← Book details Zinare Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 3 OF 3

CHAPTER 2;

Zinare Part 1 Complete Hausa Novel · about 49 min read

*WASIƘAR ALƘAWARI*


12

NAILA;
Bansan yadda zata misalta daɗin hirarsu a wannan dare ba, amma ya tunamata da abubuwa da dama, sai take jinta kamar lokacin da take yarinya ƙarama a Yankin Tudu. Sulaim bai bar Sashensu ba sai 11:00pm.

Barcinta na wannan rana na musamman ne mai cike da mafarkan cikar muradi, domin Sulaim da ta rayu da soyayyarsa a cikin zuciyarta a matsayin matacce ya bayyana a zahiri gareta matsayin rayayye, sam bata hasosa dukiya ko girman Dhahab da ƙawarsa a matsayin abinda zai zama linzamin Soyayyarsu ba, kulawarsa da mutuntawarsa garesu ya fiyemata komai.


Noorhan; tun tana sa ran Sulaim zai biyota masauƙinta ko ya turo aka kirata har ta cire rai.

Tana kuka ta kira Mahaifinta ba tare da bin ba'asi ko sanin gaskiyar abinda ya haÉ—asu ba, Mahaifanta ya ce ta turamai number Malik don bazai iya kiran Sulaim kai tsaye ba.

Ko da ya kira Malik kai tsaye Malik ya shaidamai wannan lokacin na Ahalin Sulaim ne kuma itama Noorhan tasan da haka shekararsu nawa suna tare bai ziyarci Gida ba? Idan zata jure to, idan kuma bazata jure ba zai sakota a jirgi ta dawo Gida.

Bayanin Malik ya soki zuciyar Mahaifin Noorhan, a ganinsa Æ´ar sa abar da za'a tattalace duk uzurin da Sulaim zai gabatar ya zamana tana gefensa.
Batare da Shawara da Noorhan ba, ya ce wa Malik su sako É—iyarsa a jirgi ta dawo Gida.

Gajeran Saƙo Malik ya turawa Sulaim, tabbacin ya gani kuma bai ce komai ba, yasa ya naimi tikitin tafiyar Noorhan nan take.

★washe gari Noorhan tana gama Breakfast Malik ya tura mata saƙon ta kimtsa Jirgin karfe biyun Rana zata bi, da mamaki take kallon saƙon kafin ta kira Mahaifinta. Da yake bawani tarbiyya aka horar da ita a kai ba, kai tsaye bayan ta ji shi ya yanke hukuncin tafiyartata ba tare da naiman shawararta ba ta fara yimai rashin kunya da faɗar maganganun masu kaushi.

Tasan bata isa ta jawa dukiyar Sulaim asara ba tare da wani dalili ba don haka ta shirya kayanta tana kuka.

Ummu Malik;
duk da Sulaim bai shigo gaishesu ba tukunna taji daɗin aiken kuɗin da ya yi musu, hatta Barirah da ƙunci ya hana sukuni ta ji daɗin kyautar kuɗin.

Bayan sunyi Dinner Ummu Malik take yiwa Simbi da Barirah faÉ—an su ja Naila a jiki, kishi tsakaninsu ya kau, su tuna Yankin É—aya ne ya samar da su, kar su bari son duniya ya makantarsu, su yi biyu babu.

Barirah kai tsaye ta nuna sam bazata iya mutunci da Naila ba, saɓanin Simbi da take ganin hakan kamar wani dama ne na sanin halin da Naila da Sulaim suke ciki, idan ta ja Naila a jiki dole duk zurfin cikin Naila tasan wani abu akan Soyayyarsu.

Ummi Mairam;
Duk kyautan kuÉ—in da Sulaim ya yi musu bai birgeta ba sam, burinta ya zo gareta ta gabatar masa da Barirah ko Allah zaisa ya amince mata.

Gaba É—aya bata sa abincin kirki a cikinta ba har zuwa washe garin da aka sanar da ita Sulaim zai shigo gaisheta zuwa yammaci.


SULAIM

Duk da, da zazzaɓi ya kwana hakan bai hanasa yin mafarkai masu daɗi riskar barcinsa ba, sai ya ke jinsa kamar lokacin da Mahaifinsa yake raye suke rayuwar ƙere-ƙerensu a Yankin Tudu.

Ba iya son Abota yake yiwa Naila ba kamar na shekarun baya, son aure yake yi mata idan zata amince da alƙawarinsa..

Kafin gari ya yi haske zazzaɓin jikinsa ya sauka, Da abin karin Ummi Aysha ya karya. Ummi Aysha murmushin fuskarta ƙim ɗaukewa ya yi har ta bar sashen saboda daɗin yadda Ɗanta ya saki jiki da ita.

Bayan fitarta Malik ya ziyarceshi...

Da Muryar da zai fahimcesa dakyau Malik yake yimai bayani akan su Ɗayyib karon farko tun bayan haɗuwarsu, saboda Malik ya na ganin Yaƙine da bazai iyashi shi kaɗai ba.

Bayan Sulaim ya gama saurarar Malik kansa ya ɗago yana dangana wayar hannunsa ga ƙaramin table ɗin dake gefensa.. ya ce;

"Wa su burika ka taɓa sanar da ni Naila tana da su ma? sannan Menene hukuncin da kake ganin ya dace a yiwa Ɗayyib"

Sulaim ya tambaya yana kallon tsakiyar idon Malik.

Kai Malik ya É—an sosa, a ganinsa bayaninsa ba shi da haÉ—i da burin Naila amma sai ya daure ya ce;

"Burinkanta biyu ne, cigaban Yankinmu da kuma samun tabbacin kana raye ko Dagaske ka mutu, ina ganin kuma ai muradanta sun cika, ÆŠayyib kuma kasheshi shine hukuncin da ya dace da shi"

Kai Sulaim ya É—an karkata gefe ya ce;
"A mayar da Ma'aikatar Tukwanen ZINARE tushen da aka ƙirƙiresa, duk wanda zai siya ya je har Yankinmu ya siya, Sufyan nake so ya zama GM sauran naɗe-naɗen yana hannunka, daga yau nakeson komai ya fara aiki. A filin da aka fara cinikin Tukwanen a filin za'a kafa Ma'aikatar. Ɗayyib kuma abarsa tukunna"

Sulaim ya ƙarasa faɗa yana miƙewa haɗe da ɗaukar wayarsa ya bar ƙwaƙwalwar Malik da lissafi.

Mayar da Companyn Dhahab na ɓangaren Tukwane na nufin burin Naila ya kammalu domin Yankin Tudu zai zama babban Yanki kuma kowa zai samu aikin yi Matasa Maza da Mata.

Bayyanar babban Maka'aitar Tukwanen Zinare da a yanzu a ƙasar Abyad ya fi rogowar shigowa da Sulaim kuɗi a Yankin Tudu da naɗa Sufyan a matsayin GM na nufin bugawar zuciyar Ɗayyib da Jalal... Idan ya fahimci Sulaim so yake yi su mutu da baƙin cikin abinda suka kasa kawo ƙarshensa..

Dariyar mugunta Malik ya saki har hawaye na tararwa gefen idonsa, Da zafin naman fara aiki nan take ya miƙe ya na zaro wayarsa ..


Misalin biyar na Yammaci Sulaim ya shirya cikin guntayen ƙananun kayan da suka dace da siffarsa, ƙafafuwansa sanye da Miami mule ɗin daya ƙara musu kyau.

Babu iso tsakaninsa da sashen Mahaifiyarsa, don haka ya fara shiga ya duba lafiyarta tare da shaida mata hukuncin da ya yanke a kan Ma'aikatarsa.

Ummi Aysha jin abin tayi banbarakwai yau Sulaim ya shaida mata wani yunƙuri nasa akan dukiyarsa, dariya ta saki tana nuna jinɗaɗinta, kafin addu'o'in nasara su biyo baya.

Domin ƙaramai ƙarfin gwiwa ta ce;

"Da Abduh yana raye, wannan yunƙurin naka sai ya zama babban abin alfahari a gareshi, Allah Ya kai rahama kabarinsa"

A hankali Sulaim ya ce;
"Amin"
Ƙwarin gwiwarta gareshi sun taɓasa don haka ya share sama da hour a sashenta, tana yi mai hira yana murmushi.
Ya yi godiyan tare da nuna jindaÉ—in yabonta akansa.

Ummi Aysha bata barshi ya tafi ba sai da ta shiryamai abu mai sauƙi ya sawa cikinsa.

Ummi Mairam; leɓunanta har rawa suke yi saboda maganganun da suka cika bakinta da zuciyarta, bayan surutun da take yi lokaci zuwa lokaci ita ɗaya.

Tana jin tsayuwar Motar da take kyautata zaton Sulaim ne ta miƙe da sauri.

Saboda rawar jikin tarbarsa har tuntuɓe ta yi, bai lura ba balle ya tareta don haka ta kife ƙasa.

Bata damu ba ta miƙe tana kama hannunsa zuwa ɗaya daga cikin Couch ɗin dayake parlon.

Babu cikakken nutsuwa balle karantar yanayin mutum ta fara zazzago abubuwan da suka daÉ—e suna damunta.

Bayan ta gama ta sako masa zancen Barirah kamar wacce ake kora..

ÆŠan nisawa Sulaim ya yi sannan ya ce;
"Bansan mai irin sunan da kike magana akai ba, amma maganar ya tsaya a iya na yau, ba ni da muradinsa"

Da sakakken leɓunanta da yawu ke ƙoƙarin biyowa Ummi Mariam take bin Sulaim da kallo.

Ɗan raɓo jikinsa mai ƙamshi yayi ya ɗan rungumeta sannan ya bar sashen.

Mahaifinta da ke laɓe ya na jin komai da sauri ya fito, dalilin haka yasa tayi saurin shanyen yawun da yake ƙoƙarin zubowa gaban rigarta, kafin ta fashe da kuka..

SASHEN UMMU MALIK
Bayyanar Sulaim a ɓangaren Ummu Malik ya ƙara tsuma soyayyarsa a zuciyar Barirah, tare da bawa Simbi ƙarfin gwiwar ƙulla Abota da Naila..

