← Book details Tsatsuba Book 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 3 OF 3

Part D.

Tsatsuba Book 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi

.
A can filin gasat kuwa lokacin da aka ruguntsume da azababben yaki tsakanin sadauki darkus da jaruma siyama sai da suka shafe rabin sa a cif suna kaiwa junansu SARA DA SUKA cikin tsananin zafin nama juriya da bajinta amma dayansu bai sami nasarar koda lakutar jikin daya ba
.
Al amarin da yai matukar baiwa kowa mamaki kenan da yawa daga cikin yan kallo dai sun firgice ne da al amarin siyama kai harni AlQuyraemey da nake wannan typing din na rikice da lamarinta, Kai wasu ma sai suka rinka cewa siyama ba mutum bace Aljana ce don babu yadda za ayi ace tana ya mace yar shekara tara kacal a duniya ta sami irin wannan gagarumin karfin damtse da iya yaki haka, lallai akwai aikin sihiri acikin lamarin.
.
Abinda basu sani ba shine siyama tasha Sadaukantaka ne a nono kuma tun tana da shekaru hudu kacal a duniya mahaifinta ya far bata horon yaki. Ana cikin wannan haline aka jiyo sautin tashin tambura da bushin Algaita alamar cewar ga sarauniya Luzuraina nan ta iso, take farinciki ya kama sarki hulbasu ya dubi mahaifin jaruma siyama yace
abokina ga matata nan ta iso tare da kawarta babbar bakuwarmu
.
Koda jin haka sai abul siyama ya budi baki da nufin ya tambayeshi ko wacece bakuwar, amma sai ya kasa sakamakon ganin wani irin mugun naushi da darkus ya yiwa siyama a fuska cikin tsananin shammace, saboda karfin naushin sai da jini yai tsartuwa daga cikin hancinta kuma ya yi feshi daga cikin bakinta ta tafi luuu ! Kamar zata kife kasa da baya amma sabo da tsananin juriya sai ta mike tsaye kyam ta doki kasa da kafarta guda tayi sama cikin shammace itama ta doki fuskar darkus da tafin kafarta ta dama tana mai jera masa duka uku a saman, sannan ta duro kasa ai kuwa sai gashi shima hancinsa da bakinsa na yoyon jini har shima yaji wani jiri ya kwashe shi ya tafi luuu ! Zai kife da rub da ciki amma sai yai sauri ya tokare jikinsa da hannu guda ya taso sama kamar sifirin suka ci gaba da sabon masifaffen yaki kamar ma lokacinne suka fara yakin, A dai dai wannan lokaci ne gimbiya luzuraina da shardila suka shigo cikin filin gasar suka durfafo inda su sarki ke zaune dakaru na take musu baya, tun daga nesa Abul siyama ya hango shardila sai yaji zuciyarsa ta buga da karfi irin bugawar da bai tabaji ba a rayuwarsa
.
Koda ya sake yin arba da dakarun dake yi mata rakiya wato su sadauki Murzanu sai jikinsa ya kama tsuma nan da nan gumi ya fara karyo masa domin a sannan ne ya tabbatar da abin da yake zargi duk da cewar kuwa shardila ta rufe fuskarta da bakin kyalle.
.
Al amarin shardila kuwa tunda ta shigo filin sai ta kama raba idanunta a cikin yan kallo ba don komai ba sai domin taga Abul Husna wanda danta yarima Hulkas ya bata labari domin ta gusar da wasu wasin dake cikin zuciyarta bisa wannan daliline ta yi ta ware idanuwa ko zata ga mutum mai hannu daya da nakasashshiyar kafa kuma ta rinka kallon fuskokin mutane don ta tabbatar da cewa tana yin arba da fuskar tsohon mijinta take zata shaidashi, amma har suka iso inda su sarki hulbasu ke zaune amma bata ganshi ba, abin da ya sa ko kadan hankalinta bai kawo kan Abul Siyama ba shine ta san cewa babu mai ikon zuwa kusa da sarki Hulbasu ya zauna face ya kasance jinin sarauta ko kuma wani mai fada aji a birnin, bugu da kari kuma fuskar Abul siyama a rufe take cikin rawani kuma ya lullube gaba dayan jikinsa da wanibabban mayafi na alfarma, luzuraina da shardila suka zo suka zauna kusa da sarki hulbasu daga hagunsa shi kuwa abul siyama yana zaune a damansa tun da suka zauna abul siyama bai yarda ya kalli inda suke ba shi kuwa hulbasu da yake gaba daya hankalinsa ma yana kan gumurzun da ake yi a tsakiyar filin gasar tsakanin jaruma siyama da sadauki durkus ko tunanin gabatar da Abul siyama bai yi ba awajan su Luzuraina yayin da shardila ta kyalla ido ta hango siyama a tsakiyar filin gasa wacce ke ta faman gumurzun yaki tayi arba da fuskarta sai taji zuciyarta ta buga da karfi ba komai ne ya haddasa hakan ba face jaruma siyama tana matukar kama da mahaifinta, nan take shardila ta gane cewa lallai jaruma siyama yar tsohon mijinta ce wanda take tunanin cewa ya mutu fiye da shekaru bakwai baya lallai hakan ya tabbatar mata da cewar kenan Hailur na nan a raye kuma a cikin wannan gari.
.
