BABI NA SHA BIYAR.
Uwa Uwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 33 min read
"Ya naga kun yi carko carko kamar masu barin gari, lafiya?" Alh. Rabi'u ya ce idanunsa na binsu daidai da kallo. Baki ya saki da ya hango alamun jariri ne a hannun Maimuna ba kunshin kayan da ya zata da farko ba. Tambayar mai haihuwa cikinsu ya yi Uwani ta nuna Zara.
"Shi ne ki ka taho nan maimakon ki wuce gidan mijinki daga asibitin? Me za ayi miki a nan wanda ba za ki sami dubunsa a gidan Alh. Unaisu ba?"
Innayo tayi kwafa hade da murmushi mai ciwo.
"Dama me za ta samu a gidan uban da bai san ci da shanta ba tun zuwanta duniya bare a kai ga batun hidimar aure?"
Magana ce irin wadda bai taba ji daga gareta ba, shi yasa shigarta kunnuwansa ta gigita shi. Sake kallonta ya yi ko zai ga ta inda ta kuskure da wadda ya sani mai hakuri da kawar da kai tsayin shekaru. Ita kuwa Zara ta kalla.
"Ki kira mijinki ko direbanki ko ki tura a samo miki abin hawa ki tafi."
Zara ta sake fashewa da kuka ta koma rokon Alh. Rabi'u.
"Baba ka bata hakuri na zauna a nan kamar yadda su Hajiyan Fatakwal suka ce. Idan na tafi yanzu wallahi matsala zan samu. Sun ce lallai sai na zauna nayi wankan jego..."
"Laifi kika yi? Ko sakin ki ya yi?" Ya tambayeta cikin tashin hankalin kalamanta da na Innayo.
"Saboda na sake haihuwar mace.." ta fada a kunyace murya a kasa.
Maganar ta shigi Innayo sosai don ji tayi kamar da ita ake. Ita ce ake gorantawa haihuwar mata.
Alh. Rabi'u sai ya yi nufin burge Innayo yau daya dai tunda ya fahimci ranta a bace yake. Fada ya soma ba ji ba gani.
"Amma wannan yaro anyi dan iska. Ita macen ba 'ya bace?"
"Ta ina mace take 'ya? Ai ka barshi ya wulakanta matarsa yadda aka yiwa uwar da ta raina lokacin da take ta haifar mata. Ita kuma ka barta ta koma inda ya fi gidan mahaifinta dadi. Banda abinka ai duniya tafi bagaruwa iya jima."
Juyawa tayi ta shige dakin baccinta ta barsu a tsatstsaye su da mahaifinsu. Yana son cewa wani abu domin kallon neman agaji suke yi masa sai dai bai saba ba. Matsayinsa a gidan suna ne kawai. Ba ya bi ta kan yaran sai bukatarsa ta tashi kamar yadda ya yiwa Salima da Hasiya.
Basu bar wurin ba wani almajiri ya ce ana sallama da Zara. Alh. Rabi'u sai ya leka a zatonsa mijinta ne. Maimakon ya ganshi sai direba ya gani an aiko shi da kayan tea, ruwan roba da maltina masu yawa. Zuciya ta kwadayi sai ya basu hanya suka fara shigo dasu. Kafin su gama Munzali ya dawo. Tasa motar ma shake take da duk wani kayan bukatar maijego.
"Meye wannan?" Ya ce da yaci karo da ledar kayan tea din. Madara da milo manyan gwangwani bibbiyu. Sugar na kwali guda hudu sai su ruwan.
Alh. Rabi'u da sauri ya ce "Mijin Zara ne ya aiko mata. Ku shiga dashi falona saboda 'yan barka kada su gani ayi ta hada shayi ba kai ba ...."
Ai kuwa Munzali ya hasala. A iya saninsa yana bawa mahaifinsa kudin da bai ci ace gwangwanin madara zai daga masa hankali ba. Da karfinsa kuwa yasa kafa ya yi ball dasu. Direban da ya kawo da almajirin daya taya shi shigo dasu suka saki baki. Maimuna da Hasiya kuwa hakan ya musu daidai.
"Ka dauka ka mayar ka fada musu nan ba gidan matsiyata bane. Zara kuma ta dawo gida kenan. Ita dashi sai ya zo gaban mahaifiyarta ya bata hakuri. Ka ce masa wannan sakon UBAN Zara ne!"
"Ni?" Alh. Rabi'u ya ce yana dan ja da baya. Wannan ai sanadi zai masa ya toshe kofa daya ta arzikinsa. Ya kalli direban ya ce "kai wallahi ban fada ba. Alh. Unaisun nan ba wani ganin girmana yake ba za ka janyo min matsala dashi" ya kare yana hararar Munzali.
Kallon tsanar da bai yi niyya ba ya jefawa mahaifinsa sannan ya kalli Zara.
"Ke malama ki fa daina wannan kukan. Idan kin ga kin koma gidan wannan mara mutumcin to da yawun Innayo."
Ransa na kuna ya fita ya nemo masu taya shi kwashe kayan tasa motar aka shiga dasu ciki. Uwani na kallon wannan dirama yadda Innayo ta tsame hannu akan Zara da kuma irin rokon da Maimuna, Munzali da Hasiya suka yi ta fama har ta kyaleta. Hada kayanta tayi ta shiga motarta ta bar gidan kafin a gama daidaitawa. Ita kadai a motarta take magana kamar sabon kamu.
"Dole ma na karasa gini saboda bacin rana. Ji yadda Innayo take mata kamar ba 'yarta ba. Ita ma Zara banza. Da tana da hanyar samun kudi wallahi tafi karfin wannan wulakancin. Hummm. Ba gashi Munzali na shiga maganar Innayo ta sauko ba?"
Allah Sarki Innayo. Duk barazanarta bata fatan kora Zara inda bata da daraja. Tabbas ranta ya baci amma tauna tsakuwa kawai take yi. Ta jira asa baki a bata hakuri domin Zaran ta gane da gaske take yi ne. Magiyar su Munzali taje mata akan gaba ne ba wai don nauyin aljihun dayansu ba.