Kamar yadda bai naimi iso a sashen Mahaifiyarsa ba haka ya nufi sashen su Naila.

Har bakin ƙofarsu Driver ya kaishi, kafin ya kaiga saukowa mai tsaron ƙofar har ya danna alamar zuwan baƙo...

Kaka ce ta buɗe, ta na ganin Sulaim ta saki fuskarta, har tsakiyar living room ɗin tayi masa Rakiya, kunyar jin sautin faɗuwar cokalinta da suka ji jiya na kamata, Naila da batasan da zuwansa ba, daga madafi ta fito hannunta riƙe da kofi mai kyau, haɗin kayan marmari ne a ciki tana sha, tana bawa Kaka labari..

Sauyin ƙamshin living room ɗinsu yasa ta fara raba idanuwanta, tana ganinsa ta tafi da gudu ta zauna a gefensa tana dariya.

Kaka dake kallon Talabijin da rabin ido É—aya rabin a kansu dariya ta saki.

"Ina wuni" Naila ta faÉ—a tana kallon fuskarshi, lumshe mata ido ya yi alamar ya amsa.

Idon da ya amsa dashi ta kalla kafin ta saki dariya.
Naila har cikin zuciyarta ta ce;
"Idan ka tafi zan yi ƙewar idanuwanka"

Sulaim ƙara zaresu ya yi yana juyasu.
Dariya mai ban sha'awa Naila ta ƙyalƙyale da shi. Shima murmushin ganin farin cikinta ya saki yana karɓar kofin hannunta.

"You prepared the fruits yourself?" Ya tambaya ya na jiran amsarta.

Da sauri Naila ta amsa.
Ba tare da naiman wani cokalin ba ya kai cokalin ciki bakinsa..

Ɓata fuska ya yi yana girgiza kai alamar babu daɗi, a haka ya shanye yana girgiza kai, Naila da ta gane wasa yake yi mata, madubi ta mayar da shi tana murmushi.

Kaka tuni ta daina fahimtar abinda take kallo, gaba É—aya hankalinta da rabin idonta yana kansu..

Naanah ya kira Video call, ya kamo hannun Naila ta dawo kusa da shi sosai.

Naanah murmushi take yi tana kallonsu.
A hankali ya ce tayi guessing wacece wannan ya faÉ—a yana nuna Naila.

"Naila??" Ta ambata da sigar tambaya. ÆŠaga mata kai ya yi yana dariya.

Tsananin kamanceceniyar Sulaim da Naanah yasa Naila ƙura mata ido, cikin kokwanto Naila take tambayar wacece ta haifesa "Naanah ko Ummi Aysha?" Dariyar mara sautin da Naanah ta jima ba tayi ba tasa, son Naila da burin aurensu da Sulaim na ƙara samun matsuguni a ranta.

Sun É—an jima suna waya don har da Kaka suka gaisa kafin su yi sallama.

Da ya tashi tafiya har ƙofa Naila ta rakoshi. Sallamarsu taƙaitacciya ce, don haka Naila ta dawo ciki ranta fari fes...

★washe gari saƙon sabon waya da saƙon farin Takarda ya riski Naila.

Da mamaki take kallon wayar da farin envelope É—in, a tunaninta zamani yasa an daina rubutu a takarda sai ta hanyar waya da sauransu.

Daƙinta ta shige ta kullo kanta. Saboda Yadda ta matsu da sanin abinda takarda ya ƙunsa bata wayar da aka aiko tare da shi ba.
Ga abinda wasiƙar ta ƙunsa


"WASIƘAR ALƘAWARI
Amintata ƙalilan ce, saboda da Aminta ake kai mutum ƙasa. Inajin nutsuwa a raina tun ranar da na ganki Naila! Amma nutsuwata ba zata tabbataba har sai kinyimin alƙawari!

Ba na ci ko sha daga kowa sai Naanah da Mahaifiyata, sai kuma Malik, da ke dana yarjewa. Bazan rabaki da Kaka ba, amma kiyimin alƙawari bayan Kaka bazaki Aminta da kowa ba, har ƙarshen rayuwarmu.

Rashin Aminta ba yana nufin yanke zumunci ko ƙin kyautatawa amma yana nufin tsantseni da kiyaye sirri.

Na koma da ƙewarki da sonki mara iyaka a cikin zuciyata Naila! ba kuma zan dawo ba har sai kin ɗauki alƙawari, domin ki fahimci girman alƙawarin da zaki ɗauka yasa na rubatashi da alƙami, ki kiranta har iyakar yadda zaki fahimta..

Idan baki gamsu ba, ki sanar da ni, hakan ba zai dakatar da ni daga kula dake ba har bayan rayuwarki da Ahalinki.

SULAIM ABDALLAH"

Naila ta maimaita karanta saƙon Sulaim ya fi sau uku, da ta rasa yadda zata yi sai ta nufi wajen Kaka.

Kamar Kaka zata ƙumeta haka take kallonta kafin ta ce

" da wacce dama Sartaj ya samu hanyar ciyar dake sihiri?"

"Da damar amintar da mukayi da shi" Naila ta bawa Kaka amsa muryarta a sanyaye.

"To ba Sulaim ko ni saikin ɗaukarmin wannan alƙawarin Naila"...✍🏻

Gobe Asabar hutu In Shaa Allah 🤗
[9/5, 8:52 PM] Maman Amatullahi: SASAAL

13


ÆŠAYYIB;
kwanan su biyu aka sallamo Jalal da É—auraren ciwo, domin ya ce shi ba zai yi zaman jinya a Asibiti ba.

Har Jalal da Ɗayyib suka iso Gida zuciyar kowannensu a ƙuntacce cike da ƙudirin ramuwar gayya ko ta halin ƙaƙa.

Babu wani mutum É—aya da Jalal ya lamuncewa zuwa dubashi ciki harda Sarki Hammam. A ganinsa Sarki Hammam ba shi da wani amfani shi da fadawansa da mutanen gari baki É—aya, tunda suka kasa kawo masa É—auki ko É—aukar mataki cin zarafin da Malik ya yi masa har cikin Gidansa.

Sufyan kuwa sunyi masa mummunan shirin da duk ranar da Allah Ya ƙaddara haɗuwarsu sai dai wani ba shi ba.

Bayan kwanaki
Harajin da ya tashi hankalin kowa Ɗayyib ya ƙaƙabawa Kasuwar Tukwanen Zinare. Mutanen gari har gaban Sarki Hammam suka kai kokensu. Sarki Hammam haƙuri yasa aka ba su tare da yi musu alƙawarin duba kokensu.

Da dare yayi Sarki Hammam ya buƙaci ganin Ɗayyib a keɓantaccen wajen hutawarsa.

Ba a matsayin Ɗan uwa ya bashi Umarni ba a matsayinshi na Sarkin Yankinsu ya bashi umarnin ya janye harajin da ya ƙara ƙaƙabawa Mutanen Yankin.

Ɗayyib bai cewa Sarki Hammam komai ba, har ya tashi daga gurin, ɓakar zuciyarsa na suya.

★washe gari gaggamin ɓata garin wasu Yankunan Ɗayyib ya gayyato suka zo suka shafe duk wasu rumfuna na Kasuwar.

A take suka kewayeshi da guntun langa-langa, aka fara fitar da É—akuna a ciki.

Dattijawan Yankin ne suka yi gangami har cikin filin, ÆŠayyib yana zaune fuskarsa a É—aure kamar an musanyoshi.

Cikin Taushin harshe Dattijon da ya jagoranci gangamin ya ce;
"Ka tuna wannan filin magajinsa Abduh Dhahab tuni ya sadaukar mana da shi a matsayin Kasuwar da zamu gina Yankinmu ta hanyar samun kuɗin shiga, nuna iko da kangeshi domin buƙatar kanka kai kaɗai rashin adalci ne Ɗayyib, kuma zaka tauyemana rayuwarmu har da na Ƴaƴanmu da jikokinmu da zasu so nan gaba."

Ɗayyib gyara zamansa ya yi, yana jin kamar ya zaro wuƙar jikinsa yayi gutsi-gutsi da naman jikin su.

Muryarsa babu alamar tausasawa, haka kalaman da yake shirin furtawa kalamai ne masu tsananin kaushi da ya tane da su ga duk wanda ya ƙalubalanci kuɗirinsa ya ce;.

"Na yi muku uzuri, amma ku sani daga ranar irinta yau duk wanda ya ƙara yunƙuri dakatar da ƙudirina ko ƙalubalantar hukuncin da na yanke wallahi sai na yi ajalinsa na rantse bazanyi kaffara ba. Sannan ku sani wallahi ko da Abduh zai dawo a raye bai isa ya ƙwace wannan filinba"

Ƙosassun Motocin Malik da aka yiwa ƙira mai ƙwarin hawa tsaunuka ne suka kunnawa Yankin kai.

ÆŠayyib na cikin surutansa na cin mutunci ga Dattijawan Yankin, Motocin suka biyo takan langa-langar da dama tsofaffi duk sun ji jiki.

Da gudu Ɗayyib ya miƙe ganin Motocin sunyo kansa gadan-gadan.

Dai-daita parking Drivern Malik ya yi, ragowar suma suka dai-daita nasu a gefen na Malik.

Baƙin gilashin fuskarsa Malik ya ɗan zame.
Yana tafiya ya na faÉ—in;

Waɗanda yasaka aikin su rusheshi da kansu a cikin daƙiƙu, su kuma koma Yankunan su kafin na juyo kansu.

Babu gardama tunda ÆŠayyib É—in da ya gayyatosu ya fisu tsaurin ido ya zabura balle su, dasauri suka fara kwashe komai.

Malik da har tsakiyar kan Ɗayyib yake kallo lokacin da ya matsa kusa da shi, dariyar mugunta ya saki yana shafa kan haɗe da kamoshi. Wata mitsitsiyar wuƙa mai ƙaifin gaske Malik ya zaro daga aljihun gefen wandonsa.

