← Book details Taswirar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 4

Gabatarwa

Taswirar Kaddara Part 1 Complete Hausa Novel · about 235 min read

[03/08, 11:42] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️

*TASWIRAR KADDARA*

♠️♠️♠️♠️♠️


Written by
Mrs A.M🥰

Page 1

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Ina zaune a matsakai cin tsakar gidan mu ina duba littafina kasancewar Jamb din da zan rubuta wannan shekarar gashi lokaci yana ta kurewa saura sati biyu mu zama jamb din.

Hankali na ya kasu kashi biyu, daya yana kan English din dana ke rubutawa daya kuma yana ga tunanin inda *MIMI* ta shiga, tun da akai la'asar ta fita ban kara ganin taba, kwafa nai ina tunanin yadda zan hukunta ta tunda tasan cewa bana son tana fita da yamma haka ita kadai.

Wata yarinya mai kimanin shekaru 4 fara kar kamar balarabiya sbd tsabar kyaun da Allah yai mata ta shigo gidan tana sanye da riga yar kanti har kasa duk da rigar tadan kode amma kal take a wanke sai alamun kasa kasa daka kasan rigar da alama yarinyar tayi wasa a kasa ne.

Tunda ta shigo na kafe ta da ido ina tasbihi a raina, kullum na kalli Mimi sai nayi tasbihi ga Ubangiji sbd tsabar kyaun ta, fara ce tass mai dauke da zagayayyiyar fuska tana da manyan idanu sosai tubarkalla sai dogon hanci wanda ya dace da zagayayyiyar fuskar ta sai kuma karamin bakinta jajir dashi, maida kallona kan gashin ta nai dake tufke amma jelar har kusan duwawun ta take sbd tsayin gashin ta.

Lumshe idona nai jin wani hawaye yana kokarin zubo min, muryar ta mai cike da shagwaba naji a kusa dani tana fadin *"MAA* kiyi hakuri baxan sake ba Hidiya ce tace inzo muyi wasa a garden din gidan su."

Kallon ta nake kawai ina bin kumatun ta da kallo yadda dimple dinta na gefen kumatun ta na dama yake lotsawa sosai, hakan ba karamin kyau yake karama ta ba.

Hade rai nai cikin dan fada fada da saurin maganar da nake da shi nace "ban hana ki fita ba amma wato kin fara raina ni koh Mimi shine har zaki fita BA tare da na sani ba"

Rau rau tai da idonta daya fara tara hawaye ta kama kunnuwan ta da hannayen ta tace "Maa kiyi hakuri bazan sake bafa kar kiyi fushi dani"

Daga bayan mu Umma da ta fito daga daki tayi dariya tace "zo kinji kawata kema kinsan Maa dinki baxa ta iya fushi dake ba"

Makale kafada tai tace "toh Umma ai bata ce ta hakura ba"

Janyo ta jikina nai cikin tsananin kaunar ta nace "na hakura babyta amma kar ki sake fita ba tare da kin fada min ba kinji koh"

Daga kai tai tana kuma kwantar da kanta a jikina sai shagwaba take zuba min ina biye mata, girgiza kai Umma tai kawai tana dauke kwallar dake neman sakko mata a fuska.

Muna zaune a tsakar gidan Umma da Mimi na kan tabarma ni kuma ina daga kitchen Aysha ta shigo cikin uniform din islamiyya.

Fitowa nai hannuna rike da ludayi nace "kinyi saurin dawowa yau Aysha ina su Kamal din"

Zama tai akan tabarma tana ajiye jakar hannun ta cikin gajiya tace "suna hanya Ya *BATUL* ai baxan iya jiran suba wallahi duk ba gaji fah kinji kafa ta"

Dariya nai nace shiyasa nace "sannun ku ai kun kusa sauka ki dinga hutawa kema"

Kallon Mimi tai tace "shine kika ki zuwa islamiyya yau koh ai Malamar ku tace sai ta zane ki gobe"

Murguda karamin bakin ta tai tace "ai bani da lafia kaina yake ciwo shine Maa tace nai zama na gobe sai naje"

Na bude baki zanyi magana knn su Kamal suka shigo, kallonsu nake da dukkan alamu ba lafia ba don yadda Kamal yake ta hura hanci yana goge gumi.

Kallon Khalil nai don nasan yadda kamal yake ko na tambaye sa baxai iya min magana ba, cikin saurin magana ta nace "mai aka masa naga sai huci yake ko fada sukai ne"

Goge goshin sa Khalil yai cikin nutsuwa kasancewar sa komai a nutse yake yace "Ya BATUL Manniru din gidan Kawu Nasiru ne sukai fada dashi, wai kawai don Malamar su Mimi tace bata ganta ba a gaishe mata da ita shine da muka fito ya tare mu yana fadin baiga amfanin saka Mimi a makaranta ba tunda *SHEGIA CE* ita Shi kuma khalid ya mare sa shine suka fara fada da kyar aka rabasu" ya karashe hawaye na zubo masa.

Tunda ya ambaci shegia naji kirjina na min wani irin zafi cikin masifar dake taso min na shiga dakin mu, hijab na dauko na fito dashi a hannu na ina kokarin sawa.

Umma da tai shiru kanta a kasa ta dago ta kalle ni tace "meye haka Batul ina zaki je"

Girgiza kai kawai nake don tsabar bala'in dake cina bana Jin ma zan iya magana in da abinda na tsana a duniya shine a dangan ta min Mimi da shegia tabbas nasan gaskia ake fada amma raina baci yake a duk lokacin da aka kirata da haka kuma ko waye ya fada mata sai na gaya masa maganar da nasan zai dade yana jin takaicin ta.

Da kyar na hadiyi wani yawu nace "zanje gidan su ne in jawa uwani kunne akan yaranta wallahi Umma duk lokacin da suka kara shegan tamin yarinya sai nasa an karya musu kafafu don uban babansu."

"Mai kuma babana yai haka ake zagin sa Batul".

Juyawa nai ina kallon babanmu daya shigo hannun sa rike da leda wanda wannan dabi'ar sa ce kullum zai dawo daga kasuwa sai ya siyo wani abu komai kankantar sa ya shigo da shi.

Turo karamin bakina nai gaba ciki ciki nace "Manniru neh ya cewa Mimi shegia shine zanje na jawa uwani kunne akan su kar nasa su cilla su karya min kafar su ace ban fada musu ba"

Zaunar dani baba yai akan dakalin kofar dakin mu yace "don sun ce haka sai ki biye musu, kinsan dama abinda suke so knn suyi magana wani ya biye musu su tada fitina ki rabu dasu wata rana ko ance su fadi haka baxa su fada ba Batul"

Nidai Shiru nai kawai ina girgiza kaina tunda Baba yace na rabu da su na kyale su Amma wallahi sai nasa cilla ya zane min yaron nan in da hali na ko yar karamar targade ne ya masa a kafafun.

Ina zaune a wajen Aysha ta shiga kitchen don karasa girkin da ban gama ba, su Khalil kuma sun chanja kaya sun fita, Mai da kallona nai gurin su Baba da yake wa Mimi Wasa sai dariya take tana jan gemun sa. Kafe ta nai da ido ina Jin tsoron zuwan ranar da zata tambaye ni *WAYE MAHAIFIN TA* mai zan ce Mata ban san saba ban taba ganin fuskar sa ba banma san ya yanayin sa yake ba abu daya ne nake da shi mallakin mahaifin ta shi kuma bansan ta yadda zai kaini ga mahaifin nata ba.

Lumshe idona nai tsanar ko waye baban ta yana taso min tabbas da zan ido hudu da shi da ina da dama saina caka masa wuka a kirji......


*************

Zaune suke a lafiyayyan palourn gidan daya kasance mallakin mai gidan ko wanne dare anan iyalan gidan suke taruwa suke zama tare suke cin abincin dare.

Mami ce ta shigo palourn cikin shigar ta da kowa yasan ta da shi wato lifaya mai tsadar gaske red colour wacce ta haska farar fatar ta kana kallon ta zaka san cewa ita din shuwa arab ce, zata kai shekaru 45 Amma jikin ta bai nuna ba sbd tana da jiki nai kyau.

A hankali take tafiya hannun ta rike da kaskon turaren wuta data saka, sai da ta fara ajiye kaskon a kan table din gefen manyan kujerun Palourn sannan ta juya ta kalli Abie da tunda ta shigo ya kafe ta ido yana sakar mata murmushi mai cike da ma'ana, itama mayar masa da martanin murmushin tai tana masa wani kallo na kasan ido kafin ta isa kan kujerar da suke zaune shida Mama ta zauna itama.

Gaisar da Abie tai cikin nutsuwa kafin ta juya taiwa mama sallama, ciki ciki ta amsa ta daga kanta sai hura hanci take, itama bata damu ba ta maida kallon ta kan TV tana kallon news.

*JUNAID* ne ya fara shigowa cikin nutsuwa sanye da jallabiya as usual hannun sa dauke da carbi yana ja a hankali, kara sowa yai kusa da Abie ya tsugunna ya gaishe su, cikin so Abie ya amsa yana shafa kwantaccen sumar sa.

Mami ma murmushi take kafin tace "ina ka baro Samira din yauma baka zo da ita bakoh?"

Sosa goshin sa yai yana sunkuyar da kansa don baya iya hada ido da iyayen sa yace "Mami tana gidan su ne ynxu in zan wuce zan biya na dauke ta"

Gyada kai tai tace "Allah yai muku albarka ya warware muku dukkan matsalolin ku"

Ameen ya amsa yana komawa gefen ya zauna a kasa yana jan charbin sa cikin nutsuwa.

Baiyi minti goma da shigowa ba Yusuf ya shigo bayansa Sagir ne sai auta Mufeeda, Suma sai da suka gaishe da Abie dasu Mami sannan suka koma kusa da Junaid suna masa magana kasa kasa.

Hade rai Mama tai ta sani kusancin yaran ta da su Junaid tayi yadda zata yi ta raba su Amma abin yaci tura ta zage su ta zuga su amma a banza sudai kome zata yi baza su daina kula Yan uwan suba, kusan kullum ma a part din Mami suke wuni wannan abin yafi komai bata Mata rai.

Kallon su Abie yai kafin ya girgiza kansa yace ina *AZLAN* Junaid ne ya amsa Shi da fadin "Abie yana nan zuwa da zan fito ya shiga wanka neh"

Gyada kai kawai Abie yai yana maida kallon sa TV, ba'a dau lokaci mai tsayi ba suka fara jiyo fito yana doso palourn gaba dayan su suka zubawa kofar shigowa palourn ido duk da kuwa sun san waye zai shigo din.

Cikin takun jarumta ya shigo palourn yana sanye da three quarter brown colour sai armless riga light brown wacce ya bude botir din gaban rigar guda uku hakan ya bayyana kirjin sa, kafar sa sanye da wani takalmi mai kama da silifas, kamar su daya da Junaid don kana ganin su zaka gane Yan biyu neh sai dai Shi yafi Junaid haske kuma ya fisa kyau da kirar jiki mai kyau, cikin takun jarumta ya karaso tsakiyar palourn bayan ya cire takalmin sa.

Binsa da kallo Mami tai tana girgiza kai ganin askin kansa ita ynxu ma data sanin ce masa yaje yai aski take, da kansa sumar ce kawai ya tara sosai duk da sumar tasa a kwance take kamar ta larabawa amma tace yaje ya rage ta gashi ynxu yaje an kwashe gefe data an bar masa gefe daya. Mai da idonta kan damtsen hannun sa na dama tai dake dauke da katon tattoo na zaki a jiki, sai gefen wuyansa na hagu kuma da aka masa tattoo na miciji inda aka biyi da jelar micijin har wajen kirjin sa, girgiza kai tai a ranta tace "Allah ya shirya min kai Azlan"

Daga tsayen da yaje ya dan rankwafo yana tura hannun sa a cikin aljihun sa cikin muryar sa Mai kaushi da kame wa yace "Evening Abie" ba tare daya jira amsar Saba ya juya gun Mami yace "Evening Mami", Mai da kallon sa kan Mama yai ya zuba mata manyan idon sa da suka sha kwalli yace "Eve Hajia"

Hadiye wani yawu tai a duniya tana tsoron Azlan duk iskancin da zata yi a bayan idon sa take yinsa amma tana matukar tsoron sa, cikin inda inda tace "lafia"

Yamutsa fuska yai yana duba apple watch din dake daure a hannun sa na hagu ganin pass 8 yasa shi kallon Abie yace "zan iya ware wa Abie"

Girgiza masa kai yai takaici kamar zai kashe sa yace "na fada ma wallahi yau baxa ka fita a gate dinnan ba na gaji da halin Ka in Ka fita shashancin Ka baxa ka dawo ba sa tsakar dare"

Girar sa ta hagu ya daga yana shafa gemun sa yace "ta gate nedai Ka haramta min ware koh"

Daga kai Abie yai cikin tabbatar wa, juyawa yai ya kalli su Junaid da suka zuba masa ido gaba dayan su, yana juyowa duk suka juya suka maida kallon su kan TV sai Junaid ne kawai ya tsare sa da ido yana masa magiyar ya saurara yaji abinda Abie zaice.

Tabe bakin sa yai ya kalli Mami yace "kina bina da addua fah Mami kar wata ta danne miki ni tayi min fyade ta raba ni da budurwarcin dana ke ajiye wa"

Sunkuyar da kai su Mufeeda sukai yayinda Abie ya zuba masa ido kawai yana mamakin inda Azlan ya dakko rashin kunya sam bashi da kunya ga kwarjini da Ubangiji yai masa ko shi daya ke mahaifin sa kwarjini yake masa sosai, ita dai Mami addu'ar daya ce tai masa take yi a zuciyar ta tana kuma roka masa shirya.

Juyawa yai yana tafiya cikin jarumta, sai da yakai bakin kofar palourn ya juyo ya kalli Abie yace......


Ya kukaji salon book din🥰

Littafi ne mai cike ta sarkakiya ku biyo ni don na warware muka duk wata sarkakiyar dake ciki.


Comments Nd share plz🥹


Mrs A.M🥰❤️
[03/08, 11:42] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️

*TASWIRAR KADDARA*

♠️♠️♠️♠️♠️


Written by
Mrs A.M🥰

Page 2

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Sai da yakai bakin kofar palourn sannan ya juyo ya Abie yace "baxan taka dokar kaba," daga haka yasa kai ya fita.

Da sauri Abie ya mike yabi bayansa sanin dayai masa tunda har ya shirya zai fita sai ya fitan kuma ba ta gate zai bi ba, bin bayansa Junaid yai shima da sauri yana girgiza kansa.

Azlan yana fita daga palourn bayan gidan yaje ya dakko ladder ta karfe cikin zafin nama, ya rike ta da hannu daya kamar ba abin nauyi ya dakko ba, ware ta yai ya saita a jikin bangon gidan yadda zai mai daidai, su dai masu gadi suna zaune sai satar Kallonsa suke ba halin su bari ya gane suna Kallonsa.

Cikin sassarfa ya shiga takawa hana hawa sai da ya Kai karshen sa yadda zai dira daga gidan sannan ya juyo ya kalli Abie da Junaid, shafa gemun sa yai kafin ya saki wani murmushin gefen baki daya bayyana dimple dinsa guda daya na bangaren dama, juyawa yai ya dira daga gidan.

Sai da Abie ya dafa kirjin sa yana addu'ar Allah yasa bai ji ciwo ba, maganar da Azlan yake da karfi ne yasa Abie sauke ajiyar zuciya.

Shi kuwa yana dira mikewa yai ya karkade jikin sa sannan ya kalli dogon ginin daya diro, shafa gemun sa yai yana lasar lips dinsa iPhone 13 pro max dinsa ya zaro a aljihun sa, wata number yai dialing bata dade tana ringing ba aka dauka.

A kausashe yace zo mu hade ina kofar gidan mu, daga haka ya kashe wayar, bai dade sosai a wajen ba wata lafiyayyar mota ta shigo layin, a daidai kusa da shi ta tsaya bai wani tsaya jiran komai ba ya bude gurin mai zaman banxa ya shiga suka figi motar a guje suka bar layin.

Abie kuwa girgiza kai yai kawai suka koma palourn, Mami ce ta kalle sa fuskar ta cike da damuwa tace "ya fita koh Abie"

Zama Abie yai yana ajiyar zuciya yace "don na ce masa baxai fita ta gate ba shine ya haura katanga ya dira"

Lumshe idon ta kawai tai tana binsa da addu'a duk da ya kasance mara Jin magana amma shidin mafi soyuwa a gare tane baya Wasa da duk abinda ya shafe ta kuma baya mata karya.

Mama kuwa ajiyar zuciya ta sauke cikin Jin dadi sbd dama ita duk ranar da yazo suka zauna da shi takura mata yake, ta rasa mai yasa yaron ya raina ta tunda take dashi bai taba ce mata Mama ba sai dai Hajia da Yaya ma yake ce Mata saida Abie da Mami suka dinga masa fada sannan ya fara ce Mata Hajia.

Haka suka ci abinci kafin su gama aka shiga hira, sai wajen 10 sannan Junaid ya mike kallon Abie yai yace "Abie bara na tafi zan biya na dauki Samira a gidan su"

Murmushi Abie yai cikin kauna yace "Allah ya tsare ya cigaba da kare mana ku Allah ya warware muku dukkan matsalolin ku"

Fuskar sa cike da murmushi yace"Ameen"

Kallon Mami yai cikin nutsuwa yace "Mami sakon samiran tace min kin ce zaki bada sako in taho mata da shi"

Mike wa Mami tai cike da tausayin yaron nata ta ce "muje na baka dama dambun naman da nai ne nasan tana so sosai shine na zuba mata"

Tabe baki Mama tai tana gwasine fuska itama ta kusa aurar da Yusuf dinta tayi sirikar.

Bayan sun shiga part din Mamin Mika masa leda Mai dan girma tai wacce take dauke da dambun naman a cikin, sai da ta kara masa nasiha sosai akan yadda da KADDARA sannan ya tafi.

Binsa tai da kallo cike da tausaya wa shekarar sa biyar da aure amma har ynxu matar sa ko bari batayi ba, duk inda suka je kuma matsalar daga gare sa ne amma matar tasa lafiyar ta Lau, da farko da aka gane matsalar daga gurin sane yaso rabuwa da samiran amma ta dage ita akan ta yadda da KADDARA zata zauna da shi ko da baxa ta taba haihuwa ba har karshen rayuwar su..


***********

Kallon cilla nai dake zugar sigarin sa cikin kwanciyar hankali, tsaki nai cikin fada fada nace "wallahi cilla in baxa ka rage shan sigarin nan ba zamu raba hanya haba"

Yar da sigarin yai a kasa ya murje ta sannan ya kalle ni yana murmushi yace "afuwan aminiya ta xan kiyaye Insha Allah tun safe ban sha ba fa."

Tsaki na kuma ja kafin nace "cilla so nake ka targada min Manniru dan gidan kawu nasir, yaron nan dan baya jin magana shine zai zagi Mimi"

Ashar ya saki yana jan kafar sa baya kafin yace "kika ce zagin shalele yai wallahi sai na karya sa don uwataii"

Gyada kai nai cikin takaici nace "ba sai ka karya saba kawai kasa amasa shegen duka yadda gobe ko wani ya gani zai zagi Mimi sai ya kwabe sa"

Murza kafa a kasa Cilla yai kafin yace "an gama aminiya ta kuma abokiyar shawara ta muje in taka miki ki karasa gida sbd yan jagaliya"

Jera wa mukai muna tafiya yana ban labarin yadda zai casa Manniru har muka karasa kofar gidan mu, sallama nai masa na shiga gidan, ba kowa a tsakar gidan hakan yasa na nufi palour don nasan suna zaune ynxu tunda an kawo wuta.

Da sallama na shiga palourn duk suka amsa min, Zama nai a gefen kafar baba ina cire hijab din jikina.

Kallona Umma tai tace "kin biya gurin cilla neh koh don nasan yadda kika dade din nan sai dai in kun hadu dashi"

Sosa keya ta nai nace "Umma a kofar gida muka hadu fa shine kawai muka gaisa"

Girgiza kai Umma tai tace "ni na rasa me yasa kike Kula wannan yaron wallahi sam baya ji tubarkalla"

Abba ne ya ce "A'a Umman Aysha ki bisa da addu'a kawai shima dana Allah ya shirye sa da dukkan zuri'ar musulmai baki daya"

"Ameen" muka hada baki gaba daya muka ce, mike wa nai ina fadin "sai da safe Baba gobe da school kuma ina son na fara shiga school din su Mimi"

Khalil ne yace "Ya Batul zan raka ki in zaki kaita"

Harara na sakar masa sannan na juya na nufi dakin mu nida Aysha, akan katifar mu 6 by 6 na ga Mimi tana sanye da rigar baccin ta kanta sanye da hula, murmushi nai na karasa gurin wardrobe dinmu, kayan bacci nasa na hauro kan katifar addu'a na fara ma Mimi kafin nima nayi, janyo ta jikina nai na rungume ta hawaye masu dumi suna zubo min a fuska tabbas a duniya Mimi ce rauni na ita nake kallo nake tuna *TASWIRAR KADDARAR* data same mu shekaru 5 baya.

Lumshe idona nai ina ina tuna abubuwan da suka faru shekarun baya lokacin ina da shekara 14 gashi ynxu ina 18 amma abun kamar ynxu ya faru......


**********

Kallon Haidar Azlan yai yana tabe jajayen lips dinsa yace "in baxa ka kaini club dinba sauke ni in karasa ai ina da kafa"

Girgiza kai Haidar yai yace "Azlan kayi ma kanka fada Kai ynxu ya dace ma ace kullum kana hanyar zuwa club gurin Yan mata"

Shafa gemun sa yai yadan lashi jajayen lips dinsa kafin yace ina ruwan Ka Mata ai abin nishadi neh kuma don naje AI ba budurcina zan basu baaaa.......


Comments Nd share plz🥹


Mrs A.M🥰❤️

[04/08, 20:17] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️

*TASWIRAR KADDARA*

♠️♠️♠️♠️♠️


Written by
Mrs A.M🥰

Page 3

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Assalamu alaikum Fans ina muku albishir din mai da Book din Taswirar kaddara free Book, Allah y bar kauna🥰

Tsaki Haidar yai yace wallahi gaba dayan Ka dan iska ne, ynxu kai sbd takadari ne baka da aiki sai maganar budurci daga anyi magana sai kace kana tattala budurcin Ka.

Dage gira daya Azlan yai kawai yana tsotsar lips dinsa hayaniyar ta ishe sa shiyasa kawai yaja bakinsa yana tsotsa, kallon sa Haidar yai ganin yana tsotsar lips dinsa hakan ya nuna masa cewa baxai sake magana ba kuma yan miskilan cin sun hawo knn, shima Jan bakin sa yai yai shiru ya maida hankalin sa kan titi.

Tafiya mai dan nisa sukai kafin Haidar yai parking motar juya wa yai ya kalli Azlan daya kwantar da kansa a jikin kujerar motar yana gyada kai a hankali, bai yi magana ba sai bude motar yai kawai ya sauka ya tafi don tarar Keke napeo ya mai da shi gida.

Sai da Haidar ya fita tukun ya bude idonsa a hankali yana lasar lips dinsa, fitowa yai ya shiga gurin driver sit yana tabe baki, a guje ya fisgi motar yana sharara gudu a hanya ikon Allah ne kawai ya kaisa club din lafia.

Parking motar yai a cikin katon compound dn club din tun daga yanayin motocin dake fake a gurin zaka San cewa club din sai wane da wane ne suke zuwa gurin, cikin tafiyar sa ta jarumta ya nufi cikin club din dake tashin Kida kamar zai tsage ginin Amma su wadanda suke ciki ba abinda ya dame su harkokin su kawai suke.......


************
Da safe ina tashi bayan nai sallar asuba wanka na shiga nai ina fitowa Aisha ta shiga itama don da asuba dukan mu muke wanka, bayan na shafa mai doguwar riga na zira na fito kitchen gas na kunna na dora ruwan tea don hakan ya zamar mana al'ada kullum sai mun sha tea da safe.

Ina gama fada tea din na juye a flask doya na dafa mana fara na dauki ragowar miya dake fridge na dumama, sai da na gama duka na kai palour sannan na shiga daki don dauko Mimi nai mata wanka.

A zaune na same ta tana hamma sai murza idonta take alamun ynxu ta tashi, murmushi nai da ya fito da wushirya ta na karasa gurin ta zama nai akan katifar mu na janyo ta jikina, cikin kaunar ta da baya boyuwa a fuskata nace "Morning My baby"

Murmushi tai dimple dinta na gefen kumatun ta na dama yana lotsawa, kwantar da kanta tai a jikina tana fadin "Good Morning MAA dita"

Dariya nai na girgiza kai ganin in na tsaya biye mata zamu iya makara yasa na mike na cire mata kaya, towel dinta na sa Mata naja hannun ta zuwa toilet dinmu dake tsakar gida, wanka nai mata kafin na bata ruwa na sata tai alwala.

Daki muka shiga na shirya ta cikin uniform dinta Riga da wando light blue sai karamin hijab dinta dark blue, socks na sa mata muka fito Palour karya wa mukai muna yi muna hira har muka gama na sa mata takalmin ta, Nima daki na shiga na shirya cikin uniform dina ringa da wando sai hijab Wanda ya kusa zuwa min har gwiwa ta, jaka ta na rataya na dakko ma Mimi jakar ta itama.
Ina fitowa naga Abba da Umma a zaune suna Shan tea gefensu su Khalil ne a zaune Suma suna karyawa, gaishe su nai na janyo Mimi ina samata hijab dinta, kallon Abba nai nace "mun tafi Abba"

Murmushi yai cike da dattako yace "ynxu dai sai kin je makarantar su Mimi din"

Turo madaidaicin baki na nai gaba nace "Abba in ban je ba haka malamar nan tasu zata dinga ma Mimi maganar meye ma'anar sunan da take using gwanda naje nai reporting in ba haka ba tun Mimi bata damuwa har sai abin ya soma damun ta tunda ynxu tace har classmate dinta sun fara tambayar ta Suma"

Daga kai yai yace "kuma hakane amma bar ya ni sai naje na musu magana kinga kema student ce ba lallai su baki wani muhimmanci ba amma In suka ga babba yaje zasu fi saurara koh"

Murmushi nai ina sakin hannun Mimi nace "Haka ne Abba Allah ya kara arziki da wadata ya Kara muku lafia"

A tare suka amsa da Ameen, sunkuya wa nai nayi ma Mimi kiss a kumatun ta sannan na mike na fita don na kusa makara ma karfin hali ne irin nawa kawai yasa ni cewa sai na fara raka Mimi school din su don na fara gajiya da tambayar da Aunty dinsu take mata akan meye ma'anar sunan babanta sbd tana Amfani da Khadija B ne a school shine Auntyn su kusan kullum sai ta tambaye ta meye B din yake nufi, ni kuma inaso naje na yi reporting wa headmaster dinsu tunda ai ba dole ne sai ta san ma'anar B dinba...

Ban dawo ba sai karfe 4:30 na yamma a gajiye na shigo gidan jakata a hannu na saukin tama daga yau na daina zuwa makarantar mun gama lesson ranar Monday zamu fara waec, a tsakar gida na samu Umma da Aysha suna hira sai Mimi dake zaune a cinyar Umma suna hira.

A gajiye na zauna a gefen tabarmar ina gaida Umma, a dakile ta amsa ni tana kauda kanta gefe, hannu nasa na tallafo kumatuna ina kallon ta kafin na kalli Aisha dake dariya tana kauda kanta.

Marairaice fuska nai nace "Ummana me kuma nayi ko Aisha ce ta hada min bom a gurin ki don taga bana nn"

Dariya Aisha tai tace "ba ruwana wallahi Ya Batul dazu ne aka aikowa Umma wai Manniru ba Shi da lafia machine ya kade sa ya samu targade a hannu shine fa Umma tace tasan aikin cilla ne kuma ke kikasa Shi yai ma Manniru targade tunda an hana kisa a karya sa"

Zaro madaidaitan idona nai nace "Umma ni kuma ina ruwana da wani Manniru ai kince kar nasa a karya sa kuma Umma ai Shi Mannirun bai ce cilla bane naji Aisha tace machine ne ya kade sa"

Kallona Umma tai kafin ta girgiza kai tace "Allah ya shirye ki in kin huta sai ki leka ki duba sa don dama Yakumbo tana min mitar ynxu kin dena leka ta"

Dariya nai nace "Ameen Ummana anjima sai na leka din Insha Allah"

Janyo Mimi jikina nai ina fadin "babyn wace wannan" dariya ta kalkale da shi da suka fito da jerarrun hakoran ta tace "babyn Maa ceh"

Murmushi nai ina jan kumatun ta daga kanta nai daga cinyata na mike don zuwa watsa ruwa gashi yunwa nake ji sosai, bayan nai wanka na chanja kaya dama nayi sallah a makaranta, kitchen na shiga na zubo shinkafa da wake nasa salad akai, Kan tabarma na zauna ina ci muna hira da su Umma har na gama, wanko hannuna nai na shiga daki nasa Hijab dina har kasa, hula na Sawa Mimi na shiga palour na dakko wa Yakumbo robar zobo guda daya da robar kunun ayar da nake na siyarwa, don Alhamdulillah ina Sana'a ta daidai gwargwado ina siyar da zobo da kunun Aya Allah yamin baiwar iya hada zobo da kunun Aya sosai shiyasa nake na siyar wa kuma Allah yasa ma abin albarka ana siya sosai wasu ina zubawa a roba wasu ina kullawa a leda har fridge Dan karami ne dani Wanda Abba ya siya min nake sa kayan zobo na a ciki, ga kuma cake ina yi shima don na iya sarrafa flour.

Fitowa nai hannuna rike da ledar dana Sama Yakumbo zobo, hannun Mimi na rike mukai ma Umma sallama muka fita daga gidan, cikin nutsuwa muke tafiya muna hira da Mimi tana ban labarin school dinsu har muka karasa Babban gida, ba nisa tsakanin mu da gidan a farkon layin mu gidan yake.

Muna Kiran sa babban gida ne sbd family house ne anan Yan uwan Abban mu suke zaune da matansu, muma da a bangaren da Yakumbo take ynxu anan muke da Zama da lokacin da nake da shekara goma Abba ya bar gida sbd sam Umma bata Jin dadin zama a gidan sbd Uwani matar Kawu Nasiru da kuma Hama matar Kawu Kabiru, su uku yakumbo ta haifa Kawu Nasiru ne babba sai Abba sai Kawu Kabiru.

Da sallama na shiga dogon soron gidan ina hade fuskata direct bangaren Kawu Nasiru na nufa hannu na rike da na Mimi, sallama na karayi a kofar bangaren nasu da ba kofa, shiga nai a tsakar gida na gansu zaune a kan tabarma Manniru yana kwance daga shi sai dogon wando, hannayen sa an dora akan pillow, a tsaye na tsaya ina kallon uwani dake bina da wani mugun kallo, Nima kallon da take min shi nake mata kafin na dauke kaina a kanta na maida kan Manniru da yai kalar tausayi, karkace kaina nai nace "ya jikin naka ashe hatsari Ka samu ALLAH ya kiyaye gaba"

Cikin rawar murya yace "Ameen Ya Batul" kallon Mimi yai yace "Mimi ba magana"

Murguda karamin bakin ta tai tana fari da ido tace "ai dukana kake yi wani lokacin shiyasa baxan ma sannu ba"

Karya wuya yai yace "baxan sake ko hararar ki ba Mimi ai ni ynxu kin zama kanwata ko Baki so na dinga siya miki alawar madara"

Washe kananun hakoran ta tai zatai magana na katse ta gurin fadin "Allah ya kiyaye gaba Uwani" daga haka naja hannun ta muka fita daga sassan zuwa sassan Yakumbo.

A Palourn ta muka same ta tana zaune a kasa ta mike kafafun ta da dukkan alamu iska take sha duba da rigar dake jikinta, anan muka shantake da hira don jinin mu yazo daya sosai da yakumbo duk cikin jikokin ta munfi dasawa da ita muyi fada muyi dadi haka muke lokacin da muke babban gida yawanci a dakin ta nake kwana ma sai da muka bar gidan sannan na rage zuwa gunta sbd Umma bata son muna yawan fita...


***********

Kallon Abie yai kafin ya lashi jajayen lips dinsa yace "A gidan su Haidar na kwana"

Cikin bacin rai Abie yace "ban hanaka amma kwana a waje ba na fada ma ba so daya ba ba so biyu ba duk daren da kai Ka tabbatar Ka dawo gida Ka kwana a gida"

Karkatar da kansa yai yace "Amma abie Shi Junaidu ai a waje yake kwana daki daya da mace ma watakila ma a kirjin sa take kwana me yasa shi baxa kace masa ya dawo gida ya kwana ba"

Sunkuyar da kai Junaid yai cikin tsananin kunya baisan yaushe Azlan zai nutsu ya daina iskanci ba.

Girgiza kai Abie yai duk da shima maganar Azlan din tasa shi jin kunya amma kuma ya saba da yanayin maganar sa haka yake bashi da kunya.

Girgiza kai Abie ya kuma yi yace "Ka fara mantawa cewa Shi Junaid yana da aure koh Kai kuma gwauro ne dole zai kwana a gidan matar sa kai kuma tunda baka da matar ai sai Ka kwana a gidan ubanka koh".

Dage gira yai kafin yace"nima aure xanyi na dinga kwanciya akan kirjin matata kawai" ya fada yana lumshe idonsa.

Mikewa Mami tai kawai ta shige dakin ta tana girgiza kai lokaci daya tana murmushi.

Kallon Junaid Abie yai yace duba min yaron nn ko ya sha wani Abu kafin ya shigo gidan nan.....


Comments Nd share plz


Mrs A.M🥰
[06/08, 18:23] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️

*TASWIRAR KADDARA*

♠️♠️♠️♠️♠️


Written by
Mrs A.M🥰

Page 4

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Kallon Junaid Azlan yai ya saki wani killer smile sannan ya juya kansa gefe yana shafa gemun sa, girgiza kai Abie yai kawai kafin yace "wallahi Azlan kar ka kara kwana a waje in ba haka ba sai na Saba maka wallahi"

Lumshe idonsa yai kafin ya bude su a kan Abie din, cikin kasa kasa da murya yace "insha Allah" daga haka Abie ya mike ya bar palourn.

Kallon sa Junaid yai yace "me yasa baka Jin magana ne wai Azlan kai kafison kullum Ka dinga batawa Abie da Mami rai koh, ynxu sbd tsabar rashin kunya a gaban su kake cewa mace na kwanciya akan kirjina.."

Zakudowa Azlan yai daga kan kujerar da yake ya kalli Junaid yana kankance idonsa daya sha kwalli rambadadau don shi baya ware idonsa gaba daya shiyasa ake masa kallon rikakken dan iska, tsuke karamin bakin sa yai kafin yace "ai gani nai ba karya nai ba koh abinda kuke yi knn masu auren kullum matan ku suna kirjin ku shiyasa naga nima zan maida hankali nayi auren nan ko naji abinda kuke ji"

Girgiza kai Junaid yai yana kallon Azlan kawai don shikam dama tuni Azlan yafi karfin sa, mikewa Azlan yai yana gyara wandon sa daya sassako sannan ya kalli Junaid yace "Ka gaida Mai dakin Ka ni zan wuce gurin tsoho"

Da ido Junaid ya bisa har ya fita kafin shima ya mike ya nufi part din Mami don yana son magana da ita akan tafiyar da yake son yi India akan matsalar rashin haihuwar sa...


********

Ban koma gida ba sai bayan Isha'i don Saida na gyara wa Yakumbo bangaren ta tsaf duk da ba wani datti kasancewar Yakumbo macece mai tsafta, bayan mun koma gida ban samu Umma a Palour ba nasan maybe tana daki hakan yasa nima na kwantar da Mimi da tai bacci a daki, addua nai mata sannan na fita zuwa kitchen don dora zobo na so nake nayi shi tun da daddare nasa a fridge kafin safe yayi sanyi.

Nida Aisha ne muka shiga kitchen din muna hada zobon muna hira tana bani labarin school dinsu fadan da akai yau akan wani saurayi, girgiza kai kawai nai cikin takaici ina mamakin yadda mata suke zubar da ajinsu da kimar su ta diya mace suna fada akan namiji, tabe baki nai takaici kamar zai kashe ni don haushi cikin saurin magana ta nace "ke ni ki daina bani labarin nan haba bakomai a ciki sai kayan takaici"

Dariya tai tace "dama nasan haka zaki ce ai Ya Batul don ba a gaban ki sukai damben bane ba wallahi nasan da sai kin kusa kuka kinga yadda suka yagawa juna hijab kuwa, kuma abin takaicin Wanda suke damben akansa yana zaune yana kallonsu amma ko uhm bai ce ba daga karshe ma mikewa yai ya tafi ya barsu agun irin su kashe junan nan nasu ma"

Cije lips dina na kasa nai cikin takaici nace "taya suke tunanin ma zai ga darajar su ita mace ai MAI DARAJA ce ynxu alal misali ko da ace a cikin su yana son wata wannan zubar da mutuncin da sukai a bainar jama'a ai dole ma yaji baya ra'ayin su"

Gyada kai Aisha tai tace "kuma a haka fah wai su basu yadda ba sun burge sbd sunyi fada akan abinda suke so sai hura hanci suke nidai banga karshen yadda aka kare ba na taho kar Umma tai min fada tace na dade Amma wallahi Ya Batul Allah Allah nake gobe tayi naje naji yadda ake kare"

Tabe baki nai nace "anan kika fi kauri ai son Jin gulma da munafurci"

Turo baki tai tace "ynxu ya batul nice nake da son gulmar"

Kallon ta nai nace "toh in bason gulma ba ina ruwan ki da son sanin yadda fadan ya kare"

Gyada kai tai tace "Hmm Ya Batul knn"

Kamal ne ya shigo hannun sa rike da leda yar madaidaiciya, kallona yai yace "Ya Batul yau tun da muka dawo daga school ban ganki ba ina ta tambayar Umma tace kina kin je babban gida"

Zobon dana kulla a a leda na ajiye nace ina can naje duba Manniru sai kuma na tsaya gurin yakumbo daka sani ai daka shigo gurin nata tana ta min mitar baka zuwa wai khalil ne kullum sai yaje amma banda Kai"

Dariya yai yace "rikicin tsufa ne kawai yake damunta Allah amma ko ranar Monday fa sai da naje na gaishe ta nine ma na kai mata abincin da Umma ta bayar a kaimata"

Miko min ledar yai yace "gashi inji Mansur Mai shago wai cake din ya kare nan kudin cinikin ne dubu Biyu da dari 3 shine yace na kawo miki in ba damuwa wai ki yi gobe da wuri sbd ana siya da safe sosai"

Karbar kudin nai na ciri dari ukun kai na mikawa Aisha naira dari, dari biyun kuma na bawa Kamal nace "gashi Kai da Khalil ku raba"

Godia suka fara min suna murna don dama haka nake musu in har nayi ciniki toh ina basu dari dari wannan ina ragewa Abba kudin kashewar sune tunda in na basu kudin basa tambayar Abba kudin makaranta har sai ya kare.

A gajiye na mike bayan mun gama jera Zobon a fridge nace "gaskia Kamal Ka fadawa Mansur ba lalle nayi cake din gobe ba, kaga gobe kamun Khadija kuma ni ta bawa In Mata cake da donut ga kunun Aya da zobo zanyi jibi na yini gaskia ba lallai wannan satin nayi cake ba kuma fa Monday zamu fara waec"

Marairaice fuska Kamal yai yace "Ya Batul zamu taya ki don Allah ko a cake din goben da zakiyi ki kara kayan hadin kawai sai kiyi duka hadda Wanda za'a Kai shagon"

Aisha ce tace "laaaa kuma haka ne basa banba sumu munzo da shawara mai kyau"

Harara ya sakar mata sannan ya juyo ya kalle ni yace "ko Ya Batul zamu taya ki Allah gobe Friday muna dawowa daga school in baki gama ba sai mu tayaki ko Aisha"

Harara Aisha ta sakar masa tace "wai sa'ar kace ni shekara biyu na baka amma Ka raina ni don wulakanci baxa ka dinga cemin Ya Aisha ba sai wani Aisha kana ganin yadda Khalil yake cemin duk zai kira ni sai yace Ya Aisha Amma Banda kai banza mara kunya"

Zai yi magana na janyo hannunsa na tura sa palour nace "wuce muje toh ka taya ni duba abinda Banda Shi na cake din sai Ka siyo min tunda ga kudi sun shigo"

Shiga palour mukai yana fadin "me yasa baki ce su Khadijan su baki kudi ba kafin ki musu Ya Batul"

Dariya nai nace "kawai na fison sai na gama maka abinka tsaf in kazo dauka Ka ban kudina cas kaga wannan kudin da aka ban zan ware ribata nasa a banki ragowar kuma na kara siyo kayan flour"

A Palour muka zauna muna lissafi har Abba ya shigo gidan anan aka hau hira kowa na bada labarin abinda ya faru daya basa mamaki ko wani Abu da yai Wanda Abba zai gyarawa mutun yai masa in na fada ne yayi, haka muke muna da fahimtar juna sosai mun dauki iyayen mu matsayin aminan mu da ba wani sirrin mu da muke boye musu shiyasa ko lokacin da KADDARA ta fada mana akan samuwar cikin Mimi sosai iyayen mu suka fahimci zancen kuma suka karbi KADDARAR da hannu bibbiyu duk irin bakaken maganganun da suka dinga ji suka toshe kunnen su har Mimi tazo duniya komai Abba ne yake mata sai dana fara Sana'a nema komai na samu akan ta nake karar da shi gurin siya mata sitiru masu kyau daidai talaka mai rufin Asiri.

