← Book details Siradin Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 3 OF 3

Part ɗin aunty Naja suka shiga suka gaisa,tana ta tsokanar Khairi,ita dai khairi babu baki sai murmushi kawai

Siradin Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 13 min read

Bayan sun yi musu sallama suka wuce wani waje, Khairi ya firgita ganin irin motar da Auwab ya nuna mata da sunan tata, Mercedes Maybach s650,ta daka tsalle ta ƙanƙame shi,sai ta fashe da kuka

Ya na murmushi ya ce"kuka kuma alkhairi na? saboda ɗan wannan abin? noooo You deserve more than that alkhairina, I just want to keep my promise for standing by your side and be there for you"haka suka fito daga wajen cikin farin ciki, Khairi ji take yi a duk duniya babu macen da ta kai ta dacen miji


Saboda ya siya miki mota🙄😏

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️ Nusy bee
*Young talented writers association (YOTA)*

Page 86(end)

Har sun hau titi ya kalle ta da kulawa y ace"idan an ba ni izini zan iya zuwa ziyara asibiti?ina so zan ga wata mara lafiya ne"murmushi ta yi masa ta ce"go ahead love"ya yi murmushi yana lakace mata hanci,sannan ya karya kwana ya ɗauki hanya

Wani ƙaramin asibiti suka nufa,a harabar asibitin ya tsayar da motar shi,ya ɗauko face masks guda biyu,ya saka ɗaya ya sakawa Khairi ɗaya,sannan ya ɗauki Ajmal,ya ja hannun ta zuwa cikin asibitin,ita dai sai bin shi take yi tana buɗe idanu ta ga ina zasu je


A Nurses station suka gaisa da wata nurse,ya ce"Fareeda ya jikin nata?"Nurse fareeda,wadda a qalla zata iya zama sa'ar Auwab ko ya girme shi ta yi murmushi ta ce"jiki dai gashi nan engineer"Auwab ya ce"to Allah ya bata lafiya,ga yaro na don Allah ki riƙe mana shi mu shiga mu ganta"Fareeda ta amshi Ajmal ta na murmushi,shi kuma Auwab ya ja hannun Khairi suka yi gaba

Da sallama suka shiga wani ward,cikin tsananin mamaki take kallon wata ƙwarangal ɗin mata dake kwance akan gadon asibitin,gaba ɗaya kamar ba mutum ba,sai wari ke tashi daga jikin ta,ga dai female nurses nan sanye da gloves suna ta faman gyara ta

Ƙarasawa Auwab ya yi gaban gadon yana kallon matar, Khairi ma ta bi bayan shi tana kallon ikon Allah,itama matar sai kallonsu take yi,Auwab ya ce"sannu Inaaya!ya jikin?"

Hawaye suka fara zarya akan fuskar Inaaya,cikin kuka ta ce"ka yafe min Auwab, Khairi ki yafe min,kun ga yadda Allah ya yi dani ko?komai ya ƙare min,iyaye na sun gamu da asarar dukiyoyin su,baƙin cikin hakan ya yi silar rasuwar mahaifina, mahaifiya ta ma ta rasu saboda hawan jini,bani da kowa bani da komai,raina kawai ya rage min,shima na san zan iya rasa shi kowanne lokaci,a yanzu a dalilin mijinki da na ƙuntata rayuwar shi da sunan soyayya saboda son zuciyata,shine kawai yake taimakon rayuwata,na zo a banza zan koma a banza"

Jikin Khairi ya yi sanyi sosai, tausayin Khairi da tsoron duniya suna shigarta,cikin sanyin murya ta ce"A'a har yanzu kina da dama Inaaya,ni dai na yafe miki har ga Allah kuma na san yaya ma ya yafe miki,ki koma ga Allah,ki dage da yawaita istigfari da neman yafiyar Allah,in sha Allah baza ki koma a banza ba Inaaya, Allah ya baki lafiya "Auwab dai sai kallon Khairi yake yi, soyayyarta tana sake shiga ranta,ta burge shi sosai,kuma ta ƙara ƙima a idanunshi

Kamar yadda ya saba duk sanda yabzo ya bada kuɗi mai yawa yabce a cigaba da kula da ita,tana ta masa godiya tana kuka

A mota dukkan su shiru suka yi,ganin shirun ya yi yawa Auwab yace"I'm sorry my Khair,na yi abu ba da sanin ki ba ko?"ɗaga idanu ta yi ta kalle shi,ta ce"me kenan?me ka yi?"