Kan ÆŠayyib ya saki ya koma fuskarsa da hannunsa É—aya ya matse, nan take farar fuskarsa ÆŠayyib ta yi jajir.

Karon farko kenan da ÆŠayyib ya ji tsoron da fitsari ya zubomai nan take a tarihin rayuwarsa.

Sai da Malik ya kuma sakin dariyar mugunta, sannan ya rubuta mai sunan Sulaim ɓaro-ɓaro a gefe da gefen kuncinsa a rarrabe.

Jini ne ya fara tsatsafowa yana biyo har gaban rigar ÆŠayyib, su dama Dattijawa da suka tsaya da farko tuni suka gudu tunda suka fahimci Malik ne.

Murmushi Malik ya yi ya ce;
"Nasan baka da ilimin nasara, amma kaje wajen shaiɗanin da yake duba maka wayoyi da na'urorin mutane ya sanar da kai abinda na rubuta maka, zaka tuna wanene yakeson yi maka iyaka da ƙudirinka" Malik ya ƙarasa faɗa yana sakinsa haɗe da kama gefen rigar jikinsa ya goge wuƙarsa.

ÆŠayyib kuka ya saki yana jin fuskarsa kamar an watsamai wuta, shi da kanshi yasan shi mungune amma sai yake ganin kamar Malik ya fishi iya mugunta.

Maimakon ya yi gida Asibiti ya wuce don yasan idan Jalal ya gansa a haka zuciyarsa ce zata buga ya mutu.

Duk da azabar da yake ji bayan ya isa Asibiti mudubi ya ce su bashi, sanin matsayin ÆŠayyib É—in yasa suka naimomai Mudubi a gaggauce.

Fuskarsa ya kalla kafin ya cewa Nurse É—in;

" karantamin abinda aka rubuta a gefe da gefen kuncina".

A rarrabe Nurse ɗin ya ce Sul-aim, dukka da Nurse ɗin bai faɗa dai-dai ba, sai da gilashin hannun Ɗayyib ya suɓucewar da yayi kwatsa-kwatsa a ƙasa....

SUFYAN; walwalarsa gaba É—aya ta É—auke wasu lokutan sai ya ji kamar wayarsa tana yimai gizon Hindu Mahaifiyarsa tana kiransa. A haukace zai fara neman inda ya É—ora wayar sai ya É—auko sai ya ga babu wanda ya kira shi.

Wasu lokutan kuma sai yayi ta mafarkin ga su ÆŠayyib da Jalal nan sun zo zasu kasheshi.

Baya samun hutu ko sukunin zuciya ta kowani ɓangare, ga Sumaya da ta nace da kiransa. Shi kuma ya riga yayiwa kansa alƙawarin babu zaman aure tsakaninsa da ita, saboda Hindu Mahaifiyarsa tasha faɗamai Sumaya morarshin da take yi ne yasa take son shi, ba zai yarda da maganarta ba sai ranar da Allah Ya jarabceshi da Talauci..

Shirmen da ya farayi a wajen aikin ne yasa ya yiwa Kansa faÉ—an ya nutsu ya kula da aikin saboda shi kaÉ—ai ne abinda ya rage mai.

Wata rana bayan ya dawo daga wajen aiki saƙon Malik na mayar da Companyn Tukwanen Zinare tushen da aka ƙirƙiresu ya riskesa. Sam bai fahimta ba sai da Malik ya turomai dogon saƙo mai ɗauke da bayani dalla-dalla da ƙarin matsayin da ya samu.

Rabonsa da farin cikin da zai bayyana dariyar dake fita tun daga ƙasar zuciyarsa har ya manta sai da ya karanta saƙon Malik.

Ya murmusa ya dara yayi surutai shi É—aya tunda bashi da abokin gayawa.

Ƙewar Mahaifiyarsa, da tuna burin kafuwarsa da yayi sanadiyyar ajalinta yasa shi fashewa da kuka.

Ga shi zai zama mutumin da kowa zai so ya dama da shi, zai zama abin kambabawa a Yankin Tudu kamar yadda ya jima yana buri, amma mai tayashi kokawar cikar muradin nasa ƙasa ya lulluɓe idanuwanta, inama da tana raye.. ya faɗa yana tuno Fuskarta.

NAILA;
"Na yi alƙawai Kaka" Naila ta faɗa jikinta a sanyaye.

Hannunta Kaka ta kamo, itama cikin sanyin da ya haÉ—e da tsoron rayuwar da za su iya fuskanta anan gaba tace;

"Allah Ya baki ikon cikawa Naila, shima ki turamai saƙon kinyi alƙawari, ba iya na baki ba har cikin zuciyarki, Allah Ya na tare mu kinji"

A hankali kamar mai raÉ—a Naila ta ce;
"Kaka kina ganin alƙawarin bai yi tsauri da yawa ba, kar wata rana ya canzamin bayan na guji kowa"

"Wa kike da shi bayan ni Naila? Wa zaki aminta da shi bayan ni? Ba fa zumunci ya ce karkayi ba, bai ce karki kyautatawa kowa ba, to me kike nema? mai kike yiwa fargaba?" Kaka ta faɗa tana kallon Naila da tayi ƙasa da kanta.
A hankali Naila ta girgiza kanta alamar babu komai.

A jiyar zuciya Kaka ta sauke ta ce; "maza tashi kije ki turamai saƙo".

Ɗaukar alƙawarin Naila shi ne mafarin soyayyar mai ƙarfi tsakaninta da Sulaim.

A hankali ta fahimci Sulaim wani irin so yake yiwa abu da iyaka yardarsa da dukiyarsa da kuma zuciyarsa.

Wa su lukutan haka zai kirata ya yi ta kallonta ba tare da yacemin komai ba.

Ciwonsa, damuwarsa farin cikinsa duk Naila ta karance su, maganganunsa ƙalilan ne, amma kulawarsa gareta ba shi da iyaka.

Yana yawan tunamata har yanzu bai daina jinsa a matsayin Maraya ba, duk da Ummi Aysha tana raye amma rashin samun kulawarta tun farko da rayuwar gwagwarmayar da yayi bayan mutuwar Mahaifinsa, yasa yake jin kansa a wannan yanayin. Amma idan yana kallonta ko yana saurarar muryarta sai ya ji kamar Mahaifinsa ya na raye a kusa da shi bai mutu ba, dalilin raɓar rayuwarsu da tayi lokacin da babu wani abin nishaɗi a cikinsa sai kaɗaici.

Bani da matsala da Ummi Aysha duk ƙarshen sati sai ta aikomin da kyaututuka na musamman.

Motoci daban-daban da Driver Mace Sulaim yasa ake kai Makaranta a ciki masu kyau da tsada.

Komai na daya dangi Naila ƙarara Sulaim yake nuna muhimmancinsa ga kowa.

Cikin watanni su Naila suka yi wani irin kyau ita da Kaka.

Tsakanin Naila da Yasar sai dai su gaisa da ƴan uwansa da Iyayensa domin duk yadda ta kaiga ƙoƙarin dawo da zumuncinsu na baya sam Gasar bai bata haɗin kai ba, acewarsa ta fi ƙarfinsa yana tsoron kar yin waya da ita ya kawowa aikinsa matsala. Ba don Naila t so ba haka zumuncinsu ya yanke da Yasar, kamar bamu taɓa sanin juna ba a baya.

Wata ranar sati Simbi ta kawowa su Naila ziyara.

Basu wani saki jiki da ita ba har ta tafi.

★washe gari ta ƙara dawowa, yadda ta saki jiki da fuskarta abin ya ƙayatar da su Naila, har hirar Yankin Tudu ya fara shiga tsakanin su.

A cikin wannan satin kullum da daddare Simbi a sashensu takeyin dare, su na hira da Kaka wasu lokutan har da Naila.

A cikin sati biyun da suka biyo baya shaƙuwa ya fara shiga tsakaninsu da ita, a kwai wani dare ma a sashensu ta ce zata kwana, Naila ta yi yunƙurin kaita wani ɗakin daban amma ta nuna bata da matsalar kwanansu ɗaki ɗaya.

A tunanin Naila barci ya É—auke Simbi don haka ta zubo abinci ta kira Sulaim video call.

Babu jimawa fuskarsa ta bayyana yana sanye da Pyjamas alamun ya shirya kwanciya.

Kamar kullum da ta gaisheshi bai amsa ba sai ido da ya Lumshe ya aikomata da sumbatar daya sata sakin dariya.

Tashi ya yi ya zauna, yanayin fuskarsa na sauyawa haÉ—e da buÉ—e dukka girman idanuwansa da bai fiyayi ba.

Dariyarta Naila ta gimtse tsoron sauyin da ban taɓa gani daga garesa ba na shiga zuciyarta.

kamar daga sama ta ji saukar maganar da banyi tsammani ba daga bakinsa;

"Ina jin idon mutum a kaina, wacece a É—akinki Sa'aadati?"

[9/5, 8:52 PM] Maman Amatullahi: SASAAL

14

Wani irin bugawa zuciyar Naila ya yi. Dariyar yaƙe ta ƙaƙalo kafin ta ce;

"Ido kuma bayan nawa?"

Bayason ya ƙarayin magana don haka yayimata sallama kamar komai bai faru ba.

Yana katsewa Naila ta juya gefen da Simbi take kwance da sauri, amma sai taga Simbi ba ma gefenta take kallo ba, kuma ba taji alamun motsin juyawarta ba.

Ajiyar zuciya ta sauke amma duk haka ta kasa cin abincin da ta zubo sai kitchen ta mayar da shi.

Har tsakiyar dare Naila ta kasa runtsawa, living room ta fito ta haÉ—a kanta da gwiwarta ta fashe da kuka. Tsoron gayawa Sulaim gaskiya take yi kar ya ce yarda da Simbi ne yasa ta barta har ta kwana a É—akinta.
Kasa jurewa tayi ta koma ta kullo É—akin ta waje sannan ta kira shi Video call ko Allah zaisa ya É—aga.

Bai É—aga ba, kuma bata daina kira ba, har barci ya É—auketa.
Ba tafi hour uku ba ta farka, ƙara ɗorawa ta yi da kiransa, cikin sa'a ya ɗaga.

