← Book details Zabin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 1 OF 5

INTRODUCTION

Zabin Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

"When the heart chooses, even silence speaks.
And when love travels far, memories walk back home."
a cikin rayuwa, wasu soyayya na zuwa da sauƙi – kamar iska da ke busowa daga arewa; wasu kuma na zo da wuya – kamar ambaliya da ta hana ruwa kwarara.
Wannan littafi, ZAƁIN ZUCIYA, ba kawai labari ba ne — wata zuciya ce da ta zaɓa ta ƙi mantuwa, ko da nisan da ya zo, ko da shiru ne ya maye gurbin saƙo.

It's a story of distance and nearness of souls.
a tale of rauni, of waiting, and of choosing again and again a wannan littafi:

Zamu haɗu da zuciyar da ta kasa mantawa da wanda ta zaɓa

Zamu shiga duniyar da soyayya ke jure nesa, jure sabani, kuma tana da ƙaƙƙarfan fata

Zamu fahimci cewa ba kowanne zaɓi ne mai sauƙi ba, amma wasu zaɓuɓɓuka na zuciya ba su da musanya


🎉 Happy Birthday to Me
July Girl Special 🎂✨

Wannan novel an rubuta shi ne a matsayin kyauta na musamman ga kaina — a matsayin wata ƙauna da nake yarda da ita, ko da kuwa ta zo da ciwo.

Na zaɓi na baku labarin zuciya
Na zaɓi in ba zuciya murya.
Na zaɓi “ZAƁIN ZUCIYA” – saboda ba kowa ke fahimtar irin zaɓin da zuciya ke yi ba, sai wacce ta taɓa ƙauna da rauni.

Welcome to this journey... of love, of longing, of silence that speaks louder than words.
Let the novel begin... with a heartbeat. 💔💌


**************""""""""""""""""""

A RAINY NIGHT IN JULY

“Some hearts don’t forget – they just grow quiet.”

Ƙarar ruwan sama ne ke bugun tagar ɗakin, kamar yana son shiga don ya ce mata: "Ina jin zafin ki."
Ɗakin ba mai fadi bane, amma cike da natsuwa tagar gidan karama ne, amma tsafta da kamshi na lavender ya karade ko ina.
An shimfiɗa farin farar bed sheet, wani dogon hula mai launin kore a gefe, da na'urar wayarta a gefen pillow – sai hasken screen ɗin da ke yawo da sunansa: Best Choice "Still Online..."

A gefen mirror ɗin da ke bango, tana zaune –
Ƴar shekara 21 amma idanunta na ɗauke da sirrin shekaru goma sha biyar da suka shude.
Black beauty ce – fari ba sosai, amma fata ce mai ɗaukar haske.
Lips ɗinta kamar rubutattun baitai – thin and sweetly dark, kamar an zana.
Idanunta manya, dogaye, masu cike da tambayoyi da sirri.
Gashin kanta yana da tsawo, sai dai ta na yawan ɗaure shi da bun ko kuma ta ɗaure da kyalle mai soft floral prints.

“Why am I the one still waiting?” ta furta a hankali, kamar tana tambayar tagar, ko wataƙila zuciyarta ce.
Sunan ta Ammatullah ba don suna yana da kyau ba kawai, sai don yana da ma’ana:
wacce take ba da zuciya gaba ɗaya idan ta ƙauna.


Ba ƙaramin so ta yi masa ba – saurayin da zuciyarta ta zaɓa.
kuma yanzu, a cikin watan da aka haife ta, watan da duniya ke yi mata barka, ita kuma tana jin komai yayi shiru amman ko magana bai mata ba duk da yasan wanan muhimmancin rana a garita .
Shiru mai nauyi, shiru mai wuyar fassara.


She wiped a few stubborn tears that escaped her eyes,
but her chest… it was a battlefield.
A war between silence and screams.
Suddenly, her body gave in —
her knees curled to her chest as she collapsed on the bed,
Hannu biyu biyu tasa ta toshi bakin ta tana ihu kamar ana tsibtar da ita da wuka tana amballiyar jini ..


Ammatullah burst into tears.
Not the soft sobs of a broken girl…
But the deep, painful cries of someone who had lost her future —
because to her, Nashwan was everything.

“Why…? Why me?” ta furta da raɗa, cikin kuka mai kauri da tsananin ciwo.
“Ya za a yi ace ni ce nake ƙauna da gaske,
but he’s the one who moved on so fast?”


“Na rasa komai…” ta furta a hankali, kamar tana magana da numfashin zuciyarta.
“Shine farkon zaɓina, kuma shi ɗaya ne nake so…”
tasa hannun ta a kirjinta kamar zata turo numfashin ta cikin ta.
Zuciyarta na fizgewa da ciwon da ba a ganinsa, sai dai a ji shi.
“Shi ya kamata ya tuna ni yau…” ta ce, hawaye na gangarowa.
“…amma sai yau ne ya zabi ya manta da ni.”


Wayar ta zame daga hannunta ta faɗi ƙasa.
Zuciyarta na ta kai da kawowa, tsakanin mantawa da tunawa, tsakanin fata da fargaba.
Tsakar dare, a cikin daki mai shiru, zaɓin zuciyarta ya ci gaba da hukunta ta.
“Some wounds don't bleed, they echo in silence.”

“He was my first love…”
Zuciyarta ta furta kamar wata ƙaramar murya daga ciki.
“…and he left me with a silence that screams louder than his goodbye.”
tana jin zuciyarta na fizgewa da dukan da ba ta da ƙarfi akai.
Tana jin kowane message notification kamar fata, ana wishing nata happy birthday
amma ba shi bane.
Sai take jin kamar duniya gaba ɗaya ta barta —
a ranar da ita ce birthday month ɗinta, Nashwan ya zabi ya manta da ita.

Bacci mai wahala ne ya kwashe ta,
idanunta cike da hawaye, zuciyarta a hargitse.
Ba wai saboda ba ta so ta manta dashi ba,
amma saboda zuciyarta ta zaɓa shi – kuma zuciyar tana da taurin kai fiye da kwakwalwa.

"First love never leaves… it just buries itself deeper."


Narnah ƙanwar soja ✍️


https://chat.whatsapp.com/Iw0DqQGrB3UJg7MK20pgRC


💘 ZAƁIN ZUCIYA💔
THE HEART'S CHOICE

BY
NARNAH ƘANWAR SOJA

Birthday Gift Novel by Sayeedan Adda
July queen Leo 🌙
Love , Sad × Long-Distance × Hopeful * short story


DIAMOND 💎 GLOW PEN'S TEAM


PAGE 2
best on true life story
Chapter 1 · 0% Book details