CHAPTER 1;
Zinare Part 1 Complete Hausa Novel · about 103 min read
*DOGON TARIHIN AHALI MAI ƊAUKAR HANKALI DA ƘARFIN ARZIƘI TARE DA DARAJA TA MUSAMMAN A BABBAN BIRNIN ABYAD*🔥🔥🔥
Page 1
SUFYAN
Hour biyu ya yi a kan Gadon Asibiti kafin ya farka.
Gefensa Iyayen Sumaya ne da Æ´an uwanta . A can gefe kuma Sumaya ce a zaune itama idanuwanta sun kaÉ—a sunyi jajir alamun tasha kuka.
Guri ɗaya ya ƙurawa ido farkon zuwan Bushra da Yasar makarantarsu na dawomai;
"Bushra tayimin alƙawarin komawa Makaranta bayan na fara aiki a Babban Birnin Abyad, maiyasa ban ƙara ganinta ba?"
Wani sashe na zuciyarsa ya tambayi wani sashe.
Ƙasa-ƙasa Sufyan ya ce;
"Ni na wargatsa komai da kaina, ni na cuci kaina da kaina, son zuciyata ya sa na zaɓi Sumaya na wulaƙanta Naila. Kwaɗayin duniya da shagala yasa na manta batun komawata Makaranta na baje a Gida mai na'urar sanyaya ɗaki da Ofishi, yanzu gashi duk komai ya hargitse a cikin kwanaki ƙalilan, tayaya Malik yake iya saurarata bayan baya ganina, sannan kuma bai kasheni ba mai yake nufi da ni? Maiyasa ya yankewa Baffan Mahaifina Bashar harshe? Mai Mahaifina Ɗayyib yake nema da zuri'ar amininsa Abduh Dhahab dayake kukan rashinsa kullum? Menene suka jima suna ƙullawa tun zamanin kakannin-kakanni na? A kwai abubuwa dayawa da ya kamata ace na sani, amma son kyau irin nawa ya jagoranci mayar dani mai ƙaramin ƙwaƙwalwa da ƙaranci tunani. Kurakuraina a bayyane suke, amma ta yaya zan gyara su? Na ɗauki darasi mai girma, domin duk Namijin da yaba kyawunsa zai zama lagonsa to tabbas wata rana zai faɗa a komar danasani, saboda da shi Sumaya ta rijayeni har muka fara soyayya ba don tafi Naila kyan siffa ko na haliba sai don zuzuta kyawuna da take yawan yi.
Gane lagona na son a cemin ina da kyau yasa bamayin hirar minti goma bata nanata baiwar kyan da Allah yayimin ba, tare da zuzutani, irin zuzutawar da tasan zai É—imautarni, Ni kuma gareni hakan shine so, domin ni bandamu da na yabeta ba amma ita bata gajiyawa kamar karatun bita. Har a wasu lokutan ta kan cemin babu Namijin daya kaini kyau, maimakon na fahimci kalamanta a matsayin yabo, a matsayina na masoyinta sai na É—auka dagaske Ni É—in Namijine dana fi duk Mazan Abyad kyau, samun irina sai an tona"
babu wanda ya ji abinda Sufyan yake faÉ—a sai bakinsa da suka ga yanata motsi.
Sumaya da ta kasa jurewa ƙananun maganganun da yake yi da iya motsa laɓɓansa ta ce;
"Sufyan ka nutsu ka sawa zuciyarka salama, In Shaa Allah komai zai yi sauƙi banason wannan ƙananun surutan da kakeyi Kaji"
Kamar an mintsinesa ya miƙe.
"lafiya Sufyan?" Ta tambaya itama tana miƙewa
"Zan wuce bakin aikina, kwana ɗaya na tambaya" ya faɗa yana ƙoƙarin tattara Rigarsa.
Baijira ƙorafin da sukeyi ba, ya ɗora rigar saman shirt ɗinshi da aka ciremai ya kwashi wayoyinsa da Card ɗinsa ya bar ɗakin.
Da sauri Sumaya ta rufamai baya tana kiran sunansa.
NAILA;
A zahirin gaskiya ta so ace tafiyar Mota zasuyi domin ta kalli gagaruwan da suka fi kusa da Babban Birnin Abyad, amma haka ma bata ɓaci idan suna dawowa sai su biyo Mota.
Kamar ta yi tsuntsuwa ta ganta a Babban Birnin Abyad haka take jinta, Yasar sai dariya yakemata yana tsokanata da "ƴar ƙauye zata je Birni"
Ita da Kaka duk sai da sukaji tsoron hawa jirgi duk da ita Naima wannan ne karonta na biyu. Da sannu jirginsu ya É—aga daga Birnin Abyad zuwa Babban Birnin Abyad.
Bayan sun sauka
A kwai banbanci mai girma tsakanin airport É—in Birnin Abyad da na Babban Birnin Abyad.
ÆŠan waiwayowa Yasar ya yi ya ce; "ki kirata idan babu nisa, sai nasa Drivern da zai zo É—aukata ya fara saukeku kafin mu wuce"
"Okay Sir!" Naila ta ce tana saramai, dariya suka saki dukkansu har da Kaka.
Bugu É—aya Amira ta É—aga, jindaÉ—in Naila ta ce mata gata ta iso bayyana a cikin muryarta suka gaisa. Cikin zumuÉ—i Amira ta ce, zasu turo Driver idan kuma zata yya tarar Taxi to ta ce masa ya kawota DHAHAB.
Cire komai da Naila ta yi a ranta tun kafin tahowarsu dangane da Sulaim ne yasa batdamu da sunan da Amira ta ambata ba amma duk da haka sai da zuciyarta tayi bugun ɗakiƙu.
Bayanin Yasar zaisa Drivern da zai zo É—aukarsa zai sa ya É—aukesu tayiwa Amira basai sun turo Driver ko sun hau Taxi ba. Godiya Amira tayi tare da cewa ta kirata idan dun iso.
"ta ce Dhahab za'a kai mu" Naila ta faÉ—a bayan ta sauke wayar daga kunnenta tana kallon Yasar
Murmushin fuskar Yasar ne ya É—auke lokaci É—aya.
"Dhahab? Dhahab fa kikace Naila? Ki ƙara kiranta ki ji ko jine bakiyi da kyau ba, domin bare baya shiga Dhahab kai tsaye"
Musu da haƙiƙancewa ba halinta bane don haka ba tare da tace komai ba ta ƙara dannawa Amira kira, a sarari ta saka wayar saboda Yasar yaji da kunnen sa.
Tabbacin can za'a kaisu da Amira ta bayar yasa Yasar shafa gefe da gefen fuskarsa haÉ—e da furzar da huci ya ce;
"Kin ce biki zasu yi ko?"
Da sauri Naila ta ce "eh"
Wayar Abokin aikinsa ya kira ya tambaya.
Ya shadamai bai san da wani biki ba, amma bari ya bincika sashen hadimai yaji. Domin yaji kamar Æ™iÆ™ishin-Æ™ishin É—in amincewar Sir Malik akan wani biki da za'ayi a Æangaren.
Naila da Kaka dukkamsu shiru sukayi kowa da abinda yake saƙawa a ransa.
Burina ta isa Dhahab ta ga menene a ciki.
Kaka kuma mamaki takeyi saboda sunan da yayi mata kamanceceniya da na ahalin su Marigayi Abduh da kuma yadda Yasar sam bai nuna farin cikin inda zasu je ba kamar yadda ya nuna kafin tasowarsu.
Ko minti biyar ba'a rufaba aka ƙara kiran Yasar. Tabbacin shagalin Bikin ƴar ɗaya daga cikin masu dafa abincin ɓangaren Hadiman Dhahab aka bawa Yasar, kuma da izinin Sir Malik akeyin komai.
Tsaki Yasar ya saki, bawai baya son Naila taje bane tsoro yake ji kar wani abun ya samesu.
Bayani ya yi musu a can yake aiki shima, amma bai san da biki ba Gidan, ashe ɓangaren masu dafa abincin Hadiman Gidanne suke aurar da Ƴa.
Jakar daya so faɗuwa ta ƙanƙame.
Irin kuÉ—in da Amira ta ke kashewa a Makaranta da irin motocin da take hawa na faÉ—omata.
Bayan gama wannan tunanin a zuciyarta Naila ta ce;
"Hadimai kuma? Yanzu saboda kitson ƴaƴan Hadimai masu girki, girkin ma bana mutan Gidan ba a'a na Hadimai ƴan uwansu shine zasu gayyotoni tun daga Birnin Abyad har su biyamin kuɗin jirgi ni da Kakata? to ko dai suna nufin da kuɗin da zasu bayani muka hau jirgi? Wallahi bazai saɓu ba"
maganar Yasar ne ya katsemata zancen zucin da take yi.
"Da nasan Dhahab zakije da ban amincewa zuwanki Babban Birnin Abyad ba, wallahi tsoro nake ji, amma Allah Ya sa ku shiga lafiya ku fito lafiya"
Da sauri Naila ta amshe da;
"Ameen, Nima da sani banzo ba, tayaya zanzo yiwa Æ´aÆ´an Hadimai masu yin girki Hadimai kitso tun daga Birnin Abyad, nawa suka ci nawa suka bayani, ni dai kam sun cuceni wallahi"
"In dai Hadiman Dhahab ne zasu iya biyanki kuÉ—i sama da hasashenki Naila"
Yasar ya faÉ—a ya na shigewa lafiyayyen Motar da ya zo É—aukarsu. Lokaci zuwa lokaci sai ya ja tsaki har muka fita daga Airport gaba É—aya.
TSAKIYAR BABBAN BIRNIN ABYAD
Naila ba ta yadda zata fasalta kyan Babban Birnin a zahiri ba, amma yana da kyau irin kyan da bata taɓa gani ba ko a talabijin, Gine-ginensu da komai nasu na alfarma ne. Mutanensu masu kyan gani ne sama da na Birnin Abyad, babu hayaniya da karamniyar abubuwan hawa duk masu tsada ne da kyan gani a ido, dai-dai da Motocin sufurinsu abin kallone.
Baki, hanci da ido Naila ta saki ta kallon komai tare da haddacewa don ta bayar da labari wata rana.
DHAHAB
A zuciyar Naila ta ce;
"Zan iya kiran Dhahab haɗaɗɗiyar Daula ko na ce wata duniya da wani Attajiri ya ƙirƙira a Babban Birnin Abyad"
A Gajaren Gate É—in dayake bawa na wajen damar ganin rukunin Gidajen da aka yiwa gini na alfarma Motarsu ta dakata.
Jami'ai masu murÉ—aÉ—É—en fuska da jiki ne suke gaÉ—in É—an gate É—in da mutum zai iya haurawa a guje.
Wayarta Naila ta zaro ta kira Amira domin ta sanar da ita isowarsu.
Kafin Yasar ya sauka daga motar kanshi ya juyo bayan Naila ta gama waya, daga kujerar gaban da yake zaune zuwa saitin inda take.
A hankali yadda Kaka bazata ji sa da kyau ba ya ce;
"Abune da bai taɓa faruwa ba barin Hadimai suyi shagalin bikinsu a Dhahab, don haka ku kula da kanku Naila, ba lallai na ƙara kiranki a waya ba domin ga dukka alamu Sir Malik yasan da zuwanki, idan har ya san da zuwan naki kamar yadda na faɗa to dukka maganganunmu da zarar mun shiga Dhahab tamkar a kunnensa mu keyi, haka tsarinsu yake kuma ina kyautata zaton shine Malik ɗin da kike nema. Ko da wani zai tamabayeki game da Yankin Tudu, karki nuna kinsani ko kin taɓa rayuwa a ciki. Karki sanar da Kaka abinda na faɗa domin zata iya sakin layi har Sir Malik ya gane mun tattauna dake, duk da zuwa yanzu nasan labarin muna tare ya je mai.
Ki barta tayi maganganunta domin nasan bamu da wani mugun abu da zata faÉ—a wanda zai iya kawomana matsala. Ki kula Naila domin daga yanzu zakiyita ganin abubuwan da zasu baki mamaki da tsoro matsawar dagaske shi ne Malik É—in da kike nema."
Yasar yana gama faɗa ya gyara zaman rigarsa yana barin Motar. Zuciyarta tsabar bugu kamar zai fasa ƙirjinta ya fito.
Yasar ya na fita suma Naila suka fito ƙafafuwan Naila da take ƙoƙarin saitawa suna rawa.
Kaka kuwa har ƙanƙance idanuwanta takeyi wajen kallon rukunin Gidajen haɗe da yiwa Ubangijin da ya halicci talaka da mai arziƙi tasbihi.
Naila itama ƙarewa gine-ginen kallo takeyi tana ganinsu kamar furen da aka shuka.
A kan idanuwansu Yasar da Driver su ka nuna shaidar shigarsu Dhahab suka bar su Naila a tsaye. Suma ba su fi minti uku ba mota mai kyan gasken dayasa kaka ƙara ƙanƙame luggage ɗinta ya fito ɗaukarsu.
Kafin su shiga motar sai da aka caje kayansu da su kansu, Naila da Kaka sai zare idanuwa sukeyi, ƙarfin gwiwar da sukejin suna da shi na kawowa Yankinsu cigaba ko ta halin ƙaƙa nayin sanyi.
Naila da Kaka kallon duniya daban sukeyiwa inda zasu shiga Musamman da zancen Sarkin tsafin Yankin Tudu yake yawan faÉ—omusu, ashe shiyasa Allah Ya haramta duba, da yanzu bazasu wani damuba hankalinsu kwance.
Da Bismillah suka shiga motar da ƙamshinta ya sa Naila lumshe idanuwanta, yanayin fargabar da take ciki na barin zuciyarta. Mota ce da bata taɓa hasasowa kanta shiga irinta ba, ko ba komai suma zasu bayar da labari idan Allah Ya ƙaddara komawarsu Birnin Abyad.
Duk da Kasantuwarsu a cikin mota hakan bai hanasu yin Bismillah da addu'a yayin shiga gate É—in Dhahab ba.
MALIK
A ɓangaren da idanuwansa suke Lumshe yana sauraran maganganun da Yasar ya gama faɗawa Naila ta na'urar dake maƙale a kusa da Yasar ɗin bai sani ba, miƙewa ya yi yana yana gyara zaman earpod ɗin kunnensa.
Yaƙi taimakon Naila ne saboda bayason dawo da hannun agogo baya, shiyasa lokacin daya gane Bushra ta shigar da takardun bogin Sufyan na naiman aiki kai tsaye ya ɗaukesa don gina rayuwar Naila, sai dai daga baya ya fahimci Sufyan fa ba Naila yakeso ba, kuma ba zai taɓa sonta tsakani da Allah ba.. lamarin Naila lamarine da bai isa yayimasa kutse kamar na ragowar Mutanen Yankin Tudu ba, saboda wasu dalilai, shiyasa ya haƙura ya zubawa komai ido, ko ranar da ya ganta a gidansu Yasar tsaf ya ganeta har a wajen Siyayya duk ya gane, amma bashi da zaɓi akan lamarinta banda ya zuba ido.
kwatsam satin da ya wuce Sashen Hidaman Gidan suka naimi alfarmar mai kitso zata zo tayimusu kafin su fara shagalin Biki acan gidansu, da ya bincika ya gano Naila ce zata yi musi, sai ya basu dama su yi bikin ma a Dhahab gaba É—aya ko Allah zai sa a wannan karon ya samu damar takarar lamarin Naila..
Barkanmu da zuwa DHAHAB BABBAN BIRNIN ABYAD🤗
[8/8, 8:33 AM] nafisaaliyusasaal: SASAAL
2
A ɓangaren Sufyan
Duk kiran da Sumaya take ƙwalawa masa bai saurareta ba har ta cimmai.
"Menene dukka wannan Sufyan? I'm tired of all this, har sai tsahon wani lokaci zamuyi zaman farin ciki a tsakaninmu? kai ne kullum Baabanka da Ummeenka su kiraka tambayar kuɗi, yaya kake rayuwa? mai kakeyi yanzu? su yi ta tambayarka kamar baka da Iyali, it seems kamar ma ɓoyemusu kakeyi muna tare.
Yau ka firgita gobe ka zabura duk sai wahalar da ni kakeyi, yanzu gashi ka fito kanaji ina kiranka amma kayimin banza, gaskiya na gaji"
Sumaya ta faÉ—a cikin fushi.
"Ina ruwanki da kuɗin da suke tambaya, kuɗin ki ne? Okay so kikeyi kar su kira su tambayi lafiyata saboda ke ko? Kinsan ya ya akayi ma na zo nan eh!? Kin gaji da zama da ni kika ce ko? To kije na sakeki mun rabu nima na gaji" Sufyan ya ƙarasa faɗa ko a jikinsa, yana ƙoƙarin tarar Taxi .
Cikin masifa da hargagi Sumaya ta zagayo saitin fuskarsa ta ce;
"Daga ganin wannan Yankin naku dole ka zama Violet person! tunda na lura kamar da rashin zaman lafiya da wulaƙanta Ɗan adam aka gina Yanki..."
Marin da zai sauƙaƙawa Sumaya gane da gaske Sufyan Violet person ne ya sauke mata a dama da hagun fuskarta yana tura ta gefe, har sai da ta faɗi ƙasa dafe da ƙuncinta. Kafin ta yunƙura ya tari Taxi ya shige.
Ƙurawa Taxin idanuwa tayi kamar zasu iya dawo da Taxin baya.
Ganin dai da gaske Sufyan ya tsere mata bayan furta kalmar sun rabun da ta tsana, sai ta durƙushe a ƙasa tana kuka.
A haka Æ´an uwanta da suka ji shiru suka sameta.
Tana kuka ta na fizgewar su ƙyaleta ta bi Sufyan suka turata cikin Mota.
A ɓangaren Naila
Daa can yawan surutu da rawar kai ba halinta ba ne, amma maganganun da Yasar ya faɗamata kafin shigowarsu Dhahab yasa ta ƙara nutsuwa tare da gumtse bakinta.
Basu yi wata tafiya mai nisa ba, suka sha kwana, anan rukunin Gidaje masu kyau suka bayyana, ba irin waÉ—anda suka wuto ba.
A hankali Driver ya dai-daita parking duka sauko.
Cikin rashin riƙe zance duk ƙanƙantarsa Kaka ta ce;
"Yanzu Bawan Allah menene abun hawowa Mota a nan? ji fa ga baki ga hanci, ku dai kam masu arziƙi akwai ku da son jiki wallahi" ta ƙarasa faɗa tana kallon hanyar da suka biyo.
Hannunta Naila ta kama haÉ—e da É—an matsawa.
Maimakon tayi shiru tunda ta fahimci abinda Nailar take nufi sai ta ƙaracewa;
"au to nayi shiru."
Kamar kurma haka Drivern daya É—aukosu yake babu magana babu murmushi balle dariya.
Da farin cikin Amira ta tarbi su Naila zuwa ainihin cikin gine-ginen.
Kai Naila a ƙasa su ka shiga saɓanin Kaka da take kallon komai dalla-dalla domin idan ta koma Birnin Abyad ta samu abun bayarda da Labari.
Tarba na ban girma aka yimusu a living room ɗin daya amsa sunansa. Kowa ya shigo sai ace wannan itace mai kitson da Sir Malik ya amincewa shigowarta Dhahab daga Birnin Abyad. Ko sun juya da sunan tafiya sai sun ƙara waiwayo sun kalleta, ga shi babu damar yin magana kar su je ana jinsu.
A wannan rana hutawa kawai su Naila su kayi sai ɗan hira sama-sama da Kaka take yi da yayar Mahaifin Ameera da take aurar da Ƴa.
Duk Hadiman da suke shigowa Masha Allah masu kyau da su, ga kyan fatar dake nuna kwanciyar hankali da wadataccen cima mai kyan da suke samu, uwa uba albashin mai tsokar da zai sauya rayuwar mutum da ahalinsa, amma fa banda munafiki da maci amana.
Masauƙin Ɗaki daban-daban aka yiwa Naila ita da Kaka amma suka nuna ɗaya ya ishesu.
Daga Naila har Kaka kallon ko ina na É—akin da aka kaisu sukeyi kamar ba mazauna Birnin Abyad, to idan Hadiman Gidan suna da irin wannan gatan to ina ga mutan Gidan? Kaka ta tambayi kanta tana dariya.
Duk yadda Kaka take jan Naila da hira Naila ba tacemata komai ba, cikin takaici ta ce;
"Wai ni Naila wanene wannan Sir Malik ɗin da idan aka ambaceshi sai na ga sun ƙara waiwayo sun kallemu anya babu wata a ƙasa kuwa?"
Shiru Naila tayi kamar bata jita ba, wannan dalilin yasa ta fusata tana cewa;
"Wai ni Naila mai ya canzakine kin zama kamar wata kurma, sai surutu nakeyi kin ƙi kulani, ko don kinga zaki samu kuɗi shine zaki fara wulaƙantani tun yanzu?" Kaka ta ƙarasa tambayar tana kallon Naila.
Naila batasan sanda ta saki dariya ba har da kwanciya.
"Kaka har wani irin kuɗi zan samu da zan kasa yi miki magana, ko na wulaƙanta ki? Kaka idan aka je baƙonta kame kai akeyi, kuma na ga kamar kin manta da abinda ya kawo mu" Naila ta faɗa bayan ta tsagaita da dariyar da take yi.
