← Book details Abdul Jalal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 24 OF 52

PART 1

Abdul Jalal Part 1 Complete Hausa Novel · about 14 min read

  _Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa,  ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.
Yanda nafara Allah yabani ikon kammala shi

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

Domin Samun karanta  wannan littafin yi magana ta what's app akan wannan lambar

07063065680
Kokuma addanna wannan link din domin samun novel din

🌹https://chat.whatsapp.com/EtB4KI52K0v5FQc2ELhidL

Gaskiya comments nakeso ba sticker ba kokuma Just thanks in bahaka ba zan dena typing kullum
Special thanks to my group members ina Alfahari daku comments dinku na bani karfin gwiwa
Dama dukkan masoya wannan novel ina alfahari daku ❤❤❤
     
        -My First Novel-

Not Edited

Kallonta Jalal yayi da mamaki ya kalli inda Ilham ta tarwatsa masa waya ya dawo da dubansa kanta
"Baze yiwu ba Yaya Jalal, kana wahal dani kana garani kawai dan nace inasonka amma kalli yadda wata take bayyana maka soyayyarta baka dau wani mataki ba amma ni kalli yadda kake wulakantani sau daya baka taba kallona da idon tausayiba
Meye laifina dan nace ina Sonka?"
Shi mamakima ya hana shi magana be ce mata kala ba ya durkusa yana tattara pieces din wayarasa, ya tattara ya nufi waje ze bata guri tazo ta sha gabansa
"Magana fa nake maka Yaya Jalal, let me tell you something wallahi kai nawane ni kadai babu wata Jaka data isa tayi takara dani wallahi kowace sena kauda ita gefe"
Hawayene ke fitowa daga Idonta wani irin kallon baki da hankali yayi mata ya kuma zagayeta da niyyar ya fita
Janyo shi tayi takuma tsayawa a gabansa ta kalleshi ido cikin ido cikin masifa tace
"Jalal baka isaba ina magana ka maidani mahaukaciya zaka tafi ka barni, I mean what I said wallahi, zan iya komai akan cinma burina, gara tun wuri ka gargadi zuciyarka kattayi gangancin fara soyayya kaidin nawane"
Bata rufe baki ba ya sauke mata maruka biyu masu kyau,
"Har kin isa ki tsaya a gabana kina gayamin maganganun dakika ga Dama, kin fasamin waya na kyaleki be isheki ba shine zaki tsaya a gabana kina gayamin abunda kika gadama ko yaushe ma nafara wasa dake, da kika iya tsayawa kina gayamin wannan haukan,"
"Wallahi kozaka kasheni na dena boye soyayyata a gareka koni ko ita wallahi"
Hannu yadaga ze kuma marinta
"Jalal meye haka kakeyi"
Jawwad ya karaso da sauri ya rike shi
"Haba Jawwad ba girmanka bane dukan mace, me tayi maka haka, kake dukanta"
Dawo da kallonsa yayi kan Ilham
"Ilham koma cikin Gida yi hakuri banni da shi tashi kikoma Gida"
Wani mugun kallo tayiwa Jawwad a ranta tace munafiki ai kasan komai amma a zahiri ta mike ta nufi cikin Gida tana kuka
"Haba Jalal me kayi hakane abunda kakewa Ilham yafara yawa gaskiya, koba komai kanwarka ce kuma mace ce, kadena dukanta hakan baze canza komai ba Fa"
Nunawa Jawwad wayarsa yayi
"Kalli abunda tayimin be isheta ba, ta tsaya a gabana tanamin hauka"
"Dukda haka kadinga hakuri, halin mata sekana hakuri, kasan shi so makahone waima tukuna, waima ya akayi wayarka taje hannunta har hakan tafaru?"
"Mtseww manta kawai"
Shine abunda Jalal ya fada kawai ya bi hanyar fita waje
Itakuwa Ilham tana zuwa cikin gida taga mummy a palour jikin mummy tafada tana kuka
"Ilham lafiyarki kuwa me akayi miki kike kuka,?"
"Mummy Yaya ne baya sona kwata² ya tsaneni, ni kadai nake sonshi mummy kiyi wani abu akai Dan Allah, zuciyata zata fashe"
Tausayinta ne Yakama mummy
"Is OK my dear, yi hakuri kidena kukan, Insha Allah Jalal bashi da matar data wuceki insha Allah, komai ze wuce"
"Mummy me nayiwa Yaya Jalal ne dabaya kaunata baya so naje inda yake"
"Bikiyi masa komai ba Ilham, haka dai halinsa yake na rashin son mutane, ya za ayi yace baya son mace kamarki, karya yakeyi, kidena kukan haka kar kanki yayi ciwo"
Haka mummy tai ta kwantarwa da Ilham Hankali

