← Book details Uwa Uwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 8 OF 9

BABI NA SHA BAKWAI.

Uwa Uwa Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 33 min read

"Habibu ya maganar Agent dinnan? Naga har yanzu baka ce min komai ba."
"Uwani kenan. Tsakaninmu da watan Hajji akwai watanni 5 kwarara."
Hankalinta bai kwanta ba. Ta gaji da gafara sa bata ga kaho ba. Wata uku da bayar da kudinta na kujerar Hajji amma har yau bata ga komai na shaida ba. Habibu mutuminta ne tun farkon fara aikinta a asibitin. Shi yake mata shige da fice duk lokacin da aka turo mata transfer ta cigaba da zama a Sir Sunusi. Ta riga ta kafa ta tsare. A nan take cin kasuwarta. Sai mace ta haihu ta ce ta tafi gida za ta zo tayi mata dinki mai kyau a can.
"Yawancin yaran nurses dinnan duk lalata muku jiki suke in an zo wata haihuwar sai an kara budeku. Indai ba ni nazo karbar haihuwarki ba kada ku yarda ayi muku dinki ko kun karu. Ga nambata ki nemeni da an sallameki sai ki kwatanta min gidanki nazo nayi miki. Dubu shabiyar ne amma ina miki rantsuwa mijinki ma sai ya gode min ba ke ba."
Tsarin hudubarta kenan tun a wurin awo. Irin matan da ta yiwa dinki a gida basu kirguwa. Da yake kuma ta kware din sai matan suke turo 'yan uwa da kawayensu. Kasuwa ta bude mata sosai a waje. Manyan mata ko basu haihu ba suna neman Metron Uwani ta gyarasu. Ana iya cewa wannan shi ne babbar silar samun kudinta fiye da na aikin asibitin. Matan masu kudi tana yi musu suji dadi ayi mata ihsani mai tsoka. Ga karbar haihuwa da take yi a waje. Duk wata Nos da ta san sirrinta ta nemi tona mata asiri bata kara sati biyu Habibu zai tsaya har sai an yi mata transfer.
"Yanzu sai yaushe zan sa rai? Gobe sunan kanwata. Kuma a son raina inje musu da zancen Hajjin yadda duk wani dan bakinciki sai dai ya hadiyi zuciya wallahi (tana fada, fuskar Hasiya take hangowa)"
"Kice dai 'yan bani na iya basu barki ba har yau."
Nan ta labarta masa haihuwar Zara da komai. Sirrinta da na 'yan uwanta da ya sani wani ma ya tabbata ta manta anyi.
"Ina kuma shi na gaban motar" ya tambayeta mijinta yana kyalkyala dariyar raini gareshi.
Uwani ta yi guntun tsaki, "wa yake ta wannan? Wai ni zai kalla ya ce in biya kudin makarantar yara bashi. Ya kwashe kudi yana ta uban gini, bayan na san karshenta da amarya zamu tare. Gani mahaukaciya in biya a gaba mu zo muna babatu. Nima kuma ba kudin nan gareni ba."
"Uwani sarkin babu. Ki daina kiranta wallahi kada ta shammaceki."
Harara ta doka masa "Allah Ya kiyaye. Ni babu ai garkuwa ce a wurina. Masu saka ido akan arzikin da Allah Yayi min sai dai su gaji su mayar da kwadayinsu."
"Allah Ya bar min ke Matron...au, au, Hajiya Uwani ya kamata na fara kiranki fa."
Wata shewa tayi cike da jindadi ta sabi jakarta.
"Don Allah Habibu ka maida hankali in zo na fara shiri. Bana so a fara bita ina gida."
"Kwantar da hankalinki Hajiya Uwani. Bana kam sai dai na ce Allah Yasa maqabuliya ce."
Tana tada mota ya buga uban tsaki ya gyara kwanciyarsa akan benci kasan bishiya. Shegen kudin nata ma ko albarka babu. Ko da wuka ba ya ce ga wani abin azo a gani da ya yi dasu ba sun bi ruwa sun bi iska. Rigima bata kisa bare ya tsorata ranar da kwai zai fashe.
Washe-garin zuwan su Baaba Mari Kaduna Mami Khadija ta sake aika abinci asibiti. Banda wanda su Farha suka tafi dashi da safe Suhaib ya kai na rana. Sannan yaji Abbati da Munzali suna tattaunawa game da tahowar su Baaba Mari. Iya abin da ya fahimta shi ne 'yan uwan Abbati sun taho kuma bashi da kowa da zai saukesu a nan. Ya koma gida da niyar fadawa Mami Khadija amma bata dawo daga wurin aiki ba sai bayan isha. Ta biya gidansu ne akan shirin bikin autansu da ake yi. Tana dawowa ya fada mata.
Kallonsa tayi da kyau ta kada kai "yanzu Suhaib maimakon ka kirani tun dazu sai yanzu da dare ya yi?"
"Yanzu ban burge ba? Cewa za ki yi nayi wauta ko?" Ya tambayeta yana tsuke baki.
Dariya tayi kafin ta amsa masa "ta ina ka burge? Kuma banda wauta da ka kirani ai zan ce ka tuntubesu ko suna bukatar taimako. Ba ka ce ka karbi nambobinsu shi da dan uwansa ba? Kira dayansu mu ji me zamu iya yi musu."
Da ya kira Munzali ya sanar dashi ya kama musu dakuna a Guest Inn din da ya raka shi da safe. Sannan ya riga ya sayi abinci. Suka yi sallama cikin aminci suna masu nanata godiyarsu a gare shi.
Mami Khadija tana da wani ajin da safe ranar, saboda haka sammakon tashin Sauda tayi. Mardiyya ta kwana a bangaren Nasima, dama ta saba yi mata haka tun a wancan gidan. Idan ta je wurinta kusan raba dare suke tana bugun cikinta domin ta san me da me Mami Khadija da 'ya'yanta suke ciki. Tunda da wayonta sai kawai take biye mata tayi ta hada mata zantukan da basu da kan gado tana fada.
Tsomen doya da kwai Sauda tayi wanda ya gajiyar da ita saboda yawansa. Mamin tasu tayi farfesun kaza sannan mai-aikinta ta dafa tea aka zuba a flask din gida sai na asibiti da na 'yan uwan Abbati. Ga kuma bread an hada musu dashi.
