← Book details Zamanin Mu Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 3

Sashe 3

Zamanin Mu Book 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

daga cikin dakin da take zaune, ta jiyo muryar Lami,
kallonta ta kai kan Khalifa dake kwance kan kafarta yana bacci, a yanzu ba damuwar mutanen gidance gabanta ba, damuwar ta Salis da tun jiya da suka rabu dashi bayan ya shawo kanta, har ta yadda ya dauki mahaifarta, bata sake ji daga gare shi ba, kuma ko ta kira wayarsa bai tafiya, gaba dai tana cikin rudani, kada de Salis yaudararta ya yi, tana cikin wannan tunanin, taji wayarta ta yi kara alamar shigowar message, dubawa ta yi, da sauri ta mike tsaye tana sake fito da idanunta, mikewar tata ta yi sanadin faduwar Khalifa dake kan kafarta, kuka ya saki wanda ya dawo da hankalinta kansa,

“ohh ohh, sorry Khalifa, nice ko, yi hakuri.”
ta yi maganar tana tallabosa jikinta, wayar ta sake dubawa, alert ne na dubu dari biyu, tana cikin alajabi kiransa ya shigo wayar, dagawa ta yi,

“Baby kinga kudi, na tura miki dari biyu, kiyi manegi har next week zan tura miki wasu.”

“eh na gani, amma kana nufin kudin mahaifata ne nan?.”

yar dariya ya yi kafin yace, “Aa wannan na dai baki ne, wayan can na kan hanya.”

Lami na zaune a tsakar gidan, taga fitowar Balkisu, sanye take da kayan kauyawa day,
kallon Lami ta yi tace,

“ga mu allah ya nufa mun fito zamu fita, sai a tsumaye dawowar mu.”

ta yi maganar tana barin gidan, ita dai Lami bata tanka ta ba, sai Mariya ce dake daki tace,

“to a dai bi a hankali, kar a dauko abun da yafi d’an shege.”

***************

“wallahi kasuwan sai ja baya yake yi, gaba dai na kasa gane inda masalar take.”

cikin damuwa mutumin ke magana, yana kallon yaran da ke zaune acikin dan dajin da bai yi nisa da gari ba, su ukku ne yaran,

daya daga cikin yaran ne ya ce,

“kar ka damu yanzu zamu, kona asirin da aka maka.”

wani abu dayan ya fitar daga aljuhunsa, ya bude, abune gashi kamar kasa amma wannan kalarsa baka ce sudik, zube shi ya yi a kasa, sannan ya fitar da ashana, nan ya kyesta ashanar ya jefata akan abunda ya zubar kasa, nan wuta ta tashi sosai, wani irin bakin hayaki na fita, sai da abun ya kone duka sannan, suka ce ma mutumin ya kwantar da hankalinsa yanzu bakin sihirin da aka mai dan karayar arziki ya samesa, sun karya shi,

da murnarsa ya ciro dubu dari ukku ya basu, da haka ya bar wajen,

suna ganin tafiyarsa suka kwashe da dariya, dayan yace,

“lallai sana’a ta karbu, sai fatan samun costume.”

dayan dake kirga kudin ne yace,

“yanzu fa ba wanda zai gane, kasa ce muka kwaba da petur da kala, abun ya fito sak aikin gaske.”

dariya suka sake kwashewa har suna tabawa,

“guy’s wallahi nima sai da abun ya tsorata ni, kiris ya saura ban riga ba, da sai dai mu hadu gida.”

(a kiyasi yaran nan ba zasu haura sha takwas ba, Allah ka shirya muna zuri’a🙏🏻.)

***************

a ranar wata juma’a Farida ta shirya kaima saurayinta Ukasha ziyara a hotel dinda ya fada mata su hadu, bayan ta gama shiri ta fada ma mahaifiyarta zata fita, ba tare da tanbayar ina zata ba ta mata adawo lfy, da haka ta fita, bayan ta isa hotel din, ta samesa yana jiranta,

“Sugar, ina mahaifarki take?.”

da sauri ta kallesa, jin tambayar da ya jefo mata, shima ita yake kallo,

“Sugar ban fahimta ba, kamar ya ina mahaifata ta ke?.”

“ina nufin baki da mahaifa a cikin ki, wa kika bama ita?.”

mikewa zaune ta yi, tana fadin, “wait nifa na kasa fahimtar ka, me kake nufi?.”

“idan dai ba ke kika bayar da ita ba, to wani ya dauka ba tare da saninki ba.”

“to kai ya aka yi kasan ban da mahaifa?, sannan idan wani zai dauki mahaifata me zaiyi da ita?.”

murmushi ya yi, “Sugar, kenan ba iya mahaifarki ba duk wani abu dake cikin cikin ki ina ganinsa.”

