BABI NA SHA TAKWAS.
Uwa Uwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 54 min read
Duk kokarinsa babu abin da Abbati ya iya karantowa a fuskar Farha. Abu daya kacal ya lura dashi. Wannan annurin na fuskarta yayinda take gaisawa da Baaba Mari ya dauke. Banda shi da ya san da zamansa ma babu wanda zai lura da cewa yanzu ta koma kadaran kadahan. Babu alamun bakinciki ko fushi, babu alamar tambaya ko neman karin bayani. Irin abin nan ne kawai da mutum zai iya dangantawa da dauke wuta. Iya nacinsa na takaitaccen lokaci ya yi domin ta kalli inda yake amma kamar tana sane ta fuskanci wadda yake tunanin ita ma kanwarta ce tana yi mata magana. Fita ya yi jikinsa kamar anyi masa duka ya tsaya a jikin motar ya kira Munzali.
Yana zaune baki bude yana ganin ikon Allah. Fruits Mama Nasima ta yanko masa ta kuma tura Mardiyya yi masa girki. Ya rage su biyu a falon ta zauna a kujerar dake fuskantar shi jikinta babu lullubi har lokacin sai farincikinta da yaki boyuwa.
"Wato kuna ta shan soyayya ban sani ba. Gashi kun dace. M da M. Zai yi kyau kuwa a soveniya (souvenir) da katin biki. Irin a saka katuwar M daya sai a jona karashen sunayenku." 'Yar damuwa ya gani a fuskarta ta ce wai yaushe za ka turo ne? Kai ba yaro baq. A shekarun nan naka kana bukatar iyali domin cikar kamala. Bana so ka sami shakku a zuciyarka game da Mardiyya. Na horata sosai da aikin gida. Ko kusa ban sangarta ta ba don ita kadai gareni. Girki, tsafta, kwalliya duka ta kware. Kuma ina da yakinin sauran mu'amala ma ba za ta bani kunya ba. Tun tana da kananun shekaru nake gyara abata." Ta kare magana tana dage masa gira gami da guntuwar dariyar shakiyanci.
Ita ke magana shi ne da kunya. Da za ace masa akwai ranar dai zai so kasa ta bude ya shige ciki don kunya tsaf zai karyata harda rantsuwa ma. Sai gashi a bagas ya gamu da gamonsa.
"Ahhhhhh. Wayyoooo. Cikinaaaa"
Mardiyya ta kwala ihu iya karfinta bayan ta fahimci wace irin hira Mamanta ta dauko. Haka kawai ta matso jikin kofa da taji ana ambaton kwalliya. Sai gata tana zazzare idanu da jin abin da Mama Nasima ke fada. Kunya ta kama ta sai dai babu muhallin biye mata. Idan bata dakatar da hirar nan ba to gaskiya bata san inda za ta tsaya ba. Ita shaida ce kakarta Gwaggo Ladidi ma idan suna wata hirar da 'ya'yanta mata sai ka nemi gudu. Ido ne ya bude tun da jajayen sawu ga rashin ilimin kirki. Sai suyi ta tafka rashin kunyarsu a tunaninsu wayewa ce.
Tare da Mama Nasiman suka isa kitchen din, don yadda tayi karar dole mutum ya firgita. Shame-shame suka sameta a kasa.
"Mardiyya lafiya? Me ya sami cikin naki?"
Mama Nasima ke tambayarta cikin tashin hankali. Ta dago kanta ta dora a cinya tana salati. Ita kuwa Mardiyya ta cigaba da murkususu tana nuna ciki.
"Mama ciwon cikina ne ya tashi."
Mama Nasima ta bita da kallon mamaki
"Dama kina da ciwon ciki ne? Ko menses kike."
Yadda Mardiyya ta kwabe fuska kamar tayi kuka ya kusa saka Munzali dariya. Daga bakin kofa ya tsaya saboda suna hada ido ya gane ciwon karya take yi. Ta bashi tausayi sosai gami da dariyar diramarsu ita da mahaifiyarta.
Juyo da fuskar Mardiyya tayi suna fuskantar juna hankalinta tamkar ya bar jikinta. Ira kenan 'yar, tsoka daya a miya.
"Mardiyya kalle ni nan. Na ce menses ne? Naga baki taba ciwon mara mai tsananin wannan ba."
Gara ace al'ada sau dubu da a ce menses saboda yadda ta tsani kalmar. Amma yanzu sau biyu tana jinta kuma a gaban mutumin da basu yiwa wani sanin kirki ba. Kai ta gyada don ta barta da tambayar. Sannan ta ce akwai maganin da take sha a dakinta dake can bangarensu. Mama Nasima ta mike a sukwane ta fice zuwa neman magani.
"Sai ki tashi tunda ta tafi" cewar Munzali yana dariya a hankali.
Mardiyya ta cukule fuska "dole kayi dariya tunda ka sani karya." Tana magana suna komawa falon "ka zo ka tafi don Allah kafin ta dawo."
"Korata kike yi?" Ya furta bayan ya mayar da fuskarsa kalar ban tausayi.
"Eh"
Zamansa ya yi yana danna waya "babu inda zani tunda ba ke ki ka gayyatoni ba."
A kujera mafi kusa dashi ta zauna idonta yana yawo tsakanin fuskarsa da kofa. Kuka take neman yi.
"Don Allah ka tafi. Wallahi bana jindadin abin da Mama take yi a gabanka. Da wuya ka dinga ganin mutumcinta."
"Mardiyya"
Munzali ya kira sunanta na gaskiya cike da kulawar da bai san daga ina ya samota ba. Kallonsa kawai tayi ta dauke kai saboda jin nauyi a kowacce gabar jikinta.
"Kar ki aibata mahaifiyarki. Damu da iyayenmu babu wanda yake cikakken dan Adam wanda baya kuskure. Suna hakuri damu, muna hakuri dasu. A tsakanin wannan hakurin ake neman balance don a zauna lafiya."
Wani irin rauni ne ya ziyarceta. Tana son mahaifiyarta kuma tana kyamar halayyarta. Duk da haka bata taba jin a ranta wai za ta iya jin kunyar nunawa duniya tsatsonta ba. Abin da Allah Ya baka shi ne naka, dan Adam mai Hamdala shi ne zai kokarin rike tasa kyautar da daraja.
"To kai ta yaya ka nemi balance din?"
"Yanzu nake neman samu albarkacin amini kuma dan uwa nagari Abbati. Da fari da rashin biyayya, rashin girmamawa da nesanta kaina da mahaifiyata na fara sai naga ba a dace ba. Rayuwar taki albarka yadda nake muradi."
Dokin jin yadda yake yi yanzu da tsoron dawowar Mama Nasima yasa ta cewa "yanzu fa? Me kake yi yanzu?"
"Tare zamu nemo Diamond girl. Daga yau sai mu zama abokan shawarar juna game da matan da ya kamata su fi kowa daraja a idanunmu."
Murmushi suka yiwa juna. Mardiyya ta kasa jurewa kallon da yake mata ta tashi da sauri ta shige inda yake tunanin hanyar daki ne. Wayar yaji kuma ya san Abbati ne sai bai kirata kamar yadda ya yi niyya ba. Labarin bakuwarsu ya bashi da yadda Farha tayi bayan Deluwa ta ce matarsa ce.
"Subhanallahi. Please kar ka damu. Dama dole ta sani. Zamu bata hakurin jinkirin da aka samu bata ji da wuri ba. Bari dai na fito muje. Amma ni wallahi ban san ina ne hanyar tashar Kawo ba. Ko Suhaib na kusa ka fada masa ya sake taimaka mana?"
Abbati ya girgiza kai kamar Munzali na gabansa. Kansa ya dauki chaji mai wuyar sauka. Zuwan Hanne ba tare da izininsa ba ko kadan bai yi masa ciwo kamar wayar da aka yi masa akan abin da tayi a tashar ba. Wane mai hankalin ne zai so ya amsa sunan mijin ballagaza? Aikin Hanne kenan! Yayi nasa kokarin a kanta tunda har makarantar yaki da jahilci ita ma ya kaita kamar yadda suka yi shi da Munzali. Bata koyo komai ba banda danna waya da yi masa bincike kamar wakiliyar EFCC. Bai manta silar aurensu ba shi yasa bai raba matsayinta da na takalmin kaza ba. Yana can duniyar tunani Munzali ya isko shi.
"Mutumina muje ko. Da kwatance ba za mu bata hanya ba in sha Allahu."
Mukullin Abbati ya mikawa Munzali ya zagaya daya barin zai shiga sai ga Sauda ta fito da sauri. Ba don Mami tayi magana a gaban su Baaba Mari ba da ba za ta zo ba. Ita bata yarda ba ta fara taya yayarta kishi ne akan matar Abbati.
"Uhmm dama Mami ta ce na tambayeku ko kun san tashar daga nan."
"Daga ko ina ma bamu sani ba." Munzali ya bata amsa.
"To ku jira"
Komawa tayi ta fadawa Mami Khadija amsarsu.
"Farha idan motarku da mai kuyi gaba ke da Sauda sai su biyoku a baya." (Mami Khadija ko tana hauka ba za ta yarda ace ta turasu a mota daya alhalin bata sansu ba. Sannan kuma gasu maza. Yadda take kaffa kaffa da 'yan matanta)
Sauda ta tafi bangarensu inda suke ajiye mukullin tasu motar. Guda daya ce Alh. Tahir ya saya musu saboda uzurinsu musamman na makaranta. Farha kadai ya yarda ta tuka kafin su ma su gama secondary.
A can ta hadu da Mama Nasima ta fito daga dakin Mardiyya duk ta hada zufa.
"Yauwa Sauda zo don Allah ki tayani duba maganin Mardiyya. Gata can ba yadda take ciwon ciki ya murda mata. Nayi neman har na gaji"
Kana ganinka ka san tana tare da damuwa. Idanunta sun yi zuru saboda firgici.
"Wane irin magani ne?" Sauda ta tambayeta da mamaki.
"Ciwon ciki ne dai ta ce yana yawan tashi."
Sauda sai ta shiga suka dan bincika babu. Ita ta kawo shawarar su tafi asibiti. Ta dauki mukullin motar ta kaiwa Farha sannan ta fadawa Mami Khadija cewa su Mama Nasima za ta bi. Ta bata goyon baya suka fita tare domin ita ma ta duba Mardiyyan.
