← Book details Siradin Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 3

Gabatarwa

Siradin Ukuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 644 min read

🔥SIRAƊIN UƘUBA🔥


Alƙalamin Nusaibat ibraheem rimi (Nusy bee)(marubuciyar littafan ku masu farin jini wato matar khalees da barrister Hibba)

_Free_ _book_

بسم الله الرحمن الرحيم

GARGAƊI....

Littafin SIRAƊIN UƘUBA mallakar Nusy bee ne,ban yarda a canja min shi ta kowacce fuska ba,sannan kuma ƙirƙirarren labari ne,nayi ne kawai don faɗakarwa da nishaɗantarwa,idan hali ko yanayi ko suna yazo ɗaya da na wani ko wata,to a rashin sani ne,ba da nufi nayi hakan ba

SADAUKARWA.....

Na sadaukar da littafin SIRAƊIN UƘUBA ga Makaranta littafan *NUSY *BEE ,kune ƙwarin gwiwa na saboda likes, comments da share da bakwa gajiya da yi min, Allah ya bar mu tare🥰

Littafin SIRAƊIN UƘUBA free book ne,ina addu'ar duk wanda ya amfana da wannan littafin Allah ya kai ladan kabarin mahaifi na abin alfahari na *Captain* *Ibrahim* *Yahaya* *Rimi* , Allah ya jaddada rahamar shi a gare shi da ma sauran mamatan mu,ameen thumma ameen

Page 1

GIDAN SA'IDU MANOMI,ƘAUYEN ALBASU,KANO STATE, NIGERIA

Yara ne daga shekaru goma sha shida zuwa a ƙasa da a ƙalla zasu doshi talatin,suna ta hayaniya,masu wasa sunayi,masu hira sunayi,har da masu musu,wasu kuma suna tare da iyayen su suna taya su ƙananan ayyukan da baza'a rasa ba,wasu kuma suna wajen wata dattijuwa,wadda da alamu kakar su ce tana yi musu tatsuniya suna dariya

Daga can gefe na hango ta, yarinya ce da bazata gaza shekaru goma sha uku ba,baƙa ce,doguwa,bata da jiki sosai,sanye take da wata tsohuwar doguwar riga ta atamfa, kanta ɗaure da kallabi wanda ya gaji da duniya,daga ita har kayan jikin nata babu alamun wanki ko wanka a tare dasu,ta jingina da bishiyar mangwaro da take kusa da ita,sai sharar bacci takeyi cikin kwanciyar hankali

Baba Hari,ɗaya daga cikin matan kawunnan ta ce ta kula da ita,cike da jin haushi ta girgiza kai,tana faɗin"shegiyar yarinyar nan indai yin abinda za'a zage mu ne,to ta san duk wata hanyar da zata bi ta saka a kalle mu a wulaƙance,in banda wulaƙanci da mugun hali shi kuma wannan baccin ƙaryar na menene?"ta saka ƙafa ta zungure ta da ƙarfi,ai kuwa ta farka a firgice,sai dai cikin magagin bacci,baba Hari ta take ta tana faɗin"shegiya mai baƙin hali irin na uwar ta,tashi ki je ki kwanta kar ki ja min bala'i"gwaggo sarai ta juyo tana kallon su tana faɗin"kema dai harira da ɗorawa kai kike,banda jaraba waye bai san halin UMMIYO da jarabar bacci kamar kasa ba?"harira tace"wai kar ace ka bar Maraya a wulaƙance ne,banda haka Ni ai sakawa yara na idanu ya ishe ni,babu ruwa na da yayibe yayiben yaran jama'a"Sarai ta kwashe da dariya tana kallon ummiyo da ta nufi ɗakin baba atine tana haɗa hanya,sun san irin magagin baccin ta,har waje tana ficewa idan tayi irin wannan baccin aka tashe ta, suwaiba tace"Allah ya haɗa ta da atine don uban ta"harira tace"ya haɗa ta ma,tunda bata da hankali, yarinya kullum tana girma amma tana cin ƙasa,ita ba....."ihun da ummiyo ta saka tana fitowa daga ɗakin atine da ta biyo bayan ta da bulala ne ya katse harira,sukayi shiru suna kallon yadda atine take zazzaga masifa tana zagin ummiyo ta uwa ta uba,dama ita babu wanda ta ƙyale a gidan,duk wanda ya taɓa ta ko a kuskure ne sai ta ganar dashi kuskuren shi

Gefe ummiyo ta samu ta tsugunna tana kuka, Sarai ta kalle ta ta gatsine fuska tana faɗin

"Sai kiyiwa mutane shiru,ki tashi ki nemi makwancin ki"babu musu ummiyo ta miƙe tsaye tana kuka tana susar kai,ta wuce zuwa ɗakin nata,don dukan da baba atine tayi mata ya sa ta wartsake daga nannauyan baccin da takeyi

Nadiya ce da ta shigo daga makarantar dare a lokacin da baba atine take ta masifa ta bi ta da kallo cikin tausayawa,dama kaf gidan idan ba kawunnan ta ba babu mai tausaya mata sai Nadiya,wata iriyar rayuwa Ummiyo takeyi a gidan kamar ƴar tsintuwa,ko nace bola ma kai tsaye,babu wanda ya damu da tayi wanka? ballantana wanki ko makaranta,ko uwa uba taci abinci?amma masu ɗora mata tallace tallace sun damu sosai da ta kawo musu kuɗin su daidai?ko ƙwandala bata ɓata ba? kullum rayuwar ummiyo kenan a gidan,sauran yara su tafi Makaranta ita kuma ta wuce talla,da yake bata da wayo ita abin bai wani dame ta sosai ba

Ko da ta shiga ɗakin ta ma kukan ta ta cigaba,kafin bacci ya ɗauke,duk da tarin cinnaku,kuɗin cizo,kyankyasai da ɓerayen da ke ɗakin a haka take kwana,bata tunanin ta gyara,babu wanda yake tunanin ya gyara mata,tayi kwanciyar ta a kan matacciyar tabarmar ta,tuni bacci yayi awon gaba da ita

Bata juma da kwanciya bacci ba su baffanin ta isyaku da kamilu suka shigo gidan,isyaku yana janye da rago,kamilu kuma rike da leda a hannun shi,babban ɗan shi sunusi kuma yana rike da kajin Hausa manya manya waɗanda suka ji kiwo mai kyau, dukan su fuskokin su washe da farin ciki da annushuwa,bayin Allan da ke zaune a ƙaton tsakar gidan suka fara mayar da hankalin su gare su ɗaya bayan ɗaya,yaran suka mike suna musu sannu da zuwa,suka amshi kayan da suka shigo dashi,sai murna sukeyi,don wannan alama ce ta za'ayi wasu manyan baƙi waɗanda suke da kima kwarai da gaske, baffa kamilu wanda ake kira da baban Jamila,ya amsa gaisuwar su cikin sakin fuska sannan ya shiga ɗakin matar shi ta biyu Inna haleema,wadda duk abinda akeyi bata fito tsakar gidan ba

Ba yabo babu fallasa ta karɓe shi kamar yadda ta saba,ta kawo masa tuwon daren da tayi, kasancewar yau itace da girki,bai wani ci da yawa ba ya mike ya fice tsakar gidan yana faɗin"haleematu ki fito don ina da magana da Mutanen gidan baki ɗaya"ta bi shi da kallo kafin ta taɓe baki,ta cigaba da ƙulla gyaɗar siyarwar ta,da duk sanda tayi Ummiyo ke ɗaukar mata,amma ko ladan gyaɗar bata iya bata ballantana ta bata kuɗi,amma fa idan ta ɓatar da ko ƙwandala ta rinƙa bala'i kenan sai an biya ta,inna hari ce dama mei biyan,ta gama biya ta zage Ummiyo da gori da cin mutunci,kuma baya hana gobe ma idan aka ɗorawa Ummiyo talla ta ɓatar da kuɗin ta sake biya tana mita tana surutai,ita kam Ummiyo sam abin ko damun ta baya yi

Wajen ƙarfe tara da rabi na dare isyaku wanda aka fi sani da baban Bello da baban Jamila,wato kamilu suka tara iyalan gidan a ƙaton tsakar gidan,ciki har da mahaifiyar su Inna sabuwa,daga nan cikin farin ciki suke sanar da su zuwan manyan baƙin su gobe, lieutenant general Usman Saeed albasu,da Barrister Umar Saeed albasu, waɗanda su ɗin yayye ne a wajen su

Take gidan ya ɗauki shewa,don rabon su da zuwa garin shekaru tara kenan,tunda suka zo ta'aziyyar babban yayan su da ya rasu sanadiyyar haɗarin mota,kuma sun sani,zuwan waɗannan bayin Allan na nufin buɗewar ƙofar alkhairin su

Sai da waje ya natsa sannan baban Jamila ya cigaba da bayani"a saboda haka muna buƙata ayi musu abinci mai kyau,mai rai da lafiya,don Allah ku mayar da hankali wajen tarar waɗannan baƙi masu daraja da zasu zo,abin dubawar shine ba goben zasu tafi ba,kamar sai jibi ma,don haka don Allah ya kamata ku kasance masu taka tsantsan,duk wani kayan sana'a da akeyi a daure a haƙura har sai sun tafi, saboda kun dai san yadda sha'anin mutanen Maraya yake da wahala"

Baba Hari uwar ƴan kauɗi,wadda ta kasance itace uwar gida a wajen baban Jamila,asalima itace mahaifiyar sunusi da jamilar tace"in Sha Allah zamu kiyaye, Allah ya kawo su lafiya,to dama Allah na tuba ai talla ba a gaban ɗan birni ba,amma dai ku ƙara jan kunne don akwai waɗanda bai zama lallai su ji ba"

Haleema ta yanka wa harira wani mugun kallo,don ta san da ita take,hari kam ko kallon banza bata ishe ta ba,cikin wulaƙanci da raini haleematu ta kalli baban Jamila ta gatsine fuska tace"ai kuwa sai a ɗaga min ƙafa,don na soya gyaɗa bazan bar ta tayi hunhuna ba"

Kai tsaye yace"sai ki ɗauka da kanki ko ki saka ɗaya daga cikin agololin ki,amma a yaran gidan nan babu wanda zai ɗaukar miki"

A zafafe ta mike tana masifa wai baban Jamila ya mata gori,kawai don yana riƙe mata yara,ta ƙare da faɗin"suma ai suna da gidan uba,in Sha Allahu zasu tattara su koma,don wallahi sun fi ƙarfin a ci musu mutunci"ta ja tsaki ta wuce ɗakin ta

An saba da halin ta, shiyasa a manyan babu mai ce mata uffan,yaran ne ma suke ta dariya ƙasa ƙasa,wasu kuma suna kwaikwayar ta

Ba'a juma na taro ya tashi,da nufin gobe da sassafe za'a fara shirin tarbar manyan baƙi

HAƊEJIA ROAD, NASSARAWA GRA,KANO STATE, NIGERIA

hamshaƙiyar mace ce da a ƙalla zata kai 55+ years,fara ce tas,alamun hutu da jin daɗi ya gama bayyana a tare da ita,sanye take da wani tsadadden material,lemon green,hannun ta riƙe da tsadaddiyar wayar ta da ta kara a kunne,tana ɗan murmushi,da alamu magana takeyi a wayar

"A'a fa Hajiya salma,ke matsalar ki baki iya cin ribar zaman duniya ba,ki bari mu je,zaman duniya fa dole sai da iya taku,kinsan wannan tsohuwar yanzu ƙiris take jira ta sauke mana tijara,ita gadarar ta ƴaƴan ta ne suke riƙe da mu,mu tura mata aniyar ta kawai"

Daga ɓangaren Hajiya salma tayi wani murmushin takaici tace"wannan tsohuwar har yau bata san ɗaga mata ƙafa nakeyi ba Hajiya Raheena, da ta san wacece Salma da wani abun wallahi ko da kuɗin da take jarabar so aka haɗa ta bazatayi ba,muguwa tana kusa da kabari amma bazata yarda ta mutu lafiya ba!"

Hajiya Raheena ta fashe da dariya tana faɗin"kul salma!kar ki kuskura ƴaƴan ta su ji ki,kin san akan ta basu ƙi duniya ta tashi ba,basu ƙi su rabu da kowa ba"

"Mhmmm!"a cewar salma"gaskiya dole na ɗauki mataki akan matar nan kafin ta kashe min aure,ya zama wajibi ta cire idanu daga rayuwar aure na da miji na,ta sakar mana mara hakanan muyi fitsari"Hajiya Raheena tayi murmushi tace"lallai kam Salma,mu dai don Allah ki bar mu mu rabu lafiya,bana son abinda za'a ce kayi kaza da kaza, musamman kai da kake matsayin baƙo"

Salma tayi dariya tace"sai goben idan mun haɗu Raheena,a gaida yaran"

Raheena ta amsa da"zasu ji ta ajiye wayar

To fa!yau dai ga inda Nusy bee ta kai readers😅ko yaya zata kaya?

Menene ra'ayin ku game da SIRAƊIN UƘUBA?me kuke ganin zai iya faruwa ne😍

#Likecommentshare

#Nusy_bee


I just published "SIRAƊIN UƘUBA 2" of my story "SIRAƊIN UƘUBA ". https://www.wattpad.com/1575194902?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Nusybee247

🔥SIRAƊIN UƘUBA🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee

Page 2

Ƴan mintuna bayan ta sauke wayar taji sallama,ta ɗauke kai daga kallon da takeyi a ƙatuwar plasma TV ɗin dake luxury parlourn,ta kalli saitin kofar da kulawa,wanda yayi sallamar ya bayyana

Matashin saurayi ne,giant, kyakykyawa wankan tarwaɗa,sanye yake da riga da wando na puma track suit baƙaƙe, kyakykyawan gashin shi da bai taru sosai ba ya sha gyara,yayi murmushi yana kallon ammin nashi da tuntuni murmushi yake kwance akan fuskar ta,ya ƙarasa kusa da ita ya zauna ya rungume ta yana faɗin"I miss you ou lovely mother"

Itama murmushi tayi tana faɗin"SULAIMAN ka dawo?ya aikin?"

Sulaiman ya yatsina fuska yace"aiki kadaran kadahan ammi,yanzun ma na gaji sosai,tun ɗazu na shigo gida amma sai da na fara Branching part ɗina nayi relax sannan nayo nan"

"Weldone son!I hope you are doing good"

Sulaiman yace"absolutely ammi,good evening my ammi"ya ƙarashe yana kwantar da kanshi a kan kafaɗar shi

Hajiya Raheena tayi murmushi tana kallon shi tace"kai fa baka girma ko? ɗaga ni kafin surayya ta shigo taga wannan taɓarar"

Sake maƙalkale ta yayi a shagwaɓe yake faɗin"kai ammi na,kafin ita wa kika fara sani?"

"Yayan ku mana,malam ni ɗaga ni"Sulaiman yayi murmushi sannan ya zauna sosai yana kallon ta,da serious face yake faɗin"ammi gobe da yaushe za'a yi tafiyar nan?"

Hajiya Raheena ta ɗan taɓe baki tace"Abban ku yace wajen goma na safe zamu tashi"

"Kenan ba da yaya AUWAB za'a tafi ba?"

Da sauri ammin nashi ta kalle shi yace"wanne Auwab kake Magana akai? beside,Kai yanzu akace Auwab zai je garin nan sai ka yarda?"

Sulaiman ya ɗan yatsina fuska yana girgiza kai yace"but ammi I see nothing special don Yaya Auwab ya je albasu, don't forget acan aka haifi abban mu,can ne asalin shi"

"Then,so?"ta faɗa tana hararar shi

Murmushi Sulaiman yayi yace"nothing,yaushe zai dawo ne? I'm missing him badly,my brother,my friend,my,my,Kai my everything ma kawai"ya ƙarashe yana murmushi

Hajiya Raheena tayi murmushi tace"ka bi shi mana,ko Boston ɗin baƙon ka ne?"

Sulaiman yayi murmushi ya girgiza kai yace"no!idan na bi shi ni kuma yaya zanyi da nawa aikin kenan? Allah ya dawo mana dashi lafiya kawai"

Hajiya Raheena tace"ameen"daidai nan surayya da Amra sukayi sallama suka shigo da sallama

Suka amsa musu,da girmamawa suka gaishe su,suka amsa, Sulaiman yace"sai yanzu kuke dawowa?"

Surayya ta kyaɓe fuska kamar zatayi kuka tana faɗin"wai ji nayi fa an ce gobe zamu je wancan ƙauyen,da ban so dawowa ba ma,na so booking flight gobe na saci jiki na wuce Maiduguri,kafin a matsa min zuwa wancan ƙauyen"

Sulaiman ya miƙe cike da takaici yana kallon ta,yace"a wancan ƙauyen dai da kike ƙyanƙyami bakya so anan aka haifi uban naki da kike ƙafafa dashi, saboda haka idan kika tashi ƙyamatar ƙauyen sai ki haɗa har da uban ki da shima haifaffen can ɗin ne"yana faɗin haka yace"good night ammie"bai jira amsar su ba ya fice cike da takaicin yadda mahaifiyar tasu take cusa musu aƙidar ƙin dangin mahaifin nasu,duk da ba sosai take nunawa ba

Dukkan su da kallo suka bi shi,Hajiya Raheena taji haushin abinda yayi wa ƙanwar tashi,amma sai ta share bata nuna musu ba,don duk abinda akeyi bata bada ƙofar da karami zai raina babba a yaranta,ta ɗauke kai ta kalle su tace"ku shirya da wuri Please,abban ku ya gaya mana wajen ƙarfe goma na safe zamu tafi"

Amra ta kalli ammin nasu cikin jin takaici tace"to be sincere ammi I dislike zuwa wannan ƙauyen, there is nothing special with that village,I hate it wallahi"ammie ta kalle ta da ɗaurewar fuska tace"yanzun ma zagin da kuka saba janyo min kuke so ku ja min?baki ji abinda yayan ku yace ba?acan aka haifi uban ku?to bana son shiririta,ku shirya zamu je garin ku gobe"surayya cikin sakalci irin na auta cikin shagwaɓa tace"but ammie You know that old woman is so annoying,ki ga fa nan zata zo amma sai tayi ta haɗa mu da abban mu, Aunty beely ma kina ga cewa tayi ta tsani tazo saboda kullum a cikin haɗa ta da daddyn su take,wai taƙi aure"

"Watch your tongue Amra!ita ɗin duk lalacewa mahaifiyar baban ku ce,You have to respect her for the sake of her son which is your father!"ta ƙarashe da ɗan ɗaga murya

Shiru sukayi basu sake magana ba,don sun fuskanci ran mahaifiyar tasu ya ɗan ɓaci,a hankali surayya ta ɗauki ƴar jakar ta,ta miƙe tana faɗin"good night ammie"itama Amra miƙewa tayi ta bi bayan ta,suka nufi ɗakin su dukkan su rai a ɓace

LUGARD ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA

"Mum!Wai da gaske ne gobe zamu yi tafiyar nan?"

Ta ɗaga kai tana kallon shi,fuskar shi a ɗaure, da gani yana cikin ɓacin rai,kafin ta kai ga bashi amsa suka ji Muryar beely tana dariya tace"yeah of course Yaya AZAD!that annoying old woman da baka ƙauna gobe dai zaku kwana a waje ɗaya"ta ƙarashe tana dariya

"God forbid!anya daddy yana duba mana kafin yayi abu kuwa?for God sake bana son tension,but that annoying old woman with her villagers' children and grandchildren zasu janyo jinin mutum ya kai matakin ƙarshe, Please mum kiyi wani abu Please"kallon Azad tayi cikin takaici tace"stop begging me nayi abinda kasan bazan iya ba,tun wuri nace ka koma bakin aikin ka amma kaƙi,yanzu shi Auwab da Allah ya taimake shi ya koma bakin aikin shi ba gashi nan ya huta ba?don haka kar ka dame ni,ka bar Ni da abinda yake damu na nima"tana kaiwa nan ta miƙe ta bar parlourn ran ta a ɓace,su kuma suka bi ta da kallo

Beely ce ta kalli Azad cikin kwantar da murya tace"Please yaya Azad Kar kayi Abinda daddy zai ƙullace mu,that woman is his mother,the villagers are his relatives,and he love them,so let's do something that will not hurt him,kwana ɗaya kawai zamu yi,in Sha Allah babu wata matsala,bana son abinda zai janyo mana fushin Daddy"Azad yayi tsaki yace"bilkisu wallahi bana ƙaunar garin nan,bana son haɗa sabga da ƙauyawan nan,ƙazamai ƴan rainin hankali"beely ta yatsina fuska tace"seriously Yaya Azad,amma haka zamu je kawai saboda daddy"

Feena dai na zaune daga gefe tana danne dannen waya,amma hankalin ta da kunnuwan ta suna ga ƴan uwan nata,tana jin haushin yadda suke wulaƙanta dangin mahaifin nasu wai ƴan ƙauye ne,ta girgiza kai cike da takaici,ta miƙe tsaye batare da ta kalli yayyen nata ba da ko kula da ita basuyi ba ta shige ɗakin ta

BOSTON, MASSACHUSETTS,USA
Kyakykyawan matashi ne,fari tas,yake takawa a hankali a gefen titin,kallo ɗaya nayi masa na gano kamannin sulaiman a tare dashi,sai dai shi yafi sulaiman haske,kuma yanayin shi yana gwada rashin son hayaniyar shi, saɓanin sulaiman mai yawan surutu

A nutse ya zare farar p-cap din da ke kanshi,ya zare baƙin glasses da ya kara wa farar kyakykyawar fuskar shi kyau,cikin nutsuwa ya cigaba da takawa zuwa bakin katafaren gate ɗin gidan nashi,hannun shi riƙe da p-cap da baƙin glasses ɗin nashi,ya buɗe ƙaramin gate ya shiga gidan cikin nutsuwar shi da rashin hayaniya kamar koyaushe

Yana shiga ɗakin shi wayar shi tana katsewa,ya ɗan yatsina fuska sannan ya ɗauko ya duba mai kiran, murmushi yayi ganin mai kiran,ya jefar da wayar tashi kan gado ya faɗa toilet ɗin ɗakin nashi

Bai wuce mintuna goma ba ya fito,ya shirya cikin kaya marasa nauyi ya zauna a gefen katafaren gadon shi sannan ya ɗauko wayar shi ya mayar da kiran da akayi masa, ba'a ɗauki lokaci ba aka ɗaga

"Big bruh!sai da kai babban yaya"Muryar Sulaiman ta faɗi haka daga cikin wayar

Murmushi yayi sosai kafin yace"Sulaiman!ya aikin?ya fama da mutane kuma?"sulaiman yace"normal wallahi,Abba ma ya saka na ɗauki hutu tun shekaranjiya,this time dai da shi da daddy sun yi alƙawari zamu je mu ga mahaifar su mu gaida Granny ɗin mu"

"That's good! Amra ta gaya min gobe zaku je ko?"

"Yeah!Amma for sure naga a gidan babu mai son tafiyar,daga ni sai dad"

Auwab ya ɗan yatsina fuska yace"Gaskiya sai dai daga kai sai dad ɗin,don ko Ni ba so nakeyi ba, shiyasa ma da Abba ya fara yi min batun tafiyar na cigaba da zama na anan kawai"

"Haba yaya Auwab! don't forget that anan aka haifi mahaifin mu,nan ne asalin mu,nan ne tushen mu,ka taɓa ganin mutum yaƙi tushen shi?"

Ahto!ko shege yana son tushen shi🥱

#likecommentshare

#Nusy_bee

🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee

Page 3

Auwab ya ɗan yatsina fuska sannan yace"yeah I know,kuma nima ban ce bana son su ba, I just said bana son zuwa,ba don komai ba sai bana son hayaniya,and.... sha'anin garin nan sai a hankali,they are always annoying,more especially that old woman, Inna, I hate the way she is treating me,Bata so taga ina walwala, shiyasa ko zuwa tayi nake nisantar gida"

Sulaiman ya fashe da dariyar babu shiri yace"haba big bruh!Ni ban ga laifin ta ba,ai ba ƙarya tayi ba,kayi aure,amma kai kullum cin na sadaka"

Auwab ya ja tsaki mai ƙarfi,cikin kufula yace"Sulaiman don't spoil my mood,look, let's chanje the topic kawai,ka gano wannan ɗan ta'addan?ka kama shi?ya ake ciki?"

Fara'ar fuskar Sulaiman ta ɓace a take,ya ja tsaki cike da takaici yace"na kama shi bruh,but can you imagine manyan kasar mu yakeyiwa aiki?daga sama na samu umarnin wai na sake shi?"

Auwab ya girgiza kai cike da takaici yana faɗin"dama sai da nayi tsammanin hakan, musamman yadda yake kiran ka da ƙwarin gwiwa yana maka warning ka sakar masa yara,tun a lokacin na gane akwai waɗanda suka tsaya masa, I'm wondering yaushe ƙasar mu zata hau saiti,mu kenan kullum muyi gaba muyi baya,abin haushin kuma a haka sai kaga akwai talakawan da suke mara musu baya"

Sulaiman yace"mhm!kai dai bari kawai,Ni da nake wannan aikin Ni kaɗai nasan me nake gani, yawancin lokuta I'm feeling like na ajiye aikin nima nayi joining ɗin ku na nemi kuɗi kawai"

Auwab yayi ƴar dariya yace"see you! c'mon ka ajiye batun ajiye aiki,it doesn't make sense ace azzalumai basu ji tsoro sun gudu ba sai jami'an tsaro, Allah ya cigaba da dafa muku"

Sulaiman ya ja numfashi ya fesar yace"ameen bruh,mu ka san anan dare yayi,don haka sai nace sai da safe"Auwab yayi ɗan murmushi yace"sleep well aboki na,sai goben"suka ajiye wayar

LUGARD ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA

"What do you mean barrister?I can't get you"ta faɗa idanun ta na kaɗawa da ɓacin rai

"I know you heard what I said Salma!and I will not repeat myself"

"Imagine!kana ga kayi min adalci Barrister?nawa yaran ma da yaya nake fama dasu ballantana yaran wasu?kaima dai da wani zance kake,banda haka ai kasan babu wajen zaman ta a gidan nan ko?"

Ko kallon ta baiyi ba yace"oh!haka ne fa!ashe fa ke ɗin ramin bushiya ce daga ke dai ƴaƴan ki!"

"What! Barrister abin har ya kai da haka?ni kake gayawa magana saboda ƴar ɗan uwan ka?to wallahi bazan riƙe ta ba,bazata zauna min a gida ba,idan kuma ka dage sai ta zauna na gani"

Ya ɗaga kai ya kalle ta sai huci takeyi,idanun ta sun kaɗa sunyi jajir,har wani mazarin ɓacin rai jikin ta yakeyi,ya kawar da kai yana faɗin"ashe kina da gida ban sani ba?to ƙaddara ma kina da gidan,ce miki akayi can zan kai ta? a'a gida na zata zauna,ba naki ba,kinga malama,shirya,don mu ne zamu je gidan officer daga nan mu hau hanya"

"Barrister a tsawon shekaru talatin da biyar da muke zaune da kai baka taɓa tunanin yi min gorin gida ba sai yau don ka dage zaka ɗauko wata ƴar ƙauye,kawai...."

"Idan ƙauye banza ne da baki aure ni ba hajiya,a ƙauye aka haife ni,anan na taso,daga baya na shigo birnin na zama abinda kika gani kikace kina so,zaman ƴar yaya na ɗaya ƙwaya ɗaya tilo dai a gidan nan na yanke shi,dole ta zauna,idan bazaki iya zama ba kina iya bar mata gidan"baƙin ciki ya hana Hajiya Salma magana,ta san halin mijin nata, kaifi ɗaya ne,idan yace abu to babu makawa sai ya cika shi

Da ƙyar ta iya faɗin"amma baka ganin Ni yara sunyi min yawa?meyasa baza'a bawa Raheena ba tunda ita nata ƙwaya huɗu ne kawai?ba kamar Ni mai shida ba?"Barrister Umar yace"saboda haka na yanke,a gidan nan zata zauna,wanda bazai iya zama da ita ba ya bar mata gidan, that's all"

Ta buɗe baki da zummar sake yin magana ya dakatar da ita da faɗin"look Salma! I'm doing something important, either ki ƙyale ni da shirmen ki ko ki fita"bai kai aya ba ma ta fice fuu daga ɗakin a hasale,ya ɗan kalli inda tabi sannan ya girgiza kai cike da takaici yana faɗin"women!women!!"

HAƊEJIA ROAD, KANO STATE, NIGERIA

"Amra ammi fa tace mu shirya da wuri,we should not waste time"

Amra ta ɗaga Kai daga danna wayar da takeyi tana kallon surayya da ta isar mata da saƙon, kwashewa tayi da dariya tana kallon fuskar surayyan kamar zatayi kuka,cikin kufula surayya tace"Ni saƙo aka bani,idan in je in ce bazaki je bane to,bana son wulaƙanci,kin wani saka ni a gaba kina dariya kamar kinga mahaukaciya"

Amra ta haɗiye dariyar ta miƙe tana faɗin"sorry little sister,wallahi yadda kikayi maganar ne ya bani dariya,ki gayawa ammi na gama shiryawa, breakfast kawai ya rage min,ga kayan mu can ma na haɗa mana,ni da ke"surayya ta kalli kayan batare da tace uffan ba ta fice daga ɗakin,har yanzu ranta a ɓace yake,bata son wannan tafiyar jarabar da aka ƙaƙaba musu

Wajen ƙarfe tara da rabi iyalan Barrister Umar suka iso gidan,su takwas ne,Barrister Umar da matar shi Hajiya salma,sai yaran su, Azad, Bilkisu, Aliyu haidar,feena, Ma'aruf sai autarsu Nusra,feena da Nusra ne kawai babu alamar damuwa a tare dasu,sai beely da takeyin fuska kamar babu abinda ya dame ta

Kai tsaye Hajiya salma ta wuce ɗakin Hajiya Raheena,inda ta same ta tana gyara kayan da zata tafi dasu,duk da ba masu yawa bane,kallo ɗaya Hajiya Raheena tayiwa Hajiya salma ta karanto tsananin ɓacin ran da take ciki,ta ɗan girgiza kai tace"sannu da zuwa Hajiya,har kun iso?"

Hajiya Salma ta zauna gefen kujerar dake ɗakin batare da tace uffan ba, Hajiya Raheena tace"gaskiyar magana kina son ɗorawa kanki damuwa ne kawai,banda haka,ko ni da nafi ki tsanar garin,wannan tsohuwar da tafi tsana ta fiye da yadda ta tsane ki na haƙura na watsar da komai ballantana ke da kuke ɗan ɗasawa daita?"

Hajiya salma ta kalli Raheena idanun ta sun kaɗa tace"ke dai bari Raheena,that is not the main problem, imagine Wai Barrister yake maganar wannan galmashurar ƴar yayan nashi zata dawo gida na da zama, kiji wani wulaƙanci da cin mutunci fa"

"Wait!wa kike magana akai?wacce yarinyar kike magana zata dawo hannun ki?"a cewar Raheena idanu waje

Hajiya salma ta girgiza kai cikin ɓacin rai tace"wannan ƴar yayan nashi dai, Ummul khairi"

"Yanzu ke zaki riƙe ta?ke za'a bawa riƙon ta?"tayi ƴar dariya tace"an gaida uwar marayu! Allah ya taya riƙo,amma ina taya ki jaje,maybe kinyi wani laifin ne inna zata ce a hukunta ki ta nan"

"Ba wannan ba Raheena,ina mafita?"

Hajiya Raheena ta ja numfashi ta fesar tace"a yanzu bazai yiwu kiyi denying ba,more especially da na fuskanci mijin ki yafi nawa hayaƙin kai,ki ɗauko yarinyar,daga nan sai a san abin yi"

"Mhm! wallahi ji nake kamar na kashe yarinyar,na tsane ta wallahi,da babu ruwa na daita,amma yanzu na tsane ta, could you imagine,zagi,gori,cin mutunci babu wanda Barrister baiyi min akan yarinyar ba?har yana cewa idan bazan zauna daita ba in bar masa gida?wai Ni zan bar gidan Barrister akan wannan yarinyar?"

Shiru Raheena tayi tana kallon salma cike da mamakin wannan abu,bata yi tsammanin abin na Barrister Umar ya Kai haka ba,kafin tayi magana wayar ta tayi ƙara,da azama ta ɗaga ganin mijin ta

Maganar ƴan sakwanni yayi mata,ta amsa ya kashe wayar shi,ta kalli Salma tace"hajiya mu tafi ana jiran mu"babu musu salma ta miƙe suka fito zuwa babban parlourn gidan inda mazan su da yaran nasu suke jiran su

Anan akayi gaisuwar da ba'ayi ba,suka ɗunguma zuwa compound ɗin gidan inda drivers suka fito da tsadaddun motocin nasu

GIDAN SA'IDU MANOMI,ƘAUYEN ALBASU,KANO STATE

Yau gidan da harama ya tashi,tun da sassafe su baban Jamila suka yanka kaji da ragon da suka shigo dashi jiya da daddare, mutanen gidan kuma suka hau aiki babu kama hannun yaro yaran su da manya,baba Hari ce ta umarci Nadiya ta kira mata Ummiyo,wadda tunda gari ya waye babu wanda ya ganta,tana cikin ɗakin ta tana mutumin nata,wato bacci

A kan matacciyar tabarmar ta Nadiya ta ganta,tayi ɗaiɗai tana bacci cikin kwanciyar hankali,danƙararren gashin ta da ya chanja kala saboda datti da rashin kula a waje saboda zamewar kallabin kanta, kuɗin cizo sai bukukuwa suke shiryawa a jikin ta amma saboda masifar nauyin Bacci bata ma san sunayi ba, Nadiya ta girgiza kai cike da takaicin halin da mutanen gidan suka bar wannan marainiyar Allah,tausayin ta ya cika zuciyar ta,ta ƙarasa ta kama ƙoƙarin tashin ta

"Ummiyo! Ummiyo!!ki tashi,ki tashi kafin baba Hari ta shigo"

Ta kai kusan mintuna biyar tana ƙoƙarin tayar da ita kafin ta tashi zaune tana murza idanu,cike da haushi Nadiya tace"malama kije baba Hari tana kira,anya ma kinyi sallah kuwa?"

Ita dai Ummiyo bata ce mata ci kan ki ba sai faman murza idanu takeyi, Nadiya ta kama hannun ta ta miƙar daita tsaye,sannan ta janyo hannun ta suka fito tsakar gidan,da kanta ta kai ta bakin rijiya ta zuba mata ruwa,babu musu Ummiyo tayi alwala, Nadiya ta mayar da ita ɗakin ta,tayi sallah sannan suka wuce wajen baba Hari

Da sallama suka shiga,suka gaida baba Hari,ta amsa babu yabo babu fallasa, Ummiyo tace"baba akwai ragowar gasarar?zan zo in fita talla yanzu"

Baba Hari tace"yau babu talla,sai aiki,kin san ƙannen baban ki zasu zo daga Kano,maza,wuce ki je ki kamawa su maimuna aikin can,kema Nadiya ya kamata ki shiga cikin su kuwa"Ummiyo ta miƙe babu musu ta fita, Nadiya kuwa taɓe baki tayi tana faɗin"anya kuwa zan iya wahala? gaskiya bana jin daɗi ma"ta fice daga ɗakin

#likecommentshare

#Nusy_bee


I just published "SIRAƊIN UƘUBA 4" of my story "SIRAƊIN UƘUBA ". https://www.wattpad.com/1575612645?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Nusybee247


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee

Page 4

Ummiyo Kam ba wajen aikin abincin baƙi ta nufa ba kai tsaye,sauran masu ɗora mata talla ta shiga bi ɗaki ɗaki suna ce mata babu talla,har dai ta kawo ɗakin inna haleema, fuskar nan a murtuke ta tura mata farantin gyaɗar da ta ƙulla jiya tare da faɗin

"Ta dubu ɗaya da ɗari takwas da hamsin ce,saura kuma ki ɓatar min da kuɗi ki gane kuren ki"ita dai Ummiyo ta ɗauki gyaɗa batare da tace uffan ba,dama ita ba mai yawan magana bace

Tana fita ƙofar gida suka kusan cin karo da baffan ta Aliko baban Nadiya,bai kwana a gida ba jiya,ya kwana a ƙauyen kusa dasu inda yake sana'ar shi ta dafa mazarƙwaila,da sauri ta zube tana gaishe shi gami da yi masa Barka da dawowa

Ƙare mata kallo yayi yana amsawa,sannan yace

"Waye ya baki wannan tallan?"

"Karɓowa nayi a wajen inna haleema, su baba Hari sun ce babu talla yau"

"To itama haleeman bazaki je mata tallan ba,mayar mata da kayan ta ki wuce ki kamawa ƴan uwan ki ayyukan da sukeyi na cikin gida"babu musu ta juya ta koma cikin gidan,don ta san baban Nadiya yafi dukkan ƙannen mahaifin ta zafi,tana zuwa ɗakin inna haleema tayi sallama,ko amsawa Inna haleema batayi ba ta hau surfa masifa ta inda take shiga bata nan take fita ba,tun tana yi a ɗaki har ta fito tsakar gida,ita dai Ummiyo tuni ta bar wajen ta shige ɗaya daga cikin ɗakunan da ake gyarawa baƙin

Tana shiga sameera da lubabatu sukayi hanzarin toshe hanci, lubabatu faɗi takeyi"kai don Allah Ummiyo!don Allah ki fita kar ki saka Ni amai,har hanjin ciki na ya fara juyawa,wanne irin wulaƙanci ne wannan don Allah?"

Ta ɗaga kai ta kalle ta,gaba ɗayan su huɗu da ke ɗakin ruƙayya ce kawai ta girme ta da ƴan watanni,amma dukkan su ƙannen ta ne,sai dai hakan bai saka ta damu ba,don ta saba ganin abinda yafi haka, bata ce uffan ba ta cigaba da aikin ta

Sameera ce ta buga tsaki tana faɗin"to gaskiya idan bazaki fita ba mu ba baƙin zafi bane sai mu fita, fisabilillahi sai kiyi tsiya ayi miki Magana ki yiwa mutane banza don wulaƙanci, saboda mugun halin da kika gada daga uwar ki?don naji ance itama nuƙufurcin tsiya gare ta, gaskiya idan baki fita ba zan fita"

Ba yau aka saba ciwa mahaifiyar ta mutunci a gidan ba,ba ga manya ba Baga yara ba,sai dai bata ga laifin su ba,don da bata bar ta bayan rasuwar mahaifinta ba da bata hau wannan SIRAƊIN UƘUBAr ba, ballantana har ta kai ga wannan matakin da ko kare ƙyamar ta yakeyi ballantana mutanen garin nasu,tunanin ta ya yanke sanda taji zaliha na faɗin"to ke sameera da kike maganar a bar ta a ɗakin a fita,bakya tunanin ɗakin zai kama hamamin jikin ta?kinga daga nan sai ƴan birnin su kamu da wani ciwon ko?sanadin shaƙar mummunan wari,kinsan dama mun fi su ƙwari,to a bar mu da abar mu,don haka itace ya kamata ta fita"

"Gaskiya dai,ke Ummiyo fita tun muna gane juna"a cewar lubabatu

Ko kallon banza basu ishe ta ba,duk irin zagi da cin mutunci da wulaƙancin da sukayi mata babu wadda ta cewa uffan, kuma gashi itace ƙarfin aikin

Tsayin awanni biyu da ƴan mintuna ya ɗauke su kafin su gama gyaran,suna fitowa kuma taga inna haleema a zaune a bakin ƙofar ɗakin ta fuska a cunkushe,sai ya da habaici takeyi,ashe wai agololin nata Madina da Zubaida ta bawa tallan gyaɗar,shine take ta habaice-habaicen ai tana da yaran,ƴan mutunci ƴaƴan gata,ba irin wadda aka hana ta bawa tallan ba

Wata muguwar harara ta makawa Ummiyo, Ummiyo ta ɗauke kai ta shige ɗakin ta batare da ta nuna ta san da halittar wata inna haleema ba

Bata juma a ɗakin ba ta fito ta nufi ɗakin baba Hari ta amshi kokon ta na karyawa,tana gama sha ta shige wanka kamar yadda taga kowa yanayi,sai dai ita saɓanin sauran da ruwa kawai tayi nata wankan, lokacin har an fara sauke girke girken da akeyiwa waɗannan manyan baƙi da ake ta kambamawa,ita kuwa a gare ta da zuwan su da rashin zuwan su duk ɗaya a wajen ta

Bayan ta fito daga wanka ta shafa man alayyadin da ƙawar ta saude ta ɗan tsiyaya mata a kwalba,bata sake bin ta kan komai ba tayi kwanciyar ta akan matacciyar tabarmar ta,don a gajiye take,ga wankan da tayi banda tayar da dauɗa babu abinda yayi mata,sai tsamin dauɗa takeyi,amma ko a jikin ta,tayi kwanciyar ta,har bacci ya sake yin awon gaba da ita

Bata sake sanin me takeyi ba sai da taji Nadiya na tashin ta cikin farin ciki,tana farkawa tace"Ummiyo ki fito, baƙin sun ƙaraso,baki ga motocin su ba wallahi,kamar a landan,sai ƙamshi sukeyi kamar furen aljanna,ke dai kawai zo ki gani"babu musu Ummiyo ta miƙe ta bi Nadiya don ganin baƙin da Nadiyar take ta kurarawa

MALUMFASHI,KATSINA STATE, NIGERIA

"Auta!auta!!auta wai bakya ji na ne?"

Wata mace ce wadda aƙalla zata kai shekaru talatin zuwa da biyar tayi firgigit kamar mai bacci gami da ture kwanon ɗan waken da ke gaban ta,wanda tuni ya daɗe da sandarewa saboda rashin kula shi da akayi tsawon lokacin da aka zuba shi

Wata dattijuwa ce,wadda aƙalla zata kai shekaru saba'in,amma kamala ta ɓoye tsufar ta,fes take cikin shigar mutunci,ta ƙaraso ta zauna gefen ta ta kalle ta cikin kulawa tana faɗin

"Auta tun ɗazu kika zubo abinci,ina ta jiran ki kare cin abincin kizo ki je kiran da Hajiya Hadiza take miki amma naga ko taɓa abincin bakiyi ba,ina zuwa kuma sai naga kin faɗa tunani, tunanin me kikeyi haka?"

Murmushin ƙarfin hali auta tayi tace"ba dai tunani ba ko inna?bacci ne ya fara ɗauka ta,kin san jiya hidimar bikin Abida bai bar Ni na kwanta da wuri ba, gashi na tashi saboda sauran aikace-aikace da suka rage"

Kallon tsaf inna tayi mata kafin tace"to shikenan, Allah ya kyauta,ki gama cin abincin sai ki je ki kwanta"auta bata sake magana ba ta kama cusa ɗan waken da take jin shi kamar magani, lokaci lokaci kuma tana goge hawayen da suke taruwa a idanun ta,don ita kaɗai ta san irin suyar da takeji a ranta

Inna bata juma da tafiya auta taji sallama,ta ɗaga kai da murmushi a fuskar ta tana amsawa,ya shigo ya zauna shima yana murmushi,ta gaishe da girmamawa"yaya aƙilu ina kwana!"

Da murmushi shima ya amsa mata gaisuwar kafin ya tambaye ta ya gajiyar bikin Abida,wadda ta kasance ƴar yayar ta ce da take bi zuwaira,shi kuma ƙanwar shi ce, mahaifiyar tata ta rasu shekaru goma sha biyu baya,yanzu shine yake riƙe da yarinyar

Bayan sun gama gaisuwa a nutse ya dube ta,cikin kwantar da murya ya kira ta

"HABEE"

"Na'am yaya"ta faɗa tana daidaita nutsuwar ta

"Habee menene matsalar ki?kar ki damu ki gaya min,nayi miki alƙawarin in dai ina da dama sai na magance miki matsalar ki ko ta mecece in sha Allahu"

Ƙwalla suka ciko idanun habee,ta goge sannan ta kalle shi cikin karayar zuciya tace"yaya aƙilu ina cikin damuwa,a ƴan kwanakin nan ina yawan yin mafarkin ta,ban taɓa ganin ta cikin farin ciki ba,sai dai naga tana kuka tana kira na nazo gare ta,to jiya kuma nayi mafarkin wai gata tana tafiya a cikin wata duhuwa, cikin wata ƴar siririyar hanya tana kuka,ga ababen tsoro a wajen,yaya aƙilu idan nace bana jin zafin rabuwa da ita nayi ƙarya"ta ƙarashe cikin kuka mara sauti

Duk da cewa yaya aƙilu yaji damuwar abinda ya gaya masa amma sai ya basar yana murmushin ƙarfin hali,ya dube ta yana faɗin"auta har yanzu da sauran ki,banda abin ki kin manta cewa mafarki ba gaskiya bane?kuma ma masu fassarar mafarki sun tabbatar da cewa mafarkin kuka alkhairi ne,na dariya shine sharri,sannan sauran abubuwan da kike gani shaiɗan ne kawai yake son yayi wasa da tunanin ki

Kuma ko da ace gaskiya ne idan kika riƙe addu'a inaga sai tafi yi mata amfani fiye da wannan hawayen da kike zubar mata ko?"

Kalaman Alhaji aƙilu sun ɗan sassauta zuciyar Habee,ta ja ajiyar zuciya ta sauke sannan tace"in Sha Allahu zan ƙara dagewa akan addu'a, Allah ya tsare ta a duk inda take"

Ameen ameen,yanzu dai kin san me nake so dake?"Habee ta girgiza kai batare da tace komai ba tana kallon yayan nata

Alhaji aƙilu ya cigaba"kin san dama zamu koma garin Sokoto da zama baki ɗaya, dalilin bikin Abida ne muka tsayar da tariyar sai an gama,amma yanzu in Sha Allah nan da ƙasa da wata guda zamu bar garin nan zuwa garin Sokoto,idan kin amince ki bi mu can,idan yaso sai ki koma makaranta abinki,ki manta duk wani ƙunci da kike fama dashi,amma shawara tana gare ki"

Murmushi ya faɗaɗa a fuskar Habee,tana matuƙar jin daɗin yadda yayyen nata suka damu da damuwar ta, basa ƙaunar ganin ta cikin ɓacin rai ko kaɗan,dama haka Allah yake tsara lamuran shi,sai ya buɗa maka ta wani ɓarin amma ya jarabce ka ta wani ɓarin,ita kam ɓangaren yayyen ta alhamdulillah,babu kalar tarairayar da basayi mata tunda ta dawo gida

GIDAN SA'IDU MANOMI, ƘAUYEN ALBASU, KANO STATE

Gida kam ya ɗau harama sosai na saukar waɗannan manyan baƙi masu daraja a wajen waɗanda suka kawowa ziyara, yaran gidan manyan su da ƙanana sun kewaye motocin nasu sai kallo sukeyi,masu rawar kan cikin su har da shafawa,sam basu kula da irin kallon wulaƙanci da yawancin baƙin suke bin su dashi ba

Daga bakin ƙofar gidan Ummiyo ta tsaya tana bin komai da kowa da kallo a tsanake,ita kuwa Nadiya da gudu ta ƙarasa kusa da motar kamar zata kifa haka take duƙawa don gaida baƙin,shi kanshi Sulaiman sai da abin yaso bashi dariya ganin ɗabiar mutanen,amma sai ya ayyana hakan itace yanayin rayuwar su,wadda kowa da irin tashi,don haka shi dai yabi sahun iyayen nasu masa wajen amsa musu gaisuwar cikin fara'a

Ita kam Ummiyo batayi cikakkun sakwanni biyar a bakin ƙofar ba ta juya ta koma cikin gidan,kai tsaye ɗakin ta ta nufa,ta kwanta tana kallon ramukan ɓeraye da kyankyasan da suke taya ta hira a ɗakin duk dare

A ɗakin iya Sabuwa aka sauke su,ita kanta tayi farin ciki sosai na ganin ƴaƴan nata,don kai tsaye ta nuna da su ta damu,sai wasu daga cikin jikokin nata da take so,kamar Amra da Nusra,waɗanda aka sakawa sunan ta,sai Sulaiman,a cewar ta shi ba mutumin banza bane,baya gudun asalin shi,amma ragowar dama ba shiri suke ba, musamman Azad,beely da Auwab,a cewar ta basu da tarbiyya basu da ɗa'a,wannan shaidar tana yi musu zafi, musamman Hajiya Raheena da ta san Auwab bai san yadda zai raina babba ba,asalima ita bata taɓa bari babba ya raina ƙarami,ko mijinta yana matuƙar yaba mata ta fuskar tarbiyya


Hajiya ke kika san haka😁innarmu dai bata sani ba🫣

#likecommentshare

#Nusy_bee

I just published "SIRAƊIN UƘUBA 5" of my story "SIRAƊIN UƘUBA ". https://www.wattpad.com/1575820630?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Nusybee247


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee

Page 5

Basu juma sosai a ɗakin inna sabuwa ba suka wuce ƙaton ɗakin da aka tanadar musu don cin abinci,an kai musu komai an jere,Beely da surayya ana fara serving ɗin su suka ce baza su ci ba,a ƙoshe suke

Hajiya Raheena cikin kufula ta juya shuwa ta rufe surayya da faɗa, kasancewar kaf yaran nata suna jin Yaren ta,ta nuna mata ɓacin rai sosai kan ƙoƙarin ƙara ɓata mata suna da take shirin yi a tsakiyar dangin miji,Hajiya Salma tayi saurin katse ta da faɗin"a'a Hajiya,ƙyale ta tayi ra'ayin ta,kawai don tace bazata ci abinci ba sai ki kama yi mata faɗa?ki ƙyale ta taji da damuwar dake ranta"

Shiru Hajiya Raheena tayi batare da ta sake magana ba,ta daɗe da gane salma tafi ta tsageranci da rashin kunya, shiyasa basa taɓa daidaitawa da uwar mijin nasu

Bayan awa ɗaya sun kammala komai,sun sake dawowa ɗakin inna sabuwa,ita dai Hajiya salma har ma da yaran ta ji sukeyi kamar a kan ƙaya suke

Barrister Umar ne ya kalli mahaifiyar tasu yace"Ni kuwa Inna har yanzu banga yarinyar wajen yaya Garba ba"

"Ai kuwa tana nan,ina Nadiya?ke Nadiya?"kusan ƴan mata biyar ne suka shigo suna tambayar"inna me za'ayi miki yanzu?"

Inna ta galla musu harara tace "ku fice ku bani waje, Nadiya nake Kira"lieutenant general Usman yana murmushi yace"inna bar su su gaisa da ƴan uwan su su san juna,ku shigo ku zauna,ke,je ki kira Nadiya da Ummul khairi ƴar gidan marigayi yaya Garba"lubabatu da aka aika ta amsa cikin girmamawa sannan ta fice da sauri don isar da saƙon da aka bata

Ƴan mintuna sai ga Nadiya ta shigo da sallama,ta durƙusa ta gaida su a girmame, waɗanda suka ga dama suka amsa,sauran kuma a yatsine suka kalle ta suka ɗauke kai

Barrister Umar ne ya fara tambayar su game da karatu,babu laifi duk cikin su babu wadda bata gama primary ba,kuma ba laifi suna ɗan ganewa ko da babu yawa,ya yaba musu sosai,babu jumawa Ummiyo ta shigo tana sallama da sanyin Muryar ta

Ɗakin ya ɗauki shiru da shigowar ta,sai bin ta akeyi da kallo,bata ko sake ɗaga kai ta kalle su ba ta rissina ta gaishe su, waɗanda sukayi niyya suka amsa,sauran dai sai kallon ta sukeyi a yatsine kamar sun ga kashi

Da ƙarfi Beely tace"wai tabɗijam! gaskiya an cuci ƙauye"

Barrister Umar ya daka mata tsawa,a firgice ta nutsu,cikin ɓacin rai yace"wannan ƙauyen da kika raina anan aka haifi uban naki da kike taƙama dashi"kafin ya sake magana ma sameera tace"ai bama yanayin mu ƙauyawa bane,yanayin ta ne,bata wanki bata wanka"Hajiya Raheena sai kallon su take tana jinjinawa,ita kam Hajiya Salma tuni ta ɗauke kanta

Feena ce ta miƙe tsaye ta kama hannun Ummiyo suka fice daga ɗakin,da kayan wankan ta ta taimakawa Ummiyo tayi wanka,ta wanke mata gashin ta mai bala'in cika da tsawo amma ya danƙare,don sanda ta wanke mata kan sai da aka zuba kumfa wajen sau shida sannan tayi haske,zuwa lokacin tayi kuka har ta rasa hawayen zubarwa saboda zafi,bayan ta gama yi mata wankan ta saka ta a gaba suka nufi ɗakin ta don duba mata kaya

Gaba ɗaya babu kayan arziƙi,kayan ma sai wari wari sukeyi,gasu duk a yayyage,wasu an ɗinke da zare da allura,feena ta kira Sulaiman,ƙasa ƙasa ta roƙe shi ya je kasuwa,ta gaya masa abubuwan da zai siyo mata

Tana kashe wayar ɓera yazo zai wuce da gudu,ta ƙwala ihu tayi waje,sai daga baya ta leƙo taga Ummiyo a zaune a takure,tace"ki fito don ni tsoron ɓera nakeji,ki zo muje ɗakin inna sabuwa ki shirya"da sauri Ummiyo ta girgiza kai tace"na gode anti,zan shirya anan"

"C'mon ki taso,kizo mu wuce ɗakin inna sabuwa"

"To zan iya zuwa ɗakin baba Hari?"ta tambaya da sanyin murya,feena tace "eh mu je,ni waɗannan ƙwarukan ne bana so,ki fito mu wuce"babu musu Ummiyo ta miƙe tabi bayan ta suka nufi ɗakin baba Hari don ta chanja kayan da feena ta saka Sulaiman ya siyo mata

Wata doguwar riga ta bata ta sanya,ba ƙaramin kyau Ummiyo tayi ba,feena tayi ta koɗa ta,ta bata hijabin da Sulaiman ya haɗo mata dashi,ta saka sannan suka nufi ɗakin inna sabuwa

Da sallama suka shiga, duk da cewa da farko Ummiyo ta so cogewa a bakin ƙofar,amma feena ta ja hannun ta suka faɗa ɗakin

Gaba ɗaya occupants ɗin ɗakin mayar da hankali sukayi gare su,Hajiya Salma mamaki da baƙin ciki ya hana ta magana ganin abinda feena tayiwa Ummiyo,ga waɗannan ƙauyawan da suka cika ɗakin suna ta damun su da hayaniya a cewar ta,da fara'a sosai Barrister Umar yake faɗin"Weldone feena!zo nan Ummul khairi"babu musu Ummiyo ta ƙarasa kusa dashi ta rissina ta sake gaishe su,da yawan mazauna ɗakin sai kallon ta sukeyi ganin yadda ta chanja tashi ɗaya

Sulaiman ne ya kalle ta da murmushi yana faɗin"Ummul khairi ba gaisuwa?"ta ɗaga kai cikin sanyin murya ta gaishe shi,ya amsa yana murmushi,ta gaida Azad da ya kalle ta sau ɗaya ya ɗauke kanshi ya mayar ga waya,bai amsa ba,sai ɗan kallon ta da yayi ya sake ɗauke kanshi yana danna waya yana taɓe baki, ruƙayya ce da taji a duniya babu wanda ya burge ta irin Azad, cikin karya murya tace"Yaya Azad da Kai Ummiyo take fa"

Shi karairayar da takeyi ma dariya ta bashi,ya kalle ta yana faɗin"wacece Ummiyo?"

Cikin jin daɗin ya kula ta ta nuna masa Ummiyo da ke gefe,tunda ta gaishe shi bai amsa ba ta ɗauke kai gefe

Sulaiman ne ya yatsina fuska yana faɗin"menene kuma Ummiyo?"wani banzan kallo Ummiyo ta jefa masa ta ɗauke kai,ita a ganin ta ya raina mata wayo ma,bai jira amsar ta ba yace"menene school name ɗin ki in full?"

Bata san ma da ita yake ba,sai da taji su lubabatu suna ta dariyar shaƙiyanci, ruƙayya cikin dariya tace"ai bata san me kace ba ma,bata taɓa zuwa makaranta ba, kullum aikin kenan talla"

"Talla kuma?"a cewar Beely"dama har yanzu ana wannan yayin?"

"Kin san ƙauye kuma,meye bazaki gani a ciki ba?"a cewar Hajiya Salma tana kallon Ummiyo a yatsine

Ba Sulaiman da su Barrister ba,hatta Hajiya Raheena sai da tayi saurin kallon salma, Barrister Umar ya girgiza kai cike da takaici, Salma bazata chanja ba,harshen ta bazai taɓa saituwa ba,ya kalli Ummiyo cikin tausayawa yace

"Ummul khairi kema kina son zuwa makaranta?"

Tunda suka zo basu ga fara'a a fuskar ta ba sai Yanzu, don tana jin sunan makaranta ta fara murmushi tana gyaɗa kai,cike da tausayawa da jin nadamar banzatar da rayuwar ƴar marainiyar da sukayi lieutenant general Usman yace"kar ki damu kinji, Ummul khairi,da ke zamu tafi mu saka ki a makaranta in Sha Allah,kiyi karatu,gaya min,me kike son zama idan kinyi karatu?"sam bai kula da kallon da matar shi,Hajiya Salma,da yaran su suke bin shi dashi ba,banda Sulaiman,feena,sai haidar da hankalin shi yana kan waya ma,sai Nusra

Murmushin nan bai bar fuskar Ummiyo ba ta amsa da faɗin"likita nake son zama"

An gaida likita ummiyo 😁

#likecommentshare

#Nusy_bee

I just published "SIRAƊIN UƘUBA 6" of my story "SIRAƊIN UƘUBA ". https://www.wattpad.com/1576041198?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Nusybee247


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee

Page 6

Abba yace"Weldone DR KHAIRI!in Sha Allah Zaki zama likita,ki rinƙa allura kina yanka cikin mutane ko?"abin ya bata dariya,ta rufe fuskar ta da tafukan hannayen tatana murmushi

Kallon shi ya mayar ga inna sabuwa,cikin girmamawa yace"inna da ni da barrister mun yanke shawara game da Rayuwar khairi,zata koma gidan shi da zama,zai mayar da ita makaranta,idan ta kai munzalin aure kuma zan aurar da ita ga mutumin da ya dace,tare da wannan zata yi karatun ta in Sha Allah,har sai tace ta gaji"inna sabuwa ta taɓe baki bata ce uffan ba,don dai wannan yarinya babu ruwan ta da ta mutu ko ta rayu tunda mahaifiyar ta ta ɓata kanta a wajen su shikenan gaba ɗaya abinda ya shafe ta ya fice mata a rai

Barrister ne ya kalli mahaifiyar tasu da girmamawa yace"inna ya kamata a saka mana albarka,don zumunci muke da niyyar yi,kuma baki ce komai ba"inna ta ɗauke kai tana faɗin"Allah sa albarka"

Hajiya salma kallon su takeyi cike da takaici,ganin bazata iya jurewa ba ta daure tace"inna me zai hana a bar ta a inda yafi wayo?idan aka kai ta cikin mutanen da bata saba dasu ba bakya ganin zata takura?idan yaso sai a nema mata makarantar da ƴan uwan ta na nan suke zuwa ko?"

Da yawan ƴan matan da suke zaune waɗanda suka ji ciwon abinda akace za'ayi wa Ummiyo sunji sanyi, musamman ruƙayya da ta ga tafi Ummiyo kyau,gata da ilmi,ita ya kamata tayi rayuwar birni ba Ummiyo ba,amma yanzu wai ace ba da ita za'a je birnin ba?

Kafin kowa ya sake Magana Sulaiman yace"mum there is nothing wrong idan ta zauna a can tare damu,mu zamu ja ta a jiki,mu koya mata yadda zatayi rayuwar ta tare damu,idan ma kina magana akan rashin wayon ta ne I'm telling you mum tana shiga makaranta komai zai zama tarihi"

"Da kasan haka meyasa baka bawa mahaifin ka shawara ya ɗauke ta ba?"ta bashi amsa a zafafe,daga yadda tayi maganar kawai ya bayyana tsananin ɓacin rai da take ciki

Hankalin mutanen ɗakin ya koma kanta,feena kamar ta nutse don kunya, Azad ma bai ji daɗin wannan maganar ba,Hajiya Raheena ma dai bata ji daɗin yadda kowanne lokaci Hajiya Salma bakin ta baya iya shiru ba,da ƙarin bakin ta ya saka ta ƙara baƙin jini a wajen surukar tasu

Barrister Umar ne ya kalli hajiya salma fuska a haɗe yace"khairi zata zauna damu,a gidan mu,tayi karatu,Wanda yaga bazei iya zama ba yana iya bata waje"Beely da Azad kallon baban nasu sukeyi kawai,don shi Azad babu abinda ya tsana kamar yaga ran mum ɗin shi a ɓace ko da ace da laifin ta kuwa,Beely kuwa a ranta ita tasan me take shiryawa wannan matsiyaciyar yarinyar don ta rabu dasu salin alin,a cewar ta idan sukayi sake zata raba su da dad ɗin su,to gashi tun daga yanzu ma yana faɗawa mum ɗin su magana ina ga tafiya tayi nisa kuma?

Duk abinda akeyi kan Ummiyo yana ƙasa, fuskar ta babu alamun damuwa ko walwala,su kam Barrister da lieutenant general tashi sukayi suka fice daga ɗakin, Azad da haidar da Ma'aruf suka bi bayan su,itama Beely ta miƙe, mahaifiyar ta da Amra suka miƙe,duka su ukun suka fice daga ɗakin kusan a tare, Sulaiman da Hajiya Raheena dai sai kallon su sukeyi,feena kam takaici ma bai bar ta ta kalle su ba saboda haushin halayen maman nasu

Inna sabuwa ta taɓe baki tana faɗin"shi dai Umaru baiyi dacen mata ba ta ko'ina wallahi,kwata kwata babu tarbiyya babu ɗa'a a al'amuran ta, shiyasa ga yaran nashi nan duk idanun su a fetsare,daga waɗanda suka gandame suka ƙi aure sai masu shigar fitsara,sai masu gaida manya gandaidai,gashi abin baƙin ciki an tara yara amma taron tsintsiya babu shara, Allah wadaran naka ya lalace dai!gaskiya dai gidan Umaru idan ya cigaba da tafiya a haka dole ya nemo wadda zata tarbiyantar masa da yara,idan yayi min musu irin na wannan yaron Allah yaji ƙan shi,ko da ban sallama wancan yaron ba shi zan iya sallama shi"

A razane Hajiya Raheena ta kalli inna sabuwa,a duniyar ta babu abinda ta tsana irin kishiya,sai taji abin ma kamar saukar aradu,don sai taji kamar ita inna tace ayiwa, addu'a ta shiga yi a ranta Allah kar ya bawa inna ikon saka lieutenant general yayi mata kishiya,don tana jin ranar mutuwa kawai zatayi

Cikin sanyin jiki ta rissina tana faɗin"to inna zan ɗan shiga ciki na huta,don har yanzu ƙafa ta ciwo take saboda zaman mota,mu wuni lafiya inna"

"A fito lafiya!"shine abinda innar ta iya faɗa batare da ta kalle su ba,Hajiya Raheena ta miƙe cikin sanyin jiki ta fice daga ɗakin

A can masaukin Hajiya salma kam Beely ce ta zauna kusa da ita fuskar ta babu walwala tana faɗin"mum!you have to be careful of what you are saying in front of this old woman,Kar taje tayi miki abinda zai dame ki,kinga ko me tayi miki wallahi ta gama dake don ba iya ramawa zakiyi ba"

Wani mugun kallo mum ta jefawa Beely tana faɗin"ba dai taƙamar ta ɗan ta ba?nasan ƙarshen abinda zata ce kenan ko?to sai me?tayi duk abinda zatayi,ta raba mu,duk bala'in ta dai na haihu da ɗan nata, dole a kira yaran ƴaƴan shi,kuma ace ƴaƴa na,ni bazan iya jurar ta rinƙa taka ni tana wulaƙanta ni yadda take so ba,haba!shekaru da talatin da kusan biyar da aure ana abu ɗaya?bata bar ni na huta a ɗakin aure na ba?ita haka akayi mata lokacin da take da nata mijin?waye ya matsa mata da take son matsawa rayuwa ta?bana manta zuwan ta na ƙarshe babu irin gori da cin mutunci da batayi min ba wai na kasa ɗabbaƙa sunnah na bar ki kin ganɗame ba aure, Azad da haidar kuma wai basu da tarbiyyar gaida na gaba,ita kenan kullum cikin aibata min yara,to na gaji,zan fara saka wa idanu na kwallin rashin mutunci na wanke ta ciki da bai,sai ta faɗi duk abinda zata faɗa da hujja"ta ja tsaki,ita dai Beely bata sake magana ba, tanadin ta akan Ummiyo ne kawai,wadda duk silar za'a ɗauke ta ake ta wannan ɓaɓatun

Bayan Isha'i kamar yadda aka saba mutanen gidan suka taru gaba ɗaya a ƙaton tsakar gidan,ciki har da Hajiya Raheena da yaran ta,sai dai babu Hajiya salma ita da Beely,amma sauran yaran duk sun hallara. Bayan an gama cin abinci Sulaiman yayi ta ba da labarun abin dariya ana dariya, Azad Kam ba karamin ƙular dashi Sulaiman ɗin yakeyi ba,don shi a nashi ganin bai ga abin ɓata lokaci a wajen waɗannan ƙazaman ƙauyawan ba,haka kawai su raina mutane?"

Ummiyo kam tana daga gefe kanta a ƙasa kamar koyaushe,feena na gefen ta,Amra kam ƙare mata kallo take tun daga sama har ƙasa a fakaice

Shigowar Barrister Umar da lieutenant general Usman,sai ƙannen su,baban Jamila da baban Bello ne ya katse surutun Sulaiman,gaba ɗaya aka ɗaga kai ana kallon su, ƴaƴan su da matan su sai sannu da zuwa sukeyi musu

Kai tsaye wajen inna sabuwa suka nufa,cikin girmamawa suka gaishe ta,ta goge hawayen ta tana faɗin"na gode wa da ya sake nuna min yara na a haɗe,ko a yanzu na mutu buri na ya cika,nayi farin ciki"da sauri Usman ya rike mata hannu yana faɗin"in Sha Allahu zakiyi ta ganin hakan inna,mu ƴaƴan ki ne,ko cewa kikayi mu dawo kusa da juna mu zauna hakan zamuyi"da yawan ƴaƴan nasu a firgice suka kalle shi idanu a waje,ciki har da Hajiya Raheena ma, Inna sabuwa tace"a hakan ma alhamdulillahi, Allah ya albarkace ku duka"

Umar yana murmushi ya amsa da "ameen innar mu maganin kukan mu"

Sun ɗan taɓa hira da mahaifiyar tasu,daga baya Barrister Umar ya kula babu matar shi Hajiya salma a wajen,ga matar yayan shi Hajiya Raheena,ga matan ƙannen shi da yaran su duka,hatta da baban Nadiya da baya nan akwai matar shi da yaran shi a wajen,don haka ya zare jiki a sace ya nufi ɗakin da aka sauke ta

A zaune ya ganta akan gado tana shan fruit a wani ɗan ƙaramin bowl da yake da tabbacin da abin ta tazo,daga ƙasa kuma Beely ce ta shimfiɗa darduma tana danna waya

Daga yadda yayi sallama Beely a razane ta ɗago ta kalle shi,ya kalle ta fuska babu rahama yace"ke!get out of this room! idiot!!"a gudu gudu sauri sauri ta fice,ya mayar da hankali ga mum ɗin tata da ta cigaba da shan fruits ɗin ta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali,ko kallon shi batayi ba ballantana ta damu da irin mugun kallon da yake jefa mata

"Salma wai menene matsalar ki ne?"

Ɗago kai tayi tana jifan shi da kallon rainin wayo tana faɗin"me kuma nayi?"

"Au baki san me kikayi ba ko? Salma Wai so kike saboda ke mahaifiya ta ta tsine min kafin na bar garin nan?ke kullum ƙoƙarin takalar mahaifiya ta kikeyi kamar wata sa'ar ki?baki da aiki sai tsiwa da rashin kunya kuma don rashin mutunci ki rasa wadda zakiyiwa sai mahaifiya ta?"

Wani kallon banza take watsa masa har ya gama ɓaɓatun kafin ta kyaɓe baki tana faɗin"idan Ni ban yi faɗa da mahaifiyar ka ba ko ɓata maka suna kai naga alamun so kakeyi ka zubar min da ƙima a idanun waɗannan ƴan uwan naka,me nayi maka da zaka zo ka rufe ni da masifa kamar wata ƴar ka?"

"Me kika ɗauki kanki?ko kina ganin akwai bambanci tsakanin ki da Mutanen da kika ƙi shiga cikin su?kowa na waje sai kece zaki zo don munafurci ki wani shigo ɗaki kina kitsawa ƴar cikin ki sharri?"

"Au!Wai don banyi wancan zaman majalisar bane kazo kana ta tada jijiyar wuya dama?ni na ɗauka wani abin ma akace nayi,to Allah ya bada haƙuri,na ɗauka zaman ra'ayi ne shiyasa ban fita ba,kasan ni bana son hayaniya da saka idanu ne"

Kallon ta yakeyi yana jinjina halayyar ta,sam bata jin kunya ko shakkar gatsa masa magana kowacce iriya ce, daurewa yayi yace"to ba ra'ayi bane wajibi ne,don haka tashi ki fita"

Muskutawa tayi tana yatsina fuska tace"gaskiya bazan iya ba,don ba wani daɗi nakeji ba"

Shiru yayi na ƴan sakwanni yana kallon ta,ita kam tana gama shan fruits ɗin ta ta ajiye bowl ɗin ta kama danna waya, Barrister Umar ya gyaɗa kai yana faɗin"Salma do whatever you like,lokacin ki ne, watarana da kuɗi akace kiyi bazakiyi ba"ya juya ya fice ya bar ɗakin

Gaskiya dai Hajiya Salma, with all due respect baki da mutunci 🥺

#likecommentshare

#Nusy_bee


I just published "SIRAƊIN UƘUBA 7" of my story "SIRAƊIN UƘUBA ". https://www.wattpad.com/1576263001?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Nusybee247


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee

Page 7


Yana komawa wajen ya ankara da Ummiyo da take ta gyangyaɗi,da murmushi ya ƙarasa kusa da ita ya ɗago haɓar ta yana faɗin"khairi bacci kike ji ne?"

Cikin sanyin ta ta ɗaga kai,ya kalli Nusra yana faɗin"auta zo ki raka ƙawar ki ta kwanta kinji?"babu musu Nusra ta miƙe ta kama hannun khairi suka nufi ɗakin ta

Nusra tana leƙawa taga yanayin ɗakin tayi saurin janyo hannun khairi suka dawo,ta kalli mahaifin nata tace"daddy the room is very dirty,she can't sleep there"

"Okay take her to your Granny's room before tomorrow"babu musu Nusra ta ja hannun khairi zuwa ɗakin inna sabuwa

Ware idanu tayi tana kallon inda Nusra ta kawo ta,ta kalle ta a ɗan tsorace tace"ba nan ne ɗakin nawa ba fa"

"Daddy na yace na kawo ki nan kafin gobe,kiyi baccin ki,sai da safe"ta ƙarashe tana murmushi,don ita fa khairi ta burge ta

Har tayi gaba ta dawo baya inda ta bar ta a tsaye tana bin ta da kallo,tana murmushi tace"I'm Safiyya known as Nusra,you?"

Shiru khairi tayi tana bin ta da kallo,ko me ta tuna kuma sai ta dafe kai ta ɗago tana kallon ta tace"yi haƙuri,suna na Safiyya ana ce min Nusra,ke fa?"

"Ummul khairi,amma Ummiyo ake kira na"

"Okay zan rinƙa kiran ki yadda daddy ke gaya miki, KHAIRI!sunan yayi min daɗi,ai kina so ko?"khairi tayi murmushi tana ɗaga kai, Nusra ta ɗaga mata hannu ta fice daga ɗakin

Washegari tun da sassafe baƙi suka fara shirye-shiryen tafiya,sai haɗa musu tsaraba kala kala akeyi,yau ma feena ce ta bawa khairi soso da sabulun wanka ta shiga wanka,bayan tayi wankan ta bata man shafawa,ta gyara mata gashin ta sannan ta bata ɗaya kayan da Sulaiman ya siyo mata jiya,wanda ta cire kuma ta bata kuɗi ta siyo sabulu ta wanke ta shanya kafin su tafi

Baba atine ce ke surfen masara da iya ƙarfin ta a tsakar gidan,dakan ya dami Hajiya salma da take ɗakin ta kusa da in da ake dakan,don tana dakan ne tana waƙe waƙe,gashi ba'a hankali takeyi ba,ganin bazata jure ba ta aika Beely cewa ko ma waye yake dakan ya dakata saboda yana damun ta

Baba atine ta kalli Beely a ɗage,irin kallon rainin wayo tace"ita uwar taki ce tace ana damun ta?"

Beely tayi mata kallon banza tace"eh!ana damun ta ɗin ne Shiyasa tayi magana"

"To kice mata tazo da kanta, wataƙila nafi fahimtar saƙon"ta cigaba da surfen tana cigaba da rera waƙar barmani coge mai taken ku kama sana'a mata

Daga sama har ƙasa Beely ta kalle ta sannan ta ja tsaki ta koma ɗakin mahaifiyar ta,cikin ɓacin rai ta isar mata da saƙon ƙazamar matar a cewar ta

Cikin isa da gadara salma ta fito daga ɗakin ta tana huci,kai tsaye ta nufi wajen da baba atine take surfen ta cikin kwanciyar hankali tana ta rera ƴan waƙoƙin ta,cikin izza take faɗin"baiwar Allah saƙo na bai iso miki bane?"

Shiri baba atine tayi tana jinjina rashin kunya da raini irin na mutan maraya,ta kalli hajiya Salma daga sama zuwa ƙasa tace"wanne saƙo kike magana akai kenan?"

"Cikin isa salma tace"na gaya miki wannan dakan da kikeyi yana takura min,ki bari...."

"Uban kuturu ma yayi kaɗan ballantana kuma ɗan shi!"a cewar baba atine cikin ɗaga murya

Bata bawa Hajiya salma damar magana ba ta hau surfa masifa"ke yanzu baki ji kunya ba zaki zo ki wani tsaya min ƙerere wai na daina neman kuɗi na ina damun ki?ke ba don kuɗin ba kin isa kizo gidan nan a girmama ki?wato mu ma baƙin ciki kike mana kar mu tara kuɗin mu shige raini ko?to wallahi baki isa ba,kuji ni da ja'irar mata!"

Beely da ta ƙaraso wajen ta kasa jure ɗiban albarkar da akeyiwa mahaifiyar ta,ta kalli baba atine a yatsine tace

"Ke yanzu don kina dagewa kina dukan turmi da taɓarya shine kike tunanin zaki kamo mahaifiya ta a kuɗi?idan ma zaki daina mugun mafarki ki daina,don ko ƴan aikin mahaifiya ta ba sa'annin karawar ki bane ballantana ita da kanta"ta ƙarashe tana mata kallon sama da ƙasa ta buga tsaki ta juya zata bar wajen

Sakin baki baba atine tayi tabi Beely da idanu,Hajiya Salma tayi murmushin rainin hankali tace"ba ni ba,ko ƴa ta tafi ƙarfin karawa da ke,don haka ki rinƙa sanin abinda zaki gayawa mutane,ba kowa bane sakarai da zakiyi masa abinda kika ga dama ya zuba miki idanu"tana kai wa nan ta juya zata bar wajen

Bana atine tayi wuf ta shaƙo ta tana faɗin"ina zakije?ai ba'a kara ɗin ba ballantana a ga wanda yafi ƙarfi,tsaya mu raba raini sai nasan kin fi ƙarfin nawa"babu ɓata lokaci ta hau jibgar Hajiya salma kamar Allah ya aiko ta,dama indai dambe da bawa hammata iska ne kaf garin ba ma gidan ba ko unguwar an san wacece baba atine, masifa da bala'i da tashin hankali da dambe duka gaba ta basu ba baya ba,babu wanda ta raina dalilin yin shi a cikin su,matar da wucewa ma zatayi taga ana faɗa sai ta san yadda zatayi ta shiga inaga an zo har inda take an takale ta?abinda taga dama shi takeyi a gidan babu wanda ta ɗagawa ƙafa,inna sabuwa kuwa tuni ta siye ta da ƴan kayayyakin da take siya mata lokaci zuwa lokaci,sau tari ma ita ke cefane ta bawa mijin ta da yaran,har ma da kishiyar ta, dama ita bata da rowa kwata kwata sai masifa,wannan yasa ake shakkar ta ake tsoron shiga shirgin ta,aikin ta na surfe ko dakan kukar siyarwa ko kuɓewa kuwa ko cikin dare ta so yin abin ta zatayi babu mai ce mata uffan,sai fa yau

Ihun da Hajiya Salma take kurmawa ne ya janyo hankalin mutanen wajen,da gudu Amra ta ƙaraso wajen,tana ganin abinda ke faruwa ta zaro idanu ta koma da gudu don ta shaidawa ammin ta,sai ganin su tayi suma sun ƙaraso a guje,yara da manya

Hajiya Raheena ta tsorata sosai ganin yadda baba atine take ragargazar hajiya salma,ta haɗa mata jini da majina,ga mazan basa nan,sai yara ƙanana,da ƙyar dai matan gidan suka ƙwaci Hajiya salma,da taimakon cizon da tayiwa baba atine,da ace a hayyacin ta take da ko da kuɗi akace ta taɓa fatar baba atine bazata iya ba, saboda baba Atine bata ɗauki tsafta abinyi ba

Inna talatu maman Nadiya ce ta kama Hajiya salma ta miƙar daita tsaye tana yi mata sannu,baba Hari uwar rawar kai da shishshigi da neman wajen zama ta kawo mata ruwa ta wanke fuska,don ta fasa mata baki da hanci kuma ta kumbura mata fuska, Hajiya salma ta buge butar da baba Hari take miƙa mata ta fizgi ɗan kwalin ta a hannun Inna talatu ta shige ɗakin ta,baba atine da tuni ta koma kan surfen ta dai faɗi take

"Zuwa yanzu nasan kin gane baki fi ƙarfin nawa ba kamar yadda wannan karuwar ƴar taki tace"da sauri Beely dake laɓe can baya a tsorace ta kalle ta jin abinda tace,kalmar tayi mata zafi,amma ta san yadda uwar ta ta ci uban duka yanzu itama tumurmusa ta a wajen nan ba komai bane

Baba atine ta cigaba da surutan ta"waye ya gaya miki macen da aka tara mata dukiyar miji taci itace mai ƙarfi?baki nema ba kuma ki rinƙa tunanin kina da ƙarfi?a yau mijin naki yana sallama ki dolen uwar ki ki bar gidan sai mu ga da uban me za'ayi ƙafafar,mace baki da aiki sai ci kiyi kashi kizo kina baza mana ɗuwawu wai ke matar mai kuɗi,to sai me don abu ta kazar ubanki?"babu dai wanda ya tanka mata,don ƴan gidan sun gane bata gaji bane take neman abokin cigaba

Beely ce ta koma ta bayan gidan ta kira Azad cikin kuka ta shaida masa abinda yake faruwa,baiyi wata wata ba ya juyo ya nufo gida,suma su Sulaiman suka biyo shi,don ko da bai gaya musu komai ba sun ga alamu kamar ba lafiya ba

Yana shigowa yaga surayya tana ƙoƙarin fita da trolley ɗin kayan su,ya kalle ta fuska a haɗe yace"ke!wacece wadda ta daki mum ɗin mu?"batayi musu ba ta nuna masa baba atine da har lokacin surfen ta takeyi tana waƙe waƙen ta hankali kwance

Kai tsaye ya nufe ta yana ƙoƙarin zare belt,da sauri Sulaiman ya dakatar dashi yana faɗin"bi a hankali big bruh, za'a warware komai"Azad ya hankaɗe shi yace"what are you saying?wata baƙauyiyar banza,ƙazama ta dakar min mahaifiya sannan kana maganar na bi a hankali, saboda ba uwar ka aka daka ba?wait!ka san ma wacece mum ɗina a waje na kuwa?"maganar ta bawa Sulaiman haushi,amma yasan dole ran Azad ya ɓaci saboda uwa ta wuce wasa, musamman shi da kowa yasan yadda suka shaƙu da juna,don haka yace"bana son abin ya lalace ne,idan ita jahila ce you are educated bruh,don Allah kar ka biye mata, let's fix the....."shiru yayi da mamaki yana kallon Azad da ya sauke masa mari a zuciye yayi gaba ya nufi inda baba atine tayi ready da taɓarya tana faɗin"ƙyale shi yazo,yazo na koya masa hankali kamar yadda na koya wa uwar shi"

Shigowar baban Nadiya da tsawar da ya dakawa Azad ce ta tsayar dashi,ya waigo a fusace yana kallon baban Nadiya yana faɗin"malam wannan ba matsalar ka bace,stay out of it,kasan zafin uwa kuwa?da har zaka hana ni ɗaukar mataki akan wadda ta taɓa min uwa?ko don ba taka aka taɓa ba shiyasa zaka hana ni ɗaukar mataki?"