Bayan sun gama a gajiye Sauda take cewa "Mami wai waye a asibitin ne? Jiya da shekaranjiya ma an kai ga na yau kamar masu tarbar baki."
" 'Yan uwanki basu fada miki mutumin da suka gani a asibiti mara lafiya ba?"
Da dokinta ta ce "Sun fada ban san shi ake kaiwa ba" sannan ta hau bata labarin abin da ya faru kafin ta dawo gidan "Ai jiya kafin ki dawo ne Ya Farha ta fada mana ashe wanda muka yi hoto jikin motarsu ne a plazar su Mama...Mami zo ki ga ihu wurin Ya Lilu wai mutumin ya burge shi."
"Rabani da wannan mashiriricin. Karasa hada kowanne yadda na nuna miki ki taso Suhaib tunda shi ya san dakin da mara lafiyar yake."
Tsabar son ganin kwaf Sauda ta ce "Mami ki ce yaje dani don Allah. Sai na daukar masa basket din."
"A dawo lafiya. Idan ki ka yi masa rawar kai ya make ki" Mami Khadija ta furta tana yin gaba ta fita daga kitchen din.
Kafin goma na safe sun kai abincin dakin Abbati wanda ganin Suhaib ya saka masa rai da sake ganin Farha. Da ya ga fuska daban bai nuna rashin jindadinsa ba sai aikin godiya. Haka kuma Munzali ya musu rakiya har dakin Baaba Mari.
Wannan abu ya yi mata dadi fiye da zato da tsammani. Ta dinga yi musu kyawawan addu'o'i. Wani bangare na zuciyarta yana haska mata cewa karshenta Abbatinta mutumin kirki ne sabanin zarginta. Mutanen kwarai basa rasa mataimaki a inda basa zato.
A matsayinta na uwa haka yafi komai yi mata dadi. Babu mai son rab'a danta da mummunan abu ko yaya yake sai dole. Babu wata uwa dake duka ko yiwa danta fada domin rashin so. A takaice ma tsabar soyayyar ke janyowa mu dinga kwab'ar 'ya'yanmu domin su zama nagari. Habi ta saka ta dibar musu abincin sannan ta ce ta kai ragowar dakin su Deluwa. Sai da suka ci suka koshi sannan Munzali ya daukesu suka tafi asibitin. Suna zuwa ana sallamarsa.
"Baaba za ki iya sake kwanan inda na kai ku jiya ko mu kama hanyar Kano idan mun yi azahar?"
Munzali ne ya tambayi Baaba Mari bayan sun gama gaisawa da Abbati an harhada kaya.
"Mu tafi din dai zai fi."
Deluwa taji zai bata mata shiri don so tayi su kara kwanaki ko biyu ne ta cusawa Abbati 'Yashshafa kafin su tafi Kanon. A gidansa Hanne za ta iya hana ruwa gudu.
"Kai dai wannan yaro da zakalkalewa ka ke? Ai dai ka bari wadda ta fika iko dashi tayi magana?"
Baaba Mari sai ta dauke kai kamar bata ji ba, su ma sai suka yi yadda tayi din.
"Kafin mu tafi din zai kyautu muje gidan wadannan bayin Allah muyi musu godiya. Bai dace su biyomu karbar kwanukansu ba." Ta ce da Munzali.
A ransa Abbati yake cewa kamar ta shiga zuciyarsa ta san abin da yake tunani.
"Kayan shimfidar ma duka nasu ne."
"Allah Sarki. Mutanen kirki basa karewa a duniya."
Deluwa ta jinjina kai bayan sun gama kwashe komai suna shirin shiga mota ta soma sababi. Habi da 'Yashshafa suna motar Buba. Ita da Baaba Mari ne zasu shiga baya a ta Munzali.
"Dole ki wulakantani mana Mari. Baki da laifi tunda ni na nace sai nazo duba danki. Wannan cin kashin da ki ke yi min Billahillazi kaf sai na fadawa Malam" ta kare tana yi mata kashedi da hannu.
A karo na biyu Baaba Mari ta sake bawa banza ajiyar Deluwa ta ce "Na san halinka da nawa idan ka so Abbati. Don Allah ka hanzarta yin wanka ka kimtsa yadda zamu je mu kama hanya da wuri"
Munzali sai ya kama murmushi. Da can ma Abbati komai nasa da shiri cikin tsari yake yi ballantana yanzu da zasu je gidansu Farha. Waya ya daga ya kira Suhaib ya fada masa. Sai kuma ya roke shi idan zasu iya ajiye motar Abbati a gidansu. Sati mai zuwa su zo su dauka saboda ba ya son Abbati ya gwada tuki mai nisa da fitowarsa daga asibiti.
Mami Khadija ya fara kira ya fada mata bakin da zasu yi. Tana hanya don goma ta fito daga aji kuma bata zauna ba ta taho saboda maganar bikin gidansu. Farha ta fara kira bayan sun gama magana ya fada mata karfe nawa zasu iso.
"Idan kina jin kwarin jikinki yau kisa hannu a hada musu abincin rana. Aikin zai yiwa Sauda yawa a kankanin lokaci. Mardiyya kuma tun jiya na kula da take taken Nasima saboda haka kar ki kirata har ta sami yadda take so ayi rigima. In kuma ba za ki iya ba sai a siyo musu kawai."
Bata san cewa kafin ma ta gama bayaninta ba Farha ta mike tsaye. Wannan yanayin na farinciki mara misaltuwa ya mamaye kirjinta.
"Zan iya Mami. Sai kin iso. Allah Ya kiyaye hanya."
Babu sauran ciwo bare damuwa. Dakin Sauda ta wuce ta tasota. Karatu take yi na gwajin da take dashi washe-gari litinin.
"Ayyaaaa Ya Farha test gareni. Yaushe zamu gama nayi karatu? Ni wallahi ban iya komai ba kar naci zero."
"Yi zamanki. Amma wallahi ki baza kunnuwa don Mami tana hanya. Kina jin motarta ki taho kitchen."
