawwad zancen kai kudin Auren Naja yake rashin lafiya amma be gayawa kowa ba, ga kuma tension din Jalal, yakoma daki ya tarar Jalal yanata hada kaya, ya zura masa ido, yarasa mema zece masa, kansa ne yake sarawa sosai ya kwanta akan doguwar kujera ya lumshe ido, yanata sakawa yana kwancewa.
Nana tasan da dawowar Jalila dan haka tanata murna, tana shirye2 itakuma Naja so take Jalila ta dawo ta kuntata mata rai.
Karfe biyu na rana Su Jalila suka iso kano, Nana ta fito ta taresu ta rungume Jalila suka dinga murna, Abba baya gari, ya tafi da Maama lagos, kwanansu uku da tafiya, dan haka Jalila ta budewa daddy sitting room ya zauna.
Nana ta dauki kayan Jalila ta shiga dasu cikin gida, ta kawowa daddy ruwa da lemo da Abinci.
Duk abun nan, Jawwad besan su Jalila sun dawo ba, Jalila da kanta ta tafi part din Jawwad tana shiga palourn sa ta tarar da Jawwad a kwance akan kujera ya lumshe ido Jalal kuma yasa TV a gaba amma sam ba tv yake kallo ba tunani yakeyi.
Sallama Jalila tayi, sallamar tata ce ta dawo dashi daga dogon tunanin da yakeyi, be taba zaton kafin ya tafi zega Jalila ba, seda suka danyi seconds suna kallon kallo, dauke kanta tayi ta nufi gurin da
Jawwad yake kwance,
"Yaya Jawwad" ta kira sunansa amma be amsaba, hannu takai ta dafa goshinsa yayi zafi sosai da sauri tace "Subhanallah" dan girgiza shi tayi,
A hankali ya bude ido yana kallonta murmushi yayi mata yace "Baby saukar yaushe haka ba Labari?"
Cikin kulawa tace "Yaya Jawwad baka da lafiya ne haka"?
Mikewa yayi zaune yace "kai amma nayi murna da dawowarki, munyi missing girkinki da kiriniyarki"
"Yaya Jawwad keep jokes aside ka rame sosai baka da lafiya, nakira layinka baka dagawa, Hanan ma ta kiraka amma bata shiga, yanzu daddyn Hanan ne ya kawoni, yana son ganinka"
Jawwad yace "Shikenan bari inje"
Jalal ya kalli Jawwad yace "dagaske baka da lafiya? Meyasa baka gayamin ba?"
Jawwad yace "meye Amfanin gaya maka banida lafiya? Kaika gayamin dalilin dayasa zaka bar kasar nan? se dazu daddy ya gayamin abunda yafaru, kuma matakin da kake shirin dauka shine ya dace? Gaba daya hankalina a tashe yake Jalal, ni bakasan a matsalar danake ba, gashi kaikuma da maganar dakazomin, gaba daya hope din iyayenka akaina yake, bakaga magiyar da daddy yakemin akan kar inbari ka tafi ba narasa yadda zanyi ba dole rashin lafiya ta kamani ba, gaba daya narasa meyake min dadi" gaba daya tausayin Jawwad yakama Jalila
Jawwad Ya mike ya fice a dakin ba tareda Jalal yace masa uffan ba, Jalila ma bayan Jawwad tabi.
Ba karamin tausayi Jawwad yabashi ba, shikansa yana tunanin yin rayuwa ba tareda Jawwad ba, amma yana daga cikin dalilansa na son barin kasar nan yanaso Jawwad yasamu kwanciyar hankali, ya karbi Aiki ya hutawa ransa dawainiyar daya dingayi masa tsawon shekaru a ganinsa wannan ce kawai hanyar dazewa Jawwad halaccin abunda yayi masa.
Jawwad yaje gurin daddy, sun dan dade suna magana da Jawwad sannan yayi musu sallama yatafi.
Tunda Jalila ta koma gidan Naja take habaici tana yada magana
"ko anki ko anso, koda dariya koda kuka seta Auri Jawwad, Jawwad ba mijin kafura bane"
Jalila tabawa banza ajiyarta, duk yadda Naja taso ta tsokani Jalila, Jalila taki kulata.
Bayan daddy ya tafi, bayan la'asar Jalila ta tafi dakin Jawwad domin tana son yin magana dashi matuka, dakin ta shiga da sallama amma bakowa a palourn, bedroom dinsa taje tana knocking sannan ta bude dakin, ta hango Jawwad yayi rigingine ya lumshe ido kaman me bacci, sallamar Jalila ce tasashi ya bude ido, mikewa yayi zaune a hankali tareda kakalo murmushi yace "Babyn Ummi, ya gajiyar hanya? Na zata by now kina can kina hutawa"
"ina batun hutawa Yayana ba lafiya, ya jikin naka?"
"lafiyata fa kalau"
"A'a ni ban yadda ba ina zuwa"
Jalila takoma cikin gida ta hadawa Jawwad tea ta kawo masa, ya karba ya shanye yace "Nagode Jalila"
"meye kuma na godiya? Yaya Jawwad magana nakeso muyi da kai"
Gyara zama yayi yabata dukkan Attention dinsa Jalila tace
"Yaya Jawwad meyasa ka amince da Auren Naja?"
Ajiyar zuciya yayi ya danyi shiru sannan yace "Jalila Maama ta takura na rasa yadda zanyi ne"
"Yaya Jawwad, tun tasowarmu bantaba son wani sama da kai ba, amma ganin Hanan tana sonka, kuma Maama bata son Alkarmu tare, banason tayi fushi da kai, bana son ta fadi wani mummunar kalma akanka dazeyi tasiri a rayuwarka, Yaya Jawwad ba dan nadena sonka nakoma gefe na zuba maka ido na barwa Hanan kai ba, ina ganin kona barka Hanan zata maye maka gurbina, Amma meyasa zaka yadda da Auren Naja, Na tabattar Abba besan komai game da Wacece Naja ba, ita kanta Maama akwai abubuwan da bata saniba game dasu Naja" Jalila takarasa maganar idonta taf Hawaye,
"Yaya Jawwad, Hanan zata shiga damuwa sosai, tana maka so bana wasaba shiyasa na yadda da soyayyar da Hanan take maka ne dan samun nutsuwa da daidaituwa tsakaninka da mahaifiyarka, amma meyasa zaka Amince da Auren Naja?"
"Jalila bijirewa Auren Naja ze kuma jawomin wata damuwar ne, Har Yanzu Maama takasa gane Yaya mairo ba kaunarta take ba, ta riga ta zigata idan nace banason Auren nan komai ze iya faruwa, Amma ni kaina bana son Auren nan Jalila, Jalila na hakura da kene kawai saboda nasan idan har na Aureki bazaki samu kwanciyar hankali da nutsuwa ta fannin dangin mahaifiyata ba, Jalila bayan tafiyarki Maama ta kirani akan maganar Auren tace Abba zemun zancen Auren muddin na bijire nace ke nakeso" sekuma yayi shiru yakasa cigaba
"Ina jinka bakomai karasa"
"Jalila Maama cewa tayi muddin na bijirewa maganar Auren Naja nannunawa Abba ke nakeso bata yafemin ba"
Zare ido sosai Jalila tayi, ta danyi shiru sannan ta girgiza kai
"Yaya Jawwad ka kwantar da hankalinka kayita Addu'a komai zezo da sauki Insha Allah, Allah ya ganar da Maama, Amma zaka iya Auren sister na ko Yaya?"