"Da kai da uwar taka zaman kanku kukeyi?ba a ƙarƙashin wani kuke ba?"Azad ya katse shi da faɗin"i don't care!stop interrupting me or else abin ya shafe ka"yana gama faɗar hakan ya nufi inda baba atine take ya ɗaga belt da nufin zabga mata amma sai ta goce ya samu iska

Sam bai kula da isowar Barrister Umar ba sai mahaukatan maruka hagu da dama da yaji saukar su,ya waiga da sauri yana kallon mahaifin nashi cike da mamaki

Kunya da baƙin ciki kamar ya kashe Barrister,idanun shi sun kaɗa sunyi jajur,jijiyoyin kanshi sunyi raɗa-raɗa,cikin ɓacin rai ya fara magana

"Ka kyauta Azad,ka nuna irin tarbiyyar da muka baka a bainar mutane,wannan shine mutuncin da zaka iya siya mana ko?yayi kyau,wuce mu tafi!"babu musu Azad ya wuce waje a zuciye,idanun shi sun kaɗa sunyi jajur,farar fuskar shi tayi jajur

Bai kai ga yin magana ba Hajiya salma ta fito a fusace tana kallon shi ranta a ɓace,tace"ai dama ka daɗe da nunawa duniya ni ba a bakin komai nake ba,wata banza ƴar ƙauye ƙazama ta saka hannu ta dake ni amma kazo kana dakar min ɗa saboda yace zai rama min,ko ba komai ita da nice nayi mata wannan dukan da mijin ta bazai taɓa hana ɗan ta ya rama mata ba,na godewa Allah,ko ba komai nasan naci dubu sai ceto wallahi"ta wuce fuuu har kusan takewa inna sabuwa da ta ƙaraso wajen yanzu kafa tayi bata kula ba

Kai Hajiya salma! Maganar gaskiya halin ki sai ke,bakin ki bazai taɓa barin ki ci ribar zaman duniya ba


#likecommentshare

#Nusy_bee


I just published "SIRAƊIN UƘUBA 7" of my story "SIRAƊIN UƘUBA"::https://www.arewabooks.com/chapter?id=68c69081e6afc1fcce8c3e5d


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee

Page 7


Yana komawa wajen ya ankara da Ummiyo da take ta gyangyaɗi,da murmushi ya ƙarasa kusa da ita ya ɗago haɓar ta yana faɗin"khairi bacci kike ji ne?"

Cikin sanyin ta ta ɗaga kai,ya kalli Nusra yana faɗin"auta zo ki raka ƙawar ki ta kwanta kinji?"babu musu Nusra ta miƙe ta kama hannun khairi suka nufi ɗakin ta

Nusra tana leƙawa taga yanayin ɗakin tayi saurin janyo hannun khairi suka dawo,ta kalli mahaifin nata tace"daddy the room is very dirty,she can't sleep there"

"Okay take her to your Granny's room before tomorrow"babu musu Nusra ta ja hannun khairi zuwa ɗakin inna sabuwa

Ware idanu tayi tana kallon inda Nusra ta kawo ta,ta kalle ta a ɗan tsorace tace"ba nan ne ɗakin nawa ba fa"

"Daddy na yace na kawo ki nan kafin gobe,kiyi baccin ki,sai da safe"ta ƙarashe tana murmushi,don ita fa khairi ta burge ta

Har tayi gaba ta dawo baya inda ta bar ta a tsaye tana bin ta da kallo,tana murmushi tace"I'm Safiyya known as Nusra,you?"

Shiru khairi tayi tana bin ta da kallo,ko me ta tuna kuma sai ta dafe kai ta ɗago tana kallon ta tace"yi haƙuri,suna na Safiyya ana ce min Nusra,ke fa?"

"Ummul khairi,amma Ummiyo ake kira na"

"Okay zan rinƙa kiran ki yadda daddy ke gaya miki, KHAIRI!sunan yayi min daɗi,ai kina so ko?"khairi tayi murmushi tana ɗaga kai, Nusra ta ɗaga mata hannu ta fice daga ɗakin

Washegari tun da sassafe baƙi suka fara shirye-shiryen tafiya,sai haɗa musu tsaraba kala kala akeyi,yau ma feena ce ta bawa khairi soso da sabulun wanka ta shiga wanka,bayan tayi wankan ta bata man shafawa,ta gyara mata gashin ta sannan ta bata ɗaya kayan da Sulaiman ya siyo mata jiya,wanda ta cire kuma ta bata kuɗi ta siyo sabulu ta wanke ta shanya kafin su tafi

Baba atine ce ke surfen masara da iya ƙarfin ta a tsakar gidan,dakan ya dami Hajiya salma da take ɗakin ta kusa da in da ake dakan,don tana dakan ne tana waƙe waƙe,gashi ba'a hankali takeyi ba,ganin bazata jure ba ta aika Beely cewa ko ma waye yake dakan ya dakata saboda yana damun ta

Baba atine ta kalli Beely a ɗage,irin kallon rainin wayo tace"ita uwar taki ce tace ana damun ta?"

Beely tayi mata kallon banza tace"eh!ana damun ta ɗin ne Shiyasa tayi magana"

"To kice mata tazo da kanta, wataƙila nafi fahimtar saƙon"ta cigaba da surfen tana cigaba da rera waƙar barmani coge mai taken ku kama sana'a mata

Daga sama har ƙasa Beely ta kalle ta sannan ta ja tsaki ta koma ɗakin mahaifiyar ta,cikin ɓacin rai ta isar mata da saƙon ƙazamar matar a cewar ta

Cikin isa da gadara salma ta fito daga ɗakin ta tana huci,kai tsaye ta nufi wajen da baba atine take surfen ta cikin kwanciyar hankali tana ta rera ƴan waƙoƙin ta,cikin izza take faɗin"baiwar Allah saƙo na bai iso miki bane?"

Shiri baba atine tayi tana jinjina rashin kunya da raini irin na mutan maraya,ta kalli hajiya Salma daga sama zuwa ƙasa tace"wanne saƙo kike magana akai kenan?"

"Cikin isa salma tace"na gaya miki wannan dakan da kikeyi yana takura min,ki bari...."

"Uban kuturu ma yayi kaɗan ballantana kuma ɗan shi!"a cewar baba atine cikin ɗaga murya

Bata bawa Hajiya salma damar magana ba ta hau surfa masifa"ke yanzu baki ji kunya ba zaki zo ki wani tsaya min ƙerere wai na daina neman kuɗi na ina damun ki?ke ba don kuɗin ba kin isa kizo gidan nan a girmama ki?wato mu ma baƙin ciki kike mana kar mu tara kuɗin mu shige raini ko?to wallahi baki isa ba,kuji ni da ja'irar mata!"

Beely da ta ƙaraso wajen ta kasa jure ɗiban albarkar da akeyiwa mahaifiyar ta,ta kalli baba atine a yatsine tace

"Ke yanzu don kina dagewa kina dukan turmi da taɓarya shine kike tunanin zaki kamo mahaifiya ta a kuɗi?idan ma zaki daina mugun mafarki ki daina,don ko ƴan aikin mahaifiya ta ba sa'annin karawar ki bane ballantana ita da kanta"ta ƙarashe tana mata kallon sama da ƙasa ta buga tsaki ta juya zata bar wajen

Sakin baki baba atine tayi tabi Beely da idanu,Hajiya Salma tayi murmushin rainin hankali tace"ba ni ba,ko ƴa ta tafi ƙarfin karawa da ke,don haka ki rinƙa sanin abinda zaki gayawa mutane,ba kowa bane sakarai da zakiyi masa abinda kika ga dama ya zuba miki idanu"tana kai wa nan ta juya zata bar wajen

Bana atine tayi wuf ta shaƙo ta tana faɗin"ina zakije?ai ba'a kara ɗin ba ballantana a ga wanda yafi ƙarfi,tsaya mu raba raini sai nasan kin fi ƙarfin nawa"babu ɓata lokaci ta hau jibgar Hajiya salma kamar Allah ya aiko ta,dama indai dambe da bawa hammata iska ne kaf garin ba ma gidan ba ko unguwar an san wacece baba atine, masifa da bala'i da tashin hankali da dambe duka gaba ta basu ba baya ba,babu wanda ta raina dalilin yin shi a cikin su,matar da wucewa ma zatayi taga ana faɗa sai ta san yadda zatayi ta shiga inaga an zo har inda take an takale ta?abinda taga dama shi takeyi a gidan babu wanda ta ɗagawa ƙafa,inna sabuwa kuwa tuni ta siye ta da ƴan kayayyakin da take siya mata lokaci zuwa lokaci,sau tari ma ita ke cefane ta bawa mijin ta da yaran,har ma da kishiyar ta, dama ita bata da rowa kwata kwata sai masifa,wannan yasa ake shakkar ta ake tsoron shiga shirgin ta,aikin ta na surfe ko dakan kukar siyarwa ko kuɓewa kuwa ko cikin dare ta so yin abin ta zatayi babu mai ce mata uffan,sai fa yau

Ihun da Hajiya Salma take kurmawa ne ya janyo hankalin mutanen wajen,da gudu Amra ta ƙaraso wajen,tana ganin abinda ke faruwa ta zaro idanu ta koma da gudu don ta shaidawa ammin ta,sai ganin su tayi suma sun ƙaraso a guje,yara da manya

Hajiya Raheena ta tsorata sosai ganin yadda baba atine take ragargazar hajiya salma,ta haɗa mata jini da majina,ga mazan basa nan,sai yara ƙanana,da ƙyar dai matan gidan suka ƙwaci Hajiya salma,da taimakon cizon da tayiwa baba atine,da ace a hayyacin ta take da ko da kuɗi akace ta taɓa fatar baba atine bazata iya ba, saboda baba Atine bata ɗauki tsafta abinyi ba

Inna talatu maman Nadiya ce ta kama Hajiya salma ta miƙar daita tsaye tana yi mata sannu,baba Hari uwar rawar kai da shishshigi da neman wajen zama ta kawo mata ruwa ta wanke fuska,don ta fasa mata baki da hanci kuma ta kumbura mata fuska, Hajiya salma ta buge butar da baba Hari take miƙa mata ta fizgi ɗan kwalin ta a hannun Inna talatu ta shige ɗakin ta,baba atine da tuni ta koma kan surfen ta dai faɗi take

"Zuwa yanzu nasan kin gane baki fi ƙarfin nawa ba kamar yadda wannan karuwar ƴar taki tace"da sauri Beely dake laɓe can baya a tsorace ta kalle ta jin abinda tace,kalmar tayi mata zafi,amma ta san yadda uwar ta ta ci uban duka yanzu itama tumurmusa ta a wajen nan ba komai bane

Baba atine ta cigaba da surutan ta"waye ya gaya miki macen da aka tara mata dukiyar miji taci itace mai ƙarfi?baki nema ba kuma ki rinƙa tunanin kina da ƙarfi?a yau mijin naki yana sallama ki dolen uwar ki ki bar gidan sai mu ga da uban me za'ayi ƙafafar,mace baki da aiki sai ci kiyi kashi kizo kina baza mana ɗuwawu wai ke matar mai kuɗi,to sai me don abu ta kazar ubanki?"babu dai wanda ya tanka mata,don ƴan gidan sun gane bata gaji bane take neman abokin cigaba

Beely ce ta koma ta bayan gidan ta kira Azad cikin kuka ta shaida masa abinda yake faruwa,baiyi wata wata ba ya juyo ya nufo gida,suma su Sulaiman suka biyo shi,don ko da bai gaya musu komai ba sun ga alamu kamar ba lafiya ba

Yana shigowa yaga surayya tana ƙoƙarin fita da trolley ɗin kayan su,ya kalle ta fuska a haɗe yace"ke!wacece wadda ta daki mum ɗin mu?"batayi musu ba ta nuna masa baba atine da har lokacin surfen ta takeyi tana waƙe waƙen ta hankali kwance

Kai tsaye ya nufe ta yana ƙoƙarin zare belt,da sauri Sulaiman ya dakatar dashi yana faɗin"bi a hankali big bruh, za'a warware komai"Azad ya hankaɗe shi yace"what are you saying?wata baƙauyiyar banza,ƙazama ta dakar min mahaifiya sannan kana maganar na bi a hankali, saboda ba uwar ka aka daka ba?wait!ka san ma wacece mum ɗina a waje na kuwa?"maganar ta bawa Sulaiman haushi,amma yasan dole ran Azad ya ɓaci saboda uwa ta wuce wasa, musamman shi da kowa yasan yadda suka shaƙu da juna,don haka yace"bana son abin ya lalace ne,idan ita jahila ce you are educated bruh,don Allah kar ka biye mata, let's fix the....."shiru yayi da mamaki yana kallon Azad da ya sauke masa mari a zuciye yayi gaba ya nufi inda baba atine tayi ready da taɓarya tana faɗin"ƙyale shi yazo,yazo na koya masa hankali kamar yadda na koya wa uwar shi"

Shigowar baban Nadiya da tsawar da ya dakawa Azad ce ta tsayar dashi,ya waigo a fusace yana kallon baban Nadiya yana faɗin"malam wannan ba matsalar ka bace,stay out of it,kasan zafin uwa kuwa?da har zaka hana ni ɗaukar mataki akan wadda ta taɓa min uwa?ko don ba taka aka taɓa ba shiyasa zaka hana ni ɗaukar mataki?"

"Da kai da uwar taka zaman kanku kukeyi?ba a ƙarƙashin wani kuke ba?"Azad ya katse shi da faɗin"i don't care!stop interrupting me or else abin ya shafe ka"yana gama faɗar hakan ya nufi inda baba atine take ya ɗaga belt da nufin zabga mata amma sai ta goce ya samu iska

Sam bai kula da isowar Barrister Umar ba sai mahaukatan maruka hagu da dama da yaji saukar su,ya waiga da sauri yana kallon mahaifin nashi cike da mamaki

Kunya da baƙin ciki kamar ya kashe Barrister,idanun shi sun kaɗa sunyi jajur,jijiyoyin kanshi sunyi raɗa-raɗa,cikin ɓacin rai ya fara magana

"Ka kyauta Azad,ka nuna irin tarbiyyar da muka baka a bainar mutane,wannan shine mutuncin da zaka iya siya mana ko?yayi kyau,wuce mu tafi!"babu musu Azad ya wuce waje a zuciye,idanun shi sun kaɗa sunyi jajur,farar fuskar shi tayi jajur

Bai kai ga yin magana ba Hajiya salma ta fito a fusace tana kallon shi ranta a ɓace,tace"ai dama ka daɗe da nunawa duniya ni ba a bakin komai nake ba,wata banza ƴar ƙauye ƙazama ta saka hannu ta dake ni amma kazo kana dakar min ɗa saboda yace zai rama min,ko ba komai ita da nice nayi mata wannan dukan da mijin ta bazai taɓa hana ɗan ta ya rama mata ba,na godewa Allah,ko ba komai nasan naci dubu sai ceto wallahi"ta wuce fuuu har kusan takewa inna sabuwa da ta ƙaraso wajen yanzu kafa tayi bata kula ba

Kai Hajiya salma! Maganar gaskiya halin ki sai ke,bakin ki bazai taɓa barin ki ci ribar zaman duniya ba


#likecommentshare

#Nusy_bee


I just published "SIRAƊIN UƘUBA 8" of my story "SIRAƊIN UƘUBA ". https://www.wattpad.com/1576515543?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Nusybee247


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee

Page 8

Da kallo Barrister Umar ya bi ta,kafin ya ɗauke kai cike da takaici yana girgiza kai,ya ƙarasa wajen mahaifiyar shi,da ladabi ya fara ƙoƙarin yi mata magana inna sabuwa ta dakatar dashi,cikin fusata tace"tun lokacin da zaku yi aure nace ku dawo gida ku auri ƴan uwan ku da bazasu taɓa mayar da iyayen ku ƴan iska ba,amma kuka bijire kuka je kuka auri waɗanda kuka ga dama waɗanda babu ɗigon kunya a idanun su,gashi nan suna ta haifar mana fanɗararru ai,to bazan lamunta ba,dole a san yadda za'ayi, Aure kam sai ka ƙara shi,don da alamu nan gaba kaɗan sai gidan ka ya gagare ka"tana kaiwa nan ta wuce ɗakin ta fuskar ta a haɗe

A ranar dai an rabu kawai,amma ba lafiya ba,don kusan kowa ranshi a ɓace yake,ita Hajiya salma ma abin ya zame mata goma da ashirin,ga baƙin cikin zuwa wannan garin,ga ɗauko wannan jarababbiyar yarinyar a cewar ta,ga kuma dukan da taci a hannun baba atine,kuma wani ƙarin baƙin cikin yadda Barrister ya hana Azad kakkarya wannan ƙazamar baƙauyiyiyar,wannan ma kusan yafi komai tsaya mata a rai

Da ƙyar ƴaƴan inna sabuwa suka lallaɓa ta ta hakura,sukayi sallama da mutanen gidan,suka ɗauki khairi suka nufi Birnin Kano

Suna shigowa Kano kowa ya kama hanya ya nufi gidan shi da iyalan shi,ita dai Hajiya Raheena wannan tafiyar babu abinda ta ƙara sai razana ta,tayi addu'a tafi saurin shurin masaƙi Allah ya karkatar da hankalin inna sabuwa kar ta yiwa mijin ta zancen kara aure,don ita wallahi ji take idan mijin ta ya ƙara aure zata iya mutuwa ko tayi hauka

Hajiya salma kam Barrister yana sauke su ya fice daga gidan,ta shige cikin gidan ta fuuu kamar zata kifa, Azad ya bita da sassarfa, Beely tabi bayan su jikin ta a sanyaye, Ma'aruf da haidar suka bi bayan su,feena da Nusra kam suka jagoranci khairi zuwa cikin gidan

A parlour feena tace ta zauna,su kuma suka shiga ɗakin mum ɗin su da take sharɓar kuka tana magana

"Don Allah ta yaya zan so ta?ta dage kai da fata sai anyi min kishiya,bayan na samu labarin ita nata kishiyoyin korar su takeyi kuma ta hana su haihuwa,sai ni zata hana rayuwar farin ciki a gidan aure na?me nayi mata? wallahi bazan zauna da kishiya ba, saboda baƙin hali ita ta zauna ƙalau ni zata hana ni?yayi auren mu gani,wallahi in dai ta saka barrister ya ƙara aure sai na kashe matar"

"Haba mum!don Allah ya kamata ki rinƙa sarrafa zuciyar ki kar fushi ya kai ki ga aikata danasani"a cewar feena cikin takaicin halayyar mahaifiyar tasu

Cikin tsawa mum tace"ke dalla yi min shiru, shashasha!wai ace yara na maza sun fi nuna kishi da damuwa dani akan ki,sakarya kawai wadda bata san darajar haihuwa ba,kuma na sake ganin kin shiga harkar wannan ƴar iskar yarinyar kiga yadda zan baki mamaki"

"Mum me yayi zafi haka?me tayi miki.....?"bata ƙarasa ba taji saukar mari,tayi shiru tana kallon mum ɗin tasu,kafin ta iya wani ƙwaƙwƙwaran motsi mum ta fice daga ɗakin kamar zata kifa

A parlour taga khairi zaune tayi tsumu tana kallon plasma TV dake kafe a parlourn,a kashe take amma tayi mata kyau sosai, ita dama ba wani sanin kayan zamani tayi ba,ga parlour ɗin yayi mata kyau sosai,batayi aune ba sai saukar duka taji ta ko'ina,ta ƙwala ihu a gigice,amma Hajiya salma bata da niyyar raga mata, faɗi take"gwara na huce takaici na akan ki matsiyaciya,akan ki miji na ya zage ni,yayi min gori,yayi min wulaƙanci,ke ɗin wacece da har kika isa ki shiga tsakani na da miji na wanda muke tare dashi tun kafin uwar ki tayi wayo?sai kin gane kuren ki yarinya"ta gama jibgar ta ta tsallake yaran ta da suka jeru sukayi cirko cirko ta shige ɗakin ta

HAƊEJIA ROAD, KANO STATE, NIGERIA

"Ammi Ni fa na tsorata da lamarin mum,ya kamata ki gaya mata gaskiya abubuwan da take baya dacewa,yanzu kalli yadda muka baro garin kowa maganar ta yakeyi?yanzu wannan fisabilillahi abin burgewa ne?"

Wani kallo ammin tashi tayi masa tace"kaga Sulaiman! stay away from that issue that doesn't concern you,or else Kai da mahaifin ka,ina ruwan ka da ita har kana cewa na gaya mata gaskiya,zaman kanta takeyi?ko shi mijin nata bakin shi baya amfani?"

"No ammi,naga kuna tare ne,kuma seriously babu daɗi mace da yaran ta manya kamar ta ace wai anyi mata wannan dukan a bainar jama'a,dole ɗan ta yayi misbehave,gashi kuma still ta ɓata komai,anƙi a bashi goyon baya"

"Babu wata magana kamar zaman tare, kowa zaman kanshi yake da ra'ayin shi ni daita,kar ka sake involving ɗina a matsalar nan,nima ta kaina nakeyi"Sulaiman yayi mata kallon tsaf yadda take haƙiƙancewa,yasan dalilin ta,bai wuce maganar kishiya da take tsoro ba,kawai sai ya fashe da dariya,a ƙule ta kalle shi tana faɗin"bana son shashanci,ya zaka zo ka saka Ni a gaba kanayi min dariya? mahaukaciya ka ɗauke ni?"Sulaiman yana ƙoƙarin danne dariya yake faɗin"I'm sorry ammie, kawai wani abu na tuna,bari na ɗan yi refreshing,daga nan ma zan taɓo babban yaya inaga"

Da ɗan murmushi a fuskar ta take faɗin"ka gaishe shi,ka gaya masa ina missing ɗin shi,tunda anyi tafiyar an dawo yanzu ai ya dawo mu gana ko?"Sulaiman yayi murmushi yana faɗin"rabu dashi ammie,dole zai dawo ai,kowa ya bar gida ai gida ya barshi"ammi tayi ƴar dariya,shi kam ya fice zuwa part ɗin shi


BOSTON, MASSACHUSETTS,USA


Cikin nutsuwar da ta zame masa jiki yake fito da motar shi ƙirar Lamborghini Urus daga harabar adana motocin nashi,yana daga cikin motar yayi ƙoƙarin yin controlling gate ɗin ya rufe da remote,har ya tayar da motar ya tuna yayi mantuwa,ya fito daga motar don komawa cikin gidan ya ɗauko abinda ya manta

Yau ma kamar kullum sanye yake da riga sky blue da blue jeans,ya ɗora jacket blue akan kayan nashi,ƙafar shi sanye da takalmi Boot baƙi

"Hye!"yaji wata zazzaƙar murya daga bayan shi ta faɗa

Da farko bai damu da waigawa ba,amma jin an sake yi masa tayin maganar ya saka ya juya don ganin mai wannan aikin

Matashiyar budurwa ce da bazata gaza shekaru ashirin zuwa da biyar ba,fara ce tas, kyakykyawa ce sosai,tayi murmushi dimples sun bayyana a duka kumatun ta biyu,sanye take da riga da wando na jeans, sai rigar sanyi pink color da ta saukar mata har gwiwa,kanta sanye da hula baƙa,hannun ta riƙe da ƴar ƙaramar purse

A ƴan sakwanni ya ƙare mata kallo sannan ya ɗauke kanshi yana faɗin"hye!ya faɗa gidan nashi batare da ya sake bi ta kanta ba

Ya kai kusan mintuna biyar da shiga kafin ya fito hannun shi riƙe da jakar laptop,ya Sha mamakin ganin ta da yayi a tsaye,tana ganin shi ta fara murmushi,ya ɗauke kai ya nufi motar shi,ta taso tana faɗin"excuse me Please, can we be friends?seems like we are from the same country, I'm INAAYA by name,you?"kallon nata ya kuma yi a ɗage ya ɗauke kai ya faɗa motar shi ya ja da gudu ya bar ta a wajen

Kai tsaye kamfanin su ya nufa, haɗin gwiwa ne dashi da Mr mark Anderson da Mr Johnson Philip,dukkan su abokan karatun shi ne a University of Texas da ke Austin anan US ɗin,bayan sun haɗa degree da masters ɗinsu duka akan automobile engineering suka dawo Boston da ke nan Massachusetts suka buɗe Company dake fitar da motoci da spare parts ɗin su

Mai girma injiniya nima ina son mota ɗaya 😩

#likecommentshare

#Nusy_bee


I just published "SIRAƊIN UƘUBA 9" of my story "SIRAƊIN UƘUBA ". https://www.wattpad.com/1576732411?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Nusybee247


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee

Page 9

Bai koma gida ba sai wajen biyar na yamma,don sun ɗan zauna meeting da manyan company ɗin saboda design na sababbin motoci da suke shirin fara fitarwa nan da watanni uku,sai da ya tabbatar komai yayi daidai sannan ya dawo gida

Bayan bayan yayi wanka ya ci abinci kai tsaye ya ɗauki waya ya kira Sulaiman,Sulaiman baiyi mamakin ganin kiran Auwab ba,don ya san su biyu basa shamakin kiran juna kowanne lokaci batare da sun damu dare ne ko rana ba,duk da kasancewar ƙasashen biyu US da Nigeria suna da bambanci da ratar lokaci a tsakanin su

"Weldone man!ko bangajiya bazakayi mana ba mun dawo daga garin ku ko?"

Auwab yayi ɗan murmushi yana faɗin"sarkin ƙorafi,shiyasa na kira ka yanzu,yau mun wuni aiki shiyasa ban taɓa ka ba sai Yanzu,so ya hanya?ya kuka baro su inna?"

"Mhm! almost everything is not funny Yaya Auwab,can you imagine Wai mum ɗin su Azad da wata villager suka kacame da dambe?"

Zaro idanu Auwab yayi yana faɗin"what!do you know what you are saying Sulaiman?"

"Seriously Yaya Auwab!Matar nan tayi mata dukan rashin mutunci,ga Azad Wai yazo zai shiga ya ramawa mum, imagine guy ɗin nan don na hana shi ya wanka min mari!"

Dariya ta ƙwacewa Auwab yana faɗin"I warn you times without a number cewa ka fita harkar da ba taka ba amma kaƙi,so for me I have nothing to say to you, beside,me ya haɗa mum da rigima da villagers?"

"Oho mata,kawai dai tunda muka je tana ta creating problems daga wannan sai wancan,can you remember our late senior uncle?to wai don dad yace zai ɗauko his only daughter kawai tayi ta faɗa da mutane,ta janyo inna tace wai sai dad ya ƙara aure, imagine!

Itama ammie ta tsorata da hukuncin nan,kasan ammie dai"shi kanshi Auwab sai da yayi dariya ballantana Sulaiman da yake bashi labarin, Auwab yace"Allah ya sauwaƙe,Ni dai maybe na dawo next week,Amma bazan juma ba zan dawo"

Sulaiman yace"to Allah ya kawo ka lafiya,kazo kaima ka fitar da mata kamar yadda akace mana"Sulaiman ya ƙarasa yana dariya"Auwab yayi tsaki ya kashe wayar,shi lamarin mata ma baya gaban shi ballantana a sako shi gaba da batun aure

LUGARD ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA

Khairi ce kwance a cikin ɗakin ta lulluɓa tana ta rawar sanyi,tunda mum tayi mata wannan uban dukan feena ta ja ta zuwa wani ɗaki ta haɗa mata ruwan zafi,bayan tayi wanka ta bata maganin ciwon jiki ta kwantar da ita akan gadon ɗakin,ta ƙara bata haƙuri kafin ta fice daga ɗakin, zuciyar ta cike da tausayin ta

Ta kai a ƙalla mintuna arba'in zuwa da biyar kafin taji kiran sallar azahar,ta miƙe tsaye tana ta rarraba idanu tana tunanin inda ya kamata ta shiga tayo alwala ta samu tayi sallah,ganin babu waje ya sa ta koma ta zauna tana tunanin fita,duk da bata ga alamun rahama daga wajen mutanen gidan ba,ga yunwa da take ji kamar hanjin ta zai fito,amma bata san ma yadda zata tambayi mutanen gidan abinci ba

Wata matashiyar yarinya da bai fi ta girme ta da shekaru biyu ba ta leƙo ɗakin tana faɗin"yallaɓai yake kiran ki"tana gama isar da saƙon ta juya batare da ta saurari abinda khairin zata ce ba

Cikin mutuwar jiki ta miƙe ta fice daga parlourn tana tunanin inda zata ga yallaɓai ɗin da akace yake kiran ta, Allah yayi mata gyaɗar dogo tana fitowa ta hango Daddy a zaune yana danna waya,yana ganin ta ya saki fuska sosai yana faɗin"ƙaraso nan Dr khairi,maza zo nan daughter"cikin sanyin jiki ta nufi inda yake,da sauri ta sunkuyar da kanta ganin irin mugun kallon da Beely take aiko mata,tana can second parlour kusa da ɗakin mom

A ƙasa ta zauna kusa da ƙafafun daddy,daddy yace"No!tashi ki zauna a kujera,magana zamuyi"

Kanta a ƙasa tace"don Allah ka bar ni anan baba"

"No tashi ki hau kujera"babu musu ta tashi ta zauna a ladabce,a nutse ya ƙare mata kallo kafin yace"me yake damun ki?ya naga kin chanja?"

Kanta a ƙasa tace"babu komai,gajiyar mota ce"

"To ai shikenan! khairi ya baƙunta?kinga gidan namu ko?"kanta a ƙasa ta gyaɗa kai

"Ya burge ki?"tana murmushi ta gyaɗa kai,yace"to Masha Allah

In Sha Allah satin da zamu shiga za'a kai ki makaranta,a ina kika tsaya a karatun ki na boko?"khairi ta girgiza kai tace a sanyaye"bana zuwa boko"

"Islamiyya fa?"ya sake tambayar ta

"Ina zuwa makarantar dare"

"A ina kika tsaya a karatun islamiyyar?"

"Muna wannaazi'ati,bamu gama ta ba amma"

"To Masha Allah,in Sha Allah Zaki koma islamiyyar ki cigaba da karatun ki,sannan kuma ki cigaba da karatun ki na boko har ki zama likita ko Dr?"tayi murmushi tana rufe fuskar ta

Sun ɗan daɗe yana ta jan ta da hira kafin tace zatayi sallah,ya kira feena yace ta raka ta tayi alwala

Feena ce ta nuna mata yadda zata yi amfani da kayan banɗakin,bayan tayi alwala feena ta kawo mata abin Sallah

Bata daɗe da idar da sallah ba feena tazo ta kira ta su ci abinci,babu musu ta mayar da hijabin sallar ta ta bi ta zuwa dinning area da masu aikin suka shirya mata

A ƴan seconds ta ƙare musu kallo tayi kasa da kai,mum da Beely sai aiko mata da harara sukeyi,dad Yana riƙe da jarida yana karantawa,shi kuwa Azad kallo ɗaya yayi mata ya mayar da kanshi ga danne dannen waya da yakeyi, Ma'aruf da haidar sarakan I don't care attitude sai hirar su ta ball sukeyi ta favourite club ɗin su real Madrid da ƙoƙarin da players ɗin su sukayi jiya a el classico, Nusra kam itama kallon ta takeyi tana ta murmushi

Cikin kulawa daddy ya nuna mata kujera,kanta a ƙasa tayi masa godiya ta zauna

Kwanan ta biyu a gidan a haka,ko gaida mum Bata iya zuwa saboda sakamakon da take karɓa idan ta gaishe ta,ranar da daddare bayan sun gama cin abinci daddy ya kalli Azad yace"Azad gobe idan Allah ya nuna mana kai zaka dire khausar da Ma'aruf a makaranta,daga nan zákayi enrolling khairi"

Kafin ya kai ga magana mum tace"I don't get you barrister!kana nufin makarantar da yara na suke attending nan zaka kai ta?"

Juyowa yayi ya kalle ta cikin nutsuwa yace"to menene bambancin ta da yaran naki?"

"No you must be joking barrister! imagine this girl is attending the same school with my children, impossible wallahi!"daddy yayi murmushi yace"well!na fahimce ki,tunda kin hana hakan ya zama dole na yanke abinda nakeyi na kai ta nigerian Turkish a Abuja da kaina,nasan dai ba can yaran ki ke attending ba ko?"

Abincin da ta zuba a bakin ta ya tsaya cak yaƙi gaba yaƙi baya,shi kam Barrister bai sake bi ta kanta ba ya cigaba da cin abincin shi cikin nutsuwa,su kam yaran sai kallon iyayen sukeyi duk da ba baƙon abu bane iyayen suyi tashin hankali a gaban yaran,don kowa cikin su fusatacce ne,a baya Barrister bai cika kula mum ba idan tana hayaniya,a yanzu shima ya hau layi,khairi kuwa tsumu tayi,dama ta kasa sakewa ta ci abincin, Barrister yayi murmushi yana kallon ta yace"maza ci abincin ki Dr,kinji?"tayi ɗan murmushin yaƙe tana cusa abincin

Cikin wani irin ɓacin rai da tsananin mamaki mum ta kalle shi tace"Barrister what do you mean with this girl?do you think zaka kawo ƴar wasu ka kawo gidan aure na ka fifita ta akan yara na kuma nayi shiru?to wallahi bazan riƙe ta ba, bazata zauna min a gida ba na gaya maka,don rashin adalci tun kafin aje ko'ina har ka fara rashin adalci?yara na babu yadda banyi da kai ba ka kai su nigerian Turkish inda ƴan uwan su suke yi amma kaƙi,kace day zasuyi,haka ka kai min yara intercontinental,sai wannan ƴar gold ɗin za'a kai inda ka kasa kai min yara?"

Ko kallon ta baiyi ba ya cigaba da cin abincin shi yana danna waya,ita kam masifa ta inda take shiga bata nan take fita ba, baƙin ciki ne ya tashi feena da Azad,sauran yaran kam takaici ya ƙule su,banda Beely da take tunanin me zatayiwa wannan yarinyar ta huce,da kullum sai ta saka mahaifiyar su ɓacin rai?

Mahaifiyar ki zaki bawa shawara amma babu ruwan ƴar mutane 😏

#likecommentshare

#Nusy_bee


I just published "SIRAƊIN UƘUBA 10" of my story "SIRAƊIN UƘUBA ". https://www.wattpad.com/1576944510?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Nusybee247


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️ Nusy bee

Page 10

HAƊEJIA ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE

"Sannu da gida ammi"

Hajiya Raheena ta kalle ta tana faɗin"Amra kin dawo?"

"Eh na dawo"ta bata amsa tana zama akan kujera"na gaji wallahi, Allah Allah nake driver ɗin mu ya dawo,na gaji da driving"

Murmushi hajiya Raheena tayi tace"sai ki jira kuwa,don abban ku yace babu ku babu wani driver again,kowa yayi driving kanshi"

Amra ta ɗan yamutsa fuska da takaici tace"but why ammie?ko laifi mukayi kuma?"

"I don't know,ki tambayi abban ku da ya zartar da hukuncin"shiru Amra tayi na ƴan sakwanni kafin tace"ammie wai yaushe yaya Auwab zai zo ne?kwana biyu shiru,ko a waya ya kan juma bai taɓo mutane ba"

"Maybe ya shigo next week,don kamar haka ya gayawa yayan ku"

"To Allah ya dawo dashi lafiya"

"Ameen"ammin ta amsa

Shiru sukayi gaba ɗaya, Hajiya Raheena ta kalli Amra tana faɗin"seems like akwai abinda kike son faɗa,feel free ki gaya min"

Amra ta girgiza kai da jimami tana faɗin"wallahi tausayin mum nake ji ammie,ki duba wulaƙancin da akayi mata don Allah,wai har da duka kuma ba'a ɗauki matakin komai ba,ƙarshe ma waccan tsohuwar wai har da cewa ayi mata kishiya!"

Murmushi hajiya Raheena tayi tana faɗin

"A matsayin ki na mace wadda take auren wani take rayuwa a ƙarƙashin ikon wani,kuma zata haifi yara mata ta basu tarbiyyar da zasuje gidan miji suyi alfahari daita,bai kamata Hajiya salma ta baki tausayi don anyi mata wulaƙanci ba,kamata yayi ta baki tausayi saboda bata iya controlling speech ɗin ta,bata ganin darajar mijin ta sannan bata bin duniya a sannu

Idan mace tana da waɗannan ɗabiun kullum ranta a ɓace yake,don shi fa namiji ba bawan mu bane ballantana muyi ta yi masa abinda muka ga dama ya ƙyale mu, kiyiwa kanki adalci ki girmama mijin ki sai ku zauna lafiya

Amra!kinga dai abinda ake faɗa akan Salma,to lokacin da mazajen mu suka aure mu babu kalar tsangwama da kyara da wulaƙancin da ban gani ba,kinga Salma da kuke ganin a yanzu bani da kamar ta a Kano?to ba haka bane,na dole ne,har yanzu ban manta yadda dangin mazajen mu suka fifita ta akaina ba,kawai don ita bafulatana ce ni kuma shuwa,sannan bugu da ƙari ta riga ni haihuwa,a wancan lokacin nayi haƙuri na ɗauke kai,idan aka zo taro zakiji tausayi na da mamakin yadda salma takeyi min a bainar jama'a,kawai dai daga baya na ari I don't care attitude na yafa na zauna lafiya,kuma still duk lokacin da taro ya kai mu albasu yawanci da kukan cin mutuncin da akeyi min nake dawowa, a gaba na tare da salma ake faɗin ai shuwa akwai mu da bin bokaye,turaren mu na asiri ne,bama tausayin miji da sauran su,na haƙura na shanye,gorin haihuwa kuwa da bi da wata matar kawun ku har zame mana kamar karatu yayi

Amma salma ko yaya akayi mata kuskure a cikin dangin mijin ta sai ta ɗaga murya,a dalilin haka ta kwaranyar da soyayyar da akeyi mata zuwa tsana,babu irin shawarar da ban bata ba don ta rinƙa iya bakin ta bata ji ba,wannan dalilin ya sa duk abinda tazo dashi sai na karɓa nima,na taya ta jaje,amma......"ammie tayi ɗan murmushin bakin ciki sannan ta cigaba"Ni kaɗai nasan me salma tayi min,a yanzu yarinyar da ke hannun ta ce abar tausayi ba ita ba"

Shiru Amra tayi tana kallon ammi cike da tausayin ta,kafin ta kai ga magana Sulaiman ya shigo da sallama

Suka amsa,ya ƙaraso ya zauna yana faɗin"wash!na gaji wallahi"

"Ɗan sanda abokin kowa!har da ɓarawo da ɗan iska!"a cewar Amra,ta ƙarashe tana dariya

Ya kalle ta yace"ki bari ɓarawo ya kawo ƙarar ki office ɗina a lokacin zaki tabbatar ni abokin kowa ne"ammi da Amra sukayi dariya kafin suyi masa sannu da zuwa, Amra ta miƙe don wucewa ɗakin ta,ammie ma ta kalle shi tace"kaje ka shirya kafin na haɗa maka abinci"baiyi musu ba ya miƙe yayi kissing kumatun ta ɗaya sannan ya fice zuwa sashen shi

BOSTON, MASSACHUSETTS,USA

Yau Lahadi, Auwab bai je office ba,Yana zaune akan sofa yana duba ayyukansu na gaba a laptop ɗin shi,daga shi sai riga armless fara da three quarter light brown,Yana riƙe da coffee mug yana sipping a hankali

Ƙarar intercom yaji,babu ɓata lokaci ya bayar da izinin shigowa

Ɗagowa yayi da mamaki yana amsa sallamar da yaji daga bakin mace,ya sha mamakin ganin yarinyar nan ta shekaranjiya,wadda tayi masa magana har ta gabatar da kanta da suna Inaaya

Fuskar ta kamar koyaushe yalwace da murmushi,ta ƙaraso parlourn ta samu kujera ta zauna tana kallon shi tare da faɗin"good morning Mr charming"

Kallon ta yayi don jin sunan da ta kira shi,bai kai ga bata amsa ba ta ɗora

"Tun shekaranjiya da muka haɗu ban sake ganin ka ba,shine nace bari na duba gidan ka naga ko lafiya?"

"To pa!muka haɗu kuma?da ni?"

Tayi mamakin jin maganar shi amma sai tayi fuska tayi murmushi tace"maybe ka manta ne,amma mun haɗu da kai a bakin gate ɗin ka, I even told you my name,Amma Kai baka gaya min naka ba"ta ƙarashe tana karya kai

Ɗan murmushi yayi yana taɓe baki ya cigaba da duba abinda yake dubawa,ita kuma ta zuba masa idanu tana kallon shi

Ya kai kusan mintuna goma kafin ya ɗago yana faɗin"sorry fa!aiki nake,na bar ki ke kaɗai ko?"

Tana murmushi ta girgiza kai tace"not at all,iya kallon ka ma da nayi I'm okay with it"

"So now,a kawo miki coffee?"tayi shiru tana kallon shi tana lumshe sexy eyes ɗin ta cikin wani salo

Da dabara ya ɗauke kanshi a ranshi yana karanto _a'audhu billahi minash shayɗanir rajeem_ sannan ya sake kallon ta yana jiran amsar ta,tana murmushin ta mai jan hankali tace"sai ka maimaita suna na ka gaya min naka tukunna"

Auwab yayi murmushi yana faɗin"sunan ki yana bani wahala ne,kin san ba irin namu bane,but for me I'm Auwab by name"

Murmushi tayi tana gyara zama tace"can you tell me more about yourself please?"

"I'm Auwab Usman Saeed,from kano state,nayi degree da masters ɗina a University of Texas dake Austin,akan automobile engineering,daga baya mun buɗe Company na ƙera motoci da spare parts ɗin ta Ni da abokan karatu na, I'm the first child of my parents,I have other three siblings,what about you?"

Ta sakeyin murmushi sannan ta fara"as I said my name is Inaaya mukhtar,mahaifi na ɗan asalin jihar Adamawa dake Nigeria ne, mahaifiya ta kuma ƴar asalin diffa ne dake Niger, I'm their only daughter,karatu ya kawo ni nan Boston,ina karantar business admin a University of Boston,Amma ina zaune a gida na nan kusa da kai"

"That's nice"ya faɗa yana cigaba da aikin shi

"Can we be friends?"ya jiyo tana tambayar shi

Ya ɗago yana kallon ta yana faɗin"why not?"

"Bani phone ɗin ka"babu musu ya miƙa mata wayar shi da ke ajiye kusa dashi,ta saka number ɗin ta ta kira wayar ta, number ɗin shi tayi appearing a wayar ta ta katse tana murmushi ta miƙa masa wayar shi ya mike tsaye tana faɗin

"This is my phone number,I will wait for your call"ta fara takawa ta nufi waje tana faɗin"bye!see you next time"ta fice tana murmushi

Shima ɗan murmushi yayi yana cigaba da aikin shi,don so yake nan da kwanaki uku ya bar ƙasar

LUGARD ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA

Khairi ce zaune a ɗakin ta ta rafka tagumi,abin duniya ya dame ta,a gaban idanun ta mum tayiwa yaran ta warning su fita harkar ta,dama masu shiga harkar tata su biyu ne kawai,daga Nusra sai feena,haidar da Ma'aruf kuwa su ko matsalar da ta shafi gidan ma bata gaban su ballantana tata, Azad kam tun ganin ta dashi na farko bata ga alamun tausayi ko rahama a fuskar shi ba,tsoron shi ma takeji

Buɗe ƙofar akayi,da sauri ta ɗago kai tana kallon wadda ta shigo,wannan mara mutuncin ce,wato Aunty Beely,kamar yadda taji ƙannen ta na kiran ta

Kamar kullum da suka dawo gidan,yau ma farar ƴar riga ce a jikin ta da jeans,Wanda ya kama ƴan ƙafafuwan nata,dama ba ƙiba gare ta ba,sai gashin ta da ta ɗaure ta sake shi baya,fuskar nan a ɗaure ta ƙaraso ta zauna a gaban khairi da tuni jikin ta ya fara kaɗawa kamar mazari

"Tun daga lokacin da mahaifin mu yace zai ɗauko ki zaman lafiya ya kauracewa gidannan, kullum ran mahaifiyar mu a ɓace yake saboda ke,an kawo ki tun kina baƙuwa ana ƙoƙarin fifita ki a kanmu,baƙauyiya, bagidajiya,jahila!

To ki sani,ba dai kin shigo birni ba zakiyi rayuwar jin daɗi?sai kin gwammace zaman ki a ƙauye,sai kinyi nadamar biyo mu,don wallahi yadda kika tarwatsa mana farin ciki kema baki isa kiyi shi ba,sai dai bana gidannan ko bana numfashi"tana gama magana ta miƙe ta take khairi ta fice daga ɗakin,ta bar khairi da bin ta da kallo,idanun ta suna tara hawaye

Haɗe kai da gwiwa khairi tayi tana zubar da hawaye, kewar mahaifiyar ta ta cika mata zuciya,yau da ace tana tare da ita a ƙalla da kukan maraici kaɗai zatayi,bazatayi na rashin gata ba,amma itama ta san yanzu sai yadda Allah yayi da rayuwar ta

Ranar Lahadi da sassafe Azad yayiwa mutanen gidan sallama don komawa ƙasar Australia in da yake aikin shi, Beely da Ma'aruf ne suka raka shi airport,har lokacin ba'a daɗi tsakanin mum da Daddy

Shima washegari Daddy ya shirya don komawa Abuja bakin aikin shi,ya saka khairi ta shirya ƴan kayan ta don ya kai ta makarantar da yayi niyya

Mum ce ta fito daga ɗakin fuskar ta a ɗaure take faɗin"na rantse da Allah babu wata ƴar matsiyata da aka isa a fifita ta akan yara na a gidan nan,wallahi baka isa ka ɗauke yarinyar nan ba sai dai duk bala'in da za'ayi a yi"

A nutse ya kalle ta yace"salma bani waje zan wuce"

"Wallahi bazaka wuce ba,babu wata ƴar ƙauye da ta isa tazo ta shiga gaban ƴaƴa na, wallahi idan kayi haka sai kayi nadama"

"Salma!bani hanya kafin nayi miki abinda ban taɓa yi miki ba"

"Abubuwa nawa kayi min waɗanda baka taɓa yi min ba akan wannan ƴar iskar yarinyar?sai naga yadda zaka bar gidan nan daita ai"

Barrister bai sake magana ba ya ɗaga waya ya kira yayan shi lieutenant general Usman,a taƙaice yayi masa bayanin abinda ke faruwa, girgiza kai kawai Abba yayi yace"rabu da ita,ka bawa Azad ko Ma'aruf wani ya kai ta makarantar feature leaders international school,wani lokacin biyewa mata ana hayaniya babu abinda yake ƙarawa sai ɓacin rai"

"Okay sir!bari nayi hakan"yana sauke waya ya kalli Haidar da ya shigo parlourn yanzu yana ta sauri don yana neman makara a wajen aiki yace"Aliyu mazan fama!"

Haidar ya ƙaraso yana murmushi yana faɗin"good morning Dad and Mom"Salma ta kalle shi ta watsar,daddy yace"morning jarumi na, I hope everything is okay"

"Alhamdulillah Daddy, I'm off to work"

"No before going,can you help your sister kayi enrolling ɗin ta a school Please?"

Kafin haidar yayi magana Mom tace"aa aiki zaije,ko baka ji ya faɗa bane?to babu inda za'a tura min ɗa"


Su mum masu ɗa😁


#likecommentshare


#Nusy_bee


I just published "SIRAƊIN UƘUBA 11" of my story "SIRAƊIN UƘUBA ". https://www.wattpad.com/1577162038?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Nusybee247


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee

Page 11

Barrister ya mayar da kallon shi ga mum a nutse yace"excuse me Madam!da ɗana nake magana ba dake ba" sannan ya ɗauke kai ya sake kallon Haidar yace"bari na tura maka kuɗin da za'a buƙata idan kaje can ɗin"

"Ɗan ka ko?to kai Haidar idan har ni na haife ka,kayi wata tara a ciki na kuma kai ɗin ɗan halal ne ba shege ba ban yi maka umarnin fitar da yarinyar nan ko ƙofar gida ba"

Haidar ya kalli mum ɗin nashi,bai sake magana ba yayi saurin nufar waje batare da ya sake bin takan iyayen nashi ba

Murmushin cin nasara mum tayi tana kallon yadda daddy ya bi Haidar da idanu,kafin tayi magana suka ji Muryar Beely tana faɗin"Daddy Ni zan kai ta"

Dukan su suka juya suna kallon Beely da ta haɗe cikin doguwar riga baƙa da ta haska farar fatar ta,ta ɗora mayafin rigar akanta ta saka baƙin spec,da sauri mom ta kalle ta da mamaki,tayi ɗan murmushi tana faɗin"Please mum you have to take it easy,menene a ciki don an kai ta Makaranta?idan ta samu ilmi ta zama mutum ai amfanin mu ne baki ɗaya,ko babu komai ladan kula da Maraya na dabam ne"

Murmushi ya bayyana sosai a fuskar daddy ya shafa kan Beely yana faɗin"thanks very much daughter, Allah ya albarkaci rayuwar ki,bani account number ɗin ki na saka miki kuɗin"babu musu ta bashi ya saka mata har na ƴar siyayya da zatayiwa khairi,sannan yayi musu sallama ya fita

Gaban khairi ya buga,dama ta tsorata tun lokacin da Beely tace zata kai ta Makaranta, Beely ta kalle ta tana murmushin da ita kaɗai tasan ma'anar shi tace"zamu iya tafiya?"jiki a sanyaye khairi tayi waje batare da ta amsa ba,itama Beely ta biyo bayan ta

Maimakon makaranta wani gida Beely ta kai khairi,matar gidan yarinya ce bata wuce shekarun Beely ɗin ba,ta kalli matar tana faɗin"samha gata nan,tayi miki aikin,idan batayi ba na baki dama ki ci min uban ta"samha tayi dariya tace"kar ki damu zata yi ma,ai nice fa"Beely tayi dariya tace"ƙwarai kuwa na san ki farin sani"

Samha ta gyara zama tana kallon Beely tace"ni kuwa Beely ya batun Dr mu'azzam ne?na ƙosa mu sha shagali fa"

Cikin jimami Beely tace"samha naga darasi, ke dai fara bawa yarinyar nan abin yi tukunna"samha tace "yanzu kuwa,dama ina da wanke wanke na fin sati guda tunda bintalo ta gudu,ke!tashi mu wuce"babu musu khairi ta miƙe suka nufi kitchen ɗin ta

Ta ƙofar baya ta saka ta ta fito da dukkan kwanukan wanke wanken sannan ta bata soso da abin kumfa ta koma wajen ƙawar ta

Samha da zumuɗi ta zauna tana faɗin"ƙawa ina jin ki,tell me what happened?me ya haɗa ku da Dr mu'azzam ɗin?"

Ƙwalla ta ciko idanun Beely ta kalle tana faɗin"we were together with him for almost five years,can you imagine Ashe guy ɗin nan yana da yarinyar da suke dating? suddenly sai gashi maganar Engagement ɗin shi da wata yarinya yana yawo,da nayi masa magana he was like"babe ke bakya raina ƙaramar magana,bakya bambance rumours da labarin gaskiya,kin san dole za'ayi min irin haka"daga haka na watsar,na yarda dashi hundred percent, friend ɗina da mukayi karatu a Turkey,nasma, har faɗa mukayi daita da ta dage sai tayi insisting ɗina na yarda Dr mu'azzam cin amana ta yakeyi, kwatsam sai ga wedding pics ɗin shi suna rotating a social media,da na kira shi na tambaye shi sai yace haka ne,but he still love me,yarinyar ma ƙaddara yasa ya aure ta,da na kama yi masa masifa shine har da yi min tsawa,wai shi ya godewa Allah ma da bai aure ni ba saboda bai ga alamun tarbiyya a tare dani ba, imagine samha"ta karashe tana share hawaye

Samha ta dafa kafaɗar ta tana faɗin"don't mind friend,in Sha Allah Wanda yafi shi komai zai zo gare ki,kuyi auren ku ku rayu cikin farin ciki"Beely ta goge hawayen ta tana murmushi take faɗin"yeah ko yanzu ma Allah ya bani wani,amma shi matsalar mai mata ne har da yaro"

Samha tace"then?so? C'mon ki auri abin ki,ko tsoron matar tashi kike ji ne?"Beely ta juya manyan idanun ta tana girgiza kai tace"not at all, kawai ban san fitina ne, I want peace a gidan aure na"samha tace"duk zai yiwu,if zata iya zama dake fine,idan bazata iya ba kawai mu auna ta gaba,ni don ta ni ma zan fi so mu kora ta"Beely tace"whatever!kuma fa Yana yawan kawomin complain ɗin ta,wai ta cika ɗan banzan kishi,gata ƙazama,kuma ta raina ƴan uwan shi"

"Good!ai kishiya kucaka tayi Beely!ke kuma kina shiga ki kame zuciyoyin dangin nashi,tsafta kam dama nasan ba baƙuwar ki bace,kishi kam muyi namu mai aji,mu bar mahaukaciyar"suka tafa suna shewa

Sun ɗan daɗe suna hira,har khairi ta gama wanke wanken,samha ta bata shara da mopping,garin mopping parlour ta faɗo da wata kwalbar turaren wuta ta fashe,tun kafin su gani take tsumar tsoro,hakan bai hana su yi mata dukan rashin mutunci ba,sannan Beely ta umarce ta ta gyara wajen sannan ta cigaba da aikin

Basu bar gidan ba sai wajen ƙarfe uku,khairi ce ta kammala girkin amma ko cokali ɗaya basu bata ba,da zasu tafi ne samha tace"Ni kam Beely why not ki Kai yarinyar nan wata makaranta nan kusa damu ta yaƙi da jahilci gudun kar asirin mu ya tonu wajen dad?kinga shi makirci sai ka laƙance shi kuma ka bishi a sannu gudun kar abubuwa ya kwaɓe maka,amma me kika ce?"

Beely ta yatsina fuska tace"No problem,ayi hakan, Allah ya kai mu gobe,zan kashe kamar nawa?"

"Bai fi 10k ba zuwa 15k"a cewar samha

Beely ta zaro idanu tana faɗin"really?yauwa! normal!gobe zanyi enrolling ɗin ta in Sha Allah,see you soon"sukayi sallama,samha ta koma gida,su kuma su shiga mota

A gaban khairi Beely ta gayawa mum duk yadda akayi,mum tayi murmushi tana faɗin"tunda yarinyar nan tazo gidan nan sai yanzu naji sanyi,na bar ki ki hukunta yarinyar nan daidai da irin ɓacin ran da na shiga"Beely ta miƙe tana murmushi tana faɗin"an gama lovely mother"

AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT,KANO STATE, NIGERIA

A hankali yake saukowa daga jirgin kamar mai kirga steps,Yana ta bin airport ɗin da kallo yana ɗan murmushi,shi kanshi yasan yayi missing gida, musamman iyayen shi da ƙanin shi kuma abokin shi Sulaiman

Taxi ya hau ta kai shi har haɗejia road, dawowar Sulaiman kenan daga aiki ya shigo gaida ammie kawai suka ji sallamar shi

Da tsananin mamaki suke kallon shi,don sun san da zuwan shi amma basu san yau zai dawo ba,ya ƙaraso yana murmushi ya bawa ammie side hug sannan ya rungume Sulaiman,Sulaiman ma ya rungume shi yana faɗin"oh bro!are you?dama ka shirya surprising ɗin mu haka shiyasa ka ƙi gaya min ranar dawowar ka?"

Auwab ya zauna yana murmushi yace"of course good evening ammie!"ammie dake ta murmushi tace"evening sweetheart!how was the journey?"

"Alhamdulillahi ammie,ammie I'm hungry,bari nayi wanka nayi sallah, I want to taste your food,I miss it"ammie tayi murmushi tace"bari kuwa na shiga kitchen na dafa maka favourite ɗin ka"bata jira cewar shi ba ta miƙe ta nufi kitchen,shima ya fice daga parlourn Sulaiman ya take masa baya,kowa ya nufi part ɗin shi

Bayan Isha'i suna tare a parlourn ammie gaba ɗayan su suna hira, Auwab yana ta basu labarin cigaban da suka samu a Company ɗin su,suma suna bashi labarin Nigeria,suna maida yadda akayi na zuwa garin albasu,wani suyi dariya wani kuma alhini,ammie ta kalli Auwab fuska babu rahama tana faɗin"Auwab!"

Ya ɗago yana kallon ta jin yadda ta kira shi,bata jira ya amsa ba ta cigaba

"Nasan dai kana son na zauna lafiya da mahaifin ka ko?to ina baka shawara kayi aure,kayi aure ka tsira min da guntun mutunci na da ya rage a dangin uban ka,ku shaidu ne na abubuwan da na fuskanta daga gare su, da yawan su gani sukeyi Ni na hana ku aure,ko nace nice ban baku tarbiyyar da ta dace ba,haka kuke fatan a cigaba da kallo na?"

Sulaiman yayi murmushi yana faɗin"kar ki damu ammie,zanyi magana da big bruh,in Sha Allah shima very soon zai kawo miki kyakykyawar sirika kamar shi"ammie tayi murmushi tace"Ni da zaibi ta tawa ma da yaje Maiduguri ya auri Ameera ƴar yaƴa na"

Sulaiman ya waro idanu yana faɗin"shikenan ammie mu a Maiduguri zamu tare?Ni zan auri Mifra daga Maiduguri, Amra ma zata auri Khaleel daga Maiduguri,sai big bruh,kema sury ki lalubo mana ɗan saurayi daga Maiduguri"surayya ta rufe fuskar ta tana murmushi,ammie ta kai masa duka tana faɗin"ja'iri"ya goce yana dariya

Auwab ne ya kalli sulaiman yace"bruh gobe zaka raka ni na gaida su dad"

Sulaiman yace"sai dai mom kawai,don dad ya tafi Abuja yau da safe"

"Okay then,muje mu gaida mom ɗin"

Surayya tace"daga nan sai kayiwa Dr khairi welcome"ta ƙarashe tana dariya

Auwab ya kalle ta yace"wacece Dr khairi kuma?"


Idan kaje ka ganta😁

#likecommentshare

#Nusy_bee


I just published "SIRAƊIN UƘUBA " of my story "SIRAƊIN UƘUBA ". https://www.wattpad.com/1577372072?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Nusybee247


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee
(Marubuciyar Matar Khalees da Barrister Hibba)

Page 12

Surayya ce ta kwashe da dariya tana bawa Auwab labarin khairi,ta ƙara da cewa"dad ne da tsokana wai sai ya mayar da ita likita,shine yake ce mata Dr khairi"Auwab ya taɓe baki yana faɗin"shiririta!"

Sulaiman yace"kuma ba abin mamaki bane ku ga ta zama Dr ɗin,har ma tayi muku allura"surayya da Amra suka fashe da dariya a tare, Amra tana dariya tace "maji ma gani dai,amma yarinyar fa ko a ƙauyen ita ta musamman ce,ƴan gidan fa duk suna ɗan zuwa makaranta,amma ita sai aukin talla,bata zuwa makaranta,ita uwar neman kuɗi"Sulaiman yayi ɗan murmushi yana faɗin"ki godewa Allah kasancewar kina da iyayen ki a raye,don maraici da kike jin labarin shi babu irin halin da baya jefa mutum"

"Ban gane ba yaya Sulaiman"ya miƙe yana faɗin"ai bazaki gane ba,ammi good night"shima Auwab ya miƙe yayi wa ammie sallama suka fice daga parlourn


HOTORO GRA,KANO STATE, NIGERIA


Da sallama ya shiga cikin parlourn yana ƙarewa ko'ina kallo, tana danna wayar ta bata ko kalle shi ba take faɗin"sannu da zuwa abban Aman,ka dawo?"

"Na dawo,na same ku lafiya?"tayi ɗan murmushi ta kalle shi tace"lafiya lau,shigo ga abinci"ta nuna masa abincin da ta shirya akan dinning area ɗin nasu,ya kalli abincin sannan yace"sai nayi wanka tukunna"ya wuce riƙe da briefcase ɗin shi zuwa ɗakin shi

Bayan ya fito daga wankan sai da ya kira babyn shi sukayi hira sosai,shi kanshi yayi mamakin yadda ta sake dashi sosai saboda tunda suke tare bata taɓa sakewa dashi haka ba,bayan ya gama ya fito,still tana zaune tana danna wayar ta da takeyi tun kafin ya shiga

Ɗaga kai tayi tana kallon shi fuska a ɗaure tace"tun ɗazu nayi maka maganar abinci amma ka shige ɗakin ka kayi banza dani don wulaƙanci"

"Oh!na gaji ne shine na ɗan kwanta"bata sake masa magana ba ta cigaba da danna wayar ta,shi kuma ya nufi dinning area ɗin ya bubbuɗe abincin yana kallon shi

"Mun yi baƙi ne?"ya tambaye ta

"Me ka gani?"ta tambaya tana kallon shi

Ya ja kujera ya zauna yana faɗin"babu komai"itama ta ɗauke kai ta cigaba da game ɗin da takeyi a waya

Shima dai wayar ya ɗauko ya kama chatting da sabuwar babe ɗin tashi,batare da ya damu da taɓa abincin ba


LUGARD ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA

Yau ma tun da sassafe Beely ta saka khairi ta shirya,ko karyawa batayi ba Beely ta ɗauke ta a mota suka nufi gidan samha,ita tayi wa ɗan samha wanka,tayi masa abincin da zai tafi makaranta sannan suka ɗauke ta zuwa makarantar da samha ta bayar da shawara a kai ta

Ƙarfe biyu da rabi ta taso daga makarantar ta koma gidan samha kamar yadda Beely ta bata umarni,sai da ta fara shara sannan samha ta bata abinci,duk da Beely tace kar ta bata,amma yarinyar tana burge ta saboda bata da gandar aiki,kuma tana girmama ta, gata da tsafta,gashi bata ɗauki duniyar ta da zafi ba

Bayan la'asar Beely tazo ta ɗauke ta suka koma gida bayan sun gama shan hirar su,samha ta ƙara ɗora Beely akan mugayen shawarwari game da matar saurayin ta da tace yana da ita

Da yamma khairi tana zaune tana duba aikin ta na makaranta a balcony motar Auwab ƙirar Mercedes Gwagon ta shigo harabar gidan,kallo ɗaya tayi wa motar ta mayar da kai ta cigaba da abinda takeyi

Su kam basu kula da Ita ba ma sai da suka zo daf da ita,Sulaiman ya waro idanu yana faɗin"Dr khairi!kece?"ɗan murmushi tayi da yayi wa fuskar ta kyau,cikin sanyin murya tace"sannun ku da zuwa"

"Yauwa sannu,ƴan makaranta"ta ƙara yin murmushi ta gaida su,shi dai Auwab ɗauke kanshi yayi,tunda yayi wa wadda aka kira da Dr khairi kallo ɗaya bai sake ko da duban sashen da take ba

Sulaiman yayi ta jan ta da hira yana ɗan tsokanar ta,ita dai babu bakin magana sai murmushi kawai

Daga nan suka wuce cikin gidan,inda Beely take zaune ita da feena, kowacce tana danna waya

Sallamar su Sulaiman ta sanya su ɗago kai suna kallon su,da murmushi a fuskar su suka amsa gaisuwar tasu,duk da haushin ganin Sulaiman da Beely tayi,don ba wani shiri sukeyi na azo a gani ba,suka ƙaraso suka gaisa, Sulaiman ya dube su yace"kuyi mana iso wajen mum"babu musu feena ta kira mum a waya ta sanar mata zuwan su Sulaiman,cikin abinda bai fi mintuna biyar ba mum ta sauko daga sama, fuskar ta ƙawace da murmushi

"Yau kuma engineer ne a gidan namu,kai dama officer ai ɗan gida ne"Auwab yayi ɗan murmushi,suka gaishe ta cikin girmamawa,ta amsa da fara'a tana tambayar mutanen gidan,kafin tace a kawo musu ruwa da snacks

Sun ɗan juma suna hira kafin suyi wa mum sallama su tafi,har lokacin feena da Beely suna parlour suna danne dannen waya,ita kuma khairi tana balcony tana duba ɗan karatun da akayi musu

Har zasu wuce Sulaiman ya fasa,ya dawo yana tambayar ta"khairi wacce makaranta kike zuwa ne?"

Ta ɗago manyan idanun ta tana kallon shi tace"nima ban san sunan ta ba"

"To fa!wanne kalar kayan Makaranta ne?"ya tambaya don yaji intercontinental school take zuwa ko wata dabam

Khairi ta girgiza kai tace"ba'a zuwa da wasu kayan,da kayan gida ake zuwa"

"Da kayan gida ake zuwa ko kike zuwa?"ya sake tambayar ta

"Kowa ma kayan gida yake sakawa"amsar ta bashi mamaki sosai

Ya samu waje kusa da ita ya zauna, Auwab ya kalle shi Cikin fushi yana faɗin"malam idan baka da abinyi ni inada abinyi,kasan bani da lokacin jiran ka ko?"Sulaiman yace"sorry big bruh,wait a little"Auwab bai sake masa magana ba ya wuce parking space

Sulaiman ya kalli khairi da kulawa yace"yanzu ko kaya irin na makarantar ƙauyen ku ba'a sakawa?"khairi ta gyaɗa kai a sanyaye

Shiru Sulaiman yayi kafin yace"waye ya saka ki a makarantar?"

A hankali tace"anty Beely"daga nan Sulaiman ya gano inda matsalar take,ba tun yanzu ba yasan wacece Beely,ya girgiza kai yana murmushin mugunta sannan ya kalle ta yana faɗin"kin yarda gobe nazo na kai ki makarantar da ake saka mata kaya?"

Da sauri khairi ta gyaɗa kai tana murmushi, Sulaiman yace "to ina kuke bi idan zaku je makarantar?"a ɗan kwatancen da tayi masa ya gane wajen,don haka ya mike tsaye yana faɗin"to ki shirya zan zo na ɗauke ki gobe da safe kinji?"

Khairi ta gyaɗa kai a sanyaye tace"kazo da wuri kar Aunty Beely ta riga ka shiryawa mu fita"

"Kar ki damu,makarantar zan zo ai na ɗauke ki,nasan inda take ai"hakan ya faranta wa khairi rai sosai,Sulaiman ya ɗaga mata hannu ya tafi batare da ya saurari godiyar ta ba, zuciyar shi cike da tausayin ta

Washegari kam sam ko damuwa batayi ba lokacin da Beely ta saka ta shiryawa sukaje gidan samha,tayi mata ƴan ayyukan da zatayi mata sannan ta wuce makarantar su, lokacin ma tara ta wuce

Tana zuwa bakin ƙofar makarantar taga Sulaiman tsaye a jikin motar shi,ta kama murna sosai,ya ɗauke ta a motar suka ɗauki hanya

Sunyi tafiya mai nisa kafin ta tambaye shi"yaya makarantar da nisa ne?"

Ya kalle ta yace"kin san suna na kuwa?"tayi shiru tana zare idanu,yayi murmushi yace"ki ga fa,ko suna na baki sani ba,don nasan bakya ganin mutunci na"

Cikin sauri tace"Allah yaya ina ganin mutuncin ka,ai na san sunan ka mantawa nayi kawai"

"To shikenan,na yarda, makarantar da zan kai ki da nisa,kuma kwana akeyi ma acan, kina so?"

Ta kalle shi da fara'a tace"suna duka?"ya girgiza kai yace"basa duka,kuma zaki ci abinda kike so,ki samu ƙawaye irin waɗanda kike so,sannan kiyi karatu boko da islamiyya"

"Eh wallahi ina so,ina so!"ta faɗa tana murmushi sosai,har ɗan ƙaramin dimple ɗin ta yana bayyana

Sulaiman ya girgiza kai yana murmushi,a ranshi kuma tausayin yarinyar yake ji"ko da bata gaya masa ba yasan ba daɗin gidan dad takeji ba

Kai tsaye Queen's college ya nufa da ita,tayi mamakin ganin yaya Azad a bakin gate ɗin makarantar,fuskar nan kamar koyaushe a ɗinke,yana jingina da motar shi yana danna waya,Sulaiman ya fito daga motar yana faɗin"Allah ya taimaki babban yaya da kanshi,mun iso"

A nutse ya ɗan ɗago fararen idanun shi ya watsa musu sannan ya cigaba da Abinda yakeyi, Sulaiman ya buɗewa khairi ƙofa ta fito,a ɗarare ta gaida Azad, don mugun tsoron shi takeji

Ya amsa ciki ciki,ya kalli sulaiman cikin nutsuwar shi yace"yanzu kayan zasu iso,daga nan sai ka shiga kayi mata abinda ya dace,na gama biyan komai,zasu bata har uniform"yana kai wa nan ya faɗa mota,sannan ya kalli sulaiman ya cigaba"I have to leave Nigeria for Melbourne,don Ina da ayyuka sosai na katse na taho"

Sulaiman yace"safe trip babban yaya, Allah ya tsare"Azad bai amsa ba ya tayar yayi gaba

ALU EVENUE, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA

Babbar mace ce da aƙalla zata haura shekaru arba'in da biyar,fara ce tas, kyakykyawa,wadda hutu da jin daɗi ya ɓoye shekarun ta,hannun ta riƙe da tsadaddiyar waya ƙirar Samsung latest version tana dannawa

Ƙarar intercom ce ta katse ta,ta ɗago idanun ta tana kallon ƙofar tace"come in"

Shiga tayi cikin parlourn fuskar nan babu wadatar walwala,matar ta miƙe cikin farin ciki ta rungume ta tana faɗin"I miss You so much baby, sometimes sai na rinƙa tunanin ko dai na biyo ki naga lafiyar ki,i hope you are doing well"

Inaaya ta nemi waje ta zauna tana faɗin"everything is okay Mamie,but am tired,tun shekaranjiya nake Nigeria Ina samun matsalar jirgin da zai taho Kano,daddy yana gari?"


Kamar fa boarding school sulaiman ya kai khairi ba da sanin mum da Beely ba ko?to amma Azad ɗan lelen mum me yake yi acan🥺

#likecommentshare

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee

Page 13

Mamie ta girgiza kai tace "daddyn ki yau kwanan shi shida a China,baya gari"innaya ta yamutsa fuska tana faɗin"ya kwana biyu bai je ya kai min ziyara a Boston ba, I'm missing him so much"

"Don't bother yourself sweetheart!zai dawo very soon,yanzu dai shiga ki ɗan huta,kafin nan na samar miki favourite ɗin ki"a cewar Mamien Tata tana murmushi,Inaaya ma tayi murmushi tayi wa mamien tata side hug ta nufi part ɗin ta a cikin gidan

Bayan tayi wanka ta sanya ƴar riga da fara da wando da ya haure gwiwar ta kaɗan, light blue,ta ɗauko wayar ta ta soma kiran wanda ta sauka Nigeria don shi kaɗai

A lokacin Auwab yana kwance a parlour,gama wayar shi kenan da mr Anderson,yake sanar masa da dawowar shi nan da kwana biyu,yana ajiye wayar sai ga kiran Inaaya

Yadda ta bashi wayar ba saving shiyasa baiyi saving number ɗin ba,don haka ya bi wayar da kallo yana nazarin mai kiran,ganin bazai gane ba sai kawai ya ɗaga batare da yace komai ba

"Mr charming!I hope you are doing good"

Yatsina fuska yayi yana jan tsaki ciki ciki,yace"I'm good,how was your studies?"yatsina fuska tayi tace"guess what?"

"I'm not a good guesser,just tell me"

Inaaya tayi murmushi ta lumshe idanu tana sake kwanciya akan doguwar kujerar part ɗin ta tace

"Ina Nigeria fa"

"Really?"

"Yeah of course,kuma kasan me?"

"Aa sai kin faɗa"

"Don kai kawai nazo fa"

"Really?Ashe matsayi na ya kai haka?"

Tayi fari da idanu tace"ya wuce haka mr charming,yanzu dai yaushe zaka shigo Mu gaisa? tunda dai kaga a Boston nice nazo muka gaisa ko?"

"Yayi murmushi yace"very soon miss pretty!Amma ni jibi zan koma Boston"

"To please why not bazaka shigo gobe ba?"ta faɗa a ɗan shagwaɓe

Yayi ɗan murmushi yace"okay sai kin ganni goben"

Cikin matukar farin ciki tace"I'm waiting for my great visitor, I can't wait for that great visit!see you!"sukayi sallama, Inaaya kamar tayi ihu don farin ciki

QUEEN'S COLLEGE,KANO STATE, NIGERIA

"To Dr,Ni zan tafi"ta ɗaga idanu a hankali tana kallon shi,idanun ta suka ciko da ƙwalla, Sulaiman yayi ɗan murmushi yana girgiza kai yace"kuka zakiyi?kar kiyi kuka,ko kin manta nan ne mafarin da zai kai ki ga zama likita,watan watarana mutanen da suka cutar da ke a rayuwa da waɗanda kike ganin sunfi ƙarfin ki duka zasu dawo a ƙasan ƙafafun ki,ko bakya fatan hakan?"

Murmushi tayi sosai tace"ina so,na gode Yaya, Allah ya biya ka da aljanna"

"Ameen ƙanwar yaya,yanzu gaya min,ya suna na?"shiru tayi tayi ƙasa da idanun ta tana murmushi,don Maganar gaskiya bata sani ba,shima murmushin yayi yace"suna na Sulaiman, Sulaiman Usman Saeed"

"Yaya Sulaiman,haka zan ce ko?"ta faɗa tana murmushi tana kallon shi

Shima yayi murmushi yace"Yes haka suna na yake,haka zaki ce, Ummul khair!

Don Allah kiyi karatu sosai kinji?kin ga an kashe kuɗi sosai akan makarantar ki,kar kiyi wasa kinji?ki dage don ganin kin cika burin ki,wanda mu ma shine burin mu"ƙwalla ta ciko idanun ta tace"zanyi karatu mai yawa yaya Sulaiman,na gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya ƙara buɗi"

Yarinyar ta burge shi sosai,tayi rayuwar ƙunci da matsi da damuwa a rayuwar ta,ta rayu ba a gaban iyayen ta ba kuma babu tsayayyen mai tarbiyya amma a haka idan tayi wani abun ko mai tsayayyen iyaye bazai nuna mata hankali da sanin ya kamata ba

Ya ƙara yi mata sallama ya tafi,sai da ta share hawaye,wadda zata kai ta ta kai ta har ɗakin su,da kayan ta,babu abinda ba'a siya mata ba

Matar da ke kula dasu ta kai ta wani ɗaki da ƴan mata biyu ne a zaune ɗakin,dukan su basu wuce sa'annin ta ba,tana shiga ɗaya daga cikin su kyakykyawa ce sosai mai fata chaculate colour,ta ɗago tana kallon su,matar tace"Amra ga cikon ƴar ɗakin naku"

Wadda aka kira da Amra ta sake murmushi tana faɗin"thanks very much mummy!"Matar ta shigo mata da ƴan kayayyakin ta ta taya ta jerawa sannan ta fita

A kaikaice khairi ta ɗan kalli ɗaya yarinyar,fara ce tas amma bata kai Amra kyau ba,tana da ɗan jiki amma bata da tsawo sosai,sai dai tana da dogon gashi,ba kamar Amra ba,waya ce a hannun ta tana ta dannawa abin ta, gaba ɗaya hankalin ta ya tafi ga wayar

Bayan sun gama gyara komai Amra ta kalli khairi da murmushi tana faɗin"welcome sister! I hope Zaki ji daɗin makarantar mu"

Khairi tayi ɗan murmushin yaƙe,don duk wata kalmar turanci a maganar Amra Bata wani gane ba,Amra Bata kula ba tace"suna na Amra sadeeq,ita kuma wannan"ta nuna farar yarinyar ta cigaba "sunan ta "Nabila Saleh,mune roommates ɗin ki,dukkan mu a js 1 muke mu ma"

Ɗan murmushi tayi tace"Ni kuma suna na UMMUL KHAIRI ABUBAKAR ALBASU!amma da khairi ake kira na"

Amra tace"wow!what a nice name"Nabila ta kalle bayan ta ajiye wayar hannun ta tana murmushi tace"sunan late elder sister na kenan kenan,i love the name so much"

Ita dai khairi babu baki sai murmushi kawai

LUGARD ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE

Mum waccan baƙauyiyar wai har yanzu bata dawo ba?"

Mum ta ɗaga Kai tana kallon Beely,cikin yanayin mamaki tace"I can't get you Beely"

Beely ta yatsina fuska tace"bata gidan samha,tace tun safe da mukaje tare tayi mata aiki bata koma ba,shine ta kira ni take tambaya ta ko ta dawo?"

"What do you mean bilkisu?"a cewar mum cikin ɗaga murya, lokaci guda ta firgice

Wani kallo Beely tayi mata tace"mum bana jin faɗa zai bada mafita, I'm telling you yarinyar nan guduwa tayi,muyi shawarar yadda zamu ɓullowa lamarin"

"Kamar me kenan? bilkisu ina jin tsoron abinda zai je ya dawo muddin daddyn ku ya san yarinyar nan bata nan"

Beely ta girgiza kai tana fadin"zamu samo mafita mum,kinga,bari in Kira daddy"

Mum tayi hanzarin fizge wayar tana faɗin"baki da hankali ne Bilkisu?ki ce masa me kuma?"

"Ke dai barni ki gani,bani wayar,zuba min idanu kawai ki gani"babu musu mum ta miƙa mata wayar tayi dialing layin daddy

HOTORO GRA, KANO STATE, NIGERIA

Da sauri ya ƙaraso ya fizge wayar shi daga hannun ta yana mata kallon banza,alamun mamaki suka bayyana a fuskar ta,cikin tsiwa tace"wai Dr ban gane ba, kwanan nan ka koyi wata tsurfa ta yin kaffa kaffa da waya,anya akwai gaskiya a lamarin ka?"shi dai bai tanka mata ba,tunda ya amshi wayar shi ya fice ya bata waje

Biyo shi tayi tana faɗin"malam magana nakeyi maka don wulaƙanci kana ji na kayi min shiru,wanne kalar munafunci ne kuma ya bijiro da kullum kana maƙale da waya,anya akwai gaskiya a lamarin ka Salis?"

Sam bai wani damu ba,don idan rashin mutuncin ta ya tashi tana yi masa abinda yafi haka ma

Sam baya jin daɗin zama da samha,gata da raini,ga babu abinda ta iya a gidan,hatta abinda zata ci ma yawancin lokuta order takeyi,Bata iya komai ba sai zama tana danna waya,idan kuma ya ɗaukar mata ƴar aiki ta kore ta da masifar ta da bala'in ta,har ya gaji ya daina ma

Gata da matsanancin kishi da zargi,shiyasa da farko ma yake bar mata wayar shi tayi uban da zatayi daita,amma banda yanzu da Allah ya haɗa shi da wadda yake ganin zata share masa hawaye

ALU EVENUE, NASSARAWA GRA, KANO STATE

A yau tun safe take duba kayan da ya kamata ta saka,turaren da ya dace ta fesa,abincin da ya dace ta girkawa Auwab wanda ya tabbatar mata da zuwan shi yau,don gobe zai koma US,tuni ta daɗe da bazawa mamie labari, har da daddy da sukayi waya,mamie sai ƙara koɗa ta takeyi tana murmushi,dama ita fa bata san wata kalma wai ita bari ba,ko bakiyi daidai ba,abinda ta sani kawai shine kinyi daidai

Wajen ƙarfe biyar na yamma tana ta kici kicin ɗaura ɗan kwali ta kasa,tayi ta warware ta kuma yi ta ƙara warwarewa,don dai tayi alwashi shigar hausawa zatayi don ta burge Auwab,shiyasa ta tsuke cikin wasu matsatstsun riga da skirt na wani rantsatstsen lace,amma ɗaurin ɗan kwali yana ta bata wahala

Knocking taji a ƙofar ɗakin ta,ta ajiye ɗan kwalin hannun ta tana faɗin"Yes come in!"