Sauda tayi mamakin wannan abu. Yau yayarta da kanta take gudun dan tayi? Ba wai kyuya gareta ba amma bata son shiga kitchen ita kadai. Ko baka tayata da komai ba ta dinga jin motsi ko a ayi hira. Sai kuma ta tuna hasashensu ita da Mardiyya akan wanda Munzali ya bawa wayarsa rannan. Mutumin da Farha ta ce mata shi ne mara lafiya. Shu'umin murmushi tayi ta wurgar da littafin tana dirowa daga gado tabi bayanta. Zaman daki bai kama ta ba indai akwai wainar da ake toyawa tsakaninsu gara ayi a gabanta. Akan hanyar zuwa kitchen din ta turawa Mardiyya text ta tsegumta mata.
(Ki kirani idan sun zo please)
Ta tura mata amsa idanunta akan Mama Nasima. Fatanta kada a sami akasi akan fitar da ta ce zata yi. Ta kasa gane yawan tambayar da take yi mata yau akan Yumna kawar Farha.
A zuciyar Mardiyya bata kaunar wannan hali mai kama da gulma na mahaifiyarta. Kafin ta girma duk abin da ta tambayeta take fada mata. Sai ta kula idan ta so takalar Mami Khadija rigima da wannan take amfani tayi ta sakin maganganu. Mamin ta gane abin da Nasima take yi amma bata taba nunawa yaranta su guji Mardiyya ba. Suhaib har CID ya saka mata lokacin wanda akan idonta Mami tayi masa kaca-kaca. Da shekarunta suka karu tayi hankali sai ta fahimci illar abin da take yi ta daina.
Duk lalacewar Nasima a tata zuciyar wannan karon ba da gulma take tambayoyin ba. Laluben hanya mafi sauki da za ta fadawa 'yarta auren da mahaifinta zai yi take. Yaran duka suna son babansu a iya saninta. Wannan labarin ba komai zai yi ba sai wargaza farincikinsu. Sannan tana sane da yadda Yumna ta zame musu makusanciya a dalilim Farha. Bata sani ba ko ita ma Farha tana yawo. Kada ya zamana an koyawa 'yarta bata sani ba. She was just being a Mom a yau. Sai dai rashin sabo da rashin kyawun zuciya tun farko yasa ta kasa gabatar da niyarta.
Zuwan Sauda yasa aikin nasu saurin karewa. Tuwon shinkafa Saudan tayi ita kuma Farha hadaddiyar miyar agushi. Lilu ya siyo frozen springrolls da samosa aka soya da kuma lemuka. Sai kayan marmari da aka hada fruit salad.
A gurguje Farha ta shiga wanka. Kafin ta fito Mami Khadija ta dawo taje ta duba inda aka tanadi kayan tarbar bakinsu. Komai ya yi yadda take so domin 'ya'yan nata ba daga nan ba.
"Kai Mutumina, wannan kamshi kamar gaisuwa zamu je kai wa ba godiya ba?"
Abbati ya cigaba da fesa turare yana murmushi kafin ya bawa Munzali amsa.
"Sa ido sana'ar su waye ma?"
"Zagina za ka yi saboda ka warke?" Cewar Munzali yana tasowa ya karbe turaren ya shiga fesawa "wai ma da kananan kaya za ka je gidan surukai?"
Abbati ya kalli kayan jikinsa ya dan hade gira. Jeans ya saka baki da jar riga shirt. Agogonsa na fata da takalmi covershoe duka bakake.
"So ka ke ka rage min farincikin da nake ciki shi ne za ka fara korafi akan kayana?"
"Rashin dacewa na gani. Tunda babu a kayanka idan ka amince kawai mu wuce Kano sai mu dawo daga baya idan an sami lokaci..."
Sauran maganar tasa bata sami fita ba a dalilin kansa da Abbati ya taho shi kuwa ya ja da baya yana dariya. Sauran kiris su fara halin nasu na kokawa kamar yara Buba ya kwankwasa kofar.
"Baaba ta ce in duba ku taji shiru."
Sai da Abbati ya harari Munzali sannan ya bude kofar yana cewa "ka ci sa a."
"Kai dai ka ci sa a ba don haka ba yau da sai nayi maka John Cena (sunan dan wasan wrestling ne) a gadon baya."
Yana fadin haka ya fice da sauri suna dariya harda Buba da yawan tsokanar junansu ke matukar burge shi.
Kamar yadda suka dawo masaukinsu haka suka sake shiga mota da kayayyakinsu yanzu. Habi da 'Yashshafa suna motar Buba. Habi tayi shigarta fes ita kuwa yallab'iyar kwalliyarta ta rambada tayi bajau. Banda uwar hoda da foundation wanda suka mayar da ita mutum mutumi ta kawo wata foundation din mai haske ta zana tun daga tsakanin girarta har karshen karan hanci. Irin abin nan da masu make up suke yi domin a karawa hanci tsini. Sai fuskar tayi daban daban. Jambakinta kuwa purple ne an zagaye shi da jar jagira. Abin dai sai godiya kawai. A son ranta Abbati ya karbi tukin sai ta shiga gaba. Sauran su taru a motar Buba. Deluwa da Baaba Mari suna motar Munzali a baya. Abbati yana gefensa suna ji ya gama waya da Suhaib wanda ya ce su je asibitin Doctors Haven yana jiransu a waje. Da isarsu kuwa suka hango shi a mota ya tayar su kuma suna bin bayansa.
Maganar Munzali game da kayan jikinsa ta dawowa Abbati ya dubi Munzali wanda hankalinsa yake titi don kada Suhaib ya bace masa. Yadi ne a jikinsa wanda yasa domin tsokana ga Abbati.
"Idan mun je ka zauna a mota kawai"
Munzali ya karkace kai ya ce "saboda?"
"Saboda na isa. Ko so ka ke a dinga yabonka shigarka ace tawa bata yi ba?" ya bashi amsa.
Dan waigawa baya Munzali ya yi ya ce da Baaba Mari "ki shiga tsakanina da mutumin nan. Cin zalina yake yi duk sanda ya sami dama."
Dariya suka bata ta murmusa "haka dai ku ka iya kamar kananan yara."
"Haba Baaba ina da kamar Qibdiyya ki ke ce min yaro?" Inji Abbati
"A baki ba! Kodayake gara ma kai wannan karon. Kai kuwa Munzali dama taraka nake yi. Kai baka mayar da mahaifiyar Mariya (sunan gaskiyarta take kiran Qibdiyya) ba kuma baka nemi wata ba..."
