← Book details Tsatsuba Book 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 3

Gabatarwa

Tsatsuba Book 4 Complete Hausa Novel · about 18 min read

TSATSUBA
Littafi Na Hudu (4)
Part A.
Na Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey

.
Lokacin da Shadila ta tambayi kanta a cikin zuciyarta cewar 'Anya kuwa Hailur yana raye a duniya amma bai nemeta ba? Kuma ta kasa baiwa kanta amsa sai idanunta suka kekashe ga barin barci ta kasa koda risinawa a wannan dare haka dai taci gaba da mutsu mutsu akan gadonta taci gaba da tunanin jarumi hailur.
.
A wannan rana dai shadila kwata kwata bata rintsa ba har sai da alfijir ya keto a sannan ne barcin ya saceta ba tare da ta sani ba.
.
Al'amarin su yarima hulkas kuwa lokacin da gari ya waye ya farka yaga mahaifiyarsa na ta barci bata ma da niyyar farkawa sai ya ki tashinta cikin doki da zumudi hulkas yaje yayi wanka ya kimtsa gama hakan ke da wuya sai ga yarima e ka ya shigo cikin dakin shima ya caba ado fuskarsa cike da annuri ko da yaga hulkas ma ya gama shiri tsaf sai yayi murmushi yace hakika naga alamar cewa ka fini dokin son zuwa kallon wannan gasar jarumtakar da za ayi Yau.
.
Hulkas ya maida masa da martanin murmushin yace Ai ji nake ina ma kamar na tafiyar da rayuwar da tsuntsu na ganni a can ba don komai ba sai don ma kawai na sake ganin kyakkyawar fuskar nan ta jaruma siyama kuma naga yadda zata fafata yaki da manyan mazaje barmas ya kyalkyale da dariya yace Ai dama nasan cewa tatsuniyar Gizo Bata wuce ta Koki, to ai saikayi sauri kazo muje muyi buda baki a can turakar mahaifiyata amma me ya faru naga har yanzu mahaifiyarka tana yin barci bata farka ba?
.
Koda jin wannan tambaya sai yarima Hulkas yayi ajiyar zuciya yace ina kyautata zaton cewa jiya da daddare ba tayi barci da wuri ba shi yasa yanzu take ramuwarsa cikin alamun damuwa yarima barmas yace aukuwa NA kwanaki t ke Kai by tt tttt I will t a few minutes ago rr I t I r a little more time I t a little more time t r I will have a talk a rt I t tr I have a meeting at a t a t tr a r f I r tr I will forward it t a little more time I will be rr I will be in touch soon to be in the office tomorrow and tr to get the kids to the park and ride from my account ff for Friday rr for TR he is a good guy and I think the office and I can get tytt ummina ma ba zatayi buda baki ba sai tare da mahaifiyarka don cewa tayi nazo na tafi da ku muje muyi buda bakin gaba daya kuma tare zamu tafi can filin yin yoga gasa har da sarki da kansa kana ganin cewa ba zaka tasheta daga barcin ba?
.
Hulkas yace A'a bai kamata na tasheta ba tunda akwai bashin barci a tare da ita muje a yiwa mahaifiyar taka bayani koda jin haka sai yarima barmas ya juya ya fice dagacikin dakin shi kuma yarima hulkas ya bishi da sauri suka durfafi turakar Luzuraina.
.
Turakace babba wadda aka cikata da kayan kawa irin na sarakai. A gefe daya an ajiye wani dogon teburin cin abinci mai
dauke da kujeru goma sha biyu, A kan wannan teburi an shirya abincin kalaci iri iri har kala goma sha daya bisa farantai luzuraina ce kadai zaune akan wannan babban tebur tana jiran isowar sushadila.
.
kwatsam ! Sai ta hango yarima hulkas tare da danta barmas su biyu kacal sun shigo cikin falon. Al amarin da yai matukar bata mamaki kenan domin su uku ya kamata ta gani tun kafin su karaso gareta luzuraina ta dubi yarima hulkas cikin alamun damuwa tace ina mahaifiyarka?
.