Shigowa tayi tana ta murmushi,ta zubawa Inaaya idanu, Inaaya ma kallon ta take da mamaki, lokaci guda kuma ta kira sunan ta"SHUKRA!"

"Babe meye duniyar,shikenan kawai don kin tafi karatu sai ki guje mu,haka ma Lucy da Feedy sun ce bakya ko taɓa su ta WhatsApp, idan akayi miki magana ma bakya responding,anya kuwa babe?"

Inaaya tayi murmushi tana faɗin"team Bama karɓar uzuri kenan,but I think last week ma kafin shigo Nigeria na kira ki ko?"

"Yes kin kira ni,but i think Baki gaya min zaki dawo ba"

Inaaya tayi murmushi har da lumshe idanu tace"ba zuwan kaina bane,wani na biyo"

"What! Inaaya is in love!what a great surprise!!wanne Lucky man ɗin ne haka?

Inaaya tace"Auwab Abubakar Saeed kenan, we met with him in Boston,he is very handsome guy"

"Seriously babe!yau dai ga namiji ɗaya da ya tafi da iymanin ƙawa ta"Inaaya tayi murmushi tace"bari ke dai babe,sai ma kin ganshi,classy guy dashi"shukra tana murmushi tace"wish you all the best ƙawa ta,kice aure zakiyi ki bar mu"

Inaaya tayi fari da idanu tana faɗin"is my time shukra,kuma ku jira time ɗin ku,very soon in Sha Allah"shukra tayi ɗan murmushi tace"all the best ƙawa"

Inaaya ta miƙe tana faɗin"zo ki ɗaura min ɗan kwalin nan,tun ɗazu nake ta fama"babu musu shukra ta ɗaura mata ɗankwalin,ita kanta shukra sai da Inaaya ta burge ta, Shukra tana murmushi tace"har na hango yadda gwarzon naki zai susuce idan yayi arba dake,kin ci gasar kyau tun kafin ma ki shiga"

Inaaya ta juya idanu tana murmushi tace"dama kin san Ni mai kyau ce,shiyasa bana jin zan iya auren mutumin da bashi da kyau"

Ɗan murmushi shukra tayi tace"I see,yaushe zai iso?"

"Kowanne lokaci zai iya isowa"

Shukra ta miƙe riƙe da handbag ɗin ta tana faɗin"Ni dai yanzu zan tafi,see you next time"

"Shukra ki tsaya ku gaisa mana"

"No Inaaya,till other time"Bata jira amsar inaayan ba tayi waje


#likecommentshare

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️ Nusy bee

Page 14

LUGARD ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA

Shiru daddy yayi yana kallon Beely da ta kasa daina kuka,bayanan ta suna ta masa rotating akai,gaba ɗaya ya rasa me zaiyi ma kai tsaye,zuwa can yayi breaking silence yace"Bilkisu na kasa gane yadda Ummul khairi ta ɓata,bayan bata san kowa ba,bata san ko'ina ba a garin nan,ina zata je?"

Beely ta share hawayen fuskar ta tace"a can unguwar da makarantar tasu take akwai gidan ƙawa ta,to ina ce mata taje ta jira ni kafin naje na ɗauke ta,ina tsoro ko sace ta akayi a hanyar ta ta zuwa gidan"

"Ban fahimci bayanin ki ba Bilkisu,kamar yaya gidan ƙawar ki?

Sai a lokacin Beely ta fara inda inda,don kamar ta fara sauka layi,tace"um.....ah.... akwai gidan ƙawa ta a wajen makarantar"

Daddy yayi ɗan shiru,su Haidar da Ma'aruf da ke zaune a gefe suna kallon su dai sun san akwai wata a ƙasa,amma basu san abinda ya faru ba,daddy yace

"Shikenan! gobe zan je makarantar in bincika"

Da sauri tace"Daddy naje makaranatar sun ce jiya kwata-kwata bata je ba,babu ruwan su"

Daddy yace "dole na koma Bilkisu, hankali na bazai kwanta ba har sai na ga yarinyar nan,ko an gaya miki Ummul khairi ɗan kunne ne ko zobe da zasu ɓata a kasa bin diddigi?"

Mum tayi masa kallon rainin wayo tace"saboda ƴar gold ta ɓata dole ka rinƙa ƙoƙarin yiwa yarinya ta tsawa,daga abin arziƙi sai ya zama na tsiya?"

Cikin fusata ya kalle ta yana faɗin"kar ki sake saka min baki salma tunda ke har yanzu baki da hankali!tunda ba ƴar taki bace ta ɓata ai dole kice haka,da yake ita ƴar taki tafi ki hankali ai kinga ta nuna damuwa akan ɓatan ƴar uwar ta,to kar ki sake saka min baki,don wallahi zan iya ɗauke ki da mari"

"Mari?mari akan wannan baƙauyiyar?to wallahi da kuwa kayi danasani irin wadda ka juma bakayi ba!mhm!!

Wai ni Barrister zai mara akan ƴar ɗan uwan shi,ba shakka! Allah ya bada Sa'a!"shi dai Daddy Sai safa Marwa yakeyi cikin tashin hankali da tunanin ta inda zai fara neman khairi a daren nan,tun ɗazu da Beely ta kira shi ta shaida masa cewa ba'a ga khairi ba ya yanke abinda yake ya taho,yana zuwa kuma maimakon mum ta taimaka a nemo ta sai saka masa ciwon kai takeyi

Fita yayi compound ɗin,ya kira Sulaiman ya shaida masa matsalar da take faruwa,sosai Sulaiman ya tausaya masa,sai dai lokacin bayyana komai baiyi ba,don haka yayi masa alƙawarin zasu nemo ta

Kafin daddy ya koma gida dabara ta faɗowa Beely,ta kira samha ta shaida mata halin da ake ciki,samha tayi shiru kafin tace"ki kwantar da hankalin ki,akwai wata ƙawar yaya ta,tana da makaranta,kuma makaranatar tata tana da kyau babu laifi,kawai ki ce masa ba wadda yace kika kai ta ba saboda kinga ran mum ya ɓaci,wannan kika kai ta"

Da zumuɗi Beely tace"na gode fa samha,yaya sunan makarantar?"samha ta gaya mata, Beely tace"idan kina da contact ɗin ta ki tuntuɓe ta tun yanzu,zan bata daga million ɗaya abinda yayi ƙasa,Ni dai kawai ta amsa Makarantar ta nayi enrolling yarinyar"

"Ba case,ya sunan yarinyar?"

"Ummul khairi Abubakar Saeed"

"Okay!sai kin ji ni"sukayi sallama, zuciyar Beely fes

Basu daɗe da yin wayar ba daddy ya dawo,anan ta fara aiwatar da plan ɗin ta

Daddy yayi ta faɗa ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba,cikin kwantar da kai Beely tace"daddy saboda mum fa tace idan na kai ta future Leaders zata tsine min,shiyasa kawai na kai ta can"da sauri gaba ɗaya mutanen parlourn suka mayar da kallon su ga Beely da ta langwaɓar da kai tana matsar ƙwalla,ta ɗauke kanta daga kallon mum ma baki ɗaya,Ma'aruf ya miƙe ya fice daga parlourn,shima Haidar yabi bayan shi

Shima daddyn kallon mum yayi cike da takaici sannan ya girgiza kai ya ja tsaki ya fice,itama Beely tayi azamar shigewa ɗakin ta,don tasan mum zata iya yi mata magana

ALU EVENUE, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA

Kallon shi kawai takeyi tana murmushi,shima murmushin yakeyi yana kallon ta,ta ƙarasa kusa dashi ta zauna tana kallon shi

"You look like a queen sweetheart!"ya faɗa yana murmushi

Ji tayi kamar tayi ihun murna,ta juya idanu tana faɗin"kaima haka ai, definitely look like a King"yayi murmushi yana faɗin"ko?anyi surprising ɗina sosai jiyan nan fa"

Tace"ka wuce haka ai,yanzu dai fara taɓa wannan"ta buɗe masa abinci da snacks da ta saka akayi mata,har da juice

Da ƙyar ta lallaɓa shi suka ci tare suna hirar su ta soyayya,ba shi ya bar gidan ba sai bayan Isha'i,ya tafi suna cike da kewar juna,amma ta tabbatar masa cewa zata dawo Boston zuwa next week idan baban ta ya dawo

LUGARD ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA

Washegari daddy da Beely sun je makarantar Hajiya Atika,dukkan alamu sun nuna tabbas anyi enrolling khairi a makarantar,amma bata zo jiya ba,rabon su daita ma tun shekaranjiya

Hakan ya tayar da hankalin daddy ƙwarai da gaske,gaba ɗaya laifin mum yake gani,yanzu haka ma saboda ƙiyayyar mum ɗin tayi wani wajen bata koma gida ba,shi kam bai san me zai gayawa ƴan uwan shi da suka damƙa masa amanar ta ba

Bai sake magana ba ya fice daga office ɗin ya nufi mota, Beely ma ta bi bayan shi tana ƙoƙarin turawa Hajiya Atika kuɗin da tayi mata alƙawari

Kwana biyu da faruwar hakan babu wani labari, Beely ta samu daddy a zaune a parlour tare da mum,ta gaishe shi ta nemi waje ta zauna

Ya kalle ta a nutse yana faɗin"ya dai Bilkisu?me ya faru?"

Cikin kwantar da murya Beely tace"daddy dama....iyayen manemi na ne suka ce zasu turo"

Wani kallo yayi mata yana faɗin"yanzu ne lokacin da ya dace ki same ni da batun wai manemin ki zai turo don baki da hankali?kin manta halin da ake ciki ne?"

Tace"daddy gani nayi shi abin bai shafe shi bane, shiyasa na......"

"Zaki tashi ki bani waje ko sai nayi ball dake? stupid girlkawai!"ya daka mata tsawa har sai da ta zabura

A firgice ta tashi ta bar wajen,mum tayi wa dad wani mugun kallo tace"saboda ƴar yayan ka ta gudu sai rayuwar yara na ta tsaya?wato dama ka kawo ta ne don ka tsayar da rayuwar yara na?to wallahi bazata yiwu ba,kuma magabatan manemin Bilkisu kamar sun zo sun gama ne

Naga lokacin da batayi auren ba har da mahaifiyar ka ake zagin ta da rashin auren anayi mata habaici da shaguɓe,tsabar son zuciya sun manta........"bata kai ƙarshe ba daddy ya ɗauke ta da mari yana huci

Miƙewa tayi tsaye idanunta suna rinewa da masifa ta kalli daddy tace"Umar Ni ka mara saboda ƴar ƙauye?"

"Na mare ki Salma!gobe sai ki sake yiwa mahaifiya ta shaguɓe ko ki gaya mata magana,kin wulaƙanta min ƴan uwa saboda son zuciyar ki,to in sha Allahu yarinyar da kike kira da ƴar ƙauye zata dawo gidan nan ta zauna,kuma watan watarana tafi yaran da kike gani sun fi kowa a duniya amfani"

"Wallahi tun da ka mare ni baka ga komai ba,sai kayi nadamar taɓa lafiya ta akan ƴar ƙauye,jahila bagidajiya, wallahi sai kayi nadamar abinda kayi,kuma batun aure za'a saka,ai ba kai kaɗai bane mutum da za'a kasa sakawa ko babu kai"ta faɗa cikin ɗaga murya kafin ta ja tsaki ta shige ɗakin ta

Shi dai ko kallon ta bai sake ba,daga baya ma ya fice daga gidan baki ɗaya, zuciyar shi har wani huci takeyi sai ɓacin rai

A ranar mum tayiwa ƙanin ta Nafi'u magana,da wasu yayyen ta su biyu Alhaji bilya da Alhaji adam, washegari family ɗin manemin Beely sukazo akayi baiko,aka saka rana wata biyu

Dama daddy tun sassafe yayi tafiyar shi Abuja ko sallama baiyiwa mum ba da ta ɗau gaba dashi,don haka shi bai san da batun saka ranar ba ma

Da matuƙar farin ciki Beely ta kira aminiyar ta samha ta shaida mata,samha sai ihun murna takeyi tana ƙara bata shawarwari,sun ɗan daɗe suna hira kafin su yi sallama, Beely sai murmushi takeyi, zuciyar ta ƙal


Gwara kiyi auren ki ƙyale mutane,ko a huta da jarabar ki😣

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

✍️ Nusy bee

Page 15

HAƊEJIA ROAD, KANO STATE, NIGERIA

"Wai me yake faruwa a gidan Barrister ne?me ya same shi haka ya ajiye aiki ya dawo Kano?"

Sulaiman ya kalli mahaifin shi lieutenant general Usman Saeed da yayi masa tambayar, da mahaifiyar shi Hajiya Raheena da suka zubo masa idanu suna jiran amsar tambayar mahaifin nashi,yayi murmushi yace"babu komai Abba,ƴar matsala aka samu,amma zata wuce in Sha Allah"

"Ban bane me kake faɗa ba Sulaiman! Umar yana cikin damuwa,na kira shi several times baya ɗaga min waya,kuma ni bai saba yi min haka ba wallahi"a cewar mahaifin nashi da ƴar damuwa a muryar shi

Sulaiman yayi ɗan murmushi yace"to Abba,let me tell you since you insisted"daga nan ya bashi labarin hatsaniyar da akayi akan kai khairi makaranta,da yadda Beely ta munafurci mahaifin nata,da yadda ya sani har ya chanja mata Makaranta zuwa boarding school a dalilin Azad

Shiru Abba yayi yana kallon Sulaiman,ya kasa cewa komai,Hajiya Raheena ma abin ya bata mamaki sosai,sai kallon Sulaiman takeyi,zuwa can tace"gaskiya dai wannan yarinya abar tausayi ce,me zai hana ka dawo da ita nan?"da sauri Abba ya girgiza kai yace"alƙawarin Umar ne zai riƙe ta, mace bazata saka shi karya alƙawari ba,ni kuma alƙawari na ne zan aurar da ita,ina fatan Allah ya bani iko"cikin sanyin jiki Hajiya Raheena ta amsa da"ameen"

QUEEN'S COLLEGE, KANO STATE, NIGERIA

Khairi ce zaune da littafi a gaban ta tana karantawa,Nabeela a gefen ta tana gyara mata kura kuran ta,ita kuma Amra tana daga gefe tana yankan farce,sati biyu kenan da kawo ta makaranta,tuni ta sanar wa collegues ɗin nata cewa ita batayi boko ba,don haka suka tsaya sosai suna koya mata abubuwa da yawa,da yake ta saka naci sai gashi tana ɗauke wa,bata da nauyin bakin tambayar abu idan bata gane ba,bata da gandar zuwa wajen kowaye yace zaiyi mata karatu daga na boko har na addini,don haka a sati biyun nan ba ƙaramin ƙoƙarin karatu tayi ba

Rufe littafin tayi tana gyara zama tana faɗin"wash Allah na!na gaji wallahi"Amra ta kalle ta tana murmushi tace"to kece safe karatu,rana karatu,dare karatu kamar al huda huda"khairi ta girgiza kai cikin sanyin murya tace"bazaki gane bane Amra"ta ɗago tana kallon ta tace"karatu yana iya zama gatan kowa,yana iya zama silar da mutum zai fi ƙarfin abinda yafi ƙarfin shi,yana sakawa wanda ya raina ka ya girmama ka,rashin karatu kuma yana saka akasin duk abinda na lissafa,naga misalai da yawa a rayuwa ta

Shiyasa nake so nayi karatu, saboda shi zai zame min gata,watan watarana ma shi zai zama fitila ta a rayuwa, shiyasa zan ƙarar da duka ƙarfi na a karatu"

Nabeela tace"ni duk ban wani fahimci me kike nufi ba wallahi"Amra tace"Ashe dai muna ɗaya dake Beela,nima ban gane komai ba wallahi"khairi tayi ƴar dariya tace"zaku gane nan ba da daɗewa ba, Amra haɗa min corn flakes ɗin"

Amra tayi dariya tace"nasan yaya Sulaiman idan zai zo visiting za'a ce masa ya taho da carton goma na corn flakes da carton biyar na chaculate"khairi tayi murmushi batare da tace komai ba, Amra ta haɗa mata corn flakes ɗin

Karatun su ya miƙa sosai,a ɗan lokaci khairi ta iya abubuwa da yawa,suma saboda wanzuwar khairin a cikin su sun sake mayar da hankali fiye da baya,zuwa yanzu khairi tana jin turanci sama sama,mayarwar ce dai bata iya ba tukunna,sai kananan abubuwa

BOSTON, MASSACHUSETTS,USA

Da mamaki yake bin Inaaya da ta ƙarasa shigowa tana murmushi da kallo,kamar kullum yau ma sanye take da riga da wando ta ɗora rigar sanyi akai,wandon baƙi ne,rigar kuma peach colour,ta ɗora rigar sanyi peach colour,da hular sanyi baƙa

Zama tayi tana murmushi,ta zame hular kanta,gashin ta ya zuba gadon bayan ta,ta kalle shi tana faɗin"good morning sweetheart!"

"Morning princess!you are welcome,yaushe kika dawo?"tace "jiya da daddare jirgin mu ya sauka,yau kam na kasa haƙura sai nazo na ganka"

Shima murmushin yayi yana faɗin"ya kika bar su Mamie?"ta juya idanu tana faɗin"dukan su lafiyar su lau,sun ce a gaishe ka"ya waro idanu yana faɗin"really?kice sun san da zama na"tace"ai suma sun san idan Ina son abu bana wasa dashi"

Auwab yana murmushi yace"Weldone sweetheart!"

Sun ɗan juma suna hira kafin Inaaya tayi masa tayin zuwa shan ice cream,bai mata musu ba suka jero suka fito suna tafiya suna hira cike da nishaɗi da shaukin son juna

HOTORO GRA, KANO STATE, NIGERIA

Wai abban Aman menene matsalar ka ne?kwana biyu baka da lokaci,dama ka saba ficewa da sassafe,amma ai baka saba dawo min very late at night ba,ko dai neman mata ka fara ne bani da labari?"

Ya juya ya kalle ta yadda take ta girgiza cike da tsiwa da masifa,ya ɗauke kanshi yana cigaba da murza mai a jikin shi

Samha ta ƙara ƙuluwa ta cika tayi fam,cikin masifa ta cigaba

"Wallahi kayi asara kuwa!anyi girman hotiho,fasiƙanci?bakayi a ƙuruciya ba sai Yanzu da girma yazo ka ajiye zuri'a? Allah wadaran naka ya lalace,yanzu don Allah da me na rage ka da har ka ga wata ka ke bin ta a waje fisabilillahi?"

Ko kallon ta baiyi ba yace"samha don Allah ki fita ki bani waje,ko me kike zargi kin daɗe baki yi ba,ki fita na sarara"

"Bazan fita ba sai ka bani amsa ta,ina kake zuwa kakeyin dare?"

Tashi yayi tsaye ya kalle ta fuska a ɗaure yace "zance nake zuwa saboda aure zan kara very soon, yanzu kin ji daɗi?now fice min daga ɗaki!"

"Banji me kace ba Salis,ɗan maimaita min banji ba"ta faɗa tana ƙanƙance idanu,bai sake mata magana ba ya janyo hannun ta da karfin tsiya ya hankaɗa ta bakin ƙofar ya kulle ƙofar,tana ta ihu tana auna masa zagi da cin mutunci,wai yaci amanar ta

Tana kuka ta wuce ɗakin ta ta ɗauki wayar ta ta kira mahaifiyar ta tana kuka ta gaya mata wai abban Aman yace mata zai ƙara aure,hankali kwance mahaifiyar tata tace"to sai me?ko kuma ni kaɗai ce a wajen ubanki?ko shi uban naki yafi kowa da zai ƙara aure babu mai ɗaga masa hankali sai mijin ki?to bana son sakarci"samha tana kame kamen sake magana mahaifiyar tata ta yanke wayar

Zaman dirshan tayi a tsakar ɗakin tana ta rizgar kuka da tunanin mafita,daga baya ta kira Beely cikin kuka take gaya mata

Beely tayi shiru cike da mamaki,wai duk soyayyar da samha takeyiwa Salis amma zai yi mata kishiya,bata mantawa sanda suna makaranta secondary school magana ɗaya biyu sai samha ta sako Salis,amma yanzu wai zaiyi mata kishiya,a hankali Beely tace"gaskiya dai Salis ya ci amana,ki bari in Sha Allah ko ta shigo da ƙafar ta zata gudu,don wallahi sai mun nuna mata mu ba irin matan da akeyiwa kishiya bane"

"To me kike ganin zamuyi?"

"Idan ta kama har taimakon malamai mu nema, ba'a bori da sanyin jiki"

Cikin sanyin jiki samha tace"to shikenan"

Beely tace"yauwa!kar ki sake nuna damuwar ki,ki nuna masa baki damu ba,ki ƙara yi masa biyayya da kulawa,shine zaki samu kanshi a hannu, idan matar ta shigo mu kaɗa ta ta ruwan sanyi"samha tayi murmushin jin daɗi tace"sai dake aminiya,see you!"sukayi sallama, Samha tana jin sanyi a ranta

QUEEN'S COLLEGE, KANO STATE, NIGERIA

Yau ne ranar da aka ware don visting a makarantar,ita dai khairi tayi shiru tana bin su Amra da kallo, waɗanda suke ta murna saboda zuwan da ƴan gidan su zasuyi yau,ita dai bazata ce bata murna ba kuma bazata ce tana yi ba,don bata san wanda zai zo mata ba

Nabeela Saleh aka fara zuwa aka kira cewa ƴan gidan su sun zo,da sauri ta fice a guje cike da farin ciki,babu daɗewa aka kira Amra,itama ta fice a guje cike da farin ciki,ita dai khairi ta kwanta akan gadon ta ta lumshe idanun ta, hawaye suka zubo mata saboda kewar ƴan uwa da ta kama ta

Ta san sulaiman ma'aikaci ne,na koyaushe yake available ba,bayan shi bata tunanin akwai wanda yake kallon ta da muhimmanci har tayi tunanin zai zo mata visit

Nabeela ce ta dawo ɗakin a guje, khairi ta buɗe idanun ta da sauri,kafin ta kai ga magana itama Amra ta shigo a guje,kusan a tare suka ce"khair albasu kizo ku gaisa da ƴan uwana"kasancewar yanzu sunan da suke gaya mata kenan

Kallon su tayi kawai bata ce komai ba, Amra tace"ki fara zuwa mu gaisa da Abba na da yaya na da momy na tukunna"Nabeela tace"ki fara zuwa dai mu gaisa da Abba na da sister fadwa tukunna"daga nan suka kama jayayya tana kallon su

Ƴar dariya tayi tace"muje,muje duka, waɗanda muka fara haɗuwa dasu sai mu gaisa dasu"babu musu suka fice su uku suna hirar su da raha

A ɓangaren ƴan gidan su Amra suka fara yada zango, Nabeela da khairi suka gaida iyayen Amra da yayan ta,mutanen kirki masu fara'a sai tsokanar su sukeyi,da zasu tafi abban su Amra ya basu kuɗi yace su ƙara,suka ƙi karɓa,yace"ku ba yara na bane?ko idan na bawa Amra bazata karɓa ba? ku karɓa kunji?"suka karɓa cikin girmamawa suna godiya,daga nan suka wuce wajen relatives ɗin Nabeela

Mahaifin ta ne sai ƙanwar ta fadwa,dama mahaifiyar su ta rasu shekaru biyu baya,suka rungume juna ita da fadwa,daga baya fadwa ta gaida su khairi tana murmushi,suma suka gaida daddyn ta,ya amsa cikin fara'a,cikin shagwaɓa Nabeela tace"daddy yanzu yaya Hisham bai zo ba?"daddy yace"cool down daughter!shi Hisham ɗin ne zai katse karatun shi yazo miki?"

Nabeela tace"no Daddy, I am missing him ne,rabon da na ganshi it past a year"

Daddy yace"don't worry daughter,Hisham zai dawo very soon,me kika tanadar masa?"

Nabeela tana murmushi tace"delicious dishes,sai wanda ya zaɓa"daddy yayi ƴar dariya yace"to shikenan, Allah ya dawo dashi lafiya, I will ask him yazo ya kawo miki ziyara,shi matsalar shi shigowa Kano ne,amma last two weeks yazo ƙasar nan ya sauka a gida,wai yazo ɗaurin auren abokin shi a Zaria"

Nabeela ta ɓata fuska,har da diddira ƙafa wai yaya Hisham ya daina sonta,daddy yana lallashin ta amma Amra da khairi da fadwa suna ta mata dariya

Shi kam bayan kuɗi ya kawo musu abubuwa da yawa, Nabeela ta ɗauki kwalin corn flakes tana dariya ta miƙawa khairi tace"daddy ni na sadaukar da corn flakes ɗina ga masoyiyar shi,gata nan"kunya ta kama khairi,Amra da Nabeela suka yi ta mata dariya

Alhaji Saleh bai juma ba yayi musu sallama ya tafi,suka koma wajen iyayen Amra,suma basu daɗe ba sosai sukayi musu sallama bayan sunyi musu nasiha suka tafi

Su khairi basu juma da komawa ɗaki ba, suna zaune suna dudduba kayan da aka basu suna shewar su mai kula dasu ta leƙo tana faɗin

"Ummul khairi Abubakar albasu,anzo miki"shiru khairi tayi tana mamakin wanda yazo mata,Amra tace"kije ki gani ko yaya Sulaiman ne"babu musu ta fita tana addu'ar Allah yasa shine

Daga nesa tana hango shi ta gane shi,ta kwasa da gudu tana murna,tana zuwa tace"good morning Yaya Sulaiman"

Sulaiman ya zaro idanu yana murmushi yace"is it you Dr khairi?"

Gyaɗa kai tayi tana murmushi,yace"morning dear,how was your studies?"

Tace"alhamdulillah,ya Mutanen gidan?"yayi ƴar dariya yace"turanci ya ƙare kenan likita bokan turai"tana murmushi tace"ai dama kaɗan nakeji,amma idan naji da yawa zanyi maka"yace"still kinyi ƙoƙari ai, Allah ya nuna mana lokacin da zaki ji da yawa ɗin"tace "yaya Sulaiman bari na kira friends ɗina ku gaisa"kafin ya sake magana ta kwasa a guje ta koma cikin makarantar, shi sai ta bashi dariya ma,ya kalli Azad da ya tabbatar bata kula dashi ba ma yace"kaga ƙanwar taka fa,yanzu ta sake sosai"batare da ya kalli sulaiman ba yace"good for her"

Su uku suka ƙaraso wajen, Nabeela ce ta fara faɗin"You are welcome Yaya Sulaiman"ya kalle ta yana murmushi yace"thank you our friend"Nabeela ma tayi masa sannu da zuwa,daga nan suka gaishe shi

Ya amsa sannan yace"meet my brother Saeed Umar Saeed known as Azad"sai a lokacin khairi ta kula dashi,suka gaishe shi kusan a tare,ya amsa batare da ya kalle su ba,bai ma ɗago kai daga wayar da yake dannawa ba"Sulaiman ne ya biye musu sukayi ta hira kafin ya fito mata kayan da siya mata,suka kwasa suka shiga dashi, sannan ta dawo don yi masa sallama

Ya kalle ta da kulawa yana faɗin"kin bani mamaki sosai khairi,ban taɓa tsammanin zakiyi kwazo har haka ba,ki cigaba da dagewa kinji,in Sha Allah zakiyi dariya watarana"ƙwalla ta ciko idanun ta tace"bani da bakin gode maka yaya Sulaiman,babu abinda zan ce sai Allah ya biya ku da alkhairi, Allah ya kula da naku kamar yadda kuka kula dani,kun cika min buri na,na gode"

Sulaiman ya girgiza kai yace "kar kiyi kuka khairi,yanzu ga wannan"ya miƙa mata kwalin waya,yace"ƙawayen ki su taya ki buɗe WhatsApp,zamu rinƙa gaisawa,amma da turanci idan kin yarda"khairi tayi ƴar dariya tace"na yarda ma"


Khairiri an fara iya turanci 😁


#likecommentshare


#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

✍️Nusy bee

Page 16

Yace"yauwa!yanzu kiyiwa yayanki sallama zamu tafi"ta kalli Azad da har yanzu bai ɗago kai yayi mata kyakkyawan kallo ba,ta kumbura fuska ta kau da kai gefe tace"shima ai baya yiwa mutane magana,sai yayi ta cukulewa"Azad ya ɗan ɗago ya galla mata harara ya cigaba da abinda yake, Sulaiman ya kama dariya sosai,ita dama tuntuni haushi yake bata, saboda baya fara'a,ga wulaƙanci da masifa,bugu da ƙari kallon ɗan iska ma takeyi masa, saboda bata taɓa ganin shi da manyan kaya ba,ga askin kanshi baya taɓa na arziƙi

Sulaiman ya kalli Azad yana dariya yace"to kai kaji,Sarkin cukulewa,baka kyautawa,sai ka gyara"Azad ya miƙe tsaye,da sauri khairi ta matsa baya tana kumbura fuska,ya harare ta ya kalli Sulaiman yace"ka cigaba da biye mata tana shiririta!"ya kalle ta yana sake tamke fuska yace"ya rage naki ki cigaba da karatu ko ki kama shiririta,kinga dai rayuwar ta zama dole sai da karatu, don wannan Dr ɗin da ake ƙaƙaba miki kina washe baki kamar shashasha baki isa ki zama hakan ba sai kinyi karatu"ya ciro kuɗi ya miƙa mata yana faɗin"akwai number na da ta Sulaiman duka a cikin wayar,idan kina buƙatar abu let me or Sulaiman know,kar ki kuskura ki roƙi wani,idan kika aikata hakan na samu labari kuma ranki zai ɓaci"cikin sanyin jiki ta amshi kuɗin tana faɗin"na gode Yaya, Allah ya saka da alkhairi"bai amsa ba ya kalli Sulaiman yana faɗin"officer let's go, it's getting late"babu musu Sulaiman ya ƙara yi mata sallama,suka shiga mota Azad ya tayar suka tafi

A sanyaye ta koma ɗakin, Nabeela ta kalle ta da murmushi tace"your brothers are very handsome,sun ma fiki kyau"khairi ta zauna tana murmushi batare da tace komai ba, Nabeela tace"wai waye yaya Sulaiman ɗin a cikin su?"

Khairi cikin sanyin murya tace"wanda yafi kirkin"

"Awwwn!ni kuma kinga ɗayan yafi burge ni, I like classic guys,shi ya sunan shi?"a cewar Nabeela tana murmushi,itama Amra kallon su take tana murmushi tana jiran amsar khairi

Khairi ta kalle ta tace"kamar ba'a gaban ki yaya Sulaiman yace sunan shi Azad ba"

Amra tana murmushi tace"wow! Azad!sunan shi ya dace dashi"khairi ta taɓe baki tace"ai sunan shi na gaskiya Sa'idu"dukkan su suka fashe da dariya, Nabeela tana dariya tace"menene kuma Sa'idu? Sa'idu ai baƙauye kenan,his name is Saeed, classic guy kamar wannan ai ya wuce ace masa Sa'idu"khairi ta kalle ta tace"mu kenan,kinga ni baƙauyiya ce,kuma I'm proud of that,a ƙauye aka haife ni anan na tashi kuma acan na rayu"dukkan su ta basu tausayi sosai, Nabeela ta dafa kafaɗar ta tana faɗin"ke haihuwar ƙauye ce kawai,amma ba baƙauyiya ba,ƙauye location ne,ƙauyanci shine ɗabi'a,ke kuma ba baƙauyiya bace,kuma ko a yaya kike mu dai muna son ki"murmushi khairi tayi batare da ta sake magana ba,suka miƙe suka fara jera kayayyakin da aka kawo musu yau

LUGARD ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA

"Azad nayi maka magana amma ka mayar da magana ta abin banza,wai Azad menene matsalar ka ne?"

Kallon ta yayi fuskar nan babu fara'a yace"mum what is the problem?me kuma nayi daga dawowa ta?"

Sauke murya tayi tace"amma na gaya maka kaje ku gana kai da ƴar ƙawa ta Hajiya A'isha amma banga alamun zaka je ba,wai meyasa a yara na kana neman kafi kowa bani ciwon kai ne?meyasa kake son ka sauya?"Azad ya runtse idanu cike da takaici ya buɗe sannan yace "I'm sorry mum,zan je in Sha Allah"

"When?"ta faɗa tana tsatstsare shi da idanu

"Today in Sha Allah"ya Bata amsa

Tuni murmushi ya washe mata a fuska,tace"Weldone son! Allah yayi maka albarka,idan ka tashi tafiya sai ka gaya min,zan baka saƙo ka kaiwa Hajiya A'ishan"batare da yayi magana ba ya gyaɗa kai

Bayan maghriba ya tafi gidan Hajiya A'isha dake badawa layout,har ciki akayi masa iso, Hajiya A'isha ta sauko da fara'a tana faɗin"maraba lale da mutan turai,yau a gari?"ya ɗago a hankali,cikin girmamawa ya gaishe ta,ta amsa da matuƙar farin ciki,cikin girmamawa ya bata saƙon mum ɗin shi, tana murmushi tace "Hajiya Salma ba dai hidima ba, to an gode"sannan ta miƙe tana faɗin"bari a turo maka Fadilan ko?"bata jira amsar shi ba tuni ta shige

Jinginar da kanshi yayi ya lumshe idanun shi yana nazari,kafin wani fitinannen ƙamshi ya baƙunci hancin shi

Buɗe idanu yayi da sauri yana kallon matashiyar budurwar da ta shigo masa babu sallama,a ƙalla zata kai sa'ar Beely,27-28,fara ce ƙal har wani jaja-jaja takeyi,da alamu farin mai yafi yawa,sanye take da wasu riga da skirt na atamfa da suka bi shape ɗinta suka kama ta tsam,ƙirjin rigar ta ya ɗan yi ƙasa,haka ya bawa na shanun ta damar leƙowa ta zaman rigar,kitson attachment da akayi mata ya sauka har ƙugun ta,ɗan figigin mayafin da ta ɗauko ta saƙale shi a kafaɗar ta ɗaya,hannayen ta zane da lalle ja da baƙi

A ƴan sakwanni ya ƙare mata kallo ya ɗauke kai, maganar mum ta faɗo masa a rai,wai yazo su gana da matar da tayi masa,shi bai ga mata anan wajen ba,amma yasan halin mum ɗin shi dole ya karɓa,tunanin shi ya katse a lokacin da ta zauna kusa dashi tana faɗin"sannu da zuwa yayana kuma miji na"cikin karairaya da kwainane irin na mata masu buɗaɗɗen idanu take maganar

Kallon ta ya ɗan yi ya ɗauke kai,cikin karairaya tace"me zan zuba maka? abinci ko snacks?"da sauri yace"No I'm okay,thanks"

Cikin shagwaɓa ta fara faɗin"kawai nayi wahala nayi girki kace baka so,ni dai uhm uhm uhmmmm!"ta faɗo jikin shi,cikin dabara ta fara shafa masa kirji

Shi abin ma dariya ya bashi,ya miƙe tsam yana kallon ta yace"thanks,see you next time"bai jira cewar ta ba ya fice daga parlourn

Fadila ta bishi da kallon takaici,zuwa can ta ja tsaki tana faɗin"kai ka sani! A haka kamar wayayye,ashe bagidaje ne"

BOSTON, MASSACHUSETTS,USA

Yau tsawon kwanaki uku kenan da Inaaya taki tafiya gidan ta,kullum a gidan Auwab take kwana,sai dai a ɗakuna dabam dabam,bai taɓa nuna mata wani abu ba,itama haka,sukanyi ayyukan gida tare,su fita tare,ita ta nufi makaranta shi kuma Company,su sha coffee tare su sha ice cream tare,hakan ya ƙara musu shaƙuwa mai ƙarfi

Fitowar ta kenan daga lecture mahaifin ta ya Kira ta ya shaida mata gashi nan a airport,yanzu zai ƙaraso idan tana gida,dole tayiwa Auwab waya ta shaida masa zata wuce gida mahaifin ta yazo,shima idan da hali yazo su gaisa,baiyi musu ba yace to shikenan

A ranar Auwab da mahaifin Inaaya suka haɗu, Alhaji mukhtar yaji daɗin ganin Auwab sosai,ya sanar dashi idan da gaske yana son Inaaya ya sanar da iyayen shi,idan yaso sai su gana da juna

HOTORO GRA, KANO STATE, NIGERIA

"Yanzu da me da me kika shirya mana na auren?"

Beely tayi fari da idanu tace"akwai events guda uku da zanyi,kowanne da ankon shi"

Samha tace"Allah ya nuna mana,amma banda ankon yini babu ankon da kika tura min naga irin shi"

"Dalla ke matsalar ki kenan gajen haƙuri,ke da za'a kawo miki very soon?"samha na dariya tace"to ai har yanzu banga angon namu ba,ko dai rowar ganin shi akeyi mana?"

Beely ta galla mata harara tace"har akwai wadda ta kai ki iya ɓoyon miji?almost four years da auren ki amma har yanzu ban san kalar mijin ki ba,sai ni zan bari a san nawa tun kafin auren?"

Samha tayi dariya ta dafa kafaɗar ta tace"easy Madam,ni fa tsokanar ki nakeyi"taci serious face tace"Amma maganar soyayya da kishin miji na yanzu na fara,ni fa ko hoton shi bana bari a inda nasan mata zasu kalla,ina da hotunan shi a waya ta amma bana barin su a inda za'a gani,ina ƙaunar miji na sosai"


A cigaba da ƙaunar miji Samha 😅idan mata basu ganshi ba ai shi zai gansu


#likecommentshare

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

✍️Nusy bee


Yau dai na samu nayi biyu in sha Allah, saboda yadda jama'a da yawa suke ta review akan yadda lamari zai kasance, musamman tsakanin Beely da Samha


Page 17


Beely tayi murmushi tace"all the best friend, ina bayan ki, musamman wannan lokacin da snatching yayi yawa,yanzu ni bani da hoton shi ma, kin san da farko ban wani ɗauki abin da muhimmanci ba,amma in sha Allah zan tura miki hotunan pre wedding pics da zamuyi very soon"murmushi samha tayi tana faɗin"Allah ya sanya alkhairi ƙawa,kema dai zaki shigo ki ji yadda muke ji"Beely tace"ke dai bari kawai,ina Aman ne?"

Samha ta kyaɓe baki tace"yana gidan kakannin shi wai a can zai yi week end"

Beely ta kyaɓe Baki tace"lallai kam, Allah ya kyauta to,amma da nice ke wallahi bazan bar shi ya je ba,tunda abin zalunci ne"

"Mhm ke dai bari kawai Beely,last week fa da na shiga taron su sai yada min haibaici akeyi Wai yanzu Salis zai san yayi aure"

Beely tace"ko kuma yanzu zasu gane su ƙananan ƴan iska ne ba, Allah ya kai mu,zasu sha mamaki"sun ɗan juma suna hirar kafin Beely tayiwa samha sallama, Samha ta rako ta har bakin motar ta suna ta hirar su


LUGARD ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA

"Jiya baka gaya min yadda kukayi da yarinyar nan ba fa"

Yana danna wayar shi yace"mum duk yadda kika yanke ni yayi min,indai kinga yarinyar ta dace da rayuwa ta to babu wata matsala"

Murmushi mum tayi tana faɗin"babu matsala, za'a san yadda za'ayi a haɗe auren naku da nasu Beely,ko akwai abinda zakayi?"

"No mum,kawai dai akwai hanzari ɗaya"

"Wanne hanzarin kenan?"

"Ina da wadda nake so ne nima,don haka zan iya aurenta nan da wani lokaci,sai ku sanar mata,kar ta ga kamar ban kyauta mata ba"

"Azad wacece?kuma ƴar waye?menene dalilin da yasa baka gabatar mana daita ba?"a cewar mum cikin farin ciki,don tana son ganin farin cikin ɗan ta,murmushi yayi yace"kar ki damu mum,zan gabatar da ita very soon,yanzu karatu takeyi,iyayen ta bazasu aurar da ita ba sai ta gama"

"Ji wani shirme don Allah, maimakon su aurar maka da ita idan yaso sai ta ƙarasa a gidan ka?wallahi da ko ni sai na ɗauki nauyin karatun nata"Azad dai kallon ta yakeyi har ta gama kafin ya fara ƴar dariya,mum ta ɗan bishi da kallo kafin tace"wannan shashancin fa?meye na dariyar kuma?"yana murmushi ya girgiza kai yace"babu komai,yaushe feena da Nusra zasu dawo daga Yola?"

"Sai dab da biki gaskiya,saboda ko jiya munyi waya da feena tace ba yanzu ba"

"To Allah ya dawo dasu lafiya"

"Ameen son"


HAƊEJIA ROAD, KANO STATE, NIGERIA

"Ammi Ashe an saka ranar babban yaya"a cewar Sulaiman yana kallon ta

"Eh an saka,three months"

"Masha Allah,kice a ƴan kwanakin nan muna da bukukuwa da yawa, bukukuwa huɗu kenan fa"

"Bukukuwa huɗu ko uku?"a cewar Ammi tana kallon shi da mamaki

Da sauri ya dafe baki yana dariya yace"au uku!kaji ni da suɓul da baka,bakin ne babu linzami"

Ammi ta bishi da kallo,haka kawai taji gaban ta ya faɗi,ta ɗanyi shiru tana kallon shi,kafin tace"Sulaiman what are you hiding?ka gaya min gaskiya,kar ka raina min hankali"

Sulaiman ya ci serious face yana kallon yace"wallahi ammi babu komai,kar ki damu,ke dai ki fara shirin zuwa bikin su Beely kawai"ita dai tayi shiru ba don ta yarda da abinda Sulaiman yace mata ba, sulaiman ya miƙe ya fice daga parlourn nata yana murmushi,don yasan abinda take yi wa


HOTORO GRA, KANO STATE, NIGERIA


Samha ce zaune tana game,dama yawanci aikin kenan, musamman idan ita kaɗai ce a gidan,sai ga kiran Beely

Ɗagawa tayi tana faɗin"amarya bakya laifi"

Beely tace"amarya kuma uwargida,ya garin?"

"Normal wallahi,ya naji ki shiru?"

"Calm down uwar mita,ki duba na turo miki pre wedding pics ɗin mu da miji na,na duba ban ganki online ba"samha tayi dariya tana faɗin"ƴar rainin hankali,to bari na duba"ta kashe wayar ta buɗe data ta hau WhatsApp

Kai tsaye chat ɗin su da Beely ta buɗe,inda ta tura mata hotunan su na pre wedding pics guda goma,wasu har sun fara buɗewa

Wata uwar ƙara ta saka tana ɗura ashar,wani mugun jiri ya fara fizgar ta,ta murje idanun ta tana ƙara kallon hotunan, tabbas mijin ta ne da aminiyar ta a matsayin masoya,kuma masu shirin zama ma'aurata very soon,ta miƙe a haukace ta ɗauki mayafi da makulli tayi waje,ko makullin mota bata ɗauka ba don ta san bazata iya driving ba a halin da take ciki

Tana fita ta samu napep drop ta shiga,kai tsaye ta nufi lugard road,tana ta kallon kiran Beely yana shigowa amma taƙi ɗagawa saboda bata san me zata ce mata a waya ba,gwara su haɗu fuska da fuska kawai ayi duk bala'in da za'a yi

A haukace ta shiga parlourn su Beely,a zaune ta ganta da waya a hannu,ta nufe ta da ƙaraji take faɗin"munafuka maciyiya amana,azzaluma,wannan itace sakamakon yardar da nayi dake? muguwa wadda bata san darajar zaman tare ba"

Mamaki ya hana Beely magana,samha ta shaƙe ta tana jijjiga ta tana faɗin"wallahi yau a gidan nan ko ni ko ke,tunda ke tsinanniya ce asararriya,muguwa algunguma,sai na...."

"Shut up malama!kanki ɗaya kuwa Samha?uban me nayi miki kike yi min wannan ɗiban albarkar?"

"Ubanki kika yi min! matsiyaciya kawai!"a cewar samha cikin ficewar hayyaci

"Samha lafiyar ki kuwa?ƙalau kike?"

"Kinfi kowa sani tunda kika yarda zaki auri miji na!!!"

"Mijin ki?mijin ki samha?dama Dr S.A abdallah mijin ki ne?"

Samha ta ja baya tana kallon Beely tace"miji na ne, meyasa zaki aure shi?don Allah meyasa zaki aure shi?kin san shine rayuwa ta,farin ciki na,komai na, kin san ina tsananin so da kishin miji na Beely"

Beely ta ja baya tana girgiza kai,ta kalli mum da hayaniyar ta tayar da ita daga bacci ta fito,dama su biyu ne kawai a gidan,ta sake kallon samha tace"ke kika janyo hakan ai,ni ban taɓa ganin mijin ki ba,ko full name ɗin shi ban sani ba,idan kina da adalci bazakiyi blaming ɗina ba"

Samha ta durƙusa a gaban Beely tace"to yanzu kin sani Beely,don Allah ki taimaka min ki haƙura da auren shi,wallahi ina son miji na"Beely ta kalle ta cikin idanu tace"lokaci ya ƙure samha,kema kin san anyi breaking heart ɗina a baya,a yanzu kuma duk abinda nayi ni zan cuci kaina,don haka, I'm sorry to say kawai kiyi haƙuri"bata sake sauraren ta ba ta tashi ta bar wajen ta shige ɗakin ta

Da kururuwar kuka samha ta koma wajen mum tana roƙon ta Allah da Annabi ta tilasta Beely ta janye batun auren,mum tayi mata kallon kin rainawa kanki hankali sannan tace"ku yi magana ta fahimtar juna"ta wuce ɗakin ta itama ta bar samha tana ta kuka

Haka samha ta bar gidan cikin tashin hankali ta nufi nata,a ranar hauka ne kawai batayi ba,haukan ma tayi ɗan ƙarami,don lokacin da mijin nata ya dawo fashe fashe yaga tana yi,yana shigowa kuma ta rufe shi da duka,da kyar ya samu ya kulle ta a ɗaki tana ɗura masa ashar ta uwa ta uba tana tsine masa tana kiran shi mayaudari maci amana,fasiƙi

Bayan Isha'i mahaifin ta yazo gidan saboda sanar da shi da Salis yayi,tana fitowa taga mahaifin ta ta fashe da kuka ta zube ƙasa

Mahaifin ta bai saurare ta ba ya rufe ta da faɗa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba,cikin kuka tace"Abba Aminiya ta zai aura fa,don cin mutunci da wulaƙanci wai aminiya ta!"

Abba yace"sai me?yadda zaku fi ƙarfafa aminta kenan,idan na sake jin muryar ki a sama da ta mijin ki wallahi sai na saɓa miki,tunda akayi auren ki ba'a cikakken wata baki tayar da wata fitinar ba,yayyen ki duk basayi min wannan iskancin,ga ƙannen ki ma lafiya ake zaune dasu a gidajen auren su,amma banda ke,na sake jin wata fitinar ta tashi zaki ga yadda zanyi dake,na bar ku lafiya"ya miƙe ya nufi ƙofa,Salis ya raka shi yana bashi haƙuri

Cikin zubar hawaye ta bisu da kallo,amma a zuciyar ta ko ɗar bata ji ba na abinda ta shirya yiwa Beely,wallahi sai ta san yadda zatayi ta kore ta daga gidan ta

QUEEN'S COLLEGE, KANO STATE, NIGERIA

A yau jarrabawa ta rage wa su khairi saura sati biyu,karatu sukeyi babu ji babu gani,su kenan kullum a Library,yau ma kamar kullum sun fito daga Library suka nufi compound ɗin makarantar inda aka tanadi kujeru don hutawar ɗalibai

Amra ta kalli khairi tana dariya,khairi ta harare ta,Amra tace"seriously khair You are overdosing,ko mungo park da Albert Einstein zan zama wallahi bazan taɓa wasting energy na all the time akan karatu ba,amma ke kam khair baki gani ba wallahi har ramewa kikayi"

Khairi ta taɓe baki tace"ke kika sani"Nabeela tace"wallahi kin takurawa khair albasu,shiru takeyi miki ne,da nice..."

"Ke ɗin ma me zaki iya yi hajiya?"Nabeela tace"ke dallas ware!"khairi ta miƙe tana faɗin"aikin yi kuka rasa sarakunan faɗa,for me I have alot to do"

"To sannu Madam worker,sai da ke hajiyar mu"suka kama dariya,ta kalli Amra me maganar tayi tsaki tana girgiza kai tayi tafiyar ta,suma suka biyo bayan ta

A yanzu khairi tana iya magana da turanci sosai,tana iya rubutu mai yawa kuma ta karanta,dama tun a ƙauyen su Nadiya ta koya mata alphabets da ƙananan words,don haka abubuwa sun zo mata da sauƙi sosai

Suna yawan chat da Sulaiman,Azad Kam idan tayi masa magana ma idan yaga dama sai yayi sati bai buɗe ba,don haka ita ta manta rabon da tayi chat dashi,wani lokacin ma ko magana yayi mata sai taga dama take dubawa

Babu Abinda ta nema ta rasa,a yanzu rayuwar ta ta hau kan sauti sosai,ji takeyi ta sauka daga kan SIRAƊIN UƘUBA da take kai tun daga lokacin da ta shiga maraici, mahaifin ta ya rasu, mahaifiyar ta ta tafi ta bar ta,shekaru goma kenan yau

Amma a yanzu a dalilin Sulaiman komai ya zama tarihi,itama tana walwala kamar kowa

Sun fara jarrabawa cikin nasara,kuma cikin ikon Allah jarrabawar ta zo mata da sauƙi sosai

LUGARD ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE

"Welcome Yaya Azad!da alamu dai ka kamu da wannan beautiful lady ɗin taka"

Ya kalli Beely da tayi masa maganar tana murmushi yace"ai bata kai ki kyau ba"ya kewaye ta ya shige parlourn

Biyo shi tayi cikin mamaki take faɗin"bata kai ni kyau ba Yaya Azad?"ya kalle ta yace"eh mana"Beely ta zauna ta fuskance shi tace"ni dai gani nayi duk kyan ƙanwar ka idan matashi ne baya gani,duk munin budurwa sai saurayi yace tafi ƙanwar shi kyau"

Azad yana kallon ta yace"ni ai ba maƙaryaci bane"Beely ta kama dariya tace"ai ba ƙarya bace, soyayya ce"

"Bilkisu You are disturbing me with your stupid issue,Ina mum?"

"Mum taje kasuwa,amma ina ganin ta kusa dawowa"bai sake magana ba ya miƙe ya fice ya nufi part ɗin shi


A ranar sukayi waya da Sulaiman kan batun khairi,ya sanar dashi ya ɗauko ta gobe,don a gobe zasuyi hutu

Sulaiman ya amsa da "an gama the whole babban yaya"

Azad yace"an gama mata kayan?"

Sulaiman yace"an gama,na bawa su Amra su ajiye mata"

"Okay to shikenan, idan ka ɗauko ta sai ka biya ta gidan ku ka amso mata kayan"

"Okay to shikenan, thanks so much babban yaya"Azad bai saurare shi ba ya katse wayar

Washegari da safe wajen ƙarfe takwas yayi sallama ya shiga gidan nasu,sai ya samu daddy a zaune,ya gaida daddy cikin girmamawa,daddy yace"ango ango!ya aikin naka?"

Azad ya amsa"aiki alhamdulillahi"kafin daddy ya sake magana akayi sallama aka shigo

Matashiyar mace ce sanye da hijabin ta har ƙasa,idanun ta da farar fuskar ta sun kaɗa sunyi jawur,ta zube a gaban daddy tana gaida shi,ya amsa cikin fara'a sannan ta gaida Azad,ya amsa yana ɗauke idanun shi daga kanta

Kanta a ƙasa tace"daddy wajen ka nazo"

Daddy yace"to sannun ki da zuwa,da fatan dai lafiya"

"Ba lafiya ba daddy,Amma don Allah kafin nace komai ina buƙatar ganin mum da Beely"

Daddy yace"babu laifi, Azad Kira min maman ku da Bilkisu"babu musu Azad ya wuce part ɗin mum don Kiran su

A tare suka sauko, Beely ta firgita sosai da ganin samha,samha ta wurga mata kallon zaki gane kuren ki,sannan ta ɗauke kai

Suka samu waje suka zauna,ita kanta mum ta ɗan tsorata da ganin samha,samha ma ta ɗauke kai bata ko sake kallon mum ba,daddy ya kalle ta yace"ina sauraren ki ƴata"

"Daddy dama kan batun Ummul khairi ne"

"Ina jin ki to"a nutse ta warwarewa daddy duk ƙullin da sukayi akan khairi,sannan ta ɗora da faɗin"daddy munyi hakan ne bisa umarnin mom,itace ta saka mu don tace yarinyar zata kashe mata aure,tunda ka kawo ta kake nuna bambanci tsakanin ta da yaran ta"

Tsananin mamaki ya ƙamar da mom jin irin ƙaryar da samha take shararawa, Beely tace"wallahi Daddy ƙarya takeyi,daddy....."

"Silent!"ya daka mata tsawa,sannan ya cigaba"duk abinda akayi kallon ku kawai nakeyi,nasan komai,kawai kyale ku nayi ina jiran lokacin da zaku zo da kanku ku faɗa

Ta yaya yarinya zata ɓata amma mahaifiyar ku ta rinƙa jin haushi don nace zan nemo ta?ta yaya ƴar ɗan uwa na uwa ɗaya uba ɗaya tace bazan biya mata kuɗin makarantar da nayi niyya ba da kuɗi na?to ai shikenan, Salma kinyi abinda kika ga dama,nima ba lusarin namiji bane,zanyi abinda naga dama"

"Ka daɗe bakayi ba Barrister,Wai kana tunanin nayi lalacewar da zan zauna kana gaya min magana a gaban yara?to bazan lamunta ba,kayi duk abinda kake so,bazaka burge ni ba sai ka aure ta ka kawo ta gidan nan a matsayin kishiya ta muna goga kafaɗa"da sauri Azad ya kalle ta ranshi na ƙuna,daddy yayi ɗan murmushi yace"idan ban auro ta ba akwai mata da yawa, waɗanda zan aura su riƙe min ita sannan su haifa min yara masu tarbiyya ba irin naki ba"

"Ka auro,idan baka auri huɗu ba baka cika ɗan halak ba Umar"shi dai daddy bai sake bi ta kan sababin ta ba,da murmushi sosai a kan fuskar samha tayiwa daddy sallama ta fice,ranta fes, Azad da Beely suka bi ta da kallo

Ana party ana partyyyyyyy 💃💃💃💃💃

Don Allah duk wanda yaji daɗin page ɗin yau mu haɗe a comment section 😁

Dara taci gida tsakanin Beely da Samha,ga mum a gefe


#likecommentshare

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

✍️Nusy bee

Page 18

Daddy ya miƙe yana kallon mum cikin idanu yace"ki shirya tarbar abokiyar zama a lokacin da zaki aurar da yaran ki,tabbas zan ƙara auren wadda zata riƙe min ita yarinyar da kika banzatar,ko nace kika so halakarwa,tunda ke ƴaƴan ki kaɗai kika sani a duniya!"yana Kai wa nan ya juya ya fice daga parlourn ranshi a matuƙar ɓace

Mum ta miƙe a fusace tana ɗure ɗuren ashar da ɗaukar alwashi, Beely ta miƙe don rike ta ta hankaɗe ta a fusace tana faɗin"dalla malama matsa daga kusa dani,duk bake kika ja min wannan bala'in ba?kika haɗa ni da wannan tsinanniyar ƙawar taki?"yanzu ba ga abinda kika janyo min ba?"daga nan ta cigaba da aikawa daddy zagi ta uwa ta uba,hatta inna sabuwa ma sai da ta samu nata kason,shi dai Azad ya samu ya lallaɓa ya fice daga parlourn yana jinjina ɗabi'ar mahaifiyar tashi,amma har yanzu yana mata fatan sauyawa


QUEEN'S COLLEGE, KANO STATE, NIGERIA


Yau ta kama ranar hutu,dukkan su sai murna sukeyi zasu tafi gida,ga jarrabawar su tayi kyau sosai, Amra tace"nasan daddy da mummy na zasu bani gift,term ɗina na farko a secondary na fito da wannan result ɗin?"tayi wani ihun murna

Murmushi khairi tayi tace"ni ko yaya Sulaiman baiyi min komai ba zan so naga yana murmushi a dalilin farin cikin da result ɗina zai saka shi,ina son naga na biya farin cikin da ya saka ni da farin ciki shima"Nabeela tace"nima dai zanji daɗi idan daddy ya gani, saboda zaiyi farin cikin naƙi karatu a Kaduna na taho Kano amma ban bashi kunya ba, Allah sarki yaya Hisham"

Hirar su sukayi tayi akan result ɗin su cikin annashuwa kafin Sulaiman ya kira ta a waya ya shaida mata isowar shi

Cikin sanyin jiki tayi musu sallama,suka rungume juna suna ƙwalla,don an saba sosai,khairi ta ɗauki ɗan akwatin kayan ta tayi waje suna ɗagawa juna hannu

A bakin motar shi ta hango shi,yana gano ta ya ƙaraso inda take yana murmushi,ya karɓi akwatin nata, tana kallon shi da murmushi tace"welcome yaya Sulaiman"

Murmushi yayi yace"how are you doing?"

"Alhamdulillahi, good morning Yaya"

"Morning sister,how was your studies?"

"Alhamdulillah, guess what?"ta faɗa tana kallon shi tana murmushi

"You scored your exam"ya faɗa yana tsare ta da idanu yana murmushi

Ƴar ƙara tayi tana murmushi,yayi ƴar dariya yace"na canka ko?muga result ɗin"babu musu ta miƙa masa ya buɗe yana gani

"Wow! that's my lovely sister! congratulations sister!kin saka ni farin ciki sosai yau ɗin nan"

Batace komai ba sai murmushin da ta cigaba da yi,a haka suka shige mota yana ta yaba mata

Sai da suka hau hanya ya kalle ta yace"baki tambaye ni babban yaya ba"

Khairi ta tsuke fuska tace"ai baya kula mutane,nima shiyasa na daina kula shi"

Sulaiman yayi murmushi yana girgiza kai,da alamu khairi tana da ɗabiar son kulawa da damuwa da lamarin ta,shiyasa lokacin da take zaune a albasu akeyi mata kallon miskila, bata magana da mutane,bata walwala,sai yanzu ya gane bata samun kulawa ne,take wani tausayin ta ya rufe ta tuna maganar da sukayi da daddy jiya,Amma sai yayi saurin kawar da maganar yana faɗin"Azad yana da kirki sosai khairi,dukkan mu yafi mu kirki da son mutane,kawai dai bai cika magana ba,baki fahimce shi bane"

Khairi ta yatsina fuska tace"good for him"

Sulaiman ya fashe da dariya yana faɗin"shikenan kema kin rama ta waje na,1-1 kenan"

Khairi tayi dariya tace"ni ba ramuwa nayi ba,kawai maganar ce tazo a haka"Sulaiman yace"naji to,yanzu bani labarin makarantar taku"babu musu ta fara bashi labarin queen's college da yadda take jin daɗin makarantar,shima sauraren ta yakeyi cike da bada full attention,haka suke ta hira har suka isa Kano cike da farin ciki

HAƊEJIA ROAD, KANO STATE, NIGERIA

"Yaya ango!yaushe kazo?"

Ya daga kai ya kalli Amra da ke tsokanar shi tana murmushi yace"ammi fa?tana ciki?"

"Bacci takeyi,tace kar a tashe ta saboda bata jin daɗin jikin ta"

"Okay,Ina surayya?"

"Surayya taje gidan su ƙawar ta"

"Ina Sulaiman?"

"Ya fita tun ɗazu,amma ban san inda yaje ba"bata rufa baki ba suka shigo da sallama,khairi na maƙale a bayan shi

Dukan su suka bi su da kallo, Sulaiman ya zauna kusa da Auwab yana faɗin"sai da kai babban Yaya"

"From where Sulaiman?"

"Dr khairi na je ɗaukowa daga makaranta"ya faɗa yana nuna khairi da take tsaye a ɗarare,Amra sai bin ta da kallon mamaki takeyi ganin yadda ta chanja kamar ba ita ba

"Who is Dr khairi?"Auwab ya faɗa yana yatsina fuska batare da ya koda kallon sashen da khairi ke tsaye tana rarraba idanu ba

Sulaiman yace"gata nan a tsaye"khairi ta daure ta rissina tana faɗin"ina kwana"

Auwab yayi mata wani kallon raini ya taɓe baki ya ɗauke kai yace"lafiya"sannan ya kalli sulaiman ya cigaba da tambayar shi kamar yadda ya saba,shi kuma Sulaiman yana bashi amsa

Ita dai khairi ta zauna ta takure kanta a ƙasa,duk ta muzanta da yadda Auwab yayi mata,ita da gani takeyi babu wanda ya kai Azad wulaƙanci,sai ga wanda yace wa Azad bai iya komai ba,ya dame shi ya shanye,take ta ji ko kaɗan bai burge ta ba,don ita a rayuwar ta ta tsani wulaƙanci, shiyasa ko sanda take ƙauye bata shiga cikin mutane,kuma bata sakar musu fuska

Ga wani kallon ƙasa ƙasa da Amra take bin ta dashi,gaba ɗaya taji gidan ya gundure ta

Can Sulaiman ya kalli Amra yace"Amra kawo wa khairi kayan nan da na baki ajiya" sai da Amra ta sake kallon khairi da ta ɗan saki fuska jin sunan kawar ta,sannan ta miƙe ta nufi ɗakin su

Bayan Amra ta kawo kayan Sulaiman da kanshi ya karɓa ya miƙa mata yana faɗin"kayan fitar bikin yaya Azad ne yace a ɗinka miki"cikin sanyin murya tace"to na gode Allah ya saka da alkhairi"

Yace"ameen,yanzu tashi mu tafi ma mayar dake gida"babu musu ta miƙe,amma jikin ta a mace,don Allah ya sani mugun tsoron mum takeji,musamman ma da ya kasance daga tafiya makaranta aka neme ta aka rasa,babu sanarwa,tana matuƙar jin tsoron abinda zata je ta tarar

Ya dube ta yace"yi musu sallama"cikin sanyin murya tace"sai anjuman ku"Amra ta kalle ta ta ɗauke kai tana faɗin "sai anjuma"amma Auwab ko kallo bata ishe shi ba,sai ma danna wayar shi da ya cigaba da yi,a kaikaice Sulaiman ya kalli fuskar khairi da ta nuna jin haushin abinda yayi mata,yace "muje likita bokan turai"babu musu ta juya ta fara tafiya,Sulaiman ya bi bayan ta

A mota ya kalle ta yana faɗin"sai haƙuri da babban yaya,baya son yawan magana ne"ita dai bata ce komai ba sai kalle kalle da takeyi,asalima ko a fuska bata nuna taji abinda sulaiman ɗin yace ba

A bakin gate ya ajiye ta yayi mata sallama ya tafi,ta buɗe ƙaramin gate a hankali ta shiga gaban ta na faɗuwa, Allah ya sani tana masifar tsoron mum

A babban parlourn tayi sallama Muryar ta na rawa,tana jan ɗan akwatin ta, Beely da har ta fara bacci akan doguwar kujera ta buɗe idanu tana kallon khairi,da sauri ta gyara zama tana murje idanu,cikin idanu ta kalli khairi tace"sannu,me kika zo yi?"

"Ina kwana,anyi hutun makaranta ne"cewar khairi da rawar murya

"Oh ashe hutun Makaranta akayi? matsiyaciya ashe makaranta kika koma kika bar mu muna ta shan wahalar neman ki?munafuka algunguma fice min daga nan,shegiya tauraruwa mai wutsiya!anyi miki rana kinyi wa mutane dare"

Hawaye ya kawo idanun khairi,amma still tana tsaye taƙi gaba taƙi baya,don yadda Beely bata miƙe tsaye tana masifar ba haka itama taƙi tafiya

"Hayaniyar me nake ji?"a cewar mum da ke saukowa ƙasa,ganin khairi itama ta tsaya tana kallon ta da mamaki

"Mum wannan bagidajiyar yarinyar ce ta dawo mana gida!"

Mum cikin ɗaurewar fuska ta kalli khairi tace"ke!na ɗauka zakiyi zuciya ki nisance mu bayan duk abinda ya faru!nan ɗin gidan uban ki ne da kika dawo?to maza maza fice min a gida,ki tafi gidan ubanki,idan ta kama ki bi shi kabari"Beely ta miƙe a zafafe ta fizgo ta ta hankaɗa ta balcony ta mayar da ƙofa ta rufe

Miƙewa tayi tana hawaye ta nufi tempol ɗin motocin gidan,anan ta samu waje ta haɗe kai da gwiwa tana kuka sosai,kewar iyayen ta na damun ta,a fili ta furta"Umma na ina kike kiga halin da nake ciki?Abba ka gani,na sauka daga SIRAƊIN UƘUBAr jahilci,ƙazanta da wulaƙancewa,na hau na tozarci da ƙasƙanci, Allah ka kawo min ɗauki"tana ta kuka, ma'aikatan gidan sai kallon ta sukeyi da tausayawa

Tun wajen ƙarfe sha biyu na rana take nan,har ƙarfe biyar na yamma,tana kallon su Ma'aruf da haidar da sukayi parking motar su suka shige gidan,gwara Ma'aruf ya ɗan waigo ya ƙara kallon ta,amma Haidar baiyi mata kallo biyu ba

Bayan ta idar da sallar maghriba ta jinginar da kanta a jikin bango ta lula duniyar tunani,ga yunwa,ga damuwa,ga sauro da ya addabe ta,bata ankara ba sai ga iska mai ƙarfi,da ƙyar ta iya fizgo addu'a idan iska ta taso

_"Allahumma inni as'aluka khairuha wa khaira ma ursilta biha,wa a'udhu bika min sharraha wa sharra ma ursilta biha'_

Takurewa tayi tana jin lafawar iskar a hankali,kafin tayi wani yunƙuri ruwa mai ƙarfi ya sauka

Sake takurewa tayi rungume da akwatin ta,zuwa lokacin ma ta gaji da hawayen,addu'a kawai takeyi Allah ya kawo mata mafita

Allah sarki khairi😢


#likecommentshare

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

✍️Nusy bee

*Young talent writers association (YOTA)*


Yau ma dai an taɓa ta jiya,an yi post biyu😅ba don kowa ba sai don likers da commentors 🥰


Page 19

An Kai a ƙalla awa guda ana ruwan kafin ya tsagaita,sai kuma iska mai sanyi ta maye gurbin ruwan,hakan ya saka khairi karkarwar sanyi tana bin compound ɗin da kallo tana ayyana da ace mahaifiyar ta ce da bazata taɓa yi mata haka ba

Tayi nisa a tunani har bata san sanda Azad yayi parking motar shia wajen ba,ya sha mamaki sosai na ganin ta anan,amma da ya tuna wace ce mahaifiyar shi sai ya daina mamakin hakan

Ƙarasawa inda khairi take yayi ya sanya hannu ya ɗaga ta,ta tashi a firgice zata ƙwala ihu ya daka mata tsawa,tuni ta nutsu tana kallon shi,har yanzu jikin ta rawar sanyi yake,da alamu ma kamar zazzaɓi yake son kama ta

Ɗaukar akwatin nata yayi ya ja hannun ta,kai tsaye ya nufi part ɗin shi daita,ya bar ta a parlour ya shiga cikin bedroom ɗin shi ya haɗa mata ruwa mai ɗumi ya fito yana umartar ta tayi wanka

Kafin ta gama ta sanyo jiƙaƙken hijabin ta ya buɗe akwatin nata ya ware kayan da basu jiƙe ba,har da hijabi da kayan bacci,don haka tana zuwa ya miƙa mata hijabin da kayan baccin yace"ki je ki chanja da waɗannan,sannan ki rufe kofar ɗakin ki kwanta ki huta,sai da safe"

A sanyaye ta karɓa tana faɗin"na gode yaya Azad"bai amsa ba ya cigaba da abinda yakeyi,har ta juya zata tafi yace"ga wancan abincin ɗauki ki ci"babu musu ta ɗauki takeaway ɗin da alamu ma nashi ne ya bar mata,ta sake godiya sannan ta koma ɗakin nashi ta rufe ƙofa

Tana shiga ta sauya kaya ta kama cin abincin hannu baka hannu ƙwarya,don yunwa take ji ba ta wasa ba,ta gama ta ɗaga lemon ta shanye,sannan ta ji daidai,ta koma gefen gadon tana duba wayar ta don tabbatar da ruwa bai shige ta ba

Bata ƙara cikakken mintuna goma ba bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita,ta ƙudundune a cikin bargon shi abinta tana baccin ta mai daɗi

Da asuba da ƙyar ta iya tashi sallar asuba,bayan ta idar ta zauna tana azkar,sai kuma tunanin Azad ya faɗo mata,tayi ɗan murmushi,Allah sarki!ashe yana da kirki haka!yanzu gashi ya haƙura da ɗakin shi saboda ita kawai,hawaye ya ciko idanunta,bata taɓa tunanin a duniya akwai wani mutum da zai fifita buƙatar ta akan tashi ba,ta jinginar da kanta da gado tana tuna yadda ya kula da ita jiya

Knocking ƙofar taji anyi,tayi saurin gyara zama tana tambayar "waye?"shiru taji babu amsa,da sauri ta gyara hijabin jikin ta ta ƙaraso kusa da ƙofar ta buɗe

Azad ta gani a tsaye a bakin kofar,alamu sun nuna yayi wanka ya sauya kaya,wani kallo yake mata fuskar shi a ɗaure kamar koyaushe,ta ɗan rissina tace"ina kwana"

Bai amsa ba,kuma bai daina bin ta da wani irin kallo ba,ta gatsine fuska ta ɗauke kai,ƙasa-ƙasa taji yace"baki da kunya ko?"

Idanunta sukayi rau rau tana kallon shi, buɗe idanu yayi sosai yana kallon yadda take ƙoƙarin fashewa da kuka,yace"me akayi miki kuma?"

Hawaye suka zubo mata tace"cewa kayi fa bani da kunya,bayan kuma kaine kake ɗauke min kai ko nayi maka magana kayi min banza"

Samun kanshi yayi da faɗin"I'm sorry!taho na mayar dake gida,ga kayan ki nan sun bushe"

A ɗan razane ta ja baya tana faɗin"Mom bata so,kar tayi maka faɗa faɗa"

"Kar tayi min ko kar tayi miki?"ya tambaye ta yana kallon ta

"A'a kar tayi maka,kaga ni na saba da faɗa da duka a garin mu,kai kuma kaga ɗan gata ne baka saba da ko tsawa ba"

"Da gaske?"ya faɗa yana kallon ta

"Allah kuwa,kaga kai ko magana da ƙarfi baka iya ba,dama yaya Sulaiman yace min kai Bature ne"

"Ni ɗin?"

"Eh mana,gashi jikin ka ma irin na turawa ne,kuma yadda kake magana haka sukeyi,yadda kake tafiya da saka kaya ma duk irin nasu ne"

"Mhmmm I see,to ke ina kika san turawan?"

Ta kalle shi tana sake zare manyan idanun ta tace"a Film mana,kuma suna zuwa makarantar mu fa"

Ya haɗe fuska yace"da kyau,wato gulma na kukeyi da Sulaiman ko?"tayi saurin girgiza kai tace"Allah ba gulmar ka mukeyi ba,kawai dai nace masa baka yi min magana ko nayi maka,sai yace ai kai Bature ne baka iya magana ba sosai ba"

Maganar tata ta bashi dariya,ai kuwa ya kama dariyar,khairi ta buɗe idanu sosai tana kallon yadda yake dariya a nutse,ta sake cewa"laaa!dama kana dariya?"

"Haɗe rai yayi yace"wai me kika mayar dani ne?"

Ta washe baki tace"ni fa ban taɓa ganin kayi ko murmushi ba,daga kallon banza sai harara,sai ɗauke kai, wallahi tayi maka kyau sosai,don Allah ka rinƙa yi kaji"

Ya gyara tsayuwar shi don yaga alamu hirar shiriritar nan ba ƙarewa zatayi ba,gashi yana jin daɗin ta,yace"da gaske tayi min kyau?"

Ta gyaɗa kai da full confidence tace"eh mana!kayi kyau sosai"

Ya girgiza kai yace"to ai idan inayi mata da yawa zasu ce suna so na, shiyasa bana yi,to yaya kenan?ko kina son a ɗauke miki yayan ki?"

Tace"sai kace musu aure zakayi,bana ji ance next week ne auren ka ba?"

Ya zaro idanu yana kallon ta yace"waye ya gaya miki?"

Tace"yaya Sulaiman mana,yace bikin ka da Aunty Beely ya kusa,shine ya bani waɗancan kayan ledar yace na ankon bikin ku ne"

Azad yayi ɗan murmushi yace"eh,amma nan da ɗan lokaci zan sake wani auren"

Tayi ɗan shiru kafin tace"meyasa to?amaryar taka tayi maka laifi ne?"

Ya girgiza kai yace"a'a!ai ba laifi ke saka wa mutum ya ƙara aure ba"

Khairi tace"ai kuwa a albasu a matan baffannina duk wadda tayi laifi sai inna Sabuwa tace ayi mata kishiya"

Ya jinjina hali irin na kakar su,amma sai ya bagarar da zancen yace"to ni ba dalili na kenan ba,akwai wadda nake so ne,duk da ina fargabar ko zata yarda ta aure ni"

Khairi ta buɗe idanu sosai tana kallon shi tace"meyasa bazata yarda ba?"

Ya langwaɓar da kai yace"haka kawai nakeji kamar bazata yarda ba, maybe banyi mata bane"

Khairi ta rike ƙugu tace"to inaga sai dai idan makauniya ce bata gani,amma yaya ai baka da makusa da zata ce bata son ka,tukunna ma,ka gaya mata?"

Yana kallon ta ya girgiza kai batare da yayi magana ba

Ta gyara wuyan hijabin ta tace"ai kuwa baka da hujjar yanke mata hukunci a haka,ka roƙi Allah zaɓin alkhairi sannan ka tunkare ta ka gaya mata cewa kana son ta,Ina da tabbacin zata so ka,idan ma taki yarda ka gaya min ni zan shawo maka kanta"

Murmushi ya sakeyi yace"promise?"ta gyaɗa Kai da full confidence,ya Mika mata ƙaramin ɗan yatsan shi,ta miƙa masa nata suka haɗe,yace"kin dai tabbatar ko?"tace"na tabbatar"

Yace"good!now mu wuce mu tafi kar daddy ya fita"babu musu ta fara tafiya,yayi gaba ya sunkuci akwatin kayan ta da ya gama haɗawa,ita kuma ta ɗauki ankon nata da Allah ya taimake ta ruwa bai taɓa shi ba

A parlour suka samu Beely da Ma'aruf a zaune,tana ta masa lissafi da alamu aiken shi zatayi,suna ganin su Azad suka bi su da kallo da mamaki

Khairi ta tsorata kwarai musamman ganin Beely,sai wani mugun kallo take watsa mata, fuskar Azad a ɗaure kamar kowanne lokaci yace"ina mum da Daddy?

"Good morning big bruh!"suka faɗa kusan a tare

"Answer my question first!"ya faɗa da ƴar tsawa

Beely tace"daddy Yana parlourn shi,mum tana sama"

Bai sake magana ba ya ja akwatin khairi,ta bishi da ƴan ƙullin kayan ta a hannu zuwa parlourn Daddy

Sun gaisa da daddy,cikin harshen French da ya tabbatar khairi bata ji yayiwa daddy bayanin mum tana fushi da ita ne,idan zai yiwu ya samar mata wani wajen kawai ta koma da zama

Kafin daddy ya bashi amsa sai ga mum a fusace ta faɗo parlourn,da alamu dai saƙo ya kai mata,tana zuwa batayi wata-wata ba ta ɗauke fuskar Azad da mari ta sake sauke masa wani,kafin tayi na uku khairi ta daka tsalle ta shiga tsakaninsu tana gunjin kuka tana faɗin"don girman Allah mum kiyi haƙuri,don Allah ki daina dukan shi kiyi min abinda zakiyi masa,don Allah kar ki cutar dashi na roƙe ki mum"

Daga Daddy har Azad kallon khairi sukeyi da tsananin mamaki,ita kanta mum kasa motsi tayi saboda mamaki da baƙin ciki,daga baya tayi ta maza ta hankaɗe khairi tana faɗin"ke ɗin ƴar uban waye da zaki shiga tsakanin mu da ɗana?ko uwar ki ta haifa min shi?"

Khairi ta goge hawayen ta tana girgiza kai,cikin sanyin murya tace"don Allah mum ki daina dukan shi,zaki cutar dashi"

Daddy yayi murmushi,ya miƙe yazo ya kama hannun khairi ya miƙar da ita tsaye yace"kar ki damu kinji daughter?ɗan ta ne,tafi kowa sanin ciwon shi,ta daɗe bata cutar dashi ba,ta kashe shi ma"

"Eh ɗana ne!amma baiyo hali na ba,sai yayi mugun halin ka,ka cuce ni Umar,ka cuce ni,akan wannan ƴar tsintuwar zakayi min kishiya,ka raba min kan yara,ka jefa ni a cikin baƙin ciki da takaici koyaushe, Umar anya kana son rahamar Allah kuwa?kafi kowa son zumunci ne?ko kafi kowa ƙaunar yara? lieutenant general bai fika sukuni ba?shi yace zai yi wannan karambanin ne?sai kai akarambana uban ƴan shishshigi? wallahi bazan taɓa yafe maka ba baƙin cikin da ka saka ni tsawon lokaci, azzalumi mara iymani,mahai'inci"ta juya tana kallon Azad cikin hargowa tace"kai kuma idan ka sake kula yarinyar nan,ko magana kayi mata to ban yafe maka ba"Azad yayi saurin kallon ta idanun shi waje,tace"eh haka nace,wallahi na same ka da kwatankwacin abinda na hane ka zaka ga zunzurutun fushi na"

Ta juya kan khairi,kafin tayi wani yunƙuri ta shaƙo wuyan ta tana faɗin"yau sai dai a zaɓa ko ni ko ke a gidannan"khairi taji shaƙa tana ta wutsil wutsil a hannun Mom,da ƙyar daddy ya ƙwace ta,yace ta wuce ɗakin ta,ta zube a ƙasa tana kuka tana numfarfashi tace"don Allah daddy ka mayar dani albasu,sai na rinƙa zuwa Makaranta daga can,don Allah daddy!

Tunda nazo gidan nan a dalili na ba kwa zaman lafiya,ran mutan gidan kusan koyaushe a ɓace a dalili na,na zama tauraruwa mai wutsiya!