"Kuyi hakuri an tsayar daku. 'Yar uwarsu ce babu lafiya. Ga Farha nan zata kaiku har tashar."
Mami Khadija ta fada musu bayan sun fito. Ita da Sauda suka wuce bangaren Mama Nasima. Abbati ya dubi Munzali da mamakin baro mara lafiya. Sai da yaji ciwon karya ne ya dan yi murmushi. Ta kusa dasu Farha ta zo ta wuce ta nufi motarta. Ko kallon inda suke bata yi ba sai faduwar gabanta da ya tsananta da tazo giftawa ta gefensu. Munzali ne ya yi karfin halin kiran sunanta yadda Abbati yake fada da zolaya.
"Barka da rana Ya Farha."
Watsa masa wata muguwar hararar da ita kanta bata ma san ta iya ba tayi. Abbati yana lura da duk wani motsinta. Bakinta ta dan turo kamar za ta yi magana, maganar da alamu sun nuna a tsiwace za ta fito. Sai kuma kawai ta wuce zuciyarta na dokawa da sauri da sauri.
Wani irin abu take ji game da Abbati da yafi karfin tunaninta. Ya kuma sanya jin yana da aure yi mata nauyi. Me yasa basu fada mata tun farko ba ta shirya zuciyarta? Allah Ya sani indai wannan abin da take ji shi ne so to kuwa ba kankani take yiwa Abbati ba. Gara ta kama kanta haka nan...karshenta ma matar ba daya bace. Ko yaransa nawa? Saurin girgiza kai tayi da ta fahimci inda tunaninta ya nausa bayan ta zauna a motar. Tayarwa tayi tayi ribas tana cin taya. A guje ta fice daga gidan ko tunanin na bayanta bata yi ba...
'Ina tunaninsa mana.'
' Idan na bace musu ai dole ya kirani.'
'Sai in rama nima.'
'Me za ki rama?'
'Da me za ki rama?'
Zantukan zuciyarta kenan lokacin da ta daidaita akan titi.
Tana zama a motar dama Abbati ya karbe mukullin daga hannun Munzali ya shiga mazaunin direba shi ma ya fizgi motar don kada ta bace masa.
Dariyar mugunta Munzali ya fashe da ita "Mutumina kana ruwa, a bulallen kwale-kwale, kusa da mayunwaciyar kadar da 'ya'yanta suka bata. Hodijan inji Fillo. Farha tayi fushi amma kuma naji dadi."
Abbati ya galla masa harara "ko baka fada ba na san kaji dadi mana. Ji wannan fara'a da kake yi kamar ka tsinci hakori."
Dariya ya bashi saboda kana ganinsa ka san yana tare da damuwa. Abu ne goma da ashirin, bai san ta ina zai fara ba.
"Dariya ma kake yi ko Munzali?"
"Wai kuka zaka yi ne duk ka bi ka bata rai?"
Kwafa Abbati ya yi yana dana sanin karbar tukin. Banda tsoron kada Farha ta bace masa da tuni ya kaiwa Munzali duka. Wata kwafar ya sake Munzali ya ce,
"Wallahi in ka tabani sai nayi kararka wurin Farha. Na san wannan cije leben ba zai wuce lissafin yadda za ka taba lafiyata bane idan mun tsaya. Banda haka da tuni ka fahimci nasarar dake tattare da fushin Ya Farha" ya kare maganar da zolaya.
Cike da rashin yarda Abbati ya ce "Nasara?"
"Nasara mana. Mutumina me yake saurin batawa mata rai idan suna son namiji?"
"Zancen kishiya."
"To ana kishin abin da ba a so ne?"
Kyakkyawan murmushi ne ya bayyana akan fuskar Abbati a take. Me yasa bai yi wannan tunanin ba? Munzali ya yi ta tsokanarsa har suka yi parking a gefen Farha.
Tun kafin motarsu ta tsaya take hango fuskokinsu suna dariya. Wani abu ya zo ya tokare mata wuya yaki sauka. Kishi ne wanda bata san daga ina yake tasowa ba. Gefe da gefe motocinsu suke. Sai ya zamana idan suka bude kofa ita da Abbati zasu gogi bayan motar juna. Yana sane ya matseta a wurin gashi daya barin ma akwai mota.
"Ka matsa zan tafi." Ta furta lokacin da ta harare shi.
Murmushi ya yi mata. Murmushinsa mai kyau ya ce "Idan ki ka tafi b'ata zan yi a hanyar komawa."
Har cikin ranta taji murmushin nan. Sai dai kishin ya ci galaba a kanta domin ya saka ta fadin abin da taji kunyar amsarsa
"Dariyarku ta kai ku gida."
Taji haushi ashe. Munzali kuwa me zai yi banda dariya.
Tana kallo Abbati ya harare shi kwatankwacin yadda tayi. Sadda kai tayi kasa don saura kiris ya saka ta dariya.
"Mugu, ka ce min inyi murna kishina take yi. Gashi ka sa na kuma bata mata rai. Ni wallahi da zuciya daya na damu da kai. Ko a mafarki ba zan baka gurguwar shawara ba."
Ba shiri Farha ta kawar da kanta gefe ta danne dariyarta.
"Ya Farha ki juyo don Allah."
Girgiza kai tayi don ba za ta iya kallonsa ba tare da tayi dariyar ba.
"Fita ka bata hakuri mana" cewar Abbati yana budewa Munzali kofa, duk hankalinsa ya tashi "harda wani cewa wanda ake so ake kishi."
Farha na jin abin da ya fada ta juyo da sauri suka hada ido. Bude nata tayi yadda ta saba yaji kamar ana fizgarsa cikin idanun. Kafin ya farga ta lumshe nata tana murmushi.
Shi ma murmushin ya yi har zuciyarsa yana jin wata irin nutsuwa.
"Ya Farha ki tausaya min mana. Fushin nan na kishin ne ko na gaske?"
Munzali ta kalla yana tsaye tsakanin motocin biyu. Kallonsu yake suna burge shi. Abbatinsa ya sami mata in sha Allahu.
"Ka ce masa ya bar ta a ciki?" Ta furta a hankali.
Sannu a hankali Abb
ati yaji kamar zuciyarsa ta kara girma saboda jindadi.
"Za ki jiramu?" Ya tambayeta bayan ya fito.
"Zan jira."
Sai da suka yiwa juna murmushi sannan ya juya. Munzali ya dawo jikin tagarta ta daya barin.
"Farha.." ya kira sunanta a nutse.
Waigawa tayi har taji kunyar kila ya kula da kallon Abbati da ya shiga tashar da take yi.
"Don Allah ki so Abbati. Ban san ko kina da wasu samarin ba amma da wahala ki sami mai sonki kamar shi. Tunda ya ganki na daina gane kansa. Mutumin kirki ne. Idan zan fara fada miki karuwar da nayi da zama dashi sai mun bata lokaci a wurin nan."
"Dadin baki ya ce ka zauna yi min?" Ta tsokane shi.
Yadda tayi sosai ya sake burge shi.
"Kut...wallahi kun dace! Bakinsa baya mutuwa shi ma amma a zuci saukin kansa har ya kusa yi masa yawa. Sau nawa ina masa wayo bai gane ba.." ya ce yana dariya.
"Ai kuwa ka daina daga yau..."
"Dalili?"
"Zan tare masa."
Farinciki ya mamaye Munzali. Burinsa ya cika. Abbati ya sami Farha.
Hannu ya saka a kasan habarsa ya kalli gate din tashar da Farha lokaci guda ya kada kai
"Wallahi kun dace. Sosai, sosai, sosai. Mungode Ya Farhan Abbati."
Nambar da aka kira shi Abbati yake nema zai tambayi inda Hanne take kamar an ce ya kalli hagunsa, ya hangota zaune akan benci. Hannunta tasa tana bubbuga kanta yadda ta kanyi a gida idan amosaninta ya dameta da kaikayi. Yana bata kudin zuwa salon amma don bakin hali, kamar wadda take cikin rashi sai ta soke abinta. Shampoo ma idan ya siyo ba ya sanin inda yake tafiya. Kan dai kullum dankare da amosani. Makotansu inda take zuwa kitso, tayi fada da matar duk akan tayi mata maganar neman maganin amosani. Ga gashin himili guda da tsaho da cika amma gyara sai taga dama. Da ya gaji da magana ne ya yi mata rantsuwar idan ta sake yin susa a gabansa sai ya aske shi. Shi ne ta koma bubbugawa har ta saba.
Mayafinta yana kafada. Daurinta bai rufe tsofaffin jelunan gashinta ba. A kusa da ita namiji ne yake cin abinci daga shi sai gajeren wando. Rabin cinyarsa ma a waje yake daf da jikinta. Gashi da cibiri-cibirin gashin kai mara kyawun gani. Sauran mutum biyun dake daga barin duka mata ne amma suna cin abinci ana buga shewa.
Gabansa ne ya fadi. Zuciyarsa ta tsinke har yaji kamar ya karasa ya dauketa da mari. Matsalolin Hanne suna da yawa. Ba zai taba yarda wai tashi a kauye da rashin wayewa ne suke damunta ba. Ya yi mata duk abin da ya dace domin ta gyara rayuwarta a matsayinta na mace. Da 'Yashshafa ce ta sami rabi-rabin abin da ta samu ya tabbata sai an ga canji. Duk da haka a yau dai abu daya ne ya tsaya masa a rai. Kazamar rayuwarsa ce ta gifta ta gaban kwakwalwa da zuciyarsa. Da sauri ya ja istigfari yana fesar da numfashi. Matsanancin tsoro ya mamaye zuciyarsa a lokacin da ya tuna cewa ba don rashin lafiyar da ya yi ba kila da yanzu ya koma inda yake son bari. Da bai je ba sai Allah Ya musanya masa da samun mallakar zuciyar abar sonsa. Wani abu da bai hango faruwarsa nan kusa ba in ma yana da rabo.
Hango shi Hanne tayi ya nufo inda take ta tashi da sauri. Jikinta har rawa yake saboda tsabar masifar dake cin ranta. Tsayuwa tayi a gabansa ta sanya hannuwanta a kugu tana girgiza.
