← Book details Yar Goggo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 6

Sashe 3

Yar Goggo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sirfa bala'i tana ina kuke masu gida da asali ! Mahaifiyar Bello ce ta leko sakar gida tace Gwaggo ne kishigo daga ciki mana kya saya arana !! Gwaggo tace ai nazama ya kawoni ba ina wannan dan naki maikama da inyamuri to wlh ki shaida masa yafita a sabgar jikata inbahaka ba to kararsa zankai ga hukuma !! Allah sarki madam balki tace sai hakuri wo i told this boy not to go carry rigima for me wo Bello zakazo kasameni !!! Aiko Gwaggo tace ninake kariya ( carry) wato bello ne mai gaskiya dan banyi boko ba ( boy ) to wlh ahir dinko nafi karfinku nima jikata ai ƴar boko ce !! """ Madam balki tace NO what I mean kiyi hakuri nazai sake ba , !! Sai ga Bello ya shigo gida yana WHAT IS going on .... Chakkk ya dakata da ganin kakar DEEJEE!! "" Tace nine goni kon ( going on) to wlh tafadi akanka mara mutunci . Mahaifiyar sa tace yabawa Gwaggo hakuri""' yace I'm so sorry Gwaggo tare da rike kunnuwansa . Aiko Gwaggo tasake fusata tace saurayi ( sorry) kuma kul kai ba saurayin jikata nace ko tarasa mujin aure bazata aure kaba . Tashin hankali sun fahimci suhuwar abirkice take bazata fahimce su ba suka fara lallabata ! Da kyar ta tafi tana tafe sai surfa bala'i take har ta iso gida . Inanan zaune ina jiran dawowar Gwaggo inji ya akayi sai ko tashi go ke!!!! Deejee zonan !! Cikin hanzari na iso wajenta ta min wani wawan rankwashi aka wanda yasani kara tare da rike wajen tace ƴar kwal'uba ni zaki maida sakariya ashe soyayya kuke da Bello wai daga zuwansa yace wai ni goni kon ( going on) kuma shi saurayinkine ( sorry) !!! Cikin bakin ciki nace Aradu Gwaggo karya yakemin ni ba saurayina bane sharri ne !!! Kuma sai na mai rashin mutunci . Gwaggo najin nace zanmai rashin mutunci tasan zan aikata tace yauwa DEEJEE "" kintabbata babu wata alakar soyayya ko "" nace eh "", tace to magana ta wuce daura mana tukunyar abinci !! Kidafa mana miyar bushashshiyar kubewa dan Allah tayi dadi irin na rannan .... Nace to Gwaggo fuskata a daure dan har yanzu ban huce ba har sai na zazzagawa Bello rashin mutunci Ni zaice muna soyayya wato hadani da kakata zaiyi na hura wuta nafara girki !!!!! Gwaggo sai cewa take bi ahankali karki ƙone dan takula a daddafe nake girkin har na kammala ina zancen zuci ! Na kagu gobe tayi insami zeenatu infada mata abinda Bello yamin . Ina tashi da safe nayi sallah danko Gwaggo bata tashina wai ai sallah bata hau kaina ba dudu du shekaruna Goma sha daya ne fah ake wannan badakalar . Dumamen da Gwaggo ta ajiyemin ne nagani nace nawasa ruwa nasa uniform na makaranta nabiya na amshi ƙosai da kudin mota nayi gidansu zeenatu. Ina zuwa ko nafara bata lbr abinda yafaru tace "" kina nufin yaci buluss"" nace wlh bai isa ba sai naga wanda zai kwace sa daga tuggun deejee!!! Sukayi dariya suka tafa zeenatu tace kedai muje makaranta kamin sajen Musa ya laka da mana na jaki .... Da sauri suka fito daga gida sukayi wajen BUS Ashe ba agama hallaruwa ba mukane sit muka zauna , Fauziyya ce ke harararmu mukam ko kallo bata ishemu ba dan bamu da lokacin ta mu yau da Bello muke .... Muna isowa makaranta mukayi aji uncle sani ne a aji yace yau ma kunyi late wai ku bakwa tashi daga bacci ne dawuri .. yace oya ON YOUR KNEELS muka fara zuru zuru da idanuwa dan bamu fahimci mai yake nufi ba bulala ya anso a hannun MONITOR yafara zabga mana yace dakikai ku rage sawo nace kunwani sayamin akai sai kace andasa ece .... Aikuwa ranan munci duka nacewa zeenatu wlh makarantar ALLO zan koma Ga karatu ga lada amman boko fah sai cin zali dubi uncle sani da katon kai ga sawo dama ance duk dogon mutum hankalinsa a gwaiwa yake muka fara dariya kasakasa .... Yace Au kunma maidani mahaukaci Khadijah Ibrahim and zeenatu Ismail get up kubiyoni , ... Biyoshi mukayi bayan aji yakaimu akwai wani bola mai uban doyi wai mu kwashe nace Alkur'an bazan kwasheba haka kurum cutar ta kamani sai dai akoran yace haka kikace to yauko zakibar makarantar nan office ya nufa yasanar da headmaster .... Sai da yayi ajiyar zuciya yace na gaji da case din deejee nakore ta yafi akirga BUT her grandmother tabani tausayi she explained everything for me wai marainiya ce in aka koreta abun sai yayi yawa .... Daman ba karatun takesoba ... Ya aika muzo muna zuwa muka durkusa har kasa muka gaidashi ... Yace Khadijah Ibrahim and your friend I'm tired with your Case but zandau kwakkwaran mataki akanku , go to your class.. ya zaunar da uncle sani yamishi bayanin komai yanuna masa they're villages, so they need our help!! Yanzu muna korinsu kaga bamu cimma abinda mukeso ba kakara hakuri