Sashe 4
Yar Goggo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
, bayan ko wane karshen wata ina sawa acire buhu hamsin na kowane kayan itatuwa arabawa bayi da kuma mutan gari to ina ake kaiwa ?????? Yarima yace baba karka yadda da ita tayo karya take , dan na fuskanci batada cikakkiyar lfy . Nace tab lafiya ta lau gaskiyar kawai na fada . Jikin sarki yayi sanyi tabbass ana ha'inci amman zaisa ido . Yace ke ƴar wacce unguwar anan kauyen? Nace ina layin Sabuwar namba . Yace wa fadawa su debo min duk wani iya_iyan itatuwan da yakenan asamin a buhu arakani gida dan yamma tafara . Sukace angama sarki . Haka akayi kuwa har gida suka kawo ni duk da magrib ya gabato amman layinmu cike yake da mutane dankuwa sunji labari wai sarki ya kama deejee ankaini an kulle !!!! Sai ko gani da fadawa har kofar gida aka ajiye min sukayi tafiyarsu . Na kwallawa Gwaggo kira tafito duk tashiga tashin hankali, tace deejee kece anan nawuni kuka nayi tunanin sun kasheki gashi badaman zuwa, Gwaggo harda kwalla !!!! Wani dariya na kece dashi nace kai Gwaggo mutuwa kuma ai da saurana dubi kiga ƴar yarinya dani , kingafa abinda sarki yaban . Gwoggo ta ce sarki usmanu ne yabaki deejee? Nace eh fah harda fadawansa suka rakoni . Yan gulmako sai zuwa suke wai ah deejee ta dawo innabasu lbr abinda yafaru sai su tsoke baki , zeenatu ma sunzo mukasha dariya abinmu nace musu kai wani nagani wai shi yarima wlh kamar balarabi sai shegen mugunta , sukayi ta dariya har suka tafi ... ! Ina kwance da daddare kawai nayi mafarki ga wannan karnukan lambun mai gari sunyo kaina wani ihu na kurma ! Agigice na farka na lallbo na kwanta kusa da Gwaggo, ashe dai tana jina tace"" deejee yakamata yanzu kinutsu ita wannan rayuwar asannu ake binta kuma bakisan watarana a hannun wa danda zaki faɗa ba tayo ki faɗa a hannun muggan mutane , zasu iya cutar da ke . Nace Gwaggo ba abinda zaifaru amman bazan sakeyi ba .bayan sati da faruwar haka sarki ya aiko da kayan lambu arabawa kowa kuma abi har cikin gida araba . Mutane sai sa masa albarka suke kuma har gida akazo ana jinjina min wai nayi kokari . Haka dai rayuwa taci gaba komai yayi farko yana da karshe munkammala primary school namu akaturamu Junior secondary School acen birni makarantar kwanace da gangan headmaster yayi haka !kasa muka duka muna bashi hakuri ya janye amman fir yaki sauraronmu . Ina kuka na iso gida na zube agaban Gwaggo inata zabga kuka harda burgima sai tambayata take amman naki shuru ballantana na bata amsa sai da tadau bulala na yi shuru na koramata bayani aiko tafini shiga tashin hankali, tace """ wai shi shugaban makarantar taku anya baya shaye shaye !! Ta yaya zai dau yarinya danya kamar haka ya kaita birnin kuma makarantar kwana ai bazata sakuba !! "" Bindiga a ruwa gobe zani wajensa sai ya jenye zacennan Washe gari sai ga Gwoggo a makarantar su deejee har office na head master ta shiga , tace hedmasti wato wai sotake tace ( headmaster) kaiko me jikata tayi wanda yasa kayanke mata hukunci haka har gidan yari na shekara uku . Headmaster cikin soro da mamaki yace hala dai baki fahimci inda kike ba koh to nan makaranta tace ba office na yansanda ba ne . Tace eh nasani amman abinda kake shirya yinsa tamkar a offishin iyan sanda ne ..!! Yarasa abin fada kawai yayi shuru . Tace ya kai shuru ? Aransa yace this old woman she always disturb me ... Yayi ajiyar zuciya yace ummm mama what I mean wannan cigabane yazowa dalibanmu , a da makarantar wuni akeyi kuma hakan takurace ga dalibai saboda bamuna secondary School anan sai anje birni , ganesa ga kashe kudin mota shine gomnati ta taimaka akayi makarantar kwana ka ita ta dauki duk nawinsu ba abinda zaki siya komai ta tanadeshi harda gurin kwana kuma kowa da katifarsa sannan bangaren abinci , ana dafamusu sau biyu a rana kuma duk da haka ko wane karshen mako gomnati zata dinga kamusu abin makulashe da dai sauransu.... !!!! Cikin jin farin cikin zancensa Gwaggo ta washe baki tace hedmasti har da kati fa kace dai jikata ta huta abinta . She dai headmaster dariyar kawai yakema sai sambutu take .... Yace nan da sati biyu zasu tafi anan makarantar zasu hadu da sauran daliban dankuwa motace zatazo ta kwashesu . Dajin haka Gwaggo tayo gida cikin jin dadi... ... Ina kwance naji Gwaggo na kwallamin kira nafito na taddata azaune akan taburma tana dama fura tana cewa kaiii madallah . Nace Gwaggo incedai ya hakura da zancen tafiya karatu birni ? Tace a'a deejee tafiya ai tazama dole danko abin daga gwamnati ne ba daga shiba .... Ta kwashe duk yadda sukayi da headmaster ta fadawa deejee duk da haka deejee batayi wani farin ciki ba dan bataso tayi nesa da Gwoggo dan babu mai taimaka mata tace shikenan tunda haka abin yake.... Gwoggo tazubamin damammiyar fura nafarasha ina santi ... !!!!! Ana washegari su deejee zasu je birni ! Gwoggo taje kasuwa ta sayo dutsen goge kaushe da wata sabulu HALA SOAP ita wannan hala soap a KUKAWA amarene maso anfani da ita dun suyi kyau wato dai ita HALAN . Acwar Gwaggo kar gomnati ta gane mata deejee da dauɗa ta koraota! Aiko su deejee anyi awa uku ana goge kafa !! Gwoggo na saye akanta tana gani intakamama ta tayata ! Saida kafar tayi wani ja dan durza sannan aka kyaleta. Gwoggo tace to sai kuma wanka ki tabbata kinyi da kyau ! Awankanma anyi kusa awa 2 harda omo akayi wankan da tayi kyau ... Tunda deejee tafito Gwaggo tazuba mata idanuwa tana tuna abunda yafaru shekaru goma sha 12;da suka shuɗe !! Irin mummunar ta addin da akaso aikatawa ... Wasu kwallane suka ciga idon Gwoggo! Deejee tace lfy kuwa Gwaggo kamar kwalla kike shirin zubdawa ko dai tafiya ce baki so ? Gwoggo tayi murmushi tana karewa jikar tata kallo tayi wani haske da tayi wankan Amare dama deejee farace kal , tana da dan sawo bata da jiki , gashi kam har yaimata yawa duk da ba wani samun gyara ake ba , hancinnan kamar zai shige baka ! Gwoggo tace kawai dai mamaki nake ashe dai deejee tawa kyakkyawace... Deejee sabar dariya da jin dadi ta kusa faduwa kasa . Tace kai Gwaggo ai wannan sabulunce da omo yasa nayi haske .. wasu kayantan ta nasallah tasaka acewarta daga gobe na daina sanyaku , har bacci ya dauketa . !!! Gari yana wayewa ko karin kummallo basu saya yiba sukai gidansu zeenatu dan suwuce har makaranta Gwoggo ta rakota tananan saye sai da taga tashin motarsu kamin ta koma gida ! Gwoggo