Me yasa bata biyoku ba kun taho tare, yarima hulkas ya risina cikin biyayya ya gaida luzuraina yace ina zaton cewa ummina batayi barci ba jiya da wuri sakamakon labarin dana bata akan inda muka je jiya nida barmas.
.
Koda jin wannan batu sai luzuraina tayi shiru tana tunani na tsawon yan dakiku sannan ta mike tsaye ta dubi yarima barmas tace ku zauna kuyi kalaci kai da abokinka ni ba zan yi ba har sai shadila ta tashi da kanta idan kun gama cin abincin kuje ku jira sarki a falonsa domin yana fitowa sai ku tafi filin gasa tare idan ya tambayeni ku gaya masa cewa zamu riskeku a can nida kawata shadila koda gama fadin hakan sai luzuraina ta mike tsaye daga kan kujerar da take zaune ta tafi can cikin turakarta ta barci, barmas da hulkas kuwa sai suka zauna suka yi buda bakinsu cikin sauri, suna kammalawa sai suka tafi zuwa can falon sarki hulbasu ba tare da bata wani lokaci ba kuwa sai ga sarki hulbasu ya fito a cikin gagarumar shiga ta alfarma da kasaita fuskarsa cike da annuri kallo daya mutum zaiyi masa ya gane cewa yana cikin walwala da murnar zuwan wannan rana ta gasar jarumtaka wacce ake yi a birninsa a karshen kowacce shekara, koda sarki hulbasu yaga yarima hulkas da yarima barmas su biyu kadai a zaune babu iyayansu sai annurin fuskarsa ya dauke ya dubi barmas cikin alamun damuwa yace ina iyayan naku mata?
Me yasa basu zo nan ba tare daku?
Nan take barmas ya yiwa sarki hulbasu bayani kamar yadda luzuraina tayi masa. Koda jin haka sai sarki hulbasu ya dubesu yace shi ke nan ku tashi mu tafi filin gasar nan domin na san cewa tuni an gama hallara ni kadai ake jira a fara wannan gasa
nan take su hulkas suka mike tsaye suka bi sarki a baya suna isowa babbar haraba ta bangaren turakar sarki hulbasu sukayi kicibis da dakaru a tsai tsai cikin shigar yaki bisa dawakai wadanda za su yiwa sarki rakiya izuwa filin gasar a gefe daya kuma ga dokin sarki tare wadansu dawakan guda hudu
.
Ba tare da bata wani lokaci ba aka kawo wa sarki dokinsa ba tare da bata
.
Wani lokaci ba aka kawowa sarki dokinsa ya hau barmas da hulkas ma sai aka kawo musu biyu daga cikin wadannan dawakai guda hudu suka hau aka dunguma gaba daya aka nufi filin gasar.kuma hardani kaina AlQuyraemey Ina binsu a baya
sai dai wannan filin anyi shine a tsakiyar gari kusa da babbar kasuwa ta garin wacce take gagarumin ci a duk ranar da za ayi wannan gasa.
.
Filin ya kasance katon gaske kuma an kewayeshi da katanga doguwar gaske daga cikinsa an kewayeshi da kujeru sama da guda miliyan biyu amma duk ranar da za ayi wannan gasa sai mutane sun rasa wajan zama saboda cikowa sai dai ka rinka ganin jama a akan katanga, kai wasu ma basa samun damar shigowa cikin filin gasar sai dai su hau saman benayen gidaje da bishiyoyi suna hango abinda ke faruwa a cikin filin.
.
A gefe daya ne na filin aka gina inda sarki da mukarrabansa ke zama don kallon wannan gasa duk wanda bai kasance jinin sarauta ba to bai isa yaje ya zauna ba a wannan wuri ba face ya
kasance babban attajiri ko mashahurin boka ko kuma makusancin sarki kamarni Al Quyraemey ke tare da ku.
.
Al' amarin siyama kuwa da iyayanta lokacin da gari ya waye suka gama shirin tafiya filin gasa si mahaifinta ya rufe fuskarsa da rawani ya zamana cewa idanunsa kadai ake gani sannan suka hawo dawakai guda uku suka durfafi filin gasar jarumtakar. Lokacin da suka iso bakin kofar filin gasar sai suka
iske gurin ya cika makil da mutane babu masaka tsinke ganin hakan ne yasa hankalinsu ya dugunzuma ba don komai ba sai don sun san cewa siyama ce kadai za a bari ta shiga cikin filin gasar tunda tana da shaida ta jaruman takara su kuwa sai dai su hau kan bishiya ko wani gidan mai bene.