Caraf Deluwa wadda tun dazu take neman shiga hirar ta ce "shi ma Abbatin ai sammakal. Har ma gara Munzali tunda ya ajiye kwai duniya ta shaida. Kai kuwa ka ajiye juya a gida bata komai sai ta ci ta sha tayi kashi. Ai Mari aure ya kamata ya kara ko Allah zai sa ya sami magaji."
"Ku ne 'yan birni. Me ya kamata mu kaiwa mutanen nan ne a matsayin tukwicin kyautatawarsu?" Baaba Mari tayi tambayar ga 'ya'yanta tana mai kawar da kai ga maganar Deluwa a karo na uku. Ranta yana baci ne idan tayi maganganunta to amma bata son ta biye mata. Yin hakan zai zubar musu da kima a idanun 'ya'yansu da wadanda suke tare. Ba ta son tayi abin da ko da wasa Buba zai gorantawa Habi idan sabanin yau da gobe ya hada shi da ita. Sannan ga Munzali da uwa uba 'Yashshafa wadda tayi imanin komai rashin kan gadonta, idan taga ana saitawa mahaifiyarta zama sai taji babu dadi.
Abbati ne ya amsa mata da cewa sai dai su ajiye musu kudi tunda sun riga sun biyo bayan Suhaib babu damar tsayuwa. Ita kuma ta ce ba kowa ke karbar kudi ba siyayyar za ta fi. Basu ankara ba suna shawara sai gani suka yi Suhaib ya saka trafficator ta bangaren dama. Munzali sai ya ce mata kada ta damu in Allah Ya yarda zasu kawo tukwicin ko ba yau ba.
Deluwa aka hangame baki da kofofin hanci ana kallon tafkeken gida irin wanda bata taba gani ba. To Baaba Mari ma dai sai da taji faduwar gaba. Masu kudi irin haka ne suka taimakawa danta. Anya in sun san cewa su kauyawa ne zasu kallesu ma kuwa?
"Baaba fito mana"
Muryar Abbati ce ta katse mata tunanin da bata san ma ta dulmiya a duniyar yinsa ba. Shi ma kuma suna fitowar hada ido suka yi da Munzali kowanne ya jinjina kai. Basa bukatar furta zantukan da zukatansu suke yi. Maganar daya ce tak. Gidan nan yafi karfinsu.
"Ya Farha sun iso."
Cikinta ya sake bada sauti bayan na farko da ya yi lokacin da taji an bude gate. Waskewa tayi don jikinta har wani dan rawa yake yi kamar mai shirin kamuwa da masassara.
"To kuma sai aka ce idan sun zo ki fada min? Bakin Mami ne ki je ki sanar da ita mana."
Sauda ta kama dariya "gani nayi wai kin sha wahalar yi musu girki."
Farha ta sha kunu "to biyana za su yi?"
"Eh mana. Ko dan murmushi aka cillo miki na san za ki kwana kina juyi." Tana kare magana ta fita da sauri kafin Farha ta iskota.
A can waje bangaren da aka yi domin ajiye motoci Mama Nasima ce za ta shiga motarta. Mardiyya tana gefenta ta dauko mata jaka. Suna wurin su Abbati suka shigo. Suhaib ya ajiye motarsa a inda ya saba sannan ya tafi inda suka tsaya baya kadan dashi suna jiransa. Kamar da wasa Mama Nasima ta kalli bakin da take tunanin na makiyarta ne sai idanunta suka sauka akan Munzali sannan Abbati.
Motar da bata shiga ba kenan ta bude baki ta soma cewa "Alh. Munzali" kamar ita ta rada masa sunan.
Su duka suka waiga har ta karaso wurin tana kallon mutanen da suka zo tare.
Kan Mardiyya ta dungure wadda tana jin ta kira sunan Munzali hankalinta ya tashi ta biyo bayanta.
"Wai yarinyar nan sai yanzu take fada min kuna tafe kuma harda manyanka. Shi ne fa na fito da kaina zan tarbeku." Ta dubi su Baaba Mari jikinta a dan sanyaye da yanayinsu da ya fallasa rangwamen wayewa a tare dasu. "Sannunku da zuwa Inna." Suka amsa fuska a sake don basu san wurin wa suka zo ba dama.
Mardiyya tayi karfin halin cewa "Mama ba fa..."
"Wuce muje ki hado musu juice sannan ki dora abu mai sauki (bata taba daukar mai-aiki ba saboda gudun kar a ramawa kura aniyarta)."
Duk abin da ake yi Munzali kallon Mardiyya yake wadda idanuwanta suka
cicciko da kwalla. Tana magana hawaye na kokarin sauka.
"Mama kinga tare da Ya Suhaib..."
Munzali sai ya girgiza kai da sauri saboda fahimtar halin da mahaifiyarta ta sakata. Irin wannan ai ba bakonsa bane tunda ya tashi a gaban Asabe.
"Abbati ku je da Suhaib zan shigo daga baya."
Mama Nasima ta yamutsa fuska tana hararar Suhaib "au, kun sansu ne?"
Hanya kawai Suhaib ya nunawa su Abbati "Bismillah muje."
Abbati sai ya kalli Mardiyya ya yi mata alama da tayi murmushi ga Munzali nan. Murmushin kuwa tayi ya hado da zubowar hawaye.
"Mama muje dama zan kawo miki karar Diamond girl"
Munzali ya ce domin kawar da hankalin Mama Nasima daga kansu Abbati. Ai kuwa ya yi nasara domin yana kiran 'yarta Diamond girl ta soma dariya.
"Yaran yanzu ba kwa kunyar kowa. Duk da dai kamar ma zamu yi sa'anni da kai Alhaji. Amma babu komai. Aure babu inda ba ya kai mutum. Abbanta ya girmeni sosai. Kusan kamar kai da ita."