Daddy ka bar ni na koma albasu,can ne ya dace dani"

Daddy ya kalle ta yace"babu inda zakije khairi,anan gidan zaki zauna har lokacin aurar dake yayi,ban yarje miki zuwa ko'ina ba"

Mom ta kalle shi cikin ƙunar rai tace"wallahi Umar bazan yarda kana son ta ba sai ka aure ta ka kawo ta a matsayin kishiya,yara na kam na shata musu layi,ta zauna a gidan gashi nan,amma wallahi sai ta gwammaci wannan bushashshen ƙauyen nasu akan zaman gida na,idan kai tayi maka asirin su na ƙauyawa ni na sha tabara na sha yaasin!kai Azad!tashi ka fice daga parlourn nan,idan ka yarda na ƙara ganin ka kusa da yarinyar nan wallahi sai ranka yafi nawa ɓaci"Azad da tun ɗazu kanshi a ƙasa ya miƙe jiki a mace ya fice daga parlourn bai sake kallon kowa ba,itama mom bayan shi ta bi bayan ta watsawa khairi wani mugun kallo ta buga kwafa,khairi dai kanta yana ƙasa tana goge ƙwallar da ke zubo mata,daddy bai ce komai ba ya kama hannun ta ya kai ta har ɗakin ta,ya zaunar da ita,ya zauna kusa da ita,cikin kwantar da murya ya fara magana

"Komai jarrabawa ne a rayuwa khairi,akwai wahala tabbas,amma idan aka jure za'a samu riba,na ɗauko ki daga albasu ne ba don komai na sai don na baki ingantacciyar rayuwa,idan kika isa aure na aurar dake ga wanda ya dace,zan maye gurbin yaya Garba a wajen ki,amma ban isa na saka Salma ta maye gurbin mahaifiyar ki a wajen ki ba"cikin kuka khairi ta katse shi da faɗin"daddy don girman Allah ku taimaka ku nemo umma na ku haɗa ni da ita,na kasa samun farin ciki,yanzu komai tsoro yake bani"daddy yace"kada komai ya baki tsoro daughter,kiyi rayuwar ki cikin farin ciki,ko babu kowa a rayuwar ki zakiyi farin ciki muddin kika riƙe karatun ki,shine makamin samun nasarar ki a rayuwa"a hankali khairi ta gyaɗa kai,yace"now!kiyi min alƙawari kin daina damuwa"cikin sanyin murya tace"i promise daddy"yayi ƴar dariya yace"inyeeee!kice yayan naki baiyi asarar kuɗin makaranta ba,to ki dage watarana kiyiwa mutane allura,har ma ki feɗe wasu"tayi dariya har ƴan haƙoran ta suka fito,yace "yanzu gaya min,wa zaki fara yiwa allura idan kika zama likita?"

Ta ɗan yi shiru kafin tace"baba atine!"daddy yace "saboda me?"

Khairi tace"ta cika faɗa,har bulala kawai ta ajiye duk wanda yayi mata laifi ta zane shi"daddy yayi dariya yace"to naji,albashin ki na farko kuma wa zaki fara kashewa?"kai tsaye tace"baba Hari zan biya kuɗin ta,itace take biyan dukkan sanda na ɓatar wa da mutane kuɗi"ta jinjina kai yana murmushi,amma mamakin khairi ya kasa barin shi,kwata kwata shekarunta goma sha huɗu ne amma idan tayi wata maganar kamar wata babba,ya dafa kanta ya miƙe yana faɗin"all the best daughter! Allah yayi miki albarka kinji?bari na saka a kawo miki abinci,ki ci sai ki huta"tana murmushi tace"na gode Daddy, Allah ya biya ka da aljanna"yayi murmushi ya fice daga ɗakin


To pa!mum dai bazata tuba ba🥺

#likecommentshare

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee


*Young talented writers association YOTA*


Page 20

A ɗakin ta ta wuni ranar,sai dai a kawo mata abinci ɗakin ta,idan lokacin sallah yayi ta miƙe tayi sallah,yini tayi tana chatting da su Amra a WhatsApp,sai Sulaiman,taga Azad online,tayi masa magana amma bai amsa ba,dama bata saka ran zai amsa ba,amma duk da haka ta bashi haƙurin ganin silar ta ya sha mari a wajen mum,shima dai still bai ce mata uffan ba,asalima bai ma buɗe ba

Kwana uku da dawowar ta feena da Nusra suka dawo daga garin mahaifiyar su da suka tafi, Yola

Mutanen gidan sunyi farin ciki sosai da ganin su,itama khairi da gudun ta ta fito don yi musu oyoyo amma tayi tuntuɓe da ƙafar Ma'aruf da bata kula dashi ya zauna ya miƙe ƙafar ba, ta faɗi bakin ta ya daki tiles ya fashe

Da sauri mutanen parlourn suka juya suna kallon khairi da ta zauna sosai tana kallon Ma'aruf a tsorace,shi kam ɗauke kai yayi ya janye ƙafar shi yana ɗaure fuska,ya cigaba da danna wayar da yakeyi

Da sauri feena ta nufe ta da gudu, Nusra ta rufa mata baya,amma mom tace"duk wadda ta taɓa ta a cikin ku sai ta gane kuren ta"

Tsayawa sukayi cak suna kallon mum da mamaki a fuskokin su,mum ta haɗe fuska tace"duk wadda ta sake kula ta a gidan nan ma ban yafe mata ba wallahi"tana gama magana ta juya ta nufi saman ta bata sake ko waiwayo su ba

Tsayawa sukayi suna bin khairi da kallo,Nusra ta ƙarasa kusa da ita zata ɗago ta, khairi ta ja baya idanunta cike da hawaye tace"kiyiwa mahaifiyar ki biyayya,tana son ki duk runtsi bazata taɓa tafiya ta bar ki ba,ni kuma tawa ta tafi ta barni,kar ki saɓawa mahaifiyar ki akan wadda bata san daɗin mahaifiya ba"ta yunƙura ta miƙe ta nufi ɗakin ta tana kuka,su kuma suka bi ta da kallo cikin jin tausayin ta

Daga ranar khairi bata sake fitowa daga ɗakin ta ba sai da ƙwaƙwƙwaran dalili, abinci ma daga baya sai da mom ta hana a kai mata,haka zata ƙaraci zama da yunwar ta,daga baya mai aikin ta samu dabarar zuro mata ta window,shima sai ta yini bata saci hanya ta jefo mata ba

A haka aka fara bikin su Azad,ko sau ɗaya khairi bata je ba,ankon ma ta manta dashi,tunda ta kawo shi bata buɗe taga abinda yake ciki ba,rayuwar ta ita kaɗai,daga ita sai wayar ta

Sulaiman ne yake tambayar ta ta Whatsapp meyasa bata je cocktail party ba?tace hakanan,da ya matsa mata da tambaya sai tace bata da lafiya ne, ya sake tambayar ta "an kai ki asibiti?"

Tace"a'a,amma na sha magani"dalilin hakan ya ƙyale ta duk da yasan ta faɗa ne kawai

Anyi biki sosai,ana igobe ɗaurin auren su Beely da yamma wani abin mamaki ya faru

Su baba atine ne akan gaba,ga baba Hari,gasu Inna haleema da dai sauran matan kawunnan khairi,sai wasu baƙin fuska da matashiyar mace da ta sha lulluɓi,wai amaryar daddy ce

Feena aka aika ta kira mum,a gadarance mum ɗin ta sauko daga saman ta tana taku ɗaiɗai wai ita uwar biki,da baba atine ta fara cin karo,ta daure fuska tace"baiwar Allah me ya kawo ki gida na?ko baki san anan sai na saka ƴan sanda su kama ki su lakaɗa miki duka su rufe min ke bane?"

Baba atine tayi mata kallon rainin wayo tace"gidan ki ko gidan mijin ki?to ga ƙari ma,mu bamu da lokacin ki,amarya muka kawo,ina ne ɗakin ta?"

"Amarya!amarya fa?"ta faɗa cikin ƙaraji

Khairi tana ɗaki ta leƙo ta window,nan taga inna haleema a tsaye tana maimaita faɗin"amarya fa,gata nan,ai dama tuni mijin naki yace a duba masa ƴar bazawara mai hankali ya aura,da alamu shima mugun halin ki ya ishe shi"

Wani uban ashar ta lailayo ta maka tana faɗin"wallahi bazai yiwu ba,ni Umar zai ciwa amana?"

Baba atine tace"a'a ki bari idan yazo sai kiyi masa haukan,mu bamu muka kar zomon ba,ƴan aike ne kuma kin san ɗan aike baya laifi"a fusace mom ta ɗauke ta da mari,baba atine tayi dariyar rainin wayo tace"baki daku ba kenan ko?wato jikin ki bai gaya miki yadda ya kamata ba wancan karon?to tunda kina buƙata bari kawai ki samu"kafin su inna haleema suyi wani yunƙuri tuni baba atine ta shaƙe Mom,da ƙyar suka ƙwace ta tana numfarfashi, lokacin jama'a sun taru a parlourn, amarya kuwa tuni an dangana ta da sashen ta da ke kusa da na Azad

Mom kuka da kururuwa ta rinƙa yi tana zagin daddy,khairi dai na laɓe ta window tana kallon komai, Beely tazo tana kuka ta janye hannun Mom suka nufi ɗakin ta,Nusra da feena ma cikin kukan suka rufa mata baya

Da daddare daddy ya Kira su parlourn shi baki ɗayan su,har da Azad ango da Beely amarya,har da khairi,da mom da tazo da ƙyar,idanun nan nata a kumbure alamu ta sha kuka

Dad ne ya buɗe taro da addu'a,sannan yayi musu bayanin ƙara auren Naja'atu da yayi a matsayin ta na matar shi ta biyu,ya ƙara da faɗin

"Na aure ta ne saboda wasu dalilai da na bar wa kaina,fata na,ku haɗa kan ku ku zauna lafiya,salma kece babba,don Allah ki ja girman ki, Naja'atu kece ƙarama,ki girmama yayar ki wadda ta girme ki a shekaru da gidan aure,ga ƴa ta nan Ummul khairi, marainiya ce wadda babban yayan mu ya rasu ya bar mana,na yanke cewa zata dawo hannun ki,don girman Allah ki kular min da ita kamar ƴar ki,an tabbatar min da kina da yarinya sa'ar ta ma,to don Allah ki ɗauke ta ƴar ki

Ku kuma"ya nuna yaran gaba ɗaya,ya cigaba"wannan baiwar Allah mata tace,uwa ce a gare ku,ku girmama ta,ku zauna lafiya da ita,kar naji wata fitina kar na gani,idan akwai mai magana ya faɗa yanzu"

Mom ta kalle shi cikin idanu tace"magana ta itace ka sake ni Umar,don wallahi baka isa ka ƙara aure don ka wulaƙanta ni ba,auren ma da ƴar ƙauye,wallahi na girmi kishi da ƴar ƙauye bagidajiya,don haka ka sallame ni kawai na kama gaba na,ba sai ka nuna min iyaka ta don kayi aure ba"

Daddy ya kalle ta ya jira har ta gama bayanin kafin ya sallami yaran,dukan su suka miƙe jiki a saɓule suka fita,tuni khairi ta shige ɗakin ta don irin kallon da taga Beely da Haidar sunayi mata

Daddy ya kalli Mom fuska a ɗaure yace"Salma ba kanki farau kishiya ba, kowacce mace akayi haƙuri takeyi ta zauna da mijin ta lafiya,ba wai tayi ta zubar da girman ta gaban mutane ba,kishi ai ba hauka bane,ya kamata ki san me kikeyi Salma"

Mom cikin kuka tace"amma dai Allah yayi mana hisabi da kai Umar,azzalumi macuci,kace min mahaukaciya mana,idan kaga dama kace a turu ka dauko ni,a haka dai a mahaukaciyar ka zauna dani,kuma gani nan dai,ko me akayi ni ɗin ce dai a sama"tayi tsaki ta miƙe a fusace ta fice,ya bi ta da kallo,kafin ya girgiza kai cike da takaici

Washegari tun da safe Hajiya Raheena da yaran ta suka iso gidan,tunda aka fara bikin sai dai a haɗu a wajen event kawai,amma basa zuwa,sai yau yini,ƴan albasu dai sunyi ɗaiɗai a babban parlourn gidan,daddy ya saka an kawo musu abin kari kala kala,tun ɗazu khairi tazo suka gaisa sai zuzuta girman ta da yadda ta chanja sukeyi

Da sallama su Hajiya Raheena suka shigo parlourn,suka amsa suna kallon ta,baba dije,ɗaya daga matan baban Nadiya tace"maraba lale da manyan mata"Hajiya Raheena ta zauna ta gaishe su,suka amsa,inna haleema tayi tsagal tace"ke dai Allah ya tsare kar inna tace kema a lalubowa naki mijin"gaban Raheena ya faɗi,da sauri tace"a'a ni banyi laifin komai ba, ballantana ayi min hukunci,rufa min asiri"sukayi dariya su duka

"To ni me nayi?uban me nayi?"da sauri Raheena ta kalli mum da ke saukowa daga saman ta fuska a ɗaure,tayi saurin girgiza kai tace"ba haka nake nufi ba hajiya,ina nufin........"

"Kar ki raina min hankali Raheena!dama na daɗe ina zargin kina munafurta ta,yanzu na tabbatar!ashe ke munafuka ce Raheena?kinji kunya!kinyi asara!kinci amanar zaman tare,wallahi Allah wadaran naka ya lalace!!ni nasan dama ba banza ba ɗanki ya zagaye ya kai waccan yarinyar makaranta,ashe kece annamimiyar da kika saka shi?wato kece maƙiyiya ta a ɓoye,lallai,dama ance makashin ka na gindin ka!!!"


Gaskiyar princess phadimatu fa da tace wannan matar daqiqiya ce 😁

#likecommentshare

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee


*Young talented writers association (YOTA)*


Page 21

Wani jiri ne ya fara ɗiban Hajiya Raheena,don a rayuwar ta ba ta ƙaunar hayaniya,ta zauna sosai tana kallon Hajiya salma da ta juye mata zuwa ainihin salma da ta sani,cikin sanyin murya tace"zan so ki fahimce ni hajiya,wallahi bani da masaniya a kan komai da ya faru,wanne ɗan nawa ya zagaye ya kai wacce yarinyar makaranta?"

"Ban sani ba!kar ki mayar da ni ƴar ki Raheena,munafuka!"Amra da surayya dai tuni sun fashe da kuka cikin tashin hankali,daga baya Amra ta fice daga parlourn don kiran Sulaiman,su dai mutan ƙauye sai kallon Hajiya salma sukeyi da mamaki,zuwa yanzu abin nata ya shallake tunanin su

Salma ta tako gaban Raheena tana nuna mata ƙofa ta ce"fice min daga gida Raheena,ai dama tun lokacin da naga Barrister ya kawo waccan yarinyar gidan nan baiyi yunƙurin kai ta gidan ki ba nasan da wata a ƙasa,sai gashi munafukin ɗan ki ya kai ta makaranta"

"Munafukin ɗan ta ko munafukin ɗan ki?"dukan su suka waigo suna kallon Sulaiman dake tsaye a bakin ƙofa fuskar shi ɗaure da ɓacin rai

Ita kanta khairi da ke laɓe tana leƙo su ta window ta tsorata da ganin shi,don bata taɓa ganin shi fuska a ɗaure ba sai yanzu

Ya ƙaraso gaban su,kafin yayi magana Hajiya salma ta riga shi

"Da kyau!kaima rashin tarbiyyar kazo zaka yi min?"

"Duk rashin tarbiyyar shi ai ko kama ƙafar ƴaƴan ki baiyi ba"a cewar inna haleema da tuntuni take jin haushin Hajiya salma saboda a cewar ta ta cika girman kai

Hajiya salma ta juya cikin masifa zata fara magana,Sulaiman yace"kinga mum,ni ba wannan ne ya kawo ni ba......"Hajiya Raheena ta juya shuwa ta hau shi da faɗa,bai kalle ta ba cikin harshen Hausa yace"bari a cire ta a duhu ammi na"yana kallon Hajiya salma ya fara magana

"A tunanin ki nine na kai khairi makaranta ko?to bani bane,ni umarni kawai nabi,Amma wanda ya kai ta makaranta,ya biya dukkan kuɗin makaranta,ya kula da komai nata ɗan ki ne AZAD!

Ni kawai yana saka ni yin wasu abubuwan ne,a matsayin shi na wanda ya girme ni,amma ban taɓa kashewa khairi ko ƙwandala ba,don kafin na kashe mata goma ya kashe mata ɗari,hatta da sutura da ƙanwar shi ta nemi na siya mata tun a ƙauye shine ya bani kuɗin,don banje da kuɗi ba,don haka kar ki sake ce min munafuki,kuma shima Azad ba munafuki bane, idan kina neman munafuki to gata nan a gefen ki,ƴar ki Bilkisu,kuma duk abinda yayi da sanin mahaifin shi,ko nace mahaifin shi ya sani daga baya

Ammi let's go please,don babu wata mace da ta isa tayi miki hayaniya ko shirme na zuba mata idanu"ya ɗaga ammi,suka fice ita da yaran ta jikin su a sanyaye

Har ya juya zai tafi ya sake juyowa ya kalli mum ya ce"sau tari ina ɗaga miki ƙafa ina overlooking abinda kikeyi,ba don komai ba sai don ɗan ki da ya kasance baiyo irin halin ki ba,amma yake matuƙar ƙaunar ki,kar ki kaini ƙarshen da zan daina ganin mutuncin ki nayi miki abinda bai dace ba,sai anjuma"ya rufawa mahaifiyar shi da ƙannen shi baya,yana jin su inna haleema suna shewa suna dariya

Khairi kam cikin sanyin jiki ta koma kan gado ta kwanta maganganun Sulaiman nayi mata rotating akai,ashe wai yaya Azad ne ya biya mata kuɗin makaranta?ashe shine ma ya bada kuɗi aka siya mata kaya a ƙauye? Allah sarki!ashe haka yake da kirki?hawaye suka zubo mata,a ranta faɗi takeyi"Allah sarki yaya Azad bakayi sa'ar uwa ba!"

Duk wannan budurin da akayi bai hana ɗaurin auren Beely da Dr Salis da misalin karfe goma na safiyar ranar ba,sannan aka ɗunguma aka badawa layout aka ɗaura na Azad da fadeela

Anyi shagali sosai,don bayan wani lokaci kowa ya ware aka cigaba da shagali,itama Hajiya Raheena daga baya ta dawo da yaran ta aka cigaba da sabgogi tare,ita dai khairi tana ɗaki,idan taji abin gulma sai ta leƙo ta kalla,yini tayi tana danne dannen ta a waya,da abokin ta bacci

Wajen ƙarfe bakwai na yamma aka kawo amarya fadeela,sam babu alamun tarbiyya a wajen ƴan uwan amarya ko nace ƴan matan amarya,ita kanta Hajiya salma ta tsorata da yadda ta gansu,ita kanta amaryar shigar banza ce a jikin ta ballantana ƙawayen nata, kowacce taci Bleaching ga attachment har gadon baya kala kala,na wata baƙi, wata blue,wata ja,wata maroon,wata silver color,gasu nan dai

A lokacin khairi ta fito,itama ta saka ankon ta yayi mata kyau sosai, surayya da taga tana ta kokawa da ɗan kwali sai ta karɓa ta ɗaura mata

Tana zaune a cikin mutanen albasu,suna ta hira,amma ita bata saka musu baki,wayar ta ce a hannun ta, lokacin da aka shigo da amarya ta bisu da kallo kamar taga sabon abu,tsam ta miƙe ta fice daga parlourn ta nufi backyard ɗin gidan

Ji tayi an fizgo ta,zata ƙwala ihu aka toshe mata baki,aka cigaba da jan ta zuwa can bayan gidan,sannan ya sake ta ya daidaita mata tsayuwar ta

Ware idanu tayi tana murmushi,ta ce"Yaya Azad!yanzu aka kawo maka amaryar ka,baka gansu ba ƴan gayu ita da ƙawayen ta,gata kyakkyawa"

Ya ce"ta kai ki kyau?"

Ta ce"tabɗijam!ni ɗin banza!!tafi ni mana"

"Noooo bata fi ki ba,kin ma fi ta,kuma kin fi ta gayu"

Tace"baka ga gashin ƙawayen ta da suka saka ba gwanin sha'awa,har baya,kala kala"

Yace"wannan gashin yana indicating mutum na banza ne,kinga ƙawayen ta mutanen banza ne,kar ki kuskura kiyi sha'awar shi ko da wasa"

Ta ɗan bi shi da kallo kafin tace"dama suma ƴan birni suna da mutanen banza?"

Yace"of course yes,suna da mutanen banza mana"

Ta girgiza kai tace"to don Allah ka daina irin wannan askin da ka keyi,kaga a garin mu mutanen......mhmm...kaga...to don Allah ka daina kaji?"

Yayi ɗan murmushi ya ce"nima ai mutumin banza ne ko?"tayi saurin girgiza kai ta ce"kai mutumin kirki ne yaya Azad!kana daga cikin mutanen da bazan taɓa mantawa dasu ba a rayuwa ta"hawaye suka ciko idanun ta

Murmushi yayi yana goge mata hawayen yace"bana son ki rinƙa yawan kuka Dr khairi!yanzu idan muka zo ki duba mu a asibitin naki kuka zakiyi mana?"

Murmushi tayi tana girgiza kai,ya ce"good girl!sannan bayan aski menene kike so na daina?"

Tayi saurin kallon shi ta ce"zaka daina?"ya gyaɗa mata kai yana kallon ta,tayi murmushi tace"ashe ina da matsayin da zance ka daina abu kuma ka daina?"yayi murmushi yace "fiye da haka ma,da kin ce kar na auri fadeela da zance ya yanku,yanzu ma idan kika ce na sake ta it will be done ma'am!"

Sakin baki tayi tana kallon shi har ya gama,kawai ta kama dariya har da riƙe ciki,ya zuba mata idanu har ta gama sannan ta kalle shi ta ce"yanzu me zaka gaya wa mom da mutanen da kuka tara idan ka saki amaryar ka?"kai tsaye ya ce"ce musu zanyi Dr khairi ba ta amince da auren ba shiyasa na haƙura"da sauri ta girgiza kai ta ce"na amince, Allah ya sanya mafificin alkhairi ya baku zuriya ta gari,ya kamata ka koma kaga za'a iya neman ka kowanne lokaci"

Ya ce"kin tabbatar?"ta ce"eh mana"yayi murmushi ya juya ya nufi cikin gidan,ita kam tsayawa tayi da mamaki tana bin shi da kallo

Tun lokacin da Azad ya ja khairi Sulaiman ya gan su,ya bi shi a ɓoye,don haka yana fitowa ya ga Sulaiman yana tsaye yana jiran shi,kafin yace komai Sulaiman ya ja hannun shi suka nufi garden ɗin gidan

Sulaiman ya kalle shi cikin ɗaurewar fuska ya ce"Azad what is there between you and khairi? me kake ɓoyewa ne?"Azad ya girgiza kai yace"babu komai,me ka gani?"

"Kulawar da ka ke nunawa khairi ta wuce ƴan uwan taka,sai dai SOYAYYA!kar kaje kayi abinda zakayi nadama Azad!"

"Soyayya dai! soyayya!!da khairi kuma!!!wai kuma ni ɗin?mhmm!"yayi ƴar dariya ya ɗauke kai,sannan ya sake kallon Sulaiman yace"wai ni Azad mai thirty four years na faɗa soyayya da yarinya ƴar fourteen years,yarinyar da mahaifiyar ta ma da kaɗan ta girme ni ita kake maganar wai nake so?ni? yarinyar da har yanzu ba ta san kanta ba ballantana ta san me take so ita zan so?wasa kake yi ne Sulaiman?"

Sulaiman yana murmushi ya girgiza kai yace"okay na fahimta,kulawa ce kawai,kasan Maraya sai da kulawa, wishing you all the best babban yaya!"

Har ya juya zai tafi ya dawo,ya kalli Azad yace"amma a shawarce,ka ja baya da irin kulawar da kake yiwa khairi,kar shaƙuwar ku ta wuce kima, remember khairi ba muharramar ka bace"yana magana ya juya yayi tafiyar shi, zuciyar shi cike da tausayin mutum uku

Shi dai Azad bin shi yayi da kallo gaba ɗaya jikin shi a sanyaye,kafin ya koma ya nemi waje ya zauna gaba ɗaya kanshi ya kulle

Ita kuwa khairi cikin farin ciki ta shige gida tana ƴan waƙe waƙen farin ciki,tana shiga parlourn taga ana ƙoƙarin a kai Beely,sai kuka takeyi,ta taɓe baki ta shige ɗakin ta a ranta ta ce"kukan munafurci!!"

A gidan amarya fadeela da ƙawayen ta suka kwana,ita dai khairi tana ɗakin ta,tun wajen tara na dare tayi baccin ta,dama ita har yanzu akwai ƙauna tsakanin ta da bacci

Washegari ta ga ana ta shirye shiryen tafiya da fadeela Melbourne dake Australia,ƙawayen ta sun ci wanka cikin kalolin shigar rashin mutunci,ita kanta fadeela ta haɗe a cikin wata fitted gown da ta matse ta sosai,an zubo mata kiston attachment ɗin ta har baya,ta yafa ɗan ƙaramin mayafi,su dai su feena suna gefe suna kallon ikon Allah,don su dai duk rashin mutuncin mom bata barin su suna irin wannan wulaƙantacciyar shigar

Itama khairi leƙowa tayi ta window tana kallon ƙawayen amaryar da bata saba ganin irin su a albasu ba,tana nan tsaye Azad yayi sallama ya shigo parlourn

Sanye yake da ƙananan kaya kamar koyaushe,sai dai abinda yayi mata daɗi kan nashi babu askin nan na jiya,kuma askin da ya sakeyi yayi masa kyau sosai,ji tayi kamar ta fita da gudu ta yaba masa cewa yayi kyau,amma ta sani Mom tayi masa iyaka da ita,hakan ba mai yiyuwa bane


Da alamu mum fa ta deɓo ruwan dafa Azad 😥🙆

#likecommentshare

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


SIRAƊIN UƘUBA

__Free_book_

Nusy bee

*Young talented writers association (YOTA)*


Page 22

Tana kallon yadda ƙawayen amaryar suke wata karairaya da rangwaɗa,suna farfari da idanu wai da
sunan suna gaishe shi,tsabar dariya har tana riƙe ciki ganin yadda ko kallo biyu baiyi musu ba,ya
tsallake ya wuce part ɗin mum

Da sallama ya shiga ɗakin mum,ta ɗago tana kallon shi gami da amsawa,ya samu waje ya zauna
yana gaishe ta cikin girmamawa

Ta amsa fuska babu yabo babu fallasa,sannan ta ɗora da faɗin"ka kyauta Azad!ka nuna min iyaka
ta,na gode"

Azad ya ɗan jinjina kai ya na faɗin"ayi min afuwa mum,duk da ban san me nayi ba,na san ke mai afuwa ce a gare ni,kuma kin san ba zan iya jurar fushin ki ba"

Cikin ɗaga murya ta ce"asirin ka ne ya tonu Azad!ashe kai ka kai yarinyar can makaranta?na tsane
ta,amma ka kyautata rayuwar ta don kawai ka nuna min iyaka ta ko?to na gode"

Shiru Azad yayi,zuwa can cikin sanyin murya ya ce"na karbi laifi na mom,kiyi haƙuri,in Sha Allah bazan sake
makamancin hakan ba,ni yanzu na zo neman yafiyar ki ne zamu tashi zuwa Australia,ba zan so na
bar ƙasar nan kina fushi dani ba,ke mahaifiya ta ce,idan kuma Allah ya kawo min ajali kina fushi da ni
kinga shikenan mum"
Da sauri ta girgiza kai ta ce"ni ba haka nake nufi ba,Amma shikenan, Allah ya tsare,ka kular musu da
yarinya Azad,ka riƙe amanar aure,tabbas banajin ka, amma wannan rayuwar aure ce,ta bambanta
da rayuwar yau da kullum,ka riƙe haƙuri, Allah yayi muku albarka baki ɗaya"cikin sanyin murya ya
amsa da"ameen mum,na barku lafiya mum"ya miƙe a sanyaye ya fice

Can backyard ya koma ya kira khairi yace tazo inda suka haɗu jiya ta same shi,babu musu ta sanya
hijabin ta ta fita zuwa back yard

Tana ganin shi ta kama murmushi,shima murmushin yayi,tace"Good morning Yaya Azad!"

"Morning little sister,ya taro?"

Tace"ai kai za'a tambaya taro,ni kaga ban je ko'ina ba, kullum ina ɗaki na"

"Good!dama bana so ki rinƙa yawo,ki zauna ki karanta littattafan ki ya fiye miki zuwa ko'ina"

Tayi murmushi ta ce"yaya kayi kyau sosai da kayi aski,naji daɗi da ka girmama ra'ayi na,ina alfahari da kai"

Ya ce"good!ni dai yanzu zan koma Australia,Amma yanzu dawowa zatayi min wuya,tunda kin
ga na
fara tara iyali"
Khairi tana murmushi ta gyaɗa kai tace"hakane"
Ya ce"to don Allah abinda nake roƙon ki ki ƙara mayar da hankali kiyi karatu,ki bawa duk wanda yake
ganin bazaki iya ba kunya, watarana waɗanda sukeyi miki dariya da kansu zasu girmama ki,ki zamo abar alfaharin mu,kuma abar alfaharin albasu"
Khairi ta ce"nayi maka alƙawari yaya Azad,da yardar Allah sai na zama abar kwatance in Sha
Allah,inayi maka fatan alkhairi yaya na!"
"Yauwa little sister"ya zaro kuɗi mai ɗan yawa ya danƙa mata a hannu ya ce"gashi!duk lokacin da
kika buƙaci wani abu sai ki siya,na saka a siya miki corn flakes da madarar shi,da chaculate da
yawa"tayi ƴar dariya tace"na gode yaya,waye ya gaya maka ina son corn flakes?"

Yayi murmushi yace"ai ana kallon ki an ga chocolate da corn flakes "tayi dariya,ya ɗaga mata hannu ya nufi cikin gidan,itama ta rufa masa baya

Karfe goma na safiya jirgin su Azad da matar shi da ƙawayen ta da ƴan uwan ta suka ɗaga zuwa Australia,ita kanta mum ta ɗan tsorata da ganin yanayin matar ɗan nata da ƴan uwan ta da ƙawayen ta,Amma ta basar ta bi su da fatan alkhairi

Kwana biyu da tafiyar Azad daddy ya damƙa khairi a hannun aunty Naja'atu,aunty ta amshi khairi da hannu bibbiyu, ta buɗe mata dakin ta da daddy ya gama shirya mata komai

HOTORO GRA,KANO STATE, NIGERIA

Yau kwana uku da auren salis da Beely,tunda akayi auren samha ba ta ƙara ganin mijin nata ba,soyayyar su kawai suke sha shi da amaryar shi a part ɗin ta,samha tayi kuka har ta rasa hawaye,gashi gaba ɗaya ta bi ta firgice,ba maganar wanka ko wanki, ballantana uwa uba kwalliya

Yau kam da ƙyar ta tashi ta shirya wa Aman abincin da zai tafi makaranta,wanka ma tun jiya da tayi masa bata sake yi ba,gaba ɗaya dai gata nan gata nan ne tun da Beely tazo gidan,gashi kowacce a cikin su part ɗin ta dabam

Salis ne yayi sallama ya shigo parlourn nata inda take zaune zuru bayan ta sallami Aman ya tafi makaranta,ta zubawa TV idanu tana kallon cartoon da ake haskawa a MBC 3 duk da babu abinda take ganewa saboda tunani,tayi firgigit ta amsa sallamar tana kallon shi,ya shigo yana ƙarewa ko'ina kallo fuska a yatsine

Itama a yatsinen take kallon shi,cike da fushi da tsana,cikin rashin damuwa ya ce"na same ku lafiya?"

"Cikin muryar kuka tace"kaso ka same mu lafiyar ne?"

Girgiza kai yayi yana ɗaga mata hannu fuska a ɗaure ya ce"kema ba sai an gaya miki ba,yanzu bani da lokacin shirmen ki,don Allah kalli ɗakin ki,kaca kaca kamar wajen kiwon dabbobi "

"Zakace haka mana tunda kayi aure,auren ma na cin amana,kuma idan kiwon dabbobin akeyi to ai alhamdulillahi,tunda dukkan mu dabbobin ne,har kai"shi dai bai sake magana ba ya juya ya fice,sai da ya kai bakin ƙofa sannan ya leƙo ya kalle ta cikin idanu yace"rabon kwana zai fara ranar da kika koyi gyara waje,don yanzu nayi wayon da nafi ƙarfin kwana a cikin ƙazanta"bai jira amsar ta ba ya fice da sauri

Yana jiyo muryar ta cikin kuka tana farfaɗa masa maganganu amma yayi banza da ita ya koma wajen amaryar shi da ta sha gayu cikin wasu arnan ƙananan kaya farar riga da wani wando bai fi rabin cinyar ta ba ash color,gashin ta kuwa ta sake shi baya,ta daure shi da ash color ribbon,yana shigowa ta maƙale shi ta fara aika masa da kisses,ya riƙe ta yana mata responding ya ɗora ta akan cinyarshi,suka zauna akan doguwar kujera suna ta shan soyayyar su

Samha ce ta bankaɗo ƙofar parlourn,da sauri suka daga kai suna kallon ta, ganin itace ma Beely ta sake narkewa a jikin salis, Salis ya dube ta da daurewar fuska ya ke faɗin

"Samha wanne kalar shirme ne wannan?ko kin fara shaye shaye ne?"

"Kurɓe kurɓe na fara!"ta bashi amsa cikin ɗaga murya,"kai yanzu bakaji kunya ba Salis?ko kunyar zalunci da nuna bambanci bakaji ba? wallahi muddin ka cigaba da tafiya a haka tashin hankali yanzu za'a fara shi a gidan nan!!"a nutse ya kalle ta yace"samha fice min daga nan"

"Bazan fita ba azzalumi!kazo ka fitar dani "bai sake kallon ta ba ballantana yayi mata magana, Beely ta kuma haɗe bakin su tana wani narke fuska,samha ta fice daga parlourn da gudu tana gunjin kuka

BRUNSWICK, MELBOURNE, AUSTRALIA

Yau kwana huɗu kenan da kai fadeela da Azad, tun a washegarin da suka sauka a ƙasar ƙannen mum biyu da suka tafi tare da wasu daga cikin ƴan uwan amarya suka tafi,amma ƙawayen amarya har yau dai suna nan,shi dai Azad sai dai yayi kwanan hotel kawai,don bazai iya kwana gida ɗaya da ƙawayen amaryar nan ba

Yau kam ya gaji,don haka ya kira mum ya shaida mata,mum tace zatayiwa hajiya A'isha magana

Bayan sun gaisa mum tace"ni kuwa hajiya kina da masaniyar ƙawayen amarya sun hana Azad sakat a gidan shi? sai dai ya kama hotel ya kwana fa,wanne irin shiririta ne ya sa har yanzu basu dawo ba?"

Hajiya A'isha ta yamutsa fuska tace"to fa!kuruciya,zanyi musu magana,zasu dawo,daga haka ta kashe wayar ta tana jan tsaki

Kai tsaye fadeela ta kira ta isar mata da saƙon, fadeela ta ɗaure fuska tace"ita ga mai ɗa,ai shikenan sai su tafi ɗin"Hajiya A'isha tace"ki dai bi a hankali surukar ki ce


Yacin mum kin ɗauko iyakar Azad 🥺

#likecommentshare

#Nusy_bee

Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee

*Young talented writers association (YOTA)*

Page 23


Fadeela tayi tsaki ta ce"momy kin san matar nan kin san halin ta,ba mutuniyar kirki bace, gaskiya ni dai idan na ga zata kawo min wargi ba zan ɗaga mata ƙafa ba

Ji wani abin haushi don Allah,ni na yi masa laifi amma ko a fuska bai nuna ya ji haushi ba shine har da kiran wannan tsigalalliyar uwar tashi,ni dai wallahi bazan ɗauki shirme ba,haba!sai kace wani yaro?"

Hajiya A'isha ta ce"ke kuma kinga matsalar ki kuma,daga zuwa za ki fara gwada hali,ku sallame su su tafi ɗin,ai ba wani abu bane, fadeela sai anyi haƙuri fa,zaman aure sai da haƙuri "

Fadeela ta ja ajiyar zuciya ta ce"shikenan momy,sai sun taho"momy tace"to Allah ya kawo su lafiya "sukayi sallama

Ranar da yamma suna zaune tare da ƙawayen nata a parlour,tukunyar shisha ce a tsakiyar su suna ta zuƙa,sai dai banda ita da wata ƙawar su Hafsy,ita fadeela danna wayar ta take yi,ita kuma Hafsy coffee ɗin da ta haɗa take sha, su kuma ragowar ƙawayen nasu su biyar sun saka shisha a gaba suna ta bulbula hayaƙi,sun tirniƙe parlourn

Sam Azad bai san abinda akeyi ba ya danna kai cikin parlourn da sallama,tari ne ya sarƙe shi ya juya ya bar parlourn da sauri,suka bi shi da kallo kawai, ɗaya daga cikin ƙawayen nata Seema tace"babe duba mijin naki mana,na ga ya fita somehow"fadeela ta miƙe babu musu ta nufi entrance ɗin gidan

A can ta ganshi a durƙushe riƙe da inhaler a hannun shi yana shaƙawa,bin shi tayi da kallo kafin ta ce"dama ba ka da lafiya ne?"

Bai bata amsa ba sai daidaita zaman shi da yayi ya na mayar da numfashi,ta taɓe baki ta ce"to Allah ya kyauta, Allah yasa dai ba jinya na zo yi ba,na taimaka maka ka koma ciki?"

Nan ma dai shiru babu alamun zai tanka,idanun shi ma wani wajen suke kallo,ta taɓe baki ta ce"to Allah ya sauwaƙe"ta juya ta shige ciki,ta bar shi da bin ta da kallo,a hankali ƙwalla ta ciko idanun shi tuna wai mahaifiyarshi ce ta zaɓa masa wannan a matsayin matar aure,bai san dalilin mom ba,amma shi kam yasan baiyi Sa'a ba

Daga baya ya kira ta ya sanar da ita ya siya wa ƙawayen nata ticket na tafiya Nigeria,yana gama magana ya fice ya bar gidan

Da wajen ƙarfe bakwai na dare da kanshi yazo ya kwashe su zuwa airport,a mota Hafsy da ke zaune a gaba ta kalle shi ta ce"Hi!"

Bai kalle ta ba ya ce"welcome!"tayi wani murmushi irin na ƴan duniya,da dabara tana turo kirji tana kaɗa idanun ta ta ce"I'm Hafsa Usman maitama,mahaifi na shine current Minister of housing and estate,you?"

Shiru babu amsa,ta kuma yin wani murmushi irin na ƴan bariki tace" I really like classic guys, please can we be friends?"nan ma ba amsa,ta ƙara yin murmushi,tsadaddiyar wayar ta ƙirar iphone ta daddanna,ƴan seconds kaɗan sai ga wayar shi ta na ƙara,ya ɗaga wayar yana kallon sabuwar number ɗin da take ringing,tayi ɗan murmushi ta ce"number na kenan,zamu yi zumunci mu zama friends"ta katse kiran,jiki a sanyaye ya ajiye wayar shi gaba ɗaya jikin shi kamar an zare masa laka

Sai da yayi musu komai sannan yayi musu sallama ya koma wajen motar shi,yana shirin buɗe motar yaji an manna masa kiss a Kumatu,da sauri ya juyo ya hankaɗe Hafsy da zuwa yanzu ta fara ƙular dashi, maimakon taji haushi sai gani yayi ta na murmushi,ta ce"komai naka kyau gare shi,fushin ka kyau ne dashi,you are really true definition of handsome man,aminiya ta tayi dace,much love!"tayi masa blow kiss sannan ta juya ta koma departure lounge inda su Seema ke zaune,ta bar shi da bin ta da kallo kamar soko ya na jinjina wannan abu da shi duk marasa kunyar da yake gani bai taɓa ganin ƙwararru irin waɗannan matan ba

BOSTON, MASSACHUSETTS,USA

Auwab ne zaune tare da mr Johnson Philip da Mr mike Anderson suna tattaunawa akan harkar Kamfanin su,a harabar gidan nashi,daga balcony kuwa Inaaya ce ta na ta leƙo su fuskar ta a haɗe,tun ɗazu suke meeting sama da awa biyu har yanzu basu gama ba,dole ta tsaya ta na jiran su gashi sun ɓata mata lokaci

Ganin ba zasu gama ba ya sa ta ja tsaki ta fice,ta gaban su ta wuce ta fice zuwa inda motar ta take,don haka ya nemi excuse a wajen su ya tashi ya nufi inda take

Yana zuwa da ɗan murmushi a fuskar shi ya ce"ya dai baby luv?"

Cikin shagwaɓa ta ce"su waye waɗannan?basu san ni matar ka bace suka ɓata min lokaci suka hana ka zuwa gare ni?"

Yayi murmushi sosai yace"ki daina ɓata min ranki sweetheart, I'm yours alone,babu wanda zai shiga tsakanin mu, for now dai we are discussing about something very serious,kije school,in sha Allah kika gama lectures da kaina zan zo na ɗauke ki na mayar dake gida"tayi murmushi ta na kallon shi da sexy eyes ɗin ta,ta ce"I love you!"

"Love you more!take care of yourself please!bye!"suka yi sallama ya koma cikin gidan

Yau bikin su saura sati tara,shirye shiryen jarrabawa su Inaaya suke yi,suna hutu kuma zasu koma Nigeria,a wannan hutun ne zasu zama mallakin juna

Bayan Inaaya ta gama lectures ɗin ta ta dawo inda auwab yake zuwa ya ɗauke ta ta zauna tana ɗan danna wayar ta,taji an dafa kafaɗar ta

Waigowa tayi da sauri da mamaki ta na kallon shukra,Shukra tayi murmushi ta na faɗin "yeah I'm the one babe,ya studies?"

Inaaya tayi murmushi tace"normal,ya hanya?"

Shukra ta zauna gefen ta ta na faɗin "lafiya lau, amarya bakya laifi!"

Murmushin ƙasaita tayi tana kallon Inaaya tace"muna gama exam zan ƙarasa mallake auwab,ji nake yi kamar na janyo ranar"

Shukra tayi murmushi ta ce"yeah babe!but ya zaki yi da Safwan?You know bazai iya enduring rasa ki ba,asalima kin zama rayuwar shi"

Inaaya ta yatsina fuska tace"kuma ya kamata yayi haƙuri don mallakin wani zan zama,bana so ma ya san da cewa zanyi aure,so nake na ɓace daga duniyar shi farat ɗaya"

"Wai dama ba son shi kike ba?"

"You know everything shukra!ban taɓa son wani namiji ba, Safwan ma rage min zafi kawai yake yi, shi yasa na ɓata lokaci akan shi,amma yanzu magana ta ƙare "

"Amma bakya tunanin zai san komai?"a cewar shukra

Inaaya ta ce"ko ya sani hakan ba amfani zaiyi masa ba ai tunda zan zama ta wani"

"Noooo Inaaya! Safwan yayi miki halacci sosai a rayuwa,meyasa bazaki rama masa ba?"

Inaaya ta kalli Shukra da alamun tambaya, Shukra ta gyara zama tace"I mean,ko da auren dake tsakanin ku da masoyin ki ya kamata ace baki yar da zumunci da Safwan ba,don bai cancanta kiyi masa hakan ba"

Wani kallo Inaaya tayiwa Shukra kafin tace"I can't get you!ki fito fili kiyi min bayani yadda zan gane"

Shukra tayi murmushi ta ce"yanzu menene ribar ki idan kika watsar da Safwan?"

"Saboda a yanzu aure zanyi,duk irin wannan rayuwar ya kamata na daina ta"a cewar Inaaya

Shukra ta girgiza kai ta ce"har yanzu da sauran ki a wayewa kenan,to bari kiji,duk macen da kika ga tana rayuwa cikin kwanciyar hankali a wannan zamanin to ta na da mai rage mata zafi,da wahala kiga namiji ɗaya ya ishi mace"

"Ban gane miki ba shukra!to idan asiri na ta tonu fa?miji na ya gane ina cin amanar shi?


Kema dai kya tambaya,mutanen wofi kawai🤧

#likecommentshare

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️ Nusy bee

*Young talented writers association (YOTA)*


Page 24


Shukra ta ce"ai ba cin amana ba ne,kula da kai ne, shima bai zama lallai kan ki kaɗai ya tsaya......"

"Hold it Shukra!miji na ni kaɗai yake so,ba ya bin mata,ni dai yi min bayani idan asiri na ya tonu fa"

"Asirin ki ba zai tonu ba zamu je wajen boka ya mallake miki zuciyar shi,zai nuna miki so fiye da yadda ki ke gani,bazai taɓa ganin laifin ki a komai ba,zai ji maganar ki fiye da uwar da ta haife shi ma"

Inaaya ta kaɗa kai tana faɗin "ai kuwa zan so hakan,don naji an ce mahaifiyar shi shuwa ce,kin san sun san ta kan......."kasa ƙarasawa ta yi saboda hango motar Auwab,ta ja baki ta yi shiru ta na kallon shi,itama Shukra motar ta ke kallo har ta ƙaraso in da suke

A mutunce suka gaisa da Shukra da ta ke ƙare masa kallo a kaikaice,bayan sun gama gaisawa Inaaya tavna murmushi ta kalli auwab tace"meet my friend Shukra, Shukra meet my husband Auwab"Shukra tayi murmushi,a ranta ta ce"ai kya bari a ɗaura kafin ya zama mijin naki uwar kankamba"a fili kuwa cewa tayi"congratulations for having my friend as wife,she is very nice,ina fatan zaka kula min da ita,she loves you"

Ya yi ɗan murmushi ya ce"of course,and I love her too "ya kalli Inaaya ya ce"can we?"

Inaaya ta miƙe tsaye ta na faɗin"see you soon babe, bye!"ta ja hannun Auwab su ka bar wajen batare da ta sake yiwa Shukra ko da kallon banza ba,sai da Shukran ta janye ƙafar ta ma da ta kusa taka wa


Shukra ta bi su da kallo,kafin tayi wani murmushi da ita kaɗai ta san ma'anar abin ta ta miƙe ta bar wajen


LUGARD ROAD, NASSARAWA GRA,KANO STATE


Yau ya rage sati ɗaya khairi ta koma makaranta,ta sake sosai yanzu, saboda babu abinda ta nema ta rasa a wajen aunty Naja,duk da cewa idan jarabar mom ta motsa har part ɗin aunty Naja'atu take zuwa tayi ta mata tijara,amma ko sau ɗaya bata taɓa ɗaga kai ta kalle ta ba,dama khairi tana jin ta fara hayaniya zata shige ɗakin tayi muƙus har sai ta fita,yaran mom kuwa sai tafi sati bata gan su ba

Yau ma ta na ɗaki tana ta karatun da bata rabo dashi,zuwa can ta yi tunanin ta ɗan leƙa Whatsapp,ta janyo wayar ta ta hau Whatsapp,ta na shiga taga message ɗin nabeela Saleh

"Khair albasu kin ɓuya ko ɗuriyar ki ba'a ji"

Murmushi ta yi ta bata amsa"ina nan beela Saleh,ya gidan,kuma ya hutu?"

"Wayyo khair I'm enjoying my holidays,ga yaya Hisham,ga Daddy ga kuma fadwa"

"Congratulations!ni kam kina jin motsin amra?"

Nabeela tayi mata voice ta na dariya ta ce"last week mun haɗu da ita a Lagos da muka je,wai the holiday is so boring,mum ɗin ta ta cika saka ta aiki"

Khairi ta yi dariya itama tayi voice ta ce"ai dama kin san ko a school Amra ta fi gane surutu babu aikin da ta ke yi, whatever!hutu dai ya kusa ƙarewa,na yi missing ɗin ku ku duka,nayi missing school"

Nabeela ta ce"tabɗijam! I'm enjoying my holidays,no need of missing school "khairi tayi dariya tace"oh dai,dole mu dawo school next week"haka suka yi ta tsokanar juna kafin su yi sallama

Aunty Naja ce tayiwa khairi shopping yayin komawa makaranta,sai murna khairi ta ke yi zata koma Cikin aminan ta,ranar da zasu koma Daddy da kanshi ya mayar da ita,yayi farin ciki sosai ganin yadda ta sake,ya shaida mata shima next week aunty Naja za ta raka shi Mexico,ta yi musu fatan zuwa da dawo wa lafiya

Har cikin makaranta ya kai ta,suka rabu cikin kewa ta na ɗaga masa hannu ya na ɗaga mata

Ita ce ta fara zuwa,bata daɗe ba Amra ta ƙaraso,haka sukayi ta tsallen murna suna rungume juna,suna ta shiriritar su beela ta shigo,suka hadu suna ta shirmen su cike da farin ciki, kowacce na bada labarin gida


HOTORO GRA, KANO STATE, NIGERIA


"Wai ko ba mutane a gidan ne?"a cewar matashiyar matar wadda bata wuce sa'ar matan gidan ba

Yatsina fuska ta yi ta na bin gidan da kallo kafin ta taɓe baki ta shiga parlourn samha

Ta yi matuƙar mamakin ganin samha a zaune tayi tagumi,ta zurfafa a tunani,ta ɗaga murya ta ƙwala ma ta kira"Samha Hussain!"

Firgigit ta yi ta na jan ajiyar zuciya ta na kallon ƙawar ta ta da mamaki,kafin tace"Farida kece?long time!dama ki na nan?"

Fareeda ta ɗan taɓe baki ta na gyara mayafin jikin ta ta samu waje ta zauna ta na kallon samha da take ƙare mata kallo da mamaki, fareeda ta kalle ta ta na buɗe idanu ta ce"baki iya tarbar baƙi bane madam?"

Ajiyar zuciya Samha tayi ta na ɗauke kai, fareeda tayi mata kallon tsaf kafin ta ce"ko har yanzu zafin kishin ne bai sake ki ba?naji wai an ce mijin ki ya auri Bilkisu Umar"

Hawaye suka zubowa Samha,ta girgiza kai tace"mhm!bari kawai fareeda!You know how I love my husband,haka nake kishin abu na,amma wai yayi min kishiya,kishiyar ma wai da Bilkisu Umar? imagine Bilkisu Umar fa!my best friend,Banda tafiyar ta turkey ba tare zamuyi tertiary institution ba?na yarda da ita,na bata dukkan yarda amma ta aure min miji saboda cin amana!"

Fareeda ta yi ɗan murmushi ta na girgiza ƙafa,ta dubi Samha tace"shiyasa tuntuni yarinyar batayi min ba,bama shiri,ga ta da jiji da kai ita ƴar masu kuɗi,ga wulaƙanci da rainin wayo,amma za mu yi maganin ta,da zan baki shawara ki ɗauka da komai yayi mana kyau,komai zai tafi da sauƙi,sai mu aiwatar da nufin mu cikin kwanciyar hankali, Yanzu dai,za ki yarda muyi waje da ita ko zaki cigaba da riƙe amanar ƙawancen ku?"ta ƙarashe ta na yi mata wani kallo a yatsine

Samha ta harare ta ta na faɗin "wanne ƙawance?ai yanzu ni da Beely abokan gaba ne,akan miji na babu da wadda bazan rabu ba wallahi"fareeda ta yi murmushi irin na cin nasara,dama fa ita ta tsani tarayyar Beely da Samha, saboda haushin Beely da take ji wadda bata kula mutane sai waɗanda taso,sannan kuma ko a lokacin su Beely ta fi su wayewa, kyau da kuɗi,hatta ƙoƙari a aji Beely ta fi ta,gashi ita kuma ba ta yi wa Beely ba


HAƊEJIA ROAD, KANO STATE, NIGERIA


"Ammi wai yaushe big bruh zai dawo ne?sai shirye-shirye akeyi amma babu shi"

"Kun fi kusa,ka kira shi a waya mana,mene ne na tambaya ta?"

Sulaiman ya yi murmushi,ya kwanta a kan doguwar kujerar da yake zaune ya ce"na kira shi,amma ce min yake yi kawai very soon"

Ammi tace "ya kusa dawowa ai,maybe next week "

Sulaiman yace"to Allah ya nuna mana"

Amra da ke shigowa yanzu ta ƙaraso da gudu ta na murmushi ta na faɗin"ameen yaya,na matsu ayi biki a gidan mu mu ma,mu sha shagali "

Sulaiman yana murmushi ya ce"Ammi kinji dai da kunnen ki tana gaya miki ta matsu ayi bikin ta "

Ammi ta yi ƴar dariya, Amra ta yi ɗan ihu ta na toshe baki,cikin shagwaɓa ta ce"haba yaya!ni fa Allah ba haka na ke nufi ba,don Allah ni kar ka kai ni inda Allah bai kai ni ba"

Ya kalle ta ya ce"to tunda kina son ayi biki a gidan nan meyasa ba zaki saka Khaleel ya turo ayi a gama ba?"

Amra ta haɗe rai ta na yatsina fuska ta ce"wato kai ka bar aunty mifra ta kammala karatun ta,Ni kuma ka bani gurguwar shawara na katse nawa ko?"

Sulaiman ya yi dariya ya ce"na ji mashiririciya,ina autar Ammi?"

"Auta ta tafi kai ɗinkin kayan fitar bikin ta,za ka iya ganin ta ma kowanne lokaci"

Ya miƙe tsaye ya na faɗin "to Allah ya dawo da ita lafiya,bye Ammi"

Ammi ta yi murmushi ta ce "bye"ya fice daga parlourn

Shirye-shiryen biki ya kankama sosai,ammi ta aika wa mum da katin gayyata,duk da cewa barrister Umar dole zai gaya mata,dama sulaiman ne ya kai katin, Allah ya so bata nan taje kasuwa,ya bawa Ma'aruf katin tayi tafiyar shi


Sai da ke mum tamu ta gargajiya 😂kowa ma tsoron ki yake ji


Yau ma ga posting biyu nan, saboda naji daɗin likes ɗin nan😁

#likecommentshare

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy_bee


*Young talented writers association (YOTA)*


Page 25


Ana i saura sati biyu bikin Auwab da Inaaya suka sauka a Nigeria,dukkan su cike suke da farin ciki, Auwab har gida ya kai Inaaya sannan ya wuce gida

Sulaiman ne ya kira khairi ya ke gaya mata auren,khairi ta taɓe baki ta ce"Allah ya sanya alkhairi"

Sulaiman ya ce "ameen!na zo na ɗauke ki jibi ko l?"

Khairi ta ɗan buɗe idanu ta ce"ka kai ni ina?"

Ya ce"na kawo ki gidan biki mana,bikin yayan mu na biyu za'ayi fa"a ranta tace"sai dai yayan na ku dama"a fili kuma ta ce"yaya sulaiman kaga ban daɗe da dawo wa makaranta ba,abin zaiyi wani iri ace na fara komawa gida"sulaiman ya yi murmushi kawai,shi fa ya daɗe da gane Auwab ba wani burge khairi yake yi ba,yace"shikenan, Allah ya taimaka,maybe watarana ki ga amaryar idan kika je Massachusetts"

"Ina kace?"ta faɗa ta na yatsina fuska kamar ya na gaban ta

Yayi dariya ya ce"Massachusetts state!garin da Auwab ya ke da zama,inda zai zauna yanzu da matar shi"

Khair ta jinjina kai ta ce"kuma a Nigeria ya ke?"

"A'a a ƙasar America yake"

Khairi ta taɓe baki tace"to ni mai zai kai ni can?"

Sulaiman ya yi ɗan murmushi ya ce"babu komai,kawai ziyara"khairi tace"taɓ!yaya sulaiman sai an juma"ba ta saurari maganar shi ba ta kashe wayar ta na jin haushin ya so ya ɓata mata mood da batun wannan mutumin kawai ɗin,a cewar ta

Murmushi ta yi ta na tuna yayan ta,ko a wanne hali yake?kwana biyu fa rabon su da waya ko chat,don haka ta ɗauki wayar ta ta fara daddanna wa ta na neman number ɗin shi, fuskar ta ɗauke da murmushi


BRUNSWICK, MELBOURNE, AUSTRALIA


Yau tsawon sati Uku kenan da auren Azad da fadeela,gaba ɗaya ya rame,ko ƙaunar shigowa gidan yaga amaryar tashi baya yi

Tun a ranar su ta farko fadeela ta nuna masa ƙarara ta san maza,ya ji ciwon hakan sosai,amma sai ya bar shi a zuwan tunda ta yi aure yanzu zata gyara,komai zai wuce,za ta shiryu ta tsaya a kanshi kawai

Amma sai ga ɗabiun da suka shallake kanshi, Azad mutum ne mai matuƙar tsantseni,gashi ba shi da son kwaramniya sam, dalilin haka ma bai cika tara shirgin abokai ba,ba shi da fara'a,wannan yasa akeyi masa kallon mutum mai girman kai

Ba ya taɓa barin Nigeria zuwa wata ƙasar sai da ƙwaƙwƙwaran dalili,amma a yadda ya fuskanci fadeela Melbourne ba baƙuwar ta bace, kullum tana hanyar zuwa park ko dai wani wajen na shaƙatawa

Amfanin Azad ɗaya ne a wajen ta,shine muamalar aure,idan ya nuna ba ya ra'ayi ya na shan cin mutunci da rashin mutunci da wulaƙanci a wajen ta,Azad bai taɓa ɗaga kai ya kalle ta ba,don yasan alhakin mahaifinshi ne ya faɗa masa,a matsayin shi na ɗan da mahaifiyar ta su ta ɗorawa soyayyar duniya fiye da sauran yaran ta,don haka yake karɓar sakamakon abinda takeyiwa mahaifin shi

Babu ruwan ta da shara,ko wanke wanke, mopping ko girki,baya ce mata ma ballantana har ta kai ga tashin hankali,tunda ya gwada ce mata ta yi ta ƙi yi tayi ta masa masifa shikenan ya daina sanya ta,idan ya na da hali yayi da kanshi,idan ba shi da hali ya bar shi

Kiɗa kam babu kalar waƙar da ba ta ƙurewa volume a home theater tayi ta rawa tana bi,wani lokacin ma har da ƙawayen ta turawa da sukan zo akai akai, Azad babu abinda ya tsana kamar hayaniya,don haka wani lokacin ma baya kwana a gidan

Amma kullum cikin zargin shi take yi musamman ma idan yana waya da mace,idan bai kwana a gidan ba kuwa tuhumar shi take yi kamar wani ɗan ta,don ma idan tana masifar ta banza yakeyi da ita ko ya fice daga gidan

Yau ma yana ɗakin shi yana wanka a banɗakin cikin ɗakin shi,wayar shi ta na kan dressing mirror ta yi ƙara,daidai lokacin fadeela ta shiga ɗakin,su lokacin dare ne,a nan Nigeria kuma rana ta fara yi

Ta sha wasu tsinannun sexy nighties, attachment ɗin nan an sake shi baya,ta ƙarasa gaban dressing mirror ɗin inda taji wayar tashi ta na ta ruri ta duba mai kiran

'little sister ' taga ya na haskawa a kan screen ɗin, wani kallon banza tayiwa wayar,a ranta tana faɗin "waɗannan tsinannun ƴan uwan nashi sai na raba su ɗaya bayan ɗaya,don babu wata ƴar iska da ta isa ta shiga tsakani na da miji na"batare da tunanin komai ba ta ɗaga wayar ta kai kunnen ta

Daga ɗaya bangaren khairi tace"babban yaya na! I miss You so much babban yaya!"

Shiru fadeela tayi kafin tace "wacece?"

Gaban khairi ya ɗan faɗi,amma sai tace"khairi ce"

"Wace ce khairi?"

Shiru khairi ta yi jin yadda matar ta yi magana a ɗan fusace,cikin sanyin murya khairi ta ce"ni ƙanwar shi ce"

"Au da gaske?dama bayan Nusra da feena da Beely ya na da wata ƙanwar ne?"

Shiru khairi ta yi bata ce komai ba, fadeela ta ce"ki ce min ke karuwar shi ce dai ko?ƴar iska asararriya,masu bin mazan mutane,idan na sake......."

Bata samu damar ƙarasa wa ba saboda fizge wayar da akayi,da sauri ta juya ta na kallon Azad da yake ta faman huci

Kallon shi ta ke tsaf,ya ɗora wayar a kunne,a nutse ya ce "I will call you back!"ya kashe wayar ya mayar da idanun shi kan fadeela yana yi mata wani irin kallo

Itama kallon shi take yi cike da mamaki,kafin ta ce

"Who is she da har zaka zo ka na ƙoƙarin hargitsa min kai a dalilin ta?wacece ita?mene ne alaƙar ka da ita?"

"Daga rana irin ta yau,daga yau ɗin nan,a nan ɗin nan,nan wajen,na yi miki iyaka da waya ta,na shata miki layi da ita,You have to take this as last warning, don't let me repeat myself!"ya faɗa yana kaɗa babban yatsan shi da ɗan tsakiya a fuskar ta

Wani kallon sama da ƙasa tayi masa kafin ta ce"warning kake yi min akan wata wayar ka? saboda baka da gaskiya?"yayi mata banza ya fara shafa mai a jikin shi

"Okay!you made it clear!yanzu na gane!wato saboda karuwar ka ta ....."

"Fadeela!!!"ya daka mata tsawa,jikin shi har karkarwa yake yi,idanun shi da farar fuskar shi sun kaɗa sun yi jawur saboda ɓacin rai

Tsananin mamaki ya ƙamar da fadeela,wai Azad, Azad dai da ta sani yake daka mata tsawa kamar wata ƴar shi ko baiwar shi,bai kula ba ya ci gaba"kar ki sake kiran khairi karuwa,don ita ba karuwa bace,ki fara sanin wace ce ke tukunna kafin ki nemi aibata wasu"

"Azad! Azad what are you trying to say?"ya ci gaba da abinda ya ke yi ba tare da ya sake kula ta ba

Babu abinda yake mata ciwo kamar irin shariyar da Azad yake yi mata,a taƙaice ma,ɗabi'ar da ta zame masa jiki ce muddin ta na yi masa maganar da bata yi masa ba,a fusace tace"to na faɗa,karuwa!karuwa!!kilaki!!!waye ya sani ma ko karuwar ka ce,ƴar akuya kawai mai kiran mazan mutane da.........."tuni ta yi shiru saboda marin da Azad ya sauke mata a tsananin fusace,kafin ta dawo hayyacin ta ya sake sauke mata wani,sannan ya hankaɗa ta waje ya mayar da ƙofar ya rufe ya koma gefen gado ya zauna ya na mayar da numfashi

Haki ne ya taso masa sosai,da sauri ya lalubo inhaler ɗin shi da a yanzu baya taɓa rabo dashi,ya ɗauko ya buɗe yana shaƙa,ya kai kusan mintuna biyu a kwance ya na mayar da numfashi kafin ya miƙe ya ciro pyjamas ɗin shi ya saka,ya koma kan gadon shi ya kwanta ya na sauraren yadda fadeela ke ta dukan ƙofa tavna zagin shi tana ci masa mutunci,har ta gaji ta bar wajen ta na ta zage zage

Ƙwalla ta cika idanun Azad,a sanyaye ya janyo wayar shi ya kira mum,a lokacin ta na kwance a ɗakin ta abin duniya ya yi mata yawa,sunyi hayaniya kaca kaca da daddy ya ɗauke amaryar shi sun bar ƙasar,haushin abinda tayi wa daddyn ya saka feena ta koma hostel da zama,Nusra kuma ta koma Yola, Ma'aruf da haidar ma suka bar garin zuwa Kaduna gidan yayan ta

Ta na cikin damuwa sosai saboda a yanzu babu wanda ya ke zaune kusa da ita,gashi yanzu duk hayaniyar da za ta yiwa Daddy ba zai saurare ta ba, ballantana kuma aunty Naja da ko kallon ta bata yi,yanzun ma hawaye take share wa kiran Azad ya shigo mata

Dama ringtone dabam ta saka wa Azad,tana jin ring ɗin tayi murmushi ta na janyo wayar,tana matuƙar ƙaunar Azad saboda kaf yaran ta ya fi yi mata biyayya,kuma ya na matuƙar ƙaunar ta,ta ɗaga ta kara a kunne ta na yin sallama

Shiru ya yi da farko,a hankali tace"son!"

"I love you mum!"ya faɗa hawaye na zubo masa,wani irin rauni ya shige shi jin muryar mahaifiyar tashi

"I love you more son,and I hope everything is moving smoothly"

Ɗan murmushi ya yi ya na goge hawayen idanun shi yace"alhamdulillahi mum,nayi missing ɗin ku sosai,mum ya mutanen gidan?"

Dama abinda ta ke so kenan,cikin rawar murya tace"komai babu daɗi son,yara duk sun guje ni saboda daddyn ku,sam ba sa tausaya min abinda akeyi min,haushi na suke ji,duk sun bar gidan ba tare da sun yi min sallama ba, Bilkisu kuwa sai tayi kwanaki ko a waya ba ta neme ni ba"

Abinka da ɗa da uwa,sai tausayin ta ya kama shi,cikin kwantar da murya yace"mum ki yi haƙuri,ki daina saka damuwa irin haka a ranki,ki rage sanya abu a ranki,idan wani ciwo ya kama mum mu zamu shiga damuwa,ko mutuwa kika yi mune muke da asara, Daddy zai iya chanja mata,amma mu ba zamu iya chanja uwa ba, please mum!"

Cikin kuka ta ce"son kai kaɗai ka damu dani,su feena ma duk sun guje ni,kowa haushi na yake ji"

Ya dafe kanshi ya na runtse idanu,kafin ya ce"mum we all love you,babu wanda zai iya gudun ki,maybe ba sa son ganin ki cikin ɓacin rai ne kawai,but trust me,muna matuƙar ƙaunar ki mom"ta share hawayen ta tace"to shikenan,yaushe zaka kawo mana ziyara?"ya yi ɗan murmushi yace"very soon heart beat,just relax and erase everything in your mind, I'm with you my world"yayi mata kiss ta cikin wayar,tayi murmushi,tuni ta ji ɓacin rai da damuwar ta suna kwaranyewa,cikin kwantar da murya ta ce"take care of yourself son,ka gaida iyalin taka"

"Za taji mum,bye!"ya kashe wayar,shima ya na ɗan jin relief a zuciyar shi

Number ɗin khairi ya lalubo,ya na ganin number ɗin ya yi murmushi,ya yi missing ɗin ta sosai,don rabon su da ita tun rabuwar su lokacin bikin shi

Bugu biyu ta ɗaga ta na faɗin "babban yaya!"

Ya lumshe idanu ya buɗe ya na murmushi ya ce"Dr khairi!"

Ta yi murmushi ta ce"ina kwana"

Ya ce"lafiya lau,amma mu nan ba kwana ba ne"ta yi ɗan murmushi ta ce "ikon Allah kenan!"

"So now,ya makarantar?"

"Makaranta alhamdulillahi,karatun ya na zuwa min yadda nake so sosai"

Azad ya ce"to Allah ya taimaka,your previous result appreciate me sosai, Please I want you to keep it up, I want you to continue how you start,soon sai kiga kin zama the best doctor in the whole Nation "

Murmushi tayi cike da jin daɗi ta ce"ai kuwa zan ƙara dagewa yaya na, na gode.....ya katse ta da faɗin "and..... I'm sorry for what my wife did to you"

Shiru tayi, Azad ya ce"kiyi haƙuri,don Allah komai ya wuce anan"

"Yaya komai ya wuce,ni fa ban ɗauki issue ɗin wani abu ba"

"Good girl!yanzu me kike yi?"

"Yanzu mu ka fito a Library,anjuma kuma zamuyi karatun islamiyya tunda yau asabar "

"Okay,ni yanzu bacci zan yi,sai in ce sai da safe?"

"To yaya,kayi addu'ar kwanciya bacci"

"Ni ban iya ba ai"

"To zan turo maka ta Whatsapp, zan yi maka voice"

Ya yi murmushi yace"to ƙanwa ta,na gode,ayi karatu da kyau,bye!"suka yi sallama ta kashe wayar

Washe gari da safe da safe kiɗa ne ya tashe shi daga barci,ta ƙure waƙar marhaba ta kizz Daniel,shiru ya yi a zaune ya na kallon windon ɗakin,amma a zahiri kawai ya ke kallon windon,ya lula duniyar tunani,duk da kasancewar ya yi waya da mum da khairi ɓacin ran fadeela bai bar shi ba,baiyi bacci da wuri ba,da ƙyar bacci ya sace shi har hakan ya janyo masa makara sallar asuba,kuma ya tashi ya fara karo da wannan shaiɗancin

A hankali ya girgiza kai zuciyar shi kamar ta fashe saboda baƙin ciki,ya sauko daga kan gadon shi ya faɗa banɗaki yayi wanka ya ɗauro alwala ya zo ya sanya jallabiya ya shimfiɗa abin sallah,bayan ya idar ya shirya cikin wata tsadaddiyar suit blue Black,tayi matuƙar hawa da farar fatar shi,ya feffesa turarukan shi masu tsada,ya ɗauko brief case ɗin shi ya fito zuwa parlourn

A zaune ya ga fadeela sanye da wata farar ɓingilar riga da ɗan ƙaramin wando da ko rabin cinya bai kai ba brown, attachment ɗin nan ya sha ribbon an sake shi baya

Kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kai ya cigaba da tafiya,sai jin takun ta ya yi da sauri,kamar kar ya waiga,sai kuma ya waiga,daidai lokacin da take watso masa tafasasshen ruwan zafi a fusace


Azad kai kam Allah ya haɗa ka da jar wuya😹


Yau ma in sha Allah za'a yi biyu don taya uwa Nigeria birthday 🙃

#likecommentsare

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥


__Free_book_


✍️Nusy bee

*Young talented writers association (YOTA)*

A yi min afuwa Please 🥺ayyuka ne suka yi min yawa🙏


Page 26


Da matuƙar sauri ya matsa ruwan zafin ya zube a ƙasa,amma duk da haka ya ɗan fallatsar masa,ya bi ruwan da kallo yadda yake tiriri sannan ya kalle ta,sai girgiza take yi hannun ta a ƙugun ta tana huci cikin ɓacin rai,a hankali ya ce"ba ki da hankali ne? yanzu da kin ƙona ni fa?"

Cikin hargowa ta ce"da ba za ka sake fifita wata ƴar iska a kaina ba,don ba zan ɗauki rainin wayo ba"ya taɓe baki baki ya juya ya fice daga parlourn,amma fa yau ya tsorata da haukan wannan matar ta shi


HOTORO GRA, KANO STATE, NIGERIA


Da murmushi a fuskar ta take kallon Salis da ya shigo part ɗin na ta ya na ƙarewa ko'ina da kallo zuciyar shi cike da mamaki,amma ko a kan fuska bai bayyana ba

Murmushi mai kyau ta yi ta ce"welcome sweetheart!"ɗaga kai ya yi batare da ya amsa ba,ta miƙe tsaye ta rungume shi ta na kwantar da kan ta a kan faffaɗan ƙirjin shi,shima bai yi musu ba ya karɓe ta ya rungume ta sosai,har yanzu ya na son matar shi,kuma yayi missing ɗin ta,ko mata nawa ya aura ba ya jin akwai wadda za ta goge soyayyar ta a ranshi

Murmushin cin nasara ta yi,sannan ta ɗago kai ta na lumshe masa manyan idanun ta,murya ƙasa ƙasa ta ke faɗin "I miss you my husband! I'm sorry for everything please, forgive me!"yayi murmushi ya na sa ke rungume ta yace"I love you wife! I miss you too,ina Aman?"

Tana wani langwaɓar da kai tana kaɗa idanun ta da sigar jan hankali ta ce

"Aman ya na makaranta,shima ya yi missing abban shi"ta ƙarashe a ɗan shagwaɓe

Murmushi ya yi ya ce"nima na yi missing ɗin shi"sakin shi ta yi ta ja hannun shi ta zaunar dashi a kan kujera,sannan ta kwanta a kan kafaɗar shi ta na gaishe shi cikin kissa da kulawa

Amsa wa yayi ya na murmushi,ta maƙalƙale shi ta na faɗin "na gama girki,na zuba maka kai da amarya ko na kira ta mu ci tare?"

Ya yi ɗan jummm kafin ya ce"ki kira ta mu ci tare,dama ina da maganar da zan yi da ku baki ɗaya"

Samha ta ji wani sanyi ya ratsa ta,ta wuce part ɗin Beely ta na taku tana girgiza

Ko sallama Babu ta faɗa part ɗin Beely ta na ƙarewa ko'ina kallo,ta ji zafi a ranta ganin kusan komai na part ɗin Beely yafi na ta tsada, kasancewar ba karfin iyayen su ɗaya ba,ban da haka ma Mahaifin samha matan auren shi huɗu ne,yara ashirin da uku, saɓanin mahaifin Beely mai yara shida,mata ta biyun ma sai kwanan nan ya aure ta

Beely ta na kwance a kan kujera three sitter ta na kallon Samha da ta ke ta ƙarewa parlourn ta kallo a wulaƙance,ganin abin ba mai ƙarewa bane tace"Malama lafiya?irin wannan kallon fa?bashi ko tara?"

"Lafiya ko?ai lafiya ta ƙare miki tunda kika aurar min miji,butulu,maci amana, asararriya!"

Beely tace"akwai asararriya da ta wuce ki?kar ki manta mijin ki ya sanar dani baki da tarbiyya,ke ɗin ƙazama ce,baki da tarbiyyar da zaki iya zaman gidan aure,dole yaje ya samo wadda zata kula dashi"

Duk da Samha taji zafin maganar amma tayi dariya ta tafa hannu tana faɗin "gwara ni,nice bani da tarbiyyar,kuma ko a yanzu naso zan sauya,mahaifiya ta kuwa kamar zata duƙa wa mijin ta, ba'a maganar ƴan uwana ma,kema kin je kinga yadda suke gudanar da rayuwar auren su,don Allah basu burge ki ba?don nasan baki saba ganin irin haka a wajen gyatuma ba....."

"Ke!ke!!ke!!

Kar kiyi ƙoƙarin zagar min uwa idan ba haka ba wallahi ki gane kuren ki a gidan nan!wata banza da ke ma?"a cewar Beely a zafafe ran ta yana ɓaci,tuni ta zauna daga kwanciyar da tayi

Samha tayi dariyar rainin hankali ta ce"Allah ko?Ni kuwa shawarar cin amanar da ta baki ce tayi tasiri ko kuma dai?da alamu dai rashin tarbiyya da cin amana a nono aka tsotsa aka....."a guje Beely ta yo kanta,ta juya da gudu ta koma part ɗin ta, Salis yana zaune ta shigo a guje ta maƙalƙale shi tana faɗin "wayyo Allah na!"

Beely ce ta shigo parlourn ta na huci,kafin ta yi magana Samha ta fashe da kuka tace"kawai don nace tazo mu ci abinci sai ta fara ƙoƙarin zagi na?don na ce ta daina zagi na sai ta ce zata dake ni?me na yi mata?"

Salis ya bi Beely da kallo wadda ta ƙame da mamaki ta na kallon Samha da ta ɓoye fuskar ta a jikin mijin nasu ta cukwikwiye shi

Ya kalli Beely ya ce"Bilkisu zo mu ci abinci,akwai maganar da na ke so na yi da dukkan ku Please"

"A ina zamu ci abincin?"ta tambaya cikin ɓacin rai ta na kallon shi

"A nan mana,gaba ɗaya, Samha ta shirya mana breakfast "

Sakin baki Beely ta yi ta na kallon shi kafin ta ce"to ba zan ci ba,ba zan ɗauki wannan rainin hankalin ba"ta juya a fusace ta fice daga part ɗin ta nufi nata,ta na ji salis yabna ƙwalla mata kira amma ta yi masa banza

Samha ta yi murmushin farin ciki tana tuna shawarar fareeda

_"Dole ki yi ƙoƙarin kwantar masa da kai sannan ki kunna fitina a tsakanin su,ta haka ne kawai za ki raba kansu,ki jefa masa tsanar ta,ki kafa gwamnatin ki a zuciyar shi"_

Ta yi murmushin farin ciki,a ran ta ta na faɗin"step one!"


ALU EVENUE, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA


"To yanzu ke me kika yanke?"

Shiru Inaaya ta yi ta na kallon shukra kafin ta ce"na amince,amma ya batun mahaifiyar ta shi?"

Shukra ta girgiza kai tace"a ƙa'ida za'a raba shi da kowacce mace har mahaifiyar shi,don tabbas shuwa ce,kuma kin san ba'a raba su da ƴan binne binnen nan"

Ɗan yatsina fuska tayi ta ce"kuma naji labarin wai a ƴan uwan ta ta ke nemo wa ƴaƴan ta mata ko mijin aure saboda tsabar son kai"

Shukra ta ce"mu ma ƙarfin ta muka fi ai,da yanzu an raba ku"

Inaaya ta runtse idanu tace"wai! ta yaya zan iya rayuwa babu Auwab?nibma na san nayiwa kaina ƙarya, I can't imagine my life without that charming guy"

Shukra tabyi murmushi ta ce"and he loves you too, Allah ya bar ƙauna"

Inaaya ta na murmushi ta ce"ameen"

"So now!ya batun Safwan kuma?bana son ki bar guy ɗin nan,he loves you wallahi"

Inaaya ta yamutsa fuska ta ce"kin dai dage kar na rabu dashi,to naji,but ni yanzu ko burge ni ba ya yi, Auwab kawai nake gani a matsayin namiji"

Shukra ta yi murmushi ta ce "dama duk inda auwab yake ai babu wani namiji da ya isa ya je wajen, Safwan ma za ki saurare shi ne just for the sake of his love to you"

Inaaya ta taɓe baki ta ce"okay,zamu gani, now,dame dame ya kamata muyi?kuma a ƙalla nawa ya kamata na karɓa daga gare shi?"

Shukra ta girgiza kai ta ce"ni dai shawarar da zan baki kar ki kuskura kiji tausayin shi, saboda namiji idan ana tausaya masa ya fi wulaƙanci"

Inaaya tace"ba zai daina so na ba?"

Shukra tace"sai ma dai ya ƙara son ki,kin san namiji yafi son macen da ta ke ja masa aji"

Inaaya ta gyaɗa mata kai tace"I will try in sha Allah"Shukra tayi murmushi tana kallon ta


QUEEN'S COLLEGE,KANO STATE, NIGERIA

Yau makarantar su khairi za ta gabatar da quiz competition tsakanin js 1A da js 1B, Ummul khairi Abubakar albasu ta na ɗaya daga cikin ɗaliban da zasu yi representing js 1B, Nabeela Saleh ta na ɗaya daga cikin waɗanda za su yi representing js 1A,hatta Amra sadeeq da bata cikin gasar karatu take yi babu ji babu gani

Ranar da zasu yi quiz ɗin tare suka fito su uku, zuwa lokacin sunan khair albasu yana ɗaya daga cikin sunayen da ake ambato sosai a cikin makarantar, saboda yadda ta ke ƙoƙarin fitar da ƴan ajin su kunya,to yau ma dai ana saka rai

An fara quiz ɗin cikin nasara,da farko khairi kamar ba zata yi ƙoƙari ba,har ƴan ajin su sun fara sarewa khairi ta Shammaci mutane,ta saka ƙarfi,duk da ƙoƙarin Nabeela Saleh da Zainab Musa sai da khair albasu ta yi winning,a takaice ma,itace ta samu kyautar wadda ta fi amsa tambayoyi

Js 1B sun yi farin ciki sosai,suka rinƙa murna suna celebration, Amra ta rungume khairi cike da farin ciki,tana faɗin "khair albasu kin fitar da mu kunya, proud of you our champion!"

A ɗaki nabeela ta galla wa khairi harara ta na faɗin "sai nayi manaƙisar da zaki daina shiga gasa ki na kasa mu"khairi ta kwashe da dariya, Amra tace"ai sai kiyi manaƙisar na gani,in sha Allahu mun ta cin gasa kenan in dai muna tare da champion "ta ƙarashe ta na rungume khairi da ke murmushi tana danna waya

Hotuna tayiwa kyaututtukan da aka bata ta turawa sulaiman da Azad,duk cikin su babu wanda yake online,don haka ta kashe datar ta kwanta akan gadon ta zuciyar ta cike da farin ciki

Da yamma sun fita shan iska ita da Amra sai ga kiran Azad,da sauri ta ɗaga wayar za ta fara bayani taji muryar wannan masifaffiyar matar ta shi a cewar ta

Cikin rawar murya khairi tace"ina kwana!"

"Ban sani ba!ke baki da zuciya ne,tukunna,baki da iyaye ne?to kar na sake ganin kiran ki a wayar nan, wallahi idan kika sake kira min miji sai kin yi nadama, ballantana har ki rinƙa turo masa da shirme ta Whatsapp,idan kuma ki na tantama ki cigaba"bata jira amsar khairi ba ta kashe wayar


Kamar koyaushe dai wannan mata ta Azad an gaishe ta🥱

Wannan na taya aunty Nigeriya murna ne😁

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥


__Free_book_


✍️Nusy bee

*Young talented writers association (YOTA)*


Page 27

Shiru khairi ta yi ta na bin wayar hannun ta da kallo,ikon Allah!wai mene ne matsalar matar yaya Azad ɗin nan? ina ya ke ma? Amra ta matso kusa da ita tace"khairi ya dai?"

