← Book details Abdul Jalal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 25 OF 52

PART 1

Abdul Jalal Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

  _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din

🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

Gaskiya comments nakeso ba sticker ba kokuma Just thanks in bahaka ba zan dena typing kullum
Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa

           -MY FIRST NOVEL-

Wani mugun kama Ummi taga Hanan tanayi da Jalila, ciwon goshin Hanan ta kalla
"Eyya kiyi hakuri ai munje makaranta akan case din, mun bada hakuri, babanta yace komai ya wuce kiyi hakuri Dan Allah"
"Keda kinsan da bada hakurin kika haifi Yar da bata da tarbiyya, kika haifi yarinyar Datafi karfinki ni na dauka ma Yar wata hamshakin ce Ashe ba Yar uban kowa bace face Mara galihu?"
"Duk me ya kawo wannan maganar, haba ke kuwa Jalila tana da tarbiyya rashin ji ne kawai na yara, kuma batun gata kowa gatansa Allah,"
Wani abune yakawo wa Jalila iya wuya motsa baki tayi da niyyar rashin mutunci cikin tsiwa sukayi ido hudu da Ummi seta hadiye maganarta tayi shiru
"Da wallahi niyyata ubanta zansa akoyawa hankali in yaso gobe yabawa yarsa tarbiyya ya banbance mata matsayin yayan gata da marasa galihu"
"Kar a kuma sakomin uba, a barshi ya kwanta cikin aminci a kabarinsa, ni nayi laifi ba shiba"
Jalila tayi maganar tana jujjuya idanu
"U see mummy wannan yarinyar bazata yi nadama ba memakon tabaki hakuri rashin kunya zatayi miki, in bakiyi Sa a bama zaginki zatayi, kawai kisa a dauketa a je a horata"
Hanan tayi maganar tana kallon Jalila
Da yarabanci Ummi tayiwa Jalila magana, Jalila ta yamutsa fuska ta Dan kara hade rai
"Naji yata ba Yar uban kowa bace bamu da gata se Allah mu bamu su arziki bane, amma kiyi hakuri batun a dauki Jalila a horata be taso ba, bazata karaba"
"Tsiyar talaka kenan ko ince matsiyaci, ya dakko abunda yafi karfinsa, karshe yazo yana karya murya,"
Ta maida idonta kan Jalila
"Kekuma kinci Sa a da ubanki zan Sa akama, wannan uwataki ce ma tabani tausayi, ba dan haka ba da sena Sa an sauya miki halittu, kibari kitaka wani matsayi kisamu me tsaya miki in kinyi rashin mutunci, a yanzu dabaki da galihun nan wahala zaki sha Mara tarbiyya kawai"
"Nice ma ke saboda rashin tarbiyya kuma kar......
Jalila ce tafara magana ummi ta dakatar da ita
Ummi ta kalli mummy Hanan sannan tace,
" nace kiyi hakuri ko, se magana kike akan gata se dai ko nan gaba amma a yanzu dai banajin kinsamu gatan dana samu a rayuwata, sannan yata ba Mara galihu bace ba, da gatan ta, daliline yasa kiga ganmu a haka, amma bazan gazaba Allah yabaki hakuri"
Tsaki mum Hanan tayi taja Hanan suka fita, ga magana fal abakin Jalila amma Ummi ta hanata magana,
Wata kwallar bakin ciki ce ta taru a idon Jalila, meyasa Ummi ta hanata magana daki ta wuce ta kyale Ummi a tsakar Gida