Yace "na shiga rayuwar wata baki sani ba"ta yi murmushi ta ce "rayuwar ta gaba ɗaya abar tausayi ce yaya,daga yadda na fuskanci rayuwarta bata yi dacen iyaye ba,don yaya sulaiman ya bani labarin yadda suka yi da mahaifinta,sannan kuma bata samu ilmin addini ba da alamu, Shiyasa ta aikata abubuwa da yawa,na tausaya mata "ta ƙarashe magana cikin jimami

Yabyi murmushi ya ce"da tasirin ƙawaye ma a cikin lamarinta,kin ga ƙawaye suka lalata mata rayuwa suka koya mata abubuwa marasa daɗi da yawa,ƙawaye suna tasiri sosai a rayuwar mace,kamar wata ita ma ƙawaye sun yi galaba akan ta,har suka bata maganin da ya so hana ta haihuwa"da sauri ya kalle shi ta ce"hana haihuwa kuma?garin yaya?ya za su hana ta haihuwa don zalunci?"dariya ta so ta ƙwace masa ya ce"kema dai kya faɗa,amma yanzu tana nan ta haihu abinta,ɗanta kyakkyawa Masha Allah"har ta buɗe baki zata yi magana ta gano inda ya dosa,ta galla masa harara ta ɗauke kai tana faɗin"ni ƙawaye na ba mutanen banza bane"

Auwab ya yi dariya ya ce"ni fa ba dake nake ba kika tsargu"ta ce"ni fa ba yarinya bace"ya ce "na sani,ke ɗin babbar mace ce"ta yi ɗan murmushi kawai,suka cigaba da hira cike da shauƙin juna har suka isa gida

Satinsu ɗaya da dawowa daga albasu suka je Kaduna, Khairi ta yi mamakin kyautar bajintar da Auwab ya yi wa mama Hajara,don danƙareren gida ya siya mata,ya ba ta jari mai tsoka sannan ya biya mata hajji da Umrah,har rasa bakin godiya ta yi,ita kanta Mamie ta yi matuƙar jin daɗin wannan abu da sirikin nata ya yi wa wadda ta yi sanadiyyar sake haɗuwa da ƴarta

Kwanansu ɗaya a Kaduna suka dawo,sai dai kafin su dawo Khairi da kanta ta roƙi Abba mijin Mamie cewa yayanta yana son auren Nabeela,Abba ya ji daɗin hakan sosai, Hisham da suka yi waya ma ya ji daɗin hakan

Ai kuwa sati biyu tsakani aka sanya auren Nabeela da Azad watanni uku,don karatunta ma yanzu ta haƙura da shi,don sun yi waya da Azad ya ce mata zai nema mata makaranta a Melbourne

Shima Hisham ya ce wa Azad "to tunda zaka raba ni da ƙanwa ta nima fa sai na raba ka da taka,don nima dai na ga auta,kuma I'm interested"Khairi ta yi matuƙar murna sosai,sai dai nasu da aka saka an saka watanni shida, lokaci guda da na Surayya da zata auri wani ɗan abokin Daddy

Sati biyu da saka bikin su Azad Khairi na zaune tana bawa Ajmal abinci Auwab ya shigo da sallama,ta ɗaga idanu ta na kallonshi ta na murmushi,a hankali ta ce"sannu da zuwa Abu Ajmal!"

"Yawwa mar'arussaliha!ƙarasa ba shi abincin ki ɗauko hijabinki"

Kallonshi yia yi ta ce"ina zamu je?"