Ɗan jim Kaka ta yi kamar mai tunani sai kuma ta zaro wayarta batare da ta ƙaracewa komai ba.
Har barci ya ɗauke Naila Kaka suna waya da Mallam yana yi mata bayani tare da ƙaramata wasu addu'o'in.
★Barcin mai daɗin da sukayi a lallausar katifar audigar dake Ɗakin da aka basu yasa suka makara sallar Asuba Kaka har da ɗan yawun barcinta a gefen kumatu.
Da sauri Naila ta watsa ruwa ta É—oro alolar sallar Asubahi saboda Masallin da ta ke kyautata zaton a gidan yake har sun tayar da Sallah.
Da gari ya yi haske bayan an kawo musu lafiyayyen Abincin kari, sun karya, Ameera ta zo tafiya da Naila.
Yini sukayi tana kitsa musu gashin kansu mai tsaho da shaiƙi, duk hirarrakin da sukeyi Naila batasa musu baki ba, na dariya dai takan ɗan murmusawa lokaci zuwa lokaci.
Basu gama ba sai wajen ƙarfe taran dare.
A wannan dare cikin fargabar da ya ragewa su Naila saura kwana É—aya su koma Birnin Abyad ba tare da sunga wani canji daga abinda suke zargi ba Barci ya É—aukesu.
A rana ɗaya Ubangiji yake ƙaddara ɗaukaka ko kawo ƙarshen zaluncin da al-umma suka jima a ciki, duk da za'ayi shafe shekaru ana gwagwarmaya ba tare da anci nasara ba.
★Washe gari da Safe kamar jiya Ameera ta shigo kiran zamu gaisa da BARIRAH tace kitson da ta gani a kawunansu ya birgeta a kira Naila ta ganta ko zan yimata irinsa.
BARIRAH itace wacce aka wakilta daga cikin Dhahab ɓangarensu Malik domin ta isar da kyautar da Mahaifiyar Malik tayiwa Amarya saboda ita bazata samu damar fitowa ba.
Ta canza irin canjin da zaiyi wahala idan mutanen Yankin Tudu suka ganta su ganeta, ta ƙara fari da kyan jiki kamar ka saceta ka gudu, taƙama da izzarta da talauci ya danne a shekarun baya ya bayyana daga yanayin zamanta.
Kamar bata taɓaganin mai irin halittarta ba haka Naila ta nuna tare da gaisheta tanayin ƙasa da kanta alamar girmawawa.
A É—an firgice Barirah ta amsa tare da furta tambayar da ta kasa dannewa;
"Ya ya sunanki? "
A taƙaice ta ce "Naila"
Sai da ta ƙara gyara zamanta tana matse yatsun hannunta da zobunan zinare ke jere waje ɗaya ta ce;
"Daga wani Yanki kike bayan Birnin Abyad, ina nufin asalin Æ´ar ina ce ke?"
Cikin ladabin da ya ɓoye rawar da jikin Naila yake yi ta ce;
"Birnin Abyad shine asalin Yankin da na fito"
Ba ta gamsu ba tace akira mata Kakar Naila.
WAIWAYE;
Shekarun baya rashin jituwar Mahaifin Naila da ƴan uwansa yasa Mahaifinsa bayason Mahaifiyar Naila, wannan dalilin yasa ya hana Kaka zuwa Gidansu Naila, a waccen lokacin sai ya ce ita take zuga Mahaifiyarta basa jituwa da Matan Yayyan Mijinta tunda ba ita ta haifesu ba. Wannan dalilin yasa su SIMBI da BARIRAH ba su wani san Kaka ba, sannan kuma daga Shekarun da suka bar Yankin Tudu zuwa yanzu Kaka ta ƙara tsufa, irin tsufan da shekarunta ba su kai ba, saboda jarabawar da yayita samun mu.
DAWOWAR LABARI
Wannan dalilin yasa ko da Kaka ta fito Barirah bata ganeta ba, itama Kaka da bawani saninta tayi ba sam bata ganeta ba.
Ko da ta tambayi Kaka, bayan Kaka ta gaisheta kai tsaye Kaka tace mata su asalin Æ´an Birnin Abyad ne.
Cikin rashin gamsuwa da kuma son Æ´ar uwarta Simbi ta bambance mata da gaske Naila ce ko ba ni bace ta ce;
"Salon kitson ki ya birgeni matuƙa, kuma an sanar dani lokacin tafiyarku ya yi, inason ku ƙara kwana biyu gobe sai kiyimin jibi ku wuce. Hadimai zasu rako ki."
Bata jira amsar Naila ba ta miƙe tana sharce gumin daya tsatsafomata a goshi duk da na'urar sanyaya wajen da yake aiki 24/7.
Bayan ta kai ƙofa sai da ta ƙara waiwayo ta kalli Naila sannan ta bar living room ɗin.
Su na shiga É—aki Naila ta zube akan katifa tana dafe saitin zuciyarta.
Tambaya Kaka ta titsiyeta da shi;
"Naila wacece wannan? sam banyarda da ita ba, ki yimin bayani menene ya haÉ—aku? kinsan ta ne a wani wajen? maiyasa take son sanin ko daga wani Yanki muke?"
Rasa tambayar da zata fara amsawa a Kaka tayi. Don haka ta fara bata labarin wacece Barirah ba tare da tsoron Malik yana jin su ko baya jin su ba kamar yadda Yasar ya faÉ—amata, tunda Ubangijin da zai karesu Yana tare da su.
Manyan idanuwanta Kaka ta zaro kamar zasu zubo ƙasa
"Barirah ƙanwar Malik?? tayaya Naila????"
MALIK!
Duk maganganunsu Naila da abubuwan da Barirah ta aikata duk bai samu damar saurara ba saboda uzurin da ya taso mai.
Kafin ya tafi uzurin da ya taso masa sai da ya kira Bushra ya kwantar mata da hankali ta juyemasa labarin rayuwar da Naila tayi da Sufyan da kuma wanda take kanyi da Kakarta.
Kamar yadda yafi tafiya a lokutan Asubahi kafin ketowar alfijir ko Cikin dare, a yau ma haka ya yi. Baƙaƙen kayan da ya fi amfani da su ya sanya hatta gilashinsa da ya sakaya idanuwansa dashi baƙine. Da ƙaramin Luggage ya bar Dhahab zuwa nahiyar Turai.
YANKIN KAHALA BIRNIN HONOLULU JAHAR HAWAII
Lemon da aka ajjiyemai Malik ya taɓa haɗe da ɗanyi balance yana danna wayarsa.
Ƙarfin ƙamshi da takun dake ƙara kusantosa ne yasa ya ɗan zabura yana gyara zamansa haɗe da zame baƙin tabaran fuskarsa.
Balmin Shirt dark blue, da Black three quarter trousers Matashin da ya bayyana a gaban Malik yake sanye da su.
Zama ya yi a Couch É—in da ke kallon na Malik suna fuskantar juna.
Malik zamansa ya gyara tare da haÉ—e yatun hannusa waje É—aya bayan ya tattaro nutsuwarsa sannan ya ce;
"Barka da yamma"
Maimakon amsa fararen idanuwansa dake kan fuskar Malik ya lumshe, wanda a wajensa shine a madadin amsar gaisuwa.
A hankali Malik ya ɗago fuskarsa bayan ya ƙara saita nutsuwarsa, cikin daƙiƙa biyu ya ƙarewa Matashin da ƙirar jikinsu yake kusan iri ɗaya kallo, sai ɗan tsaho da Matashin yafishi, kansa ya mayar ƙasa a hankali ya motsa laɓɓansa da tambayar "ya ya mai jiki?"
Tambayar ya ya mai jikin da Malik ya yi masa ne yasashi ƙara ɗago idanuwansa yana kallon cikin idanuwan Malik.
Da É—aurarrariyar fuskarsa mai tsananin kyan gasken dake É—auke da idanuwa masu haske ya cigaba da kallon Malik ba tare da ya ce komai ba.
Kasa jurewa kallon fuskarsa yasa Malik yin ƙasa da nasa kan yana murza Diamond Bracelet ɗin hannunsa.
ya ɗauki daƙiƙu yana karantar Malik kafin ya furta;
"Alhamdulillah" da muryasa mai tsada a wajen mutane da daɗin sauraro ga wanda ya samu ji😄
KAFIN MU SAN WANENE WANNAN MATASHIN BARI MU SAN AINIHIN DALILIN DAYA JANYO KASHE-KASHE A MARAUTAR YANKIN TUDU DA KUMA SU WANENE SUKE AIKATA SHI, SANNAN MUSAN SHIN DAGASKE SU ABDUH DHAHAB SUN MUTU, KO KUWA SUNA RAYE KU BIYO NI;
[8/8, 8:34 AM] nafisaaliyusasaal: SASAAL
3
Kamar yadda Kaka ta taɓa bawa Naila labari a baya a zamanin mulkin Sarki Musa ya yi sauƙin kai ga mutanen Masarautarsa da na Yankinsa wannan yasa kowa yake sonsa.
Jamil Kakan Jalal shine Aminin Musa tare suke komai, sai dai daga lokacin da Sarki Musa ya tura Abdulyasar Babban Birnin Abyad wajen abokanan hulɗarsa da sunan naiman ilimi ya dawo da dukiya har ya samu laƙabin Dhahab, komai ya canza a ɓoye a ɓangaren Jamil acewarsa;
"mai zaisa Sarki Musa ya munafurceni ya kai É—ansa inda zai zama Attajiri amma bai haÉ—a da nawa Æ´aÆ´an ba?"
Wannan arziƙi da Abdulyasar ya dawo da shi, shi yazama tsatsa a zuciyar Jamil da zuri'arsa ba tare da kowa ya sani ba.
Jamil mutum ne mugun gaske kuma mai riƙo da kafiya. A kwai fahimta sosai tsakaninsa da Sarki Musa, amma wannan dawowar ta Abdulyasar Dhahab da arziƙi mai tarin yawa daga Babban Birnin Abyad sai ya gurɓata son dayakewa Sarki Musa, a take ya fara shirya kaishi ƙasa duk da bayanin da Sarki Musa ya yi mai dayaga alamar kamar baiji daɗi ba;
" Ni ban tura Abdulyasar domin ya naimi kuɗi ba balle ya tara arziƙi. Na turashi ne domin ya naimi ilimi ya kuma samu kariya daga ragowar Iyalina" maganganun Sarki Musa tamkar rainin hankali suke a wajen Jamil da kuma ƙara tunzura zuciyarsa, amma bai nuna ba ya barwa zuciyarsa.
A hankali shida ragowar Iyalin Sarki Musa da suke ganin ya fifita Abdulyasar akansu suka yi masa sihirin da ya sashi kwanciya dogon jinya har Ubangiji Ya ƙaddarar ajalinsa.
Cikin ikon Allah, Allah Ya bawa Jamil tsahon rai har Ubaidullahi Dhahab Ɗan Abdulyasar ya ƙara zama mai arziƙi akan idanunsa. Wannan yasa ya yi alƙawari tare da alwashin yaƙi da wannan Laƙabi da suke amfani dashi, har ƴaƴansa ya cewa; "laƙabin Dhahab(Zinaren) da suke yiwa kansu sai ya zama Tarihi a Yankin Tudu nayi alƙawari! Kuma ko bayan raina ku sanar da jikokina su shirya Yaƙar Dhahab har sai sun ɓatar da fuskokinsu a Yankin Tudu da duniya gabaki ɗaya. Tunda Musa ya ci amanata to nima zanyi ramuwa gayya gareshi, ramuwa mafi ciwon da babu kamarsa!"
Jamil bai ɗora zuri'arsa akan komai ba sai hassada ƙyashi da tsananin mugunta tare ramuwar gayya ga duk wanda ya cucesu. Da haka ya raini Mahaifin Jalal, shima Maihaifin Jalal da haka ya raineshi, shima Jalal ya raini Ɗayyib a haka Ɗayyib kuma ya kasa rainon Sufyan daya fita Zakka.
Kamar yadda Jamil ya yi alƙawari kuma Allah Ya cikamasa Kafin ya koma gareSa ya girbi abinda ya shuka, Jamil bai bar duniya ba sai da yaga gawar Ubaidullah, kuma ya mallaki filin mafi girma a kaf faɗin Yankin Tudu ya haɗa har da na Al'umma a ciki...
Tun suna yara aka shirya Abotar Ɗayyib da Abduh Dhahab saboda da Ɗayyib zasu yaƙi Abduh. Ɗayyib tun yana yaro akwai basira da nuna kamar bai san komai ba kuma shi babu ruwansa a kan duk wata badaƙala dake faruwa a Masarautarsu wannan dalilin yasa Abduh ya yarda dashi irin yarda dake tsakanin Aminai. Irin wannan Abotar Ɗayyin yaso ƙullawa tsakanin Sufyan da Sulaim sai dai Zaren ba kalar yadin ba ne!
*Menene ya faru da Abduh da Sulaim? Da gaske sun mutu? Wanene ya kashe su? Wanene ya yankewa Dattijo Junaid harshe? Wanene Abdallah kuma wanene ya ƙullamai sharrin fyaɗe? Da gaske Salman ya mutu, wanene ya kashe shi? Idan da gaske ya mutu to wanene Uzair?
Ya ya akayi Malik ya yi kuÉ—i?
ABDUH DHAHAB; tun da ya kalli fuskar ÆŠayyib lokacin da ya je dubashi a Gidan Jalal, maganganun da Abokin ÆŠayyib ya faÉ—amai a sirrince ya faÉ—omai na ÆŠayyib yana son ganin bayansa ya shirya sayar da komai ya bar garin ya hana shi sukuni.
A take Abduh ya yankewa kansa shawarar tafiya amma ya yi alƙawarin ko ya tafi zai turo wakilin da zai kawowa Yankinsa cigaba, domin da wannan kuɗirin Iyaye da Kakanninsa suka rasa Ransu.
Tun bayan sayar da Tukwanensa ga Baƙin Turawa, ya je Iyakar Yankin Tudu ba tare da sanin kowa ba, ya kira Abokanan Kasuwancinsa da suke mutunci su Naima mai Matsuguni a ƙasar Abyad.
Tunda ya dawo a ranar yake tsammanin zuwan wani daga Masarautar amma ya ji shiru.
Bayan kwana biyu da wannan Mutanen Masarautar Yankin Tudu suka cimmai.
Baisan san da Sulaim ya tashi ba, amma ihun Sulaim na farko ne ya tashesa. Tsaf ya ke kallon yadda ÆŠayyib yake yankarmai jikin ÆŠa mafi soyuwa a garesa domin ta muryarsa ya gane ÆŠayyib ne.
Bai motsaba domin bashi da ƙarfin yaƙar su saboda yasan bashi kaɗai bane dole akwai wasu. Sai dai cikin ikon Allah, hankali Ɗayyib ya kai kan Iyalinsa Mairam. Ɗayyib yana tafiya wajen Mairam Abduh ya sanɗa ya fara jan Sulaim a hankali dai-dai lokacin da Mairam take kallonsa, saɓa Sulaim ya yi a kafaɗa yana jan buhun kuɗin da yake rinjayarsa a hankali.
A hankali ya bi ta ƙofar baya ya isa gidan Mallam. Mallam da ya riga yasan da batun shirin Masarautar Yankin akan Abduh kamar yadda Abduh ya sanar mai a tsakar gidan yake sallar dare ba ya komawa cikin ɗaki har sai yayi sallar Asubahi ko Allah zaisa Abduh ya ƙwanƙwasa.
Don haka Mallam yana ji an ƙwanƙwasa ƙofa ya buɗe da sauri kafin ya nufi kekenunsa, da ƙarfin hali Abduh ya iso wajen Mallam da sauri.
Mallam shi ya É—auki kuÉ—in Abduh ya goya a baya kekensa, shi kuma Abduh tuni ya nufi Asibiti da Sulaim da É—aya keken.
Mallam saƙon Iyalinsa ta tafi Yankinsu ya bata idan Asubahi tayi, zai biyo bayansu idan ya dawo.
Bayan sun isa Mallam a gaggauce ya É—aurewa Sulaim ciwo ya ce;
"Abduh ku tafi wataƙila su iso garemu, bana so su cimmana, In Shaa Allahu wata rana zamu sake haɗuwa ka ji" ya ƙarasa faɗa da rauni a muryarsa. Kuka Abduh ya fashe dashi yana ƙara saɓa Sulaim a kafaɗarsa. Suna tafiya suna kuka, sai da suka ɗanyi nisa kaɗan sannan Mallam ya ajjiye buhun kuɗin yana kallon Abduh kafin ya fashe da kuka, Abduh yana kiransa da magiyar ya dawo ya bashi kuɗi amma Mallam bai juyo ba sai hannu daya ɗagamai.
Da gudu Mallam ya ƙaraso Asibitin sai dai yana buɗe ofishin likita ya samu ƴan shaye-shayen wasu Yankin su uku maza a zaune wai suna neman likita, yana zuwa Mallam ya ce musu ya nufi hanyar fita domin zuwa Gida. yana fitowa yayi cikiɓus da su Ɗayyib.
Zage-zage da neman da suke yiwa su Abduh yasa ƴan shaye-shaye neman maɓoya gudun karsu kashe su, sai dai tura Mallam ciki tare da sanyawa Asibitin wuta ne yayi ajalinsu dukka.
Wannan dalilin yasa aka samu gawar mutum huÉ—u.
Nannaɗewar Ɗayyib cikin abun rufa na da alaƙa ne da ƙarfen da Sulaim ya cakamai gudun Iyalinsa da mutanen gari su sani, dama kuma ya ƙirƙirarwa kansa ciwo ne, don kawar da hankalin Mutanen Yankin daga kansa, Surutai da Kukan da yake yi duk don ya kawar da zargin mutanene a kansa tunda kowa yasan shi ɗin Aminin Abduh ne.
Tun lokacin da Dattijo Junaid ya ɓullo da zance bincike aka waɗanda suka sakawa Asibitin Mallam wuta, Bashar ƙani ga Jalal uwa ɗaya uba ɗaya ya fara shirin kawo ƙarshen Dattijo Junaid. Sai dai sun tsayar da shawarar kashesa ba mafita bane, Bashar da kansa ya kawo shawarar a cirewa Dattijo Junaid harshe, kuma ya jagoranci Ƙattin matasan da suke yi musu aiki har gidan Dattijo Junaid. Bayan matasan sun banƙare Dattijo Junaid, Bashar da hannunsa ya yankemai harshe. Tare da gagargaɗin idan ya bari kowa ya sani ko ya ƙara tsoma baki akan mutuwar su Abduh kansa zasu cire.
Abduh ya ci baƙar Azaba shi da Sulaim. A jeji suka kwana, sai da gari yayi haske suka samu amalanken daya fitarsu da su Iyakar Yankin tudu.
Ba su yi minti biyu da zuwa ba Abduh ya naimi mai maganin gargajiya domin duba ciwukan Sulaim, saboda duk azabar dayake ji baya magana sai rawa da jikinsa yake yi.
Duk irin jan da Abduh yake yiwa ƙaton buhun hannusa babu wanda ya kawo zunzurutun kuɗi ne a ciki.
A lokacin babu masu musayar kuɗi a Iyakar Yankunan balle ya canza su zuwa na Ƙasar Abyad, kuma tsoron kai kuɗin Ɗan ƙaramin Bankin da ke gurin yake yi kar wani ya cucesa. Cikin ƙasa da hour biyu Sulaim ya samu Barci a rumfar mai maganin da suka raɓe. Shima mai magani bai san kuɗi bane a ƙaton ɓakin buhun wajen Abduh har yamma tayi suka samu Motar Kayan da zai tafi Birnin Abyad.
A bayan mota Abduh da Sulaim sukayi tafiyar kwanaki. Ko da suka isa, a bayan garin Abyad suka naimi matsuguni.
Washe gari da tambaya Abduh ya samu addireshin Abokin kasuwancinsa daya kira a waya.
Harun É—an asalin Abyad ne da Æ´aÆ´ansa biyu Abdallah da Bushra.
Bayan sun haÉ—u da taimakon Harun suka kai Sulaim asibiti. Har suka gama hidimar Asibiti Abduh bai nunawa Harun tarin kuÉ—in da ya zo da su ba saboda tsoron kowa yake ji.
A lokacin Abdallah babban É—an Harun saurayine daya yi karatun likitanci yake kan naiman aiki Bushra kuma tana Æ´ar mitsisiya.
Bayan kwana biyu
Abduh ya kasa daina tunanin mutanen Yankinsa da su yake kwana yake tashi. Cikin girmamawa Abduh ya roƙi alfarmar Abdallah yaje Yankin Tudu ya koyamusu aikin likitanci da zasu dogara da kansu, ya yi alƙawarin biyansa duk wata.
Da farko Harun bai amince ba amma dayaga Abduh ya lissafo kuɗin wata biyar ya bawa Harun ya canza zuwa na ƙasar Abyad, a take suka shirya tafiyar Abdallah.
A wannan lokacin ne Abdallah ya bayyana a Yankin Tudu a matsayin jami'in jinyar da Gwamnati ta turo.
ÆŠayyib da kansa yayiwa Yarinya fyaÉ—e ya ajjiyeta a bayan ofishin Abdullah.
A wacce lokacin Harun Abokanan hulÉ—arsa na bakin Iyakar Yankin ya tura suka É—auko Abdullah a Yankin Tudu, domin tun a daren da abun ya faru bayan Abdallah ya dawo hayyacinsa ya kira waya ya sanar.
