← Book details Zabin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 4 OF 5

INTRODUCTION

Zabin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

16 /7/2025
"When the heart chooses, even silence speaks.


Bayan sallar Ishaa, gidan ya lullube da natsuwa da sanyin dare. Safiya na gefen Mama suna gyara kwanon abincin da suka ci tuwon masara da miya kuɓewa mai ɗan yaji, wanda Amatu ke matuƙar so.

Baba na zaune a jikin kujera yana duba littafin karatun sa, zuciyarsa cikin shiru, kamar yana nazarin wani abu. Sai kawai Amatu ta fito da ƙaramar jaka daga cikin daki, ta buɗe ta fito da zunzurutun kuɗi na Naira dubu hamsin, ta miƙa masa da girmamawa da murmushin ƙauna:

“Baba, ga wannan. Dan Allah ka karɓa, nasan zaka yi amfani da shi da albarka.”


Baba ya karɓa yana kallon kuɗin da ta miƙa, sai ya ɗan jinjina kai da murmushi.

“Wannan duk name Amatu? Ina kika samo kuɗin nan haka kamar mai albarkar hatsi?”

Amatu ta ɗan yi ƙasa da murya tana murmushi cikin jin kunya:
“Nashwan ne Baba. Ya turo min a matsayin kyautar birthday. Kullum haka yake min, ba ya taɓa barin ranar ta wuce haka kawai.”

Baba ya kalli Amatu sosai, kamar yana nazarin fuskarta da zuciyarta a lokaci guda, sai ya furta:
“Ikon Allah. Shi Nashwan kam baya gajiya. Kuɗin da ya aiko miki da su, wallahi shine albashi na gaba ɗaya a wata. Na yaba da irin karamcin sa. Amma…”
ya tsaya yana jinjina kai sannan ya ce da tsantsar tausayi da damuwa:
“Sai dai me, ke Amatu... sai yaushe zai turo kansa? Ina jin tsoron kada wannan juyin zuciya ya zame miki juyin rayuwa. Idan har yana sonki da gaske, me zai hana ya taho ya gabatar da kansa? Ya zo ya gaishe mu, mu san iyayensa, su san mu? Ni nake fatan hakan... ba wai zuba ido muna jiran sakon waya da alert ba.”


Amatu ta yi shiru, zuciyarta cike da ruɗani. Tana son Nashwan fiye da kowa, amma tambayar Baba tana da nauyi har yanzu, Nashwan bai taɓa fitowa fili da maganar aure ba ya cika da kyaututtuka da kulawa, amma shiru kan abinda take mafarki da fata...

Baba ya ƙarasa da faɗar cikin murya mai sanyi:
“Na fi son yazo ya ce min da bakinsa, ‘Baba na zo neman Amatullah, ku bani dama’ — haka kawai zuciyata zata huta da murmushi.”


Amatu ta ɗan sunkuyar da kai, tana wasa da yatsun hannunta, zuciyarta na faɗin: “Ya Allah ka shiryar da Nashwan ya gane muhimmancin hakan...”


Ta koma ɗaki, lokaci ya kusa da ƙarfe goma na dare. Tana cikin shirin kwanciya, rigar bacci jikinta, fuska a gajiye amma zuciya na yawan tunani. Wayarta ta yi tsit, sai kawai ta hango missed call ɗin Nashwan har sau biyu. Ta ɗan jiyo numfashinta cikin damuwa, tana mamakin dalilin kiransa a wannan lokaci.

“Ina ma ba za’a gama da kiraye-kirayen dare ba...” Ta furta a hankali, sai kawai wayar ta ƙara ringing. Da kyar ta ɗaga, muryarta cike da gajiya da sha’awar bacci:
“Hello…”
agefe guda, muryar Nashwan ta karade kunne da sanyi da nutsuwa, kamar mai ɗauke da busar sarewa mai sanyi da tsantsar natsuwa.
“My Amatu, kin tashi lafiya? Na gaji da rana, wallahi sai yanzu nake samun kansa.”


Amatu ta lumshe ido, murya a sakakke:
“Lafiya lau, na ga missed call naka. Nayi zaton ka manta dani ne…”
ya ɗan murmura, muryarsa na ɗauke da raɗa:
“Kamar ya manta dake? Ai ke ce zuciyata. Kawai ne nayi busy sosai yau, kin san aikin nan... amma a duk inda nake, wallahi ke na ke tunani.”


Sukayi hirar da bata fi minti biyar ba, amma kamar zasu baje da soyayya. Sai Amatu ta nutsu ta faɗa masa:
“Baba ya karɓi kuɗin da ka turo, kuma ya ji daɗi sosai. Yace duk da farin ciki da jin dadin karamcin ka, yana tambaya sai yaushe zaka gabatar da kanka.”


Shiru ya biyo bayan kalmarta na ƴan dakiku. Sai daga baya Nashwan ya sauke ajiyar zuciya sannan ya furta da gaskiya:
“Soyayya ta da ke ba wasa ba ce, Amatu. Wallahi da gaske nake. Amma akwai abubuwa da nake gyarawa yanzu, sai dai insha Allahu—nan da shekara mai zuwa, zan turo iyayena. Zan zo da kaina, mu gama magana cikin mutunci.”


