ABOUT THIS BOOK
Description
“sallama ta a gare ka, ma’abocin kyau da tsafta, barka da isowa Habiby.”
ta yi maganar lokacin da ta iso inda ya ke tsaye a kofar gidansu,
“barkanki dai Baby, yana same ki.”
ya na maganar ya jawo ta jikin shi, bakin shi ya kai tsaitin kunnenta, ahankali ya furta,
“tun ranar da na fara magana da ke, zuciyata ta samu natsuwa, ke ce addu'ar da ban san ina yi ba, amma Allah ya amsa min, muryarki tana kwantar min da hankali, idan kina kusa, komai yana yin kyau ina sonki Baby.”
ajiyar zuciya ta sauke, kalamanshi na rasa kowani gaba na jikinta,
“Thank you for coming into my life Baby, alamu sun tabbatar min da yanzu ne zan san dadin rayuwa da kuma dadin dake cikin soyayya.”
kama fuskarta ya yi cikin tafukan hannayen shi, suna kallon juna cikin ido ta hasken farin watan da ya haske wajen,
“let me go Baby, I got something to do now, dama zu dai na yi in ganki.”
bata fuska ta yi, “tun yanzu Baby, gaskiya ni ban gaji da ganinka ba.”
“to me zaki ban idan na tsaya?.”
ya yi maganar da tunanin Allah yasa ta amince da bukatar shi, dan dama abun da ya kawo shi kenan, ba wata soyayya ba,
dan shuru ta yi kamar mai nazari kafin tace,
“What do you want.”
“ko me nike so zaki bani?.”
“eh,me zai hana.”
“promise.”
ya mika mata hannunshi alamar ta yi alkawarin, daura nata hannun ta yi tana fadin,
“Promise.”
“ke nike bukata.”
idanu ta zaro tana kallon shi, bawai dan bata yi tunanin jin haka daga gare shi ba, Aa sai dan tana ganin hakan ya yi wuri, bugu da kari kuma a inda suke,
“saboda son da ni ke miki ne Baby, ina sonki ba tare da sharadi ba,ina son ki da gaskiya, da hakuri, da niyya ta har abada, idan duniya zata juya miki baya, ni zan tsaya a gefenki Domin zuciyata ta riga ta zabe ki, ki saki jikinki mu zama abu daya, dan ni na riga na zabe ki, kuma bazan taba gudun ki ba,”
“amma fa kada ki damu, idan baki bukata bazan miki dole ba.”
“no Baby kada ka damu ai ba komai.”
Anan kofar gidan suka shiga aikata masha ar su ba tunanin kada wani ya gitta ya gansu ko iyayenta su fito balle kuma tsoron mai duka dake sama yana kallon su,
***************
a cikin gidan ko, mahaifinta ne ya fito daga daki yana tambayar Mahaifiyarta dake kwance,
“Hauwa, ina Farida take?.”
juyowa matar da ke kwance ta yi, tana kai kallonta ga dattijon da ke tsaye,
“tana waje.”
ta amsa tana mayar da kanta ta kwantar,
“ban gane tana waje ba, yanzu fa shabiyu na dare, me take yi waje?.”
“Malam yanzu fa yariyar nan ba budurwa bace, idan kace zaka rinka mata irin takurar da ka mata da tana budurwa, ta ya zata iya tsayuwa da kafarta, ko zaka biya Bilal kudin shi ne?, ha ah ba ka bari yariya ta nemi kudi ba, kuma kai ba bata zaka yi ba.”
“haba Hauwa, kina sane fa da yariyar nan akwai aure kanta, amma zaki ringa goya mata baya akan duk abun da ta ga damar yi.”
“to so kake in barta ta zauna duk mu taru mu lalace, Ah’ah abarta ta nema.”
“yanzu wannan rayuwar da take yi, yau a ganta da wannan gobe a ganta da wancan, shine dai-dai?.”
“baka ji masu iya magana na cewa, hannu da yawa maganin kazamar miya ba, ai waka daya bata kai tsafe, dole sai ana yi ana canza wa, sannan idan ka manta in tuna maka, yariyar nan fa furucinka na aiki a kanta, ko ka manta kai mahaifi ne a lokacin da ka mata baki.”
“Hauwa ai inde a haka ne to baki na bazai taba dakatawa da yin furuci akan yarki ba.”
shigowar Farida gidan ya dakatar da mahaifiyarta furta maganar da ta ke da niyar furtawa,
daga kofar gidan ta tsaya tana kallon, mahaifinta dake jifanta da mugun kallo, ganin ya nufo inda take, yasa ta rugawa da gudu ta shige dakinta hadi da rifo kofar,
“shegiya wasassiya, wallahi Farida karshen ki ba zai yi kyau ba idan dai har ba zaki ji maganar iyayen ki ba.”
“Aa fa, maganar ka de, dan ni kam tana jin nawa, kuma ni wallahi ban ga wasassiya ba, sannan da wannan cikin nawa na dauke ta har tsayin wata tara, kuma kai shaida ne akan yadda aka yi na dauki cikin, to ta ina ta zama shegiya.”
Comments
Sign in to comment.