.
Koda siyama ta lura da irin damuwar da iyayanta ke ciki sai ta nunawa masu gadin filin shaidarta ta jarumar gasa kuma ta gaya musu cewa ga iyayanta a tsaye tana son ta shiga tare dasu ciki koda jin haka sai shugaban masu gadin wani narkeken katon badakare ya dubi siyama sama da kasa cikin raini ya bushe da dariya yace yanzu ke wane ganganci ne ya sa kika shiga wannan gasa kina matsayin mace, kuma yarinya karama haka ? Shin iyayan naki sun gaji da ke ne shiyasa suke so su ga irin kisan gillar da za ayi miki? Toki sani cewa indai fili ya cika babu mai sake shiga ciki face sarki da mukarrabansa, ko ki shiga ke kadai ko kuma ki fasa yin gasar gaba daya, a wannan lokaci su kansu tsirarun 'yan kallon dake tsaye a kofar filin wasan kallon siyama suke yi kawai wasu suna mamaki wasu suna ta sheka mata dariya suna yi mata kallon mahaukaciya wacce ta gaji da zaman duniya, wasu ma sai suka kama tsegumi suna cewa bata da iyaye, baiwa ce kawai iyayan gijinta suka gaji da ita.
.
Lokacin da jaruma siyama ta ji cewar ba za a bar iyayanta su shiga filin gasar ba sai ranta ya baci ta yunkura zata bude kofar da karfin tsiya su kunna kai ciki kawai sai mahaifinta ya dubeta yayi mata inkiyar kada ta aikata hakan ta hakura, cikin sanyin jiki ta juyo ta fuskanceshi tace yakai abbana yanzu mene ne abinyi?
Zamu koma gida ne ko kuwa zamu hau sama ne muyi kallo abul siyama ya gyada kai yace mu dakata har sarki ya iso na tabbatar muku da cewa zamu shiga wannan fili na gasa yayin da sarki yazo nan, koda jin wannan batu sai mamaki ya kama siyama domin bata ga dalilin da zai sa a barsu su shiga cikin filin wannan gasa ba idan sarki yazo tunda dai su basu kasance masu sarauta ba ko wani matsayi haka dai siyama tare da mahaifanta suka koma gefe daya suka tsaya suka zuba idanu kawai.
.
A wannan lokaci tsirarun attajirai da masu fada aji ne kadai ke wucewa cikin filin gasar kuma suna shiga sai a janyo kofa a sake rufewa kawai jim kadan kuwa sai ga sarki Hulbasu tare da
yarima basmar da yarima Hulkas sun nufo kofar filin gasar bisa dawakai dakaru na take musu baya ana busa Algaita gami da buga tambura nan da nan jama a suka dare aka basu hanya jama ar gari kuwa suka kama yiwa sarki Hulbasu kirari gami da jinjina sabo da nuna soyayyarsu a gareshi.
.
Koda ganin wannan al amari sai yarima hukas ya tuno da rayuwarsa ta can birninsa yadda jama ar gari ke sonsa da nuna masa soyayya sannan kuma ya tuno da yadda talakawa ke tsananin tsoron sarki Shardas saboda rashin imaninsa da cin zalinsa nan take hulkas ya tambayi kansa a cikin ransa yace wai shin menene dalilin da yasa mahaifina ya kasance azzalumi ? Kuma sabo da me halayansa suka banbanta da nasa alhalin ance barewa bata gudu danta yayi rarrafe amsar da yarima hulkas ya kasa baiwa kansa kenan yana cikin wannan haline sarki hulbasu da tawagarsa suka sake kusanto wajen tun daga nesa dasu yarima barmas suka hango jaruma siyama tsaye a wajan tare da iyayanta sai suka cika da mamaki
sabo da kamata yayi ace ta dade da shiga ciki tun daga nesa da sarki hulbasu ya hango mahaifin siyama tare da matarsa a tsaye da kuma 'yarsu siyama sai ya kura musu idanu kawai har
suka iso bakin kofar shiga filin gasar da isowarsu sai mahaifin siyama ya risina ya gaida sarki ba zato ba tsammani sai akaga sarki yaja linzamin dokinsa ya tsaya cak! Saboda tsananin mamaki da kuma ganin wannan mahaifina siyama a wajan nan, amma kafin nan zanso ku biyoni a labari na gaba domin jin yadda za a kaya a tsakanin su shin meye dalilin da yasa shi tsayawa yana kallonsa hm Nima ban sani ba.