Khair ta girgiza kai ta ce"nothing,na kira yaya na ne ban same shi ba,bari na kira yaya sulaiman"bata jira amsar Amra ba ta fara ƙoƙarin kiran yaya sulaiman,ya na ɗagawa taji ya ce"Allah ya taimaki likita bokan turai!"

Dariya ta kama yi, shiyasa ta ke son waya da sulaiman,dole ya yi abinda zai bata dariya,ta ce "yaya sulaiman Barka da yamma!"

"Barka dai manya,ya quiz, congratulations sister!dama na san za ki iya,kuma gashi kin yi"

Khairi ta yi murmushi tace"na dai ƙoƙarta,ya shirye shiryen bikin?"

"Au kin damu da bikin dama?"ya faɗa ya na ƴar dariya

Khairi ta taɓe baki tace"Allah ya sanya albarka"

"Ameen!ba kin ce ba za ki dawo ba?"

"To karatu na fa yaya sulaiman?"

"To na fahimta, shirye-shirye ana nan ana ta yi,bikin big bruh next week in sha Allah"

"To Allah ya sanya alkhairi"

"Ameen!zan zo miki visit in sha Allah,zan taho miki da tawa gift ɗin for appreciating me"

Ta yi murmushi sosai tace"ai kun gama bani gift a rayuwa ta tunda ku ka kaini makaranta yaya sulaiman, Allah ya cigaba da dafa wa rayuwar ku ya tsare mana ku"

"Ameen my lovely sister,sai nazo"

"Okay yaya sulaiman,bye!"sukayi sallama ta na ta murmushi


BRUNSWICK, MELBOURNE, AUSTRALIA


Zuciyar ta a zafafe ta ke kallon shi yadda yake ta baccin shi cikin kwanciyar hankali,sannan ta sake kallon message ɗin da aka yi masa ta Whatsapp,wadda ta shaida mai number ɗin, ƙawar ta ce Hafsy

Message na farko an rubuta"I love you so much you handsome!"

Bai yi mata reply ba amma ya buɗe,na biyu kuma ta ce"jiya na yi mafarkin ka,na yi mafarkin Ni da kai mun zama abu guda"shi ma dai ya buɗe amma babu reply

Na uku kuma ta ce"I'm sure idan ka aure ni you will never regret it,don zan ba ka abinda wannan matar ta ka bazata ba ka ba,zanyi maka abinda ba za ta iya yi maka ba"shima dai babu reply

Na ƙarshe kuma cewa ta yi"ni ko baka aure ni ba zan iya sadaukar maka da kai na,na baka kaina kuma ni taka ce"shima dai still Babu reply

Sai ta koma na khairi da ta turo masa hotunan kyaututtukan da ta samu na quiz,ta ce"yaya na yau munyi quiz,ka ga abinda na samu"

Ajiye wayar tayi tana kallon shi zuciyar ta kamar ta fashe,kamar an tsikare ta ta sake ɗaukar wayar a fusace ta lalubo number ɗin mum ta danna mata kira,tunda ta san a Nigeria yanzu dare bai yi ba

Mum ta na ɗaga wa fadeela ta fashe da kuka,mum ta ce"subhanallahi! lafiya?ina mai gidan naki?"

Fadeela ta share hawayen ta ta ce"mum ba lafiya ba, Azad neman mata yake yi!"

Zuciyar mum ta buga da ƙarfi,a tsorace tace"kamar yaya?neman mata kuma? Azad ɗin?"

"Mum na ga ya na chat ɗin banza da wata yarinya,na san yarinyar ƴar unguwar mu ce, mutuniyar banza ce,sannan kuma still ya na maganar banza da wata yarinya da naji ya na kira khairi,amma don munafurci ya yi saving ɗin number ɗin ta da little sister,babu ranar da ba ya kiran ta ko chat ɗin banza,akan ta ya mare ni ya ci min mutunci,akan ta yayi iƙirarin sai ya sake ni,akan ta yace ya tsane ni "

Shiru mum ta yi zuciyar ta kamar ta fito don tsananin baƙin ciki,dama Azad bai rabu da wannan matsiyaciyar yarinyar ba duk warning ɗin da ta yi masa,da ƙyar ta iya furta"ba shi wayar!"

"Barci yake yi,kin san mu nan dare ne"

"To shikenan!"ba ta jira amsar fadeela ba ta kashe wayar, fadeela ta kalli Azad da ke ta barcin shi cikin kwanciyar hankali ta na wani murmushi da ita kaɗai ta san ma'anar shi

Washe gari ita ta shirya musu breakfast ta jere musu a dinning,da shirin shi ya fito zai fita ta ce masa

"Ga abinci nan na shirya mana"ya kalle ta yace"thanks, I'm okay"ya ci gaba da tafiya

"Saboda ni matar ka ce?da khairi ce ai ba zaka ƙi ci ba ko?"

Tsaya wa yayi cak,cikin sanyin jiki ya dawo ya ajiye brief case ɗin shi ya samu waje ya zauna,tayi serving ɗin shi

Tea ne da omelette,sai chips,ta na ajiye masa plate ɗin ƙarnin ƙwai ya dake shi yaji kamar ya miƙe ya tafi

Shiru ya yi bayan ya kai lomar farko,ita kanta bata wani mayar da hankali ta na cin abincin ba,sai danna waya take yi,shi dai da ƙyar ya yi loma uku ya miƙe yana faɗin "thanks,na tafi"

"To wannan kuma wa ka rage wa?"kallon ta yayi ba tare da ya ce uffan ba,a ranshi yana jinjina yadda take gatsa masa magana yadda taga dama,bai sake yi mata magana ba ya suri brief case ɗin shi ya yi waje

Wajen ƙarfe biyu na rana ya na office ɗin shi kiran mum ya shigo, da sauri ya ɗaga wayar ya na sallama, shiru ya ji mum ta yi

Yasan idan ta yi haka cikin biyu ɗaya,ko bata da lafiya ko ranta a ɓace,cikin barkwanci ya ce


"Allah yaja da ran mummy na abar alfahari na!"

"Azad!na gode!ka kyauta!!"

Gaban shi ya faɗi,a hankali yace"mum me nayi?"

"Baka yi komai ba Azad,kayi abinda ka ga ya fiye maka!"

"I'm sorry mum!don Allah ki gaya min me nayi? hankali na ya tashi mum,kin sani ba na son damuwar ki ..."

Ta daka masa tsawa"ba ka son damuwa ta?ni zaka yaudara Azad?dama ashe har yanzu ka na tare da wannan yarinyar khairi? yarinyar da ta tarwatsa min farin cikin gidan aure na ita kake bibiya?wai ma uban me yasa ka kasa nisantar yarinyar nan ne?to wallahi idan baka fita harkar ta ba ban yafe maka ba,ban haifi yaron da baƙauyiya za ta juya ba"

Cikin kwantar da murya yace"I'm very sorry mum,don Allah kiyi haƙuri, wallahi kawai ina kula ta ne kasancewar marainiya ce, tausayin ta na ke ji kawai"

"Ko mece ce ita ina ruwan ka?

Kafi ragowar dangin na ku sanin ciwon ta ne,ka fi su tausayi ne?kai mahaukacin ina ne da bazaka yi harkar gaban ka kamar kowa ba?"

"Amma mom. ....'

"Kar ka dame ni!zaɓi ɗaya zan baka,ka zaɓa ko ni ko ita, wallahi sai dai ka zaɓa,don babu yadda za'ayi yarinyar nan ta tarwatsa min gidan aure sannan kuma in zuba idanu ta tarwatsa naka,akan ta mahaifin ka ya mare ni,kai ma gashi ka mari matar ka har da cin mutuncin ta akan ta,wai uwar wacece ita haka ne?ko asirin su na ƙauye ta yi muku?tunda an ce itama kakar taku ta na ɗan biye biye?to wallahi ba'a haifi yarinyar da ta isa ta tarwatsa min gida ba,next,ka nisanci yarinyar nan,ko na tsine maka Azad!!!"

A gigice yace"subhanallahi!mum me yayi zafi haka?yanzu zanyi blocking ɗin ta ma,don Allah ki yi haƙuri,kema kin san ba'a haifi macen da zan zaɓa akan ki ba, I'm very sorry mummy na"bata sake magana ba ta kashe wayar

Gumi ne ya rinƙa yanko wa Azad,yayi matuƙar gigita da lamarin mum,hannun shi na rawa ya janyo wayar shi yayi blocking khairi ta Whatsapp ba tare da ya bata amsa ba,yayi blocking ɗin call logs ɗin su,ya ajiye wayar ya dafe kanshi da hannu bibbiyu,kafin ya ankara haki ya nemi hana shi numfashi,sai da yayi amfani da inhaler ɗin shi

Mayar da kai ya yi ya jingina da bango ya lumshe idanu ya na sauke numfashi, tunani ya cika zuciyar shi,kafin auren nan nashi sai yafi ƙarfin wata bakwai athma ɗin shi bata tashi ba,sai dai ƙura ko wani abin haka,shima ya na matuƙar kiyayewa,amma yanzu yawanci ba ya sati sai ta motsa masa saboda damuwa da ɓacin rai

Daga maganganun mum ya fuskanci fadeela ta kira ta ta shaida mata ƙarya da gaskiya ne,dama gashi yaga an buɗe message ɗin da bai san dashi ba ma,amma babu komai,in dai khairi ce ya bar ta kamar yadda mahaifiyar shi ta buƙata,komai lokaci ne

Bai koma gida ba sai yamma,a parlour ya iske fadeela a kwance tana ta rawar sanyi jikin ta zazzaɓi,ta na ganin shi ta fashe da kuka,ta na faɗin "heartbeat zo ka ji jiki na, zafi,haka na wuni bani da lafiya,gashi baka nan"

Shiru ya yi ya na kallon ta,a hankali ya ƙarasa kusa da ita ya taɓa wuyan ta,zafi zau,sai kuma ya ji tausayin ta,ya zauna kusa da kujerar da ta ke zaune,cikin sanyin murya ya ce

"Tun yaushe kike fama da wannan zazzaɓin?"

Numfashin ta ya na fita da ƙyar ta ce "tun da na tashi bana jin daidai,baka juma da fita ba kuma zazzaɓi ya rufe ni"shiru ya yi kafin ya ce"to meyasa ba ki kira ni ba?"

"Wayar ta na ɗaki,idan na miƙe jiri na ke gani, shi yasa kawai na haƙura sai ka dawo"

Ya miƙe yace"dole muje asibiti yanzu, wannan zazzaɓin ba na lafiya bane"

Ɗaukar ta yayi cak ya fice da ita daga parlourn bayan ya ajiye brief case ɗin shi

Shi ne ya yi driving ɗin su zuwa Melbourne private hospital,a can aka yi admitting ɗin ta don ta ɗan ji jiki,aka fara duba ta

Sai wajen tara na dare aka kawo masa result,ciki gare ta sati shida,duk da haushin ta da yake ji sai yaji ya daina ji,ya cika da farin ciki,ya gode wa Allah,ya kira mum ya sanar mata,duk da cewa tana fushi dashi itama sai da taji ya wanke mata zuciya

Cikin farin ciki ta ce"Azad ka kular musu da yarinya don Allah, kar ka ɓata mata rai,ka yi abinda ta ke so Indai kana son ɗan ku da lafiya, Allah ya raba su lafiya "

Cikin jin daɗi ya ce "ameen mummy na, I hope kina lafiya "

"Lafiya ƙalau,take care of yourself son!"ya yi murmushi ya ce"I love you mum"

Ita ma ta na murmushi ta ce"love you more lovely son"

Bai samu ganin fadeela ba sai washe gari da safe,ta na zaune da alamu ta ji sauƙi,ya na ganin ta ya tafi da sauri ya rungume ta ya na murmushi,ta narka fuska tace"me akace ya na damu na?"

Ya na murmushi yace"guess what?"

"Just tell me please "

"We will soon be parents in sha Allah,you are re pregnant wife "

Shiru ta yi ta na kallon shi kamar b ata gane me ya ke faɗa ba,kafin ta ce"I can't get you Azad!"

"Kina da ciki fadeela we will soon be parents in sha Allah!"

"Are you ready to be a father for now?"

Ya buɗe idanu ya na kallon ta ya ce"of course dear,tunda muka yi aure ai we are ready for that"

"But for me I'm not ready! Azad na ga alamu kai Mutum ne mai son kan shi,idan kana son abu babu ruwan ka da ni ina so ko bana so,wacce rigar rayuwa ce wannan?to cikin biyu ɗaya,ko ka samo mai haife maka cikin nan ko na ɗauki matakin da ya dace akan shi,don ban shirya lalace wa da ƙuruciya ta ba, Allah ya sa ka fahimta!"


Fadeela kika ce me😡


Ga masu son VIP group zasu iya yi min magana a wannan number 08125952284

#300 ne kacal


#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_


✍️ Nusy bee


*Young talented writers association (YOTA)*


Page 28

Gaban shi ya buga jin abin da ta ce,a hankali fara'ar fuskar shi ta ɗauke ya na kallon ta,a hankali ya ce "what do you mean fadeela?"

"Da Hausa fa na yi magana Azad!na ce ban shirya haihuwa yanzu ba, saboda son kai da rashin sanin darajar aure babu ruwan ka da cewa. Ina so ko bana so,ka zo ka na maganar zan haifa maka ɗa,to ba yanzu ba"ta ƙarashe cikin ɗaga murya

"Fadeela!wanne kalar shirme ne wannan?ya ki ke abu kamar jahila mara ilmi?"

"Kai ne dai alamun jahilci su ka bayyana a tare da kai,ko na ce na son zuciya,amma ka sani wallahi ba zan haifi cikin nan ba"

Shiru yayi yana kallon ta,kafin ya ce"to me za ki yi masa bayan an riga an same shi?"

Kai tsaye ta ce"zubar da shi zanyi,don kamar yadda na gaya maka ban shirya haihuwa yanzu ba"

"What!zubar wa kika ce fadeela?to wallahi ban amince ba,ban yarda ba,idan kuwa ki ka kuskura ki ka zubar min da ciki za ki ga abinda bakya so,zan baki mamaki"

"Mamaki?ai ka gama ba ni mamaki yanzu,ka daina ma tunanin zaka buɗe min idanu,don wallahi cikin nan ko sama da ƙasa za su haɗe sai na cire shi

Azad!you didn't know who is fadeela!Amma zaka sani very soon,don Allah ka tashi kar ka fusata ni "

Ya miƙe tsaye zuciyar shi na ƙuna ya ce"nima dama na gaji da zama kusa dake,amma kar ki ce ban gaya miki ba,idan ki ka cire cikin nan sai kin gane kuren ki, wallahi sai kin gwammaci ba ki san ni ba"ya juya ya fice batare da ya sake ko kallon ta ba,shi dai Allah ya jarabce shi da jidali


HAƊEJIA ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA


"Yanzu wannan kuɗin bai yi yawa ba Auwab?"

"Ammi bai yi yawa ba,me ki ka gani?"

Shiru ammi ta yi,kafin ta ce "gaba ɗaya abinda ka kashe na lefe da sadaki da kama halls ya kai ko 40m ma?"

Ya yi ɗan murmushi yace "Ammi tayi min list hidimar su da yawa,kuma suma suna bikin su na al'ada kamar mu ma,don haka bari na tura mata kawai Ammi "

Ammi ta yi shiru ta na kallon shi kafin ta ce"to kai za ka je bikin nasu ne?"

Auwab ya girgiza kai ya ce"kin san bana zuwa irin waɗannan tarkacen bukukuwan,ko wanda za kuyi na gidan nan ma babu wanda zan halarta,Ni nawa na sallame ku ne kawai"

Ammi ta yi shiru ta na ɗan kallon shi,ita fa ba ta gamsu ba,asalima ta fara tsoron kar Auwab ya auri wadda zata raba ta da yaron ta,yaya za'a ce wai hidimar shagalin biki kawai 50m?a hankali ta ce"to Allah ya sanya albarka, Allah ya sa ayi lafiya a gama lafiya "

Auwab ya yi murmushi ya na kallon ta ya ce"ameen ammi na!haka ya kamata ki faɗa tun farko,amma tambayoyin nan na ki taorata ni suke yi"murmushi kawai tayi batare da tace komai ba

An yi shagali sosai, Hajiya Salma ba ta zo ba,amma yaran ta mata sun zo,su kuma mazan sun je Alu evenue ɗaurin aure

Itama dai Inaaya kamar fadeela sai da aka fara kawo ta gidan sirikar ta,amma maimakon tarin ƙawaye ita ƙawar ta ɗaya ce sai ƴan uwan ta na family da ƴan uwan mahaifiyar ta,su Beely sai kallon ta suke yi,daga yanayin amaryar Auwab sun san definitely yafi yayan su dacen mata

Ammi ta karɓe ta da fara'a,itama Inaaya babu laifi ta girmama Ammi, Amra ta jagorance su zuwa ɗakin da aka ware musu ita da ƙawar ta da ƴan uwan ta da za su wuce Massachusetts gobe

Washegari karfe biyu na rana jirgin su Auwab ya ɗaga zuwa Massachusetts,daga ɓangaren Ammi dai ƙannen ta biyu aunty jalila mahaifiyar mifra budurwar sulaiman,sai aunty abida itama ƙanwar Ammi ce sune suka tafi da masu kai amarya,auwab ya yi wa su Amra tayin zuwa suka ce a'a, musamman da Amra ta ga wani kallon banza dangin amaryar su ke yi wa mutane, musamman tsirarun mutanen albasu da suka zo bikin

Kwanan masu kai amarya ɗaya suka juyo gaba ɗaya,ciki har da Shukra,ƙawa ɗaya tal da ta raka amarya

A ranar Inaaya ta yi amfani da magungunan mallaka da su ka karɓo a wajen hatsabibin bokan su,don ta shigo da ƙudurin mallake auwab ita kaɗai,kuma za ta yi ko menene don tabbatar da hakan

Tsafi gaskiyar mai shi!a satin da Auwab ya yi aure ya manta da babin Ammi ballantana ƙannen shi,baya tuna kowa a cikin su sai wanda ya kira shi,su kansu sun san da tsawa,faɗa-faɗa yake amsa musu gaisuwa idan suka kira shi a waya

Sosai ammi ta shiga damuwar wannan sauyi na Auwab,don haka ta saka sulaiman ya kira shi ya ji me yake faruwa ne?ko wani laifin akayi masa?

Sulaiman ya yi murmushi kawai lokacin da Ammi take bashi wannan umarnin,don faɗa suka yi kaca kaca da Auwab lokacin da ya kira shi don yaji me yake faruwa? Auwab ya kaɗa masa warning ya fita daga rayuwar shi, sulaiman yayi murmushi yace

"Haba best friend!yau ni ka ke cewa na fita sabgar ka?tare muka tashi,tare muka ....."

"And so?"ya katse shi a zafafe"sulaiman lokaci yayi da ya kamata ka san ciwon kanka,yanzu ba da bane,ka gane?so......"

"Yaya Auwab!what is all this?wai me ya shiga kan ka a ƴan kwanakin nan ne?"

Sai da Auwab ya ɗanyi shiru sannan yace"sulaiman! sulaiman!!sulaiman!!!sau nawa na kira ka?"sulaiman yayi shiru ranshi ya na ɓaci, Auwab bai damu ba ya cigaba

"Ba dai zumunci ba ne?to a haƙura da zumuncin,don tabbas ka sake kira na ka na yi min titsiye sai na maka rashin mutunci"bai jira sulaiman ya sake magana ba ya kashe wayar shi

Sauke ajiyar zuciya ya yi bayan ya tuna artabun da suka sha da shi da ɗan'uwan na shi,Ammi cikin sanyin murya ta ce"sulaiman ko da matsala ne?"

Sulaiman ya girgiza kai ya ce"babu wata matsala Ammi,ina su Amra?"

"Amra ta tafi Maiduguri,ka san ana daf da fara bikin sumayya yayar mifra"

"Oh! haka ne fa!to Allah ya sanya albarka,ni bari na tafi don ana nema na a wajen aiki,daga can zan kira big bruh yadda muka yi zan sanar miki"

Cikin sanyin murya ta ce"to shikenan"ya miƙe ya fice zuciyar shi cike da tausayin ta


HOTORO GRA, KANO STATE, NIGERIA


Yau kwana biyu kenan da wani gagarumin faɗa da Beely da Samha suka yi,wanda har Beely ta fusata ta watsa wa Samha Black tea mai zafi da ta ke tafasawa Samha tazo ta saka ta a gaba da neman tsokana, Beely bata iya cacar baki ba, shi yasa da Samha ta kai ta maƙura kawai ta ɗauki ƴar tukunyar tea ɗin dake daf da tafasa ta watsa wa Samha,ya same ta a ƙafa kuwa,Samha ta rinƙa ihu da kururuwa,a guje salis ya shigo ya zo ya iske wannan aika aikar

Ko da ya tuhumi Beely dalilin ta na yin wannan ɗanyen aikin kai tsaye ta ce ta yi ɗin,kafin ta yi wani bayani ma ya ɗauke ta da mari,ta fusata ta fara zage zage,kafin ya ƙara mata ne Samha ta yi azamar riƙe hannun shi ta na kuka tace"don Allah abban Aman ka rabu da ita,ka daina ganin laifin ta,ni ganau ce ba jiyau ba haka uwar ta take yi wa uban ta,don Allah ka ƙyale ta ka cece ni"Salis yayi wa Beely dake daskare ta na kallon su kallon banza ya ɗauki matar shi ya saɓa ta a kafaɗa ya nufi ficewa daga part ɗin da ita,ta faki idanun shi ta yi wa Beely gwalo,duk da har lokacin ƙafar ta ta na mata raɗaɗi

To fa tun ranar Salis ya fita a harkar Beely,itama girman kai ya hana ta je ta bashi haƙuri,tsawon waɗannan kwanakin ta yi su ne da ƙunar rai,yau dai ta gaji,don haka ta shirya don zuwa gidan su

A harabar gidan suka haɗu,fuska a ɗaure ya kalle ta ya ce"ina zaki je?"

Kallon banza tayi masa ta ɗauke kai ta ce"gidan mu, inda aka san daraja ta"

"To ban amince ba,don haka koma"

"Pardon?"ta faɗa ta na ma sa kallon rainin wayo

"Cewa na yi ki koma ciki,babu in da za ki je"

Wani murmushin takaici ta yi ta ce"zuwa ma kamar na yi na gama ne,don wallahi babu wanda ya isa ya dakatar dani"ba ta sake ba shi damar magana ba ta fice ko waiwaye ba ta yi

Salis ya bi ta da kallo ran shi yana tafasa,duk rashin mutunci da rashin kunyar Samha idan ya hana ta fita sai dai ta zauna ta yi ta masifa,amma yau ga wadda ta fi ta rashin kunya,amma zai yi maganin ta,ya shiga motar shi zuciyar shi cike da ƙunar rai ya tayar ya bar gidan


Samha fa tana da gaskiya 🥱


#Nusy_bee

Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️ Nusy bee

*Young talented writers association (YOTA)*


Page 29


Kai tsaye gidan su ta wuce a napep,ta na shiga ta ga su feena a zaune a parlour kallo

Kallon kallo suka yi da ita,kafin ta ce"ina mum?"

"Mum ta na ciki,ki shiga ciki"a cewar feena wadda ta ke ƙare mata kallo da mamaki


Ba ta sake magana ba ta shiga ɗakin mum,ba ta juma da tashi daga bacci ba,don yanzu ma ta fito daga wanka take shiryaw a

A firgice ta kalli Beely ta na faɗin "kan ki ɗaya kuwa Bilkisu?lafiya za ki faɗo min ɗaki irin haka?"

"Ba lafiya ba mum,mum wallahi gaba ɗaya rayuwar ta yi min zafi,dududu watannin auren mu nawa da Salis zai fara wulaƙanta ni? kullum da sabon abu da zai ɓullo dashi,can you imagine shekaran jiya mari na ya yi don na watsa wa matar shi ruwan zafi....?"

"Wait Bilkisu!kin san me kika faɗa kuwa? kin watsa mata ruwan zafi wannan wanne irin rashin imani ne?sai kace wata yankakkiyar kaza?"

Hawaye suka zubo mata ta ce"mum ta ɓullo da hanyoyin hana ni zaman lafiya a gidan,ta fiye takala ta,kuma sai ta yi ta gaya masa wai kema ba tarbiyya gare ki ba ballantana ki bani,shi kuma ya ɗauka,mum da wanne zan ji?ya na kallo na a banza,ni nata bai dame ni ba,amma shi kuma fa?"

Shiru mum ta yi ta na kallon ta,kafin ta ce"to yanzu da ki ka dawo mene ne hikimar hakan?"

Ta goge hawayen ta tace"ya san amfani na mana, wallahi ko zan koma ba nan kusa ba"

"A'a Bilkisu,kar ki yi haka,ya kamata ki rinƙa sanin me zaki yi idan kina cikin ɓacin rai,ya za ki watsawa mutum mai rai ruwan zafi?"

"Mum I told you gori take yi min ta na gaggaya miki maganganu,ta yaya zan iya jurar hakan?"

Shiru mum ta yi ta na kallon ta,jikin ta duk ya yi sanyi,kafin ta yi magana Beely ta goge hawayen ta ta ce"dole na ƙwatarwa kai na haƙƙi,in da na gode wa Allah na san komai nata,wajen malamai ta je,nima zan je wajen waɗanda suka fi na ta hatsabibanci"

Wani mugun kallo mum ta watsa mata ta ce"boka?a gida na? Bilkisu anya kanki ɗaya kuwa?to ban haifi wadda ta isa ta taka gidan boka ba,ni dai barni da masifa ta da tayar da zaune tsaye,amma bansan hanyar wajen boka ko malaman tsibbu ba,kuma yaran da na haifa ma baza su sani ba!"

Beely dai kallon ta take yi har ta gama,sannan ta zauna kusa da ita,cikin kwantar da murya ta ce "mum ba fa malaman tsibbu ko bokaye ba ne,malamai ne waɗanda suke bayar da taimako saboda ginuwar zaman aure da gyaruwar shi fa"

"Allah ko?"a cewar mum

Bilkisu ta yi murmushi ganin ta fara shawo kan mum ta ce"wallahi kuwa mum,kinga da ran ki yayi ta ɓaci a banza,aka kawo wannan matsiyaciyar yarinyar,ƙarshe a dalilin ta Daddy ya yi miki kishiya ya zo ya na fifita ta akan ki,yaran ki kowa yayi ta jin haushin ki,amma taimako ɗaya zan karɓo miki komai ya kau,ba sai kin bayar da kuɗi ba,da kaina zan amso miki "

Mum ta saka idanu ta na kallon ta kawai har ta gama sannan tace"yanzu Bilkisu amfani za ki yi da halin da nake ciki a gidan miji ki ɓatar dani? Bilkisu ni ban je wajen boka ba,haka uwa ta ma, to ke a ina kika samu wannan mummunar ɗabi'ar?"

"Mum nace miki....."

"Hold it Bilkisu!!kin san mene ne ma'anar zuwa wajen boka kuwa?imanin ki ya mutu,duk wani kusancin ki da Allah ya ƙare,kin zama babbar abokiyar shaiɗan,ashe hakan riba ne?"

Shiru Beely ta yi zuciyar ta na yi mata zafi,da ta san haka mum za ta karɓi maganar ai da bata fara yi mata ba,ita dai mum ta yi ta mata nasiha wadda a wajen Beely ta zagaye ta bayan kunne,bayan ta gama Beely ta miƙe ta na faɗin"to mum!bari na je na huta"ta shige cikin gida


BRUNSWICK, MELBOURNE, AUSTRALIA


"Madam daga ina kike?"

Juyowa ta yi a ƙasƙance ta na kallon shi,kafin ta ce"yaushe aka fara yi min query don na fita kuma malam?"

Azad ya gyara tsayuwar shi yace"a da kiyi abinda kika ganin shine daidai,amma a yanzu ya kamata ki san kina da limit,har zuwa lokacin da zaki haifar min ɗa na sai ki koma ki ci gaba da abinda za ki yi "

Wata dariyar rainin wayo tayi kafin ta ce"ɗa?ɗan ka?au wai ka na tunanin wannan ihun da kayi min a asibiti shine zai bani tsoro na ƙi zubar da cikin?"ta kwashe da mahaukaciyar dariya har da riƙe ciki, sannan ta gintse ta na kallon shi tace"to cikin naka da kake taƙama da ƙafafa dashi ban baro asibitin da suka gano shi da shi ba,don na gaya maka matsaya ta,babu wanda ya isa ya saka ni haihuwa a yanzu,ban shirya mata ba"

Azad kallon ta yake yi kanshi ya na juya wa,tun yana gane abinda take nufi har ya daina,a hankali ya zame ƙasa ya zauna ya na kallon yadda ta wuce cikin ɗakin ta ta na taku ɗaiɗai

Saboda tsananin baƙin cikin abinda ta yi masa ya na dawo wa hayyacin shi ya fice daga gidan,kai tsaye hotel ya je ya yi hiring ɗaki ya rufe kanshi a ciki,gaba ɗaya duniyar ta yi masa ƙunci,ta ko'ina ba ya jin sassauci,ko jiya ma da suka yi waya da mum sai da ta sake jaddada masa ya kula da ƴar mutane, saboda mai juna biyu ta na son kulawa,shima a ƴan kwanakin nan duk abinda ta ke yi masa saboda darajar cikin jikin ta ko haushi baya ji,ashe ma babu cikin

Yayi nisa a tunani ya ji ƙarar wayar shi,ya janyo ya duba,sulaiman ne,ya ɗaga,sulaiman ne ya fara faɗin"Allah ya taimaki babban yaya da kanshi!"

Lumshe idanu yayi ya buɗe ya ce"man ya aiki?ya kwana biyu kuma?"

"Alhamdulillah!kwana biyu shiru,Dr khairi ta ce min ba ta samun ka a waya,ni ma ayyuka suka sha kaina ban samu na kira ba sai yanzu"shiru Azad yayi bai ce komai ba,jin shirun sulaiman ya ce"yaya Azad are you okay?"

Azad ya sauke ajiyar zuciya ya ce"we will discuss later,yanzu ban juma da shigo wa gida ba,na gaji sosai,idan na huta zan kira ka"bai jira amsar sulaiman ba ya kashe wayar

Ya na ajiye ta wani kiran ya shigo,shima dai number ta Nigeria ne amma babu suna,ya ɗaga ya kai kunne ba tare da ya ce komai ba

"Good morning my love!"muryar Hafsy ƙawar fadeela ta doki dodon kunnen shi

Bai amsa ba,ta cigaba"na sauka a Nigeria,kuma don kai na zo,ka na ina ne?ko na biyo ka gida?"

Shi dai mamakin wannan rashin kunya da rashin tarbiyya ya ƙi barin ran shi,abin ya wuce na takaici ma sai dai abin dariya

Jin ya yi shiru ta ce"Hello! honey are you there?"

"Eh ki zo gidan"ya ba ta amsa,sannan ya kashe wayar shi

Murmushi ya yi sosai,idan ita ba ta da hankali ba ya jin ta kai fadeela hauka,su je can su ƙarata

HAFSY

Ita kam Hafsy kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha don farin ciki,ta gyara zaman wani gantalallen mayafi da ta dora akan riga da wandon da suka kama ta tsam,kitson attachment na Ghana weaving yayi matuƙar amsar ta,ta ja ɗan ƙaramin akwatin ta ta tari cab zuwa Brunswick

Fadeela ta na ɗakin ta bayan ta fito daga wanka ta ji sallamar fadeela,tana jin sallamar ta ɗauki murya,don haka ta fito ta na kallon Hafsy da ta ke ta karkaɗa jiki,wayar ta a hannun ta ta na ƙoƙarin kiran Azad

"You are welcome!"taji muryar fadeela

Ɗago wa fadeela ta yi ta na kallon ta,ta saki fuska ta na faɗin "amarya bakya laifi, gaskiya Azad ya iya kiwo,ji yadda kika murje ki ka yi kyau kamar ba ke ba"

Fadeela ta yi murmushin da ita kaɗai ta san ma'anar shi ta ƙaraso kusa da ita ta na yi mata wani kallo ta ce"shine kema ki ka zo ya yi miki irin kiwon?"

"I can't get what you are saying fadeela"a cewar Hafsy tana zaro idanu

"Ai ba za ki gane komai ba,amma ki sani,duk messages ɗin da kike turo wa miji na ya na nuna min,nice na ke cewa ya bar ki kar ya baki amsa"

Hafsy ta san halin ƙawar ta,don haka ta yi wata dariyar rainin hankali tace"kuma da haka ya ce yau na zo na rage masa dare ba,don kin gundure shi,ya na son ya ji sabon waje"

Zuciyar fadeela ta harzuƙo,don tayi tunanin Azad zai iya gayawa Hafsy haka musamman yanzu da ya ke cikin ɓacin ran abinda ta yi masa,kafin ta ankara, Hafsy ta fizgi akwati ta nufi ɗakin azad


Ahayyeeeee sha madarar lilo 💃💃💃💃💃


#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee

Page 30

Da wani mugun ƙarfi fadeela ta janyo ta ta shaƙe mata wuya,itama dai Hafsy ba baya ba wajen ƙarfi,ta murɗe hannun fadeela daga wuyan ta ta hankaɗe ta baya, fadeela ta yi taga-taga, Allah ya bata Sa'a ta dafa kujera,ita kuwa Hafsy babu kunya ta sake nufar ɗakin Azad da tun lokacin da aka kawo fadeela ta sanar da su shine ɗakin shi

Fadeela ta sake janyo ta a fusace ta na faɗin "duk wannan haukan da kike yi baya nan,ki fice min daga gida,kin san wacece fadeela dai, kin san irin haukan da zan iya yi miki,don haka salin alin kizo ki fice min daga gida tunda ba na uban ki ba ne"

Hafsy tayi mata kallon banza ta ja tsaki ta tsartar da yawu ta ce"kin sani ai fadeela, na fi ki dattin ƙwaƙwalwa,duk akuyancin ki sai maman ki ta yarda kike yi,ni kuma kin san yadda muka rabu,ko ita ban raga wa ba ballantana wata ke haɗuwar bariki,dalla bani hanya tunda kema ba gidan uban na ki bane,na san ai baya nan,ajiyar kaya na na zo yi na bishi inda yake,don ya ce ba zai iya kwana a gidan nan ya na kallon mummunar fuskar ki ba,har wani wari wari ma kike yi,in ji shi,kuma ni ma na ji"ba ta jira amsar fadeela ba ta ƙarasa ɗakin ta ajiye kayan sannan ta fito ta raɓe ta gefen fadeela ba tare da ta yi mata ko kallon banza ba,ta fice ta na ƙoƙarin kiran Azad


HAƊEJIA ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA

"Ammi! Ammi!! Ammiiiii!!!"

A firgice Hajiya Raheena ta ɗago ta na kallon Surayya dake mata irin wannan kiran,a sanyaye ta ce"Surayya wannan kiran fa?lafiya? me ya faru?"

Surayya ta zauna gefen gadon da Ammi take zaune ta na kallon ta,a sanyaye ta ce"Ammi me ya faru na ga kin zurfafa tunani haka?"

Ammi ta sauke nannauyar ajiyar zuciya ta ce"babu komai,na gaji ne,ina Amra?"

Kallon ta Surayya take yi batare da ta sake magana ba,don ta san ammin tana da damuwa amma bata son ta sani, Hajiya Raheena tace"tambayar ki nake yi ina Amra?"

Surayya ta kawar da kanta,cikin sanyin murya ta ce"ta na ɗakin ta ta na bacci,tunda ta dawo daga school ta ce kanta yana ciwo shine ta kwanta bacci"

"Okay! Allah ya sauwaƙe, Sulaiman ya shigo ne?"

Surayya ta girgiza kai ta ce "tukunna dai,amma na san duk inda yake ya na hanya yanzu"

Ammi ta ce"to Allah ya dawo da shi lafiya"

Surayya ta ɗan yi shiru kafin ta ce"mum yaushe rabon da kuyi waya da big bruh ne?yanzu bana samun shi a waya"

"Nima ban sani ba, Surayya bar ni don Allah,bacci nake ji "babu musu Surayya ta miƙe ta fice daga ɗakin batare da ta sake magana ba, zuciyar ta fal tausayin ammin ta su,don ta san mene ne matsalar ta,yayan su ne,a da kullum a cikin kulawa dasu yake ko a waya ko a zahiri,amma tunda ya yi aure komai ya zama tarihi

Tana fita suka gamu da sulaiman a main parlour ɗin,cikin sanyin murya ta ce "sannu da zuwa yaya Sulaiman!"

"Yauwa sannu!Ammi fa?"

"Na baro ta yanzu,ta ce bacci zata yi"

"Okay!Nima bari na shiga na ɗan huta before ta tashi"

Har ya juya zai tafi,cikin sauri ta ce"yaya Sulaiman!"ya juyo ya na kallon ta,cikin sanyin murya ta ce"can we talk please? just two minutes"

Bai yi magana ba ya dawo ya zauna ya na kallon ta

Ƙwalla ta ciko idanun ta,ta ce"yaya me ya faru da big bruh?what changed him like that?our brother is very kind,but for now he changed totally,ko waya ba ya ɗagawa, daga baya ma muka daina samun shi,me yake faruwa ne?"

Sulaiman ya girgiza kai cikin sanyin murya ya ce "ban sani ba Surayya, almost a month kenan bamu yi waya da big bruh ba,tun da na kira shi ya gaggaya min magana,yanzu idan na kira shi ma bana samun shi"

Shiru Surayya ta yi kafin ta ce "to yaya why not baza kaje ka duba ko lafiya yake ba?"

Sulaiman ya girgiza kai yace"ƙalau yake Surayya,he just chose his wife over his family,mu bar shi yayi abinda yake so kawai"

"But yaya ya akayi ka san lafiya yake?"

Bai yi magana ba ya Ciro wayar shi ya buɗo hotunan Auwab da Inaaya da ya saka wani yaron shi yake bibiyar masa shi ya turo masa,ya nuna wa Surayya

Hotunan sun kai biyar,daga Auwab sai Inaaya,cikin matuƙar farin ciki suke da walwala, sai dai idan ba idanun ta keyi mata gizo ba sai taga kamar ya rame, hawaye ta goge ta miƙa wa Sulaiman wayar shi ba tare da ta sake magana ba, sulaiman ya amshi wayar,a hankali yace"kiyi masa addu'a,amma Auwab ya na buƙatar addu'ar mu sosai"bai jira amsar ta ba ya miƙe ya fice daga parlourn zuwa part ɗin shi


LUGARD ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA


"Mum kina nan?na same ki lafiya?"

Wani matsiyacin kallo ta watsa mata sannan ta ce"Bilkisu daga ina kike?"

Shiru ta yi ta na zama a gefen gadon ta ce"ba wani waje mai nisa na je ba,gidan ƙawa ta Nafisa naje ƴar ta na zazzaɓi na je dubiya"

"Okay!kina nufin kin baro gidan mijin naki ne don ki samu lasisin gantali yadda kike so?"mum ta faɗa a harzuƙe

"Mum gantali kuma? gantali kamar ya?"ta tambaya cike da takaicin maganar mum ɗin

Mum ta girgiza kai cikin takaici ta ce"wato Bilkisu kin baro gidan auren ki kawai don ki ja min matsala ko?wato so kike ki kashe naki auren kuma ki kashe min nawa ko?"

Zuciyar ta cike da haushi ta ce"mum me ya kawo wannan maganar kuma?"

"Look Bilkisu!kar ki raina min hankali!!na gaya miki ya rage naki ki ji ko kiyi kunnen uwar shegu,kar na sake ganin kin fita daga gidan nan ba tare da mijin ki ba,wato saboda wulaƙanci so kike ki janyo min magana a wajen daddyn ko?to ba zan iya wannan rashin arzikin ba,tafi ki bani waje"babu musu Beely ta ɗauki jakar ta da mayafin ta ta shige ɗakin ta ta na sauke ajiyar zuciya ganin da gaske mum bata gane inda taje ba,don faɗan mum ɗin bai wani dame ta ba


BRUNSWICK, MELBOURNE, AUSTRALIA


Waje ta samu ta zauna saboda ta gaji da tsayuwa,a karo na barkatai ta sake danna kiran number ɗin Azad wadda ake ta gaya mata a kashe ta ke,ta yi shiru cike da tashin hankali,don har magungunan mata ta sha don ta birkita Azad ya zamo nata ita kaɗai,amma a ƙarshe gashi sai kiran shi take yi wayar taƙi shiga

Ajiyar zuciya ta sauke ta tari cab ta wuce hotel ɗin da ta saba sauka ta yi hiring ɗaki zuciyar ta kamar ta fashe don ƙuna,ta samu waje ta zauna a gefen gadon ta ciro wayar ta ta ƙura wa hoton Azad da ya ɗora a dp ɗin shi na Whatsapp idanu,ya yi kyau sosai cikin wasu ash color hoodie riga da wandon ta,a hankali ta furta

"Ina son ka!ina ƙaunar ka!!kuma dole sai na mallake ka!!!"

AZAD

Kwanan shi biyu a hotel ɗin da ya kama,ya kashe wayar shi,sai dai idan yaso magana da mum ɗin shi ya nemi aron waya ya kira ta,ya rame sosai,amma ya ƙara fari,ko aiki baya zuwa don ya san fadeela za ta iya bin shi can

A kwanan shi na biyun ne ya shirya koma wa gida,shima bai isa gidan ba sai wajen karfe tara na dare

A parlour ya iske fadeela zaune,bai yi mata kallo biyu ba ma ballantana ya gane me take yi,sai dai bai kai ga shiga ɗakin shi ba ta tari gaban shi cikin ɗaga murya ta ce "Azad daga ina kake?"

Sheƙeƙe ya kalle ta, hankalin shi a kwance yace"bani hanya na wuce"

"Ba zan ba da hanyar ba,fasiƙi daga ina kake?"ta faɗa cikin ɗaga murya

"Fadeela!bani hanya na wuce!"

Cikin tsawa ta ce"bazaka wuce ɗin ba,baka isa ka shigar min gida bayan ka gama fasikanci da wata tsinanniya ba,ashe kai ɗan akuya ne ban sani ba?kalle ka kamar na kirki ashe fasiƙi ne?to ka koma wajen ta,don wallahi ba za ka shigar min gida ba"

Tsaki ya ja ya bangaje ta ya wuce,ta biyo shi ta na masifa,amma kafin ta kai ga shiga ɗakin ya hankaɗa ta ya rufe kofar ya bar ta ta na ta bala'in ta

Tunda ya shiga ɗakin bai fito ba sai washe gari,shima a parlour ya samu fadeelan,kafin ya ankara ta daka tsalle ta shaƙe masa wuya,ya sa hannu ya cire hannun ta,a nutse ya kalle ta yace"kina cin darajar mahaifiya ta ne yasa na ke ɗaga miki ƙafa,amma banda haka ke baki isa ki hau ko hanyar da nabi bane ballantana kizo kina yi min irin wannan rashin hankalin a gida"

"Kai ne mahaukaci!maci mana azzalumi!!me na rage ka da shi da har zaka tafi wajen wata?me take dashi da har tafi ni?"

"Wai ke a yadda kike ɗin gani kike ke mace ce?to you Are deceiving yourself Madam!ki fara sanin wace ce mace,sai ki san yadda za'ayi ki zamo kamar ta,amma ke baki kai nayi miki kallon mace ba"ya na kai wa nan,bai kula da yadda take bin shi da kallo ba ya zagaye ta ya wuce

Sai dai bai kai bakin ƙofa ya ji saukar abu akan shi da karfi,da sauri ya waigo ya na kallon fadeela riƙe da wani ƙaton ƙarfe,kafin ya yi magana jini ya wanke masa kai ya gangaro fuskar shi,shima a hankali ya fara ganin parlourn na juya masa ya na ganin komai bibbiyu,kafin wani lokacin ya daina gane komai,duhu ya mamaye jin shi da ganin shi,kafin ƙifta wa da bismillah ya sulale a wajen sumamme


Inyi ta Fulani,aradun Allah Azad kana cikin wani hali🥺

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee


*Young talented writers association (YOTA)*


Page 31

QUEEN'S COLLEGE, KANO STATE, NIGERIA

Ita kaɗai ce a zaune a ɗakin, Amra da Nabeela sun tafi wasannin sports da su kan yi a duk weekends,itama ta na zuwa,amma yau gaba ɗaya bata jin fitar ne shi yasa ta zauna ta na sake dudduba kyaututtukan da Sulaiman ya kawo mata a matsayin sakamakon winning na quiz da ta yi,sai dai kuma gaba ɗaya jikin ta a sanyaye yake,tunda ta turawa Azad saƙon kyaututtukan da ta samu na quiz ba ta sake samun shi ba ko a waya ko a Whatsapp,ta rasa menene matsalar,cikin sanyin jiki ta janyo wayar ta ta na kallon chat ɗin su na ƙarshe,inda yake jaddada ma ta zai yi mata komai in dai ta mayar da hankali ta yi karatu

Wayar ce ta yi ƙara,ganin number ɗin sulaiman yasa ta ɗaga da zumuɗi,ya na amsa sallamar ta ya ce"Allah ya taimaki likita bokan turai"

Dariya ta yi,ta gaishe shi a ladabce,ya ce "ga big bruh ku gaisa"

Ɗaure fuska ta yi,ta yi sallama a ciki,amma muryar wanda ta ji ya sa ba ta san sanda fara'ar fuskar ta ta dawo ba,da matuƙar farin ciki take faɗin "yaya Azad!"

"Khairi!ya makaranta?"

"Alhamdulillah yaya Azad!kwana biyu,ina aunty amarya?"

Ya yi murmushi ya ce "kwana biyu ayyuka sun yi min yawa,na ga nasarar da kikayi,yanzu da sulaiman ya zo ya sake tabbatar min, congratulations!zan ba shi alƙawarin da na yi ya kawo miki,ina fatan ki ɗore a haka"

Ba ta yi mamaki ko damuwa da rashin amsa mata tambayar aunty amarya da ta yi masa ba,don wannan ba komai bane a halin Azad rashin bawa abu muhimmanci,amma ta ji shi ba yadda ta saba jin shi ba,ta ce"yaya baka da lafiya ne?"

Ya ce"eh,ɗan zazzaɓi na yi,but I'm okay now,ki yi min addu'a kawai,bye!"ya kashe wayar

Khairi ta bi wayar da kallo jikin ta a sanya ye,a hankali ta furta "Allah ya baka lafiya yaya na"


BRUNSWICK, MELBOURNE, AUSTRALIA


Kallon shi kawai Sulaiman yake yi,bayan ya kashe wayar ya mayar da kanshi da ya sha naɗi da bandage jikin gadon da yake kwance ya kwantar ya lumshe idanu, sulaiman ya zuba masa idanu ya na kallon yadda ya rame ya yi haske,duk ya yi sanyi,ya chanja kamar ba Azad da ya sani ba

Azad ya buɗe idanu ya na kallon shi ya ce"sai yaushe su mom ɗin za su iso?"

Sulaiman ya girgiza kai yace"ban sani ba wallahi"

"Kai yaushe ka zo?"ya sake jefa masa tambaya ya na kallon shi

"Yau kwana na biyu, fadeela ce ta kira ni take shaida min abinda ya same ka,shine na taho ko su mum ban sanarwa ba,kuma n azo na same ka unconscious"

"Me ta ce ya same ni?"mamakin tambayar ya kama sulaiman,amma sai ya kanne ya ce

"Cewa ta yi accident ka yi ka bugu a kai"Azad bai sake Magana ba ya jinjina kai,sulaiman ya ce "ga abinci ma ta kawo maka"

"I'm okay,zo ka samo min tea kawai"

"Gashi nan ta haɗo har da shi ai"Azad ya yi jummm kafin ya ce"ko da yake bar tea ɗin ma,samo min fresh milk kawai"

Sulaiman bai yi masa musu ba ya fita don samo masa, Azad ya lumshe idanun shi abinda ya faru ya na dawo masa akai

Yau kwana huɗu da faruwar lamarin,tunda abin ya faru yake a sume, fadeela ce ta kai shi asibiti ta na gunjin kuka na tashin hankali,aka karɓe shi aka wuce emergency room dashi,a lokacin ta ɗauko wayar shi,ta so kiran iyayen shi amma tsoro ya hana ta,dole ta karkatar da akalar kiran ga Sulaiman da suke yawan communicating duk da cewa akan khairi ne,amma ita ba ta iya bata sani ba,tayi masa ƙaryar Azad ya gamu da accident,yanzu haka ya na asibiti bai san inda kan shi yake ba,Sulaiman ne ya ce ta kwantar da hankalin ta,a ranar ya yi boarding flight ya taho Australia

Bayan ya sauka ne da ya ga halin da yake ciki sai ya sanar da mum, Daddy da kuma Abba,yanzu haka mum da Abba suna hanyar zuwa Australia, daddy ne dai ba zai samu damar zuwa ba sai nan da ƴan kwanaki saboda aiki

Sulaiman bai jima da fita ba fadeela ta shigo ɗakin da sallama,jikin ta a sanya ye,ya amsa ba tare da ya buɗe idanun shi ba,ta samu waje ta zauna ta na faɗin "sannu,ya jikin?"

Bai buɗe idanu ba ya gyaɗa kai kawai,itama shiru ta yi ta na rarraba idanu gaban ta na faɗuwa,haka ta dage ta aro jarumta,cikin rawar murya ta ce

"I'm sorry please! I'm sorry!!in sha Allah hakan......"

"You are sorry?for what?"da sauri ta kalle shi,har yanzu idanun shi a lumshe,muryar shi ba ta fita sosai saboda yanayin jikin shi

Shiru tayi ƙwalla na tarar mata a idanu,ta na masifar son mijin ta bata son ta rabu dashi,bata taɓa yin abu taji ta yi nadama ba sai yau,bata kai ga sake magana ba Sulaiman ya shigo da sallama

Dukan su suka amsa,ya ƙaraso ciki,suka gaisa da fadeela a mutunce,yayi mata ya mai jiki?ta amsa, bai sake magana ba ya ɗauko cup ya na ƙoƙarin zuba masa fresh milk ɗin da ya siyo masa


"Bani a haka kawai"ya faɗa ya na miƙawa Sulaiman hannu, sulaiman ya miƙa masa gorar ya na kallon shi,suna kallon shi ya ɗaga gorar ya kafa a baki,sai da ya kusa shanyewa sannan ya ajiye ragowar ya sake jinginar da kanshi jikin gadon da yake kwance,dukkan su suna kallon shi

Har dare wata magana ta azo a gani bata shiga tsakanin Azad da fadeela ba,gashi Sulaiman tunda ya ga jikin Azad da sauƙi kuma yana samun kulawa bayan maghriba ya tafi masaukin shi bayan yayi musu sallama

Itama dai ganin babu wata makama yasa dole ta tafi gida jiki a saɓule,don duk tsiyar da take yi Azad baya tanka mata,hakan ba ya na nufin tsoron ta yakeji bane,itama ta sani,sai dai itama ta sani fushin mai haƙuri bai cika zama da daɗi ba

Washe gari wajen ƙarfe takwas na safe ta isa asibitin,a can ta samu Sulaiman ya na shirye shiryen zuwa ya taho da su mum da jirgin su ya sauka yanzu

Tunda taji batun saukar jirgin su mum gaban ta ya yi mummunan faɗuwa,ta ji kamar ta saki fitsari,a sanyaye ta ƙaraso ta gaida Sulaiman,ya amsa da fara'a,sannan ta gaida Azad,shima ya amsa kadaran kadaham,amma ko kallon ta bai yi ba


LUGARD ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA


Tana kallon wayar ta ta na ta ringing amma taƙi ɗagawa,sai murmushi take yi ta na faɗin "yadda na wahala kaima sai ka wahala wallahi,sai ka gane Bilkisu ba gama garin mata ba ce"ganin ya dame ta ma sai ta janyo wayar ta kashe ta,ta koma ta kwanta ta na ayyana yadda zata gara salis kafin ta koma gidan shi

Feena ce ta yi sallama ta shigo ɗakin da sallama, Muryar ta da alamun damuwa, Beely ta ɗago ta na kallon ta ta na amsa wa,feena ta samu waje a gefen gadon ta zauna fuskar ta da alamun damuwa

Beely ta ƙare mata kallo tace"ya dai?"

Hawaye ya zubowa feena tace"yayan mu bashi da lafiya,yanzu haka mum ta tafi Australia"

"Yayan mu ba shi da lafiya?tun yaushe?kuma yaushe mum ta tafi ban sani ba?"

Feena ta sauke ajiyar zuciya cike da damuwa tace"bakya nan yaya sulaiman ya kira ya shaida mata wai yayan mu ya yi accident ya na asibiti bai san inda kanshi yake ba"

"What!"Beely ta faɗa a firgice tana kallon ta idanun ta waje"ya akayi ba mu sani ba sai da yaya sulaiman ya kira ya sanar damu?"

"Nima ban sani ba aunty Beely,sai mum ta isa can zamu ji"

"To Allah yasa mu ji alkhairi, Allah ya bawa yayan mu lafiya "Beely ta faɗa jiki a sanyaye

"Ameen ya Allah "feena ta amsa,duk jikin ta a sanyaye


MELBOURNE PRIVATE HOSPITAL, MELBOURNE, AUSTRALIA


"Meya same ka haka son?garin yaya?"a cewar lieutenant general Usman cikin taushin murya

Ya ɗan kalli mum da take ta sharar ƙwalla,sannan ya kalli fadeela da ta yi tsuru tsuru,ya ɗauke kai ya mayar ga Abba,cikin girmamawa ya ce

"Abba ba wani abu bane,kawai ɗan saɓani muka samu da iyali na wannan tsautsayin ya gifta"

"What!me kace Azad?You mean fadeela ce ta ji maka wannan ciwon?kashe min kai tayi niyyar yi ko me?"a cewar mum a matuƙar kiɗime


Ko menene ya faru ai ke ki ka ja masa Hajiya mum!kowacce uwa fatan ta ta ɗauko wa ɗanta mace ta gari amma ke kika ɗaukowa ɗanki mutuniyar kawai


Kar dai a manta akwai VIP group #300 ne kacal

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️ Nusy bee


*Young talented writers association (YOTA)*


Page 32


Azad bai sake magana ba sai kanshi da ya jinginar jikin gadon ya lumshe idanun shi,daga Abba har Sulaiman kallon fadeela suke yi da matsanancin mamaki da kaɗuwa,ita kuma fadeela suman tsaye ta yi,a firgice take kallon mum da take mata wani mugun kallo

"Kashe min shi kika yi niyyar yi kenan?wannan shine sakamakon abinda nayi miki?na san ɗa na baya son ki amma nayi masa dole akan ya aure ki,ya aure ki ya zauna da ke,amma ƙarshe haka zakiyi min?wannan shine sakamakon abinda za ki yi min?to da kyau,na gode"mum ta ƙarasa ta na goge hawayen idanun ta

Abba ne yayi gyaran murya ya ce"duk abin bai kai haka ba Hajiya Salma,a zauna aji menene abin da ya haddasa wannan fitinar har ta kai wannan yarinyar ta yi wannan rashin wayon"Sulaiman ya miƙe tsam zai fice,don ya ga kamar abin bai shafe shi ba,mum ta ce"sulaiman ina zaka je?ka na jin za'a sabauta maka ɗan'uwan ka?"ba ta rufe baki ba Abba ya ce"Sulaiman have a seat!"babu musu ya zauna ya na sauraren mataki na gaba

Fadeela ta fashe da wani matsanancin kuka,Abba ya ce "calm down madam!ni tambayar ki kawai zanyi,menene ya kawo wannan tsautsayin har ki ka yi masa illa haka? ki duba fa,kwanan shi huɗu a asibiti bai san inda kanshi yake ba,to da kuma kin kashe shi fa?"

Cikin kuka ta durƙushe a wajen ta na faɗin"Abba laifin shi ne,bibiyar mata yake yi wallahi,har gida karuwar shi ta je wai ta na neman shi,na yi masa magana ya wulaƙanta ni ya fice daga gidan yaje ya kwana biyu da ita,raina ne ya kai ƙololuwar ɓaci shiyasa na yi masa haka,amma ku tambaye shi kuji hakan ba hali na bane"

Dukkan su kallon Azad da yake wata iriyar dariyar takaici suke yi,su dai kalaman fadeela ya basu mamaki don da alamun gaskiya a maganar ta

Abba cikin kwantar da murya ya ce"baba na!"Azad ya amsa cikin girmamawa"na'am Abba!"

"Mene ne gaskiyar abinda yarinyar nan ta faɗa?"Azad ya warware musu komai,tun daga lokacin da ta kwanta jinya har zuwa yau

A zabure mum ke kallon ta cikin kaɗuwa, sulaiman ma kallon nata yake yi da maɗaukakin mamaki,Abba cikin sanyin murya ya ce"abinda ya faɗa gaskiya ne?"

Fadeela ta ɗanyi shiru,sulaiman a fusace ya ce"Madam ba ki ji bane magana ake miki?"

"Gaskiya ne"ta bayar da amsa muryar ta na rawa"amma sharrin shaiɗan ne "

Mum ta fashe da kuka ta ce"yanzu fadeela niyyar ki ki kashe min ɗa saboda wani banzan kishin ki na wofi? fadeela dama kin zubar da cikin jikan nawa na farko da na ƙwallafa rai?kin cuce ni fadeela,amma bakiyiwa kowa ba sai kanki,akwai wani shaidan ne da ya wuce ki?kuma !n dai ni na haifi Azad auren ku ya ƙare daga yau"kafin ta rufe baki fadeela ta ruga da gudu ta kama ƙafafuwan mum ta na ihun kuka ta na ba ta haƙuri,mum ta hankaɗe ta a fusace ta fice ta bar ɗakin

Abba da Sulaiman kuwa kusan suman zaune suka yi da tsananin mamaki, Sulaiman ya zuba wa Azad idanu cike da tausayin shi,zuwa yanzu ya sake mayar da kanshi ya jinginar,da alamun damuwa ƙarara akan fuskar tashi

Daga baya Sulaiman ya kalli fadeela da take ta gunjin kuka,a ɗan fusace yace"Madam a asibiti muke, kuma mijin naki har yanzu ba lafiya ce dashi ba,don haka wannan koke koken ba buƙatar shi muke yi ba"tuni ta fara ƙoƙarin rage kukan ta na goge hawayen ta da yaƙi tsayawa,ita fa babu abinda ya ɗaga mata hankali kamar maganar sakin ta da taji mum ta na yi

Washegari aka sallami Azad,a ranar daddy ya zo,dukan su Brunswick suka ɗunguma suka tafi,mum sai kaffa kaffa take yi da ɗan ta da take jin kamar kowanne lokaci za'a iya raba ta dashi

Gidan dai sai a hankali,mum ce ta ɗan gyara wajen da za su zauna sai mita take yi tana surutai,don duk masifa da bala'i da rashin mutuncin mum ta tsani ƙazanta

Daddy ne ya fara kallon fadeela cikin kwantar da murya ya ce "meyasa kika yi hakan daughter?"

Ta share hawaye ta ce "sharrin shaiɗan daddy,amma in sha Allah hakan bazai sake faruwa ba"

"Ai hakan ba zai sake faruwa ba kuwa,don zaman ki da Azad yazo ƙarshe "a cewar mum a fusace

"Salma bana son jin bakin ki anan,ki bari mu bi komai a sannu"

"Daddy ni ba zan saki mata ta ba ma,shine kawai"

Ba Daddy ko mum ba,hatta ita kanta fadeela, sulaiman da Abba sai da suka kalli Azad da ya ɗauke kai bayan ya yi wannan bayanin

Shiru parlourn ya ɗauka na ƴan mintuna kafin Daddy ya ce"to Allah ya sake kaɗa fitina,don Allah ya kamata mu rinƙa danne fushi,sannan mu fahimci abokan zaman mu tare da yi musu uzuri,sannan magana ta gaba,tunda kuka zauna ƙarƙashin inuwar aure maganar ba'a shirya wa haihuwa ba bata taso ba,amma ke idan bakya so ya kamata ki yi masa adalci ya auro wadda zata haifar masa"

"Na amince ma Daddy!na yarda zan haihu wallahi "ta faɗa cikin rawar murya"Daddy ya cigaba da yi musu nasiha,mum dai kamar ta fashe,basu juma ba suka yi musu sallama suka tafi masaukin su,amma mum a gidan zata kwana

Yana zaune a bedroom ɗin shi yana shan farfesun kifin da mum ɗin shi ta yi masa,wayar shi a hannun shi ya na chat da ƙannen shi da suke tambayar jikin shi,akwai matuƙar shaƙuwa tsakanin shi da ƙannen shi duk da kasancewar bashi da yawan magana da fara'a,yana matuƙar ƙaunar duk wani jinin shi a rayuwar shi,shi yasa suma suke ƙaunar shi

Sallamar fadeelaya ji, fuska babu yabo babu fallasa ya amsa,ta ƙaraso ta na tambayar shi jiki,ya amsa da sauƙi batare da ya kalle ta ba,cikin sanyin murya tace

"Ina so muyi magana Azad"

"Kar ki damu, faɗi duk abinda zaki faɗa"

Ta goge hawaye tace"don Allah kayi ......"

"Enough please fadeela!bana son dawo da hannu agogo baya,say something different please"

Shiru tayi,shima ya cigaba da abinda yake yi,dama ko sashen da take bai kalla ba

Mum ce ta shigo da sallama,tana jin sallamar mum ta miƙe a firgice, fuskar mum murtuk ta dube ta tace"me kike yi wa ɗa na?ko zuwa kika yi ki ƙarasa abinda kika fara?"shiru ta yi ta na ƙiƙƙifta idanu,mum ta nuna mata hanya ta na faɗin "bamu waje,zan tattauna da ɗana"sum sum sum fadeela ta fice daga ɗakin

Mum ta dube shi fuska a ɗaure ta ce"ka ce ba za ka sake ta ba ko?"

Ya ɗago kai a nutse ya kalli mum ya ce"eh mum!ke ce ki ka zaɓa min ita,a lokacin idan baki manta ba sai da nace idan ta yi miki ni ma tayi min,ba wai ina nufin wani abu ba sai tarbiyyar ta,tun lokacin da na fara ganin ta na san ba ta da tarbiyya,kema kin san da hakan,amma kika rufe idanun ki ki ka ce na aure ta,mum tun a lokacin kika yankar min ticket na hawa SIRAƊIN UƘUBA!gashi nan har yanzu ban sauka ba,kuma ban san ranar sauka ba,don tunda ki ka zaɓar min ita mum bazan sake ta ba,abu ɗaya kawai,na gaya miki zan ƙara aure idan lokaci yayi,kuma har yanzu ina da wannan ƙudurin,ina fatan idan lokaci ya yi za ki bani goyon baya "yana kai wa nan ya miƙe tsaye yace"excuse me mummy na!"ya shiga banɗaki ya bar mum da ta yi mutuwar zaune ta bishi da kallo


HOTORO GRA, KANO STATE, NIGERIA


Tura ƙofar ta yi kai tsaye ba tare da ta yi sallama ba,mayafin da ta ɗora akan kafaɗar ta ta cire ta riƙe a hannu ta na jefa wa Samha dake zaune ta na ba wa ɗan ta abinci wani mugun kallo,kallo ɗaya Samha ta yi mata ta ɗauke kanta ta ci gaba da abinda take yi

Salis ya miƙe da sauri ya rungume Beely ya na kissing goshin ta,itama ta sake rungume shi sosai,murya ƙasa ƙasa ya furta "I miss you so much babe!gidan nan yayi duhu da babu ke"

Murmushi ta yi ta sake rungume shi, kafin ta janyo hannun shi suka fice daga parlourn suka bar Samha da baki buɗe tana bin su da kallo

Suna daf da fita ta juyo ta kashe wa Samha ido ɗaya ta na murmushi sannan ta juya ta bi shi suka fice daga parlourn

Daga lokacin zaman ya sauya salo,duk wani makirci da kissa na Samha sai dai ya tashi a banza, Beely ta mallake gidan, kullum samha bata da aiki sai kuka

Yau Samha ta gaji, wulaƙancin Salis ya ishe ta,don haka kai tsaye ta nufi part ɗin Beely inda suke zaune suna shan soyayya

Da sallama ta shiga muryar ta a sanyaye saboda kukan da bata rabo dashi kusan koyaushe, Beely ta ɗago a wulaƙance ta kalle ta ta ɗauke kai, Samha cikin sanyin murya ta ce"abban Aman ina son magana da kai"

"Ina jin ki"ya amsa fuska babu yabo babu fallasa

Shiru ta yi ta na kallon shi,ya ɗaga kai ya na kallon ta fuska a ɗan ɗaure,ita dai Beely dake kwance a kan ƙirjin shi ko kallo biyu ba tayi mata ba

"Please zaka iya bani two minutes muyi magana a waje?"girgiza kai ya yi ya ce "ko me zaki faɗa ki faɗa anan"

Cikin kuka tace"amma abban Aman ya kamata ka ji tsoron Allah,yanzu a gidan nan yaushe rabon ka da yi mana rabon kwana?ka zo ka tare a part ɗin ta, ko ƴar leƙawar da kake yi mana ka na ganin lafiyar mu yanzu ka daina, Aman bashi da damar da zai zo ya ganka,wai duk meye wannan ne?"

"Ra'ayi na!haka na ga dama!idan kuma ba za ki iya ba kina iya tafiya,sai ki zaɓa "

"Amma abban......."

"Silent Madam!na gama magana "Samha ta kalle su hawaye ya na ambaliya a idanun ta,kafin ta juya ta koma part ɗin ta tana kuka har da shashsheƙa,gaba ɗaya kanta ya kulle, tunanin yadda za ta yiwa Beely kawai take yi ta rasa mafita

BOSTON, MASSACHUSETTS,USA

Cikin bacci take jin ringing ɗin wayar ta na tashi,a hankali ta buɗe idanu tana ƙiƙƙifta su,ta ja wani siririn tsaki ta na janyo wayar,kafin ta ɗaga ta katse,bata duba sunan mai kiran ba ta mayar da wayar ta sake kwanciya

Wani dogon tsakin ta sake ja lokacin da wayar ta sake ruri a karo na biyu,ta janyo wayar ta duba mai kiran, Shukra ce,ta ɗaga ta saka a speaker ta fara gyara dogon gashin ta ba tare da tayi magana ba

Shukra ce ta fara magana "babe gashi na zo,ina airport"

"Ki ƙaraso"amsar da ta bawa Shukra kenan ta kashe wayar

A kasalance ta miƙe ta shiga toilet tayi wanka,babu maganar Sallah,ta sauya kaya cikin wasu riga da wando da ya haura gwiwa da kaɗan,ta saki yalwataccen gashin ta baya,ta fito parlourn ta na ƙare wa ko'ina kallo

Yau Auwab kwanan shi biyu a China,sun je wani taron ƴan kasuwa shi da mr Johnson Philip,dama shi yake gyara ko'ina idan ya na nan,babu abinda take yi sai shan soyayya da mijin ta

Tsaki ta ja ta na tunanin ko mei aiki za ta ɗauka,amma ita bata son mai aikin da za ta shiga tsakanin ta da mijin ta,asalima ta tsani wata mace ta shigo musu ko a yaya ne kuwa,yadda take jin so da kishin Auwab da tana da hali da sai ta yi masa yadda ba zai taɓa kallon wata mace da sunan mace ba

Tana zaune a parlourn tana danna waya Shukra ta shigo,ta ɗaga kai ta na ƙare mata kallo, sanye take da wasu skinny riga da wando,ta ɗora wani matsiyacin mayafi akan attachment ɗin kanta,ta saka baƙin spec da ya cinye kusan rabin fuskar ta

Kallon ta kawai Inaaya take yi fuska babu rahama, Shukra ta ƙaraso ta zauna ta na murmushi,a gadarance Inaaya ta ce"wannan shigar fa?"

"Haba babe!ke fa kika ce baya nan"

"To idan ya dawo fa?"Shukra tayi murmushi ta ce"mijin ki ai mijin ki ne,babu wata mace da ta isa ta shiga tsakanin ku ko ta burge shi ma,ni ba wannan ba ma,ga maganin,kuma Safwan ya na gari"ta ƙarasa ta na miƙa mata wani ƙullin magani da ta ɗauko a jakar ta

Inaaya ta amshi maganin da yatsu biyu ba tare da ta yi magana ba,sai yatsina fuska da ta ke yi cike da isa,Shukra ta ce"yace aikin ne ya yi sanyi, shi yasa kwanakin nan ya chanja miki ba kamar baya ba,yanzu dai ga wannan,a abincin shi za ki saka masa,wannan kuma a fuskar ki za ki shafa,in dai ya kalle ki to magana ta ƙare "

"Ya yi,nawa ne cikon kuɗin shi?"

Shukra ta juya kai ta ce"na cika miki,2m za ki bayar yanzu kawai"babu musu Inaaya ta ɗauko wayar ta ta turawa Shukra 2m, Shukra kamar zata kifa saboda farin ciki,amma ba ta nuna ba

Da yamma tare suka fita, Shukra ta kwana wajen wani saurayin ta,ita kuma ta kwana a wajen Safwan

Washegari Safwan da Shukra suka koma Nigeria bayan Inaaya ta sallami Shukra da 1m,kuma ba tare da ɓata lokaci ba ta fara aiwatar da amfanin ta da magungunan ta

Tabbas ta ga sauyi,don ba ƙaramin rikice mata Auwab yayi ba da ya dawo, Inaaya dai rayuwar ta na yi mata daɗi sosai, Auwab ya zama nata ita kaɗai,ko tuna Nigeria ba ya yi ballantana yayi tunanin kai mata ziyara

Yau suna zaune a parlourn su suna shan soyayyar su,sai shagwaɓa ta ke zuba masa,kiran Abba ya shigo wayar Auwab

Da farko bai yi niyyar ɗaga wa ba,amma jin kiran akai akai ya sa ya janyo wayar ya duba,ganin Abba ya sa ya ɗaga da sauri

Abba bai saurari gaisuwar shi ba ya ce ya na bakin gate ya zo ya buɗe masa ƙofa

Tare da Inaaya suka nufi bakin gate ɗin,a gadarance Inaaya ta ke tafiya,amma suna buɗe ƙofa suka yi arba da Abba a tsaye tuni ta sunkuyar da kanta, saboda kwarjinin da yayi mata

To pa!ga Abba a gidan Auwab?ko yaya za ta kaya? Azad ya yi daidai da ya ce ba zai saki Inaaya ba?

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️ Nusy bee


*Young talented writers association (YOTA)*


Page 33


A nutse lieutenant general Usman yake ƙare musu kallo, Auwab ya rissina ya na masa barka da zuwa,ya amsa fuska babu yabo babu fallasa,ita ma dai Inaaya bata da zaɓin da ya wuce rissina wa ta gaishe shi

Auwab ne ya jagoranci Abba zuwa cikin gidan,bayan sun zauna suka gaida Abba a ladabce

Shima ya amsa gaisuwar cikin kulawa, Auwab cikin zaƙu wa ya kalli Inaaya ya ce"a kawo wa Daddy abin taɓa wa"don Allah ya sani ya yi kewar family ɗin nashi sosai,wani irin nishaɗi da annushuwa ya ji yana shigar shi saboda ganin Abba

Abba ya yi saurin dakatar da ita da faɗin "no!bar shi kawai,ɗan bamu waje dai zamu yi magana"Inaaya ta miƙe a hankali ta fice daga parlourn,amma sai ta samu waje ta laɓe don jin me za su tattauna

Abba ya mayar da hankalin shi kan Auwab da ya yi ƙasa da kanshi ya na sauraren abinda zai fito daga bakin mahaifin nashi,a nutse Abba ya fara

"Muhammad ka ɗauke ƙafa,babu kira,babu zuwa,babu wanda yake jin motsin ka,ka yi faɗa da brother ɗin ka da yake a matsayin ƙani,yaya,amini, abokin kuka kuma abokin dariya a gare ka,ka rabu da mahaifiyar ka da take ƙaunar ka,baka da kamar ta,me yayi zafi haka?laifin me akayi maka haka?

Yanzu haka maman ka ta na cikin damuwa, ba'a maganar ƴan uwan ka,amma ko a waya ba ka kira ka ji lafiyar su ba, ballantana a saka ran za ka je ka gansu, aure fa ba hauka bane Muhammad,aure hankali yake saka wa ba shirme ba,yanzu kai baka koyi da ɗan'uwan ka?shima yayi aure,ko nace ya riga ka ma,ya yi nesa da gida,amma har yanzu ya na communicating da ƴan uwan shi, mene ne yake faruwa ne Muhammad?"

Shiru Auwab ya yi kanshi a ƙasa,ya rasa hujja ɗaya da zai riƙe ya bawa Abba,shi dai haka yaji all of a sudden ba ya ƙaunar ko kiran shi a yi a waya idan ba matar shi ba, Abba ya yi masa nasiha sosai,a ƙarshe yace"ka kira ɗan'uwan ka Azad,bashi da lafiya,ka duba shi,ni zan tafi"ya miƙe tsaye

Shine ya rako Abba har bakin gate bayan sun yi sallama da Inaaya da ta ke ta hararar abban a fakaice,dattijon arziƙi ya ankara da ita,amma sai ya nuna kamar bai ganta ba,bayan Abba ya shiga taxi ɗin da Auwab ya yi masa boarding ya dube shi a nutse ya ce

"Muhammad!kar dai a rinƙa wasa da Sallah,a riƙe addu'a,ita ce makamin mumini"

"In sha Allah Abba,na gode sosai, Allah ya tsare hanya"

"Ameen,idan ka samu lokaci ka kira mahaifiyar ka ka gaishe ta,hakan zai rage mata damuwar da take ciki"

"Zan yi hakan in sha Allah Abba!"

"Ya yi kyau,sannan ka kira ɗan'uwan ka ku sasanta,na san Sulaiman ba shi da matsala,kuma kai ma ina fatan ka dawo hayyacin ka"

Auwab ya sunkuyar da kai kawai, motar su Abba ta tashi,suna ɗaga wa juna hannu, Auwab ya koma gidan da saɓulallen jiki

A cikin gida kuwa,can cikin ɗakin ta Inaaya ta shige ta rufe ƙofar,hakan bai mata ba sai da ta shige cikin banɗakin dake cikin ɗakin nata ta rufo ƙofar ta ɗaga waya ta kira Shukra

Shukra ta ɗaga waya ta na faɗin "sai da ke matar engineer!"

"Ba lokacin shirme ba ne Shukra,ina cikin damuwa,baya ta haihu Shukra"

"To fa!me ya faru kuma?"

Inaaya ta bawa Shukra labarin zuwan mahaifin Auwab da irin maganganun da taji ya na gaya wa ɗan nashi, Shukra ta yi shiru kafin ta ce"don wannan kar ki damu,suma dangin na shi zamu yi musu aike su manta da shi"

"Kamar yaya su manta da shi?"

"To mene ne amfanin tunawar?ba gwara su manta shi ba?idan ba haka ba yanzu suka fara yi muku zarya tunda su wahalallu ne"

Inaaya ta ja numfashi ta fesar ta ce"to ayi hakan kawai,ko nawa ne zan biya,idan yaso sai ki kira ni ki gaya min"

"Babu Matsala,sai kin ji ni"Inaaya ba ta sake magana ba ta kashe wayar tana hura hanci,ran ta a matuƙar ɓace


BRUNSWICK, MELBOURNE, AUSTRALIA


A karo na kusan uku ta sake yunƙurin shiga ɗakin na shi,wannan karon dai ta yi ta maza ta shiga,ya na zaune daga shi sai shortneaker da singlet,tuni ciwon nashi ya warke,don yau tsawon sati hudu kenan da faruwar al'amarin,kuma tunda su mom suka tafi suka fara wani irin zama,ita dai ba zata ce ya ɗaure mata fuska ba,amma ba ta ganin fuskar komai daga gare shi,ba ta nema ta rasa ba,amma sam zaman gidan baya yi mata daɗi,kuma ya ƙaurace mata kwata kwata,tunda ya gane ta zubar masa da ciki bai ƙara yarda wani abu ya shiga tsakanin su ba,dama ta daɗe da fahimtar Azad mutum ne mai ƙarancin sha'awar mace,kishi ne ya rufe ma ta idanu har ta yi abinda ta yi masa da sunan hukunci kan ya na bin mata

Ya amsa sallamar ta ba tare da ya kalle ta ba,takardu ne a hannun shi ya ke dubawa,ta shigo jiki a sanyaye ta nemi waje ta zauna,a sanya ye ta ce"good evening sweetheart!"

Ba tare da ya kalle ta ba ya ce"evening ma'am!"

Shiru ta yi bata sake magana ba, saboda ta rasa abin cewa,shi kam dama ba daina abinda yake yi ya yi ba

Da ƙyar ta iya jarumtar faɗin"dama ina so mu yi magana ne"

"Uhm! I'm all ears!"ya sake faɗa ba tare da ya kalle ta ba

"Dama.... dama.....na ga kwana biyu ba ka kula ni ne"

"Kula ki kamar yaya?"

Shiru ta yi, don duk fitsarar ta ta na shakkar Azad

Ganin ba shi da niyyar magana ya sa ta ƙara dagewa ta ce"game da haƙƙi na....na....na....aure"

Shiru ya yi bai tanka ta ba,dama duk abinda akeyi ko sau ɗaya bai kalle ta ba,har ta fitar da rai zai sake magana ta ji yace"ba yanzu ba,sai kin shirya wa haihuwa"

Da sauri ta kalle shi,a raunane ta ce"na shirya wa haihuwa wallahi,ko yara nawa ka ke so a shirye nake da na haifa maka"

"Ayya!Ni kuma kinga batun haihuwar yanzu ya fice min a kai,sai dai ko nan gaba"

Ta ɗan yi shiru kafin ta ce"to me zai hana mu dakatar da haihuwar yanzu,idan yaso a lokacin da ka buƙaci haihuwar sai mu haihu?"

Girgiza kai ya yi ya ce"yadda na ce hakan za'a yi,hakan na zaɓa,idan baki da wani abin faɗar I need space please!"

Ta fashe da kuka ta ce "don Allah Azad ka yi haƙuri, wallahi hukuncin nan yayi min tsauri,yanzu......"

"Excuse me ma'am! I need space!!"ya faɗa da ƴar tsawa tsawa yana kallon ta fuska a murtuke.. miƙewa tayi cikin kuka ta fice daga ɗakin, zuciyar ta kamar ta fashe saboda tashin hankali da damuwa


HAƊEJIA ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA


"Yanzu sati biyar ya rage mifra ta kammala karatun ta,kuma ta na kammala wa za'a saka bikin ku,ga Amra,ga kuma feena ƴar wajen Hajiya Salma"

Sulaiman ya ce"Allah ya nuna mana Ammi,yanzu dai me za'a shirya?"

"Abubuwa da yawa mana,don na san dai ba za'a saka bikin da nisa ba"

Sulaiman ya ce"to Allah ya bamu ikon shiryawa da kyau,ina Surayya?"

Ammi ta na murmushi tace"auta ta?har yanzu ba ta dawo daga school ba,gaba ɗaya kewar ta nake yi kamar na bi ta"ta ƙarashe ta na murmushi,don ta san halin Sulaiman

Sulaiman ya taɓe baki yace"gaskiya ne zaki bi ta,mu dama ai mun daɗe da sanin mu ba ƴaƴa bane,sai wata auta"Ammi ta kwashe da dariya ta ce"amma anji kunya Sulaiman,yanzu da autar tawa kake kishi?"