Auwab ya ce"ke dai kammala ba shi abincin zan gaya miki "babu musu ta cigaba da bawa Ajmal abinci,wanda shi kuma gaba ɗaya hankalinshi ya koma kan abban nashi da yake ta masa wasa,shi kuma ya na ɓangale masa baki

Ta na gamawa ta ɗauki hijabinta,shi kuma ya ɗauki Ajmal,ta saka hijabinta suka fice daga parlourn

Ɗaure fuska ta yi ganin sun nufi part ɗin Sulaiman,da sallama suka shiga, Mifra da ke zaune kan kujera ta ɗago da fara'a ta na amsawa, Sulaiman da ke zaune kan study table daga gefe ya ɗago ya na ɗan murmushi,ya ce"an gaida babban yaya!"

Auwab bai amsa ba,ya samu waje ya zauna, Mifra ta gaida shi,ya amsa da sakin fuska, Khairi ta gaida Sulaiman,shima ya amsa,ya na murmushi, Auwab ya kalli Khairi ya ce"Khair ba ki gaida yayarki ba"

Shiru ta yi ta na cin magani,kafin a daƙile ta ce "ina kwana!"

Murmushi ya yi kawai ya na girgiza kai,ya san halin khairi sarai,yanzu ƙarfe takwas na dare ne amma ta ce ina kwana, ya tuna zaman su a Boston,idan ta juya irin wannan gaisuwar to bata yi niyya ba,ya mayar da hankalin shi ga Mifra da ta amsa gaisuwar da fara'a,ya sake kallon Khairi da ta ɗauke kai,ya ce"Ummul khairi ki bawa yayar ki haƙuri,kinga ita ke sama da ke,bana jin daɗin yadda kuke samun saɓanin nan,abin ya isa haka"

Baƙin ciki ya ƙule Khairi,har ta buɗe baki don ta bayar da haƙurin Sulaiman da ke zaune daga can gefe ya ce

"Abin fa da ciwo ayi maka laifi ace ka bada haƙuri"Khairi tana jin haka ta ja baki ta tsuke

Mifra ta kalli mijin nata da ya yi fuska,a sanyaye ta ce"ki yi haƙuri maman Ajmal,don Allah, sharrin shaiɗan ne"Auwab ya kalle ta ya kalli Khairi ya ce"kema ba ta haƙuri,bana son taurin kai please"ta tura baki ta ce"yi haƙuri"Mifra ta yi murmushi ta ce "ni ya kamata na baki haƙuri,don Allah komai ya wuce "

Khairi ta ce"ya wuce"ta ɗauki Ajmal ta na sassauta fuskarta ta ce"sai da safenku"bata jira amsarsu ba ta fice

Auwab ya rufe Sulaiman da faɗa ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, murmushi kawai yake yi ba tare da ya kalli Auwab ɗin ba, Auwab ya fice daga part ɗin a fusace

Ƙarshe dai sai washegari Ammi ta sasanta su,komai ya wuce kamar ba su ba

Kwana uku tsakani Auwab da Khairi suka tare a tamfatsetsen gidansu da ke kusa da gidan Daddy a lugard road,har da Mifra aka raka Khairi sabon gidan da Auwab ya ce mallakin Khairin ne

Lokacin bikin su Nabeela Khairi Kaduna ta koma,a can ta haɗu da ƙawarta Amra sadeeq, su kayi ta murnar ganin juna,ita kam tana India tana faman karatunta na medicine,da Khairi take daf da farawa a University of Boston inda Auwab ya yi mata komai zuwa yanzu

Daga Kaduna sai da aka fara kai ta gidan Daddy,aunty Naja ta tarbe su sosai,su Khairi dai sune manyan aminan amarya kuma ƙannen ango,don ma wannan cikin ya ɗan zo mata da laulayi

Bayan an gama biki Auwab ya tattara matar shi suka bar ƙasar zuwa Boston bakin aikin shi,sai dai ya sauya musu gida,don baya son ta rinƙa tuna abubuwan da suka faru a baya

Bayan kwana uku da komawar su wanda yake kula da Inaaya ya kira shi ya sanar masa da rasuwar ta,ya jinjina ya yi mata addu'ar neman rahamar Allah,ya sanar da Khairi,itama ta bita da addu'a


BRUNSWICK, MELBOURNE, AUSTRALIA

A hankali take buɗe idanunta ta na kallon shi, murmushi ne kwance akan fuskar shi, itama murmushin ta yi ta lumshe idanunta,ya lakace mata hanci yana murmushi ya ce "it is time my lady,wake up"shiru ta yi ko niyyar tashi bata yi ba,ya na murmushi ya ce "ko jikin ne?"

