Sashe 1
Zamanin Mu Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ZAMANIN MU
AUTHOR
Najaatu Muhammad kamuna
👸🏻Queen mk👸🏻
BRAIN IN PEN WRITERS TEAM✍📚
marubuci zababben mutum ne da ake zaben shi dan sauya rayuwar al'umma ta hanyar amfani da kwakwalwa zuwa alkalami
B.I.P.(🤝hadin kammu shine nasarar mu.👊)
“Gajeren labari ne, dan Allah a tsaya a saurara, zai amfanar musamman ga iyayen mu dake tunanin da sun aurad da yaro shikenan sun sallame shi,sun gama bashi tarbiya ba ruwanku kuma da rayuwar shi, ta bangaren mata kuma, wasu iyayen na tunanin da sun yi ma yariya auren fari, kaddara ta gifta auren ya mutu ta dawo gida, shikenan sa idon su a kanta ya kare, ta na da damar yin duk wani abun da take so tunda yanzu ita ba budurwa bace,
“Wasu bangare a labarin true life story ne, wasu kuma kirkira ne dan sakon da nike son isarwa ya isa yadda ya kamata,”
Wannan littafin sadaukarwa ne ga iyayenmu.
BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM
ꨄFARKO.…
Kwance take a cikin dakin da ya kasance mallakinta tun tana budurwa, har izuwa yanzu da aurenta ke kan iska yana yawo, waya ce manne a kunnenta, wanda da alama magana take yi,
“Baby kace yau zamu hadu, gashi yanzu har karfe goma baka zo ba, kuma ni gaskiya idanun na na begen sake saka ka cikinsu, kasan fa na kamu sosai Baby.”
daga daya ban garen, saurayin dake zaune a kofar gidan da yake mallakin shi ya amsa da,
“ku mata kuna ban mamaki, haduwar jiya da dare shine har kike rawar jiki haka, kuma ina da tabbacin ko a hanya kika ganni ba zaki iya shaida fuskata ba.”
“Baby kenan, ai soyayyar gaskiya bata bukatar dogon lokaci kafin ta kama mutum, kuma bata bukatar ganin fuska, kyawon jiki, ko nasaba da arzikin hannun mutum, kar ka yi mamaki akan son da nike maka, dan zan iya yin komai saboda abunda nike ji yanzu a kan ka.”
jin furucinta na karshe, yasa shi sakin murmushi, da bukatar ya canza niyar shi a kanta, dan alamu sun nuna tarkon shi abu biyu ya kama a masayin daya,
“Na gode da kauna Baby, kiban 15mn yanzu zaki ganni gidanku.”
murmushin jin dadi ta yi, tana mikewa zaune daga kwancen da take,
“zan kasance cikin dakon zuwanka, har izuwa lokacin da idaniya na zasu yi tozali da kai, ina fatan allah ya kawo min kai lfy.”
“ameen Baby, I love you.”
“I love you more Baby.”
ta amsa tana sakarma wayar kiss
bayan ta kashe wayar, mikewa ta yi, ta rage kayan jikinta single zani ta daura, ta fita da niyar ta yi wanka, a sakar gidan ta iske mahaifiyarta kwance daga saman faranda, da yake lokacin zafi ne ana kwanan waje, ba tare da ta magantu ma mahaifiyar tata ba ta dauki bokiti ta isa bakin rijiya, ruwa ta ja kafin ta dauka ta shige toilet din da ke daga gefen sakar gidan,
***
Ata bangaren saurayinta kuma tana kashe wayar WhatsApp message na shigowa wayar, da sauri ya shiga dan dama a WhatsApp din ya ke kiranta ya shigo, bude sakon ya yi, murmushi ya yi bayan ganin abun da sakon ya kunsa, yadan yi shuru kamar mai tunani kafin ya fara rubutu kamar haka,
“7hundred thousand zaka bayar tunda 5m kake so, tun da ni zan tsaye sauran turaruka da za’a yi amfani dasu, kai dai kawai ka tabbata ka tanadi duk abubuwan da na fada maka, nan da kwana ukku kudadenka zasu kammala, naka dauka ne kawai.”