Sulaiman yayi dariya ya miƙe ya na faɗin"Ammi bari in ci abincin nan nawa kar ya sandare"ya wuce dinning area inda ta shirya masa abincin dare


QUEEN'S COLLEGE, KANO STATE, NIGERIA


Bahaushe yace yau da gobe bata bar komai ba,kwance tashi babu wuya wajen Allah,yau ne su khairi ke hutun session,sai murna suke yi saboda result ɗin su ya yi kyau sosai,kuma a wannan hutun ne khairi zata ziyarci albasu kamar yadda take roƙon Daddy,zasu tafi tare da aunty Naja
Yanzu zaman ta a gidan babu wata matsala,tunda mum taje Australia gidan Azad, watanni uku kenan shikenan ta rasa nutsuwar ta,hakan baya rasa nasaba da sanya wa da tayi a rai cewa fadeela zata ƙara cutar mata da ɗa, shiyasa kusan kullum cikin kiran shi take ta ji lafiyar shi

Yanzu wannan damuwar ta shafe tunanin komai a ranta, shi yasa aunty Naja da khairi ba sa gaban ta,yanzu rayuwar su sukeyi peacefully a gidan ba tare da wata tsangwama ko kyara ba

Kamar yadda ta saba yau ma sulaiman ne ya zo ya ɗauke ta ya mayar da ita gida,a ranar suka shirya duk abinda suke buƙata,duk da cewa bata yi zama mai daɗi a albasu ba amma tana kewar garin

Washegari da safe wajen ƙarfe tara motar aunty Naja ta ɗaga ita da khairi suka nufi albasu cike da ɗokin ganin ƴan uwa,khairi gani takeyi kamar ba'a sauri

To sai mu ce Allah ya kai ku lafiya matafiya😍


Kar dai a manta akwai VIP group #300 kacal


#Nusy_bee


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️ Nusy bee


*Young talented writers association (YOTA)*


Page 34

Tafiyar ƴan awanni ya kai su ƙauyen albasu,khairi sai kallon ƙofar gidan su take yi tana ta murmushi

Nadiya ce ta fito daga gidan hannun ta riƙe da bokitin ɗibar ruwa,da gudu khairi ta buɗe motar ta fice ta nufi Nadiya ta rungume ta tana murna

Da maɗaukakin mamaki da farin ciki Nadiya take kallon khairi

"Ummiyo!yau ke ce a garin namu?"khairi dai ba baki sai murmushi da ta ke tayi

Aunty Naja da ta rufe motar ta ƙaraso ta na faɗin "mu shiga daga ciki ko? sai a fi jin daɗin murnar"babu musu Nadiya ta ja hannun khairi suka yi cikin gidan da sauri ta na faɗin "jama'a ga ummiyo yau Allah ya kawo mana ita,yau dai ga ummiyo a gidan mu"

Kusan kowa fito wa ya yi yan a kallon khairi,sai murmushi take yi,ta yi ƙiba sosai abin ta,fatar nan tayi fes,tayi haske,asalin chaculate skin ɗin ta ta bayyana,ta juye kamannin mahaifiyar ta sak,duk da ita ba fara bace,tayi kyau sosai cikin tsadaddiyar abayar da daddy ya siyo musu ba da jumawa ba da yaje Umrah

Inna sabuwa ya fara zuwa ta gaida,sai kallon ta take yi kamar ta ga baƙuwar halitta,amsa wa ma a ciki ciki tayi,bata kula ba,don ta saba da abinda yafi haka ma, Nadiya ta raka su suka gaida sauran matan gidan,sannan suka fice suka nufi rafin garin

Anan su ka zauna suna hira,Nadiya take bata labarin ai anyi auren da yawa daga ƴan matan gidan,suma jira suke yi su rubuta placement sai ayi nasu bikin

Khairi ta ce"ikon Allah!yanzu an yi auren su lubabatu?"

Nadiya ta ce"anyi auren su,don yanzu Maryama ma tsohon ciki haihuwa Yau ko gobe,sameera tayi ɓari har sau biyu,zainaba ma dai cikin yau ko gobe "

"To Allah ya raba su lafiya,idan na samu dama zan leƙa musu,kema Allah ya kawo naki lokacin da alkhairi "Nadiya tana murmushi ta ce"ameen ummiyo,kema Allah ya kawo naki da alkhairi "khairi ta yi murmushi ta ce"mu kam aure ai ba yanzu ba,don mu a can wadda ta bani shekara shida ma ai yarinya ce"

"Wai!shekarun ki sha huɗu fa yanzu kin shiga sha biyar ma ummiyo!yanzu sai a kira ƴar shekara ashirin yarinya?"

Khairi ta na murmushi ta ce"zan so watarana kije ki ga rayuwar maraya,komai nasu ba irin namu bane,suna bawa karatu muhimmanci sosai,saɓanin nan karkara da muke fifita talla"

Nadiya ta na murmushi ta ce"mu ma dai Allah ya sa muna da rabon rayuwar birnin nan"

Khairi tace"ameen Nadiya, Allah ya kawo mijin ki ya dawo birni gaba ɗaya da zama,kema ya mayar da ke makaranta ki cigaba da karatun ki"Nadiya ta ɗaga hannu sama ta na faɗin"ameen dai ƙawar arziƙi, wallahi ba ni da burin da ya wuce na gan ni ina karatu, karatu akwai daɗi"khairi tace"sosai ma kuwa Nadiya"suka cigaba da hirar su cikin farin ciki da kewar juna


HOTORO GRA, KANO STATE, NIGERIA


"Please sorry wife! ki daure ki ci ko yaya ne,ba na jin daɗi idan na ga kina zama da yunwar nan"ta sake narke masa a jiki ta na ta zuba shagwaɓa,da ƙyar ya samu taci faten wake da alayyahun da ya karɓo mata yanzu a wajen hajiyar su,ganin ta na yunƙurin amai ya sanya ya yi saurin ajiye cokalin da yake bata ya rungume ta ya na bubbbuga bayan ta kaɗan har abincin ya lafa mata

Bayan dawowar ta babu juma wa sosai ta fara jinya,gwajin farko da yayi mata da kanshi sai ga ɗan ƙaramin ciki,yayi matuƙar farin ciki,to fa tun daga lokacin ya fara bata wata iriyar kula wa kamar ba'a taɓa yi masa haihuwa ba,ita kuwa sai sake taɓarewa take yi,samha kuwa tuni aka daɗe da jinginar da ita a gefe,daga ita har yaron ta sun zama abin tausayi a gidan

Ta yi yaji ta je gida,amma mahaifiyar ta ta fatattake ta,a cewar ta dama itama samha ɗin ba ta son zaman lafiya,tilas ta zo ta zauna rayuwar ƙunci,tunda yanzu ko ta yi makircin baya tasiri,idan ta ce zata tayar da hargitsi ma abin kan ta yake ƙare wa

Yau ta na zaune a parlourn ta,girki ta ke so ta je ta ɗora saboda Aman da ya kusa dawo wa,amma gaba ɗaya damuwa ta hana ta motsawa

Ta rame sosai,ta fice a hayyacin ta,ɗan gayun da take yi yanzu sam babu shi

Tana nan zaune ta ji sallama,da sauri ta ɗaga kai ta na amsa sallamar yayar ta aunty Asiya

"Sannu da zuwa aunty!yau kece a gidan namu?"aunty Asiya ba ta amsa mata ba ta shigo ta nemi waje ta zauna ta na kallon ta

Gaishe ta tayi,aunty ta amsa ta na kwanto goyon da yake bayan ta, Samha ta miƙe ta kawo mata ruwa da lemo

Aunty Asiya ta ce"ba zama nazo yi ba Samha,ɗazu ɗazu jirgin mu ya sauka daga Lagos,bayan na zo gida nake jin wani labari a wajen fati(autar ɗakin su)me yake faruwa ne Samha?ya na gan ki haka?"

Hawaye suka zubo mata,ta na girgiza kai ta ce"aunty wallahi yanzu auren Dr ya fice min akai,wulaƙanci,kyara,cin mutunci babu wanda ba ma gani a gidan nan ni da ɗana,amaryar shi yanzu itace komai nashi,ko magana nayi baya sauraro na,jiya da na yi masa maganar bayan na same shi a parking space sai ya rufe ni da faɗa wai na bar shi ya sha iska,matar shi ta na da ciki,na gwada duk wata kissar mu ta mata bata aiki,gani nake yi kamar asiri ta ke masa ......."

"Kul!kul!!ke kina da tabbacin abinda kika faɗa na cewa kishiyar ta ki tana biye biyen bokaye?ke Samha! kar ki je ki daure kanki,zato zunubi ko da ya kasance gaskiya"aunty Asiya ta katse ta a ɗan zafafe

Cikin kuka Samha ta ce"ina da tabbaci aunty, saboda lokacin da Dr zai ƙara aure ta gaya min mu nemi malamai, matsiyaciyar ashe ita zai aura,kuma a ƴan kwanakin nan na samu na shawo kan miji na,amma ta sake janye masa hankali da asiri,yanzu ko kallon banza ban ishe shi ba,ni ban ce kar ya so matar shi ba,amma ya yi mana adalci, fisabilillahi a haka zan ƙare rayuwa ta kenan?"

Shiru aunty Asiya ta yi,duk da itama ta san ƙanwar ta ta bata ji amma ta ba ta tausayi,akwai ciwo sosai mijin da mace ta ƙwallafa rai akan shi ya juya mata baya,ta ɗan nisa kafin tace"to ko ma dai mene ne,wani kuka ko baƙin ciki ba zai magance shi ba, Samha ki tashi ki nemi taimakon Allah,ba wai ina nufin kema ki nemi malamai ba, a'a,ki rungumi Alqur'ani da sunnah

Na farko ki dage da yawaita karanta Alqur'ani a gidan ki,ko ba ki karanta ba ki rinƙa kunna wa,ya zama na a gidan ki akwai wani sauti da yake tashi na Alqur'ani,ki yawaita azkar a kowanne lokaci na rayuwar ki,sannan ki rungumi haƙuri,ki mayar da komai ga Allah,ki saka a ranki cewa Allahn da ya jarabce ki shi zai yaye miki,babu mai yi miki sai shi,ki mance da wani tuggu da makirci don ba shi da amfani,ba shi da rana,ki gwada hakan na tsawon wata guda kacal,ki kira ni ki ba ni labari

Sannan magana ta gaba kuma,kar na ji kar na sake ji kina gaya wa mutane wai ƙawar ki ta yaudare ki ta aure miki miji, Allah ya ƙaddara shine mijin ta ita ma,ku gina rayuwar aure akan ibada da neman aljanna,hakan zai fi muku,da tun farko akan hakan ku ka gina rayuwar auren ku da ba za ki damu ba idan ki ka gan ta a matsayin kishiya, itama ba za ta damu ba idan ta ga mijin ki ta aura"aunty Asiya ta miƙe tsaye ta na faɗin"sai na jiki,don yanzu ni dai banga ta zama ba"cikin sanyin jiki Samha ta rako ta ta na mata godiya,ita kuma ta na ta jadadda mata abubuwan da ta gaya mata

Ƴar wannan tattaunawar da Samha ta yi da yayar ta ya saka mata nutsuwa,bayan tafiyar yayar ta ta ta ja ajiyar zuciya ta koma cikin gida,ta kama tattare gidan bayan ta kunna suratul baƙara a wayar ta,ita kanta da tana sauraren karatun wata nutsuwa ta musamman ce ta ke saukar mata


BOSTON, MASSACHUSETTS,USA


Da alamu dai aikin su Inaaya yayi tasiri,don tun daga lokacin da Abba ya zo babu wanda ya sake bibiyar Auwab,shima tuni ya manta da wasu family ɗin shi,rayuwa suke yi cike da farin ciki shi da matar shi abar ƙaunar shi Inaaya

Baya ga aikin da ta saka aka yi na mantar da dangin Auwab shi ta saka ayi wa Daddy aikin da za'a jefa masa wata matsananciyar cutar,don tabbas ranta ya ɓaci saboda shishshigin da ya yi mata a cewar ta

Da ƙyar aikin ya yiwu,shima sai da aka dangana da ƙasar India,don Daddy na matuƙar ƙoƙarin riƙe addu'a a duk inda yake

Bayan ta samu wannan tabbacin ne sai ta ci gaba da rayuwar ta cikin kwanciyar hankali,ƙarshe ma sai ta saka Auwab ya ɗauki hutu suka bar ƙasar zuwa Mauritius,don huta wa acan


HAƊEJIA ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA


Yau tsawon sati biyu kenan da Abba ya zauna a gida ba ya zuwa ko'ina saboda matsanancin ciwon ƙafa da yake fama dashi, dalilin haka aka ɗage maganar bikin su Sulaiman, saboda ƙafar ta matsa masa sosai,sun bi private hospitals masu kyau a Kano, Kaduna,Abuja da Lagos,har ma da wasu garuruwan a sassan Nigeria amma babu wani cigaba,asalima abu ɗaya ake faɗa duk sanda akayi wa ƙafar hoto cewa lafiya ƙalau take,gashi kuma bata barin shi ya yi ko da barci ne

Ammi kam gaba ɗaya hankalin ta ya tashi,ta gigice sosai, ba'a maganar su Surayya da Amra,don kuka ma suke yi idan suka ga yadda mahaifin nasu yake wahala

Sulaiman ne ya shirya fita dashi ƙasar Egypt,shima dai hankalin nashi ba'a kwance yake ba,gaba ɗaya ya rame,ga shi kusan dukkan su akwai abinda suke tunani sai dai sun rasa mene ne shi,banda damuwar Abba akwai damuwar da take damun su da suka kasa gane ta mece ce ma ballantana su yi tunanin yadda za su magance ta

Barrister Umar ya zo dubiyar yayan na shi wajen sau huɗu,don da shi ma aka kai abban Lagos,shima dai gaba ɗaya hankalin na shi a tashe yake,ga mum da har yanzu ta ƙi kwantar da hankalin ta akan ɗan gold ɗin ta a cewar shi


New turn to this innocent family 😭


Kada dai a manta VIP group #300 ne kacal

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️ Nusy bee

*Young talented writers association (YOTA)*


Page 35

GIDAN SA'IDU MANOMI,ƘAUYEN ALBASU,KANO STATE, NIGERIA

Yau kwanan su khairi biyar a albasu,ita dai aunty Naja kwanan ta ɗaya a gidan su khairi ta tafi gidan su,bayan kwana biyu kuma ta zo da ƴar budurwar ƴar ta sa'ar khairi da mahaifiyar ta take riƙo,yarinyar mai sunan Rabi mutuniyar kirki kamar mahaifiyar ta,a ranar ita ta da Nadiya suka raka khairi ta zaga cikin ƙauyen nasu sosai,har gidajen ƴan uwan su da su ka yi aure, waɗanda suka yi ta kallon ta kamar sun ga sabuwar halitta,ba su dawo ba sai bayan maghriba,suka raka Rabi ta koma gida,suma suka dawo gida


Yau da suka cika kwana biyar itace ranar da daddy ya basu umarnin su koma gida,don haka suka tattara komai nasu da ƴar tsarabar su da suka samu,baba hari uwar ƴan shishshigi har da yiwa khairi alkaki,dama tunda khairin taje a ɗakin ta ta sauka,khairi kuwa ta ji daɗin alkakin nan sosai,don adana shi ta shirya yi ta kai wa su Amra da Nabeela ƙawayen ta a makaranta

Da yamma su ka iso, kasancewar ba su taso da wuri ba, lokacin da su ka zo sun samu Daddy a gida, suna shirye-shiryen wucewa da Abba zuwa Egypt

Ita dai khairi ta yi masa fatan samun sauƙi,sannan tayi wa lesson teacher ɗin ta magana cewa ta dawo,wanda aka samar mata yake mata lesson duk lokacin hutu

** ** **

Kwanan su khairi biyu da dawo wa su Daddy suka ɗauki Abba zuwa Egypt,acan ma dai bata sauya zani ba, saboda iya gwaje-gwajen da aka yi masa lafiya ƙalau,ko ƴan larure-laruren nan na zamani ba ya fama dasu,lafiyayyen mutum ne mai yawan motsa jiki,gashi da kiyaye abinda zai ci ko ya sha, shi yasa ko cututtukan girma baya fama dasu

Hankalin su ya tashi sosai,amma sai suka wuce India,acan ma duk abu ɗaya gwajin yake cewa,daga nan ne Abba ya ce kawai su mayar da shi gida,sun so musa wa amma ya nuna musu baya buƙatar zuwa ko'ina,dole suka dawo da shi gida ba don suna so ba

A satin da suka dawo a satin su khairi suka koma makaranta,wannan karon driver ne ya mayar da ita makarantar saboda sulaiman baya cikin nutsuwar shi,ita ma bata damu ba,farin cikin ta za ta shiga js2,kuma Sulaiman ya yi mata albishir cewa In dai ta cigaba da mayar da hankali to a js2 ɗin za ta rubuta placement ta wuce ss1, shi yasa karatun ta ya ƙaru babu ji babu gani


HOTORO GRA, KANO STATE, NIGERIA


Ita kam ɓangaren Samha lamarin sai sam barka,da farko dai yawan karatun Alqur'ani da take kunnawa ta na saurara,da kuma yawan karanta wa,ta na yawaita addu'o'in da aunty Asiya ta bata,don ta turo mata wasu ta Whatsapp ma


Kafin sati guda ya cika abubuwa da yawa suka chanja,ta na zaune a uwar ɗakin ta bayan ta kai Aman makaranta,ta kunna Alqur'ani ƙira'ar maheer cikin suratul naml ta ji sallamar Salis

Ta yi mamaki ƙwarai,duk da cewa ba abin mamaki ba ne,kaɗan kenan daga ikon Allah,cikin sanyin murya ta amsa,a ladabce ta gaishe shi,ya amsa cikin sakin fuska,ya zauna ya na tambayar lafiyar ta da ta Aman

Fuskar ta ɗauke da murmushi ta ce"komai lafiya, Aman ma ya tafi makaranta,amma mun yi kewar ka"

Salis ya yi ɗan murmushi,cikin jin kunya ya ce"Nima na yi kewar ku,ki shirya anjuma zamu je unguwa"ta na murmushin farin ciki ta ce"to da kamar yaushe?"

Ya ce"da yamma,bayan la'asar"

Samha ta ce"to Allah ya nuna mana da alkhairi"ya miƙe ya na faɗin "ameen, ni zan tafi wajen aiki"ba tayi magana ba ta miƙe ta rako shi har bakin mota, zuciyar ta cike da matuƙar farin ciki

Akan idanun Beely suka fito,da tsananin mamaki take kallon su,ta riƙe ƙugu ta na ƙare musu kallo,wato wani sabon makircin Samha ta samo kenan,ba tayi dogon tunani ba ta fice zuwa harabar gidan inda suke tsaye suna shan soyayya,ta na zuwa ta bangaje Samha ta ƙarasa jikin mijin nasu ta kwanta ta na ƙananun kukan shagwaɓa

Samha tana kallon ta,wani irin zafi ya yunƙuro mata a ƙirji,amma tuna maganar aunty Asiya yas a tayi saurin fara ambaton inna lillahi wa inna ilayhi rajiun a zuciyar ta,ta ɗauke kan ta ta mayar da kallon ta bakin gate

Ga mamakin su su duka biyun ture Beely ya yi da saurin shi,ya na faɗin "Bilkisu mene ne hakan?a gaban mutane muke fa!"

Da tsananin mamaki Beely take kallon shi, Samha ta yi kamar bata ji su ba,ta kalle shi cikin kissa ta ce"to abban Aman Allah ya tsare"ya dube ta ya na murmushi yace"ameen momyn Aman "ya faɗa mota

Ita ma Samha ba ta jira komai ba ta juya ta koma cikin gidan zuciyar ta fal nishaɗi,ta na zama Beely ta shigo a fusace ta na yi mata wani mugun kallo,kallo ɗaya ta yi mata ta cigaba da gyaran cabbage ɗin da ya fara bayan shigowar ta

"Da kyau uwargida!ki aika jinjina ga bokan ki,aikin ku yayi kyau,amma ki sani in dai da ni kike magana aikin kamar ya rushe ya gama ne"

Samha ta watsa mata kallon banza ta ce"ko?to idan ba ki sani ba bari na faɗa miki,nafi ƙarfin boka sai dai ubangijin boka,kema da za ki gane da kin fahimci aikin boka aikin banza ne,kin daina wahalar da kanki,kuma da izinin Allah yanzu kika fara gani ƙalubale a aikin ki muddin ba za ki saka Allah a lamarin ki ba"tana kai wa nan ta miƙe ta bar Beely a tsaye,ta shige ɗakin ta ta na waƙe waƙe,ta bar Beely da bin ta da kallo

Da yamma kamar yadda salis ya yi alƙawari suka shirya fita shi da Samha da yaron su Aman, Beely ba ta san da maganar ba sai da ta ji motsin su a parking lot,ta na leƙawa ta window ta hango su da shirin fita,sai hira suke yi suna dariya cike da farin ciki,ai kuwa ta zabura a fusace ta nufi parking lot ɗin

Sam basu kula da ita ba sai da suka ji ta ce"lallai kam!!ina zaku je?"

Salis ne ya waiga ya kalle ta,ta riƙe ƙugu ta na girgiza,ita kam Samha ko kallon banza ba ta samu daga wajen ta ba, Salis ne ya bata amsa

"Unguwa zamu je"fuskar shi babu alamun damuwa

"Unguwa?wacce unguwar?kuma shine don munafurci sai ka tafi da wannan guzumar ni ka bar ni a gida?"

"Idan ita guzuma ce kema guzuma ce,sannan kuma tsawon wanne lokaci na ɗauka ina fita unguwa da ke ita ta na gida?don haka yau ranar ta ce,momyn Aman shiga mota, lokaci yana ƙurewa"

Wani uban ashar Beely ta ƙunduma ta na faɗin" na ga yadda za'a yi ku bar gidan nan alhali da rai na da lafiya ta!"babu wanda ya sake kula ta dai,suka nufi shiga motar amma ta daka tsalle ta shaƙe wa Samha wuya,da gudu Salis ya ƙaraso ya fizge ta ya ɗauke Beely da mari,ya tura Samha mota shima ya shiga,ya tayar su ka fice suka bar Beely a inda ta yi zaman ƴan bori ta na kuka cike da tsananin mamaki da baƙin ciki


BRUNSWICK, MELBOURNE, AUSTRALIA


A hankali ta share hawayen idanun ta ta na cigaba da kallon shi,tun da ta yi sallama ta shigo ɗakin bai ɗaga kai ya kalle ta ba,ya amsa da yanayin da ya saba amsa mata sannan ya cigaba da abinda yake yi

Jera kaya yake yi a akwatin shi,da alamu tafiya zai yi, bai yi mata maganar ba ballantana ta sani,asalima yanzu bata sanin komai na shi,babu ruwan shi da ita

Zama ta yi kusa dashi ta jingina da kafaɗar shi ta fashe da wani irin kuka mai motsa rai,ya kalle ta,sai kuma ya ji ta bashi tausayi,don yadda ta ke kukan kaɗai ya bayyana irin ciwo da ƙuncin da zuciyar ta take ciki,cikin sanyin murya ya ce"kema shirya, Nigeria zan tafi, uncle ɗina ne babu lafiya"

A ƙalla dai an samu ci gaba akan baya,don haka cikin zumuɗi ta miƙe tana murna,ta kalle shi ta na ɗan murmushi ta na goge hawaye,cikin sanyin murya ta ce"na gode!"ta faɗa toilet don yin wanka


Wataƙila miji da matar nan shirya wa zasu yi abin su😄


Kar dai a manta VIP group #300 ne kacal

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee

*Young talented writers association (YOTA)*


Page 36

Ba su sanar da kowa isowar su Nigeria ba,sai dai kawai ganin su aka yi,anyi murna sosai, kuma har zuwa lokacin mum ba ta wani sake wa fadeela,wadda a yanzu ta rame sosai saboda tunani

Sun yi hira sosai da mum ɗin shi,ya ba wa fadeela izinin tafiya gida ta gaida mahaifiyar ta,anan yake sake tambayar jikin Abba

Cikin jimami mum take bayanin yadda jikin na shi ya kasance,da yadda ake ta wahalar zuwa asibitoci na ƙasashe kala-kala amma ba'a dace ba, shiru Azad ya yi kafin ya ce"Allah ya bashi lafiya,anjuma zan je dubiyar shi in sha Allah"

"Sai ku gaisa da kakar ku,don an tabbatar min ta na hanya za ta iya zuwa kowanne lokaci ta ga jikin ɗan ta"Azad ya ɗaure fuska ya ce"za ta zo ta yi abinda ta saba kenan!uwar rigima da neman hargitsi!!"

"Look Azad!babu ruwan ka da ita, jikin ɗan ta ta zo gani,me ya shafe ka da ita? mahaifiyar baban ku ce,don Allah zagin da ake janyo min a family ɗin mahaifin ku ya ishe ni haka,ka shirya ku je,don naji an ce matar daddyn ku ma za ta je"shi dai Azad ya ɗauke kai gefe bai sake magana ba,shi dai maganar zuwan kakar shi ya ɓata masa Budget

Da yamma Azad ya isa gidan lieutenant general Usman,a bakin gate ya yi parking motar shi ya shiga gidan,su ka gaisa da mai gadin kamar yadda ya saba ya nufi harabar gidan

A main parlour ya samu Sulaiman a zaune,da mamaki Sulaiman ya ke kallon shi,ya ƙaraso ya bashi hannu suka tafa,ya ce"long time the whole babban yaya!ya jikin?"

"Wanne jiki kuma man?ai mun daɗe da samun sauƙi,ya mai jiki?"

Sulaiman ya ɗan girgiza kai cike da jimami ya ce"mai jiki alhamdulillahi za'a ce,ƙafar ma kwana biyun nan kumbura take yi,sam babu wani ci gaba da ake samu"

"Ya Salam!kuma har zuwa yanzu ba'a gano kan matsalar ba?"

Sulaiman ya girgiza kai ya ce"ba'a gano ba big bruh!duk yawace yawacen asibitin da muka yi a banza, ƙarshe haka ya matsa mana muka dawo gida,yanzu kuma gashi ƙafar ta fara kumbura"Azad ya sauke ajiyar zuciya cike da damuwa kafin ya ce"to Allah ya bashi lafiya,mu je ka raka ni naga jikin nashi"

Sulaiman ya yi murmushi ya ce"muje "yana miƙewa

Azad ya ɗaure fuska ya na kallon sulaiman yace"that annoying old woman,ta ƙaraso?"

Sulaiman ya yi ƴar dariya ya ce "wace ce annoying old woman kuma?"Azad ya ƙara ɗaure fuska ya ce"You know who I'm talking about man!"sulaiman ya yi dariya sosai ya ce"yeah!ta ƙaraso ta ga ɗan ta,da wata matsala ne?"

Azad bai ce komai ba ya ja tsaki ya yi gaba,sulaiman ya bishi a baya yana ƴar dariya

A parlourn shi suka same su,Abba,Ammi, Daddy,kawu Aliko baban Nadiya,sai inna da ta harɗe fuska a ɗaure ta na kallon ƙafar ɗan nata tana ta sababi

Babu yabo babu fallasa ya gaida su ɗaya bayan ɗaya cikin girmama wa,ciki ciki baban Nadiya ya amsa masa,don har yanzu a ƙule yake dashi tun rashin kunyar da ya yi masa kan faɗan mum da baba Atine,inna kuwa ko amsa wa bata yi ba,a maimakon haka ma sai ta hau sababi

"Da aka gwada magungunan naku na ƙarya bai yi ba mai ya hana ka koma tushen ka?akwai magunguna masu kyau ba irin na barga irin naku ba,yanzu gashi nan ai,baka wani girma na azo a gani ba amma gashi nan kana fama da ciwon ƙafa,duk ka ƙara tsofewa tun baka kai shekarun tsufa ba"

Shiru parlourn ya ɗauka kowa ya na sauraren inna ta na ta zuba sababin ta,babu wanda ya tanka sai da ta yi shiru, Sulaiman ya dube ta,cikin kwantar da murya ya ce "inna ayi haƙuri,kin san larura irin wannan idan ta zo kowa ruɗewa yake yi,dabarar hakan ce bata zo mana ba,amma in sha Allahu duk lokacin da kika yarje mana za mu wuce can albasu,ki nemo mana mai maganin gargajiya da kanki mu kai shi,fatan dai bai wuce Allah ya bashi lafiya ba"

Azad ya taɓe baki,ya sake gaida Abba, Abba ya amsa da sakin fuska na ƙarfin hali,ya yi masa sannu da jiki,sannan ya miƙe ya fice daga parlourn

Inna ta sake duban Daddy ta ce"to kai Umaru ina yarinyar wajen ɗan nan?tun da nazo ban saka ta a idanu na ba"

Cikin kwantar da murya Daddy ya ce"inna tana makaranta ne"

"Au!ita ma karatun yahudancin na ku kuka saka ta?yadda idanun ta zai fetsare ta rinƙa kallon mu a banza kamar sauran ƴaƴan ku?"

Da sauri Sulaiman ya kalle ta,a ranshi ya na ayyana wannan mata bata son zaman lafiya,wai fa ɗan ta ne a kwance babu lafiya ta zo ta na irin wannan sababin, tunanin shi ya yanke lokacin da ya ji Daddy ya na magana cikin kwantar da murya

"Inna ai khairi ikon ki ce,mu ma ai ikon ki ne,ko yanzu kika ce ayi mata aure za muyi mata"inna ta yi shiru bata ƙara tankawa ba,sai hura hanci take yi

Washegari wajen sha ɗaya na safe Sulaiman ya wuce Hadejia road,ya yi matuƙar sa'ar samun Azad shi kaɗai a part ɗin shi,don mum ma lokacin ba ta nan,gashi har lokacin bai bawa fadeela izinin dawo wa ba

A kwance kan doguwar kujera ya samu Azad ya na kallon news,suka tafa kamar yadda suka saba, Azad yace"Man ya ake ciki ne?ya jikin Abba?"

Ya zauna ya na faɗin "Daddy jiki da sauƙi, Old woman ce dai ta dage sai an mayar dashi albasu,don ayi masa maganin gargajiya,tace wai maganin mu duk ƙarya ce"

Tsaki Azad ya ja ya ce"wannan matar ta cika kawo matsaloli daga wannan sai wannan,shi Abban ɗin za'a yi ta cusa wa magungunan gargajiya?na wacce cutar ma tukunna?tunda dai har yanzu ba'a san me yake damun shi ba?"

"Ɗan ta ne fa,bar ta,mu ba ta lokaci mu gani,idan maganin bai ci ba sai mu lallaɓa ta mu ɗauko abban mu cigaba da nema masa magani"Azad ya taɓe baki bai ce komai ba,sai ma mayar da hankali da ya yi ga TV

Sulaiman ya na kallon shi da kyau ya ce"sai wata sabuwar tsirfa da ta zo da ita,wai ayi wa khairi aure"

Sulaiman yana ankare da yadda Azad ya zabura ya na kallon shi a ɗan tsorace,zuwa can kuma ko me ya tuna?sai ya daidaita nutsuwar shi yace"aure kuma?lallai matar nan rigimammiya ce ta ƙarshe,ita khairi ɗin ce tace mata aure take so?"

Sulaiman ya girgiza kai yace"a ina suka ga juna ma?kawai dai rigima ce irin ta ta "

"Lallai!to wa za'a aura mata?"

"Ban sani ba wallahi, maybe kuma already ta tanadar mata miji acan garin,za ta matsa a mayar da ita can ta aura mata wanda ta so,kuma maybe ita khairin ta na da wanda take so,kasan matan ƙauye"

"Soyayya?a shekarun ta ita khairin?nawa take gaba ɗaya ma?"

Sulaiman ya gyara zama ya na masa kallon tsaf ya ce"soyayya a wajen su ba wani abu bane, abinda sai ka ga yarinya ƙanwar khairi ma anyi mata aure?su rayuwar su ba irin tamu bace ai"

Shiru Azad ya yi ya na kallon waje ɗaya,tsaf sulaiman yake ƙare masa kallo,kafin Azad ya ɗago ya na kallon shi,sam bai kula ba ma yadda muryar shi ta yi rauni ya ce"ita khairin ce ta tabbatar maka ta na da wanda take so?"

Sulaiman ya yi murmushi ya na kallon shi yace"a'a, hasashe ne kawai,amma zai iya yiyu wa ne,duk da ina da tabbacin babu kowa a rayuwar khairi,sai karatun ta"

Ya na kule da yadda Azad ya sauke ajiyar zuciya a hankali har yana lumshe idanu, sulaiman ya ɗan gyara zama ya na kallon shi ya na faɗin"man mu yi wata magana mana"

Azad ya ɗan kalle shi ya ce"wacce maganar ce?"

"Menene tsakanin ka da Ummul khairi?last time na taɓa yi maka wannan tambayar amma ka bani wata amsa dabam,yau dai ka yi min bayani, menene tsakanin ka da Ummul khairi? gaskiya na ke so ka gaya min Please"

"Tsakani na da Ummul khairi?kamar yaya kenan?"Azad ya faɗa ya na ɗan yatsina fuska

"Kamar yadda ka ji na tambaye ka Mr Saeed!just give me answer man!"

Kallon wasu seconds ya yi masa kafin ya ce"alaƙa irin wadda ta haɗa ni da kai,ita ce ta haɗa ni da Ummul khairi"

"Let me repeat myself Azad!you love Ummul khair! me yasa ka ke son nuna ba hakan bane bayan........"

"Excuse me sulaiman!me ka ke nufi ne?wanne kalar shirme ne wannan?are you questioning me?

Ummul khair ba kowa ba ce a gare ni face ƙanwa ta kamar su Beely,don Allah daga nan bana son ka sake mayar min da wannan zancen Please!"

Sulaiman kallon shi yake yi har ya ƙare bayani yana huci, sulaiman ya yi murmushi yace"to amma me ya kawo kishin ta a idanun ka da na yi maka maganar zata yi aure da wani?"

"Ba kishin ta na ke yi ba,bana son rayuwar ta ta nakasa ne,ayi mata aure da shekarun yarinta,kuma ban san wanda za'a aura mata ba,amma ban da haka babu abinda ya shafe ni da auren ta"sulaiman ya taɓe baki yace"anyway! Allah ya kyauta!Ni zan wuce,idan mum ta dawo ka gaida ta,amma zan gaya maka abu ɗaya, ba'a fafe gora ranar tafiya,sau tari muna rasa wani abu mai muhimmanci a rayuwar mu idan muka siyar wa duniya ƙaryar ba ya gaban mu"Azad bai ba shi amsa ba, sulaiman ɗin ma bai tsaya saurara ba,ya yi sauri ya fice cike da tausayin shi,don ya san abinda yake faɗa ba haka yake a zuciyar shi ba,kuma wannan abin da yake yi shine zai hana shi damar auren ta,wata ƙila ma na har abada


Jarabar duniya 😏yace ba ya so ya ce baya so a ƙyale shi mana haba 😬ko ana so dole ne 🙄


Kar dai a manta da VIP group #300 ne kacal

#Nusy_bee


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee

Page 37


A ranar Azad wuni ya yi cikin damuwa,wai aure, imagine za'a yi auren yarinyar da ko autar su ta girme ta,ya ja tsaki yafi sau a ƙirga,a ranar wuni ya yi a sashen shi

Da yamma kasa jura ya yi,ya dauki motar shi ya tafi Queen's College ba tare da kowa ya sani ba,don ko mum ce mata ya yi wajen wani abokin shi zai je


QUEEN'S COLLEGE, KANO STATE, NIGERIA


Yau Khairi ta tashi da menstrual cramps da tsawon rayuwar ta bata taɓa yi ba,sai jiya,yau ta wayi gari da ganin period na farko a rayuwar ta,duk da cewa ta san duk yadda zata yi saboda su Nabeela suna yi kuma sun koya mata,amma ganin shi ya sa ta tsorata sosai,har da kuka,tun su Amra suna mata dariya suna tsokanar ta,ganin abin na ta ba ba ƙare bane suka koma tausayin ta, ƙarshe dai da ƙyar suka samu suka lallashe ta ta haƙura, Amra ta haɗa mata ruwan wanka, Nabeela kuma ta samar mata ruwan zafi da zata sha tea,ta bata pad ɗin ta,suka karɓo mata magani,ta sha ta kwanta sai bacci

Tun wajen ƙarfe tara na safe take bacci bata farka ba sai wajen karfe ɗaya,ta tashi zaune tana miƙa duk jikin ta babu ƙwari,cike da kulawa Amra dake zaune tana karatun English Novel take jera mata sannu,a lokacin Nabeela bata nan,tana ɗakin kusa dasu,suma classmates ɗin su ne

Bata amsa sannun ba sai ɗan gyaɗa kai da ta yi,gaba ɗaya bata son magana ko kaɗan, Amra ta haɗa mata ruwa mai ɗumi sosai ta shiga wanka

Bayan ta gama shirya wa Amra ta yi juyin duniyar nan taƙi cin abinci,da ƙyar ta yarda ta dama mata Custard mai zafi,yau dai babu batun corn flakes

Tana cikin shan Custard ɗin a hankali mai kula da su ta leƙo ta ce ana kiran ta,shiru ta yi da mamakin wannan mai kiran nata, Amra sai kallon ta take yi,ganin bata da niyyar tafiya Amra ta ce "khair kiran ki fa ake yi"cikin sanyin murya khairi ta ce "naji,amma waye zai kira ni yanzu?"

"Maybe yaya sulaiman ne ko?"

Khairi ta girgiza kai tace"yaya sulaiman ba zai kira ni yanzu ba, saboda jinyar Abba suke ta fama, ko jiya da safe munyi chat dashi"

"To ki je ki jiyo dai, wannan canke canken ba shi da amfani"a sanya ye ta miƙe ta fice daga ɗakin

Tun daga nesa take kallon shi cike da tsananin mamaki, yaushe ya dawo ƙasar?ba ta sani ba,ta ƙare masa kallo,ya yi kyau sosai cikin ƙananun kayan da ya saba saka wa,sai danne dannen wayar shi yake ba tare da ya damu da tahowar da take yi ba,ta na ƙaraso wa cikin sanyin jiki ta ce"yaya Azad yaushe ka dawo?sannu da zuwa"

Ɗago wa ya yi ya na kallon ta,a hankali ya ce "ko dai in koma ne?"ta girgiza kai ta na murmushi,shima ya yi murmushi,ta gaishe shi cikin sanyin murya,ya amsa cike da kula wa,ta na murmushi ta ce"na yi kewar ka yaya Azad!na yi kewar ka sosai,babu kai a waya,kuma gashi ka yi nisa"

Ya yi murmushi ya ce"Nima na yi kewar ki,amma baki da lafiya ne?You look so lean!"ya ƙarashe da serious face

Ɗan murmushi kawai ta yi ba tare da ta amsa ba,haka kawai ya ji abin ya dame shi,cikin wata murya da bai san ma ya na da ita ba yake faɗin "Please khairi! what's wrong with you? please tell me,ko kina son ganin yayan ki cikin damuwa ne?umm?"

Ɗan murmushi ta yi ta ce"zazzaɓi na yi,amma na sha magani,na yi bacci ya sauka"

"Ayya!ko na koma ne,sai na dawo next time?"

Tun kafin ya kai aya ta fara girgiza kai tana marairaicewa,yabyi murmushi yabce"to magana zamu yi khairi,amma ban sani ba ko za ki karɓi abinda na zo da shi"babu musu ta yi masa jagora zuwa kan wasu kujeru suka zauna ta na fuskantar shi

Sai da ya ɓata wasu ƴan mintuna ya na tunanin ta inda zai fara,kafin ya yi ta maza ya ce"Ummul khairi yanzu kina da ra'ayin ci gaba da karatu bayan kin gama makarantar nan?"

Jinjina masa kai ta yi da cikakken kwarin gwiwa ta na kallon shi,ya ce"good!so what if su Daddy suka ba ki zaɓi akan aure ko ci gaba da karatu?"

Ta ɗan yi shiru ta na kallon shi,kafin ta girgiza kai tace"karatu na ke so na yi,ina fatan na zama likita na taimaka wa marasa lafiya,banda haka ma zan yi course na musamman akan masu matsalar numfashi ma in sha Allah"

Bin ta da kallo yayi na ƴan seconds,kafin yace"masu matsalar numfashi? me yasa to?"

Cikin yanayin jimami ta sunkuyar da kai ta ce"yaya sulaiman ya ce kana da athma,kuma ta na baka wahala, shiyasa nima nake son na yi maka wani abu a ........"


"Kina karatu ne don ki rama abinda na yi miki?"

Ta girgiza kai ta ce"a'a,kawai dai zan so na yi wani abu wanda zaka ji daɗi,ko babu komai ka yi min komai,ka zama jigo a gare ni,ina fatan Allah ya dauwamar da farin ciki a rayuwar ka"ta ƙarashe hawaye na taruwa a kwarmin idanun ta

Ɗan murmushi ya yi ya na kallon ta ya ce"kuka?to tunda kuka za kiyi bari na tafi"da sauri ta goge hawayen ta na girgiza kai ta na murmushi,ya yi murmushi ya ce"good girl!ni dai yanzu abinda nake so dake shine ko da ace su Daddy sun tambaye ki kice ke yanzu karatu za kiyi tukunna,babu aure a tsarin ki,fata na ne na ga kin zama mai ilimi wanda zai amfanar da al'umma,ki kasance ɗaya daga cikin mutanen da wata rana za'a ambace su da alfahari,kin ji?"

Ta ɗan yi shiru kafin ta ce"to yaya me yasa kake maganar za'a yi min aure yanzu?ki fa babu wanda ya taɓa yi min maganar aure"

"Kakar ki ce ta ce ayi miki aure, ta ce kin girma,shi yasa "

Lokaci guda sauran fara'ar fuskar ta ta ɗauke, jikin ta ya yi sanyi,ta ce"inna?"

Da kallo yake bin ta kafin ya ce"eh,me ya faru na ga yanayin ki ya chanja?"

Ta ɗan yi shiru kafin ta ce"idan inna ta ce ayi abu dole ayi,yanzu inna ba za ta bar ni na yi karatu na ba?yanzu hope ɗi na na zama mai gata zai tashi a banza kenan?"sai ta fashe da kuka sosai cikin tashin hankali

Hankalin Azad ya tashi,ya ce"no Ummul khair!bai zama lallai ba,kin ga nima da Auwab ta daɗe ta na maganar mun ƙi yin aure,ga Beely ma,amma duk su Daddy ba su damu ba sai ke?kar ki damu,cewa fa na yi maybe su baki zaɓi,ga abinda za ki zaɓa,don Allah ki daina kukan nan"Khairi ta ce"da sauri ta share hawayen ganin yadda duk ya bi ya kiɗime,sai da ta daidaita nutsuwar ta sannan ta ga shima ya daidaita ya na sauke ajiyar zuciya

Cikin rawar murya ta ci gaba da faɗin "yaya Azad da ni da ku ba ɗaya bane a wajen inna, musamman da yake rayuwar ku da ta wa ba ɗaya bane,babu mamaki ita har yanzu kallon ƴar albasu ta ke yi min,ina tsoron abin da zai iya biyo wa baya"

Cikin kwantar da murya ya Azad ya bata amsa

"Ummul khairi maybe a wajen inna muke dabam,but believe me khairi,a wajen Daddy da Abba duk abu ɗaya ne,za su san yadda zasu yi duk yadda za su yi don ganin kin samu ingantacciyar rayuwa"Khairi ta ɗauke ajiyar zuciya ta na jin relief a zuciyar ta

"So feel free Khairi! I'm sure daddy ba zei yi miki abinda bakya so ba,more especially aure a shekarun ki, ballantana a aura miki wanda bakya so,ko kina da wanda kike so?"yayi tambayar ya na kallon ta da ganin reaction ɗin ta

Kallon ta yi shi ta girgiza kai,yace "are you sure?"

"Ni ban taɓa soyayya ba,ban taɓa saurayi ba, rayuwa ta a albasu na rayu ne a matsayin UMMIYO ƴar talla,jahila,ƙazama,kaima shaida ne,to waye zai kwashe ni ya kai gidan shi a haka?

A yanzu kuma da nake rayuwa a matsayin Khairi bani da burin da ya wuce na yaƙi jahilcin da yake kai na,na san duk inda umma na take a faɗin duniya za ta so gani na da ilmi,don haka Ni bani da wanda nake so,asalima ban san soyayya ba, ballantana na san yadda take"

Tausayin ta ya kama Azad,ya yi zuru ya na kallon ta,cikin sanyin jiki ta goge ƴar ƙwallar da ta ciko idanun ta,sannan ta ɗaga kai ta na kallon yadda ya yi zuru ya na kallon ta cike da tausayin ta,bata kula ba ta cigaba da magana

"Abinda yake burge ni na ga tsakanin ɗa da mahaifiyar shi akwai kulawa da damuwa,wata uwar kuma ka ga za ta iya komai don ɗan ta,mum ta na matuƙar burge ni,ko a yanzu Allah ya raba ta da yaran ta ba za su manta da ita ba, saboda ta sauke dukkan wani haƙƙi na uwa da yake kan ta,amma ni kuma ka ga mahaifiya ta ta na raye,sannan kuma an ce ba talakawa ba ne,sai dai ta watsar da ni,bata so na,ban san laifin da na yi mata,ban sani ba ko mahaifi na....."

"No khairi!ki daina irin wannan maganar,babu wata uwa a duniya da bata son abinda ta haifa,duk uwar da kika ga ta nisanci abinda ta haifa ba ƙaramin abu ta fuskanta ba, kuma ina da tabbacin cewa tafi ki jin ciwo da raɗaɗin rabuwar ku,don haka Please Ummul khairi!ina roƙon ki ki cire dukkan wani tunani daga ranki,a shekarun ki basu kamace ki ba, karatun ki shi ya kamata ki mayar da hankali,kuma ba zai yiwu kina irin wannan damuwar ba"ya ƙarasa faɗa shima jikin shi a sanyaye,amma bai bari raunin shi ya bayyana ba

Murmushi ta yi masa,shima ya mayar mata,ya na gyara zama yace "baki tambaye ni auntyn ki ba"

Khairi ta ɗan yi murmushi ta ce"kai ka mantar dani ai"

Ya waro idanu ya ce "Ni kuma?ta yaya?"

"Eh mana,da farko murnar ganin ka,na biyu ka zo min da batun inna"murmushi ya yi sosai ya ce"ke ma complain ɗin ta za ki bayar?"

Ta kalle shi sosai ta ce"a kaf jikokin ta babu wanda ta tsana kamar ni,ko gaishe ta na yi sai ta ga dama take amsa wa"ta ƙarashe cikin jin haushin abinda innar take yi mata

"Damuwa kika yi?to ni idan na gaishe ta ma bata amsa wa kwata kwata, saboda ita na tsani zuwa garin albasu,kuma ba na so ta zo,kin ga Auwab ma ba ya yarda su haɗu kwata kwata"

Yatsine fuska ta yi tana taɓe baki ta ce "Auwab?waye Auwab kuma?"

Kallon ta ya yi da mamaki jin wai bata san Auwab ba,amma yace"yayan sulaiman mana"

"Oh dama yana da yaya?"ta faɗa cikin halin ko in kula

Wani kallo ya yi mata ya ce" da gaske kike ba ki sani ba?ko dai wulaƙanci ne?"

Kamar jira take a zafafe ta ce"wulaƙanci har na kai shi?shi da wai yaya sulaiman ya ce ga Dr khairi wai don wulaƙanci wai wace ce Dr khairi?ɗan rainin hankali kawai"tana magana tana yatsina fuska cikin jin haushi

Sam bata kula da irin kallon da Azad yake mata ba bakin shi buɗe,tana dire wa kuwa ya kama dariya sosai,ya kula Khairi a wuya take da Auwab,kamar ma bayan haka akwai abinda ya yi mata take jin haushin shi,ban da haka ma ya ga alamun sam jinin su bai haɗu ba

Sai kuma taji kunya ta kama ta,ta sunkuyar da kai ta na murmushi, Azad ya miƙe tsaye yana murmushi y ace"wannan likitar dai da alamu rigimammiya za'a yi,to Allah ya bada haƙuri,ni dai zan tafi"

"Yaya Azad na gode,na gode sosai,ka gaida su mum"sai da ya sake kallon ta jin abinda ta ce, yarinyar ta na burge shi sosai,ya yi ɗan murmushi ya ce"za su ji,yau dai banzo da chaculate da corn flakes ba"ta yi ƴar dariya ta ce"yanzu ai na rage shan su,sai dai ko gaba"Azad ya ce"to shikenan,ni dai na tafi"ta rako shi har wajen motar shi, suka yi sallama ta koma ciki cike da farin ciki


HAƊEJIA ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA


Yau ne za'a tafi da Abba zuwa albasu don magani,tare da sulaiman da daddy za'a tafi,kuma tafiyar ta sassafe za'a yi,don haka tun da wuri suka fito da shirin su suka nufi albasu

Mota biyu suka yi,daga motar Daddy,wadda suke da driver ɗin shi da Abba, sai Sulaiman da ya ɗauko inna Sabuwa ta na ta zuba masa ƙorafi,wani ya amsa wani ya yi mata shiru

Suna sauka ko huta wa basu yi ba Saleh, ɗa ne a wajen baban Jamila da shi da sulaiman suka tafi wajen masu magani

Da kanshi mai maganin ya zo don bincikar ƙafar Abba da bashi magunguna

Sai dai tsawon kwanaki biyu ba'a dace ba,sati ɗaya,biyu,uku shiru, Daddy ya umarci sulaiman ya koma bakin aikin shi,don tuni Azad ma ya koma Australia,sai dai shi kaɗai ya koma,bai koma da matar shi ba,asalima ta na gidan iyayen ta bata san ma ya koma ba


Abba Allah ya baka lapia😭

Kada dai a manta VIP group #300 ne kacal

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee


*Young talented writers association (YOTA)*


Page 38

Sulaiman ba shi da zaɓi sama da baro albasu ya dawo Kano ko don saboda aikin shi da baya son wasa,amma lamarin jikin mahaifin shi ya na damun shi sosai,a ce ciwo tsawon wannan lokaci babu wani improvement? hankalin sulaiman yana matuƙar tashi

Ya na waya da Khairi sosai,ita ma ta na damu wa da halin da ƙanin mahaifin na ta yake ciki,don haka duk sanda suka yi waya sai ta tambaye shi jikin abba,ya na jin daɗin hakan sosai

Kusan watannin Abba uku a albasu,ganin babu nasara yas a inna dole ta haƙura suka dawo Kano,a lokacin Khairi shirye-shiryen rubuta placement take yi, sai dai bata jin daɗi kasancewar su Nabeela js3 ɗin su zasu tafi don sun abokan karatun nata,kuma mutanen,kusan shekarun su ɗay,sai dai su sun fi ta wayo da buɗewar idanu, kasancewar su sun rayu a cikin mutane kuma wayayyu ne sosai

Lokacin da sulaiman ya kai wa Khairi ziyara makaranta take tambayar shi jikin Daddy, sulaiman ya furzar da iska cike da damuwa ya ce"har yanzu dai babu wani sauƙi,ana ta ci gaba da neman magani amma a banza,don ƙafar sai sake ruruce wa take yi,rabon Abba da bacci ni kaina ba zan iya tuna lokacin ba"

Shiru Khairi ta yi kafin ta kalle shi ta ce"kuma kun gwada na Islamic?"

Shiru ya yi ya na kallon ta ya na nazari, me yasa ba su taɓa tunanin hakan ba?Khairi ta katse masa tunani da faɗin"ku gwada na Islamic yaya sulaiman,in sha Allah babu abinda ya gagari ayar Allah"
Sulaiman ya yi murmushi sosai ya ce"in sha Allah kuwa zamu gwada,na gode sosai likita bokan turai"ta yi ƴar dariya kawai bata ce komai ba

Ai kuwa sulaiman ya na koma wa abinda ya fara yi shine gana wa da limamin babban masallacin alfurqan na Alu evenue, shine ya ba shi ayoyin Ruqiyya da yadda zai bi don warwarewar dukkan wani sihiri,a ranar sulaiman ya fara aiwatar da abinda aka bashi

Cikin hukuncin Ubangiji mabuwayi,ciwon da ya ɗauki wata da watanni ya na matsa wa Abba a sati guda kacal ya fara sauƙi,kowa sai farin ciki yake yi sosai, Sulaiman da kanshi yake yawan kunna karatun Alkur'ani mai girma a cikin gidan

Ba'ayi cikakken wata ba Daddy ya warke kamar bai taɓa jinya ba,cike da farin ciki Sulaiman ya kira Khairi ya bata wannan good news ɗin

Itama tayi matuƙar farin ciki sosai,tace"Allah sarki Abba, Allah ya ƙara tsare shi daga dukkan sharri,ashe ga inda matsalar take amma bamu sani ba"

"Sulaiman ya yi murmushi ya ce"ai kece silar wannan nasarar Dr khairi, Allah ya nuna mana ranar da zamu zo asibitin ki kiyi mana allura"Khairi ta yi dariya ta ce"kuma za ka tsaya nayi maka?"

"Sulaiman yace"me zai hana?na tsaya wasu suka yi min ma ballantana ƙanwa ta?"Khairi ta yi murmushi cike da jin daɗi,tana matuƙar girmama duk wanda yake son wannan burin na ta,haka ya yi ta tsokanar ta kafin ya yi mata sallama


HOTORO GRA, KANO STATE, NIGERIA

Rayuwa fa ta chanja wa Beely a gidan Dr Salis,ko ta yi asirin ma ba wani ci yake yi ba,ko da ya kama Salis ɗin na ƴan kwanaki ne zai koma su cigaba da soyayyar su da Samha,wadda a yanzu ko me Beely zata yi mata bata ɗaga kai ta kalle ta,babu ruwan ta da rayuwar ta ma,mijin ta da ɗan ta sun fiye mata komai

Yau kam faɗa Beely da Salis suka yi kaca kaca, saboda ta hana shi shiga sashen Samha,a cewar ta ranar girkin ta ne,shi kuma yace bai ga wadda ta isa ta saka shi ko hana shi a cikin matan shi ba, dalilin haka ta gaggaya masa magana wadda har ta kai ya ɗauke ta da mari,don haka ta tattara ƴan kayan ta ta na kuka ta wuce gida,ta gaban shi ta bi amma ko kallon banza bai yi mata ba,ya ci gaba da wayar da yakeyi


LUGARD ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE

A hankali mum take buɗe idanu,don baccin da take yi baiyi nauyi sosai ba,ta sake kasa kunne ta na jin sallamar da akeyi,har da jan tsaki

"Ni gaskiya momy I'm tired of this,su wannan family ɗin ji da kansu ya yi yawa ga rainin hankali na bala'i, gaskiya banda ina son Azad wallahi Banga dalilin da zai saka na nemi koma masa ba"taji muryar fadeela raɗau ta na faɗin haka

Mahaifiyar fadeelan taji ta na cewa "ke dai fadeela wallahi sokuwa ce,idan kina Irin wannan shirmen ta yaya zaki ci ribar zaman duniya?to bari kiji,a rayuwar nan idan baka iya kama ɓarawo ba shi ɓarawo sai ya kama ka,don haka ki bi rayuwa a sannu"

Basu sake samun damar magana ba saboda shigowar mum a lokacin ,itama nuna musu ta yi bata ji abinda suke cewa ba,ta saki fara'a ta na faɗin "a'a! Hajiya A'isha yau kune a gidan namu?"

Tan a kallon yadda fadeela ta kalle ta a kaikaice ta kawar da kai,Hajiya A'isha ta ce"to ya muka iya Hajiya Salma?na zo ne don jin ya batun igiyar auren ƴa ta?ke taki kin kai ta gidan miji tana rayuwa cikin jin daɗi,ji kuma tawa ɗanki ya zo ya dire min,ita ba mai aure ba ita ba sakakkiya ba,da sakin ta yayi ma da yanzu ta samu wani mijin,wataƙila ma da ta yi aure"

Murmushi sosai Hajiya Salma ta yi ta ce"ai dai kwa tsaya a gaisa ko Hajiya?daga baya ko mene ne ma ai sai a tattauna "babu musu suka zauna suna gaisa wa,Hajiya Salma ta saka mai aiki ta kawo musu lemo da snacks

Bayan sun gama gaisa wa ne Hajiya A'isha ta kalli Hajiya Salma fuska babu yabo babu fallasa ta ce"Hajiya bamu ji kun ce komai akan batun yaran nan ba,idan auren auren,idan kuma zaku bar min ƴa ta ne sai in ji"

Ɗan shiru mum ta yi ta na kallon su,kafin tace"wannan ai hukuncin ya na hannun Azad,sai dai na tambaye shi"

"Kamar yaya Hajiya? haba Hajiya!ni fa ba ƙaramar yarinya ba ce,kawai don tsautsayi ya faru sai ki shiga tsakanin ɗan ki da farin cikin shi? gaskiya dai wannan zalunci ne

Ni wallahi ba don yarinyar nan ta nace ba ma da cewa nayi a haƙura kawai,babu amfanin wulaƙanci ya shigo cikin maganar aure"Hajiya A'isha ta faɗa a ɗan zafafe

"Momy ni fa ina son miji na,kar a raba ni da abu na"a cewar fadeela ta na yatsina fuska

"Ki na son na shi kika nemi kashe shi?ai da ace kina son Azad ba za ki nemi ki kashe shi saboda kishi ba,don haka wannan soyayyar taki akwai gyara a ciki"

"Kin ga Hajiya!an san yarinya ta ta aikata kuskure kuma ta yi nadama,don haka ya kamata mu ji matsayar auren su,idan akwai to muji,idan babu ma sai mu ji,ya za'a kai min yarinya wajen watanni shida ta na zaune? shi yasa yau muka zo ayi ta ta ƙare kawai"

"Azad dai ba ya ƙasar nan,sai ya dawo tukunna"mum ta faɗa ta na miƙewa

"Hajiya Salma ayi maganar gaskiya,ke kika saka ɗan ki ya kai min ƴa ya jingine,kamar kema baki da yara matan nan,to bari kiji,duk wanda ya ce tukunyar wani ba za ta tafasa ba tashi ba za tayi ko ɗumi ba,da nasan gidan ƙananan mutane irin ku na kawo ƴa ta ai da ban yarda an yi wannan haɗin ba"ta na rufe baki Beely ta shigo da sallama

Bata fuskanci abinda ke faruwa ba,ta gaida Hajiya A'isha da girmama wa,Hajiya A'isha ta amsa ta na kallon akwatin da take ja,kafin ta ce"lafiya dai ko?"

Duk juriyar Beely sai da ta fashe da kuka ta ce"wallahi mutumin nan bashi da mutunci, kullum a cikin wulaƙanta ni yake"ga mamakin Beely sai gani ta yi Hajiya A'isha ta rangaɗa guɗa kafin tace"uwar ki ta jawo Miki yarinya,haka ta sa aka wulaƙanta tawa ƴar, dama nace idan bani da haƙƙi sai ta gani akan ku,gashi ta fara gani"

Mamakin kalaman Hajiya A'isha ta ƙamar da Beely,ta kalli fadeela wadda ke ta danne dannen waya,bata sake magana ba ta ja akwatin ta ta shige ɗakin ta,itama mum cewa ta yi su gaida gida ta wuce nata ranta a ɓace,suma ba su da zaɓin da ya wuce su miƙe su fice daga gidan,har yanzu suna maganganu


HAƊEJIA ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA


Tuni an cigaba da shirye shiryen bikin Sulaiman da budurwar shi mifra,sai Amra da Khaleel,a ta bangaren mum ma tana ta shirye-shiryen auren,don har da feena za'a haɗa, Daddy da Abba ne da kansu suka nufi albasu don sanar wa mahaifiyar ta su


Suna zaune a ɗakin nata inda ta shimfiɗa musu tabarma,bayan sun gaishe ta a girmame Daddy yace "to inna! Allah dai ya kawo lokaci,zamu sake aurar da yaran mu"ya ƙarashe ya na ɗan murmushi

Shiru inna ta yi kafin ta ce"to Allah yasa albarka,su nawa ne yaran?"

Abba yace "su uku ne,ni zan aurar da biyu shi zai aurar da ɗaya"

"Ya yi kyau!to ya batun ƴar gidan ɗan nan?"

Su Daddy suka kalle juna da mamaki,kafin Abba cikin nutsuwa ya ce"wannan karatu take yi inna, dududu ma nawa take?su surayya da Nusra ma duk sun girme mata"

"Wannan bai dame ni ba! abinda nake so na ji shine za'a yi gaggawar sauke haƙƙin marainiya a lokacin da ya dace!ba na son jin anyi auren waɗannan yara babu ita a ciki!!!"

Duk yadda suka so fahimtar da inna abu ya ci tura,a ƙarshe ma sai ta fashe da kuka ta na faɗin"yanzu saboda wannan yarinya zaku daina yi min biyayya kamar yadda ɗan nan ya bijire min a dalilin uwar ta?"tilas babu yadda suka iya,haka suka baro albasu cikin damu wa da tashin hankali


Auren ƴar gidan ɗan nan🤔 gaskiya wannan tsohuwa da rigima kike🙄


Kada dai a manta VIP group #300 ne kacal

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee


*Young talented writers association (YOTA)*

Page 39

Daddy ya tattauna da aunty Naja sosai akan batun auren khairi,ta nuna masa babu komai,ko da an yi auren ai ba zai hana ta karatun ta ba,kan haka Daddy ya sanar da mom batun auren

Ko a jikin ta,asalima murna ta yi wannan alaƙaƙai ɗin za ta bar mata gida,duk da cewa yanzu ta Beely take yi,wadda ta dawo gida kamar da ciwo,yau da lafiya gobe babu,ga cikin jikin ta da yake wahalar da ita

Abba da daddy sun tattauna sosai kan mijin da zasu aura wa Khairi,wadda yanzu haka ta gama placement ɗin ta ta dawo gida, lesson teacher ɗin ta ya ɗora mata karatun da yake mata kasancewar yanzu ss1 zata tafi,Kuma science class za ta tafi


** ** **


Dawowar mum daga asibiti kenan, kasancewar jikin Beely yaƙi daɗi ta kai ta,sai kuma aka yi admitting ɗin ta,ta na shigowa ta ga Azad a zaune yana danna waya,tsam ta tsaya da mamaki ta na kallon shi,ya miƙe ya rungume ta ya na murmushi,ya ce"I miss you so much mummy na"

"Azad! welcome!zuwa haka babu sanar wa?"

"Daddy ne ya kira ni wallahi,ya ce na zo urgently,ban sani ba ko wata matsalar ce"

Mum ta zauna,ya gaishe ta da girmama wa,ta amsa da kula wa,ta ce "ka ci abinci ka huta tukunna,zan yi magana da kai,Ni ma yanzu zan yi wanka na huta ne, kuma zuwa anjuma zan koma asibiti feena ta dawo gida"

"Waye babu lafiya?"

"Bilkisu ce wallahi,ciki gare ta yake bata wahala,yanzu haka ma an saka mata drip,ga mijin nata don wulaƙanci ya watsar da ita ko tuntuɓar mu ba ya yi "shi dai Azad bai ce komai ba banda Allah ya sauwaƙe,ya miƙe ya nufi part ɗin shi

A garden ɗin gidan ya hango Khairi ta na ta karatun Alqur'ani cikin ƙira'ar ta mai daɗi,ba tare da ɓata lokaci ba ya nufi can

Ta na hango shi ta rufe Alqur'anin cike da mamaki ta na murmushi ta na kallon shi,shima murmushi yake yi ya na kallon ta,gaba ɗaya ta sake sauya wa,kamar ma ya ga a ɗan lokacin da bai ganta ba kamar ta sake zama budurwa,yanzun ma ta na sanye da hijabin ta ɗinkin jilbab milk color da ya dace da chaculate skin fatar ta

Waje ya samu ya zauna yabna kallon ta ya na faɗin "an gaida Malama Khairi!"

"Yaya Azad!yau kune a garin namu?sannu da zuwa,ya kowa da kowa?ya baka zo da aunty na ba?"

Murmushi ya kuma yi yace"tun ɗazu na zo ai kina bacci,na leƙa mun gaisa da aunty Naja ta ce kina bacci, auntyn ki dama ta na Nigeria,maybe ta zo bikin da za'a yi"

"To Allah ya nuna mana da alkhairi,ya aikin?"

"Aiki alhamdulillahi,ya karatu?"

"Karatu alhamdulillahi!mun gama junior secondary,sauran mu senior "

"To Allah ya bada Sa'a,yanzu bari na shiga na yi uzuri,zan je gidan Abba mu gaisa"

"Ka ce ina gaishe shi"

Har ya yi gaba ya juyo ya na kallon ta ya na murmushi ya ce"ko dai za ki je ne?"

Ta yi saurin gyaɗa masa kai,ya ce"to ki shirya sai mu tafi"cikin ɗoki ta ce"to yaya"

Bayan rabin awa ta fita don ta same shi, dama sai da ya fitar da mota sannan ya kira ta ya ce ta fito ta same shi, saboda mum,ta chanja hijabin jikin ta zuwa sea green,ta ɗauki wayar ta ta fito,ya ɗauke ta suka nufi Hadejia road


HAƊEJIA ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA


"Ammi ya kamata a duba makomar yarinyar nan,kar a lalata mata goben ta, lokaci ya yi da ya kamata a daina biye wa inna ta na mulkar mutane da gigin tsufan ta, tsakani da Allah yarinyar nan wahalar da rayuwar ta kawai za'a yi"

Ammi ta kalli sulaiman da ya ke magana rai a ɓace,ta yi ɗan murmushi tace"to in banda abin ka sulaiman uwa ce a wajen waɗanda suka isa da yarinyar da ka ke magana akai,suma tunda ka ga sun karɓi maganar babu yadda za su yi ne"

"To amma ba zai yiwu a chanja angon ba? I mean,a ba wa yarinya zaɓi ta auri wanda take so ko?"

Ammi ta girgiza kai tace"haka suka tsara, tuntuni,a yadda na fuskanta ma tun bayan rasuwar mahaifin yarinyar babu daɗewa,don haka naka addu'a ne kawai, Allah ya ba su zaman lafiya"

Shiru sulaiman ya yi jiki a sanya ye,zuwa can ya ce"to mum why not a ɗaura auren sai ta ci gaba da zuwa makaranta?idan yaso ko secondary ta gama sai ayi tariyar?"

Ammi ta ce"kai baka san wacece kakar ku ba har yanzu,da ka san wace ce ita da baka zo da wannan zancen ba"Sulaiman ya yi shiru cikin jimami,duk abinda inna take yi bai taɓa yi masa ciwo ba sai wannan,daidai wannan lokacin ya ji sallamar Azad da Khairi

Kamar an tsikare shi ya tashi ya fita,bai taɓa ganin dacewar su kamar na yau ba,ya ji wani tausayi ya shige shi, Khairi ta gaishe shi ta na murmushi,ya amsa shima fuska a sake,sannan ya ce ta shiga su gaida Ammi,idan ta fito kuma ta je su gaisa da Abba

Ta na shiga Sulaiman ya ja hannun Azad suka fice zuwa part ɗin shi,bayan sun zauna Sulaiman ya ce"big bruh matar nan fa rigimar ta yawa gare ta fa!"

"Wacce matar?"Azad ya tambaya ya na kallon shi

"Inna mana,can you imagine baiwar Allan nan ta dage wai sai an yi auren Khairi?zancen da nake yi maka yanzu su Daddy suna shawarar wanda zasu bawa ne"ya ƙarashe yana tsare shi da idanu

A zabure Azad ya ce"yaushe?ita yarinyar ta sani?"

"A'a bata sani ba,asalima su kansu a cikin jimami suke"Azad bai sake sauraron Sulaiman ba ya miƙe ya fice daga part ɗin ya bar Sulaiman da bin shi da kallo,kai tsaye parking space ya nufa ya faɗa motar shi ya bar gidan da gudu,ko khairin ma da ya zo da ita bai ɗauko ba

Sanda ya je mum bata nan,ta koma asibiti,don haka ya kira ta a waya,ta tabbatar masa dama drip ne za'a saka wa Beely,anjuma za su dawo


KHAIRI


Da fara'a ta gaida Ammi cikin girmama wa,amma ta amsa ta na kallon ta cike da tausaya wa,ta rinƙa ɗan jan ta da hira ma,kafin ta miƙe ta nufi part ɗin Abba

Sun gaisa sosai da Abba da Daddy da yake nan, Abba ya na ta tsokanar ta kamar yadda ya saba ta na murmushi,sun ɗan juma suna hira da ita,kafin ta fito parlour ta na ƙoƙarin kiran Azad ta ji yana ina

Kusan cin karo su kayi,ta ɗaga kai ta na kallon kyakkyawar fuskar shi da take a ɗaure kamar wanda aka aikowa saƙon mutuwa,ya yi kyau sosai cikin wasu designer riga blue Black da baƙin wando,kanshi sanye da baƙar hula p-cap,idanun shi sanye da baƙin glasses,ƙafar shi sanye da wani baƙin canvas,baƙin sajen nan na shi ya sake ƙawata kyakkyawar farar fuskar shi,wadda take a ɗaure

A seconds biyu ta ƙare masa kallo sannan ta ɗauke kai ta zagaye shi ta wuce,ya bi ta da kallo, kafin ya ɗauke kai ya shige parlourn Abba

Kusan rabin awa suka ɗauka kafin su fito,dukkan su fuskokin su babu wata rahama

A lokacin Khairi ta na zaune a parlourn ta na chat da su Amra ƙawayen ta,ta na nan zaune Amra da Surayya suka shigo,ganin sun ɗauke kai ya sa ita ma bata yi musu magana ba ta cigaba da chat ɗin ta

Daddy ne ya mayar da ita gida,ya ce mata kar ta yi bacci zai zo su yi magana,tabce to Allah ya dawo dashi lafiya

AZAD

Da sallama ya shigo ɗakin mum,ta amsa cike da kulawa,ya kalli Beely da ke kwance,ta rame ta ƙara yin fari,kafin ya yi magana ta yi murmushi tace"good evening big bruh!"

"Evening Bilkisu,ya jikin?"

"Jiki alhamdulillahi,na samu sauƙi"

"To Allah ya ƙara afuwa,mum dama zuwa na yi mu yi wata magana"

"Mum ta kalle shi ta ce"to Azad,ina jin ka"

Waje ya samu ya zauna,ya tattaro duk wata nutsuwa da ƙwarin gwiwar shi ya fara magana

"Mum kin tuna?kin tuna lokacin da zan auri fadeela na ce miki ina da wadda nake so ko?"

"Eh na tuna son, fadeela ma a yanzu idan baka son ta na baka go ahead ka rabu da ita,babsu da kirki daga ita har uwar ta"

Azad ya sauke ajiyar zuciya cike da fargaba ya ce"mum ko ban rabu da ita ba babu Matsala, lokaci ya yi da zan ƙara aure, lokaci ɗaya tare da su feena, saboda wadda nake so ɗin ta ƙare karatun,mum roƙo na ɗaya kawai ki bani dama ɗaya kawai"

Da murmushi sosai ta na kallon shi ta ce "na yarje maka Azad,wace ce ita?ƴar waye?daga ina take?in sha Allah zan shige maka gaba ka aure ta,nima dai na faranta wa wannan ɗan nawa da ya fi yi min biyayya akan dukka yara na"

Sosai Azad ya ji relief,yabyi murmushi yabce"ba wata babce mum,UMMUL KHAIRI CE!"

A mugun kiɗime mum ta ke kallon shi,da ƙyar ta fizgo kalmar "wacevce Ummul khairi?"

"Ummul khairi dai tamu ta gidan nan,na rayu da matsanancin son ta tsawon lokaci,tun sanda na fara ganin ta, saboda ke na haƙura,don Allah a wannan karon ina roƙon ki mum ki daure na samu muradin raina,don Allah mum,mum idan na rasa ta na san zan iya mutuwa"ya ƙarashe ya na zubewa a gaban mum ya haɗe hannayen shi biyu


To fa!kuna ganin anya mum za ta bari Azad ya auri Khairi?yarinyar da ta tsana fiye da komai?wadda ta ɗora wa laifin duk wani abu da ya same ta?


Kada dai a manta VIP group #300 ne kacal

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee

*Young talented writers association (YOTA)*


Page 40

Shiru mum ta yi ta na kallon shi,kanta har wani juya wa yake yi tsabar tashin hankali da mamaki,a hankali Beely da ke kwance ta tashi zaune ta na kallon Azad da har yanzu yake durƙushe gaban mum ya na fatan ta yarda da buƙatar shi, Beely ce ta fara magana

"Yaya Khairi kuma?Khairi dai ta gidan nan?"

A sanyaye ya kalli Beely yace"ita nake so Beely,ban taɓa soyayya ba,ban san yadda take ba sai akanta,na fara son ta tun lokacin da kowa yake ƙyamar ta,ake kallon ta a matsayin abin gudu,na yi tsammanin tausayi ne,sai yanzu na gane tsananin soyayya ce, Beely ina jin idan ban aure ta ba zan iya mutuwa"ya ƙarashe Muryar shi a karye

"To kuwa wallahi sai dai ka mutu Azad! ka cuce ni Azad!yau na gane ashe munafurta ta kake yi? mene ne tare da wannan matsiyaciyar yarinyar da har kake son ta?wacece ita?to wallahi ko zaka mutu ba zaka aure ta ba, wallahi tallahi duk ranar da ka kuskura ka nuna wa daddyn ku ka yi kana son ta sai na tsine maka!

Tuntuni na gaya maka ka fita sabgar ta,ashe baka fita ba? Azad saboda wannan yarinyar da ta saka miji na ya wulaƙanta ni ka saɓa min? abinda ba ka taɓa yi ba tsawon rayuwar ka?yayi kyau"cikin kuka mum ta yi wannan maganar,sannan ta miƙe fuuuu ta fice daga ɗakin

Hawaye tuni ya daɗe da wanke wa Azad fuska,jin shi yake yi cikin tashin hankali irin wanda bai taɓa fuskanta ba a rayuwar shi,ya gama saka rai da auren khairi musamman lokacin da ya sanar da mum cewa yana da wadda yake so ta amince,bai taɓa tsammanin ƙiyayyar da mum take yi mata ta kai ta zaɓi ya mutu don kar ya auri Khairi ba,ya rarrafa kusa da Beely da ta ƙame cike da mamaki ta na kallon shi,ya kama hannun ta cikin tashin hankali yake faɗin"Bilkisu ki taimaka min, I know kin san mene ne so,kin ɗanɗana zafin rashin masoyi,kin san yadda yake,to ki ƙaddara idan nine zan shiga ninkin halin da kika shiga sau dubu,ina roƙon ki ki taimaka min ki roƙar min mum ta bar ni na samu Khairi, wallahi idan ban same ta ba komai zai iya faruwa Beely!"

Ta tausaya wa yayan nata,amma ta ji zafin wannan mummunar bagidajiyar yarinyar wai wannan classic yayan nata yake nema ya haukace akan ta,cikin ɓacin rai ta fara magana

"Yaya Azad ya kamata ka dawo hayyacin ka!wace ce kuma wata khairi da ......."

"Ba kowa bace khairi sai yarinyar da nake mutuwar so kamar rai na Bilkisu,ba zan iya rayuwa babu ita ba"

"Ai kuwa yaya Azad ya kamata ka cire ta a ranka, can't you remember a dalilin ta farin cikin da muka ginu dashi ya tarwatse? beside,me zaka yi da wannan mummunar yarinyar?"

Wani mugun kallo ya watsa mata ya ce

"Mummuna!khairin?amma ai tafi ki kyau,ke ba'a ce me za'a yi dake ba sai ita?"ya faɗa cikin ɓacin rai,sannan ya miƙe ya fice daga ɗakin a fusace

Beely ta bi shi da kallo cikin tsananin mamaki,lallai so makaho ne, banda haka idan ba ta manta ba kafin bikin su da fadeela ta taɓa kiran fadeela kyakkyawar matar shi,amma ya ce ita ta fi ta kyau,yau kuma ya ce Khairi ta fi ta kyau,kuma ita duk da ta san da gaske tafi fadeela kyau,amma ai fadeela tafi Khairi,a fili ta furta"in sha Allah yadda ba zaka koma cikin mum ba haka ba zaka taɓa auren wannan yarinyar ba har abada,ko mum bata hana ba ni sai nayi manaƙisar da zan saka abin ya lalace in sha Allah "ta buga tsaki cike da jin tsanar khairi a ran ta


HAƊEJIA ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA


"Good evening Ammi!"ya faɗa cikin dakakkiyar Muryar shi, wadda babu alamun wasa ko fara'a a ciki

Ɗago wa ta yi ta na kallon shi,babu shiri hawaye ya ɓalle mata,cikin hawaye take faɗin"ka kyauta Auwab!na gode!!ka nuna min cewa matar ka tafi mu ni da ƴan uwan ka,baka da sauran abinda za ka gaya min "

"Don girman Allah Ammi ki yi haƙuri,nayi laifi,na yarda,kiyi min duk hukuncin da zai sanya ki ji sanyi,amma na haɗa ki da girman Allah ki daina zubar min da hawaye,don girman Allah Ammi "ya faɗa yana kai gwiwar shi ƙasa hankali a tashe

Ammi ta yi masa banza, Sulaiman da yake tsaye a bakin ƙofar ya na kallon su cike da tausayawa ne ya shigo da sallama, Ammi ta amsa ba tare da ta kalle shi ba

Zama yayi,cikin nutsuwa ya kalli Ammi,cikin yaren ta ya ce"a yi haƙuri Ammi,a bi komai a sannu,babban yaya ya yi kuskure,ki karɓi tuban shi,fushi da shi sam ba alkhairi zai zame masa ba, please Ammi ki yi masa afuwa"ya juma a sashen yana roƙon ta,da ƙyar ta haƙura ta sauko

Da kanshi ya ja shi zuwa part ɗin shi,cikin tashin hankali Auwab yake kallon Sulaiman ya ce

"Bruh yanzu ya zan yi?su Abba sun shammace ni,daga zuwa sai ayi min aure?wallahi ban shirya wa hakan ba,me zan gaya wa Inaaya ta fahimce ni?"

Ran sulaiman ya ɗan ɓaci,wato duk wannan tashin hankalin da ake ciki shi damuwar shi matar shi,amma haka ya danne ya rinƙa bashi haƙuri da shawarwari ya na kwantar masa da hankali,amma still ya kasa yarda,wai su Abba zasu yi masa auren dole,kuma ga dukkan alamu ammien shi ma ta na goyon bayan hakan


LUGARD ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA


"Mum don Allah ki yafe min laifin da na yi miki,ki ji ƙai na mum,kin san ni mai biyayya ne a gare ki,ba na taɓa saɓa abinda kike so ko da kuwa bana so,a karo na farko mum ina roƙon ki da girman Allah ki taimaka ki barni na auri zaɓin raina,don Allah mum,ki ceci rayuwa ta"feena da ke shigowa parlourn ta goge hawayen ta cike da tausayin yayan nata ta na kallon mum ɗin su da ko kallo Azad ɗin bai ishe ta ba, Azad ya sake matsa wa cikin tsananin tashin hankali ya kama ƙafar ta ya na mata magiya,amma sai ta ɗauke fuskar shi da mari,cikin ɓacin rai take faɗin

"Na haramta maka auren yarinyar nan har abada Kamar yadda Allah ya haramta wa matacce dawo wa duniya,idan kuma ka nace,to sai ka biya ni nono na da kuma zaman da ka yi a ciki na,na bar mata kai"

Cikin tashin hankali mai tsanani yake kallon ta hawaye na bin kuncin shi,mum ɗauke kan ta tayi,asalima sai ta miƙe ta bar parlourn don kar ya karya mata zuciya

Cikin tashin hankali Azad ya miƙe a firgice ya fice daga parlourn ya nufi part ɗin shi,feena ta bi shi da kallo ta na share hawayen tausayin shi

KHAIRI

Bayan tayi sallar isha'i tayi wanka ta shirya cikin kayan bacci,ta ɗauki wayar ta da take chaji ta haye gadon ta ta lulluɓa da duvet ɗin ta ta hau online ta fara chatting da su Amra ƙawayen ta

Aunty Naja ce ta leƙo ɗakin,sai dariya Khairi take yi saboda Amra da tace itama dama ta rubuta placement ɗin ta zo gida ta yi kwanciyar ta,tana shirin bada amsa sai ga aunty Naja

Shaida mata ta yi cewa Daddy na kiran ta,bata ce uffan ba ta ɗauki dogon jilbab ɗin ta ta sanya suka nufi parlourn aunty Naja

Da sallama suka shiga part ɗin daddy,ya amsa ya na murmushi,yace"an gaida uwa da ƴar ta!"suka yi ƴar dariya, Khairi ta zauna kusa da ƙafar shi,cikin sanyin Muryar ta ta furta

"Good evening daddy!"

"Evening daughter!ya karatun?"