'Yar karamar jakarsa mai cin kayan da basu fi seti uku ba ya zuge sannan kamar wanda ya yi aikin karfi ya zauna akan gadon a gajiye. Rashin kuzarin zuciyarsa ne ya harbi duka gabobinsa har ya haddasa masa wannan yanayin kamar na mai ciwo. Babu sauran jirgi mai zuwa Abuja yau. Shi kuma halin da yake ciki ba zai barshi yaji dadin tuka mota zuwa Abujan ba. Kansa yaji ya sara kamar an buga guduma lokacin da Hanne ta shigo dakin ta buga kofar da karfinta. Damuwa ce fal a ransa ya rasa wanda zai iya fadawa domin ya sami mafita.
"Ashe daki ka shigo ina ta faman jiranka na zata kana wurin Munzali."
Kansa ya rike da hannu biyu saboda magana ma kara masa ciwo take ga wayar Shazali dake shigowa babu kakkautawa. Hanne bata kula da yanayin nasa ba ta soma fada masa tasa an kawo mata mai-aiki ya kawo kudin sallamar wadda ta kawota.
Da kyar Abbati ya iya bude bakinsa ya ce "yaushe muka yi dake zaki dauki mai-aiki da har zata zo ban sani ba?"
Tabe baki tayi kafin ta ce "tohhh, daukar mai aikin ma sai na fada maka? Naga ba sabon abu bane tunda dama akwai tafiya tayi."
Abin da ke ransa yafi karfin wata rashin kunya da Hanne za ta yi masa. Kada kai kawai ya yi ya bata kudin da ta tambaya sannan ya tashi.
"Abuja zan tafi yanzu. Ban san kwana nawa zan yi ba amma bana sa ran yin sati in sha Allahu."
"Adawo lafiya" Hanne ta ce hankalinta yana ga kudin da take kirgawa.
Shi ma bai kulata ba ya dauki jakarsa ya fice. Sai da ya zauna a mota ya saka wani hadadden bakin gilas sannan ya tayar ya fita daga gidan. Ya kusa Unguwa Uku wayar Munzali ta shigo masa. Gidan mai ya shiga ya bi gajeren layin dake ciki sannan ya gyara murya ya amsa wayar.
Munzali da shigarsa gida kenan "ina kaje ne? Na dawo babu motarka."
Abbati ya dan kaurara murya yana murmushi "kai fa ka fiye naci. Yanzu daga baka ganni ba sai kira. Wannan idan kayi aure matarka ta shiga goma bama uku ba."
"Naji. Ni dai ka fada min inda kaje. Wallahi ina ganin babu motarka gabana ya fadi shi yasa na kira ba wai don na damu da kai ba. Banda ni ma waye zai iya zama da masifaffe. Ka wani zama mafadacin karfi da yaji kwanakin nan. To dai ina kake in zo?" Munzali ya yi maganar yana shiga motarsa.
Dariyar da Abbati bai son yi ce ta kubuce masa har Munzali yaji sautinta.
"Ina hanyar Abuja."
"In kaje ka gaida Zuma rock."
Ya san bai yarda ba sai ya rantse masa tare da fadin karyar da ya shirya tunda Shazali ya kira shi kwanaki biyu da suka wuce.
"Chief Harrison ke nemanmu. Shazali ya yi masa bayanin mun daina yaki yarda. Shi ne yace gara daya daga cikinmu yaje muyi masa bayani baki da baki. Wai a haka yana iya zargin ko hadin baki ne muka yi da abokin nan nasa da suka yi fada."
Saboda yadda yake fitar da maganar daki daki da sanin cewa karya ce ya sharo har wani irin bugu yake jin zuciyarsa tana yi. Da wahala idan akwai watarana da suka taba yiwa juna karya shi da Munzali.
Munzali ya saurari dogon bayanin amma abu daya ne yafi daukar hankalinsa. Hade girar sama da kasa ya yi kamar Abbati na kallonsa ya ce
"Wait! Ba mun ce ko waya ba za ta sake hadamu da Shazali ba? Menene nasa na kiranka yanzu?"
"Na fada maka..." Abbati ya soma fada yana jan motarsa gaban bututun zuba man.
"Yes ka fada naji amma ban yarda ba. Haba Abbati! Shazali dan is** ne kuma gogaggen makaryaci. Ka sani ko wata manakisar ya shirya maka tunda ya san Chief yana mutuwar sonka."
"Nima nayi tunanin haka sai na ce gara naje dai muyita ta kare dasu kawai." Shi ma da yake maganar ba shigarsa take ba saboda raunin hujjar da ya bayar. Da wane baki zai fada masa cewa kwanaki biyu kenan da ya sami alert mai tsoka kuma ana jiran yaje ya yu aikin kudin?
"To amma me yasa baka fada min ba? Me yasa kuma baka jira mun tafi tare ba?"
Abbati sai ya amsa masa da cewa baya so ya kawo masa matsalar da zata sa ya bar 'yan uwansa a yanayin da gidansu yake. Ya dora da nuna masa illar rashin ganin ko mutum daya cikinsu saboda matsayin irin mutanen da suke bi a da.
Munzali tun yana ta kokarin kure shi da tambaya saboda rashin gamsuwa har ya hakura ya amince.
"Don Allah ka kiyaye kar suyi maka wayo don na sanka sarai."
Abbati ya saki rai jin Munzalin ya dauko wasa.
"Ai baka da kunya dama kuma yau tun safe bamu hadu kayi min ba. Zan kira ka idan na kuma tsayawa yanzu zan hau titi."
Sun gama sallama Munzali zai katse kiran ya fasa. Haka nan yake jin wani irin nauyi a ransa.
"Abbati wallahi idan ka bari suka yi wani abu da kai ALLAH YA ISA."
Wani irin radadi ya rike duka jijiyoyin idanun Abbati saboda kukan da yake jin zai iya yi. Tafiyarsa daidai take da cin amanar Munzali, Baaba Mari da tuban da ya kuduri niyar yi.
"Me ka ce?"
"Allah Ya isa na ce. Mutumina kayi duk yadda zaka yi ka fito lafiya. Kaga ka jirani in zo mu tafi tare mana" ya kare a raunane yana mai jin tsoron kada ayi amfani da saukin kan Abbatin.