Maman Hanan ce hakimce akan kujera dauke da remote a hannunta, yayinda Hanan ta kwanta akan cinyarta tana kallon TV
Sallama Abdallah yayi yayan Hanan
Sannan yasamu guri ya zauna
"Da girman kujerarki mum barka da Gida"
Ya mutsa fuska tayi ta nisa
" "Yar uban waye ta dakarmin yarinya kunje kaida daddyn Ku amma ba wani mataki daya dauka, waye ubanta a garin nan"
Kallonta Abdallah yayi da mamaki
"Ohh I think dad has already closed this case, meyasa kike kokarin dawo da maganar nan, an sulhunta komai"
"Dalla yimin shiru, a gurina be wuce ba tambayarka kawai nayi Yar inace waye ubanta?"
Tai maganar cikin fushi
"Amm Mum Dan Allah kiyi hakuri zancen nan ya wuce wallahi kanwar abokina CE, kuma mum dinta tabada hakuri sosai, tundaga kano Wan babanta ya taho yau duk Dan subada hakuri fa, to mu suwaye daba zamu hakura ba"
"In kaga ma yimin nasihar tashi kabarmin parlour"
Be kuma cewa komaiba ya fice
Hanan ce takuma fashewa da kuka "mummy ciwon zafi yakemin kaina se ciwo yake wallahi ni ban hakura ba"
Tayi maganar tana kuka
"Yi shiru mana sannu, nima ba hakuran nayiba ai, ai jininki baze zuba a banza ba nasan matakin dazan dauka"

Abbane ya fito ze tafi, Jalila tafito da sauri daga dakinta tana kallonsa domin jin wani hukunci aka yanke akanta
Siyama ce tabiyo bayanta itama
"To se yadda ta yuwu, ummu Jalila ki hada mata kayanta in Allah ya kaimu sati me zuwa koni ko Jawwad zamuzo mu tafi da ita, tunda bata jin magana"
Abban Jawwad yayi maganar yana kallon Ummi
Kuma fashewa da kuka Jalila tayi
"Ummi nace na dena fa bazan kuma ba Dan Allah kiyi hakuri"
Girgiza kai Abba yayi
"A a senaga kindena din tukuna, a yanzu dai ban yaddaba zuwa sati me zuwa insha Allah in kin canza halinki, shikenan ta fiya kano bayan zuba"
Gyada kai tayi tana goge hawaye itakam Ummi banza tayi mata taki kulata
"Abba insha Allah bazata karaba ta dena"
Cewar siyama
"Anya kuwa wannan kawar taki batta kawai akwai rashin ji"
Abba yafada yana nuna Jalila
Haka Jalila ta cigaba da kuka tana magiya akan suyi hakuri
Abba yayi musu sallama ya koma, kano yayinda still Ummi taki kula Jalila
Abun duniya ya ishi Jalila, Jalila tayi trying lambar Jawwad har tagaji amma akashe
"Haba Yaya Jawwad kaima Fushin kake dani haka, shikenan kowa ya tsaneni"
Haka dai Jalila ta cigaba da sake² aranta tana kuka

Hannah ce take ta trying lambar Jalal taki shiga tayi messages din ba adadi amma shiru
Layin Jeje ta kira
"Da girman kujerarki, gimbiya sarautar mata farar mace Alkyabbar mata, Zara acikin mata, daya tamkar da goma, tauraruwa me wutsiya ganinki ba alheri ba"
Murmushi Hannah tayi da jin wannan kirari da jeje yake mata
"Jeje ya akayi ne dazu muna cikin waya da Jalal naji ta dauke nayi trying tun dazu wayar bata shiga"
"Wow har ya fara yadda ya amsa wayarki kice tarkon ya fara kamashi"
"Ina fa da sauran aiki Ja wallahi, shammatarsa kawai nake naji ya daga wayar, yanzu dai yana ina ne?"
"Nima bansan inda yake ba rabona dashi tun last week, wannan mayen ya hanashi zuwa inda nake"
"Allah sarki simple dashi abokin nasa da akansa zanyi aikin nan da yanzu nakusa nasara, shikam taurin Kaine dashi"
Dariya jeje yayi
"Lallai baki San Jawwad ba zahirinsa kika gani, tsawon shekaru shiya hana aikinmu tafiya yadda ya kamata anyi masa barazanar amma, bashi da niyyar hakura duk abunda kikayiwa Jalal, kai tsaye kamar kinyiwa zuciyar Jawwad ne"
"Tab amma gaskiya yana kaunar JALAL, yanzu dai ka bincikomin inda Jalal yake, inason zuwa"
"To bari in jarraba"

