← Book details Abdul Jalal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 18 OF 52

PART 1

Abdul Jalal Part 1 Complete Hausa Novel · about 12 min read

  _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din

🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

I want comments not stickers or just thanks😢😢😢😢
Your comments give me courage

     
        -My First Novel-

Malamai ne suka jeru suna shirin janyowa Jalila inda zata karanta
Itakam tayi shiru ta kurawa camera ido haka nan taji gabanta na faduwa dukda tasaba zuwa musabuka amma takejinta wani iri

Jalal ne ya kurawa TV ido gani yake kaman shi Jalila take kallo so yake ya tabbatar itace kuwa a jikin allon TV kokuwa kamrun dayasha ce tafara gaya masa karya(giya)
Ita kam Ilham kara shige masa take tana kuma zuba masa Wayne tana mika masa
"Ilham ki kyaleni please"
"Yaya J why?"

Tayi maganar tana kuma kwanciya a jikinsa
Shikam yakoma kaman wani karamin yaro
"Bana so Ilham ki kyaleni kwanciya zanyi kaina ciwo yake"
Dan dagashi tayi ya koma ya kwanta akan kujerar yana kallon TV kasa²
A hankali Ilaham ta mika hannunta tana shafa sajensa
"Sannu Yaya J"
Gyada mata kai yayi

"Ilham karki kuma saka turaren nan inzakizo inda nake banaso"
Yai maganar a hankali
"To na dena"
Tv ya kuma kalla Jalilan ce dai sedai wannan karon annurin fuskarta ya gushe ta dai²ta nutsuwarta aka janyomata inda zata biya
A hankali tayi bismillah tafara karanto Qur'ani cikin sauti me dadi
Ture Ilham yayi daga Jikinsa ya lumshe idonsa jin sautin karatun nata yake yana ratsa ko ina na jikinsa yana saukar masa da nutsuwa Ji yayi kasalar tana sakinsa duk yayinda ya bude Ido seyaga kaman Jalila shi take kallo jinsa yake kaman ba Shiva
Ilham hannu ta kuma mikawa zata taba shi ya daka mata tsawa
"Ke wace irin banzar yarinya ce waima tukuna me kikemin anan gurin ne tashi kibar min daki kafin in zaneki banza kawai"
"Haba Yaya amma
" bazaki fitan ba kenan kalli Tv duk rawar kanta kalli yadda take karatun Qur'ani gwanin burgewa keko sha³ baki iya komaiba se hauka get out from my room"
Idonta ta kai duba kan Tv Jalila tagani tana zuba kira'a kaman ba itace me shegen surutu da Neman magana ba, wani abu taji yazo ya tokaremata zuciya wato tun dazu da ya kurawa Tv ido ita yake kallo kenan
Wani mugun kallo taimasa
"To ai gara ni inazuwa Islamiyyar kai...........
Bata rufe bakiba yasaka kafafuwansa ya take nata kafar wani irin ihu tayi da karfi kuma yaki dagawa
" Dan girman Allah kayi hakuri, wallahi bazan kuma ba"
Kara takesu yayi
"Dan ina daga miki kafa ina nan a Jalal dina da kikasani, yanzuma Sa a kikaci da wallahi sena zaneki da belt, tashi kifita wawiya kalli rigar jikinki sokuwa kawai"
Da kyar taja kafa ta fita kafarta se zugi takeyi ta koma dakinta ta hau gado ta kama kuka
Wani uban tsaki ya ja yanemi guri ya zauna
Tashar da suke haska musabakar su Jalika sun tafi talla dan haka
ya dauki cup din giyarsa ya cigaba da sha yakuma zubawa ze sha aka kuma hasko Jalila haka nan se ya aje giyar hannunsa shima ya kuramata ido, yanayin Jalila ne ya nuna kaman bata da nutsuwa
Aka kuma janyomata karatu amma tayi shiru ta tafi tunani kowa ita yake kallo
Jikinta ne yayi sanyi jitake kaman wani abune ke shirin faruwa, mafarkanta datakeyi yan kwanakin nan ne suke fado mata a rai taji gabanta yacigaba da faduwa.
a hankali tayi ajiyar zuciya ta Dora inda aka janyomata da karatun ta cikin birgewa

Bacci ne yafara fusgar Jalal dan haka anan gurin ya zube ya lumshe ido yana sauraren karatun Jalila har bacci yayi awon gaba da shi

