← Book details Tsatsuba Book 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 2 OF 3

Part C.

Tsatsuba Book 4 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Na Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi

A dai dai wannan lokaci ne filin gasar yayi tsit tamkar mutuwa ta gifta kawai sai mai gabatarwa ya kira sunan jarumin da zai kara da darkus ba wani bane jarumin face jaruma SIYAMA.
.
Koda jama a sukaji an ambaci sunan ya mace sai kowa ya gwale idanunsa domin yaga ko wacce jaruma ce haka mai tsautsayi wadda ta gaji da zaman duniya. Domin manyan mazaje ma da suka kasance sadaukai kuma wadanda suka sha gwagwarmaya iri iri a filin daga suna tsoron a hadasu gumurzu da darkus don su san cewa ajalinsu ne ya zo.
.
Kwatsam ba zato ba tsammani sai akaga wata yar matashiyar budurwar yarinya ta taso daga wajan da su sarki ke zaune tana sanye da kayan yaki ta shigo cikin tsakiyar filin gasar ko garkuwa babu a hannunta kuma takobinta ma na cikin kube sakale a kuibin cinyarta ta hagum nan fa mamaki ya turnuke jama a wasu suka kamu da tsananin tausayin siyama har suna zubar da hawaye saboda suna ganin cewa mugun kisan gilla darkus zaiyi mata.
.
Wasu mutanan kuwa sai suka kama tsinewa
mutanan da suka yi sanadiyyar shigar wannan kyakkyawar yarinya cikin wannan gaasa yarima hulkas da barmas kuwa hankalinsu ne yayi matukar dugunzuma ainun har jikinsu ya kama tsuma bisa ganin cewa Siyama zatayi Yakine da DARKUS hm Nimafa nayi mamaki kamar na tsaya da typing amma muje kawai.
.
Duk da cewa sun ga irin jarumtakarta sai da zuciyoyinsu suka karaya yarima barmas bai san sa adda ya taso daga inda yake zaune ba
yaje inda sarki da mahaifin siyama ke zaune ya dubi mahaifin siyaman a dimauce yace haba ya abul siyama yanzu kana gani za a kashe yarka amma kayi shiru hm AlQuyraemey nake tabbas wannan hadi da akayi babu adalci acikinsa kawai so ake a kashe yarka koda jin wannan batu sai mahaifin siyama yayi murmushi ya dubi yarima barmas cikin girmamawa yace kwantar da hankalinka yakai yarima babu abinda zai sami yata, ka koma wajanka ka zauna ka morewa idanunka da kallon abin mamaki cikin alamun tsananin damuwa yarima barmas ya juya ya nufi can wajen zamansa yana waigen mahaifin siyama amma duk sa adda ya waigo din sai yaga shima ya kurawa hulkas idanu yana yi masa wani irin kallo mai dauke da ayar tambaya.
.
A wannan lokaci ne sarki Hulbasu ya dubi mahaifin siyama cikin alamun mamaki yake yakai abokina wai shin mene ne dalilin da yasa ko yaushe kake rufe fuskarka ne da mayafi, ni kaina ban taba ganin irin kamanninka ba kuma ko yaushe a haka kake koda kuwa a cikin daji kake shin ina dalilin yin hakan?
.
Sa adda mahaifin siyama yaji wannan tambaya sai yayi murmushi ya ce ya shugabana kayi hakuri ba zan iya baka amsar wannan tambaya ba a yanzu saboda wani muhimmin dalili da ya shafi rayuwata amma nayi maka alkawarin idan lokacin da ya kamata ka sani yayi zaka sani, ina boye wannan sirri ne sabo da samar da tsaro ga rayuwata data iyalina ya shugabana idan ba zaka damu ba nima ina da wata tambaya guda daya a gareka wai shin wane ne wancan yaro wanda ke tare da danka yarima barmas daga ina ya fito kuma mene ne dangantakarsu da sarauta?
.
Koda jin wannan tambaya sai sarki hulbasu ya kyalkyale da dariya sannan yace akan wanne dalili zan baka amsar wannan tambaya da kayi mini alhalin nima ina da nawa tambayoyin kwatankwacin irinsu a kanka kuma kaki ka bani amsa tun daga ranar da na fara ganinka ?