" Ina 'Yashshafan take? Hmmm, wallahi kada ma ta gwadani don ba mutumci ne gareni ba."
Abbati kam sai da ya daure zuciyarsa sosai ya iya cewa "su waye suke binki bashi a nan?"
Shekeke ta kalle shi a zuwan ya ma raina mata wayo
"Auuuu, wai nan bagarar dani zaka yi don na barta? To Yasin uban kuturu ma ya yi kadan. Kowa yaci tuwo da ni miya ya sha wallahi tallahi"
Mutane har sun soma kallonsu ya jinjina kai cikin son ya hadiye fushinsa.
"Nine kuturun kenan, mahaifina kuma bai isa ba?"
Fahimtar katobararta tayi sai ta kama bakinta ta tsuke. Mutumin da ya kira shi a waya ya taso da ya ga ta tsaya dashi. Kudinsa ya fada da na mai abinci duka Abbati ya basu sannan suka kamo hanyar fita daga tashar.
Munzali da Farha suna can suna hira kamar sun saba. Dama ya fi Abbati saurin jan mutane. A haka ya gane Farha ma ba baya ba. She is very friendly ga iya magana.
"Yanzu nan gaba kuma idan ya hadu da wata, haka za ka tsaya kana wasa shi a gabanta ko?"
"Ba fa zan gaji da cewa kun dace ba. Wato nan bugun cikina za ki yi ki ji ko akwai wata. Abbati ake yiwa wannan wayon ba ni ba."
"Shi ma din ai ka gama yi masa wayon daga yau."
"Na yarda fa. Amma ki kwantar da hankalinki. Daga ke babu kari."
Mahaifinta ta tuno taji kunci na neman rufe farincikinta. Karin aure ba shi bane matsalarta. Munzali da ya kula da fuskarta sai ya ce,
"Matarsa ma bata da matsala, in sha Allahu zaku zauna lafiya."
Tunda yake bai taba jin Abbati ya zagi Hanne ba shi ma ba zai fara ba a bayan idonsa. Yana dai kawo masa korafi idan abu ya ishe shi amma iyakarta kenan.
Ita ta fara hango su saboda tana fuskantar gate din tashar. Gabanta faduwa ya yi taji ta karaya. Yau dai bata shirya ganin matarsa ba. Kuma bata ga dacewar su hadu a tasha ba. Munzali da ya bada baya kuwa sai hira yake mata yana jingine da tasu motar.
"Zan yi gaba kafin su karaso in jira ku a can" ta nuna titin da yake kallonsu wanda shi zasu bi su koma.
"Ba za ki jira ku gaisa ba?"
"Idan munje gida sai mu gaisa." Ta amsa a hankali. So take kawai ta bar wurin kafin su iso.
Abbati yana tunanin da kalmar da zai gabatar dasu da juna kawai ya ga motarta tayi ribas kuma ko ta juya ta kallesu. Numfashi ya sauke ya mikawa Munzali mukulli. Shi ma bai tambaye shi dalili ba saboda yana iya ganin damuwa da bacin rai shimfide a fuskarsa.
"Ka kora su 'Yashshafan ne?" Hanne ta tambayi Abbati da dan hope dinta.
" 'Yashshafa zan kora ko su 'Yashshafa? Ita mutum daya ce. Su kuma yana nufin harda surukarki wadda ta tsuguna ta haifeni."
Gefe ta muskuta saboda kunyar da ta sake ji sai tayi shiru. Lokaci lokaci take yin tsaki ko tayi kwafa cikin bacin rai. Mai rabata da 'Yashshafa yau sai ya shirya.
Da shirun ya gagara tana gudun zuciyarta kar ta fashe ita daya sai ta soma surutai
"Wai ni za a yiwa bariki? Hmmm. Har tayi girman sanin kissa? Yarinyar da a gabana ta fara kirgar dangi..."
Fadan da baya son yi ya hau ta dashi. Don wata tsawa da ya yi mata sai da ta kusa sakin fitsari a zaune.
"Hanne!!!" Ya kira sunanta da karfi da kuma alamun gargadi. Ko kula da yadda take zazzaro idanu bai yi ba ya cigaba da yi mata masifa
"Wallahi zan fasa miki baki kuma na mayar dake tashar ki koma Kano. Kin sha burkutu ne da za ki shigo mota kina yi min wannan haukan? Ya dace kiyi magana irin wannan a gaban Munzali?"
Girgiza kai tayi da sauri.
"Bude baki za ki kiyi min magana. Nace ya dace?"
"Bai dace ba" Hanne ta bashi amsa baki na rawa. Bata zata zai tanka ba tunda ta saba debo shirmen haukanta tana yi baya kulawa.
Duk abin da suke yi Munzali bai tanka ba. In da akwai wurin da suka shatawa juna layi duk da basu furta da baki ba to zamantakewarsu da matansu ce. Suna kaiwa juna korafi da neman shawara. Amma babu zaman zubarwa matan da mutumci. Ko babu komai dukkaninsu 'yan uwansu na jini suka aura. Yanzu ma parking ya yi ya fita daga motar. Farha bata kula sun daina binta ba don tunda ta ga ba Abbati ke tukin ba ta daina kallon motar ta madubi.
"Yanzu me nayi da har za ka ci mutumcina a gaban Munzali? Saboda Allah a dakeni a hanani kuka?"
"Ni ne ma na zubar miki da mutumcin Hanne? Yau ko ciki daya muka fito da Munzali ya dace ki dinga zancen kirgar nono a gabansa?"
"Kirgar dangi na ce."
"Kar kisa in zageki Hanne. Ko kirgar kindirmo ne ai ya san me kike nufi. Wannan shirmen ne ya kawoki dama ba duba mijinki ba?"
"Sannu ya jikin?" Ta ce a sakarce.
Madadin ya amsa sai ya ce "tsabar kishinki na banza ya saka ki fitowa ko kaya babu? Da ba yau zamu koma ba haka za ki zauna?"
Gefen kafafunta ta hau lalube tana cewa "Da kayana. Na taho da kaya." Sai ta dafe kai "washhh, Yasin suna shagon mai shinkafar nan."
Yi mata magana ma bata lokaci ne. Fada ko duka asarar energy. Fita kawai ya yi ya fadawa Munzali ta baro kayanta.
"Ku wuce can zan koma tashar na dauko. Tafiyar tamu kamar da wuya dai a yau. Bana son fitar yamma bare ta dare."
"Ba ayi haka ba."
Munzali ya ce da Abbati. A dalilin Hanne tayi tafiya ya dace ya kaita ta dan huta kafin su kuma daukar hanya. Sannan suna bukatar yin magana a junanau. Wanda ya kira Abbati akan bashin da Hanne ta ci suka sake kira aka kwatanta masa jakar. Suka yi masa alkawarin dubu biyar idan babu abin da ya salwanta ciki sannan suka rabu. Munzali ya koma tashar, Abbati ya wuce gidan Alh. Tahir da Hanne. Su biyun sun gane hanyar a bi daya tak.
Fafur Mardiyya taki zuwa asibiti saboda ciwon karya ne. Ta dai nuna taji sauki. Sai da Mami Khadija ta fita daga dakin sannan Mardiyya ta yiwa Sauda bayanin abin da ya faru.
Dundu ta yi mata a baya "Amma dai baki kyauta ba, baki ga yadda hankalin Mama ya tashi ba."
"Haka shi ma ya ce."
Da shakiyanci Sauda ta ce "Shi? Har kin fara ce masa shi? Lallai Abba ya fara tari auta ta isa aure."
"Ba fa haka bane. Kinga babba ne. Bai dace na kira sunansa kai tsaye ba." Mardiyya ta ce da nufin kare kanta.
"Hakkun. Ladabi da biyayya akwai dadi."
Shan kunu tayi don tsokanar Sauda bata karewa. Idan ta saka mutum a gaba sai ya kusa kuka.
"Bana so...abokan shawara kawai ya ce mu zama kar ma ki fassara."
"Hakka!" Ta ce bayan ta tashi tsaye tana dariya "su abota manya."
Tsokanar da take gudu Sauda ta sami kofar yi har sai da ta nuna kamar ranta bai baci ba. Sannan ne Saudan ta turawa Farha text wadda a lokacin suka isa tashar ta fada mata Mardiyya kalau take. Sauran bayani sai ta dawo.
Lilu ne ya tuko motar Suhaib, shi kuma ta Abbati wadda take asibiti suka dawo gidan tare. Wurin parking suka nufa kowa ya daidaita motar da yake ciki bisa tsari.
Kafin shigowarsu Baaba Mari ta dinga jin kamar suna takurawa masu gidan. Sun zauna jiran su Abbati batare da sanin ko masu gidan suna da uzuri ba. Dadin dad'awa ga an ce 'yar gidan babu lafiya. Babu alamun canjin fuska ko kadan a tattare da matar gidan amma da yake bata saba ba sai take jinta a takure. Ga Deluwa da 'Yashshafa sai kai hannu suke cikin tray din snacks suna dauki daidai.
"Kiyi hakuri mun zo mun dora miki dawainiya."
Mami Khadija ta sake fadada fara'arta
"Me ya kawo wannan magana? Ni wallahi baki ji yadda nayi farincikin zuwanku ba. A haka fa ake kulla zumunci kiga har 'ya'ya."
Baaba Mari sai dariya "kayya Hajiya. Mu fa 'yan kauye ne. 'Yan birni suna zuwa kauye?"
"Har kinsa naji babu dadi. Muma ai zama ne ya kawo mu nan amma silar kakaninmu kauyen ne. Mu 'yan Soba ne kuma har yanzu muna ziyartar dangi a can. Garinmu a karkashin Kaduna yake."
Uwar azarbabi Hajiya Deluwa mai hangen surukuta za ta hadata da Mami tayi saurin shiga hirar.
"Mu kuma daga Kirikasamma muke. Amma ita Mari aure ne ya kawota. Ita 'yar Maigatari ce."
Baaba Mari bata gwasaleta ba. Hirar sai ta tafi su uku. Deluwa ta rasa inda za ta saka kanta don murna. Da mace mai aji irin Mami Khadija take hira. Takaicinta ma na rashin bude kwanukan abincin da Baaba Mari bata bada fuskar yi ba ya yi sauki. Sai kayan fulawa suke ta gabza.