Yana zaune idanuwansa da barci sosai a cikinsu don haka ya rage girmansu kamar baya kallonta..

"Kayi haƙuri" Naila ta faɗa tana fashewa da kuka haɗe da dafe bakinta.

Bai ce mata komai ba sai wayan da ya kai saitin laɓɓansa ya sumbata sannan ya ɗan saki murmushi.

Ta yi tunanin zai tambayeta dalilin da yasa take bashi haƙuri har da su kuka, sai ta faɗamai gaskiya, amma sai ta ji bai tambaya ba. Maimakon haka da muryarsa da ya ɗan yi nauyi ya ce;

"Kalli yadda kike kuka Sa'aadati, matso daina kuka faÉ—amin menene?"

Ido Naila ta rintse tana jin soyayyarsa kamar ya yi mata yawa. Kai ta girgiza saboda ta kasa cewa komai.

Murmushi ya yi kaɗan yana shafa sumar kanshi kafin ya ƙara sumbatar wayar.

Noƙe kafaɗa Naila tayi alamar ba wannan take so ba.

Girarshi ya É—age alamar tambayar "dagaske?"

Ɓata fuska tayi tana sosa hancinta.

"Babu laifin da zakiyimin, na kasa hukuntaki Sa'aadati, saboda ina sonki, son da babu rabuwa, amma karki bari ta ƙara kwana a Ɗakinki kinji"

Naila da sauri ta É—aga kai, tana share hawayenta. Mamakin yadda yasan Simbi tana É—akinta na kamata amma babu damar tambaya.

"Ki je wani É—akin ki kwanta" ya faÉ—a yana jingine wayar a saitin fuskarsa

Fara buÉ—e Simbi Naila tayi Sannan ta shiga wani É—akin ta kulle har lokacin Sulaim yana kan layi.

Kwanciya tayi ta duƙunƙune cikin abin rufa tana kallon yadda yake kallon wani waje daban da alama labarai ko wani abun yake kallo mai muhimmanci. Yanayin fuskarsa da babu wasa sam sai yana kallonta na matuƙar birgeta, takan ji a ranta kamar tafi kowacce ƴa mace Sa'a.

"Na gama" Naila ta faÉ—a tana kallosa

hankalinsa ya maido kanta.
Maimakon ya yi magana, sai ya yi mata alamar da hannu ta matso.

"Ta ina zan matso" Naila da faÉ—a tana dariya.

Shima murmushi ya yi, kamar yadda ya saba ya kai wasu daƙiƙu yana kallonta, sannan yaƙara sumbatar saitin inda goshinta ya bayyana a tasa wayar.

A kunnen Sulaim Naila tayi addu'a kafin ya mata alamar ta jingine wayar tayi barcinta.

A kan Bedside lamp ta jingine wayar. Sanin waya ɗaya ne a tare da ita yasa ya kunna karatun Abdurrahman Bin mus'ad ta ɓangarenshi haɗe da rage sautin labaran da yake ji.

A hankali sanyin sautin karatun Alqur'anin yake shiga kunnen Naila yana sanya mata nutsuwa a cikin zuciyarta, tun tana É—an buÉ—e ido tana kallon gefen fuskarsa idan tayi sa'a ya juyo suka haÉ—a ido ya aiko mata da sumba har barci mai daÉ—i ya É—auketa. Sai da ya tabbatar barcinta yayi nisa sannan ya katse kiran.


SULAIM
Tun bayan komawarsa Kahala Noorhan ta fara ziyartarsa babu dare babu rana.
Bai ɓoyemata ya rabu da ita ba, amma sam ta nuna wallahi bai isa ba, ita zai rainawa hankali ko ya ɗauko ita irin Matannan ne da Namiji zai so a lokacin dayaga dama kuma ya rabu da su a lokacin dayaga dama?. Ko don yaga yana da kuɗi? Ita babu inda zata je idan zai dawo hankalinsa ma ya dawo.

Duk mitar Noorhan da kalamanta masu kama da nuna iyaka ko gadara Sulaim bai taɓa kulata ba.

Lamarin su yayi ƙaramari ne data fara binsa har office da duk wani wajen taro da zai je sai ya ganta a harabar wajen, hatta Asibiti wajen Naanah zuwa takeyi ta zauna a harabar wajen. Kuma duk haɗuwar da zasuyi sai ta biyosa har jikin mota tana mita. Bai taɓa sawa a wuƙantata ba.

Noorhan anata ganin Sulaim ya ƙyaleta tana cimai zarafi ne don yasan ba shi da gaskiya kuma itama Mahaifinta ai mai kuɗine.

Ranar da ta kaishi ƙarshe ta biyoshi har cikin office tana zage-zage, kai tsaye ƙararta ya shigar kan shiga haƙƙinsa, cin zarafi, takura da ɓatamai suna.

Abu kamar wasa Sulaim ya nuna mata ikonsa da dukiyarsa da take ganin kamar zasu aunu a ma'auni É—aya da na Mahaifinta.

Da kuka da magiya tare da alƙawarin ɗauke Noorhan su mayar da ita Lebanon Iyayenta suka shawo kan Sulaim ya janye ƙarar da ya shigar..

Wannan ne sanadiyyar fitar Noorhan daga cikin rayuwarsa.

Al'amarin Naila gareshi babba ne, domin ba iya kallon Matar da zai aura yake yi yiwa Naila ba, harda kallon aminiya ƙanwa kuma uwar ƴaƴansa yake mata.

Babu rabuwa da ita a tsarinsa amma ya lura Naila sam bata da wayo, kuma ita mutum ce da zata iya sadaukar da farin cikinta don na kusa da ita yaji daÉ—i, da wannan damar Simbi take neman shiga jikinta.

Tun zuwanta Simbi sashen a ranar farko labari ya riskesa, ba shi wani makusanci da ya yarda da shi É—ari bisa É—ari, domin ko Malik akwai wanda kawai aikinsa lura da motsin Malik ne , ba tare da shi kanshi Malik É—in yasan da zamansa ba sai manyan Securities É—in Dhahab, domin a matsayin mai bawa shukoki ruwa yake rayuwa a Gidan.

Saukar numfashin Simbi da yasan tana fitarwa ne da gan-gan ya bashi tabbacin tana É—akin kamar yadda aka bashi rahoton tunda ta shiga sashen bata fito ba.

Idan ya yiwa Naila kashedi akanta har sau uku bata ji, to zai yimata hukuncin daya dace da ita...

SIMBI.

Tana sane ta dinga fitar da numfashinta da ƙarfi saboda tasan waye Sulaim, ba zai taɓa son kwanciyarta a ɗakin Naila ba, kuma gaskiya ya faɗa lokacin daya bayyana akan screen ɗin wayar Naila, idanuwanta ƙuri suke akansa sai dai dayake bata saitin Camera shiyasa bata fito ba, a hankali ta juya domin tasan dole Naila ta waiwayota bayan ya katse kiran.

Da Naila ta kullota a ɗaki dasauri ta miƙe ta ɗauki ɗayan wayar Naila da ta bari.

Babu password babu komai sai Apps É—in karatun Alkur'ani kala-kala har ta gama bincikenta bata ga komai ba, asalima babu layi akan wayar.

★washe gari bata tsaya jiran tashinsu ba ta tattara ta bar sashen.

Tsaf ta zauna ta karya da Iyayenta har tana tsokanar Barirah da take cika tana batsewa.

Bayan ta shiga Ɗaki Taswirar Dhahab da aka yiwa ado da kaloli ta manna shi a bangon ɗakinta take kallo. Zama tayi tana tunano irin dukiyar da Sulaim ya mallaka a iya ƙasar Abyad, amma ace Naila ita kaɗaice ta samu zama a cikin zuciyarsa. Mai zai hana ya ɗauko bare haɗiɗɗiya ƴar manyan mutane mai kyau da aji daga wata nahiyar ya aura? Naila fa? Naila ƴar Mahmoud madinkin da bai taɓa ɗanɗanar arziƙi ba har ya bar duniya.

Ina laifin ma ya zaɓi Barirah tunda tafi Naila ilimi da wayewa..

Banbancin kishin Barirah da Simbi. Barirah mace ce mai faɗa saurin fushi lokaci, ɗaya da son cin zalin yara ta hanyar Dukansu tun tana yarinya ƙarama, son girma da mulki tun bata san zasu riski kansu a Babban Birnin Abyad ba. Amma bata da baƙin ƙishin cutar da wani ta hanyar sharri ko asiri, barta da masifa da ƙunci. Saɓanin Simbi bata da hayaniya amma wani irin kishi ne da ita daya haɗe da hassada, kuma akan cikar muradinta bata ƙi tayiwa mutum sharri ba, a baya hassada yasa take ganin wawtar ƴar uwarta akan son Sulaim duk da itama dama ne bata samu ba, amma yanzu da yake son Naila sai take ganin gara kawai ya je ya ɗauko bare.

Naila da Barirah ba su dace da shi ba, ko kuma dai ya ɗauki Barirah ya rabu da Naila. Simbi har ta gama Makaranta bata yarda kina ƙawance da ita kiyi da wata ba, da zarar ta ganki da wata musamman wacce ta fita sai ta fara kishi, waɗanda ba su fuskanceta ba sai suke yimata kallon wata manufa daban..

ÆŠAYYIB
Ko ina na jikinsa rawa yakeyi, sai da ya share mintuna goma bai dawo nutsuwarsa ba. Gumi kuwa kamar an watsamai ruwa suna zubowa yana sharcewa.

Da sauri Nurse ya fito don kiran babban Likita kar Ɗayyib ya mace ba tare da yayi yunƙurin komai ba

Fargaba yasa jinin ÆŠayyib ya yi mugun hawa bayan likita ya gwadashi dole suka bashi gado.


Da dare yayi ÆŠayyib fitik-fitik ya yi sai sun sallamesa ya koma Gida saboda bayaso Jalal yaji labari ko ya ga fuskarsa balle yasan gaskiyar abinda ya faru.