Sai karfe 10 sannan Abba ya kashe TV yace kowa yaje ya kwanta dama haka dokar sa take tun muna kananu karfe goma kowa yake shiga daki ya kwanta sbd school sai in ranakun daba makaranta ne ma yake barin mu wataran mukai 11, dakin mu muka shiga nida Aisha su Kamal ma suka tafi dakin su dake jikin dakin mu, sai dakin su Umma dake kallon dakunan mu, koda muka shiga daki sai da muka sha hira sosai nida Aisha kafin mu kwanta bacci.

Washe gari da kaina na raka Mimi makaranta bayan tasa nai mata alkawarin zan koma na dauko ta da kaina, ina komawa gida na fara aikin cake dina tunda da wuta Allah ya taimake ni kafin 11 har na gama don da toaster biyu nake yi da toaster daya ce dani da aka fara bani order din cake na biki ko suna sai na tara kudina na siya wata toaster din sbd na rinka sauri, doughnut din na kwaba na ajiye a rana, hijab dina na zumbula har kasa dark blue nai ma Umma sallama na tafi school din su Mimi dake cikin Unguwar mu.

A compound din school din na same su itada Hidaya suna zaune suna wasa da kasa, suna gani na suka taso a guje suka taho suka rungume ni, dariya nai ina shafa kansu ina son Hidaya sbd ita kadai ce kawai Mimi mutane sun jahilci Kaddarar data same mu basa son yayansu suna kawance da Mimi duk da kuwa yadda yarinyar take da farin jini amma banda cikin layin mu don duk Wanda yasan ta yadda aka same ta kyamar ta suke banda gidan su Hidaya.

Riko hannun su nai sai murna suke nazo daukan su, sai da na tsaya na siya musu awara ta goma goma da ice cream sai murna suke suna tsalle, har gida na kai Hidaya kasancewar gidan su a jikin gidan mu yake mamarta ba wata babba bace Aunty Zainab tana da kirki sosai Hidaya ce yar ta kadai sai ynxu da take dauke da wani cikin.

Muna shiga gida wanka nai ma Mimi na sa mata atampar ta ta sallah powder da kwalli na samata sai vaseline dana shafa Mata a lips dinta, dankwalin ta na daura mata, abincin da Umma ta dafa na Rana na zuba mata na koma gurin aikin doughnut din da nake, kafin karfe 2 na gama doughnut din na ajiye a gefe, kafin na mike daga gurin kanwar Khadija da yayar ta suka shigo, gaisawa mukai bayan sun gaishe da Umma, a tare muka kirga cake da doughnut din sai da na tabbatar ya cika iya adadin Wanda suka ban na jera su a cikin kwali, dubo Goma Yayar Khadija ta miko min tace "ga kudin nan Batul mun gode sosai sai gobe insha Allah kinsan yini da wuri ake yi don Allah kafin karfe daya muke son zobon da kunun Aya."

Karbar kudin nai na mikawa Umma sannan nace "Insha Allah zaku samu da wuri sai dai ku kawo kulolin da zan sa zobon a ciki tunda kinga sai na zuba kankara akai yadda zasuyi sanyi koh"

"Insha Allah goben da safe za'a kawo mun gode sosai"

Kati ta mika min guda biyu tace"gashi na kamun ne karfe 4 ne za'a yi don Allah kuzo keda Aisha"

Kallon Umma nai ganin bata kallona ma yasa na karba nace "zan Kira Abba na tambaye sa in ya bari mai zai hanani zuwa"

Har kofar gida na raka su sannan na shigo na gyara gurin Aisha da dawowar ta knn ta tayani muka kintsa inda na bata, cake din da nai na zuba a Bokitin fenti na ajiye a gefe ina jiran khalil ko kamal wani ya shigo na basa ya kaiwa Mansur, Zama nai gurin Umma muna lissafin yadda za'a yi da kudin sai murna muke sbd wannan ne order da aka taba bani mai tsoka ragowar duk basa wuce na 5k koh 7k Amma ynxu gashi 10k zuwait ga gobe ma Insha Allah zan musu zobo da kunun Aya na 5k.

Kasancewar inada banki da nake tara kudi kodan university din da nake son shiga in na gama waec, sbd na ragewa Abba wani abun yasa Umma yanke shawarar a ajiye 10k din duka a bankin nawa,

Kallon Umma nai nace "a'a Umma keda Abba kudai dubu biyar kusa albarka ko Umma"

Girgiza kai tai tace "A'a basai mun dauka ba ke da kike Tara kudin ki"

Damun Umma nai dole sai da ta dau 2k tace "zamu raba wannan nida Abban naku Allah ya karo kasuwa mai albarka yai muku albarka gaba dayan ku"

Nida Aisha muka hada baki gurin fadin "Ameen Umma"

Wayar Umma na karba don kiran Abba na gwada tambayar sa zuwa bikin Khadija ko Allah zai sa ya barmu


*********

Gyara zaman sa yai yana kallon Baffa yace "toh kai tsoho meye damuwar ka da aure na"

Kallon sa baffa yake yana gyara zaman glass din idonsa yace so nake kaima kayi aure kamar yadda da uwan Ka yai kana kallo dai shekarar Dan uwanka biyar da aure amma kana zaune Kai baka da aiki sai zuwa gidan casu kuna juya mazaunai"

Murmushi Azlan yai har saida jerarrun hakoran sa suka bayyana yace "tsoho kaima fa Ka iya vawulence fah ynxu meye na cewa mazaunai"

Salati Baffa ya saki yace "ynxu Azlan nine na iya vawulence din"

Gira daya ya daga yace "yesss tsoho"


Comments are share plz


Mrs A.M🥰

[07/08, 22:05] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️

*TASWIRAR KADDARA*

♠️♠️♠️♠️♠️


Written by
Mrs A.M🥰

Page 5

Barkan mu da shan ruwa Allah y karbi ibadun mu Ameen

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Girgiza kai Baffa kawai yai yana bin Azlan dake danna min waya da kallo, ganin shirun bana karewa bane yasa Baffa cewa "kana zuwa gurin aikin kama kuwa Hussaini"

Dagowa yai daga danna wayar sa da yake ya zubawa Baffa lumsassun idonsa yace "me Ka gani tsoho"

Dan daure fuska Baffa yai kan yace"gani nai kamar baka zuwa don shashanci sun dauke ma hankali"

Hade rai shima yai sosai ya koma asalin Azlan din da Yan mata suke matukar tsoron tunkara, zakin da Maza suke tsoron shiga gonar sa, kallon baffa kawai yake yana kara kankance idonsa, tsaki baffa yai yace "ynxu dai ya maganar koyar war Ka yadda zaka fara"

Dan tsuke bakin sa yai ya juya fuskar sa gefe yace "Tsoho bana son wannan lecturing din da wanne zanji ga company ina zuwa ga kuma wani lecturing ni nasan Abie yana son na fara ne kawai sbd na zama busy sosai"

Ruwa Baffa ya dauka ya kora kafin yace "aikin companyn fa ba ko yaushe kake zuwa ba da akwai ranakun daka diba kake zuwa mai zai hana Ka karbi tayin koyarwar in yaso rabakun da baka zuwa aiki sai Kana shiga makarantar kana koyarwa"

Dan tsirawa Baffa ido yai kafin yace "mai yasa kuke son dole wai sai na fara lecturing bayan kunfi kowa sanin bana son hayaniya kuma baxan iya jurar magana mai tsayi ba ga students"

Murmushin manya Baffa yai yace "zaka iya *ZAKI* Insha Allah kawai dai ynxu kana ganin abin kamar da wuya amma daka fara zaka saba"

Hade rai yai ya kwantar da bayansa a jikin kujera kafin ya mike hannun sa na dama yana kallon zanen tattoo din zakin dake kwance a damtsen hannun sa, dan lasar lips dinsa yai kafin yace "shiknn zan yi amma sai wata shekarar baxan yi joining ynxu ba gaskia"

Murmushi Baffa yai yace "Alhamdulillah dama ai yardar taka kawai muke Jira tunda dai baxa ama dole ba Allah yai muku jagora"

A kasan lebensa ya amsa da Ameen, daga haka ya kwantar da kansa a jikin kujerar yana tunanin yadda zai fara lecturing a university sufa su Abie gani suke kamar shiririta yake yi baya maida hankali a companyn da yake aiki, wani malalacin murmushi yai yana tuna zanen gidan da yai kasancewar sa Architecture...

Baffa ganin yadda yai yasa shima yaja bakinsa yai shiru ya maida Kallonsa kan TV yana kallon Sunna TV...


*******
Cikin farin ciki muka fara waec don Alhamdulillah ina da basira sosai, satin mu biyu da fara waec mukayi yi jamb kamar dai yadda yake duk Wanda yai jamb hankalin sa ba'a kwance yake ba har sai yaga result dn nima haka yake a gurin na, duk da Alhamdulillah ina saran na yi abin kirki tunda nasan fiye da rabin questions din kuma na amsa su sbd nacin karatun da nai akan jamb din ga kuma Abba yana tayani kullum da daddare sai ya mun lesson kasancewar sa principal din makarantar gwamnati.

Jiran result nake yau sbd tun jiya an fara saki munea yau muke saran za'a saki namu, a hankali na janyo sabuwar wayata Tecno wacce Abba ya siya min satin dana fara waec ya bude min email da WhatsApp a ciki sbd wasu abubuwan ana turowa ta WhatsApp bama masu yin waec, kafin ya ban wayar sai da ya min nasiha sosai akan yadda zanyi amfani da wayar kuma ya ja mun kunne, ranar daya ban wayar su Aisha sunfi ni murna ma, Mimi kuwa sbd murna ranar ko kofar gida bata je ba tana tare dani motsi kadan zata ce nai mata hoto.

A hankali na janyo wayar na Kara tura message ga numbern da za'a turo mana jamb result dinmu ta ciki, ai kuwa ko 3 minutes ba'a dauka ba message ya shigo ta numbern, a zabure na mike ina yarfe hannuna ciki na na juyawa sbd tsoron abinda zan gani.

Da gudu na fada palourn mu ina haki, dagowa Umma tai ta kalle ni kafin tai tsaki ta juya tace "ke kuwa wani lokacin kamar baki da man kai ynxu meye na fado min a guje kamar yarinya"

Yarfe hannu nake kamar zan fashe da kuka na mika mata wayar nace "Umma duba min an turo min result dina na Jamb wallahi tsoron budewa nake Umma"

Hannu tasa ta karbi wayar ta shiga message dn ta duba, da Dan karfi tace "Alhamdulillah ya Allah"

Tsugunnawa nai na fada hannun ta nace "Umma nawa naci nayi kokari ko"

Wayar ta miko min fuskar ta dauke da murmushi mai nuni da tsantsar farin ciki, cikin rawar hannu na karbi wayar na duba, ihu nasa cikin murna kafin na kalle ta nace "Umma 228 na samu Alhamdulillah"

Itama dariya tai tace "Maza Kira Abbanku ki fada masa don shima Naga alama komai yake cikin sanyin jiki yake yana jiran yaji nawa kika samu"

Da sauri na danna numbern Abba sai da ta kusa katsewa sannan ya dauka, yana dauka ko magana ban bari yai ba nace "Abba Albishirin Ka"

Murmushi yai yana sauke ajiyar zuciya daga Jin muryar ta yasan ta samu point din da take so cikin zakuwa dason sanin nawa ta samu yace "Goro fari kar"

Dariya nai nace "Abba 228 na samu Insha Allah in naci waec dita Nima next year zan shiga university"

Dariya shima Abba yai yace "Alhamdulillah har an fara maganar university knn toh Allah ya bada sa'a ya tabbatar da alkhairin sa"

Murmushi nai nace "Ameen Abba sai Ka dawo" kashe wayar nai na zauna ina kallon Umma da take kallona, dariya nai nace "wallahi Umma tunda aka fara cewa an saki result nake gudawa ynxu ma fa wata nake ji bara naje nayi kafin su Mimi su dawo daga islamiyya yau wainar fulawa zan mana"

Tabe baki Umma tai tace "ku kuka sani nidai baxn ci wannan wainar taki ba wacce kuke cikawa yaji duk ta batawa Mutum ciki"

Mikewa nai ina dariya nace "Ummanmu knn ai Abba yana ci nasan in nayi zai ci Shi"

Kitchen na shiga na dora abincin dare ina yi ina duba Physics dina, bayan na gama daki na koma na kwanta akan gado.

Janyo wayata nai na bude WhatsApp anan naga kowa yana tura nawa ya samu a jamb, Wanda yaci na tayasu murna wadanda suka fadi kuma nai musu jaje, wata Halima Umar ceh ta tambayar ni kona duba nawa kuma nawa na samu, screenshot din danai na tura musu, nan suka hau taya ni murna don kusan dukan su nafi su samu.

Safiya idi ce tace dama Batul Auwal kokarine dake shiyasa bakya shiga cikin mutane ana hira, emoji din murmushi kawai na tura musu don bana magana sosai a group din haka kuma ko a school ban cika magana ba don bana son tashin hankali mutane da yawa sunsha samu na su fada min irin gulma ta da ake akan wai bana shiga cikin jama'a ana hira dani sbd ina da kyau kuma ina da kokari sai dai kawai nace Allah ya kyauta don ni tun da Mimi tazo duniya naja jikina da mutane sbd wulakanci da nuna kyama da wasu suke min, wai a haka don Abba ya chanja min makaranta knn ma.

Ina kwance ina game Mimi ta fado jikina tana fadin "Washhh Maa dita bayana lugude yake"

Ajiye wayar nai ina dariya nace "Mimin MAA dinta bayan ne yake lugude"

Lumshe idonta tai tace "uhm Maa na gaji sosai kawai ki barni na kwanta bacci abuna"

Mikewa nai nace "tashi magriba ta matso ki bari in anyi isha sai ki kwanta ko baki so ki samu ladan sallah ne"

Turo baki tai tace "inaso mana Maa"

Kaya na chanja Mata muka fito Palour ana nake fadawa su kamal nawa na samu a jamb, sai sabuwar murna ta barke mana Umma na zaune tana kallon mu fuskar ta dauke da murmushi, a kullum ta kalli yaran nata taga yadda suke hada kansu komai tare suke farin ciki ke lullube ta tana addu'ar Allah ya cigaba da hada mata kan yaran ta.

Sai bayan Magrib da Abba ya dawo hadda tsire ya siyo mana ai kuwa mun ji dadi sosai, wainar fulawar na soya mana nida Aisha sannan na bawa Aisha ta kai palour, sai da na wanke abinda muka bata Wanda Aisha bata wanke ba sannan na shigo palourn, fridge na nufa na dakko mana Zobo Mai sanyi na ajiye a tsakiyar palourn.

Mimi da tun da aka ajiye tsiren take zaune tana kallon ledar ce ta kalle ni tace "Maa party muke yi yau"

Dariya muka sa Mata mu dukan mu, Abba ne ya janyo ta jikin sa yace "zo na sa miki tsiren nan a baki dai ki dandana ko hankalin ki zai kwanta"

Washe yan kananun hakoran ta tai ta zauna akan cinyar sa, cikin nutsuwa muke ci muna hira rabin hirar duk nida Abba ne ina tambayar sa yadda university take yana bani amsa dai dai da tambaya ta, ji nake kamar na janyo tym na ganni a university a matsayin student, bayan mun gama physics na dakko Abba yana kara koya min inda yake ban wahala kasancewar Shi zan rubuta gobe sai wajen 11 na tafi daki lokacin Mimi da Aisha sun dade da bacci Nima fitanai toilet na kama ruwa nai alwala, kwanciya nai a gefen Mimi ina fuskantar ta lumshe idona nai da hawaye ke son zubo min a hankali na dora hannuna akan fuskar ta nace "INA KAUNAR KI MIMI duk ta yadda aka same ki mu muna sonki sosai kuma zan kasance mai kaunar ki har karshen rayuwa ta."

Kallon fuskar ta nake da bana gajiya da kalla ina tunanin duk yadda akai Mimi da Mahaifin ta take kama nidai kowa ya ganni yasan bana kama da Mimi don Mimi fara ce tass har wani jaja take ni kuma Baxa a kirani da baka ba kuma bana cikin jerin farare, kuma bankai Mimi manyan ido ba don idona madaidaita ne, hanci ne kawai za'a dan iya kamanta mu shima don dukkan mu muna da dogayen hanci ne amma ni nawa hancin yafi na Mimi siriri, sai lips inda na Mimi suke sirara kuma kananu nawa kuma madaidaita ne kuma suna da dan tudu kadan sannan a zagaye suke, ko gashin kai nawa da nata ya banbanta ni nawa kana gani zaka ga gashin mune na hausawa dai dai misali, nata kuwa yawansa da tsantsin sa yafi kama dana larabawa.

Maganar kyau kam nasan Mimi ta fini kyau nesa ba kusa ba kuma ba inda ta dakko ni, Murmushi nai kawai ina ja mata hular ta data zame sai kuma na hade rai ina jawa kowa ye mahaifin Mimi Allah ya isa don haka ya zamar min jiki in har zan kalli Mimi sai na tsinewa Babanta, ina wadannan tunanin har bacci ya dauke ni....


Asuba ta gari Batul🥱


Comments Nd share plz


Mrs A.M🥰
[09/08, 17:45] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️

*TASWIRAR KADDARA*

♠️♠️♠️♠️♠️


Written by
Mrs A.M🥰

Page 6

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Washe gari tare muka fita nida Mimi sai da na fara rakata har makaranta sannan na fito don karasawa tawa school din kasancewar 9 ina da paper, a hanya na hadu da cilla yana gani na na tsaya yana sosa keya.

Harara na maka masa kafin nai gaba don haushin sa nake ji shekaran jiya nai ta kiransa yaki daga wayata, kuma bai kirani back ba har ynxu(Hajia Batul yada karfin hali haka)

Dan sauri yasa ya dawo gefen ta amma dan nesa da ita yadda kusancin su bazai yawa ba, cikin muryar katuwar muryar da yace "haba Uwar dakina kiyi hakuri wallahi wayar tawa bata hannu na kika kira kuma dana karbi wayar zare sim dina nai naje na siyar da ita ynxu dai wata sabuwar nake son siya"

Wani kallo na watsa masa da idanuna masu matukar kalli da sheki kafin na tabe bakina nace "toh ynxu daka min wannan tambayar na tambaye kane"

Murmushi yai yana kallon ta daga dukkan alamu yau Yan miskilan cin ne a kusa da mutuniyar tashi gwara ya lallaba ta su rabu lafia, cikin kwantar da murya yace "ina so na kiraki tun jiya inji nawa kika samu a Jamb din ki naji an saki result"

Sai lokacin nadan saki fuskata ne nace naci "Alhamdulillah 228 na samu"

Murmushi yai yace "barka uwar dakina nida ma nasan insha Allah zaki kwashe ta ai kedin ta daban ce"

Girgiza kai nai nace "kai nawa Ka samu"

Shafa kansa yai dayai masa askin samarin zamani yace "184 na samu"

Dan tsayawa nai da tafiyar da nake na juyo na kalle sa nace "don Allah fah"

Dariya yai yace "wallahi da gaske nake Nima nayi mamaki na dauka fa irin 40 dinnan zan samu AI da aka duba min a cafe da farko kin yadda nai sai da mutane da yawa suka duba aka tabbatar nawa ne sannan na yadda"

Dariya nai nace "Alhamdulillah baka ji yadda naji ba tun jiya dama nake tunanin Kai nawa Ka samu don ina fatan mu shiga school dinnan tare muyi komai tare bana son shiga shirgin mutane kar ma a raina Ka"

Dariya cilla yai yana gyada kai yace "Allah ya taimaki Uwar dakina"

Nidai banyi magana ba har muka karaso bakin titi, kallon sa nai nace "Ka gaida Baba kace mata zan shigo Insha Allah anjima in na dawo"

Daga min kai yai yace "kamar kinsan kuwa jiya ta gama min maganar kwana biyu bata ganin ki nasan zata ji dadi sosai in na fada mata"

Sallama nai masa na karasa makaranta, binta da ido Cilla yai yana matukar ganin girman Batul kaf layinsu ita ta fara masa kallon mutum mai mutunci kowa a matsayin Dan iska ya dauke sa sbd yanayin shigar da yake da kuma irin maganar sa don da ya taba dabanci har taba yana sha, fara shirinsu da batul ya rabu da dabancin da yake ya kuma daina shan taba, da taimakon Abbanta ya sama masa aiki a wani garagi, shiyasa har Mamansa take mutunta lamarin Batul din.

Shi kadai ne wanda Batul take gani a matsayin Aboki don ko lokacin da KADDARA ta fada mata bai taba gazawa gun tausar taba shiyasa shima bashi da aminiya irin ta komai nasa ta sani, ynxu haka tare suka rubuta Jamb din wanda Saida batul tai masa karamin hauka sannan ya yadda ya rubuta dama yana da waec dinsa tare suke son shiga university sai dai kowa da course din da yake son karanta.

Koda ya fadawa Mamansa ra'ayin sa na son komawa makaranta ba karamin murna tai ba don ba yadda batai da shi ba amma fafur yace shi baxai wani karatu ba don kwakwalwar sa bata daukan komai sai gashi shima ya samu jamb din, bashi da matsalar kudin Makaranta tunda yana tarawa a banki kuma mahaifiyar sama tana Sana'a sosai Alhamdulillah suna da rufin asiri daidai gwargwado.

Murmushi yai yana mamakin son girma irin na Batul a kalla ya bata shekara 7 don shi shekarun sa 25 amma ta maida Shi kamar kanin ta, girgiza kai yau yace "Allah ya nuna min ranar da wani da wani zaiyi wuf da zuciyar ki in aurar dake don ranar hadda ni a masu Kai amarya ai ba Zama aminiya guda tana aure"


**********

Cikin takunsa na cikakken namiji ya fito daga dakinsa yana gyara neck tie dinsa, kusan karo suka kusa ci da Abie da sauri yai baya yana Dan kau da kansa.

Da mamaki Abie yake Kallonsa ganin sa sanye da suit ash colour da tai matukar amsar jikinsa, kallon agogon sa Abie yai kafin ya maida dubansa gurin Azlan yace "lafia kuwa naganka cikin shigar nan kuma zaka fita da sassafe"

Da dan mamaki Azlan ya bi jikinsa da kallo sai kuma ya saki wani munafikin murmushi yace "Lau Abie office zani"

Ware ido Abie yai yace "office kuma dama kana zuwa office har ynxu neh"

Wannan karan sai da ya dan gyara tsayuwar sa yana zuwa hannunsa cikin aljihun sa yace "ina zuwa mana Abie sai dai ba kullum ba sai ta zama dole ynxun ma wani zane ake so nayi na wata makaranta shiyasa zanje Amma ina gamawa zan fece"

Gyada kai Abie yai sai kuma ya kalli idon Azlan daya sha kwalli rambadadau yace "toh shi kwallin zaka office ma sai Ka sashi wai ni ban gane maba meye amfanin wannan kwallin ne"

Cike da shakiyanci ya kankance idonsa ya janyo lip dinsa na kasa ya kasa sannan yace "na farin jini ne Abie kasan na gaji da rungumar pillow shine nake sawa ko zanyi budurwa Nima Ka aurar dani na danka mata budurcina don naga magauta sun fara kawowa budurcina Hari"

Sakin baki Abie yai kafin ya girgiza kai yace "ynxu duk yan matan da suke sonka ko acikin yan uwa ne basu ishe Kaba sai Ka wani sa kwalli ga yar uwar Ka Zainab kowa yasan irin son da take ma amma kayi banxa kamar baka san me take nufi ba"

Shafa kirjin sa yai yace "Abie basu min ba duk kwailaye ne ita kuma Zainab din inaji kirgan dangi ta fara ne ko yaya ne gata a tsaye kamar sanda ba gaba ba baya ynxu fisabilillah Abie in na aure ta a wani kirjin zan dinga kwanciya maimakon na kwanta naji laushi saidai naji kasusuwa."

Salati Abie yasa kafin ya juya da sauri kamar zai kifa ya nufi part dinsa yana salati wallahi Azlan ya fi karfin sa ynxu har shi zai tara yana ce masa kwailaye waye da waye..

Shi kuwa Azlan murmushi ya saki yace daidai nake da ku Allah baxan auri kwaila inzo ina taga taga ba na fison naji komai dumi dumi abina haba.

Part din Mama ya nufa don zai karbi wayar sa da Mufeeda ta karba jiya wai xatai hoto Shi yama manta bai karba ba, yana zuwa ya tura kansa cikin dakin yana sallama kasa kasa, Mama ce kawai zaune tana Shan tea tana ganin sa ta gyara zamanta tana dan hade rai.

Dafa kujera yai ya dan daidaita tsayuwar sa yace "Hi Morning Hajia"

Kallonsa tai takaici kamar zai kashe ta ta rasa me yasa Sam Azlan ya raina ta wai Hi Morning Hajia, gyada kai tai tace "lafia"

Shiru yai ya zuba mata lumsassun idonsa yana kallon ta shidai baxai ce komai ba saita tambaye sa, dagowa yai caraf suka hada ido ya zuba mata idon nan nasa da suke matukar tsorata ta, sanin baxai magana ba tunda yai hakan yasa ta fadin "wa kake nema ne"

Agogon sa ya kalla ganin tym na gudu yace "Mufeeda"

Yana tsaye Mama ta kwalawa mai aikin ta Kira tana zuwa tace taje ta cewa Mufeeda tazo inji Azlan, basu dade ba suka dawo Mufeeda na baya tana sanye da kayan bacci hannunta rike da wayar sa.

Cikin girmamawa tace "Ya Azlan Good Morning kayi hakuri wallahi jiyan bayan na gama sai kuma battery din yai kasa shine na Sama charging kuma na manta ban kawo maba"

Karbar wayar yai yace "bana hanaki yawan rantsuwa ba"

Marairaice wa tai tace "kayi hakuri baxan sake ba na manta ne"

Bai ce komai ba sai kallon Mama da yai ya daga mata hannu alamun bye ya fita yana takun sa cike da jarumta, yana fita gurin motar sa ya nufa ya shiga da wani mugun guda yaja ta yabar gidan don ana jiransa a jiya aka basu contract din ginin makarantar da gwamnati zata gina kuma shi ake son ya zana..

Tafiyar minti 10 ta kaisa companyn sbd gudun daya keyi, yana zuwa bai ko tsaya amsa gaisuwar mutane ba ya nufi office dinsa dake hawa na 2, katon office ne mai dauke da doguwar kujera ta hutawa sai kujera da table dinsa a gaban table din kujeru biyu ne da baki suke zama akai ga kofar toilet dinsa a gefe shima gefe daya fridge ne dan madaidaici office din ba abinda yake sai kamshi.

Gurin wani katon shelf ya nufa dake dauke da manyan littafai, tura shi yai sai yai baya daki ya bayyana, shiga ciki yai yana bin ko ina da kallo dakin zanen sane anan yake Zane in yana office cikin nutsuwa ya dauko duk abinda zai bukata na zanen makarantar da zaiyi so yake kafin ya bar office yau ya kasance ya gama zanen, remote din AC ya dauka ya kure ta sannan ya sassauta neck tie din sa ya zauna, janyo wayar sa yai ya kunna suratul Bakara cikin kira'ar Sheik sudais cikin nutsuwar da ban taba ganin sa da shi ba ya shiga bin karatun cikin kwarewa da bawa ko wane harafi hakkin sa a hankali ya dauki Pencil yai bismillah ya dora akan paper ya fara xaneeee.......


**********

Cikin Amincin Allah mun gama waec Lafia sai fatan result yai kyau, tunda muka gama na maida hankali kan sana'ata sosai don ynxu har doughnut nake yi a fitar min da shi, ga kuma kunun Aya da zobo na.

A tsakanin lokacin nan na shiga tahfiz weekend da safe ina so kafin na samu admission na haddace izu 10 tar a kaina, sosai Allah ya Sama Sana'a ta albarka ina ciniki sosai, ganin wani lokacin da yamma ba abinda nake yasa nayi shawara dasu Abba na fara zuwa gidan Aunty Zainab maman shahida koyan dinki tunda tana dinki, AI kuwa dana tambaye ta akan ina son zuwa na fara koyan dinki ckin farin ciki ta amince.

Fara zuwana koyan dinki ya Kara maida ni busy sosai sam bani da ishashhen lokaci ga hadda ina yi, cikin haka result dinmu na waec ya fito, Alhamdulillah naci sosai don A har uku nake da shi.

Haka kuma na fara karatun post utme don Buk na cike ita nake son zuwa fatan dai na samu naci post utme din, tunda ynxu makarantar ma ko kaci wani lokacin danne wa yayan talakawa ake yi a bawa yayan masu dashi.

A hankali hannuna yake kwarewa a dinki na dinkawa Mimi riguna har biyu masu kyau irin na yara...


***********

A xaune yake a kasan carpet ya mike kafafunsa dake dauke da kwantaccen gashi, yana sanye da three quarter da kuma singlet data fito da kirar sa ta cikakken namiji, kallon Junaid yake daya kwantar da kansa akan cinyar Mami yana hawaye gefensa Samira ce tana sanye da abaya kanta a kasa itama kukan take kasa kasa..

Cikin muryar data shake sbd kuka Junaid yace "Mami sunce wai ba lallai naga dana a duniya ba wai wannan aikin da aka min basu da tabbas akan sa kawai sunyi ne sun Dora ni akan magani, ni in nayi hakuri Samira fah ita haka zata rayu baza taga danta a duniya ba knn anya xaman mu ba cutarwa"


Allah sarki Junaidu🥹


Comments Nd share plz


Mrs A.M🥰

[10/08, 19:56] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️

*TASWIRAR KADDARA*

♠️♠️♠️♠️♠️


Written by
Mrs A.M🥰

Page 7

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Da sauri Samira ta dago ta kalle sa cikin damuwa ta rarrafo ta iso gaban Mami itama, hannun ta ta dora akan na Junaid tace "baxan taba barin Kaba Hub duk halin daka shiga Nima shi na shiga ina kaunar Ka a haka ina sonka sosai"

Murmushi Mami tai tana kokarin mayar da hawayen ta cikin dakewa tace "ku kwantar da hankalin ku yarana Insha Allah za'a dace ma Junaid komai zai zo ya wuce"

Shidai Azlan yana zaune ya zuba tagumi yana kallon shidai har ga Allah baiga wani abun damuwa ba dududu auren Junaidu shekara biyar ne amma ya tayar da hankalin sa sbd ance baya haihuwa ai ya bari ya shekara 20 haka sai ya fara damuwa, Shi Sam yara basa gabansa ma sbd dakinsa suke Shi kuma baya son hayaniya.

Kallon sa Junaid yai yace "Azlan baka ce komai ba Ka zuba mana ido kawai"

Kankance idonsa yai yace "Junaidu mai xance ma toh addu'a kawai zan taya ka Allah ya kara lafia amma in kana bukatar maganin karfi ne kafada min zan nemo ma"

Da mamaki Junaid yake kallon sa Samira kuwa sunkuyar da kanta kasa tai tana mamakin rashin kunyar Azlan hatta Mami sai da taji kunya ta lullube ta.

A kufule Junaid yace "banson iskanci meye haka wai"

Jingina bayansa yai a jikin kujera yana rungume hannun sa a kirji yace "misali in so daya kake yi kaga sai Ka Kara kaimi kana yi kamar so uku haka koh shine kawai kaga in yi dayan ba'a dace ba kasani ko ana biyun a dace don't feel shy Ka fada min zan nemo ma"

Sakin baki Junaid yai fa takaici GA kunya data rufe sa, fahimtar hakan yasa Mami itama ajiye kunyar ta agefe tace "tashi ku tafi Junaid sai da safe Allah yai muku albarka"

A hankali suka amsa suka mike suka fita, da kallo Azlan ya raka su nai bai ce komai ba, maida dubansa ga Mami yai yaga ta zuba masa ido hakan yasa shi sosa keya ya saki wani munafikin murmushi yace "Mami ya kinsani Jin kunya kuma kar ki kawo tunanin komai a ranki Nima kawai nasan ana yi fiye da daya ne amma budurcina lau yake"

Girgiza kai Mami tai tace "Allah ya shirya min kai Azlan ya nuna min ranar da zaka yi aure Ka daina kiran wannan budurci"

Dan tsai yai da idonsa yana kallon ta sai kuma ya tsuke bakinsa yace *"MAA* ynxu in nayi aure shiknn kowa ya daina min kallon Mai budurci knn"

Mikewa Mami tai tana cewa "bara na tafi Azlan baza ka samin hawan jini ba, kuma kar ka manta da akwai taron Family karshen watan nn nasan halin Ka zaka iya kin zuwa"

Shidai rakata yai da ido kawai har ta shige dakin ta sai kuma ya mike ya nufi part dinsa, yana isa ya zauna akan lafiyayyan gadonsa, shifa su Abie sun kasa gane sane baya son mace tazo ta ce tana sonsa yana son mace Mai aji matuka, yana fatan ya ga ranar da wata mace zatai masa duba ba irin na soba, yana son ya kasance ko sonsa zai kashe mace ta ja ajinta taki fada masa har sai in shine ya fada mata cewa Yana sonta, Amma Allah na tuba Mai zaiyi da wata Xainab shekarar ta 24 amma kallon kwaila yake mata sbd duk ciko take.

Shi babbar samuwar Sama ynxu wannan family meeting din da zaka ayi sam baya sonsa sbd wasu dalilai nashi, karamin tsaki yai gashi tunda Mami tace yaje baxai iya musu ba zuwa ya zamar masa dole, kwanciya yai yana lumshe idonsa cikin wani yanayi da yakan shiga.......


********

Dawowa ta knn daga tahfiz a gajiye nake sosai duk jikina ciwo yake min ma, Zama nai a kasan carpet din palourn mu ina mike kafafuna, cikin gajiya na kalli Umma da take duba littafin Seera turo baki nai gaba cikin shagwaba nace "Umma kina kallo na shigo fah"

Banza tamin sai da ta dau mintuna sannan ta kalle ni tace "toh da kika shigo mai zan miki ne ehe in zaki Saba ma gwanda ki saba jami'a zaki shiga tohm"

Nidai ban kuma magana ba mikewa nai na shiga kitchen Dan wake na dora mana, ina cikin yi Mimi dasu Kamal suka shigo Suma saida na gama Dan waken na zuba mana a babban plate muka hadu gaba dayan mu muka ci har Umma, bayan mun gama su kamal ne sukayi wanke wanke ni kuma nai wa Mimi wanka, cikin rigunan dana dinka mata na dauki daya nasa mata sai murna take an sa Mata sabon kaya.

Kallona tai tace "Maa unguwa zamu je kin samin sabon kayan da kika dinka min"

Dariya nai ina taje mata dogon gashin ta nace "a'a babban gida zamu gurin yakumbo kinga mun dade bamu je ba ko Babyna"

Daga Kai tai tana murmushin dake kara wa fuskar ta kyau sosai, hula na samata na rufe Mata gashin ta ruf, kallon ta nai bayan na dafa kanta nai mata addu'a nace "Maza jeki gurin Umma ko su Ya Khalil kuyi hira bari Nima nayi wanka koh"

Da gudu ta fita na bita da kallo ina murmushi, kayana na cire na sa zanin wanka na na fita don wanka, ban dade ba na shigo dakin mu shiryawa nai cikin riga da skirt simple style ne amma sun kamani, a hankali na taka har gaban Mirrow dinmu na tsaya ina karewa kaina kallo.

Bana cikin jerin masu kiba kuma niba sirirya bace Allah yamin halitta Mai daukan hankali sosai, ina da cikar Kirji sosai haka kuma ina da diri ga hips sai yanayin jikin nawa yasa ake min kallon mai kiba, ina da karuwar jiki ta yadda duk taku daya in nayi gaba daya jikina sai ya girgiza duk abinda zansa kuwa sbd yanayin jikin nawa nake sa bra ta kamani kuma nake sa tight a cikin dukkan kayan da zansa amma a banxa shiyasa duk inda zani nake zumbula hijab har kasa duk da shima hijab din ba wai yana hana jikin nawa rawa bane amma yana taimakawa gun rufe min kayan arzikina..

Powder na shafa nasa kwalli da lip gloss, hijab dina dake kan katifar mu na janyo nasa ya fesa turare na mai sanyi oud, Dan kallon kaina nai a mirror naga yadda nayi wani sassanyan kyau murmushi nai na fito hannuna rike da wayata.

Sallama mukai wa Umma bayan na daukar wa Yakumbo zobo, a kofar gidan babban gida mukai kicibus da Shamsiyya yar gidan Kawu Nasiru, kusan sa'a tace sai dai ta girme ni da watanni, kallon kallon mukai kafin na ja gefe don bata hanya ta wuce ina kuma binta da kallo ganin yadda ta tsuke cikin riga da skirt sai wani yalolon mayafi data yafa a kanta, kauda kaina gefe nai ina jiran ta wuce

Ita kuwa Shamsiyya zuba min ido tai tana kallona cikin bakin ciki ita tana adawa da komai na Batul sbd ta fita komai tafita kyau iya magana sura mai kyau, tsaki taja ta sauke kallon ta akan Mimi cikin tsanar yarinyar tace "ke baki iya gaisuwa bane kina ganin manya"

Turo baki Mimi tai kafin ta waina manyan idonta tace "kema ai bakya gaishe da Umma kullum kullum ina kallon ki"

Zare Mata ido tai tace "ke ni sa'ar kice zaki dinga fada min haka banxa sheg........

Da wani muguwa tsawa nace "kul na rantse da Wanda yake busan numfashi in kika karasa sai na fitar Miki da hakori wallahi wallahi"

Ganin yadda nai mata magana ina zare Mata idanuna masu sheki da suka fara rinewa sbd bacin rai yasa ta Jan tsaki ta yi gaba tace "banxa banda lokacin ku ai"

Tsaki naja nima nace "da kin sani kin tsaya ai banxa karamar yar iska daidai nake da ko wacce banxa"

Tafin Mimi ne ya sani kallon ta sai gani nai tana tsalle tana tafi, sakin baki nai ina kallon ta nace "ke meye haka"

Washe hakoran ta tai tace "Maa dita hero ce taji tsoron ki ta gudu ai da ta tsaya Maa ki goge Mata bakinta da bango"

Rike baki nai ina gyara tsayuwa ta nace "ban hanaki shiga maganan manya ba uhm"

Hannu tasa ta rike lips dinta tace "na daina Maa dita baxan kuma ba ynxu ma murna ce ta min yawa" ta karashe tana washe kyawawan hakoran ta

Cikin gidan muka shiga ina mamakin yadda Mimi take da matukar wayo kamar ba yar shekara hudu ba ga shegen suruta a cikin ta kamar zata siyar da mutum.

Ban shiga kowanne sassa ba sassan Yakumbo kawai muka nufa, a tsugunne ta same ta tana alwala cikin tsokana nace "ke kuwa wannan tsohuwa sai ynxu kike shirin sallah"

Harara ta galla min tace "ina ruwanki yar sa ido ai ni dake munyi baram baram ja'ira"

Dariya na kwalkwale da ita na zauna akan kujera yar tsugunno Mimi kuma ta zauna akan tabarma tana wasa da zaren tabarmar, muna zaune har yakumbo ta idar da sallah anan muka shiga hira da ita.

Kallon ta nai nace "tsohuwa Mai ran karfe na kusa shiga jami'a fah"

Salati Yakumbo tasa tace "kar kice min makarantar gaba da sakandare"

Farr nai da idona nace "hakkun itafa insha Allahu gobe ma zamuje muyi jarrabawa a jami'ar in na haye shiknn na zama yar jami'a"

Tagumi Yakumbo tai kafin ta kalli Mimi ta juyo ta kalle ni tace "ke da nake fatan zakiyi aure abinki ki huta shine zaki wani cigaba da karatu"

Dan hade rai nai nace ni "Yakumbo tunda muke dake kin taba ganin nayi saurayi, nifa baxan yi aure bama gaba daya don bana son Mimi tayi agolanci"

Kallona Yakumba tai tace "ynxu in auren zakiyi da Mimi zaki tafi gidan mijin ai in aure xakiyi ma anan zaki barta"

Hade rai nai sosai na shiga masifa ni ba inda zan bar yata ni auren ma gaba daya baxan ba, itadai yakumbo kyale ni tai kawai tana kallona don tasan ta gama bata min rai daga kashe ma mikewa nai nace mata kuma sai na yi watanni bata ganni ba.