Bayan Abdullah ya tsira daga Mutanen Yankin Tudu
Daga lokacin Harun Mahaifin Abdallah ya tattara komai nasa ya bar su Abduh batare da ƙara waiwayarsu ba.
Jin mutuwar Mallam a bakin Abdallah yasa jikin Abduh ƙara rikicewa kullum ba shi da aiki sai kuka..
Sulaim baya magana, komai Mahaifinsa ya yanke dai-dai ne, sai dai a gaɓar da mutanen Yankin Tudu suka ƙullawa Abdallah sharri suka kashe Mallam Sulaim ya cewa Mahaifinsa ya kamata ya manta da al'amarin mutanen Yankinsu su fuskanci rayuwar da take gabansu, domin komai yawan kuɗin da yake tunanin ya tara wata rana zai ƙare.
Tunanin halin da mutanen Yankin Tudu suke ciki da wanda Mallam yake cikine ya kwantar da Abduh ciwo duk da nasihar da Sulaim ya yi masa, sannan Bautar da ya kwashi shekaru ya na yi ba tare da hutawa ba ya taka rawar ganin kwantar da shi jinya mai tsaho.
A lokacin Sulaim ya fara fuskantar rayuwa, ya kuma tsaya tsayin daka domin gina Dhahab ɗin da Jamil yayi alƙawarin rusawa.
Da farko buhun kuɗin Mahaifinsa ya ɗauka zuwa kasuwar canjin da suke yawan zuwa da Harun, saboda kaɗan-kaɗan Abduh yake canza kuɗin har Harun ya gujesu bai taɓa sanin akwai dukiya mai yawa a tare da Abduh ba.
Wuƙa Sulaim ya soke a ƙugunsa. Su kansu masu canjin sai da suka tsorata da irin kuɗin da Sulaim ya kawo a buhu, bayan sun canza masa ya ƙara ɗuresu ya taho gida. Ashe wasu sun biyosa sun ga Gidan.
A wannan dare Æ´an daban da aka turo daga kasuwar canji suka farmaki Sulaim ya kawo kuÉ—in da ya canzo.
Sulaim ya yi yanke-yanken daya ƙara gusar da imaninsa a wannan dare domin bai barsu sun tsira da ko sisi ba. Duk Abduh yana kwance jikinsa babu ƙarfi sai kuka da yake yi.
Sulaim sai da ya share sama da sati baya barcin dare na ranar ma na lokaci ƙalilan yakeyi, suma ɓarayin haka suka share kwana uku suna zuwa su yayyaki juna da Sulaim, ƙarshe su gudu babu ko sisi.
A fuska Sulaim sai ya koma kamar Ɗan daba saboda ƙaton Yankar da ke tsakanin kuncinshi da idonsa.
Mai mota ya nemo suka tattara kayansu zuwa cikin Birnin Abyad, a ranar Sulaim ya binciki ofishin dillacin gidaje suka kama gida mai sashe-shashe.
Washe gari da tambaya Sulaim ya samu Banki bayansa É—auke da Abduh a goye. Bayan ya buÉ—e komai ya wuce da Babansa Asibiti.
A Asibiti Sulaim yake kwana, har Abduh ya yi sati biyu suka tattaro suka dawo gida ba don ƙarfin jikin Abduh ya dawo gaba ɗaya ba, sai lallaɓawa da yake yi.
A ranar da Sulaim ya ƙarasa kai dukka kuɗaɗensu Banki tunda kaɗan-kaɗan yake kaiwa, a ranar ya yi fafutar neman maƙera a Birnin Abyad.
Ƙaramin ma'aikatar ƙera Tukwane na Salman Ɗan asalin ƙasar Abyad mai ƴaƴa ƴan biyu Maza Zubair da Uzair Sulaim ya samu. Sai dai bai ɗaukesa aiki ba ya ce yaje ya dawo.
★washe gari da Sulaim ya koma, Salman Æ™in kulasa ya yi acewarsa Sulaim kama yake yi mai da ÆŠan daba kar ya zo ya kasheshi ya kashe mai Æ´aÆ´an da yake ji dasu....âœðŸ»
[8/8, 8:36 AM] nafisaaliyusasaal: SASAAL
4
Haka Sulaim ya haƙura ya dawo Gida.
Bai haƙura ba, kullum ya na gama hidimar Mahaifinsa sai yaje gaban ma'aikar maƙeri Salman ya zauna.
Tun maƙeri Salman bai amince da Sulaim ba har ya haƙura ya bashi dama.
A ranar da Sulaim ya fara yi musu Tukwane Salman ruÉ—e ya yi yana tambayarsa daga ina yake, Sulaim bai iya surutu ba don haka amsoshinsa sam basu gamsar da Salman ba, wannan dalilin yasa yace yana son ganin Mahaifinsa da ya ce suna tare.
Sulaim bai musa ba, ya kaishi har Gidansu.
Cikin bayanin da Salman zai gamsu Abduh da damuwa da ciwo suka ramar da shi yake bashi labari. Sosai Salman ya tausayamusu ya kuma É—auki nauyin abincin cin su kullum, domin Abduh bai sanar da shi akwai tarin dukiya a tare da su ba.
A zaman wata ukun da Sulaim ya yi da Salman da ƴaƴansa Zubair da Uzair ya gane mutane ne masu amana da dattako, don haka Sulaim ya samu lokaci ya tattauna da Mahaifinsa Abduh kan jan Salman a jiki su ƙirƙiri Ma'aikata mai girma da dukiyarsu da ke ajjiye.
Kai kawai Abduh ya É—agawa Sulaim alamun ya amince, Sulaim yakai minti biyar yana kallon Mahaifinsa shima yana kallonshi, kowannen su yana kallon iri lalacewar da ÆŠan uwansa ya yi, ba su da kowa ba su da kwanciyar hankali, Harun da suka sani ya gujesu.
Kukan da ba kasafai Sulaim ya cika yi ba, ya saki yana rungume Mahaifinsa.
Shima Abduh kuka yake yi yana cewa ;
"Allah Ya zama gatanka Sulaim yasa maka albarka a duk abinda ka sawa hannu, duk tsananin karka manta da mutanen Yankina idan ka samu sukunin rayuwa ka naimi Kakarka da Mahaifiyarka ka faɗa musu irin ƙewarsun da na yi, idan Allah Ya ƙaddara haɗuwarku da Mairam ka roƙamin yafiyarta. Iyalan Mallam suma ka nemesu ka ji halin da suke ci. Gwargwadon samunka gwargwadon kyautarka Sulaim karka gajiya, Allah yana tare da Kai, ko bayan raina inaso ka kafa Dhahab ka raya mutanen Yankina a cikinta, kayi aure ka hayayyafa, sannan ka faɗa musu har bayan barowata Yankinmu ban daina son su da begen su ba, na roƙeƙa Sulaim, idan da hali ka tura Yankin Tudu wani ya koyamusu ƙera Tukwanen da zasu dogara da kansu kayimin alƙawari!" Sulaim wani irin juyi yayi da Kansa yana zaro Mahaifinsa daga jikinsa, laƙwas Abduh ya yi yana kallonsa da fararen idanuwansa da suka ƙara haske alamun alƙawarinsa ya ke jira.
Cikin kuka Sulaim ya ce; "na yi alƙawari amma dan Allah karka tafi ka barni Baaba ba Ni da kowa"
"Ka na da Allah Sulaim! Sannan ka tuna Naila? Æ´ar gidan Abokin Mahmoud?" gane wayo yake son yimai yasa ya girgiza kansa yana kamo hannunsa.
A wannan rana daƙyar Sulaim ya fita aiki.
Ko da ya je wajen aiki yakasa yin komai balle su tattauna da Salman kan zuba jarin da sukayi magana da Mahaifinsa. Yamma na yi ya taho gida bayan ya biya ya siyowa Babansa kayan marmari.
A kwance ya samesa kamar kullum, sai dai daya mirginasa ya gane dagaske wannan Baaban daya rainesa da izinin Allah ya wahala kan bauta da ƙera Tukwane don cigaban mutanen Yankinsa ya yi barcin da ba zai ƙara farkawa ba anan gidan duniya ba.
Hannunsa dayake wani irin rawa yasa ya kamo farar Fuskarsa Mahaifinsa daya koma ɗan siriri ya bushe. Rayuwarsu na Yankin Tudu ne yake dawomai da yadda Mahaifinsa yake bugun ƙarfe dare da rana, yau gashi ya mutu bai mori ko sisinsa ba, Sulaim hawayensa basu gusheba har sai suka jiƙa gaban rigarsa.
Bayan mintuna Sulaim ya saɓa Abduh da jikinsa ya saki gaba ɗaya, zuwa Asibiti ko zasu ce mai dogon suma ya yi.
Da gaske Abduh ya mutu ya bar Sulaim cikin maraici!
Sulaim ya yi kuka irin kuka da har duniya ta tashi bayajin zai ƙarayin irinshi. Da taimakon Salman da mutanen Ma'aikatarsa aka binne Abduh.
A tsakanin kwanakin da Sulaim ya rayu shi ɗaya ya fuskanci kuɗi suna gaba da komai a rayuwar wasu Mutanen, na wasu Mutanenma muninsa ya yi yawa. Kamar Salman tunda ya turo su Zubair sau ɗaya bai ƙara turosu ba balle ya zo da kansa acewarsa aiki ya yi musu yawa a Ma'aikata.
Idan har kuɗine sune gishinƙin da zai cika masa burikansa mai zai hana ya neme su?
Cikin tsanani da wahala Sulaim ya fara gwagwarmayar kafa kansa da zuciya da ƙwanjinsa bai bi takan komawa Makaranta ba tukunna har sai komai ya dai-daita.
Garin shiga can faɗa nan Sulaim ya samu mutumin da zai taimakamai ba tare da yaƙarabin takan Salman ba. Cikin ƙanƙani lokaci tunda da kuɗi masu yawa a ƙasa Sulaim ya fara kafa Ma'aikatar Sarrafa shinkafa.
A kwai mabaratan da suke yawan zuwa bakin ma'aikatar tun kafin gininsa ya yi nisa, wata rana Sulaim ya taho da Baturen da aka haÉ—ashi da shi zai taimakamai, ya gane ashe su Malik ne.
A yadda ya tsani duk wani jinin Yankin Tudu baiyi niyyar kulasu ba, sai dai tuna wasiyyar Mahaifinsa yasa ya isa garesu.
Da farko sun tsorota tare mamakin dama basu mutu ba suna raye?
Mahaifin Malik da suke Bara tare yayi kuka da yaji labarin mutuwar Abduh, shima Sulaim ya tausayamusu jin tsahon lokacin da suka É—auka a Birnin Abyad suna Bara tare da kwana dukkansu a É—aki É—aya. Daga wannan rana su Malik suka samu muhalli mai kyau.
Malik da Iyayensa sun san halin Sulaim tuntuni balle yanzu da yake jinsa shi kaɗai a duniyarsa, dalilin wannan yasa suka zaunar da jununsu suka yiwa kansu nasihar riƙon amana da riƙo da gaskiya komai ɗacinta.
Labarin kafuwar Ma'aikatar Sulaim ne yasa Salman naimansa da kansa, ya kuma baiwa Sulaim haƙuri. Sulaim bai manta halaccin Salman ba kuma ya yi masa uzuri tunda da ma'aikatar suke ci suke sha, sakaci dashi kan damuwarsa shi kaɗai zai iya rusa masu kasuwancinsu.
A cikin wannan tsukin Harun ya ƙara dawowa, daƙyar Sulaim ya sauraresa suka dai-daita shima da yaji mutuwar Abduh har da kwanciya a gadon Asibiti.
Har Yankin Tudu Sulaim ya tura Malik ya sirrince, ya kwaso rahoton halin da Yankin yake ciki. Malik ya dawowa da Sulaim mummunar labarin irin talaucin da mutanen Yankin suke ciki.
Kamar yadda Mahaifinsa ya roƙesa kafin ya bar duniya Sulaim ya samu Salman da batun tura wani Yankin Tudu ya koyawa Mutanen Yankin ƙera Tukwanen da zasu dogara da kansu.
Cikin kasada Salman ya amince Ɗansa Zubair ya je ya koyamusu ƙera Tukwanen da Abduh yake yi kamar yadda Sulaim ya koya musu tuntuni. Sai dai Uzair ne zai fara zuwa tunda yafi Zubair iya tsara kalami, idan yaso idan suka bashi masauƙi sai ya dawo Zubair ya zauna.
Zubair shine ya rayu a Yankin Tudu da sunan Mahaifinsa Salman, yawancin maganganun Abduh da yake yi Malik ne yake faɗamai ta ɓoyayyiyar wayar da ya tafi da ita.
Bashar da muƙarabansa har da Jalal su sukayi ta'asar kashe Zubair da Dattijo Junaid, wuƙa suka ɗan sokawa Ɗayyib gudun tonuwar asirinsu.
A daren da abun ya faru labari yajewa Malik ta hanyar waÉ—anda ya saka gadin lafiyar Zubair.
Dama kuma a daren suka iso iyakar Yankin domin tafiya da Zubair, kafin labari ya isa kunnen Sulaim da baya ƙasar Abyad Malik ya yanke nasa hukuncin akan Bashar .
Lokacin da gawar Zubair ya isa ga É—an uwansa Uzair da mahaifinsu Salman sunyi kuka, tare da tsanar Yankin Tudu da mutanen cikinta.
ÆŠAYYIB
Baƙin cikin bayyanar hannun Bashar a cikin kisansu Abduh maimakon ya nuna bai san wanda ya yanke masa harshe ba ne ya tunzura zuciyar Ɗayyib, har ya shaƙawa Bashar gubar daya tanada tuntuni a aljihunsa lokacin da suke yunƙurin kaishi Asibiti. Dama ya tana de shi ne idan har ya tabbata da gaske bayanin ɗaya daga cikin iyalin Abduh Bashar yake kwatantawa, Gara ya mutu daya tona musu asiri.
Mairam Matar Abduh Dhahab a ranar data fara magana ɗan leƙen asirinsu ya kai musu labari, a daren ranar ya tura ƴan daba su kashe Mariam, fitowar Mahaifiyar Naila kama ruwa ne yasa suka ɗauka Mairam ce, don haka suka farar sararta ta ko ina har sai da ya daina numfashi, Iyayen Mairam da sukayi laƙwas a ɗakunansu, ƴan daban suna tafiya suka fito suka tattara kayansu suka bar Yankin.
ÆŠayyib Babu irin bincike da naiman da baiyiwa Sarah Matar Mallam ba, amma babu wanda yasan duniyar da suke.
Menene burinsu ÆŠayyib? Su kashe sunan Dhahab su kuma samu É—aukaka da dukiya ko da jinin dukka mutanen Yankin zai salwanta, su dasa tsoro a ran Mutane yanda zasuci karansa babu babbaka ba tare da wani ya tanka musu ba.
SULAIM
Kisan Zubair yasa ya dakatar da Malik daga sanar da shi duk wani abu daya shafi Yankin Tudu da kowa na cikinta, duk wanda yaga ya cancanta ya taimakamai albarkacin Mahaifinsa ba sai ya sanar da shi. Wannan dalilin yasa Malik kasa taimakon Naila saboda yasan ita ba taimako take buƙata ba, burinta tasan Sulaim ya mutu ko yana raye.
Sulaim ya zama hamshaƙin Attajirin gaske a ƙasar Abyad da ya sakaye Sunansa da Muhammad Dhahab kowa da haka ya sansa,
ya kafa Unguwa guda da Rukunin Gidaje masu yawa mai suna Dhahab a Babban Birnin Abyad da kuÉ—i masu nauyi.
Malik da ahalinsa, Salman da Iyalinsa, sai su Kabeer, har da Mariam da Iyayenta da Malik ya binciko su ma suna aikatau a Birnin Abyad, sai wasu mutanen Yankin Tudu da cirani ya kawo kusa da Birnin Abyad sukayi katari da Malik. Su suka taru suka raya Dhahab suke rayuwa a ciki.
Matar Mallam babu inda Malik bai bincikaba amma ya kasa samunta.
Malik bai gajiya ba sai da ya binciko Mahaifiyar Sulaim da Kakarsa bayan ya kashe dukiya masu nauyi. Wannan ya ƙarawa Malik daraja a idon Sulaim.
Ranar da Malik ya kawo Aysha mahaifiyar Sulaim da Kakarsa Nanaah da kuma Farheen ƴar ƙanwar Aysha Dhahab Sulaim ya zo daga inda yake rayuwa domin ganinsu, wannan zuwa nasa sai yasa kishi ya lulluɓe zuciyar Mairam duk da Abduh baya raye, a ganinta kamata ya yi Sulaim yafi ƙaunarta akan Mahaifiyar data haifesa, tunda ta gudu ta barshi.
Da Sulaim ya tashi tafiya ƙasar da yake rayuwa da Kakarsa Naanah da yaji ya fi so a ransa ya tafi, saboda ciwon zuciya da take fama da shi, Mahaifiyarsa kuma aka ware mata Sashe na alfarma tayi rayuwa ita da ƴar ƙanwarta Farheen
A ina Sulaim yake rayuwa??
Kahala Birni mai daraja a Honolulun Hawaii, banbancin daÉ—in rayuwarsa da Babban Birnin Abyad, kamar babbancin Babban Birnin Abyad ne da Yankin Tudu.
Rashin son ya raɓi kowa yasa yaje can ya kafa Kasuwanci siyar da zinare da kayan sawa da kayan ƙyala-ƙyalai, cikin ikon Allah ya samu karɓuwar da ya ƙara mayar da shi Attajiri a can.
Duk wani hukunci da Malik ya yake yakewa, akanki kansa yake yi kamar yadda Sulaim ya sakarmai ragamar komai. Amma duk da haka rashin yarda da baiyi da kowa ba, yasa ya ajjiye Ma'aikata na musamman masu lura da motsin Malik a sirrince a harkokin da suka shafi Dhahab ba tare da shi kansa Malik É—in ya sani ba.
SULAIM
Ya manta da Naila da dukka wani abu daya shafeta a zahirinsa ya kuma toshe duk wata hanya da wani zai sakomai zancen aure.
Batun wanzuwar Sufyan a É—aya daga cikin ma'aikatansa da Kabeer, bai sani ba, shi ko Kabeer É—in da ya fi Sufyan matsayi bai san dashi ba, Uzair da Malik kawai ya sani.
A can Dhahab
Mutanen da suke rayuwa a cikinsa suna rayuwa a matsayin sun san Sulaim yana raye bawai don suna ganinsa da idanunsu ba ko mu'amalantarsa.
Tsantsenin Cikin Dhahab da kula da motsin komai duk Sulaim ne ya tsarashi Malik yake kula da komai da taimakon ragowar Ma'aikata, domin da mutum ya yi cin amana a Dhahab gara ya barta gaba É—aya.
Maiyasa Mairam bata taimaki Naila da kakarta ba duk da tasan inda samesu?
Kishi da burin son Sulaim ya dawo gareta yasa take ƙoƙarin duk ranar da Allah ya ƙaddara dawowar Dhahab tun bayan tafiyar da Kakarsa ta gabatar mishi da Barirah domin har biyayyar dole takeyiwa Aysha Mahaifiyar Sulaim, duk don su yi masa taron dangi ya auri Barirah. A ganinta idan Sulaim ya auri wata mantawa zaiyi da ita gaba ɗaya ƙarshe ta koma Yankinnsu da suka gudo, jawo Naila a jikinta gani takeyi shima matsalane kar Sulaim ya ganta ya tuna da shaƙuwa daya wanzu a tsakaninsu shekarun baya har ya nuna yana sonta, daganan ya aureta itama tasa ya koreta saboda kashe Mahaifiyarta da akayi ta dalilinta, gara Barirah da bawani sonta tasan zaiyi ba.
Wannan dalilin yasa Barirah take yiwa Ummi Mairam kamar yadda suke kiranta biyayya sama da Mahaifiyar Malik da yake ruƙonta.
Malik yasha jawa Baririh kunnen karta ɓata shekarunta wajen jira Mutumin da bai san da ita ba. Amma kallon mahassadi takemai.
..âœðŸ»
SASAAL
5
*Wani irin rayuwa Sulaim yake yi Kahala?*
Rayuwa sakewa da morewa arziƙinsa, kyansa da Mutanen Yankin Tudu suka kasa mantawa dashi yaƙara fitowa, ginannan jikinsa dake samun hutu, cima mai kyau, da motsa jikin da ya dace, yaƙara zama abin so ga duk wata Ƴa Mace musamman Mace mai son Naira da Namijin liƙawa a goshi. Rashin yawan son maganarsa bata sauya ba sai abinda ya yi gaba.
A cikin zuciyarsa kuwa babu ƙiyayya, babu ramuwa, sai dai ya goge kafanin Mutanen Yankin Tudu daga cikin rayuwarsa.
Babu yadda rayuwa Namiji kamar Sulaim zai gudana ace babu Mace a ciki, wannan daliline ya shigo da Noorhan ƴar asalin ƙasar Lebanon cikin rayuwarsa.
Noorhan;
Kyakkyawar gaske, ƴar Attajirai gaba da baya kuma ƴar gatar da ta yiwa addininta na Musulunci riƙon ganin dama, su ma Mazauna Kahala ne da Mahaifanta.