Sai da ya dake ya iya cewa "kaima ka san zan kiyaye. Idan na sami damar ganinsa a daren yau ma to gobe zan dawo in sha Allahu."
"No..a'a fa. Wane irin da daddare? Ka jira gobe ku hadu koda a restaurant ne da rana tsaka kuma a wuri mai mutane. Ka fada masa komai ka. Kuma ka tsaya akan bakanka ka ce musu mun daina duk aure zamu yi." Ya dan sako wasa yana dariya kasa-kasa "Idan kana dawowa ka jirani a Kaduna inje wurin Diamond girl."
"Wai da gaske ka ke akan yarinyar nan?" Kyakkyawar fuskar Farha na dawo masa tar a idanunsa.
"Tausayinta naji ranar nan. Sai nake ganin kamar irina ce ta tashi uwa bata damu da ita ba. Tunda kai ka fasa da yayarta ni dai ina ciki da kanwar. Allah Ya kiyaye hanya."
Daga haka ya ajiye wayar zuciyarsa babu dadi. Abbati kuwa kwalar idonsa ya hana zuba sai zafin dake yawo a ilahirin jikinsa. Dama can sun san haram suke aikatawa amma shaidan yafi karfin zukatansu. Yanzu kuma da suke jin sun shirya komawa ga Allah sai shaidanu suke neman hanasu. Wani irin abu ne ya soki kokon ransa da ya ayyana a ransa ko bashi da rabon tuba ne? Ko dai baya cikin masu dacewa da rahamar Allah? Zuciyarsa sai ta sare. Karfin gwiwarsa ya ragu. Tsoro da fargaba suka mamaye dukkan tunaninsa. Me yasa suka biyewa son zuciya a wancan lokacin? Ya akayi ya zama daga cikin masu raya zunubin mutanen Annabi Lu
u AS? Tabbas ya san basu da alhakin dulmiyar da kowa amma idan ya tuna sun rayu kwatankwacin rayuwar karuw
a sai yaji ya tsani kansa. Sun bi musulmi sun bi kirista. Manyan masu fada aji a kasar nan duk suna tafin hannunsu domin sun san sirrinsu. Kafin ya isa Kaduna zazzabi ya rufe shi. Tukin gagararsa yake neman yi don sau biyu yana auna arziki bai karawa wani ba. Da tambaya ya samu aka kwatanta masa asibiti mafi kusa da titin da yake bi na fita gari.
DOCTORS HAVEN
Shi ne sunan da ya gani an rubuta kato a jikin bangon dake kallonsa na asibitin.
(Yana daga cikin kokarin Shaidan la'ananne akan bayin Allah ya sarar musu da gwiwa yayin tuba. Ya kan sanyawa mutane hopelessness har kaji kamar tuban ba zai amfaneka ba. A bangare guda kuma Allah SWT zai iya jarabtar bawa da kalubale domin Ya kara masa ladan hakuri da jajircewa wurin tuba. Muhallishshahid shi ne kada mu karaya. Mu dage iyakar dagewa mu tsaya akan bakanmu. Idan Allah Yaso sai mu rayu cikin zunubi kuma Ya saukaka mana tuba da komawa gareShi. Sannan rahamarSa ce idan Ya so ya kawo mana nau'ikan jarabawa akan hanyar tubanmu domin mu kara imani. ALLAH SHI KADAI NE BASHI DA ABOKIN TARAYYA. Ya bamu ISTIGFARI domin Ya daukaka darajarmu rana gobe kiyama. Idan mun tsaya da ikilasi to lallai Allah zai bamu mafita da izininSa.)
Mami Khadija na daki tana aikin tsara slides (power point) na lecture din da take dashi da 'yan masters sati mai zuwa taji kamar ana kiranta a waje. Gilashin idonta ta tura ciki sosai ta tashi daga gaban teburin aikinta da sauri.
"Sauda? Farha? Mardiyya? Kai waye yake min wannan kiran ne kamar ana kuka?"
Hanyar fita zuwa bangarensu tabi inda take jin muryoyin. Sai da tayo kusa ta fahimci Sauda da Mardiyya ne suke kukan. A bakin kofa taci karo da Sauda wadda ta taho domin kiranta. Nan kuma idanunta suka sauka akan Mardiyya tana girgiza Farha tare da kiran sunanta cikin kuka. Da gudu gudu ta karasa gabansu ta durkusa a wurin.
"Me ya sameta?"
"Bamu sani ba Mami. Daga duba status din Yumna ta fadi." Cewar Mardiyya hannunta na rawa wurin shafawa Farha ruwa a fuska.
Ran Mami Khadija ya baci sosai ta ce "Yumna? Gaya min yadda abin ya faru. Sauda dubo min mazan nan mu kaita asibiti."
Bayan fitar Sauda ne Mardiyya ta fadawa Mami abin da suka sani.
"Na duba banga hoton ba amma na tabbata ganinsa ne ya sumar da ita."
Fuskar Mami tamkar bata taba murmushi ba ba
e dariya ta tashi tsaye. Lilu ne ya shigo lokacin Farha ta bude ido da kyar.
"Ku bani wayata" ta ce a tsorace tana gudun kada su ma su gani.
Yadda tayi ya tabbatarwa Mami Khadija cewa lallai hoton ya shafi mahaifinsu. Wayar ta mika mata don ta sami saukin rai har tana nuna mata kamar ranta ya baci ganin bata da lafiya amma tana neman waya. Farha bata ce komai ba sai kai da ta sunkuyar. Kunyar mahaifiyar tasu take ji sosai da tausayi. Ga wata irin tsana mara takunkumi da take hauhawa a zuciyarta ta mahaifinsu.
Mota ta ce su wuce ta tafi dauko mayafinta a daki. Ta dauko jakarta ta saka wayarta a ciki. Ji take kamar ana caccakarta da allura saboda bakin cikin halin da Alh. Tahir ya sakasu a ciki. Albarkacin 'ya'yan nan yaci kuma yake kan ci da tuni ta bar gidansa. Ba za ta yarda ya lalata mata tasu rayuwar da rashin kamun kansa ba.