ya tura sakon, sannan ya sake yin typing din account no din shi ya tura, sun dan sake yin magana da wanda ke turo sakon, kafin wucewar 4mn saiga Alert ya fado wayar shi, dubawa ya yi, nan yaga Tree hundred thousand, murmushi ya yi, yana juya bayan wayar ya zare sim din daga wayar ya karya ta biyu ya wurgar, bayan ya yi transfer din kudin ta ainihin account din shi, mikewa ya yi ya shiga cikin gidan, koda ya shiga dan madaidaicin parlorn shuru ba kowa, yasan matarshi da d’anshi sun yi bacci, dan haka juyawa kawai ya yi ya fita,
********
“sallama ta a gare ka, ma’abocin kyau da tsafta, barka da isowa Habiby.”
ta yi maganar lokacin da ta iso inda ya ke tsaye a kofar gidansu,
“barkanki dai Baby, yana same ki.”
ya na maganar ya jawo ta jikin shi, bakin shi ya kai tsaitin kunnenta, ahankali ya furta,
“tun ranar da na fara magana da ke, zuciyata ta samu natsuwa, ke ce addu'ar da ban san ina yi ba, amma Allah ya amsa min, muryarki tana kwantar min da hankali, idan kina kusa, komai yana yin kyau ina sonki Baby.”
ajiyar zuciya ta sauke, kalamanshi na rasa kowani gaba na jikinta,
“Thank you for coming into my life Baby, alamu sun tabbatar min da yanzu ne zan san dadin rayuwa da kuma dadin dake cikin soyayya.”
kama fuskarta ya yi cikin tafukan hannayen shi, suna kallon juna cikin ido ta hasken farin watan da ya haske wajen,
“let me go Baby, I got something to do now, dama zu dai na yi in ganki.”
bata fuska ta yi, “tun yanzu Baby, gaskiya ni ban gaji da ganinka ba.”
“to me zaki ban idan na tsaya?.”
ya yi maganar da tunanin Allah yasa ta amince da bukatar shi, dan dama abun da ya kawo shi kenan, ba wata soyayya ba,
dan shuru ta yi kamar mai nazari kafin tace,
“What do you want.”
“ko me nike so zaki bani?.”
“eh,me zai hana.”
“promise.”
ya mika mata hannunshi alamar ta yi alkawarin, daura nata hannun ta yi tana fadin,
“Promise.”
“ke nike bukata.”
idanu ta zaro tana kallon shi, bawai dan bata yi tunanin jin haka daga gare shi ba, Aa sai dan tana ganin hakan ya yi wuri, bugu da kari kuma a inda suke,
“saboda son da ni ke miki ne Baby, ina sonki ba tare da sharadi ba,ina son ki da gaskiya, da hakuri, da niyya ta har abada, idan duniya zata juya miki baya, ni zan tsaya a gefenki Domin zuciyata ta riga ta zabe ki, ki saki jikinki mu zama abu daya, dan ni na riga na zabe ki, kuma bazan taba gudun ki ba,”
“amma fa kada ki damu, idan baki bukata bazan miki dole ba.”
“no Baby kada ka damu ai ba komai.”
Anan kofar gidan suka shiga aikata masha ar su ba tunanin kada wani ya gitta ya gansu ko iyayenta su fito balle kuma tsoron mai duka dake sama yana kallon su,
***************
a cikin gidan ko, mahaifinta ne ya fito daga daki yana tambayar Mahaifiyarta dake kwance,
“Hauwa, ina Farida take?.”
juyowa matar da ke kwance ta yi, tana kai kallonta ga dattijon da ke tsaye,
“tana waje.”
ta amsa tana mayar da kanta ta kwantar,
“ban gane tana waje ba, yanzu fa shabiyu na dare, me take yi waje?.”