Kallon ban hakuri Mardiyya take yi masa. Shi kuma ya nuna mata ko kadan bai shiga damuwa ba. Da ido kadai yake karfafa mata gwiwa har taji saukin zuciyarta akan abin da mahaifiyarta tayi. Basu sani ba ashe kallonsu Mama Nasima take. Ta sake kallon motar da Munzalin ya tuko taji sanyi a ranta. Watanni kalilan suka ragewa Mardiyya da Sauda su gama secondary. Ranar jarabawar karshe in sha Allahu za ayi kamun 'yarta. Aurar da ita zata yi ga kamilallan mutum ko hankalinta ya kwanta. Bangaren zuciyarta da bai manta rayuwarta da ta mahaifin Mardiyya ta baya ba yana cike fal da tsoron kada wata rana kaddara ta giftawa tilon 'yarta.
Suna shiga falonta ta yar da mayafi akan kujera ta fada kitchen. Sai lokacin Mardiyya ta iya yi masa magana.
"Ni wallahi ban ma san me zan ce maka ba. Don Allah kayi hakuri."
Kashe mata ido ya yi fuskarsa a sake ya ce "Kar ki damu Diamond girl. Ina jin fa gara wannan maman tamu akan wadda na baro a Kano."
Abin sai yaje mata bambarakwai. A iya saninta mahaifiyarta ce kadai me wannan halin.
"Da gaske?"
"Zan kaiki ki ganta sai ki tabbatar."
'Yar dariya tayi, yaji wani irin sanyi a ruhinsa sai da ya kai ga lumshe ido. Kamar da wasa ya cewa Abbati zai nemeta sai dai bai taba zaton zai ji komai a ransa ba game da ita. Ya zata tausayi ne kawai...
"Ka kaini ka ce mata wa? Bamu da 'yan uwa a Kano na san ma Abba ba zai bari muje ba."
Muryar Mama Nasima suka ji tana cewa "kina nan kin saka shi a gaba da zance maimakon ki biyoni kitchen ko? Wannan ni kike son ki tozarta a zaci ban miki tarbiyya ba. Alh. Munzali sai kayi hakuri fa. Matar taka akwai kuruciya ga autanci yana damunta."
Tamkar Mardiyya ta nutse a kasa don kunyar mahaifiyarta. Sai gashi Munzali ya kara mata da cewa "kinji Mama ta bada amsar idan na kaiki Kano da wane suna zan gabatar dake ga iyaye da 'yan uwana."
"Sannunku da zuwa. Sannunku. Ku zauna don Allah"
Mami Khadija kenan take yiwa su Baaba Mari barka da zuwa cike da fara'a da kyautatawa. Baaba ta saki fuska ita kuwa Deluwa duk ta gigice da sanyin falon. Haushin shareta da Baaba Mari ta dinga yi ya bace a lokacin. Suhaib take kallo tana sake kallon zinariyar 'yarta wani abu yana darsuwa a zuciyarta.
"Shafa'a (tana jin kamar idan ta kara 'tu' din sunan zai yi kauyanci) koma motar ki shigo da kwanukan da suka yi ta mana hidima dasu mana."
'Yashshafa ta tashi ta fara zumbura baki sai ji tayi Deluwa ta ce da Suhaib "Sha'aib rakata kaji dan albarka."
Abbati ya harbo jirgin ya ce 'Allah Ya 'yantani' a ransa sannan ya mike kafin ta sake magana.
"Muje na tayaki."
Deluwa ta hade rai kamar ta rufe shi da duka. Sanda taso ya kula 'yarta yaki, yanzu ta sami wani zata cusawa yana neman hana ruwa gudu.
'Yashshafa tayi waje tana ta karairaya sai ka rantse kugunta bai zauna daidai ba. Abbati ya tabe baki yana dariya a ransa. Banda rigimar Deluwa daga ganin mutum ta fara tunanin hada shi da 'yarta. Kafin ta karasa kunyatasu gara ma suyi su bar gidan. Sai da suka isa jikin motar Suhaib ya fito ya karbi mukullin motar Abbati dake asibiti. Lilu zai dauko a gidansu abokinsa sai ya kai shi ya dauko motar. Bakin Abbati baya gajiya da yi musu godiya. Bayan ya tafi ne ya mikowa 'Yashshafa tissue.
"Goge fuskarki kafin mu koma. Da ace naga wannan adon bararojin tun kafin mu fito ba zan yardi ki biyomu a haka ba."
"Ni dai gaskiya Yaya Abbati ka bar min kayana ina so. Duk wata mace da ta amsa sunanta yanzu sai da me-uf (make up)."
Magana zai sake yi mata kawai ya hango Farha ta fito daga wata kofa da bata da nisa da wadda suka fito. Doguwar rigar atampa ce a jikinta sai mayafin mai kauri wanda ta dora a ka ba tare da ta saka dankwali ba. Bata san ya ganta ba tayi saurin buya a bayan wasu fulawoyi masu tsayi da suka cike tazarar dake tsakanin bangarensu da na Mami Khadija.
Kwando daya ya mika mata ya ce "jeki, iyaka dai duk wanda ya yi mafarkin fuskarki a gidan nan yau alhaki a kanki."
Tana soma tafiya ya hango Farha ta kuma lekawa sannan ta buya a zatonta tare zasu koma ciki. Har ya lallabo ta gefen bangaren Mami Khadija ya tsaya a bayanta bata sani ba. Kallonta ya dinga yi kamar babu kowa a duniya sai su kadai.
Farha da bata san yana wurin ba ta sake lekawa sai bata ga kowa ba. Sauke ajiyar zuciya tayi kanta cunkushe da tarin tambayoyi. Bata san ma'anar wannan bakon yanayi da take tsintar kanta game da Abbati ba. Sai tuhumar zuciyarta ma da take yi wurin azalzalarta da yawan tunaninsa.
Kafa ta daga za ta bar wurin ta bangaren nasu dakin Abbati ya yi mata magana da sauri.
"Abin da muke buyarwa din har ya tafi ne?"
Ba karamin tsorata tayi ba harda ja baya. Tabbas taji kamshin turare mai ratsa zuciya amma bata kawo cewa a bayanta mai shi yake ba. Ga kunya ga kuma mamakin yadda yazo wurin bata sani ba, basarwa tayi ta ce masa,
"Me kake yi a nan?"
Takowa ya dinga yi a hankali zuwa inda take. Ta rufe ido har ya karaso domin tamkar a tsakiyar kanta take jin sautin duk takunsa.