Shiru yayi bece komai ba
"Yaya Jawwad nida Hanan duk dayane, tana sonka sosai Zata kulamin da kai yadda yakamata, Insha Allah zanyi duk kokarin da zanyi amma bana son kacigaba da damuwa"
"To Babyn Abba na dena Insha Allah"
"Yawwa Yaya Jawwad dina, kamanta da wannan batun gaba daya, Mutum managarci kamarka be dace da mace irin Naja ba, kadena damuwa kar ciwo yakama ka"
Gyada mata kai yayi yana murmushi. Jalila ta mike ta fito daga dakin tanajin wasu Hawaye, harga Allah tana kaunar Yayan ta a zuciyarta babu macen dazata so tarasa managarcin mutum kamar Jawwad, harzata fita ta hango abu akan center table, dan haka ta dawo da baya ta tsya tana dubawa.
Jalal yana dakinsa yakuma tattar dukkan wani abu dayake bukata, ya hadesu guri daya sannan ya fito ya tafi cikin gidansu, dakin daddy ya tafi ya tarar dashi yana Aiki akan system dinsa.
Daddy na ganin Jalal ya ture system din yana murmushi
"Welcome my son"
"Thank you dad"
Jalal yasamu guri ya zauna sannan yace "Daddy naga bazan iya tafiya ba tareda nayi maka sallama ba, ina kaunarka fiye da tunani dukda kamin abunda bazan manta ba, amma bazan iya rabuwa da kai ta har Abada ba, daddy duk inda zan kasance a fadin duniya muna tare, Dubai zan tafi zamu dinga haduwa in kaje can, zan dinga zuwa Nigeria saboda wasu mutane, Amma Mummy taje ta riki Ilham a matsayin yar data haifa "
"My son nibana farinciki da wannan tafiyar taka, nafison ka kusada mahaifiyarka, Jalal idan katafi ba idon kowa akanka babu mece maka bari, bam san wace irin Rayuwar zakayi a can ba, Dan Allah Jalal
" Ya isa haka daddy karka rokeni dan Allah
, Mummy bata sona bata kaunata, bata son farinciki na kanta kawai tasani, damuwarta ce kawai damuwa damuwar wani bata ta bace, daddy kasan yadda zuciyata takemin idan nasan cewa uwata na raye amma bana tareda soyayyar ta saboda wani dalili nata, kalli Rayuwar danakeyi saboda son zuciyarta, daddy Jawwad yayi yayi yaga nakoma mutumin kirki amma abu ya gagara, Amma wani dalili da ban taba tunani ba yana kokarin sani in rabu da shaye2, daddy idan har na cigaba da zama a kasar nan Mummy tanamin abunda takemin to bana tunanin bakin ciki ze bari in rabu da shaye2" Hawaye sosai Jalal yake kaman mace
Jalal yakamo hannun daddy ya rike a cikin nasa, Sannan yadanyi murmushi yace "Daddy na kasan wani abu? Inada Ajiya a Nigeria bazan iya barinta gaba daya ba, in kaga nabar Nigeria gaba daya to Ajiyata na dauka, kamin fatan Alkhairi daddy na"
Yana gama maganar ya sumbaci hannun daddy ya sakeshi ya juya ya fice, daddy yarasa abunda yake masa dadi, idan Jalal bayaji ta wani fannin baya ganin laifinsa saboda tabbas rayuwarsa cike take da kalubale daban2.
Jalila takoma daki sukayi waya da Hanan amma batace mata komai akan Batun Auren da za'ayiwa Jawwad ba, sannan tacigaba da kokarinki kwantarwa da Jawwad Hankali tareda bashi karfin gwiwa,
Jalila sam taki kula Naja, ta maida ita kamar wata mahaukaciya, tayi zage zagenta da habaici amma Daga Nana har Jalila sukaki kulata.
Ilham ta shirya takuma zuwa gidansu gurin ummanta, domin din yadda sukayi da malaminsu,
"Ilham malam ya tabattar min Jalal baya neman mata, Sannan aikin da'akayi masa har yanzu yana nan ajikinsa, amma akwai matsala"
Da sauri Ilham tace "matsalar menene kuma?"
"Malam yace aikin da'akayi masa ya rage tasiri akansa, saboda akwai wanda yake ta kokarin rusa komai"
Girgiza kai Ilham tayi tace
"Umma wallahi wannan yarinyar ce da na nunamiki a Asibiti, hatsabibiya ce ta gaske ni Jalal yaciwa mutunci agaban iyayensa yace ya tsaneni ya tsani me sona"
Zare ido Umman tayi "Yatsaneki ya tsani me sonki dan Iskanci, kan bala'i ai wallahi daga shi har khadija basu isaba senaga abunda ya turewa buzu nadi"
"to ai Umma ba wannan bama, akan case din nan na zargin yana neman mata, yace kasar nan ze bari wai inyaso Mummy ta rikeni ni ta haifa bashi ba"
"Yabar kasar nan saboda me? Ke Ilham akwai aikifa baki kirin agabanmu, idan yaron nan ya tafi be Aureki bafa? Ita khadija me tace?"
"me kuwa zata ce ranar kaman ze rufeta da duka"
"tsinanniya ni dama ya daketa ta mutu in yaso yakare rayuwarsa a prison"
"Ahha umma akan me? Ta mutu akaishi prison bamu mallaki dukiyar damuke Hari ba?"
"to ai Ilham tsawon zamanki a gidan nan ba wani kokari da kikeyi, ace duk wannan shekarun ko kallon kirki baya miki sema tsana"
"to Umma yazanyi? Ni tun farko sonayi inyi me gaba daya kowa ya huta, kuma kiris ya rage amma ina shegen taurin kaine da shi kamar dutse ne a kirjinsa ba zuciya ba"
Umma ta numfasa tace "Munyi maganar da maman Yaseera, tacemin akwai wani malaminta a can Nijar, munyi da ita zanje ta rakani shima mu jarraba irin nasa Aikin mugani"
"to Amma Umma tayaya? Kasar fa ze bari"
"Dan ubanki kije kiyi duk yadda zakiyi, ki lallabashi in ta kama hada kuka akan bakya so ya tafi, ni nama rasa dalilin dayasa ya tsaneki haka wallahi, keba muniba to kodai yasan abunda mukeyine?"
"Haba dai yaza'ayi yasani? Ni dai Umma dan Allah ki kai Sunan yarinyar nan kawai intakama a kasheta, dan wallahi yanzu ba zargi nake ba, na tabattar ita yakeso"
"tayaya kika sani?"
"Umma ninake ganin abunda nake gani, wallahi Umma idan kinga Jalal ya tabani to bisa kuskure ne, koda wasa baya bari ya tabani, bama ni kadaiba kinsan halinsa bayason mata su rabe shi, amma ganin idona naga ya rungumeta, itakuma makirar tsinanniya tayi luf a kirjinsa, Allah ka dai yasan abunda sukeyi wallahi na tsaneta kamar mutuwata, kuma bakiga yadda baban Jalal din yake mutunta ba, keba shi kadai ba har Mummy bakiga yadda take mata ba"
Jinjina kai Umma ta shiga yi sannan tace
"kyaleni da ita, zata gane kuskurenta, nasan yadda zan bullowa lamarin zata gane bata da wayo, kafin inje gurin malamin, zan gayamiki yadda zakiyi kowa se ya tsaneta"
Haka sukayi ta hirarsu su saka wannan su kwance wancan.
Jalila kullum dare setayi salla takaiwa Allah kukanta haka take raba dare, gata gwana gurin yawan tilawar Alqur'ani, shiyasa Jalila ta yadda da duk wani abu da take aikatawa a rayuwarta take Nasara tasan dogaro ga Allah, riko da ibada
da nacewa Alqur'ani shine matakin dukkan wata Nasara a rayuwarta, duk abunda ta tinkara setaga bayansa, ta taba duk wanda takeso komai matsayinsa amma babu abunda ze faru da ita, ta yadda da dukkan abunda ta roki Allah intaga bata samu ba to lokaci ne beyiba, ta yadda wannan shine matakin Nasararta a rayuwa wadda Umminta da akewa kallon tubabbiyace ta dorata a wannan tafarkin.