Jawwad Yana ta duba ta inda Jalal ze taho ya hangoshi yana nufo inda motarsu take da ledoji a hannunsa da sauri Jawwad ya karaso
"Ina ka tsaya daga siyen abu"
"Au fitowa kayi nemana, da nasani kulleka nayi a cikin mortar"
"Bar wannan maganar ban mukullin mota ni zanyi driving dinmu"
"Me yasa?"
Jalal ya tambayi Jawwad da mamaki, be bashi amsaba yasa hannu ya karbi key din daga hannun Jalal, suka shiga suka tada mota
Jalal ne ya kalli Jawwad
"Nifa bangane wannan abun da kakeyiba, ina kuma zamuyi , ba gida zamu tafi ba?"
"No wani guri zaka rakani"
"Ina kenan?"
"Just watch" inda sukayi zasu hadu da Hannah ya kaisu, ya kulle Jalal a motar ya fita da wayar Jalal kaman yadda shima yayi masa dazu lambar Hanna ya kira
"Kina dai² ina gamu munzo restaurant din"
"Nabar nan gurin ina bayan layinku rukunin sababbin gidajen nan"
"Haba Hannah amma ba haka mukayi da farko ba"
"Na canza ra ayine ina daf da zuwa gidansu Jalal in bakuyi Sauri ba" katse kiran yayi ya koma motar da sauri ya kunna ya ja motar ya bar gurin
"Nikam naksa gane ma'anar abunda kakeyi Jawwad wai meye haka?"
"Zaka gane ma'anar abunda nake yanzun nan"
Inda Hanna tayiwa Jawwad kwantace nan Jawwad ya kaisu ya kirata yace gasu sunzo, sannan yacewa Jalal ya fito daga motar, ba musu ya fito daga motar yana kallon Jawwad, daga cikin tata motar Hannah ta fito tana wani taku cike da iyayi da isa wata shedaniyar rigace a jikinta straight found ce amma yadin roba² ya kwanta a jikinta yakamata tsam se Dan kwali data daure kanta dashi ta fito da Wig's dinta ya bazu a gadon bayanta,
Da mamaki Jalal ya kalli Jawwad cike da tuhuma da sauri Hannah ta karaso domin rungume Jalal amma yayi saurin matsawa baya
"Meye haka wannan wane irin shirmene baki da hankali niza ki hugging? Meye ma anar hakan daka kawoni nan gurin Jawwad?
Yai maganar a fusace yana kallon Jawwad, Jawwad bece masa komaiba
" ba laifinsa bane, ni nace yakawomin kai ko in maka ba dai² ba kuma Dan na rungumeka ai ba laifi bane,  Jalal why are you avoiding me? do you thinks am Jocking danace ina sonka, se wulakanci kake min haba Jalal kalleni sama da kasa banyi kama da irin matar daza a wulakanta ba meye aibuna"
Kallon Jawwad yayi
"You see, meye amfanin hakan dakayi, ka dakkoni ka kawoni gurin wannan mahaukaciyar yarinyar, kalleta kalli jikinta, dan ta rainamin hankali kuma tace tana sona, koda nake shan giya nasan abunda ya dace dani"
Jalal se fada yakeyiwa Jawwad duk yadda Jawwad yaso ya kwantar da hankalinsa yayi masa bayani yaki yadda se fada yakeyi, murmushi Hannah tayi sannan tace
"Masoyina naji kana kasan abunda ya dace da kai, ai babu wani abu me kyau da yadace da kai babyna, nidin dai nina dace da kai, kai duba da yanayin taka rayuuwar, da kuma tawa suna kamanceceniya babancin kadanne kawai"
Kurawa Jawwad ido Jalal yayi"kagani ko ka kyauta" shine abunda Jalal yafada Yakama hanyar tafiya, da sauri Jawwad ya bishi "Dan uwa Dan Allah ka saurareni"
"Nika rabu dani babu abinda zaka gayamin, wallahi in kayi wasa sena Sa an batarmin da yarinyar nan, Dan me zaka dinga cusamin ita dolene sena dinga shiga sabgar matan, I hate her"
Ya juya yayi tafiyarsa yabar Jawwad a nan gurin a tsaye Hannah kuwa dariyar farin ciki tayi saboda tayi nasara, so take dama ta Dan janye Jawwad daga jikin Jalal don tasamu damar gudanar da abinda tayi niyya, tayi nasara tunda Jalal har yayi fushi haka
Jawwad ne ya dawo inda yabar Hannah cikin damuwa ya dubeta
"Haba Hannah baki kyautamin ba kalli yadda yayi fushi, ba  haka mukayi dake ba, anya son gaskiya kike masa?"
"Kwarai kuwa son gaskiya nake masa, kayi kokari nagode daka yi dalilin dayasa naganshi at least dukda yaji haushi amma ka faranta min"
"Dan Allah ina rokonki, karki je gidansu Jalal a hakan ma fama ake akan ya canza halayensa, in kika kuma sanadin lalacewarsa biki kyauta ba, Hannah ke mace ce baza kiso ace Jalal danki ne ko yayankine a haka ba"
Yadda Jawwad yai maganar abun tausayi har Hannah taji yana nema ya kashe mata gwiwa Dan haka da sauri tace
"Thank you, ni na tafi semun kuma haduwa"
Ta juya tai shige motarta, bashi dazabin da ya wuce shima ya tafi, Dan haka ya hau motar da sukazo ya tafi