"Naga kin buya ne shi ne nima na taho kar abin da kike gudu ya kamani."
Tura baki tayi don ta boye kunyar da ta kama ta ta ce "babu abin da nake gudu ni."
"Da gaske? To ko ni ki ke kallo?"
Ba shiri ta daga kai ta zuba masa kyawawan idanunta "me zai sani kallonka?"
Hannuwansa duka biyu suna aljihun wando, ya jikina da bango ya dubeta da kyau kafin ya ce
"Nima haka nacewa kaina. Me zai sa ki kallona?"
Karkata kai tayi ta dan kalli yanayinsa da ido daya sai taji babu dadi.
"Wai haushi kaji?"
Shi da zai yi fushin wasa tana neman saka shi dariya. Da kalma daya ya amsa mata kada dariyar ta subuce masa
"Eh"
Farha ta sake ware idanu wanda ya fahimci tana yin hakan cikin mamaki ko tsoro. Yadda yake ji a ransa a lokacin zai iya rantsuwa babu wanda ya taba son wata mace kwatankwacin yadda yake jin Farha a ransa.
"Fushin gaske ko na wasa?"
Ya marairaice mata fuska "na gaske mana. Abbati bashi da abin da zai sa Ya Farha ta kalle shi ai dole in ji babu dadi."
"Ni yaushe nace maka haka?" Ta fada hankalinta yana neman tashi. Abbati kuwa kamar ya zuba ruwa a kasa ya sha saboda ya amince ba haukansa yake shi kadai ba.
"Kin yarda ni ki ke kallon? Uhmm?"
Yadda ya tsareta da ido sai taji kamar tayi tsuntsuwa ta bar wurin. Motarsu ta nuna da hannu ta fice daga wurin yana bin bayanta.
"Motar nan nake kallo ina tunanin kafin ku fito na zo na dauki hoto..."
"Cewa za ki yi baki manta alkawarinmu ba. Ina fata baki manta ba?"
Ko kadan bakinta da zuciya basa son yi masa musu. Sai dai bata saba ba sannan tana jin kunya. Kofar bangaren Mami ta kalla ta ce,
"Zan kirga goma duk wanda ya fara fitowa shi zai daukemu. Idan na gama ba a fito ba sai dai ka hakura."
"Na yarda. Bari na taya ki kirgawa."
Idanunsu akan kofar ta fara kiran 'daya' yana tayata. Suna kaiwa shida ya ce a sake wai da sauri take yi. Haka nan ta amince saboda bata son ta fara bada kanta a gabansa. Ta fahimci nan gaba kadan za ta kasa jurewa rashin kallonsa da ta tilasta kanta.
"Daya, da digo daya, digo biyu, digo..."
"Wannan kirgen naka ya sunansa?"
"Farhan Abbati style" ya fada kai tsaye yana yi mata wanu irin kallo. Kai ta sunkuyar ba tare da ta bashi amsa ba. Ya kawo ido ya zuba mata yana ta doka murmushi.
"Yaya Abbati ka zo in ji Mooomina"
'Yashshafa ce ta fito tana wannan tafiyar irin ta wanda ya sha da kyar daga kamuwa da cutar shan inna. Haushi ya kama shi na yadda ta bata daddadan moment dinsa da Farha.
"Mominki kuma 'Yash..."
"Shafa'a. Suna na Shafa'a" ta gabatar da kanta ga Farha da sauri kafin ya karasa fadin sunanta.
Abbati ya kada kai ya ce "to Shafa'a wace momin ke kirana?"
Ta san ya gane yake son bada ita a gaban wannan kyakkyawar matar.
"Moomina dai da muka zo tare."
Sai ya yi kamar lokacin ya fahimta "Au wai Gwaggo Deluwa?"
'Yashshafa ta juya a fusace ta bar wurin tana buga kafa don takaici.
Farha sai da tayi dariya sannan ta ce masa "baka kyauta ba. Ka fahimceta amma ka nuna baka gane ba?"
"Laifin naki ne don ke take son burgewa. Haka kawai muna 'yan kauyenmu don ta ganki ta fara kiran Innarta da Moomi" ya kuma fada yadda 'Yashshafan take cewa.
Farha dai hannu ta sa ta kare bakinta tana dariya kasa kasa.
"Kana da abin dariya" ta ce a hankali da suka shiga falon Mami Khadija daga bakin kofa.
"Zan yi komai domin ganin dariyarki Ya Farha. Idan kin bani damar zama abokin raba duk wani yanayi da za ki tsinci kanki daga yau har karshen rayuwarki ga mahaifiyata can..." ya nuna Baaba Mari wadda suke hira da Mami Khadija tamkar sun dade da sanin juna "zuwanki gabanta ku gaisa shi ne zai tabbatar min da cewa wannan Ya Farha Farhata ce"
A hankali ya yi maganar daidai jinta domin ita ce a gaba yana biye da ita a baya. Kalamansa sun fito da sigar roko, tararrabin rashin samun karbuwa da zallar soyayya. A duniyar Farha bata taba shiga yanayi makamancin wannan ba. Idan haka ake soyayya bata fatan ta sake yiwa kowa bayan Abbati. Wucewa ciki tayi ba tare da ta juya ko ta amsa masa da baki ba. Maimakon ta wuce ta damanta inda zai fi saurin sadata da Baaba Mari sai ta zaga ta hagu. Abbati yaji kamar ana ajiye masa duwatsu a zuciyarsa don tsoro. Sai da ta gama ja masa rai sannan tayi takun karshe ta zube a gaban Baaba Mari.
Sama sama yake jin muryoyinsu suna gaisawa. Farinciki ya mamaye zuciyarsa har yana neman yi masa yawa. Inda ya tashi ya je zai zauna waya ta shigo masa. Bakuwar namba ya gani ya dauka da sallama. Muryar wani da bai gane ba yaji.
"Idan kai ne Abbati ina tare da matarka ta ce sunnanta...ke ya ma sunanki?"
"Hanne" ya ji muryarta tar tana bada amsa.
"Yauwa Hanne. Wai wayarta babu chaji tana nan tashar Kawo ka tura a daukota. Sannan ta ci shinkafa da miya a wurin Esther, ni kuma ta sha lemo da ruwa a shagona. Kudin da ake binta dubu daya da dari uku ta ce za ka biya."