Washe gari muka je mukayi post utme fatan nasara kawai ranar sbd murna na shiga university Naga yadda take har da sadakar zobo nayi wa almajiran layin mu, itadai Umma da Abba dariya kawai suke min.


*******

A hankali muke tafiya nida Cilla ina sanye da dogon hijab har kasa maroon colour ya min kyau sosai duk da ba komai a fuskata, cikin farin cikin da yakasa boyuwa a fuskata nace "Cilla Alhamdulillah mun samu Admission fah"

Shima murmushin yake yace "bari uwar dakina ban taba Jin ina son karatun sosai ba sai ynxu"

Murmushi kawai nai ina kallon takardun hannuna da muka je cafe mukai photo copy dinsu don gobe zamu je school mu karbi Admission letter dinmu, muna tafiya muna hira munzo dai dai tsallaka titi knn wata azababbiyar mota tazo a guje saura kiris ta buge min kafa, wani malulun haushi ne yazo ya tokare ni da sauri na sunkuya na dauki dutsen da na kusa bige kafata da shi na wulla wa motar.

Cilla ne ya kalle ni yace "uwar dakina ya xaki wulla musu dutse kin ga mota daga gani wallahi ta masu hannu da shuni ce data fasa musu glass din ya zamuyi"

Cikin masifa na dago xan masa magana saidai maganar tawa ta makale sbd motar data shiga dawowa a hankali, gyara tsayuwa ta nai sosai ina jiran koma waye ya fito.

A hankali mai motar ya fito Wanda fitowar sa tai daidai da wani irin bugawa da kirjina yai har sai da nai baya zan fadi da sauri cilla da bai taba rike min koda Dan yatsa ba yai hanzarin riko min kafaduna yana gyara min tsayuwa ta, Shi kansa jikin sa rawa yake yana kallon Wanda ya fito ya zuba musu lumsassun idonsa yana musu wani kallo...........


Ina Jin dadin comment dinku fans Allah yabar kauna🥰🤝


Comments nd share plz


Mrs A.M🥰
[11/08, 22:56] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️

*TASWIRAR KADDARA*

♠️♠️♠️♠️♠️


Written by
Mrs A.M🥰

Page 8

Dedicated to ta hannun damata Garkuwar Macizai Mom Ahlan ina godia mutuniyar arziki🤝🥰, Allah y raya mana yaranmu yai musu albarka Ameen🥰


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Tun daga kafar sa na fara kallo yana sanye da takalmi half cover Wanda ya bayyana fatar kafar sa fara tas mai sirki da ja, a hankali na soma bin jikin sa da kallo yana sanye da three quarter light blue sai rigar sa armless dark blue, idona ne ya sauka akan tattoo din hannun sa na zaki sai kuma jelar micijin da ta biyo ta gefen wuyansa, a hankali na daga kaina zuwa fuskar sa wani irin bugawa kirjina yai dahar Saida na dafe hijab dina.

Kamar su daya da Mimina, Mimi diyata yarinyata suna kama kamar yayi kaki ya tofar idonsa bakinsa girar sa har yanayin gashin sa dukda yayi aski amma ba salsal yai ba aski yau irin na yan iskan samari, kara kure fuskar sa da kallo nake ko zanga wani abu daya banbanta shi da Mimina diyata amma babu ina Kara Kallonsa kamannin sa da Mimi suna Kara bayyana.

Yatsina fuska Azlan yai yana kallon ta ganin yadda ta zuba masa ido tana kallon sa har wani Kara bude ido take, cikin takunsa ya fara takowa har ya iso daf dani, ganin haka yasa na ja baya kadan amma still idona na cikin nasa ina ganin ikon Allah har irin kallon da yake haka Mimi take kallo.

Dan lasar lips dinsa yai cikin husky voice dinsa yace "hey baki da hankali ne zaki gefa min dutse a mota"

Wani irin kallo nai masa kafin na juya idona Wanda hakan ya zamar min jiki in har zanyi fitsara sai na juya su nace "koh, kai baka lura dacewa Ka kusa take min kafa bane ko baka gani ne"

Ware manyan idonsa yai akanta cikin kufula yace "kutttt***** ke ni kike zagi sbd baki da tarbiyya"

Kallon sa nai tundaga kasa har Sama kafin na tsaida idona akansa nace "sannun Baba in Ka koya min tarbiyyar ai na lefi bane"

Matso ni ya shiga yi ina baya cikin bacin ran da ya taso masa don tunda yake ba'a taba zagin sa haka ba sai gashi wata kwaila tana zaginsa akan titi, ganin ina baya yasa shi tsayawa yace "ki tsaya na koya miki tarbiyyar mana"

Miyau na hadiya don Allah ya sani na tsorata da yadda yake biyo nin nan gashi hanyar ba mutane sosai, kallon cilla nai daya sunkuyar da kai harara na balla masa da sauri ya karaso gun da muka tsaya yace "kayi hakuri don Allah kuskure ne"

Takaici ne ya kamani hakan yasa nace "Kai cilla meye zaka dinga wani basa hakuri bayan shi ya kamata ya bamu hakuri bige mana kafafu ya kusa yi fa daya murje mana yatsu ya gudu shiknn ya nakas tamu dama su masu kudi wasun su shegen iya mugunta ne dasu"

Cikin neman sulhu cilla yace "uwar dakina mubi komai a sannu kinji"

Tsaki naja nace "amma ka bani kunya bansan cewa kana da tsoro ba sai yau kai ynxu wannan ne zai baka tsoro"

Rungume hannu Azlan yai yana binta da kallo cike da mamaki yarinyar da zata yi sa'a da Mufeeda autar gidan su itace Take tsaye a gabansa tana zabga masa rashin kunya haka, cikin wata murya yace "Ashe bakin ciki ne yasa kika wurga min dutse a mota sbd kinga ina da kudi"

Baki na bude ina kallon sa kamar zanyi magana sai kuma nai Shiru kawai na kalli cilla, cikin takaici na warci takadduna a hannun cilla na tsallaka titi ina tafe ina masifa gefe daya kuma zuciya ta tana wani irin bugu sbd kamannin sa da ya tsaya min a wuya.

Cilla ne ya karaso inda yake yace "kayi hakuri don Allah uwar dakina ce wani lokacin tana da zafi amma bata da damuwa kuma ita bawai bakin ciki ne yasa ta wurga maka dutse ba kawai yadda kaso take mune kuma kayi gaba"

Tabe baki yai kafin ya juya ya shige motar sa yaja da mugun gudu ransa na baci fuskar sa har tayi ja sbd bacin rai badaban duka ba dabi'ar sa bace ba abinda zai hanasa rufe wannan fitsararriyar yarinyar da duka.

Kwafa yai kawai har ya isa gidan Baffa, yana zuwa tun daga waje yake ganin motoci karamin tsaki yai shifa wannan meeting din ba karamin takura sa yake ba.

A waje yai parking motar sa shima ya shigo gidan kansa tsaye, tun daga kofar babban palourn baffa yake jiyo hayaniya da magana na tashi ana dariya, girgiza kai yai yasan yau da ciwon kai zai kwana and wannan hayaniyar da zai shiga.

A hankali ya tura kofar ya shiga bakinsa dauke da sallamar da shi kadai yasan yai kayansa, gaba daya mutanen palourn dagowa sukai suna kallon sa, hakan yasa shi hade rai sosai dama ga bacin ran da ya kunsa kafin ya shigo.

Cikin takunsa na cikakken namiji kuma lafiyayye ya nufi gurin Baffa dake zaune a 1 seater, a hankali ya zauna a kasa kusa da kafar sa, dauke kansa yai kawai ya kasa bude baki ma ya gaishe sa shi sai ynxu ma yake mamakin kansa da har ya tsaya ya biye mata yau shine rana ta farko daya tsaya gaba da gaba da mace sukai musayar yawu sukai magana don shi baya tsayawa ma a kusa da mace Sam sbd gudun raini ko Mufeeda zai wa magana sama sama yake ya wuce.

Baffa ne da ya zuba masa ido sbd tun shigowar sa ya lura ransa a matukar bace yake ya dora hannun sa akan gashin sa yana shafawa a hankali, lumshe ido Azlan yai yana sakin ajiyar zuciya ba abinda yake hangowa sai fuskar ta tana juya ido da tsuke baki tana masa rashin kunya da sauri ya bude idonsa da suka juye suwa jaa sai kuma kawai ya saki wani murmushi yana shafa gemun sa.

Da mamaki Baffa ya zuro kansa ya leka fuskar Azlan ganin da gaske murmushi yake yasa shi fadin "ZAKI meye kuma nake gani haka"

Dago idonsa yai ya sauke akan Baffa kauda maganar yai ta hanyar ce masa "Ina wuni"

Gyada kai Baffa yai don ya gane ma'anar hakan da yai baya son ayi maganar knn.

Juyawa Azlan yai ya kalli Uncle Mustapha kanin Abie ne kuma tasu tazo daya sosai don baya takura masa sai dai ma duk lokacin da suka hadu zai masa wa'azi ne akan ya rage wasu halaye da yake ba kyau, Amma sam baya masa fada kasancewar sa mutum ne Mai sanyin hali yace "Good Afternoon Uncle M"

Murmushi Uncle M yai yace "Afternoon Son ya kk ya kuma aiki"

Lumshe idonsa yai yace "Alhamdulillah Uncle M"

Maida duban sa gun Mommy yai itama kanwa ce gurin Abie kuma yayar Uncle M, ita kam mace ce mai masifa da kuma zafi don har tafi Abie zafi kuma tana da nuna isa da iko akan komai, jinin su Sam baizo daya da Azlan ba sbd yadda take son taga tana juya su Shi Sam baya yadda da haka.

Dan rage fara'ar sa yai yace "Good afternoon Mum"

Sai da ta tabe baki tace "sannu bature da baxa ka iya gaishe da mutum da yaren hausa ba sai dai Ka masa yaren nasara"

Kankance ido yai yace "fyn ki dawo min da gaisuwar tawa kawai"

Cikin masifa tace "ni kake fadawa haka Azlan wai Kai mai yasa baka da kunya ne gaba daya dama xaman nan da mukai kai muke jira kawai kuma akan ka akai wannan zaman halayen Ka sun ishe mu kana kallon Dan uwanka shekarar sa biyar da aure amma kai kana zaune ba abinda kake sai shashanci"

Baffa ne yace"Ke Hafsatu dakata mana ki rage tsaurin maganar ki ai ba ta haka zaki masa magana ba koh"

Hade rai tai tana juya fuska cikin Jin haushin katse ta da Baffa yai itafa badon komai take son ayi maganar auren Saba sai sbd diyarta Zainab data mace akan son sa amma in ba haka ba ita ina ruwanta bata shiga sabgar sa sbd bashi da kunya ko kadan.

Kallon yaron palourn baffa yai yace "ku shige dayan palourn zamuyi magana"

Mikewa jikokin sukai gaba dayan su banda Junaid ya rage palourn daga Abie sai Mami da Mama sai Uncle M da matar sa Aunty Sarah sai kuma Mummy da Baffa sai Oga kwata kwata AZLAN.

Kallon Azlan Baffa yai yace "Zaki tunda har ynxu baka da wata budurwa shine muka ce Mai zai hana ka nemi yar uwarka Zainab tunda kowa yasan tana sonka kuma kaga ta gama karatu sai ayi tuwo na maina kawai."

Kankance ido yai kafin ya juya ya kalli Baffa yace "tsoho Umarni kake ban ko kuwa shawara ce"

Murmushin manya Baffa yai yace "shawara ce zaki"

Kallon Abie Azlan yai yadan daga hannun sa yace "ra'ayina ake bukatar ji Abie kar kace nai rashin kunya"

Kallon Baffa yai yace "tsoho bana so, sbd tamin kankanta in na damke ta sai na karya ta kuma gaskia ni ina son mace mai abubuwan laushi manya sbd na dinga matashi da su"

Salati Mummy ta dauka ita da Mama, yayinda Mami da Aunty Sarah suka sunkuyar da kansu kawai, Abie Kam tagumi yai yana kallon Azlan cike da mamakin sa.

Dan gyaran murya Baffa yai yace "kai shine abinda kake so knn amma tarbiyyar zaka duba Zaki"

Dan tsotsar lips dinsa yai kafin yace "da wannan amma baxan iya auren taba tsoho in ba haka ba kuma kullum sai an kaita asibiti an dinke ta, wannan tanadi danai na budurci na na dinga tattalin sa dukda hare haren da ake kawo masa ai dole na samu wacce zata iya jure ni koh kar aje nayi kisan Kai daren farko Nima a kashe ni"

Mikewa Mummy tai cikin masifa tace "wannan budurcin da kake fada na banxa da wofi waye baisan cewa kana zuwa club ba duk dare kalle Ka don Allah da irin shigar da kake in ba yan uwa ba waye zai baka auren yar sa"

Shima mike wa yai yace "kuma nace bana son auren a wajen da kike ganin baxa a bani ba nan zanje gidan mutunci aban"

Matsowa kusa da shi tai tace "ni kake wa rashin kunya wai ko da yake ba laifin Ka bane duk laifin Haj Maryam ne ita ce bata kwafar Ka in kana yi gashi ynxu ai Ka zama tsagera"

Rintse ido Mami tai ita ba abin tai magana ba sbd tana gaban Baffa Amma ta rasa mai ta tsare wa Haj Hafsat da sam bata sonta duk wani abu da zata nuna cewa ta gaza gurin bawa yayanta tarbiyya Shi take fada duk da kuwa Allah ne shaidan ta tana iya kokarin ta akan tarbiyyar yaranta Maza guda biyu da ALLAH ya bata, ko Azlan duk abinda yake tana godewa Allah da baya shaye shaye baya wani abin assha club din da yake zuwa ne kawai da yanayin dressing dinsa, neman Mata ma tana masa kyakkyawan zato cewa bayayi don Azlan baya karya.....

Muryar Mummy ce ta katse Mata tunanin da take tana fadin "iskancin banxa da wofi budurcin yaci ubansa waye baisan cewa kana zuwa club ba in kaje club din salati kake yi ina mata ne a gurin kamar tsirara suna yawo"

Kankance ido Azlan yai yace "in na fahimci zancen ki Hajia Mummy kina tantama akan budurci na dana kewa Iyalina tanadi, dage kafadar sa yai yace fyn bara na bude Miki ki duba kiga yana nan ko baya nn"

Belt din wandon sa ya cire ya shiga kiciniyar zuge zip din wandon sa, salati mutanen palourn suka dauka, cikin daga murya Baffa yace "Zaki meye hakan me kake kokarin yi"

Cikin rashin damuwa yace"zan bude ne ta duba taga ko budurcin nanan ko baya nn" ya karashe yana Zara zipping wandon sa......


***********

Ina masifa har na isa gida da Mimi na fara cin karo tana wasa da yar tsana a gurin famfo wai wanka take Mata, zuba mata ido nai ina kallon tsantsar kamannin ta da Mutumin daya kusa bige ni dazu.

Cikin rashin kwarin jiki na isa gurin ta "nace me kike yi ne Mimi"

Dagowa tai ta zuba min idonta da suka sani Jin cikina ya karta tace "Maa ina yiwa babyna wanka tayi datti"

Murmushi kawai nai mata na mike na shiga palour, ajiye takaddun nai a dakin mu na fito Palour daidai fitowar Umma daga dakin su, Zama nai ina bata labarin yadda muka yi photo copy din takaddun mu.

Cikin nutsuwa Umma tace "lafia kike kuwa Batul mene yake damun ki"

Gaba nane ya yanke ya fadi cikin damuwa na shiga tunanin shin na fadawa Umma mutumin da na hadu dashi yau ko kuma kar na fada mata.......


Comments Nd share plz


Mrs A.M🥰

[12/08, 21:24] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️

*TASWIRAR KADDARA*

♠️♠️♠️♠️♠️


Written by
Mrs A.M🥰

Page 9

Gaskia Azlan Ka fita idon Innar Nawaz don ta kawo min karar Ka cewa Ka na Mata signal kuma Ka kusa tara mata jama'a yau a titi sbd fitsarar ka🤣🤣

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Dan yatsina fuska nai nace "Umma wani ne ya kusa markade min kafafuna fah, kuma wai sbd mugunta ni ban masa rashin kunya ba amma ya nemi ya zage ni"

Kura min ido Umma tai cikin rashin yadda da abinda na fada mata tace "anya Batul meya hada ku toh"

Turo baki nai nace "Umma kawai fa daga nace masa ya kula sbd gaba in ni ya kusa kade ni banyi magana ba wasu in ya musu sai sun zage sa shiknn ya fara zagina"

Girgiza kai Umma tai tace "da ban sanki badai Batul amma na tabbata kin masa rashin kunya ne ko kuma kin fada masa maganar da ba haka ba wallahi ina hanaki wannan tsiwar taki amma bakya ji"

Langwabe kai nai nace "ynxu Umma da an kawo miki ni ranga ranga fah ya take min kafa fah"

Tsaki Umma tai tana juyawa cikin kufula tace "Allah ya nuna min ranar da zakiyi hankali"

Sakin baki nai ina kallon Umma, sai kuma na mike na fita kitchen don dora abincin dare.


**********

Junaid ne ya mike da sauri yazo ya janyo Azlan yace "lafiar ka qalau kuwa Azlan me kake shirin yi taya zaka cire wando don Allah"

Kasa kasa da murya Azlan yai ta yadda Junaid ne kadai zai jisa yace "kai mai Ka maida ni ne ina da hankali fah taya zan cire wando na barazana ce kawai ai ko aure nai kafin na cire wandon nan sai an hada da nasiha"

Ajiyar zuciya Junaid yai don shifa lamarin Azlan tsoro yake basa mutum kamar aljani don da ya fara tunanin ma ko aljanu ne da Azlan din sai daga baya ya fahimci cewa kawai tsabar tsageran cine.

Dan daure fuska Azlan yai yace "Ka barni Junaidu na cire mata wandon na nuna mata budurcina da nake tana dawa iyalina" ya karashe yana kamo hantsar wandon sa yana wani zunkuda kafada.

Abie ne ya mike yace "in baka daina wannan shirmen ba sai na Saba ma wallahi mara kunyar banxa da wofi"

Murmushi ya saki yana maida zip dinsa, juyawa yai ya kalli Baffa yace "tsoho zan iya fecewa"

Baffa da tunda yai magana sau daya ya zubawa sarautar ALLAH ido yana mamakin shakiyancin jikan nashi ya daga masa kai kawai yana binsa da addu'ar shiriya.

Cikin takunsa ya karaso kusa da Mami ya tsugunna yai mata kiss a kumatu yace "sai anjima MAA" daga haka ya juya ya fice daga palourn.

Mummy ce ta kalli Baffa cikin rawar murya tace "ynxu baffa kana kallon yaron nan abinda yai min amma baxa ka masa fada ba"

Murmushi baffa yai yace "Hafsatu knn ai dama koda kika zo da maganar wannan hadin a take a gurin nace Miki ba lallai ne wannan abun yai ba sbd sanin halin sa danai amma kika dage akan a tuntunbe sa aji gashi ynxu ai ya fada bashi da ra'ayi kuma gaskia ni baxan masa dole ba tunda ya fadi dalilin sa"

Abie ne yace "Amma Baffa ai mune muke gaba dashi kuma duk abinsa haihuwar sa akai shekarar sa 33 amma har ynxu yaki hankali ni a yadda nake ganin take taken Sama ba aure sam a gaban sa"

Dan hade rai Baffa yai ya kalli Uncle M da yai shiru yana kallon su yace "Mustapha rufe mana taron da addua"


*********

Washe gari muka je muka karbi Admission dinmu inda zan karanta architecture shi kuma cilla zai karanta library science, sosai muke murna don mun fara jin kamshin Zama cikakkun yan University.

Da daddare muna zaune ina bawa Abba labarin yadda Makaranta take Mimi na kwance akan cinyata tana bacci.

Murmushi nai nace Abba nan da wata daya fah zamu fara zuwa koh wallahi na matsu sosai.

Murmushi Abba yai yace Allah yasa ku fara a sa'a Batul ki maida hankali sosai ba ruwanki da biye wa kawayen banxa dama nasan Alhamdulillah ke ba mai biye biye bace, amma ina Kara tuna Miki bake ba lecturers tsakanin ki dasu karatu ban yadda kina zuwa office din lecturer ba ke kadai ko kiranki yai kuje keda wasu ki kama mutuncin ki Batul, kuma kiji tsoron Allah a duk inda kike sannan ki maida hankali akan karatu don Allah duk da baki da Wasa amma still ina kara tuna Miki wannan karatun da irin Wanda kika saba bane sai kin dage sosai Allah ya bada sa'a.

Kaina a kasa na amsa da "Ameen" sai kuma naji jikina yai sanyi. Kallon Umma Abba yai yace "Umma baki ce komai ba"

Dan murmushi Umma tai tace "ai Ka gama fadin komai Abba sai dai kawai Nima nace ki kula sosai ki rike mutumcin ki Banda kawayen banxa sannan ki dage da karatu jami'a ba wajen wasan yara bane"

Daga Kai nai na kalli Abba nace "Abba ni kun fara tsorata ni in kuna cewa na dage da karatu Allah"

Dariya Aisha tai tace "ai tunda kika tsoro ta mu kuma fah Ya Batul ai sumu inaga tun ranar da muka samu admission zamu fara zawo har ranar da zamu fara lecture"

Hararar ta nai kawai na juya gurin Abba daya miko min kudi, kallon sanai ganin haka yasa shi fadin "ungo 15k ne kiyi siyayyar hijabai da takalmi sai jakar makarantar da zaki yi amfani dasu".

Cikin farin ciki na karbi kudin nace "angode sosai Abba Allah ya kara arziki ya Kara lafia da nisan kwana mai albarka ai kuwa gobe Insha Allah zanje kasuwa na siyo yadikan hijabai guda da kuma material ko Umma sai na siyo jaka a gwanjo mai kwari wacce zata dinga dauke min komai guda biyu"

Khalil ne yace "Ya Batul zan raka ki don Allah"

Da sauri kamal yace "ni zan raka ta ai ba Kai ba"

Tabe baki nai nace "ba wanda zanje da shi ni kadai zanje na dawo"

Kallon Umma nai nace "Umma wannan kudin da nake ajiye wa a gurin ki don Allah in zan samu sai na hada dasu goben na siyo material da dan yawa Wanda zan na Sawa dama nai WA Aunty zainab magana Zan dinka abina da kaina"

Gyada kai Umma tai tace "mai zai hana ki samu kuwa suna nan na ajiye miki dama ai su munyi dake zaki siyo material ne goben in Allah ya kaimu sai na baki"

Murmushi nai cikin Jin dadi na mika mata kudin da Abba yaban nace "Toh gashi Umma ki ajiye min wannan ma"

Mikewa nai na dauki Mimi na kwantar da ita, Nima kwanciya nai don gobe da wuri nake son zuwa kasuwar, lumshe idona nai saidai kuma duk yadda naso baccin ya dauke ni ya kasa zuwa sbd fuskar wannan mutumin kawai kemin yawo, a hankali na bude idona na zuba akan fuskar Mimi gani nake kamar Mutumin ne kwance a gefena.

Mikewa nai na zauna ina kallon Aisha dake shirya littafan ta acikin jaka nace "Aisha kinsan me"

Dan juyo wa tai tace "A'a Ya Batul"

Ajiyar zuciya na sauke nace "wani abin mamaki na gani wallahi jiya nida Cilla bayan mun fito daga cafe wani ya kusan take min kafa, kin san Mutumin yana kama da Mimi sosai kamar yayi kaki ya tofar har yadda yake magana da yadda yake bata fuska duk irin na Mimi ne"

Xaro ido Aisha tai tace "kuma kin fadawa Umma Ya Batul"

Girgiza kai nai nace "ban fada mata ba bana son na kama Mata ciwon da take kokarin rufe wa ne"

Zama tai a gefena tace "Ya Batul kina tunanin xai iya xama baban Mimi"

Da sauri na yatsina fuska nace "Allah ya kiyaye insha Allah ma ba shi bane babanta, toh meye ma ya dame ni da sanin ko waye baban nata, bana ma fatan sanin sa don duk ranar da muka hadu nida shi Allah ne kawai zai kwace sa a hannuna"

Tagumi Aisha tai tana kallo na ganin yadda nake faman tsinewa baban Mimi Wanda ko kalar fatar jikin sa ban sani ba.

Haka nai bacci sbd sa abin a raina har mafarki nai wai mutumin dana hadu dashi yazo yace na basa Mimi yar sa CE, ai kuwa haka na tashi raina duk a bace, da kyar naje kasuwar na siyo duk abinda zan bukata na tahowa da Mimi dogayen rigunan Yan gwanjo guda uku na siyo mata sabon takalmi.


Kwanci tashi har mun fara shiga university muna bude file nida Cilla muke tafiya komai tare muke yi kafata kafarsa har muka gama, gobe Insha Allah dukkan mu zamu fara lecture gaba daya cikin zumudi muke koda aka ban time table sai da naje nai photo copy daya ba barsa a cikin jakata daya kuma na sa salatif na manna a jikin bangon dakin mu.

Yau sbd zumudi da wuri nai bacci bayan na shirya kayana dazan sa goben in Allah ya kaimu..


*********

A hankali yake gyada kansa kamar salihi yana Jin abinda Abie yake cemasa.

Girgiza kai Abie yai yace "don Allah Azlan Ka dinga zuwa duk ranar da kake da lecture kar kasa shiririta kuma Ka dinga suturta jikin Ka kaji"

Daga Kai yai yana lumshe idon sa sam wannan lecturing din da zai fara kawai don ba yadda zai yi ne amma ayyukan office kadai ma aka barsa dasu na sun ishe Shi ga kuma wannan nauyin an Kara dora masa.

Shiru yai yana jin Abie da Mami suna masa nasiha Shi dariya ma suke basa yadda suke wani lallabasa akan lecturing din toh sun san halin sa a goben da yake da class zau iya kin zuwa ya kwanta yai baccin sa hankalin sa kwance.

Sai da suka gama masa nasihar sannan ya mike ya fita bayan yai musu sai da safe


Comments Nd share plz


Mrs A.M🥰
[13/08, 15:50] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️

*TASWIRAR KADDARA*

♠️♠️♠️♠️♠️


Written by
Mrs A.M🥰

Page 10

Dedicated to ♠️TASWIRAR KADDARA♠️ Group ina jin dadin comments dinku sosai Allah ya bar zumunci🥰

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Washe gari karfe 7 a BUK tai min kasancewar muna da class karfe 8, hall din da zamuyi lecture din na shiga na samu front sit na zauna, ajiyar zuciya na sauke ina gyara zaman sabon hijab dina.

Ban dade da zama ba hall din ya fara cika, kusan kowa a gaba yake zama karfe 8 dai dai lecturern da zai mana maths ya shigo, sai da ya fara da introduction kafin ya fara mana revision akan maths din da muka bari a secondary school, sosai na maida hankali kansa ina saurara wasu abubuwan kuma ina jotting a book dina dana ware don haka.

Sai karfe 9 ya fita amma lecturern da zai mana physics bai shigo ba hakan yasa kowa ya fara sha'anin gaban sa tunda dama physics din muke da 9-10 daka nan kuma muna da interval har sai 1:30.

Maths din da aka mana na maida hankali sosai ina dubawa har lokaci yaja sosai, sai da na gaji na ciro wayata na shiga WhatsApp ina duba status, ina zaune wata tazo ta miko min wayarta tace in sa mata number na za'a bude group ne na yan course din ta yadda za'a na fadan duk abinda ya shafi course din, ban musa Mata ba na sama ta number din.

Sai karfe 1 na mike na fita don zuwa masallaci nai sallah, ban wani sha wahalar neman masallacin ba sbd lokacin da muka zo bude file anan nake sallah, ban dade ba na koma sbd class din da muke da shi tym din, a sit din dana zauna anan na zauna ina Zama lecturern na shigowa, sai karfe 3 muka fito.

A gajiye na fito cikina in banda karar yunwa ba abinda yake yi, cikin gajiya na daga wayata na Kira cilla don shi ma kusan tare muka fito, ina tsaye ya karaso shima dai kallo daya zaka masa kaga gajiya tattare da shi.

Kallona yai cikin kulawa yace "uwar dakina wallahi na gaji ga yunwa dake ta kwakwula ta"

Ajiyar zuciya na sauke nace "Cilla nima nan a gajiyen nake ai baxan sake wannan kuskuren na kin cin abinci ba Allah kuma sai na dinga tahowa da cake da doughnut da zobo muna ci muna rage zafi in bamu koshi ba muje cafeteria muci abinci ko mu siya waina ko gurasa"

Murmushi yai yace "toh hakan dabara ce sosai don baxan iya wannan horon yunwar ba nifa SBD yunwa wannan lecturen ta karshe da mukai ba abinda na fuskanta"

Dan dariya nai nace "Allah ya shirye ka cilla wallahi ynxu kace ba abinda Ka kwashe kawai Zama kai kana kallon malamin"

Gyada kai yai yace "rass ma kuwa Uwar dakina ai kinsan irin wannan yunwar daina gani ma take sa mutun yi"

Haka muka cigaba da hira har muka fita school din Shi ya tarar mana adaidaita muka hau, ni aka fara sauke wa shi kuma za'a karasa dashi kofar gidan su.

Cikin gajiya nai sallama na shiga gida, da Umma na fara cin karo tana tankade garin dan wake tana gani na ta saki dariya tace "kaga Yan jami'a ya naganki haka kamar wacce aka koro"

Turo baki nai nace "Umma ina wuni"

Dariya tai tace "lafia qalau ya makarantar"

Zama nai akan tabarma nace "Hmmn Alhamdulillah Umma duk abinda aka mana yau na gane sai dai yunwar dake cinye min yan Hanji"

Da mamaki tace "ba Abba ya baki kudI ki sayi abinci ba in kinji yunwa"

Mike wa nai nace "Hmm Umma tsautsayi yasa nai tunanin baxan ji yunwa ba ai kuwa na azabtu ai daga yau da cake zan na zuwa Allah"

Kitchen na shiga na zubo abinci na zauna ina bawa Umma labarin yadda yau ta kasance a school, sai da na koshi naji dai dai sannan naje nai wanka, ina fitowa sallar la'asar nai na mike kafafuna na kalli Umma dake kan sallaya tana jan carbi nace "Umma kuma wai a haka fa don karfe 3 na dawo yau gashi gobe har 6 zan Kai tab ashe haka ake Shan wahala"

Tabe baki Umma tai tace "tukunna ma yarinya"

Daren ranar gaba daya nayi Shi ne ina bawa su Abba dasu Aisha labarin makarantar da yadda take.

Cikin satin sosai na maida hankali na akan karatu duk da bawai an shiga cikin karatun bane introduction kawai ake mana amma na nutsu kullum in ina school in har bamu da class zama nake nayi karatu na in kuma cilla shima bashi da class muje mu zauna a cafeteria muci cake dinmu kowa ya duba littafi ko kuma muyi hira, sosai Amincin mu da cillah ya Kara daduwa sbd tare muke zuwa mu dawo sai dai in zan rigasa shiga lecture ne shine kawai nake rigasa tafiya.

Ban Kula kowa a course mate dina tsakanina dasu gaisuwa ce shiknn sai dai kuma ina maida hankali ina karantar su wasu tunda ga satin farkon zaka gane sun shigo show off ne kawai duba da yanayin shigar su.

A cikin satin farko lecturer da zai dinga mana physics shi kadai ne bai shigo mana ba, muna da physics har biyu a sati amma bai shigo ba sai dai an fada a group din da aka bude cewa uzuri ne ya hanasa zuwa amma sai shigo wani satin insha Allah.

Ranar Monday kamar yadda muke da lecture tun karfe 8 da wuri na shigo school kuma na samu front sit bakin window na zauna, har malamin da zai mana maths ya shigo ya fita, yana fita Wanda zai mana physics ya shigo.

Jin class din yai shiru kamar anyi ruwa an dauke yasa ni dagowa don ganin dalilin dayasa class din Shiru haka, tun daga kafar sa na soma kalla gabana yana bugawa da karfi yana sanye da takalmi boots black colour sai wandon jeans fari kar sai Riga daya sa black wacce ta dan kamasa kansa sanye yake da p-cap, a hankali idona ya fada cikin nasa daya sha kwalli sosai sai sheki yake, kallo daya yamin kusan a tare muka janye idanun mu.

Cikin faduwar gaba nake tunanin badai shine malamin namu ba tab, jinai cikina yayi kugi da yasani saurin dafe cikin ina tuna rashin kunyar danai masa.

Azlan kuwa kallo daya yai mata ya janye kansa a ransa yace lallai wato shiyasa tai masa fitsara ashe tashen balaga take yi ita zata shiga jami'a, kankance idonsa yai bayan yadan lashi jajayen lips dinsa ya fara bayani cikin harshen turanci.

Yadda ya hade rai yana bayanin yasa ni maida hankali sosai ina jotting duk wani Abu mai muhimmanci don jikina naban yadda nai masa rashin kunyar nan tsaf zai iya bani carry over.

Hour daya ya dauka ya fita bayan ya dauki attendance kuma bai fita ba Saida ya bamu assignment yace ayi submitting gobe karfe 8 in ya wuce 8 baxai karba ba, yana fita aka fara magana akansa matan ajin sai zuzuta kyan sa suke suna fadin shine sabon lecturer da ake maganar sa Ashe.

Nidai tagumi nai na zubawa assignment din ido, ganin hakan baxai fishshe niba yasa na fara solving assignment dina tunda yace gobe karfe 8 yake so ayi submitting nasan class rep za'a bawa, saukin tama goben muna da class karfe 8.

Sai da na gama assignment din na kara dubawa na tabbatar nayi daidai sannan na mike na fita don zuwa cin abinci, a inda muka Saba haduwa da cilla na gansa yana zaune yana cin meat pie da lemo, yana gani na yace "uwar dakina tun dazu nake zuba ido ai naga baki fito ba ina shirin in na gama ci naje na duba ko lafia sai gaki lafia kuwa?"

Zama nai na sauke ajiyar zuciya nace "Hmm cilla ina ruwa kusa da Kada wallahi"

Da mamaki yace "lafia wani abun ya faru ne"

Sosa gira ta nai nace "ai komai ma ya faru cilla ina wannan mutumin mai kama da Mimi Wanda ya kusa kade min kafa na masa rashin kunya"

Gyada kai cilla yai yace "ai baxan manta Saba uwar dakina kodan yadda yake kama da shashalelen ki"

Sai da nayi murmushi kafin na girgiza kai nace "shine lecturer dinmu na physics wallahi ni nasan da kyar in baxai ban carry over ba ya rama abinda nai masa"

Zaro ido cilla yai yace "kice min wannan maganar ba haka bane uwar dakina"

Dan cizar lip dina na kasa nai nace "Hmm cilla ina ruwa gashi daga gani bashi da kirki har ya bada assignment fah kuma wai ayi submitting gobe in ya wuce 8 baxai karba ba ai assignment din na tsaya nai shiyasa ban fito da wuri ba".

Tagumi cilla yai yana ajiye meat pie dinsa a gefe yace "da damuwa uwar dakina Allah yasa dai bai gane kiba"

Girgiza kai nai nace "ya gane ni don Saida muka hada ido da shi sannan ya janye idon sa ni bansan ya zanba har wani zazzabi ma nake ji"

Nan mukai zugun zugun nida Cilla har lokacin sallah yai duk sona da abinci kasa cin komai nai, sallah naje nai na koma hall din da xamuyi next lecturen mu, ana tashi mun fito nida cilla muna tafiya kamar ance na daga idona suka sauka akan sa Yana tsaye tare da wani suna magana shima dago idonsa yai ya zuba a fuska ta kuma yaki dauke wa ganin haka yasa ni balla masa harara na murguda masa baki, sai kuma na zare idona ina dafe bakin, ganin ya ware min manyan idon sa irin ni dinnan, da sauri na juya na kalli cilla Naga hankalin sa Yana gurin nema mana abin hawa, sai nai Shiru kawai gabana yana faduwa

Shi kuwa Azlan da mamaki yabi bayanta da kallo, gyada kai yai yace "uhm lallai"


Ranar haka na wuni a gida suku suku, Umma ta tambaye ni har ta gaji daga karshe sai ce Mata nai malamin physics din da nace mata bai shigo bane ya shigo kuma har ya bamu assignment yace muyi submitting gobe ai ko Karen hauka ne ya cije ni baxan ce Mata wanda ya kusa bige ni bane sabon lecturer dinmu karshe sai dai tace Allah ya kara maganin mai tsiwa.

Washe gari da wuri na fita sai dai na kasa samun abin hawa da wuri sai wajen 7:45 na samu adaidaita kamar zanyi fitsari a wando haka nake ji, ban shiga school ba sai 8:15 cikin sanyin jiki na nufi hall din da za muke da lecture tuni lecturer ya shiga amma ganin baya hana wadanda suka zo a makare yasa na shiga cikin sanyin jiki, yau a baya na zauna don ba waje a gaba.

Sai 9 ya fita yana fita na mike na nufi gurin class rep din mu, cikin damuwa nace "Hamza har anyi submitting assignment din jiya koh"

Daga mun kai yai yace "nima nayi mamaki dana ga baki zo da wuri ba ya akai haka"

Kamar zanyi kuka nace "wallahi abin hawa na rasa shiyasa, ynxu don Allah ba yadda za'a yi Ka kaimin nawa tun jiya na gama wallahi"

Zare ido yai yace "wa ai saidai kije ki Kai masa ko zai karba don nikam ba ruwana, da na kai masa saida yace na Kara fada in 8 ya wuce duk Wanda yakai masa baxai karba ba"

Shiru nai cikin damuwa nidai banason nayi missing wannan assignment din don yace zai iya Zama first test dinmu, ajiyar zuciya na sauke nace "toh don Allah ina ne office din nasa"

Kwatance yai min na fita don bamu da lecture sai 11, sai da na fara biyawa na taho da cilla Wanda bai shigo ba sai 9 tunda 11 yake da lecture, tare muka nufi office din nasa gaba na Yana faduwa.

A kofar office din muka tsaya na daga kai na kalli inda aka rubuta sunansa *AZLAN MUHAMMAD ABDULLAH* knocking nai sau daya Jin shiru yasa na Kara wani, ciki ciki naji ance come in.

A hankali na tura kofar muka shigo nida Cilla, sai da na sauke ajiyar zuciya jin office din yana wani sassanyan kamshi ga sanyin AC dake tashi, dago kaina da zan suka fada cikin nasa yana zaune akan doguwar kujera ya mike kafafun sa yana sanye da kananun kaya kafarsa ba takalmi sai sheki take.

Zuba min ido yai shima tun daga Sama ya kalle ta tana sanye da hijab brown colour dogo har kasa, sai jakarta data rataya shidai kullum da hijab yake ganin ta, maida dubansa kan cilla yai dake bayanta kansa a kasa yana mamakin meye alakar ta da wannan namijin da kullum zaka gansu tare suna tafiya kuma da dukkan alamu ba gida daya suke ba.

Maida duban sa kanta yai hakan yasa ni bude baki a hankali nace GOOD MORNING SIR.............


Comments Nd share plz


Mrs A.M🥰

[15/08, 15:42] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️

*TASWIRAR KADDARA*

♠️♠️♠️♠️♠️


Written by
Mrs A.M🥰

Page 11

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Maida dubansa kanta yai haka yasa ni bude baki a hankali nace "Good Morning Sir"

Tabe karamin bakin sa yai ya zuba mata ido yana mamakin rashin kunyar yarinyar Ashe ma level 1 take lallai bata gama balaga ba.

Dan dago idona nai caraf idonmu suka hadu, yamutsa fuska yai cikin husky voice dinsa yace "me ya kawo ki office dina"

Cikin dauriya nace "sir assignment din da Ka bamu jiya ne, tun jiyan na gama sir yau ban samu abin hawa da wuri ba kuma da nazo already lecturer ya shiga sir"

Dage gira daya yai yace "so"

Hadiye wani yawu nai nace "shine shine nazoo nayi submitting sir"

Kallon Cilla yai cikin hade rai yace "kai mai kazo yi kuma"

Da sauri cilla ya dan zaro ido sannan yace sir "rakota nai"

Sai da ya dan saci kallon ta sannan ya maida dubansa kan cilla yace "fyn zaka iya fita tunda ba abinda ya kawo Ka"

Da sauri na kalli cilla daya juya zai fita cikin saurin magana nace "Sir Abba ya hana fa yace kar na dinga zuwa office dn lecturer ni kadai"

Kankance ido Azlan yai yana bin ta da wani mugun kallo cikin zuciyar sa yace lallai yarinyar nan bata da man kai ni Azlan take fadawa haka, bata san yadda nake tattalin budurwarcina ba ai ni ya kamata naji tsoron kebewa da ita ko dan yadda ake kawowa budurcina Hari ta kowanne bangare.