Tunda Jalal yace zeyi tafiyar Nan Mummy hankalinta yakasa kwanciya, gashi tasan yadda Jalal yakejin haushin nan nata baze saurareta ba, Amma yazama dole Jalal ya Auri Ilham dan cikawa Saudat Alkawarin ta wannan ne kawai abunda zatayi ta wanke laifin ta a gurin Saudat.
Mummy tayiwa daddyn Jalal magana akan yayi wani abu ya hana Tilon danta tafiya ya yabarta amma amsar daya bata ta mata ciwo
"da lokacin danake miki maganar ki hakura da tafiya karatu kikula da tilon danki da kinji magana ta da koba duka ba ko yaya da Jalal yaji maganarki, ko kin manta watansa bakwai kika dena bashi Nono, a wata bakwanma se lokacin da kika gadama, niba abunda zan iya ki kyaleni"
Ba karamin ciwo maganar daddy tayi mata ba amma ba yadda ta iya.
Ilham ta shirya taje dakin Jalal don jarraba ganin ko ze saurareta amma kusan ya kwashe komai nasa dake dakin nan se abunda ba'a rasa ba, tasan yana gidansu Jawwad dan tunda abun nan ya faru yakoma can dan haka ta bishi can gidan.
Jalila ta kaiwa Jawwad Abinci amma baya nan, se Jalal a palour, bata kulashi ba ta shiga tana gyrawa Jawwad bedroom. Tagama ta fito palour yana zaune inda Tabarshi yana daddana waya, ta fito tazo ta zauna a teburin dake gabansa, tana fuskantar sa, dagowa yayi ya kalleta, kallon dayake mata dukta tsargu, basarwa tayi tace
"Abokin Yaya wai dagaske tafiya zakayi?" A ranshi yace lallai yarinyar nan sekace bata san sunansa ba, nikam nace ai kaima haka kake cemata kanwar Jawwad
Sauke idonsa yayi sannan yace "Kafin kiyi tafiya ai nagaya miki ko?"
"Aini ban zaci dagaske kake ba" dagowa yayi yana kallon ta karo na biyu yace "na taba yimiki karyane? Ko Ba kya son in tafine?"
"to inma ka zauna mekake karamin inka tafi hutunane ai, dan ba karamin wahala nake sha saboda kai ba, da inka tafi na huta banga abunda kayiba balle inji haushin ka, amma ni Su Mummy nake dubawa da Yaya Jawwad"
Ilham ce ta shigo dakin da Sallama Amma abunda ta gani zata iya kiranshi da mummunan gani, Amma ta dake tunda sulhu take nema, gaba daya suka daga kai suna kallon Ilham, tattara nutsuwarta ta boye damuwar ta ta tako a hankali tazo gaban Jalal ta tsuguna tace "Yaya gurinka nazo"
Bece mata uffan ba itama Jalila bata tashi daga gabansa ba, Ilham tace "Yaya Jalal san girman Allah dukda kace baka sona, dan Allah karkayi tafiyar nan, bana son ka tafi, Mummy ta shiga damuwa sosai bata iya cin Abinci se kuka takeyi dan Allah kayi hakuri nikaina zan shiga damuwa sosai, Jalal so fa ba karyane ba ni ganin gilmawarka a cikin gidanma ya isheni farinciki amma bansan dalilin dayasa kake kina hakaba "
Wani kululun bakinciki ya tokarewa Jalal rai a fusace yace " dalla malama ki tashi kibani guri, ai bakinku daya Mummy karkinemi ki rainawa kanki hankali, bana sonki bana kaunarki kifita daga rayuwata tun kafin inyi miki Illa, babu wanda ya isa ya hanani tafiya ba kukan Jini ba ko Hawayen karfe zatayi ba ruwana, ta manta sanda nake mata magiya take tafiya tana barina, lokacin danake matukar bukatar ta, kinga dalla bacemin daga nan ko in ballaki" yakarasa yana zazzare ido gaba daya jikinsa bari yake
"wai dan Allah wace irin zuciya ce da kai, baka yafiya baka mantuwa, koma metayi maka ai ita takawowaka duniya, tana sonka shiyasa bata so ka tafi, Yaya Jawwad ya dena zaman gidan nan saboda bayason ya dinga tuna zakayi tafiyarka ka barshi, kalli yadda Ilham take kan gwiwoyinta tana kuka amma kai ko a jikinka meye hakane?"
Kafe Jalila yayi da idanuwansa da ita kanta wani lokacin suke bata tsoro, gashi yakara hade rai sosai.
Wani bakinciki yakara tokare kirjin Ilham kamar zuciyarta ta fito waje.
A hankali yafara motsa baki yace
"Wallahi idan har banyi tafiyar nan ba to bana raye, ba ruwana da halin da wani ze shiga saboda babu wanda ya damu da halin da nake ciki" yafada yana kallon kwayar idon Jalila
Kawai sukaga Jalila tana dariya, wadda ke matukar kara mata kyau tace
"to shikenan Ai seka tafi in gani" ta mike tsaye takuma kallon sa ta kwashe da dariya seka dawo, karka fasa tafiya naga ta inda zaka tafi ai, kekuma Ilham na dawo koki dawo da abunda kika dauka kokuma inzo da kaina"
Kawai ta juya ta fice ta barsu a zaune suna mamakin maganar ta.

Mikewa Jalal yayi ze fice yabar dakin Amma Ilham ta mike ta sha gabansa
"Haba Jalal yanzu bazakaji magiyar
danake maka ba, dan Allah Jalal kayi hakuri, karkayi tafiyar nan, zan shiga mugun yanayi dan Allah Jalal, wallahi ina sonka, tunda kuruciya ta har kawo I yanzun"
"Ke waini sa'an wasankine? Wallahi koki matsa ko in tattaka ki"
Ya tureta gefe ya fice Abunsa, Abun duniya duk ya dami Ilham, Jawwad ne kadai ke iya sarrafa zuciyar Jalal wani lokacin, yanada matukar kafiya da taurin kai, gaba daya tunanin ta ya kwace.
Jalila takoma cikin gida ta tattara abubuwan dazata bukata dan gobe in Allah ya kaimu zata koma makaranta,
Karamar wayartace ta cika dakin da ringing, Jalila taga bakuwar lamba ta share tacigaba da Aikinta, amma still aka cigaba da kira har kusan karo uku, seda ta danyi tsaki sannan taja wayar tasa a kunnenta
Ajiyar zuciya akayi sannan akace "Masha Allah, kin karyamin record bana kiran mutum sama da sau biyu, komai tsananin bukata ta kuwa, Amma ta dalilin son danake miki har sau hudu ina kiranki"
Sarai ta ganeshi amma ta maze tace "ko zan iya sanin da wa nake magana"
"Ohh am sorry dear, bankoyi miki sallama ba, balle mugaisai nafara miki surutu, Ahmad ne"
"Ok Allah sarki yakake ya gida ya iyali"?
"Alhamdilillah queen, kin tafi bako sallama, ban san zaki koma kano ba ai"
"Aikam abune na gaggawa ya tasomin, in ban manta ba ranar agabanka aka kirani"
"Hakane fatan kowa da komai lafiya"
"lafiya kalau, ya na baroku?"
"komai lafiya amma kintafi kin barni da kewarki, duk lokacin danake wani abu kona rufe idona ke nake gani Jalila, kitemaki zuciyar maraya" ya karasa maganar cikin sigar magiya
"Kai karka bada maza mana, yanzu idan abokan Aikinka sukaji wannan aise suyi Maka dariya, babban soja kaman kai kana haka akan mace, macenma wata 'yar yarinya"
Murmushi yayi yace
"Jalila ai babu wani batun namiji ko soja in ana maganar fage irin na soyayya, ba ruwansa da matsayinka, girmanka ko mukaminka, ba ruwansa da na birni kona kauye, dan haka kidena wani batun maza"
"hmm Wannan bayani haka yakamata ka bude makaranta ka dinga bada darasi"
Murmushi yakumayi yace "Tunda haka kikeso ai se ayi, kece director mukuma dalibanki"
"Tab aini bansan komai a wannan harkar ba"
"Ahh haba dai?"