Koda gama aiyana hakan sai shardila taci gaba da kalle kallen ko ina a cikin filin gasar ko zataga Hailur shi kuwa Hailur da ya lura da ita da kuma halin da take ciki sai ya noke yana mai sunkuyar da kansa kasa yaki yarda su hada idanu, saboda ya tabbatar da cewa suna hada idanu zata shaidashi duk kuwa da cewa ya rufe fuskarsa da rawani idan kuwa ta shaidashi a gaban kowa zata fashe da kuka ta rungumeshi, tana yin hakan kuwa asirinsa zai tonu su sadauki Murzanu su shaidashi idan kuwa suka shaidashi komai ya tabarbare ke nan domin sai labari ya riski sarki shardas cewa har yanzu yana nan a raye, da zarar hakan ta faru kuwa hatta sarki hulbasu ya shiga cikin tashin hankali kenan da masifa don sarki shardas Cewa zaiyi ya boye babban makiyinsa a birninsa don haka sai ya yakeshi ya kau dashi kuma ya mallake kasar ma gaba daya, nan take idanun Hailur suka ciko da kwallah suka fara zubar da hawaye domin shi a zatonsa ma tuni shardila ta dade da mutuwa, amma yanzu da ya ganta a cikin shiga ta alfarma irin ta sarakai, kuma yaga su sadauki Murzanu na take mata baya sai ya kamu da tsananin bakinciki mara misaltuwa domin ya gane cewa lallai a yanzu ta zama matar sarki shardas, aikuwa bayan su shardila sun zauna sai hailur yaga yarima
hulkas ya mike zumbur ya tafi izuwa wajan shardila ya rungumeta nan take zuciyar hailur ta sake bugawa da karfin gaske a karo na biyu ya tambayi kansa acikin zuciyarsa yace ' shin wannan yaro dana ne ko kuwa dan sarki shardas ne tabbas wannan yaro da uwarsa yake kama don haka bani da tabbacin cewa dana ne, tabbas shardila na dauke da cikin dana, wai shin kana zaton cewa sarki shardas zai amince ne shardila ta haife danka a cikin gidan sarautarsa, kai hailur ! Idan ma mafarki kake yi toka farka ''
.
Wannan shine gargadin da zuciyar hailur takeyi masa nan fa yaji cewar babu abinda yake bukata sama da ya sami damar tattaunawa da shardila domin ta bashi amsar wadannan tambayoyi dake yi masa yawo a cikin zuciya lokacin da shadila tayi arba da jaruma siyama taga fuskarta a zahiri sai hankalinta ya dugunzuma ainun kuma taji zuciyarta taci gaba da dukan uku uku ba komaine ya janyo hakan ba face ganin cewa tabbas siyama tana tsananin kama da tsohon mijinta hailur babban abin ma da ya kara dugunzuma hankalinta shine ganin irin yanayin yadda take yin yakinta iri daya ne sak dana tsohon mijinta Hailur.
.
Kafin shardila ta ankara tuni ta fara kuka tana mai zubar da hawaye gami da ci gaba da kalle kalle da waige waige a cikin filin gasar ko zata hango masoyinta hailur amma shiru kamar maye yaci shirwa ashe duk wannan hali da ta shiga Hailur ya lura da ita duk da cewar fuskarsa a rufe take cikin rawani kuma yana zaune a daman sarki ita kuma tana tare da luzuraina abarin hagun sarkin.
.
Lokacin da jaruma siyama da sadauki darkus
sukaci gaba da fafata kazamin yaki a karo na biyu sai ya zamana cewa karfi yazo daya an rasa wanda zai iya cutar da wani a cikinsu, duk da tsananin karfin damtse irin na darkus sai gashi naci da juriyar siyama da tsabar horon yaki da ta samu a wajen mahaifinta yasa ta iya kwatar kanta awajensa tun suna kaiwa junansu sara da suka da takubban hannayansu har sai da suka gaji ainun makaman nasu suka subuce daga hannayansu suka ci gaba da gabzar juna da hannu, Duk irin naushin da darkus yayiwa siyama sai aga ta rama wato dai itama tayi masa irinsa. Kai ! Tun suna tsaye akan duga dugansu tsabar masifar yaki sai da takai ga sun durkushe kasa a tare kuma a lokaci guda suka ci gaba da gabzar junansu a hakan kowannansu ya kama layi kamar wanda ya sha giya suka bugu har izuwa lokaci mai tsawo suna cikin wannan hali daga can kuma sai duk su biyun suka bingire da baya luuu ! Suka baje a kasa tare suna numfarfashi kamar ransu zai fita...........
.
A nan ne Littafin Tsatsuba Na Hudu Yazo Karshe Marubucin Littafin yace....
.
YAYA KARSHEN WANNAN GASA ZATA KASANCE TSAKANIN SADAUKI DARKUS DA JARUMA SIYAMA ???
.
WAYE ZAI SAMU NASARAR ZAMA ZAKARAN GASAR JARUMTAKA A TSAKANINSU ?
.
MAI ZAI FARU IDAN GIMBIYA SHARDILA TA GANE MASOYINTA KUMA TSOHON MIJINTA HAILUR DA SUKA RABU TSAWON LOKACI ?
.
SHIN ASIRIN ABUL SIYAMA YANA TONUWA HAR LABARI YA KAI KUNNEN BABBAN MAKIYINSA SARKI SHARDAS WANDA ABUL SIYAMA KE ZARGIN YA AURI MASOYIYARSA KUMA MATARSA?
.
MAI ZAI FARU IDAN YA SAMU LABARI ?
.
Marubucin littafin yace mu hadu a littafi na 5 donjin cigaban wannan kayataccen kasaitaccen labari Daga mai debe muku kewa a ko yaushe Ni ne dai Abubakar Saleh AlQuyraemey nake cewa Mu zama Lafiya.
.
Amma Ku meye kuka hango a haduwar Hailur da shardila wata irin Dambarwa za a yi ne kam sai naji daga gare ku...
Chapter 3 · 0% Book details