Jawwad ne yabi bayan Jalal
"Yanzu dai kayi hakuri zomuje se a siyo wata wayar"
Bece komaiba yabi Jawwad sukaje suka siyo sabon waya, yabada wadda Ilham ta tarwatsa aka gyara, domin ya kwashe abubuwansa masu mahimmanci na kan wayar, wayar ta daku, Dan karfinta Ilham tasaka ta buga wayar,
  Jawwad ne ya dakko wayarsa don kiran Abba yaji koya dawo, seyaga wayar tasa akashe, be tunanin komaiba ya kunnata Abba ya kira yaji ko yakaraso, yace masa yana hanya.
Ya kashe kiran kenan message ya shigo wayarsa
Jalila ce ta turomasa message,
   "Yaya kaima fushi kake dani 
     Shikenan kowa yatsaneni
     Abba yayi fushi, Ummi ta     
     Dena kulani, Dan Allah kai
      Kar kayi fushi dani"
"Allah sarki sisyna ni Sam bana fushi dake"
Jawwad yai maganar a fili Jalal da yake driving ya Dan kalleshi ya basar
Jawwad ne yaketa kokarin kiran Jalila amma taki dagawa, be fushiba haka ya dinga kiranta har daga karshe ta daga tana daga wayar sautin kukanta yaji
"Yaya  Jawwad kaima fushi kake dani ko? Nakiraka dazu ka daga kaki magana daga baya kuma ka kashe wayarka"
"Nidin Jalila? Ni na isa in miki haka sedai matsalar network, a duniya banga laifin dazakiyi min in ki daga wayarki ba baby"
"Yaya Jawwad Ummi sunyi fushi dani wai se sun dawo dani kano, Dan Allah kabawa Abba hakuri,"
"Kai sisy to meye a ciki kinga seki dawo kusa damu naji dadin hakan"
Cikin shagwaba tace
"Ni wallahi, Yaya bana son zaman kano, ni nafi son zama a gurin Ummi"
"Hmm mune ba kyason zama damu ko"?
"A a Yaya nifa bahaka nake nufi ba, Ummi tace wai in na dawo kano garinsu zata koma"
"No, calm down sisy, dena kuka nan is OK ko so kike nima kisani kukan, bana son kukan nan"
Jalal da haushi ya isheshi Hannu yasaka ya fizge wayar daga hannun Jawwad
"Kana ta shirme da yarinya ko kunya bakaji, se wani shagwaba take kana lallabata"
Jawwad ne ya bishi da kallon mamaki
"To ina ruwanka dani so kake in kyaleta taita kuka in kanta yayi ciwo fa?"
"A'a bindiga kan nata zeyi ba ciwo ba, kukan dadi take da sojoji basu karairayota sun zubowa Abba a boot ba yakawo maka"
"To naji ban wayata"
Kashe wayar Jalal yayi,
"Na hana in munkoma Gida idan nabar gurin seka cigaba, kokuma in baka wayarka in tsaya ka sauka, seka samu gurin zama a titi, ka cigaba da shiriritar"
"Yanzu kiri² bazaka bani wayata ba"?
"Eh bazan bayar ba"
"Allah sarki baby, nasan kukan zata cigaba, Dan Allah kabani in rarrasheta"
"Aiko sedai ta mutu, in seka rarrasheta zata dena"
"Shikenan zan ramane"
Haka suka tafi Gida suna tafe suna fad'a
Memakon  Jalal ya kaisu Gida se ya canza hanya
"Ina kuma zamuje"
Jawwad ya tambayeshi
"Yunwa nakeji ice-cream kawai zan siyo ko fura"
"Kwadayayye kawai"
"Eh naji kwadayayyen ne nasan duk haushina kake ji Dan na hanaka waya, kuma bazan bayarba"
Yasa hannu ya dau wayar Jawwad, ya bar wayoyinsa sabuwa da tsohuwar a cikin mota ya bude motar ya fita