Doctors Haven asibitin da suke zuwa duka gidan Lilu ya kaisu. Farha da kafarta ta shiga kuma tana ta rokon Mami akan su koma gida.
"Zan saba miki idan ki ka sake magana Farha."
Bata sake cewa uffan ba har aka kira sunan file dinsu suka shiga wajen likita. Abu na farko da likitan ya fara gani shi ne jininta dake barazanar haure mizanin zaman lafiyar dan Adam.
"Hawan jini nema yake ya tashi daga ciwon manya zuwa na kowa da kowa."ya ce a kokarinsa na yiwa Mami Khadija bayani "ki saka mata ido ta cire damuwa daga ranta kada a gaba ya zame mata ciwo."
"In sha Allahu zan kula doctor. Nagode."
'Yan rubuce rubuce ya yi a takardar gabansu ya mikawa Farha takardar. Magungunan da zasu saya ne ya rubuta.
Shiru suka fito babu mai magana sai hannunta da Mamin ta rike. Gani take kamar idan ta saketa damuwar dawowa za ta yi har ta kuma sumar da ita.
"Jeki mota ki huta na karbo magungunan."
Muryarta can kasa duk tayi laushi ta ce "zan iya Mami ki je ki zauna."
Lilu yana bangaren da aka jere kujeru ya hangosu ya taso. Mami ta ce ya tafi da Farha mota su jirata. So take kawai su bar inda take ta samu ta fito da zahirin halin da zuciyarta take ciki babu rufa rufa. Tana kallo suka sauka daga matattakalar kofar fita waje sannan ta sami wuri ta zauna maimakon sayen maganin. Hawayenta ta bari suka sauko a lokacin da ta sanya fuskarta a kan tafukan hannayenta. Yana daga cikin abin da take gudu ace duka 'ya'yanta sun san halin mahaifinsu. Sai gashi bayan Suhaib ga dukkan alamu Farha ma ta sani yau. Rayuwarta da ta sadaukar saboda karesu tana shirin zama shirme da bacin lokaci muddin aka tafi a haka. Yaranta zasu daina ganin girman mahaifinsu. Tarbiyarsu za ta tawaya domin yana da hakkin matsayin uba a wuyansu. Wace irin rayuwa zasu yi a gaba? Wane irin mutum Allah Ya jarabceta da aure? Yana da damar karin aure. Ga kudi. Kai idan ya so ma ya sake su duka ya sake sabon zubi a gidansa da dai wannan kazamar rayuwa mara fasali.
A cikin motar Lilu ne yake ta damun Farha akan ta fada masa wane irin hoto Yumna ta turo mata. Tausayin yayar tasa yake ji har yana hasashen ko dai mutumin wani ne da Farhan take so a gefe.
Maganar hankali irin wadda bai saba ba yake yi mata tare da ban baki
"Kin san dai babu wanda zai auri matar da ba tasa ba. Ki bar mata shi kawai. Naki mijin fa idan ya tashi zuwa sai Kaduna ta girgiza."
Murmushi tayi wanda ya hade da zubowar hawaye. Za ta barshi ya cigaba da wannan tunanin har zuwa lokacin da kowa zai sani. Iyaka dai bata fata ko kadan wani ya fahimci akwai mummunar alaka tsakaninsu tun a waje.
A lokacin da suke 'yar hirarsu ne kuma idanun Lilu suka kai bakin gate din asibitin. Motar Suhaib ce take shigowa yana waya dasu Sauda masu damunsa yaya jikin Farha. Motar bayansa wanda ya zata mai ita yana jiran ya wuce ne shi ma ya yi nasa parking din ta soma karar horn da karfi.
Tsaki ya ja da karfi saboda anki daina danna horn din "Zan kiraku Sauda" ya jefa wayar gefensa ya kauce.
Har ya gama parking babu sassauci a karar horn din. Mutane suka fara kallon motar ana 'yan surutai. Kimanin minti biyu a tsakani da suka fahimci ko motsi motar bata yi sai hankula suka fara tashi. Suhaib yana so ya shiga ya ga halin da kanwarsa ke ciki ya dakata. Shi ya fara zuwa gefen direban ya kama hannun zai bude yaji a rufe. Gashi gilas din da duhu baya ganin komai. Farha da Lilu da 'yan tsirarun mutanen wurin sun firfito an tsaya a wurin. Ta gilas din gaban motar suke iya ganin kan matukinta akan sitiyarin kuma baya motsi.
"Ki koma mota Farha bari mu gani ko zamu iya balle kofar a fito dashi" cewar Suhaib ganin tana tangadi kamar za ta fadi.
Bata san me ya fito da ita ba kamar yadda Abbati bai san ya akayi ya iya daga kansa dake tsananin ciwo a lokacin ba. Sannu a hankali yake dagawa saboda kwankwasa gilas din da ake yi ta kowane gefe ana cewa ya bude domin a taimaka masa.
Sakan daya, biyu, uku...goma, talatin...idanun Abbati suka sarke cikin na Farha suna kallon juna. Bata tabbatar shi ne na diamond plaza ba amma fuskar ba bakuwarta bace. Abbati kuwa mamaki ne ya kashe shi a zaune. Da ace bai ga Lilu yaron da ya fara tsayuwa yin hoto a motarsu ba, da Suhaib wanda ya bashi hakuri da sai ya ce lallai gizo take yi masa. Kai ya girgiza a hankali ya runtse idanunsa sannan ya sake budewa yana kallon inda take. Fuskar da ta zame masa hoton zuciya ya sake gani ta dan yamutsata tare da dafa gaban motar don kada ta fadi. Rana ce ta take sosai mai zafi.
'Uncle Abbati?' Ta yiwa kanta tambayar da sunan da ta lakaba masa lokacin da ya dinga kiranta Ya Farha.
'Bata da lafiya' shi kuma wani sashe na zuciyarsa ya sanar dashi yana mai jin karfi na zuwar masa. Cire lock din kofar ya yi Suhaib ya bude da sauri. Ya zuro kafarsa waje hasken rana na saka shi kare fuskarsa da hannu saboda yadda yaji kamar ta kara masa ciwon kai.