Tabe baki yai cikin husky voice yace "ki koma class ki bawa class rep dinku, duk Wanda bai submitting ba yayi kafin 1 yazo ya min submitting and ki fada masa this should be the last da zan bada assignment Ince Amin submitting aki yi akan tym", daga haka ya maida kansa jikin kujerar ya lumshe idonsa.

Sai da na maka masa harara sannan nace "thank you sir"

Muna fitowa daga office din nida Cilla a tare muka saki ajiyar zuciya sai kuma muka sa dariya, muna tafiya muna gulmar sa har muka isa hall din.

Assignment din na bawa class rep din sannan nai masa bayanin abinda ya fada min muka juya nida Cilla don yunwa nake ji ko breakfast ban yiba.

Cikin lokaci kankani karatu ya fara daukar zafi sam bana wasa don sosai abubuwa sun dau zafi har Dan ramewa nai, har lokacin banyi wata kawa ba don bana son shiririta, duk inda zani tare muke zuwa nida cilla kuma shine yake rakani.

Yau ma kamar ko yaushe na nutsu fiye da yadda bake nake nutsuwa sbd physics din da muke da shi ynxu Wanda Mr Wicked yake mana kamar yadda nasa masa suna, ina cikin duba joter dina sbd yace yau zai mana test shiyasa duk a rikice nake don malamin mugu ne baya mana Wasa ko kadan, sallama naji a kaina hakan yasa na dan dago don ganin wace, murmushi nai ganin Asma'u Hamza course mate dita ce kuma mun dan fi shiri a cikin class din don itama da dukkan alamu karatu ne ya kawota ba shirme ba.

Zama tai a gefena tace sannu "Batul sarkin karatu"

Dan dariya nai nace "sannu Malama Asma'u kinga laifina ynxu karatun ya dau zafi sai kana yi kullum kana dubawa in ba haka ba kazo karatun exam kanka yai bombing"

Dariya tai tace "kuma hake ne, ke ba ruwan ki baki shiga cikin mutane"

Dan murmushi nai nace "toh in shiga in batawa kaina lokaci, tym din da bamu da lecture nafi gane wa in zanci abinci naci, in kuma bana Jin yunwa na duba papers dina in na koma gida ba lallai na duba ba sbd gajiya"

Murmushi tai tace "haka ne shiyasa Nima nace bara dai na dawo gurinki na dinga Zama naga serious student ce keh in ba damuwa"

Dan murmushi nai nace "laa ba komai Allah mu dinga zaman tare nima wani tym dn zama haka yana damuna"

Zatai magana knn Mr Wicked ya shigo hakan yasa ta yin Shiru, Nima bakina naja nai Shiru duk muka nutsu muka zuba masa ido......


************

Cikin shesshekar kuka tace "ynxu Mummy me na rasa da Ya Azlan zai bude baki yace baya sona, ina da kyau na Mummy kuma yadda Maza suke bibiyata shi Mai yasa baya min haka"

Kwafa Mummy tai tace "goge hawayen ki Zainab in ina raye sai kin auri Azlan, shegen yaro ya kalli tsabar idona yace baya son ki ni bansan dalilin Baffa na goya masa baya ba wallahi"

Hawayen zainab ta goge cikin shagwaba tace 'Mummy ai kema kinsan Baffa yafi sonsa akan kowa nidai ki taimake ni Mummy ki shawo kan Baffan ya amince In ban aure Saba mutuwa zan yi Allah"

Da sauri Mummy ta rufe Mata baki tace kiyi min shiru kedai kawai ki hada kayan ki kamar yadda na tsara Miki, kije gidan Ya Muhammad din ai gidan babanki ne, kuma in kinje bangaren Hajia Maryam zaki sauka, ina Kara fada Miki kiyi duk abinda zakiyi don jawo hankalin sa gare ki sannan ki daina sa bra guda 1 ki dinga sa biyu kuma masu push sosai badai kwaila yake ce Miki ba in kika koma sa biyu ai sai ya dawo miki kallon mai abubuwan arziki, sannan kije kasuwa ki siyo abin cikin duwawu haka ni dai Wallahi bani kuka gado ba da ace ni kika gada AI karyar Azlan ya kiraki da kwaila.

Dafe kumatu Zainab tai tace "Mummy ai yasan bani da boobs din in nayi ciko baxai gane ba kuwa"

Tsaki Mummy tai tace "ke dallah rabu da shi bai wani san yadda kike ba kawai yafada ne shi Azlan din har wani ganin ki yake da zai San yadda kike, kedai kiyi abinda nace sannan in kinga Yana guri kidinga dan karairaya kina turo kirji"

Dariya suka saki suka tafa kamar kawaye Saida Mummy ta gama fada mata duk yadda zatai sannan ta mike ta bar dakin tana jaddada Mata tai hanzarin shiryawa don yau take son ta tafi gidan Abie.

Bin bayan Mummy da kallo tai sannan ta mike ta nufi gaban Mirror tana karewa kanta kallo, tana da kyau sosai don fara ce tass kuma kasancewar ta yar gayu Mai gyara fatar ta da lura da ita yasa skin din nata Kara wani haske, sai dai kawa katon bakin dayai ma fuskar ta cikas, don tubarkalla tana da babban baki amma ba'a cika ganewa ba sbd yadda take kullum cikin makeup hakan yake taimakawa gurin boye girman bakin nata.

Kallon kirjin ta tai da yake kamar lemon tsami don bata da kirji sosai kamar wacce ta fara kirgan dangi sai duwawun ta da yake shafe, a takaice dai bata da body structure a tsaye take number 1, ajiyar zuciya tai tana tunanin yadda zata dinga ciko tana masa karairaya, wani tsallen dadi tai tana jin kamar ta aure ta gama ne donfa ita tayi alkawarin auren Azlan ko ana ha Maza ha Mata........


*********

Cikin aji ta waina manyan idonta ta kalli kawayen ta tace "Nana kinsan Allah gayen ya mugun tafiya dani, tun ranar dana fara ganin sa na kamu da mugun sonsa" sai ta sauke ajiyar zuciya tana dafe saitin zuciyar ta tace "kinsan ya hadu ne koh"

Murmushi Nana tai tace "Ai ni Zuby mamaki kike bani ashe zaki fada soyayya ta gaskia"

Hararar nana tai tace"gashi kuwa ni har na fadawa Dad na samu mijin aure"

Zaro ido Hafsa tai da tunda suka fara maganar bata ce komai ba tace "Zuby are u serious? Mutumin nan fa ko sanin zaman ki baiba amma har kin fadawa dad kin samu miji"

Dan bata fuska tai tace kina tunanin baxai soni ba kome, mikewa tsaye tai tana dan gyara budaddaiyar abayar jikinta Wanda ya fallasa Riga da wandon dake jikin ta da suka kamata sai mayafi data yafa a kanta, juya jikin ta tai tace "meye baiji ba anan"

Bin ta da kallo sukai tana da diri dai dai gwargwado kuma tana da boobs madaidaita sannan tana da kyaun fuska don fara ce duk da dai farin hadda na bleaching, gyada kai Hafsa tai tace "komai yaji kawata"

Wani Murmushi tai tace "toh kunga ai kawai nasan zaima fada tarkon Sona don wallahi sai na aure sa haba wannan daga gani ba karamin haukata mace zaiyi a bed ba" ta wani lumshe ido tana lasar Baki

Wani ihu suka saki har saida mutanen dake gefen su suka juyo suka kalle su, dariya Nana tai tace "Zuby me ya kamata mu farayi ynxu toh da zai sa yasan da zaman ki"

Hafsa ce tai caraf tace "abu Mai sauki ai gurin sa zaki je kina karairaya kice kinzo ya koya miki abin da yai mana dazu baki gane ba AI kin gane
koh"

Tafawa sukai suna shewa inda ta mike tana kara fesa turare a jikin ta ta nufi Office din Mr Azlan Muhammad Abdullah.

*Wacece Zuby*

Ya daya tilo ce a gurin Alh Ahmad Muktar da kuma Hajia Badiyya, ita kadai Allah ya basu haka yasa suke nuna mata soyayya mai tsanani dukkan abinda take so Shi take yi hakan yasa ta taso sangartacciya ta riga ta saba duk abinda take so Shi zatayi ba Wanda zai kwabe ta, tana da girman kai sosai ynxu haka tana level 3 a BUK inda take karantar Architecture.

Tun suna level 1 suke tare da Nana da kuma Hafsat haka yasa suka zama aminai sosai, ba laifi tana da kokari kodan kasancewar ta mara son raini a gurin course mate dinta hakan ke sata dagewa tayi karatu don kar ta samu carry over...

Tana da tarin samari sosai wadanda kawai cin kudin su take sai kuma irin wadanda ake soyayyar shan minti ayi romance amma ba'a zarcewa.


******

Yana zaune yana shan drink aka yi knocking kofar sai da yai kamar baxai amsa ba sai kuma yace "yess come in"

A hankali ta turo kofar ta shigo tana yin sallama, a kasan baki ya amsa mata kallo daya yai mata ya kauda kansa sbd yadda jikinta yake bayyana.

Karasowa tai ta tsaya daga dan nesa da shi cikin kissa tace "Good Afternoon sir"

Gyada kai kawai yai yana cigaba da duban system dinsa, cikin kwarewa da iya seducing namiji ta dan janye mayafin ta saman kirjin ta da ya taso yadan bayyana, sai da ta daidaita kanta sannan ta matso kusa da table dinsa ta sunkuyo yadda kirjin ta zai bayyana tace "Sir dama abinda Ka mana dazu ne ban gane ba shine nazo ka min bayani plz in ba damuwa"

Dagowa yai zai Mata magana caraf idonsa suka fada kan kirjin ta da suka dan bayyana ta sama...........


****
Da Mamaki na kalli Asma'u nace "da gaske wai Matar aure ce keh"

Dariya tai tace "wallahi Amma auren wata 2 knn"

Ajiyar zuciya nai nace "tab amma baku more amarcin ku ba"

Dan bude ido tai sai kuma tai dariya tace "Ashe kina magana haka nifa da kallon da nake miki san baki magana"

Murmushi nai nace "ina yi mana saidai bada kowa nake na gaskia"

Murmushin tai itama tace "kinga Baby yana kira nasan yazo dauka ta ko zaki zo muje ku gaisa daga nan sai mu rage Miki hanya"

Hararar ta nai nace "wallahi ki shiga hankalin ki kawai baki san halina ba kina cewa nazo muje mu gaisa da mijin ki tab, lallai da sauran ki ai kuwa in haka kike ki chanja don ynxu yaudara tayi yawa a duniya"

Murmushi tai tace "duk da bansan halin kiba Batul amma na yadda dake ai shiyasa nace Miki kizo ku gaisa din amma Nima ina kiyaye wa fah"

Gyada kai nai nace "better dai"

Dariya tai tace "tab kice haka kike da kishi wannan za'a sha kallo"

Nidai ban mata magana ba sai hannu dana daga mata kawai, murmushi nai don naji dadin yau din sosai ko dan sbd hirar da mukai da Asma'u ne, Nima fta nai na samu abin hawa don Cilla bai zo na yau...


Toh fans ga Zainab nan fah ta danno da karfin ta zata gidan Abie farauto zuciyar Azlan🤞 koya zata kasance zatayi nasara ko kuwa🤔


Ga kuma zuby fa itama tace bata yadda ba sai ta aure sa Don ita ta gama fadawa Dad dinta ma ta samu miji aure kawai za'a daura🏌️‍♀️🏌️‍♀️🏌️‍♀️


Ku kawo dauki za'a yiwa Oga Azlan fyaddd*****


Comments Nd share plz


Mrs A.M🥰
[16/08, 20:08] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️

*TASWIRAR KADDARA*

♠️♠️♠️♠️♠️


Written by
Mrs A.M🥰

Page 12

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Dagowa yai ya kalli fuskar ta yaga ta wani zuba masa ido tana masa wani kallo, hade rai yai ya mike tsaye ya dafa table din yace "karatu kika zo ko kuma tallan jikin ki kika zo min"

Da sauri ta dago ta kalle sa ganin yadda ya hade fuska yasa ta cikin inda inda tace "uhm uhmm sirr"

Tsaki yai ya nuna mata kofa yace "get out"

Zata sake magana ya daka Mata tsawar da bata son lokacin data kwasa a guje ba tafita.

Zama yai yana sauke ajiyar zuciya yana tunanin mafitar da zai dauka don gaskia baxai iya daukar wannan Risk dinba....


*********
Ina shiga gida da sallama na shiga palourn mu ganin Umma bata nan yasa na kalli Aisha dake assignment nace "Aisha ina Umma"

Dagowa tai d a fara'a tace "Maman hidaya ce ta haihu Ya batul shine Umma ta shiga itada Mimi, Nima da zan bisu sai Umma tace na zauna in kin dawo ma shiga tare"

Cikin murna nace "Kai don Allah Maman Hidaya ta haihu mai aka samu"

Murmushi tai tace "Namiji aka samu, kar kiso kiga Mimi da aka fada mata kamar zata yi hauka da kyar ta Jira Umma don da tace ita wallahi baxa ta Jira umma ba zuwa zatai taga baby"

Dariya nai nace "Allah ya raya sa, amma ALLAH ya shirya min Mimi wallahi ko meye na zumudin"

Dariya ita ma tai tace "Ai ya Batul Baki sani ba rige rige suke ita da Hidaya wai duk Wanda ya fara daukar babyn toh babyn sane kin san su ai da son girma"

Girgiza kai kawai nai nace "mai aka dafa ne don ina Jin yunwa"

Sai da tayi dariya tace "jallof din taliya ce tana kitchen"

Mikewa nai naje na zubo na zauna ina ci muna hira da Aisha har na gama, ina bata labarin Asma'u yau nayi kawa dai finally.

Sai wajen magrib Umma ta dawo ita kadai, kallon bayanta nai bayan na gaishe ta nace "Mimi fah Umma"

Tabe baki tai tace "taki dawowa wai bata gama ganin babyn ba ni kuwa na kyale ta tunda zaku shiga sai ku dawo tare"

Daga kai nai nace "dama mu jiran ku muke amma mun shirya bara mu shiga kafin Abba ya dawo"

Hijab dina na gyara muka fita nida Aisha zuwa gidan Maman hidaya, acan muka sami Mimi kuwa ta kankame ita da Hidiya sun kafa sun tsare duk wanda ya dau babyn sai sunje sun makale shi suna leka babyn.

Zama mukai bayan mun gaisa ina wa Maman Hidaya sannu, karbar babyn nai ina kallon sa Allah ya zuba min son Yara sosai a zuciya ta, murmushi na saki na dago na kalli Mimi data zubawa yaron ido itama.

Dagowa tai ta kalle ni tace "Maa Nima ki siyo min baby irin wannan"

Kallon ta nai gabana yana faduwa ynxu kullum zan kalli Mimi sai fuskar Mr Wicked ta fado min a rai, dan murmushi nai nace "ba ga shi ba Mamn Hidaya ta siyo muku"

Make kafada tai tace "Maa wannan brother dn Hidaya ne kinga maman tace ta siyo mata kuma a gidan su yake, nima ki siyo min nawa sai ya ringa kwana a gidan mu kina goya min Shi"

Aisha dake sauraran mu tayi dariya tace "Ya batul sai ki shirya siyo na shalelen ki baby don tunda ta fara wannan maganar nasan kullum sai ta ishe mu akan zancen baby"

Banxa nai musu na maida hankali na gurin maman hidaya muna hira, muda muka ce zamu tafi da wuri dai gamu har 9, sallama mukai Mata bayan munyi maganar ni zan Mata snacks da drinks na suna.

Koda muka koma gida Mimi cika ma Abba kunne tai da labarin sabon baby, marairaice wa tai ta kalli Umma tace "Umma nace Maa ta siyo min baby tace baxa ta siyo ba toh ke ki siyo min kawai"

Dafe kirji Umma tai tace "ni kuma Mimi da tsufana"

Daga kai Mimi tai tana mar mar da ido tace "Uhm Umma kawai ke ki siyo min zan dinga ma babyn wasa"

Kallona Umma tai tace "tab wannan aikin sai dai Maa din taki amma bani ba ita dai zaki sa gaba ko zata maida hankali ma ta fara kula manai manta"

Hade rai nai na kalli Abba nace "Abba kaji Umma zata fara koh"

Murmushi Abba yai yace "gaskia take fada miki Batul, ni kaina maganar da mukayi da Yakumbo knn yau tace ya kamata ki maida hankali a kan masu zuwa neman auren ki, kullum girma kike sake yi"

Kokarin maida hawayen nake nace "Abba ni baxan yi aure ba, baxan rabu da Mimi ba kuma bana son tai agolanci azo ana mata gori"

Salati Umma ta saki tace "kice so kike ki tsufa a gida muna goga kafada, in an shigo a rasa wace matar gidan wace yar gidan koh Batul, wai yaushe xakiyi hankali ne maganar Mimi dama wani yace zai raba kune"

Abba ne ya karba da fadin kuma baga Yusuf ba yaron nan ya yadda da Kaddara yace Shi ahaka yake sonki kuma zai rike Miki Mimi kamar Shi ya haife ta amma kinki sauraran sama gaba daya"

Cikin rawar Murya nace Abba taya zan saurari Yusuf shin kun manta waye Yusuf Abba, saurayin..... Sai kuma na fashe da kuka ina rungume Mimi a jikina, sosai nake kukan wanda hakan yasa Mimi fashewa da kuka itama tana rungume ni sosai......


Kuyi hakuri da wannan na fita ne kawai na muku typing nema😊


Comments Nd share plz


Mrs A.M🥰

[18/08, 02:50] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️

*TASWIRAR KADDARA*

♠️♠️♠️♠️♠️


Written by
Mrs A.M🥰

Page 13

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Shiru su Abba sukai kawai suna binta da kallo ganin kukan da take, ni kuwa sai da naga Mimi tana kara volume dn kukan ta sannan nayi shiru na goge hawayena ina rarrashin ta cikin lokaci kankani tai bacci.

Ajiyar zuciya Abba ya sauke yace "Batul bawai muna son takura ki bane ko mun gaji dake, a'a kawai muna son ki samu farin ciki ne kema Yusuf ya yadda da dukka abinda ya Faru yace zai aureki kuma zai rike Mimi, ba dama shine damuwar ki ba?"

Shesshekar kuka kawai nake na kasa magana taya Abba suke tunanin ma wai Zan iya auren Yusuf, ai baxan taba wannan cin amanar ba.

Tsaki Umma tai tace "kai ne kake lallaba ta Abba, ai ita ba yarinya bace shekara 19 zata shiga sa'annin ta sun fara aure suna zaune dakunan mazajen su, amma ita tana nan tana shirmen baxa tai aure ba, nidai a matsayina na Mahaifiyarki ina baki shawara daki zauna kiyi tunani da kyau, har yaushe zaki cigaba da zama da tabon dake cikin zuciyar ki?"

Lumshe ido nai kawai ban yi magana ba, Dan murmushi Abba yai yace "baxan Miki dole ba Batul, amma ta bakin mahaifiyar kine ki zauna kiyi tunani Allah ya zaba Miki abinda yafi alkhairi, zan bawa shi Yusuf din numbern ki kuna gaisawa"

Daga haka ya kalli Umma yace suje su kwanta, na dade a zaune a gurin kafin na mike na dau Mimi na shiga dakin mu, kwantar da ita nai na Mata addu'a na zubawa Aisha ido dake bacci.

Nima kwanciya nai na lumshe idona ina tunanin shin su Abba basa jin kamar cin amana zanyi in na auri Yusuf?

Shiru nai na dade ina tunani ganin kwakwalwata tana daukar zafi yasa ni mikewa naje nayi alwala nazo na tayar da sallah ina neman zabin Allah akan wannan al'amarin daya danno kai cikin rayuwata.


**********

Shan fruit dinsa yake hankali kwance yana kallo, dagowa yai a karo na uku ya kalli Zainab data ke kaiwa da komawa tunda ta gansa a Palourn tana sanye da English wear riga da skirt da suka kamata, sai turo kirji take tana wani karairaya kamar zata karye.

Maida dubansa gurin Mami yai ta dago itama ta kalle sa, murmushi yai yace "Maa wai ni ake son a yaudara ake wani ciko ana turo kirji"

Kama baki Mami tai ta dan saci kallon Zainab data fito daga kitchen hannun ta rike da cup, maida dubanta gurin Azlan tai tace "ban gane ba"

Murmushin gefen baki yai ya dan sosa bayan kunnen sa yace "turo ta uwar tai tazo tana ciko tana karairaya sbd nace mata kwaila ce ta min yarinya bata san ina gane ciko bane hala"

Girgiza kai Mami tai tace "wai yaushe zaka nutsu Ka rage rashin kunya ne Azlan"

Waro idonsa yai sosai yace "Maa wani abun nai kawai fa gaskia na fada"

Girgiza kai Mami tai tana masa addu'ar shirya a zuciyar ta.

Cikin fushi zainab data gama Jin komai ta shige dakin da aka sauke a Palourn ta rufe kofa, gaban mudubi taje ta zubawa kanta ido tasha heavy makeup sosai duk sbd ta birge sa gashi yau bra har 3 tasa Ashe ya gane ciko tai.

Cikin bakin ciki ta fashe da kuka, tunda tazo gidan basu hadu ba sai yau kamar yasan tana nan baya shigowa sai ya daidaici bata nan, gashi ita gaba daya zaman gidan ya gundureta bata wani sakewa, da sassafe take fita gidan kawayen ta suyi ta yawo joint joint suna chilling sai ta kwana ta yini ma basu hadu da Mami ba.

Wayar ta ta janyo dan kiran Mummy sbd ta gaji so take ta koma gida gaskia, asan kuma yadda za'a yi tunda wannan hanyar da suka dauka tun ba'a je ko ina ba ya gane.


A Palourn kuwa Azlan ajiye bowl din da yake shan fruit dn yai ya kalli Mami yace "Maa in tambaye ki don Allah"

Maida hankalin ta Mami tai gunsa Jin yai magana cikin nutsuwa sosai kamar ba Azlan ba, ajiyar zuciya ta sauke tace "ina Jin Ka"

Sai da ya dan yi shiru na kamar 2 minutes sannan yace "mai yasa wasu suke sa hijab kullum ne wai Mami basa jin zafi suna yawo da hijab dogo har kasa kullum a cikin rana"

Bin sa da kallon mamaki Mami tai tunda take da Azlan bai taba mata maganar abinda ya shafi Mata ba ko kuma yanayin shigar su ba, ganin kallon da take masa yasa shi fadin "shiknn ma"

Murmushi Mami tai tace "Hijab mutunci ne ai Azlan, kuma musulunci ma ya umarci mace data rufe jikinta kawai ba'a amfani da koyarwar musulunci ne amma duk wadda kaga tana sa hijab tana yi ne dn rufe jikinta da kuma killace jikinta, abinda matan ynxu basa ganewa ita mace Mai DARAJA ce ZAKI bai kamata komai nata a same sa a arha ba"

Ruwa tasha tana kallon yadda ya mai da hankalin sa sosai kanta yana sauraran ta hakan yasa ta cigaba da fadin "dukda ynxu wasu suna amfani da hijab dn gurin fitsara sai kaga yarinya tasha dogon Hijab har kasa amma da zaka bude hijab dn tsirara take amma ba duka aka xama daya ba, Shi Hijab rigar mutumci ne kuma ana ma duk Wanda take yawan sa shi tana rufe jikinta kallon Kamila."

Gyada kai yai ya juya, murmushi mami tai tace "amma dai mai yasa Ka tambaya Zaki"

Dan tabe bakinsa yai yace "wata fitsararriyar yarinya ce take sashi kullum na ganta dashi nake ganin ta, amma abinda yake ban mamaki meyasa mara kunyar yarinya zata dinga sa hijab a university kullum, kowa dai yasan bata da kunya tunda bata ma yawo da Mata sai Maza kullum zaka ganta ita da wani gardi a gefen ta sun jera suna tafiya," sai kuma yai tsaki ya kalli Mami yace "wai uwar dakina gardin yake ce Mata fa katon saurayi yana fadawa karamar kanwar sa uwar dakina ita kuma amsawa"

Murmushi kawai Mami take zatai magana Junaid da tunda Azlan ya fara magana ya shigo ya tsaya yana ji yace "Wace mai sa'ar ce wannan datai tsaye a xuciyar mazage har yake maganar ta yau, Mami da gaske ne abinda kunne na ya jiyo min yau Azlan ne yake maganar wata mace gaskia yau ranar ta musamman ce har sadaka zanyi Ashe dai aljanar da muke xargin ta aure Ka ta sake Ka"

Kallon Junaid yake yana kankance idonsa yace "Junaidu yaushe na fara wasan banxa dakai?"

Kama baki Junaid yai yace "wai Azlan nida kai waye babba ne?"

Mitsi mitsi yai da idonsa har ya bude baki zai magana kawai kuma sai yai shiru ya janyo lip dinsa na kasa yana tsotsa ahankali.

Murmushi Junaid yai ya zauna a kasa kusa da kafar Mami suna gaisawa, juyawa yai ya kalli Azlan daya hade rai yana kallo yace "Zakin Baffa yaushe zaka zo gidana ne wai kaci abinci, kullum sai Samira tamin korafi akan baka zuwa Ka daure kazo don Allah ko weekend ne"

Juyowa yai ya zubawa Junaid idonsa daya sha kwalli sai sheki suke kafin yai tsaki yace "Allah ya kiyaye naje gidan kanwata cin abinci sai kace wani mayunwaci zaka ce nazo gidan Ka cin abinci"

Girgiza kai Junaid yai yace "koma meye ai ta zama yayarka tunda tana auren yayanka ko?"

Mikewa Azlan yai ya kalli Mami yace "Maa bara naje gurin Abie ina son magana da shi, sannan ki dinga ma min addu'a sosai MAA plz ana kawowa budurcina hare hare sosai"

Daga haka ya sa kai ya fita daga palourn, yana takunsa cikin jarumta, binsa da kallo dukansu sukai kafin Junaid ya kalli mami a tare suka saki dariya...


Part din Abie ya nufa don yasan ynxu haka yana gida, sai da ya tsaya yai knocking kofar aka basa ikon shiga sannan ya shiga, Abie ne kawai a Palourn sai Mama a gefensa tana hada masa tea.

Karasowa yai ya zauna a kan kujerar dake kallon ta Abie yace "Ina wuni"

Binsa da kallo Abie yake yana karantar sa yace "lafia qalau ya aikin"

Gyada kai kawai yai ya kalli Mama da tun shigowar sa ta maida hankalin ta kan abinda take yace "Evening Hajia"

Dan dagowa tai ta daga masa kai kurum ta mikawa Abie tea dinsa tana gyara zaman ta don ba inda zata je zama zatai duk abinda zasu tattauna itama ayi agaban ta taji.

Jin yaki magana yasa Abie fadin "Ina sauraren ka"

Dagowa yai ya kalli Abba yace "so nake nabar lecturing din da nake don bana jin zan iya Abie"

Jinjina kai Abie yai shidama yasan ba'a banza ba Azlan zai shigo gurinsa saidai in wani abun ne, ya dan Jima yana nazarin sa saidai ba alamar ko da Wasa yake dukda dama yasan in har zaiyi magana toh da baya fada da Wasa iya gaskiar sa yake fada.

Gyada kai Abie yai yace "ko Zan iya sanin dalilin dayasa kake son barin lecturing din?"

Kai tsaye yace "fyade ake son min yau saura kadan wata ta rabani da budurcina da kyar na sha"

Sunkuyar da kai Abie yai yana shan tea din sa yayinda Mama ta shiga girmama lamarin rashin kunyar Azlan wai fyade aka kusa masa.

Dagowa Abie yai yace "dama ana yiwa namiji fyade ne Azlan"

Gyara zaman sa yai yadan lashi jajayen lips dinsa yace "sosai ma tunda naje makarantar nan Mata suke kawo min hari, sai suna shiga ta banxa suna zuwar min office da sunan wai Zan koya musu abu basu gane ba ko kuma kai tsaye su aiko min da letter wai suna Sona"

Shiru yai ya kalli Abie ganin Shi din Abie yake kalla yasa shi fadin "yau wata shigo min tai cikin masassun Kaya ya bude Rabin kirjin ta haka ta janye mayafi kuma ta sunkuyo yadda in na dago dole idona zai fada cikin rigar ta, ina dalili ina da lafia fa Abie don banyi aure ba bawai hakan na nufin ina da nakasu bane lafiyayyan namiji ne ni toh shiyasa tun kan wataran sufi karfina su hadu su lalata ni na shiga uku nace xan yi resigning"

Murmushi Abie yai yace "mai yasa kai baxa Ka dau mataki ba da kanka"

Shiru yai don ya fuskanci Abie bawai xai goya masa baya bane gashi yai wa Baffa alkawarin baxai yi resigning ba sai da izinin Abie.

Mikewa kawai yai ya tura hannun sa cikin aljihu yace "sai da safe"


Binsa da kallo Abie yai yace "Allah ya cigaba da tsare min kai"

Tabe baki Mama tai ta juya keya tana kallo, itafa iskanci Azlan yana isar ta komai budurci ta rasa gidan uban waye yake da budurcin, bayan kowa sheda ne akan rashin jinsa da yadda yake zuwa club duk dare..


********

Washe gari da ciwon kai na tashi hakan yasa Abba cemin na kwanta basai naje makaranta ba, Asma'u na Kira nace don Allah tamin attendance baxan samu zuwa ba banda lafia, sosai ta nuna damuwar ta har tace da zata biyo in an tashi nace mata da sauki ai ciwon kan kafin muyi sallama.

Ina kwance a daki ina kallon Aisha dake shirya Mimi don bana Jin zan iya shirya ta da kaina sbd yadda kaina yake min ciwo, tun ina kallon su har bacci ya dauke ni bansan yaushe suka tafi ba.

Ban tashi ba sai karfe 11 saura, a hankali na mike ina mika duk jikina ciwo yake min kodan sbd baccin da bana yi ne na safe yau kuma na samu nai.

Fitowa waje nai banga Umma ba nasan tana dakin ta, wanka nai ma shirya cikin simple riga na dauki breakfast dina ina cikin ci naji wayata tana ringing, banxa nai da ita ganin sabuwar number sai dai kirin da aka sake yi ne yasa ni daga wayar.

Ciki ciki na yi sallama muryar data amsa nice tasa gabana faduwa, daure wa nai nace "waye yake magana"

Daga dayan bangaren aka ce "Yusuf ne........"


Wai shin waye wannan Yusuf din ne🤔🤔

Mai yasa Batul bata son ta aure sa shin amanar waye zata ci da take cewa in ta aure sa taci amana🤔🤔🤔


Comments Nd share plz


Mrs A.M🥰
[18/08, 18:39] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️

*TASWIRAR KADDARA*

♠️♠️♠️♠️♠️


Written by
Mrs A.M🥰

Page 14

Dedicated to Mufeeda🥰

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Sai da gabana ya buga da karfi amma na tattaro nutsuwa ta nace "ina kwana Ya Yusuf"

Ina Jin sautin murmushin Shi cikin nutsuwa yace "Lafia qalau ya jikin Baba yace min baki da lafia"

Ajiyar zuciya na sauke nace "da sauki Alhamdulillah"

"Masha Allah, Allah ya kara sauki yasa kaffara ne"

A hankali nace "Ameen"

Shiru mukai dukan mu, shine ya ce "sai anjima tohm Allah ya kara sauki kiyi saving number ta kinji zan Kira anjima Insha Allah"

"Toh" kawai nace na kashe wayar dagowa nai idona suka fada cikin na Umma da ke tsaye a kofar dakin su tana kallona, marairaice fuska nai amma tai banxa dani ta wuce kitchen.


Kwana na biyu bana zuwa makaranta sbd ciwon kan dake damuna, saukin tama duk abinda kai Asma'u tana turo min kuma tana min attendance, a kwana biyun nan kuwa Yusuf ya taso ni gaba da Kira, don jiya ma sai da yazo dubani nidai ban fita ba kwanciya nai nayi lambon bacci sai Aisha ce taje ita da su Kamal suka gaisa ya basu leda Mai dauke da kayan kwalam su bani.

Yau da wuri na shiga makaranta kasancewar jikin nawa da sauki sosai, a hankali nake tafiya ina sanye da hijab dina kamar kullum dark blue ba rataya jaka a kafada ta, cikin sanyin jiki nake tafiya nayi nisa a tunani kawai naji na bangaji mutum, da sauri na dago ganin waye na bangaja a tare kirjin mu ya buga.

Zuba mata ido yake yana kallon ta kwana biyu knn baya ganin ta, tun shekaran jiya daya shiga musu lecture har yai ya fita bata zoba kuma jiya ma yana lura da abokin ta Shi kadai yake yawo a school Banda ita hakan ya tabbatar masa da cewa bata zoba knn don da tazo da zai gansu tare.

Nima zuba mishi ido nai ina kallon sa sai kuma na turo baki na kauda kaina gefe, ciki ciki nace "Good Morning Sir"

Maimakon ya bani amsa sai jinai yace "mai yasa baki zo school ba"

Da mamaki na dan saci kallon sa sai kuma na juya ina matsa hannuna nace "Banda lafia ne shiyasa banzo ba sir"

Kankance idon sa yai yana kallon ta yace "amma baki rame ba"

Turo baki nai nace "na rame mana"

Gira daya ya daga yace "really"

Dagowa nai na bansan ya akaiba na maka masa harara, ware idonsa yai akan fuska ta yace "ni kike ma rashin kunya"

Da sauri na girgiza kai nace "sir ba haka bane sorry idona ne a haka sometimes sai yayi kamar ina harara"

Dan kallon gefen sa yai ganin mutane suna kallon su yasa shi yin kasa da murya yace "in kika Kara min da wannan abin sai na tsone Miki ido". Rana ni yai ya wuce da kallo na bisa kafi na tabe baki na juya Zan wuce Shan gabana naga anyi da sauri nadan ja baya ganin saura kadan mu hada kirji da wata.

Cikin Huci Zuby tace "mai kika tsaya yi keda Mr Azlan, Mai yake ce miki ke har kin isa ki tsaya kusa da Mr Azlan dina kina masa magana kina wani yanga?"

Dan kallon ta nake a kaikaice ina kokarin fahimtar mai take nufi ganin tana hakikan cewa yasa ni fadin "akan wa wai kike wannan hayaniyar"

Zagi Nana ta kutuntuma tace"Zuby lallai yarinyar nan bata da mutuncin ji yar iskar yarinya ta maida mu mahaukata, tambayar ki muke mai kuke fada keda Mr Azlan"

Kankance ido na nai cikin rashin tsoro na tako ahankali har gaban ita wacce ake cewa zubyn nace "mai zai hana kije ki tambaye sa mai muke cewa"

Cikin masifa tace "ni kike fadawa haka kinsan ko wace ni kuwa a fadin makarantar nan"

Saida na juya idona nace "kece mana student data zo neman ilimi kamar yadda nake student dana zo neman ilimi nima"

Ina fadin haka na juya nai wuce wata ina jan tsaki a raina ina fadin banxa mara aji ta rasa akan wa zatai fada sai akan Mr Wicked.

Kasa magana Zuby tai sai bina da kallo kawai tai, Nana ce ta jata zuwa wani guri suka zauna tana cewa dole su Nemo ko wace ni don su koya min hankali.

Yinin ranar sukuku nai sai duk bani da kwarin jiki, har Asma'u itama ranar duk wani iri tai ta don nidai ko fita daga hall dinmu ban ba dama kuma period nake ba sallah zan ba.

Ina komawa gida wanka nai na shiga kitchen na dora mana abincin dare ina cikin yi Yusuf ya kirani, kamar baxan dauka ba sai kuma na dauka, ai kuwa nayi nadamar daukar wayar don ya fada min sakon daya bata min Rai cewar yana zuwa bayan sallar magrib.

Umma na fadawa bayan na ajiye wayar, nan da nan far freea'a ta mamaye fuskar Umman ta shiga tambaya ta mai za'a tare sa dashi, Dan sassauta yanayin fuska ta nai kodan sbd fara'ar dana gani a fuskar Umma.

Nidai bance komai ba sai Aisha ce ta shiga kokarin ganin ta sa masa cake da doughnut din da nake a wani bowl na tangaran ta rufe ta kuma dauko zobo ta juye a jug dn Umma yasa a fridge wai yadda in yazo sai dai kawai a dakko a basa.

Nidai ina kallon su ni kadai nasan yadda nake ji, zuwan da zaiyi yau kuwa na tanadi tambayoyin da zan masa ko Allah zai sa ya dawo cikin nutsuwar sa ya tuna da babban cin amanar daya ke shirin yi.

Ana Magriba Umma ta sani a gaba wai nai wanka duk kaurin girki nake, kamar zanyi kuka na sake wanka amma ina fitowa Mai kawai na shafa na zira rigar bacci ta na zumbula katon hijab har kasa ash colour sabo ne ban taba sashi ba, turare na dan fesa kadan na kalli wayata dake ringing, cikin sanyin jiki na dauka na Kara a kunne a kunne, a hankali cikin nutsuwa y sanar min da karasowar sa, Nima banyi wani hauka ba sai cewa danai gani nan zuwa kawai na kashe wayar.

Gurin Umma naje kamar zanyi kuka nace "Umma wai yana waje"

Mikewa tai tace "toh Masha Allah sannun sa da zuwa jeki Maza bara na bawa Khalil dadduma ya kawo muku zuwa anjima sai a kai masa abin tabawar koh"

Nidai ban mata magana ba sai kaina dana sunkuya kasa idona na cikowa da hawaye, kallona Umma tai ta tabe baki tace "zaki wuce ne toh ko kuma tsayawa zakiyi anan"

Ban mata magana ba na fita cikin sanyin jiki, a waje na gansa tsaye kusa da dakalin kofar gidan mu ya jingina da motar sa Yana sanye cikin manyan kaya, Yusuf kyakkyawa ne don bakin bafulata nine yana da rufin asiri daidai gwargwado don yana aiki, bashi da makusa mutum ne shi mai fara'a da barkwanci sam bashi da damuwa.

A hankali na karaso ina dan sassauta yanayin fuska ta nace "ina wuni yasu Mama"

Murmushi ya min yace "lafia qalau Batul yasu Mimi dasu Umma"

A hankali nace "Alhamdulillah"

Shiru nai ban sake magana ba sai maida kallona gurin Khalil danai daya ke tahowa dauke da dadduma, yana zuwa shinfida mana yai aka dakalin dayake yana da dan girma ya gaishe sa ya juya ya koma cikin gida.

Kallona yai yace "Bismillah zauna"

Ajiyar zuciya na sauke na zauna daka can karshen dakalin, murmushi yai ya girgiza kansa dama yasan Batul zata iya abinda yafi haka ma.

Zama yai shima ya dan yi shiru kafin yace "nasan zaki ji wani iri a bisa ra'ayin auren ki dana nuna Batul, in har kin amince Zan aure ki kuma xan rike Mimi na Miki alkawarin baxan taba banbanta ta da yayan da zan Haifa ba"

Kallona yai yaga kaina a kasa yake ina jujjuya wayar hannuna ya cigaba da fadin "baxan takura kiba Batul kina da damar da zakiyi rejecting dina, in har ban kwanta Miki ba kar kiji komai ki fada min don Allah"

Ajiyar zuciya na sauke nace "Yusuf baka jin kunyar wannan cin amanar da kake so nayi ko ka manta Kai din saurayin waye?"

Zuba mata ido yai kafin ya girgiza kai yace "Batul ban manta ba amma ynxu gare ki nazo ina neman amincewar ki, kuma ba cin amana bane Batul bata inda mukai cin amana"

Kallon sa nai da mamakin Jin cewa wai ba cin amana yake shirin samu yiba tab lallai ma Yusuf, na bude baki zanyi magana knn Kamal ya fito daga gida hannun sa dauke da tray gefensa Mimi ce tana sanye da kayan bacci kanta sanye hular sanyi kasancewar garin dakwai sanyi.