Mami Khadija ce ta sake komawa bangaren Mama Nasima tunda bata san ciwon karya bane. Ta damu da Mardiyya kamar yadda ta damu da nata 'ya'yan. Da ta dawo Baaba Mari ta ce ta kaisu su gaishe da marar lafiyar. Mami Khadija kuwa taji dadin kyawun tunanin Baaba Mari. Su biyu suka bi ta. 'Yashshafa anyi gamo da samosa ta kasa hakura ta bisu. Tun dazu Deluwa take yi mata inkiya da hannu akan ta barshi haka don ita ma ta ci amma taki. Sai da suka fita taji falon ya yi tsit sai karar AC. Ita kadai ta firgita kanta da muggab tunani.
"Wannan shuuuuuu haka kamar wucewar fatalwa?" ta ce da rawar baki.
Guntuwar samosar hannunta ta ajiye ta tashi a hankali ta sulale waje. Da baya da baya take tafiya tana kiran Deluwa a tsorace.
Kai tsaye Lilu ya danno kai bangaren Mami Khadija sai ganin yarinya ya yi a gabansa a bakin kofar shiga.
Gewayen fuskarta da dan karan hancin nan sun yi fari saboda hoda da foundation. Bakin da ya ci samosa kuma maiko ya zagaye shi. Idan ka kalleta dole kayi dariya ko baka so. Mami Khadija kanta girma ne kawai da sanin mutumcin bako ya hanata darawa. Sauda tayi a fakaice.
Idanunta ta zaro tana kalle-kalle a farfajiyar gidan ko za ta hango mahaifiyarta.
Lilu sai ya sauka daga matattakalar ya jira Suhaib ya karaso. Hab'a ya rike ya ce da yayansa,
"Ya Suhaib, yaushe watan Ramadan ya tsaya har goman farko ta wuce ban sani ba?"
"Ban gane ba."
"Kaga karfin hali" ya nuna 'Yashshafa "masu Iya duba-duba na gani a kofar Mami. Yanzu ashe har cikin falo suke shiga in sun zo. Shi ma ya hau next level kenan."
"Kai fa ka fiye shiririta. Gabadaya ban fahimci kalma daya cikin zantukanka ba."
Hannu ya mika masa yana dariyar da ta bawa 'Yashshafa haushi.
"Bani canji ko dari biyu ce in sallameta tukunna."
Sai lokacin Suhaib ya karasa hawa matattakalar ya kalleta. Duka ya kaiwa Lilu ya goce da sauri.
"Kanwar Abbati ce fa."
Da ya soma dariya sai da ya durkushe a wajen
"Wannan din? Kalleta da kyau Ya Suhaib 'yan Iya duba-duba ne."
Kyale shi Suhaib ya yi ya dubeta duk tayi wuru-wuri kamar wadda ta yiwa Sarki karya. Rangwadar nan ma babu alamunta. Dole Lilu ya cr tashe tazo. Kalmar ce ta bace masa yake ta cewa Iya duba-duba.
"Me ya fito dake?"
"Innata. Inna Deluwa nake nema."
Lilu ya sake kwashewa da dariya "kana ji fa Imna Deluwa take nema sannan ka ce ba ..."
"Ya isheka Lilu" Suhaib ya ce rai a bace. 'Yashshafa ya tambaya inda suka je har aka barta ita kadai.
"Wai wata ce bata da lafiya shi ne suka tafi da matar gidan nan" ta nuna bangaren Mami "cikin kuma sai nake jin kamar fatalwa tana shawagi. Sai shuu, shuu ake yi."
Shi ma mai fadan dariyar sai gashi yana yi harda kyakyatawa. Cikin sa'a kuwa sai ga su Mami sun fito. 'Yashshafa tana hangosu ta sauka da sauri. Gayun ya dawo da karfinsa tunda yanzu dai ta san ba gidan yan kan kai bane yadda ta soma hasashe.
"Mooomi. Moomii"
Hanjin cikin Deluwa a take ya bada wani irin sauti mai karfi. Tsinuwa ta shiga yarfawa aljanun 'Yashshafa wanda ta kwaso a makatantar kwana. Kunya kamar ta nutse. Sai kuma dole ta nema mata sauki domin indai sune suna wahalar da ita. Wani zubin sai tayi wata guda a gida ana tsakar zangon karatu.
"Me ki ka ce Shafa'a?" Ta riko hannayenta tana jin kamar ta fashe da kuka. Yanzu idan Sha'aib ya gujeta dole sai dai ta komawa Abbati.
'Yashshafa tayi murmushi a zatonta sunan ne ya burge Deluwa.
"Moomi."
Kowa yana ji ta ce ''oh ni 'yasu. Makaranki su rasa wurin tashi sai nan?"
"Makarai? Aljanu ne da ita?" Cewar Mami Khadija tana dan matsowa da taussyawa.
Lilu kuwa bayan Suhaib ya koma ya labe a firgice har yana tuntube. Cartoon ma baya kallon mai dodanni saboda kafirin tsoro bare kuma a ce gashi kusa da mai aljanu.
"A makarantar kwana ta kwaso su. Da alama yau bafillatani ne ya tashi kenan." Cewar Deluwa tana marairaicewa "Karshenta shanunsa ne suka bata ya fito nema. Banda haka me zai kai budurwa kiran wata Moomi ana zaune kalau?"
Lilu na jin tsoro amma bai hana shi dariya ba. Suhaib ya figi hannunsa saboda kallon da Mami Khadija tayi musu.
'Yashshafa tana son yiwa Deluwa bayani amma kuma Mami Khadija tana gefensu sai sannu take yi mata. Cikin falon suka koma Baaba Mari ta dinga girgiza kai. Tana ji tamkar ta janyo su Abbati su zo su bar gidan nan. Duk wani abu da zasu yi takama dashi na kare mutumci Deluwa ta zubar dashi. Bata ganin laifin 'Yashshafa domin kuwa yarinya ce mai bin maganar uwa sau da kafa. Duk abin da take yi bai wuce dorar da tarbiyar mahaifiyarta ba.
Manyan mata ne a zazzaune suna hira ana ciye ciye da shan lemuka. Manyan mata a matsayin arziki domin ba dukkansu bane masu shekaru. Babu 'yar kass da talatin dai cikinsu. Suturunsu da duk wani abu da yake jikinsu ya isa shaidar cewa suna ganiyar jin dadin rayuwa. Su tara ne kuma kowacce cikin lemon gabanta anyi masa hadi da kwaya daidai ra'ayinta. Wasu har sun fara tambele suna magana irin ta gogaggun 'yan duniya.
Wata hamshakiya da ta gama tumsewa ce ta mike tana wata irin rawa ta tsantsar rashin kamun kai. Suka tashi suna ihu aka soma tayata da liki.
"Ku barni in warwasa kawayena. Jiya na hadu da namijin da ya amsa sunansa ba irin dan rakiyar da nake aure ba..."
"Yeeeeyyyy"
Suka hau shewa ana dariya. Ta cigaba da cewa,
"Saurayin kanwata ne amma ina ganinsa na san dan harka ne. Bugu daya ya kawo min kansa hotel jiya."
Wata shewar ta cika falon da suke. Matar gidan wadda tayi musu masauki ta doki cinyar Jiddo tana dariya.
"Jiddo ta Alhaji Tahir bamu labarin naki mutumin. Ya ku ka kare da makaniken nan na Kano?"
Jiddo bata son a ce ta gaza. Ba yau suka fara harkokinsu ba. Yanzu dai duk sun chanja samari ne. Ta fada musu haduwarta da Danladi amma shiru bata labarta musu yadda aka kare ba.
"Sai zama na gaba za ku ji bayani."
"Amma dai ya turo miki hotuna bayan kin tura naki ko?"
Karya ta gillo musu mai jirwaye da gaskiya "ai tun bayan ganin hoton shegiyar nan a wayar Alhaji nake kaffa kaffa da wayata. Ya turo" sai ihu har sun fara matsowa ganin gulma ta kara da cewa "ina gani na goge."
Mata ne wadda kowacce take dauke da tabo ko bacin ran namiji. A nasu jahilcin da bacewar basirar ne suke tunanin wannan rayuwar ce za ta wanke musu zukata.
Neman matan Alh Tahir bai wani dami Jiddo ba. Amma rashin haihuwa ya mata karan tsaye. Tun tana nema har ta saduda. Duk tarin arzikinsa ba za ta tsira da komai ba sai tumunin takaba in ya mutu...a zatonta!
BABIN
ARSHE.
Buba da Habi sun shigo gidan sun tarar da Deluwa cikin tashin hankali da fargabar abin da ya sami 'Yashshafa. Sai fada take tana nanatawa lalura ce kuma babu wanda yafi karfin ta kama shi. Talaka da maikudi. Dan kauye da dan birni babu inda ba a aljanu. Su gidan wani abokin Buba suka je. Mutumin da kansa ya zo ya tafi dasu tun kafin fitarsu Abbati. Habi tana jin abin da ya faru ta yi 'yar dariya. Kafadar 'Yashshafa ta dafa ta ce,
"Gwaggo Deluwa dake take fa. 'Yashshafa ko ba Momi kike nufi ba na 'yan gayu?"
'Yashshafa dai kamar ta nutse a kasa. Idanuwa duka a kanta. Dadinta daya ma wannan mai dariyar da yayansa basu biyosu ba. Mami Khadija ma dariyar tayi ta tashi ta shiga ciki za ta hado musu 'yar tsaraba, musamman ma dai 'yar budurwar nan mai abin dariya. Deluwa na ganin ta rufe kofar kori
o din da zai sada ta da dakinta ta kaiwa 'Yashshafa duka a baya rai duk a bace.
"Yanzu ke Momi din ne baki iya fada ba ki ka hau kukan saniya? Ca nake 'yar gidan Bibalo ba momi suke ce mata. Kawai sai mooo, mooo ake ji kamar saniya ta tsinke daga turkenta. Mtseww"
Buba da Habi suka bushe da dariya. Sallamar Farha suka ji Baaba Mari ta soma hamdala. Tafiya zasu yi yanzu yanzu in Allah Ya yarda. Bata bukatar Hanne ta zo ta bar nata abin fadin kamar na Deluwa da 'Yashshafa.