******

da gudu ta shigo gidan, tana kuka da fadin,

“Wayyo Mama na bani na lalace, Wayyo Allah na, Mama na shiga ukku shikenan na kashe kai na.”

fitowa Mama ta yi daga daki tana fadin,
“ke lfy me ya faru ne, waya mutu ne kike wannan kukan.”

gabanta Farida ta zube tana sakin wani ginjin kuka,

“ke wai miye haka fada min waya mutu.”

“Mama Kabeer ya cuce ni, ya gama da rayuwata, mahaifata Mama mahaifata.”

“ban gane Kabeer ya cuce ki ba, me ya miki, kuma me ya sami mahaifar taki, nifa ban gane ba.”

“Mama Kabeer ya dauke min mahaifata, wallahi ya dauke ta.”

ta sake fashewa da kuka tana kaiwa kwance a wajen,

“ban gane ya dauke miki mahaifa ba, yaushe ya kaiki asibiti aka miki aiki, kuma me zaiyi da mahaifarki?.”

“Mama Kabeer dan Malam-Malam ne, wallahi kudi zai yi da mahaifana, shi kenan na shiga ukku, na cuci kaina, me ya kaini aikata haka, wani son abun duniya ne ya sa na dauki kaina na kai ga halaka, kaicu na.”

ai itama Mama jin furucin Farida, wai Kabeer dan Malam-Malam ne, yasa ta zaunawa dabas tana daura hannu a kai, tama rasa kuka zata yi ko ihu,

a haka Baba ya shigo gidan ya tarar da su, ko da ya tambaye su meke faruwa kasa fada masa suka yi, sai da ya daka ma Farida tsawa sannan ta yi mai bayani, duk da shima abun ya dake shi sai ya dake yana fadin,

“abun da nike, ankarar da ku kenan, wannan hanyar daku ka bi bamai bullewa bace, son kudin ku wata rana zai kai ku ga halaka, to yau ga ranar ta zo, yanzu waye da dana sani.”

“Baban Farida wannan abun fa ba muka dai ya sama ba, kuma ai in kusu da tsata to daddawa ma da wari, wannan abun da ya faru da gudun mawarka ciki, tunda kullum furucin ka akan yariyar nan bana alkhairi bane, to dama taya zata ga dai-dai bayan akwai bakinka a kanta.”

“ohh wai yanzu a kaina zaki daura laifin, to dama taya zanyi fatan khairi da kyakkyawan furuci ga yariyar da ta baro gidan mijinta, ta kama yawon banza da igiyar aure a kanta, ai ko ban ce komai ba dama hakkin mijinta dana aure bazai barta ba.”

“sai kuyi kokarin boye sirrinku kamar yadda kuka saba, in ba haka ba kuma,ku duniya zata sani.”

yana gama maganar yasa kai ya bar gidan.

*******

kafin kwanaki ukku cikakku, labarin abun da ya faru da Farida ya bi gari, har hukuma sun shigo ciki, dan dama ana neman yan Malam-Malam din amma rashin hujja da kuma sanin inda za’a tunkara kai tsaye a kama su yasa ba ayi wani yunkuri akan hakan ba,

har gida motan sojoji fin Hudu suka iske Farida, gaba suka tasata akan sai ta nuna musu inda wanda ya dauke mata mahaifar yake, bata da zabi haka suka zankaya har zuwa shagon Kabeer, da baiyi sammani ba kawai sai ganinsu ya yi, kafin kuma ya yi yunkurin guduwa suka cafke sa, anan suka sa ma shagon shi wuta da mashin din shi, suka jefa shi bayan mota bayan sun mai dukan da ko motsi bai iyawa, a haka suka shiga zagaye garin da shi yana nuna musu sauran abokan aikinsa,

Bayan wata ukku

acikin watannin nan abubuwa da yawa sun faru, a inda ta bangaren Farida, Bilal ya nuna yana sonta kuma zai zauna da ita ko bata da mahaifa, a haka ta hada kayanta ta bishi,

Bangaren Kabeer kuma, an sako shi dan shaye-shayen da yake yi ya taba mai kwakwalwa yanzu hauka yake tuburan,

Bangaren Balkisu ko, tun bayan dubu dari ukkun da Salis ya bata bai sake bata komai ba, saima labarin kamasa da taji anyi, yanzu ta shiryu ko ina bata zuwa , duk yawon banzan nan ta daina……✍

END

DARASIN DA KE CIKIN LABARI,
1 illar shaye - shaye
2 illar rashin sarrafa harshe
3 illar rashin jin maganar iyaye
4 illar damfara da cin hakin da banaka ba,

(Allah ya sare muna imanin mu, yasa mufi karfin zukatan mu, kuma yasa mu gama da duniya lfy)
Chapter 3 · 0% Book details