"Lilu kula da Farha kafin mu shigar da mutumin nan ciki"
Sune kalaman da Abbayi yaji matashin da ya bude kofar yana kokarin rike shi ya fada. Dubansa ya kai gareta yaga yadda take takawa a hankali duk da daya saurayin wanda yake tsammanin shi ne Lilu din ya riketa. Takunta da duk wani motsinta ya dinga zama a zuciyarsa tamkar ana zana shi da kakkaifan alkalami. Yana da tarin matsaloli a kansa amma sake ganinta sai ya kankantar da komai. Tubalin dan guntun ginin da ya soma yiwa zuciyarsa katanga daga barin soyayyarta ya ruguje baki daya. Irin wannan coincidence din yafi karfin rainawa. Bai iya dauke ido daga kallonsu ba har ta shiga mota ta kwanta a baya.
Bin Suhaib da wani Security din asibitin ya yi ciki. A hanya suka hadu da Mami Khadija, wata mace da ya gani mai cike da haiba da nutsuwa tamkar mahaifiyarsa Baaba Mari. Wannan kam da gani babu tambaya uwa ce ga wadannan bayin Allah. Fuskarta kamar ba ita tasha kuka ba. Bandaki ta shiga ta wanketa sannan ta goge kwarmin idonta da kwalli ya bata ta daidaita shi. Kallon Abbati tayi wanda ko ba a fada ba ta san bashi da lafiya sannan ta tambayi Suhaib ko waye shi. A takaice ya labarta mata yadda suka hadu ta kalle shi da tausayawa.
"Bari na kaiwa Farha maganin sai naja motar shi kuma Lilu ya jiraka. Ka zauna dashi har ya dan sami kuzari sai ku kira 'yan uwansa." Ta sake kallon Abbati "Allah Ya sauwake kaji."
Tafiya tayi suka karasa reception. A nan Suhaib ya fahimci Abbati bashi da file a asibitin da ya amsawa matar wurin cewa babu amma zai iya budewa yanzu.
"Kiyi masa amfani da namu" cewar Suhaib yana tura mata file din da ta dauko lokacin "idan yana bukatar budewa ayi daga baya. He needs a doctor now (yanzu likita yake bukata)"
Abbati ya yi masa godiya sosai. Da zai shiga wurin likita sai Suhaib ya tambaye shi wanda ya kamata a sanarwa yana asibitin.
"Daga Kano nake kuma Abuja zan wuce. Idan na fito zan kira kanina" ita ce amsar da ya bashi.
Suhaib sai yaji ba zai iya tafiya ya barshi ba. Jira ya yi har likitan ya leko ya ce waye ya kawo Auwal. Tunda bai san sunansa ba sai ya dan yi daburce kafin ta tuna cewa wanda ya rako shi kadai ne ya shiga ciki.
"Gani" ya fada yana mikewa.
"Yauwa Suhaib ashe dan uwanka ne. Koda yake naga file din gidanku. Me yake faruwa ne ake ta zuwa da hawan jini. Nasa is very bad damuwa tayi masa yawa dole zan kwantar dashi don nayi monitoring dinsa."
Bin bayansa Suhaib ya yi. Nan ya tarar da Abbati a zaune amma ya kifa kansa a teburin likitan. Da fitar likitan wayar Shazali ya amsa wanda ya fada masa maganganu masu tada hankali. Yayi haka ne saboda gudun kada Chief Harrison ya nemi Shazalin ya maido da nasa kamashon kudin.
"Ran Chief ya baci fiye da zatonka. Yanzu haka ya tura gidanka na Kano a taho da kai. Mutanen sun tabbatar masa baka gida ya ce a dauko Munzali tunda tare kuke."
Abbati yana da saukin kai. Saukin kan da yawansa ya sanya Baaba Mari gudun tafiyarsa almajiranci. Gashi yau dashi Shazali yake amfani.
A raunane ya yi magana "Na fada maka ina hanya. Gani a Kaduna da kyar na karaso asibiti. Bani da lafiya Shazali." Kausasa murya ya yi duk da bata fita da karfi ya ce "Idan ka shigo da Munzali cikin abin kuma wallahi sai na nuna maka nawa kalar haukan".
Ya san Abbati sarai. Ba zai taba yi masa karya ba saboda shi mutum ne kaifi daya kuma mai yawan kyautata zato. Ba dabi'arsa bace bincike da bin kwaf balle ya gano karyar da ya yi masa. Hasali ma Chief Harrison ya bashi damar kawo masa kowane irin namiji. Da ya ce zai kawo Abbati ne ya kara nasa dubu dari akan abin da ya bashi.
"Tsakaninmu bata baci Abbati. Ka maida wukar. Zan yi masa bayani sai na hada shi da wani."
Suhaib ne ya taimaka masa zuwa dakin da aka bashi ya kwanta. Yana wurin aka zo aka dibi jininsa domin gwaje gwajen cututtuka irinsu maleriya. Bayan an gama an soma yi masa karin ruwa aka hada da allurar bacci. Baccin na fizgarsa Suhaib yana son sake tambayarsa wanda zasu nema ya kula baya cikin hayyacinsa saboda karfin allurar. Likitan ya ce yana bukatar hutu sosai.
Waje ya koma inda Lilu yake zaune akan mota yana jiransa. Mukullin ya cilla masa yana yi masa bayani.
"Ya yi bacci kafin ya bani nambar wani nasa na kira. Zan zauna kaje gida ka karbo bedsheet da bargo don na kula akwai hadari."
Lilu ya tafi shi kuma ya koma ciki. Har Lilu ya dawo da kaya niki niki wanda Mami Khadija ta hado domin kwanciya Abbati bai farka ba. Suhaib ya duba wayarsa amma a rufe take bare ya dan duba sunaye. Hakura ya yi tunda Mami ta ce ya jira ya tabbatar wani nasa ya zo.
Ba jimawa da Suhaib ya ajiye wayar a kan wani tebur da ake ajiye kayan abinci na mara lafiya Munzali ya kira. Sun yi dashi zai kira shi idan ya tsaya amma shiru. Daya layin nasa wanda wayar tana mota yana shiga shi ma bai ji an dauka ba. Haka ya dinga kira babu kakkautawa saboda hankalinsa dama bai kwanta da tafiyar ba. Haka kawai tunane tunanen ban tsoro suka far masa ya kasa sukuni. Kasa zama ya yi ya tashi ya tafi gidan Shazali. Ya san da wuya ya ce masa yana gida idan kira ya fara yi.