Kafin ta shigo tun a waje Lilu ya tareta ya bata labarin gamonsa da 'yar tashe. Dariya taso yi aka kuma bude gate Abbati ya shigo. Zuciyarta tayi wani irin dokawa mai wuyar fassara. Abin sai ya bata mamaki tunda a hanya ta san Munzali ke jan motar. Bata ga alamun Munzalin ba sai mace. Shi ne ta shige bangaren Mami da sauri don ma kada su hadu.
Ya kula da irin saurin da take yi wanda yake da nasaba da gudun haduwa da Hanne. Da gaskiyar Munzali dai da ya ce masa kishinsa take.
"Wai shiga ka ke so nayi na kirasu? To wane bangaren zan je?"
Hanne ta katse masa tunani da ta bude kofa za ta fita.
"Don Allah Hanne ki kama kanki. Kin san abubuwan da bana so. Kar ki gwada musu a gidan nan. Godiya kawai muka zo yi musu na kyautatar da suka yi mana."
Ya san halinta. Ko babu komai tsakaninsa da Farha ba zai so ta shiga tayi abin da zai zubar mata da kima a idonsu ba. Idan Farha rabonsa ce zai so ta shigo gidansa tana ganin mutumcin wadda ta tarar kuma kanwa gareshi.
"Naji" ta amsa da kunkuni.
Abbati dakatawa ya yi aka yi musu izinin shiga bayan ya yi sallama. Yana saka kafarsa Farha na shigewa wata kofa da yake tunanin kitchen ne. Murmushi kawai ya yi sannan aka gabatar da Hanne ga Mami. Anyi sa a Mami Khadija tayi mata kwarjini shi yasa ta gaisheta a mutumce.
Da kyar Mami Khadija ta samu suka ci abincin don sun matsu su tafi Kano a ranar. Basu dade suna jiran Munzali ba ya iso. Wurin Mardiyya ya fara zuwa suka yi sallama. Mama Nasima tana son tambayarsa alakarsa da abokan tafiyarsa da Mami Khadija amma yau ba hali. Ciwon karyar Mardiyya duk ya tsaya mata a rai.
Da zasu bar gidan Abbati ya so Farha ta fito ko yaya ya sake ganin fuskarta amma taki. Tsoron ganin matarsa take yi. A yadda ta ganshi hadadde dan gayu da wuya ace matarsa ba haka take ba. Idan kuwa haka ne kila sai ta raina kanta. Karshenta kuma tafiyar da bata taba irinta da wani d'a namiji ba ta sami tangarda. Gara dai kada ta kai kanta kallon abin da zai iya tada mata hankali.
Fitar su Hasiya ba dadewa Ale Gambo ya dawo. Salima na durkushe bakin murhu tana faman hura wutar itace cike da tashin hankali saboda daren da girkin ya yi. Gashi itacen danyene, yaki kamawa sai hayaki yake ta fitarwa. Daga bakin rariyarsu 'yan matanta ne suke wanke wanke.
Takunsa dif-dif tamkar wani doki mai ji da karfi ya shigo tsakar gidan. Sannu da zuwan da yaran suke yi masa ma bai ji ba sai kira yake kwalawa Salima. A razane ta fito domin da wuya suke wanyewa lafiya idan ya shigo a wannan yanayin. Cikin tsananin fushi da mamakin rainin da ya soma shiga tsakaninsu ya nuna ta da dan allinsa. Har wani haki yake ga feshin yawun da ya kan yi in yana magana cikin fushi.
"Hasiya na gani ta fita."
"Wani abin ne ya sameta?" Salima ta tambaye shi da firgici.
"Nawa ta baki?"
Maganar ta doketa sosai ba kuma don yau aka fara ba. Mijin aurenta ne, uban 'ya'yanta, wanda bai taba sanin darajarta ba yake yi mata wannan tambayar. Duk inda mutumci yake sun dade da yin hannun riga da Ale Gambo. Maganganunsu dasu Hasiya na dazu suka dawo mata. Tabbas zancen Ayaah gaskiya ne, babu wanda zai iya k'watar mata 'yanci a wannan yanayi sai ita da kanta. Tana jin tsoronsa har cikin kasusuwanta domin dukanta yake kamar ya sami gardi daidai dashi. Amma haka ta daure ta yatsina fuska tana magana cikin bacin rai ita ma.
"Ajiya ka bata ko bashi?"
Hagu da damansa ya waiga babu kowa sai yaransu suna kallonsa. Ya dawo da idonsa kanta tare da nuna kirjinsa.
"Wai dani kike Salima?"
Haka kawai taji kwarin gwiwa yana ciccibata. Daurin zaninta da yake neman kwancewa ta gyara tana cewa,
"Idan akwai wani Gambon a gidan nan bayan kai to dashi nake."
Jikinsa sai ya hau tsuma kamar mazari. A zatonsa ko hauka take bata isa ta maida masa magana haka ba. Daga shi har ita sun ji karar kwanukan wanke wanken domin a tsorace yaran suka mike. Sun tabbata sai ya dakar musu uwa. Hularsa ya cire ya yar a gefe. Kodaddiyar babbar rigarsa tabi bayanta.
"Baba kayi hakuri"
Ko kallonsu bai yi ba ya dubeta yana jinjina kai. A firgice take sosai amma tayi alkawarin daukar mataki.
"Dama ina da labarin Hasiya" ya ce yana kumfar baka "ance tafi kowa rashin kunya a cikinku. Wato zuwa tayi ta kitsa miki gaibu tace kiyi min rashin kunya ko? Tunda baki da hankali har ki ka karbi shawararta za ki ga abin da zai biyo baya. Wallahi Salima daga yau ko daga ido ki kalleni kin daina.."
"Idan ka isa ka kasheni kawai ka huta." Ta bashi amsa da kuka.
"Mama kiyi shiru don Allah" cewar autarta.
Ita da yaran babu wanda ya kula da lokacin da ya hanyo igiyar gugar rijiya. Murdeta kawai ya yi ya kama daidai inda zai masa dadin riko ya shiga lafta mata.
Salima taki yin ihu kamar yadda ta saba. Tsayuwa tayi kyam dukan yana sauka a jikinta amma zuciyarta ke karbar zafinsa.
Shi kuma gogan rashin jin magiyarta ya sake tunzura shi. Hannu ya daga ya kai mata dukan da yafi kama da naushi a gefen fuska. A lokaci ne kuma ta aiwatar da shawarar Ayaah. Tafiya tayi luuu ta zube a kasa. Yaran suka yo kanta suna kuka. Ale Gambo ya soma masifa yana jiran ta tashi yaji shiru.
"Ke Salima. Salima? Tashi mana" ya ce jikinsa na yin sanyi. Igiyar ya saki ya dan ja baya.
Babbar 'yar tasu mai shekaru sha uku Ihsan tana ganin ta fadi ta ruga makota a guje tana kuka. Duk da haka Ayaah ta ce suyi amma a tsorace take ko suman gaske Ummanta tayi. Kuka take tana kururuwa kamar yadda Ayaah ta fada mata a dan tsukin lungunsu.
"Wayyo Allah. Baba ya kashe mana Umma"
Hankalin Ale Gambo ya tashi sosai da yaji me take cewa. Girgiza Salima ya shiga yi yana faman kiranta kamar mahaukaci. Durkushe a wurin makotan da suka fara shigowa suka same shi.
"Haka kawai naga ta fadi nima." Ya dubi yaransa a darare "ai ban mata komai ba ko?"
Basu amsa masa ba sai ihun da suka cigaba da yi.
"Baba ya kashe Ummanmu da duka."
Salati kawai ake ji sai matan da suke neman taimaka wa Salima.
Shi kuma Ale Gambo sai huci yake da surutai mara sa kan gado. Duk wanda ya gan shi a wannan lokacin ya san ya shiga rudani, amma yana kokarin boyewa don kada ya tonawa kansa asiri. Hannuwa yake ta dagawa kamar mai shirin tashi sama.
"Ni ban mata komai ba! Daga maganar fatar baki sai mutum ya suma? Salima ki ji tsoron Allah ki mike. Wai me nayi miki?"
Ba a dauki lokaci ba ta dan farfado musu amma taki ta sha ko da ruwa ne ga kuma baki duk sai fitar da jini yake. Gefen fuskar nan inda ya daka ya kumburo suntum kamar alkubus. Kan a ce me gida ya kacame da 'yan jaje cikin daren, daman makotan ta da dama suna da masaniyar ba yau ya fara bugun ta ba.
Wani dan tsoho da yake yawan zama nan gindin bishiyar kofar gidan nasu ne yace to ya zama tilas su nemo iyayenta a sanar dasu kafin ya kashe musu 'ya wataran sai dai a kai musu gawa.
Kowa ya yi na'am da zancen. Shi ya saka wasu magidanta biyu tare da Ihsan suka hau adaidata zasu je a fada wa iyayenta halin da ake ciki. Ale Gambo yana neman yi musu taurin kai domin ya gudu samarin layin suka kama shi. An tsayar da magana cewa da an dawo da iyayenta zasu wuce dashi ofishin 'yan sanda.
Idanu ta runtse tana mai jin haushin kanta. Shigowar Innayo ta bakwai kenan dakin amma ta kasa motsa baki tayi mata tambayar dake cin ranta. Dangin Babansu da makota da dama sun zo mata barka. Amma yadda babu kowa daga gidan mijinta haka nan babu daga dangin Innayo. Hatta na cikin Kanon babu wadda ta zo. Abin ya yi mata ciwo. Indai ba su ma din sun tsaneta ba me zai hanasu zuwa? Ga yaranta da take masifar kewa kamar tayi hauka.
Sallamar Uwani ta jiyo tayi saurin share kwallarta. Sai dai tuni Uwanin ta gani lokacin da ta bankado labulen dakin.
"Kuka Zara? Naga uban kayan abinci su akarambana (Hasiya) suna gyarawa wai na suna. Ba dai rigima ku ka yi da Alh. Unais ba?"