Dan murmushi Jawwad yayi
Jalal kaima ai rigimammen ne
Jawwad ya furta hankali

Jeje tun dazu se trying lambar JALAL yake amma baya shiga
Yanzun ma kuma trying yayi by luck wayar ta shiga
Jawwad dake kashingide a cikin mota yaji wayar Jalal tana ringing da ya duba ba suna ya daga yasa a kunnensa ba sallama ba komai Jeje yafara magana
"Ina ka shigane tun dazu nake kiran wayarka amma yaki shiga"
"Sorry ba shi baneba wayarsa ce ta Dan samu matsala"
Jeje yagane muryar Jawwad amma alamu ya nuna shi Jawwad be gane shiba Dan da ya ganeshi baze daga wayarba ma
"OK Dan Allah yana ina yanzu"
"Mun Dan fita dashi, yanzu muna kabuga ya Dan fita ne yanzu zamu karasa Gida insha Allah"
"OK nagode"
"Wa zance masa?"
"No bakomai zan kuma kira"
"OK"
Jawwad ya katse kiran

Jeje ne ya kira Hannah a waya
Bugu biyu ta dauka
"Ya"?
" ke kin ban wahala gaskiya tun dazu nake kiransa a waya se yanzu na same  shi a waya, shima ba shi ya daga ba mayensa ne ya daga wai wayar Jalal dince ta lalace, sun Dan fita yanzu zasu koma Gida"
"Au nice ma nasaka wahala kamanta aikin naka ne?"
"Hakane fa tuba nake me idon zinari"
Murmusawa Hannah tayi
"Weldon yanzu kuma zanyi nawa aikin, zan Dan jefa masa fargaba a zuciyarsa"
"Meye shirin naki?"
"Ba ruwanka kai dai zuba ido"

Jawwad yafara gajiya da zaman jiran Jalal
"Kome ya tsaya yi oho"
Jawwad yai maganar tareda duba wayar Jalal don ganin lokaci message ne yake shigowa wayar


  "Yau kaki daga wayata, ka jefa Zuciyata cikin matsala, ko Abinci nakasa ci dan haka Kaima zan saka taka zuciyar a damuwa Ina hanyar zuwa gidanku
Zakazo ka sameni a gidanku
Cikin dakinka, kuma komai
Ze iya faruwa in aka ganni a
Dakinka, in baka son hakan
Ya kasance mu hadu a  
Restaurant din damuka hadu
Da farko mintuna goma sha
Biyar kawai kake dashi
          From your lovely bae
           (Hannah)

Wannan wace irin jaraba ce, haka Jalal yai maganar hankalinsa a tashe, bayaso sunan Jalal ya kuma baci, da sauri yayi dialing number da aka turo message din da ita amma taki dagawa,
Yasalam Jalal ina ka tafine ana shirin jefaka cikin matsala

Daren ranar ma Jalila batayi ishashen bacci ba ko abinci taki sakin jiki taci, Ummi se rayuwarta take ita kadai ba tare da ta shiga sabgar Jalila ba dukda a cikin zuciyarta bata jin dadin abinda takewa Jalilan amma yazama dole ta nuna mata bacin ranta akan abunda Jalilan takeyi
   Washe gari da safe Jalila haka Jalila ta shirya ta tafi makaranta, tana zuwa yan ajinsu yan son jin gulma sun so su tambayeta yadda akayi amma ba fuska ta hade rai se muzurai take, suna tsoron su tambayeta suma ta juye musu kwandon bala'i
Mummy Hanan dakanta tare da wasu sojoi Guda biyu suka kawo Hanan makaranta cikin wata CRV me tint glass, sojoji guda biyu na gaban motar, sun dan jima a kofar makarantar koza suga wucewar Jalila amma basu ganta ba daga baya, mummy tace Hanan ta shiga school ita tasan abunyi
Tsakanin Jalila da Hanan ba Wanda ya kula wani, duk yanda yan aji sukaso jin gulma basu samu dama baa