.
Nima ba zan iya baka amsar wadannan tambayoyi na ka ba saboda tabbatar da tsaro a kan wannan yaro domin kuwa idan wani abu ya sami lafiyar wannan yaro bama niba gaba daya jama ar dake cikin wannan nahiya tamu sai sun shiga uku, sa adda mahaifin siyama yaji wannan batu daga bakin sarki sai kansa ya daure ya cika da mamaki fiye da ko yaushe har ya budi baki da nufin ya sake yiwa sarki wata tambaya sai kawai yaga dakus ya ruga da gudu izuwa kan siyama yana mai daga takobinsa sama kuma yana mai kwarara uban ihu mai tsananin firgitawa irin wanda ka iya tarwatsa dubunnan dakaru a filin daga kuma ya furta tane a cikin mugun nufi na gamawa da ita farat daya ita kuwa siyama sai ta tsaya cak a inda take to gezau batayi ba kuma ko kifta idanunta ba tayi ba koda dakus ya iso daf da ita sai ya kawo mata wani irin wawan sara a wuya da nufin ya cisge mata kai cikin bakin zafin nama jaruma siyama ta tale kafafunta tayi kasa, takobin darkus din ta bysari iska ya sake kai mata wani mugun sara a fusace siyama tana durkushe a kasa tayi wata irin alkafira cikin gwaninta ta kaucewa harin nasa, koda takobin darkus tasari kasa sai ta nutse izuwa cikin karkashin kasar gaba dayanta saboda tsananin karfin saran nasa da nauyinsa kafin darkus ya zaro takobin tuni siyama ta doki kasa da tafin hannunta na hagu tayi sama sai
kawai ta doki gadon bayansa da kafafunta biyu darkus yaji kamar wani dankareren kato ne yayi masa dundu a gadon baya kuma duk da tsananin girmansa da nauyinsa sai da ya tafi taga taga da gaba kamar zai kife kasa, da kyar ya iya cijewa ya tsaya kyam a tsaye.
.
Al amarin da yai matukar razanashi da bashi haushi kenan, domin wannan ne karo na farko da aka taba samun jarumin da ya sami nasarar
.
Dukan jikinsa har ma ya kusan kaishi kasa, koda yan kallo sukaga wannan gagarumar jarumtaka da siyama tayi sai suka cika da tsananin mamaki filin ya kaure da ihu gami da shewa aka shiga yiwa siyama kirari gami da jinjina, yarima hulkas kuwa saboda murna ma bai san sa adda ya daka tsalle ba daga kan kujerar da yake zaune yana shewa shewar tasa ce tasa har siyama ta juyo ta dubeshi kawai sai tayi masa murmushi, take hulkas yaji wani irin farin ciki mara misaltuwa da dadi ya lullubeshi saboda wannan murmushi da tayi masa shi kuwa sadauki Darkus fusata yayi ainun ya juyo da sauri ya sake rugowa izuwa kan siyama aikuwa itama sai tayi wuf ta zare takobinta ta tareshi suka ruguntsume da azababben yaki mai tsananin ban tsoro da razanarwa, gaba daya jama ar dake filin wannan gasar sai da hankalinsu ya
dugunzuma gaba daya saboda tun da aka fara wannan gasa ta jarumtaka tsawon shekaru ba a taba ganin gumurzu ba irin wannan mai tsananin hadari wow.
.