Bangare daya na fatan haka ne ko don tayi mata dariya. Ta jima tana fada mata kudin miji ba a tinkaho dashi. Burgewa shi ne ki tashi ki nemi na kanki. Daya bangaren kuma mai sauran imani yana fatan ba haka bane. Shi ma kuma domin kada 'yan bani-bani su kara yi mata yawa idan Zaran ta durkushe ita ma.
"Bama waya ma" ta amsa mata muryarta tana karyewa "sai dai matsalarsa bata gabana. Na san yadda zan yi na rama duk abubuwan da suka yi min shi da Haj. Fatakwal."
"To meye kike hawaye?"
A waje Maimuna, Hasiya, da Murja da Ummita wadanda daga gida suka wuto nan din kai tsaye ke ta aikin kayan miya da nama. Yaran Maimuna duka maza ne. Biyu cikinsu, manyan sune masu yayyanka nama. Hira suke yi cike da nishadi Ayaah sai ta dinga jin kanta kamar bare. Gefe ta koma tana daddanna waya amma ko kadan abin baya burgeta. So take ayi da ita amma bata san kan hirar ba. Zantuka ne da dukkansu suka san wani abu a kai.
Hasiya tana ta lura da ita. Yanzu kam tana sane ta ki sakota cikin hirar saboda ta kara gaskata maganar Salima. Ta kuma samu abin da take so. Ayaah ta bata rai sai wani karkada kafa take wanda ta san da wata cikin yayyenta za ta yi mata magana karshenta a kare da rigima.
"Ayaah."
Kamar jira take ta amsa kiran Antinsu Maimuna da sauri.
"Na'am"
"Jeki ki karbo jaririyar nan wurin Zara na goya miki ita. Kin dai iya goyo ko?"
Yanzu ma da saurinta ta gyada kai "na iya"
"Dan wa ki ka taba goyawa?"
"Aji tsoron Allah dai banda karya"
Cewar Ummita da Murja suna mamakin yadda ma ta amsa mata a ladabce. A zatonsu gefen da ta kebe kanta tana danna waya duk cikin rashin kunyarta ne.
"Ku kuma don baku taba gani ba sai ku yanke mata hukunci da rashin iyawa?"
Mamaki ya kara kamasu. Anti Hasiya ce fa ta kare mata! Anya yau lafiya kuwa? Kara musu mamakin tayi ta hanyar kallon Antin tasu suka yiwa juna murmushi sannan ta kallesu ta murguda baki. Da sauri ta ta juya ganin Anti Hasiyan ta bude baki. Bata so tayi mata fada yau. Kullum ita ce mai laifi idan abu ya hada da yayunta. Yau dai ita aka tarewa. Duniya tayi mata dadi.
Innayo ta fito daga bandaki ta jiyo muryar Uwani da Zara a cikin daki. Bata ji shigowar Uwanin ba ta shiga wanka bayan ta gama hadin sabulun salo na jaririyar da take nuna bata damu da ita ba. Hannun kofar ta kama za ta bude ta ji zancen da suke yi wanda ya sake tsinka mata zuciya game da sha'anin 'ya'ya.
"Yo don dangin Innayo basu zo miki barka ba sai ki hau kuka? To ko dai kin ji wata magana ne?" Uwani ta furta da bacin ran ashe duk kukan Zaran ma mara dalili ne a ganinta.
"A cikin gidan fa nake amma ko mutum daya ban ji ta kira ta fada musu haihuwar ba. Ai dole abin ya yi min ciwo. Kuma ita ma bata taba daukan yarinyar nan duk kukan da za ta yi."
"Kinga Zara bana son munafunci fa. Ni ce ba wata ba da za ki fake da rashin zuwan dangin Innayo don ki boye 'yar tsamar dake tsakaninki da mijinki. Daukar jika kuma ina ce haka kike so?"
Daidai lokacin Ayaah ta shigo. Murmushi ta yiwa Innayo tunda sun gaisa lokacin da suka zo. Tashin maganganun da ta ji ita ma sai ta kasa karasawa dakin. Fita ya kamata tayi amma ta kasa lokacin da ta kula idanun Innayo a birkice suke. Akwai boyayyen bacin rai da damuwa a cikinsu. Sai kuma kwallar da ta cika shi taf amma taki bari ta zubo.
"...ba har gidanki ki ka kirani akan in zo in karbarwa su Innayo tsofaffin kayan da baki dinka ba don kada su zama abin kallo wurin taron suna ba?Ko baki dinga yamutsa fuska da na baki labarin tana ciwon hakori ki ka ce kazanta bace? Shi ne yanzu za ki dinga kukan karya kamar kin fi kowa damuwa da ita..wai ma da kin taba gayyayarsu suna ne?"
"Meye na daga muryar? Kuma duk abin da ki ka fada ai bai canjata daga zama uwata ba." Zara ta ce da sanyin muryar wanda hankali ya fara ziyarta.
Uwani tayi wata irin dariya ganin kamar rainin hankali Zara take yi mata.
"Daga baya kenan amma kin san sai dai ki fadawa wanda bai sani ba ko? Na san Innayo za ta ji dadi. Ko ba komai yadda ta dade tana son ki dinga rabarta sosai yau ta samu tunda baki da tudun dafawa."
Allah Sarki Innayo, kwallar sai ta sauko a guje. 'Ya'yan cikinka su yi maka irin haka ba karamin ciwo gare shi ba. Ji tayi kafafunta suna neman sakinta a kasa sai hannuwan Ayaah suka tareta.
Tausayin Innayo ya tsirga mata. Tunda suka shigo matar nan tana kan kafafunta. Amma ita ce 'ya'yanta suke yiwa haka.
Daga ciki suka ji Zara na cewa "Ko ma me za ki fada kiyi ta fada. Na riga na fara ganin nawa sakamakon, ki jira naki."
"Ba zan ga komai ba sai alheri. Wato rashin kunyar da ki ka kwana biyu baki yi ba saboda kin dawo gida mai soro ce tasa ki cewa nazo dama?"
Zara ta share kwallar da ba za ta ce ga aihinin dalilinta ba.
"Ki barshi kawai."
Ayaah kasa jurewa ganin hawayen Innayo tayi ta juya za ta fita. A yau ta fahimci me yasa a gida ake bukatar wanda ba ya shakkar kowa.
"Ina za ki?" Innayo ta tambayeta cikin dusashewar murya.
Kofar dakinta ta harara tukunna sannan ta ce "Anti Hasiya zan kira."
Innayo ta murmusa ganin ran Ayaah yana neman fin nata baci
"Dawo abinki Hajara. Idan babarki ta zo raina sai yafi yanzu baci. Ba wani hakuri gareta ba bare jin magana a irin wannan yanayin."
Ayaah bata san lokacin da tayi murmushi ba "da gaske ita ma bata jin magana?"
"Ban ce ba" Innayo ta amsata cike da kulawa.
Sautin tsakin Uwani wadda ta mike suka jiyo tana mai cewa
"Aikin banza. Kin san abubuwan da na katse na zo? To wallahi sai kin biyani tunda a bakin aiki nake ki ka sani fitowa."
Zara ta auna ta ga a neman lafiya babu ji da kai. Idan tayi shiru kanta za ta cuta. A yadda ta wahala kwanakin farkon haihuwarta ba za ta so a maimaita ba.
"Wurin dinkin nan nake so ki duba min. Ina jin kamar bai yi ba."
Metiron Uwani ba mutumci. Banda tana tsoron kada kasuwar ta watse da sai tayi dariya. Ai tun ranar da Innayo ta saka ta duba Zaran ta kula dinkin zai iya samun matsala saboda rashin kulawar da ya samu. Duk da cewa a ranar a tsorace take amma ta san muddin Hasiya tana wurin bata isa ta karbi kwandalar Innayo ba. Ashe kuwa tana da rabo. Tunda Zara ta sake kawo kanta wallahi sai taci kudinta.
Tashi tayi kamar za ta fita daga dakin a zuwan bata damu ba ta ce "Aiki ne na ku
i Zara. Sannan dole ki san karyar da zaki yi ki zo ki sameni a gida. A nan Innayo..."
Innayo kawai ta bude kofar. Su biyun kowacce ta zaro idanu. Jaririyar ta nunawa
Ayaah.
"Dauki kanwarki ki fita kuma kada ki manta abin da na fada miki."
Umarni ta bi ta koma tsakar gida da 'yar jaririyar wadda ta sake nannadewa a shawul.
"Uwani"
Cikin Uwani sai da ya tsirga don tsoro ne ya cika mata zuciya. Yanayin Innayo yasa taji kamar tayi tsuntsuwa ta ganta a nata gidan.
"Ba dake nake ba?" Innayo ta yi mata tsawa.
"Na'am" Muryarta har rawa take da ta amsa.
"Ban ce ki duba min Zara zan biya ki ba rannan?"
"Kin ce."
"Isa ne ban yi ba ko? Saboda bani da wannan mutumcin a idonki."
Maganarta ta biyu babu hargagi balle daga murya. Amma zukatan fitinannu cikin 'ya'yan nata sun girgiza. Duk abinsu bata taba nuna musu wannan bangaren nata ba. Sai suka zata duk wani rashin albarkarsu za ta karba saboda tana son su.
"Wallahi Inn..."
Katseta tayi da cewa "Duba ta."
Zara ta kwanta da tsoron kada fadan ya dawo kanta. Uwani na dubawa ta ce sai an sake dinkin. Hawaye ta soma fitarwa kawai saboda tuna irin azabar da tasha a 'yan kwanakin da suka wuce. Tana ji Innayo ta ce da Uwani ta je ta dauko kayan aikinta. A gurguje ta fice. Duk da dan akwatin tafi da gidanka da take yawo dashi yana mota ita dai burinta ta ganta a waje. Bayan fitarta ne Zara ta kasa daurewa ta kira Innayo a raunane.
"Innayo."
Bata amsa ba ta fita daga dakin. Wurinsu Hasiya ta tafi ta ce komai suka gyara su adana shi suna sai wani satin.
"Wani abin ne ya faru?" Cewar Maimuna.
"Maijego babu lafiya. Banda ma sun dorawa kansu waye yake wani taron suna a haihuwa ta biyar?"