Da safe Jawwad ne yazo ya tarar dashi yana bacci a parlour a kasa kan carpet ga kwalbar giyarsa yasha fiye da rabi
Girgiza kai Jawwad yayi
"Allah ya shiryeka Jalal"
Yasa hannu ya kwashe kwalbar da kofin ya fita dasu ya dawo ya tashi Jalal don yasan be salla ba balle ya karya
Hannu ya kai ze tasheshi yaji kansa yayi zafi, bayansa ya Dan bubbuga a hankali Jalal ya bude ido ya mayar ya lumshe
"Ka tashifa gari yayi haske kayi salla kazo mu karya"
Jalal ne yake tunano abubuwan dasuka faru jiya da daddare gaskene kokuma mafarki yayi ji yai kansa yakuma sarawa

"Kaina ne yakemin ciwo sosai Jawwad"
"Sannu ka tashi in muka karya seka sha magani"
Da kyar ya lallabashi yaje yayi wanka yai sallar asuba, Jawwad ya dakko musu Abinci

Ilham CE ta fito tana taka kafa da kyar mummy ta kalleta
"Meyasameki kike taka kafa da kyar"
"Dutse na taka jiya a garden"
"Subhanallah bakiji ciwo ba dai ko?"
"A a banjiba kafar ce dai kawai take ciwo"
"To ko asibiti za a kaiki a duba kafar"
"A'a mummy zata dena ne Insha Allah"
"To shikenan ni zan fita ne zanje ganin likitan Ido, ga breakfast can na gama in wancan Dan zeci yazo ya dauka kema kije ki dau naki"
"To mummy adawo lafiya"
"Allah yasa"
Mummy ta fita

Jalal ne ya dakko wayarsa ze kira daddy yaga message ya shigo wayarsa Dan haka ya bude message din bakuwar lambs ce

      "Barka da safiya jarumin     
        maza fatan kana lafiya       
       Zanso ace a halin yanzu
       Muna tare ina kallon                  wanna kyakykyawar fuskar
      Amma lokaci na nan zuwa
       Dazamu kasance tare kaji          Dadinka masoyina
             From ur lovely bae"

Wani uban tsaki Jalal yayi
"Nasan Ilham ce zataci kaniyarta zata gane innin sa,'anta ne"

"Ya dai meyafaru ne kake surutai haka"?
Jawwad ya tambaheshi
"ba komai ci abincinka kawai"
Ya mike ya nufi cikin Gida tundaga parlour yake kiran sunan Ilham amma bata nan dakinta ya nufa yana zuwa ya tarar tana dakinta tana karyawa
A firgice ta dago tana kallonsa

"Uban meye wannan kika turomin a waya wai meyasa ba kyajine Ilham"
Kallonsa tayi cikin rashin fahimta
"Wane sako kuma ni ban turomaka komai ba"
Ransa ne ya kuma baci wato raina masa hankali zatayi gadan² ya nufi inda take da niyyar ya ci kaniyarta
Ta mike tsaye tafara kuka tana
"Wallahi Yaya bansan laifin danayiba"
Yana karasowa Inda take yaji tana warin wannan turaren na jiya kansa ne ya Sara yaji yana Neman ya fadi, da sauri ta taho inda yake
"Yaya menene?"
"Dalla tsaya karki karaso inda nake"
Bango ya daddafa yabi kofa ya fice da kyar ya koma part dinsa Jawwad ne ya ganshi ya rike kai yana dafa bango
"Subhanallah Jalal kanne dai"
Jawwad yafada yana riko JALAL
"Jawwad kaina kaman ze fashe"
"Bari mu tafi asibiti ina key din motarka?"
"Kaga kyaleni bazani wani asibiti ba"
"Meyasa meye amfanin ka zauna a Gida baka da lafiya"
Guri Jalal yanema ya kwanta ji yake duniyar tanata jujjuyawa
  Kai tsaye cikin gidan Jawwad ya tafi ya nufi part din daddyn Jalal yasameshi a parlour yana breakfast
Suka gaisa Jawwad yagaya masa halin da Jalal yake ciki, tare da daddy suka taho gaba  daya part din Jalal
Suka tarar dashi a kwance yanata juyi akan gado ya rike kai Juyin duniya ya tashi su tafi Asibiti yace baza shi ba kunsan mutumin da taurin kai
Se wani likita aka kirawo yaimasa allura se yasamu yayi bacci

Alhamdilillah Jalila ita tazo na biyu a gasar musabaka da akayi tasamu kyautuka da dama kuma an karrama malamanta
Ita Jalila duk ba haka taso ba na daya taso tazo
"Duk wannan sakaran ne yajamin haka kawai naita mafarkinsa nazo musabaka ya hanani sukuni"
Haka taita mita suka kamo hanyar dawowa Kaduna suna murna amma ita haushi duk ya isheta
Har Gida motar makaranta takai Jalila, siyama tana gidan tana Jiran isowar Jalila
Ummi tana ganinta ta rungumeta tana murna, amma Jalila tai kicin² da fuska
"Lafiya kuwa babyna?"
"Ummi ta biyu fa Nazo"
Tafada kaman zatayi kuka