Bai nufi sashen Jalal kai tsaye ba sai da ya fara tsayawa a nashi sashen yayi wanka tukunna.

Jiki a sanyaye ya nufi Sashen Jalal fargabar sunan da Malik ya rubutamai a kuncinsa har lokacin bai gama sakinsa ba, duk da yasan ba'a mutuwa a dawo.

Ko da ya isa wajen Jalal ya tambayeshi game da aikin filin daya fara shiru yayi kamar bai ji sa ba, har sai da ya ƙara maimaita tambayarsa.

Sannan ÆŠayyib da har lokacin jikinsa yake a sanyaye, ya sanar da Jalal abinda Malik ya ce akan filin ya kuma saka an rushe komai.

Shiru Jalal ya yi, yana runtsewa idanunsa, irin azabar da Malik ya ganamai na dawomai.
Hukuncin da yake ganin shine mafita Jal ya sanar da ÆŠayyib, na zuwansa wajen Bokan Tsaunin da shi kaÉ—ai ya rage musu.

A wannan dare ÆŠayyib ya yi sallama da Jalal, ya koma sashesa ya shirya kayansa.

★washe gari da Asubahi ya saɓa jakarsa domin tafiya ƙasar Abyad, wajen ƙasurgumin Bokan Tsaunin da Jalal ya kwatantamai, a wajen wasu tsaunuka bayan garin Birnin Abyad...

NAILA;

Bayan ta idar sallar Asubahi alfijir ya fara ketowa ta kira wayar Sulaim kamar yadda ta saba.

Ya É—aga amma bai buÉ—e idanuwansa ba, jingine wayar yayi ya barta tana kallon fuskarsa.
Naila kallonshi take yi tana murmushi kamar wacce ta samu matsalar kai.

Farin hannusa ya miƙo, Naila ta na dariya da tai kai bakinta kan wayar dai-dai saitin inda hannun yake ta sumbata, shima murmushi ya saki yana gyara kwanciyarsa.

Naila tana kallon Sulaim da idanuwansa suke kulle har ta koma kan gado ta jingine wayar, a haka Barci itama ya ɗauketa, wayar da kanta ta mutu bayan chajinta ya ƙare.

Wannan shine daily routine É—in Sulaim da Naila..

Da gari yayi haske, Kaka ta umarci Naila ta taso Simbi suyi Breakfast.

Wayam ta samu ɗakin. Daga ita har Kaka basu wani damu ba, saboda kai tsaye tunaninsu kan wataƙila dan Kar ta takura musu ne tayi tafiyarta.

Da yammaci sai ga Simbi ta ƙara dawowa, hirar tana son yin wani cos a makarantarsu Naila take yi musu, dan haka ta roƙi dan Allah idan zata je tayimata waya su fita tare..

Naila bata kowa komai ba a ranta, washe gari bayan ta kimtsa ta kira Simbi ta layin wayar da ta bata.

Da Simbi ta fito Kai tsaye Driver ta hana shiga, ran Naila babu daɗi takeyiwa Drivern ƙorafin ɗaukar Simbi ai ba wani matsala ba ne, tunda Makaranta ɗaya zasu je.

Abinda Naila bata sani ba Simbi bata da mai biyamata irin jami'ar da take zuwa, kawai tayi hakane saboda tasan labari zaijewa Sulaim, kuma ƙorafin Nailan akan lallai sai an ɗauketa tamkar Sulaim tayiwa tunda da yawunsa Drivern take magana.

Driver zuwa tayi ta dawo, ba tare da ta ƙaracewa komai ba tace Simbi ta shiga su tafi.
Har sun yi nisa Simbi tafara lalubar jakarta, tsaki ta saki tana faÉ—in;
"Subhanallahi wallahi na manta takarduna a gida Please Driver ajjiyeni anan"

"A'a mai zai hana mu koma ki É—auko" Naila ta faÉ—a da zuciya É—aya

"Karki damu zan fita da motata kawai"

Simbi da fuskar alhinin manta takardun da tayi a gida, acewarta sukayi sallama da Naila.

Murmushi Simbi ta saki bayan ta sauka, tana ƙoƙarin lalubo wayarta don kiran Drivern su, Mota mai kyau ya tsaya a saitinta.

Kyakkyawan matashine, farinsa har kashe mata ido yakeyi, yana tsayawa ya sauko ba tare da ɓata lokaci ba yana yi mata sallama.

Fuskarsa take kallo har zuwa takalmin ƙarfarsa baƙi wuluk, baƙin har wani irin gizo yake yimata.

Amma da yake taga alamar tarin dukiya a tare da shi, sai ta amsa sallamarsa tana É—auke kai, amma zuciyarta cike da farin cikin babban kamun da tayi, wayancewa tayi da kiran Driver kamar bata damu da Mutumin da ya tare ta ba
[9/5, 8:59 PM] Maman Amatullahi: SASAAL

15


SIMBI

Cikin salo da iyayi take sanar da Driver ya taho mata da Motarta, haÉ—e da kwatantamasa inda take.

Cikin É—an kame fuska ta dawo da hankalinta kan Matashin da ya tsaya jiran ta gama amsa waya.

"Barka da safiya Hajiya Simbi, ina fatan ban dameki ba ko?" Matashin ya faÉ—a yana kallon fuskarta.

DaÉ—in muryarsa da daÉ—in da take ji acikin zuciyarta yasa ba tayi tunanin ina Matashin yasan sunanta ba.

"Sunana Ɗayyib amma zaki iya kirana da Dee, ni mazaunin Babban Birnin Abyad ne, mamallakin kamfanin sarrafa shinkafa na D&J a Birnin Abyad, na ji daɗin haɗuwa da ke, ina fatan kema haka?" Matashin ya yi bayanin kansa a taƙaice yana karantar yanayin Simbi.

Wani irin fari tayi da ido tana ƙaremai kallo, kafin ta saki murmushi tana miƙamai hannu alamun ya kawo wayarsa.

Wayar hannusa ya miƙa mata yana murmushi.

Ƙirar wayarsa da kyanta sam ba irin manyan wayoyin ƙasar Abyad ko ta ce na duniya gabaki ɗaya data Sani bane, "kenan ƙera mishi tashi akayi daban? Gaskiya na yi babban kamu, yau na fito a sa'a yaushe rabon da wani ya tare ni da sunan yana so na, hmm! gaskiya Allah Ya na so na"

Simbi ta faÉ—a a cikin zuciyarta lokacin da take jujjuya wayar Dee a hannunta kafin tasamai Number wayarta.

Tana samai, ya karɓi wayar ya juya ya shiga Mota. Simbi tayi tunanin tafiya zai yi sai taga ya fito da abu a nannaɗe a cikin takarda mai tudu da kauri. Sai da ya miƙa mata yana murmushi sannan ya ce;

"Ga wannan kisha Ice cream babu yawa, sai na kiraki ko?" Ya ƙarasa faɗa yana yimata alamar kira da hannunsa.

KuÉ—in Simbi ta shafa, wani irin kuÉ—i ne dashi haka, da zai yimata kyautar kuÉ—i irin wannan daga haÉ—uwa?,

"gaskiya na yi babban kamu" ta faɗa ƙasa-ƙasa tana murmushi

Bayanshi tabi da kallo tana shafa kuÉ—in hannunta har ya shige mota ya tasheta yabar wajen.

Daa Simbi tasan Ɗayyib ɗin Yankin Tudu lokacin da yake Matashi kamar yadda su Malik suka sanshi, da ganin fuskar Matashin da ya tsayar da ita kaɗai sai ya sata yin gudun da bata taɓayi ba, ko zuciyarta ta buga nan take.

Amma maimakon wannan tsoron tunda ba sanin ÆŠayyib tayi yana Matashi ba, sai tayi ta sakin murmushi har Driver ya zo É—aukarta..

MALIK
A ɓangaren Malik tun safiya yayiwa Yankin Tudu tsinke, domin duba yadda aikin Ma'aikatarsu ya ke gudana.

Bayan ya yi sallar Magriba yana ƙoƙarin kimtsawa domin tafiya Masauƙi, kwatsam ya ji Muryar mutum a gefensa.

Malik bai zabura ba, saboda bashi da tsoro ko ƙanƙani sai tsayuwarsa da ya gyara yana waiwayo gefensa.

Sarkin tsafin Yankin Tudu ne ya bayyana a idon Malik.

Malik bai ce komai ba sai tsayuwarsa da ya ƙara gyarawa haɗe da ƙara matse fuskarsa, cikin ƙasa-ƙasa da murya ya ce;

"Mai kake nema? Mai ke tafe da kai yi bayani a gaggauce"

"Yau kwana biyu da tafiyar Ɗayyib wajen Bokan Tsauni, ɗaya daga cikin Bokaye mafiya hatsari a Ƙasar Abyad, zai iya bayyana ba iya wajenku ba har a cikin Dhahab, Zai shafe Tarihin Dhahab da wanda ya kafata idan har ya bayyana a cikinta ba tare da an dakatar da shi ba, lokaci ƙalilan ne ya rage, ƙarin haske na wajen Simbi ƴar uwarka" Sarkin Tsafin Yankin Tudu yana gama faɗa ya ɓace.

Motsi biyu Malik yayi shine É—auko wayarsa da turawa Sulaim bayanin komai nan take.

Idan Malik ya ce bai ji tsoro ba ya yi ƙarya, amma babu wani Mahaluƙi daya isa ya rusa Dhahab matsawar su na raye..

Tsoron da ke neman mamaye zuciyarsa ya fatattaka ya dannawa Driver kira.

Cikin mintuna ƙalilan Driver ya ƙaraso.

Bayan Malik ya shiga Mota saƙon Sulaim ya shigo wayarsa, gumin da rabonsa da yin irinsa ne ya shiga tsatsafomai mai yana sharcewa, hannunsa yana rawa ya dannawa Sulaim kira...


NAILA

A ɓangaren Naila bayan sun tashi, bata tsaya wani ɓata lokacin biyawa wajen cin abinci ba Driver ta dawo da ita Gida..

Kamar yadda ta saba bayan ta iso gida ta huta, wayar Sulaim tafara kira, amma har sau uku bai É—aga ba.