Bata da burin lallai SM Dhahab ya aureta kamar yadda take kiransa da wasu Abokanan Kasuwancinsa. Burinta soyayyarsu ta faɗaɗa ya wuce sumbata da sauransu, ya mayar da ita kamar Iyalinsa idan da hali harta haifa mai ƴaƴan da zai ƙulla alaƙa mai ƙarfin tsakaninsu har ya kaiga Aurenta ko baya so.
Kallonsa, salon tafiyarsa, iya riƙe matsayinsa da izzarsa, da rashin son hayaniyarsa wani irin birgeta suke yi, uwa uba Nairan daya tara babu magaji. Wasu lokutan tana kuka da magiyan ita ta sallama masa kanta amma sai ya yi biris da ita, idan ta matsa sai ya tuna mata abinda take so ya wuce ƙa'idarsa da ita.
Tasha sanya masa abu a lemo ya zubar, abinda bata sani ba, yarda da Mutum wani tsohon abune da Sulaim ya jima da daina yayinsa, idan har kaga ka cucesa akan kuɗi ko wani abun kasha to tabbas Allah ne ya ƙaddara hakan amma ba dai dabarar mutum ba. Da ya ga taƙi dainawa fuska da fuska ya gargaɗeta idan ta ƙara ba iya rabuwa da ita kaɗai zai yi ba har ƙararta zai kai.
Babu wanda ya yiwa Sulaim cushen Noorhan da kanshi ya ganta ya tura aka haÉ—asu, domin ragewa kansa kaÉ—aici.
Kakarsa Nanaah da ya É—auko rayuwarta kusan rabi a Asibiti yake gudana domin bini-bini jikinta ya tashi.
Malik ne kaɗai yake yawan kawo masa ziyara idan buƙatar aikinsa ya taso.
Tsakaninsa da Malik akwai girmamawa mai faɗin gaske, kasantuwarsa Ubangidan Malik kuma mai ɗauke kai da bashi damar yin duk abinda ya ga dama da dukiyarsa. A ɓagaren hira, hirar aiki ne kawai yake haɗa su banda na mutanen Yankin Tudu, kuma shima sunfi yi a rubuce saboda rubutu yafi yiwa Sulaim sauƙi akan doguwar magana, yakan jima ya na yin hira da Malik a rubuce amma idan da baki ne hirarsu taƙaitaccen ne.
Wannan shine Matashin da Malik ya je wajensa da abubuwan da suka faru tun shekaru baya a Yankin Tudu.
*DAWOWAR LABARI*
Murmushi Malik ya saki yana ƙara gyara zamansa don jiran abinda zai ƙara cewa.
"Na turo maka saƙo, idan aikin komai ya kammala sai ka wuce"
Sulaim ya faɗa yana ƙoƙarin miƙewa. Sai dai har ya miƙe ya fara yunƙurin tafiya Malik yana zaune bai motsa ba.
A wajensu dukka sabon abune rashin miƙewar Malik ɗin, don haka Sulaim ya fahimci Malik yana da saƙon dayake buƙatar attention ɗinsa.
Dawowa ya yi ya zauna idanunsa ƙyam a kan fuskar Malik dake sunkuye kafin ya ce "menene matsalan Malik?"
Sai da Malik ya saita kansa sannan ya ce
"ka gafarci furucina da kuma labarin da nake tafe da shi" kai Sulaim ya É—aga alamun ya basa dama.
A É—an rarrabe Malik cikin kame-kame tsoron abinda zai biyo baya ya ce;
"Nailar Yankin Tudu, Æ´ar Mahmoud maÉ—inki..."
Ido Sulaim ya lumshe har baya ganin fuskarka Malik dakyau, a hankali yayi baya ya jingina da Couch É—in dayake kai. Hakan da yayi ne ya bawa Malik damar cigaba da maganarsa
Kamar mai karanta labarai a gidan radiyo ko talabijin haka Malik yake koromai labarin komai dalla-dalla tunda ya basa dama, har zaman Sufyan da abinda ya aikatawa Naila da cin zalin da yayi mata, da ciwon da tayi kamar yadda ya kwantarwa da Bushra hankali ta bashi labarin komai ta waya kafin zuwansa Kahala, da zuwansu Babban Birnin Abyad a yanzu a matsayin makitsiya, kuma Mahaifiyarsa ta hanasa taimakonta saboda abinda Mairam ta tsiro da shi.
Malik bai rage komai ba, tunda ɗorewar zaman amanarsu shine rashin ɓoye-ɓoye. Domin ko Noorhan Malik ne kaɗai yasan da ita a matsayin Budurwar Sulaim shiyasa yake jawa Barirah kunne.
Idanuwansa da ya zuƙe ya ɗan buɗe kaɗan yana gyara zamansa, kamar daga sama Malik yaji sassanyar muryarsa;
"Inji Ni ka sanar da Naila da Kaka! A Sauya mata Jami'a a Babban Birnin Abyad,a basu mazauni na musamman a Dhahab ta kuma daina kitso har abada. shi kuma Sufyan ku barshi ya ci abinci shi da Iyayensa daga dukiyar da Allah Ya bamu."
ya na gama faɗa ya ɗan sosa ƙarshen dogon hancinsa yana miƙewa.
Har lokacin idanunsa da suke bayyana jin daÉ—insa ga abu ko akasinsa a lumshe suke ba a ganinsu da kyau, balle Malik ya tantace yadda ya É—auki zance.
"Ka sauka lafiya Malik ina gaida kowa" ya ƙara faɗa yana barin living room ɗin daya lashe manyan kuɗaɗe.
LV Maimi Mule ɗin daya haska kyakkyawar ƙafarsa Malik ya bi da kallo kafin shima ya miƙe a hanzarce yana ɓoye ainihin yanayin dayake ciki.
Malik ya na fitowa harabar Gidan ya samu waje ya zauna yasha murmushin da ya kasayi a ciki, yana godewa Allah domin matsalar Naila ce Matsala ta Farko tun bayan barowarsa Yankin Tudu da ƙiri-ƙiri yasan arziƙine maganinsa amma ya kasa maganceshi, saboda wanzuwar Naila a Dhahab kamar dawo da Tarihin Yanki Tudu ne a rayuwar Sulaim, shiyasa bai isa ya yisa kai tsaye ba shi kaɗai.
Yasan da wahala Namijin da ya taka Matsayin Sulaim ya so Mace irin Naila, da wannan saƙe-saƙen ya duba saƙon Sulaim kafin ya wuce addireshin wajen taron daya turamai.
Sai yamma liƙis su Malik suka gama taro ya nufi masauƙi, ko Rigarsa bai gama cirewa ba saƙo ya shigo ta E-mail ɗinsa. Bai kawo saƙo mai muhimmanci ba ne, don haka ya shiga wanka ya gabatar da Sallah.
Bayan ya ci abinci yakira Ummeensa yana bata labarin abinda ya faru, hamdala tayi kafin suyi sallama, Bushra ya yi niyyar kira amma yafasa ya janyo ɗaya wayarsa don turawa Sulaim saƙon yadda komai ya wakana ga mamakinsa ashe saƙon Sulaim ne ya shigomai tuntuni. Sunan Jami'a ya turomai da taswirar Dhahab sannan ya yi pointing ɗin wani guri, ko Malik bai tambaya ba yasan yana nufin anan yake so a ajiye su Naila, sai guntun rubutun nemarwa dukka ahalinta da suka nuna suna ra'ayin aiki a Dhahab, a bashi aiki da matsuguni na musamman a estate ɗin Companynsu( inda Sufyan yake).
Sai da Malik ya gama ƙyaƙyata dariyar muguntarsa daya haɗe da zallar nishaɗi sannan ya binciko sunan jami'ar da Sulaim ya turomai. Iya adadin kuɗin Makarantarne yasa Malik ƙara sakin dariya, kafin ya ƙara zuƙo Taswirar Dhahab daya turamai dakyau, inda Sulaim ya yi pointing gine ne dake tsakanin inda Mahaifiyarsa da Danginta da suka ƙara biyota daga baya suke rayuwa, ginin babu kowa a ciki domin an tanadeshi da can saboda Sulaim ɗin kansa amma ya nuna baya so, kuma ɓangaren shine ɓangare mafi samun tsaro dakyau a Dhahab. "kenan anan Naila da Kakarta zasu zauna?" Malik ya tambayi kansa wani dariya ya ƙara kwashewa da shi har da kwanciya.
Rasa wanda zai kira da yasan Naila suyi sharing É—in daÉ—in dayake ji yasa ya kira Bushra.
Bayan sun Gaisa ya gama bata labari ihun
Bushra ihu murna tasa tana tsalle tare da alƙawarin baro ƙasar da take domin taya Naila murna.
"amma kana ganin Mahaifiyarsa(Aysha) zata amince baza'a samu matsala da ita ba, tunda ba wai auren Nailan ya ce zai yi ba" Bushra ta faÉ—a murnarta na komawa ciki.
Dariya da kai tsaye za'a kirasa na isa Malik ya saki ya ce
"Bushra! baki ji na ce miki ya ce "Inji shi" ai ya gama magana kenan, Mahaifiyarsa Macece mai sanyi, kuma barinsa da tayi tsayin shekaru yasa take lallaɓashi babu shaƙuwa a tsakaninsu. Baya magana mutum ya sauyamai sai dai Allahn da Ya haliccesa! Don haka ina jiran zuwanki" Dariya Bushra ta saki tana jero Sulaim kiraraki, da shaƙiyancinsu suka ƙare wayar.
Ajiyar zuciya Malik ya sauke Noorhan da yake ganinta a matsayin katanga mai tsaho a tsakanin Sulaim da Naila na faÉ—omai domin bayasa Barirah a lissafinsa....
Washe gari da Asuba ya ɗauko hanyar Ƙasar Abyad, bayan ya ajjiyewa Sulaim saƙo don bai koma gidan ba...
[9/5, 8:36 PM] Maman Amatullahi: SASAAL
6
SUFYAN;
Bai yi nadamar furucinsa ga Sumaya ba, saboda yana ganin abinda ya dace da ita kenan, burinsa kawai ya gansa a Babban Birnin Abyad a ofishin aikinsa ba su sallamesa ba.
Masauƙin da suka sauka shida Sumaya ya je, ya kwashe kayan amfaninsa ya nufi Airport.
Gabansa ya na faÉ—uwa ya nufi estate É—in Companynsu.
Ajiyar zuciya ya sauke lokacin daya da zura ɗan mukullin ɓangarensa yaji ya buɗu.
A gaggawace ya shirya cikin baƙin kayan da suka yi mai kyau, sannan ya lalubo wayarsa hannunsa da zuciyarsa suna rawar amsar da Driver zai ba shi ya danna masa kira ya ce ya zo ya kaishi Office.
Da girmamawa ba tare da ɓata lokaci ba Driver ya ce gashinan zuwa.
Sufyan bai san sanda ya zamo ƙasa ya yiwa Allah sujjud ba, domin ya yi imanin a yanzu shine Kaɗai gatansa.
Babu abinda ya sauya a ofishinsa sai ƙamshi ma da yake yi a gyare tsaf. Rintse ido Sufyan yayi yana yiwa kansa alƙawarin riƙo da gaskiya tare da aiki da amana.
Bayan ya dawo gida
Da dare ya raba kasa barci ya yi ƙewar Naila da yadda yake bautar da ita ya juyata yadda yaga dama na addabar zuciyarsa, babu ƙewar Sumaya ko wani abu daya dangaceta a cikin ransa, saboda don ita da Mahaifinsa ya kashe wayarsa Karma su kira su samesa.
Sallar daren da Sufyan bai taɓayi ba a rayuwarsa ya ɗauko prayer mat bayan yayi alola ya tayar, zuciyarsa cike da yaƙinin samun mafita a wajen Ubangijinsa.
★washe gari da ya fita ofishi yaƙara ganin abubuwan da suka ƙara kwantar dashi, saboda zazzaɓi mai zafin da ya rufe sa. Ya ga Kabeer ido da ido a matsayin Uban gidansa, sannan ya ga Dr. Abdallah da ya taɓa zuwa Yankin Tudu shekarun baya.
Menene yake faruwa? Daga ina suke ɓullowa, ko dai kasheshi suke son yi? Tambayoyin da yake ta yiwa kansa kenan
Har gari yayi haske Sufyan bai runtsa ba. A daddafe ya nufi office kansa kamar zai faɗo, Misalin ƙarfe tara na safiya ya shiga ɗakin taron da zasuyi, fuskokin wasu daga cikin mutanen Yankin Tudu ya fara gani ciki har da Sartaj da'aka nema aka rasa. Bibbiyu ya fara gani kafin ya ƙwala ƙarar da ya janyo hankalin mutane kansa.
Rai a hannun Allah aka wuce da shi Asibiti a karo na uku.
NAILA;
Ita da Kaka kwanan fargaba sukayi, har ɗaki Ameera ta biyo Naila tana bata haƙurin irin tambayoyin da Barirah ta titsiyemsu da shi.
Æarawon barci ne yayi nasarar É—aukesu bayan sallar Asubahi.
Da gari ya yi haske bayan sun karya Ameera aka turo ta kirasu, wai Barirah tace su taho har da Kaka, É—an yamutsa fuska Naila ta yi ta ce;
"ba ta da hurumin da zata ce don zan yimata kitso sai na tafi da Kakata, idan bata son zuwana ni kaɗai ku biyani haƙƙina mu koma inda muka fito"
Dan jim Ameera tayi kafin ta ce;
"okay ba damuwa muje"
Naila ta na kallon Kaka ta na yunƙurin kamo hannunta tayi kamar banganta ba, ta bi bayan Ameera.
Da suka fito Parlon
Mama Yayar Mahaifin Ameera da zata raka Naila da mamaki take tambayar ya ya basu fito tare da Kaka ba? Abinda Naila ta gayawa Ameera na maimaita mata.
Itama É—an jim tayi kafin tayi gaba Naila binta a baya.
Æangaren Mahaifan Malik suka fara zuwa jami'an wajen suka sanar da su saÆ™on Barirah, wai ta ce su biyota É“angaren Ummi Mairam.
Cikin biyayya Maman da ta raka Naila ta sunkuyar da kanta haɗe da ƙarayin gaba.
Zuciyar Naila kamar ana hura wuta saboda takaici.
Babu hassada living room ɗin su Ummi Mairam abin a yabane ta kuma jinjinawa ƙwararren da ya tsarashi.
Mairam Matar da Mahaifiyar Naila ta fuskanci mutuwar azaba ta sanadin kula da ita, idanuwan Naila suka ganemata, Tayi kyau irin kyan dake bayyana hutu da sukunin rayuwar da take ciki.
Kamar bata taɓa ganin Naila ba haka ta ɗauke kai tana shan ruwan tataccen kayan marmarin da yake hannunta. Barirah tana zaune a gefenta tana latsa waya.
Naila tsayawa a matsayinta abune da ta jima da sanyawa zuciyarta shi, don haka ta naimi ƙasa na zauna, kamar bata sansu ba dukkan su.
"Ina Kakarki, maiyasa baku zo tare ba?" Barirah ta tambaya cikin isa.
A take Naila ta bata amsa!
"Banzo da ita ba, saboda ba ta iya tafiya mai nisa, kuma ai bata iya kitso ba, Ni kaÉ—aice na iya."
wayar hannunta Barirah ta ajiye a gefe tana ƙanƙace idanunta, sannan ta ƙara cewa;
"Ke har kina da Audacityn bani irin wannan amsar, lafiyar ƙwaƙwarki kuwa?"
Cikin kameme Mama tace;
"Ayi haƙuri kinsan halin Yara, Kakarta ta ce batajin daɗi"
"Ko bata jin daÉ—i a É—aukominta ita haka, tambaya nakeson zanyi musu tare"
Barirah ta ƙara faɗa a gadarance tana juya wayar hannunta.
Zuciyar kamar ana hura wuta a maƙera, baƙin ciki tuni ya lulluɓe ganinta, kamar zata amayar da wuta ta ce;
"Ƙarya kike Barirah! Bakiyi wannan arziƙin ba, wacece ke? Ko da bansan ƙaddarar arziƙi ba babu yadda za'ayi mai sana'ar maganin gargajiya ya mallaki Dhahab, dole arziƙin wani kuke ci." Naila tƙarasa faɗa tana huci.
Mari Barirah ta taso zata tsinkawa Naila.
Naila ta kama hannunta na gantsara mata cizon da iya kaifin haƙwarana daya da Barirah kwarara ihu.
Cikin zare ido Mairam ta saki kofin hannunta ta ce;
"Ke fita ki kiramin Securities su fitarmin da wannan abun" Mairam ta ƙarasa faɗa tana pointing Naila.
Ƙasa Mama ta durƙushe tana bata haƙuri
Cikin zafin murya da zafafan kalaman da suke fitowa tun daga ƙasar zuciyar ta ce;
"Ba iya kamani zakisa ayi ba kisa akasheni kamar yadda kikayi sanadiyar mutuwar Ummeena kika gudu kika samu daula kika manta dani, idan kuwa baki yi haka ba to tabbas! baki cika butulu ba Mairam dake da ahalinki! Wallahi da na cigaba da ganin fuskarki Gara kisa ayimin kisa mafi ƙanƙanci akan na Mahaifiyata," Naila ta ƙarasa faɗa kamar zata daketa.
Mairam batayi gigin kawo farin sol É—in hannunta ba gudun abinda Nailar tayiwa Barirah.
Sak Mairam tayi tana kallon Naila, kafin rufuwar Seconni saiga Mahaifanta da kuɗi yaƙara gyarasu sun bayyana.
Kamannin Mahaifiyar Naila a bayyane yake akan fuskarta da gangar jikinta don kallo É—aya sukayimat suka shaida ta amma saboda su tabbatar sai Mahaifinta ya ce;
"yarinya daga ina kike?"
Babu shakka balle kwana-kwana Naila tace ;
"Yankin Tudu Daular Sarki Hammam, Naila Æ´ar gidan Mahmoud MaÉ—inki wacce ta rasa Mahaifiyarta dalilin baiwa Mairam Matar Abduh Dhahab kariya."
Ido Mahaifin Mairam ya rutse son zuciya na bijiromasa da kuma burin da suka san ya jima a zuciyar Æ´arsu ya ce;
"Yarinya bamu sanki ba, Barirah maza kira jami'ai"
Kallon tsohon Naila takeyi bata ce komai ba.
Mahaifiyar Mairam ba tayi magana ba, sai kuka da takeyi alamun lamarin baiyi mata daÉ—i ba.
Za'a iya kiran musayar yawunsu da Naila na farko daya taɓa faruwa tsakaninsu da masu yi musu Hidima tun bayan kafuwar Dhahab. Don haka kafin kace kwabo ƙofar sashen su Ummi Mairam ya cika da asalin mutanen Dhahab.
Ita dai Mama da ta rako Naila kuka takeyi tana magiyar suyi haƙuri.
Mahaifiyar Sulaim ce ta fito cikin shigar dake nuna matsayinta, kafin a tafi Naila kamar yadda Barirah ta basu umarni ta buƙaci jin abinda ya faru ta bakin Mama dake kuka a durƙushe tana magiya.
"Daga ina yarinyar take" Ummi Aysha ta tambayi Mama.
Da rawar murya Mama ta ce;
"Allah Ya taimake ki daga Birnin Abyad take ƴar ƙanina ce ta gayyatota kitso kuma da izinin Sir Malik, amma yanzu naji tana cewa daga Yankin Tudu take" Mama ta ƙarasa faɗa cikin kuka.
Ummi Aysha idanuwata da suke iri É—aya da na É—anta Sulaim ta lumshe soyayyar Abduh Dhahab daya kasa barin ranta na bijiromata.
Kai tsaye ta ce akiramata Malik kafin a tafi da Naila domin bata yarda da garaje ba a rayuwarta, domin garaje ne yasa ta tafi tabar Abduh a ranar da nasararsu ta tabbata.
Kafin su samu layin Malik, Armored Toyota LC300 BaÆ™i mai shaiÆ™i ya karyo kwanar Æangaren.
Basa dariya sai sunga mugunta wannan inkiyar Malik ne da Ubangidansa.
Don haka fuskarsa da babu fara'a sam yake É—aure tsam kamar ya É—auresa da igiya.
Baya yiwa kowa a cikin su aiki balle yayi musu biyayya don haka kowa ya kame kansa, Barirah kamar ta fashe don takaici.
Mahaifin Mairam daya biyewa farin cikin ƴarsa, gumin daya tsatsafomasa ya sharce. Ita dama Mahaifiyarta tana ciki ko leƙowa batayi ba.
Bayan ya zuro da gangar jikinsa waje, ɓakin tabaran fuskarsa ya zame. Malik yana da salon tsayuwar da yakeyi wanda dole kowa ya shiga taitayinsa.
"Menene yake faruwa" Malik ya tambaya da nannauyar muryarsa. Da harshen nasara shugaban Securities daya zo wajen dai-dai zuwan Malik yake tambayar kowa na wajen da karfi.
Dukkansu Barirah data kirasu suke kallo, domin babu bayanin komai tace su zo su tafi da Naila.
Haɓarsa Malik ya ɗan shafa yana matsowa wajen da kyau, sai a lokacin yaga Naila dake tsugunne taci kuka jijiyoyin goshinta sun fito sunyi ruɗu-ruɗu.