Karasowa gurin sukai ajiye tray dn Kamal yai a tsakiyan mu, Mimi kuwa kallon sa take tana son zuwa gunsa amma tana kallo na don na hanata zuwa gurin ko wanne namiji in basu Kamal ba sai kuma cilla bayan haka ma Mimi bata da saurin sabo da mutane, Murmushi Yusuf ya sake Mata yace "Mimi baki gane niba"

Turo baki tai tace "na gane Ka Uncle Ina wuni"

Dariya yai yace "lafia qalau Mimi yasu Umma da Hidaya"

Sai lokacin tayi dariya tace "Hidaya Mummyn ta ta siya Mata baby, Nima nacewa Maa ta siyo min tace baxa ta siyo ba kuma fa nace mata baxan dinga dukan babyn ba wasa kawai zan na Mata"

Kallona yai yana dariya yace "gaskia ya kamata ki samo Mata baby itama tana so ko Mimi"

Sunkuyai da Kai nai kunya na kamani ita Mimi yarinya ce bata san ya ake samun babyn ba ni kuwa ai da wayo na na sani, ina kallon su suna hira sai biyewa shirmen ta yake hakan yasani jin wata nutsuwa tana shigata, tun ina kallonsu har nima na fara sa baki anayin hirar dani.

Sai wajen 9 muka shiga gida bayan ya bawa Mimi ledar kayan cwt sai murna take tana tsalle, sallama nai masa ina murmushi na shige gidan.

Ranar Umma kamar zata goya ni ganin banyi complain ba na saki raina ina hidima ta har lokacin kwanciya yai.


Koda muka zo kwanciya sai daya kirani, mun dan dade muna hira kuma ba laifi na saki jiki ba kamar kwanakin baya sai da na fara jin bacci sannan nai masa sallama na kashe wayar......


Comments Nd share plz


Mrs A.M🥰

[21/08, 09:55] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️

*TASWIRAR KADDARA*

♠️♠️♠️♠️♠️


Written by
Mrs A.M🥰

Page 15


*BABY BEAUTY LOUNGE*

*INA YAN GAYUN SUKE MASU BUKATAR GYARAN JIKI, HENNA BLACK AND RED, PEDICURE AND MANICURE, MAKEUP, SALON KU GARZAYO ZUWA BABY BEAUTY LOUNGE DOMIN SAMUN DUKKAN WANNAN ABUBUWAN, HAKIKA GYARA SHINE MACE KUMA KO WACCE MACE YAR ADO DA KWALLIYA CE*

*INA MASU BUKATAR KOYAR MAKEUP DA SALON DUK MUNA YI A BABY BEAUTY LOUNGE CIKIN FARASHI MAI RAHUSA ZAKU SAME MU A TUDUN MALIKI TITIN ALASURE NO.995*

PHONE NUMBER 08183462148 OR 07058457638

*MUNA SIYAR DA MAGUNGUNAN MATA DANA MALLAKA DUK A BABY BEAUTY LOUNGE*

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Washe gari bamu da lecture da safe sbd lecturen yace baxai samu zuwa ba, bacci na nayi sai karfe 10 na tashi na shirya na fita makaranta.

Muna zaune nida Asma'u revision muke na maths sbd muna da test, nidai revision din kawai nake amma hankali na gaba daya baya kan karatun, Asma'u dake min magana ganin nai shiru yasa ta tabo ni.

Da sauri na juya na kalle ta, ajiyar zuciya na sauke nace "mai kika ce Asma'u ban ji kiba"

Rufe book din da muke solving maths din tai ta kalle ni tace "Batul wai me yake damunki kwana biyu ina lura dake kina cikin damuwa don Allah ki fada min mai yake damun ki"

Shiru nai ina wasa da pen din dake hannu na bana jin zan iya fada mata damuwa ta don wannan sirri nane, ajiyar zuciya na sauke nace "Hmmm ba wani abinda ke damuwa kawai mood swing ne kinga ina period"

Dariya tai tace "haka ne sannu Amma ki daure mu karasa wannan kinga test din da zai mana yace da ita zai mana amfani a semester dinnan"

Murmushi nai na janyo book din na bude muka cigaba da revision din, karfe 11 lecturen ya shigo mukai test din gaba daya a gajiye nake don ji nake kamar an min duka ga mara ta dake dan murda min kadan kadan.

Muna zaune Mijin Asma'u ya kirata akan mamanta bata da lafia, hawan jinin ta ya tashi ya taho daukan ta suje asibitin da aka kwantar da ita, tana kashe wayar ta fara kuka ni nake rarrashin ta har ya karaso dole yau ni na rakata gurin motar tasa bamu wani gaisa cikin nutsuwa ba sbd kukan da Asma'u take, sallama nai mata bayan nai mata alkawarin zuwa duba maman tata in tambayi Abba.

Komawa nai na zauna gashi yau har 6 zamu kai a school ga cilla ma bai zo ba, haka mukayi lecturen karfe 1 to 3 muka fito sai na 4 to 6 kuma, a wannan interval din duka takure nake don ina Jin yadda nake zuba da gudu gashi na manta ban taho da pad ba ga bansan inda zan siya ba da kyar ma in banyi staining Ash colour hijab dina ba.

Ta bayan office din malamai naje na zauna ji nake kamar xanyi kuka a jikina ina jin yadda nake bukatar changing pad ga kuma tsoron kar aje nayi staining hijab dina don rushing nake sosai, hade kai da gwiwa nai ina damke cikina dake murda min.


Cikin takunsa na cikakken namiji mai cike da jarumta yake tahowa bayan office din, yana sanye da Riga da wando black colour da suka matukar masa kyau kansa sanye da p-cap black itama sai boot din kafarsa black, yayi kyau sosai bama yadda shigar ta haska farar fatar sa.

Tafiya yake yana duba wayar sa don so yake ya shiga office dinsa ya tattare kayan sa ya tafi yana da aiki a companyn su, kamar ance ya dago yagan ta a daidai lokacin da itama ta dago kanta Jin takun tafiya, da mamaki yake kallon ta yana mamakin mai ya kawota nan gurin kuma bayan ba yawan mutane agun.

Nima a nawa bangaren kallon sa nake yadda shigar tai masa kyau sosai dukda p-cap dinsa ta dan rufe masa fuska, saurin kau da kaina nai na mike shaf na manta da tunanin ko nayi staining din hijab dina, a hankali na fara tafiya ina runtse idona sbd yadda marata ta fara kartawa da karfi.

Zaro manyan idonsa yai yana bin bayanta da kallo tabbas jini yake gani a bayan hijab dinta ya bata hijab din da dan yawa dan sosai ake gani, tunani ya shiga yi mai zai kawo jini jikin ta kuma sai ya ware idonsa da mamaki ya furta "badai wannan kwailar al'ada take ba". Ganin ba mai basa ansa kuma gashi tana neman karya kwana ta fita cikin mutane a haka yasa shi daga kafa sosai har ya kamota.

Cikin tsare gida yace "hey",

A hankali na juyo nace "Good Afternoon sir"

Tabe baki yai yace "Al'ada kike yine kin bata jikin ki ko ynxu kika fara baki san yadda ake gyara wa ba?"

Dan satar Kallonsa sa nai jin tambayar rainin hankalin dayai min, amma Jin yace na bata jikina yasa ni saurin juya wa in ga inda na bata sai kamo hijab din nake amma na kasa gani.

Kankance idonsa yai yace "follow me"

Da sauri nace "sir", tsura min ido yai hakan yasa ni saurin sunkuyar da kaina kasa don ba karamin kwarjini naga yai min ba.

Gaba yai sai da ya tabbatar ba mutane a gun sannan ya dawo yace "muje" ban iya masa musu ba don bai ma bani fuskar da zan masa din ba.

Cikin nutsuwa na shiga bin bayansa ina rintse idona, shi ya fara shiga office din na shiga Nima gaba na yana faduwa, tsakiyar office din na tsaya nayi tsamo tsamo kamar wacce aka tsamo daga ruwa, ban taba Jin kunya ta kamani ba irin ta yau.

Shi kuwa Azlan zaman sa yai akan kujerar sa ya dau wayar sa ya dannawa Mufeeda Kira dake itama tana level 1 a university din, sai da ta kusa katsewa ta dauka, cikin hade gira kamar tana ganin sa yace "kina ina"

Mufeeda dake tare da friends dinta da sauri ta mike ta matsa gefe tace "Ya Azlan ynxu na fito daga lecture"

Gajeran tsaki yai yace "kije gurin mota ta ynxu zan fito zaki rakani wani waje" daga haka ya kashe wayar.

Mikewa yai yaga yadda take yamutsa fuska tana shafa cikinta ta cikin hijab, tabe baki yai yace "ciwon al'ada kike yine"

Ya salam ji nai kamar na fashe da kuka wai al'ada Shi ko kunya baya ji maimakon yadan tsakaya yace period, Shiru kawai nai hakan yasa shi tsaki ya ce "xanje na dawo kar ki sake ki fita ki Jira ni"

Bin bayansa da kallo nai har ya fita, ajiyar xuciya na sauke ganin ya rufe kofar da key ta waje, da sauri na cire hijab dn jikina ai kuwa yayi staining sosai, har rigata itama ta baci sosai kawai na fashe da kuka shiknn Mr Wicked ya gama kallona a haka waya sani ma ko daga yau kallon kazama zai dinga min, tsugunnawa nai akan tiles dan baxan xauna masa akan kujera ba naje nai staining dinta itama.


Azlan gurin parking spaces ya nufa a jikin motar ya tarar da Mufeeda tana tsaye tana jiransa tana ganin sa ta Kara daidaita tsayuwar ta ta nutsu, bai ko kalle taba ya bude motar ya shiga hakan yasa itama budewa ta shiga.

Fita yai daga school din ya hau titi sai kuma ya juyo ya kalle ta yace "ina ne ake siyar da kayan mata"

Da sauri ta juyo ta kalle sa tace "na'am yaya"

Hade rai yai yace "inda ake siyan da kayan mata nace miki koh"

Ajiyar zuciya ta sauke tana sosa keya tace "Yaya za'a samu a sahad ma"

Bai sake mata magana ba har suka isa, kallon ta yai yace "zo muje ki rakani inda zan samu"

Fitowa tai yana gaba tana binsa a baya har suka je inda ake siyar wan, kallon kayan yake a hankali idonsa ya sauka akan wata doguwar riga maroon colour readymade, karasa yai gunta ya dakko tabe baki yai yace "maybe ma tai mata yawa" ya fada yana bin breast curve din rigar da kallo, gurin hijab ya nufa ya dauki wani maroon colour shima dogo har kasa a basket din hannun sa ya sa har ya juya sai kuma ya tuna ai tayi staining kenan tana bukatar pad da pant.

Gyada kai yai ya nufi gurin pants, binsu da kallo yake yana tunanin wanne zai dakko tunda baisan size dinta ba, kundunbala yai kawai ya dakko wasu guda 6 XXL yace "in sun Mata yawa tasan yadda zatai dasu ai dole ma suyi mata yawa wannan kwailar"

Zaro ido Mufeeda tai ganin ya dauki pant da sauri ya share gumin fuskar ta tana kara murza idon ta, tunda take da Azlan zata iya rantse wa bata taba gani ya sai wani abu daya shafi mata ba, ko ita take son Abu in ta fada masa kudin kawai zai bata yace taje ta siya bata gama fitowa daga shock din ba taji muryar sa Yana fadin "kee ina ake siyar da audugar Mata"

Da sauri ta dago tace "audugar Mata kuma yaya"

Harara ya banka Mata yace "wacce kuke amfani da ita in kuna al'ada mana"

Da sauri tai gaba tace "bata nan suke ba ai Yaya bara naje na dakko ma"

Yana tsaye taje ta dauko ta kawo, karba yai suka je gurin biyan kudi ya biya a bayan mota ya ajiye har zai shiga motar sai kuma ya tuna ai tana ciwon al'ada tsaki yai ya dakko wayar sa ya dannawa Junaid Kira, ringing biyu ya dauko bai magana ba sai da Junaid din yace "Zakin Baffa lafia kuwa naga kiranka"

Hade rai yai yace "ynxu Junaidu baxan iya karanka ba sai da dalili"

Dariya Junaid yai yace "ai nasan kane Kai da baka neman mutane ynxu dai fada min meyasa Ka kirani don nasan da akwai dalili"

Shiru yai kamar baxai magana ba sai kuma yace "Mene maganin ciwon al'ada?"

Da mamaki Junaid ya kalli wayar sa ganin da gaske dai Azlan ne ya kirasa yasa shi fadin "lafia Azlan mai ya hada Ka da maganin al'ada kuma"

Tsaki Azlan yai yace "zaka fada min ko kuwa a'a ina ba kai kadai ne doctor ba a duniya"

Da sauri Junaid yace "Allah ya baka hakuri, ya yanayin yadda take Jin ciwon yake"

Dan lumshe idonsa yai yace "mara ne kawai inaga"

Sunan maganin Junaid ya fada masa sannan ya kashe wayar, a hanya ya tsaya ya sai maganin ya siya yogurt da meat pie, bai sake yiwa Mufeeda magana ba har suka isa makarantar.

Parking yai ya kalle ta yace "fita saura kuma naji labarin cewa na dauke ki munje wani gurin sai na gurza bakin ki a bango"

Da sauri ta daga kai ta fita tana mamakin wace wacce yayan nata ya siya wa Kaya haka har dasu always.

Shi kuwa Azlan ledojin siyayyar sa ya dauka ya nufi office dinsa yana tafiya yana tunanin ko mai take ynxu oho shidai fatansa kar ta zauna masa a kujera ta bata masa da abin al'adar ta.

Yana bude kofar da ita ya soma cin karo tana tsaye sai gyara hijab take, bakinsa ya tabe ya ajiye mata ledojin a kusa da kafar ta.

Da sauri na dago na kalle sa sai kuma na sunkuyar da kaina kasa, Tabe baki yai ya nemi guri ya zauna akan doguwar kujerar dake office din ba tare daya kalle taba yace "dauki ledar nan kije toilet ki raba kanki da kazantar nan"

Shiru nai kamar ban ji sa ba ni yau ai baxan iya rashin kunya ba ciwon marar da nake ji kadai ma ya isa yasa ni nutsuwa ga kuma abin kunyar da nai Mutumin da nake tsulawa rashin kunya shine ya ganni cikin wannan yanayin.

Ganin taki daukar ledar yasa shi mikewa ya tako har gabanta, da sauri na yi baya Jin hucin numfashin sa daf dani, dagowa nai ba inda idona suka fada sai a cikin nasa da sukai dau da kwalli, sunkuyar da kai nai kasa ina Mirza hannu na.

Hade rai yai yace "ba magana nake miki na, dau ledar nan ki shiga toilet ki cire kayan ki ki chanja duk kin cika min office da karnin jini"

Jinai kamar na fashe da kuka Amma bani da yadda zanyi, tsugunnawa nai na dauki ledar na nufi hanyar toilet din daya nuna min, ina shiga naji ya fita daga office dn gaba daya.

Ajiyar zuciya na sauke ina bude ledar, da mamaki na fito da komai dake ciki, rintse ido nai ganin hadda pant da pad tunanin yadda zan saka na shiga yi amma bani da option duk kayan jikina sun baci dole na chanja.

Kayan jikina na cire duka na sa a cikin ledar bayan na cire kayan daya siyo na ajiye a cikin sink, shower na sakar ma kaina sai da nai wanka da sabon sabulun dana gani sannan na shirya cikin kayan daya siyo, kallon kaina nai a jikin mirror din toilet dn kamar ya auna jikina har pant din yamin daidai.

Murmushi nai bayan na daidaita hijab din a jikina sai ynxu nake Jin wata nutsuwa tana ratsani ga iska dake shiga cikina, ledar kayan nawa na dauka bayan na bar masa ragowar pant da pad din a toilet ba tare da tunanin komai ba.

Fitowa nai daga toilet din daidai lokacin da shima ya shigo.......


Comments Nd share plz


Mrs A.M🥰
[22/08, 20:11] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️

*TASWIRAR KADDARA*

♠️♠️♠️♠️♠️


Written by
Mrs A.M🥰

Page 16


*BABY BEAUTY LOUNGE*

*INA YAN GAYUN SUKE MASU BUKATAR GYARAN JIKI, HENNA BLACK AND RED, PEDICURE AND MANICURE, MAKEUP, SALON KU GARZAYO ZUWA BABY BEAUTY LOUNGE DOMIN SAMUN DUKKAN WANNAN ABUBUWAN, HAKIKA GYARA SHINE MACE KUMA KO WACCE MACE YAR ADO DA KWALLIYA CE*

*INA MASU BUKATAR KOYAR MAKEUP DA SALON DUK MUNA YI A BABY BEAUTY LOUNGE CIKIN FARASHI MAI RAHUSA ZAKU SAME MU A TUDUN MALIKI TITIN ALASURE NO.995*

PHONE NUMBER 08183462148 OR 07058457638

*MUNA SIYAR DA MAGUNGUNAN MATA DANA MALLAKA DUK A BABY BEAUTY LOUNGE*

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Da sauri na sunkuyar da kaina kasa ina wasa da ledar hannuna, kasa cigaba da tafiya nai na tsaya a bakin kofar toilet din.

Karasowa ciki yai sai da ya zauna akan kujera yace "dauki waccan ledar naki ne"

Bin hannun sa nai da kallo zuwa ga ledar daya ke nuna min tana ajiye akan table din, ban masa musu ba naje na dauko ledar budewa nai naga Meat pie da yogurt mai sanyi hadiyar yawu nai don dama yunwa nake ji, satar Kallonsa sa nai ganin bama ni yake kalla ba danne danne yake a system dinsa yasa ni zama a kan doguwar kujerar office din na juya masa baya na shiga shan yogurt dina Ina korawa da meat pie cikin kankanin lokaci na cinye duka sai kuma a lokacin naji kunyar yaga cewa na cinye komai.

Ina cikin tunanin yadda zan yi kawai naga hannun sa ya ajiye min kwalin magani da ruwa a Kan cinyata, bin maganin da kallo nai da mamaki ganin irin sa nake sha aduk lokacin da ciwon mara ya taso ni gaba, dauka nai na balla nasha.

Sai da na nutsu sosai sannan na sauke ajiyar zuciya na dakko waya ta dan duba tym ganin 5:40 hakan yasa na mike na dauki jaka ta, takowa nai na isa gaban table dinsa dan sassauta fuskata nai nace "Thank you Sir zan tafi, gobe insha Allah zan dawo ma da kayan"

Kallona yai yana kankance idonsa yace "me zanyi da kayan in kin dawo dashi, ko sawa xanyi"

Sunkuyar da kaina nai nace "Sorry sir"

Tabe baki yai yace "u can go"

Ledar kayana na dauka na fita daga office din, ina fita na sauke ajiyar zuciya a hankali kuma hankalina ya dawo jikina sai na fara tunanin Mai zan cewa Umma ba in ta tambaye ni ina na samo kayan.

Kafin na isa gida Saida na samo amsar duk tambayar da nasan zata min don nasan in na fada mata Mr Wicked ne ya siya min Kaya kuma a office dinsa na chanja na mutu kawai.

Da sallama na shiga gidan da mimi na fara cin karo tana wasa da yar tsana a tsakar gida sai Umma da Aisha da alama aiki suke a kitchen, duk zuba min ido sukai suna kallona tun daga sama har kasa.

Murmushin yake nai ina hadiyar yawu cikin dauriya da kokarin saita kaina nace "Umma ina wuni ya aiki"

Karasowar kusa dani Umma tai tace "a ina kika samo kayan nan"

Dafe kaina nai nace "Umma ai yau Allah ne ya taimake ni da badan Asma'u ba da bansan yadda zanyi ba", ledar kayan nawa na bude nace "na manta ban tafi da extra pad ba gashi ina rushing wallahi Umma duk na bata kayana har hijabi na"

Hade rai Umma tai sosai tace "ba wannan na tambaye kiba ina kika samo kayan jikin ki"

Sosa gira ta nai nace "Asma'u ce ta bani sababbine ma a kayan lefen ta ta dakko sbd mamanta bata da lafia an kwantar da ita a asibiti sai ta taho da kayan ta wanda zata chanja don tana so ta kwana a gurin maman tata, sune ta bani tace sai ta koma gida ta dauko wasu"

Ganin kallon da Umma take min yasa ni marairaice wa nace "wallahi Umma ita ta bani kuma zan iya kiranta ma ki tambaye ta, nace mata ma zan tambayi Abba in ya barmu nida Aisha sai muje duba maman tata"

Ajiyar zuciya Umma ta sauke tace"Allah ya kara sauki, cire kayan toh ki wanke mata gobe ki mayar dasu"

Daga kai nai na shiga daki na chanja kaya nafito a gurin fanfo na zauna ina wanke wa ganin kayana dana wanke Wanda sukai staining sosai su suka sa Umma kwantar da hankalin ta.

Da daddare muna zaune nake tambayar Abba akan zuwa duba maman Asma'u da nake son yi bai musa min ba yace "Allah ya kaimu"

Duk da ina da lecture gobe amma karfe 2 zan dawo nasan tym din Aisha ma ta dawo daga school sai mu tafi tare gaba daya.


********

Azlan kuwa bayan barin ta office din mikewa yai yace bara yaje yaduba toilet dinsa ko ta masa kazanta a ciki, yana budewa yaji kamshin air freshener ya doki hancin sa, Dan tabe bakinsa yai har zai juya idonsa ya sauka akan sink nan yaga pant da pad da alama dai daya kawai aka taba aka bar ragowar.

Gyara tsayuwar sa yai ya dafe kansa cikin takaici yace ynxu data bar min wannan kayan anan in wani yazo ya gani fa wani irin kallo xai min masa da mutuncin sa.

Dauko wa yai sai kuma ya samu kansa da bin pant din da kallo, sa sauri ya kauda tunanin dake neman bijiro masa ya fito hannun sa rike da pant da pad din, da sauri ya tsaya ganin Haidar tsaye a tsakiyar office din yana kallon sa.

Saurin kallon abin hannun Azlan haidar yai sai kuma ya maida duban sa gurin Azlan din da mamaki yace "Azlan mai xan gani haka meye kake yi da kayan mata"

Hade rai Azlan yai ya nufi kan table dinsa yana boye pant din a gefen rigar sa, haka kurin ya samu kansa da kin son haidar din ya ga pant din, janyo jakar sa yai ya sa pant da pad din sannan ya juyo gurin Haidar daya saki baki yana kallon sa.

Kara hade rai yai yace "taya zaka shigo min office ba tare da sanarwa ba"

Dan tsaki Haidar yai yace "me kake yi da kayan mata Azlan nidai a iya sanina baka hulda da Mata"

Lasar lip dinsa yai yana "kankance ido yace budurwa ta ce take jini shine na siyo mata ko da magana ne?"

Hangane baki Haidar yai yace "budurwa kuma yaushe kayi budurwar?"


Kuyi manage plz na fita ne kawai na muku ne don kar Kuji Shiru ngd sosai.


Comments Nd share plz


Mrs A.M🥰

[23/08, 16:22] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️

*TASWIRAR KADDARA*

♠️♠️♠️♠️♠️


Written by
Mrs A.M🥰

Page 17


*BABY BEAUTY LOUNGE*

*INA YAN GAYUN SUKE MASU BUKATAR GYARAN JIKI, HENNA BLACK AND RED, PEDICURE AND MANICURE, MAKEUP, SALON KU GARZAYO ZUWA BABY BEAUTY LOUNGE DOMIN SAMUN DUKKAN WANNAN ABUBUWAN, HAKIKA GYARA SHINE MACE KUMA KO WACCE MACE YAR ADO DA KWALLIYA CE*

*INA MASU BUKATAR KOYAR MAKEUP DA SALON DUK MUNA YI A BABY BEAUTY LOUNGE CIKIN FARASHI MAI RAHUSA ZAKU SAME MU A TUDUN MALIKI TITIN ALASURE NO.995*

PHONE NUMBER 08183462148 OR 07058457638

*MUNA SIYAR DA MAGUNGUNAN MATA DANA MALLAKA DUK A BABY BEAUTY LOUNGE*

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Jakar sa ya dauka yace "tunda ga zubairu komai sai na fada muku koh, ya karashe yana dage girar sa guda daya."

Girgiza kai Haidar yai yasan karya Azlan ke masa ba wata budurwa da yai amma kuma mai pant da pad suke a office dinsa.

Zama Haidar yai yace "biyo wa nai ta hanyar shine nace bara nazo mu gaisa Naga yadda Azlan yake lecturing".

Dan tsaki yai yana sosa girar sa ya lashi jajayen lips dinsa yace "bari kawai na gaji so nake nayi bar aikin amma hakan baxai yiwu ba don nayi ma Baffa alkawarin ban barin aikin sai da yaddar Abie", ajiyar zuciya ya sauke yace "kuma kasan Abie baxai taba yadda na bar shi ba ga aikin company nidai an maida ni kamar engine."

Dariya Haidar yai yace "hakuri zakai mutumin, Ka ki fito da mata daka fito da ita da duk ba haka ba"

Kankance ido yai yace "ban shirya rabuwa da budurci naba, kai nifa ba wannan ba kunya ma nake ji ace inyi aure ina aure kowa yasan Mai zan dinga yi."

Kalkalewa da dariya Haidar yai har yana rike cikin sa yace "na shiga uku ni Haidar dama da abinda Oga Azlan yake jin kunyar sa."

Dan hade rai yai kadan yana kokarin hana kansa murmushi yace "eh mana gashi Ka gani kuwa, wai dama wa yace muku bani da kunya ni ko hannun mace kunyar rike wa nake."

Sai da suka gama Wasa da dariya sannan Haidar yace "kar na manta mutumina maganar aurena kasan saura wata daya, mai dame kake tunanin zamuyi su dai tace min zasuyi kamu da walima ni kuma ina son muyi dinner da."

Karkada kafa Azlan yai yana yamutsa fuska yace "meye kuma dinner?"

Harara Haidar ya watsa masa yace "baka da kirki wallahi Azlan don Allah ni Ka maida hankali muyi magana kasan kaine amini na da kai kawai nake shawara kuma nasan halin kane zan iya hadawa kace baxa kaba."

Kafadar sa ya daga yace "kadan daga aikina knn, amma zanje ai taka ce mune a gaba gaba gurin cin cake."

Yadda yai maganar yasa Haidar dariya, sun dade suna tattauna sai da aka Kira magriba sannan suka fito kowa ya shiga motar sa ya tafi gida.


Gidan Baffa ya nufa don ya dade bai je ba, a Palour ya same sa yana zaune yana Jan carbi idonsa akan Sunna TV, shigowa yai bakinsa dauke da sallama.

Dagowa Baffa yai ya sakar masa murmushi yace "sannu da zuwa Zaki"

Shima dan gajeran murmushin ya saki ya zauna a kasa kusa da kafar Baffa yace "barka da dare tsoho"

Murmushi shinfide akan fuskar Baffa yace "barka kadai gauro mai tsoron Mata"

Wani miskilin murmushi yai yana shafa gashin bakinsa yace "Uhmm tsoho knn bara dai nai shiru kar kace Banda kunya amma da nace wani abu"

Dariya Baffa yai yace "Zaki Allah ya shirye ka, amma ya kamata Ka duba kaga kullum girma kake ko baka so na dauki gudan jinin kane kafin na mutu."

Yamutsa fuska yai yace "tsoho meye kuma haka ana magana zaka kawo zancen mutuwa."

Murmushi Baffa yai yace "mutuwa dole ce ai Zaki, kuma tunata wajibi ne ga duk mai Imani."

Shiru yai kawai ya lumshe idonsa sai kuma ya shiga tunanin wannan mara kunyar yarinyar yadda bakin ta ya mutu, baiyi tunanin wani Abu zai iya sata ta shiga hankalin taba sai gashi ta nutsu ko harara batai masa ba.

Baffa daya zuba masa ido yana ganin yadda yake ta murmushi yace "lafia Zaki tunanin wa kake haka yau"

Mikewa yai daga kishingiden da yake yace "sirri ne tsoho, in na fada ma zaka ce na zama Dan iska toh gwanda nai Shiru."

Binsa da kallo Baffa yai ganin ya koma kan kujera ya kwanta, da mamaki yace "anan zaka kwana ne?"

Daga masa kai kawai yai ya lumshe idonsa fahimtar hakan yasa Baffa sanin cewa Yan miskilancin ne suka motsa knn, shima Shiru yai amma yana cikin tunanin mafita akan maganar da Mummy tazo masa da shi.

Tazo masa da maganar auren Zainab da Azlan dinne daya nuna mata kin hadin sbd abinda Azlan yace sai ta sa masa kuka tace taga kamar baya so ayi auren ne kuma gashi zainab din kullum cikin kuka take sbd son da take ma shi Azlan din, shiyasa duk ya rasa yadda zaiyi yana bukatar tunani sosai tunda Azlan yace baya so yasan ya fada ne har cikin ransa kuma shi ya fada mata baxai ma Azlan dole ba in har ya Kara tuntubar sa akan maganar yace baya so toh Zainab dn tayi hakuri ta fidda miji a cikin masu sonta.


************

Tafawa sukai kamar kawaye cikin farin ciki Zainab tace "Mummy naji dadi amma sosai wallahi ba ta biyun ki Mummy, ni nasan dama tunda kika ce na kwantar da hankalina kamar na gama Zama matar Ya Azlan ce kawai."

Murmushi Mummy tai itama tana sa kazar data yaga a baki tace "ai sai da na tabbatar na fada masa da jikin sa zaiyi sanyi sannan na tafi, haka kurin"

Saudat ce kanwar Zainab da ta zuba musu ido tace "wallahi Ya Zainab da nice ke hakura zanyi da shi, ya Azlan yace baya sonki Amma kin dage ke dole sai kin tusa kanki rayuwar sa a haka zai soki ana cusa masa ke"

Wurga mata jarkar ruwa Mummy tai tace "rufemin baki munafukar banxa ke na rasa wani irin Hali ne dake maimakon ki taya yar uwar ki neman abinda take so Amma so kike ki sanyaya mata gwiwa"

Tsaki Zainab tai tace "wallahi Mummy wannan Yarinyar kamar bake kika haife taba kwatakwata bata hawa hanyar abinda kike dorata akai shegia kawai"

Mikewa saudat tai tana turo baki ta fita daga palourn tana musu fatan shirya don tana jin Mummy na dada fadawa Zainab in Azlan din yaki yadda ma gurin malamai zasu Kaisa.


********

Mun fito daga lecture knn kafin mu shiga wata na yi sauri na nufi office dinsa hannuna rike da ledar kayan sa dana saka aciki, a hankali nayi knocking sai da nayi knocking sau uku sannan naji ance "come in"

Tura kofar nai na shiga da sallama yana zaune akan kujera hankalin sa na kan laptop din kan table dinsa da yake sarrafawa sai kuma wadannan da suka taba tareni ahanya su uku ne amma ynxu da alama assignment suka zo submitting don naga papers a hannun dayar.

Dauke kaina nai daga kansu na nufi table dn gaba na Yana faduwa.

Su Zuby kuwa zuba mata ido sukai cike da bakin ciki, ji take kamar ta janyo ta ta shake, tun dazu suka zo submitting assignment din da ya basu tunda yace su ajiye a gurin bai Kara daga kai ya kalle suba, ita kuma zuby sai tambaya take masa akan course din wani zai bata ansa ne wani kuma banxa yake mata.

Cikin nutsuwa da saurin maganar da nake yi nace "Good Morning Sir"

Dagowa yai daga aikin da yake yi ya kalle ta tana sanye da doguwar riga mai budewa sai mayafi data yafa a kanta ta rufe sosai har kirjin ta.

Hade rai yai haka kurin ya soma tunanin haka ta shigo school da wannan shigar duk da rigar budaddadiya ce amma sam ransa bai masa dadi ba ganin ta a haka ba hijab.

Kara hade rai yai yace "mai yasa baki sa Hijab ba yau"

Dan ware ido nai na kalli jikina sai na kalle sa da mamakin Jin tambayar sa.

Ganin yadda tai ne yasa shi kara hade rai kawai samun kansa yai wani bacin rai yana lullube sa.

Ni kuwa duk da maganar sa ta ban mamaki amma haka na kanne a raina ina fadin ji wata gulma kuma meye hadin sa da Hijab dina.

Ledar na ajiye akan table din nace sir ga kayan na gode Allah ya saka da alkhairi.

Dan kallon ta yai ya kalli ledar sai kuma yayi baya da jikin sa akan kujerar kafin ya mike cikin takunsa na cikakken namiji kuma lafiyayye ya karasa gaban ta ya tura hannun sa cikin aljihun wandon jikin sa.

Dan baya nai gaba na Yana faduwa sbd kusancin mu dayai yawa, hade rai ya sake yi cikin husky voice yace "ce miki nai ki dawo min da su"

Kamar zanyi kuka nace "Sir toh ai ba nawa bane kuma cema Umma nai friend dita ce ta bani in na ce mata kaine kaban kashe ni zatai inaga"

Tsayuwar sa ya gyara yace "dauki ki mayar dasu na ki ne ai ko so kike na dinga sawa ne ina yawo, haka kika bar min kayan kazantar ki a toilet ynxu da wani ya gani fa"

Da sauri na sunkuyar da kaina kasa cikin kunyar maganar sa, cikin lallashi nace "sir toh gashi na dawo dasu"

Daga kafada yai yace "baxan karba ba in nayi kyauta bana karba ragowar kayan naki ma suna jaka ta," juyawa yau ya bude jakar ya fito da pant da pad din tsirara ya miko min

Kallon hannun sa nai ganin abinda yake miko min yasa ni juya masa baya da sauri nace "na shiga uku"

Wani murmushi ne ya subuce masa da bai shirya masa ba.

Su Xuby da dukkan du suka hangame baki suna kallon ikon Allah da sauri Nana ta tabo Zuby ganin hawaye na zubo Mata, ajiye papers din Tai kawai na nufi kofa tana fashewa da kuka, suna su Nanan baya suka mara Mata da sauri.

Suna fita na juyo kamar zanyi kuka nace "sir ynxu me zasuyi tunani kace na bar kayana a toilet kuma Ka dakko wannan abun"

Kankance ido yai yace "ke me kike tunani badai kina tunanin vawulence ba kwaila da ke har kin iya wannan tunanin"

Zaro ido nai ina kama baki na nace "sir" sai kuma na ajiye masa ledar na juya cikin sauri na fita.

Shima idonsa ya zaro ganin yadda mazaunai suke rawa sbd sassarfar datai, cikin mamaki yace badai yarinyar nan ciko take ba, Tabe baki yai yana fadin kai kuma meye naka Azlan.

Komawa yai ya zauna amma sai ya kasa aikin masa kawai tunanin yadda take yawo a school ba Hijab yake Maza suna kallon ta.


************

Uku saura na karasa gida a gajiye nai wanka naci abinci Sannan na shirya cikin riga da skirt simple style na yada babban mayafi na rufe jikina, Aisha ma data sa irn kayana itama mayafin ta yafa.

Mimi nake sawa takalmi data dage akan sai ta rakani hadda birguma a akasa dole na shirya ta itama.

Mikewa bai bayan na gama samata takalmin na kalli Umma da take cewa kar mu manta mu tsaya mu siya mata fruits na dubiya daga Kai nai nace "Insha Allah Umma baxa mu manta ba"

Muna fitowa daga gidan mukai kicibus da cilla a daidaita zai wuce, tsayawa yai ya sakko yace "uwar dakina barka da wannan lokacin"

Murmushi nai don Allah ya sani kwana biyu nayi missing cilla don ma kusan kullum sai munyi magana ta WhatsApp, daga kai nai ina kallon sa yana ma Mimi magana suna dariya.

Kallon adaidaitar nai nace "ina Ka sami adaidaita cilla"

Dariya yai yace "ta saminu ce ta ban nadan yawata Nima a ciki ynxu xan fita ma mu gwada sa'ar mu"

Murmushi nai cilla yana burgeni sam bashi da matacciyar zuciya yana da zuciyar nema sosai, cikin Raha nace "toh muje mu zaka fara dauka asibiti muka nufa duba maman Asma'u"

Adaidaitar ya shiga yace "Bismillah uwar dakina shigo muje Allah sarki Nima na samu na duba ta"

Ciki muka shiga muna hira har muka isa asibitun bayan mun tsaya na sai musu kayan fruits na 1k din da Abba ya bayar.

Cikin asibitin muka nufa cilla na rike da laidar ni kuma ina rike da hannun Mimi, kasancewar Asma'u ta fada min number din dakin yasa bamu sha wuya ba gurin Nemo dakin.

Knocking mukai aka bamu izinin shiga muka shiga cilla kuma ya tsaya a waje tukun, ba mutane da yawa a dakin daga mamn tasu dake zaune akan gado sai Asma'u sai wani namiji da kallo daya zaka mai kasan yayan Asma'u ne.

Cikin girmamawa muka tsugunna har kasa muka gaishe da maman Asma'u da tambayar ta ya jiki, cikin sakin fuska ta amsa mana.

Kallon Asma'u nai wacce tun shigowar mu ta kafe Mimi da ido cike da al'ajabi murmushi na sakar mata nace "Asma'u ya mai jikin ALLAH ya Kara sauki"

Ajiyar zuciya ta sauke tace "da sauki Batul jikin Alhamdulillah anjima ma za'a sallame mu"

Masha Allah na fada ina gyara zamana don duk a takure nake sbd kallon da Yayan Asma'u yake min, Mimi ce dake Kan cinyata tace "Maa mun bar uncle a waje fah"

Dan bude baki nai na kalli Asma'u da kanta ya Kara daurewa Jin sunan da Mimi ta cemin nace "Asma'u tare muke da cilla shima yace zai duba jikin mama yana waje"

Ita ta shigo dashi shima yai mata ya jiki sannan muka muke bayan na ajiye mata ledar kayan Fruits din, sallama mukai wa Maman tasu ita kuma ta rako mu waje.

Rike hannun Mimi tai tace "wannan ma kanwar kice amma bakwa kama sam ni wallahi da Mr Azlan ma take min kama sosai kamar an tsaga Kara"

Duk da gabana ya fadi Jin sunan Wanda ta ambata amma hakan daure nace "Yata ce fa ni na haife ta"

Wani ja tai ta tsaya tana kallona sau kuma ta kalli Mimi tace "yar kice bana son wasa don Allah"

Murmushi nai ina cigaba da tafiya nace "wallahi yata ce kinji ma na rantse"

Da mamaki sosai tace "dama kin taba aure"

Shiru nai kawai ban mata magana ba ina kokarin controling mood dina har muka karasa gurin adaidaitan, shiga mukai nayi Mata sallama mukai gaba.

Har kofar gida cilla ya maida mu sannan na basa kudin motar, dakyar ya karba da yace baxai karba ba sai da na bata rai sannan ya Karba yana dariya.


Washe gari da wur na tashi don karfe 9 muke da lecture, amma sai Mimi ta tashi da rigima itama akan sai ta bini tunda an musu hutun boko da islamiyya duk yadda na rarrashe ta kin yadda tai hadda birgima akasa tana ihun wayyo Maaa ta daina sonta.

Kamar zanyi kuka na kalli Umma da tai kamar bata San muna yi ba, dole na shirya ta cikin doguwar rigar atampa na sa Mata baby hijab ba karamin kyau tai ba kamar ka saceta bama baby hijab din daya kasance dark blue sai ya haska fatar ta sosai.

Kudin kashewa na kara tunda da Mimi zanje ai nasan dole na tafu da kudi don Mimi bata shiri da yunwa.

Sallama mukai wa Umma da take dariya a ranta kuma tausayin Batul ne fal, murmushi tai tana binsu da addu'a.


A adaidaita sai da na gama ja Mata kunne akan Banda suruta kuma ban yarda ta yiwa kowa magana ba ba ruwan ta da mutane ita dai daga min kai kawai take bakin ta kamar zai tsage sbd murnar zan tafi da ita school dinmu itama.


Lokacin da muka isa har 9 ta kusa hakan yasa ni sauri ina rike hannun Mimi, sakin hannu na tai tana dariya tai gaba tana fadin "Nima zan iya MAA mu tafi toh"

Mun kusa zuwa hall dinmu sbd lecture din Mr Wicked ne shiyasa nake saurin zuwa don kar ya rigani shiga, da sauri na juyi Jin Mimi ta saki Kara a razane na kalli wanda ta bangaja din ina baya kamar zan fadi gabana yana tsanan ta bugawa.

Sir Azlan da yake tahowa hankali sa na kan wayar sa sbd wani sako da yake dubawa yasa bai San da mutum a gaban sa ba kawai sai ihun yarinya yai, da sauri ya sa wayar a aljihun sa yana sa hannu ya dago Yarinyar data sunkuya tana duba hannun ta data bige san da shi, wani irin bugawa kirjin sa yai da karfi sanadin arba da fuskar yarinyar da yai............