Tasan bazai wuce fushin tafiya da sukayi da Simbi Makaranta tare ba, ita gaskiya ta gaji, to so yake yi ta dinga wulaƙanta su tana nuna musu ita tafisu, gaskiya bazata iya ba.

Kasa riƙe zancen tayi, ta fara bawa Kaka labarin ko ƙarasawa Makarantar fa basu yi ba Simbi ta sauka amma shine zai yi fushi har ya ƙi ɗaga kiranta..

Kaka bata tofa ba, a ganinta faÉ—an masoya ne zasu shirya daga baya.

Naila har ta gama cin abinci bata daina mitar
"gaskiya ni bazan jurewa wannan ƙa'idojin nasa ba"

SIMBI
A ɓangaren Simbi har takai gida bata daina murmushin babban kamun da ita yi ba.

Tana isa cikin sashensu kai tsaye ɗakinta ta wuce har da kullo ƙofar ɗakin da mukulli gudun kar wani ya shigo ya ga kuɗin data samu, Surprise take son yi musu.

Kafin ta shiga wanka sai da ta ɗan yaga takardar da aka lulluɓe kuɗin da shi taga Dagaske dai kuɗaɗe ba ɗan kaɗan ba.

Dariya ta saki har da tsalle tana juyi. A É—an hanzarce ta wuce Washroom tana juyi har da juya idanuwanta.

Bayan ta fito daga washroom, kimtsawa tayi cikin kayan shan iska, da murmushi ta juyo don É—aukar kuÉ—in ta fita da su ta nunawa Ummee da Barirah su ga irin Babban kamun da tayi, tana waiwayo inda ta ajjiye kuÉ—in sai ta ga wayam babu kuÉ—in babu dalilin sa..

kuyimin afuwa da guntun paji uzurine ya riƙeni, Na gode🙏🏻
[9/5, 8:59 PM] Maman Amatullahi: SASAAL

16


SIMBI;

Dukka idanuwanta ta zaro tana dafe saitin zuciyarta da yake tsananin bugu.

"Wanene ya shigomin É—aki?" Ta tamabayi kanta tana kallon inda ta ajjiye mukullin É—akin. Yananan yadda ta ajjiyeshi.

Cikin sanɗa ta nufi ƙofar, ta murɗa a hankali, tana murɗawa ta ji shi a kulle alamar ba'a buɗe ba. Da sanɗa taƙarasa kusa da mukullin ƙofar tayi wuf ta ɗauke, hannuwanta na rawa ta zura ɗan mukullin, tana buɗewa ta fito a guje ta nufi hanyar ɗakin Ummeensu tana ƙwala Ihu kiran sunanta.

A ɓangaren Ummu Malik daƙyar ta iya samun waje ta zauna, tunda Sulaim ya kirata da kansa ya sanar da ita naɗar duk wani motsin Simbi ko kalamanta, yana zargin ansamu matsala, kuma karta kirata ta bari har sai ta dawo.

Abunka da zuciyar Uwa sai ta kasa sukuni, tana tunanin mai Simbi ta aikata da har zaisa Sulaim ya kirata a karon farko a rayuwarsu, tasan koma menene baƙaramin abu bane.

Da ta ga tunanin zai yi mata yawa sai ta ɗoro alola ta tayar da Sallar nafila tun da lokacin ƙarfe 9:40 ne na safiya.
Ba ta jima da idarwa ta ji ihu, kamar na Simbi.

"Yaushe Simbi ta dawo gidannan bansaniba?" Ta tambayi kanta asarari tana miƙewa, bayan ta saita wayarta ta ajjiye a gefe.

A bakin ƙofa suka ci karo da Simbi tana zare idanuwa.

"Simbi! Lafiyarki kuwa? Wannan ihun naki ai sai ya firgita mutum" Ummu Malik taƙarasa faɗa tana kamota zuwa jikinta.

Da rawar murya Simbi ta ce;
"Ummee kuÉ—i saurayina ya bani, daga ajjiyesa akan gado na shiga washroom, ina fitowa naga babu kuÉ—in kuma wallahi na kulle É—akin da hannuna"

Da alamar tambaya Ummu Malik ta ce;
"Saurayi kuma? Yaushe kikayi Saurayin da yake baki kuÉ—i bansani ba Simbi? Kina son ki fusata Yayanku ko?"

Kai Simbi ta girgiza. Babu wani nutsuwa a tattare da ita take bawa Ummeenta labarin yadda suka haÉ—u da ÆŠayyib.

Da mamaki da tsoro Ummu Malik ta ce;

"Ai Companyn masarrafin Shinkafar D&J da ke Birnin Abyad na Mahaifin Bushra ne, anya ba ÆŠan damfara ko Aljani kika haÉ—u da shi ba Simbi????

Sai a lokacin ta gano ina Sulaim ya dosa, ashe baƙaramin matsalane yake ƙoƙarin kunna musu kai ba.

Hannunta da yake rawa tasa ta janyo wayarta, duk bayanin da Simbi take koromata sam ba ta fahimta har sai da tabbatar saƙon Muryar Simbi data naɗa ya isa ga Sulaim....


SUFYAN;

A ɓangaren Sufyan tun bayan samun saƙon Malik ya ke cikin farin ciki, ƙuncin da yake fama da shi kwana da kwanaki sai ya kau, hankalinsa ya mayar kan kammala ayyukan da suka ragemai bai ƙarasa ba.

Ba su taɓa haɗuwa da Kabeer sun yi gaisuwar dake nuna sanayya ko abota a tsakaninsu shekarun baya ba. A matsayin Ubangidansa kullum yake gaishe da Kabeer.

Bayan sati É—aya, yana zaune a office kiran Kabeer ya shigo ta wayan ofishinsa. Bayan ya É—aga Kabeer ya shaidamai yana nemansa idan ya gama abinda yake yi.

Sufyan ji yayi gabaki É—aya aikin da yake yi a lokacin ya fitarmai daga rai, burinsa kawai ya ji, wani babban daliline zai sa Kabeer ya nemesa a irin wannan lokacin.

Bayason Kabeer ya yi zargin wani abun ko nuna zumuɗinsa kan kiran da ya yi mai, wannan dalilin yasa ya danni zuciyarsa yaƙara Minti Talatin kafin ya miƙe.

A gaggawace ya nufi ofishin Kabeer da ya jima da sani, amma bai taɓa samun damar shiga ba.

A ɓangaren Kabeer
Babu kowa a ofishinsa sai shi É—aya yana danna wayarsa. Naiman izinin shigowar Sufyan ne yasa shi ajjiye wayar a gefe yana ba shi izinin shigowa.

Kamar yadda suka saba gaisawa haka suka gaisa bayan Sufyan ya zauna a kujerar da ke fuskantar na Kabeer.

Gyaran murya Kabeer ya yi sannan ya ce;

"Jiya na haɗu da Mahaifinka Ɗayyib amma shi bai ganni ba, ina tunanin zai iya riskarka a kowani yanayi, kuma ina gudun abinda zai biyo baya, mai zai hana ka dawo wajenmu da zama, kafin saƙon ganinsa dana tura ya isa ga Sir Malik".

Tun lokacin da Kabeer ya ce ya haɗu da Mahaifinsa, Sufyan ya sunkuyar da kansa ƙasa

Cikin kuka Sufyan da yake ganin kamar gashi ga ajalinsa ya ce;

"Idan har ya samu ƙwarin gwiwar isowa Babban Birnin Abyad menene ya ragemin Kabeer, Gara na tsaya ya kasheni duk guje-gujena wata rana zai riskeni ya kasheni, Kabeer tsoro nake ji"

Tasowa Kabeer ya yi ya matso kusa da shi yana lallashinsa...

NAILA;

A ɓangaren Naila har ta gama mitarta ta shige Ɗakinta Kaka bata tanka mata ba.

Kasa jurewa tayi bayan ta shiga ɗaki, ta ƙara neman layin Sulaim amma ba'a ɗaga ba. Jifa ta yi da wayar tana hura siririn hancinta.

A ganinta zaƙewar Sulaim ya yi yawa, tayaya zaisata ta guji Simbi alhali shi yana tare da Yayanta dare da rana ta waya? So yake yi ita tayi baƙin jini kenan?.. ta tambayi kanta.

Babu kalar tambayar da Naila bata yiwa kanta ba kafin ɓarawon barci ya sace ta.

Ba ta farka ba, sai gab da Magriba shima Kaka ce ta tasheta.

Bata jima da yin wanka ba aka kira Sallar magriba a masallacin Dhahab. Dama tayi alolarta bayan ta yi wanka.

A ɗakinta tayi sallah saɓanin daa da takeyi a ɗakin Kaka.

Bayan ta idar gajeran saƙo ta turawa Sulaim tana tsimayin kiransa.

Tana zaune har aka kira Sallar ishsha'i amma Sulaim bai kira ba, zuciyarta babu daɗi ta miƙe ta tayar da Sallah.

A ɓangaren Kaka. Ta yi mamakin rashin fitowar Naila , amma da ta tuna ƙorafin Sulaim da ta wuni tanayi tun bayan dawowarta daga Makaranta ta gane dalilin maƙalewarta ta a ɗaki.

Dama sararin yin waya Kaka take nema, don haka ta kulle É—akinta ta kira mutanen Yankin Tudu, don jin labarin abubuwan da suke wakana.

SULAIM;
A ɓangaren Sulaim tun lokacin da aka sanar da shi, Naila ta kafe dole sai sun tafi Makaranta tare da Simbi ya ce abi bayansu.

Sulaim ya samu labarin Saukar Simbi daga Motarsu Naila da murmushi akan fuskarta, sannan bayan ɗan daƙiƙu wata Mota ta tsaya a gefenta. Amma har wanda ya bi bayansu ya share mintuna kusan goma daga inda yake zaune cikin mutanen da suke hada-hadarsu bai ga kowa ya fito daga cikin Motar ba, sai Simbi da ya hango tana magana ita kaɗai bayan tagama amsa waya. Bayan ɗan wani lokaci, ya ga motar ta bar wajen ba tare da kowa ya fito daga ciki ba, bayan tafiyar Motar, Motar gida ya iso ya ɗaukarta...