har da zubda kwalla gani take anrabata da deejee. !!!!! Nima ( Sayyada) harda iyar kwallata narasa wazabi deejee ko Gwaggo!!! Kai garadai nabi deejee birni , wata mota nagani irin na masu saidai itace na haura😄 nace mubi bayan motarsu deeje dankar suɓacemin da gani mukayo birnin amman kashh na nemi motarsu DEEJEE na rasa sana diyar wata motar da tayo kanmu kamar zata bigemu ta wuce nace kai mubi waccan motor sai naga waye aciki🤔. BIRNI Dai dan wani katafaren shop motar tasaya !!!! Wani hadadɗen saurayi nagani wanda bai wuce 27yrs ba yafito daga mota farine kal , da wani kwantaccen gashi kansa kamarna larabawa yana da sawo bashi da kiɓa , sanye yake da wata shadda kana ganinta kasan ta taci NAIRA dankin have jampa akayi wani farin glass ne a idonsa , daga gani dai kasan wannan daga cikin daula yafito .mabiya bayansa nagani sunshige cikin shop din suka sanar Ga YARIMA MAHEER yashigo kowa yafita zaiyi siyayya!!! Bai fi mintina ba sai naga kowa fitowa yake jiki na kyarma akasaya daga gefe ... Sannan yafara takunsa cikin izza da takama dan MAHEER akwai ji da kai baison raini ..... Yashiga shop din sai da yagama siyayyar yafito kaminnan naga mutanen da suke waje suka fara kusa kai cikin shop din dan su kammala nasu siyayyar. Inanan MAHEER yaja motarsa da masu mara masa baya sukabar haraban wajen ... ( Nace tab baza abarni abayaba sai naga ina MAHEER zaije sannan dan wani hamshakin mai kudine haka . Wani dan sahu na hau nafara binsu MAHEER abaya......) To kuma kubiyoni danjin wai maike faruwane abirni sannan waye wannan MAHEER din da alamu dan masu fada ajine tunda har zai iya fidda wasu yayi uzurinsa. REST HOUSE nasa yawuce yana shigowa kai saye dakinsa yawuce ya tadda ta akwance da ita sai wani have_vest da gajeren wando iya cinya bai kulata ba yayi toilet ya wasa ruwa, yafito daure da towel a kugu da wani ƙaramin ahannunsa yana goge jikinsa da shi tasowa tayi cikin tata salon ya rungume sa ta baya , cikin hanzari ya da katar da ita yace bana sallameki ba ! Mesa baki tafi ba cikin cool voice yake maga danshi baya son hayaniya..... Tace I need.... Yadakatar da ita dacewa get out kinsan ni bana sex sai romance So is better for you ki tafi sai na nemeki . Sayawa tayi tana kallonsa da kananun idanuwanta wanda suka cika da sha'awar sa tarasa yadda zatayi kuma tasan halinsa abinda take nema bazata samuba . Yakammala shirinsa yajefa mata bounch na kudi yace kada na sake kallonki ! Tadau kayanta tamaidasu jikinta tai gaba . Waya yadauka yace kashigomin da ita ... Wata kyakkyawar budurwa akashigo da ita yasaya yana kare mata kallo "" cikin soro tace dan Allah kabarni intafi "" taku yayi a hankali har zuwa kusa da ita yace na kiraki shene kika gudu amman danasa yarana suka daukoki ta karfi shine zaki ban hakuri to kisani sai nagama duk abinda zanyi zaki tafi inkuma bansami yadda nakeso ba anan zaki kwana "" jikinta yafara kƴarma cikin e"e"na tace ka...kaaa rufamin asiri wlh bansani bane na hankadeka kamin rai .... Sai ta fara kuka "" cikin Cool voice nashi yayi murmushi irinma mugunta yace kina tunanin zan kyaleki ne ? Gyallenta ya zame daga jikinta yafara shafa gashin kanta yace ummm you