"Haba baby Wanda yazo na karshe kuma yace me? Daga na daya fa seke haba babyna"
"Gaskiya aminiya inkakiyi haka baki kyauta ba kullum zakiyita zuwa na dayan, hakan ma mu munyi murna"
"Yawwa ai gara kigayamata siyama, adinga godewa Allah Baby"
Ummi tayi maganar tana dungurewa Jalila kai Dan turo Baki JALILA tayi
Taje tayi wanka suka kule dakii itada siyama suna hira
"Kinsam wani Abu aminiya"
JALILA tai maganar tana kallon Siyama
"A'a sekin fada"
Siyama ta bata amsa
"Wallahi Jiya agurin musabaka naji gabana yanata faduwa ina tuna mafarkin nan danake"
"Kai Aminiya meye kuma na tunawa ABU ya Riga ya wuce kimanta kawai
Bari inbarki ki huta kishirya ranar Monday insha Allah za a koma school"
"Can ta matsemusu bazan komaba senagama hutawa ki gaida umma"
"Aminiya halinki seke tararki za aci fa in baki koma ran Monday ba"
"Hhh tab Tara sedai a ci wasu Tara ba dai niba"
Sukai sallama ta Raka Siyama kofar Gida ta dawo dakinta ta kwanta akan katifa domin huce gajiya


Mummy ce ta dawo Ilham tagaya mata ai Jalal ba lafiya suka tafi part dinsa, yana kwance akan gadonsa yana bacci jijiyoyin kansa duk sun daga dagani baccin ba dadi yakemasa ba, warin turaren Ilham yakuma shaka dukda bacci yake seda ya yamutsa fuska ya juya wani bangaren
A hankali mummy ta kai hannu ta shafa sumarsa tana fadi
"Allah yabaka lafiya son"
ILHAM ta amsa mata da "Ameen"
Se bayan azahar ya farka Jawwad ya shiga cikin gida yace Ilham ta hado tea ta kawowa Jalal,

Jawwad ne gefen Jalal yana masa sannu
"Ya kakejin jikin naka yanzu"?Jawwad ya tambayi Jalal
"nifa har yanzu yanamin ciwo, amma bakaman dazu ba"
"To ai kaima ance muje asibiti kaki ka manne a Gida"
"Ni ba wani asibiti da zanje"
Sakone ya shigo Wayar Jalal, Jawwad ya miko masa wayar

         "Barka da wannan lokaci
           Lovely am missing ur
           Handsome face wish to
           See u soon
           Love u so much
           From ur lovely bae"
"Mtseww wannan wace irin jaraba ce"
Yana aje wayar tafara ringing an kira yafi sau uku yaki dagawa
"Jalal wayarkace fa ke ringing
Ka daga mana"
"Bazan daga ba in ka gaji da karar kai ka daga"
Girgiza kai Jawwad yayi halin JALAL se hakuri
Hannu yasa ya daga wayar se yaga unknown number muryar mace yaji
"Hello babyna fatan kana lafiya"
"Sorry ba me wayar bane, me wayar baya jin dadi amma wa za ace masa"
"Eyyah shiyasa naji ni bani da lafiya nima ko abokinsa ne JAWWAD"
"Dan uwansa dai"
"To amin afuwa Dan uwansa"
"Eh nine"
"Hannah ce ai masa sannu, ko zaka bani address din inzo in dubashi"
"Ohh no daga nan ma kiyi masa addu'a mungode"
"Anyway Allah yabashi lafiya amma banajin zan iya komai bayan mallakin zuciyata ba lafiya,
Ka gaisheshi please"
"Zeji insha Allah"
Jawwad ya katse kiran ya kalli Jalal
"Mutumin yaushe kafara soyayya ba labari wace kuma Hannah"
"Mtsewww soyayyar banza kai kasanta"
"Easy mutumina adena cika baki wadda takiraka din nan bakaji kalaman data fada tace agaya maka ba"
"Dan Allah ka kyaleni inji da kaina"
"Ohh sorry nadena sannu,
Yanzu za a kawo maka tea"

ILHAM kam wani tunani tayi this is another opportunity for her to use that medicine again
Tunda wancan lokacin be Ciba a abinci yanzu tasan zesha a tea
da rawar jiki Ilham ta mike taje ta nufi kitchen ta hada tea ta zuba wani maganin a ciki ta juye tea din a flask ta doro cups akan plate ta nufi sashin Jalal

