← Book details Taswirar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 3 OF 4

Part dn Zeey ya nufa don ta Sama masa abinci kuma tazo ta gyara part din don gaskia kyankyamin sa yake ji.

Taswirar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ba kowa a Palourn sai ya nufu dakin ta yana kyautata zaton acan zai same ta.

Har ya dora hannun sa akai zai murda yaji maganar Zeey data sashi kamewa a gun.

Cikin shewa Zeey tace "Ai Malika brain dinki yana ja, kinsan cewa ynxu komai yana tafiya according to our plan abinda nake Jira ynxu kawai ya saki shegiar ta Kara gaba".

Gyada kai Malika tai tace "ke an fada miki ni ta wasa ce ai na fada miki dama tunda baki son cikin baki shirya haihuwa ynxu ba kuma shi gogon yana son cikin sosai da shi zamuyi amfani mu cimma manufar mu, gashi ynxu kin zubar da cikin kuma kin netsan tasu da juna".

Ajiyar zuciya Zeey ta sauke tace "bari kawai Aminiya wato ai dama in fada miki tunda na balli maganin kinsan kin fada min dama biyu kawai zansha kuma na tabbatar ina sha zubar da sauran a inda ba wanda zai gani, balla nai na boye a cikin bra dita, inda Allah ya taimake ni ina zuwa na same ta a part din ta kawo masa abinci ai kuwa nace tamin zobo inaso".

Tsaki Malika tai tace "ita kuma shashasha tayi Miki dake bata da wayo".

Tafawa sukai, Zeey tace "eh mana tana kawo min ai na faki idon Yaya na sa maganin a bakina na kora da zobon, kuma na shanye zobon duka kar ma yasha kinga plan dinmu zai rushe ".

Shewa sukai Malika tace "tunda shi asiri baya kamasa ba sai a masa makirci na Mata ba gashi nn komai ya tafi daidai, Ince dai baki fadawa Mummy ba"

Tsaki Zeey tai tace "waya aike ni fada mata ai tunda nace mata kin bani magani na dinga zuba masa a abinci ta dinga min nasiha tun daga nan na daina fada Mata komai".

Tabe baki malika tai tace "kin huta kuwa, ynxu dai shiri zamu yi babba wanda zai sa ya sake ta Su tarkata su tafi ita da shegiar yar ta".

Shiru Zeey tace tace "mai kike ganin zamu yi Mata"

Cikin rashin tsoro tace "sharrin Zina zamu yi Mata kawai"

Banko kofar Azlan yai jikinsa sai rawa yake masa, kallon su yake yama rasa mai zai ce musu, kallon Zainab yai yace "5 minutes kawai na baki ki ficemun daga gida"

Da sauri ta mike tana Dora hannu aka tace "Yaya don Allah kayi hakuri wallahi duk ba laifi na bane Malika ce ta sani".

Hankada ta Malika tai ta kwasa a guje ta fice da part din gaba daya ko takalmi bata tsaya sawa ba.

Kallon Zainab yai yace "na rantse da Allah in kika Kara 5 minutes a gidannan a bakin auren ki", daga haka ya juya ya fice hannun sa rike da kansa.

A zabure ta ja mayafi ta yafa wayar ta kawai ta dauka ta fita daga gidan sai sauri take tana duba wayar ta.......


Shi kuwa Azlan ya dade yana tunano irin abinda ya adinga yiwa Batul da yadda take kuka tana fadin ya yadda da ita ba zata iya aikata abinda yake zargin ta akai ba amma yayi mirsisi ya dinga shuka mata rashin mutunci.

Kamar Wanda aka tsikara a zabura ya mike ya nufi part dinta, a zaune take tana sanye da free doguwar riga shinkafa da wake take ci a cikin tray na zabga yaji tana ci tana kallon Indian hausa.

Zubewa yai a gabanta kansa a kasa, a dan tsorace na kalle sa nace "lafia"

Dora kansa yai akan cinya ta kawai ya fashe da kuka........


Team Batul kuna inaaa💃💃💃💃💃💃


Shin wani mataki kuke tunanin Azlan zai dauka akan Zeey?

Batul zata yafewa Azlan kuwa?

Tukunna ma waye yake zagaya wa gurin karuwa?


