Part ɗinta ta koma,har yanzu Auwab ya na zaune,ta ɗauke kai ta nufi ɗaki,ya tashi ya janyo ta ya rungume ta ya na murmushi
Siradin Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
"Ni cika ni, tunda haka ne "
Ya sake rungumeta ya ce"me na yi miki?"ta ce"yaudara mana,kawai ka tayar min da hankali ka hana ni bacci"babu shiri ya kama dariya,ta sake kumbura,cikin kufula ya ce"dole ka yi min dariya tunda ka hana ni bacci"ya juyo da ita ya na murmushi ya ce "ban san har yanzu alkhairi na tana yi na ba sai da na ga ta hana idanunta bacci, after every minute sai ta duba ta ga Auwab ɗin ta yana numfashi?a sannan na san Yes har yanzu ban fita a zuciyar alkhairi na ba"kunya ta kama ta sosai,ta sunkuyar da kanta,ya ɗago haɓar ta yana son haɗa idanu da ita,ta yi ƙasa da idanunta,ya raɗa mata a kunne "da farko na sare,na sallama,na yi tsammanin bani da rabo,amma a yanzu na samu ƙwarin gwiwa!ina alfahari da alkhairina,ta zame min komai,ta cike kowanne gurbi a raina,I love you more and more lovely wife"kunya ta rufe ta,ta kwantar da kanta akan ƙirjin shi,ya rungume ta sosai a jikinshi yana aika mata da kisses ta ko'ina cikin shauƙin so da kulawa
Shine ya taya ta suka gyara gidan,ta sauka sosai sai hirarsu suke yi,yana tuna mata da rayuwarsu ta Boston kafin komai ya lalace,suna gama ta miƙe zata fita ya riƙo ta ya ce "ina za ki je ne Madam?"
Kallon shi ta yi ta na ɗan murmushi ta ce"Ajmal zan ɗauko a part ɗin Ammi"ya janyo ta jikinshi ya na faɗin "kafin nan ƴan mata,sai kin fara koya min rawar da har yanzu aka gagara cigaba,na matsu na ga na iya rawa sosai,kamar dai alkhairina"Khairi ta kama dariya ta ce"ai sai dai na fara daga farko,don wallahi yaya babu abinda ka iya a rawa"ya buɗe idanunshi yana murmushi ya ce"to laifin waye?"ta na murmushi ta ce"na waye banda engineer?"ya yi dariya ya ce"Ni ban nan yarda ba,ba laifi na bane"ya janyo ta sosai a jikinshi ya ce"Ummul khairi tell me now,do you love me?"
Lumshe idanunta ta yi tana murmushi,a hankali ta jinjina kai,ta ce"I love you more Abu Ajmal!"
Da ƙarfi ya rungume ta ya na murmushi ta lumshe idanunta ta fara
"You drive me crazy baby can't you see 🎼🎵
Whenever you are ready
Tell me I will be ready yeah🎵🎼
Let me dance with your body kokoko 🎼🎶....."
Sai ji ta yi ya amshe ya na mata raɗa a kunne
"I wanna move with your body lololo 🎵🥰.."da sauri ta buɗe idanu ta na kallonshi da mamaki ta na murmushi,shima murmushin yake yi yana kallonta,ta ce"yaya kaima ka iya waƙa?"
Ya ce"can you remember ana i gobe za ki ɓata?na zo na same ki kina jin waƙar kina yiwa Ajmal,tun daga nan waƙar ta shiga rai na,sai da na nemo ta,idan ina kewarki sai na kunna na ji ta"murmushi ta yi ta ce"Allah sarki yaya na,amma ni ba ɓata na yi ba"Auwab ya ce"okay!a bar maganar kawai,mu je mu ɗauko Ajmal dare yana yi"babu musu ta miƙe suka fice daga part ɗin suka nufi na Ammi
A ranar tare suka kwana a part ɗin nashi,ko Ammi bata sani ba,kuma washegari tare suka shiga kitchen don girkin abinda zasu ci,suna ci suna hira,gaba ɗayan su rayuwar su ta Boston ce ta dawo musu, Auwab sai taɓa khairi da maganar yake yi,ita ma tana biye masa suka yi ta hira,karo na farko kenan Ajmal da ya ga iyayen nashi cikin so da shauƙin juna
Da yamma ya ce su shirya ta raka shi unguwa,ta yi kwalliyar ta cikin Egyptian abaya off white,da kanshi ya naɗa mata mayafin ya na faɗin "inyeeeee!what a beautiful lady!!mata ta tafi ta kowa"sai murmushi take yi,itama ta na gyara masa zaman rigar jikinshi ta ce"mijina ya fi na kowa"ya yi murmushi ya ɗauko Ajmal da ta shirya shi shima,suka fice daga part ɗin suka rufe,suka shiga part ɗin Ammi suka shaida mata za su fita
Ta ɗaga kai ta na kallon su,wani sanyi ta ji ya ratsa ta,don ita sai yanzu ta gansu tare,ki jiya da suka zo ɗaukar Ajmal Auwab a bakin ƙofa ya tsaya,ta yi murmushi ta ce"to Allah ya tsare,sai kun dawo"daga nan suka fice zuwa inda motar Auwab ke ajiye a parking space
Daga nan kai tsaye lugard road suka nufa, Khairi sai da ta yi kuka ganin sashen mum a kulle,don Beely dai ta koma gidan mijinta,feena dama ta na ɗakin ta, Nusra kuma ta koma wajen aunty Naja
Hannunta ya riƙe yana kallonta,a hankali ya ce"alkhairina kukan me kike yi?"
Ta kalle shi cikin rawar murya ta ce "wasu shekaru baya part ɗin mum ne kaɗai inda yake da mutane,kowa a nan yake rayuwa,yau an wayi gari an rufe shi, saboda mum bata raye"
Auwab ya riƙe hannunta sosai,cikin kwantar da murya ya fara magana
"Ummul khairi!haka rayuwar duniya take, shiyasa zalama bata da daɗi bata da amfani a cikin rayuwa, saboda watan watarana Allah zai iya juya lamarin daga yadda muke kallon shi zuwa wani bigire da bamu taɓa tsammanin zai je ba,shekaru biyar baya ban taɓa tsammanin wata mace za ta shiga rayuwata ba,ban taɓa tsammanin a duniya akwai wanda zai juya min ra'ayi ba baya ga iyaye na,tun a wancan lokacin mahaifina ya taɓa gaya min cewa akwai matar da zai aura min,but I'm free na auri wadda nake so, Ummul khair ban taɓa tsammanin kece ma wadda suke nufi ba,ban taɓa tsammanin zan ɗauke ki a matsayin mata ta ba,duk hakan ya faru,mun sani dole watarana zamu mutu,babu abin mamaki da rasuwar mum,kuma tunda ta rasu komai ma daga baya ne,don haka bin ta da addu'a shine kawai gatan da zamu iya yi mata"
Sosai ta ji tausayinshi,ta ce"Allah ya ji ƙan mum,amma yaya meyasa bazaka cire abinda Inaaya ta yi maka daga ranka ba?"
Ya kalle ta cikin kulawa ya ce"ba abu ne mai sauƙi ba,amma na yafe mata,kuma ina fatan Allah ya raba ni da wata masifar irin wannan"ta yi murmushi ta ce"Ameen mijina abin alfahari na"ya yi murmushi yana gyara riƙon Ajmal suka nufi cikin gidan