Comments Nd share plz


Mrs A.M🥰
[24/08, 15:22] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️

*TASWIRAR KADDARA*

♠️♠️♠️♠️♠️


Written by
Mrs A.M🥰

Page 18


*BABY BEAUTY LOUNGE*

*INA YAN GAYUN SUKE MASU BUKATAR GYARAN JIKI, HENNA BLACK AND RED, PEDICURE AND MANICURE, MAKEUP, SALON KU GARZAYO ZUWA BABY BEAUTY LOUNGE DOMIN SAMUN DUKKAN WANNAN ABUBUWAN, HAKIKA GYARA SHINE MACE KUMA KO WACCE MACE YAR ADO DA KWALLIYA CE*

*INA MASU BUKATAR KOYAR MAKEUP DA SALON DUK MUNA YI A BABY BEAUTY LOUNGE CIKIN FARASHI MAI RAHUSA ZAKU SAME MU A TUDUN MALIKI TITIN ALASURE NO.995*

PHONE NUMBER 08183462148 OR 07058457638

*MUNA SIYAR DA MAGUNGUNAN MATA DANA MALLAKA DUK A BABY BEAUTY LOUNGE*

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Cikin tsananin bugawar zuciya ya sunkuya kasa ya Kara riko fuskar yarinyar cikin rudani, itama Mimi manyan idonta irin nasa sak ta sake ware wa tana budewa kamar yadda yake da nasa a duk lokacin da wani Abu ya basa mamaki, "Subhanallah" ya fada yana shafa fuskar ta.

Cikin sauri na matso gurin gabana yana faduwa na finciko Mimi nace "zo mu tafi"

Cikin shagwaba tace "Maaa to ai uncle din nan ne ya bige ni kamar ya karyan kafa ma"

Na bude baki xanyi magana naji muryar sa data fara shakewa yace "zo beauty muga kafar ko na karya din"

Ganin ya biye mata yasa ta cire hannun ta daga cikin nawa ta tafi gunsa tana turo baki, murmushi ya saki Wanda ya bayyana hakoran sa farare ya riko hannun ta.

Kara sunkuyar da kansa yai gun kafar sa cikin faduwar gaba yake kallon kafar ta shape din kafar sa ce sak banbancin kawai wannan ta Yara ce, lumshe idon sa yai yana ambaton sunan Allah a zuciyar sa.

Hannu Mimi ta dora a kansa cike da shagwaba tace "Uncle baka duba kafar ba har ynxu na gaji"

Saita kansa yai kafin ya duba kafar Tata duk da yasan ba wani abinda ya Sami kafar kawai ragonci take, dagowa yai yace "uhm beauty ashe raguwa ce keh haka ba kiji ciwo ba"

Washe baki tai tace "toh Masha Allah, Uncle kaima a school din nan kake MAA dita ma anan take da kyar ta yadda tazo dani sai da na dinga birgima a kasa ina ihu"

Gajeriyar dariya Azlan yai yace "ni teacher dinsu ne, mai yasa bata so tazo dake"

Daga kafada Mimi tai tana ware hannu alamun itama bata sani ba

Jan kumatun ta yai yana rike Mata hannu yace "muje toh class din ynxu su Maa din taki zan koyar"

Da sauri ta tari gabansu cikin tsiwa nace "Sir ka sakar min yarinya ta zan shiga da ita"

Bin ta da kallo yai tundaga Sama har kasa wai yarinyar ta lallai yarinyar nan ta raina Sama tabe baki kawai yai ya zagaye ta ya nufi hall din

Kamar zan kuka na bi bayan su GA Mimi ina hango ta sai zuba take masa.

Muna shiga Hall dn gaba daya ido ya dawo kanmu bama Mimi dake rike da Azlan, ganin idon mutane yasa nayi gurin Asma'u wacce itama idon ta zuba mana na Kai tsakiya knn Mimi ta daga murya tace "Maa ki tsaya ni toh"

Ido na lumshe ina dana sanin zuwa da Mimi da nai, banza nai mata kawai don haushin ta nake ji na zauna gefen Asma'u.

Kallon sa Mimi tai ta dago ta kalle ni harara na watsa mata sai ta juya gunsa tace Uncle Maa haushi na take ji zata min fada bara naje gun ta

Daga Mata kai kawai yai ta juya tana tafiya har ta iso gurina, a kan cinyata ta zauna tana murza idonta wai don kar na Mata magana, banza nai Mata na maida hankalina kansa.

Jikinsa duk wani iri yake jinsa sbd arba da wannan Yarinyar da yai kamar sa da ita har ta baci har yanayin dimple dinsa irn nata ne komai nata irin nasa ne bai wani tsawaita ba don baya cikin mood Mai dadi ko assignment bai bayar ba.

Gurin da muke zaune ya taho idonsa akaina, murguda baki nai na juyar da kaina gefe gabana yana faduwa, tsayawa yai a gaban sit dn da muke ya miko wa Mimi hannu, ban wani damu ba don nasan Mimi bata da saurin sakewa da mutane amma ga mamakina sai Naga cikin sauri ta Mika masa hannu ta sauka daga jikina.

Juyawa sukai zasu fita haka yasa na mike nima da sauri na mara musu baya, muna fita daga hall din na kalle sa nace "Sir ina zaka kaimin yarinya ta"

Kallona yai yace "siyar da ita zanyi"

Wata harara na watsa masa kafin na dauke kaina na maida shi gun Mimi da ta sake rike hannun sa sosai tana wasa da xoben sa.

Kamar zan kuka nace "sir don Allah Ka sakar min yarinya mu koma kaga muna da lecture ynxu Kar lecturen ya shiga"

Daga kafadar sa yai yana tabe baki yace "ina ruwana ki koma mana"

Da sauri nace "Mimin fa"

Kallona yai yana kankance idonsa yace "in kun gama komai zaki iya samun mu a office dina"

Zaro ido nai nace "da Mimi zaka tafi office din naka wallahi baxan yadda ba yadda duniya take ba gaski....." Ban karasa ba sbd yadda ya juyo a fuskace yana kallona idonsa har ya soma kadawa zuwa jaa

Da sauri na sa hannu na toshe bakina cikin tsananin tsoro don ni ban taba ganin sa cikin wannan yanayin ba, kuma Allah ya sani bansan na fadi abinda na fada ba

Juyawa yai kawai da Mimi suka tafi ina tsaye har suka wuce hawaye ke kokarin zubo min gashi ba halin binsu don test muke da shi ynxu dole na koma hall kamar na fashe da kuka ina mitar baxan sake zuwa da Mimi ba.


Mimi kuwa suna tafiya tana masa hira yana biye mata har suka karasa office dinsa duk inda suka wuce sai an bisu da kallo don yadda suka jeru dinnan haka ya Kara fito da kamannin su da juna sosai.

Suna shiga office din Mimi ta kalle sa tana sakin hannun sa tace "Uncle nan ne office dinka"

Murmushi yai yace "eh kina sonsa"

Dariya tai tace "sosai ma yayi kyau kuma da akwai AC ina son Ac amma bamu da shi a gida".

Murmushi Azlan yai yace "kice wa Daddyn ki ya siya miki".

Turo baki tai tace "Banda Dad ni Maa tace Dad dina ya mutu baxai dawo ba."

Dan maida hankalin sa yai gun ta yace "wace Maa din taki?"

Murmushi tai cikin farin ciki tace "ai kaganta Uncle itace Maa dita muna zaune a gidan mu da Abba da Umma da Maa da Ya Aisha da Ya Kamal da Ya Khalil sai ni."

Sam shi bai gane mai take fada ba tace bata da Daddy kuma tace Abba da Umma, cikin son fahimtar maganan ta yace "kin ce baki da Daddy kuma kince Abba da Umma?"

Dariya tai tace "Abba baban Maa ne Umma ma Maman Maa ce ni kuma granny tace Ya Aisha Aunty nace Ya Khalil da Ya Kamal uncles dina ne ta karashe tana washe baki."

Cikin Mamaki yace "ita MAA din taki wace ita?"

Turo baki tai tana Zama akan kujera tace "Maa ce fah Mamana toh Uncle".

Zaro ido yai yace "ita ce Maman ki?"

Daga masa kai tai tana juyi akan kujerar sa cikin nishadi, mamaki ne sosai ya rufe sa sai a lokacin ya tuna yadda take cewa ya ajiye mata yarta Ashe maman tace amma wannan Yarinyar har ya isa ta haifi kamar yarinyar nan.

Mikewa yai ya nufi gurin fridge dinsa, budewa yai ya dakko ice cream ya nufi gurin Mimi da shi, Zama yai shima akan kujera yace "zo musha Ice cream"

Washe baki tai ta matso kusa dashi ta zauna tace "Ina sonsa sosai Uncle"

Murmushi yai yace "what's ur name beauty?"

Debo ice cream dn tai a spoon tana kaiwa baki Saida ta shanye sannan tace "My name is Khadija B"

Kallon ta yai yace "meye ma'anar B din?"

Cikin rashin damuwa tace "sunan Maa ne Batul"

Cikin mamaki yace "me yasa baki sa sunan Daddy dinki ba?"

Tabe baki tai tana lasar lips dinta tace *Maa ce ta samin bansan sunan Daddy naba"

Shiru kawai yai don baya so ya takura yarinyar da tambaya ahakan ma yaga kokarin ta da alama tana da wayo sosai.

Shan ice cream din suka cigaba suna sha tana basa labarin school dinsu da friends dinta, biye mata yai sosai yake Jin kaunar yarinya tana ratsa shi, shi sam baya Wasa da yara ko zama a kusa da su bayayi a cewar sa ciwon kai suke sashi sai gashi ya zauna yana hira da yarinya.

Sosai ta sake dashi don ta gama basa labarin kowa na gidan su hadda yadda Maa dinta take da cin abinci sosai, har labarin Hidaya sai da ta fada masa da maman ta.

Kallon ta yai yace "ynxu Maa din taki baxa ta siya miki wani babyn ba ki dinga wasa"

Marairaice fuska tai tana kalar tace haka tace "Uncle wai baxa ta siyo min ba ai maman hidaya ta siyo mana, kuma ni na fison ita ta siyo min mu dinga kwana tare dukkan mu"

Rike haba yai yace "gaskia MAA bata kyauta ba zan lallashe ta amma ta siyo miki wani babyn koh?"

Tsalle tai tace "thank you uncle"

Jan kumatun ta yai yace "ki daina cemin uncle ni Daddy dinki ne tunda kince baki da Daddy"

Ware manyan idonta tai tace "da gaske Uncle Ka zama daddy na?"

Daga mata kai yai yana karantar farin cikin dake dauke a fuskar ta

Murmushi tai tana tsalle tace "toh Daddy kazo school dinmu nima na nunawa friends dina kai nace musu ga Daddy na su daina cewa banda Daddy."

Mikewa yai yace "zanzo har school din naku Beatty nace musu nine daddyn ki"

Rungume sa tai tana murna rike Mata hannu yai suka fita don yasan ynxu haka sun fito daga lecture din duk da baya jin zai iya bata Mimi ynxu sam baya son rabuwa da yarinyar haka kurin yake Jin son kasancewa da ita, hakan yana sashi tsintar kansa cikin farin ciki.

Cafeteria suka nufa duk inda suka wuce binsu ake da kallo kawai bama ynxu da mutane sosai suka fito, ko a jikin sa da yadda ake kallon su don shi baya son shirme.

Kaita yai ta zabi abinda take so bayan ya jido Mata ice cream da chocolate a leda, sosai ta ci abincin da aka kawo mata don tana ganin kaza tace masa ita take so, fried rice da kaza ya karbo mata sai ruwa, zuba mata ido yai yana kallon ta tana cin abincin ta cikin nutsuwa.

Daukar wayar sa yai kawai ya shiga mata hoto sai style take masa tana turo baki suna yi suna dariya, duk students din da suke gurin kallon su suke suna mamakin dama Mr Azlan yana Wasa da dariya haka.....


**********

Hawayena na goge na kalli Asma'u nace "kina gani har ynxu yaki dawo min da yarinya ta fa Asma'u"

Dafa ni Asma'u tai tace "ki taso muje office din nasa toh mu duba mu gani, amma dama ya san kune?"

Girgiza kai nai cikin nadamar zuwa da Mimi nace "ina fa ya san mu kawai kalan dangi ne ni ban taba ganin Saba ma Sai a school dinnan"

Rike habar ta tai tace "amma wai baki ganin kamar Mimi da Mr Azlan kuwa?"

Hade rai nai nace "ki daina yada min yarinya da Mr Wicked fah Asma'u ba abinda ya hada su"

Dariya Asma'u tai ta mike tace "muje toh mu dubo su toh Maman Mimi"

Mikewa nai ina rataya jakata a kafada nace "yau Mai rabani da Mimi sai Allah wallahi tana ji fa ina mata magana amma tai min banxa ta bisa sbd ta raina ni ba"

Ita dai Asma'u bata ce komai ba sai murmushi da tai kawai, office dinsa muka nufa nan muka yita knocking amma a banxa ba a amsa mana ba, wani student ne dake zaune daga gefe yace "baya nan fah"

Da sauri nace "ina yaje don Allah?"

Sai da ya dan kalle mu na seconds Sannan yace "kamar cafeteria ya nufa shida wata yarinya"

Da sauri nace "mun gode"

Hannun Asma'u na janyo mukai gaba, muna shiga cafeteria kuwa idona ya sauka akan su ga Mimi da gabanta ke shake da plate tana cin kaza shi kuma yana daukar ta hoto a wayar sa sai dariya Mimi take shi kuma yana murmushi.

Raina naji ya Kara baci hakan yasa na karasa gurin su ina huci, Mimi da ta kai cinyar kaza bakinta tana murmushi dago idon ta tai muka hada ido da sauri ta ajiye kazar ta mike tsaye tana mar mar da ido alamun rashin gaskia............


Comments Nd share plz


Mrs A.M🥰

[26/08, 19:05] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️

*TASWIRAR KADDARA*

♠️♠️♠️♠️♠️


Written by
Mrs A.M🥰

Page 19


*BABY BEAUTY LOUNGE*

*INA YAN GAYUN SUKE MASU BUKATAR GYARAN JIKI, HENNA BLACK AND RED, PEDICURE AND MANICURE, MAKEUP, SALON KU GARZAYO ZUWA BABY BEAUTY LOUNGE DOMIN SAMUN DUKKAN WANNAN ABUBUWAN, HAKIKA GYARA SHINE MACE KUMA KO WACCE MACE YAR ADO DA KWALLIYA CE*

*INA MASU BUKATAR KOYAR MAKEUP DA SALON DUK MUNA YI A BABY BEAUTY LOUNGE CIKIN FARASHI MAI RAHUSA ZAKU SAME MU A TUDUN MALIKI TITIN ALASURE NO.995*

PHONE NUMBER 08183462148 OR 07058457638

*MUNA SIYAR DA MAGUNGUNAN MATA DANA MALLAKA DUK A BABY BEAUTY LOUNGE*

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Hade rai nai nace "wuce mu tafi"

Juyawa Mimi tai ta kalli Azlan da ya nade hannun sa yana kallon su kamar ya samu TV sai kuma ta juyo ta kalle ni kamar zatai kuka tace "Maa bamu gama magana da Daddy bafa"

Zaro idona nai bansan lokacin dana ce kuttt***** cikin bacin rai nace "ta ina ya zama daddyn naki"

Da sauri Mimi ta koma jikin sa ta rungume sa sbd yadda nayi zagin da kuma yadda nai mata magana ba karamin tsoro ya bata ba.

Hade rai Azlan yai yana kankance idonsa yace "kar ki sake yiwa yarinya ta ihu haka bare ki kai ga zagi"

Kallon sa nai sai na juya na kalli Asma'u kawai na fashe da kuka cikin kuka nace "Asma'u kina ji wai yarinyar sa banda kalan dangi ina Shi ina Mimi wallahi ba abinda suka hada dashi."

Kallon ta kawai yake yana kokarin controling kansa kar yai dariya lallai yarinyar nan, sbd kawai yace wa Mimi yarinyar sa shine take kuka wani Murmushin mugunta ya saki ya janyo Mimi sosai jikinsa yace "yarinyar Daddy kar kiyi kuka kinji zo mu tafi"

Daga masa kai tai tana satar kallo na sai boye fuskar ta take a jikinsa sbd kar mu hada ido, binsu da kallo nai har suka fita daga cafeteria din suna rike da hannun juna.

Zama nai akan kujerar da Mimi ta tashi na dora kaina a jikin table din ina sake fashewa da kukan bakin ciki, yau nice Mimi take kallo ina kuka amma ko ta tsaya Mimin da In taga raina ya baci hankalin ya yake tashi ko Umma ce tai min fada Mimi bata sake yiwa Umma magana ta dinga fushi da ita knn sai gashi tana kallo ina kuka da hawaye amma tabi wani Wanda bata San sa ba sai yau dole nai kuka ai.

Dafa ni Asma'u tai tace "kiyi hakuri mana Batul sai kace wata yarinya kin zauna kina kuka kinga da duk mutane kallon ki suke".

Girgiza kaina na shiga yi ina fadin "baxa ki gane halin da nake ciki ba Asma'u, yau ni Mimi zata tozarta don ubanta"

Zaro ido Asma'u tai tace "ynxu ita Mimin kike zaga"

A fusace na mike nace "na zage tan kuma wallahi har dukan ta zanyi in mun koma gida don ubanta."

Kama haba Asma'u tai tana jinjina lamarin lallai abin yai tsamari tunda batul ya bude baki ta zagi Mimi, mikewa nai na share fuskata muka fito daga cafeterian.

Kallona Asma'u tai tace "ina muka nufa ynxu"

Cikin fushin da har ynxu yaki sauka nace "office din Mr Wicked zamu, don ni ban yadda dashi ba gaba daya kina gani fa ko ke Mimi bata sake dake ba har ynxu amma daga haduwa da wannan mugun lecturen har tana ce masa dadi," hawaye na share ina gyada kaina kawai.

Ita kam Asma'u ynxu abin dariya ma yake bata, Shiru tai kawai don ta kula a yadda Batul take in ta matsa ita kan ta sai ta zage ta.

Jamim hijab akai da karfi Wanda har saida Hijab din ya sauka daga kaina ya dawo kafada saukin tama ina da hula akai amma itama hular sai da tayi baya sosai gaban gashina ya bayyana.

A hankali na juyo ina hadiyar zuciya sbd wani turiri dana ji kirjina yana min, Zuby CE tsaye ita da kawayen ta wani mugun kallo na zuba mata nace "sakar min Hijab"

Sakin Hijab din tai tana wani yatsina fuska tace "zuwa nai na Miki gargadi wannan ya zama na farko kuma na karshe da zaki dinga shiga harkar Mr Azlan, don na kula kin cika rashin kamun Kai sai tusa kanki kike garesa sbd yace yana sonki toh kwalelen ki yafi karfin ki."

Kallon ta kawai nake ina tauna lips dina, ganin nai mata banza yasa Nana fadin "bada ke ake magana ba yar rainin hankali kawai sbd kin raina mutane suna maki magana kina musu banxa"

Zuby ce ta cafe da fadin "bar yar iska ashe ma matar aure ce shine sbd rashin kamun Kai take makale wa wani daban, har da makala masa shegiar yarr...... " Kasa karasawa tai sbd wani zazzafan mari dana shinfida mata a fuska.

Zaro ido Asma'u tai tana kallona don bata san lokacin dana yi tsalle na koma gaban Zuby ba kawai karar marin taji.

Nana da Hafsa ma bude baki sukai suna kallona ku kalle ni su kalli Zuby data dafe kunci tana kallona.

Cikin bacin rai ta bude baki tace "ni kika mara"

Takowa nai har gabanta nace "an mare ki ko zaki rama ne ehe karamar yar iska, kar kiga ina miki shiru ki dauka ko ina Jin tsoron kine kawai ina yin shiru ne don baki kai matsayin da zan tsaya ina sa'in sa dake ba ni nasan darajar kaina."

Numfashi na sauke na dan juya na kalli yadda aka samu a tsakiya ana kallon mu, dan tabe baki nai nace "ki kiyaye zagar min yarinya zaki iya min komai na kyale ki amma banda zagar min ya, sannan Shi malamin da kike magana akan sa ke ya dama ni bays gabana don ba wannan nazo yi makaranta ba.."

Juyawa nai na kalli Nana nace "amma dai kinyi asara sbd kwadayi kullum kina tare da wannan kafa da kafa sbd abin duniya Allah ya kyauta, sannan kar ki kara sani a shirmen ki don ni ba sa'ar ki bace"

Janyo hannun Asma'u nai muka juya don na fasa ma zuwa office din nasa tunda akan sa ake min wannan wulakancin aikin banxa kawai na fada a fili ina Zama a kan kujera.

Ban Kara waiwayar su Mimi ba sai da muka gama lecturen mu 4 bayan munyi sallah sannan muka nufi office din sa nida Asma'u ina mitar ynxu in naje karbar yarinya ta ya hanani mana in ya isa..

Knocking nai ba tare dana tsaya jiran aban izinin shiga ba na tura kaina kawai, suna zaune akan doguwar kujera sun dukufa suna kallon wayar sa da dukkan alamu game suke sai dariya suke su biyu sam basu ji shigowar mu ba.

Nida Asma'u kasa karasowa cikin office din mukai muka zuba musu ido, gabana ba abinda yake sai faduwa har yanayin dariyar su iri daya da yanayin dimple dinsu na gefen kumatun dama, lumshe ido na nai ina ambaton sunan Allah.

Dagowa yai ya kalle mu sai ya hade rai, muna hada ido da shi na falla masa katuwar harara na murguda masa baki ina kauda kaina gefe.

Lasar lip dinsa kawai yai ya kalli Mimi da ta kara kwanciya a jikinsa tana kallona, sbd ita kanta hararar na ke Mata.

Cikin kausasa murya nace "tashi kizo mu wuce tun kafin ki gama kaini bango"

Mikewa tai tana kallon sa rungume sa tai tace "bye Daddy"

Kallon ta kawai yai ya kasa magana ji yake kamar ya hanata tafiya amma yasan bashi da wannan damar, lumshe ido kawai yai yana taunar lips dinsa.

Ina janyo hannun Mimin sai da na saki wata ajiyar zuciya sannan na dube sa nasan zai jini hakan yasa ni fadin "kuma wallahi a dinga sa tsoron Allah a cikin lamuran rayuwa a daina kwacewa iyaye yaran su."

Banxa yai mata don bashi da lokacin tanka mata, shidai abinda ya sani kawai baya Jin zai iya kwanaki ba tare da ya kuma haduwa da Mimi ba, haka kurin Allah ya dora masa kaunar ta a cikin zuciyar sa.

Fitowa mukai daga office din ko magana ban yiwa Mimi ba don itama sunkuyar da kanta tai taki yadda ta dago mu hada ido, sallama nai wa Asma'u muka hau adaidaitar dana tsayar.

Ban ce mata uffan ba Saida muka isa gida, nan na zauna na zayya nawa Umma komai, abinda na boye mata kawai kamar da suke da juna.

Tagumi Umma tai ta kalli Mimi tace "mai yasa kikai haka uhm Mimi"

Hawayen ta take sharewa tace "baxan sake ba Umma Allah ki bawa Maa hakuri"

Tsaki nai na galla mata harara na mike daga gurn na shige daki, tana ganin na bar gurin Umma ta rungumo ta jikin ta tace "ban labari mai dame Daddyn naki ya baki"

Washe baki tai ta shiga bawa Umma labarin yadda Daddyn ta ya dinga lallaba ta yana bata chocolate.

Dariya tai tace "Umma har kasa ya siyo min katuwa, kuma yace zai ge school dinmu yace shine daddy na"

Murmushi Umma tai hankalin ta yana kwanciya daga bayanin da Mimi take Mata ta gane ko waye wannan Daddyn nata yana sonta sosai, amma kuma meye dalilin dayasa Batul bata sonsa.

Tashi tai kawai ta shiga kitchen ta bar Mimi agun tana wasa.

Sam kin sakar mata fuska nai har muka zo kwanciya, duk da hakan yana damuna amma na maze don so nake ko gaba in suka kara haduwa taki yadda dashi duk a bana fatan su sake haduwar ma.

Mirginowa Mimi tai ta rungume ni tace "Maa kiyi hakuri baxan sake ba Maa, dama sbd yace Shi Daddy nane shiyasa nake ta murna Nima na sami Daddy kuma yace zai je school dinmu yace shine daddy na sbd yan class dinmu su daina cewa banda Daddy"

Rintse idona nai sai kuma tausayin ta ya kamani, a hankali na rungume ta nima ina shafa kanta nace "shiknn Daughter amma kar ki sake yadda kije gunsa kinji"

Daga min kai tai ta rufe idon ta, ni kuwa tunani na shiga yi kawai sai da tayi bacci na mike a hankali na kunna fitilar dakin dana kashe, juyawa nai na kalli Aisha ganin bacci take na dan sauke ajiyar zuciya.

Wardrobe na bude na dauko wata jakata da ta dade sosai a hankali na bude jakar hannu na zura cikin karamin zip din na zaro wani kyakkyawan bracelet na Maza mai kyau, walwalin da yake ne zai nuna ma na gold ne.

Warwarw Shi nai na kura masa ido shine kadai abinda nake da shi mallakin baban Mimi, sai dai bansan ta yadda abin zai kaini gare sa ba Kura masa ido nai sosai ganin rubuta karami mai kyau a jiki, cikin rawar jiki na kara Kura masa ido gabana yana faduwa zaro ido nai ganin ansa *AJ* Shiru nai ina tunanin Mai hakan yake nufi ganin ba mai bani amsa yasa na mike kawai na maida jakar Inda na dauko ta Shi kuma bracelet din na wulla cikin jakata ta makaranta.

Kwanciya nai Nima ina addu'ar bacci, ban dade da kwanciya ba bacci ya dauke ni......


Comments Nd share plz


Mrs A.M🥰
[28/08, 19:03] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️

*TASWIRAR KADDARA*

♠️♠️♠️♠️♠️


Written by
Mrs A.M🥰

Page 20


*BABY BEAUTY LOUNGE*

*INA YAN GAYUN SUKE MASU BUKATAR GYARAN JIKI, HENNA BLACK AND RED, PEDICURE AND MANICURE, MAKEUP, SALON KU GARZAYO ZUWA BABY BEAUTY LOUNGE DOMIN SAMUN DUKKAN WANNAN ABUBUWAN, HAKIKA GYARA SHINE MACE KUMA KO WACCE MACE YAR ADO DA KWALLIYA CE*

*INA MASU BUKATAR KOYAR MAKEUP DA SALON DUK MUNA YI A BABY BEAUTY LOUNGE CIKIN FARASHI MAI RAHUSA ZAKU SAME MU A TUDUN MALIKI TITIN ALASURE NO.995*

PHONE NUMBER 08183462148 OR 07058457638

*MUNA SIYAR DA MAGUNGUNAN MATA DANA MALLAKA DUK A BABY BEAUTY LOUNGE*

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Washe gari ina kallon yadda Mimi take kallona ina shirin tafiya makaranta nai mata banxa don na gane mai take nufi wato na tafi da ita, da yake kuma tasan tai min ba dai dai ba bata fito kuri ta fada min manufar zagayen da take ba.

Sallama nai wa Umma na fita ina jaddada wa Aisha kar ta sake ta cimin kudin ciniki nada ake yi in na tafi makaranta.

Ban sha wahalar samun abin hawa ba, ko dan na fito da wuri ne ban sani ba.

Ina zuwa makaranta hall din da muke da lecture kawai na nufa don ban duba littafina ba jiya sbd takaicin da Mr Wicked ya kunsa min Shi da Mimi.

Ina zaune Asma'u ta shigo itama zama tai a gefena tana fadin "wash Allah na"

Dan Kallon ta nai nace "badai kin gaji ba wai"

Lumshe idonta tai tace "wallahi baki ji kafafuna ba kamar an min duka, ni da cewa nai ma baxan xo ba sai da Hubby ya lallabani"

Kallon ta nai nace "Anya kuwa Asma'u ke kadai ce kodai kodai" na karashe ina fashe wa da dariya

Harara ta tai tace "kodai me ban gane mai kike nufi ba"

Juyawa nai ina dariya nace "wa ya sani ko an kusa yiwa Mimi kani ko kanwa"

Dundu Asma'u ta sakar mu muka shiga dariya anan take fada min ciki ne da ita wata biyu knn, sosai nai mata murna don ni kaina sai na shiga lallabata ina tambayar ta mai take so na flour nai Mata na kawo mata gobe.


Cikin lokaci kan kani karatu ya dau zafi don sati mai zuwa zamu fara exam din first semester shiyasa gaba daya mun xama busy, karatu kawai muke sosai.

Mr Wicked kuwa bama haduwa da shi sai dai ko a class shima bana yadda mu hada ido da shi.


***********

Dan bude idonsa yai Jin maganar Baffa, a hankali ya mike daga kwancen da yake ya kalli Baffa daya zuba masa ido yana jiran ansar sa.

Ganin ya ki magana yasa Baffa Kara fadin" Mai ke damun kane Zaki? Ina lura da kai gaba daya ynxu Ka chanja kamar wani Abu na damun Ka."

Ajiyar zuciya ya sauke yana lumshe idonsa gaba daya baya Jin dadin rayuwar ne, ko mai yake tunanin Mimi yake tun ranar daya ganta Allah ya dora masa kaunar yarinyar ji yake tabbas suna da wata alaka Mai karfi tsakanin sa da ita, amma ya rasa tame har mafarkin ta yake tana Kiran sa da Daddy yazo suyi wasa.

A hankali ya bude idonsa ya zuba wa Baffa yace "tunanin wata yarinya ne yake damuna"

Zaro ido Baffa yai yace "wata yarinya ce haka tai nasarar damkar zuciyar ka da karfi haka har tunanin ta yake damun Ka"

Dan yamutsa fuska yai yana murza idonsa da bai Sawa kwalli ba yau yace "Kaga tsoho bana son Vawulence, karamar yarinya ce fa shekarar ta hudu."

Kallon sa Baffa yai yana gyara zama yace "yar shekara hudu kuma kake so zaki mun shiga uku"

Hade rai yai sosai yace "Yarinya tace fah kake cewa ina son ta Baffa, ina sonta mana amma ba irin Wanda kake tunanin ba"

Cikin rashin fahimta Baffa yace "ban gane yarinyar Kaba yimin bayani."

Lasar lip dinsa yai yana shafa gemun sa yace "kana ji tsoho a cewar student dina wai yar tace ita ta haife ta ni kuma gaskia ban yadda ba don basa ma kama?"

Kallon sa Baffa yai ganin yai shiru yace "ina jin Ka mana"

Wani shegen murmushi yai yana shafa gemun sa yace "Yarinya dani take kama kamar nayi kaki baka ganta ba har dimple dinta irin nawa ne, har shape din kafar mu."

Mikewa Baffa yai ya nufi gurin da Azlan yake hannun sa yasa a wuyan Azlan ya taba sai ya kalle sa yace "kuma gashi jikin Ka ba zafi bare nace zafin zazzabi ne yake damunka."

Dan hade rai Azlan yai ya zaro wayar sa gallery ya shiga ya nemo pics din daya musu shida Mimi, mikawa Baffa yai yace "kalla toh"

Karbar wayar Baffa yai ya zubawa Hoton ido salati ya saki sai ya kalli hoton ya juya ya kalli Azlan, wuce wa yai ya zuba ma wani wanda Azlan yai mata ita kadai ta ware ido ta tsuke baki, gabansa ne ya fadi sbd yadda tai kamar Azlan da yana yaro tabbas Yarinyar kamar Azlan yai kaki.

Duk da kamar Azlan da Junaid daya amma suna da banbancin Shi Junaid fari ne Azlan kuma Ja ne sannan Shi Junaid Dimple duka kumatun sa yake da sabanin Azlan da yake da na gefen kumatun dama kadai, sannan shape din idon Suma ya banbanta na Junaid manyan ido ne dashi Azlan kuma sexy eyes ne dashi shiyasa bai cika bude suba kusan kullum in zai kalli mutum sai ya kankance ido, yarinyar ya sake kalla kamar ta daya sak da Azlan ba inda ta baro sa komai irin nasa ne har yanayin murmushin su.

Ajiyar zuciya Baffa ya sauke ya Kalli Azlan yace ikon Allah kamar ta baci fah zaki

Shima ajiyar zuciya ya sauke yace "wallahi tsoho so daya na ganta amma tunda na ganta na rasa nutsuwa ta nidai yarinyar nan ina ji a jikina jini nace amma bansan ta ina ba kuma nidai ina tattalin budurwarcina bare nace ko na danne wata ne"

Dan tsaki Baffa yai yace "meye kuma haka ana zancen Arziki Ka kawo zancen budurci"

Kankance ido yai yace "ai dole nayi haka tsoho baka ga kamannina da yarinyar bane, ni fa badan badan ba da sai na fara xargin budurcina anya baxan je asibiti a duba min lafiyar sa ba kuwa"

Salati Baffa ya saki hakan yasa Azlan fashewa da dariya yana kashe wa Baffa ido daya.

Shiru sukai kafin Azlan yace "kuma tace min bata da Daddy mamanta tace Mata daddyn ta ya mutu amma kuma bata san sunan dadyn nata ba, shiysa kawai nasa ma Yarinyar question mark"

Baffa ne yace "A'a Zaki badai kasan maman yarinyar ba kawai inaga kamanni ne zuka zo daya"

Shiru kawai Azlan yai kansa Yana masa ciwo, amma shifa gaskia bai yadda beauty dinsa yar wannan mara kunyar bacee.....


**********

Cikin nutsuwa Samira take takowa tasha kayan baccin ta masu daukar hankali sai zuba kamshi take, a hankali take tafiya har ta iso bayan kujerar da Junaid yake zaune baisan ta iso ba sbd yadda gaba daya hankalin sa yake kan wayar sa.

Zuro fuskar ta tai ta leka wayar tasa ganin pic din babies kawai yake kalla, idonta ne ya soma Tara kwalla da sauri tasa hannu ya goge su, zagayo wa tai ta gaban sa ta dauke wayar hannun sa da sauri ya dago ya kalle ta yana sakin ajiyar zuciya.

Dan hade rai tai tace "haba Noor ban hanaka sawa kanka damuwa ba ynxu in wani ciwon ya kamaka fa, Ka kwantar da hankalin ka insha Allah komai zai warware lokaci ne kawai."

Kallon ta yake cikin tausayin ta dake kwance a idonsa ya janyo ta jikin sa ya rungume yana lumshe idonsa yace "Noor ina son ganin gudan jini na dake nima, yau naji ana cemin Baba amma sai naji kamar baxan taba samun wannan damar BA"

Da sauri Samira ta sa hannu ta rufe masa baki tace "don Allah kayi shiru Noor kar na sake jin wannan maganr daka bakin Ka bana so komai mai wuce wane kuma lokaci ne ka Kwantar da hankalin ka."

Daga mata kai yai yana sake rungume ta sosai, yana son Samira don mace ce ta gari, yar kanwar Mamin suce tun tana karama yake sonta shiyasa itama ta girma da sonsa bai bata damar Kula ko wanne saurayi ba bayan shi, kuma tunda iyayen su dama sunsan da son junan da suke shiyasa Koda ya nunawa Abie yana so a masa aure yana da shekara 28 Abba bai wani damu ba tunda lokacin ya fara aiki kuma ya kai minzalin aure, Azlan ne dai ba yadda baiyi da shida shima ya samo Mata a musu aure lokaci daya amma sai ya ce masa budurcin sa bai nuna ba tukun...


***********

Alhamdulillah cikin Amincin Allah mun fara exam gaba daya banda lokacin kaina don karatu kawai nake yi, ko a gida bana wani biyewa Aisha ko Mimi kullum ina daki da paper ina karatu, har tsokana ta Umma take wai na sassauta wa kaina.

Cikin sati biyu muka gama exam dinmu sai dai fatan Allah yasa result yai kyau.

Kamar yadda class rep dinmu yace washe garin ranar da aka gama exam muje mu karbi test din Mr Wicked, badon Asma'u baza taje ba sbd bata Jin dadi da ba abinda zai sani zuwa amma dole naje na karbo mana ni da ita.

Shiryawa nai cikin doguwar rigar atampa na dora hijab iya gwiwa light pink ban shafa komai ba amma nayi kyau, bama yadda hancina ya kara tsayi sbd ramar da nayi.

Mimi dake kallona tace "Maa plz zan raka ki kinji"

Kallon ta nai kamar zanyi magana kawai kuma sai na ce zo mu tafi don nasan ba lallai mu hadu da Mr Wicked ba kuma ko mun hadu ai na dade wa zanba.

Jaka ta na dauka na chanja wa Mimi Kaya zuwa wata riga da wando na English wear sai hula dana samata tayi kyau sosai kamar ka sace ta, dafa kanta nai na Mata addu'a, juyawa nai nace "Umma mun tafi baxa mu dade ba Insha Allah"

Aisha ce ta fito daga daki itama sanye da Hijab tace "don Allah Ya Batul Nima zan raka ku yau dai naga ya university take."

Na bude baki zanyi magana Umma tace "ku tafi tare mana Batul"

Daga kai nai ina maka ma Aisha harara, dariya tai tana riko hannun Mimi sallama mukai wa Umma muka fito.

A bakin titi muka samu adaidaita, muna zuwa makarantar hall din da class rep dn yace azo a karbi test din muka nufa sai suruta Aisha take min tana fadin "Nima na matsu nayi na gama secondary dinnan Ya batul wallahi"

Tabe baki nai nace "meye na sauri ki nutsu ma ina fada Miki, ni baki ga yadda na rame ba"

Dariya tai tace"duk da haka wallahi Allah ma ya taimake ni Abba ya yadda nai jamb a SS 2"

Dariya nai nace "yarinya zaki gane kuren ki ne"

Muna hira har muka isa hall din, bamu dade ba na karbo mana nida Asma'u jakata na bude nasa, tsautsayi garin zuge zip din ya balle tsaki nai ina gyara zaman lafia ciki yadda baxa zu zube ba.

Mun iso daidai gurin da ake parking motoci idon Mimi ya sauka akan Azlan da yake sauri ya shiga ya tafi kasancewar family meeting suke kuma sai da Abie yai masa magana akan in ya kuskura yaki zuwa zasu hadu ne shiyasa yake sauri ya tafi dama Abu ya shigo dauka.

Cire hannun ta daga na Aisha tai ta kwasa da gudu ta nufi gurin sa tana fadin "Daddy oyoyo"

Wani irin faduwa gabana yai daidai lokacin daya juyo yana ganin Mimi ya bude Mata hannu da sauri, fadawa jikin sa tai a tare suka sauke ajiyar zuciya.

Dago da fuskar ta yai yace "Beauty na nayi missing dinki sosai"

Itama shagwaba fuska tai tace "Nima nayi missing dinka Daddy kullum sai na fadawa yan school dinmu nayi sabon daddy amma sai suce karya nake yi"

Shafa kanta yai yace "kyale su zanje har school din naku ai kina lafia"

Murmushi tai tace "eh Daddy kullum In nayi wa Maa maganar ka sai tace na daina mata maganar ka in ba haka ba saita Zane ni"

Zaro idonsa yai yace "ta zane min ke"

Dariya tai har hakworan ta na bayyana tace "ai ba duka na zatai ba Daddy, Maa bata duka na"

Shima murmushin yai mata yana jan kumatun ta.

Aisha data yi mutuwar tsaye cikin rawar baki tace "Ya Batul Mai nake gani waye wancen mai kama da Mimin mu"

Banxa nai Mata na nufi gurin su raina yana baci bansan wata masifa ke damun Mimi ba da inhar taga Mutumin nan take manta wa dani.

Azlan da yana ganin tahowar batul ya bude motar ya sa batul a gaba ya zagaya shima ya shiga driver sit hadi da kunna motar.

Cikin tashin hankali na shiga ihu ina fadin a taimaka min zai gudar min da yarinya ganin ba mutane a gurin gashi reverse yake hakan yasa ni janyo hannun Aisha na bude back sit na tura ta ciki nima na shiga.

Ihu nake masa a motar ina fadin ya bude mu mu fita amma yamin banxa kamar bana Jin sa, Mimi kuwa tuni ta sunkuya a kasa don kar na dake ta kuka kawai nake ina fadin "wallahi Ka bude mu in ba haka ba sai na kaika Kara police station"

Bai tsaya ko ina ba sai a compound din gidan baffa yana tsayawa ya zagayo ya bude ma Mimi kofa ya dauke ta cak ya nufi palourn baffa, da gudu ma mara masa baya ina fadin "baxa ka tsaya ba"

Da kafar sa ya tura kofar ya shiga duk juyowa mutanen palourn sukai suka zuba masa ido sauke Mimi yai yana sauke numfashi.

Da sauri Baffa, Abie, Uncle Mustapha, Mami, Mummy, Mama, Aunty Sarah sai Junaid suka mike tsaye cikin rudewa ganin Mimi tsaye tana kallon su itama sai kuma ta rungume Azlan tana fadin "Daddy tsoro nake ji"

Da sauri nace "a gidan ubanki ya zama Daddyn naki Mimi"

A fusace Azlan ya juyo ya kalle ni yace "ban hanaki zagar min yarinya ba"

Fashewa na sake yi da kuka nace wallahi ba yarinyar Ka bace kuma Baxa ta taba Zama ba har abada.........