Sai Kuma Allah ya kaimu Gobe kenan ku huta lafiya.......


TSATSUBA
Littafi Na Uku (4)
Part B.
Na Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi
.

Ba zato ba tsammani sai akaga sarki yaja lin zamin dokinsa ya tsaya cak, take kowa dake bayansa ma ya tsaya sarki ya sauko daga kan dokinsa fuskarsa cike da annuri ya durfafi mahaifin siyama, yana riskarsa sai ya rungumeshi sannan ya janye jikinsa daga cikin nasa ya dubeshi cikin mamaki yace yakai babban masoyi menene dalilin da yasa baka amsa kirana ba bayan mun rabu a daji a wannan rana.
.
Koda jin wannan tambaya sai mahaifin siyama yayi murmushi
yace ya shugabana kayi hakuri mu sami lokaci saimu tattauna yanzu kamata yayi mu shiga cikin filin gasa domin zuwanka kadai ake jira.
.
Koda jin haka sai sarki yayi murmushi ya kama hannunsa yaja shi izuwa cikin filin gasar shima sai ya ruko matarsa yarima barmas da yarima hulkas kuwa sai suka jera tare da jaruma siyama suka shiga cikin filin gasar, yayin da shima.
.
Koda su sarki Hulbasu suka shiga cikin filin gasar sai kowa ya mike tsaye don nuna girmamawa a gareshi filin ya cika da shewa aka ci gaba da yiwa sarki jinjina da gaisuwa ehm har sai da sarki da mukarrabansa suka je suka zauna a inda aka tanadar musu sannan filin yayi tsir aka yi shiru kamar mutuwa ta gifta a dai dai wannan lokaci ne mai gabatar da taro ya tashi yayi jawabi kamar yadda aka saba sannan yaci gaba da fadin sunayan jaruman da za su yi gasar a yau da gobe har tsawon kwanaki bakwai, a wannan lokaci jaruma siyama na zaune a tsakiyarsu yarima hulkas da yarima barmas amma sai ta lura da cewar yarima hulkas yana ta satar kallonta kuma yana son yayi mata magana, haka ma yarima barmas koda ganin haka sai ta murtuke fuska taki yiwa dayansu magana kuma taki basu damar yi mata magana ta hanyar kin sakar musu fuska, ba tare da bata wani lokaci ba aka buga gangar fara gasa aka kirawo sunan wadansu jarumai guda biyu suka shigo cikin filin kowannansu na rike da takobi da garkuwa daya dogo ne kuma kakkaura mai kwarjini da kirar sadaukai ana kiransa da suna MULAGUS, dayan kuwa gajere ne amma shima yana da kirar sadaukantaka ana kiransa da suna KUMAR, A cikin dokar wannan gasa an yarda a soki mutum ko a sareshi da a ko ina koda kuwa hakan zai iya zama sanadin ajalinsa amma ka idar nasarar gasar shine kawai akai mutum kasa ya kasa mikewa tsaye kafin a kirga bakwai, Malagus da kumar suka gyara tsayuwarsu suka fara kallon kallo kowannansu yana nazarin abokin gwaminsa, a dai dai wannan lokaci ne Hulkas ya dubi yarima barmas yace yakai abokina a ganinka wane ne zai lashe
wannan gasa tsakanin Mulagus da Kumar?
.
Koda jin wannan tambaya sai Barmas ya tuntsure da dariya sannan yace haba ai da ganin kura an san taci mutum Ga abu nan a zahiri kowa yana gani ai ko a ba a gwada ba linzami yafi
karfin bakin kaza....