A can gidan sarauta kuwa gimbiya shadila bata farka ba daga barci har sai bayan lokaci mai dan tsawo koda ta bude idanunta taga ashe ma tuni gari ya dade da wayewa har rana ta kwalle kuma taga babu jarumi hulkas kwance a kusa da ita akan gadon da take kwance sai ta mike zaune zumbur a lokacin da zuciyarta ta buga da karfin gaske, kawai sai ta sauko daga kan gadon da sauri ta leka bandaki don tunanin ko hulkas na ciki yana wanka amma sai ta iske bandakin wayam babu kowa a cikinsa a gigice shadila ta gaggauta tayi wankanta sannan ta kimtsa gama shirinta keda wuya sai taji an kwankwasa mata kofa saiga wata kuyanga ta shigo, kuyangar ta zube kasa bisa guiwoyinta ta ce ya shugabata sarauniya ta turoni nayi miki jagora zuwa can turakarta domin tana jiranki kuyi kalaci, cikin mamaki shadila ta dubi yadda rana ta kwalle ta cikin tagar dakin nata sannan ta dubi kuyangar tace yanzu kina nufin kice har yanzu sarauniya bata yi kalaci ba, kuyangar ta sake risina tace ai saboda kina barcine shi yasa taki tayi kalacin da kanta, amma tafi sa a biyu da gama kimtsawa har ma sarki dasu yarima sun dade da tafiya kallon GASAR JARUMTAKA.
.
Koda jin wannan batu sai shardila taji zuciyarta ta buga da karfi kuma ta ji babu abinda take so sama da ta ganta a filin wannan gasa, don haka cikin sauri tace da kuyangar yi maza ki kaini wajan sarauniya ba tare da bata wani lokaci ba kuwa sai kuyangar ta juya da sauri ta fice daga cikin dakin shardila na biye da ita, luzaira na zaune akan teburan cin abincin dake falonta ita kadai tana jiran sai ga kuyanga tare da shardila sun shigo, cikin murna luzaira ta mike tsaye da sauri ta taryo shardila ta kamo hannunta ta kawota izuwa kan kujera suka zauna tare, ba tare da bata wani lokaci ba suka kama cin abincin har suka kusan gama cin abincin dayansu baice kala ba a sannan ne shardila tayi gyarar murya ta dago kai ta dubi luzaira tace yake kawata ki gafarceni na bata miki lokaci da kika kawo har yanzu baki yi kalaci ba domin barcina ne yayi nauyi, kafin shardila ta gama wannan magana sai luzuraina ta tari numfashinta tana mai kallonta cikin murmushi tace haba yake kawata kada ki sawa kanki damuwa akan hakan domin danki ya gaya mini cewar yana
zaton jiya bakiyi barci da wuri ba shin kina da wata lalura ne ta rashin lafiya ko kuwa akwai wata matsala dake damunki.
.
Koda jin wannan tambaya sai shardila ta yi murmushi tace kawata babu abinda yake damuna kuma bani da wata matsala haka kawai dai naji idanuna sun bushe jiya da daddare wata kila bakunta ce ta janyo hakan
koda jin haka sai luzuraina ta kyalkyale da dariya ta yiwa shardila wani irin kallo na rashin yarda domin ba ta yarda da abinda ta fada ba sai dai ta dubeta tace ko dai kewar sarki shardas ce ta hanaki barci kinga tashi mu hanzarta mu tafi filin gasar nan domin na san cewa yanzu tuni an dade da fara wasa babu mamaki ma an shiga kewaye na uku. .
.
Kafin luzuraina ta gama rufe bakinta tuni shardila ta wanke hannayanta ta mike tsaye saboda dokin zuwa wannan filin gasa, nan dai suka gama kimtsawa suka nufi wani babban fili inda aka tanadar musu keken dokin da zasu hau tare da dakarun da zasuyi musu rakiya tun daga nesa shardila ta hango dakarun sai tayi sauri ta rufe fuskarta da wani
bakin kyalle ya zamana cewa idanunta kadai ake gani ba komaine yasa shardila ta rufe fuskarta ba face a rayuwarta babu abinda ta tsana sama da mutane suyi ta kallonta, abinda bata sani ba shine tsananin kyawun fuskarta da kyan surar jikinta ne ya janyo mata kallon da ake yi mata nan dai su luzuraina suka shiga cikin keken dokin aka ja
aka fice daga cikin gidan sarautar aka durfafi filin GASAR JARUMTAKA.
.
NIMA KUMA sai na dakata anan na nufi Filin daga Wato neman na Abinci Kuma sai Allah ya kaimu Gobe zamu ci gaba
Nidinne dai

TSATSUBA
Littafi Na Uku (4)
Chapter 2 · 0% Book details