A cikin bacci Jalila taji kirjinta ya tsanan ta bugawa Ilham kawai take gani a mafarkinta a hankali ta bude ido gabanta ne yacigaba da faduwa meke Ilham ke shirin yine nake ganinta a bacci na
"Laila ha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin"
Shine abinda Jalila taita maimaitawa kamar wadda aka tsikara tayi zumbur ta  mike zaune ta dakko wayarta


Sallama Ilham tayi tana kokarin shigowa
Jalal ne ya Daka mata tsawa
"Tsaya a nan malama karki karaso inda nake"
"Haba Jalal wai meyasa kai ba a maka gwaninta ne"
Saroro Ilham ta tsaya tana kallonsu
"Eh naji ba amin gwaninta amma karta shigomin nan"
Mikewa Jawwad yayi ya karbo tray din hannunta
"Kiyi hakuri ILHAM kinji zedena ne nasan ba kyajin dadin abunda yake miki, nan gaba in ance yayi koda kudi baze miki ba"
Gyada masa kai kawai Ilham tayi tabashi tray din kayan tea ta koma
Gaban Jalal ya dawo ya zauna
"Bross Ilham kanwarka ce yadda kake treating dinta Sam be dace ba"
"To mekakeso in mata indinga goyata ko kuma in zauna ina mata dariya a hakanma kana ganin rashin kunyar da takemin har ta kalleni tace ni take so sa'anta ne ni?"
"Jalal Ilham itama yarinya ce, kuma so ba karya ne ba bazaka gane hakan ba se ranar da yai maka kamun kazar kuku"
"Naji labarin ya isheni haka, hadamin tea in sha"
Jawwad na cikin hada masa tea dinne Jalila takira wayar Jawwad
Murmushi yayi sannan ya daga wayar
"Sisyna am sorry nayi laifi ban kiraki naji yakike ba yau hankalina ne ba a kwance baya musabakar?"
Seda ta tura baki kaman tana gabansa
"Yaya Jawwad ta biyu fa nazo"
"Kai amma nayi murna, dole inzo Kaduna muyi celebrating"
"Wani celebrating bafa ta daya Nazo ba wai ta biyu"
"To ai kinyi kokari baby meye kuma na bata rai? Aini a hakan ma kinfiyemin Wanda yazo na daya"
  "Dan Allah ka aje wayar nan, ko kabani tea din in hada da kaina"
Jalal yai maganar a fusace

"Ohhh sorry bari in hada maka"
Jawwad yai maganar yana kashewa Jalal ido
  "Yayana kaida waye ne?"
Jalila ta tambaya
"Nida yayanki ne bashi da lafiya tun jiya yake fama da ciwon kai an masa allurai amma har yanzu kan bedena ciwo ba, shine zan hada masa tea yakemin masifa"
Dan tabe baki Jalila tayi

"Dama yana salla ne se ince ko beyi Azkar ba, to Wanda be salla ba ya za a tambayeshi yayi Azkar ma, kasan in mutum ya nisanta kanshi da Allah komai ma seya sameshi"
Dan kallon Jalal Jawwad yayi yaga idonsa a lumshe se yayi tunanin ko bayajin me Jalila take fada, amma tsaf yaji me tace
"Hmm Adduar ki kawai muke bukata baby"
"To Allah ya shirya ya bashi lafiya, ka kama kansa ka karanta mai bismillah kafa sha Tara se ka biya masa ma tayassara minal Qur'an"

"Godiya muke ya sayyada, Allah yakara hasken makaranta
Brother tashi ka karbi tea din"
Yafada yana Dan jijjiga Jalal
Tashi zaune Jalal yayi ya karbi tea din ya kai bakinsa ya Dan fara sha
"What!! tea naji kace"
"Eh tea zan bashi ya sha kinga yana da dumi"
"Waye ya hada tea din?"
"Ilham ce ta hada masa mana"
Jawwad yabata amsa

Dan tunani Jalila tayi
Meye yasa ta dinga faduwar gaba tun agurin musabaka har yanzu bashi taita ganin Ilham da sauri tace

"What Ilaham kuma? Karya sha tea din nan Yaya Jawwad ka karbe tea din nan"
Tafada cikin karaji

Share please
More comments more typing......

Comments dinku yayi kasa zanyi yajin typing 😈😈😈


🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️
[8/31, 8:26 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

    _ABDUL  JALAL_
           (2020)

      _WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
    (Daddy's girl)

               PAGE-  22&23
Chapter 18 · 0% Book details