"Kowa ya koma bakin aikinsa" Malik ya faɗa idanuwansa akan Barirah data yi ƙasa da Kanta.
A zafafe Ummi Mairam ta ce;
"Babu inda zasu je, domin nice Uwar data raini wanda suke yiwa aiki don haka dole su tafi da ita, su hukuntata sannan su mayar da ita asalin Yankinta"
Baki Malik ya taɓe yana yiwa Mairam kallon da bai taɓa yimata ba ya ce;
"Ya ce in ji shi! ta rayu a Dhahab ita da ahalinta da duk wanda taga dama, bazaki sauyamin aiki ba, amma yanzu ki kirashi tunda ke Uwa ce idan ya canza magana sai muma canza"
Hannu na rawa Mairam data kwashe imaninta ta siyarwa ShaiÉ—an ta dannawa layin Sulaim na musamman kira"
Abune mai wahala ka kirasa ya É—auka nan take amma tana kira ya É—aga, cikin kukan take koramai jawabin ga wata tazo tanayimata rashin kunya ta ce akamata Malik ya ce bata isa ba.
Mahaifiyar Sulaim Ummi Aysha ƙwallane ya cika idanuwanta saboda yadda Mairam take yaƙin lallai sai ta rabata da ɗan da batasha wahalar haifarsa ba, bata wankemai bayan gida ba, bata wankemai fitsari ba, kawai abincin da Mahaifinsa yake siyowa take dafawa su ci, amma dai-dai da tarbiyya Sulaim Abduh ne yayi masa da Kansa domin barcine kawai yake rabasu.
Sulaim
Cikin taushin murya dake bayyana izzarsa ya ce;
"wacece ita? Maiyasa zatayi miki rashin É—a'a? Kunsan juna ne?"
Shiru Ummu Mairam tayi, ta kai daƙiƙu biyu kafin ta fara lalubo abin faɗa sai da ta gama kame-kamenta ta gane ya jima da katse wayar tun bayan tambayar da ya yi mata, tayi shiru.
Saƙon Sulaim ne ya shigowa Chief securityn Dhahab.
Umarnin kora ya rubuto ga Securities ɗin da suka amsa umarnin Barirah saboda bai san kallon wani iri matsayi sukeyi mata ba, da har zata bayarda umarni subi batare zurfafa bincike ba. Sannan kowa yabi umarnin Malik a cikin daƙiƙu, wanda yaƙi a gaggauta fitar dashi daga Dhahab gaba ɗaya kuma babu dawowa.
Chief security na gama sanar da saƙon Sulaim a sarari, Malik ya goge gilashinsa da salo ya mannawa idanuwansa haɗe da bawa Securities mata Umarnin su taimakawa Naila ta miƙe.
Har Malik ya juya Ummi Aysha da ta kasa jurewa tace;
"Ka roƙamin alfarmarsa ya bar securityn da aikinsu" ta faɗa da tausayi a muryarta.
Malik bai jirkintawa maganar Ummi Aysha ba ya turamai saƙo.
Rashin bayar da amsarsa na nufin amincewarsa don haka Malik ya ce abar Securities da aikinsu, amma ayi suspending É—insu na watannin da suka dace domin kiyaye gaba.
Babu halin musayar yawu da hukuncin Sulaim, don haka Ummi Mairam da Barirah harma da Mahaifin Mairam da kunyar Malik ya hanasa sukuni suka shige ɓangarensu.
Itama Ummi Aysha ɓangarenta ta nufa fuskarta ɗauke da murmushin alfarmar da Sulaim yayimata a matsayin biyayya akaron farko.
UMMI AYSHA
tambayar da take yiwa kanta shine; "Wacece Naila, menene matsayinta a wajen Sulaim har da zai shiga lamarin Dhahab akanta" tattaunawar da suka wuni sunayi kenan ita da Æ´an uwanta.
A ɓangaren Barirah da dare ya yi tazo kwanciya maganganun Naila ta tuna;
"Ƙarya kike Barirah! Bakiyi wannan arziƙin ba, wacece ke? Ko da bansan ƙaddarar arziƙi ba babu yadda za'ayi mai sana'ar maganin gargajiya ya mallaki Dhahab, dole arziƙin wani kuke ci"
WaÉ—annan Kalamai su suka addabi zuciyar Barirah, a wannan dare bata runtsa kuka kuwa tayisa kamar zata makantar da idanuwanta.
Wanda yaji daɗin cizon da aka yiwa Barirah ya dannamin like😂
In Shaa Allah gobe zai zama ranar hutu. Na gode
[9/5, 8:36 PM] Maman Amatullahi: SASAAL
7
SULAIM
Bayan ya gama waya da Ummi Mariam mamaki ne ya kamasa.
A kaf zamansa da ita bai san wani hali taƙamaimai na ta da zai kwatanta ta da shi ba, domin rayuwarsa a gidansu na Yankin Tudu daban yake da na ta, a wasu lokutan ma sai dare suke haɗuwa ko Safiya idan zai je Makaranta, kawai dai abinda ya sani suna kwana a gida ɗaya.
Abu É—aya zai iya faÉ—a akanta shine tayi wahalar kai shi Asibitoci domin yayi walwala ya dawo kamar kowani Yaro, kenan banda wannan halin kirkin nata, tana da wani hali daban da bai sani ba?
Kulle idanuwansa ya yi saboda jin alamun shigowar mutum, yasan ba zai wuce Noorhan ba, domin ita kaÉ—ai ce take da wannan alfarmar.
Babu alamar tana da haɗi da musulunci a yanayin shigarta, kyakkyawar fuskarta a ɗaure ta ƙaraso inda yake bakinta ɗauke da sallamar daya kafamata sharaɗinsa.
Ɗan ɓata fuska taƙarayi tana gaishe shi, kafin ta ajjiye siririn dogon farin takardar dake ɗauke da sunayen abubuwan buƙatarta.
Lumsassun idanuwansa da suka ɗan sauya kala ya ɓude akan takardar. Card ɗin daya tanada don zuba kuɗin buƙatar Noorhan ɗin ya miƙa dogon hannunsa ya ɗauko ya miƙa mata.
Tuni fuskarta ya washe tunda dama ta ɗauresa ne saboda tasan tambayar kuɗinta ga Sulaim ya zarce ƙa'ida ko Iyayen da suka haifeta, bata isa su kashe mata kuɗin da take chajar Sulaim ba.
Murmushi tayi tana juya idanuwanta ta ce;
"Inajin daÉ—in yadda kake kashemin kuÉ—i Habibi, na gode"
Kai Sulaim ya jinjina mata, tana yunƙurin sako hirar data saba yimai taga ya miƙe, kafin ta yi ƙorafi ya dakatar da ita ta hanyar sumbatar saman goshinta ya bar wajen.
Baki ta saki tana bin bayansa da kallo. Card ɗin hannunta ta zauna jujuyawa, tunanin abin yake neman sauya mata shi lokaci ɗaya takeyi mata. Ta ɗan jima kafin ta miƙe tabar Gidan.
★washe gari da yammaci da sabon kwalliyarta Noorhan ta kawowa Sulaim ziyara.
Maimakon samunsa a zaune a irin wannan lokacin yana aiki, sai ta samesa a kishingiÉ—e da System a gefensa idanuwansa a kulle kamar dai yadda ta samesa jiya.
Cikin ɗan takaicin abin yake shirin taɓamata shi ta ce;
"Tun zuwan Malik kwana biyu da suka wuce ka sauyamin why the Sudden change?"
Idanuwansa da suka tara ruwa aƙasa ya buɗe amma ba dukka ba, yanayin lumshewarsu kamar wanda yake fama da zazzaɓi mai zafi, cikin taushin muryar dake ƙara matar da zuciyar Noorhan akansa ya ce;
"Beg your pardon?"
Gashin kanta ta É—an hargitsa tana matsowa kusa da shi da kyau, sai dai takasa kallon cikin idanuwansa da har lokacin suke a kan fuskarta, domin wasu lokutan idanuwansa tsoro suke bata.
Kuka ne ya fara zuwarmata kafin ta fara koro bayanin ya sauya tun zuwan Malik kuma shima yasan haka dan Allah karya bari a rabasu, ta roƙesa. Ita bazata takuramai ba duk lokacin daya shirya aurenta zata jirashi.
Har ta gama magana Sulaim bai motsa ba bai kuma daina kallonta ba, wannan dalilin yasa takai hannunta gefen wuyarsa. Zafin jikinsa yasa tayi ƙasa da Kanta, sai a lokacin ta raina wayonta da kuma dasa Ayar tambaya wa soyayyar da take yi mai anya ba na kyansa da kuɗinsa ba ne? Idan da gaske tana sonsa yakamata ta fahimci bashi da lafiya tun daga sauyin idanuwansa da zaman da yayi yakasa aiki, domin Sulaim baya wasa da naiman kuɗi.
Kanta ta juyar gefe kunyar kanta na mamayeta, cikin ƙarfin hali ta ce; "I'm sorry"
Idanuwansa ya ɗan lumshe alamun ya karɓa kafin ya ɗauki wayarsa ya tura mata saƙo. Yana tura mata ya miƙe, kunyar bin bayansa yasa tabi shi da kallo.
Tasani Allah ne yake sonta ya turomata Sulaim cikin rayuwarta amma ta lura ba lallai ya zama mallakinta ba saboda sam yanayin halayyarsu ba ɗaya bane, tsabar son da takeyimai gaba ɗaya sai ya zamana kamar tana shiga haƙƙinsa ta hanyar takuramai, gani take yi dole fa sai ta zaƙe kar a ƙwace mata shi.
Sulaim bayan ya shiga É—aki kwanciya ya yi.
Ya kai wasu daƙiƙu a kwance kafin ya lalubo wayarsa ya danna Kiran layin Malik.
Bayan Malik ya amsa sallamarsa, da muryasa da ta yi sanyi, irin sanyi da Malik bai taɓa ji ba ya ce;
"Yaya Naila ta daina kuka? Kana ganin zamanta a Dhahab kaÉ—ai zai sata farin ciki ko nazo ta ganni? ko kar nazo saboda kar ta ji tsoro?"
A ɓangaren Malik katse kiran ya yi, domin bai yarda Sulaim bane, ko da ya duba ya tabbatar layin Sulaim ne, kai tsaye masu kula da lafiyarsa ya kira, su shiga Gidan su bincika wani ya shiga har ya samu nasarar ɗauke wayar Sulaim.
Sulaim dake kwance da Noorhan dake zaune har lokacin a living room mamakin ƙarar da suka ji na alamun akwai matsala ne ya tashi kowannensu tsaye.
A ɓangaren Sulaim kansa ya dafe yana jinjina Soyayyar Malik garesa don ko shakka bayayi aikin Malik ne. Tunanin zasu iya riƙe Noorhan da tuhumarta a matsayin mai laifi yasa ya fito daga ɗaki.
Ya kuwa samu sun zagayeta wasu na ƙoƙarin bincika Bedrooms ɗin da suke cikin Sashen.
Fitowarsa yasa sukayi ƙasa da Kansu tare da shaidamai Umarnin Sir Malik ne, bayan tabbatar da lafiyarsa suka bar Noorhan da sakakken baki.
Suna fita kiran Malik ya shigomai bai ɗaga ba ya katse kiran nauyin kalaman da ya furta har yasa Malik yake tunanin ba shi bane ya sashi sakin ƙaramin murmushi.
Malik Noorhan ya kira, jiki na rawa ta ɗaga, kai tsaye tun kafin Malik ya tambayeta ta fara zubomai labarin sauyin Sulaim da zazzaɓin da ta samesa da shi. Dan Allah ya sanar da ita menene matsalar?
Kwantar mata da hankali Malik ya yi tare da bata shawarar ta koma Gida ciwone kawai ya sauyasa amma babu matsalar komai.
MALIK;
Ajiyar zuciya ya sauke bayan gama waya da Noorhan, ya É—auka wanda ya san da zaman Naila ne ya tafi har can Kahala yake kiransa ta wayar Sulaim,
"to amma ta yaya hakan zai faru?" Ya tambayi kansa. murmushi ya saki ya É—an marin fuskarsa.
Anya hasashensa bazai zama gaskiya ba kuwa? Na Sulaim zai dawo da soyayyarsu da Naila.
Wajensu Naila da yayi niyyar zuwa ya nufa.
NAILA;
Har aka kaita bakin Sashen su Mama a motar Malik bata daina Kuka ba, fuskar Mariam da ta wulaƙantata na sukar zuciyarta. Ta yi tunanin da ta ganta zataci albarkacin Mahaifiyarta a wajenta ko da bazata nuna ta santa ba, ta hana Barirah wulaƙantata, ashe ita zata bawa Barirah lasisin mayar da ita abar kwatance.
Kaka hankalinta a tashe ta tarbi Naila domin tun tafiyarta ta kasa zaune ta kasa tsaye, saboda tsoron tozarcin da Barirah za iya yimata.
Ko ɗakin da suke daa ba'a barsu sun koma ba Malik ya cewa Mama ta canza masu ɗaki. Ɗakinta dayasha ƙawa ta kai su jikinta yana rawa. Tashin hankali bai sa Kaka ta gane Malik ba.
Da Naila ta zo bawa Kaka labari kasawa ntayi saboda kukan dake sarƙemata murya. Rungumeta Kaka tayi tana bubbuga bayanta.
Kafin Sallar magrib zazzaɓi mai zafi ya rufeta.
Malik daya bada umarnin gyara sashen da zamu koma Mama ta kira. Gudun matsala Malik ya turawa Ubangidansa saƙo.
Umarnin akaita tsadadden Asibiti Sulaim ya bayar.
Sai bayan sun kai Asibiti anbawa Naila gado Kaka ta gane Malik.
ÆŠimuwarta da Kaka ta shiga ne yasa Malik kiranta guri na musamman a cikin Asibitin.
Sai da Kaka ta tofe Naila dake barci da ƙarin ruwa a hannu da addu'o'i sannan tabi bayan Malik, zuciyarta cike taf da tsoro.
Bayanin komai da wanzuwar Sulaim a doron ƙasa yayimata, tare da shaidamata mutuwar Abduh bayan barinsa Yankin Tudu.
Kaka tayi sabon kukan mutuwar Abduh Dhahab, ta kuma yi farin cikin Sulaim dayake raye da zaman da zasuyi a Dhahab.
Sai dai a take Shaiɗan ya fara bijiromata da maganar Sarkin Tsafin Yankin Tudu dayaƙi barin zuciyarta ta huta, nan take jikinta ya yi taji murnarta na komawa ciki.
Duk da wannan Kaka bata musawa Malik zamansu a Dhahab ba, sai dai tace bazata iya shaidawa Naila Sulaim yana raye ba, duk ranar da Allah ya ƙaddara haɗuwarsu zata gani da idonta. A kan haka sukayi sallama da Malik ya wuce Gida.
Sai tsakiyar dare Naila ta farka, itama Kaka da idarwarta daga Sallar nafila kenan miƙewa tayi ta zauna a gefenta.
"Sannu" take ta maimaitawa Naila.
Sai da Naila ta É—an huta Kaka ta haÉ—a mata Shayi tasha sannan ta fara bata labari abinda ya faru, sai bayan ta gama Kaka ta sakomata hirar zamanmu a Dhahab. ÆŠan jim Naila tayi itama maganganun Sarkin tsafin Yankin Tudu da Kaka ta sanar da ita na neman yiwa nutsuwata Illa, ambaton Allah tafarayi a cikin zuciyarta tana neman tsari daga sharrin shaiÉ—an.
Haka suka ƙare wannan a kan tattaunawar zamansu a Dhahab.
★washe gari maimakon a sallami Naila sai akace saita ƙara hutawa.
A yammacin rana Malik ya zo duba su, da zai tafi ya buƙaci mukullin sashensu na Birnin Abyad domin kwaso takardun Makarantar Naila da kuma bawa masu gida mukullinsu. Jakar da ke tare da Kaka ta duba ta ɗauko mukullin ta basa..
Bai jima ba ya bar Asibitin.
Washe gari sai ga Bushra ta kawo musu ziyara.
Naila tayi farin cikin ganin Bushra bayan tsahon lokacin da suka kwashe Basu ga juna ba. Ta wayarta suka gaisa da Yasar, ya tayamu murnar zaman da zasuyi a Dhahab da kuma nasihar Naila ta mayar da hankali kan karatuntaa daga haka suka yi sallama, duk da akwai abubuwan dayawa da Naila take so su tattauna.
Da aka sallami su Naila washe gari Bushra da Driver ne suka zo É—aukarsu, maimakon su nufi Gida wajen siyayyar kayan sawa suka wuce.
Ba su yi mamakin irin siyayyar da Malik ya bawa kuɗi Bushra tayi mu su ba kamar yadda ta faɗa, sun jima Bushra tana kwasar suturar sawa da duk wani kayan buƙatarsu sannan su ka nufo gida.
Kyan Muhallin da aka basu a Dhahab ba ƙaramin birgesu ya yi ba, saboda ba su san ma yadda zasu kwatanta kyan matsugunin na su ba, a taƙaice dai zasu iya kiransa da aljannar duniya.
Kaka manta ƙalubalen dake gabansu ta fara takawa bayan tayi sujudar godiya ga Ubangiji.
Bayan sun gama murna sun huta, Naila ta kalli kan Bushra dake tsafe tace ta taho tayi mata kitso.
Kai Bushra ta girgiza ta ce;
"mai Dhahab ya ce babu ke babu kitso har abada, ko kina so afara hukuncin ta kaina ne? ke da ma baki da lafiya"
Ƙyam Naila tayi da idona akan fuska Bushra ta ce.
"wanene mai Dhahab? Shin shi zai dinga biyana kuɗin da zan kai cigaba Yankina ne da har zai hanani yin sana'ar kitso?" Naila ta ƙarasa faɗa tana haɗe fuskarta
Da mamaki Bushra ta amsamata daa;
"Malik bai faÉ—amiki wanene shi ba, sannan ai yace ku faÉ—i duk wanda kuke so a É—auka aiki a danginku"
Naila ko a jikinta ta ce;
"Ban san shi ba, kuma bashi da hurumin dakatar dani, idan ya ɗauki Matasa masu ƙarfin a jiki aiki, waɗanda suka tsufa fa kuma ba su da ƴaƴa ko Mijin da zasu turo ya ya zasuyi?"
Dariya Bushra ta saki haÉ—e da kama bakinta mamakin irin son da Naila take yiwa Mutanen Yankinta na kamata.
Bushra zata ƙara magana Kaka ta katseta da ce wa;
"Bushra É—an zo mana kinji"
Ba musu Bushra ta miƙe tabi bayan Kaka.
Jan kunnen Bushra Kaka tayi, kar ta sanar da Naila komai ta yi shiru har sai ranar da idonta ya gane mata.
Duk nacin da Naila tayi Bushra bata bari n
tayi mata kitso ba har ta bar Dhahab.
Bayan tafiyar Bushra
Da lallashi da ban baki Kaka ta taushi Naila ta haƙura da zancen kitso, amma duk da haka da Malik ya dawo sai da Naila ta ƙara tuntuɓarsa.
Malik murmushi ya ɗanyi yana waskewa daga tambayar data yi mai na wanene Mai Dhahab, sai amsar biyanta albashi duk wata da ya yi. Tare da alƙawarin ɗaukar duk wani ɗan Yankin Tudu aiki matsawar zai dinga tura kuɗi gida.
Babu wanda ya leƙo su Naila har suka yi kwana biyu.
A kwana na ukun su a Dhahab Mota da Drivern daya sa Naima jinta wata ta musamman ya zo É—aukarta wai Inji Sir domin kaita Makarantar da batasan yaya yake ba Malik dai ya turo mata Numbern wanda zata kira.
Shigar Naila Jami'a mafi tsada a Babban Birnin Abyad kamar yadda ta duba sunan Makarantar a wayar hannunta yasa ta ƙara tambayar kanta.
"Wanene mai Dhahab? Wani irin zuciyar taimako ne da shi?"
UMMI AYSHA
Da yammaci ta naimi Malik a waya saboda tambayoyin daya hanata ita da Æ´an uwanta sukuni.
Bayan Malik ya isa Sashenta sun gaisa, ya É—an motsa bakinsa da kayan da suka jeramai Ummi Aysha ta kallase da kyau ta ce;
"Wacece Yarinya da Sulaim ya zaÉ“i ajjiyewa a kusa dani? daga ina take? Menene alaÆ™arsu?....âœðŸ»
[9/5, 8:36 PM] Maman Amatullahi: SASAAL
8
SUFYAN;
A wannan karon shi kaÉ—ai ya yi jinyarsa da nurses da suke kula da motsinsa, sai kuma coworkers da suke shigowa dubasa.
Ya yi zuru-zuru kamar ba Sufyan ba. Tun kafin a sallamesa ya yanke shawarar zuwa Yankin Tudu ya ga halin da Mahaifiyarsa take ciki, domin ya kira wayarta sau babu adadi baya samu. Jikinsa ba ƙarfi ya kunna wayarsa.
Ko minti biyu baiyi da kunna wayar ba kiran ÆŠayyib ya shigomai.
Jiki a sanyaye ya É—aga da Sallama.
Cikin alhini kamar gaske ÆŠayyib ya ce;
"Ɗa na Sufyan mai kake gudu daga gareni ka ƙauracewa waya da ni?"