Maigadinsa bai hana Munzali shiga ba tunda ba bako bane.
"Ka dage kafi Abbati bashi farinciki. Ina mai tabbatar maka duniya sabuwa za ka bude idan ka kama manyan nan a hannu."
Kalaman da suka sauka a kunnuwan Munzali kenan yana shirin yin sallama a budaddiyar kofar shiga gidan Shazali. A shirye yake yana takowa bakin kofar yana waya zai fita. Idanunsa na sauka akan na Munzali da yake bashi da gaskiya sai ya ja baya. Munzali kuwa ya ce da wa Allah Ya hada shi....cakumar wuyan Shazali ya yi gami da yi masa mummunar shaka.
Da ihu yake masa magana idanunsa sun gama kankancewa.
"Ina Abbati?"
"Wane Abbatin?"
Rufe bakinsa ya yi daidai da saukar naushi a bakin.
"Wane Abbati? Ni ka ke tambaya wane Abbati?"
Shazali sai ya fara kokawar kwatar kansa saboda Munzali zai iya yi masa lahani.
"Kaga Malam nima da na ce yaje Abuja ya musu bayani bai karasa ba. Dazu muka yi waya ya ce min yana asibiti wai bashi da lafiya."
"In na yarda Allah Ya tsine min. Kai Shazali! Dubeni da kyau wallahi. Munzali ne. Ka sanni ba tun yau ba. Bani da mutunci ko kadan akan abin da ya shafi Abbati. Ina yake?" ya furta a fusace. Jijiyar kansa tuni sun firfito idanu sun yi ja.
Cikin jin haushin naushin da ya masa ya ce "Dama ta ina zaka yi mutumci a kansa tunda har yanzu kana begen ku cigaba da..."
Wannan karon bai gama hada kalamansa ba wani naushin ya sauka. Munzali ta dinga dukansa a haukace yana cewa ya fada masa inda Abbati yake.
"Indai kana tunanin waccan soyayyar nake yiwa Abbati to kayi kuskure. Ni da Abbati ma'abota inuwar Al'arshi ne in Allah Ya yarda (duba hadisin Qudsi dake magana akan mutanen da Allah zai sanya a inuwar Al'arshi ranar lahira. Allah Ya amintar damu da masoyanmu na gaskiya da wannan ni'ima. Amin). Wannan shi ne tsakanina da Abbati!"
Karfe bakwai da rabi Abbati ya tashi. Ya farka kansa ya yi nauyi amma babu ciwo sosai. Munzali ne ya fara fado masa a rai da ya hango duhun waje. Da sauri ya shiga laluben wayarsa saboda ya san dole yana can cikin tashin hankalin jinsa shiru. Inda Suhaib ya ajiyeta ya hangota. Zai dauka Suhaib din ya dawo daga masallacin kofar asibitin.
Godiya sosai Abbati ya sake yi masa.
"Babu komai. Za ka samu ka kira wani ko?"
"Eh yanzu zan kira. Nagode."
"To ga abinci nan. Zan dawo da safe in sha Allah. Ko in zuba maka?"
Saukowa daga gadon Abbati ya yi "ka barshi naji kwari ai. Zan fara yin sallolina tukunnan."
Suhaib ya fita shi kuma ya shiga bandaki. Da ya idar da sallah ya dauko wayar domin ya kira aka yi rashin sa a chaji ya kare. Aljihunsa da inda ya ga wayar ya duba babu mukullin motar balle ya je ya dauko chaja da daya wayar. Fita ya yi cikin sa a ya sami motar an gyara mata parking. Duk yadda aka yi wanda ya gyara din bashi da nufin cutarsa. Zuwa wayewar gari idan ba a kawo ba sai ya yi cigiya. A reception din ta sake tsayuwa ya tambayi wadda take kan aiki aron waya. Mata ta hade girar sama da kasa.
"Ba sai kin bani ba. Zan fada miki nambar idan an dauka ki ce a kira Abbati ne."
Kunkuninta tayi ta gama sannan a wulakance ta ce ya fadi nambar. Bai nuna jin haushin abin da tayi ba ya fada mata ta kira. Munzali na dauka a dakile ta ce "ka kira layin nan wani Abbati yana son magana da kai."
Yana dakinsa lokacin ya rasa me yake masa dadi. A gefe ga jaka ya hada kaya da duka atm cards dinsa a ciki. Waya kuwa baya nisa da ita yana ta adduar Allah Yasa ba mugun hannu Abbati ya fada ba a hanya.
Wannan wayar ta shigo a kan gaba. Matar na kashewa ya kira hannunsa har rawa yake. Da wayar kamar bata so haka ta mika masa.
"Munzali kayi hakuri" Ya fara cewa sannan ya fada masa abin da ya same shi.
"Yanzu yaya jikin naka? Zan taho na san in sha Allahu kafin sha biyu na iso."
"Kar ka soma tafiyar dare. Bani da wata matsala yanzu."
Duk yadda Munzali ya so Abbati hana shi tahowa ta yi.
Da bacin rai karara a muryarsa ta ce "Da asuba zan taso."
"Naji. Allah Ya tsare hanya." Abbati ya amsa da murmushi.
Mai waya dai sai cika take tana batsewa wayar tasa ta kusa minti shabiyar. Da ya gama ya mika mata ta dan murguda baki. Wani murmushin ya yi sannan ya zura hannu a aljihu ya ciro dubu uku ya bata.
"Ga ladan aron waya"
Kunya ta kama ta amma bata sa ta mayar da kudin ba. Sai ma dannesu da tayi da hannu.
"Laahhh babu komai fa. Idan baka gama ba ka kira shi ma." (Kudin wayar bai wuce naira hamsin ba)
"Mun gama. Nagode"
Ya fara bin hanyar dakin da yake yaji tana cewa "ni suna na Rufaida. Idan kana so ka dinga zuwa aron wayar kafin a sallameka."