Comments Nd share plz


Mrs A.M🥰

[29/08, 18:53] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️

*TASWIRAR KADDARA*

♠️♠️♠️♠️♠️


Written by
Mrs A.M🥰

Page 21

*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃


*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*

*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*


*LOCATION KANO*

08062073990

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Shiru nai ganin manyan mutane a Palourn, sunkuyar da kai na nayi ina goge hawayen fuska ta.

Baffa ne yace "zo kinji jikata shigo ciki ba Wanda zai rabaki da yarinyar ki."

Ajiyar zuciya na sauke haka kurin naji maganar tsohon ta ratsani, hannun Aisha na rike sosai muka shigo cikin palourn tsugunna wa mukai muka gaishe su, komawa gefe nai na tsaya ina kallon Mimi dake kare boye fuskar ta a jikin sa.

Abie ne ya kalle ni yace "ku zauna kunji"

Gefen carpet din muka samu muka zauna nidai banda ajiyar zuciya ba abinda nake yi, ina auna yadda zanyi kuli kuli da Mimi yau don ta kaini karshe sosai.

Kallona Abie yai yace meye hadin ki da Azlan diyata

Fashewa nai da kuka nace "ba abinda nai wa Mr Wicked wallahi, haka kurin ya takura min ya tsane ni so daya na taba zuwa da yarinya ta ya dauke ta ya tafi da ita office yana nuna min fin karfi akan ta, ynxu kuma tsautsayi na sake zuwa da ita shine kawai yasa ta a mota, da badan mun shiga motar ba tafiya zaiyi da ita."

Duk mutanen palourn zuba min ido sukai suna kallona Jin sunan da na Kira Azlan dashi.

Da mamaki Azlan yake maimaita Mr Wicked a ransa, kasa rike wa yai sai da yace "Ke nine Mr Wicked din?"

Harara na galla masa ina murguda baki sannan na juya idona nace "kai ne mana da waye toh"

Baki ya bude yace "Ke ni sa'an kine naga alama kin raina ni wallahi"

Tabe baki nai ina juyar da kaina gefe nace "waye yace ka sace min yarinya"


Murmushi kawai Baffa yake yana kallon su wani abu na darsuwa a ransa, tabbas wannan yarinyar ita ce daidai Azlan da alama ba karamin drama zasu nayi ba.

Mummy ce da tunda suka shigo ta kalli gabanta yake faduwa tace "ke baki da kunya kike ce masa Mr Wicked"

Sunkuyar da kaina kawai nai ina Kara damke jakata, don ni ba Zama ne ya kawo ni ba ana miko min yarinya ta Zan kama gabana.

Baffa ne ya daga mata hannu ya kalle ni yace "jikata meye sunan ki"

Dan dagowa nai na kalle sa sannan na sunkuyar da kaina kasa a hankali nace "Batul"

Murmushi Baffa yai ya kalli Aisha da tunda muka shigo kanta yake kasa gaba daya ta rasa ma tunanin mai xatai, da farko kamannin da Mimi take da Azlan ne ya kusa sata karamin hauka don brain dinta dena aiki yai sai dai kuma lokacin da suka shigo idonta ya sauka akan Junaid Wanda Batul bata lura da shi ba shine abin ya rikita ta.

Maganar Baffa dake tambayar ta sunan tane ya dawo da ita daga tunanin da take, Dan Murmushi tai nai kama da yake tace Aisha.

Mai da kallon sa gun Batul Baffa yai yaga sai aunawa Mimi dake jikin Azlan harara take, girgiza kai yai yana murmushi yau ga wacce tafi jikansa tijara, gyaran murya Baffa yafara yi yace "ina mahaifin yarinyar nan yake Batul"

Da sauri na dago kai na kalle sa, ganin kallon da nai masa yasa baffa gyara maganar sa gurin cewa "ina nufin Ya sunan mahaifin ta, a yadda zaki ya ban labari yarinyar tace masa bata da baba bata son sunan saba ma."

Turo baki nai a raina ina fadin meye za'a tisani ana tambaya ta mahaifin yarinya ta, amma sbd girman mutumin daya mun tambayar yasa ni "fadin Ya rasu"

Dan tsura min ido Baffa yai a hankali yace "Allah ya jikansa," ba dab ya yadda da abinda tace ba.

Mami kuwa tunda suka shigo ta zuba wa Mimi ido tana kallon ta kamar su daya da Azlan lokacin da yana yaro sai kallon ta take daga sama har kasa.

Mama ma dai itama tunanin yadda yarinyar take kama da Azlan take, a zuciyar ta kuwa fara take a ce yarinyar Azlan ce ko ya daina damunsu da zancen budurci.

Mike wa Azlan yai ya janyo hannun Mimi, da sauri na mike nima har ina neman faduwa nayi sauri na rike dayan hannun Mimin.

Kallon sa nai nace "Ka cika min yarinya ta wallahi ba abinda kuka hada kai da ita kuma baxa ku taba hadawa ba Insha Allah"

Zuba min ido yai yace "zaki sake ta ko kuwa."

Zare masa ido nai kamar na wani yarona nace" baxan sake ta ba sakar min yarinya ta," kallon Mimi nai ina hawaye nace "Mimi ni zaki yiwa haka koh Maa dinki kike gudu koh Mimi"

Fashewa da Kuka tai ta juya ta kalli Azlan sai ta juyo ta kalle ni tace "Maa kiyi hakuri baxan sake ba"

Girgiza kai nai nace "sakar masa hannu toh Mimi, sake shi kizo mu tafi gida ba Saida na miki fada ba akan ba ruwanki da shi Mimi amma ynxu baki jin magana ta koh kin manta wace ni Maa ce fah"

Fashewa Mimi ta sake yi da kuka da ihu tana fadin "kiyi hakuri Maa, juyawa tai ta kalli Azlan tace sake ni Daddy zan tafi gurin MAA dita"

Tsawa na daka mata nace "baxa ki daina ce masa Daddy ba, a ta ina ya zama daddy wai me yasa kike so ki dinga bata min rai ne"

Yarfe hannu take tana kuka jikin ta yana rawa don yadda nake mata magana tasan da kyar in baxan dake taba, tsugunna wa Azlan yai ya rungume ta yana shafa bayanta kallona yai yace "baxa ki daina yiwa yarinya ta ihu ba"

Hannun mimi na saki na juya na kalli Baffa ina hawaye nace "kana ji yana cewa yarinyar sa wallahi na yar sa bace"

Sudai su Baffa ido kawai suka zuba mana suna kallon mu, da alama kowa baya son saduda akan yarinyar.

Sungumar Mimi Azlan yai zai fita ban san lokacin dana janyo masa riga ba nace "sauke min ita don Allah kayi hakuri baxan sake maka rashin kunya ba Allah kayi hakuri Baba Azlan"

Zaro ido yai yana yatsina fuska yace "nine baban?"

Da sauri na girgiza kai nace "Yaya Azlan zance Allah baxan sake ba nabi Allah na bika Ka sakar min yarinya ta"

Wani makircin murmushi Azlan yai yana Kara rike Mimi sosai yace "Kin yadda ta dinga ce mun Daddy knn"

Harara na watsa masa ina murguda baki nace "Wallahi baka isa ba kuma"

Baffa baisan lokacin da ya sa dariya ba Yana fadin "ikon Allah"

Juyawa yai zai fita da sauri nadaga kafa zan bisa bugewa nai da center table gaba nai Zan kife inda jaka ta ta fadi ta bude a tsakiyar palourn kayan ciki suka tarwatse, kafin na kai kasa naji an janyo ni na fada jikin wani.

Da sauri na dago dan ganin waye na fada jikin sa, zaro ido nai ganin mai kama da Mr Wicked sak sai dai shi ba irin kayan jikin Mr Wicked ne dashi ba amma kamar su daya banbancin kadan ne kuma shima ina hango kamannin Mimi a fuskar sa.

Kafin na dawo daidai naji an fizgo ni da karfi na fada kirjin wani, dago wa nai cikin tashin hankali don ganin kirjin wa na fada ynxu kuma ga wani irin bugawa da kirjina yake tunda yau kwallo ake dani a kirjinan kattai, Mr Wicked ne fuskar sa tayi ja da sauri na juya don ganin inda ya ajiye Mimi don nasan da a jikin sa take.

Cikin fushi daya bayyana akan harshen sa da furucin sa yace "Junaidu wani irin iskanci ne wannan zaka riko hannun ta har kana rungume ta matar kace ita?"

Da Mamaki Junaid yace "meye hakan Azlan faduwa fa zatai ko baka gani ba da ban rike taba ai zata iya Jin ciwo"

A hasale yace "taji ciwon mana ba gwanda taji ciwo ba da ka rike taba"

Kallon sa Abie yai yace "kai meye sa ka rike ta toh sakar ma mutane yarinya"

Hade rai yai yana sakar mata hannu yace "ai ni dashi daban banci ni daban Shi daban Abie"

Mummy ce da takaici ya gama cikata na iskancin da suke yi kamar ba manya agun tace "kai daka rike ta matar kace?"

Kankance ido yai yace "waya sani ko munyi aure"

Da sauri nace "Allah ya kiyaye"

Kallona yai yace "me kike nufi?"

Harara na maka masa ina dauke kaina daga kansa, Baffa da murmushi ya kasa barin fuskar sa gemun sa ya shafa kawai yana binmu da kallo yana karantar kowa.

Idona ne ya sauka akan kayana da suka watsu a kan carpet da sauri na kai hannuna don dauke bracelet din da na manta yana cikin jakar ma, nasa hannu Azlan yasa hannu shima da sauri muka dago muka kalli juna da wannan damar yai amfani ya dauke bracelet din yana juya Shi a hannun sa cikin mamaki.

Kallona yai yace ina kika samu wannan abin

Dauke kai na nai kawai don na gaji da magana ma

Abie ne ya kalli hannun Azlan da sauri ya zo ya karbi abin kallon Junaid yai yace zo Junaid

Matsowa Junaid yai da mamakin ganin na biyun abin hannun sa a gurin yarinyar nn, don Abie ne ya siya musu Shi da Azlan wani zuwa dubai da yai yasa aka musu iri daya guda biyu aka sa AJ a jiki ma'ana Azlan Junaid.

Hannun Junaid Abie ya rike ya Janye hannun rigar sa zaro ido nai ganin irin sa sak a hannun Mai kama da Mr Wicked, da sauri na matso kusa da shi don na kara tabbatar wa AI kuwa shine har AJ din iri daya komai da komai wani irin bugawa gabana yai da karfi.

Abie ne ya kalli Azlan yace "ina naka yake in baxan manta ba bayan bikin Junaid na tambaye Ka ina abin hannun sa bana ganin sa kace ballewa yai Ka kai gyara kusan shekara biyar knn ynxu ina yake toh ban sake ganin Ka da shi ba"

Dagowa yai ya kalli Junaid sai ya kalli Abie baisan mai zai ce ba hakan yasa shi fadin "barayi ne suka sace", jiri na soma gani da sauri nayi baya ina fadin Innanillahi wa innanillaihir raji'un a hankali idona ya soma rufewa kawai sai gani sukai na zube a gun.

Aisha da Mimi kusan a tare suka taho gurina da gudu suna kuka, girgiza ni Mimi take tana fadin "Maaa kiyi hakuri baxan sake ba ki tashi"

Mami da Aunty sarah ne suka zo suka dago ni akan kujera suka kwantar dani, kallon Junaid Mami tai tace "zo ka duba min yarinyar nan Junaid mai ya same ta"

Da sauri Azlan ya janyo Junaid baya ganin yana nufar inda take, kallon Mami yai yace "Maa a Kira likita mace tazo ta duba ta mana ba dole sai Shi ba"

Tsaki Mami tai tace "Azlan bana son shirme don Allah ceto rayuwar yarinyar nan za'a yi har sai an wani tsaya jiran likita mace bayan ga doctor muna tare dashi"

Girgiza kai yai yace "Mami baxa ki fahimta ba kawai ya fada min abinda za'a yi a ceto ta ki sai na mata amma gaskia shi baxai taba ta ba maman Yarinya tace fah"

Kallon sa Baffa yai yace "zaki bana son gardama, kai Junaid jeka duba ta"

Kallon Baffa yake idonsa na sheki sbd tsabar bacin rai, sai hadiyar zuciya yake ji yake kamar ana Kwara masa ruwan zafi a kirji.

Kallon Junaid yai yace "Junaidu, Junaidu, Junaidu kaga so uku na kira Ka koh wallahi ko hannun ta Ka rike sai na karya ma shi don iskanci taya zaka taba mamar yarinya ta........."


Comments Nd share plz


Mrs A.M🥰
[30/08, 18:52] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️

*TASWIRAR KADDARA*

♠️♠️♠️♠️♠️


Written by
Mrs A.M🥰

Page 22

Dedicated to TASWIRAR KADDARA Fans group ina Jin dadin comments dinku Allah ya bar mu tare🤝🥰

*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃


*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*

*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*


*LOCATION KANO*

08062073990

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Tsayawa Junaid yai cak ya juyo ya kalli Azlan yana mamakin abinda yake nufi da in ya taba ta sai ya karya sa, ya bude baki zai magana Baffa ya daga masa hannu dole yai shiru kawai yana kallon Azlan.

Ruwa Baffa ya umarci Mami data shafa mata a fuska, da sauri Aunty Sarah ta mika ma Mami ruwan shafa mata mami tai amma bata motsa ba cike da tsoro mami ta Kara shafa mata ruwan.

Wani ajiyar zuciya na sauke mai karfi ina jan numfashi na, a hankali na soma bude ido na hawaye ne Mai zafi ya sauko min, in har abinda na gani kuma naji ne gaskia knn Mr Wicked ne baban Mimi.

Lumshe idona nai ina fadin Innanillahi wa innanillaihir raji'un, Mami data zuba mata ido tana kallon ta a hankali ta dora hannun ta akaina tana shafawa, hakan dana ji kawai na fashe da kuka.

Zaro ido Azlan yai yana kallon ta, ta tabbata knn tana da aljanu yarinyar nn kallon baffa yai yace "tsoho ko Malam Sule za'a kirawo ne da alama kanta na motsi."

Harara Baffa ya jefa masa yace "Ka shiga hankalin kafa zaki"

Tabe baki yai yana daga kafadar sa yace "gani nai tana abun masu motsi a ka shine kawai na bada shawarar"

Girgiza kai Baffa yai kallon Aisha yai yace "ina ne gidan ku"

A hankali tace "Hausawa ne Baffa"

Gyada kai yai yace "bara na sa a maida ku gida kinji"

Abie da yake ta juya bracelet din yace "Aisha a ina kuka samu wannan abin hannun."

A tsorace ta dago ta kalle sa sai kuma ta juya ta kalli Batul da ke kwance har lokacin hawaye kawai take, ganin alamun tsoro a tare da ita yasa Baffa cewa "ki kwantar da hankalin ki kinji Aisha ba abinda zamu muku tambayar kawai zaki amsa"

Cikin rawar baki tace "na baban Mimi ne'

Da mamaki sosai Mami tace "baban Mimi kuma? Nidai a iya sanina wannan abin guda biyu ne iri daya na Junaid dana Azlan gashi kuma wannan ma iri daya ne sak alamun na Azlan ne kenn.."

Baffa ne yace "kar ku ruda ta zo kinji jikata'

Sai da ta kalle ni taga idona a rufe yake sannan ta juya ta kalli Mimi dake bacci jikin Azlan sannan ta nufi gurin Baffa tana juyo wa tana kallo na, dafa kanta Baffa yai yace kamar ya na babban Mimi ba kunce ya rasu ba

Girgiza kai tai tana hawaye tace "bamu San ko waye baban taba abinda muke dashi Wanda zai nuna mana baban ta wannan bracelet din ne kawai"

A ynxu kuwa kan kowa dake palourn ya rude, cikin bugawar zuciya Azlan yace "kee me kike nufi da baku san waye baban beauty ba"

Daga kai tai tana hawaye tace "bamu san waye baban taba wannan bracelet din ne kawai mallakin baban ta da yake hannun Ya Batul"

Mikewa Baffa yai ya kalli Abie yace "Muhammad zama bai ganmu ba a wannan gabar, gidan su yaran zamu je mu gana da iyayen su, don kaina ya rude kuma."

Shima Abie da ya gama rudewa Jin wannan maganar yace "Baffa muje toh," kallon Aisha yai yace "xamu samu baban ku a gida ynxu"

Daga masa kai tai tana share hawaye, Mika mata waya Baffa yai yace "samun number dinsa na kira sa tukun kar muje masa haka kawai"

Cikin rawar jiki ta karbi wayar tasa ma baffa numbern Abba, dialing numbern Abba yai ringing biyu ya dauka

Sallama Baffa yai cikin muryar sa mai cike da dattako

Daga can bangaren Abba ya amsa yana gaishe sa Jin muryar ta babban mutum.

Cikin dattako Baffa yace "muna tare da su Aisha ne da Batul in ba damuwa muna son zuwa mu hadu in zamu same Ka a gida"

Cikin dan fargaba Abba yace "suna lafia? Ko wani abun sukai"

Murmushi Baffa yai yace "ba abinda sukai magana ce dama muke so muyi akan Mimi"

Da mamaki Abba yace "Mimi kuma?"

Daga kai Baffa yai yace "eh ita shiyasa nace in ba damuwa zamu iya samun ka ynxu"

Abba da yake zaune a gefen Umma yace "insha Allah ina gida dama zan fita ne amma zan tsaya na Jira ku"

Murmushi Baffa yai yace "mun gode sosai sai mun iso"


********
Umma da tunda Abba ya fara waya take kallon sa da son Jin karin bayani duk da kuwa wayar a speaker take, kallon ta Abba yai bayan ya ajiye wayar yace "Umman Aisha bari naje na Kira yan uwana su zo kafin su iso duk da ban san me suke so suyi magana akai ba amma ina ji magana ce mai muhimmanci"

Daga kai Umma tai tace "Allah yasa muji alkhairi dai kawai amma ni duk gabana sai faduwa yake Abba"

Murmushi Abba yai yana Jan kumatun ta cike da kauna yace "yaushe Sadiyayye ta ta fara jin tsoro nidai nasan Sadiyayye ta jaruma ce"

Murmushi Umma tai tana juya idon ta tace "har ynxu baka tsufa jika ce fa dakai"

Murmushi yai ya dan dale mata baki yace "kul kika Kara cewa bana tsufa har ynxu jina nake garau, ko so kike na auro yar yarinya ce na tabbatar Miki da garau nake"

Harara Umma ta sakar masa tana turo baki, dariya Abba yai yace "Sadiyayye ta uwargida kuma amarya har abada Insha Allah, Allah yai miki albarka Matata"

Murmushi Umma tai tace "Ameen Mijinaa."

Sai da ya tabbatar hankalin ta ya kwanta sannan ya fita don zuwa tahowa da su kawu Nasiru


*********
Baffa ne yace Muhammad sai mu tafi ko da Mustapha da Junaid sai Azlan ku matan ku zauna.

Mummy da take so ayi komai a gabanta tace Baffa don Allah muma muje tare mana ayi komai muna gun

Hade rai yai yace banyi ra'a yi ba ku zauna mazan ne kawai zasu je, mikewa yai ya kalle ni da har ynxu nake kwance sai dai na dena hawayen amma idona a rufe yake.

A hankali cikin nutsuwa baffa yace "taso kinji jikata"

Ban masa musu ba na mike a hankali don dama na gaji na rasa yadda zanyi ne kawai bana.

Ko bangaren da Mimi take ban kalla ba na fita daga palourn motar Junaid muka shiga nida Aisha sai uncle Mustapha a gaba, Azlan kuma ya dauki Baffa da Abie sai Mimi dake kwance a jikin Baffa a back sit.

Tafiyar minti 30 ce ta kawo mu kofar gidan mu, muna zuwa na bude kofar na fita na shige gidan a soron gidan na hadu dasu Kawu Nasiru a gaggauce na gaishe su na shige cikin gidan, ban hadu da Umma ba haka yasa na shige dakin mu kawai na kwanta akan katifa ina rufe idona.....

Aisha ce data shigo ganin su Kawu Nasiru yasa ta fada musu bakin suna jiran su a waje, fitowa sukai sai dai Suma tozali da sukai da su Junaid ba karamin daga musu hankali yai ba bama ganin mimi kwance a jikin Azlan.

Khalil da yazo wuce wa Abba yasa shi shiga da Mimi cikin gidan gabansa yana faduwa da alama magana ce mai muhimmanci za'a yi yau dinnan.

Babban gida suka nufa gaba daya don gidan Abba ba gurin da za'a sauke su, a Palourn baki suka zauna bayan an gaisa Baffa yai gyaran murya yace "abinda yasa muka zo nan sbd wani Abu daya shige mana dubu gaba dayan mu, na farko kamannin da Mimi take kama da jikokina kamar an tsaga Kara na biyu kuma abin hannun jikana da ya bata kusan shekara biyar knn sai gashi yau a jakar Batul, sannan kuma Aisha tace abin hannun na baban Mimi ne toh abin ya daure mana kai sosai shiyasa nake son sanin shin waye *baban Mimi?*"

Sunkuyar da kai Abba yai hawaye na taruwa a idonsa, Kawu Nasiru ne ya gyara zama yace "gaskia ba'a san waye baban ta ba don fyade akai ma Yarinyar mu ta haife ta"

Salati Baffa yai yace "subhanallah amma naga karamar yarinya ce Batul din har yaushe ta haifi Mimi"

Azlan kuwa sunkuyar da kansa kawai yai gaban sa yana faduwa jin ta hanyar da aka samu Yarinyar sa lallai da zaiyi ido hudu da ko waye sai yaci ubansaa

Murmushi wanda yafi kuka ciwo yace *"BA BATUL BACE MAHAIFIYAR MIMI"*


Comments Nd share plz


Mrs A.M🥰

[31/08, 11:28] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️

*TASWIRAR KADDARA*

♠️♠️♠️♠️♠️


Written by
Mrs A.M🥰

Page 23

*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃


*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*

*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*


*LOCATION KANO*

08062073990

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Murmushi wanda yafi kuka ciwo Abba yai yace "ba batul bace mahaifiyar mimi".

Cike da Mamaki su Baffa suke kallon sa, kasa jure wa Abie yai yace "ba ita bace mahaifiyar ta?"

Daga kai Abba yai yace "bara a takaice na baku labarin rayuwar ta"


*WAIWAYE*

Kamar yadda kuka sani haihuwa 3 ne Umma tai amma haihuwar ta farko ta haifi Yan biyu mata masu kama da juna inda aka sa musu suna Khadija da Fatima Batul sai ta biyu ta samu Aisha ta uku kuma ta kara twins maza Kamal da Khalil.

Sun taso kansu a hade duk da Khadija ta kasance mai sanyin hali da mutukar hakuri yayinda Batul kuma ta kasance Mai zafi da rashin daukar raini, kamar su daya sak don ta halayen su ne kawai ake banbanta su da kuma saurin maganar Batul.

Ajin su daya a makaranta komai tare suke basa boyewa juna komai, wannan hadin kan nasu ba karamin faranta ran iyayen su yake ba.

A lokacin da suke da shekaru sha uku wani mummunan abu ya faru da wannan ahalin wanda ya kasance sanadiyar tarwatsa musu farin cikin su.

Cikin sauri Umma ta fito daga kitchen ta daga kai ta kalli yadda garin ya hada hadari sosai gashi bata da magin da zata sa a girki ga kuma Magriba ta doso kai, kallon Khadija tai dake xaune tana bitar karatun Qur'ani.

Daki ta shiga ta dauko kudi ta mikawa Khadija tace "ungo Mamana yi sauri kije shagon Muntari ki siyo min magi na 50 da onga na 30 kinga magriba ta doso kuma gashi hadari ne a garin bana son aiken su kamal ne don wasa zasu tsaya yi."

Cikin nutsuwa ta mike tace "toh Umma" karbar kudin tai ta fita daga gidan tana tafiya cike da nutsuwa.....

Kusan minti 30 da fitar ta amma bata dawo ba, Batul da hankalin ta yaki kwanciya tun fitar Khadija ta kalli Umma da itama hankalin nata ba'a kwancen yake ba don har an Kira sallah tace "Umma bara naje na dubo ina ta tsaya, kinga har ynxu bata dawo ba kuma shagon Muntarin ba nisa ne da shiba"

Cikin fargaba Umma tace kiyi sauri don Allah kema kar ki tsaya kinji

Daga kai kawai tai ta sa hijab dinta ta fice daga gidan, shagon Muntarin ta fara zuwa amma yace mata bai ga Khadija ba, hankalin ta a tashe ta soma zagaye unguwar ko taje wani shagon bana muntarin ba amma duk inda taje sai ace mata bata zo ba.

Daidai wani uncompleted building dake kasan layin su tazo wucewa taji kamar muryar Khadija cikin kuka tana fadin "don Allah kayi hakuri ka kyale ni mutuwa zanyi"

Wani irin bugawa kirjin ta yai cikin sanyin jiki da kasala data rufar Mata jikin ta na wani irin rawa ta zagaya cikin ginin da sauri ta runtse idonta ganin wani mutum dake sanye da bakaken kaya ya danne Khadija dake kwance tsirara duk ya yaga kayan jikinta ga ruwan sama dake dukanta..

Wani karfi ne yazo mata tasa ihu Wanda ya fargar da Mutumin da sauri ya daga Khadija ya juya da nufin guduwa batul ta maza ta cafki hannunsa dambe suka fara Yana son ya kwace kansa ita kuma tana kaimasa duka da karfi tana kokarin bude fuskar sa don ya rufe fuskar da hular rigar sa, karfin mace dana miji ba daya hankada ta yai da karfi Wanda ita kuma dake rike da hannun sa ta fincike abin hannun da taji.

Guduwa yai bata tsaya bin sa ba ta kwasa a guje gurin Khadija dake kwance cikin jini tana kuka, tana zuwa ta rungumo ta a jikinta tana fashewa da kuka, wani irin kuka Khadija itama ta kara fashewa dashi mai cike da tausayi da rauni.

Cikin rawar murya tace "Batul ya cuce ni ya raba ni da martaba ta"

Runtse ido Batul tai ta cire hijab dinta ta lullubawa Khadija, cikin karfin hali tace "Zaki iya tashi mu tafi gida"

Girgiza Mata kai kawai Khadija take idonta a rufe mike wa tai tace "ki tsaya kinji bara naje na Kira Umma"

Daga mata kai Khadija tai tana rufe idonta.

Cikin sanyin jiki Batul ta nufi gida a kofar gida ta tarar da Umma da Abba suna tsaye da alama Abban ya dawo ne.

Kallon ta kawai suke ganin tana tafiya tana kuka ga ba hijab a jikinta, da sauri Umma ta riko ta tace "lafia kin ganta Batul"

Fadawa jikin Umma tai tana fashewa da kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro

Cikin tsinkewar zuciya Umma tace "ki min magana mana bana son iskanci"

Nuna musu hanya kawai take tana kuka, Abba ne yai dauriyar riko batul yace "Batul muje ki nuna min inda take"

Ina gaba suna bina a baya har muka isa kangon, a lokacin da muka isa Khadija bata numfashi tayi fayau kamar ba rai a tare da ita.

Umma da kafafun ta ke rawa ta isa kusa da Batul ta kasa kuka ma cikin rawar jiki ta warware hijab din da batul ta yafa mata ta sama ta a jikinta, janyo ta tai gabanta na faduwa.

Abba daya fahimci halin da aka jefa yarsa ya juya da sauri yace "bara na samo mana abin hawa mu kaita asibiti,"

Umma bata iya magana ba idonta kuri akan Khadija da bata numfashi, bai dade ba ya dawo da adaidaita shida Umma ne suka shiga ni kuma Abba yace na koma gida.

Lokacin da na shiga gida da kyar na iya zama akan kujera Jin wani abu a hannuna yasa na bude shi, wani kyakkyawan bracelet na gani sai kwalli yake wani irin jifa nai da shi cike da tsanar ko waye mai shi don nasan shine silar lalacewar rayuwar yar uwata.

Kamal dake kallona yaje ya dauko ya kalle ni yace "Ya Batul me yasa kika yar da shi na waye ne wannan abin kingan sa mai kyau".

Ban basa amsa ba sai hawayena da nake sharewa kawai

Aisha ce ta kalle ni don itama tana da dan wayo shekarar ta 11 lokacin tace "Ya Batul ina Ya Khadija dasu Abba"

Cikin dauriya nace "sun tafi Kai Khadija asibiti bata da lafiya"

Fuskar tausayi dukansu sukai suka ce Allah ya bata lafia


**********

Lokacin da su Abba suka kai Khadija asibiti kin karbar ta akai wai sai an zo da dan sanda, dole Abba ya kira kawu Nasiru ya fada masa halin da ake ciki.

Cikin dimuwa Kawu Nasiru ya kira wani dan sanda dake unguwar su tare da shi suka zo asibitin sannan aka shiga da Khadija, numfashin ta aka soma samu ya dawo daidai sannan aka duba ta abin tausayi har dinki aka mata don Wanda ya mata fyaden karfi yasa Mata.

Sai da tayi sati daya a asibiti sannan aka sallame ta kuma tunda ta farka batai magana ba, batai kuka ba ko an mata magana sai dai kawai ta daga kanta ko ta girgiza kanta, Batul kuwa bata taba zuwa ba kullum tana gida ita ke kula da abincin su.

Tuni labarin abinda ya faru da Khadija ya karade Yan uwa da mutan unguwa, don tunda uwani taji da hama suka shiga barbadawa, inda Shamsiyya ma ta fada a makarantar bokon su da islamiyya cewa an kama Khadija tana iskanci shine aka fake da cewa fyade aka mata.

Ranar da aka sallami su Khadija, ina xaune a tsakar gida ina tankade garin masarar da zan mana tuwo anjima suka shigo Umma ce rike da Khadija dake tafiya a hankali sai Yakumbo a bayan su.

Dagowa nai muka hada ido da Khadija kawai ta ware min hannunta, cikin karyewar zuciya na mike da gudu naje na rungume ta itama rungume ni tai kawai muka fashe da kuka.

Umma itama da kukan yazo mata shigewa daki tai tana fashewa da kuka, Yakumbo ce ta goge hawayen ta ta shiga rarrashin mu.

Da kyar mukai shiru na rike ta muka shiga palour, sai dai me muna zama Uwani da Hama suka shigo.

Kallon Khadija Uwani tai tace "sannun yar nan ashe haka abu ya kasance toh Allah ya kiyaye gaba amma kam an cuce ki ynxu ke waye ma zai aure ki bayan wannan tabon da aka shafa Miki."

Hama ce ta cafe da fadin "ai abin tausayin ma in an samu wani ya aure ta tofa iyalan ta ne abin tausayi shiknn sai ana musu gori cewa Uwarsu ba budurwa aka same taba.."

Umma da ta fito daga daki tace "bakin ku ya sari danyan kashi , Insha Allah ba abinda zai biyo baya sai alkhairi kuma kaddara ce tana kan kowa"

Da sauri Uwani tace "dakata Sadiya ban gane mai kike nufi da kaddara na kan kowa ba badai fata kike ace muma yayan mu amusu fyaden bakoh?"

Hama tace "kyaleta Uwani inaga bakin ciki take mana mu ya'yan mu suna nan da budurcin su ita kuma nata gashi an dauke na daya saura biyu"

Umma zatai magana Yakumbo ta daga mata hannu, kallon su Uwani tai tace "xaku iya tafiya in kun gama fitsarar taku zan hadu da mazajen naku"

Cikin dan tsoro suka fita don sun san halin Yakumbo bata sakar wa sirika fuska kuma yayanta suna matukar Jin maganar ta, tabbas in ta fada musu sun kade..

Matsa hannun ta nai dago idon ta dake zubar da hawaye tai ta kalle ni, murmushi na sakar Mata ina goge Mata hawayen...

A daren ranar na nunawa su Abba abin hannun dana cire a hannun mutumin, naso yarwa Abba yace na ajiye wata ran zaiyi amfani.


Tun daga ranar rayuwar mu ta sauya koda muka koma makaranta gaba daya sai aka tsane mu duk inda muka wuce sai an nuna mu ana fadin gasu can waccan ce wacce aka kama tana iskanci, a islamiyyar ma bamu tsira ba gashi a unguwa duk kawayen mu sun daina kulamu.

Hakan yasa nima na Kara zama mara hakuri da farko in aka zage mu shiru nake amma daga baya daina shiru nai ana zagin mu ina ramawa in ta kama ma na zaune yan iska mu dambatu.

Dole Abba ya chanja mana makarantar boko da islamiyya, kawayen layin mu kuma duk na watsar da Yan iska, a unguwar ma da maman Hidaya kawai muke shiri don lokacin tana amarya.

Rashin kawayen da nai yasa muka Saba sosai da cilla, a gidan su ake mana markade kuma ni nake kaiwa, tun in nakai muna fada da shi sbd a lokacin yana ganiyar rashin jinsa duk da ya girme ni kuma in ya min abu ramawa nake har muka zo muka Saba sosai.


Wata uku da faruwar lamarin Khadija ta soma wani irin haske, ga kwadayi da ba ruwanta amma ynxu komai ta gani sai ta ci ita tasa na fara kayan cake sbd son da take masa, ga cin abinci ko yaushe bakinta cikin motsi yake.

A wannan lokacin kuwa hankalin Umma ba karamin tashi yai ba don ta fahimci ciki ne da Khadija, koda ta fadawa Abba ce Mata yai ta bari a tabbatar tukun.

Asibiti ya kai Khadija gwajin farko likita ya tabbatar da ciki ne da ita na wata uku har da sati biyu, zan iya cewa tashin hankalin da muka shiga baxai iya misaltuwa ba, ba yadda Umma batai ta a zubar da shi amma Abba da Yakumbo suka hana.

Uwani da Hama kuwa an samu abin yamadidi a unguwa yadda suka sako Umma a gaba sai da Yakumbo tace musu duk Wanda ya Kara wata magana sai tasa mijinta ya sake ta sannan suka shiga taitayinsu.

Nidai na tsani cikin Khadija bana sonsa don kiyayya nake nuna masa kuru kuru wani lokacin har dukan cikin nake bama daya soma girma.

Tunda cikin yai wata biyar Khadija ta daina fita ko kofar gida, tayi kiba sosai muna iya kokarin mu ganin mun kwantar Mata da hankali, Abba ne ya bawa Umma kudi taje kasuwa tayi siyayyar baby badon ranta naso ba.

Cikin Khadija tun da ya shiga wata tara rabonta da lafia knn, kullum cikin ciwo take yau ciwon baya gobe ciwon kafa jibi ciwon ciki.

Muna kwance a katifar mu hira muke Sama Sama don bacci nake ji, kallon Khadija nai data min kyau sosai tayi haske Dan tsaki nai nace "ke dallah ki daina kallona haba kin ishe ni"

Murmushin ta mai sanyi tai tace zanyi kewar ki yar uwata, ina matukar kaunar ki sosai yar uwata

Gaba nane ya buga da karfi cikin dauriya nace "ina zaki da za kiyi kewar tawa"

Murmushi kawai tai ta janyo hannuna ta dora akan cikin ta, Dan zabura nai jin cikin yana motsi sosai, ganin yadda nai ta fashe da dariya tace "matsoraciya"

Murmushi nai kawai duk da na sani cikin Amma sai na kasa dauke hannu na, a hankali itama ta dora hannun ta akai tace "baby kina ji ko wannan itace mamanki sunanta Batul kiyi mata biyayya sosai tana sona"

Dan hade rai nai Zan janye hannuna tai Maza ta rike tace "Batul meyasa baki son cikin nan"

Dan kallon ta nai sai na juya nace "sbd cikin mutumin dana fi tsana ne a rayuwata Wanda yai silar lalacewar rayuwar mu"

Murmushi mai sauti tai tace "amma ai hadda jinina a jikin cikin koh, kuma nasan ni kina matukar sona baxa ki kaunaci cikin ba kodan sbd ni batul, yau cikin nan in ya fito duniya zai budu idonsa ne a matsayin kece mahaifiyar sa in kina nuna masa kiyayya ya zaiyi?"

Zare hannuna daga kan cikin nai nace "naji zan kokarta"

Dariya kawai tai tana lumshe idonta, daren ranar haka kurin na kasa bacci sai zubawa Khadija dake bacci cikin nishadi ido nai, sai gaf da asuba na matsa jikin ta na rungume ta ina sauke ajiyar zuciya.

Washe gari da Asuba Khadija ta fara nakuda, a rikice Yakumbo dani da Abba muka nufi asibiti da ita, ko da muka je nurse din data dubata tace ce haihuwa ce mu zauna a asibitin.

Shiru amma har la'asar sai wahala da Khadija take sha kawai, kanwar Umma Aunty Bilkisu itama tazo gurin azahar.

Nidai sbd tashin hankali ko ruwa ban shaba nayi zuru zuru sai gab da asuba sannan haihuwar tazo, labour room aka shiga da ita a lokacin Abba daya koma gida shima ya zo don kasa bacci sukai shida Umma gashi kuma sunyi kawaicin kin kiran wayar su Yakumbo su tambaye su.

Minti 40 da shigar su nurse ta fito da guje ta nufi office din likita sai gasu sun dawo da likitoci biyu, mudai muna tsaye a gun muka ji kukan jaririya.

Likitan ne ya fito yace wace "Batul a cikin ku"

Cikin bugawar zuciya Abba ya nuna ni, daga Kai likitan yai yace "biyo ni".

Da wani irin rawar jiki nabi bayansa har cikin labour room din, a kwance Naga Khadija ta kara haske sosai dukda an mata kasanta zanu hakan bai hanani ganin yadda Jini yake gudu a jikin taba.

Nurse ce ta miko min babyn data shirya cikin fararen kayan sanyi sai motsi take tana tsotsar hannu, Dan zuba mata ido nai ina tasbihi a raina sbd tsantsar kyaun yarinyar kamar yar larabawa lokaci daya naji wani masifaffiyar kaunar ta yana huda zuciya ta.

Cikin dashewar murya Khadija ta miko min hannun ta tace "zo yar uwata"

A hankali na daga kafa ta har na isa kusa da ita, hannuna ta kama tana murmushi ta kalli fuskar yarinyar sai ta sa dariya mai hade da kuka, cikin muryar ta data dishe tace "ga yarinyar kinan batul na bar miki ita duniya da lahira dama kuma taki ce, bana son tasan cewa bake kika haife taba don Allah kina sonta"

Da sauri na daga mata Kai hawaye suna zuba daga idona, murmushi tai tace "in anga babanta kice masa na yafe masa Batul"

Dan hade rai nai nace "ni baxan taba yafe masa ba"

Girgiza kai tai tana dariya tace "kicewa Umma da Abba da kowa ya yafe min kinji"

Tsaki nai nace "ke Khadija bansan iskanci meye kike mun magana kamar wata mai barin
Wasiyya"

Murmushi tai jikin ta na rawa ta dora hannun ta akan yarinyar tace *"ALLAH YA MIKI ALBARKA YA KARE KI ADUK INDA ZAKI SHIGA"*

Murmushi nai nace "Ameen"

Hannuna ta rike tana kallona fuskar ta dauke da murmushi ta shiga yin kalmar shahada ni ma sai na shiga yi ina sakar mata murmushi don a nawa tunanin tana yine kawai.

Idonta ne Naga ya tsaya cak sai hannun ta daya saki, murmushin dake Kan fuskata ne ya dauke nace "Khadija ya kikai shiru"

Girgiza ta na shiga yi amma bata motsi gaba daya jikinta ya saki, a rikice na juyo gurin doctor da nurses din da suke tsaye suna kallon mu cike da tausaya wa, cikin tashin hankali nace "doctor bata motsi"

Janye ni wata nurse tai ta fitar dani daga dakin, muna fitowa ta kalli Abba tace "sai dai hakuri Allah ya mata cikawa, Allah ya jikanta"

Salati Yakumbo da Aunty Bilkisu suka saki yayinda Abba ya rufe idonsa hawaye yana zubo masa.

Ni kam daina gane komai nai sai binsu da ido da nake yi kawai, gawar Khadija aka bamu lokacin dasu Kawu Nasiru suka zo da mota.

Gida aka nufa da ita ina rike da babyn a jikina na rungume ta sosai, gaba daya kaina daina aiki yai sai bin mutane da kallo kawai nake.

Umma ba karamin dauriya tai ba ita da Yakumbo ne suka ma Khadija wanka suka shiryawa aka ajiye ta a tsakar gida kafin azo a fita da ita, Aisha dasu kamal sai kuka suke suna zaune a gabanta suna mata addu'a kamar yadda Aunty Bilkisu tace musu.