Kai Sufyan ya É—an girgiza kamar ÆŠayyib yana ganinsa ya ce;
"Baaba ba ni da lafiya, amma cikin satinnan ina nan zuwa duba lafiyar ku"
Duk nacin da Ɗayyib yayi wajen sanin taƙamaimai abinda yake damunsa, Sufyan bai faɗa ba, daga ƙarshe haka sukayi sallama ran kowannen su cike da zullumi.
Kwana biyu bayannan aka sallamo Sufyan ya naimi alfarmar zuwa dubo Mahaifiyarsa.
A ranar ya kimtsa kayansa ya nufi Yankin Tudu.
Lokacin da ya isa iyakar Yankin Tudu, wani Matashin da bai taɓa ganinsa ba, ya miƙomai farar Takarda a nannaɗe wai inji Sir Malik.
Tuni gumi ya fara tsatsafowa sassan jikinsa, hannunsa yana rawa ya warware takardar don ganin maiya ƙunsa....
BARIRAH;
A ɓangaren Barirah kullum fuskar a kumbure kamar an kwaɓa fanke ya tashi. Breakfast ma bata sonyi. Dama ba wani ɗasawa sukeyi da Simbi ba a wasu lokutan, don haka Simbi da take jin haushin abinda Barirah ta aikata duk da sunan son abinda yafi ƙarfinta tattarata tayi ta watsar kamar batasan abinda ya faru ba.
Ummu Malik data kasa jurewa yanayin Barirah janyota a jiki tayi saboda Mahaifinsu bayanan.
Da taushin murya ta fara yi mata nasiha;
" Ba ina yimiki iyaka da Mairam ba ne, amma ina yi miki gargaɗi akan abinda take ƙoƙarin ɗoraki akai, daga mu har ita babu mai gadon Dhahab a cikinmu, domin tuni Sulaim ya fitar mata da haƙƙinta. Ba ita ba ko Aysha da ta haifesa rayuwa suke yi a mabanbanta duniya, sannan ke saboda sokuwa ce sai ta ƙara ɗoraki akan lallai sai kin auri mutumin da ya yiwa duniyar iyayenki da Iyayensa nisa. Kiyi tunani Barirah ko Sulaim bai taka wannan Matsayin ba, ba ajin aurenki ba ne, kuma itama Mairam tasan haka, Nailar da kike ƙoƙarin mayar da kanki sakarya akanta ki tuna ita ce ta samu damar raɓarsa bayan Mahaifinsa, kuma kinji labarin da Malik ya bayar da kunnenki, lokacin da Maihaifinsa zai taushesa da mutanen da zai iya riska bayan mutuwarsa har da Naila a cikinsu. Nasan baki ɗaukeni a matsayin Uwa ba tuntuni, amma ki sani Macen da tayi butulci wa irin halaccin da Mahaifiyar Naila tayi mata to tabbas kema wata rana zata yimiki wanda ya fisa Zafi"
Ummu Malik ta ƙarasa faɗa muryarta cike da haushin abinda Mairam take ƙoƙarin ɗora Barirah akai.
Barirah ba tace komai ba, sai kuka da takeyi kamar ranta zai fita.
Da Ummu Malik ta faÉ—a mata sashen da aka kai su Naila su zauna a Dhahab da irin Makarantar da Naila fara zuwa birkicewa tayi, kuka harda bige-bige tana cewa; ita tafiya zatayi.
Domin zuwan Naila Babban jami'a irin wannan a Babban Birnin Abyad na bata tabbacin labarin zuwan Naila Dhahab ya riski Sulaim.
Tana cikin wannan rashin kirkin Malik ya shigo, bai yi wata-wata ba ya wanketa da marukan da sukayi connecting jijiyoyin ƙwaƙwalwarta ta dawo hayyacinta ta nutsu waje ɗaya tana sauke ajiyar zuciya.
Da zafin muryar takaicinta ya ce;
"Za ki tafi who cares? Za ki kashe kanki who cares? Kinsan wa ma kike so kuwa? Sau nawa nake ja miki kunne? Ohh wannan yawon Barar da mukayi a Birnin Abyad ne bai isheki ba ko so kikayi ki koma?
Wallahi Daga yau idan na ƙarajin motsinki akan Naila sai na maimaita miki Tarihin shekarun baya da suka wuce, fool!"
Babu wanda ya motsa a living room É—in, saboda girman muryarsa da ya cika ko ina. Ya na fita Barirah ta bi bayansa da kallo kamar zata haÉ—iyi zuciyarta.
A ɓangaren Ummi Aysha;
Babu wani kwana-kwana Malik ya sanar da ita gaskiyar komai.
Bayan tafiyarsa hirar su ce take ta kai kawo a cikin zuciyarta, ba ta ƙin Naila, amma tabbacin Sulaim yanayin dukka waɗannan abubuwan ne domin faranta ran Naila yasa ta buƙaci ganinta, ta ga menene take da shi wanda sauran mata basu da shi, ko kuma kawai sa'ace Allah Ya bata....
ROYAL UNIVERSITY ABYAD; har Naila ta bar Makaranta bayan ta haÉ—u da wanda Malik ya ce ta kira ya cikemata komai, bata daina sawa wanda ya biyamin kuÉ—in Makarantar albarka ba.
Da Driver ya zo ɗaukarta a Mota mai taushin kujeru da sanyin raɓa sai ta lumshe ido daɗi kamar ya sumar da ita har wani matse hannu takeyi tana ɗan zaro harshe ko wa take yiwa gwalo oho? Ta faɗa a cikin zuciyata tana sakin dariya.
Wajen cin abincin da ya dawo da ita asalin ƴar Yankin Tudun da bata taɓa zuwa ba Driver ya kai ta, wai ta huta ta ɗan ci abinci karta ƙarasa gida da yunwa inji Sir Malik.
Driver yana fita kafin ya zagayo ya buɗemata ƙofa ta saki dariya tana jijjiga kaina tare da juya idanuwana kamar zata wurgosu ƙasa.
Gaba É—aya É—an daÉ—in da ta É—anÉ—ana na wannan rana sai ya sata jin kanta da ganin kanta kamar wata ta musamman.
Da ta kai Gida Kaka tasha labari har da ƙari da zuzutawa kamar a gabanta akayi komai.
Bayan Magrib saƙon kiran Ummi Aysha ya riskesu ita da Kaka.
Zuciyarsu fal tsoro suka nufi Sashen.
Sautin Hermes flat shoe da ƙamshin turaren ta ne ya ankarar da su Naila fitowarta, Naila da Kaka nutsuwarsu suka tattaro waje ɗaya.
Bayan mun gaisheta ta amsa sai da ta ɗan ƙarewa Naila kallo na ɗakiƙu sannan ta ce;
"Naila"
Da sauri Naila ta amsa tanayin ƙasa da kanta alamar ladabi.
Da maganar mai cike da nutsuwa Ummi Aysha tace;
"Sunana Aysha Matar Abduh Dhahab, Mahaifiyar Sulaim" ta ƙarasa faɗa tana kallo yanayin Naila
A zabure Naila ta miƙe ta nufeta ta rungumeta da ƙarfi kamar zata ɓallata tana cewa;
"Dama nasan dole jinin Sulaim ne ya kafa Dhahab, kema kin ji labarin ƙonewarsu ko?"
Ido Ummi Aysha ta zaro tana kallon Kaka dake saitinta, kai Kaka ta girgiza mata.
Jin tayi shiru yasa Naila ta dawo hayyacinta ta saketa da sauri tana zamewa ƙasa.
Kafin Naila ta fara bata haƙuri Ummi Aysha ta ce;
"Ban sani ba Naila! dama Sulaim ya ƙone har ya mutu shine Malik ya kasa sanar dani don yaga bazan iya zuwa Yankin Tudu ba, maiyafaru bayan tafiyata? wanene ya ƙona min Ɗana da Mijina Abduh" Ummi Aysha ta faɗa kamar gaske, dama kuma ta jima tana naiman wanda zai bata labarin bayan tafiyarta don ta kasa tambayar kowa saboda kunyar guduwar da ta yi.
Ita dai Kaka kallonsu take yi musamman Ummi Aysha.
Kamar an kunna gidan radiyo haka Naila ta zauna tana bawa Ummi Aysha labari, wasu labaran duk ba a haifeta ba aka yi su a bakin Kaka ta ji.
Wasu Labaran Ummi Aysha ta murmusa wasu kuma ƙwalla ya tararmata a ido.
Sai da ta gama taji maganar Ummi Aysha
"Idan Sulaim zai dawo a raye zaki so shi kuyi Aure?" Ummi Aysha ta tambayetahar cikin zuciyarta domin a bayaninta ta fuskanci sam Nailan batasan Sulaim yana raye ba.
NAILA; murmushi nayi kunyar maganarta ya sata ƙarayin ƙasa da kanta, sai lokacin kunyar zubar da ta dage tanaayi, ita a dole masaniyar tarihin rayuwar Sulaim ya kamata.
Ummi Aysha bata ƙara ce mata komai ba, har masu hidimar shashenta suka gabatar mu su da Abincin dare.
Bayan tafiyarsu Naila..
Ummi Aysha kasa runtsawa tayi har sai da ta shawarci ƴar ƙanwarta Farheen da Naila ta taɓa gani a Birnin Abyad a gidansu Yasar lokacin dayake jinya.
Farheen Bata yanke hukunci ba ta ce ta bari gobe da safe taje har sashensu Naila ta ganta kafin su san abin yi.
★washe gari da yamma Farheen ta nufi Sashensu Naila.
Tarbar dake nuna asalin tarbiyyar da su Naila suka samo tun daga tushe Farheen ta samu daga garesu ƙarin abinda ya birgeta shine wasa da dariyar su, tsayawa a matsayinsu duk da karramawar da Sulaim yayi musu na kawosu cikin su.
Bayan ta koma Sashen Ummi Aysha suka haÉ—a Plan É—in da dole zai dawo da Sulaim Naila ta gansa, "ko yaya zata ji?"
Ummi Aysha ta tambayi Farheen.
Dariya suka saki lokaci É—aya.
MALIK;
Bayan ya gama abubuwan da zai yi ya shirya komawa Kahala don dubo lafiyar Sulaim
kafin ya isa ya kira Managernsa ya haÉ—asa da likitan Sulaim da bai ma san ba shi da lafiya ba, tunda bai sanarwa kowa ba
Malik sai da ya jira likita suka nufo Gidan...
A living room suka samu Noorhan lulluɓe cikin Abaya fuskarta babu kwalliyar da Malik ya saba ganinta da shi.
Yana ganin haka yasan ba lafiya ba. Itama tana ganinsu ta miƙe tana kukan su taimaka, Habibi baya ɗaga kira kuma tafi hour biyu a zaune bai fito ba, tayi knocking bai amsa ba.
Malik ɗan harararta yayi ta ƙasan ido wai "Habibi mtsw" ya faɗa ƙasa-ƙasa yana nufa hanyar daƙin da Sulaim yafi zama a ciki.
Shima ya buga bai buÉ—e ba, don haka ya fara bi É—akunan yana dubawa.
Malik yana cikin haka Sulaim ya shigo Gidan, Kyakkyawar fuskarsa ta faÉ—a sosai kamar ya yi shekara yana jinya.
Da gudu Noorhan ta miƙe sai dai yanayin tsayuwarsa da yanda yake kallonta yasa ta dakata tana wasa da yatsun hannunta. Maimakon rungumarsa da ta yi niyyar yi sai ta kamo hannunsa.
Da kai ya amsa gaisuwarsu yana zama a gefen Likitansa, hucin zafin zazzaɓinsa na busowa likitan.
Shima Malik waje ya samu ya zauna, zuciyarsa cike da mamakin rayuwar Sulaim, to ko dai kashe kansa yake son yi, tunda yana ganin kamar bashi da kowa. Banda haka tayaya namijin daya mallaki hankalinsa kamar Sulaim zai zauna yana wasa da lafiyarsa?...
Bayanin Sulaim ya haƙura su tafi Asibiti likita yake ta yi da sigar lallashi da tausasa harshe, har da ce mai Naanah Kakarsa kullum sai ta ce Sulaim ya rage zuwa.
Kalllon Likita Sulaim ya yi a hankali ya ce;
"Maiyasa zaka yi ƙarya daga wajen Naanah fa nake"
Dariya likita da Malik suka gimtse ganin ya harbo Likita kai tsaye. Banda Noorhan da burinta kawai Sulaim ya miƙe su tafi Asibiti ya yi ya warke su komawa Soyayyar su.
Malik yana shirin yin magana wayarsa ta fara vibrating. Bayan ya gama saurarar Farheen miƙewa yayi ya na furta "Innalillah! When accident ɗin ya faru?"
A ɓangaren Farheen dasauri tace " a safiyar ranar".
Kai Malik ya ɗan girgiza kafin ya naimi excuse ɗin zai ƙara kiranta. Suka yi sallama
Idon da Sulaim ya zubawa Malik na nufin ƙarin bayani, don haka Malik ya ce;
"Ummi Aysha ce ta yanke jiki ta faɗi jiya da daddare, garin zuwa dubata Naila ta zame I think kamar Farheen na bayanin ƙafar ya samu matsala, kuka ma takeyi."
"Ka shirya komai zuwa safiya mu isa Abyad" Sulaim yana faɗa ya miƙewa.
"Habibi ni fa" Noorhan ta tambaya kamar zata yi kuka...☹ï¸
Ma su son a tafi Æ™asar Abyad da Noorhan ya dannaâ¤ï¸ mara so kuma su dannaðŸ‘ðŸ»
Mu yi voting 😂
[9/5, 8:36 PM] Maman Amatullahi: SASAAL
9
A ɓangaren Sufyan;
Yana buÉ—e takardar yaga an rubuta;
"Barka da zuwa Iyakar Yankinka Sufyan! Rubutu na bazai tsawaita ba saboda wa su dalilai, amma duk tsananin da komai zaiyi babu zuwan Jalal da Ɗayyib Babban Birnin Abyad. Dawowarka zai tabbata ne idan ka ƙauracewa abincin cin su da shan su. Daga ƙarshe ina tayaka alhinin rashin da kayi. Ba lallai ka fahimceni ba amma ka haddace saƙona ka kuma sanya kunne da ido akan komai, ga na'urar naɗar komai ta sirrin da zaka saurara kai tsaye ta wayar hannunka. Zaka fahimci abinda na rubuta dalla-dalla."
Sufyan gumin fuskarsa ya zarce hannunsa yana rawa ya yaga dakartar gudun kar wani ya gani sannan ya ciro ƙaramar na'urar dake ciki envelope.
A karo farkon da ya fara wasa ƙwaƙwalwarsa ya nutsar da kansa kafin ya kutsa cikin Yankunansu.
Maimakon ya wuce Yankin Tudu sai ya wuce Yankinsu Mahaifiyarsa Hindu.
Ya samu Kakarsa cikin daular rayuwar da baiyi tsammani ba, tayi masa tarba ta musamman duk da bata san da zuwansa ba. Yana kallonta komai saƙon Malik ya na dawo masa, wannan dalilin yasa bai taɓa komai da Kakarsa ta gabatarmai ba, sai Mahaifiyarsa da ya tambaya tana ina? Murmushi tayi tare da shaidamai Hindu ta tafi Nahiyar Turai jinya, ai shi yasa ma baya samunta a waya.
waje ta bashi wai huta ya ci abinci, Sufyan amfani ya yi da basirarsa wajen jagwalgwala abincin kamar ya ci, abinda bai sani ba Kakarsa tana laɓe tana kallonsa. Bayan yayi mata sallama kafin ya isa Yankin Tudu ta kira Ɗayyib ta sanar dashi isowar Sufyan amma fa baici komai ba tana zargin jimamin rashin samun Mahaifiyarsa ne ya hanasa ci.
Lokacin da Sufyan ya isa Yankin Tudu abubuwa sun sauya, Talakawan Yankin sun samu cigaba ƙwarai kamar ba Yankin Tudu ba, ko da ya tambaya bayan ya huta sai ake sanar dashi ai Naila ce da Kakarta suke turo kuɗi, yanzu haka da safe kafin isowarsa dogon mota ta kwashi matasa sun samu aiki a ƙasar Abyad duk ta sanadin Naila, shiyasa jinin Jalal ya hau yanzu haka yana kwance babu lafiya.
Sufyan yana jin haka ya nufi ɓangaren Sarki Hammam da sunan isar da gaisuwa, domin ko da suka haɗu da Mahaifinsa ya dai jashi a jiki da bashi umarnin ya kwanta ya huta amma bai sanar da shi Jalal bashi da lafiya ba.
Sufyan yasan Ɗayyib da Jalal basa dogon hira gudun kar wani ya ji su don haka daya isa living room ɗin Sarki Hammam dayake zama wasu lokuta da Iyalansa ko baƙi masu muhimmanci sai ya ajjiye na'urar da Malik ya basa a gefen da bazasu ankara da wuri ba.
Da ya je Sashen Jalal ba a barsa yaga Jalal ba don haka ya koma nasu sashen, a living room É—in Mahaifiyar ya zauna yayi shiru.
Har zuwa wasu ɗaƙiƙu yana zaune zaman jiran tsammani da abu maƙale a kunnensa, yana ƙoƙarin miƙewa sai ga Ɗayyib da sallamarsa.
lallashinsa ya hau yi akan rashin Mahaifiyarsa da ta tafi nahiyar Turai jinya kafin ya sako masa zancen yana so ya bishi Babban Birnin Abyad idan zai koma domin ya ga yaya ma'aikatarsu take. Sufyan kai tsaye ya ce; "haba Baabah ba Lallai su amince ba kuma ai babu abinda zaka je yi, amma bari mu gani zuwa safe idan na tuntuɓesu"
Shafa kanshi ÆŠayyib ya yi da wani irin salo ya ce;
"Babu Matsala Sufyan ka tuntuɓesu, yanzu bari a kawo maka abinci da abin sha ko?"
Kai Sufyan ya É—aga alamar ya ji.
Ɗayyib yana fita ƙwaƙwalwar Sufyan ya harba maganganun Malik suka ƙara dawomai kenan cin abinci daga garesu na nufin dole ya kaisu Babban Birnin Abyad ko da a ɓoyene su rayu da shi domin kutsawa cikin Dhahab, shin maiyasa Mahaifansa basason kwanciyar hankalin Talakawansu wacce iriyar zuciya garesu da babu tausayi da imani?
Yana cikin wannan tunanin Abinci ya iso, maimakon zama a inda yake, abincin ya ɗauka ya shiga chan ƙuryar ɗakin Mahaifiyarsa mai duhun da babu wanda zai iya ganinsa sai Mahalaccinsa.
Yana shiga ya ajjiye abincin a gefe ya mayar da hankalin kan hirar da Sarki Hammam yake yi da iyalinsa. Minti uku bayannan Muryar ÆŠayyib Mahaifinsa ya bayyana.
ÆŠAYYIB
Bayan sun gaisa da Sarki Hammam, Sarki Hammam yake tambayarsa
"ya ya jikin Jalal?" Ɗayyib baiyi magana ba ya yi shiru har na wasu daƙiƙu sannan ya ce;
"Abincin da Jalal ya tanada ya isa ga Sufyan, ranar tafiyarsa zamu tafi tare da shi, mu bincika ina mutanen Yankin Tudu suke zuwa a cikin ƙasar Abyad, sannan mu san wanene mamallakin ma'aikatar su Sufyan"
Gwauron numfashi Sarki Hammam ya sauke ya É—an kalli abinda Sufyan ya ajjiye danna ya ce
"Amma kana ganin babu wanda zai faɗawa Sufyan azabtar da ka ganawa Hindu bayan yin wayarsu ta ƙarshe, har binnenta da kayi shekaran jiya da ranta" Sarki Hammam da zuciyarsa sam babu sukuni ya tambayi Ɗayyib yana fatan Sufyan ya jishi.
A kasashe ÆŠayyib ya ce;
"Babu wannan Mutumin a duniya, domin babu wanda ya sani kuma duk wanda ya ci amana a tsakaninmu to zai bi Hindu inda taje, na binne Hindu da ranta a tsakiyar ɗakinta ne domin ta girbi abinda ta shuka, saboda itace ta ɓata komai ta zuga Sufyan ya tafi Birnin Abyad, har da Naila. Yanzu gashi Talakawa duk suna walwala a Yankin Tudu su na jinsu kamar kanmu ɗaya da su, ba ni da haufi akan hukuncin da na yankewa Hindu ko da Sufyan zai ji wata rana. Domin abinda ya shuka shi ta girba"
A ɓangaren Sufyan kuka ya kece da shi jikinsa ya na rawa, katse komai ya yi, ya kuna fitilar wayarsa, cikin zafin nama ya ɗaga gadon Mahaifiyarsa, guri ya gani manne da tiles ɓaki sabo. Kuka ya saki yana kwanciya a wajen, saƙon Malik ya tuna "ina tayaka alhinin rashin da kayi" tayaya Malik ya sani, tabbas yana buƙatar ganin Malik ko ta halin ƙaƙa amma ta yaya zai tserewa su Ɗayyib????
SULAIM
kallon mamaki ya yiwa Noorhan na daƙiƙu, amma ko don tasan matsayinta ya kamata taje ƙasar Abyad. Idanuwansa ya mayar kan Malik da yake jiran umarninsa ya rausayar da kansa alamar ya amince aje da ita.