Ta shagwaɓe fuska,ya sa hannu ya ɗago ta ya rungume ta,har yanzu jikinta da zazzaɓi sosai,cike da jimami ya ce"anya kuwa zaki iya Nabeela?kullum cikin zazzaɓi?"

Ta tura baki ta ce"ni dai zan iya,kuma ni da kaina zan haihu,ai Mamie ta gaya min zan daina idan ya kai wasu watanni"zaro idanu ya yi ya ce"gayawa Mamie kika yi?tona min asiri kika yi?"ƙwalla ta ciko idanunta ta ce"Ni fa ce mata na yi bani da lafiya shine ta gaya min yadda zan yi"

Ya goge mata hawayen cikin lallashi ya ce"is okay!daina kukan na fahimce ki,to ya batun taryar baƙin namu?"

Ta kalle shi ta ce"Allah ya kawo su lafiya,wai su waye za su zo ne?"

Ɗan shiru ya yi yanayinshi yana sauyawa,kafin ya ce"budurwata ce zata zo!"

Kallon yadda yanayinta ta sauya kawai yake yi,a hankali ya ce"ko na ce mata ta koma?"

Ta kwantar da kanta a ƙirjinshi ta ce"a'a, Allah ya kawota lafiya"ya yi ɗan murmushi kawai yana shafa kanta,da gaske ya na alfahari da Nabeelan shi, Allah ya yi masa kyakkyawan sauyi mafi alkhairi,akwai ta da hankali da nutsuwa, sam bata da hayaniya ballantana rigima,ga haƙuri da juriya,ya shafa fuskarta ya ce"sai na dawo,bari na ɗauko ta"Nabeela ta ce"Allah ya tsare"Azad ya fice daga ɗakin,ta bishi da kallo hawaye ya na zubo mata

Kifa kanta ta yi akan pillow ta na kuka,ta daɗe ta na son Azad tun kafin ta san menene so, Allah ya sani ta na kishinshi,amma ta ƙudurce a ranta za tayi masa komai yake so don ta faranta masa

Kitchen ta shiga ta fara ɗora abincin da bazai ɓata mata lokaci ba,tana girkin tana toshe hanci,don kwata kwata ƙamshin abincin baya yi mata daɗi

Ta na cikin girkin ta ji shigowar su,kamar a mafarki ta ji muryar Khairi,da sauri ta fito daga kitchen ɗin,ta yi arba da Khairi da cikinta ta fito sosai

Sam ta manta da wata jinya ta tafi da gudu zasu rungume juna,cikin wani irin zafin nama Azad ya yi caraf ya cafke ta yana faɗin "relax Madam!ko kin manta ba ke kaɗai ba ce?"

Sakin baki Khairi ta yi tana kallon su, Nabeela ta shige jikin shi tana murmushi, Khairi ta ce"kan bala'i!"Auwab ya ce"with due respect sir!Nima matar tawa ba ita kaɗai bace,yallaɓai!"Khairi ta kama dariya

Sun zauna suka yi ta hira sosai, Khairi ganin yanayin Nabeelan ya sa ta karɓi girkin gaba ɗaya

A ranar ba su bar gidan ba sai dare,dama wani aiki ya kawo su Sydney suka ƙaraso Melbourne, Nabeela ta so abar mata Ajmal Khairi ta ce bazai yiwu ba,wahala zai saka ta saboda yanayin jikin ta

Nabeela ta yi matuƙar farin cikin wannan ziyarar, musamman da ya kasance da farko bata saka rai da ganinsu ba

Washegari suka koma US bayan sun zo har gida sunyi musu sallama, Khairi sai tsokanar Nabeela take yi, Nabeelan tana ramawa,amma Khairi ba ƙaramin farin ciki ta yi ba ganin alamu sun nuna Azad ɗinta ya dace da mace ta gari


BAYAN WASU SHEKARU......