bayan tafiyar Hanan ba dadewa sega malama ramatu an sauketa a napep zata shiga cikin makarantar
Dan sauke glass mummy Hanan tayi
"Sannu dai"
Mummy Hanan tafada cikin ISA da iyayi
Malama ramatu na ganin mota
Ta washe baki da durkusa
"Yawwa sannu madam ina kwana"
A dan wulakance mum Hanan ta amsa
"Yawwa lafiya, if u don't mind please I have an issue to discuss with you"
"A a ba wata damuwa, madam ina jinki"
Alama tayiwa malama ramatu data shigo cikin mota
Ba tayi tunanin komai ba ta shiga
Mummyn Hanan ta numfasa
"Da alama kema staff ce a school din nan ko?"
"Yea of course"
"Good, kinsan case din da akayi a school din nan da akayi fada tsakanin dalibai biyu aka daki yarinya Yar gidan captain rasheed "
Se a lokacin malama ramatu ta kalli suwaye a gaban motar taga sojoji nan take ta sha jinin jikinta
"Emm...e..eh nasani madam amma wallahi bana gurin akay...."
"Inma kina gurin ke kikasani tambayarki zanyi kikamin karya, zaki gane kurenki ne"
"Zanma fadi gaskiya wallahi"
"Wacece Jalila Aliyu Imam Yar uban waye ita?"
Nan take malama ramatu ta karkace ta dinga rattaba bayanin karya da gaskiya
"Ba Yar uban kowa bace ba, a sanina ma bata da uba, amma naji ana wai ya mutu ko karya akema ohoo, daga  ita se uwattta suke zaune baata da wani gata, se tsabar iskanci da Neman rigima"
Haka taita zuba, kaman ruwa ba comma ba full stop
"Ke surutun ya isa haka bani address din gidan su"
Malama ramatu ta bata address
Maman Hanan Tabawa malama ramatu 5k a wulakance sukaja mota sukayi gaba

Kuma trying lambar Hanna Jawwad yayi da wayar Jalal
seda taja aji, azatonta Jalal ne sannan ta daga cikin yanga tafara magana
"Baby lokacinka ya fara karka dauka da wasa nake wallahi dagaske nake in samu haduba gidanku zanje"
"Amm Hanna ba  JALAL bane nine Jawwad dan Allah karkiyiwa Jalal haka, dama yan anguwa sun samasa ido, yanzu in kikayi haka zaki kara bata masa suna kisa akuma tsanarsa dan Allah karkiyi haka duk abun Jalal baya bin mata kuma mahaifinsa yana gari in ya ganki bazeji dadi ba"
Nisawa Hannah tayi
"Jawwad dan uwanka yafiye taurin kai yaki karbar bukata ta, gara in biyo masa ta inda yakamata, mintuna sha biyar ne kacal daku, in bakuzoba wallahi zanyi shigar danaga dama ince karuwarsa ce ni kuma har Gida xanje, ko dayake nasan hakan ba lallai yabata masa ba but at least ze gane da gaske nake, ganinsa kawai nakeso nayi in samu sauki a raina, zabi ya rage naku dan uwa na gari"
Ta kashe wayar
"yasalam wannan wane irin abune, Allah ya fidda kai sharrin wannan yarinyar Jalal, ohhh gara muje mu sameta karta bishi Gida daddy bazeji dadi ba dama ga yan unguwa sunsawa Jalal ido, inaga kuma aga karuwa taje gurinsa "
Jawwad ne Ya bude motar da sauri ya fita Neman Jalal

Ko islamiyya Jalila ba taje ba, kuma Ummi batace ta shirya taje ba, ta kyaleta idonta duk ya kumbura saboda kuka
"Allah sarki baby na banajin dadin ganinki a haka amma kedin ce Zuma seda wuta, gara in horaki" Ummi tayi maganar a zuciyarta
Da yamma likis su Jalila sukaji tsayuwar mota a kofar Gida, Jalila tana tsakar Gida ta zurawa Ummi ido kaman bata Santa ba, Ummi tanaa shan fura,

Cikin izza sukaji sallama
Ummi ce ta amsa sallamar tare da jiran shigowar Wanda yayi sallama
Jalila tana zaune bata amsa sallamar ba balle ta motsa daga inda take,
"Sannu da zuwa shigo"
Ummi tayi maganar tana mikewa tsaye bata gane matar ba tayi zaton irin customers dinta ne
"Ba zamane ya kawoni ba"
"To lafiya meyafaru?"
Ummi ta tambaya
"Nasan baki sanni ba nice Hajiya Safiyya Mrs. Captain Rasheed "
Da sauri Jalila ta daga kai tayi arba da Hanan da mamanta
Maman Hanan ce ta janyo hannun Hanan
"Kalli duba ta'addancin da y"arki tayi kina tunanin kunci bulus ne?"
Gaban ummine ya fadi da taga Hanan

Share please
More comments more typing............
Ina alfahari da masoyana da masu yi min addua ina godiya ❤❤❤
Masu bukatar shiga group dina akwai link din group din Asama amma akwai dokoki

🖊️🖊️🖊️🖊️🖊️
[9/12, 6:02 AM] +234 816 830 7871: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

    _ABDUL  JALAL_
           (2020)

      _ STORY & WRITTEN BY AISHAHUMAIRA_
    (Daddy's girl)

               PAGE-  26
Chapter 24 · 0% Book details