← Book details Zamanin Mu Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 3

Sashe 2

Zamanin Mu Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tsayawa ta yi ta juyo, ta kalli dattijuwar dake tsaye a kofar daki,

“wai nikam Harira, yaushe ma daren ya yi ne da zaki kai loma a ido, wannan yar iskar idan ta fita jikinki ta ke kaiwa ne ko me?, da kullum kike damun mutane da wa’azi.”

maida kallonta ta yi ga Mariya kishiyar mahaifiyarta da ta yi maganar , itama tsaye take a kofar kitchen, dan itace da girki,

“dakata war me kika yi, tafi mana ko wani ya rike ki ne, tafi kodan wannan shegen da kika ajiye.”

kallonta ta kai ga yaron da ke tsaye gefen matar da ta kira Mammamu, tana jin wani kuna a zuciyarta,

“d’ana ba shege bane, dan da ubansa, kuma wallahi duk matar da ta sake sheganta min d’a zata ga true color dina.”

dariya Lami ta yi tana taba hannu, tace,
“sabon salo gemu a kafada, waushe shege ya taba zama d’a, balle kuma wannan da ko sanin ubansa ba’a yi ba.”

“ke ko Lami, ai ba wanda zai dafa kaza ya yar, ko kin taba ganin inda hannun mutum ya rube ya ya yanke ya yar, barta ta so d’anta ba ita ta haifesa ba.”

“kowa yasan ta hanyar aure na haihu, shikenan dun Allah ya raba sakani na da mijina shine d’ana zai zama shege? to ban gani ba kuma bazan gani ba, kuma wallahi ko wace mata ta rike girmanta.”

“d’an da tun yana ciki ubansa ya sheganta sa, kuma aka rasa wanda za’a cinnawa, hmmm ayi dai ma gani yadda barahuni zata tuya kosai.”

Baba na zaune daga kofar dakinsa duk budurin da ake yi a gidan yana jinsu kuma yana kallo, amma ya yi burus da su.”

“kiyi hakuri Mamammu amma zan fita.”
tana fadin haka ta sa kai ta fice daga gidan,

bayan fitar ta daga gidan bakin titi ta isa, ta tsaya tana jiran abun hawa, bayan kuma ta san ko nera biyar ba ta da, tana nan tsaye wani mai mashin ya tsaya gaban ta yana fadin, “tafiya ne?.”

“Eh tafiya ne,daba zaka kaini.”

“Ok kudinki dubu daya.”

“ah haba malam dubu fa, kamar zamu bar gari, kai baka daya daga cikin mazan da basu karbar kudi daga hannun macce mai kyau ne?.”

tayi maganar tana murmus
kallonta ya yi, gaskiya kam kyakkyawa ce, ba laifi,

“bazan ce eh ba dan kin san kamawa ta ke yi.”

“to yanzu dai muje ai bazamu rasa na yi ba.”

ta fadi tana hawa mashin din.

*****************

safiyar Alhamis, zaune ya ke a cikin shagon p o s din da ya bude dan ganin dama da kuma kauda hankalin mutane akansa, tare ya ke da abokinsa Husain,

kallonsa Husain ya yi, yace, “wai Kabeer mene sirrin ne, kaga yadda kake hutawa ko, baka rasa komai ba, ni gani nan zaman ya isheni, dan buga-bugan da mutum keyi yanzu ya daina tafiya.”

dagowa Kabeer da hankalinsa ke kan wayarsa da yake chatting da Farida ya yi ya kalli Husain,

“Husain wannan sirrin abar mana kayan mu kawai.”
“Aa kamar ya a bar muku kayan ku, baku son wani da karuwa kenan?.”

“ba haka bane, aikin ne da wuya, kuma yana bukatar sirri.”

“kai Malam, kawai bani insha, Allah na tuba wani irin wahala ne bamu gani ba da idanun nan namu, sirri kuma kazo gidan shi.”

ajiye wayar hannunsa ya yi, ya dau dayar dake ajiye, kudin da Farida ta nema hannunsa ya yi mata transfer, sannan ya mayar da wayar ya ajiye yana maida hankalinsa ga Husain, da ganin abun da Kabeer din ke yi ya sake jan hankalinsa ga son fara ko wani irin aiki ne ma Kabeer din ke yi,

“kasan wayan da ake cema yan Malam-Malam?.”

muryar Kabeer ta ankarar da Husain,

“ni ko na san su, tunda sun damfare ni dubu darin da na dau watanni fin bakwai ina tarawa, kuma ma kaf garin nan yanzu waye bai san su ba.”

murmushi Kabeer ya yi, dan ba tare da sanin Husain din ba shine ya damfare shi,

“zaka iya farawa kaima.”

“me?, Malam-Malam din hara mun ne fa.”

“ai kaji, to waye yace maka ba haramun bane, Malam in zaka waske tun wuri gara ka waske, kudade ake magana, wayanda inkana so ma zaka iya barin kasar.”

shuru Husain ya yi, yana tunani,
ganin ya yi shuru, yasa shi ci gaba da zuzuta mai lamarin, har sai da yaga Husain din ya yi Na’am da zancen, suna nan zaune, Kabeer ya ga giftawar wani mutum, da kallo ya bi mutumin yana mikewa,

“ina zaka?.”