A nutse take ƙarasa shirinta cikin wani tsadadden lace maroon color da aka yiwa ɗinkin doguwar riga,ta yafa mayafin ta mai ɗan girma wanda ya dace da kayan nata,ta ƙarewa kanta kallo a madubi don ganin inda ta yi kuskure don ta gyara

Auwab da ya shigo yanzu ya rungume ta tsam a jikinshi,a kunnenta ya raɗa mata"congratulations DR UMMUL KHAIRI ABUBAKAR ALBASU! Allah ya yi riƙo da hannayen ki"juyawa ta yi tana murmushi tana kallon shi,ta yi cupping fuskarshi,cikin wata murya mai jan hankali ta ce"kaine silar komai,kaine komai,kuma ka gama yi min komai, babu abinda zan ce,face Allah ya cigaba da buɗa maka,ya albarkaci zuriyarka, Allah ya bar mu tare nisfu hayaty"ta ƙarashe tana rungume shi,yana murmushi ya kamo hannunta don zuwa buɗe katafaren asibitin ta da Daddy da Auwab ɗin suka gina mata,shi kuma Abba, da Azad da Sulaiman suka zuba mata duk abinda take buƙata a asibitin,kama daga kan manyan abubuwa har zuwa ƙanana

A yanzu ta zamo ƴar gata a family,kowa ji da ita yake yi,a wajen mijin ta kam ji take yi Kamar babu wadda ta kai ta dacen miji

A can suka haɗu da su Nabeela da Azad, waɗanda a yanzu yaran su huɗu,na farko ƴan biyu maza,sai mata biyu da suka biyo su,sai Nusra,ita kam yaran ta biyu,sai Amra ƙawar Khairi,ita ƴar ta ɗaya,sai sulaiman da Mifra,suma bayan Anam yaransu biyu yanzu,sai Amra ƙanwar Auwab da ke da uku, sai Beely da itama yaran ta biyu

Tana zuwa suka kewaye ta da farin ciki kowa yana mata barka,sai murmushi take yi cike da farin ciki

Taro ya tashi lafiya,anyi cikin nasara da farin ciki,babu abinda ya ɗauki hankalin mutane kamar ɓangare na musamman da aka yi don duba masu ciwon athma kyauta, Khairi ta ce ta sadaukar dashi ga yayanta,aminin ta Saeed Umar Saeed wato Azad,kusan duka ƙannen Azad ɗin sai da suka yi hawaye, Azad ya ji daɗin wannan abu sosai, Khairi dai farin ciki babu kama ƙafar yaro,a ranar yaranta suna wajen Sulaiman da shima tuni ya koma gidanshi

A yanzu bayan Ajmal yaranta biyu itama,ta farko sunan mum aka saka mata,suke kiran ta da Junaina, lokacin da suka sanarwa yaran mum sunan yarinyar sun yi matuƙar mamaki da farin ciki,na ukun kuma aka sanya masa sunan Daddy ake kiran shi da affan

A yanzu farin ciki ya wanzu sosai ga wannan ahali,kansu a haɗe yake sosai, barrister Umar da lieutenant general Usman babu abinda suke yi sai hamdala ga Allah sun san ba yin kansu bane ballantana iyawar su,a kullum yaran nasu basu da buri sama da na faranta musu rai


TAMMAT BIHAMDULILLAH

Nan na kawo ƙarshen littafi na mai taken SIRAƊIN UƘUBA, abinda na rubuta na kuskure Allah ya yafe min,ina matuƙar godiya ga readers har ma da reviewers ɗin wannan littafi,ina alfahari da ku da fatan Allah ya bar mu tare

Sai Allah ya haɗa mu a labari na gaba in sha Allah mai taken KADDARAR MU CE (ta zo a haka)wanda shima ya ɗauki salo dabam da na sauran littafai na,ku dai kada a baku labari,sai mun haɗu kawai😅

Taku har kullum, Nusaiba Ibrahim Rimi (Nusy bee)
Chapter 3 · 0% Book details