“Malam yanzu fa yariyar nan ba budurwa bace, idan kace zaka rinka mata irin takurar da ka mata da tana budurwa, ta ya zata iya tsayuwa da kafarta, ko zaka biya Bilal kudin shi ne?, ha ah ba ka bari yariya ta nemi kudi ba, kuma kai ba bata zaka yi ba.”
“haba Hauwa, kina sane fa da yariyar nan akwai aure kanta, amma zaki ringa goya mata baya akan duk abun da ta ga damar yi.”
“to so kake in barta ta zauna duk mu taru mu lalace, Ah’ah abarta ta nema.”
“yanzu wannan rayuwar da take yi, yau a ganta da wannan gobe a ganta da wancan, shine dai-dai?.”
“baka ji masu iya magana na cewa, hannu da yawa maganin kazamar miya ba, ai waka daya bata kai tsafe, dole sai ana yi ana canza wa, sannan idan ka manta in tuna maka, yariyar nan fa furucinka na aiki a kanta, ko ka manta kai mahaifi ne a lokacin da ka mata baki.”
“Hauwa ai inde a haka ne to baki na bazai taba dakatawa da yin furuci akan yarki ba.”
shigowar Farida gidan ya dakatar da mahaifiyarta furta maganar da ta ke da niyar furtawa,
daga kofar gidan ta tsaya tana kallon, mahaifinta dake jifanta da mugun kallo, ganin ya nufo inda take, yasa ta rugawa da gudu ta shige dakinta hadi da rifo kofar,
“shegiya wasassiya, wallahi Farida karshen ki ba zai yi kyau ba idan dai har ba zaki ji maganar iyayen ki ba.”
“Aa fa, maganar ka de, dan ni kam tana jin nawa, kuma ni wallahi ban ga wasassiya ba, sannan da wannan cikin nawa na dauke ta har tsayin wata tara, kuma kai shaida ne akan yadda aka yi na dauki cikin, to ta ina ta zama shegiya.”
“Hauwa ki bi ahankali, dan zanin aro bai rufe katara, wannan hanyar da kuka zabar wa kanku bazai bulle muku ba.”
“idan ba’a daura da kyauba ko?.”
ganin maganar shi bata da amfani yasa ya koma daki, zuciyarsa fal takaicin irin rayuwar da ake gudanarwa a gidansa.
**************
zaune yake acikin parlorn gidan da har yanzu yake shuru ba motsin komai sai na fregje da AC dake aiki
“yanzu ka tura min 1.5m, ni zan mayar maka da 2m, kamar dai yadda muka saba, ina baka riba ko wani lokaci.”
daga daya bangaren, aka amsa da, “ok ka tura account, zan sa yanzu.”
“kasa ga account din da na tura maka last time.”
da haka ya ajiye wayar yana jawo kwalbar alcohol ya kai bakin shi sai da ya sha sosai sannan ya sauke yana yasina fuska, sigarin dake cikin hannun shi ya kai bakin shi nan ya shiga zukanta kamar an aiko shi, kafin wucewar 10mn har ya zuke kwali guda kalbar wen din nan ko har ya karar da ita, cikin mayen da ya fara dibansa ya ji shigowar message, ba tare da ya duba ba ya zare sim din ya jefa bakinsa sai da ya taune sannan ya tofar, anan parlorn kan carpet ya yi bacci.
*************
“Balkisu kar ki fita daga gidan nan.”
“Mamammu idan na tsaya zaki bani abun da nike bukata ne?.”
ba tare da ta tsaya daga tafiyar da take yi da niyar fita daga gidan ba ta amsa,
“Balkisu wai me kike son mayar da kanki ne?, ta wannan hanyar ne kadai zaki nema, Balkisu ki guji bakin duniya.”