Ransa in ya yi dubu kuwa ya baci. Me yasa za ta wulakanta shi haka? Banda tahowa ba da izininsa ba harda cin abinci a tasha...kuma bashi!
Tashi ya yi bayan ya fadawa mutumin cewa gashi nan zuwa.
"Ina za ka je mu da muke jiranka mu kama hanya?" Baaba Mari ta tambaye shi.
"Wane irin kama hanya ko ruwa baku sha ba balle aci abinci? Don Allah ku zauna. Sauda duba ki gani idan plates din zasu isa." Inji Mami Khadija tana tashi.
Sai Abbati ya mata bayani a takaice "Baaba ku zauna Hanne zan dauko a tasha wai yanzu ta iso. Idan na dawo sai ku fito mu tafi." Ta gane ransa a bace yake sai ta ce masa sai ya dawo. Ta san zai yi mata bayanin komai idan sun kebe.
Yana daf da fita Mami Khadija ta ce "ba dai wata 'yar uwar taku bace ta iso? Allah Yaso baku kama hanya ba da kunyi sabani."
Deluwa fadi ba a tambayeka ba tayi tsagal ta ce "matarsa ce."
Bai gama fita ba saboda haka yaji abin da ta ce. Tsayuwar dole ce ta kama shi ya waigo a hankali yana neman idanun Farha domin ya gane tasirin maganar aurensa gareta.
Anti Hasiya ta gama shirinta da yamma za ta je gidan Salima. Washe-gari ne zai kama sunan Zara. Anyi mata waya an fada mata batun haihuwar amma har yanzu bata leka gidan ba. Shi ne Innayo ta ce taje ta duba mata. Maimuna ta zama mai wankan jaririya da kanwarta. Innayo ko kallo Zaran bata isheta ba. Jaririyar kuwa ko sau daya bata dauketa ba. Abin da ya tsayawa Zara a kahon zuci har ya zarta damuwarta na shariya daga Innayo.
Abinci dai mai rai da lafiya da kanta take dafawa ta kuma tabbatar ta ci. Daga nan bata sake bi ta kanta sai wani girki. Zara taji ta muzanta ta tsani kanta. Ko hira ta dauko Innayo ba ta taba amsa mata. 'Yan uwanta sun san me yake faruwa amma sun zabi su zuba ido 'ya da uwa su daidaita da kansu.
Da Anti Hasiya ta kira Honourable ta fada masa ta shirya sai ya ce ta tafi da Ayaah. Ta so yi masa musu sai ya nuna mata ya yi haka ne domin ta dinga shiga cikin ragowar kannen mahaifiyarta. Ba zai yiwu su zuba mata ido sai yadda take so ba. Amincewa tayi da kudurin idan Ayaah ta kawo mata raini za ta dauki mataki.
"Ke da wadda zamu gidan nata waye babba?"
Mamakin tambayar tayi tunda tun fitowarsu take zumbura baki. Anti Hasiya ta dauke kai ne kawai don bata son abin da zai janyo Ayaah tayi mata rashin kunya a adaidaita sahu.
"Daga Yaya Maimuna sai ita sannan Zara."
"Ita ce farar nan ramammiya kamar tsohuwa da muka gani a dakin Innayo da sallah?"
Anti Hasiya ta daga yatsa tana kada shi a gaban Ayaah.
"Ki kiyayeni Ayaah. Ban fito dake don ki ci mutumcin 'yan uwana ba."
Da yake bakinta bashi da linzami sai ta rage murya amma yadda ta san Antinta za ta ji.
"Ai dai kin san gaskiya na fada."
Anti Hasiya sai taki kula ta. Gaskiya Ayaah ta fada. Duk gidansu babu wanda ya kai Salima lalacewa a gidan miji. A kalla duk talaucin mijin Maimuna yana kaunar matarsa. Ita kuwa Salima Alh. Rabi'u ya gama cutarta. Duk dan Adam din da za a biya bashi dashi ina yaga daraja?
Daga soron gidan suke jin hargagin Maigidan Ale Gambo yana ta zaginta.
" 'Yar bakinciki, muguwa, azzaluma. Ban fada miki kafin na dawo ki je gida ba? Ace 'yar uwarki ta haihu kin kasa zuwa barka balle ki karbo min..."
Niyar Anti Hasiya ta gama jin dalilin wannan tijara. Idan ba haka ba Salima ba za ta taba fada da bakinta ba. Ayaah kuwa sai ta fada gidan tana doka sallama iya karfinta. Ta san duk abinsa dole ya sararawa matarsa a idon baki.
"Salamu alaikum. Anti Salima kina ina ne? Ina ta doka sallama naji shiru."
Baki Anti Hasiya ta rike tana biye da ita har tsukakkiyar tsakar gidan. Wai tana ta doka sallama. Harda wani Anti Salima kamar gaske.
Salima na ganinsu ta share hawayenta da sauri amma duk sun gani. Ale Gambo ba kunya ya amsa sallamar ya dora da karyar ceton kai.
"Yauwa Hasiya naji dadin ganinki. Don Allah ki fadawa Innayo babu hannuna a ciki. Tun ranar da aka sanar da batun haihuwar Zara nake cewa ta tafi gida barka taki."
Salima ta kalle shi da jajayen idanunta ka kawar da kai. Ale Gambo ya karar da duk wani kuzarinta. Fadan da damuwa tayi har sun haddasa mata hawan jini. Zaman 'ya'ya ukun da suka haifa take yi sai ko gudun karawa Innayo nauyi. A haka ma ita ce karfinta, ina ga ta koma gidan da yara? Dalilinta kenan na daina tanka masa duk bala'insa. Ta daina yin yadda yake so tun lokacin da Innayo tayi ciwon hakori. Duka da zagi babu irin wanda bai yi mata ba a tsukin lokacin. Yau ma tashi ya yi babu komai a jikinsa sai naira dari. Shi ne ya dauka ya bata wai taje gida barka sai ta fadawa Innayo tana son kudi. Ko dubu goma ce ta samo masa kamar ya bata ajiya. Kin tafiyarta be ya janyo mata abin da su Ayaah suka tarar.
"Zan yi mata magana." Kawai ta ce yasa kai ya fita.