"dagaske nake fa"
"Aikam zan koyardake yadda yakamata"
"to shikenan seda safe, gobe in Allah ya kaimu zanje school"
"hakane hakan yayi kyau, Allah yabamu alkhairi, zamu hade a dreams zanbiyoki har kano kan shinfidarki"
Murmushi Jalila tayi "Allah yabamu Alkhairi"
Ta katse wayar ta danyi murmushi, can ta hango Nana ta shige bargo ga uban zafi se wani kashe murya take ba'ajin abunda take cewa, Jalila ta mike ta yaye bargon, Nana ta hada gumi amma ko zafin bataji saboda tana soyewa da Mahmud, Jalila tace "Allah ya shiryaki".
Ilham ta dade tana Nazarin me Jalila take nufi da Jalal baze tafi ba, danta fara karaya da lamarin Jalila yarinyar sekace Aljana idan tayi niyyar abu setayi shi.
Jawwad sam yaki kula Jalal gashi gobe in Allah ya kaimu karfe biyu na Rana ze tafi, yanzuma da Jawwad yadawo daga sallar isha'i daki yayi tafiyarsa ya kwanta, Jalal yabishi dakin ya zauna kusa dashi yace "Haba nawan yanzu fushi kake dani haka?"
Mikewa zaune Jawwad yayi yace
"Jalal dan Allah ka kyaleni, kace zaka tafi gaka nan ga hanya seka dawo"
"Jawwad nima inajin abunda kakeji a ranka, A tunanin ka rabuwa da kai abune me sauki a gurina, shekaru Ashirin da bakwai muna tare idan ban manta lissafin ba, Jawwad tafiyata shine samun saukinka, kaima ja maida kai karasa gina rayuwarka, bazan iya barin Nigeria gaba dayaba saboda ku biyu daddy zamu dinga haduwa a can dubai dashi"
"Jalal wannan ba uzuri bane ba, ni na gaba gayamaka na gaza da kai menakeyimaka na wahala, Allah ne ya hada jinina da kai bani da dan uwa Namiji kaidin nan dai tare muke faduwa mu tashi tsawon wannan lokacin, sannan lokaci daya kace Zaka barni tayaya zanyi farinciki Jalal"
"Am sorry Jawwad nasan babu dadi, kuma kana tunanin Wace irin Rayuwar zanyi a inda zanje, Jawwad Ina kokarin dena shaye2, A sanadinka a tsatsonka nasamu me haskamin bakar hanyar danakebi, dama lokaci dayawa kadaici da bacin rai dakuma miyagun abokai kesani kara kaimi gurin shaye2, Amma yanzu an janye miyagun abokai daga jikina, Jawwad idan na tafi inason in koma makaranta "
Sa sauri Jawwad ya kalleshi yace" dagaske kake? Da kanka kake fadin zaka koma Makaranta? "
" Kwarai kuwa zankoma Insha Allah "
Rungumeshi Jawwad yayi yana cewa" naji dadi dan uwana amma naso ace kana nan kusa dani, Amma dukda haka ni zan dinga biyoka Dubai din"
Kasan zuciyar Jalal ba wata makaranta kawai dan hankalin Jawwad ya kwanta ne
"kobakazo bama nizan dinga zuwa akai2"
Haka suka cigaba da hira.
Da wuri Yau Jalila ta shirya manu driver ya kaisu makaranta, 'yan ajinsu Jalila sunyi murnar dawowarta nan aka dinga nunawa wanda basu santa bama, hatta malaman dasuke tsangwamarta suke ganin bata iya komai ba tabasu mamaki kwarai dagaske, saboda ba'a mata tambaya ta amsa a Aji, se lokacin data ga dama take zuwa lectures, wataran ma bata Attending, bata handout sedai in malami zeyi lectures ta dakko jotter, idan malami yayi ba dai2 ba bazatayi shiruba setayi magana, wannan bakin nata kesawa a koreta daga Aji, Akwai malamin da har test ya hanata yi, Amma a haka babu wanda yake da points dinta a kaf department din nan, hakika wasu mutanen 'yan baiwa ne, shiyasa har Abada karka wulakanta mutane dan kowa baka san irin baiwar da Allah yayi masa ba. Ba iya dalibai ba hatta malamai sunyu mamakin Jalila ce takeda wannan kwazon.
Amma ita Jalila abunda yafi daukar hankalinta be wuce yadda har yanzu ake surutu akan abunda yafaru da Saleema da mahaifinta, Saleema ta warke amma bata iya shiga cikin mutane dan gaba daya ta dena zuwa makarantar, Sameera kam da farko ta tausayawa kawarta abunda yasameta Amma daga baya tunda aka sakesu daga police station tacigaba da abunda takeyi.
Jalila a ranta ta dinga jin anya kuwa ta kyauta abunda tayi, yanzu tayiwa Saleema dalilin dena zuwa makaranta, ta kunyata ta a idon duniya itada mahaifinta, Amma data tuna abunda Alhaji Kabir ya aikatawa Jalal, dakuma yadda ya dinga takuramata se yayi lalata da ita, da yadda ita kanta saleema suka addabi makarantar se taji hakan shi ya dace dasu.
Tun safe Jawwad ya bar gida sukayi sallama da Jalal yabar gidan.
Wajen sha biyu na rana Jalal yagama shirinsa tsaf, ya tsaya ya duba passport dinsa don yasa a karamar Jakarsa, Amma passport yace daukeni inda ka ajiye, ya duba ya duba amma be ganshi ba, hankalin sa ya tashi sosai ya duba kayansa be ganshi ba, gidansu yatafi ya duba dakinsa amma be barshi acan ba, yana kokarin fita daga dakin ne Mummy ta shigo dakin.
Ya tsaya yana kallon ta,
"Yanzu Jalal tafiya zakayi ka barni, laifina har ya kai ka kauracemin gaba daya, Haba Jalal koba komai nifa mahaifiyarka ce, kai kadai nake da baka tunanin halin dazan shiga inka tafi ka barni?"
Maganganun Mummy sam basuyi tasiri a zuciyarsa ba, seda yabari tagama gaba daya, kawai yaraba ta gefenta ya fice, danshi mugun haushin ta yakeji.
Mummy tarasa abunda yake mata dadi, ta zauna t
a rushe da kuka a gurin, Abunda yakara bawa Jalal haushi be wuce yadda yana fitowa yakuma cin karo da Ilham ba, itama magaiyar take masa amma yai biris yai ficewarsa.
Jalal yayi duk tunanin daze yi amma ya rasa inda Passport dinaa yake, wayarsace tayi kara alamar sako ya shigo, Abuda ke cikin sakon ne ya razanashi sosai yasashi mutuwar tsaye wai an soke visa dinsa.
"Why!!!? Ya fada da karfi ji yayi yana neman ya fadi jikinsa na rawa, yanemi guri ya zauna ya dafe kai yai shiruu to laifin meyayi aka soke masa visa haka? Shidai yasan a Dubai be taba zuwa yayi laifi ba, Meyasa haka kodai Jawwad ne ya dauke masa passport, kai yasan Jalal beze masa hakaba Anya ba daddy ne yasa aka soke visa ba.
"Seka tafi in gani Ai, naga ta inda zaka tafi"
Maganar Jalila ya tuna, "to Amma tayaya Jalila zata iya sawa a soke masa visa, wata sani babba haka dazata saka ayi masa haka? Koma ita ta dauki passport dinsa, kai baya tunanin Jalila zatayi haka"
Amma dayayi shiru ya tuna irin gwaramar data hadawa Jeje da Alhaji Kabir abun ya zarce hankalin sa. Aikuwa a gigice ya tashi ya fito ya nufi gidansu.