.
Kafin Hulkas ya budi baki ya sake cewa wani abu sai jaruma siyama ta tari numfashinsa tace ai sai an gwada akan san na kwarai tunda komai zai iya faruwa a ko yaushe. Koda hulkas da barmas sukaji siyama ta tsomo baki a cikin zancensu sai farin ciki ya lullubesu hulkas ya dubeta ya ce ashe dama mahaifinki
da sarki sun san junansu amma baki gaya mana ba
.
Sa adda siyama taji wannan tambaya sai tayi murmushi tace ni kaina nayi mamaki ban san cewa sun san junansu ba sai yanzu, amma dai abin da na ke zargi shine a daji suka hadu a wajan farauta sabo da duk su biyun babu abin da suke so a rayuwarsu sama da farauta, zan tambayi abbana dai naji daga gareshi, gama fadin hakan keda wuya sai sukaga mulagus da kumar sun ruga izuwa kan juna sun kacame da azababben yaki suna masu kaiwa juna SARA DA SUKA cikin zafin nama juriya da bajinta, ana fara gumurzun ne filin yayi tsir ba a jin sautin komai face karar takubbansu ihunsu da karajinsu da takun sawayan kafafunsu, nan take kowa ya gane cewa Mulagus yafi karfin damtse to amma kuma shi Kumar yana da tsananin naci juriya da kwarewar iya yaki da farko duk sa adda mulagus ya kawowa kumar sara idan kuma ya kare da takobinsa sai kaga har darkushewa kasa yakeyi saboda karfin saran da nauyinsa, wani lokacin kuma sai kaga mulagus ya gabzawa kumar naushi ko bugu da hannu ko da kafa har kumar na durkushewa kasa amma kafin mulagus ya kaiwa kumar sara ko suka sa adda yake durkushen tuni kumar ya mike tsaye zumbur ya ci gaba da kare kansa kuma yana maida martani.
.
Abin ka da wanda yafi ka karfi cikin kankanin lokaci mulagus ya hadawa kumar jini da majina kuma ya sami nasarar yankarsa da takobinsa har sau uku ya zamana cewa jini na zuba a jikin kumar kuma jiri na dibarsa amma saboda masifaffen naci da azababbiyar juriya yaki yarda ya fadi a wannan lokaci gaba daya jama ar dake wajan sun saddakar da cewar mulagus ya gama samun lagon kumar don haka a ko yaushe zai iya bazar
da shi kasa a haka dai suka ci gaba da gumurzu har tsawon rabin sa a mulagus bai sake samun wata nasara ba akan kumar abin ka da jiki da jini sai shima mulagus ya fara gajiya haki ya yawaita gareshi da yawan numfashi shi kuwa kumar sai ya samu karfi a wannan lokaci tamkar ma a sannan ne ya fara gumurzu sai gashi nasa karfin Saran da sukan yafi na mulagus nauyi da karfi hakika masu iya magana sunyi gaskiya da sukace sai miya ta kare sannan ake sanin maci tuwo ! kuma ance a dade ana yi sai gaskiya domin dadewar da jaruman biyu sukayi suna fafata wannan masifaffen fada yasa aka gane jimrau a tsakaninsu kuma aka fahimci wanene mayakin kwarai
cikin kankanin lokaci kumar ya kuntata mulagus ya hanashi sakat ya zamana cewa kwata kwata mulagus baya iya maida martani sai kokarin kare kai, koda kumar yaga ya sami wannan nasara sai ya shammaci mulagus ya daka tsalle sama ya doki fuskarsa da kafa, saboda kargin dukan sai da mulagus ya juya sau biyu a tsaye, kafin kumar ya duro kasa tuni ya sa takobinsa ya sarewa mulagus hannunsa na dama mai rike da takobi, take hannun ya fice fit jini ya kama feshi da tsiri daga cikin dungulmin a lokacin da mulagus ya kwarara uban ihu wanda ya firgita komai da kowa dake wajan har dama halittun dake cikin gari da kewaye take mulagus ya kife kasa sumamme, ai kuwa sai filin gasar ya rude da shewa gami da jinjina a lokacin ne shima kumar ya durkushe kasa bisa guiwoyinsa sakamakon gani da yake dishi-dishi da idanunsa da kuma jinin dake zuba a jikinsa nan take likitoci suka rugo cikin filin gasar da dakaru aka dauke jaruman biyu aka shige dasu izuwa cikin wani babban daki dake gefe daya a cikin filin gasar wanda aka tanadeshi a matsayin asibitin da za a rinka duba jaruman gasa, ganin yadda aka zubar da jini ne a filin wannan gasa yasa hankalin yarima hulkas ya dugunzuma ainun kuma ransa ya baci take ya aiyana a ransa yace in da zan zamo wani babban sarki a wannan nahiya tamu da sai na hana gabatar da irin wadannan wasanni wadanda ake zubar da jini domin ban ga amfanin ace zubar da jini shine Jarumtaka ba.