Jikina na rawa lokacin dana ga anzo fita da ita na karasa inda take, akan gwiwowina na tsugunna na bude fuskar ta babyn na dora akan kirjin ta nace "Khadija ta ki tashi kinji, ni nasan Wasa kike min ba ki mutu ba ga babyn fa kin ganta mai kyau da ita, don Allah in tsorata ni kike don nace bana son babyn wasa nake miki Allah ina Santa"

Kuka mutanen gurin suka kara saki, Abba ne yazo ya dauki babyn ya mikawa Yakumbo don itama ta farka sai ihu take, janye ni ya shiga yi ina mika hannu ina kamo makarar ina fadin "don girman Allah Abba kayi hakuri kace kar su tafar min da ita wallahi Wasa nake mata ina son yarinyar"

Umma ce ta rungume ni kawai na tusa kaina a jikinta na fashe da wani irin kuka, itama lumshe idon ta tai hawaye masu zafi suna zubo mata a daidai lokacin da ake fita da gawar Khadija...

(Innanillaihi wa innanillaihir raji'un😭😢😭 Allah ya jikan Al'ummar musalmai muma in tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da Imani Ameen )

Mutuwar Khadija ta girgiza mutane da dama, ko su uwani sunji mutuwar ta tun daga lokacin na dauki kauna da soyayyar da nake ma Khadija ta koma kan Khadija small, wacce aka mayar Mata da sunan khadija nake ce mata Mimi.

Duk abinda na gani in har mimi tana so sai na siya Mata, sbd ita na fara Sana'a don na ringa siya Mata Kaya da abin wasa duk da ba abinda Abba ya rage ta dashi.

Tunda ta budi baki take cemin Maa don a fahimtar ta nice mahaifiyar ta, haka kuma duk Wanda ya sanni bayan mutuwar Khadija dauka yake nice asalin mahaifiyar Mimi.

Mutuwar Khadija yasa na kara tsanar ko waye baban Mimi kullum sai na masa Allah ya isa ba tsallake duk da Khadija tace ta yafe masa ni ban yafe ba.

Yusuf ya kasance saurayin Khadija ne wanda yake sonta, kowa a familyn mu ya san soyayyar da yusuf yake ma Khadija itama kuma tana sonsa, lokacin da tsautsayin ya fadawa Khadija baya nan yana Malaysia karatu sai bayan rasuwar ta ya dawo.

Ba karamin mutuwar ta yaji ba da tausayin Mimi shine ynxu kuma yake nuna cewa yana Sona da aure kuma zai rike min Mimi.

Ni Kam mai zanyi da Yusuf Allah na tuba in ba cin amana ba taya Zan auri Wanda Khadija ta taba so ai har abada.....


*Cigaba*

Hawaye Abba ya share yace "wannan shine asalin sanadin Mimi kuma a takaice rayuwar Mimi da yadda aka same ta."

Hawaye Baffa ya share yace "tabbas kunga jarrabawa amma don Allah kuyi hakuri dan ynxu Ka Haifa baka haifi halin Saba"

Abie da jikinsa ya gama sanyi ya kalli Azlan da kansa yake sunkuye yace "Amma Ka bani kunya Azlan, ban taba tunanin cewa haka kake na Ashe bayan yawon club har fyade kake ma kananun Yara"

Da sauri ya dago ya kalli Abie sai ya juya ya kalli Baffa yace "Abie baka yadda ina da budurci naba wai?"

Xaro ido Kawu Kabiru yai yace "dama Maza suna da budurci"

Cikin tabbatar wa Azlan ya daga kai yace ban taba kusantar wata mace ba Kuma ni yadda nake tanadin budurcina ai baxan haike wa yarinya ba don nasan ko babba
Ce na kamata mutuwa zatai

Junaid ne yace na shiga uku Azlan meye haka don Allah wai Kai baka da kunya

Kafada ya daga yace Junaidu ina zanyi kunya kana ji ana tantamar budurci na

Abie ne ya mike a fusace ya "dauke fuskar sa da mari cikin fushi yace don ubanka in ka kara magana sai na nuna ma ni dinnan Muhammad nina haife Ka kuma nafi Ka iskanci, abin hannun da aka cire a hannun mutumin naka ne, mimi dakai take kama kaine mara ji duk cikin Yayana sannan ga dan uwanka nan shekarar sa biyar da aure matar sa ko batan wata bata bata yi ba sbd baya haihuwa kana kallo kullum cikin yawon neman magani yake a duniya shi kake so mu zarga ko me?"

Azlan da tunda Abie ya mare sa ya sunkuyar da kansa a hankali a dago fuskar sa datai jajir idonsa ya kada yayi wani irin ja gashi dama yau ba'a sa masa kwalli ba cikin rawar murya yace kayi hakuri Abie karya nake MIMI *JININA CE YARINYA TACE*


Yau dai ba korafi na muku da yawa🥱


Comments Nd share plz


Mrs A.M🥰
[31/08, 16:31] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️

*TASWIRAR KADDARA*

♠️♠️♠️♠️♠️


Written by
Mrs A.M🥰

Page 24

*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃


*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*

*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*


*LOCATION KANO*

08062073990

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Duk mutanen palourn zuba masa ido sukai, ganin haka yasa shi mikewa a hankali ya durkusa a kusa da Abba yace "don Allah ku yafe min kuskure ne da sharrin zuciya so daya na taba yi ashe hadda rabo"

Baffa ne yace "meye haka kuma"

Juyo wa yai ya kalli Baffa yace "lokacin nima kuruciya ce ke damuna, amma na gane kuskure na tun daga lokacin ban sake ba".

Kallon Abba yai yace "don Allah ku yafe min, Allah ya jikan Khadija ya gafarta mata."

Wani murmushi Abba yai tun daga lokacin da yaron ya fara magana yake karantar sa tabbas wani abu ya darsu a zuciyar sa amma ya gyada kai yace "bkm nidai na yafe ma kuma itama Khadijan tace ta yafe, zan yiwa mamanta magana itama nasan zata yafe din insha Allah."

Baffa ne yace "Alhamdulillah, dama haka muke so amma tabbas Ka cika mahaifi na kwarai ba ko waye bane za'a ma diyar sa wannan abun amma ya yafe lokaci daya da alama itama Khadijan tana da kyaun Hali, Allah y jikanta"

Sai da aka Kara godewa su Abba akan yafiyar da sukai sannan Baffa yace "in ba damuwa ina nemawa Azlan auren babar Mimin Batul"

Da sauri Abba ya kalli Baffa sai kuma ya kalli su kawu Nasiru.

Azlan ma dagowa yai ya bude baki zai magana Baffa ya zare masa ido dole yai shiru.

Kawu Nasiru ne yace "zamu yi magana akai insha Allah Baffa, duk yadda muka ce zamu Kira ku".

Murmushi Baffa yai yace "Allah yasa muji alkhairi".

Mikewa Azlan yai ya fita yana sakin wani makirin murmushi ransa fess....


Bayan tafiyar su Baffa kallon Kawu Nasiru Kawu Kabiru yai yace "Yaya ya kuke gani ynxu nidai bansan Mai zance ba"

Murmushi kawu Nasiru yai yace "da alama gidan dattako ne, kuma a yadda yaron ya bada hakuri yana da hankali kamar, sannan bayan wannan hakan da za'a yi shine rufin asirin Mimin kaga zata tashi cikin dangin mahaifin ko dan sbd gaba, sannan kaga da alama baza a iya raba batul da Mimi ba don haka duk lokacin da ita Batul din tai aure ta tafi da Mimi gidan aurenta ko shi mijin bai goranta ba a cikin dangin sa sai an samu wani yayi".

Gyada kai Kawu Kabiru yai yace "tabbas haka ne Yaya kuma kaga ita Mimin ko auren ta aka tashi sai an samu Wanda ya ce ba mijin Batul ne mijin taba kaga dole a binciko dangin Mahaifin ta, amma in suna tare da Mahaifin nata komai zai tafi lafia insha Allah"

Kallon Abba sukai da tunda suka fara magana baice komai ba amma fuskar sa dauke da murmushi sannan Kawu Nasiru yace "bakai magana ba kai ya kagani"

Yalwataccen murmushi Abba "yai yace hakan shine daidai Yaya amma zan same su na fada musu tukun aji ta bakin yarinyar, sannan kaga sai na fadawa Yusuf shima tunda ya nuna yana son Batul din da aure"

Sai da suka kara tattauna wa sosai sannan kowa ya shige gida don fada ma iyalin shi bayyanar mahaifin Mimi.

Lokacin da Abba ya shiga gida tuni Aisha ta soma fesawa Umma duk abinda ya faru a gidan baffa, Sawa Abba yai aka Kira masa Batul sannan yafada musu komai har ma da auren da suke so a basu na Batul

Da sauri Batul ta kalli Abba tana hawaye tace "Abba aure na kuma?"

Daga kai Abba yai yace "hakan shine rufin asirin mu da na Mimi, zata tashi tare da mahaifin ta kema baki da fargabar komai akan dangin mijin ki wata ran zasu iya miki gori"

Kuka na fashe dashi nace Abba "don Allah kayi hakuri wallahi na tsane sa"

Shiru Abba yai yana tunani kafin ya kalli Umma data ke kallon Batul kamar ta make ta murmushi kawai yai yace "tunda baxa ki iya ba Batul, Aisha ke zaki aure sa?"

Da wani irin sauri Batul ta dago ta kalli Abba kirjin ta na wani irin bugawa tace "Aisha kuma Abba sai ta auri Mr Wicked?"

Gyada kai Abba yai yace "tunda ke baxa ki iya auren sa ba Batul ina jin kunyar nace ma tsohon baxan iya basa jinina ba sai na bawa Aisha kawai"

Mikewa nai ina kuma fashewa da kuka na shige daki, dukkan su da kallo suka bini sannan Abba ya kalli Umma, ciro wayar sa yai yace ma Yusuf yana son ganin sa, mikewa yai yace ina zuwa ku jira ni anan Zan dawo na muku bayani.

Yusuf bai dau lokaci ba ya iso, tare da Abba suka tafi babban gida sun dade suna tattauna wa kafin Abba yace "zan fada ma lokacin da za'a tsayar da ranar bikin sai Ka fadawa magaba tan Ka, tunda so nake a hade bikin gaba daya kuma Aisha bata gama secondary school ba wannan shekarar dai zata gama"

Sunkuyar da kai Yusuf yai cikin kunya yace "ngd sosai Allah ya kara girman"

Mikewa yai ya fita fuskar sa dauke da murmushi, sai da suka kara tattauna wa sannan Kawu Nasir ya Kira ya fada ma Baffa sun yadda sai dai kuma ga abinda Batul din tace shima dai sun dade suna magana kafin ya kashe.

Ajiyar zuciya Abba ya sauke yace "Alhamdulillah"

Da ya koma gida har lokacin Umma da Aisha suna zaune sai maida maganar suke, Zama yai ya musu bayani gwari gwari sannan ya umarci Umma ta same sa a daki da kwai maganar da zasu karasa.

Ran Umma fess ta bi bayan Abba Jin ta take cikin farin ciki auren Yaya Mata biyu lokaci daya ba tare data kawo ba, gasu tana aurar dasu ba wata a gabanta ai abin a mata murna ne.

Ina kwance sai dai na daina kukan sai tunanin wai Abba zai bawa Mr Wicked Aisha ne kawai yake damuna a raina.

Dagowa nai jin shigowar Aisha, kallon ta nai naga sai murmushi take da sauri na mike nace Aisha wallahi kar ki yadda mutumin nan ba na kirki bane mai zaki yi da shi Allah kar ki soma yadda

Zama Aisha tai ta juya idonta tace "Ya Batul me yasa, yana kama da Mimi fah sosai baki gansa ba mai kyau in na same sa matsayin miji ai na haye wallahi."

Tsaki nai nace "baki da hankali ke ana maganar hankali kina wani hauka meye kyau kuma, dallah ki nutsu ki gane mana bashi da hali mai kyau Dan iska ne"

Da Sauri Aisha tace "nidai Ya Batul ki daina iskanta min shi, kuma Abba har sun Kira Baffa sun fada masa cewa ke kince a'a amma ni sun bashi ni"

Da sauri nace "Mai Baffan yace"

Murmushi tai tana janyo dankwalin ta tace "murna sukai sukai godia, Abba ya fada musu dai kema dama da wanda kike so sai a hada bikin lokaci daya"

Zaro ido nai nace "ni kuma waye Wanda nake so din?"

Kallona tai da mamaki tace "Ya Yusuf mana, Abba ma ya fada masa shima ya shirya ina gama secondary school za'a yi biki ynxu dai zasu tsayar da rana kinga saura wata 5 mu fara WAEC lokacin kema kin gama second semester dinki kawai sai musha biki"

Kasa magana nai sai binta da kallo kawai nake sai iyayi take tana yafa mayafi a kafada irin matan auren nan..


********
Kallon Azlan Mami tai da kansa yake kasa, gaba daya ta kasa yarda cewar Azlan ne zai aikata wannan abun sai dai kuma hujjojun da suka bayyana da kuma yadda ya amsa da kansa yasa bata da yadda zatai.

Mama kuwa ba karamin farin ciki tai ba ko bakomai wano tabo ya shafi Mami jikarta ta farko shegia ce.

Cikin nutsuwa Uncle Mustapha yace "har aure Baffa ya karbo masa na maman yarinyar, duk da an samu matsala amma sun mana bayani yace duk lokacin da muka shirya asa rana."

Cikin fushi Mummy da tunda aka fara maganar take tunanin halin da yar ta zata shiga tace "amma kawai sai a nema masa auren ta, bayan bama ita ce ta haifi yarinyar ba"

Baffa dake kallon ta yace ko "banyi daidai bane uwata"

Da sauri Mummy tace "ba haka nake nufi ba Baffa amma a duba, shi baya ra'ayin auren yarinya kuma tun tuni ake binsa da zancen Xainab yana botsarewa ynxu ya zata ji Baffa don Allah" ta karashe cikin rawar murya.

Shiru Baffa yai yayinda Abie yace "Baffa a duba lamarin gaskia kodan sbd Zainab din kowa yasan tana son Azlan"

Da sauri Azlan yace "Abie don Allah kuyi hakuri wallahi horon ya min yawa taya za'a bani mitsilar yarinya kuma azo ace za'a hada ni da Zainab wallahi hauka zan fara inaga, gurin wa zanje na sauke budurcina....."

Make masa baki Abie yai yace "kar na sake jin Ka ambaci budurci ko ranka ya baci"

Murmushi Baffa yai ya kalli Azlan ya ce "Allah ya baka ikon yin adalci a tsakanin matan naka da Xainab za'a hada ayi auren rana daya zaka angwance da Mata biyu Insha Allah nan da Wata bakwai"


Comments Nd share plz


Mrs A.M🥰

[03/09, 18:26] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️

*TASWIRAR KADDARA*

♠️♠️♠️♠️♠️


Written by
Mrs A.M🥰

Page 25

*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃


*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*

*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*


*LOCATION KANO*

08062073990

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Sunkuyar da kai kawai Azlan ya kasa dago kansa ya kalli, kowa.

Kallon sa Baffa yai yana son yai magana don shirun sa tabbas ya bashi tsoro, a yadda yasan Azlan tabbas bai tsammanin zai yi shiru ba.

Abie ma kansa shirun Azlan ya a ynxu ba shi tsoro a yadda yasan danshi ba irin sune ake ma dole ba akan abinda basu da ra'ayi ba amma gashi an bashi mata biyu a rana daya kuma dukkan su ba ra'ayin sa ba har ansa rana amma baiyi magana ba.

Ajiyar zuciya Baffa ya sauke yace "zaki baka ce komai ba"

Sai da yadan dau seconds sannan ya dago idonsa da suka yi wani irin jaa sbd bacin rai, murmushin gefen baki yai yace "mai zance tsoho kun gama yanke hukunci Allah ya kaimu"

Mikewa yai kawai ya fita daga gidan gaba daya...

Shiru palourn yai kafin Baffa ya sallami kowa, bayan ya fadawa Abie ya Kira Abba ya fada masa sun sa nan da 7 months tym din Aisha ta gama secondary.


**********
Wani irin ihu Zeey tai ta fada jikin Mummy tace "Mummy ynxu dai nan da 7 months zan zama matar Ya Azlan?"

Murmushi Mummy tai tace "insha Allah kuwa, matsalar kawai auren da Baffa yace zai masa da waccen shegiar duk da naji baban yarinyar ya Kira yana ma baffa wata magana amma banji ba Allah yasa ma suce baza su bashi auren ba"

Zama zeey tai tace "Mummy ai ni wannan auren da za'a masa sam baya gabana, nasan kowa za'a aura masa baxa ta kama kafata a komai ba don haka kar ma ki damu, kuma ina shiga ciki zamu San yadda zamuyi mu fita da ita."

Murmushi Mummy tai ta shafa kan Zeey tace "dama ai ke nake ji kar ki tada hankalin ki Amma tunda kin kwantar da hankalin ki ynxu kawai zamu shiga gyara kine yadda in ya shiga gonar ki sai ya raina kansa".

Wani juya ido zeey tai tace "yauwa Mummy na shiyasa nake sonki sosai".

Dariya sukai suna tafawa


*********
Tunda abin ya faru gaba daya ba Zama wata suku suku bama dana ji Umma tana gayawa Aunty Bilkisu data zo cewa ansa ranar biki wata 7, ga Aisha ynxu ta koyi wasu kalar hauka bata da aiki sai karatun littafan Hausa, da na mata magana sai cemin tai wai zaman aure take koya da yadda zata Kula da Mijin ta.

Yau sati daya da faruwar abin knn muna zaune a tsakar gida nida Aisha sai Umma, Mimi na daga kofar kitchen tana gera kayan wasan ta wai girki take yi.

Hira muke wanda yawanci Umma ke mana nasiha da yadda ake rike Miji da kuma Kula da jiki da tsafta.

Janyo wayar ta tai tace "bara na Kira Bilkisu ma na tuna mata kar ta manta tace zata je shagon Aunty Baby Mai baby beauty lounge ta karbo muku maganin sanyi, gwanda ku fara sha tun ynxu"(08183462148 or 07058457638 tana saida magungunan sanyi masu kyau da inganci sannan akwai Kayan da'a masu inganci Wanda zasu gigita oga🙈)

Nidai banyi magana ba sai Aisha ce take kallona tana wani murmushi, harara na maka Mata ina jan tsaki.

Shigowa kamal yai dauke da sallama, Zama yai akan tabarmar sannan ya kalli Mimi yace "Mimi Daddyn ki yazo yana waje"

Da gudu Mimi ta taho gun kamal dafa gwiwowin sa tai tace "da gaske Daddy na yazo Ya kamal"

Dariya Kamal yai yace "yana waje ma"

Da gudu ta kwasa tayi waje, ni kuwa da tunda kamal yace Mr Wicked yazo naji wani irin bugawa da kirji na yai sai kawai na saukar da kaina kasa ina duba wayata duk da kuwa ba abinda nake gane wa.

Kallon Aisha kamal yai yace Ya Aisha kije wai yana jiranki

Da sauri na dago na kalli Aisha don Jin wani amsa zata bawa Kamal, sai dai ga mamaki na sai Naga Ka kalli Umma, daga mata kai Umma tai hakan yasa ta mike da sauri ta shige daki, minti kadan ta fito sanye da hijab ta dan fesa turare ta gyara fuskar ta.

Raka ta nai da kallo har ta fice, juyawa nai naga Umma ta zuba min ido tana kallo na, juyar da kaina nai amma ji nake kamar na dora hannu a Ka na fashe da kuka.

Bata dade ba ta dawo fuskar ta a washe sosai, kallon Umma tai tana sosa kai tace "Umma yace wai in tambaye ki in kin yarda zamu rakasa super market nida su khalil da Mimi".

Murmushi Umma tai tace "Allah ya kiyaye in har da su Khalil ne ai baxan hana ba, ko ba komai yayi spending tym da Mimi."

Tsalle Aisha tai cike da murna tace "mun gode Umma bye," kallona tai tace "sai mun dawo Ya Batul."

Da harara na bita har ta fice daga gidan, juyowa nai na kalli Umma nace "ynxu Umma kika barsu suka fita tare da Mr Wicked bashi da hali mai kyau fa Umma kina kallo dai shine mahaifin Mimi"

Kure ni da ido Umma tai kafin tace "Batul ki shiga hankalin ki akan aibata wannan mutumin, ke ynxu in Mimi taji ki zata ji dadi ki sani duk lalacewar Uba, uba ne kuma kar na Kara ji kin fadi wata kalma mara dadi ko ba komai shine zai auri kanwar ki, yau da gobe kuma wataran zata ji haushin yadda kike masa."

Kwalla ce naji tana kokarin zubo min kawai na juyar da kaina ina wasa da wayata.

Ban san mai yasa ba amma tunda suka fita hankali na ya kasa kwanciya bini bini na kalli kofa ko na duba ogoga na.

Sai gab da magriba suka shigo hannun su dauke da manyan ledoji, sai walwala suke.

Nuna wa Umma sukai kayan kwadayi ne ya siyo musu sai kayan wasa dasu teddy daya siyo ma Mimi.

Ledar dake hannun Aisha ta mikawa Umma tace "Umma kinga mai ya siyo min" ta fada fuskar ta dauke da murmushi.

Karba umma tai ta bude iPhone x ce mai kyau golden colour, kallon ta Umma tai tace "ke kika ce ya siya Miki"

Da sauri ta daga hannun ta tace "ba ruwana Umma cemin yai ina da waya nace a'a shine yace amarya kamar ni banda waya ni banma san ya siyo ba sai da muka dawo ya ban yace har SIM ya samin"

Ajiye ledojin Umma tai tace "angode sosai ku ajiye a Palour sai Abba yadawo a nuna masa"

Nidai ko uffan ban ce ba, koda Abba ya dawo aka nuna masa godia yai yace ma Aisha ta Kula da yadda zatai amfani da wayar.

Tunda ga lokacin kullum Aisha tana manne da wayar ta bata da aiki sai chatting da waya, sai kuma zance don ba'a sati ba tare da tai zance ba wataran da Mimi take fita wata ran kuma ita kadai.

Nidai nawa ido amma Allah ya sani ba karamin azabtuwa nake ba, bama in tana waya tana kashe murya ji nake kamar na karbi wayar na rotsa a kasa, nidai bansan mai yasa nake haka ba amma na barshi a matsayin kawai don bana son Mr Wicked ne kuma na tsane sa sbd abinda yai ma Khadija.

Aunty Bilkisu har gida tazo ta kawo mana magungunan sanyi Wanda ta karbo mana a gurin Aunty baby, sosai Umma ta dage akan Kula da yadda muke amfani dashi, don ta hana mu tsarki ma da ruwan sanyi sai na dumi, kuma ta hana mu Shan abu mai sanyi.

Alhamdulillah kam maganin sanyin yana da kyau sosai don muna ganin amfanin sa, ganin kyaun sa yasa Umma itama ta fara sha don tace itama bata tsufa ba in dai gyara ne.

Cikin haka muka koma makaranta, result dinmu yai kyau sosai komawa ta makaranta shi yake dan rage min wani radadin, don tsaf na fita harkar Mr Wicked ko class dinmu ya shigo bana yarda mu hada ido, kuma abinda na Kula shima ya watsar da ni ba abinda ya shafe sa, in yazo abinda ya kawo Shi yake yi ya fita.

Sosai na maida hankali akan karatu na bana wasa, nida Asma'u mun Kara zama kawaye sosai har auren mu na fada mata date din amma ban ce mata Mr Wicked Aisha zata aura ba.

Itama ta dage sai fada min tips din rike miji take yi, sai dau kawai na zuba mata ido ina kallon ta don a ganina Mai zan dauka tunda har ga Allah nidai ba son Yusuf nake ba, ni ynxu ma sai muyi sati bamuyi magana ba dama dama a WhatsApp yana dan mun magana sama sama.

Kwanci tashi gamu yau mun gama exam din second semester Wanda yai saura wata daya bikin, Aisha ma tun wancan watan ta gama WAEC.

A gajiye na isa gida, a Palour na tarar da Aunty Bilkisu da Umma suna magana gyaran jikin sa Aunty baby zata mana gaishe su nai na shige daki.

Kallon Umma Aunty Bilkisu tai tace "munyi magana da ita tace sbd nice a gida zata musu na sati biyu, ga kayan da'a dai na karbo musu masu inganci wadanda za'a basu su tafi dashi gidan mijin."

Ajiye ledar kayan da'ar Umma tai tace "baxa a basu wani ynxu ba knn"

Murmushi Aunty Bilkisu tai tace "Aunty Sadiyya nidai ba ruwana wallahi haka kurin a dura ma Yara magunguna mata azo miji ya musu fata fata, tsumin tsassaken baure kawai xamu basu sai zumar mata sun isa gaskia, sai a musu kaza da Hadin kankana in satin bikin ya kama."

Dariya Umma tai tace "hakan yayi, Allah ya nuna mana lafia, munyi magana da Abba ma akan kayan kitchen, nima nawa Mama magana ina so na siyar da gona ta a hada kudin ayi komai tunda daga kansu na gama kuma, sai na mike kafa na cigaba da kula da mazan"

Sun dade suna tattauna wa kafin Aunty Bilkisu ta shigo dakinmu ta samu a gaba tana fada mana sirrin rike Miji, nidai kaina na kasa sbd kunya don Aunty Bilkisu bata rufe komai, fada mana take.

Wani Abu da Aunty Bilkisu ta fada sai da Aisha ta fashe da dariya, girgiza kai kawai nai ina murmushi duk da bana cikin dadin rai.

Kusan rana daya aka kawo mana lefe nida Aisha, ni akwatuna 12 Aisha 10 kayane masu kyau a ciki da tsada.

Su Uwani da suka zo ganin lefen kamar zasu yi hauka sai sakin magana suke akan aikin banxa abinda ma mazinaci wata zata aura, ba Wanda ya kula Su haka sukai suka tafi.

Ni Kam tun ynxu na fara missing gida da kuma cilla don nasan rabuwa dasu ba abu bane mai wuya.

Sosai hidima ake kusan kullum Aunty Bilkisu damu muna kasuwa gurin siyayyar kayan kitchen, gaba daya na kara ramewa sai boobs da hips tubarkalla.

Mama kuwa gudunmawar turaren wuta da Humra da kolacca ta siyo mana a gurin Maman Sudais (08062073990) lokacin da Mama ta kawo mana sai da Umma ta karbi numbern Maman Sudais din da farko so tai ta diba Mama ta hanata shine ta karbi numbern zata siyo itama don humrar data shafa ranar taji kamalai a bakin Abba😉.

Sati biyu kafin bikin muka fara zuwa gidan Aunty baby gyaran jiki, kwana uku da fara zuwa mu kadai munyi wani irin fresh ba karamin gyara mu take ba har gashin mu turara sa ake, cikin sati daya gaba daya mun chanja duk inda muka gifta sai mun bar kamshin jikin mu Mai sanyi da dadi, gashin mu kanshi kamshi yake.

Duk yadda nake cikin bacin rai da auren nan bama yadda Yusuf baya zuwa zance kuma ynxu bama waya kwata kwata, amma wannan gyaran jikin da aka fara mana ba karamin faranta min rai yai ba, kullum cikin taba jikina nake, munyi fresh sosai Aisha ma tayi kyau sai shakiyanci take wai saura sati daya akai ta gidan miji taji mai ake ji.


**********
Bangaren Zeey ma sosai take Shan gyara gurin Mummy da Mama sai banka mata magungunan mata suke ko maganin sanyi na sati daya suka bata aka shiga banka Mata magungunan mata, gashi ya siyo supplement na Kara kiba sbd ta cicciko amma sam taki cikowar sai ramewa take.

Tunda kuma aka sa ranar bikin ko ta Kira Azlan baya daukar wayar ta duk da haka bata daddara ba kullum cikin tura masa messages take na soyayya.

A ynxu damuwar ta events din da suka hada wajen biyar don tun satin bikin zasu fara amma sam sun rasa ta yadda zasu fadawa Azlan..

A haka biki yazo aka shiga hidimaaaa amarya ba gyaran jiki sai magungunan mata kawai ake sha...


********

Kansa na kasa yana sauraran Abie, dagowa yai yace "duk yadda kake so kayi kawai Abie"

Shiru Abie yai yana kallon Azlan, shi ynxu Shirun yaron ya fara damunsa gaskia, kwata kwata baya magana komai aKa ce masa cewa yake duk abinda aka ga ya dace ayi.

Ajiyar zuciya Abie yai ya kalli Mami da itama ta zuba masa ido yace "kina jin danki ko ya bude baki ya fada min wani irin gida yake son zama tunda Mata biyu zai aura amma yayi shiru"

Dan murmushi Mami tai ta kalli Azlan tace "kayi magana mana Azlan a wani irin gida kake son zama"

Shiru yai yana kallon carpet din kokari yake ya hana kansa murmushi don shi yadda ake lallabasa ynxu abin burgesa yake shiyasa yake shiru shiru kamar salihi.

A hankali ya dago ya kalli Abie yace "Abie duk Wanda Ka bani ina godia Allah ya saka da alkhairi"

Gyada kai Abie yai yace shiknn da kwai gidana a sultan road gobe in Allah ya kaimu zan bawa Malam habu driver mukullan part din ya kai gidan amaren naka, part uku ne na tsakiya naka ne na gefe da gefen kuma kowa ya dau daya.

Murmushi yai yace an gode daga haka ya mike ya fita daga part din zuwa nasa, yana shiga ya fada gado yace a daura auren ni kuma lokacin Zan koma asalin Azlan dina wani murmushi yai yana shafa gemun sa..


Comments Nd share plz


Mrs A.M🥰
[04/09, 18:10] Deejarh🤍: ♠️♠️♠️♠️♠️

*TASWIRAR KADDARA*

♠️♠️♠️♠️♠️


Written by
Mrs A.M🥰

Page 26

*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃


*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*

*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*


*LOCATION KANO*

08062073990

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Yau ta kasance Wednesday kuma gobe zamu fara bikin, ranar Thursday za'a yi kamu ranar friday kuma daurin aure da yini.

Gaba daya na kara figewa sau ido da suka fito tubarkalla, Mimi kuwa sai murna take ana bikin Maa dinta ta tana ta shiga tana fita, itama duk kayan da zata sa a bikin Mami ce ta kawo mata.

Muna zaune a shagon Baby Beauty lounge na Aunty Baby, ana aka wanke mana kai aka zuba mana lafiyayyan kitso, ga lalle ja da baki bayan an wanke kafar.

Sai bin hannu na nake da kallo nayi kyau sosai lallen yayi kyau ya zanu kamar dora shi akai, murmushi nai ina kallon Aisha dake waya sai zuba shagwaba take.

Juyar da kaina nai cike da tausayin ta sai murna take bata San ko waye shiba, sai la'asar muka koma gida a kofar gida Naga cilla tsayawa nai nace ma Aisha ta shige.

Cikin sanyin jiki cilla yace "uwar dakina ynxu jibi zaki tafi ki barmu"

Juya kaina gefe nai Jin idona yana kawo kwalla, daure wa nai nace "ai zamu dinga haduwa a makaranta, kuma kai baxa Ka dinga zuwa gidan nawa ba"

Zaro ido yai yace "rufa min asiri uwar dakina, haka kurin naje gidan ki ango ya karya ni"

Harara na maka masa nace "waya isa ya karya aminin Batul"

Sai muka sa dariya a tare, mun dade muna hira sai da Umma ta aiko kirana sannan nai masa sallama muka shiga gida.

Gidan mu ya cika da Yan uwan Umma, dama yan uwan Abba na nesa a babban gida aka sauke su, sai bayan Isha'i Aunty Bilkisu da wadanda suka je mana jere suka dawo sai yaba gidajen suke.

Washe gari aka tashi da hidimar kamu wajen la'asar aka tafi hall din da aka kama, dama iya Mata ne.

Munyi kyau sosai nida Aisha mun sha lace dinmu maroon colour, a shagon Baby Beauty lounge aka mana makeup mun yi kyau har mun gaji don sosai Abba ya sakar ma Umma kudi don shima yace mune matan da zai fara aurar wa kuma na karshe.

An sha hidima sosai a gurin event din sai bayan Isha'i aka tashi, nidai jikina duk yayi sanyi ga faduwar da gabana yake in na tuna cewa gobe an daura min aure da Yusuf.

Muna komawa gida wanka na shiga nai, na wanke fuskata sosai jikina sai kamshi yake yana sulbi, murmushi nai bayan na shiga daki a can karshen katifa na kwanta kawai sai na fara tunanin Khadija da yadda muke cewa tare za'a mana aure, kuka na fashe dashi don mutuwar ta sabuwa ta dawo min yau dinnan.

Ganin kukan baxai min amfanin komai ba na mike na fita zuwa tsakar gida, har lokacin da kwai masu hada hada gurin yanke yanken kabewar da za'a yi amfani da ita gobe, wuce su nai zuwa toilet alwala nai na koma daki.

Na dade ina sallah ina addu'a akan Allah ya min jagora akan sabuwar rayuwar da zan fara, akan sallayar bacci ya dauke ni...

Washe gari tunda na tashi gabana yake faduwa, muna gama karyawa muka tafi shagon Aunty baby don makeup din daurin aure data yini za muyi baxa mu chanja kayaba sai za'a kai kowa dakin mijinta.

Karfe 12 aka gama mana muka koma gida, kowa sai tsokanar mu yake nidai nawa murmushi ina tare da Asma'u data zo duk da girman cikin ta don haihu yau ko gobe.

Ina zaune a dakin su Kamal sai duba agogona nake gabana yana wani irin bugawa ganin karfe biyu tayi duk yadda akai ynxu an daura....


***********
Lumshe idonsa yai Jin sanarwar daurin auren sa, yana sanye da wata lafiyayyar shadda fara an mata dinki da zare light blue ya kafa hula light blue yayi kyau har ya gaji, Amma fuskar sa ba alamun farin ciki shifa ji yake an daddaure sa taya za'a aura masa Mata biyu rana daya lallai kuwa za'a sha fama.

Dafa sa Haidar yai yace "mutumina gaskia kai Mai sa'a ne irin wannan aure haka na gata, Mata biyu rana daya wo Kai mai budurci."

Yatsina fuska yai yana ture hular kansa yace "kai kar Ka dame ni fah bana son hayaniya, ji nake kamar kaina zai fashe".

Dariya Haidar ya tuntsire da ita yace "ni muje na taya ka parking angon mata biyu don Abie yace daga yau ya yaye Ka daga kwana a gidan sa."

Dan dagowa yai ya zuba wa Haidar ido yana kankance idonsa sai kuma ya gyada kai yana wani shegen murmushi yace "muje"

Kin tafiya Haidar yai yace "meye Naga kace muje nifa rashin gardamar Ka akan auren nan yana ban tsoro."

Tabe baki yai yace "so kake nayi gardama a ce nayi rashin kunya, badai sun aura min Mata biyu ba ai sun gama nasu ynxu kuma turn dina ne"

Baki sake Haidar yake binsa da ido har sai da taga Azlan ya shige mota sannan yayi saurin daga kafa shima kar ya tafi ya barsa tunda yasan kadan daga cikin aikinsa.


**********
Muna zaune su Kamal suka dawo sai murna suke an daura auren, nan da gida ya cika da guda da murna.

Ni kam ji nake kamar na tsunduma ihu Allah ya sani bana son Yusuf Amma ya zanyi an riga da an daura.

Fitowa mukai aka shiga Kidan kwarya an kewaye mu nida Aisha, murmushi ne ya kubuce min ganin Mimi da Hidiya sai rawa suke sun kama kugun su sai juya wa suke.

wajen karfe 6 Aunty Bilkisu ta samu wanka shirya wa mukai cikin atampa iri daya nida Aisha aka rufa mana mayafi, tuni na soma kuka Aisha ma haka, feshe mu da turare Aunty Bilkisu tai aka kaimu gurin Umma dake zaune a Palour.

Nasiha tai mana sosai nida Aisha muka rungume ta muna kuka, tsaki Umma tai tana kokarin mai da kwallar idon ta tace "bana son sakarci Maza ku muke Allah ya shige muku gaba yai muku albarka"

Kara rungume ta nai ina kuka sosai, da kyar aka rabani da jikinta kasancewar motocin daukar amare sunzo dukkan su kuma an riga an fada musu sai Aisha ta rakani gidan hakan yasa da muka shiga aka nufi damu babban gida don acan su Abba suke dasu Kawu Nasiru.

Mama da Yakumbo ne suka shigar damu palourn Kawu Nasiru, sai da suka gaishe su sannan suka mana nasiha muma.

Miko min Kudi Kawu Nasiru yai yace "ga sadakin ki dubu dari an daura miki aure da baban Mimi, dama kuma dashi din za'a aura miki abinda yasa aka boye Miki kike ganin kamar shi zai auri Aisha sbd kin nuna kin amince wa da auren tin farko, bayan kuma mun san rabuwa da Mimi zai Miki wahala haka shima baban nata baxai yadda ki tafi da ita wani gidan ba a matsayin agola.
Aisha da kike ga tana waya da zance duk da Yusuf take shiyasa shi ya janye jikin sa daga gare ki, ita ynxu matar Yusuf ce Allah yai muku albarka gaba daya ya baku zaman lafia, sannan kuma bake kadai bace matar sa ku biyu aka aura masa yau"

Wani irin bugawa kirjina yai ni aka aurawa Mr Wicked, kuma wai mu biyu aka aura masa tabdijan....

"Ameen" mutanen palourn suka fada, Abba ma nasiha yai mana shima sannan yasa mana albarka, fito wa mukai a mota daya aka ajiye mu nida Aisha Yakumbo na gefena sai Mama a gaban sit.

Ni aka fara mikawa gidana sai santin gidan suke, basu dade ba suka fita gaba dayan su ko mutum daya ba'a bari ba, suna fita ana kawo Zeey, wannan ya tabbatar Kenan Batul ce uwargida..

Ina zaune akan gadon har akai sallar Isha'i, mikewa nai na shiga toilet nayi alwala akan carpet din tsakiyar dakin, ina zaune akai har bacci ya dauke ni ban sani ba...


**********

A bangaren Zeey kuwa ana kaita part dinta nan Yan uwanta suka fara caa akan delay din da sukai na kin kawo Zeey tunda rana gashi an fara kawo kishiyar ta kuma itace uwar gida.

Zeey Kam ko magana ta kasa sai kuka da take sbd bakin ciki, duk saurin da sukai ana idar da sallah aka taho kawo ta sai gashi amma wai sbd bakin ciki ynxu itace amarya kuma knn sai Azlan dinta ya fara kwana a dakin ta kafin ita.

Wannan abin yafi komai bakanta Mata rai, itama dai haka aka watse aka barta zaune tana jiran angon ta ya shigo ya ga kwalliyar da aka masa.


*********
Ban garen Azlan kuwa yana kwance a daki sai magana Haidar yake masa akan ya tashi ya shirya ya rakasa gidan sa amma yaki, sai da ya fadawa Mami ta shigo tai masa magana sannan ya mike ya shiga wanka.

Shiryawa yai cikin three quarter fari sai riga armless ash colour ta dame sa sosai yayi kyau, kwallin sa ya dakko ya rambada a idonsa sannan ya tura shi cikin alijun wandon Kar ya manta, a ransa yana fadin sai ya koma gurin da yake siyan kwallin wannan da aka kawo masa bashi da quality.

Turare ya fesa ta gyara sumar sa ya juya yana kallon Haidar daya zuba tagumi yana kallon sa, hade rai yai yace "muje don Allah bacci nake ji"

Tsaki Haidar yai yace "kaji shi kamar zai iya baccin bayan yana da tsala tsalan Mata har biyu"

Kankance idonsa yai yace "Haidar yaushe kaima ka iya vawulence wai, ya kake so Ka iskan tani kai baka san tsoron Mata nake ji ba."

Hararar sa Haidar yai yace "a tsoron matan Ka yi cikin Mimi ba"

Datse lip dinsa na kasa yai yana rike haba yace "ynxu shiknn kowa kallon mara budurci yake min koh"

Salati Abie dake bakin kofa yai yace "yaushe hankali zai shiga kanka wai Azlan baxa Ka daina irin wannan maganar ba"

Langwabe kai yai yace "Abie maganar gaskia ina kaunar budurci na wancan ma nasan garin kuruciya ne ya tafi Amma ynxu d akwai wani"

Juyar dakai Abie yai yace"bana son shakiyancin zoka wuce gidan Ka"

Marairaice wa yai kamar zaiyi kuka yace *Abie nifa tsoron Mata nake ji maganar gaskia bara na fada, haka kurin azo a lalata ma ni in dinga bin....."

Dakuwar da Abie yai masa yasa shi fashewa da dariya yana shafa kansa, murmushi kawai Abie yai ya juya yana girgiza kansa Yana ma Azlan fatan shirya da farko ya dauka ya shiryu da yaji ya daina maganar budurci Ashe lambo ya musu.
Chapter 1 · 0% Book details