Husain ya tambayesa ganin ya na niyar fita daga shagon,

“ina zuwa Husain, bari in dawo.”

ya fadi yana ficewa, a hankali yake bin bayan dattijon, ganin sun dan kauyanta daga idon mutane yasa shi yin sauri ya shige gaban dattijon, alokacin da ya gifta dattijon, ka fadar sa ta gogi ta mutumin, juyowa ya yi, ya kalli mutumin da ya dago ya kalle sa,

“yi hakuri Baba, ban kula da kai ba.”

ya yi maganar, bata re da ya jira jin amsar mutumin ba ya yi wucewarsa,

“wayan nan kudaden fa, ina ka fito da su?.”

Husain ya yi tambayar yana kallon dudaden da Kabeer din ya ajiye, wayan da a kalla zasu kai dubu dari biyar,

“kudaden mutumin can ne daya wuce yanzu.”

da mugun shock Husain ya furta,

“what, taya ka iya amso kudin daga hannunsa? aljuhunsa ka yanke?.”

murmushi Kabeer ya yi, “daya daga cikin sirrin mu ke nan, ba tare dana yanki aljuhunsa ba, kawai taba jikinsa na yi.”

“O M G, I really appreciate this work.”

(Ya Allah ka sake sare muna imanin mu🤲🏻 )

*******************

Balkisu, bayan fitowar ta daga Daba, dan can ta kwana, kai tsaye JUST ONE ta wuce wajen wani saurayin ta da tun jiya suka shirya haduwa, amma tasan ba wasu kudi zata samu wajen shi ba, dan haka ta wuce Daba,

“Baby tun jiya muka aje zamu hadu, shine kika barni pending ko.”

“to kai din ne baka iya cirewa ka bayar ba, ba kara inje inda zan samo kudi ba.”

“kudi dai kudu Baby, to zo ga shawara ta samun kudi ba tare da an wahala ba.”

da sauri ta masa inda yake, ta shige jikinsa tana fadin,

“A aikata kawai ba sai an tsaya yin wani shawara ba.”

“aa bari dai ayi shawara.”

ya yi maganar yana murmushi,

“to minene?.”

“mahaifarki zaki bayar muyi kudi da ita.”

ya fadi kansa tsaye,
da sauri ta mike tana fadin,

“what, are you serious, in bada mahaifata, ayi kudi da ita?.”

“ban da abun ki Baby, ai hannun hagu ba bakon duwawu bane, menene ban-bancin abun da kike yi yanzu da wanda nace kiyi, duka sabon allah ne.”

kai ta gargiza tana cewa, “ina bazan iya ba.”

“ok to yanzu zo kiji wata.”

ya sake jawo ta jikinsa,

*****************

“Mama,ni ban ce muku zan rabu da matata ba, kuma idan ma Allah ya kaddari rabuwar sakanin mu, to bana bukatar komai daga gare ku, duk abun da na muku na yafe.”

“Ah ah kai de Bilal, kar muyi haka, ka rike wannan kudin million daya ne, du da nasan wanda ka kashe basu kai su ba, amma dai ka rike, sakin kuma in kaga bazaka iya fadi ba sai ka tura mata ko ta waya ne.”

“Mama da dai anyi hakuri an bar maganar nan, idan ma wani laifi na yi, sai a fada min in gyara.”

“wai kai Bilal magana bata isar ka ne, ka dau kudin nan ka tafi nace.”

shuru ya yi, dan shi bai jin zai iya rabuwa da Farida, mikewa ya yi ba tare da ya taba kudin da ta ajiye ba ya mata sallama, ya fita,

**************

a yadda yake tuttula ma cikinsa hayakin sigari da giya kadai ya isa ya bayyana maka ba a cikin hayyacin shi yake ba, Farida ta turo kofar dakin hotel din da yake ciki, da sauri ta isa inda ya ke ta amshe kwalbar dake hannunsa ta ajiye tana fadin,

“Baby mene haka kashe kanka zaka yi ne, ko so kake su birki ta maka kwakwalwa?.”

“Baby I want it more, please let me drink.”

ya yi maganar cikin maye,

“no bazaka sha ba.”

ta tarkata kwalbar da kwalauen sigarin da ya sha,ta ajiye a gefe, kwanciyar shi ta gyara mai,kafin ta zauna gefensa, tana nan zaune ta na chatting da friends din ta, message din Bilal ya shigo wayar, bude sakon ta yi da sauri dan ita a tunaninta sakinta ya turo mata,

“Farida,dan Allah zaki iya fada min laifin da na miki da kike son rabuwa da ni?, ko a cikin zaman mu na taba zaluntar ki ne?.”

dogon tsaki ta ja, ta fara typing,
“wai kai Bilal, wani irin mara zuciya ne, nace ban sonka na fasa auren, to ka sake ni mana, ko ana dole ne?.”

“baki min komai ba Farida kuma ni ina sonki, dan haka ki sa aranki bazan taba sakin ki ba, mutuwa ce kadai zata raba ni da ke, duk inda kike jin zaki je da aurena kije, kuma insha Allah zaki dawo ga reni.”

tana gama karanta sakon ta yi wurgi da wayar a kan gado, tana sake jan wani tsaki, wayar Kabeer dake saman gadon ce ta kawo haske, hakan yasa ta juya ga wayar, da har zata share sai kuma ta kai hannu ta dauki wayar, da sauri ta sa hannu ta murza idanunta, tana sake ware su akan screen din wayar,

“What, 10millions fa, O M G, kuma wai duka na Kabeer ne ,? ko dai kuskuren hanya suka yi?.”

**************

“wai ina gantalallan ne ya baza’a fita yawon gantalin bane?.”
Chapter 2 · 0% Book details