.
Bayan an gama dauke jaruman gasar biyu daga cikin filin gasar sai mai gabatar wa ya kirawo sunan jarumi na gaba wanda yayi
wasa waishi DURKUS, koda yan kallo sukaji sunan wannan jarumi sai filin ya cika da shewa tamkar dodon kunne zai dode, shidai wannan jarumin Dukrkus din a gaba daya nahiyar babu wani jarumi da ya kaishi girma, da iya yaki tare da kuma daukaka kuma duk shekara shine yake lashe wannan gasa ta jarumtaka dukkanin jaruman da suke zuwa wannan gasa daga
sauran kasashe na duniya komai girmansa da iya yakinsu suna tsoron durkus babu wanda yake son a hadashi dashi, ba don komai ba sai don sadauki Durkus ya kasance gabjejen kato mai kirar mutanan Farko sannan kuma yana da tsananin karfi na Allah ya isa gashi da tsawon tsiya kamar ba mutum ba kuma kakkaura ne sosai a takaice dai kirarsa ta samudawa ce baya ga wannan rashin imanin Darkus yayi yawa domin duk jarumin da ya hadu dashi sai ya mutu sadauki Darkus bai taba yin wasa ya bar abokin gwaminsa da raiba don tsantsar zaluncinsa, kuma kafin ma ya kashe abokin gasar tasa sai ya sassare masa gabban jiki yai gungudwa gungudwa da sassan jikinsa sannan ya kashe shi kisan wulakanci bisa wannan daliline yasa duk sa adda zaiyi yaki a filin gasa masu raunin zuciya basa iya
kallon wasansa, domin duk sai dai kaga suna ta kumallo a filin gasar suna koke koke yayinda yake aiwatar da zaluncinsa ga abokin gasarsa.
.
Koda aka kirawo sunan wannan Jarumi wato Darkus ya shigo tsakiyar filin gasar sai aka kama yi masa jinjina da kirari sai shima ya kwarara uban ihu mai karfi da firgitawa ya fara dukan
kirjinsa da tafkeken hannunsa ya shiga rerowa kansa kirari yana mai cewa,,,
Ina bakon lahira to ya fito ya tareni, Nine bakin takobi mai raba kowa da masoyi, nine dajin mutuwa kowa ya shige ba rai zai fita ba a raye ba. Kuma nine ISKAR ANNOBA kowa ya shakeni sai ya kwana kiyama. Guguwar kan dutse nake ban fito ba sai da na shirya sawun giwa nake wanda na take na dukkan dabbobi Ina mai jida jarumta da juriya da naci to ya fito ga dillalin mutuwa hm Ni AlQuyraemey sai naji kamar na fita haka dai Darkus yaci gaba da yiwa kansa kirari har ya gama ya tsaya cak a waje daya yana huci da muzurai tamkar wani bakin kumurci kai yaran dake cikin wannan filin gasa boye fuskarsu
suka kama yi domin da zarar sun hada idanu da darkus sai suga kamar dodo ne tsaye a gabansu wanda zai suresu da hannu daya ya jefa baki ya lankwame...
Nima dai bari na dakata a nan wajan saboda tsaro Amma
kafinan Nidinne dai mai deɓe maku kewa.

TSATSUBA
Littafi Na Uku (4)
Chapter 1 · 0% Book details