Zahra batazo makaranta ba sunyi waya da Jalila tace mata batajin dadi ne shiyasa batazo school ba, bayan sungama lectures din farko Jalila tafita neman abunda zataci, gashi tana son zuwa banki ATM dinta yayi expire, dan haka ta siyi Ruwan jarka da biscuit tasaka a Jakarta ta nufi banki dan taje ta dawo da wuri, wayartace tafara ringing kaman karta daga, ta daga setaji muryar Ahmad, gaisawa sukayi suka shiga hira, Ahmad ya iya hira ga ban dariya shiyasa Jalila take sauraronsa, gashi ya iya soyayya da tattali, tabar department tayi nisa tana tafiya da waya a kunnenta taji Anyi wani jakin parking a bayanta, tsayawa tayi ta waiga a birkice dan ganin wani me kokarin ne haka, Amma wanda taganine yasa gabanta dukan biyar biyar, Jalal ne babu alamun Rahama a fuskar sa, ya tamke fuska sosai kamar be taba dariya ba.
Addu'a ta shiga yi a zuciyarta Allah yasa kar yayi mata tijara a bainar nasi. Ahamd yanata magana a waya amma shiru, Takowa yashiga yi yana nufota, yayinda ita kuma tarasa abunyi, ta kame a guri daya tana zare ido, yana zuwa yasa hannu ya janyo ta, ba musu tabishi ya bude gaban motar ya turata ya rufe, ya zagaya ya kunna motar yafizgeta a guje, tunda suka shiga motar bece mata uffan ba itama haka, Sedai tasaka hannunta ta rike kanta ta sunkuyar da kai dan tana matukar tsoron tukin Jalal, tukine na ganganci yakeyi kamar mara hankali.
Can Jalila taji yawan karar motoci ya ragu, A hankali ta bude ido taga sun doshi wani katafaren gida, yana zuwa masu gadi suka bude masa gate, ya shiga da motar yayi parking, se daga masa hannu sukeyi amma ko kula su beyiba,
bude motar yayi ya fito ya bude mata a tsawace yace mata "fito" ba musu ta fito yakuma fizgarta
zuwa cikin gidan dabata san ko inane ba,
A can kasar zuciyarta tana ta Addu'a kuma tanada yakinin Jalal baze cuceta ba.
Suna zuwa wani tankasheshen palour, ya saketa ya kalli cikin idonta da yau ya raina fata take tsuma, a tsawace yace mata "Ina passport dina?"
"Ni ban dauka ba"
"Karya kikeyi"
"Niba karya nakeyi ba, ban dauka ba"
"Jaleela you are lying" jin yadda ya fadi sunan tayi ya tsarga tundaga kanta har kafarta.
"Nifa ba karya nakeba, dan Allah ka maidani, inada lectures fa"
"Ba abunda ya dameni bane, ni kika hana nawa uzurin kike gayamin kinada lectures, kibani passport dina"
"wai waya cemaka nina dauka? A ina zan ganshi?"
"keki gayamin jiya, kuma kika cigaba da rainamin hankali sena kakkaryaki, kibani passport dina ko in babbalaki"
"to Amfanin me zemaka bayan an soke visa?"
"Kekika dauka kenan? Ban abina tunda banaki
bane, meyasa kikayimin haka? Akan me? Me nake tsinta a kasar nan banda bakinciki, Wace Rayuwa ce me Amfani nakeyi anan din, kowa yana kyamata da halayena babu soyayyar uwa a taredani ta fifita bukatarta akan farinciki na, se kokarin cusamin yarinyar dake neman halakani take, mahaifina danake da kwarin gwiwa akansa amma shike zargin ina neman mata, zaman menake a Nigeria banda takura da bakin ciki? Kowa kyamata yake akanme? Ba gara inje inda ba'asanniba inyi Rayuwata ba wanda yasanni ba, kibani passport dina" idonsa gaba daya ya koma Ja, jikinsa tsuma yakeyi.
Jalila ta fuskanci idan tayiwa Jalal rashin kunya yadda yake a fusacen nan ze iyayi mata ba dadi, dan haka ta kwantar da murya tace
"Shikenan is Ok, samu guri ka zauna zamuyi magana"
Cikin tsawa yace "bazan zaunaba, kibani passport dina"
"Idan baka zauna ba bazan gayamaka inda yake ba, Zauna tukuna"
Seda ya danyi jimm sannan ya zauna, ta zuge jakarta ta dakko ruwan da ta siya zata sha, ta bude ta mika masa, ba musu ya karba ze fara sha tace "Kayi Bismillah" seda ya dan harareta sannan yayi ya shanye ruwan se sauke numfashi yakeyi saboda bacin rai
"Kasan wani abu? Nina ga passport dinka akan center table na dauka, sannan nina saka aka soke maka visa"
Tsareta yayi da ido amma bece komai ba
"banyi haka dan inbata maka ba, nayi hakane dan sama maka mafita, kasan hukuncin me sabawa iyaye, muddin kayi tafiyar nan bada san ransu ba zaka iya samun matsala, Abokin Yaya laifin da mahaifiyar ka tayi maka wannan tsakanin tane da mahaliccinta, Amma abunda kake mata ba dai dai bane ba, kamata yayi ku zauna lafiya cikin hikima ka nunamata kuskuren da take aikawa, na baka misalai wancan karon daka kusa karyamin hannu, inkaji kaddarar wani zakaga taka ba komai bace ba, nima misali ce a gareka, na tashi ba mahaifi Allah ya karbi abunsa inada karancin shekaru, ga tsangwama saboda mahaifiyata daga baya ta musulunta, yanzu itama babu ita bansan a ina take ba, Natashi da kaunar Yayana, amma mahaifiyarsa batasona inaji inagani saboda kar mahaifiyarsa tayi masa baki na sadaukar da soyayyata na hakura "
Ta danyi shiru hawaye nabin fuskarta "ABDUL nasan dacin a tsangwami mutum amma kai da gatanka kana tareda iyayenka, kana da gata, suna kaunar ka wata kaddarace ta gifta dazaka iya gyarata, yau inka dena shaye2 ka gyara tsakaninka da Allah da iyayenka ze wuce kamar bakayi ba, nikuwa fa? Nasani ko Aure nayi se an gorantamin rashin dangin uwa, na ubanma waye Abba ne kawai, tare kuke da Yaya Jawwad kasan komai wani abunma ni bansaniba, Why Jalal, wanda yarasa iyaye yayi kuka, kai kana taredasu amma idonka ya rufe"
Sosai Jalila take kuka, yayinda jikin gogan yayi sanyi gaba saya, Jikin Jalal yayi sanyi matuka, kura mata ido yayi, yana tuno lokacin dasuke mata wasa shida Jawwad yana tuno abubuwa dasuka shude gaba daya tausayinta ya kamashi, handkerchief ya dakko a Aljihunsa, yana goge mata Hawayane yayinda taketa sheshaekar kuka kaman wanda akayiwa dole yace
"kidena kuka please"
"Ni kylaeni bazan dena ba din" tasa hannu a jakarta ta dakko passport din ta aje masa "ga passport dinka nan, seka dawo" tana kokarin tashi seji tayi yace
"Aina fasa" tsayawa tayi tana kallonsa
"Eh dagaske nafasa"
"Meyasa kafasa?"
"da farko kin dakukemin passport, kuma kin lallaba kinsa an sokemin visa daya zan tafi?"
"Kayi hakuri nasan kaji ba dadi abunda nayi, amma zaka iya nema na wani kasar katafi"
"Nafasa amma ya akayi kikasa aka soke visa na"
Ta goge hawayenta sannnan tace "daddy Hanan nagayawa ranar dazamu dawo, shine yace kar indamu zssa a soke"
Jinjina kai yayi ya danyi shiru tace
"nika tashi ka maidani"
"Saboda me?"