Bayan Sulaim ya gama saurarar bayanin wanda ya tura,
Bayanin Drivern da take kai Naila Makaranta ya shiga ya duba.

"Simbi ta sauka ne dalilin manta takardun Makarantarta a gida kamar yadda ta ce" yana gama karantawa ya rintse idonunsa. Bai yi ƙasa a gwiwa ba a wannan tsakankanin ya kira Ummu Malik..

Duk kiran da Naila take yi bai san ma tanayi ba saboda kansa da ya É—au zafi.

Ba shi da niyyar ramuwar gayya a cikin zuciyarsa, amma yana ganin idan bai motsa ba, babu abinda zai hana burin Jamil na shekaru aru-aru cika akansa, tunda yanzu shi kaÉ—aine ya rage sunyi nasarar kashe ragowar.

Abokanan Kasuwancinsa ya fara kira, su naimo mai Babban Islamic scholar kafin dare ya rufa.

Sallah ce kawai take tashinsa daga inda yake, tsabar kallon System idanuwansa har jaa sukayi.

Bayan Magriba da saƙon Malik ya riskesa na batun Sarkin Tsafin Yankin Tudu sai ya ƙara tabbatar da mai siffar Ɗayyib aka turo, domin yayi amfani da Simbi wajen rusa Dhahab tunda zuciyarta cike take da ƙyashi da hassada.

A wannan dare Sulaim ya shirya tafiya ƙasar Abyad.

Sai da ya yazo kwanciya sannan ya tuna kwata-kwata bai kira Naila ba tun wayar Asuba da sukayi.

Yana É—auko wayarsa da suke waya da shi ya samu miss calls É—inta rututu.
ÆŠan murmushi ya yi, a zuciyarsa yana faÉ—in "Allah Ne kaÉ—ai yasa kukan da zatayi da irin zagin da zansha a wajen Kaka"
Bayan ya danna kiranta ya jingine wayar yana jiran É—agawarta..

NAILA;
A ɓangaren Naila kukan takaici tasaka, baa ta alaƙanta ƙin ɗaga kiranta da Sulaim ya yi da komai ba, sai don ya nuna mata ita ɗin ba komai ba ce, amma har wani irin laifi zatayi mai da zata kirasa kusan sau talatin yaƙi ɗagawa?

Da lallashin Kaka ta ci abincin dare tana ci tana ƙorafin rashin ɗaga kiranta da Sulaim ya yi, har ta gama mitarta kamar kullum Kaka bata tofa mata ba.

Naila ta yi tunanin lamarin zai zo mata da sauƙi bayan ta koma ɗaki ta manta komai ta kwanta tayi barcinta hankali kwance, amma sai ta ga lamarin ya gagareta.

Tana cikin jan tsaki kiransa ya shigo mata...
[9/5, 9:01 PM] Maman Amatullahi: Nafisat Aliyu Sasaal


Page 17


NAILA;
Hannunta yana rawa ta janyo wayarta, zaman hular kanta ta gyara saboda video call ne. Sai da ta ɓata fuska sannan ta ɗaga..

fuskar Sulaim ce ta bayyana yana kwance. Murya ciki-ciki Naila ta ce;

"Barka da dare"

Sulaim bai amsa mata ba ya ce;
"Kin jini shiru ko, aiki ne ya riƙeni ina fatan kina lafiya"

Sai da Naila ta marairaice fuskarta sannan ta ce;
"Nasan babu wani aikin da ya yi maka yawa kawai kaƙi ɗaga kirana ne, saboda munje Makaranta tare Simbi, ban san maiyasa kake son shafamin baƙin jini ba, bayan kai kullum kana tare da Yayanta"

A ɓangaren Sulaim lumshe idanuwansa ya yi yana saurararta
Har ta É—isa aya bai ce mata komai ba.


Naila jin Sulaim ya yi shiru kamar ma baya kallonta sai ta fashe da kuka tana mitar ita fa ba wai aminta tayi da Simbi ba, kawai mutunci suke yi, a matsayinsu na Æ´an Yanki É—aya.

Sulaim dai bai ce mata komai ba, har sai da ta haƙura tayi shiru dan kanta sannan ya ce;

"Me kikeso Nailaa bayan alƙawarin da kika ɗaukarmin?"

Da sauri Naila ta share hawayenta ta ce; "ka barni muyi zumunci Ni da Simbi"

Sulaim idonsa da sukayi ɗanyi jaa ya buɗe saɓanin daa da suke lumshe ya na kallon fuskarta, sun kai wajen minti ɗaya haka yana kallonta tana kallonsa sannan a hankali ya furta;
"Na barki Naila shikenan?"

Kai Naila ta É—aga, alamar eh tana murmushi, "kamar sunana na ji ya kira" ta tambayi kanta a cikin zuciyarta.

Maganarsa ce ta cire mata kwakwanton da take yi a cikin zuciyarta;
"Na gaji Naila da safe zan kira ki, anan Kahala yanzu dare ya raba"

Da rawar murya Naila ta ce.
"Maiyasa yau ka kiran sunana baka ce Sa'aadati ba, ko har yanzu fushi kake yi da ni"

Sai da Sulaim ya É—anyi murmushi sannan ya ce;
"Na tambayeki me kike so bayan alƙawarin da kika ɗaukarmin, kika ce na barki da Simbi. kuma na ce na barki, karki ƙarawa kanki damuwa, Allah Ya tashemu lafiya"

Da wani irin zare idanuwa kamar zasu faɗo ƙasa Naila take tambayarsa "ka barni? ka barni fa ka ce? to ai ban fahimci ka barni ba, kayimin bayani"

Babu bayanin komai Sulaim ya datse kiransa.

A ɗimauce Naila tafara kira layukan wayarsa amma yaƙi ɗagawa.

Batasan sau adadi nawa ba ta kira layukan wayarsa a wannan dare ba amma sam bai É—aga ba.
Da dai ta fuskanci Dagaske bazai É—aga kiranta ba Kuka ta rushe da shi tana dafe kanta.

A ɓangaren Kaka ƙarfin kukan Naila ne ya tasheta daga barcin da bata jima da farasa ba.
A ɗimauce ta nufo ɗakin, babu irin bugun da batayi ba amma Naila taƙi buɗewa.

Kaka masifa da mitar maza ta kashe kanta ta fara yi tana cigaba da bugun ƙofar. Amma Naila tayi biris da ita.

Har dare ya raba Kaka bata koma ɗakinta ba tana tsaye jikin ƙofar Naila tana lallashinta ta ɓude tunda tayi masifa da zage-zage bata buɗe mata ba.

Gajiya Kaka tayi da tsayuwa da zama ta koma ÆŠakinta, haushin kafiyar Naila na damun zuciyarta

★har washe gari da Safe Naila ƙin buɗe ƙofarta tayi, duk naci da magiyar da Kaka tayi mata bata buɗe ba, wannan dalilin yasa ta nufi Sashensu Simbi.

SIMBI
A ɓangaren Simbi daƙyar Umminsu ta kwantar mata da hankalin ta nutsu, amma gargaɗeta da ta kiyaye, kuma duk inda taga mutumin ta riƙe addu'a a bakinta karta ƙara kulashi ko da yayi mata magana.

Har dare ya yi Simbi bata wani saki jikinta ba. Rashin sukuni da yadda ta dawo shiru-shiru ne yasa Barirah bayan ta dawo daga wajen aiki ta ce tazo ta rakata su je Siyayya.

Ba don hankalin Ummu Malik ya kwantaba ta barsu suka fita.

A motar Barirah suka bar Gidan. Wajan Siyayyar kayan shafe-shafe suka shiga, Barirah tana gaba Simbi tana binta a baya.

Kamar ance Simbi ta waiwaya gefen hagunta ta hango Dee cikin shigar wasu kayan daban ba irin wanda ta gansa da shi da safe ba.

Ya yi matuƙar yimata kyau a ido, tuni addu'ar da Mahaifiyarta ta ce tayi idan ta gansa ya bar kanta, burinta hankalinsa yayo kanta ta bashi labarin kuɗinfa da ya bata aljanun gidansu da batasan da su ba sun ɗauke. Tana so kuma ta tambayesa maiyasa bai kirataba, ta manta tsarin data saka wayarta na idan bata da lambar mutum ko ya kira ba zai zo ba.

Maimakon Simbi tabi bayan Barirah sai tasha kwanar inda ta hango Dee.
Tana kuwa matsawa tayi sa'a Dee ya hangota.

A ɓangaren Dee da murmushi ya nufo Simbi da wani salon tafiya da zai ƙara siye zuciyarta.

Da Muryarsa mai daÉ—in daya siye zuciyarta ya ce;
"Barka da dare Gimbiyata Simbi"

Ido Simbi ta lumshe, tana ƙanƙame wayar hannunta saboda daɗi.

Murmushi Dee ya yi, kafin ya ƙara ce wa; "idan babu damuwa zamu iya tattaunawa daga waje" ya ƙarasa faɗa yana giftata ya nufi hanyar fita.

KafaÉ—unta Simbi ta É—age dukka biyu tana juya idanuwanta kafin tabi bayansa.

Tsayuwarsa Dee ya gyara lokacin da Simbi ta ƙaraso gefensa. Sai da yayi gyaran murya Sannan ya ce;
"Wai wanene ya kafa Unguwarku, kyansa ya birgeni."
Shiru Simbi tayi kamar bata wajen.
Dee kansa ya É—an dafe ya ce;

" Ohh kiyi haƙuri naga kamar tamabayar bata yi miki daɗi ba, kyan Unguwar ne yasa na tambaya, amma kamar yanzu fuskarki tafi annuri Gimbiyata, da safe da muka haɗu kamar akwai abinda yake damunki ko kuma akwai wacce take son yi miki shishigi a cikin rayuwarki, kinsan ni ina da ƙwaƙwalwar saurin nazartar mutane, ko zan iya sanin wacece wannan, na taimakamiki da shawara ko wani abun?"