LV Jogger da free size shirt dukka baƙaƙe sai GG sneaker ya yi sassanyar adonsa mai birgewa, don tafiya Airport.
Noorhan dake lulluɓe cikin Abaya kallon takunsa take yi zuciyarta na ƙara macewa Soyayyarsu.
Idanuwanta ta lumshe a hankali tunanin na zurfafa a cikin daƙiƙu, wai gasu sunyi aure har sun haifi yara kyawawa irinsu..
A gurguje Noorhan taje gida ta kwaso Kayan buƙatarta da Passport.
Sulaim bayason takura shiyasa shi da Noorhan kowa ya zauna a mabanbanta waje. Hakan ba ƙaramin daɗi yayiwa Malik ba, itama Noorhan bata wani damu ba tunda zata je Abyad ƴan uwansa su san da zamanta.
Ummi Aysha;
Ummu Malik da Simbi ne suka je dubata, laƙwas tayi kamar gaske, tana amsawa daƙyar don tasan Malik ne ya sanar da su.
Daganan su Ummu Malik da Simbi ɓangarensu Naila suka wuce don duba nata jikin, sai dai a tsaye suka samu Naila tana ciye-ciye haɗe da bawa Kaka labari.
Naila batayi rawar kan nuna murnarta ba kar su gwaleta, saboda wannan ne karonsu na farkon haÉ—uwa fuska da fuska tun bayan barin su Yankin Tudu.
Sai dai yadda suka rungumen Naila da Kaka kuma suka saki jikinsu yasa itama Naila nuna farin cikinta.
Bayan sun motsa baki da cookien da kaka ta gabatar musu Ummu Malik ta ce;
"Ashe ƙafa ya yi sauƙi Naila, ai a bayanin Malik ya ce Farheen ta kira tana kuka, wallahi sai muka ɗauka ƙafar karyewa tayi, Allah Ya kiyaye gaba, itama Ummi Aysha Allah ya tashi kafaɗunta"
Naila da Kaka wayancewa suka yi suka amsa da "Ameen" har da Simbi data ƙurawa Naila ido. Domin Ita bata yarda da jin ciwon ƙafar Naila ba wani abun take zargi daban.
Gaba ɗaya sai hirar ta su ya koma kamar na yaƙe domin daga Naila har Kaka jira sukeyi su Ummu Malik su tafi Naila taje ta tambayo Farheen abinda ya faru.
Fuskantar hakan yasa Ummu Malik yi musu sallama amma a nata ɓangaren gani takeyi baƙonta ce tasa suka kasa sakin jiki da su.
NAILA;
Suna fita kaka ta ce;
"Maza tashi kije kiji menene ya sameta"
Guntun light orange rigar da bai ƙarasa ƙasa bane sosai a jikin Naila Abaya mai maɓallai ta ɗauko ta ɗora akai ta ɓame maɓallan da sauri, bata damu da Ɗankwali ba tunda duk cikin gida ne, yasa ta yafa malulluɓin Abayar a kanta...
Ummi Aysha;
Bayan sun shirya faɗuwarta ita da Farheen da karyewar ƙafar Naila har sukayi nasarar Sulaim ya ce zai taho, sai ta rasa kuma ta hanyar zata nunawa Sulaim fuskar Naila ta hanyar bazatan da zai birgesa, don haka ta fara neman layin Malik, cikin sa'a tana kira ta samesa, ya shaida mata sun iso Airport ɗin Ƙasar Abyad.
Tana yunƙuri kiran Farheen domin samun mafita amintacciyar Hadimarta ta naimi izinin shigowa.
Tana jin ta ce Naila ce tazo gaisheta ta gyara zamanta tace ace ta shigo.
A ɗan gefen Couch Naila ta zauna ta gaisheta har ya sanar da ita shigowarsu Ummu Malik Sashensu amma kuma takasa tambayarta maiyafaru su Ummu Malik suka ce ta karye a ƙafa.
Ummi Aysha ta gane ina Nailan ta dosa tunda ta sanar da ita shigowarsu Ummu Malik wajen su.
Cikin dabara da sanyi Ummi Aysha ta ce;
"Naila É—an taimaka ki dafamin Noodles mana É—azun Farheen ta dafamin sam banji daÉ—insa"
Da sauri Naila ta ce "to" tana miƙewa.
Dakatar da ita Ummi Aysha ta yi ta hanyar cewa;
"rage wannan Abayar Naila karki samu matsala da wuta, ga scarf can ki É—aure kanki"
Babu damar musu, don haka Naila cikin kunya ta ɓalle maɓallan Abayar jikinta, ta cire ta ajjiye a gefe da mayafinsa, sannan ta ɗauki ɗan Scarf ɗin da Ummi Aysha ta nuna mata.
Zata tafi Ummi Aysha ta ƙara dakatar da ita tana cewa;
" É—aura mana mu gani Naila"
Cikin kunyar daya kasa sakin Naila ta ɗan ɗaurashi, kwantaccen sumar kanta ya bayyana agaban goshinta da bayan ƙeyarta.
Murmushi Ummi Aysha ta yi kafin ta bata umarnin tafiya.
Da taimakon masu Hidimar sashen Naila ta isa madafin Ummi Aysha.
Bayan fitar Naila ajjiyar zuciya Ummi Aysha ta sauke tana gyara kwanciyarta.
Sai dai kamar ana jiran fitar Naila, motsin Dhahab ya sauya saboda motsin motoci da ƙarin jami'an tsaron da suka fara mamaye kowani sashi na Dhahab.
Ummi Aysha murmushi ta saki lokacin da ta ji alamun kusantowar motocin sashenta, dalilin jiniyar da ke bawa Securities alamar buɗe ƙaramin gate ɗin da yayiwa Sashenta iyaka da ragowar sashen dake cikin Dhahab, tun kafin isowarsu kar Sulaim ya ɓata lokacin zaman daƙiƙu a cikin mota.
Farheen dake sama tanajin alamar chanjin da rabonta da jin irinsa tun shekarar da Sulaim ya É—auke Naanah tayi wuf ta zura tsadadden abayarta, turare kuwa kamar zata juyeshi dukka ajikinta. Kamar zata faÉ—o haka take saukowa daga stairs da gudu kar ayi babu ita, domin tasan da zarar ya shiga to ma su tsaron lafiyarsa da zasu jirasa a living room bazasu barta ta shiga ba kuma ko sun kira Malik ba zai bari ba.
A hankali ƙarfin ƙamshin Sulaim ya fara mamaye living room ɗin Ummi Aysha kafin ya fara gangarawa ɗakunanan sashen da madafin abincin da Naila take ciki.
Ido Ummi Aysha ta lumshe ƙwalla na taruwa a cikinsu lokacin da tayi tozali da jarumin Ɗanta.
Bai yiwa kansa mazauni a ko ina ba sai gefen lafiyayyen tattausar katifar dake saman gadon da take kwance a kai, kafin ya gaisheta sai da ya fara rungumarta ya sumbaci goshinta da hannunta, sannan ya gaisheta Cikin taushin murya da Yaren ƙasar Abyad da sukafi amfani da shi. Kuka ta fashe dashi tana ƙanƙame hannunsa ta kasa amsawa.
Noorhan da Malik da suka zauna a Couch É—aya Ummi Aysha ta kalla.
Cikin girmamawa suka gaisheta, da kai ta amsa kafin ta yafito Malik da hannu, raÉ—a tayimasa a kunne, kan ya yiwa Securities magana su bar Naila ta shigo.
Kafin Malik ya fita aiken Ummi Aysha suka gaisa da Farheen, Sannan Noorhan da take kallon komai dalla-dalla tana lissafa iya adadin dukiyar da aka kashe kafin mallakarsa ta gaishe da Farheen tana hura hanci.
Da Sulaim Farheen tayi gaisawar ƙarshe tana murmushin jiran ta inda Naila zata ɓullo.
Noorhan zamanta ta gyara tana jiran Sulaim ya gabatar da ita ko su Ummi Aysha su tambayesa wacece ita, amma sai taji shiru har Malik dayake gimtse dariyar gano Plan aka shiryawa Ubangidansa ya dawo daga aiken Ummi Aysha ya zauna.
Naila ƙamshin turaren Sulaim har cikin siririn hancinta, jin alamun jiniya yasa ta matsu ta koma gurin Kaka taji menene yake faruwa.
A plate mai kyau ta juyo Noodles ɗin dayake tiriri da ƙamshi mai daɗi, Securities ɗin data gani yasa ta ɗan ja da baya, amma suka bata umarnin ta shiga inji Ummi Aysha.
Jiki a sanyaye Naila ta kutsa da Sallama.
Malik, Noorhan, da Farheen, idanuwansu kamar zasu zazzago wajen kallonta, musamman Noorhan da Malik.
Gaishesu Naila tayi Noorhan da Malik da kaa suka iya amsawa, saɓanin Farheen da ta amsa tana ɓoye dariyarta, da yaba basirar Ummi Aysha.
Sulaim bai damu da shigo ba tunda bai san wacece ba, hannun Ummi Aysha ya ƙara kamowa zai sumbata, jajayen siraran laɓɓansa suka maƙale a kai dai-dai lokacin da Naila ta ƙaraso ta ajjiye abincin hannunta a table ɗin dake gefen bedside.
Da tsoron ganin baƙin fuskar dayasa ta jin kunya tana ɗan zare ido ta kallesa da harshen ƙasar Abyad daya kama sassanyar muryarta ta ce;
"Ina wuni Sir,"
Sulaim ya kasa amsawa ya kuma kasa cire laɓɓansa daga hannun Ummi Aysha balle ya ajjiye hannun, lumsassun idanuwansa da zazzaɓi ya kama ya ɗago ya zuba mata....
😄
[9/5, 8:36 PM] Maman Amatullahi: SASAAL
10
SUFYAN;
Zamewa yayi daga saman wajen yana kallon baƙin tiles ɗin da jajayen idanuwansa. dagaske Mahaifiyarsa Hindu ce a ciki. Kenan ba zai ƙara ganinta ba, ta yi wahala ta ɗorashi akan aƙidar gina kansa da kawowa Yankinsa cigaba ba zaman yin gasa ko kashe wasu ba. Ita ta fara tunamai, Sulaim da Abduh sun maƙale a zuciyar mutanen Yankin su ne saboda cigaban da suka kawo, don haka shima ya fita ya yi ilimin da babu mai irinsa ya kuma kawo cigaban da zai zama abun yabo wa mutanen Yankinsa, kuskurenta ɗaya don zuciyarta akan kowa matsawar zai zama abinda take buri, saɓanin Mahaifinsa da burinsa ya tusa masa aƙidar da suka taso akai na kashe-kashe da ramuwar gayya.
Da ace idan ya fasa ramin domin bazai kirasa kabari ba, zai samu masu tsayamasa su karesa daga Ɗayyib ya ciro Mahaifiyarsa da ya cirota ya yi mata wanka ya kaita Maƙabarta ya binne kamar kowa, amma ba shi da wannan damar.
Tuna irin azabar da ya san dole zatashashi a hannun Mahaifinsa, wanda kuma ita kaɗaice zata iya basa labari amma bata raye yasa ya fashe kuka. Tsanar Mahaifiyar da ta yi masa ƙarya saboda duniya na mamaye ko ina nashi.
Ɗayyib har ya yunƙura zai miƙe idanuwansa suka sauka kan ɗan na'urar da Sufyan ya ajjiye, kallon Sarki Hammam ya yi yana nazartar yanayinsa kafin ya ce ;
"Sufyan ya shigo nan ne?"
Sarki Hammam cikin Basarwa,dakiya da shariyar da ya É—auki tsayin shekaru yanayi ya ce;
"Ya shigo ya gaisheni bai jima ba ya miƙe, da alama sauri yake yi."
Kai Ɗayyib ya jinjina ya wayance ya durƙusa ya ɗauke na'urar.
Da yake dare ya yi sosai ÆŠayyib sashensa ya wuce da Na'urar bai nemi Sufyan ba. washe gari da sassafe
yana fita kai tsaye wajen mutumin da ya taɓa bincikamai wayar Naila ya nufa da kansa. Tabbacin na'urar naɗar sautin da ake amfani da shi don naɗar sirri ya tabbatarmai, tare da shaidamai dole wani ne ya taho dashi daga wata nahiyar, Sarki Hammam ba shi da ikon mallakarsa ta daɗin rai.
Kamar zai huda ƙasa haka Ɗayyib yake taka sawayensa, zuciyarsa kamar ana gobara saboda yadda ko ina nasa ya ɗauki zafi.
Dakewa ya yi, ya cije bayan ya dawo Gida har sai da ya bari dare ya yi sannan ya nufi wajen Sufyan.
Kaifaffen wuƙar ƙugunsa ya shafa yana lumshe fararen idanuwansa kafin ya buɗe su, sun koma jajaye. Babu sallama ya kutsa sashen Hindu....
UMMI MAIRAM;
Tun ranar da hatsaniya ta haɗasu da Naila take kuka, Mahaifinta mai son zuciya da fifita farin cikin nasa akan na wani, sai mita yake yi yana kwashewa Naila albarka, acewarsa bai san uban daya kawosu Dhahab ba. Dama daga gani Malik baƙin ciki yake yi da zamansu. Ban da haka tayaya zai marawa Naila baya kai tsaye ba tare da bari a yankemata hukunci ba?
Kukan da Mairam ta dage tanayi kamar ƙaramar yarinya da zugata da Mahaifinta yakeyi ne yasa Mahaifiyarta ta magantu;
"Kina ba ni mamaki Mairam, mahaifiyar yarinyarnan tun kafin Mijinta Mahmoud ya mutu take hidima da ke, Mijinta ya mutu ta dawo kula dake gaba ɗaya, sanadiyyar haka ta rasa ranta, a tunanina duk ranar da kikaga Naila sai kin fi kowa farin ciki, amma son zuciya na neman makantar da ke, Yaron nan da kike kwaɗayin abinda ya tara yana da Uwa kuma ko ya mutu baki da gadonsa, yana kyautata miki dai-dai iyawarsa, amma ke burinki ya manta uwarsa ya nunawa duniya ke ce kika haifesa tun da shi mahaukaci ne ko? Ko Barirah kinsan ba halin ƙwarai gareta ba, amma duk kin toshe jinki da ganin ki burinki kawai ya aureta ki samu fada a wajensa, ai sai mu ga idan kina da ikon auramai son ranki, sha-sha-sha mara tsayawa iyakarka kawai"
Kaf maganganun Mahaifiyarta Mairam bata É—aukesu da muhimmanci ba, a ganinta ai Ummi Aysha guduwa tayi mai zai sa a yanzu ta dawo Sulaim yafi fifitata a kanta?
Ummi Mairam bata ƙara birkicewa ba, sai da Barirah ta kirata a waya ta sanar da ita ai tuni ma Sulaim yasan da zaman Naila tunda har Malik ya naima mata tsadadden Makaranta da matsuguni na musamman ɗin da ko ita da ta zauna da shi bayan Mahaifiyarsa ta gudu ta barshi bata samu ba.
Tana cikin jinyar zamansu Naila a waje na musamman a Dhahab, sauyin Dhahab alamar Sulaim ya dawo ya ƙara hargitsata. idanuwanta har zurma sukayi ciki kamar zasu faɗo saboda zarensun da takeyi tana jiran Sulaim ya fara shigowa Sashenta ya gaisheta kafin ya isa ga Mahaifiyarsa.
SASHEN UMMI AYSHA;
ido Naila ta ɗan zare tana kallon laɓɓansa da ya kasa ɗaukewa da ga kan hannun Ummi.
Ƙara maimaita gaisuwarta ta yi da harshen nasara ko Yaren ƙasar Abyad ne baya ji.
Still bai amsa ba sai kallon fuskarta da yake yi kafin ya gangaro da kallonsa kan kyawawa ƙafafuwanta da take tsaye a kai.
Ido Naila ta ƙara zarowa, Ummi Aysha da daɗi yakama kamar ta tashi ta rungume Naila, a hankali ta ce;
"Zaki iya tafiya Naila, ki ce ina gaishe da Kaka"
Sulaim hannun Ummi Aysha ya zame a hankali daga kan laɓɓansa, sai dai bai ajjiye hannun ba mannawa ya yi a gefen fuskarsa yana lumshe idanuwansa. Kunya ce ta mamayesa son Mahaifiyarsa na ƙara kamashi.
Don ya gane plan ta shiryamai tunda ga Naila tsaye akan ƙafafuwanta kuma saboda ta nunamai Naila a lokacin da zai fi birgesa sai tasa ta dama mata Noodles domin ya yi tozali da ita.
Ƙara buɗe idanuwansa ya yi ƙaɗan yana kallon yadda Naila take yunƙurin ɗaukar Abayarta da sauri, ba tare da ta zura ba ta nufi hanyar fita.
Kamar wanda ya ƙware haka ya ƙirƙiro tarin dole.
Ummi Aysha da sauri matse dariyarta tana ce wa Naila;
"Naila tsaya ki nutsu ki lulluɓe jikinki kinji"
Malik da Farheen kamar jiran fitar Naila sukeyi. Tana fita suka saki dariyar da babu sauti haÉ—e da dafe bakunan su.
Sulaim hannun Ummi Aysha dake gefen fuskarsa ne fara motsawa, alamun dariyarsa takeyi.
Cikin taushin Muryar dake fita da sautin mai sanyi ya ce;
"Ummiih, kinsa na ji kunya, wani iri nake ji, dama wayo kikayimin"
Ummi Aysha miƙewa ta yi zaune tana dariya haɗe da rungumoshi, shima ƙaramin dariya ya saki yana ɓoye fuskarsa a bayanta.
Noorhan hannunta da ƙafafuwanta ne suka fara rawa, wayarta da ta riƙe tana dannawa kamar batasan abinda suke yi ba, shima yafara rawa.
"Wacece wannan yarinyar, Sulaim bai sanar da ni yana da ƙaramar ƙanwa ba, maiyasa yake kallonta irin haka?" Noorhan ta tambayi kanta tana satar kallonsu Malik da har lokacin suke ɓoye dariyarsu...
NAILA;
Tana isa Sashensu ta ƙwalawa Kaka kira
"Kakaaa!!!"
Kaka da sauri ta fito tana tambayar "menene ya faru Naila?".
"Kaka wani mutum na gani tare da su Malik a sashen Ummi Aysha, Kaka kinganshi,?"
"A'a Naila banganshi ba, maiyasa sameshi" Kaka ta tambaya da son jin zance.
"Kaka yana da kyau, kinga yadda yake kallona, Ni kuma na É—an zaro ido, kai Kaka ya ruÉ—arni wallahi"
Kaka da labarin yake yiwa daÉ—i dariya tasa ta ajjiye cokalin hannunta haÉ—e da cewa;
"sai ya ce miki me? Yana sonki?"
Tsabar yadda zancenta yayiwa Naila daÉ—i sai da ta saki dariya tana juya idanuwa ta ce;
"Kaka ko fa magana baiyi ba, kinga bakinsa hmmm😄!"
"Bakinsa me?? Ke ki saki jiki ki bani labari mai ya samu bakin na sa?" Kaka ta faÉ—a tana dariya.
"Kaka fa tsabar kyawuna da yake kallo kasa cire bakinsa ya yi daga hannun Ummi Aysha, ga idanuwansa masu kyau, shiyasa fa nima na ɗan zaro nawa idon, saboda ya ƙara ganin kyansu, yasan nima kyakkyawa ce. Ko da yake ni fa bai wani birgeni ba, kamar zai yi tsaho da yawa"
A wannan karon Kaka garin dariya har cokalin gefenta ta wurga, da salon ƙara zurma Naila tunda tuni ta samu labarin zuwan Sulaim ta bakin Hadimansu ta ce;
"Kuma baiyi miki kama da wani wanda kika sani ko kika taɓa gani ba?"
ÆŠan jim Naila tayi kafin ta ce;
"Ai Sulaim ne kawai da ya girma a raye ya samu kuÉ—i zai yi irin wannan kyan, wai Kaka kinga idanuwansa kuwa? Sak irin na Sulaim idan yana kallona a Yankin Tudu, amma wannan sai wani iyayi ko gaisuwata fa bai amsa ba"
Kaka da dariyarta yaki yankewa miƙewa tayi tana hasaso duk ranar da Naila ta gane Sulaim yana raye yaya zata ji??..
Kamar sakarya haka Naila ta koma lokaci zuwa lokaci sai ta zaro ido ta ƙyaƙyale da dariya.
A living room ta zauna tana roƙon Allah Ya sa Ummi Aysha ta aiko kiranta, amma har wajen goman dare bata turo ba don haka ta haƙura ta kwanta barci.
A SASHEN UMMI AYSHA
Farheen ce ta fara miƙewa tana yiwa Noorhan maganar ta zo ta kaita masauƙi, kafin Malik ya bi bayansu, don duba gyaran da aka yiwa Masauƙin Sulaim.
Bayan sun fita zame jikinsa Sulaim ya yi, ya zauna da kyau sannan a hankali ya furta;
"Na gode"
Kai Ummi ta janjinamai haÉ—e da cewa;
"Nasan ba lallai ka ziyarceni ko da kaji ina halin jinya ba, saboda girman laifina daka kasa mantawa, amma idan na haɗa da ni da ita, nasan dole ka ziyarcemu, ba ni da abinci mai daɗin da zan gabatar maka ko wani abu da zan shiryamaka da zai birgeka sama da nuna maka fuskar masoyiyarka da ka manta tun zamanin ƙuciya.
faɗamin ya ya kaji da ka ganta? Ka ganta kyakkyawa ko? Tun da gashi hannuna har maƙalewa ya yi"
A karon farko Sulaim ya saki dariyar da ya bayyana jerarrun haƙoransa yana miƙewa saboda kunya.