Bayan sallar magariba Jalila durkushe agaban Ummi tana kuka"Ummi Dan Allah kiyi hakuri, najanyo anzo har Gida anci zarafinki nasan laifinane amma insha Allah bazan kuma ba kiyi hakuri Dan Allah "
Hannu Ummi tasaka tana gogewa Jalila hawaye"ya wuce baby amma ki canza halinki ki rike maraicinki ki dena dakko mana magana"
"Ummi na dena insha Allah"" yawwa baby nima ba a son rains name fushi dake ba" rungume Ummi Jalila tayi"nagode Ummina Allah yabaki tsawon rai me amfani"
"Ameen, Allah ya shiryamin me yabaki miji nagari" shiru Jalila tayi tareda kuma gyara kwanciyarta a jikin Ummi
"Ummi amma kinfasa maidani kano ko?
" tafiyarki kano tana nan"
"Ummi meyasa?"
"Haka mahaifinki yace kafin ya rasu" dagowa tayi ta kalli Ummi
"To amma ai yanzu baban nawa baya nan,"
"Zaki kumako ai bazaki canza halinki ba dagani ni"
Mikewa tayi daga jikin Ummi taje ta samu guri ta zauna tana tunani

Duk yadda Jawwad yaso ya shawo kan Jalal ya nuna masa dalilin dayasa ya kaishi gurin Hannah amma Jalal yaki saurarensa
Haka Jawwad ya hakura ya kyaleshi ya tafi gida, yaje yayi salla sannan ya shiga cikin Gida bangaren Abba, ya tarar dashi yana kallon labarai
"Sannu da zuwa Abba ya kabarosu ya hanya"
"Lafiya kalau Jawwad, ai tun dazu na dawo naita zuba ido in ganka, amma banganka ba"
"Mun Dan fitane da Jalal, Abba ya akayi da case din, munyi ways da wani Dan ajinmu yacemin ai ita yarinyar kanwarasa CE"
"Eh kam mun hadu yace ya sanka, ajinku data, Ai Allah ya temakemu abun yazo da sauri,"
Abba ya labartawa Jawwad abunda ya faru
Jinjina kai Jawwad yayi"amma Abba Jalila takirani a waya tana kuka, tace kunce nan zata dawo, zama tare damu"
Murmushi Abba yayi
"Hakane amma Dan mu tsorata ta ne mun yanke seta kammala wannan ajin da take, sannan zata dawo nan, kasan wasiyyar kanina kenan, gara ta dawo nan maybe sekaga ta nutsu"
"Hakane, to Abba ita ummin fa haka zata cigaba da zama ita ka dai"
"A a Jawwad itama zata koma gurin iyayenta ne, intaje insun karbeta se akai Jalila taga dangin mahaifiyarta, ina ganin in Jalila ta dawo nan bata ganin idon umminta zata dena fitina"
"Hakan yayi kyau Abba Allah yasa mudace,"
"Ameen Jawwad"
Haka suka cigaba da tadi daga baya Jawwad ya fito ya koma gurin Jalal amma da yaje baya nan ya kirashi a waya amma baya dagawa,
Girgiza kai Jawwad, yayi yasan ba makawa Jalal ya tafi mashaya
Aikuwa hasashen Jawwad yazama gaskiya domin kuwa don kuwa bayan abunda yafaru tsakaninsa da Hannah da Jawwad, Jalal yakoma Gida yaji ransa yakiyi masa dadi, ransa yagama baci Dan haka ya fita ya tafi mashaya
Aikuwa Jeje ya takewa Jalal cikinsa da giya yayi mankas ya fita hayyacinsa sannan ya kalli Jalal
"Mutumina wai me yabata maka raine haka naganka some how"
Cike da maye Jalal yafara magana yana tangadi
"Wata usless creature ce take son takurawa rayuwa ta, ga Jawwad shima ya bata min rai mtseww, wai meyasa mata suke da matsala kasan mene ma"?
Murmushi Jeje yayi
"sekafada nawan"
"Kasan wannan kanwar tawa ko? Ilham itama fa hadamin zafi tayi da safe so nayi in tattakata amma Jawwad ya hanani kaga itama wannan banzar da take takuramin wallahi so nake inyi maganinta"
Seda Jeje yakuma banka masa giya sannan yace
"To meye a ciki man Hannah ta kai macen daza a sota she's so beautiful fa" Jeje ya dakko waya yana nuna masa hotunan Hannah da wasu irin kaya a jikinta me bayyana surarta
Ture hannunsa Jaalal yayi yana tsaki
"Kai jeje ni bana sonta bana son shirme aikin banza kaima batamin rai zakayi meye hakane kakeyi"
Jalal Ya mike yana tangadi yana shirin tafiya
Jeje a ransa yace lallai gayen nan akwai taurin kai a bugen ma yana da lissafi amma muje zuwa zaka gane kuskuren ka
A zahiri kuma mikewa Jeje yayi ya riko Jalal in bahakaba ze iya faduwa, Dan baze iya tuki ba Dan sosai yake tangadi