"Saboda haka nace, meyasa zaka kawoni inda ban saniba, ga gidan bakowa ni gaskiya ka maidani"
"hmm hakane nan inda baki sani bane, zan maida ke amma sekin gama kukan, nan gidanmu ne na gadon kaya inda aka haifeni, inda nayi rayuwa me dadi, dukda ba me dadi ce yadda nakeso ba, amma nayi Rayuwa dani da Jawwad daddy Rayuwa me cike da jin dadi" ya mike tsaye yace 'ina zuwa"
Ya hau kan benen ya dan jima sannan yafito da wata Jaka a hannunsa duk ta danyi kura, yadawo yasamu guri ya zauna, har yaje ya dawo Jalila bata dena kukan datake ba, yasa hannu ya dan karkade Jakar sannan ya bude zip din, wasu uban hotuna ne aciki masu tarin yawa, yasa hannu ya debo wasu, ya mikawa Jalila, tasa Hannu ta karba tafara dubawa a tsanake, fuskarta sharkaf da hawaye amma hoton farko data gani yasata yin murmushi, Jalal ne da Jawwad suna kanan basufi shekaru biyar ba sun zazzaro ido suna sanye da kaya iri daya, haka ta dinga kallon hotunan tana dariya, galibin hotunan hada Umminta a ciki kan wani hoto taje, Jalal ya nutsu ya dauki wata Jaririya yana kallon ta,
Tace "Wannan wacece? Kanwarka ce"
"gata nan dai kalleta baki gane wace ba?"
Jinjina kai tayi alamar Eh, karba yayi yakuma duba wani yabata yace "wannan fa" itace batafi shekara biyu ba Idonta duk hawaye Sunsata a tsakiya
Ba karamin dariya hoton yabata ba "Wannan ai nice"
"wancan ma kece ai"
"to a ina kasamu wannan hotunan haka"
"Abee yanada camera da, shiyake mana hotuna in aka wanko daya abawa Ummi daya abani nake tara nawa, wasu kuma a gurin ummi na karbesu, wasu hotunan bani dasu suna gurin Ummi"
"lallai ka iya Ajiya"
Nan tadinga kallon hotunan, har hoton Iyayen Ummi akwai seda ya nuna mata, gaba daya ya manta da fushin dayakeyi, ita kuma ta manta tanada lectures
kan wani hoto ta kai, Ummice a jiki da Abeenta, sunsakata a tsakiya duk sun kalleta suna murmushi, ta tsaya ta zubawa hoton ido, sekuma Hawaye ya shiga zubowa daga idonta kuka sosai
Jalal yai kuri da ido yana kallon ta, hannu yasa ya zare hoton
"Bani tunda kuka zakiyi, ban hotuna na"
Cikin kukan tace "yi hakuri na dena"
"baza'a hakuran ba, bani nan"
Yasa hannu ya tattare su, rikewa tayi "dan Allah kabari in karasa"
Yana kokarin fizgewa ne hotunan suka zube a gurin, idonta ne yakai kan wani hoto dayasa taji hantar cikinta ta kada.

Da sauri ta dauki hoton tace "Wannan wacece?"
Karba yayi ya duba sannan yace "bakisan wannan ba? Kakarkuce wadda ta haifi su Abba"
"Wannan ai kakar su Hanan ce"
"kamar yaya?" ya tambayeta cikin rashin fahimta, nan ta kwashe komai tagaya masa na zuwanta bauchi jinjina kai yayi yace "masha Allah, nina san wannan kamar da kuke ba'a banza ba, tabbas abunda kakar Hanan tagaya miki haka yake, Sun baro garinsune saboda hari da ake kaimusu, amma yanzu karkiyi saurin fada, Abba yakamata kifara samu da wannan maganar, ya dade yana bincike ko Allah zesa yasamu wani daga dangin iyayensa, tunda basu san kowa ba daga family dinsu, Inna kawai suka sani da baba"
"Allah yasa gaskene Su Hanan 'yan uwan su Abba ne, inda suke sunada yawa sosai estate ne guda gaba daya family dayane"
"' yan uwankune Insha Allah, bari in mayarda hotunan nan se in maida ke"
Ta gyada masa kai ta jirashi ya mayar ya dawo, ya kalleta yace
"muje ko"
Ta wuce gaba ya biyo ta abaya ta tsaya ta wigo ta kalleshi "dan Allah karkayi wannan tukin, dan Allah" bece komai ba ya bude motar ya shiga, itama budewa tayi ta shiga ya kunna motar, aka bude masa gate ya fita, masu gadi nata daga masa hannu amma yayi musu banza,
"Suna maka magana amma kayi musu banza ba dadi fa"
"to mezan musu? Ko sokike in sauka in tsaya ina surutu?"
"A'a bahakaba at least ko daga musu hannu kayi"
Be kuma kulataba ya cigaba da tukinsa,
Sarkar wuyansa ta kalla, sekace ba
an musulmi ba, "Kafasa tafiyar dai ko?"
"baki yadda dame na fada bane?"
"A'a ni banceba, Amma dan Allah kadena yi wa Mummy abunda kake mata, dan Allah"
"Waike ba Adda tagaya miki komai game da rayuwata ba mekikeso inyiwa Mummy?"
"Bahaka bane ba, inka mutu tana fushi da kai Allah ma zeyi fushi da kai, kila sanadiyar yafemata kaga Allah ya daidaita maka Al'amuranka, mutane zasu dena kyamarka"
"Anya Al'amurana zasu gyaru? Mutane bazasu taba sakin jiki daniba kowa ya riga ya gujeni se kalilan din mutane"
"Al'amuranka zasu gyaru inkaso mana"
"Ta yaya?"
"I will help you do that, sekowa ya dawo yana sonka"
"how?" ya tamabayeta a takaice
"Just believe me, you Can change, I will help you change your life, trust me"
Kallonta yayi sannan yai murmushi "I have trust you already, ko iya haka you bring a lot of changes in my world, Thank you"
"kasan wani abu daga lokacin da ka kasance tareda abunda kakeso lokacin kake kara samun nutsuwa da kusanci zuwa gareshi, Iyaye abun sone, dakana kokarin ka manta abunda Mummy tayi maka ka kyautata mata wataran zaka manta da komai"
"bazan manta ba kuma ni yadda take kara cusamin Ilham ke batamin rai"
"wai me Ilham tayi maka haka?"
Kallon Jalila yayi irin kin rainamin hankali
"kinsan komai amma kina rainamin hankali, lokacin dana kwanta a Asibiti kikace musu ina bacci, sunsaki baki itada mahaifiyarta naji duk abunda suke cewa kuma kina tambayta me tayimin bansaniba"
Dauke kai tayi ta danyi murmushi.
Suna shigowa bakin layin suka ga wani dattijo yanata tattare ledojin da suka dan bata layin, da Sauri tacewa Jalal ya tsaya
"me zakiyi?"
"Kaga dattijon can zamu tsaya mu gaisar kaimasa Alheri"
"saboda me?"
"Maganar me mukayi dazu, you want change"
Hade rai Jalal yayi "Wannan mutumin ba irin zagin dabemun ba farkon fara shaye2 na"
"kayi hakuri ka nuna masa ka manta please"
Jalal yaja motar suka karasa inda dattijon yake suka gaisa sukayi masa sannu da aiki, sannan Jalal ya dakko dubu daya ya bashi yasa hannu ya karba ya dinga godiya sannan suka wuce,
"Kiduba Ajiyata dana gaya miki"?
Ya jefo mata tambayar, Jalila bata son rigimadsa tasan intace Ilham ta dauka fada zasuyi dan haka tace
"Wace Ajiyar fa?" ta tambayeshi irin ta manta din nan
Ya gano so take ta raina msa hankali dan haka ya kyaleta yayi parking Akan idon Ilham Jalila ta fito daga motar Jalal.