Simbi, Dee ya sosa mata inda yake yimata ƙaiƙaiya, duk da tana ganin kamar bai dace su tattauna irin wannan matsalar daga haɗuwarsu ba, sai dai a cikin zuciyarta ji takeyi kamar ana ingizata.

Zata yi magana kenan suka hango Barirah ta fito tana rarraba ido alamun ita take nema.

Dasauri Dee ya kamo hannun Simbi ya dunƙulamata wani ɗan kulli, sannan a gurguje ya ce

"Ko wacece ki sa mata a abinci zata koma inda ta fito ta bar muku Gidanku, amma baki faÉ—amin sunan wanda ya kafa Unguwarku ba"

Da harshenta da ya yi mata nauyi ta buɗe baki zata bashi amsa Barirah data hangota ta ƙwala kiran Sunanta.

Da saurin da ya bawa Simbi mamaki Dee ya shige tsakankanin Motocin dake wajen.

Ƙullin da ya damƙa mata ta riƙe da kyau.

Kafin Barirah ta ƙaraso tuni ta saita nutsuwar haɗe da zura ƙullin da Dee ya bata a ciki jaka.

A ɓangaren Ummu Malik, bayan fitarsu Simbi, baifi da mintuna goma ba, Malik ya kirata kar a bari kowa ya fita, ya kira Securities su datse Dhahab ba shiga ba fita.

Da fargaba take sanar da shi ai su Simbi da Barirah ba su jima da Fita ba, ihun salatin daya tashi hankalinta Malik ya saki, kafin ya ce takirasu kuma idan sun dawo babu shiga babu fita.

Ko da su Simbi suka dawo Simbi bata gayawa Mahaifiyarta ta haÉ—u da Dee ba.

Ummu Malik Kashedin da Malik ya ce ayi musu ta sanar musu jikinta a sanyaye.

Bayan Barirah da shiga É—akinta bakinta ta turo aganinta kawai izzar Malik É—in ne ya motsa banda haka, maiyasa zai ce ba shiga ba fita Sai kace ana wani tashin hankali, ko don kawai an É—aukewa Simbi kuÉ—i shine zasu takurawa Mutane.

Ita ma Simbi É—akinta shige ta kullo kanta ba tare da ta naimi jin ba'asin hukuncin Malik ba.

Ƙullin da Dee ya bata ta fito da shi tana kallo, zuciyarta na kitsa mata kawai ta sawa Naila ta tattara ta koma Yankin Tudu, Sulaim ya auri Barirah ko ya samo wata can daban, sai dai tayaya zata sa bayan Mahaifiyarta ta sanar da su ba fita ba shiga? Ɗakyar ɓarawon barci ya saceta.

★washe gari suna cikin yin kari Kaka ta shigo, tunda batasan sharaɗin da Malik ya zana ba, kuma Securities basu hanata zuwa ba.

Da magiya Kaka take yiwa Ummu Malik bayanin tanason Simbi ta biyota su lallaɓa Naila ta buɗe ƙofarta tun jiya ta kulle kanta taƙi fitowa.

A zuciyar Simbi Allah-Allah takeyi Mahaifiyarta ta amince.

Barirah kuwa tashi tayi tabar wajen tana taɓe baki.

Sai da Ummu Malik ta É—an nisa sannan tace Simbi ta É—auko Mayafinta su je, amma karta daÉ—e ta dawo da wuri.

Jikin Simbi har ɗan rawa yakeyi tabi bayan Kaka bayan ta soƙe ƙullin maganinta a ƙugu.

NAILA;
Kwana tayi kiran Sulaim, amma bai ɗaga ba, bayan Sallar Asubahi da ta ƙara kira sai ta ji wayar a kashe.

Tabbacin Kaka bazata tankawa matsalarta ba ne yasa tayi biris da ita taƙi buɗe mata ƙofa.

Bayan sallar Asuba da Kaka ta dawo tana ƙwanƙwasawa barci mai nauyi ya fara ɗaukarta .

Ko da ta farka ta fito bata ji motsin Kaka ba, bata damu ba.
Kitchen ta wuce ta haÉ—a É—an shayin da zata iyasha.

Tana cikin shan shayin Kaka da Simbi suka shigo.

Sama-sama Naila ta amsa gaisuwarsu, tana cigaba da shan shayin dayake ƙona mata baki.

Ƙin tashi Simbi tayi ta koma Sashensu.
Guri ta naima kusa da Naila t ta zauna tana janta da hirar da ba wani amsar kirki take samu ba.

Kaka dama ÆŠakinta ta wuce, bata zauna ba.


Naila surutun Simbi ne yake hawa kanta, sam bata son hayaniya tafison ta zauna shiru ko zata samo mafitar bawa Sulaim haƙuri.

Naila tunanin tayiwa Ummi Aysha wani abu mai daÉ—i ta kai mata ne yazo zuciyarta, daganan sai ta sanar da ita abinda yake faruwa ko zata taimaka mata.

Da ƙwarin gwiwarta ta miƙe ta nufi Kitchen, Simbi tayi wuf ta rufamata baya.

Simbi tana maƙale a gefen Naila tana yimata hira, Nailan tana amsa mata sama-sama tare da cigaba da abinda take yi.

Da salon dakar ciki Simbi ta ce;
"Me kike haÉ—awa haka da safenan, ayi dani nima zanci"
"To " kawai Naila ta ce ta cigaba da aikinta.

Naila ji tayi kamar wayarta da ta bari a parlor yana ƙara, da sauri ta saki aikin tana addu'ar Allah Ya sa Sulaim ne.

Bayan fitar Naila ta wannan damar Simbi tayi amfani, kafin ta biyo bayan Naila tana faÉ—in;
"Yau na ga bakyason kulani, bari na koma Sashenmu sai anjima"

Haushinta da Naila take ji yasa ko gefenta bata kalla ba ta cigaba da amsa kiran Abokiyar karatunta.

Bayan Naila ta koma Madafi ta gama aikinta, wanka tayi ta shirya, har ɗaki tabi Kaka ta sanar da ita zata je ɓangaren Ummi Aysha ta dawo.

Addu'ar a dawo lafiya Kaka tayimata.

Yadda Naila ta samu sashen Ummi Aysha anata hidima ne ya sanyaya jikinta, bayan ta miƙa mata Snacks ɗin da ta nannaɗe da foil paper sai ta kasa faɗar abinda ya kawota.

Ummi Aysha, da farin ciki ta karɓi kyautar Naila, tana ɗan janta da hira. Amma bata yimata hirar Sulaim ko abinda ya dangacesa ba har Naila ta bar Sashen.

UMMI AYSHA Batasan akwai matsala a tsakanin Naila da Sulaim ba, don haka ta ajjiye abinda Naila ta kowamata domin nunawa Sulaim idan ya iso.

SULAIM
A ɓangaren Sulaim duk kiran da Naila takeyi baisan tana yi ba, saboda wayar a Silent take, batun barinta da ya ce yayi, ya faɗa ne, don ta dawo hankalinta saboda ya lura son dayake mata na naiman kawo rashin girmamawa a tsakaninsu.

★Da Asubahi aka sanar da shi ansamu Malamin daya ce a naimomai, kai tsaye ya haɗa Malamin da Malik. Bayan gama wayarsa da Malik ya ankara da tarin kiran da Naila tayi mai, maimakon ya amsa kiranta data cigaba da kira da Asubahi sai ya kashe wayar gaba ɗaya.

Kamar yadda ya tsara bayan gari ya yi haske ya kira Mahaifiyarsa ya sanar da ita zuwansa.

Ummi Aysha tayi mamakin zuwansa a irin wannan lokacin tun da bai jima da tafiya ba, sai da yayi mata bayanin uzurine zai kowasa.
Da wasa da dariya take tsokanarsa ko dai Naila zai zo gani?
Sulaim murmushi kawai ya yi bai ce komai ba har sukayi sallama.

Shirye-shiryen tarbarsa Naila ta samu anayi a ɓangaren Ummi Aysha.

Kafin Sulaim ya isa Dhahab, Malik da Mallamin da daya je ya É—auko sun rigasa isowa.

A ɓangaren Malik bayan sun iso Dhahab da Mallam, a sashensa yayiwa Mallam masauki.
Mallamin ko hutawa baiyi ba ya ce akirawomasa Simbi.

Ko da Malik ya je, Simbi ta kulle kanta a ɗaki da sunan tana barci, da Malik ya dawo ya gayawa Mallam Simbi tana barci cewa yayi su tasheta, idan taƙi tashi su kirasa..

Lokacin da Sulaim ya iso ƙasar Abyad a sirrince aka ɗaukosa zuwa Dhahab babu chunkoson jami'an tsaro da yawan Motoci.

Ɓangaren Ummi Aysha ya sauka kamar waccen karon.

Ummi Aysha bakinta ya kasa rufuwa sai fara'a takeyi, tana jansa a jiki.

Abincin data shiryamai da kanta ta gabatarmai har da Snacks É—in da Naila ta kowamata masu kyan gani a ido ta jera a gefe.

Maimakon ya ɗaibi abinda yake gabansa, sai ya kai hannunsa kan Snacks ɗin da sukayi matuƙar burgesa.

Ummi Aysha dariyarta ta ƙunshe tana jiran yakai bakinsa sannan tayimai tsiyar wato Naila ta gayamasa ta kawo mata Snacks shine zai ajjiye nata girkin ya fara dana Naila.

Ya na kaiwa baki ya gutsira ya tauna ya haÉ—iye.

Dariyar Ummi Aysha ta saki tana yi mai tsiya ba tare da ta lura da sauyinsa ba.

A hankali ya jingine bayansa da kujerar dayake kai, Fuskarsa ya sunkuyar ƙasa, kafin wuyar ya karye kamar wanda barci ya kwashe a zaune.

Dariyar Ummi Aysha ne ya ɗauke lokaci ɗaya, ta miƙe ta nufosa tana faɗin;

"lafiyarka Sulaim menene haka ka karya wuya, kayimin magana mana!"
Chapter 3 · 0% Book details