Sani ninasan matakin da zandauka ..... Muna shigowa aji ana buga bell antashi ba abinda mukayi sai punishment yau jiki yayi tsami !!! Muna dawowa gida nasha magani na kwanta sai bayan la'asar natashi liyin su Bello naje akacemin yatafi bautar ƙasa cikin jin ba dadi nadawo gida . Muna tafe muna hira ni da su zeenatu da Maryam da Abida , muntashi daga bakin rafi daman nan mukezuwa muyi wanki a ranakunda bamu da makaranta , yunwa mukeji sosai nace zeenatu yunwa nakeji itama hakan tace takeji ... Wata gonar gyada muka gani muka shiga muka fara cira muna ci , nace kai wlh danyar geɗa da dadi take , zeenatu tace aikyace da dadi tunda ansamin nabanza , nace kijita anida tasa munjaye dai munsami na banza, aiko mukashi yin dariya, har mai gonar yajiyomo , wata ƙatuwar itce yadauko yayo kanmu da gudu muka bar gonar muka kwashi kayanda muka wanke mukai gaba , sai surfa bala'i yakeyi yana zanyi maganinku marasa hankali . Wani babban lambu muka hango wanda yaji kayan ita tuwa , wani nunannem mangoro na nani har yayiwani ja dashi ,nace wai yau sai naci wancan mangoro ko mai zai faru sai dai yafaru , maryam tace kul deejee wlh kina shiga yau sai yadda akayi dake , kinmanta wannan lambun na mai garine fa , nace sai me su sunkoshi sunbarmu da yunwa wlh cira zanyi insun kamani suyanka , suma sukace to mushiga . Kayan wankin muka ajiye daga gefe , daman wani wando burgujeje da riga kamar mutum biyu su shiga nasaka dawani hijabina duk ya fara fita hayyacinsa nasaka , hijabin nacire na daura damara dashi na nannede kafar wondo da ta hanu na haura saman ginin na fada ciki ina murnan naci nasara , nace sujirani ta waje zan dinga jeho musu idan na sinko aiko ina sinkowa kuma ina jefa musu sukuma a kan kayan wankinmu suke Tarawa , banga kowa ba acikin wajen dan haka na haura wani katon itacen mangoro nadinga jidowa ina jeho musu kawai na wullo wani katon mangoro kan wani bafade jikake kauuuu ! Sunzo wucewa tacikin wajen dan suna danjin alamun motsin . wai kara yasa dankuwa sai da yayi wani super ya diro ta baya !! Dariya na kyalkele da shi , dan kuwa har sunso sujini , dayan bafaden yace kaii Alqur'an kabugu daman nafada maka akwai aljanu akan bishiyoyi nnan , yace aradu nabugu wannan jifar na mutanen boyene , ya taimaka masa sukayi waje .... Sai da nat sinka iya wanda zai ishemu nafara kokarin saukowa , wasu manya manyan karnuka nagani masu gashi sai wani gurnani suke , haba da sauri na koma daga sama !aiko sunajin motsina suka fara haushi , nawani kurma ihu dango dayan karan yayi wani salle da kadan yakamo kafata yadiro dani kasa , sai ga fadawan sarki suka shigo , suna duddubawa hangoni sukayi asaman bishiya duk na rude , sukace kaiii aljana da rana saka !!! Lallai yau munyi gamo aiko da gudu suka ruga sukayi gidan sarki , suka sanar da sarki wai sun kama aljana!!! Abunka da 'yan kauye sai gasu acikin lambur da sarki da dansa yarima wai sunzo ganin aljana. Ina makale asama , su zeenatu ko tun yaushe suka ari na kare sukayi gida . Yarima Abdallah yace ke aljana mai bayyanuwa da rana mai sa kika zabi zuwa anan amasayin maboya , to kisani yau ni dan sarki yarima Abdallah sai na kasheki !!! Wani uban ihu na daka danaga ansaitamin takobi dai dai kaina , nafado daga saman bishiyar ina 'yan uwan bil adama wlh ni mutum ce kumin rai Gwaggo batasan nazo nan ba ,har kasa na durkusa. SARKI yace ku dakata gaskiya ne ba aljana bace kunganta nan . Yarima cikin izza da mulki yace to uban wa yashigo dake tanan kuma ta ina kikabi kika shigo ???? Duk da naji ya ambaci uba sai naji soronsa yafita araina nace , kul Yarima akan mongoro zaka zagi ubana mai yamaka ?? Yace eh lallai mutum ce yayi wani sayuwa ya wankeni da mari ..... Na fadi akasa yace kafff kauyennan har akwai wanda zanmai magana ya maidamin .... FADAWA sukace hattara dai yarinya . Sarki ya dakatar da yarima yace ke maisa kika shigo nan ko dai abinki ne yafado kika biyo ki dauka . Nace karya haramun wlh ba ko daya yunwa nakeji kuma naga kafin naje gida zan iya galabaita shine na hau ta wannan garun na diro dan insaka abakin salati .wani kakkarfar ajiyar zuciya sarki yayi yana mamakin yarinyar . Yarima Abdallah yace nayi tunani ba a hayyacinki kika shigo ba ashe dai mahaukaciya ce .....!!! Nace Ni ba mahaukaciya bace rasssss nake da hankali na gani nayi kun ajiye ku baku ci ba mu bakubamu ba , ga mabukata na so wasu su kwana da yunwa amman ku ko ajikinku . Yasake yunkurowa zai sake marina .... Sarki ya da katar dashi ta hanyar daga mai hannu. Cikin bakin ciki ya saya yana kallona kamar ya shakoni .... Sarki yace kintabbata cewa mutan gari suna son abinda muka shuka amman basuda hali cira shine suka hakura
Chapter 3 · 0% Book details