Comments Nd share plz


Mrs A.M🥰

[26/09, 16:53] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️

*TASWIRAR KADDARA*

♠️♠️♠️♠️♠️


Written by
Mrs A.M🥰

Page 41

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


*TALLA TALLA TALLA*💃💃💃💃


*Mrs Dnah perfumes nd more*

*Ina masu bukatar kamshi da kayan gyaran fata duk ga dama ta samu, ku garzayo gun Mrs Dnah perfumes and more domin samun kayan kamshi, turaren wuta da Humra da kuma mayukan gyran fata yadda zaki dinga walwali kina daukar hankalin oga😉*

*Muna Saida*

*Perfumes*
*Turaren wuta*
*Humra*
*Kindikay(turaren jiki da na Kaya wanda ake yi a kujera da gabbasa)*
*Freshner*
*Turaren Mopping*
*Soaps*
*Body creams da anything na gyaran fata*.


*Duk wani Abu da kuka sani na kamshi da kuma wanda zai gyara maka skin muna siyar wa cikin farashi mai sauki.*


*Phone number*
+234 702 577 7778

Location kano


Tsoro ne ya kamani ganin yadda yake kukan kamar yaro, hannuna na dora akan sa nace "lafia"

Dagowa yai ya zuba min idonsa da har lokacin hawaye suke zubuwa, hannuna ya rike sosai yace "Ban san ta inda zan fara baki hakuri ba Baby"

Hade rai nai nace "waye kuma baby"

Girgiza kan sa yai yace "don Allah ba dan niba kiyi hakuri ki yafe min, na san bai kamata ki yafe min ba sbd na miki laifi babba amma ki duba"


Kallon sa kawai nake a kaikaice nace zlaifin me kamin ni kuma batul da har kake son na yafe ma".

Shiru yai yana kallona ganin naki dauke idona a kansa yasa shi fadin "na zarge ki akan laifin da ba ke kika aikata ba, Zeey ce ta hada komai wallahi kiyi hakuri ynxu naji suna maganar ita da kawar ta, ki yafe min na bata miki rai sosai".

Mikewa nai tsam na dauki tray din abinci na, kallon sa nai nace "ai ni baka min komai ba duk abinda kamin gani kai na cancan ci kamin shine". Daga haka na wuce dakina, ina shiga na rufe kofar da key.

Lumshe idona nai nace "Alhamdulillah ya Allah"

Wayata na ciro daga aljihun rigata na Kira Aunty Bilkisu bata dade ba tana ringing ta dauka.

A nutse nace "Ina wuni Aunty Bilkisu"

Murmushi tai daga can bangaren tace "lafia qalau Maman Mimi y kuke?"

Yar dariya nai nace "Alhamdulillah yasu Nana, ina gaishe su sosai".

"Zasu ji insha Allah"

Dan shiru nai Kan nace "Aunty kinsan me?, ynxu Daddyn Mimi yazo yana kuka wai na yafe masa"

Da sauri Aunty Bilkisu ta mike daga kwancen da take tace "me kika ce masa kuma"

Turo baki nai nace "nuna masa nai ni ban san wani abu daya min ba kawai na tashi ta shige daki"

Dariya tai tace "da kyau ynxu so nake ki nuna masa darajar ki kafin ki nuna masa kin yafe masa, kar ki sauko da wuri ki dan basa wahala kinji koh".

Dariya nai nace "toh insha Allah Aunty Bilkisu".

Mun jima muna wayar tana Kara koya min dabarun jan hankalin sa da yadda zan dinga kunnasa ina masa kwalele.

A Palour kuwa da mamaki Azlan ya bi bayanta da kallo ajiyar zuciya ya sauke ynxu kuwa ya tabbatar yana ruwa don bai ga alamun sassauci ba a gun Batul.

Lumshe idonsa yai yana fito da wayar sa daga aljihun sa, sunan Baffa ya gani kamar kar ya dauka sai kuma ya daga yana sa wayar a kunnen sa.

Cikin dakewar murya da bada umarni Baffa yace "duk inda kake kazo ynxu ina neman Ka".

Cire wayar yai daga kunnen sa Yana jan gajeran tsaki shifa sam bai shirya fita ynxu ba amma ba yadda ya iya dole ya fita sbd cika umarnin Baffa.
Chapter 3 · 0% Book details