Zuciyar Amatu ta cika da farin ciki da fargaba a lokaci guda. Shekara guda? Haka za ta jira? Amma a lokaci guda, ta ji kwanciyar hankali da yadda ya furta kalmomin, ba da wasar magana ba, ba da ɗoki na banza ba. Da karamin murmushi ta ce:
“Na yarda. Na karɓa. In Allah ya yarda, zan jira har sai lokacin nan.” Nashwan ya ce da ƙayatarwa:
“Kuma har lokacin nan, soyayyata ba zata gushe ba. Na fi ƙaunar ki fiye da na kaina, Amatu.” ta saki ajiyar zuciya, murya a raɗa:
“Ni ma ina son ka Nashwan... fiye da yanda zan iya faɗi.”


Wayar ta kashe ne da salati da addu’a daga gare shi. Ta zuba wayar a gefe, ta lumshe ido da murmushi a fuska. Zuciyarta ta nitsar da wani irin sanyi — sanyi mai ɗauke da fata, ƙauna da alkawarin gobe...


Washegari...

Tun karfe bakwai da rabi Amatullah ta tashi, jikinta na da sauƙi, zuciyarta cike da kwanciyar hankali da farin ciki na soyayya. Tana gab da isa bakin titi sai Habibu ya zo kamar yadda ya saba da napep nasa. Ta shiga ba tare da wata damuwa ba, amma a zuciyarta tana jin sanyi... Nashwan dai ya saka haske a rayuwarta.

Da suka isa asibiti, ta faɗa Layla rai a ɗumɗum. Bayan sun gama shiryawa a office, suna cikin sassanyar rana, suka zauna a gefen taga suna ɗan hutawa kafin fara aikin rana. Layla ta lura da murmushin Amatu, da wata annuri a fuskarta da ba kasafai ake gani ba.
“A’ah ke dai yau kamar an baki labari mai daɗi. Me ke faruwa ne da wannan murmushin sirri?” Layla ta tambaya tana ƙara matsowa kusa da ita.


Amatu ta lumshe ido tana ɗan kallon taga, sai ta juya da ɗan shafa sumar kanta tace:
“Layla... Nashwan zai turo iyayensa — amma ba yanzu ba, sai shekara mai zuwa.”

Layla ta zaro ido, ta rike hannunta cike da sha’awa da farin ciki:
“Shekara mai zuwa?! Subhanallah, ke wallahi wannan albishir ne! me kika ce masa?”
“Na ce zan jira shi duk da lokacin yana da nisa, amma kalmarsa ta daɗe da natsuwar sa sun saka na yarda. Soyayyarsa ta fi ni’imtar zuciyata.”


Layla ta fashe da dariya tana girgiza kai:
“Ke dai kina cikin naki duniya Amatu, Allah ya tabbatar da alkhairi. Wallahi Nashwan yana da kirki. Amma dan Allah... wato bazai yi tun da wuri ba kenan?”


Amatu ta nisa “Yace yana gyara wasu abubuwa ne. Na fahimta kuma na yarda. Na fi son abu ya zo da tsari da cikar mutunci fiye da sauri ba tare da shiri ba.”
Layla ta jinjina kai, tana murmushi:
“Toh ai Allah ya sanya alkhairi. Amma sai ki shirya kyau-kyau da addu’a. Zaman jira yana buƙatar haƙuri da jajircewa.”
“Na shirya,” Amatu ta amsa a hankali, “In har zan samu Nashwan a ƙarshen jirana — to na yarda da komai.”


Suka ci gaba da hira cikin nutsuwa da kwanciyar rai. Soyayya ta gaske ke kera zuciyar Amatu, tana girgiza tunaninta da fatan gobe. Kuma da ƙawarta Layla a gefenta, sai ta ji kamar rayuwar ta na gyarowa cikin salo mai tsafta da albarka...


SHIN WANAN JIRAR NA AMATULLAH ZAI HAIFAR DA ƊA MAI IDO
SHIN NASHWAN ZAI CIKA ALƘAWARIN SA.

LALLAI NASHWAN SHINE ZAƁIN ZUCIYA AMATULLAH
MUCEE GABA DA KASANTUWA ANA MIN UZURI DA RASHIN ISASSHEN POSTING A KOYAUSHE FATAN ALHERI 🥳🎊


https://chat.whatsapp.com/Iw0DqQGrB3UJg7MK20pgRC


💘 ZAƁIN ZUCIYA💔
THE HEART'S CHOICE

BY
NARNAH ƘANWAR SOJA


🎉 Happy Birthday to Me
July Girl Special 🎂✨

Na sadaukar da wanan littafin wa karan kaina kasancewar sa a watan haihuwa ta July..

Welcome to this journey... of love, of longing, of silence that speaks louder than words.
Let the novel begin... with a heartbeat. 💔💌
Love , Sad × Long-Distance × Hopeful * short story


DIAMOND 💎 GLOW PEN'S TEAM


PAGE 7 & 8


best on true life story
Chapter 4 · 0% Book details