Ilham aranta tace "dama tazo dazan bakantawa Jalila insa a tsanate" dan haka Ilham da gudu ta shiga cikin gida tana kwalawa Mummy kira ta samu Mummy a daki idonta yayi Ja saboda kuka tana lazimi
"Mummy wallahi Jalal bashida mutunci bashida Imani, duk yadda kikayi kina kuka bakyason ya tafi seda ya tafi, gashinan a banza mace tasashi ya dawo yafasa tafiyar, wallahi gaskiyar daddy Jalal neman mata yakeyi"
Cikin rashin fahimta Mummy tace "Ke bangane me kike nufi ba"
"Mummy Jalal yadawo be tafi ba saboda Jalila"
"Kamarya saboda Jalila?"
"Oho musu dai, wallahi gashi can shida Jalila sun dawo, saboda ita yafasa tafiyar"
"ke ya akayi kikasan saboda ita yaki tafiya?"
Ilham ta gyara zama tace "Mummy nifa shiru kawai nakeyi, Allah kadai yasan abunda nake gani a tsakaninsu, bana son yawan bata miki raine"
A fusace Mummy tace "Ilham bana son shirme da shashashanci, kimin bayani yadda zan gane, ban fahimci ke kadai kika san abunda kike ganiba kimin bayani"
"Wallahi Mummy ba tun yauba akan yarinyar nan bakiga rashin mutuncin da takemin ba, kuma wallahi ita take ziga shi yakemiki wani rashin mutuncin, har dakinsa take zuwa gurinsa, Allah kadai yasan me sukeyi"
Mummy tayi shiru tace "lallai yarinyar nan makira ce, agaban idona take bude baki tacewa Jalal mara tarbiyya, Ashe itama mara tarbiyya ce, tunda take biye masa suna lalacewa, wallahi bata isaba dole in nesan tata da dana, dan bazan zuba ido yana ta'amalli da itaba, akan me na yadda da ita
ina mata kallon mutuniyar kirki amma zatayi min haka? Gaskiyar dsddynsa yana neman mata kenan inbahakaba uban me take zuwayi dakinsa, kema banda rashin mutunci ubanme ya hana ki gayamin abun tun farko"
" Mummy dan Allah kiyi hakuri, kawai nidai bana son ki tayara da hankalinki ne a zatona zan iya shawo kan abun, tunda naga abunda yafaru yau kalli banbamin dayake miki dankice kar ya tafi, Amma dayake akwai abunda sukeyi ai baze iya hakura ya tafi ba, yanzu ki kwantar da hankalinki kawai dai kiyi kokari ayi mana Aure da shi a wuce gurin "
" Ke kina batun inyi kokari ke wani kokarin kikayi?, tsawon shekaru kina gidan nan amma kinkasa janyo hankalin sa, Amma kanwar kanwarki wannan 'yar yarinyar hartasan taja hankalinsa duk taurin kansa, da uwar me tafiki? Niba ina nufin ki zubar da mutuncinki ba amma abun ya dauremin kai, ace har taci mutuncinsa agabana amma dayake bashida zuciya har tasamu kusanci dashi fiye dani da kema gaba daya Kinga tashi kibani guri ni raina ya gama baci"
Ilham ta mike ta fita tana zunbura baki, Amma dai tayi Nasara tunda har Mummy tafara daukar zigarta ta harzukata haka yanzu saura next plan dinta.
Jalila ta tsaya ta kalleshi tace "to ni zan shiga gida, Amma kabawa daddy hakuri"
"Hakurin me zan bashi? Jiya da daddare ya tafi U.K ai"
"to Mummy fa?"
"mezan mata, akanta nake kokuma wani abun nayi mata? "
"Ohh God kanada taurin kai, Just recently kace you want change, kuma yanzu kana wata magana, she's your Mother, komene halinta kuwa, Aljannarka tana karkashin kafarata, ko kanaso kashiga wutane?"
Tayi masa tambayar kaman tana tambayar karamin yaro
Kallonta yayi amma bece komai ba
"Kadinga zuwa inda take, kayi hakuri da duk yadda take, kadena bata mata rai, kaji dan gidan daddyn sa, your Mum is so kinda, she loves you, you have to show her love too, batun Ilham kuma babu dadi kace baka son mutum agabansa kaji"
Tai maganar tana murmushi sannan ta shige gida.
Sumar kansa ya shafa yayi murmushi shima.
Gida ya shige yayi wanka ya ci Abinci ya tafi gurin Jawwad, Jawwad na ganinsa yafara dariya "mutanen Dubai ya akayine?"
Jalal ya dan hade rai "naga alama da hadin bakinka kanwarka tasa aka hanani tafiya"
"niba hadin bakina, amma nasani daddyn Hanan tagayawa, tun a lokacin nasan za'a soke visa dinka, amma nayi shiru ban gaaya maka ba, Amma ya akayi kasan itace tasaka, ina fatan zakayi hakuri karka hukunta ta"
"Hmm Jawwad kenan, yarinyar nan nasan halinta sarai, tun ana gobe zan tafi take dariya tace taga ta inda zan tafi, kaga inba itaba babu memun haka, akwai abunda tayi da har yanzu yake bani mamaki shiyasa akwai abubuwan da idan tayi bazan mamaki ba. Sannan yazan mata ta riga tayi, ban mata komaiba tare muka dawo ma"
Murmushi Jawwad yayi yace "zoka bani Labari, yaushe kuka dena fada ne? Ya akayi ka sakko da wuri haka? Nazata inka gano itace semunzo ban hakuri kar a hukuntata hukunci me tsanani"
"ta fini gaskiya ne, a da dinma abubuwan da take fada akaina gaskiya take fada, nina nake fadan rashin gaskiya, sedai tafiya tsiwa a gadarance take gayamin magana abunda yake harzikani kenan"
"to yanzu fa?"
"Bansaniba babana kasani agaba se antayamin tambayoyi kake, sekace EFCC, kaje ka tambayeta mana"
Dariya Jawwad yayi tareda dan jan kunenen Jalal dake cin Abinci ta sigar wasa yace "Allah ya huci zuciyarka ranka ya dade nidai tunda baka hukunta taba kagama min komai"
Murmushi Jalal yayi sannan yacigaba da cin Abincin sa.
Sunata hirarsu shida Jawwad gwanin sha'awa,
Naja tana gaban mudubi, tasha kwalliya kaman zata gasar rawa, duk tabi ta tsuke jikinta, ta feshe jikinta da turare se taunar chewing Gum takeyi
Nana tace "Ehemm su hajiya Naja ko anyi sabon kamune wannan wanka haka?"
"bawani Sabon kamu, gurin Masoyina zanje tunda shi bezoba ai gara inje inda yake"
Jalila kallin Naja take kawai dan ba karamin tausayi take bata ba yanzu, rashin sani yafi dare duhu, da Jalila zata fadi wani abu data rusa duk wannan rawar kan da farincikin Naja har karshen rayuwarta, abunda ita kanta Najar bata san dashi ba "Allah ka kiyayemin Yaya Jawwad dina ka tsaremasa Imaninsa tareda dukkan Musulmi, dan a wannaan shigar da Naja tayi tana wannan masifaffen Kamshin indai Lafiyayyane namijine da wuya ya iya shallake wannan mugun tarkon na shedan.
Nana ko cewa tayi" kekam dan rashin aji dan yaki zuwa ke sekije inda yake, Sannan kalli shigar ki bata daceba kayan sun matseki"
"A'a ke kyaleni, A haka zanje irin wannan shigar da ita ake kama zuciyar masoyi kuma tana kara kusanci da kauna"
Itadai Jalila batace komai ba har Naja ta fice, sedai girgiza kai datayi tana cigaba dayiwa Jawwad addu'a.