Da sauri sauri har yana tuntube Alh. Tahir ya nufi bangaren Mami Khadija inda aka ce masa Farha tana kwance. Ya saba duka yaransa banda Suhaib yana waya da kowa kafin ya baro office. Shi yasa babu matsalarsu da bai sani ba. Rashin miji a wajen Farha kuwa nasihun da yake mata suna matukar tasiri a ranta. Yau da bai sameta ba sai ya shiga damuwa. Idan ya kirata kiran na shiga take rejecting call din. Shi ne ya kira Sauda take fada masa bata da lafiya har sun je asibiti sun dawo. Meeting suke yi mai matukar mahimmanci amma haka ya fito ya ce gobe a cigaba.
Ya kusa kofar dakin daga bayansa yaji kira daga Mami Khadija.
"Ina son magana da kai amma a dakinka."
Kallon mara tunani ya yi mata. Wace irin magana zasu yi a kebe Farha ba lafiya
"Ko ma meye ki jira don Allah in duba yarinyata."
Hannuwanta ta harde a kirji ta ce "abu mafi muni da za ka yi mata a yanzu shi ne ka nuna mata fuskarka a yau."
A tsorace ya juyo "fada mata zan auri Yumna kika yi? Haba Khadija! Ba na ce zan yi musu magana da kaina ba?"
Gaba tayi abinta. Bashi da zabin da ya wuce binta dakinsa. Suna shiga ta ce ya dauko wayarsa ya kira Yumna.
"A wane dalili?"
"Ka kirata ko ni na kira."
Da gaske take yaga alama. Kiran ya yi ai kuwa Yumna ta dauka da salon muryar da take yi masa idan suna tare.
"Zakina"
Mami Khadija ta tabe baki "daga Diya kuma yanzu Zaki ka koma? Tafe tafe sai an sami mai kiranka kadangare."
Harara ya jefa mata ransa na baci. Zai yi magana ta karbi wayarsa.
"Yumna ki saurareni da kyau ki ji abin da zan fada miki."
Hantar cikin Yumna ta kada amma ta kasa kashe wayar. Mami Khadija ba sa'ar yinta bace. Akwai layin da duk rashin kunyarta bata isa ta ketare ba.
"Babu ruwana da abin da ya hadaki da Maigidan nan. Duk wani shirme da shiriritar da ki ke yi da rayuwarki ya tsaya kanki da abokan shaidancinki" tayi maganar idanunta a kansa. Wani irin sanyi yaji ya ratsa shi na tsantsar kunya. Amma bai ce komai ba har ta cigaba da magana.
"Ki fita harkar 'ya'yana. Babu ke babu Farha. Bana bakinciki da shigowarki gidan nan a matsayin matar aure amma muddin ki ka dasawa ranki taba min yara to ki saka a ranki ke da Tahir sai dai a titi. Bana magana biyu saboda haka don't try me."
Wayarsa ta ajiye masa a kusa dashi ta fice daga dakin. Jiki na rawa ya kuma kiran Yumna.
"Turo min abin da ki ka turawa Farha har ya sumar da ita."
"Zakina.." ta ce tana shekar kukan kissa.
"Zakin uw**ki. Ki turo min yanzu yanzu kafin na tambayeta." Ya daka mata tsawa.
Yumna sai ta rikice. Gumi ya dinga karyo mata. A haka ta tura masa video din jiki ba kwari.
Alh. Tahir zabura ya yi da ya bude. Nasa gumin tamkar an kwara masa ruwa. Yanzu ace wannan abu Farha ta gani? Mutumcinsa kaf ya zube tunda ya san cewa ta gama ganinsa a wannan yanayi. Kulle kansa ya yi a daki ya rasa tudun dafawa. Yana son Farha amma ya tabbata yadda Suhaib ya guje shi ita ma haka za ta yi.
Tun Yumna na jiran ya kirata yayi masifa har ta hakura. Bata san abin zai hada da asibiti ba. Sannan gashi a gabansa kuma da wayarsa Mami Khadija tayi mata magana. Hakan na nuni da cewa wanda take yi dominsa shi ma yana shakkarta. Status din nata dama ta rufe babu mai gani sai Farha saboda kar ta sami matsala a gida. To gashi ta sami matsala da wanda take shirin shiga gidansa.
Bacci rabi da rabi Farha tayi a daren ranar saboda tana rufe ido abu daya take gani a mafarki. Mami Khadija bata matsa mata da tambayar me ta gani ba. Ta dai ce mata kar ta ja da hukuncin Allah game da mijin da Yumna za ta aura. Addu'a ce kawai tasu tunda basu isa su haramta halal ba. A gefe daya ga tunanin mutumin nan na asibiti da ya addabeta. Ji take ta tsani maza babu sauran nagari tunda mahaifinta ma bai tsira daga tarkon shaidan ba. To amma ta kasa cire yanayin da ta ganshi na rashin lafiya daga tunaninta. So take taji halin da yake ciki ko za ta sami sauki a zuciyarta. Abin gabadaya sai ya dinga bata haushi. Emotions sun yi mata yawa suna ta karo da juna.
Da gari ya waye sai ta tashi da ciwon barin kai saboda rashin isasshen bacci. Mami Khadija ta bata magani tun asuba. Karfe bakwai da rabi ta gama shiri saboda tana da aji karfe goma a ABU. Direbanta har ya iso ita yake jira sai ga Suhaib.
"Ina zuwa da sassafen nan na ganka a shirye?"
"Wallahi Mami mukullin motar mutumin jiya ne na gani a aljihuna da asuba. Ya barshi a motar da na gyara masa parking ashe ban ajiye a dakin ba."
"Ai kuwa gara kayi maza ka kai masa." Ta kalli Farha wadda ana ambatonsa taji faduwar gaba "yi maza ki shirya ki bishi." Sannan ta juya ga danta "Suhaib ta sake ganin likita. Da ciwon kai ta kwana. Hawan jini yana sa ciwon kai. Bana so ya zame mata ciwo tun da kuruciyarta. Gara taje ta sake yiwa doctor din complain. Ga wannan ku tafi wa mara lafiyar dashi" ta ajiye kwandon abincin da aka hada mata na zuwa office. Damuwar Farha ta mantar da ita tasa ayi abincin safe dashi.