Ilham ce take ta kaiwa tana kawowa a dakinta tana tunanin me yakamata tayine, dan tayi Alkawarin fitinar Jalal tako ina bazata bari yafara soyayya da wata banza ba, ba itaba Dan hakan dai² yake da rushewar shirinmu ana samun kuskure komai ze lalace, dabara ce ta fado mata
Dan haka gaban mudubi taje ta zauna, ta fara shafa mayuka a jikinta, tareda fara tsara simple make up a fuskarta, dogon wando tasaka skin tied se wata karamar Riga body hook, ta dakko wannan turaren ta shafe jikinta da shi, parking din gashinta tayi ta Dan Dora mayafi akanta ta nufi hanyar fita
Jeje ne yakawo Jalal gida a buge part dinsa ya kaishi ya kwantar da shi
Jawwad da yake kofar gida yaga wucewar motar Jalal koba a gaya masa ba yasan Jeje ne yakawo Jalal, kuma ba makawa a buge yake, girgiza kai Jawwad yayi cikin bacin rai yakoma cikin gida
Bayan jeje ya kwantar da Jalal ne yazo fitowa daga part din Jalal sukayi clashing da Ilham
"Wow so cute, common beb u look so beautiful"
Jeje yai maganar yana mata wani shedanin kallo
"Kai kashiga hankalinka, ka kiyayeni, bani hanya"
"Meyasa kikeso in baki hanya me zakije kiyi masa? Gaskiya na kyasa ya za ayine?"
Wani mugun kallo Ilham tayi masa
"Eh kaman ba gidan ubanka bane nan, meye na tambayata me zanyi masa kai me kayi masa, ka kiyayeni ka fita hanyata, niba Sa arka bace sakarai kawai"
Ta hankade Jeje ta wuce ajiyar zuciya Jeje yayi "gaskiya yarinyar nan ta hadu I have to do something"
Yasa kai ya fice, Ilham har cikin bedroom din Jalal ta shiga ta ganshi kwance yayi dai² akan gado yana bacci. Murmushi Ilham tayi ta shiga cikin dakin ta samu gefen Jalal ta zauna hannu tasa ta Dan shafa sajensa zuwa cikin sumarsa
Dan jijjigashi take
"Yaya Jalal wake up please"

Share please
More comments more typing................


🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️
[9/12, 6:02 AM] +234 816 830 7871: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

    _ABDUL  JALAL_
           (2020)

      _ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_
    (Daddy's girl)

               PAGE-  27
Chapter 25 · 0% Book details