Jalal yagama cin Abincin sa ya dakko system dinshi yana dubawa yace
"Jawwad next month fa zaka tafi Abuja gurin Aikinka"
Da sauri yace
"Saboda me?"
"Saboda nima haka na shirya maka kafin intafi, dan haka seka tafi"
"haba Jalal meyasa, Abba na kokarin bude mana store ne muyi ruining dinsa da kanmu kaga base nayi aikin gwamnati ba mun huta"
Dan tsurawa Jawwad ido yayi a ransa yace "mezanmaka a rayuwa Jawwad in biyaka kauna da alherinka, Sarai Jawwad yasan Jalal yanada tarin dukiya a kasa, Amma bayason ya kashe masa zuciya kar ya nemi na kansa"
"Kaga idan ka tafi nika barni da harkar kasuwancin zanyi mana, Amma seka tafi fa"
"Amma Jalal hakan......
" Salam Alaikum "
Muryar Naja ta katsesu gaba daya suka juyo suna kallonta
Wato har wani pink take saboda tsabar bleaching, saboda daganin wannan farin banata baneba, ga gaba daya dakin ya gauraye da kamshin turarenta tareda karnin mayukan da take Amfani dasu, tasaka riga da skirt na material dasuka kama jikinta matuka duk saman kirjinta a waje.
Dauke Kai Jalal yayi, yacigaba da danna system dinsa
"Masoyina gurinka nazo fa"
Tai maganar tana kokarin zama a kusada Jawwad, Jalal kam mikewa yayi ya shige bedroom din Jawwad, yana tunanin meyasa wasu matan basuda kunya basu san ciwon kansu ba, ace mace budurwa kaman wannan amma tana nanikar namiji haka ba kunya ba tsoro, hakama Ilham take masa wani lokacin, To Amma meyasa ita Jalila bata haka? Shidai yasan ba ruwansa da mata hasali yana gudun taba macen daba maharramarsa ba, Amma ita Jalila bayajin komai dan ya tabata, yana jin kaman hakan shi a gurinsa ba laifi bane, sannan duk lokacin da hakan tafaru a tsakanin su yana ganin matukar tsoro da rikicewa a idonta. Haka yacigaba da zancen zuci yanata tunani daban2.
"Haba masoyin, Meyasa baka zuwa inda nake Yaya Jawwad, wallahi banajin dadin abunda kakemin sam baka nunamin soyayya"
Matsawa yayi daga kusada ita yace "Naja soyayya daban Aure daban a yanzu keba halalina bace ba meyasa zakimin irin haka? Ke ko kunya ta bakyaji ne haba Naja kidinga kama kanki mana"
Matsowa takumayi jikinsa tana kashe murya tace
"meye wani kama kai, Aurena fa zakayi dan Allah kasaki jiki ka nunamin soyayya haba Jawwad" takai hannu tana shafo fuskarsa
Gaba daya jikin Jawwad rawa yakeyi Tsaki yayi yana kokarin mikewa, tunda ya fuskanci bazata ganeba
Riko hannunsa tayi tana kokarin Rungumeshi, A fusace ya hankadeta kasa yana kokawa da numfashi,
Tashi takuma yi tace "bazanyi zuciya ba" sekace mayya take kuma shanye ido kamar tana maye, ta rungume shi.
"Ke!!!" ya daka mata tsawa a fusace wadda seda yasa Jalal fitowa a sukwane yayi jifa da ita
"ki tashi kibarmin dakina, Allah ya shiga tsakanina dake ban taba aikata mummunan sabo ba bazan fara akanki ba, get out from my room ko in illataki" idon Jawwad yayi jawur jikinsa yana rawa, gaba daya ta kasa gane dama Jawwad yana fushi haka? Jalal ya karaso ya rike Jawwad yace
"Jawwad kyaleta yi hakuri, calm down"
"bazanyi hakurin ba ka kyaleni, wallahi takuma zuwarmin daki sena bata mamaki, bata san a bisa umarnin Maama zan Aureta ba, in bahakaba me zanyi da ita? Me take dashi daza'a kalla a ce wannan mace tagari ce ya dace a Aureta? Itada mahaifiyarta sun shiga sun fita sun rabani da kanwata shekara da shekaru suna uzzuramata suna bata mata rai suna cimata mutunci, na hakura, ance sena Aureta na hakura nayi biyayya, be isheta ba seta nemi tasana aikata laifi me muni"
Kallon Naja Jalal yayi, kaddai ace wannan yarinyar ya yadda ze aura, Amma Jawwad hakurin nasa yayi yawa. Naja ba karamin mamakin abunda Jawwad yayi mata tayi ba, ita babban mamakinta bata taba ganin yana fada ba, saboda tasan mutum ne me kunya da kawaici.
Jalal yace "Naji kadaiyi hakuri"
"bazanyi hakurin ba Jalal"
Jalal yace "da nine da yanzu kacemin masifaffe, haba dan uwa Aliyu Haidar zakin Allah, katangar sikari na Hanan kowa ya jingina da kai seya lasa, fari me farar aniya kai a cikin masu sunan ma na dabanne kayi hakuri" Jalal yana lallaba Jawwad ne saboda yasanshi be iya fushi ba, seya shafe shekaru be fushi ba amma idan yayi abun baya kyau.
Naja tace "kagama duk masifunka, wallahi nidin dai ni zaka Aura kuma zaka gane baka da wayo, bari Maaman ta dawo zaka gane ka taka tarkon mace.
Jalal ya hanashi magana, suka kyaleta a gurin yaje ya dinga rarrashin Jawwad, ana haka Hanan ta kira wayar Jawwad, Jalal yai murmushi yace "kaga ka daga wayar nan ayi maka kalamai, zaka huce"
"A'a ka kyaleni, am not in mood"
Aikuwa Jalal ya daga wayar suka gaisa yace "Hanan ga mutumin naki, Amma ransa a bace yake fa"
"Subhanallah dan Allah wayakai min zuciyarsa bango har akasamin shi fushi, dan Allah ka bashi wayar"
girgiza masa kai Jawwad yayi alamar baze karba ba
"kiyi hakuri, baze karba ba fa, ransa a baci yake"
Hanan a shagwabe
tace "Shikenan tunda baze karba ba amma zuciya ta bazataji dadi ba, Allah kuka zan tayi duk daren nan, wallahi har naji tawar zuciyar tafara nauyi"
Ai tuni Jawwad ya zare wayar a hannun Jalal yasa a kunnensa yace
"Hello Hanan kina jina?"
"haidar dina me akayi maka?"
"wani little issue ne, kuma yanzu komai yayi settling"
"little issue baze bata maka raiba"
"ki manta kawai, kar inga abunda yasamin ke kuka"
Jalal yaji Jawwad ba kunya anataya masa kalamai agabansa. ya minstili kafar Jawwad yace "dan rainin hankali kawai"
Jawwad yai murmushi
Jalal ya daga masa hannu ya wuce gida.
Yanayin maganar Hanan kaman Jalila, tuno moments dinsu yayi dazu dayake ta dage bilhakki tana masa fada, da yadda take da ido idan batada gaskiya murmushi ya dingayi shi kadai, har ze kwanta ya tuno maganganun Jalila game da Mummy.
Mikewa yayi ya nufi cikin gidan, babban palourn Mummy yasa hannu ya bude kofar. Salla takeyi yanemi guri ya zauna, rabonsa da dakin
nan harya manta yana jiranta yana sake2 a zuciyarsa mema ze ce matane?.
Ta idar tagama lazimi, ba karamin mamakine yakamata ba ganinsa a part dinta
Ta kalleshi tace "Lafiya kuwa? Ashe baka tafi ba, uwarka wadda tafini, wadda take baka abunda bana baka ka fasa tafiya saboda ita.
" Wakenan? "