Cikin minti ashirin ta shirya cikin riga da sket na atampa. Hijabi mai hannu ta saka navy blue wanda ya kusa kwaurinta. Fuskarta tayi fayau babu kwalliya sai hoda da kwalli.
A mota Suhaib yake ce mata kamar ya taba ganin mutumin.
"Kamar shi ne mai motar nan na diamond plaza."
"Ikon Allah" ya dinga cewa yana murmushi "idan kuwa haka ne ai ku bashi hakuri wannan karon tunda wancan lokacin kun gudu."
Da suka shiga asibitin Suhaib sai ya wuce dakin da Abbati yake ya ce in ta gama ta biyo shi sai su gaisa. Ita ma bata sami ganin likitan ba ance sai karfe tara zai zauna. Yanke shawarar bin Suhaib ya zo ya kaita gida kawai tayi. Kila idan tayi bacci za ta ji sauki.
"Jiki ya yi kyau gashi har kayi wanka" Suhaib ya ce da ya shiga dakin ya ajiye kwandon hannunsa.
"Alhamdulillah. Nagode sosai da taimakonku gareni."
Munzali wanda ya iso awa daya da ta wuce ya taso ya mikawa Suhaib hannu suka sake gaisawa. Wayar matar jiya ya kira ta kwatanta masa asibitin.
"Nagode sosai. Daga yau ka zama dan uwanmu kaima. Ni sunana Munzali, kai fa?"
"Suhaib"
Mukullin motar ya mikawa Munzali yana basu hakurin mantuwarsa. Sun nuna masa babu komai har suka soma taba hira. A dan wannan lokacin ya fahimci yadda suke son juna. A haka dai kamar su ga hanjin juna da mara lafiyar da mai jinya. Sai kawai ya dinga murmushi yana kallonsu.
Su ukun suka kalli kofar dakin da aka kwankwasa gami da yin sallama da tattausar murya amma ba a bude ba.
Abbati ji ya yi duk wata na'urar jikinsa ta tsaya. Ashe dadin muryarta da yaji a waya ba komai bane. Yanzu ya san yaji muryarta domin duk wani gashi na jikinsa ya mike kamar zasu amsa sallamar.
"Yi hakuri kanwata ce. Na ce ta sameni a nan ne idan ta ga likita."
"Meye abin bada hakuri? Kanwar dan uwanmu fa kanwarmu ce" Cewar Munzali ya daga murya ya ce "shigo."
A hankali ta turo kofar kamar tana jin tsoron. Kanta a kasa ta shiga ta sake wata sallamar. Munzali da Suhaib kadai suka amsa. Abbati kuwa yawun bakinsa ma ya kafe.
"Kanwarmu ya jiki? Kin sami ganin likitan?"
Kallon mai tambayar tayi niyar yi sai idanunta suka sauka akan na Abbati. Da sauri ta kawar da kanta gefe ta amsawa Munzali wanda yake mata fara'a.
"Da sauki amma sai tara Doctor din zai zauna. Ya Suhaib ko za ka kaini gida kawai?" Ta marairaicewa Suhaib saboda a takure take jin kanta.
"Sai dai ki rakani ATM . Maybe kafin mu dawo taran ta yi"
Munzali ya kalleta ya girgiza kai "bata da lafiyan za ka kwasheta wani wajen? Barta kawai ta zauna a nan ko ka kaita gidan idan babu nisa. Amma kafin nan don Allah rakani in kama mana hotel idan akwai a nan kusa. Da alama yau za a sallamemu. Gashi bana son mu kama hanyar Kano sai ya kara jin sauki. Ni kuma ban san kan garin nan ba."
Suhaib ya ce akwai wani kurkusa dasu su je ya nuna masa. Mukullin motar da suka zo ya mikawa Farha ya ce ta jira shi a motar kafin su dawo.
Munzali ne ya fara fita sai Suhaib din. Farha ta kusa bakin kofa Abbati ya kirata. Zuciyarsa taki bashi hadin kai na kar ya kula ta.
"Ya Farha" Abbati ya furta da wata irin siga da ta tsaya mata a zuci. Tsayuwa tayi gabanta na harbawa da sauri.
"Yaya jikin naki?"
Kunya sai ta lullubeta. Shi da ya kwana a asibiti ko gaishe shi da jiki bata yi ba. Bata san me yake damunta ba. Murmushi tayi ta juyo amma kanta tana kasa.
"Ina kwana? Ya jikin? Allah Ya kara sauki."
"Lafiya kalau. Jiki da sauki. Amin Ya Rabb." Ya amsa da murmushi.
Yadda ta jero tambayoyin haka ya amsa su. Dariya hakan ya bata amma sai tayi murmushi kawai.
"Subhanallah" ya furta da sauri saboda yadda murmushin ya daki ko'ina a jikinsa.
Farha sai ta kalle shi saboda bata ji me ya ce sosai ba "Na'am?"
"Babu komai Ya Farha."
"Ka daina ce min Ya Farha."
Dumi dumi yaji a zuciyarsa. Salon maganar ya burge shi. A lokaci guda ya hau musu da zuciyarsa.
'Bata san shagwaba take bane? Anya ba kasheni yarinyar nan take son yi ba? Dama haka ake son mutum? Wannan ya zan ji idan ta ce tana sona?'
"Ka ji." Ta maimaita a zatonta bai ji bane.
"To me kike so na kira ki wanda zai kusantoki gareni ba tare da na bata miki rai ko na cutar dake ba?"
Babu wata kalma da ya fada da bata ji ba amma bata gane komai ba. Ta dai ji ya ce 'kusantoki gareni'. Sauran kuwa kamar ba da hausa ya yi ba.
"Kin yi shiru."
"Me ka ce?"
"Cewa nayi in dinga kiranki Farha-ta?" ya tsokaneta ganin ta tafi duniyar tunani.
Yana ganin yadda idanunta suka kara girma da mamaki ta yi saurin cewa "wallahi ba haka kace ba."
"Kin tabbata?" Ya tambayeta yana dariya.
Soyayyar Farha ta zame masa jinin da yake yawo a jikinsa. Anya daidai ne ya biyewa zuciyarsa?