Hasiya kamar bata yarda ba. Dama ta kula da wani irin yanayi da Ayaah ta fito dashi kamar tayi kuka. Ana haka Uwani ta dawo. Bata cewa kowa komai ba ta shige ciki.
Innayo ta bi bayanta ta rufe kofar falonta. Kafin a fara tasa Zara kiran Alh. Unais. Sai da tayi masa kira hudu sannan ya dauka a wulakance.
"Ina fata ba cewa za ki yi kayan abincin sun yi kadan ba. Sannan ki fadawa Innayo dinnan don Allah ayi abinci maidadi saboda dangina da zasu zo da na Laurat. Ayi abin fita kunya."
Taji zafi kwarai da jin kalamansa. Sai dai kuma har duniya ta nade Zara bata da wata uwar sama da ita. Babu mai daukar wannan bakin halin duk son da yake mata ya ce zai jure ya cigaba da kulawa da ita irin na uwa da 'ya. Ita din cw dai dolenta.
"Innayo dinnan ce ba Zara ba. Ka fadawa danginka suna sai wani satin. Idan kuma za ku iya hakura gabadaya zai ma fi."
A hanyar komawa gida yake daga kasuwa. Yana baya direbansa yana ja. Jin muryar Innayo ba shiri ya tashi zaune daga kashingidar da ya yi.
"Wani abin ne ya faru?"
"Ba ta da lafiya."
Ya san Haj. Fatakwal ba za ta lamunce ba shi yasa ya ce zai sanar dasu yadda idan sun zo ba za su takura mata ba.
Gaban Zara yana dukan uku uku ta ji Innayo ta cigaba da cewa
"Baka fahimceni ba kenan. Kwata kwata bana son danginka su zo gidan nan gobe. Bayan wulakancin da ku ka yi min akan zamanta a asibiti da rashin lekowar waninku dubata sai ace za a zo suna? Ga kayan abincinku nan 'yan uwanta sun muku kara sun gyara. Ka aiko a dauka tunda matar taka bata nuna maka mutumcin mazaunan gidan nan ba balle ka zo da kanka. Sannan kasa a kawo mata 'ya'yanta su dubata."
Dammmm...Zara da Alh. Unais da ma Uwani dake tsaye a gefe kowa yaji gabansa ya fadi.
Tsoro ya ji kada ta ce ya sakar mata 'ya ya soma bata hakuri. Yana son Zara har yanzu.
"Kiyi hakuri zan zo. Amma don Allah ayi sunan saboda Hajiyata."
Wato saboda Hajiyarsa. Matar da bata san ciwon tata 'yar ba.
"Suna kam babu shi Unaisu. Idan kun zo ma ba za ku sameta a gidan ba"
Ta kashe wayar ta ce da Uwani tayi aikinta.
"Kinga ya soma warwarewa ne Innayo. Ko in ware duka na sake sabo?" Uwani ta tambaya gudun yin laifi.
"Ni da ban taba shiga aji ba ina zan sani? Ke dai kiyi aikinki zan biya."
Uwani ta san gatse ne. Yau bata san me ya faru ba amma tsoron bacin ran Innayo take irin wanda bata taba ji ba a baya. Haka nan dai ta duka tayi aikinta gabanta yana faduwar da bata san musabbabinsa ba.
Kafin a gama Zara ta kusa suma. Ihu ko surutu irin na mai jin jiyo bata sami zarafin yinsa ba. Tsoron sake batawa mahaifiyarta rai take yi. Wani abu da ya dade bai ziyarci zuciyarta ba. Innayo na ganin yadda take cije lebe da damkar gefen katifa sai ta matsa kusa da gadon. Hannunta kadai ta rike tana girgiza mata kai da rarrashi amma sai taji salama. Ciwon ya ragu sai wani irin abu da take ji game da matar da ta kawota duniya. Hawaye ne ya balle mata bata sharesu ba kuma babu niyar tsayuwarsu. Fuskar nan da ta tashi tana gani a bakin murhu a yau ta maye mata gurbin duk wata allurar kashe ciwo. Bata sani ba ko rashin kula ne amma kamar yau ta fara tantace komai na fuskar Innayo. Idanuwanta sun fada ciki ana gani za a gane wahalar rayuwa ce ta kawosu. Farar fatar da suka gada ta dusashe sosai. Wanda ya san kuruciyarta kadai zai iya bada shaidar ita din fara ce a da. Ga layukan girma don ba a ce tsufa ba sun zane mata fuska. Hannun da ta riketa dashi kuwa ba ka ce na mace bane. Babu kanta kamar da tunda ta daina kaso tamanin cikin ayyukan da take a baya. Amma fatar ayi wani irin tauri kamar na kakkarfan namijin da ya sha aikin hannu. Hannuwa ne da suka raini tare da aurar da mata har guda tara! Mata da masu kudin cikinsu suka juyawa hannun alkhairi baya. Matan da ita Zara take cikinsu! Kawai sai ta fashe da kuka. Ta sake yiwa hannun Innayo wani irin riko tamkar tare da rayuwarta yake tafe. A haka baccin wahala ya dauketa ga gumi ya wanke mata fuska.
Uwani ta gama tattara kayanta ta ajiye pain reliever din da Zara za ta sha idan bukatarsa ta taso. Tsakar gida ta fito za ta tafi daidai lokacin da Ummakati ta shigo gidan da sallama. Ita ma tunda Munzali ya yi mata magana akan gyaran zumuntarsu da 'yan uwansu ba karamin dadi taji ba. Baudadden miji gareta sai da kyar da sudin goshi ya barta ta fito barka da yamman nan.
Ta tsaya suna gaisawa Asabe ta jiyo muryarta tayo waje. Bata ga dalilin wannan shishshigi da 'ya'yanta suka fara ba cikin kwanakin nan. Fadan da ta taso yiwa Ummakati bai samu ba ta tsaya kallon wasan kwaikwayo a cewarta.
Innayo ce tayi saurin fitowa kafin Uwani ta bar gidan.
"Nawa ne kudinki?"
Sai taji kunyar idanun dake kansu. Ko babu su ita yau tsoron Innayo din ma take.
"Ki barshi ba zan karba ba."
Innayo ta hade rai sosai ta ce "Idan baki tsaya kin karba ba daga yau in kin zo gidan nan kar ki kuma shigar min daki."
Maimuna sai ta tashi da sauri "Subhanallahi. Innayo me ya yi zafi?"
"Kar ku saka min baki." Ta kuma kallon Uwani wadda duk ta tsure "nawa ne?"
"Dubu shabiyar. Don Allah ki barshi Innayo." Ta ce kamar za tayi kuka. Kowa ita yake kallo kamar basu santa ba.
Innayo bata saurareta ba ta kwance gefen zaninta. Dubu takwas ta hado dama ta san bata da shabiyar din. A rashin hankali na Uwani idan ta so kin karba da sai ta yanko kudin kasa sosai. Ita dai Innayo sai ta kalli Hasiya da Maimuna,
"Nawa zan samu wurinku?"
Hasiya ta so cewa kar ta biya sai dai ta kama bakinta. Dubu uku ta bayar ta bar dari biyu da zasu yi kudin adaidaita sahu ita da Ayaah. Maimuna ta bada dubu biyun da Innayo din ta bata dazu. Samarin 'ya'yanta kamar hadin baki kowa ya ciro dari biyar kudin da aka basu sallama na aikin kafinta da suke koyo. Murja ta dauko jakarta ta mika dubu daya. Ummita dari bakwai gareta a hannu ita ma ta mika. Ummakati ma da bata san silar abin ba ta bayar da dubu biyu. Ayaah ta bada dari ukun da ita kadai ta rage mata.
Uwani ta kasa motsi balle magana. Kannenta ne da 'ya'ya su duka amma haka suka hada kudin domin fitar da Innayo kunya. Da taki mika hannu ta karba sai Innayo ta kamo hannun ta dora mata kudin a tsakiya.
"Ai na ce miki zan biya ki. Allah ba zai bari naji kunya ba."
Ranar farko da Uwani ta ji muguwar kunya kenan a rayuwarta. Abin da ya faru yanzu shi ne asalin kaskanci a gareta. Tafi kowa kudi cikinsu. Amma sun hada sun bata. Bata iya kwakkwaran motsi ba sai da aka fara kiraye kirayen sallar magariba. Sannan ta farga ashe duk sun watse. Babu kowa a tsakar gidan duk suna falon Innayo sai ita kadai. Kwalla taji tana neman zubo mata tayi saurin sharewa ta fita a fusace.
Innayo sai ta saki labulen dakinta ta koma ta zauna. Tayi minti goma tana karantar yanayin Uwani. Addua take Allah Yasa shiriyarta ce za ta zo ita ma. Ko kusa bata ji dadi abin da tayi mata ba. Sai dai Uwani tana bukatar sabon karatu game da sanin hakki da darajar mutane ba ma mahaifiyarta ba ita kadai. Kudi sinadari ne amma ko kusa ba shi ne rayuwa ba kamar yadda ta zata.
"Kwarankwatsa dubu na gaji shika nake bida. Wannan wane irin aure ne? Ki don daga kauye ka auroni?"
Tashin hankalinta yafi tsoro akan na uwargidansa. Bai hango wani dalili nan kusa da zai sa ya saki Ummule ba. Balle yanzu ma da take dauke da cikinsa. Zaunar da ita ya yi a gefensa yana bata hakuri ta soma kuka. Zabi biyu ta bashi kuma kowanne mai tsauri ne a gareshi.
Salihi ya san cewa ta fi shi gaskiya sai dai kuma ya rasa yadda zai bullowa lamarin balle ya iya fadawa Uwani cewa ya yi mata kishiya watanni biyar da suka gabata. Yana jin kwarewa wurin iya masifa da kaskantar da mutum da Uwani take gwada masa ne suka mayar dashi lusarin namiji. Ba ya iya sakata ba kuma ya iya hanata. Dama kuma shi mutum ne mai yakana da hakuri. Ko kadan baya son hayaniya. Yana da rufin asiri daidai gwargwado, wannan ne ma yasa zaman nasu ya yi karko. Daidai da ashana Uwani bata taba karar saya idan bai bayar da kudin ba. Ita fa a dole ba za ta yi rayuwa irin ta Innayo ba. Miji ba zai kwanta ya mori arzikinta ba. Ita da kyautatawa ta miji da mata sai suka yi hannun riga. Babu wata riba cikin aurensu da zai d'orar banda yaran da suka haifa guda hudu. Su ma yaran bata basu mahimmanci kamar yadda take bawa aikinta. Tsabar son kudi a asibitinsu duk wadda bata son yin aikin dare kudi kawai za ta bata tayi mata. Haka suka tashi babu shakuwa tsakaninsu da ita. Shi kuma Salihi babu kulawa daga matarsa.