"Alhamdulillah,muna ta yi daddy"

"To Masha Allah daughter! Allah ya ƙara taimaka wa,yawwa!dama magana nake so na yi dake"

"To Daddy "

Sai da ya ja numfashi cike da damuwa ya sauke,da ƙyar ya iya tattaro nutsuwar shi sannan ya yi mata bayanin duk yadda suka yi da inna

Duk da cewa ta san za'a yi haka,amma hankalin ta ya tashi sosai,ta goge hawayen idon ta,cikin kwantar da murya Daddy yace"ki yi haƙuri Khairi,babu yadda zamuyi ne,mun yi ƙoƙarin nuna mata illar hakan amma taƙi sauraren mu ma, ƙarshe take ƙoƙarin ta jingina laifi akan babban yayan mu, mahaifin ki"

Khairi ta daidaita nutsuwar ta ta ce"babu komai Daddy, abinda Allah ya tsara shine daidai, Allah yasa hakan ya zama mafificin alkhairi"

Cike da tausayin ta da jin daɗin yadda ta karɓi maganar ba tare da ɓacin rai ba Daddy yace"ameen ameen daughter! Allah ya yi Miki albarka kinji?sannan ki kwantar da hankalin ki batun makaranta,wanda zamu aura Miki zai bar ki kiyi ta karatun ki in sha Allah,har ki zama likita,da kaina ma zan buɗe Miki asibiti in sha Allah"ta yi murmushin yaƙe kawai

Daddy ya cigaba da faɗin "kar ki ji komai,ba wani bare za'a aura miki ba,yayan ki ne,kar ki damu,in sha Allah zai kula da ke tamkar muna wajen,kar ki saka damuwa a ranki"ta yi murmushi ta ce"to Daddy,na gode "

"Yauwa ƴar albarka,yanzu ki tashi ki je ki kwanta,gobe zamu ƙarasa magana"ta miƙe a sanya ye ta na faɗin "to Daddy,na gode da dukkan kulawar ku a gare ni, Allah ya biya ku da aljanna "

"Ameen daughter,kema Allah ya albarkaci rayuwar auren ki,ya baki zuriyar da za su yi miki biyayya fiye da yadda kika yi mana"khairi bata sake magana ba ta miƙe ta nufi ɗakin ta, Daddy ya bita da kallo zuciyar shi cike da tausayin ta,sam bata san daɗin rayuwa ba,amma ya na fatan Allah yasa ta samu farin ciki a gidan Auwab

Ita kuwa tana shiga ɗaki ta fashe da kuka cike da tashin hankali da rashin hope,shikenan komai ya ƙare, karatun da ta ƙwallafa rai akai zai tafi a banza kenan,duk da har yanzu tana da hope,sai dai kuma tana cikin damuwa don bata san wane ne angon nata ba


Tsakanin Azad da khairi wai waye ya fi zama abin tausayi ne🥹🥲😥

Kada dai a manta VIP group #300 ne kacal


#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee

Page 41

A ranar bata yi wani bacci na azo a gani ba,ta raya daren ta da salloli da roƙon Allah ya kawo mata ɗauki,bata samu bacci ba sai daf da asuba,ko da ta yi bacci ma munanan mafarkai ta rinƙa yi kan batun wane ne mijin na ta,da yaya auren zai kasance


AZAD


Faɗar irin tashin hankalin da yake ciki ma ɓata lokaci ne,a haukace ya koma side ɗin shi,ya na zama kuma numfashin shi ya nemi sarƙewa,ya gaggauta shaƙar inhaler ɗin shi har numfashin ya daidaita ta,ya koma ya kwanta akan sofa ya na sauke ajiyar zuciya,ji yake kamar numfashin shi zai rabu da gangar jikin shi tsabar tashin hankali,ya san wacece mum ɗin shi sarai,ya san ta idan ta dage akan abu, tunda ta dage mawuyacin abu ne ta yarda da auren nan,a hankali zazzaɓi mai zafi ya lulluɓe shi,ya janyo duvet ɗin shi da ƙyar ya lulluɓa ya na karkarwar sanyi,ji yake a duniya babu wanda ya kai shi shiga tashin hankali,ji yake ya tsani duniyar, komai ya fita a ran shi,ji yake idan bai samu khairi ba rayuwar shi ta zo ƙarshe


HAƊEJIA ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA


Gaba ɗaya Auwab ya zama kamar wani zautacce saboda tashin hankali da damuwa,ko abinci baya iya ci sai Sulaiman ya yi masa dole,Ammi kuwa tuni ta fita a lamarin shi, Daddy kam artabun da aka sha akan batun auren nan ya sa ya ɗauke masa wuta,don ya ga alamun idan ya ba shi fuska ba zai yarda ayi auren nan ba, Auwab ya so samun dama a wajen barrister,amma shima ya nuna masa auren nan dole ne fa, dalilin hakan ya shiga tashin hankali irin wanda bai taɓa shiga ba,a wajen Sulaiman kaɗai yake samun relief,da ya ce masa ya kwantar da hankalin shi,zai san yadda za'a yi a fasa auren

Shi kam Sulaiman ya tabbatar da soyayyar da Azad ke yiwa Khairi duk da Azad ɗin ya musanta hakan,amma so yake ya sake zama da Azad ɗin sannan sai yayi wa su Daddy magana,idan suka amince sai a mayar da auren kan Azad,ba don komai zai yi haka ba sai don ya ga idan ta auri Auwab ba zata ji daɗin zaman gidan shi ba,tunda baya son ta, saɓanin Azad

A ranar da ƙyar ya samu Auwab ya kwantar da hankalin shi,shi kuma ya shirya ya tafi lugard road don tattaunawa da Azad


LUGARD ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA


Yau da safe bayan khairi ta gama shirin ta ta karya ta samu Daddy,bayan sun gaisa ya sanar mata wanda yake a matsayin angon nata na gobe,cikin fara'a ya ƙarasa da faɗin "kinga yayan naki dama ba mai son hayaniya bane kamar ke ko?kuma na san shi,zai kula da ke sosai"

Bayyana irin tashin hankalin da khairi ta samu kanta a ciki ma ɓata lokaci ne,amma ta yi ƙoƙarin controlling kanta a gaban Daddy,wanda bai kula da yanayin da ta tsinci kanta a ciki ba ya sallame ta ya na saka mata albarka,ta miƙe ta shige ɗakin ta ba tare da ta sake Magana ba

Ta na shiga ɗaki ta faɗa kan gadon ta ta fashe da kuka mai tsuma zuciya,ita a kaf dangin ta bata jin akwai wanda ta tsana kamar bawan Allan nan,a cewar ta ya na da wulaƙanci, ya na da rainin hankali,sannan ba shi da kirki,tuni ta ji ɗan hope ɗin ta na karatu ma babu shi,gaba ɗaya ta ji yanzu ta sake koma wa UMMIYO ɗin ta ta asali mara gata,mara madafa,wadda bata da sauran buri a duniya

Tana ta gursheƙen kuka har bata san ma lokacin da aunty ta shigo ɗakin ba,sai ji ta yi ta ɗaga ta ta na faɗin "mene ne abin kukan kuma?Ni a gani na ai farin ciki ya kamata kiyi ko?"

Kasa magana tayi,sai kuka take yi, aunty Naja ta rungume ta ta na faɗin "mu yi magana khairi, mene ne matsalar?me ya faru kike kukan nan?"

"Aunty ba zan iya auren shi ba,don Allah ki cewa Daddy ko albasu ya je ta samo min kowaye zan aura,aunty ba zan iya zama dashi ba,tsoron shi nake ji aunty, don Allah ki yi wani abu akai,don ......."

"Shshshsh!!!!!!wannan kukan haka!kina matsayin mace?wai kina tsoron namiji?haba alkhairin mata!wannan ai ba da mutanen albasu za kiyi,haba khairi!tashi muyi magana"babu musu khairi ta zauna sosai ta na share hawayen ta,cikin kwantar da murya aunty Naja ta fara magana

"Ke fa mace ce khairi,kina da ilmi na boko da addini,kin san abinda ya kamata da wanda bai kamata ba, kazalika na san zuwa yanzu baki da wanda kike so,ko kina da shi na yi magana da daddy?"cikin sanyin jiki ta girgiza kai ta ce"bani da wanda nake so,amma ina son na yi karatu na,Daddy ya saka min rai zan zama likita wata rana, amma kuma ko secondary ɗin ban ƙare ba karatu na ya na neman ya zama tarihi,aunty ina jin tsoron idan na aure shi babzan ji daɗin zaman gidan shi ba,ba shi da kirki kamar su yaya Azad da yaya Sulaiman,ya na da wulaƙanci da rainin hankali"

"Irin hakan ma ai yafi,shi namiji a fuska ne za ki ga kamar ba zai juyu a wajen mace ba,amma idan kika bi wasu hanyoyin sai kiga yafi son ki ma fiye da matar shi ta gida"

"So na?kuma fiye da wadda yake aure?aunty ta yaya kenan?"ta faɗa har zuciyar ta ta na jin hakan ba mai yiyuwa bane

Auntyn Naja ta gyara zaman ta ta fara mata bayani cikin bada ƙwarin gwiwa

"Na farko sai kin fara karɓar ƙaddarar shi ɗin mijin ki ne,kuma duk inda mace take ga mijin ta sai ta rissina masa,ki zamo mai biyayya a gare shi,ki san abinda bakin ki zai gaya masa,ki gane abubuwan da yake so da wanda baya so,ki ƙware wajen iya sarrafa masa abinda zai ci,ki yawaita yi masa shagwaɓa,ko ma nace ki mayar da kan ki yarinya a gaban shi,ki gane abinda yake so da wanda baya so,wanda yake so ɗin ki dage da yi masa,wanda baya so ki nisance shi

Sannan ƙarin shawara,ko da kin yi masa maganar karatu yace a'a kar ki tayar da hankali,akwai hanyoyin da za ki bi da kissa ki saka shi juya ra'ayin shi,sannan ki ƙara haƙuri akan wanda na san ki dashi,ki ƙara tsafta akan wadda na san ki da ita,haka ma ibada,sannan ki riƙe gaskiya da riƙon amana,magana ta ƙarshe ki san irin zaman da za kiyi da abokiyar zaman ki,don ko ciki ɗaya kuke da kishiya shaiɗan ya na iya galaba akan ta

Don Allah khairi ki cire damuwar nan,ki gode wa Allah za kiyi aure ki rabu da ƙananu ƙananun maganganun nan,a rayuwa fa ke za ki yiwa kanki yaƙi,babu wanda zai yi Miki,kuma ke mace ce duk da ƙarancin shekarun ki,aka zo wajen kissa da tarairayar miji babu babba babu yarinya"

Shiru khairi ta yi ta na sauraren aunty Naja,duk jikin ta a sanyaye,aunty tace"ki saki jikin ki,ki shirya ga malamin ki can yazo,sai ki fito"ta miƙe ta fice daga ɗakin,khairi ta bita da kallo, maganganun ta suna yawo akan ta

AZAD

Daren ranar sam bai runtsa ba, saboda tashin hankali da kuma ciwon da ya same shi,da ƙyar ya iya tashi ya yi alwala ya yi sallar asuba ya koma ya kwanta,ji yake dama zai mutu da hakan zai fi masa sauƙi,ji yake ya tsani komai da kowa,bashi da fata da buri sama da mallakar abar ƙaunar shi khairi

Mum ta san ɗabi'ar Azad,baya dogon fushi,amma ganin yau kwata kwata bai fito ba har yanzu da ake maganar biyar na yamma sai ta yi tunanin ko fushin ya yi,hakan ya ƙara zafafa zuciyar ta,wato saboda son waccan yarinyar da ta tsana fiye da komai a rayuwar ta Azad zai yi fushi da ita?ai shikenan,don ma kar zuciya ta ja ta ta ga halin da yake ciki ya sa ta shirya ta yiwa driver Magana ta fice daga gidan

Bata fi mintuna goma da fita ba Sulaiman ya shigo layin,ya na shigowa kuma ya gamu da haidar,cikin girmamawa haidar ya gaishe shi,ya amsa ya na bashi hannu,suka yi musabaha kafin ya ce

"Babban yaya fa?"

"Gaskiya yau dai through out ma ban gan shi ba,yana cikin part ɗin shi"

"Kamar yaya kenan?"

"Eh gaskiya ban ji motsin shi ba,sai dai na duba maka"

"What are you saying Aliyu?ko ka manta larurar da ke damun yayan naku ne da har zai wuni bai fito ba ku kasa zuwa ku duba shi?"cikin faɗa yake maganar

Haidar ya sunkuyar da kan shi ya ce"I'm sorry yaya,mum ce ta ce mu ƙyale shi,wai sun yi magana ne jiya shine ya yi zuciya"Sulaiman bai jira ƙarshen batun ba kai tsaye ya nufi part ɗin

Ta bakin part ɗin aunty Naja ya bi, kasancewar part ɗin Azad a kusa da na aunty Naja yake,don haka khairi da ke zaune bakin window tana kalle kalle ta ganshi ya wuce,babu ɓata lokaci ta fito ta na leƙen shi

Sun ɗan kwashi mintuna suna bugu,har sai da suka fitar da rai,gashi babu mai makullin part ɗin,sai ga Azad ya buɗe ƙofar

Dukkan su bin shi suka yi da kallo,ya rame ya yi haske,daga gani ya na matuƙar jin jiki,basu ankara ba sai gani suka yi ya yanke jiki ya faɗi

Cikin tsananin tashin hankali suka ɗauko shi suka fito da shi,a guje khairi ta fito ta na faɗin "yaya sulaiman me ya samu yaya na?"

Bai samu zarafin kula ta ba,suka sanya shi a mota, itama ta shige motar, Sulaiman ya ja suka nufi asibiti

Allah sarki Azad 😭 Allah ya baka lafiya 🥹


Kada dai a manta VIP group #300 ne kacal


#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️ Nusy bee

*Young talented writers association (YOTA)*


Page 42

Wani tsadadden private hospital suka nufa,suna zuwa aka shiga da Azad emergency room don har zuwa yanzu numfashin shi bai dawo ba,ga shi da matsalar athma,wadda likitan shi ya sha warning cewa a rinƙa bin shi a sannu,don ciwon ya taɓa shi sosai,wannan sanannen abu ne a duka family ɗin

Daga Sulaiman har khairi zuru suka yi a reception,khairi ta yi tagumi ta na ɗan goge hawaye lokaci lokaci

An kai a ƙalla awa biyu kafin likitan da yake duba shi ya fito ya na ta share gumi,da sauri suka miƙe,ya dubi Sulaiman ya ce"officer biyo ni office, I want to discuss something with you"Sulaiman babu musu ya miƙe ya bishi ba tare da ta ce uffan ba,ita ma Khairi da sauri ta biyo su, Sulaiman ya ce"khairi jira mu kin ji?yanzu zan dawo"

"Me ya samu yaya na?"ta faɗa da Muryar kuka hawaye ya na wanke mata fuska

"Kar ki damu,in sha Allah ba wata matsala bace,ki yi masa addu'a kin ji?bari naje na jiyo"bai jira amsar ta ba ya yi saurin bin bayan likitan da tuni ya shige office ɗin shi

Bayan Sulaiman ya zauna ya kalli Dr ya ce"Dr Mahfouz me ya samu Azad?"

Dr Mahfouz ya ja ajiyar zuciya cikin damuwa yace"me ya haɗa Mr Saeed da ciwon zuciya?"

"Ciwon zuciya kuma?"sulaiman ya tambaya a firgice

A nutse Dr Mahfouz ya ce"ciwon zuciya,kuma a binciken mu ya daɗe da kama shi,sai dai a hankali yake girma,zuwa yanzu kuma lamarin ya fara worst,idan ba'a ɗauki mataki akan hakan ba komai zai iya faruwa,ciki kuwa har da rasa shi"

Sulaiman ya furzar da zazzafan huci yabna furta"inna lillahi wa inna ilayhi rajiun!

Doctor yanzu menene abin yi? I mean,menene Abinda za'a yi don kauce wa wannan matsalar?"

Dr Mahfouz ya ce"dole a nisanta shi da abinda zai saka shi a damuwa,kuma a sada shi da abinda zai saka shi a farin ciki ya kawar masa da damuwa"

Jiki a saɓule Sulaiman ya bawa Dr hannu suka sake musabaha ya na faɗin"na gode Dr!"sannan ya juyo ya dawo reception

Khairi ta na ganin shi ta miƙe zumbur ta na jiran ya ƙaraso ya yi mata bayanin abinda ke faruwa,amma tuni ya zaro wayar shi daga aljihun shi ya fara ƙoƙarin kiran Haidar,ya gaya masa anyi admitting ɗin Azad,ya gaya masa sunan asibitin

Ya na waya ya na tafiya har ya fice daga reception ɗin,bayan ya kashe wayar ya samu waje ya zauna yabna jan ajiyar zuciya, zuciyar shi cike da damuwa da kuma tausayin Azad

Ƙasa da rabin awa motar Haidar ta shigo cikin asibitin,tare suke da mum da feena,cikin tashin hankali mum ke tambayar Sulaiman

"Sulaiman ina Azad ɗin?me ya same shi?"Sulaiman ya ɗaga kai ya kalle ta,cikin sanyin murya ya ce "ki kwantar da hankalin ki mum,in sha Allah everything will be okay!muje ciki mu samu likitan ya yi miki bayani da kanshi"babu musu suka wuce cikin asibitin

Khairi ta na zaune ta yi tsumu,sai rarraba idanu take cikin tashin hankali,fargaba sosai take ciki da abinda zai samu yayan nata,ta na cikin wannan halin su mum suka shigo

Duk da firgici da fargaba da mum take ciki amma ganin khairi bai hana ta watsa mata mugun kallo ba,ta wuce ta suka nufi office ɗin Dr Mahfouz, khairi ta bita da kallo a tsorace

Khairi ta na zaune ta ga mum ta fito cikin kuka da tashin hankali,ita ma bata san lokacin da ta miƙe tsaye ba ta na fashewa da kuka ba,mum ta ƙaraso gaban ta ta na kallon ta cike da tsana ta ce"kin yi nasara!kin samu Sa'ar kassara min ɗa,to don Allah ina roƙon ki ki fita daga rayuwar mu, bala'in ya ishe mu haka,daga wannan sai wannan,tunda kika zo gidan mu kullum da kalar sharrin da yake zuwar mana,ba kya tare da kowanne irin alkhairi,kin ruguza min farin ciki,yanzu kuma me kike anan?don Allah tashi ki fita,ba na buƙatar ganin ki anan"

Sam zantuttukan mum ba su dami khairi ba,cikin kuka take faɗin"me ya samu yaya na don Allah?"

"Yayan ki?a gidan uban wa yake yayan ki?na ce fita ki bani waje ko na illaki a asibitin nan"babu musu ta juya ta nufi fita ta na kuka, Sulaiman bai sake magana ba ya bi bayan ta

A harabar asibitin ya samu Khairi ta rakuɓe ta na ta kuka,da sauri ta ƙarasa ya ɗago ta ya na faɗin"is okay!ki yi haƙuri,ki daina kukan nan kar mu koma gida a haka ayi tunanin wani abin"

Cikin kuka Khairi ta ce"to me ya samu yaya na?don Allah ka gaya min?"

"Yayan ki attack ya samu,amma in sha Allah komai zai zo da sauƙi a yau ɗin nan ma"

Cikin kuka tace"to zan jira ya tashi sai mu tafi"

Ya yi saurin girgiza kai ya ce"ba zai yiwu ba khairi,kin ga mum ta na nan,idan ranta ya na ɓace shima na shi zai ci gaba da ɓaci,kuma kin ga mum da kanta ta ce ki tafi,ki yi haƙuri mu tafi"kan dole ba don taso ba ya saka ta a mota suka tafi

A ranar kwanan tashin hankali kusan duka gidan aka yi,wai Azad da ciwon zuciya bayan athma ɗin da yake fama da ita,hatta da su Sulaiman ɗin sun shiga damuwa,don haka washe gari da sassafe Sulaiman ya nufi asibitin

Haidar ya samu a can, Haidar ya gaida Sulaiman da girmamawa, sulaiman ya amsa yavna tambayar shi ya mai jiki, Haidar ya amsa "jiki alhamdulillahi!gashi ya samu sauƙi"

Sulaiman ya mayar da hankali kan Azad da ya idar da Sallah yanzu,ya ce"babban yaya da kanshi! good morning!"

Ɗaga kai ya yi a sanyaye ya na kallon sulaiman,ya sake ramewa ya ƙara fari,sai karan hancin da ya sake zama akan fuskar shi,a sanyaye yace"morning bruh!ka je gida lafiya?"

Sulaiman ya zauna kusa da shi ya na faɗin "alhamdulillahi!ya jikin?"

"Jiki alhamdulillahi! dama ina son magana da kai"

Shiru sulaiman yabyi yanayin shi na chanjabwa,kafin ya ce"da ka bari ka sake jin sauƙi big B"

Girgiza kai ya yi ya ce"no need! Aliyu Please ɗan bamu waje"babu musu Haidar ya miƙe ya fice daga ɗakin

Azad ya ɗaga kai ya kalli Sulaiman,cikin sanyin murya ya ce"man ka ji abinda ya same ni ko?"

"Naji! Dr Mahfouz ya ce ka kamu da ciwon zuciya, Allah ya baka lafiya"

Azad ya girgiza kai,cikin sanyin murya ya ce "ba wannan ba ne matsalar Sulaiman

Sulaiman zuciya ta bata yi min adalci ba,ya jefa ni a cikin soyayyar wadda baza ta taɓa zama mallaki na ba, soyayya irin wadda ko a labari ban taɓa tsammanin zan so kamar ta ba,and......."ya runtse idanun shi ya na jin zafin raba shi da khairi da mum take son ta yi

Sulaiman ya tausaya masa sosai,irin wannan ranar ya guje masa a baya amma a ƙarshe gashi sai da ta kai ga ya riske ta,ya dube shi ya na faɗin

"Ummul khair ce ko?"Azad ya ɗago ya lalle shi a sanyaye ba tare da ya ce uffan ba, Sulaiman ya jinjina kai yace"na daɗe da sanin ka kamu da soyayyar Ummul khairi,kuma daga baya na fuskanci kaima ka san hakan, saboda gujewa matsala irin wannan na same ka na yi maka magana amma ka nuna min ba haka ba,yanzu gashi abin da ya zo ya faru, komai ya kwaɓe,wanda idan ka sake ƙin ba ni haɗin kai ba zai taɓa gyaruwa ba"

"Bazai gyaru ba Sulaiman,ta yaya zan yi aure babu yardar mum ɗi na?mum ita ce komai na rayuwa ta,ita ce farin ciki na,amma a dalilin khairi mum ta yi fushin da bata taɓa yi dani ba, I have no any hope,na haƙura kawai, Allah ya bani wadda ta fita, idan jarrabawa ta kenan Allah ya bani ikon hayewa "hawaye Masu zafi suka zubo masa

Tausayin shi ya kama Sulaiman,ya ji shima kamar ya yi kukan ko zai samu sauƙi,haka dai ya danne zuciyar shi ya yi ta kwantar wa Azad da hankali,duk da cewa Azad ɗin ya ji shi ne kawai

Kwanan Azad biyu a asibiti aka sallame shi,jiki dai ya yi sauƙi,sai kuma jinyar zuciya kuma, kwanan shi biyar da dawowa daga asibiti ya tattara inashi inashi ya koma Australia

Kwanan shi biyu da tafiya Australia,da sassafe mum ta na ɗakin Beely ta na duba ta, saboda kwana da zazzaɓin da ta yi ta ji sallamar Hajiya A'isha da fadeela

Yau ma ba ta nuna musu komai ba ta karɓe su da fara'a,Hajiya A'isha ta kalle ta a yatsine ta ce"ba zama ya kawo mu ba, matsiyacin ɗan ki za ki kira ya zo ya bani takardar ƴa ta,wannan rainin hankalin kuma ya ishe ni,ya za'a zo a jingine min ƴa kamar haja?banda son zuciya ma irin naki Hajiya Salma ke baki ga naki yaran sun fi nawa aibu ba?sai......"

"Kin ga don Allah Hajiya dakata,mene ne haka kuma da sanyin safiya za ki zo ki nemi ɗora min hawan jini?sai kace abin masifa?"


Ko masifar ce ai ke kika ja Hajiya😁


Kada dai a manta VIP group #300 ne kacal

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️ Nusy bee

*Young talented writers association (YOTA)*


Page 43

"Ai ya wuce wai,abin masifa ne,sai ka ce baki san darajar ƴaƴa ba da za ki zubawa ɗanki idanu ya wulaƙanta min ƴa?ke idan aka yi miki haka za ki ji daɗi?wato dai yanzu na gane kin nema wa ɗanki auren ƴa ta ne kawai don ki wulaƙanta min ƴa ko?to lalacewar ƴar tawa bata kai haka ba,ki kira matsiyacin ɗan ki ya sakar min ƴa"

Da kallo mum ta bisu,ita kanta fadeela sai girgiza jiki take yi cike da salon raini,kafin ta ce komai Ma'aruf ya shigo parlourn fuska a ɗaure

Kallon Hajiya A'isha yayi ya ce"Hajiya kar ki zo har gida ki gaya wa mahaifiya ta magana,sannan yaya na ba matsiyaci bane,don haka ki iya bakin ki!yauwa!"

"Na san baka da tarbiyya ko baka tabbatar min ba,ita kanta uwar taku ma banda ƙaddara ko hanya ta isa in haɗa da ita?"

"Rashin tarbiyya ya ƙare akan gantalalliyar ƴar ki,kuma wallahi da ta kashe min yaya na sai na yi Shari'a da ku,waya sani ma ko uban ta da muka ji ance ya mutu uwar ta ce ta ......"marin da fadeela ta ɗauke shi da shi ne ya sanya shi yin shiru,ya na juyowa kuwa ya sauke mata na shi,take hayaniya ta kaure a wajen, don fadeela ihu ta rinƙa yi ta na zage-zage ta na rantsuwa sai ta rama

Wannan bala'in ne ya janyo hankalin dukkan mutanen gidan,ciki har da Daddy da aunty Naja,da yake yau a ɗakin ta yake,da su Beely da Amra,kafin wani lokacin parlourn ya cika da mutane

Fadeela ta na ganin Daddy ta zube a gaban shi ta na rusar kuka,cikin kwantar da murya ya ce"is okay daughter, tell me,me yake faruwa ne?"

Cikin kuka fadeela ta ce"Daddy mum so take ta raba ni da Azad,kuma ina son miji na,yanzu gashi ta saka Ma'aruf ya mare ni don kawai na ce zan koma gidan shi"

Ita dai mum ta na gefe a sandare da mamaki kan mamaki,ba ta taɓa tsammanin su Hajiya A'isha haka suke ba,da tun farko ba zata ɗauki ɗan gold ɗin ta ta aura masa wannan matsiyaciyar yarinyar ba

Ba ta gama ƙamewa da mamaki ba sai da taji Daddy na faɗin "kwantar da hankalin ki daughter!in sha Allah ba zaki yi twenty four hours a Nigeria ba,maza je ki fara shirin bin mijin ki, Allah ya kai ku lafiya "cikin farin ciki fadeela ta miƙe ta na faɗin"na gode Daddy "ta yi gaba, Hajiya A'isha ta biyo bayan ta fuskar ta a washe,dukkan su ko kallon inda Hajiya Salma da yaran ta ba suyi ba suka fice daga parlourn

Mum ta fashe da kuka ta na faɗin "haba barrister!don Allah ka taimaki rayuwar ɗa na!yanzu haka ma ya na fama da larura,ta yaya zata je ta sake ɗora masa wani ciwon?ya kake so ya yi don Allah? don Allah kar a kashe min ɗa na,na roƙe ka!"

Tuni aunty Naja ta juya ta fice daga parlourn ganin abin bai shafe ta ba,amma fa tabbas ta tausaya wa Azad,komai ya kwaɓe kan shi yake rikitowa

Daddy ya kalle ta fuska babu yabo babu fallasa yace"ko me ya faru ai kamar ke kika janyo ko?ke kika zaɓowa Azad mata a matsayin shi na ɗan ki, wanda kika fi kowa iko akanshi?a lokacin da ace na nuna miki ba na goyon baya da sai raina ya yi mugun ɓaci,to yanzu kuma gashi kin yi abinda kike so?sai lokacin da za ki ga abinda ba kya so kice hakan ba zai faru ba?kema kin san waƙa kike yi,matar shi ce har yanzu,don haka ki bar ta ta koma ɗakin ta kamar yadda kema kike ɗakin ki "yana kaiwa nan ya fice ya bar ta da yaran ta da bin shi da kallo

KHAIRI

Tun lokacin da Azad ya kwanta a asibiti bata cikin wata cikakkiyar nutsuwa, saboda har yanzu ba ta ganshi ta ji jikin shi ba,sai dai su yi waya da sulaiman,daga baya ma sai Sulaiman ɗin ya ce mata ya bar ƙasar ya koma bakin aikin shi

Ranar ta sha kuka sosai,don ta san ya san tana son taji jikin shi amma ya tsallake ya bar ƙasar,duk da haka bata yi fushi da yayan nata ba,ta ci gaba da bin shi da addu'ar neman sauƙi

Yau kam duk bala'in da aka sha ba ta sani ba ma, saboda jiya bata kwanta da wuri ba,yau kuma ta tashi da ramuwar bacci,aunty Naja kuma bata tashe ta ba

Washegari da safe Daddy ya tura fadeela zuwa Australia,don rashin mutunci har gida ta zo yiwa mum sallama,wadda zuwa yanzu ma ba wani jin daɗin jikin ta take yi ba,gashi har yanzu Beely ta na fama da laulayi,gashi mijin Beely ko da wasa bai taɓa zuwa ba ballantana su su saka ran komawar ta gidan mijin ta,shi kuwa Daddy bai taɓa yin magana ba,ya dai zuba musu idanu kawai

Lokacin biki ya na ta ƙaratowa, shirye-shirye sun kankama,Abba ne yayiwa amaren duka furnitures,babu abinda ya bambanta su su duka,su kuma iyayen amarya kowacce ta na yiwa ƴar ta gyaran jiki na musamman

Abba ne yayi wa Auwab jan ido akan ya zo ya ga Khairi su tattauna akan bikin da abubuwan da suke buƙata ita da ƙawayen ta,baƙin ciki kamar yavyi hauka,haka ya taho gidan Daddy ran shi a ɓace,ikon Allah ne kawai ya kai shi gidan saboda mahaukacin gudun da yake yi a hanya

Da ya zo kuma sai ya rasa yadda zai yi ya yi mata magana,daga baya dai ya samu Ma'aruf ya yi masa maganar ya kira masa wannan yarinyar

Ma'aruf ya san wadda yake nufi,don haka ya leƙa sashen aunty Naja ya sanar mata ana kiran khairi

Lokacin khairi ta na kwance a ɗakin ta,abin duniya ya dame ta,har yanzu a ƙawayen ta su Amra babu wadda ta sanar wa auren da ake shirin yi mata

Aunty Naja ce ta leƙo ta ce mata ta fito ana kiran ta a babban parlour,a sanyaye ta sanya hijabin ta ta fito zuwa babban parlourn da yake kusa da part ɗin Daddy

Da sallama ta shiga ta na kallon wanda aka ce ya kira ta,ko kallon banza bai yi mata ba,kuma babu alamun zai amsa gaisuwar, hankalin shi na kan tsadaddiyar wayar shi ya na dannawa, fuskar shi ko ɗigon walwala babu

Bata yi fushi ba ta nemi waje ta zauna ta ɗan rissina ta gaishe shi,wannan karon ma ko arziƙin kallon banza bata samu ba ballantana ta yi tunanin zai amsa, asalima sai ya yi tamkar bai san mutum ya shigo parlourn ba

A nan ran Khairi ya ɓaci,ta ja baki ta tsuke ba ta sake magana ba sai wasa da yatsun hannunta da ta ke yi,ko kallon sashen da Auwab ɗin yake bata sake ba,shima dai haka,asalima tamkar bai san da halitta a cikin parlourn ba

Ganin zaman shirun ya ishe ta sai ta miƙe da nufin koma wa cikin gida,a ranta ta na tsaki da jinjina wulaƙanci irin na wannan mutumin

Har taje bakin ƙofa ta ji yace"hey!"juyowa ta yi da salon rainin hankali tace"da ni kake?"ta na yi masa kallon sama da ƙasa fuska a ɗaure

"A'a da shi nake!"ya amsa da ɗaurarriyar fuska"Khairi ba ta damu ba ta ce"au na ɗauka da ni kake"ta juya ta fara fice wa daga parlourn

Bata san ma ya ƙaraso inda take ba sai ji ta yi ya finciko hannun ta,ta juya a firgice ta na kallon shi,cikin idanu yake mata bayani ba tare da ya damu da ta na jin abinda yake faɗa ba ko bata ji

"Did I look like your mate ne da zan kira ki ki rinƙa ƙoƙarin raina min hankali?baki da kunya ne?or do you think na karɓi maganar aurena da ke ne da har za ki zo kina min rashin kunya?

Wait!wai tukunna ma,ke ɗin ji kike mace ce?so don't deceive yourself,ki lallaɓa su Daddy su janye aure na dake,ki koma ki nemi ilmi ina ganin kamar ya fi Miki,idan kuma auren kika fi so,na san ku mutanen ƙauye,sai ki koma a baki daidai ke,ga Azad nan,ko Sulaiman, waɗannan ma ba sa'annin ki bane,sai dai Ma'aruf or Haidar

Ko da ace kin zama macen ma ni ba zaki taɓa zama mace a idanu na ba, saboda mata ta ita ce abinda idanu na ke gani a kowanne lokaci,idan ta na raye babu wata mace da za ta iya raɓa ta ballantana ta yi tunanin zama inuwa ɗaya da ni da sunan mata,so choose what is the best for you,na gama magana,idan ki ka zaɓi wrong choice duk abinda ya biyo bayan hakan ke kika janyo wa kan ki"ya na kai wa nan ya zagaye ta ya tafi ya bar ta a tsaye a wajen

Kan bala'i 🥺🤔

Kada dai a manta VIP group #300 ne kacal


#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee

Page 44

Da kallo ta bi shi baki a sake har ya ɓace wa ganin ta,a hankali wata ƙwalla mai zafi ta ciko idanun ta,kuma sannu a hankali ta gangaro kan kuncin ta,babu ɓata lokaci ta nemi waje ta zauna ta yi kuka sosai,kalaman shi na yi mata yawo a kai,ta na jin ciwon su,ganin ɓata wa kanta lokaci take yi sai ta miƙe a sanyaye ta goge hawayen idanun ta ta koma part ɗin aunty Naja,tana jin duk ta muzanta da cin mutuncin da Auwab ya yi mata

Tsawon sati biyu da faruwar hakan khairi ta kasa manta waɗannan maganganu na Auwab,gaba ɗaya jikin ta ya ƙara sanyi,duk da cewa ita ma ba son Auwab take ba,amma kuma in dai ta tafi gidan shi a haka ta san akwai gagarumar matsala

Yau ya rage auren su saura sati ɗaya,Daddy ya umarce ta da ta shirya ta je albasu su gana kafin ranar auren nata,a sanyaye ta shirya driver ya ja ta suka nufi albasu


BOSTON, MASSACHUSETTS, USA


Wai ina labarin Inaaya ne?

Tun bayan kwana biyu da tafiyar Auwab ta daina samun shi a waya,ko ta kira bata samun shi,ta san halin shi wani lokacin ko ɓata masa rai aka yi sai ya kashe wayar shi,amma ta san ko da ace haka ta faru ai ita ɗin ta dabam ce a wajen shi,ta yarda da irin son da mijin nata yake mata,ba zai taɓa iya tafiya ya bar ta ba tare da ya kira ta ba ko da da wayar wani ne kuwa,amma duk da haka sai tabyi masa uzurin wataƙila abubuwa ne suka yi masa yawa

Sati ɗaya da tafiyar ta shi ya kira ta a waya,ta ji daɗin hakan,amma ba ta ji daɗin yadda ta ji muryar shi ba,ta san maybe dalilin rashin neman su da bai yi bane, whatever dai su suka sani

Yau ta na zaune ta ɗauko wayar ta ta hau Instagram,rabon ta da hawa Instagram ma ta manta,don dama ita social media ba damun ta tayi ba

Kanta ta ji yavna juya wa ganin wani invitation card,ita dai sunan mijin ta da ta hango ɓaro-ɓaro Auwab Usman Saeed shi ya gigita mata lissafi tun kafin ma ta kula da sunan yarinyar da zai aura

Cikin tsananin tashin hankali ta kira Shukra, Shukra ta na ɗagawa bata jira cewar ta ba ta ce maza maza ta bincika mata,ta ga invitation ɗin auren Auwab,shine ko wani Auwab ɗin dabam, Shukra ba tayi mata musu ba ta amsa sannan ta kashe wayar

Mintuna goma sha biyu Shukra ta ɗauka kafin ta kira ta,a waɗannan mintunan Inaaya ji tayi kamar shekaru goma sha biyu ne,sai imagining take yi idan wannan magana gaskiya ce ya zata yi?ji tayi numfashin ta ya na ƙoƙarin fizga,kanta sai juyawa yake yi,haka ta tashi ta kama zaga parlourn

Bata san irin son da take yiwa Auwab ba,bata san iya adadin kishin shi da take yi ba,bata san yadda zata yi ba idan ya tabbata Auwab ne zai ƙara aure

Shukra ta na kiran ta ta ɗaga,ita kanta Shukra sai da ta jinjina baƙin kishi irin na aminiyar ta ta,matar da idan aka kira ta sai ta gama wulaƙanci take ɗagawa,amma ta yakice,cikin kwantar da murya ta ce"Aminiya da buƙatar kizo fa,don dole ake so ayi wa mijin ki amma yace shi bazai iya rayuwa da kowacce mace ba sai ke!"

"What!wanne azzalumin ne yake so ya rusa min farin ciki na?waye yake son kai kan shi ga dana sani?don wallahi babu yadda za'a yi na zuba idanu a ga baya na"a cewar Inaaya cikin ɗaga murya tana miƙewa tsaye

"Wai iyayen shi ne,amma ki zo don dakatar da lamarin"Inaaya bata sake magana ba ta kashe wayar ta shige ɗakin ta da sauri sauri ta shirya cikin riga da wando ta ɗora jacket akai,ta ɗora ɗan ƙaramin mayafi da sneakers ta dauki passport ɗinta da ƙananun abubuwan ta ta zuba a ƴar ƙaramar jaka ta fice daga gidan

Allah ya taimake ta awa ɗaya da ƴan mintuna suka rage wa jirgin da zai tashi zuwa Nigeria,don haka ta zauna jira,duk da wannan jiran ji tayi kamar tana jiran shekaru ɗari

Ko a jirgin ma ji ta yi bata taɓa doguwar tafiya ba irin wannan,tashin hankali da bala'in da take jin kanta a ciki ba zai misaltu ba,fatan ta dai Allah ya bata ikon dakatar da auren nan kafin lokaci ya ƙare


BRUNSWICK, MELBOURNE, AUSTRALIA


Yau kwana goma kenan da dawowar fadeela Australia, Azad bai yi mamakin ganin ta ba saboda Haidar ya gaya masa komai ya wakana a waya,shima bai ji haushin daddyn ba don ya san haka ne ya dace da shi,amma still bai chanja tsarin zaman su ba kafin su bar ƙasar

Yau kam fadeela ta gaji,don haka ya na dawowa daga aiki ko sallamar shi bata amsa ba,shima bai damu ba ya shige ɗakin shi,ta bishi da kallo zuciyar ta cike da haushi da takaicin shariyar Azad

Ya na shiga ɗakin shi ya ajiye brief case ya rage kayan shi ya saka bathrobe ya shiga wanka,ya na fitowa ya ganta a tsaye tana girgiza da alamun rashin mutunci,gaba ɗaya ran ta a matuƙar ɓace yake

Baiyi mata kallo biyu ba ya wuce ya fara shirya wa,a fusace ta ƙarasa kusa dashi ta ce "Azad yau dai ayi ta ya ƙare,na baka haƙuri,na jure wulaƙanci da cin mutuncin ka kan kuskure ɗaya,duk abinda ya dace na yi maka na yi amma kana wulaƙanta ni,yau dai ayi ta ta ƙare,ka gaya min me kake nufi dani?"

A kaikaice ya juya ya kalle ta ya ce"pardon?"

"Me kake nufi da jingine ni kamar wata baiwa?bani da amfani a komai,baka da lokaci na, baka tuntuɓa ta,zaman aure muke yi ko zaman doya da manja?"

Shiru yayi kamar bai ji ta ba,ta fashe da kuka cikin baƙin ciki cikin tsananin ɓacin rai da gushewar hankali take faɗin "matsiyaci!mugu azzalumi!! saboda zalunci ka zo ka jingine ni ka cigaba da harkokin ka kamar ka bar wata wadda bata da rai?to yanzu ayi ta ta ƙare,ka gaya min matsayi na a gidan nan!'

Shirun nan na shi da ya saba ya yi mata ya na ƙarasa shafawa jikin shi lotion,ya na gamawa kuma ya kewaye ta ya wuce closet ɗin shi

Ta gaban ta ya zo ya wuce abin shi,ko kallon ta bai yi ba,yayi kyau cikin T-shirt fara da wando Blue

Zuciya ta ɗebi fadeela ta shaƙe masa wuyan riga,da matuƙar sauri ya cire hannun ta daga wuyan shi,ta tsare hanya ta na faɗin "to wallahi sai ka gaya min menene matsayar auren mu,idan ba haka ba kuma na kashe ka na kashe kaina,idan ya so sai a kai mu tare!"

Azad ya dube ta cikin idanu yace"shikenan? matsayar auren kike so ki sani ko akwai wani abu dabam?"ta na girgiza tace"eh!matsayar auren nake so na sani!!"

Ya ce "alright!to kije na sake ki,yanzu hankalin ki ya kwanta?"ya faɗa idanun shi fes cikin nashi

Har wani taga-taga ta yi kamar z ata faɗi saboda tsabar yadda maganar ta dake ta,wai Azad ya sake ta,kamar an tunzura ta kuma ta kurma ihu ta na faɗin"Azad!saki!!saki kuma!!! haba Azad!wai abu ba ya wucewa a wajen ka ne,don Allah Azad ka yi haƙuri,ya za ka rabu da ni?ka san ina son ka,don girman Allah ka yi haƙuri "ta zube a gaban shi ta kama ƙafafuwan shi cikin gunjin kuka take faɗin"na yi maka alƙawarin na daina duk abinda ba ka so,ka yafe min Azad! wayyo Allah zan mutu,don Allah ka janye sakin nan,ka rufa min asiri na roƙe ka"shi dai Azad ya tsallake ta ya fice ya bar mata ɗakin ta na ta ihun kuka cike da tashin hankali


HAƊEJIA ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA


Gaban shi ne ya yanke ya faɗi ganin mai kiran,ya rinƙa bin sunan da kallo kafin ya yi jarumtar ɗaga wayar,cikin sanyin murya ya ce "wife!"

Ji yayi ta fashe da matsanancin kuka,a gigice ya miƙe ya na faɗin "ya dai wife?me ya faru ne?me ya same ki?don Allah ki yi shiru ki gaya min, Please kar ki tsinka min zuciya na roƙe ki da girman Allah"

Da ƙyar ta haɗiye kukan da take yi tace"Are you available now?"

Cikin sauri yace"yeah!"

"Na dawo gidan mu,ina son ganin ka yanzu,nan da ten minutes "

"Consider it done wife!gani nan"bata sake magana ba ta kashe wayar,shi kuma ya miƙe cikin sauri ya sauya kaya daga jallabiyar da ke jikin shi zuwa riga da wando na ƙananan kaya,ya ɗora wa lallausan baƙin gashin shi da bai cika ganin mai aski ba p-cap ɗin shi ta ƙa'ida,ya zura takalmi ya fito da sassarfa ya nufi parking space

A can ya haɗu da Sulaiman da shigowar shi kenan,sanye da baƙaƙen suit,ya fito a asalin ɗan sandan farin kaya abin shi,da idanu yabi Auwab ganin kamar bai lura dashi ba

Ganin da gaske zai fice ya bar shi ya sanya shi faɗin "hey engineer!Ina zuwa haka?"ɗaga masa hannu kawai yayi ba tare da ya iya cewa komai ba ya ja motar, sulaiman ya bishi da kallo kafin ya taɓe baki,ya juya ya nufi cikin gidan zuciyar shi fal takaicin yadda nutsatstsen yayan shi,mai kamala da rashin hayaniya ya susuce don ya auri waccan yarinyar

Shi kuwa Auwab kai tsaye Alu evenue ya nufa,ya na isa a bakin gate ya yi parking motar shi ya ƙwanƙwasa ƙaramin gate,mai gadi ya na ganin shi ya yi azamar buɗe masa ƙofa,ya yi saurin shiga ya na sake kiran Inaaya da taƙi ɗaga masa waya


Waje ya samu ya na cigaba da kiran ta,wanda a ɓangaren ta ta na kallon dukkan kiran da yake mata,don suna zaune ne sun saka wayar a gaba ita da Shukra da ta bata shawarar yadda zata yi, don mumyn ta faɗa ta yi ta yi ita ƴar ta tafi karfin ayi mata kishiya,ko ita duk girman ta ba'a yi mata kishiya ba ballantana ƴar ta

Hankalin Auwab idan ya yi dubu ya tashi,ya rubuta mata gajeren saƙo da rokon don Allah ta ɗaga masa waya,don ya san zuwa yanzu ta ji abinda yake faruwa, still Babu amsa,cikin damuwa ya cigaba da kiran wayar tata,cikin Sa'a sai ya ji an ɗaga


A ƙarshe dai auren ɗan Gwal ya sheƙa🥹 Auwab kam ana cikin tsaka mai wuya 🥲


Kada dai a manta VIP group #300 ne kacal

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️ Nusy bee

*Young talented writers association (YOTA)*


Page 45

Ta na ɗagawa tabyi shiru,bai damu ba,cikin kiɗima ya ce "wife ga ni na zo,ina compound,don girman Allah ki zo ki same ni"

"Ka shigo parlourn mu"abinda ta ce kenan kawai ta kashe wayar

Shiru ya yi ya na tunanin ta inda zai fara shiga cikin gidan,amma tuna wacece Inaaya idan ta yi fushi bai san sanda ya nufi cikin gidan da sassarfa ba

Mai aikin gidan ce ta yi masa iso zuwa babban parlourn cikin gidan,ya ce mata ta kira masa Inaaya,ta amsa da girmamawa

A maimakon Inaaya sai ga mahaifiyar ta,cikin ladabi ya rissina ya na gaishe ta,amma sai ta yi kicin kicin ta na faɗin "y ayi maka kyau Auwab!wato ka aurar min yarinya shine tun bata wani gama zama ƴar gida ba za ka zage kayi mata kishiya saboda cin mutunci!

Yanzu in banda rashin adalci da son zuciya, su iyayen naka da suka zuga ka ka yiwa ƴa ta kishiya,ba su biyu kawai suke ba?to in dai kana son kanka da arziƙi ka gaggauta ajiye wata maganar ƙarin aure ko ka sakar min yarinya"ta na kaiwa nan ta juya ta bar wajen rai a ɓace

Da kallo ya bi ta ya na jinjina abin a ranshi,kafin ya yi wani tunani sai ga inaaya ta shigo fuska a ɗaure

Da bala'in sauri ya miƙe ya riƙe ta ta na tutturjewa,ya durƙusa har ƙasa ya na faɗin"don Allah wife ki saurare ni!kin san ke ce farin ciki na!ke ce walwala ta,ke ce kwanciyar hankali na,idan kika yi fushi da ni ji nake zan iya mutuwa,don girman Allah ki taimaka min ki sauko muyi magana "

Waje ta samu ta zauna fuska a ɗaure, shima ya zauna kusa da ita,cikin isa ta ce"na ji,amma babu wata magana da zamu yi, kawai zan baka sharaɗi akan yarinyar,idan ka amince to,akasin haka kuma sai ka nemi wata matar ko ka zauna da ita "cikin zumuɗi ya ce"na amince ma,menene sharaɗin?"

Cikin isa ta kora masa bayani da jawabin da Shukra ta kora mata,babu musu ya ce"na amince wife!dama Nima niyya ta bata wuce haka ba,na amince "

A ranar dai sun rabu gashi gashi nan, Auwab dai yaga ta kanshi kan wannan ƙaddararren auren a cewar shi

Ita kuwa khairi kashe wayar ta ta yi,don a jikin ta take ji ta rabu da su Amra kenan,ta koma sai bin mutane da kallo take yi,har yanzu maganganun Auwab basu daina rotating akan ta ba,kuma ta rasa takaimaimai dalilin da yasa abin ya dame ta,ita dai feena ta na ƙoƙarin jan ta a jiki duk da mum bata son hakan,amma mai yiwa feenan gyaran jiki ita ce take yiwa khairi, ba tare da mum ta san feena ce ta biya kuɗin ba


BRUNSWICK, MELBOURNE, AUSTRALIA


Ya na zaune a gefen gadon shi,waya ce hannun shi ya ƙura wa hoton khairi idanu,a wani lokaci ne ya yi mata hoton a gidan su tana ta faman zuba masa shiririta,bata kula ma ya yi mata ba,ta yi kyau sosai cikin hijabi ɗinkin jilbab onion color,ta washe haƙoran ta ta na murmushi,sun fito farare tas dasu,ƴar wushirya ta ratsa haƙoran ta na sama,ta yi murmushi sosai ƴan ƙananun dimples ɗin ta sun fito a both kumatun,ta na ta zuba ba ta san ma ya yi mata hoton ba,ya na daga cikin ire-iren hotunan da yake yi mata, waɗanda sune rabi da quarter na hotunan dake wayar shi

Da sallama fadeela ta shigo ɗakin murya a sanyaye,ya amsa babu yabo babu fallasa,ta ƙaraso ta nemi waje ta zauna,ya ɗago ya zuba mata idanu yana jiran abinda zata ce masa

Ta rame ta fice daga hayyacin ta, saboda tsabar tashin hankali da damuwa,kullum a cikin bin shi take ko zai mayar da ita amma ko lokaci baya bata,tsawon sati kenan da sakin,sai fa yau

Cikin sanyin murya ta ce "Azad mene ne laifi na?zubar da ciki ko?to na yi alƙawari zan haifa maka yara ko dubu ne idan kana so

Sai kuma khairi ko?to ba ni da ja,ka auro ta ka kawo ta, wallahi zan yi mata biyayya ma,in sha Allah zan rinƙa tafiyar da rayuwa ta wajen yi maka biyayya,ka yarda na yi nadama akan abinda na aikata,ko Allah ma muna masa laifi ya yafe mana"ta durƙusa gaban shi ta haɗe hannayen ta,cikin zubar hawaye tace"don Allah Azad!ka taimake ni!idan ka sake ni ban san yadda zan yi ba,zaman da nayi a gida da ka kaini ji na yi kamar zan mutu saboda damuwa,ban san yadda zan yi rayuwa babu kai ba,don Allah, wallahi Azad ba zan iya misalta irin son da nake maka ba"

Ɗauke kan shi ya yi,ta ba shi tausayi,amma hakan ba zai hana ya rabu da ita ba,cikin kwantar da murya ya ce"Fadeela zauna mu yi magana "babu musu ta zauna sosai ta na goge hawayen idanun ta da gefen hijabin jikin ta

Ya dube ta sosai ya ce"Fadeela you know that, lokacin da aka ɗaura mana aure babu soyayya a tsakanin mu"da sauri ta katse shi ta na faɗin"wallahi ina son ka tuntuni Azad,ban taɓa son wani makamanciyar soyayyar da na yi maka ba"

Ya gyara zama ya na faɗin"okay!na fahimta,but I'm sorry to say ni bana son ki,asalima mace ɗaya nake so wadda zan iya rayuwar aure da ita a duk faɗin duniyar nan,ita ce Ummul khairi wadda kika sani da khairi,amma kin san meyasa na amshi auren ki ko da wasa ban bawa mahaifiya ta excuse ba?"ta girgiza kai a sanyaye ta na kallon shi,bai damu ba ya ɗora

"Saboda soyayyar da nake yi wa khairi, akan na samu Khairi zan iya yin komai in dai bai saɓawa shari'ar addini na ba,zan iya sadaukar da dukkan farin ciki na akan na same ta,maybe kina da burika da yawa, waɗanda kike fatan cikawa, ni kuma buri ɗaya tak gare ni,shine na mallaki khairi,sai dai unfortunately shigowar ki cikin rayuwa ta ya ɓata komai"ya ƙarasa faɗa Muryar shi tna rawa,gaba ɗaya rauni ya bayyana a tare da shi, idanun shi suka kaɗa suka yi jajur

Ya yi shiru ya na ƙoƙarin daidaita nutsuwar shi, Fadeela kam kuka take yi kamar ranta zai fita,Azad bai damu ba ya ci gaba"dama mahaifiya ta bata son ta,na ɗauki waccan ƙiyayyar a rashin fahimta,wadda nake fatan na chanja ta sannu a hankali,amma sai kika ɓata wannan shirin nawa,kika ɓata khairi a wajen mum,a dalilin ki mum ta furta min kalmar da ban taɓa tunanin za ta furta wa ko da kare ba ma ballantana ni ɗan ta da duniya ta shaida tafi so,wato zata tsine min

A taƙaice dai, Fadeela kin taka muhimmiyar rawa wajen tarwatewar farin ciki na, I'm sorry to say ba zan iya cigaba da zama dake ba,ba zai yiwu kina matsayin mata ta ba kuma na kasa daina jin haushin ki,tabbas naji zafin zubar min da ciki da kika yi saboda ina matuƙar son ganin ɗa na nima,amma zafin zubar min da cikin bai kai ko da 1% na zafin raba ni da khairi da kika yi ba,don haka ina neman yafiyar ki idan nayi offending ɗinki, Allah ya baki Wanda yafi ni"

Kuka take yi sosai cikin tsananin tashin hankali, zuwa yanzu ta tabbatar ta rasa Azad,ya ɗauke kanshi,a hankali ya ce"ki shirya,gobe da safe zamu tashi zuwa Nigeria,kin san za'a yi bikin ƙanne na"bata ba shi amsa ba ta fice daga ɗakin tana gursheƙen kuka

Ko da suka isa Nigeria har gida ya kai ta sannan ya wuce gida

Ya na shiga motar da aka dawo da khairi ta na shigo wa,yau ta dawo daga albasu inda ta je ta yi kwana uku ta na zaga dangi,take ya ji zuciyar shi ta karye,amma hakan bai hana shi tunkarar ta ba ya na murmushi

Ta na fito wa daga mota ta gan shi,ta bude baki zata yi magana sai ta fashe da kuka, da sauri ya ƙarasa gaban ta ya na faɗin"I'm sorry!me ya faru? Please khairi,don Allah ki daina kukan nan"

"Shine ka yi tafiyar ka ko tuna wa dani ba kayi ba,gashi idan na kira ka ba ya shiga"ya sauke ajiyar zuciya a ɓoye ya ce"I'm sorry,yanzu dai ki shiga ki huta,anjuma sai mu haɗu a garden mu yi hira,kin ji?"ta ɗaga kai,ya ce"good girl!now ki wuce ki je ki huta kin ji?"babu musu ta juya ta wuce part ɗin aunty Naja

Ranar juma'a bayan an sauko da sallar juma'a aka shaida ɗaurin auren Safeena Umar albasu,da angon ta saifullahi mukhtar,sai kuma na Auwab Usman albasu da na amaryar shi Ummul khairi Abubakar albasu,su kuma su Sulaiman dama Maiduguri suka wuce, inda aka ɗaura auren shi da amaryar shi Amina Ibrahim wato mifra,sai Safiyya (Amra) da angon ta khaleel Ishaq

Wannan rana ta yi albarka sosai,sai dai ran Abba ya ɓaci da ya tabbatar da cewa Auwab bai halarci ɗaurin auren ba, saboda hakan ma ya na ɗaya daga cikin shirin inaaya da Shukra,kuma ko da ya kira wayar shi ba ta shiga,a lokacin ma ya na can tare da Inaaya a ɗakin hotel da ta saka ya kama musu,sai dai shi ɗin a zaune yake jugum zuciyar shi cike da damuwa,yayin da ita kuma Inaaya wayar ta take ta dannawa abin ta

Awanni kaɗan da ɗaurin auren su Sulaiman suka dawo da amarya mifra,a cikin gidan Daddy zai zauna a part ɗin shi,don haka already an gyara komai anyi furnishing part ɗin da tsadaddun furnitures

Basu fi hour ɗaya da isowa ba suma su Amra suka tafi Maiduguri,sai kuka take yi,ita kanta Ammi sai da tayi kuka

Duk wannan gwagwarmayar da ake sha Auwab baya gidan,asalima bai dawo ba sai washe gari da yamma,daga Abba har Ammi babu wanda ya ce masa uffan

Ita dai amarya khairi ranar ɗaurin auren ma ɗakin ta ta shige ta yi kwanciyar ta,ta sha kuka sosai da aka tabbatar mata da ɗaurin auren ta da Auwab, washegari kuma bayan ƴan kai amarya sun watse ta yi kwanciyar ta ta sha baccin gajiya,dama ita ko event daya bata yi ba,to dama ba ƙawaye ne da ita ba

Sai bayan kwana biyu Auwab ya zo ɗaukar ta,su uku ne kawai za su tafi,daga shi sai inaaya,wadda tayi ziyarar farko gidan sirikai a lokacin,kuma ko a fuska bata nuna wata matsala ba,ta girmama su Ammi sosai,Ammi sai tausayin ta take ta ji kasancewar ta san zafin kishi

Sai da aka fara kawo khairi gidan Ammi sannan suka shirya don bin jirgin ƙarfe bakwai na yamma,sulaiman ne ya kai su airport,inaaya sai ƙarewa khairi kallo take a kaikaice, kasancewar dukan su a baya suka zauna,ta ji sanyi a ranta sosai ganin cewa tafi khairin kyau

Ita kam khairi abinda ya dame ta dabam, tunanin yadda za ta zauna da wannan mutumin a matsayin miji take yi,duk sanda ta tuna da hakan ma sai ta ji faɗuwar gaba ta tashin hankali

Bayan Sulaiman ya sauke su ya yi musu sallama ya tafi,shi kuma Auwab ya ja hannun matar shi suka shiga lounge,khairi ta bi su a baya kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki

Duk da bata iya ɗaura seatbelt ba,asalima ita bata taɓa shiga jirgi ba Auwab sam bai yi tunanin taimaka mata ba,asalima sun zauna a wasu seats nesa da ita ne,sai wata mata maƙwabciyar ta ta roƙa ta taimaka mata,ta sunkuyar da kai idanun ta na tara hawaye

Ita dai bata ga sauki a tare da waɗannan bayin Allan ba,bata ga soyayya daga mijin da ake kira nata ba,ko ma dai menene,ita dai gata a hanyar gidan shi


To fa!ga khairi ga Auwab ga inaaya!wannan zama fa sai kun biyo Nusy bee don jin yadda zata kaya


Kada dai a manta VIP group #300 ne kacal

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️ Nusy bee
*Young talented writers association (YOTA)*

Page 46

Ƙarfe biyar na yamma agogon ƙasar US suka sauka a Massachusetts airport,sun riga khairi fita saboda ta na bayan su ne,cikin sanyin jiki ta janyo ɗan akwatin kayan ta,don bata taho da kaya da yawa ba,ta fito daga cikin jirgin ta na ta kalle kalle

Can nesa ta hango su ya na janye da jakar kayan su,da alamu ma kamar sun manta da ita,sai hirar su suke cike da farin ciki da soyayyar juna,ganin suna daf da ɓace wa ganin ta ya sa ta ƙara sauri ta cin musu

Taxi Auwab ya ɗaukar musu,a gadarance Inaaya take ba wa khairi umarnin ta zauna a gaba kar ta takura musu,babu musu ta shiga gaban ta zauna,su kuma suka shige baya

Har suka isa gida khairi sai kalle kalle take yi,ƙasar ta burge ta sosai, ko'ina kyau yake yi mata

A bakin gate suka tsaya, Auwab ya sallami cab ɗin suka fito,yanzun ma shine ya ɗauki kayan su, inaaya ta rungume shi,khairi ta bi su a baya janye da akwatin ta tana ta rarraba idanu

Suna shiga main parlour na gidan inaaya ta juyo tana kallon ta a raine,ta ce"ga ɗakin ki can"ta nuna mata shi da hannu,ta ci gaba"ki zauna a can ki jira ni kafin na sallami miji na"babu musu khairi ta ja akwatin ta ta nufi ɗakin da Inaaya ta nuna mata,ita kuma ta ja hannun mijin ta suka nufi bedroom ɗin su

Tana nan zuwa a ɗakin ta yi tsumu,har wajen ƙarfe bakwai na dare,ga yunwa ta na damun ta, ta janyo wayar ta a sanyaye ta na duba wa,ta karya asalin layin ta, saboda so take ta manta da Queen's College ma da duk abinda ya dangance ta saboda ta na jin ciwon ɗauke ta da aka yi batare da ta cimma ko da hanyar burin ta ba,amma har yanzu akwai hotunan ta da videos ita da aminan ta na amana, Amra sadeeq da Nabeela Saleh,akwai waƙoƙin da ta sani a dalilin su,kuma ta na son su sosai,don su suka koya mata nishaɗi,sun ƙware sosai da kunna waƙa a waya su yi ta rawa,tun ba ta iya wa har ta koya,har ta zo ta fi su iyawa ma

Murmushi ta yi sosai lokacin da ta yi playing wani video ɗin su ita da su Nabeela,sun ƙure waƙar romantic ta korede Bello da tiwa Savage sai rawa suke yi suna bin waƙar, Amra ce ta yi musu video ɗin da wayar khairi ɗin,ta na haska kan ta ta na hasko su,duk wadda aka haska sai ta ɗaga hannu ta yi ƴar rawa ta na murmushi, video ɗin har ya fara shagaltar da ita ta manta wa da halin da take ciki na fargaba

Muryar su Auwab da ta ji suna hira suna dariya cike da soyayya ne ya sa ta yi saurin kashe wayar ta mayar da ita jaka,ta sake takurewa tana zazzare idanu

Shigowa suka yi kai tsaye ba tare da sun yi sallama ba,kallo ɗaya ta yi musu ta kawar da kai cike da kunya,don irin shigar da ke cikin su su duka,ita Inaaya riga ce wadda bata fi rabin cikin ta ba,sai wani ɗan iskan gajeren wando da ko rabin cinya bai kai ba,dogon baƙin gashin ta da yasha gyara ta raba shi biyu ta ɗaure ta sake shi gefe da gefen kafaɗar ta,shi kuma Auwab singlet ce a jikin shi da short neaker shima,gaba ɗaya siffar mazantaka da Allah yayi masa ta bayyana sosai,kuma sun rungume juna kamar za su mayar da juna ciki

Gyara zama ta yi sosai ta na gyara mayafin ta,ta sunkuyar da kai,suka ƙaraso suka zauna a sofa ɗin dake ɗakin suna fuskantar ta

Inaaya ta kalle ta tun daga sama har ƙasa, yarinya ce sosai,don bata wuce 15-16 years ba,duk da cewa yana da garin jiki,kuma baƙa ce duk da ba can ba,sai dai tana da sexy eyes da dogon hanci da cikar gashin gira da zara zaran gashin idanu,sai madaidaicin baki da ƴar doguwar haɓa, inaaya ta kyaɓe baki,don ko da ace ta na da kyan ma ta san ko ƙafar ta bata kama ba

Kallon ta ta yi ta na yatsina fuska ta ce"what's your name?"

"Ki yi mata Hausa,bai zama lallai ta ji abin da kika ce ba"a cewar Auwab ya na sake rungume ta,har yanzu bai yi wa khairi kallo biyu ba

Maganar shi tayi wa khairi zafi,kafin ta kai ga magana Inaaya ta ce"oh na manta fa,ance ƴar ƙauye ce ko?cewa na yi yaya sunan ki?"

Banza khairi ta yi da su,sai da inaaya ta maimaita tambayar,cikin fushi khairi ta ce"ask your husband!"

Da wani irin mamaki Auwab ya ɗago ya na kallon ta,ba wai mamakin shi turancin da ya ji ta yi ba,don ya san ta yi makaranta,mamakin shi irin amsar da ta bayar,kuma har yanzu kan ta a ƙasa,babu wanda ta sake ɗagowa ta kalla,cikin mamaki da haushi inaaya ta ce"ke!dama an gaya min baki da kunya,rashin kunyar za kiyi min?da ki ke cewa na tambayi miji na an gaya miki yana da lokacin ki?banza ƙazama,baƙauyiya,idan kika ce irin wannan rashin kunyar za kiyi a gidan nan wahala za ki sha wallahi"ita dai khairi bata sake magana ba idanun ta na wani wajen dabam

Inaaya ta ja tsaki tace"koda yake kar Allah yasa ki faɗi sunan ma,bana buƙatar ji,daga yau ƴar ƙauye zan rinƙa kiran ki,dama zuwa na yi na gaya miki dalilin da ya sa miji na ya yarda ya auri bagidajiya irin ki,ba ni da mai aiki ne, shi yasa na yarda ya auro ki,daga yau gyaran gidan nan,kama daga shara,wanke wanke da mopping da sauran ayyuka da girki duk ke za ki rinƙa yi,idan akwai aike akwai driver za ku tafi tare da shi kije kuyi cefane,ina zuwa makaranta,miji na kuma ya na wuni a wajen aiki,don haka za ki rinƙa kular mana da gida,ba kyauta za kiyi ba,albashi zamu yanka miki daidai da ke,ba zan maimaita abinda na faɗa ba,idan kika kuskure ko ki kayi wasa da aikin ki hukunci mai tsanani zai biyo baya,ya rage naki ki kiyaye ko kiyi sakaci"ta na kaiwa nan ta miƙe tsaye,shima Auwab ya miƙe suka fice daga ɗakin,sai da suka fita sannan khairi ta ɗago kai ta na kallon hanyar da suka biyo hawaye ya na zubo mata


Yanzu zamu waiwaya baya don jin su wanene waɗannan AHALI

WAIWAYE.........
(adon tafiya)

Malam Sa'idu haifaffen garin albasu ne,kuma mazaunin garin,mutumin kirki ne mai iya mu'amala da mutane,matar shi ɗaya safiya,wadda yaranta suke kiran ta inna,mutan gari kuma suke kiran ta da sabuwa,masifaffiyar mace ce wadda bata barin ko ta kwana tun zamanin ƙuruciya,saɓanin mijin ta da wani lokacin duk rashin mutunci da za'ayi masa ko hayaniya baya ɗaga kai ya kalli mutum saboda tsananin haƙurin shi,kuma ya sha yi wa Sabuwa magana akan ta rage wannan zafin ran,shima dai ba koyaushe take ƙyale shi ba

Bayan sabuwa malam Sa'idu ya auri mata har uku,dukkan su basa zama saboda sabuwa ta tsani kishiya,kuma bata jurar zama da kishiya,ko dai bala'in ta ya fitar da kishiya ko kuma ta yi mata asiri ta bar gidan

Yaran ta biyar ta haifa a gidan,Garba ne babba,babu abinda ya bari na halayyar mahaifin shi,mutum mai tsananin haƙuri da neman na kai,bayan shi sai Usman,sai Umar,sai kamilu,sai auta isiyaku

A kaf matan malam Sa'idu banda inna babu wadda ta taɓa haihuwa da shi sai Adama,itace ta haifi Aliyu,wanda suke kira da aliko

Dukkan su su shida sun taso cikin ƙaunar juna,amma inna sabuwa sai da ta san yadda za tayi ta fara raba su da Aliko,a dalilin haka ne Usman ya ce shi makaranta zai tafi(almajiranci)jin haka ya sa shima ƙanin shi Umar ya bi bayan shi,suka nufi garin Maiduguri

A can maimakon almajirancin kawai sai suka haɗa da sana'a,a hankali kuma sai sha'awar karatun boko ya kama su,kowa a cikin su ya nemi makarantar yaƙi da jahilci don su fara karatu mai zurfi

Shi kuwa Garba babu daɗewa da tafiya yayi aure,ya auri matar shi mutuniyar kirki yar garin albasun ce,mai suna suwaiba


Kada dai a manta VIP group #300 ne kacal

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee

*Young talented writers association (YOTA)*

Page 47

Tunda aka kawo Suwaiba kuma sai lamari ya ƙi daɗi,don irin yadda take saka kishiyoyin ta a gaba haka ta saka ta,ita ce take yi mata ayyukan gida,ita ke yi mata sirfe da take yi na kuɗi,wankau,da sauran su,kuma sisin kwabo ba ta bata,sai tarin zagi da tsinuwa da take sha

Suwaiba akwai haƙuri,ba ta taɓa ɗaga kai ta kalle ta ba, Malam Sa'idu ne mai yin faɗa akan hakan,duk da haka Sabuwa ba ta saurara mata,a cewar ta ɗanta take aure,dole ta bauta mata

Sai kuma wata sabuwar matsalar,shekaru biyar da auren Garba da Suwaiba amma babu ko ɓatan wata,babu kalar gori,habaici, baƙar magana da Suwaiba ba ta sha a wajen inna sabuwa,amma da yake mai tsananin haƙuri ce bata ko ɗaga kai ta kalle ta

Babu yadda bata yi da Garba don ya ƙara aure ba amma ya ƙi,ta gaji da masifar da bala'in ta zuba musu idanu

Su kam ɓangaren su Usman abin sai sam barka,don bayan wasu shekaru sun samu sun gama matakin secondary,sun rubuta SSCE da JAMB,kuma alhamdulillahi sun yi nasara,kai tsaye suka wuce zuwa jami'a,shi dai Umar kano ya dawo jami'ar Bayero in da ya fara karanta doka (law)

Shi kuma Usman jarrabawar NDA ya rubuta,cikin ikon Allah ya haye,ya fara karatun shi a matsayin soja

A shekarar Umar ta ƙarshe a makaranta ya haɗu da Salma,a lokacin ya na zaune ya na karatun exam ita kuma ta shigo ta na neman venue ɗin da zata zana post UTME,da ya yi mata kwatance ya ga baza ta gane ba ya sa da kanshi ya kai ta har venue ɗin,ta ji daɗi sosai ta yi ta masa godiya,ta shige shima ya koma

Bayan ƴan sati biyu suka sake haɗuwa,ita ta fara nuna ta gane shi,shima bai ƙi ta ta ta ba don ya ji daɗin yadda ta yi masa,ta girmama shi sosai

A hankali suka saba,ta na yawan zuwa duk da lokacin fara lecture ɗin ta bai yi ba,ta shaida masa ita ƴar asalin garin Yola ne Adamawa,amma anan ta na hannun ƙanwar baban ta ne da take aure a nan Kano

Sau uku ya na zuwa gidan ƙanwar baban nata,ya samu tarba mai kyau a gidan sosai,daga baya dai haka ya bar garin zuwa Lagos inda aka yi posting ɗin shi law school

Itama Salma babu daɗewa ta fara ɗaukar lecture ɗin ta inda take karantar business admin

A dalilin Umar Salma ta daina kula kowa,duk da bai furta mata so ba amma ita ta ɗauki kulawar da yake bata a matsayin soyayya,kuma ta na fatan wata rana ya furta mata soyayyar

Shi kam Usman da wata shuwa Arab ya haɗu tun a Maiduguri,waje ɗaya suke neman kuɗi da yayan ta,ta na yawan kai masa abinci ko wani abin buƙatar idan ya nema,a hankali suka saba da Usman har soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakanin su,tun a lokacin ta sha faɗa da ƴan mata idan ta ji ko a labari sun nuna suna son shi

Kusan lokaci ɗaya suka gama karatu, Usman ya fito a matsayin second lieutenant Usman Saeed albasu,yayin da Umar ya fito a cikakken barrister ɗin shi,kuma bai juma da fitowa ba cikin Sa'a ya samu aiki

A cikakkun mutane suka koma albasu,inna sabuwa ta yi matuƙar murna ganin ƴaƴan ta ababen alfaharin ta sun zama wani abu a rayuwa,ta fara rawar kan ai ta samar musu matan aure,amma kowa a cikin su ya katse mata hanzari ta hanyar bata labarin zaɓin da ya yi kuma a inda ya yi

Tabbas ranta bai so ba,amma dai ta karɓa,a lokacin Aliko,Kamilu da Isiyaku duk sun yi aure,kuma Saboda masifar ta,har Isiyaku ya ƙara aure,a cewar ta matar shi ba ta da kunya dole a hukunta ta da kishiya

An yi bikin su Umar lafiya,dukkan su sun samu sukunin rayuwa sosai,har ma sun tallafawa ƴan uwan su,har a wannan lokacin Suwaiba bata taɓa ko da ɓatan wata ba,sau biyu inna sabuwa ta na matsawa Garba yin aure,amma matan ba sa zama saboda bala'in da suke sha a wajen ta,kuma a cewar su bautar aure suka zo ba bautar sirika ba

Shekara ɗaya da auren su Usman Allah yayiwa malam Sa'idu rasuwa,mutuwar ta girgiza su sosai,duk sun zo gaisuwa har da matan su,bayan rasuwar ne da kwana tara matar Umar ta haihu aka mayar da sunan malam Sa'idu,amma mahaifiyar shi take kiran shi AZAD

Har a lokacin Raheena matar Usman ba tayi ko ɓatan wata ba,ga ta da masifar son yara,a da dai lafiya ƙalau za ta aika gidan faccalar ta ta a ɗauko mata Azad,ta na matuƙar son yaron sosai,amma wani zuwa da su kayi albasu ya tarwatsa komai


Inna sabuwa ce ganin irin kulawar da Raheena ke yiwa Azad take tambayar su"wai wacece uwar tashi a cikin ku ne?"

Salma ta yi ƴar dariya, Raheena ta nuna Salma ta na murmushi,inna sabuwa ta ce"au Allah?kuma ƴan birnin na ga alamu ku ma sakarkaru ne ko?yo in banda sakarci Kya ɗauki ɗan ki ɗaya tilo ki damƙawa faccala?salon ta yi masa wani ƙulumboton don ita bata haihuwa?"gaban Raheena ya buga,ta ɗaga kai ta na kallon su,Harira,wadda ta kasance ɗaya daga cikin matan gidan ne ta yi karaf ta ce "wallahi kuwa inna,don faccala ai tafi kishiya, musamman da ta ga ba ta haihuwa,tuni za'a yi wa yaron wani ƙulumboton a kashe shi"to tun daga lokacin Salma ta tsorata,ta yiwa Raheena iyaka da Azad

Raheena ta yi kuka sosai, musamman a gaban ta su Salma za su zauna suna hira suna faɗin ai shuwa mugaye ne,akwai baƙin asiri,sannan kuma ga su da hassada,ita dai bata ga ta inda ta yiwa Salma wani abu mai zafi ba da har ta sako ta a gaba haka ta

Raheena ta rayu tsawon shekaru biyu bayan haihuwar Azad a haka,ta na shiga dangi za'a fara yar musu da habaici ita da Suwaiba,sai dai su sha kukan su su haƙura

Cikin hukuncin Allah sai ga ciki a jikin Raheena,ta yi murna tayi farin ciki, musamman da taje albasu ta samu Suwaiba itama da ciki,sun yi murna ƙwarai,sun yi farin ciki,sun tuna baya sun yi kuka tare

Sai dai cikin Suwaiba ya zo mata da matsala,ta fara naƙuda tun kafin lokacin haihuwar ta,ƙarshe dai haka ta rasu a wajen haihuwar da ko samu ta haihun ba tayi ba

Tabbas Garba ya shiga tashin hankalin rasuwar Suwaiba,har ɗan ƙaramin hauka ya yi,daga baya kuma Allah ya saka masa dangana ya haƙura

Raheena fa ta tsorata,a dalilin haka har jinin ta sai da ya hau,amma Usman ya yi ta kwantar mata da hankali,a ƙarshe dai Allah ya sauke ta lafiya ta haifi kyakkyawan yaron ta mai tsananin kama da ita sak

Sun yi matuƙar murna sosai,daga lokacin bakin masu gori ya mutu,ranar suna Usman ya bata zaɓi,da kanta ta sanya masa suna MUHAMMAD AUWAB

Wani abin Allah watan Auwab uku Raheena ta ƙara samun wani cikin,bata sanar wa kowa ba baya ga mijin ta,haka suka yi ta rainon abin su har ya isa haihuwa

Shima dai baby boy suka samu,Usman ya saka masa suna SULAIMAN

Ganin haka ya sa Salma ta sake jan ɗanta Azad a jiki sosai,wanda a yanzu ya shiga shekara ta huɗu,tana matuƙar ƙaunar yaron,har bata iya ɓoyewa,tana jin shi a ranta fiye da komai nata

Bata sake haihuwa ba ba sai bayan da Azad ya shekara bakwai, lokacin shekarun Auwab huɗu da watanni,shi kuma Sulaiman uku,kuma still ita ma Raheena tun daga kan Sulaiman shiru bata sake haihuwar ba

A wannan karon mace ta samu, Umar ya sanya mata suna BILKISU

daga Bilkisu babu jumawa Salma ta sake haifar Aliyu Haidar, shekara ɗaya da haihuwar Aliyu itama Raheena Allah ya bata ƴa macen,wadda Usman ya saka mata sunan inna wato safiya,amma ake kiran ta da Amra

Babu jumawa Salma ta haifi Muhammad Ma'aruf,daga nan Raheena ta haifi Surayya,sai Salma ta sake haihuwar autar ta mai sunan inna,ake kiran ta da Nusra

Yadda aka haifi Auwab da sulaiman kusan lokaci ɗaya sai suka tashi tamkar ƴan biyu ko aminai, kasancewar kamar su ɗaya ma,sai dai Auwab fari ne ƙal,asalin jinin shuwa,amma Sulaiman yana da ɗan duhun fata,sun tashi kai ɗaya,sun yi tsananin shaƙuwa duk da halayen su ya bambanta


Kar dai a manta VIP group #300 ne kacal


#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee

Page 48

Shi Auwab ya na da sanyin hali,bashi da yawan magana da kwaramniya,akwai shi da haƙuri,sai dai ba shi da son mutane,asalima baya son taro ko yawan shiga sabgar mutane,amma fa akwai shi da kafiya akan ra'ayin shi, ba'a chanja masa ra'ayi,shi kuma Sulaiman saɓanin Auwab mutum ne mai surutu ga fara'a,akwai barkwanci da yawan tsokana,akwai shi da son mutane,kuma ya na da sauƙin kai

Shi kam Azad miskili ne sosai, bai cika shiga sabgar da bata shafe shi ba,amma ya na da matuƙar son ƴan uwa da son taimakawa mutane,abu ɗaya ne raunin shi a rayuwa shine mummyn shi,wadda ba ya haɗa son ta da na kowa a rayuwar shi

A wannan halin ne Garba ya dawo daga Malumfashi jihar Katsina da wata yarinya da ba ta wuce shekara sha biyar ba da sunan matar shi ce,an yi bala'i sosai kafin a tabbatar da maganar shi,kamar marigayiya Suwaiba inna ta so bautar da wannan amarya mai suna HABIBA,sai dai Habiba da baƙin miskilanci da wulaƙanci bar mata aikin ta take yi,kuma duk masifa da jarabar da za tayi mata bata ɗaga kai ta kalle ta

Kaf matan gidan duk da cewa da yawan su sun haife ta shakkar ta suke yi,don babu ruwan ta da sabgar kowa,amma ba'a taɓa ta a kwana lafiya,cikin ruwan sanyi take mayar da raddi,hakan yafi komai baƙantawa inna sabuwa

Cikin hukuncin Allah bayan shekaru biyu da auren sai ga ciki, Garba yayi farin ciki sosai,ya taya ta su kayi ta tattalin abin su

Bayan watanni tara da ƴan kwanaki ta haife ƴar ta mai kama da ita sak,sai dai ta ɗauko duhun fatar baban ta

Ranar suna an sha bala'i sosai, don inna cewa tayi sai dai a saka sunan ta,Garba ya na ta bata haƙuri, Habiba ko a jikin ta,ita bata ɗauki maganar innar da wani muhimmanci ba ma,da kanta ta sanar da mutane sunan yarinyar,sunan da suka zaɓa wa yarinyar tuntuni,wato UMMUL KHAIRI

Ummul khairi ta taso cikin gata da kulawa da soyayya,babu ruwan Habiba da kasancwar ta ƴar fari,kulawa take bata sosai,don haka ta na shan zagi a gidan saboda a cewar su bata da kunya bata da kara,bata ɗaga kai ta kalli kowa,harkar gaban ta kawai take yi

Sai dai wannan tafiyar bata yi nisa ba, don shekarun Ummul khairi,wadda suke kira da Ummiyo huɗu da haihuwa Garba ya yi hatsari ya rasu, Habiba ta shiga tashin hankali irin wanda bata taɓa za ta tsammanin shiga a rayuwar ta ba, ba'a maganar inna Sabuwa da ta yi ta sambatu

A lokacin Ummiyo baiwar Allah ba ta gane komai sai bin mutane da idanu saboda ƙarancin shekarun ta,sam bata gane abinda ya faru ba ballantana ta gane irin rashin da ta yi

Bayan Habiba ta fita takaba inna sabuwa tayi mata tayin auren Umar,don a lokacin sam an daina shiri tsakanin ta da Salma ,don Salma ba ta da haƙuri ko kaɗan,ba ta da kunya,ba ta iya lamuntar kama karyar da inna Sabuwa take yi mata,ba iyaka ta zo garin ba, a'a,ko ita inna Sabuwa ta zo gidan ta bata fasa nuna mata iko,a cewar ta ita ta haifi mijin da take taƙama da shi

Ita kam Habiba kai tsaye ta nuna hakan ba mai yiyuwa bane,don bata da burin sake yin aure a dangin Garba,don tabbas ta ji daɗin zama da mijin ta,amma bayan wannan baza ta iya ɗorar da wani farin ciki a rayuwar auren ta ba,daga wajen sirikar ta zuwa faccalolin ta

Hakan kuwa ya ƙona ran inna Sabuwa,ta na ji ta na gani Habiba ta tattara komai nata don wucewa Malumfashi

Sai dai an yi bala'i sosai akan Ummiyo,wannan karon kam su inna Sabuwa sun yi nasara,ba su raba Ummiyo da Habiba don suna son ta ba,sai dai don inna ta cuzgunawa Habiba,haka Habiba ta bar gidan cikin zubar da hawayen raba ta da gudan jinin ta

Ummiyo ta taso cikin tsangwama da kyara a tsakanin ƴan uwan ta yara,duk a cikin su ita kaɗai ce ba ta zuwa makaranta,kullum babu wanka babu wanki,aikin kenan talla da duk wanda ya ga dama zai ɗora mata babu mai hanawa,bata da magana ko hayaniya tamkar mahaifiyar ta,a haka ta gudanar da rayuwar ta har zuwa lokacin da Usman da Umar suka yanke shawarar ɗauke ta daga garin, Umar ya raine ta, idan ta girma kuma Usman ya aurar da ita ga Auwab babban ɗan shi,ba su sanar da matan su ba sai dai kawai su aiwatar,ita Raheena ta saba da bin ko menene yazo a sannu, saɓanin Salma mai zafi da ƙalubalantar duk abinda ya saɓawa tsarin ta,wanda a dalilin boren da ta so yi ne har inna ta saka Umar ya ƙara aure don dole, don ita inna Sabuwa ta yarda matuƙa da hukunta sirikan ta da umartar mazajen su da ƙara aure,duk da cewa ita bata yarda ta zauna da kishiya ba

Wannan shine tarihi,kuma rayuwar ahalin izuwa yanzu


ASALIN LABARIN

Khairi ta sha kuka sosai,don ta ji haushin wannan wulaƙanci da aka yi mata,ga yunwa ta na ji,haka dai bacci ya sace ta ba tare da ta sani ba

Washegari wajen ƙarfe shida na safe Khairi ta ji saukar ruwan sanyi sosai a jikin ta,a firgice ta farka, kasancewar bata yi bacci da wuri ba ya sa ma ta makara sallar asuba

Inaaya ta gani a tsaye a kanta da kofi a hannun ta,da alamu na ruwan da ta watsa mata ne,sai aika mata da saƙon harara take yi,ta tashi zaune jikin ta ya na rawar sanyi,cikin izza da gadara Inaaya ta fara magana

"Wato shi ɗan ƙauye bai iya samun waje ba ko?kalli,har yanzu bacci kike yi, to maza maza tashi ki shiga kitchen ki fara haɗa mana breakfast,don yau bana son eight ta yi min a gida"

Ko kallon ta Khairi bata sake yi ba ta sauko daga gadon ta nufi banɗaki,cikin fushi Inaaya ta fizgo ta ta ce "ke har kin isa ina yi miki magana ki chanja hanya?wuce ki je ki yi min abinda na saka ki"

A nutse ta kalle ta ta ce"alwala zan yi na yi sallah ne,kin ga ban yi Sallah ba"

"Baza kiyi ba! kin san da sallar kika ƙi tashi kiyi sai da na tashe ki?to ban tashe ki don uzurin ki ba,na tashe ki ne don nawa,don haka wuce kije ki ɗora min girki"

Khairi bata sake kula ta ba ta sake nufar banɗaki,anan Inaaya ta kai ƙarshe ta finciko ta ta fara aika mata da mari,har da haɗa mata da duka ta na faɗin"ke har kin isa na yi miki magana ki manna min hauka,shegiya ƴar ƙauye bagidajiya,jahila"

Tun daga ɗaki Auwab yake jiyo dukan da kukan Khairi,da sauri ya shigo ɗakin ya na tambayar matar shi"wife lafiya?me ya faru haka?"