Itama Ummi Aysha haƙoranta ta ƙara washewa ranta fari fes, zata iya rantsewa tun bayan sanin Sulaim yana raye bata ƙarajin daɗin da ta ji irin na yau ba.
Ta ji zafin jikinsa ba kamar na mai cikakken lafiya ba don haka bayan fitarsa ta lalubo wayarta ta kira Malik.
Malik Bai ɓoyemata zazzaɓin da Sulaim ya kwana biyu yana yi ba.
Likintanta tayiwa waya, bayan sun gama tattaunawa ta miƙe ta ɗauki Noodles ɗin da Naila ta ajjiyemata, ai ko babu daɗi dole ta ci, balle daɗinsa abin a yabawa Nailan ne da tukwaici mai tsoka.
Ƙaramin Sashen dake jikin na Ummi Aysha aka gyarawa Sulaim, masu tsaron lafiyarsa zagaye da ko ina na sashen da Dhahab gaba ɗaya.
Noorhan; tana wanka tana Kuka, kenan Sulaim ya kawota ƙasar Abyad ne domin ya nuna mata matsayinta, suma mugayen ƴan uwansa suna kallonta amma ko su tambayesa wacece ita? Wallahi dole Sulaim ya sanar da su matsayinta idan ba haka ba ita ta sanar da su da kanta...
SULAIM;
Yana wanka fuskar Naila da yadda ta zare ido tana gaishesa da muryarta da ya sauya daga na Æ´an yara zuwa na Æ´ar budurwa na kai kawo a cikin idanuwansa, kunnen da zuciyarsa.
Nailarsa da zama Æ´an mata ta girma, to maiyasa bata gane shi ba?
Ya tambayi kansa bayan ya fito daga wanka ya na zura Soft Pyjamas ɗin da Malik ya kawomasa, tunda baya tafiya da kaya sai dai idan yaje ƙasa ko gari ya siya idan zai tafi ya barsu a can.
Yana shirin kwanciya bayan ya taɓa sassauƙar Abincin da Malik ya kawomai Ummi Aysha ta iso da Likita.
Yana son taji daÉ—i ya nuna mata itama Uwa ce data isa É—anta kamar ko wacce Uwa don haka ya amince Likita ya dubasa haÉ—e da samai ruwa.
Noorhan;
tayi tunanin za'a kirata Dinner amma sai ta ji shiru, sai É—aki da'a biyota da shi.
★washe gari ma tana sa ran zasu kirata shima ta ji, shiru. Wanka tayi ta shirya cikin kalar Abayar daya haskata tana girgiza ƙafarta tana jiran Sulaim zai turo a kirata ko bazai turo ba, ta kirasa ta WhatsApp baya ɗauka kuma ita bazata kira Malik ya fahimci halin da suke ciki ba.
Ummi Aysha da Farheen.
Ummu Aysha bayan ta dawo daga wajen Sulaim sun sha hira Farheen cikin farin ciki, musamman Farheen da har kwaikwayar kallon Sulaim takeyi.
★washa gari Ummi Aysha da kanta ta shiryawa Sulaim Breakfast, kuma ta ɗauka ta nufi Sashen.
A kwance ta samesa cikin Armani lounge wear jajayen da suka yi mai kyau, har lokacin ganinsa bai dawo dai-dai ba jikinsa a mace.
Shi ya fara gaisheta ta amsa tana yimai ya ya jiki?
Da kai ya amsa mata yana gyara zamansa.
ÆŠagowa ya yi a hankali ya kalleta kafin ya ce;
"Tana zuwa Makaranta?"
Ummi Aysha da daÉ—i yasata sakin murmushi saboda gane ina ya dosa amma sai tayi fuska kamar ba ta gane ba ta ce;
"Wacece? Ai Farheen tuni ta gama Makaranta, ko su Simbi ƙanen Malik kake nufi?"
"Ummiiih" ya faÉ—a yana É—age cikakkiyar girarsa É—aya da murmushi kwance a saman fuskarsa.
Ummi Aysha wani irin daÉ—i takeji É—anta ya saki jiki da ita a karon farko.
Saboda taga yadda zai yi sai ta ƙara cewa;
"To ai bangane ba, auuw! ohhh! Naila ka ke nufi😄?"
Juya mata baya yayi yana dariyar da ke motsa kafadunsa.
Itama Ummi Aysha dariya tasa kafin ta kira sashen Hadimai su sanar da Naila tana nemanta a sashen Sulaim idan bata gane ba su rakota.
Bata ajjiye wayar ba sai da ta kira Malik ya sanar da Securities su bar Naila idan ta iso ta shigo.
NAILA; lokacin da saƙon Ummi Aysha ya jewa Naila, daƙyar ita da Kaka suka daure Hadiman suka fita, suna fita Kaka tasa dariya tana dafa Naila dake juya idanuwa kamar zasu zazzago.
Ta ɗauko dogayen Riguna sufi kala goma tana nunawa Kaka, Kaka tace basu yi kafin ta zaƙulo Royal blue mai kyau.
Bata wani fesa turare sosai ba, kar ace sonshi takeyi da addu'ar sa'a Kaka ta rakata suna dariya...âœðŸ»
[9/5, 8:50 PM] Maman Amatullahi: SASAAL
11
SUFYAN; Tuna abinda ya ajiye a living room É—in Sarki Hammam yasa ya É—ebi rabin abinci ya watsar a lungu, ya dai-daita zamansa amma har lokacin ya kasa tsaida hawayensa. Tun yana sa ran ÆŠayyib har ya cire. ido buÉ—e ya kwana yana kallon inda Mahaifiyarsa take ciki.
★har gari ya waye dare ya kuma sallace kawai take tashinsa ya kasa saka komai a cikinsa..
Yana zaune ya jiyo zafin takun Ɗayyib, miƙewa ya yi kafin ya shigo ɗakin ya riskesa. Domin da ga yanayin takunsa da jiyo ya fuskanci yaga abin ya ajjiye, don haka maganar ɓoye-ɓoye ya kau tsakaninsu.
ÆŠayyib ya na shigowa Sufyan ya taresa da cewa;
"Don me zaka binnemin Uwa da rai! Na ce don me zaka binne min Uwa da rai!! Ka zo ka sareni da wuƙa ne? ka sare ni nima ka binne Ni? To ka sareni mana!!!"
Sufyan yaƙarasa faɗa yana kallon cikin jajayen idanuwan Ɗayyib haɗe dukan ƙirjinsa.
Murmushi Ɗayyib ya yi yana cije haƙwaransa sai dai kafin ya zaro abinda ya yi niya Sufyan ya kai mai naushin daya sashi zubewa yana mayar da numfashi, kafin ya yunƙura ya miƙe, ihu ya karaɗe Daular gaba ɗayanta da kiran sunan Ɗayyib.
"Menene ya ke faruwa?"
WAIWAYE
Ranar da saƙon Malik ya isa ga Sufyan kafin ya shiga Yankin Tudu, A ranar Su Malik sauka baro Kahala.
Sanin hatsaniya zai iya biyo bayan zuwan Sufyan Yankin Tudu kamar yanda Sarki Hammam ya sanar mai yasa ya shirya tafiyarsa Iyakar Yankin Tudu bayan isarsa Kahala.
Malik da suka dawo Dhahab da Sulaim Bayan ya duba, Masauƙin Sulaim komai ya yi dai-dai ya miƙa masa abinci yayi sallar magrib ya kimtsa zuwa Iyakar Yankin Tudu ta ɗaya daga cikin jiragen da suke amfani da shi, sai dai da dirarsa waya ya riskesa daga Sarki Hammam Ɗayyib ya gano abinda Sufyan ya ajjiye, a wannan dare Malik da masu yi masa Hidimar sirri a Iyakar Yankunan suka isa Yankin Tudu har ɓangaren Jalal.
Da farko Jalal da ya ke kwance bai gane tsayuwar Malik ba saboda babu wadataccen haske, sai dai yankar da Malik yayiwa ƙwaurin ƙafarsa ne ya sashi miƙewa jikinsa yana rawa.
Cikin tsoro da ganin mutuwa muraran Jalal ya ce;
"wanene ya turoka? mai kake nema da n..."
Wani irin Yanka mai shiga jiki Malik ya ƙara yiwa rabin fuskar Jalal dayake kallonsa da shi ya na tambayarsa. Ihun azabar da ya amsa Masarautar ya saki yana lalube domin ko baiyi magana ba, yasan Malik ne ya riskesa.
Da ƙarfin Muryar da bai san yana da shi ba yake kiran Ɗayyib dake wajen Sufyan.
DAWOWAR LABARI
Da gudu Ɗayyib ya miƙe ya nufi Sashen Mahaifinsa Sufyan ma ya bi bayansa.
Babu wanda ya leƙa wajen Jalal saboda tsoro kowa laƙwas ya yi saboda suna kyautata zaton Malik ne ya bayyana a wajensa. Wa su dai sunyi ƙarfin halin fara neman Ɗayyib ta hanyar kiran Sunansa.
Malik tsayuwarsa ya gyara.
ÆŠayyib yana Kunno kai ya yaye mayafin fuskarsa suna kallon juna.
Cikin kuka ga jinin da ke bin jikin Jalal da har lokacin yake yashe a ƙasa a gefen Malik yake cewa;
"Ka ceceni Ɗana Ɗayyib haƙiƙa Malik ya bayyana gare ni.."
Wani irin ɗauka Malik yayiwa Jalal kamar tsumma, ya ɗaga wuƙar hannunsa ya Chaka mai a saman kafaɗarsa yana kallon tsakiyar idon Ɗayyib ta ɗan hasken da Malik ɗin ya kunna da kansa..
Ihun azaba Jalal ya saki..
Cikin kaushin Muryar dake nuna zafin kan Malik da haushinsu daya rayu da shi ya ce;
"Bayan tasha uƙubar watanni daga gareka yanzu awoyinka hamsin da huɗu da binneta, ka je ka cirota da hannunka Ɗayyib! a wanketa a kaita Maƙabarta idan ba haka ba, wallahi! Wallahi!! Sai na tafi Babban Birnin Abyad da kawunanku" Malik yaƙarasa faɗa yana murza wuƙar da bai cire ba a saman kafaɗar Jalal da azaba ya jima da sumarwa.
Tsayawa Ɗayyib ya yi yana jin kamar ya taro ƙarfin duniya a jikinsa ya kashe Malik da Sufyan nan take, amma abin taƙaicin ko Bafade ɗaya babu, kowa yana gudun ransa.
Ganin Ɗayyib ya ƙame a tsaye yasa Malik ya ce;
"Iya adadin mintocin da ka ɓata iya adadin jinin Ubanka da zai salwanta har ya rasa ransa, kaga ka rasa Shaiɗanin Uban daya horar dakai yake kan tayaka ɓarna" Malik ya ƙarasa faɗa yana watsar da Jalal a gefe..
Gane gaskiya Malik ya faÉ—a kuma babu abinda ya isa yayi mai idan Jalal ya mutu, ya sa ÆŠayyib fita da sauri, waÉ—anda suka tayasa binne Hindu ya nemo da Gatari da komai da sukayi amfani suka fasa da sauri, sai gashi sun cimma gawar Hindu da ya karaÉ—e ko ina da wani wari...
Sufyan wajen Malik ya je ya ɗurkushe ƙasa yana kuka haɗe da haɗa hannayensa da suke rawa waje ɗaya alamar godiya domin tsoron Malik ba zai barsa ya yi magana ko ya iya kallonsa ba.
Ɗayyib suna tono gawar Hindu ya komo wajen Mahaifinsa sai dai babu Malik babu Sufyan. Da sauri ya ɗaukesa zuwa cikin Mota da taimakon abokan ɓarnarsa suka nufi Asibiti da shi.
A wannan dare Sufyan ya dinga bi gidajen Dattawan Yankin yana kukan su taimakamai, tunda Malik tuni ya bar Yankin.
Jin abinda ÆŠayyib ya aikatawa Hindu ya sa suka tausaya mai, duk suka É—aure hancinansu suka dumfari gawar Hindu..
Da taimakon Matar Babban limamin Masarautar da ma'aikatan Jinya aka suturta gawar Hindu iyakar yadda zasu iya..
★washe gari Dandazon Mutanen Yankin Tudu ne suka yiwa gawar Hindu rakiya zuwa makwancinta.
Sufyan ya yi musu godiya yana kuka. Bayan ya tsaya a kabarin Mahaifiyarsa ya yi mata addu'a ko minti biyar bai ƙaraba ya koma gida ya ɗauki jakarsa da bai taɓa komai a ciki ba ya bar Yankin Tudu zuwa Babban Birnin Abyad. Tare da sawa zuciyarsa ya tafi kenan har abada.
NAILA;
Da taimakon Hadiman sashen Ummi Aysha Naila ta isa sashen Sulaim.
Ƙofar Sashen a buɗe yake don haka tana zuwa Securities suka barta ta shige.
Ƙamshin sashen da tsaftarsa yasa Naila ƙara nutsuwa. A zaune ta samesu shi yana Breakfast Ummi Aysha kuma tana danna waya.
Gaisuwar Naila kawai Ummi Aysha ta amsa da fara'a a kan fuskarta ta miƙe tana kafa waya a kunnenta alamun amsa kira.
Da harshen nasara Naila ta gaisheshi tana yin ƙasa da kanta.
Da kaa Sulaim ya amsa mata yana nuna mata gefenshi, wajen da Ummi Aysha ta tashi.
Ƙafafuwan Naila su na harɗewa ta taso ta zauna, gaba ɗaya sai take jin saman kanta kamar an ɗora mata duniya saboda girma.
Kofin hannunsa ya ajiye yana gyara zaman da ya bashi damar fuskantarta da kyau.
"Naila" ya faÉ—a yana kallonta.
Still Naila da zuciyarta take bugawa da sauri-da sauri bata É—ago ba.
"Ki É—ago ki kalleni ko zaki ganeni, tunda kin kasa tuna muryata" ya faÉ—a a hankali kamar mai tsoron magana.
A hankali Naila ta ɗago, ƙwaƙwalwarta ya shiga lissafin kyansa amma har lokacin kai tsaye ta kasa gano wani abu ɗaya na shi. Domin fuskar waccen Sulaim ɗin da ban da wannan, shi waccen aikin wuta ne sana'arsa, ga rayuwar ƙunci da kaɗaici da yakeyi saɓanin na yanzu da yake rayuwarsa cikin raɓa dare da rana, iyayensa da danginsa duk su na kewaye da shi, kowa gudun ɓacin ransa yake yi, dai-dai da muryarsa ya canza yaƙara zama mai sanyi da daɗin sauraro, irin sanyin da kuɗi da nutsuwa ne kawai suke iya samar da shi.
Ganin da gaske Nailan ta kasa tunashi sai ya ɗan motsa laɓɓansa tare da buɗe muryarsa kaɗan yadda zata ji shi da kyau..
"Yankin Tudu! Daular Sarki Hammam, sassanin wasannin ƙarshen mako, gidan Abduh Dhahab maƙerin Tukwanen ZINARE! Sulaim mai kaiki Makaranta a keke"
Sulaim yaƙarasa faɗa yana ɗage dukka girarsa murmushin yadda Naila ta zaro dukka idanunta na ƙara faɗaɗa a saman fuskarsa.
Da sauri, ƙwaƙwalwar Naila yake ƙara lissafa mata komai na fuskar Sulaim, kafin idanuwanta suyi juyewar da tayi baya zata kife ƙasa.
Da sauri ya kamota ya gyara mata kwanciya.
Bayan wani lokaci
Lokacin da Naila ta farfaÉ—o babu mutumin da ya ce mata shi Sulaim ne, sai Ummi Aysha. Da taimakon Ummi Aysha ta koma sashensu.
Tana kwance Kaka ta shigo da Dinner a hannunta, kafin ta karɓi abincin ta ce;
"Kaka da gaske ne?"
"Da gaske me? Tunda ke babu nutsuwa a lamarinki"
Kaka ta faÉ—a kamar zata kai mata dukka.
"Kaka to kiyimin bayani, ni fa gani nakeyi kamar na daina gane komai, Yasar ya taɓa faɗamin Muhammad Dhahab shine ya kafa Dhahab kuma babu wanda ya san Asalinsa amma wa su sunce ɗan asalin ƙasar Abyad ne, Ni fa kamar ma na ƙara manta fuskarsa" Naila ta faɗa da iyakar gaskiyarta.
Abincin Kaka ta dangwarar mata tana jan ƙaramin tsaki, haɗe da cewa;
"idan zaki nutsu ki nutsu domin da gaske Sulaim kika gani, idan ya shigo dubaki mutuwa zaki yi ba suma ba, tunda kuɗi da raɓa sun sa kin zama fara🦗, daga ganin mutum ya ce miki Yankin Tudu sai ki Sume, kuma a haka ki ishi mutane da daa Sulaim yana raye da shine kaza da shi zaima kaza, Ni ce ma shi ina zan kulaki na zama mai arziƙi"
Kaka taƙarasa faɗa tana taɓe baki
kafin ta bar daƙin Naila ta miƙe da sauri tana sha gabanta..
"Kaka dan Allah to kiyimin bayani, yanzu Ni ce fara🦗?" Naila ta tambaya tana marairaice fuskarta.
Domin sauƙaƙawa Naila saboda an turo neman izinin Sulaim zai shigo dubata Kaka ta zaunar da ita. Bata rage mata komai ba a labarin da Malik ya bata, sannan ta ɗora da nasihar Nailan ta kula, saboda daga yanzu komai zai iya sauyawa.
Naila bata motsa ba, a hankali komai yake warware mata, irin kuÉ—in da Malik yake kashewa da irin girman da yake ba su ashe da dalili, Dagaske kamar yadda take ji ajikinta ashe Sulaim bai mutu ba ya na raye.
Naila bata kawo zuwansa kusa ba tunda ba'a daÉ—e da yin sallar magrib ba, living room ta fito ta zauna, Kaka da bata yarda da Mai hidimar dafa abinci ba tana madafi tana shirya kayan tarbar Sulaim duk da tasan ba lallai ya ci ba.
Ana knocking Naila ta tashi da kanta ta tafi buÉ—ewa.
Tana buɗewa da fuskarsa tayi tozali babu kowa a bayansa, jikinsa sanye da kaya masu kauri baƙaƙe, sai hular sanyi mai taushin daya rufe rabin girarsa. Hannayensa zube cikin aljihun wadonsa, da alama sanyi yake ji.
kallonta Sulaim ya tsaya yi yana karantar yanayinta, ganin zasu jima a haka ba tare da ta iya cewa komai ba sai ya kamo hannunta suka dawo living room É—in tare, a gefen Couch É—in da ya zauna, ya zaunar da ita.
"Ina wuni" Naila ta faÉ—a a hankali tana kallon dogon hancinsa ta gefen fuskarsa.
Hannunta dake cikin nasa ya matse alamun ya amsa.
"Ka yi haƙuri" shima bai amsa ba still hannunta ya ƙara ɗan matsawa alamun ya ji.
Waiwayowa ya yi yana kallon fuskarta da ta sunkuyar, cikin sanyin muryar daya haɗe da zazzaɓin dayaƙi barinsa ya ce;
"Na dawo Abyad ina murnar zan ganki har ciwo nake yi amma kin ganni kin suma, kin daina son abotarmu ko?"
Naila da daÉ—i ke neman gusarwa da nutsuwa dasauri ta É—ago kanta tana girgizashi.
DaÉ—in muryarsa da yadda kai tsaye yake nuna kulawarsa akanta ya sata sakin murmushi kafin kuka mai sanyi ya biyo baya.
Yau ga ta ga Sulaim sun girma sun zama manya kuma a raye ba a mace ba.
"Na tafi bakyason ganina?" Ya tambaya kamar ba Sulaim ba.
Kai Naila ta girgiza da sauri tana ƙanƙame hannunsa.
Ƙarar faɗuwar cokalin hannun Kaka dake laɓe tana kwallon su ne, yasa Sulaim ɗan sakin murmushi, itama Naila murmushi ta saki tana dafe bakinta.
Kaka akwai son bin diddigi.
"Ki kirata mu gaisa zan tafi tunda kuka kikeyi bakyason gani na" Sulaim ya faÉ—a da wasa.
Naila da take jin kamar su dawwama a haka kai ta ƙara girgizawa da sauri.
" Kiyimin magana Naila, ki kalleni a waccen Sulaim ɗin, ba wannan ba, ( ya faɗa yana nuna ƙirjinsa) kiyimin hirar da kika saba, ki bani labari, Kinyi kuka da ake ce na Mutu?"
Ya tambaya idanuwansa na kai kawo a saman fuskarta..
Naila da daÉ—i yayiwa yawa har ta rasa wajen zuba extra kuka ta fashe da dashi mai tafe da dariya lokaci É—aya...
Barkanmu da dareðŸœ
[9/5, 8:51 PM] Maman Amatullahi: 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
ZINARE
2
BY
NAFISA ALIYU SASAAL