Watarana anyi jinkirin biyan albashi ya roketa bashi zai biya kudin makarantar yaran. Yana dan yin rance wurinta amma wannan kudin yafi na ko yaushe yawa. Kamar ba za ta bashi ba tana ta kiran babu don kada ya soma saka ido akan abin da take tarawa. Sai da yaran suka yi sati a gida, gashi ta dauki hutun shekara. Rashin sabo da zama dasu sai take jin sun caza mata kai. Hutun da take nema babu. Hayaniya taki karewa. Ba shiri ta ce ta dauki adashi ya zo ya karba. Sunyi akan ana albashi zai biyata sai gashi har an soma zancen jarabawar karshen zangon. Uwani panicked! A zatonta ya yi sama da fadi da kudinta. Ai kuwa ta tayar masa da hankali. Shaf ta manta ya aurar da kannensa biyu mata a wannan tsukin lokacin. Albashin nasa ma bai ishe shi ba sai da ya ci wani bashin. Ita dai kudinta kawai.
Takanas ta taka har gidansu. Mahaifiyarsa tayi mamakin zuwanta ta kuma tsorata. Saboda Uwani bata zuwa sai da dalili. Ba kunya ta fada mata halin da suke ciki.
"Wallahi idan bai bani a watan nan ba hukuma za ta shiga tsakaninmu. Ni ba irin sakarkarun matan da ake yiwa wayo suyi ta bautawa miji da 'ya'ya a banza bace."
Kwantar da kai tayi ta bata hakuri. Ita kuma sai wani jijjiga jiki take kar ta sassauta a fara kira mata ta yafe tunda mijinta ne.
"Gobe in sha Allahu za a kawo miki kudinki Uwani. Nawa ne?"
"Dubu dari biyu da tamanin da hudu."
"Kije gida ba zai gagara ba in Allah Ya so."
Babu sallama ta fice abinta. Mahaifiyar Salihi bata tsaya nemansa ba tunda ta san lokacin da ya ranta da dalilin da ya hanashi biya. Ranta dai ya baci sosai. Sarkar zinarenta ta karshe da maigidanta ya bata kafin rasuwarsa ta dauko daga ma'ajiyarta. Kai tsaye gidan Dillaliyar unguwarsu ta nufa. Haka ta bata sarkar jingina ta karbo bashin dubu dari uku. Da Salihi ya zo da yamma ta kulle a leda ta bashi.
"Idan Allah Ya hore maka da wuri ka kawo kudin na maidawa Dillaliya."
Sunkuyar da kai ya yi cike da kunya da takaicin Uwani. Karshe ma yaji kamar zai zubar da kwalla. A tausashe mahaifiyarsa ta ce,
"Kada ka bari zancen nan ya tsaya maka rai. Maganar guda ce. Ba zan saka ka saki matarka ba amma indai ka haifu za ka kara aure. Ka nemo 'yar masu mutumci ka aura (haka kawai 'ya'ya su dinga janyowa ana aibata dattakon iyayensu)."
Ya nuna mata ya haifu kuwa. A cikin wata guda ya hada kudin nan ya kai aka karbo mata sarkarta. Tayi ta saka masa albarka kuwa. Bayan wata uku ya ce su tura kauyen 'Yar gaya ya sami mata.
Ita da 'yan uwansa basu kyamaci 'yar kauyen da ya kawo ba. Yarinya ce mai saurin shiga rai da faram faram da jama'a.
Matsalar farko da suka fuskanta shi ne rashin samun kwarin gwiwar fadawa Uwani zai yi aure har aka yi. Tsoron tashin hankalin da za ta yi masa yake ji. Sai gashi ya buge da rokom Ummule tayi hakuri har ya sami damar fada. Gida ya kama mata a wata sabuwar unguwa. Daga office yake biyawa amma bai taba kwana ba. Haka take ta hakuri.
Aurensu na da wata biyu barayi suka haura mata cikin dare. Tsananin firgita da tayi yasa ta suma. Sun kwashe kayan kallo da kudi amma basu tabata ba. Koda ya iso gidan bayan anyi masa waya daga makota tana da zubar jini. Ashe ciki gareta basu sani ba har ya zube. Musabbabin rigimarsu ta yanzu kenan. Ta roki ya raba musu kwana a kalla barayin da aka san 'yan unguwa ne zasu ga namiji na kwana. Idan ba zai iya ba kuma za ta koma gidansu. Da kyar ya lallabata da alkawarin zai fadawa Uwani yau ya tafi.
Yana fita Ummule ta zari mayafi tabi bayansa a adaidaita sahu. Ba za ta yarda ta zauna tana cutuwa ba. 'Yancinsu ita da dan cikinta take neman karewa.
Samari ne su hudu cikin wani tafkeken daki wanda ya wadata da kayan alatu. Daki ne wanda uku daga cikinsu suke haya a ciki a matsayinsu na daliban jami'ar Bayero. Uku a cikinsi babu wanda zai kai shekara ashirin da biyar. Tun daga suturarsu da ta juyawa mutumci baya har zuwa wayoyin hannuwansu za ka san 'ya'yan masu hannu da shuni ne. Kawunansu babu kyawun gani kuma wai nan duk a cikin gayu ne. Cikon na hudun nasu dan saurayi ne wanda da alama sun girme shi. Shi riga da wando na yadi ne a jikinsa. Ko kadan babu alamun shashanci tare dashi sai damuwa shimfide a fuskarsa. Daya daga cikin samarin ne ya tsaya a gabansa yana magana yana jejjefa hannuwa kamar mai rapping. Wandonsa ya kusa gwiwa sai na cikin da ya bayyana cikin wani salon wulakanta kai mai suna ass-down.
"Oh boy ya ka ke mana yawa ne? Nifa gaskiya bana son eh-yane, ai ka gane. Kawai idan maiko ba zai samu ba ka ware. Clique (kungiyar abokai) dinmu ba na yawa-boys bane."
Tashin hankali ne ya kara bayyana a fuskar yaron da yaji sauran suna cewa ya tafi. Ya matsantawa kansa son yin abota dasu saboda duk makarantar babu masu tashe irinsu. Kowa ya sansu kuma yana shakkarsu. A gidansu shi da 'yan uwansa tamkar babu wanzuwarsu. Mahaifiyarsu neman kudi tasa a gaba. Babansu bashi da katabus sai tsoronta. Gashi bata nuna musu shiga dangi ba. Basu saba da kowa ba balle su ji dadin mu'amala da makusantansu.
Yara kala kala ne. Akwai masu son ayi feeling presence dinsu idan suna waje. Suna son a yaba musu ko ayi musu fada. Su dai ka nuna ka san dasu kuma suna da mahimmanci a wurinka. Idan suka kasa samu a gida sai su fita. Irin haka ce ta faru da Mubasshir Salihi. Rayuwar gidansu babu dadi. Daga karatu sai karatu. Tun suna yara idan suka fara wasa Uwani ke hanawa tayi ta fada har suka daina yi da junansu. Yanzu shiga dari fita dari sai dai ka samesu kowanne rike da waya kamar ibada.
"Nawa zan kawo to?" Ya tambayi mai yi masa magana.
"Contribution ne kawai na daidai kudin gidansu mutum.." sauran suka kwashe da dariya "kada dai ka kawo kasa da 50k domin zamu tafi da babes. Ka san mata da son ayi musu barin kudi."
"Shike nan, zan kawo."
Fita ya yi da rawar jiki kada a fasa zuwa yawan bude idon da suka shirya zuwa Tiga dam dashi. Yana fita suka kwashe da dariya suna tafawa. Mubasshir ba ajinsu bane. Za dai su tatse shi da kyau su yar ne kawai.
Babur dinsa ya hau wanda da kyar da sudin goshi Uwani ta saya masa. Shi ne danta na fari. Yana level one.
Ya san yau aikin kwana gareta. Kannensa mata duka ukun suna makarantar kwana. Da mukullinsa ya bude gidan. Kofar dakinta a kulle da mukulli. Guntun tsaki ya yi ya dauko spare wanda abokan nasa suka sa ya yanka. Ashe ga ranarsu nan. Hankalinsa a kwance ya dinga sauke mata akwatuna yana bincike saboda bai sa ran dawowarta yau ba. Babansu ma kwanakin nan idan tana da aikin dare baya dawowa da wuri. Wani envelop ya samu a can kasan wardrobe dinta ya dauko ya zazzage akan gado. Bai san ko nawa bane don yawan bandiran da ya gani. Ga kuma kananun box din sarkar gwal guda uku. Dariyar shakiyanci ya yi da ya kwatanta bawa duk yarinyar da za a hada shi da ita a Tiga da ita matsayin kyauta. Ya san sai ya doke ragowar abokan nasu wurin samun fada da kulawa.
Mubasshir yana dakin Uwani yana barna ta iso gida. Tana gyara parking Salihi ya iso. Jira yake ta gyara motar shi ma ya ajiye tasa sai ga adaidaita sahu ya tsaya a jikin katangarsu. Ummule ce ta fito ta nufi motarsa tana cewa ya bata dari uku ta biya mai adaidaita sahu.
Uwani da ta dawo gida da bakincikin abin da ya faru a gidan Innayo sai ta tsaya tana kallon ikon Allah. Yarinyar da ta fito daga adaidaita sahu murmushi take yi. Salihi kuwa a firgice yake!
TAMMAT.
MU HA
U A KASHI NA BIYU.
Times New Roman
Times New Roman
Symbol
Symbol
Arial
Arial
alibri
Calibri
SimSun
Cambria Math
Cambria Math
!%),.:;>?]}
$([{
SummaryInformation
DocumentSummaryInformation
WpsCustomData
M2006C3LG
TECNO LD7
WPS Office
f07080c5e67148cc85ac090e26dfe502