Hannun Salima ta ja rai a bace suka shiga dan mitsitsin falonta. Yadda ta san halin Hasiya sai ta fara bata hakuri tun kafin tayi magana.
"Zan je barkar fa. Dama saboda halin Zara ne na ce sai na sami lokaci."
Hasiya ta dage gira ta sha kunu "sannu shugabar kasar Najeriya. Karshen aiki dai kenan da rashin samun lokaci."
"Baki yarda ba kenan?" Salima ta tambayeta tana kirkiro dariyar dole.
"Kema da ki ka fada baki yarda da kanki ba sai ni? Tun yaushe yake dukanki?" Da tayi shiru bata amsa ba sai Hasiya ta canja tambayar da cewa "me yasa baki taba fadawa kowa ba?"
Fashewa Salima tayi da kuka mai cin rai. Tana yi tana sheshsheka saboda yadda ya dade yana ci mata rai.
"Baba dai babu abin da zai yi min idan na fada. Innayo kuma in dai ba ajalinta kike so nayi ba ai ya kamata na hakura haka. Ita ba za ta huta ba Hasiya? Kullum cikin nema banda ma ciwon ido da hawan jini sun hanata sukuni kina tunanin da har yanzu bata cigaba da abinci ba?"
Hasiyan ma sai hawayen tausayin Innayo da Salima. Ta san da Innayo tana da karfi da tuni ta raba 'yarta da wannan kaddararren auren.
Share ido tayi ta kalli Salima "kin san dai bai kamata ki cigaba da zama a haka ba. Idan ya kuma zuwa zai dake ki kar ki yard. Ki kokarta ki kwaci kanki ko da cizo ne."
Ayaah na gefe da 'yat kwallarta saboda tausayin halin da Salima take ciki. Bata taba sanin abin da ya shafesu zai dameta ba amma yau da akayi a kunnenta taji sai ya tsaya mata a rai. Tana jin gurguwar shawarar Anti Hasiya a cewarta ta shiga zancen nasu ba jiran gayyata.
"Wane irin ta kwaci kanta Anti Hasiya? Ko dai baki kula da girmansa bane? Jibgege ne, wannan idan aka sami akasi ta iya cizonsa wallahi karshenta ya zubar mata da hakora. Bai yi ruwan imani ba ko kadan."
Da hawayen sai da tasa Salima yin murmushi da ta ce wai bai yi ruwan imani ba. Hasiya ta ma manta tare suke saboda basu saba hada fita ba. Daure fuska tayi a zatonta Ayaah rashin kunya za ta yi musu.
"Sai ki kawo taki shawarar tunda baki san idan manya suna magana ki kama bakinki ba."
Ayaah ta tsuke bakin tsiwarta "naga nima dai kanwar mamana ce Anti Saliman nan. Abin da ya shafeta ai ya shafeni."
"Haka! Wanda ya shafeni ne bai shafeki ba ko?"
Salima me zata yi banda dariya. Rabonta da ganin Ayaah an kwana biyu. Amma idan ta hadu da Hasiya da wuya su rabu bata dauko zancenta ba. Abin mamaki shi ne kullum hirar korafi ce akan rashin ji da rashin kunyar Ayaah gareta, amma fa ko Innayo ta fahimci ba karamin so take yi mata ba. Irin son da akasarin uwaye suke yiwa tabararrun 'yan autansu.
"Nima ai baki damu da abin da ya shafeni ba."
"Ayaah banda rashin kunya mana. Shi yasa kuke fada da babarki. Wane dan arzikin ne iyayensa suna fada yana fada banda abinki? Bata hakuri." Salima ta umarceta.
Sai da ta yatsina baki ta bada hakurin. Hasiya za tayi magana Salima ta girgiza mata kai da sauri sai tayi shiru.
"Sai ki kawo taki shawarar tunda tawa bata yi ba."
"In yi magana kuma ace bani da kunya?" Ayaah ta fada idonta akan Anti Hasiya.
"Tunda ita ta baki dama ki fada mana. Idan baki fadi taki ba zan dauki ta Hasiya. Iyaka dai ya zubar min da hakora ku zo dubiya."
Anti Hasiya da Ayaah suka yi dariya tare. Sannan Ayaah ta ce,
"Anti Salima idan ya sake zuwa dukanki kar ki gudu kuma kada ki kare. In zaki iya ma ki takali fadan don ayi a wuce wurin. Daga nan dukan farko ki zube kasa ki daina motsi. Don Allah Anti duk yadda zai yi kar ki motsa. Wai baki da 'ya'ya ne?" Ta tambaya tana duba cikin falon kamar lokacin zasu bayyana.
"Allah dai Ya shiryeki. Su Murja sun san kowa cikin 'yan uwansu banda ke. Su uku ne. Babban namiji yana makarantar kwana. 'Yan matan kuma suna islamiyya."
"Sun kai shekara goma?"
"Goma da sha uku."
Ayaah tayi dariya "sun san yana dukanki?"
"Sun sani."
"Anti Hasiya don Allah mu zauna har su taso in yi musu karatun ceton uwa."
Salima da Hasiya sai suka jidadi. Ko me zata ce zasu saurara domin su kara janyota jikinsu ta san mahimmancinsu. A nata bangaren kuwa hasashen yadda zata taimaki kanwar mahaifiyarta take yi.
For once in her life Ayaah sai taji dadi wai yau ita Anti Hasiya ta bawa dama har take saurarenta haka.
Akan hanyarsu ta zuwa gidan Innayo, bayan sun bawa Ayaah dama ta yiwa kannenta hudubar taimakawa mahaifiyarsu ne Hasiya ta dinga maimaita kalan Salima a zuciyarta "Wasu yaran tsabar son ki sauraresu yake saka su fandarewa ko yin abun daukar magana. Da gangan Ayaah take tunzuraki dazu don kawai ki kulata taji dadi. Da alama mai son kulawarce sai aka yi rashin sa'a masu sauraronta basu dorata a turba mai kyau ba har zamanku ya kasance irin haka. Daga yanzu ki dinga janta a jiki kamar yadda kike yiwa 'yan uwanta kina nuna mata cewa tana da matsayi a wurinki ita ma."
Chapter 8 · 0% Book details