Ta na huci ta ce"wannan ƴar ƙauyen har ta isa na tashe ta ta wani bani uzuri wai zata yi sallah?idan ta damu da sallar uban wani ya hana ta tashi sai da na tashe ta?"

Auwab ya yi ɗan murmushi ya na kama hannun ta ya ce"give her just some minutes please wife! don't bother yourself yanzu za ta gama"ita khairi tuni ta shige banɗakin ta ma ta na ta kuka

Abinci kusan kala biyar Inaaya ta saka ta yi musu kawai don ta wahalar da ita,kuma suka ci suka ɓata wajen sosai,ita dai Khairi bata ɗaga kai ta kalle su ba ta gyara wajen,bayan wani lokaci suka fito manne da juna kamar yadda suka saba suka fice daga gidan ko kallon ta basu yi ba

Yinin ranar a tsorace ta yi shi,ko mopping da ya kamata ta yi bata yi ba saboda a tsorace take,ta na jin shigowar motar tasu ta fito parlourn da sauri ta na murna,a parlour suka yi kiciɓus Inaaya ta na bin ko'ina da kallo fuska a ɗaure

"Me ya hana ki yin mopping?"ta watsa mata tambaya

Khairi ya gyara tsayuwa ta ce "gaba ɗaya gidan ne yake ba ni tsoro, shiyasa na kasa fitowa daga ɗaki na, shine......."marin da Inaaya ta sauke mata wanda ya sa ta ga wasu taurari suna juyawa a idanun ta ne ya katse bayanin nata,cikin masifa Inaaya take faɗin "lallai duk yadda aka yi da jaki sai ya ci kara,wata tsiyar ce a gidan da za ta kama ki?to idan ma za ki saba ki saba,ba zan fasa school ba,kuma miji na ba zai fasa aiki ba,ya rage naki ki koyi zama ke kaɗai ko ki ci gaba da jin tsoro "ta na kaiwa nan ta kama hannun Auwab ta bangaje Khairi suka wuce ciki suka bar ta da sharar hawaye


Maganar gaskiya Khairi kina ganin wata rayuwar bayan wadda kika baro a baya😥

Kada dai a manta VIP group #300 ne kacal

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️ Nusy bee

*Young talented writers association (YOTA)*

Page 49

Haka Khairi ta yi mopping gidan tabna kuka,bata daɗe da gamawa ba Inaaya ta bata umarnin ɗora girkin dare,ta na gamawa ta jera musu abincin a dinning area ta koma ɗakin ta bayan ta ɗebi nata

Ta na kwance ta na danna waya ta ji an taɓa ƙofar, kasancewar ta na shigowa ta kulle ta ciki,ɗaga kai ta yi ta na bin ƙofar da kallo,jin an fara bugun hauka ya sa ta tafi da sauri ta buɗe

Kamar yadda ta zata, Inaaya ce a tsaye a bakin ƙofar ta na aika mata mugun kallo,ta rissinar da kai ƙasa gaban ta ya na faɗuwa,don mugun tsoron wannan matar take ji

"Wulaƙanci ne ya sa kina ji na ina bugu kika yi min banza?"a cewar Inaaya a fusace

Cikin sanyin murya tace"ki yi haƙuri"Inaaya ta ja tsaki ta ce"sai ki fito,magana zamu yi "ta na faɗin haka ta juya, khairi ta bi bayan ta ta na tafiya kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki

A parlourn ta iske Auwab a zaune da computer a hannun shi, Inaaya ta ƙarasa ta rungume shi,ya ɗago ya na ɗan murmushi ya manna mata kiss a goshi,itama ta manna masa a Kumatu ta na sake shigewa jikin shi,tilas ya ajiye danne-dannen da yake yi a laptop ya mayar da hankali kanta

Khairi ta zauna ta na watsa musu harara a fakaice,a ranta faɗi take "anyi waɗanda suka fi ku fitsara ma,suma sun gaji ballantana ku ƙananun marasa kunya"

"Yauwa!ke ƴar ƙauye!"a cewar Inaaya a gadarance, Khairi bata amsa ba ta ɗaga kai ta na kallon su, Inaaya bata damu ba ta cigaba da bayani

"Kan batun aikin ki ne,na yi Miki bayanin aikin yanzu kuma miji na zai yi miki bayanin kuɗin da zai rinƙa ba ki"

Khairi ta ɗan taɓe baki,haka kawai kalmar 'miji na' da Inaaya ta ambata ta fara yi mata yawo akai,da ƙyar ta iya buɗe baki ta ce"idan da hali kawai a kaini makaranta,ba sai an biya ni kuɗin aikin ba"

Inaaya ta kalli Auwab,ya yi saurin cewa "a kai ta makarantar kawai,kin ga tafi buƙatar karatun fiye da kuɗin"

Inaaya ta taɓe baki ta ce"tashi kije,sai da safe"Khairi ta miƙe ta bar wajen, inaaya ta raka ta da harara

Kafin ta kwanta sai da ta karanta Alqur'ani izfi biyu kamar yadda ta saba tun fara karatun ta a Queen's College,bayan ta gama ta ɗauko wayar ta tana kallon videos ɗin da suka yi da ƙawayen ta,sai a lokacin ta ji nadamar karya layin ta da ta yi, don kewar su ce ta kama ta sosai,amma kallon videos ɗin nasu da suke ta zuba shirme da shiririta ya tafiyar mata da damuwa sosai

Satin ta biyu a gidan ta na rayuwa a matsayin ƴar aiki saɓanin matsayin da ya kawo ta wato matar gida, kasancewar ta na kiyaye dokokin Inaaya yanzu ta rage hantarar ta,kuma ta saba da zama ita kaɗai,asalima saboda rashin kunyar da suke zubawa ba ta sakewa kwata kwata idan suna nan

A lokacin ne Auwab ya yi enrolling Khairi a makaranta,bai yi tsammanin ta wani ja sosai ba,don haka ya yi tsananin mamaki ganin ƙoƙarin ta,an yi mata interview ta haye,don haka aka bata ss1 a science class,kamar yadda ta buƙata

A hanya ya kasa daurewa sai da ya tambaye ta

"Kin yi makaranta ne a garin ku?"

Ta yi masa banza,wai ma bai san ta na ciki dashi bane da zai zo ya na mata wata tambaya?don har yanzu Khairi ta na jin haushin maganar da ya gaggaya mata ana saura sati ɗaya auren su

Shima da farko shiru ya yi yana sauraren ta,sai da ya ga da gaske ba zata bashi amsa ba ya ce"tambayar ki fa nake yi,ko ba kya ji ne?"

"Au!kaima ai ka san babu makaranta a ƙauye,ni ban taɓa zuwa wata makaranta ba,ko ka ga na yi maka kalar mai zuwa makaranta?"kallon ta yayi a kaikaice ya ci gaba da tuƙin shi

Ya ɗan girgiza kai ya ce"bakya son a zauna lafiya na ga alamu,ke kullum daga tsiwa da fitsara sai baƙar magana"

A fusace ta ce"to ai gona ta aka shiga!ina ruwan mutum da ni da zai san hali na idan bai shiga gona ta ba?kowa ya yi harkar gaban shi,a daina shiga harka ta"ta gatsine fuska ta kawar da kai gefe,ya ɗan kalle ta sannan ya taɓe baki ya ci gaba da tuƙin shi

Sati biyu da kai khairi makaranta tafiya ta kama Auwab zuwa Japan,in da zai yi sati biyu,don haka inaaya ta kira khairi ta kora mata warning akan ta kular mata da gida zasu yi tafiya, kasancewar tare za su tafi

Kuka sosai khairi ta yi cike da tashin hankali,don yanzu zai zama ita kaɗai kenan take rayuwa a gidan

Washegari suka bar ƙasar,inda ita kuma khairi ta ci gaba da rayuwa cikin damuwa da rashin makama, zuciyar ta cike da fargaba da taraddadi,duk dare haka take yin tsumu,ta yi bacci a takure,har ma ta fi jin daɗin makarantar da take zuwa sosai akan gidan

Sai ya zamana idan ta tafi makaranta bata son dawowa ma saboda babu kowa a gidan,ta kan tafi gidan su ƙawar ta da basu da nisa da makarantar ,mai suna Vanessa,sai taga yamma ta yi take dawowa

Yau ma ba ta dawo da wuri ba,ta kai har wajen biyar na yamma a gidan su Vanessa,ta shigo gidan ɗan ƙaramin hijabin ta a hannu,don yanzu ta fara sabo da rayuwar su Vanessa,yawo kai babu ɗan kwali ba baƙon su bane

Wanda ta gani zaune a parlourn ya sa ta firgita sosai,ta juya da gudu da zummar ficewa daga parlourn

Auwab ta daka mata tsawa"hey!idan kika fita sai ranki ya ɓaci,are you stupid?dalla dawo!!"

Maƙalewa ta yi a ƙofar parlourn ta na kallon shi,cikin ɓacin rai ya taso da sassarfa ya ƙaraso gaban ta,tuni jikin ta ya ɗauki kyarma,a fusace ya ce"daga ina kike?"

Ta runtse idanun ta gam ba tare da ta yi magana ba, ya sanya hannu a fusace ya finciko ta,sai ta sake ƙanƙame jiki ta fashe da kuka ta na faɗin "wayyo Abba naaaaa!"

Gaba ɗaya jikin shi sai ya yi sanyi,tausayin ta ya kama shi ,ya sake ta ya koma gefe yana kallon yadda ta durƙushe a wajen ta ƙanƙame jiki tana cigaba da kiran Abban ta,ganin abin ba zai ƙare ba ya durƙusa a kusa da ita ya na faɗin "is okay!is okay!! Allah ya ba ki haƙuri,yi haƙuri,ki daina kukan nan don girman Allah"ya ƙarashe cikin ɗan ɗaga murya

A hankali ta fara rage kukan,ya sa hannu ya goge mata hawayen ya na faɗin "don Allah kar ki sake tafiya ki zauna a waje irin haka"

Cikin muryar kuka ta ce "to ya kuke so na yi?bakwa nan kun barni a gida,ni kuma tsoro nake ji idan dare ya yi"ya yi ɗan murmushi ya na kallon ta ya ce"to in sha Allah daga yau no more tsoro,tunda gashi na dawo,itama matar gidan don ta je gida ne mahaifin ta babu lafiya da tare zamu dawo"

A ranta ta ce"to ni ina ruwa na?"a fili dai bata yi magana ba

Shi ya taimaka mata ya ɗaga ta ta tashi,ya kai ta ɗakin ta ya fice daga gidan

Sanda ya dawo ya same ta ta yi wanka ta sauya uniform ɗin jikin ta zuwa wasu riga da wando da suka ɗan kama ta,gashin ta mai gazarzar da yake shan gyara an tufke shi da ƙaton ribbon,ta na zaune ta na danna wayar ta

A kaikaice ya ƙare mata kallo, koda kasancewar ta yarinya ƙarama bai zama lallai a kallo ɗaya mutum ya gano hakan ba, kasancewar akwai ta da garin jiki,sai tafi kama da ƴar shekara sha takwas

Abinci ya kawo mata a takeaway,kallon banza tayi wa abincin ta ɗauke kanta ta na faɗin "ni naci abinci"

Shiru ya yi da ƴar damuwa a fuskar shi,ya san fushi ta yi,kuma haushin shi take ji, ya zaro wayar shi ya daddanna ya fara kira

Few seconds aka ɗaga,da yake wayar a speaker take khairi ta na iya jiyo muryar Abba

Bayan sun gaisa da Abba ta ji Auwab na faɗin "Abba dama Ummul khair ce take so ku gaisa"Abba yace"to bata wayar"

Tayi farin ciki sosai da suka gaisa da Abba,ya tambaye ta ko Auwab ya siya mata layin ƙasar?tace a'a,ya ce to ta gaya masa ya siya mata layin US

Daga nan Abba ya bawa Sulaiman wayar,Auwab dai sai kallon ta yake yi yadda ta sake da Sulaiman a waya suna ta hira da raha, kafin su yi sallama tana ta murmushi

Ta na kashe wayar ta ɗinke fuska tsaf,ta miƙawa Auwab wayar shi fuska a ɗaure ta na faɗin "Abba ya ce ka siya min layi"ganin bai karɓa ba ta ɗago ta na kallon shi,shima kallon ta yake yi fuska a ɗaure

Ta ɗan tsorata,amma sai ta yi fuska,ta ajiye masa wayar shi a gefen shi ta ɗauki tata ta ci gaba da kallon video ɗin waƙar da take yi ta na bin wakar, Auwab ya yi ƙwafa ya ɗauki wayar shi ya fice daga ɗakin

An gaida Auwab da khairin shi 😁😆😄

Kada dai a manta VIP group #300 ne kacal

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee

*Young talented writers association (YOTA)*

Page 50

Washe gari da safe ta kama asabar,Khairi bata da makaranta,Auwab ya na ɗakin shi,farkawar shi kenan ya ji waƙa sama sama ta na tashi, fitowa ya yi ya bi inda waƙar take fitowa,hanya ta kai shi kitchen

Tsaye ya yi ya na kallon Khairi har ya na harɗe hannayen shi a ƙirji,yau ma dai riga da wando ne a jikin ta sun kama ta sosai,kan nan babu ɗankwali,sai rawa take yi sosai, idan ta ɗan yi rawar sai ta koma kan girkin ta da ta ɗora akan wuta na abincin breakfast ta duba,idan ta yi abinda zata yi sai ta ci gaba da tiƙar rawar ta,ta na yi ta na bin waƙar show me the money da ta kunna ta Wizkid

Jin kamar ana kallon ta ya sa ta juyo da sauri a firgice,bai yi tsammani ba amma sai ya yi fuska ta ɗauke kai daga kallon ta,ya shigo kitchen ɗin ya na taɓe baki,ta na ganin shi ta maƙure jikin bango ta na kallon shi,ya buɗe fridge ya ɗauki ruwan sanyin da bai san me zai yi dashi ba,sai da ya rufe fridge ɗin sannan ya kalle ta ya ce"ke baki iya gaisuwa bane?"

Ta faki idanun shi ta galla masa harara ta ce"ina wuni"

Yace"a'a riƙe wunin ki,dama ke kaɗai kika wuni uwar tsiwa da rashin kunya"ya na faɗin haka ya juya ya nufi ƙofa

Har ya kai ƙofa ya juyo ya na kallon ta,tuni ta gyara fuska daga kallon banzan da take aika masa,ya gan ta sarai,amma sai ya share,ya ce"ki kashe waƙar nan kina damun mutane,sannan ki yi abinda ya dace,kar na sake shigowa na same ki kina shiririta,wato don kin ga matar gidan bata nan shiyasa kike abinda kika ga dama ko?"ya na kai wa nan ya fice daga kitchen ɗin

Jiyo ta ya yi ta na faɗin"mtseeeewwwwww!jarababbe masifaffe!anyi ɗin,ita matar gidan idan ta isa ta zo ta yi da kanta mana,nima a bari idan na auri miji na sai na yi masa,amma an saka ni ina bautawa gardin wata"sam bai yi niyyar nuna mata ya ji ta ba,don a ƙunƙuni ta yi maganar,amma maganar ta ta ƙarshe ta daki zuciyar shi,a fusace ya koma kitchen ɗin,ta juya ta na aikin ta ta na ci gaba da surutan ta ƙasa ƙasa ya damƙo mahaukacin gashin ta,ta ƙwalla ƙara,a fusace ya ce"maimaita abinda kika ce yanzu!"

Sam tunanin ta bai kawo mata maganar ta ta ƙarshe yake magana akai ba,ta yi tunanin don tayi batun matar shi ne,ta runtse idanu ta ce"Allah ya baka haƙuri,ni ba da wani abu na faɗa ba,ka yi haƙuri,ba zan sake taɓa maka matar ka ba"kallon ta yay i kawai,ganin ita bata ma fahimci dalilin da ya sa ya yi mata hakan ba,a hankali ya sake ta ya juya ya fice daga kitchen ɗin

Itama bata sake magana ba ta cigaba da aikin ta ta na sharar hawaye

Akan dinning area ta shirya masa abinci,ta ƙaraso cikin parlourn tana hararar shi ta ce"na gama!"

Banza ya yi mata ya ci gaba da danna wayar shi,ta kufula,cikin tsiwa ta sake cewa"na ce na gama!ka duba kar azo ana cewa ban yi daidai ba"nan ma dai ko ɗaga kai bai yi ba ya kalle ta ba,ta gatsine fuska ta yi gaba ta na faɗin "ai Allah yasan nayi daidai"

Sai da ta shige ɗakin ta ya saki murmushi, yarinyar ta na burge shi sosai,sai yanzu da yake zaune da ita yake fuskantar halayen ta,sai yanzu ya gane dalilin da ya sa suka shaƙu da Azad,dama shi Sulaiman na mutane ne, ba shi da wahalar sabo

Bai gama tunanin ba ta sake fitowa ta na kumbura,don da gaske ta ji haushin abinda ya yi mata,wanda ta kira wulaƙanci,a kufule ta ce"ina layin da Abba yace ka siya min?"

Fuskar shi akan wayar shi ba tare da ya kalle ta ba yace"ba zan siya ba!"

"Ai bani na faɗa ba, Abba ne,shi za ka cewa baza ka siya ba"ya ɗaga kai ya watsa mata manyan idanun shi,ta ɗauke kai ta juya ta nufi ɗakin ta ta na gatsine fuska,ya daka mata tsawa"ke!",a ɗan razane ta juyo ta na kallon fuskar shi da ya haɗe girar sama da ƙasa,a lokaci guda kuma ta na ci gaba da matsawa zuwa bakin ɗakin ta

"Idan kika sake matsawa na riƙe ki sai na karya ki,zo nan"fashewa tabyi da kuka iya ƙarfin ta,bai sake magana ba ya koma ya zauna,ita kuma ta samu damar tserewa zuwa ɗakin ta

Daga lokacin sai ta koma wasan ƴar ɓuya da shi, ya na kallon ta amma ba ya kula ta,don da ya yi niyyar rutsa ta da tuni ya yi hakan

Washe gari Lahadi da yamma ya na zaune a parlour ya na chat da Inaaya da take sanar masa dawowar ta gobe,ya sake tambayar ta mai jiki da yi mata fatan dawowa lafiya,sai ya ji shashsheƙar kuka

Mamaki ya kama shi,to me aka yi mata?ya dai miƙe ya leƙa ɗakin inda take takure tana ta rizgar kuka,yau dai babu riga da wando, doguwar riga ce a jikin ta,amma kan nan babu ɗan kwali sai gashin da aka ɗaure a tsakiyar kan,ta kifa kanta akan gwiwowin ta tana ta kuka

Ƙarasawa ya yi kusa da ita ya durƙusa,ya ɗago kant a yana kallon fuskar ta da ta yi kace kace da hawaye,ya ce "me aka yi miki kuma?kukan na menene?"

Cikin shashsheƙar kuka tace"to ba kai bane na ce ka siya min layi ka ƙi? shikenan ni kullum bana jin motsin mutane,kuma ka hana ni zuwa gidan su Vanessa! "

Ɗan tsaki ya ja jin dalilin sannan ya ce"wacece Vanessa?"

Ta goge hawayen ta ta ce ƙawa ta ce"

"Okay tara ƙawaye kika fara daga zuwan ki?"

Hawaye suka zubo mata ta ce"to ya zan yi?bani da kowa,babu wanda yake taya ni hira, shiyasa nake zuwa gidan su,amma ka hana ni"

"Allah ya kyauta! shirya ki tafi gidan na su,zan yi miki layin zuwa gobe in sha Allah "ya faɗa ya na miƙewa

Da tsananin murna ta riƙe masa hannu ta na faɗin"da gaske?na gode na gode"ta sake shi ta shige banɗaki da gudu,ya bi ta da kallo ya na jinjina shirmen ta

Da kamar mintuna goma ya na zaune a parlour ya na kallo sai gata ta fito,tun daga sama har ƙasa yake ƙarewa farar shirt da jeans ɗin da ta saka,sai wata riga da ta ɗora akan shirt ɗin jikin ta fara,kanta kuma ta naɗe shi da ɗan ƙaramin mayafi

Tun daga sama har ƙasa yake ƙare mata kallo, hankalin ta a kwance ta kalle shi ta ce"yaya zan tafi,sai na dawo"

A zafafe yace "za ki tafi ina?"

Da mamaki take kallon shi,tavce"yaya kaine fa kavce in je gidan su ƙawa ta,ko ka manta ne?"

"Baza ki je ba!"ya bata amsa a ɗan tsawace

Hawaye suka cicciko idanun ta,ta juya a sanyaye ta shige ɗakin ta ta rufe ta fashe da kuka sosai

Har dare ba ta fito daga ɗakin ba ta na ta kuka,shi kam da farko haushin yadda ta fito ta ce za ta fita ne ya hana shi bibiyar ta,amma ganin dare ya yi ba ta fito ba sai ya bita ɗakin

Ko da ya bubbuga ɗakin ma bata buɗe ba,sai da ya fara dauko spare key ya buɗe ɗakin,ya same ta zaune inda ta yi sallar isha'i tana ta share hawaye

Girgiza kai ya yi kawai ya na ɗan murmushi,sannan ya zauna a gefen ta,ta ɗago ta na kallon shi idanun ta cike da fal da hawaye

"Khairat! what's the problem?"

Tana goge hawayen ta,a fusace ta ce"ba khairat suna na ba,ni suna na Ummul Khairi"

Ya ce"na sani,kawai na ga kin fi kama da khairat ɗin ne,kuma ai Ummul khairi khairat ce,yanzu dai ba wannan ba, amsa min,me ya faru kike kuka?"

Kuka sosai ta sake fashewa da shi ta ce"kaine fa ka hana ni zuwa gidan su Vanessa,ka ce naje kuma ka sake hana ni,yaya don Allah me nayi maka haka da zafi ne? meyasa ka tsane ni?"

Kallon ta kawai yake yi,a ranshi faɗi yake"this girl! this girl is silly!!"

A fili kuma sai ya gyara zama,cikin kwantar da murya yace"ki daina kukan nan,ki zauna muyi magana"

Babu musu ta fara goge hawayen ta na rage kuka,cikin kwantar da murya ya fara magana


Da alamu fa Inaaya tayi sagegeduwa🤣💃😎😁😆😆😅🤣

Kada dai a manta VIP group #300 ne kacal

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a

🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee

*Young talented writers association (YOTA)*

Page 51

"Ummul khairi try to understand me mana,ke ɗin amana ce a gare ni,idan ban manta ba a iya tsawon gani na da ke ban taɓa ganin ki da wata shiga wadda ba hijabi ba,amma a gidan nan da kika shigo shi a matsayin matar aure,bai kamata ki rinƙa yin shigar da ba ta dace ba irin haka,ban hana ki don ba na son kiyi farin ciki ba,sai don shigar da kika yi bata dace ba,but I'm sorry "

Kallon shi kawai take yi kawai kamar idanun ta za su faɗo, ta jira ya gama tsari sannan ta watso masa tambaya

"A haka dai kamar ba ruwan ka,Dama ƙare min kallo kake yi har ka san suturar da nake sakawa a gida?amma ko gaishe ka na yi sai ka ɗauke kai kana wani taɓe baki,ko ka yi min banza

Sannan ba kai da matar ka bane kuka gaya min cewa ka fi ƙarfin zama da ni a matsayin matar aure?sai dai ƴar aiki?to ni da nake matsayin ƴar aiki ba sai ka bar ni na yi shigar da nake so ba?aiki kuka ɗauko ni kuma kuna biya na,to ba shikenan ba?tunda ina yi muku aikin ku yadda ya dace?"

Har wani juyawa ya ji kanshi ya yi jin waɗannan tambayoyin daga bakin wadda bai taɓa tunanin tana da wannan wayon ba,a hankali ya ɗago ya kalle ta yace

"Wether I like it or not ke ƴar uwa ta ce Ummul khairi, abinda ya yi mahaifin ki shi ya yi mahaifi na,don haka yadda zan tsaya na sanyawa rayuwar su Amra idanu gudun kada su lalace haka zan sanya miki, ballantana da kika dawo hannu na kacokam,babu su Daddy

Maganar aure kuma,khairi aure ya wuce wasa,ko na so ka na ƙi akwai igiyar aure na akan ki,wadda tafi ƙarfin ayi wasa da ita,idan muka yi hakan dani dake duka Allah zai iya fushi damu,kuma ya kamata ki san cewa ke ɗin musulma ce,bahaushiya,wadda ya kamata ace ta riƙe addinin ta da kyakkyawar al'adar ta, Please Ummul khair ya kamata ki san daidai tun kafin ma nace miki ga daidai,In dai kika kiyaye nayi Miki alƙawarin zan daina yi Miki masifa da jaraba,kin san ni masifaffe ne kuma jarababbe "ya ƙarashe murmushi ya na son kufce masa,idanun shi ƙyar a kanta

Kanta a ƙasa cikin tsananin jin kunya,wato gaya mata yake yi ya ji ta na kiran shi masifaffe jarababbe,yayi ɗan murmushi ya ce"na san baki ci abinci ba,ɗauko hijabin ki muje na siya miki abinci "babu musu ta miƙe ta janyo hijabin ta,ya kama hannun ta suka fice daga gidan

Washegari ta na dawowa gida ta samu Inaaya ta dawo, lokacin Auwab ya na wajen aiki,sai da gaban ta ya faɗi,duk da Inaaya ɗin bata wani nuna mata wata damuwa ba

Bata yi mamaki ba da Auwab ya dawo ya koma mata asalin Auwab da ta sani,a ranta tace"munafiki matsoraci!!haka za'a yi ta muzurai kamar namiji,ashe fanko ne"

Karatun ta ya miƙa sosai,tuni Auwab ya kawo mata layi,ta na chat da sulaiman da su Nusra,sai dai tun ranar da ta yi wa Azad magana ta gabatar da kanta bata sake samun shi ba,asalima bai yi mata respond ba,bata ga alamun ma yana hawa whatsapp ba,ta kira wayar a kashe,hakan ya na damun ta sosai

A ɓangare guda kuma kullum sai ta karanta izu biyar a gidan,da farko a fili ta fara, Inaaya sai da ta sauke mata maruka zafafa,ta ƙara da cewa ta fi su son addini ne ko ta fi su sanin ya kamata? saboda haka tayi wa Sulaiman voice ta na kuka take gaya masa,dama shi ya saka ta,shine ya bata shawarar ta rinƙa yi a ɓoye,ta rinƙa yawan karanta ayatul kursiyyu,ikhlas da falaƙi da nasi ta na tofawa a gidan,kuma duk tana yin hakan

Tsawon watanni uku suna rayuwa a haka,a wannan ɗan lokacin Khairi ta ci duka a wajen Inaaya sau babu adadi kan dalilai mabambanta,dukan ya na damun Auwab sai dai ko a fuska baya nunawa

A wannan lokacin ne tafiya ta kama Auwab zuwa ƙasar Uganda,kuma ba da iniaaya zai tafi ba,gashi kuma zai yi sati biyu acan,ranar da zai yi tafiyar rungume shi Inaaya ta yi ta na kukan shagwaɓa,ita fa bata son ya tafi,don Allah ya zauna kusa da ita,da sauran su

A ranar ma sun sha zagi a wajen khairi a zuciya,sai shige da fice take yi tana ayyukan ta tana hararar su,Inaaya sai wani kukan shagwaɓa take yi Auwab ya na tarairayar ta

Jiyo Inaaya tayi tana magana cikin shagwaɓa "yanzu shikenan ko love?yanzu ba zan sake ganin ka ba sai nan da two weeks? gaskiya ni ba zan iya jure rashin ka ba, Please kace musu zan biyo ka love"sai ta ji Auwab ya kwantar da murya ya na ta mata kalaman kwantar da hankali cikin matuƙar soyayya da kulawa,a bayyane ta furta "ashe soyayyar ƙarya ce ma da ba zaka haɗiye ta ku tafi tare ba!"

Inaaya ce ta raka shi airport ta dawo gida,ta na zuwa kuma ta kama sabgogin gaban ta

A wannan halin ciwon mara na al'ada ya zo mata,tunda ta yi na farko sau biyu ta ƙara yi,kuma duka lokacin ta na Nigeria, tunda tazo US ba ta taɓa yi ba, hankalin ta ya yi matuƙar tashi,ta kwanta a parlour ta dafe mara da dukkan hannayen ta,ta yi ta murƙususu tana juye jiye, tun tana yi ta na jurewa har ta fara sarewa, ƙarshe a parlour ta baje dafe da mara ta na murƙususu ta na kuka

Inaaya ce ta fito da shirin ta,riga da wando ta ɗora rigar sanyi akai,ƙafar ta sanye da takalmi mai tsini,hannun ta riƙe da ɗan ƙaramin akwati,cikin kuka da fitar hayyaci ga fara faɗin "aunty ki taimake ni,zan mutu aunty,don Allah ki taimaka min,ki taimaka min zan iya mutuwa,mara ta aunty! ciwo take yi min"

A yatsine ta kalle ta tace"in taimake ki kamar yaya?"

"Mara ta ciwo,zan mutu,don Allah, wayyo!wayyo Allah na!mhm!mhmmm!!"Inaaya ta yi mata kallon banza ta ce "Allah ya taimake mu baki ɗaya!idan kin gama iya shegen sai ki tashi ki gyara min gida"ta tsallake ta ta yi wucewar ta

Cikin tashin hankali khairi ta fara faɗin"don Allah aunty ki taimake ni ba don hali na ba,zan mutu,na roƙe ki da girman Allah,don Allah aunty,wayyo mara ta"inaaa!tuni Inaaya ta fice daga gidan ma bata san tana yi ba

A lokacin ne khairi ta sake tabbatar da cewa bata da gata,ita dai tun ta na gane halin da take ciki har komai ya ɗauke mata,ta daina ji ta daina ganin komai

Ba ta farka ba sai washegari,da idanu tabi inda take,da sauri ta tashi zaune ta na kallon ɗakin da take da kayan jikin ta,tabbas a asibiti take,kuma kayan asibiti ne a jikin ta,to waye ya kawo ta? Vanessa?kai Vanessa bata san gidan su ba,ko dai Inaaya ce ta ji tausayin ta ta dawo? tunanin hakan ya sa ta ji Inaaya ta yi ƙima a ranta,ta na ta tunane tunane aka buɗe ƙofar likita ta shigo

Weldon Ma'am!how are you feeling?"ta tambaye ta fuskar ta faɗaɗe da fara'a

Gyaɗa kai ta yi kawai, mamakin wanda ta gani a bayan likitar ya na kama ta,ya ƙaraso ya kama haɓar ta ya ɗago ta,cikin taushin murya ya ce"khairat ya jikin?"ta sunkuyar da kai tace"da sauƙi,sannu da dawowa"

Ya zauna kujerar dake gefen ta ya na kallon ta cike da tausayawa,ya na tuhumar kanshi akan banzatar da rayuwar ta da yayi,ya ce"tafiyar bata samu ba,sai nan da wani lokaci,shine na dawo,har munje Washington inda zamu haɗu muyi tafiyar aka soke,shiyasa muka dawo

Unfortunately kuma na shiga na gan ki a halin jinya"

Lumshe idanun ta ta yi hawaye suka wanke mata fuska,ya rungume ta ya na goge mata,ya ce"I'm sorry! I'm sorry please,don girman Allah ki daina kukan nan,idan baki daina ba zan tafi fa"da sauri ta fara ƙoƙarin haɗiye kukan,shi kuma ya na share mata hawayen

Da kan shi ya siyo mata pads ɗin da zata yi amfani dasu,har da pants,kunya ta kama ta sosai ganin kayan da ya siya mata,amma shi ko a jikin shi,babban burin shi da damuwarshi bai wuce Allah ya bata lafiya ba,ya dage sosai ya na bata kulawa

Kwanan ta biyu aka sallame ta,ta warware sosai,duk wasu matsaloli da dokokin asibitin an gayawa Auwab, ranar da suka dawo ma still basu samu Inaaya a gida ba,kuma suna waya da Auwab sosai,bai taɓa tambayar ta inda taje ba,asalima ma bai nuna mata ya san bata nan ba,itama bata taɓa sanar dashi bata gida ko ga inda taje ba

Da kanshi ya haɗa mata ruwan zafi ta yi wanka,ta sauya pad ɗin ta ta sanya doguwar riga,sannan ya kira ta zuwa parlour

Ta na shigowa ya nuna mata waje ta zauna,shima ya zauna,fuska a ɗaure yake tambayar ta

"Ummul khair ina kika samu maganin dakatar da menstruation?waye ya baki shawarar hakan?and, me yasa kika yi hakan?"

Shiru ta yi kanta a ƙasa cike da kunya da tsoro,ya ce"I'm asking you Ummul khair!me ya sa kike dakatar da menstruation ɗin ki a ƙananun shekarun ki?"ɗagowa ta yi ta na kallon shi a ɗan tsorace,a fusace cikin ɗaga murya ya ce"Madam don't let me repeat myself!"

Kuka ta fashe dashi a tsorace ta na kallon shi,ya furzar da zazzafan huci sannan ya sake kallon ta ya ce"is okay!Daina kukan"ya taso ya dawo kusa da ita ya rungume ta,ƙasa-ƙasa yake faɗin "is okay umm?yi shiru to,mu yi magana a tsanake,gaya min waye ya baki?"

Cikin rawar murya tace"idan ya zo min wahala nake sha ne"yace "eh na sani,amma waye ya baki maganin dakatar da zuwan nashi?"

Cikin rawar murya ta sake cewa"siya muka yi"

"Ke da wa?"

"Ni da su Amra"

"Amra? Amra kuma?yanzu Amra ce ta biye Miki kika siyi wannan maganin?tukunna ma,a ina kuka haɗu da ita kuka aiwatar da wannan shirmen?"

Kallon shi ta yi a sanyaye tace"Amra ƙawa ta,a makarantar mu"

"Okay na gane,to meyasa kuka sha ba tare da kun tuntuɓi likita ba?ko wani likitan ne ya rubuta muku?"

Cikin rawar murya tace"idan na zo yi ina wahala, shine na gaya wa su Amra,shine Amra ta ce akwai maganin da yake stopping ɗin shi,shine muka yi searching a Google,da yaya Sulaiman zai je min visit sai na tura masa sunan maganin shine ya siyo min,da na dawo gida ma na sake siya"shiru yayi yana kallon ta mamaki fal ranshi,wai kamar wannan yarinyar ce ta iya dabarar wannan shirmen,duk da ya gane dalilin da yasa Sulaiman ɗin yake siyo mata,amma sai yace

"Shi Sulaiman ɗin kike turawa sunan maganin ki ce ya siya miki maganin dakatar da menstruation? girgiza kai ta yi,a sanyaye ta ce"ban gaya masa amfanin shi ba,kawai cewa na yi ya siyo min maganin"ya jinjina kai yana kallon ta,kafin ya ce"suma ƙawayen naki suna sha?"

Girgiza kai ta yi ta ce"ai su basa shan wahala kamar no"

"shekarar ki nawa?"

Ta ce"sha biyar da wata huɗu "

Ya ce "har yanzu ke yarinya ce ƙarama sosai,wannan haukan bai dace dake ba,kar ki sake shan maganin da ba licenced health personnel ne ya rubuta miki ba,In dai ba so kike ki kashe kanki ba

Kin yiwa kanki illa sosai, Allah ya taimaka ma doctors ɗin da suka yi attending ɗin ki ƙwararru ne,da tuni ba za ki taɓa haihuwa ba"a firgice ta kalle shi,tayi rau rau da idanu,ya yi murmushi ya ce"ai yanzu sai kin ƙara wani shirmen,yanzu alhamdulillahi kin ji sauƙi ko?"ƙwalla ta ciko idanun ta,ta gyaɗa kai,yace"good girl!now daina kuka, maza tashi muje ki kwanta dare ya yi"ta yunƙura ta tashi jikin ta babu ƙwari, ganin tafiyar sai a hankali ya sa ya ɗaga ta cak suka nufi ɗakin ta

Har da zan tausayawa Inaaya kuma sai na yi tunani na fasa🥱

Kada dai a manta VIP group #300 ne kacal

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a

🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee

*Young talented writers association (YOTA)*

Page 52

Kwana huɗu ta yi tana period ɗin ta gama,a waɗannan kwanaki ta ga kulawa sosai daga Auwab,har ma ta manta da wata Inaaya can,ta daina fargabar za ta iya zuwa ta same su,still tan a chat da sulaiman har yanzu,ya kan gaya mata wasu addu'o'i ko ayoyi da za ta rinƙa yi,har ta rinjayi Auwab ɗin ya yi shima,kuma alhamdulillahi an samu ci gaba ta wannan fannin,yanzu Auwab yana yawan kiran gida, tuntuni ya komawa ɗan uwan shi Sulaiman sun ci gaba da zumuncin su,da yake Sulaiman ɗin ya san komai ko a fuska bai nuna masa wani abu ba

Tsawon sati ɗaya suna tare a haka, Khairi ce abokiyar hirar shi, su yi wasa da dariya, girki ma tare suke yi,su ci abincin su tare,fita tare suke yi,sai dai a yanzu ya kafa mata dokar ɗora hijabi babba akan kayan makarantar ta saboda yadda suke,kuma tuni ta amince da hakan

A yanzu a ɗaki ɗaya suke kwana,tun lokacin da take jinya ya koma taya ta kwana don duba jikin ta,to har yanzu da ta warke ma a ɗakin ta yake kwana

Yau suna kwance,ta ƙwakume shi ta na ta zuba masa shiririta, labarin albasu take ba shi da yace rabon da yaje tun tana ƴar yarinya,sai washe baki take yi ta na ƙara bashi labarin rayuwar ta ta can, ƙawayen ta, Nadiyar ta,da baba Hari da ke kulawa da ita,sauraren ta yake yi,amma babu abinda yake fahimta a labaran da ya kira na shiririta,asalima hankalin shi ya na wani wajen

Gani ta yi ya kashe dhoom light ɗin ɗakin,kallon shi ta yi a cikin duhun ta ce"me yasa ka kashe?"

Rungume ta ya yi sosai,a kunne ya raɗa mata"Ummul khairi kina son aikin lada?"

Shiru ta yi,kafin ta ce"ina so"

Ya ce"za ki iya wani aikin lada yanzu?wanda baki taɓa yi ba?"

Shiru ta yi ta na rarraba idanu,can ta ce"zan iya"ya ƙanƙame ta,a kunnen ya ya raɗa mata"kin yi alƙawari?"ta gyaɗa kanta,amma ta ɗan fara tsorata saboda yadda yake yi mata sam bai saba yi mata haka ba,ya yi murmushi ya ce"thanks very much Ummul khair!"

Abinda ta ji ya na ƙoƙarin yi mata ne ya ba ta tsoro,cikin gigita take faɗin "wayyo yaya!don Allah ka yi haƙuri,zan iya mutuwa,ba zan iya ba wallahi"

Da wata iriyar murya ya ce"zaki iya Ummul khair, Please ki taimaki yayan ki,ba za ki mutu ba amma ni kuma idan baki yarda ba zan iya mutuwa, Please Ummul khair!"ba ta sake magana ba,amma jikin ta sai karkarwa yake yi,a hankali Auwab ya haɗe bakin su waje ɗaya

LUGARD ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA

Wai ina labarin Azad namu ne?

Bai halarci ɗaurin auren Khairi ba,amma su Ma'aruf sun je,kuma a kunnen shi suke lissafa waɗanda aka ɗaurawa auren,suma sai jinjina auren khairin suke yi

Bai ce komai ba,sai bin su da idanu har suka gama labarin nasu,a nutse yake kallon Haidar da har lokacin bayani yake yi na yadda aka ɗaurawa Khairi aure,tsam ya miƙe ya fice daga parlourn ya nufi part ɗin shi,ya na shiga ya zube ƙasa ya haɗa kai da gwiwa ya na sauke numfashi a hankali, daidai lokacin Beely ta shigo, kasancewar akan idanun ta ya fita daga part ɗin mum,sai ta bishi

Ta na ganin halin da yake ciki ta tafi a guje ta sanar da mum,sai ga mum da sauran yaran nata da wasu daga cikin ƴan biki,mum tuni ta fashe da kuka

Kai tsaye asibitin farko aka mayar dashi,sai dai kafin ma akai ga isa asibitin ya suma,kuma iya ƙoƙarin da suka yi don ba shi taimakon gaggawa hakan ya ci tura,kwata kwata zuciyar shi bata responding, Dr Mahfouz ya yi wa mum bayanin cewa in dai har bai samu abinda yake so ba ba za'a rabu da matsala ba,kuma tabbas komai zai iya faruwa,ciki kuwa har da rasa shi kacokam,mum ta yi kuka sosai,ba ta taɓa nadamar hana Azad auren Khairi ba sai yanzu da take shirin rasa shi,asalima a halin da ake ciki Yanzu Azad ya shiga coma

Daddy bai taɓa nadamar zubawa mum idanu ta na yin yadda ta so da rayuwar Azad ba sai yanzu,cikin kuka mum take faɗin "da na sani da na yarje masa auren ta, shikenan yanzu zan rasa ɗana,ka yafe min Azad,don Allah kar ka tafi ka bar ni, wallahi ina son ka Azad"a wannan lokacin ne Daddy ya ritsa Haidar da tambaya,shine yake masa bayanin duk abinda ya sani daga bakin Beely, Daddy ya ji baƙin ciki sosai,amma bai yiwa mum magana ba,ya shirya masa fita zuwa India

Da haidar kawai ya tsara tafiyar, mum da ta ga ba za'a yi da ita ba sai ta fashe da kuka ta na faɗin "don girman Allah barrister ka taimake ni na je na ga ɗana, wataƙila ganawar ƙarshe zamu yi,ina buƙatar kasancewa kusa da shi barrister,ba zan samu nutsuwa ba idan bana tare da shi"

Da ƙyar yake danne ɓacin rai da baƙin cikin shi,ya ɗago a nutse ya kalle ta ya ce"Kar ki damu,idan Allah ya yi masa cikawa nan za'a dawo dashi ayi masa jana'iza,zaku sake haɗuwa,amma yanzu dai babu inda zaki je"mum ta fashe da kuka sosai tana zubewa ƙasa,ta ce "don Allah barrister ka yi masa addu'a ya samu sauƙi, wallahi bana son na rasa shi"Daddy ya ce"a'a Salma ƙarya kike yi,ba kya buƙatar shi a rayuwar ki shiyasa kika yi ta gana masa wahala da sunan soyayya,kin ga idan ya rasu ta dalilin ki ai soyayya ta yi rana ko?"bai sake sauraren ta ba ya fice,ta dafe kai ta na kuka zuciyar ta cike da nadama da rashin madafa,Beely da Nusra suka rungume ta suna kukan suma

Washe gari aka fita da Azad daga ƙasar zuwa India,a ranar mum ta kwanta jinya sosai,amma ta ce ba zata je asibiti ba,idan ma mutuwa zata yi su mutu tare da ɗan ta

Beely dai ta shiga tashin hankali sosai,daga ita har Nusra da Ma'aruf,feena ma a wata ɗaya ta zo sau babu adadi, banda kiran waya da take yawan yi

Tsawon wata guda babu wani ci gaba daga ɓangaren Azad,suma dai magana ɗaya suka maimaita,yana cikin damuwa mai tsanani ne,idan kuma ba'a ɗauki mataki ba akwai matsala

Shi kan shi Aliyu Haidar abin ya girmi tunanin shi,bai taɓa tunanin yayan na shi zai iya son wata mace kwatankwacin yadda yake son Khairi ba, ballantana shi Azad mata ma sam ba sa gaban shi,aikin shi na Melbourne shine sana'ar shi,mace ɗaya da ya saka a rayuwar shi wadda zai iya komai don ita ita ce mum ɗin shi,da ko su sun shaida cewa ya fisu son ta da shaƙuwa da ita,ya fisu ƙaunar farin cikin ta,yafi su yi mata biyayya

Shiyasa mum ba ta shakkar umartar shi ya yi mata komai,don ta san bazai ƙi ba

Sai da suka sare, Daddy har ya fara batun gwara su koma Nigeria kawai, saboda itama mum zuwa lokacin jikin ya ƙi daɗi,amma bata yarda ta kwanta a asibiti ba,likita ke zuwa ya duba ta ya yi mata treatment ya tafi

Abin mamaki sai a lokacin jikin Azad ya fara responding,a hankali jikin nashi ke motsawa,daga baya kuma Allah ya yi ya dawo hayyacin shi,kuma cikin hankalinsa

Sai dai sai da ya yi sati biyu cif a jere bai cewa kowa komai ba,kuma doctors ɗin na shi sun duba shi sosai,sun ce basu ga wata matsala ba,kalma ta farko da ya fara faɗa cikin sanyin murya yana kallon Haidar ita ce

"Ina mum?"

Haidar ya kalle shi da sauri cikin fara'a ya ce"me kace yaya Azad?"

Shiru Azad ya yi ya na kallon shi,da sauri ya ƙarasa kusa da shi ya riƙe hannun shi ya na faɗin "yaya yau ka yi magana, Allah ya ƙara sauƙi

Mum Bata zo ba, Daddy ne ya ce ba sai ta zo ba"Azad yace"kira min ita a waya"babu musu Haidar ya kira mum,ta na ɗagawa da farin ciki sosai a muryar shi ya ce "guess what mummy!"

Shiru ta yi kafin ta ce cikin sanyin murya "ya jikin Azad?"

Haidar ya yi murmushi ya ce"eh to!bari ya gaya miki da kan shi"bai jira amsar ta ba ya miƙawa Azad wayar

Azad ya na karawa a kunne ya ji mum na faɗin"Azad!son!don Allah da gaske ne?"

Azad ya lumshe idanu ya buɗe, hawaye suka ciko idanun shi,cikin rawar murya ya ce"mummy na! I miss you mummy na, I wish you are by my side"

Ta fashe da kuka sosai ta ce "ka yafe min Azad!na yi nadama,don Allah....."

"No mummy na!ki bani umarni kawai,na yi miki alƙawarin zan karɓa,Ni ɗan ki ne,naki ne,kuma ikon ki ne, I love you so much mum!"

Mum ta share hawaye ta ce"love you more sweetheart,ya jikin?"

"Ina samun sauƙi mum, yaushe za ki zo?"

"A'a Azad! mahaifin ka ya ce kar nazo,na gwammace na zauna na yi maka addu'a" ɗan murmushi ya ce"to mummy na,na ji sauƙi ma,in sha Allahu kusa dawowa gare ki,ki ci gaba da yi min addu'a"

"To son,ka gaida su daddyn naka"

Ya amsa da zasu ji,ya kashe wayar

Ɗaga kai ya yi ya na kallon Haidar da ya zuba masa idanu cikin tausayawa,ya ɗan ɗaga gira ya na kallon shi,ya ce"ya dai?"

Girgiza kai ya yi yace"yaya ka yi haƙuri ka ji, Allah ya sa haka ne mafi alkhairi a gare ka,da izinin Allah biyayyar da kayi wa iyayen mu baza ta tafi a banza ba"Azad bai sake magana ba ya mayar da kanshi ya kwantar ya lumshe idanun shi ba tare da ya ce komai ba

Wato duk inda uwa take uwa ce!duk ɗa na gari komai lalacewar uwa ba ya daina yi mata biyayya,salute to you Azad, Allah ya baka lafiya 🥺

Kada dai a manta VIP group ₦300 ne kacal

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a

🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee

*Young talented writers association (YOTA)*

Page 53

Daddy da yake ta tsaye a bakin ƙofa ba su kula da shi ba ya ƙaraso cikin ɗakin idanun shi akan Azad, Haidar ya tashi daga kujerar da yake zaune, Daddy ya zauna ya na kallon shi cikin tausayawa

Cikin tausayawa da tausasawa ya fara magana idanun shi akan Azad,wanda na shi idanun ke lumshe,"komai na duniya muƙaddari ne daga Allah,duk abinda kaga ka samu a rayuwar ka to dama can Allah ya tsara rabon ka ne ko da baka nemi hakan ba,kuma duk abinda ka ga ka rasa a rayuwar ka to dama can Allah bai ƙaddara naka bane ko da ka nemi hakan,da wancan da wannan ɗin duk wanda ya same ka sai ka mayar da al'amarin ka ga Allah,kuma ka gode masa, Allan da ya jarabce ka da rashi shi zai baka mafiyin abinda ka rasa in sha Allah "ɗago kan shi ya yi ya buɗe idanunshi ya kalli Daddy,cikin raunin murya ya ce"da gaske zan samu wadda ta fi Khairi?"Daddy ya gyaɗa masa kai cikin sigar ba shi ƙwarin gwiwa

Ya sake cewa"kuma zan so ta fiye da yadda na so Khairi?"nan ma Daddy ya sake gyaɗa masa kai ya na kama hannun shi ya dunƙule cikin na shi

Murmushi mai ciwo Azad ya yi ya ce"Daddy ba zan iya son wata mace ba ballantana na so ta kamar yadda na so Ummul khair,na yarda na rasa ta, Allah ya bani dangana, Allah ya sa na manta da ita, Allah ya cire min soyayyar ta da na daɗe ina raino tun ta na......."shiru ya yi saboda kukan da ya taho masa,rauni sosai ya ji ya dirar masa a yanzu da daddy yake ƙoƙarin lallashin shi

Tsam Haidar ya miƙe ya bar ɗakin zuciyar shi cike da tausayin yayan na shi, Daddy kuma ya fuskanci Azad cikin tausasawa ya ce"baba na kai mutum ne wanda ya yarda da Allah,da kuma ikon Allah, me yasa akan lamarin khairi kake son butulcewa rahamar Allah?"

"Astagfirullah!in sha Allah zan yi duk yadda zan yi na daina tuna ta,ina so na koma bakin aiki na Daddy"

"Za ka koma son,da kai na ma zan mayar da kai,amma kafin nan ina so ka fara zuwa wajen mummyn ka, ba'a fushi da mahaifiya ko me ta yi"

"Daddy ba na fushi da mum, asalima ba na fatan wani dalili da zai kai ni na yi fushi da ita,ka sani Daddy babu wata mace ma da ta isa ta shiga tsakani na da ita,kawai dai zan fi nutsuwa ne idan na yi ɗan nisa da gida,na san mum zata fahimce ni,Kuma idan na gaya mata za ta iya zuwa nan ma"

Shiru daddy ya ɗan yi kafin ya ce"to ai itama ba daɗi take ji ba,kaima kuma haka,don haka ya kamata ka koma gida ka ɗan huta,idan yaso da kaina zan mayar da kai Australia "

"Me ya samu mum ɗina?"

"Ta ce min zazzaɓi take yi,ta ji sauƙi ma"haka kawai ya ji bai yarda ba,amma sai ya ce"to Allah ya bata lafiya, Daddy ka ce ayi discharging ɗina,na gaji da asibitin nan"Daddy ya yi murmushi ya ce"ko dai ka ce a sallame ka za ka je ka ga mum ɗin ka ɗan mummyn shi,ina za ka mummy,daga ina kake mummy,me zaka yi mummy, ita ma dai da alamu mantawa take kai ne yaya take ririta ka ko?"

Murmushi ya yi sosai har haƙoran shi suka bayyana,shima Daddy murmushi ya yi ya ci gaba da faɗin "in sha Allah ɗan mummyn shi zai koma gida very soon, Allah ya ba ka lafiya babban yaya"ya yi ɗan murmushi kawai ya na jinjina kai

Kwana shida suka ƙara a India gaba ɗaya aka sallamo su, washe gari suka dawo gida,mum ta yi murnar dawowar ɗan lelen nata,sai dai ta yi kuka saboda yadda ta rame,shima sai da ya zubar da hawayen yadda ya ga ta rame sosai,da alamu ita ma jinya ta sha sosai

Washe gari Beely ta bashi wayar shi dake hannun ta,har yanzu ita ma dai ta na gida babu wani ci gaba,ga ciki ya yi nauyi haihuwa yau ko gobe,cikin ma ya zarce watannin shi amma anje asibiti sun ce babu matsala

Ya yi matuƙar mamaki da ya ga saƙon da Khairi ta bar masa, ya runtse idanun shi, zuciyar shi na tunatar masa da cewa yanzu Khairi ta haramta a gare shi,tuna hakan kawai ya sa ya ji yarrr a jikin shi,amma kuma ya zai yi?wannan itace gaskiyar da bayaso,ita ce ƙaddarar shi a rayuwa,a yanzu Ummul khairi matar ƙanin shi Auwab ce

Bai bata amsa ba sai goge chat ɗin da ya yi gaba ɗaya,a ranshi ya na faɗin "ya Allah ka yaye min son abinda ba nawa ba,ka azurta ni da rabo na na alkhairi"

Bai sake cikakken sati guda a Nigeria ba ya koma bakin aikin shi,don a ganin shi hakan ne mafitar shi kawai,duk yadda mum ta so dakatar da shi hakan ya gagara,ita ma dai ba ta son yi masa dole,don haka ta na ji ta na gani haka ya cale zuwa Melbourne bakin aikin shi

BOSTON, MASSACHUSETTS, USA

Dawowar shi kenan daga masallacin asuba,da saurin shi ya shiga cikin gidan,kai tsaye ɗakin Khairi ya nufa ya murɗa ƙofar,har yanzu kofar a rufe,ya jingina da bango ya na furzar da zazzafan huci cikin damuwa,kafin ya fara magana cikin kwantar da murya

"Don Allah Khairat ki buɗe ƙofar,ko ki cire key dake jiki,kinga ba ki da lafiya kina buƙatar taimako na"shiru babu amsa,tunanin shi ya rinƙa ba shi Babu lafiya, musamman a yadda ya fita jiya da dare ya bar ɗakin,ya je ne don nema mata magani bayan ya sanya ta ta yi wanka, saboda zazzaɓin da ya rufe ta ga kukan da take yi,to kafin ya dawo kuma ta datse ƙofar ɗakin ta,tun jiya da daren yake lallaɓa ta ta buɗe ɗakin taƙi,yanzu ma taƙi

Cikin tashin hankali yake dukan ƙofar,ya na faɗin "Ummul Khairi don girman Allah ki buɗe ƙofar nan, wallahi babu abinda zan yi miki,magani kawai zan ba ki,idan kika ce ba kya son shiga ruwan zafin ma sai na ƙyale ki"

Ganin da gaske ba buɗewar za tayi ba ya dawo parlourn ya tsaya cikin rashin sanin abin yi,kallo ɗaya za'a yi masa tashin hankalin da ke kwance kan fuskar shi,dabara ce ta zo masa,ya yi saurin ɗauko wani ƙarfe ya fara dukan wajen makullin,cikin Sa'a kuwa ya karya shi

Da sauri ya tura ƙofar ya faɗa ɗakin,turus yayi ya na kallon ta a kwance,wani irin tashin hankali ya dirar masa,ya fara ambaton _hasbunallahu_ _wa_ _ni'imal_ _wakeel_ a ranshi,cikin ikon Allah yaji nutsuwa ta saukar masa,ya durƙusa kusa da ita yana duba ta gaban shi ya na bugawa

Mamaki ya kama shi ganin baccin ta take yi cikin kwanciyar hankali, sai sauke numfashi ta keyi a hankali,sai a lokacin ma nutsuwa ta zo masa ya gane sallar asuba ta yi ta yi kwanciyar ta akan dardumar da ta yi sallar

Ɗan murmushi ya yi ya na jinjina nauyin barcin ta,ya sanya hannu ya ɗaga ta zuwa kan gadon da ita,sai da ya kwantar da ita sannan ta farka a firgice ta na kallon shi,ya na kallon ta da murmushi sosai a fuskar shi ya ce"kin gaji da kwanciyar ƙasan ne,shine na dawo dake gado,yi baccinki alkhairi na!"babu musu ta lumshe idanu da nufin komawa bacci,ya shafi gefen fuskarta ya na murmushi,ta sake buɗe idanu ta na kallon shi ta na lumshe idanun,ya yi ɗan murmushi, ƙasa-ƙasa ya furta"I'm proud of you alkhairi na"ta sake mayar da idanun ta rufe,shima ya kwanta a gefen ta ya rungume ta sosai,a haka bacci ya yi awon gaba da su

Cikin baccin nashi ya jiyo sautin kuka,da sauri ya farka ya na kallon Khairi dake zaune a takure a gefen gado ta na ta kuka,da sauri ya ƙarasa inda take zaune ya janyo ta ya rungume ta ya na kallon fuskar ta ya na faɗin

"Khair me ya faru?Are you okay?"

"Ni dai ka mai dani wajen aunty"ta faɗa da muryar kuka

"A'a khair,ki daina kukan nan please,zan kai ki amma sai lokaci ya yi "

"Ni dai ka mai da ni gidan dadyyyyy"ta faɗa cikin gunjin kuka

"Shshshsh!is okay khair!! zan kai ki gidan Daddy,amma sai kin kwantar da hankalin ki kin samu lafiya, amma idan ba haka ba ba zan mayar dake wajen Daddy ba"babu musu ta yi shiru ta na jan numfashi,ya miƙe ya shiga banɗakin ta ya haɗa mata ruwan zafi sosai

Da kan shi ya gasa mata jiki kamar yadda ya yi mata jiya,duk da koke-koken da take yi sai dai ya yi ta lallaɓa ta ya na bata haƙuri

Da kan shi ya shirya ta cikin doguwar riga mara nauyi,ya kawo mata abin breakfast,ta na cikin karyawa ya ji ƙarar doorbell ɗin entrance ɗin gidan

Kallon ta ya yi da kulawa yace"I'm coming back right now,ki jira ni kin ji"bai jira amsar ta ba ya yi kissing goshinta ya miƙe ya fice daga ɗakin

Tsam ya yi ya na kallon Inaaya da ta zuba masa idanu ta na ɗan murmushi,kafin ta rungume shi ta na faɗin"I miss you so much babe,my honey,yau dai gani na dawo,yaushe ka dawo?"

Heeeee ahayyeeeee ruwai😅😁🤣💃ga sabon ango ga uwar gida, Auwab kana cikin bala'i dumu-dumu 😁

Kada dai a manta VIP group ₦300 ne kacal

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a

🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee

*Young talented writers association (YOTA)*

Page 54

Auwab ya dube ta fuska babu yabo babu fallasa ya ce "welcome Inaaya, saukar yaushe?"

Ta manna masa kiss a kumatu ta ce"saukar yanzu, I miss you so much"bai ce mata komai ba ya ja trolley ɗin ta zuwa cikin gidan kamar yadda ya saba,ita ma ta biyo bayan shi ta na ta zuba masa surutu,ta na ba shi labarin yadda ta yi kewar shi

A parlour ta yada zango ta na ƙwala kiran "ke ƴar ƙauye!zo ki gyara min ɗaki ki haɗa min ruwan wanka"Auwab ya kalle ta fuska a ɗan ɗaure yace"it's better to call her with her name Ummul khair,kuma bata da lafiya,don haka babu wani aiki da za tayi Miki yanzu"ya na faɗin haka ya juya ya nufi ɗakin Khairi

Baki a sake da mamaki ta bishi da kallo,shi kam bai sake waiwaya wa ya kalle ta ba ya shige ɗakin Khairi,wadda ta yi kwanciyar ta kan dardumar da ya shimfiɗa mata ta ci gaba da baccin ta hankali kwance

Ƴar dariya ya yi ya na jinjina wannan son baccin nata,ya sa hannu ya tayar da ita zaune ya na kallon ta, buɗe idanu tay i ta kama ƙoƙarin fashewa da kuka,ya ce"in dai kika yi min kuka babu ke babu gidan Daddy"tuni ta ja bakin ta tsuke,a hankali ta ce"ni bacci nake ji"

Ya ɗan rungume ya na kwantar da kan ta akan ƙirjin shi,murya ƙasa ƙasa ya ce"cewa fa na yi ki jira ni na je na dawo kawai na zo na same ki kina bacci,kuma ga shi baki gama breakfast ba,ki ƙarasa za kiyi baccin kin ji alkhairi na?"ita dai ba ta ce komai ba

Ya na cikin ba ta abincin ne Inaaya ta shigo ɗakin da tsananin mamaki ta na kallon su,ya kalle ta fuska babu yabo babu fallasa ya ce "any problem?"

"Auwab me nake gani ne haka?"

Ɗauke kan shi ya yi ya ce"ba ta da lafiya,shine nake kula da ita,da wani abu ne?"

"Bata da lafiya?to ta mutu mana,don ba ta da lafiya kai ne za ka kula da ita?wait ban ma gane kan wannan aikin ba,waye kai a wajen ta da har za ka zauna kana kula da ita da sunan bata da lafiya? "cikin masifa Inaaya take faɗar haka, Khairi sai runtse idanu take yi don jin hayaniyar take yi har cikin kanta

Auwab ganin ta ƙoshi ya goge mata baki da tissue ya goge hannun shi,ya kwashi kwanukan ya miƙe tsaye,cikin nutsuwar shi ya na kallon Inaaya ya ce"ina kula da ita ne a matsayin yayan ta, kuma MIJIN TA!!!"

Daga nan ya fice daga ɗakin ba tare da ya kula da yadda Inaaya ta daskare a wajen ta na kallon shi ba

Ta bishi da kallo cikin tsananin mamaki,ita kuma Khairi da ta sake kwanciya bayan fitar Auwab ta yi ta bin ta da kallo,ta juyo ta na kallon khairi dake kwance ta na ta kallon ta,kawai zuciya ta ɗebe ta ta ƙarasa kusa da ita a sukwane ta shaƙe mata wuya,ta na faɗin "bari na kashe ki idan ya so sai na ga wadda Auwab zai sake kiran kan shi da mijin ta bayan ni, shegiya tsinanniyar yarinya,kina ƴar ƙanƙanuwar ki amma kin iya barik......"

Saukar marin da ta ji ne ya sa ta saki khairi dake kakari ba tare da ta san tayi hakan ba,ta ɗago da wani irin mamaki a kan fuskar ta ta na kallon Auwab wanda idanun shi suka kaɗa suka yi jajur,da sauri ya durƙusa ya ɗago khairi da ta yi collapse a ƙasa ta na ƙoƙarin daidaita numfashin ta, rungume ta ya yi ya na ɗan mata fifita da hannun shi, tsabar kiɗima ma ya manta bata jin Yaren shuwa,haka ya yi ta lallaɓa ta da yaren da daga ita har inaaya babu mai ji

Ita dai khairi ta na dawowa hayyacin ta ta sake fashewa da kuka sosai ta na ƙanƙame shi,cak Auwab ya ɗauke ta ya bi ta gaban Inaaya ya fice da ita daga ɗakin zuwa parlour

A parlourn ya dire ta kan kujera,kafin ya kai ga magana ta fara magana cikin kuka

"Na ce ka maida ni gida kaƙi,ni bana son nan gidan,in dai ba so kake aunty ta kashe ni ba,ta ce sai ta kashe ni"

"In dai za ki rinƙa yi min rigima ba zan mayar da ke gida ba,kuma ni dai na san Khairi na ba matsoraciya ba ce"ya yi ɗan murmushi ya na kallon ta yace "ko ni kaɗai kika raina?ni kaɗai wannan bakin yake iya yi wa tsiwa ko?"ya faɗa ya na kewaye bakin da yatsan shi manuniya

Shiru ta yi idanun ta a lumshe ta na sauke ajiyar zuciya a hankali, daidai nan Inaaya ta shigo parlourn ta na kallon Auwab da ya mayar da hankali kan Khairi

"Auwab!ta kira sunan shi hawaye ya na wanke mata fuska,har yanzu tsananin mamaki ya kasa barin ranta,cewa wai Auwab ne ya ɗaga hannu ya mare ta saboda ta taɓa khairi

Ɗaga kai ya yi yana kallon ta kamar koyaushe fuskar shi babu yabo babu fallasa,ta ci gaba "Auwab yau ni ka mara akan bagidajiya, jahila, ƙazama, baƙauyiya? tukunna ma,ka gaya min me ka yi da yarinyar nan da kake narke mata kana wani bin ta zalo zalo? wallahi yau ɗin nan ko na kashe ta ko na kashe ni da ita ko na kashe kowa a gidan,don yau ko me zai faru sai dai ya faru,amma bata isa ta sake kwana a duniya ba,ƙaramar karuwa!"

Har Auwab ya buɗe baki zai bawa Inaaya amsa Khairi ta saki ihu ta na kuka,ya mayar da hankali gare ta ya na faɗin"me kuma ya faru?ko bakya son komawa gidan Daddy?"

"Cewa fa ta yi za ta kashe ni fa kana ji,kuma har ta na ce min karuwa,ni dai Allah ya isa na!"

"Rabu da ita kar ki kula ta,in dai kina so na kai ki wajen aunty duk abinda zata faɗa baza ki kula ta ba,kin yarda?"ta gyaɗa masa kai ta na jan ajiyar zuciya

Murmushi ya yi ya ce"da kyau little sister ɗin Azad da Sulaiman!"murmushi ta yi ita ma,ya kwantar da ita akan kujerar da suke zaune yana faɗin "just two minutes alkhairi na"sannan ya miƙe ya finciki hannun Inaaya dake daskare ta na kallon su,ya nufi ɗakin ta kai tsaye

Ya na shiga ya dube ta fuskar nan babu rahama ya ce"tambaya kike?to yanzu zan baki amsa, Khairi ƙanwa ta ce,kuma matata kamar yadda kike matata, maganar abinda na yi da ita kuma, abinda nake yi dake, bambancin kawai ke baki taɓa saka ni a farin cikin da ta saka ni ba

Then sai me?za ki kashe ta ko?kiyi mata mugun kallo ma talkless of duka ballantana a zo ga wata cutarwa,ba ki san wane ne Auwab ba da alamu,to kar ki kai ni inda za ki san ni,da ke da ita dukkan ku mata na ne,ba zan lamunci wata ta cutar da wata a cikin ku ba

And lastly,ba na son ki sake aibata ta,abin ba zai mana kyau ba,sunan ta Ummul khairi,ba ƴar ƙauye,ko bagidajiya,ko jahila ko ƙazama ba,take note please,ki kama girman ki a matsayin babbar mata ta,kuma wadda tafi Khairi shekaru, I know Khairi very well,bata shiga sabgar wanda bai shiga tata ba,amma bata barin bashi,don haka ina maimaita miki ki ja girman ki Please,i married Khairi not because I love her,but I'm sorry to say I love her for now, and, I love you both,don haka ina fatan zaki kiyaye abinda na gaya miki "

"Ba zan kiyaye ɗin ba! wallahi ba zan kiyaye ba,wato saboda zalunci irin na maza ka rasa wadda zaka haɗa ni da ita sai wadda muka kawo gidan nan da zummar aiki,to wallahi sai ka yi nadamar abinda kayi, sai ka yi nadamar mari na akan wannan bagidajiyar, azzalumi maci amana!ai cewa ka yi aiki zata yi mana,ashe kai kaɗai zata yi wa aikin"ta fice daga ɗakin ta na gunjin kuka

Bin ta yayi da kallo bata re da yace mata uffan ba, kafin ya girgiza kai ya fito daga ɗakin ya dawo wajen Khairi

Tuntuni ta koma barcin ta,ya shafi gefen fuskar ta ya yi kissing kumatun ta sannan ya miƙe ya koma ɗakin shi

Inaaya kuwa Shukra ta kira ta sanar mata abinda yake faruwa ta na kuka,ita kanta Shukra ta yi matuƙar mamakin abinda aka ce mata Auwab ya yi duk da cewa aikin da suka yi masa ba ƙarami bane

Aikin ku ɗin banza🙄

Kada dai a manta VIP group ₦300 ne kacal

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a

🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee
*Young talented writers association (YOTA)*

Page 55

Shukra ta ce"lallai wannan yarinyar hatsabibiya ce,yanzu duk aikin da muka yi masa sai da ta lalata take nufi ko me?"da sauri inaaya ta ce"a'a bata lalata ba,bata isa ta lalata ba ma,don wallahi na fi ƙarfin ta!na fi ƙarfin uwar ta da uban ta,shegiya baƙauyiya,jahila!"

"No Inaaya,kar mu ginu akan zato,bari na bincika naji,idan ta lalata kin ga dole a sake sabon zama ko?akwai sababbi da na samu masu aiki mai zafi, idan ya zamana ta ɓata ɗin dole mu yi aiki mai zafi"

"To shikenan,ki bincika, wallahi idan ya zamana ta lalata mana aiki sai na saka ta ta tsani kanta,sai na ƙuntata mata,shegiya ƙaramar karuwa "

"Mhm!bari na bincika ɗin"ta kashe wayar ba tare da ta saurari Inaaya ba

Ƙasa da rabin awa sai ga Shukra ta kira, Inaaya ta ɗaga a firgice ta na faɗin "ya ake ciki ne Shukra?"

Cikin jimami Shukra ta ce"wallahi kaf aikin mu baƙin aiki ne kawai ya rage ba ta kassara ba,amma dukkan ayyukan mu ta lalata mana,dole ki yi wani abu akai,don yanzu matsayin ku ɗaya da ita,idan kika yi wasa ma sai ta fiki matsayi,yadda kika ce yake rawar ƙafar nan"

Shukra ta ɗora hannu aka ta na kuka ta na faɗin "na shiga uku wayyo Allah!!amma wannan yarinyar ta cuce ni ta gama dani, azzaluma muguwa"

"Ki kwantar da hankalin ki,ba dai kuɗi ya na aiki ba?to a yau ba gobe ba zan fara duba miki manyan malamai,sai kin kwace mijin ki very soon,idan ya so sai kiyi yadda kika ga dama da yarinyar,ke dai kawai ki saki kuɗi "Inaaya ta goge hawayen ta ta na faɗin"kuɗi ba matsala ba ne Shukra,ni dai ayi duk yadda za'a yi Auwab ya dawo nawa,ita kuma na san yadda zan yi da ita"

"Baki da matsala uwar ɗaki"a cewar shukra, Inaaya bata sake magana ba ta kashe wayar ta

Yinin ranar Auwab da khairi suna tare,gashi kuma da ta ga yadda yake tarairayar ta sai taɓara da sakalci suka ƙaru,abu kaɗan sai ta fashe masa da kuka,shi kuwa sai nan nan yake da ita ya na faɗin bata ƙarasa bashi labarin albasu da take bashi ba,ita kuma tana ta narkewa da taɓara kala kala

Har dare suna ɗaki tare,ita dai Inaaya bata fito ba yinin ranar,suma dai idan ba uzuri ba ba sa zuwa ko'ina

Washegari shine ya shirya Khairi suka fita tare ya sauke ta a makaranta sannan ya wuce wajen aiki, lokacin da aka tashe su kuma sai ta wuce gidan ƙawar ta Vanessa,ba ta dawo gidan ba sai da yamma, lokacin daga Auwab har Inaaya basa nan

Wanka ta yi ta sauya kaya zuwa wata ƴar riga da dogon wando,ta yi sallar la'asar sannan ta zauna ta na gyara gashin ta

Ji ta yi an riƙe comb ɗin da take ƙoƙarin taje gashin na ta,ta ɗago da idanun ta ta na kallon Auwab ta cikin madubin,ya yi mata murmushi ya na kashe mata idanu,ta yi ƙasa da idanu ta na faɗin cikin sanyin murya ta ce"sannu da dawowa"

"Yawwa alkhairi na!ya makarantar?kin yi karatu sosai?"

Gyaɗa kai ta yi kawai ba tare da ta yi magana ba,yayi kissing kumatun ta ya yi mata raɗa a kunne

"Ya jikin baby na?ta warke?"

Sunkuyar da kanta ta yi ba tare da ta amsa ba,ya yi ɗan murmushi ya cigaba da gyara mata gashin

Cikin sanyin murya ta ce"ka bani na gyara"

Yace"um um!da kai na zan gyara abu na!"tura baki ta yi ta ce"ni kar ka ɓata min,ka bani na yi abu na"ya na murmushi ya ce"waye ya ce miki zan ɓata miki?see your head, yarinya na fi ki iyawa ma,kuma bari ki gani"bata sake magana ba ta na kallon shi ta madubin ya na gyara mata gashin gently

Ta yi mamakin yadda ya gyara mata shi sosai,duk da tsawon gashin da cika da taurin shi,yayi mata parking uku da madaidaitan ribbons ɗin ta masu kyau

Kallon ta yake ya na murmushin yadda ta ke ƙarewa kan ta kallo ta madubin,sai kuma ta kama shura ƙafa ta na ƙananun kukan taɓara,ta na faɗin ita ba yarinya ba ce ƙarama da zai yi mata abin yara, Auwab ya yi ƴar dariya ya ɗaga ta ya suka wuce bakin gadon ta,ya dire ta yana ƙare mata kallo a cikin peach colour rigar ta da blue jeans da suka ɗan kama ta,ya ce"inyeeeee!kin gan ki kuwa? sarauniyar Auwab,ba dai ni za'a yiwa kwalliyar ba?to wannan nake so,in dai ana so na yaba abar min abu na"ta tura baki tana gyara kwanciyar ta a jikin shi,ya yi kissing gefen fuskar ta ya na faɗin "I LOVE YOU so much alkhairi na! I can't wait na ga alkhairi na ta na fama da unborn ɗina ya na rinjayar ta,sai....."

Ƙananun kuka ta fara ta na kai masa duka a ƙirji,cikin shagwaɓa take faɗin "ni ba na so!ni ka daina faɗa ba na so"

Rungume ta ya yi sosai,cikin kwantar da murya ya ce "ba kya son ki haifa min baby girl mai kama da ke?me yasa?"

"Ni tsoro nake ji,ba zan iya haihuwa ba,idan an zo haihuwa mutuwa ake yi"

Maganar ta ta ta bashi dariya,amma sai ya ce "wace ce ta mutu a wajen haihuwar?"

Ta tura baki ta ce"aunty bashariyya mana,ƙawa ta wadda muka yi makarantar dare fati ma ta rasu wajen haihuwa,kuma ko haihuwar ma bata yi ba"kallon ta yake yi yadda yanayin ta ya sauya,da alamu har yanzu Khairi tana jin mutuwar ƙawar ta,dama ta daɗe da fuskantar khairi akwai ta da saka abu a rai,cikin kwantar da murya ya ce

"Duk wadda kika ga ta rasu a wajen haihuwa lokacin ta ne ya yi Ummul Khairi,idan kika duba za ki ga mutane da yawa sun haihu kuma ba su mutu ba,kamar Ammi na,umman ki,mum ma,da wasu da dama,ko?"

Ta gyaɗa kai a hankali,ya ce"good girl! so ki daina jin wannan tsoron, in sha Allah lafiya zaki haifo mana baby,ko?"ta lumshe idanu tana ɗan murmushi, ya ɗago ta ya na haɗe bakin su waje ɗaya

Soyayyar su suke sha cikin kwanciyar hankali, Auwab ya san Inaaya bata nan,sai dai yadda bata gaya masa fitar ta ba haka shima bai neme ta ba ko a waya,daga shi sai alkhairin shi,tare suke yin komai kafin su fita,idan sun tashi daga makaranta kuma yawanci shi yake ɗauko ta ya dawo da ita

Cikin ɗan lokaci Khairi ta sake da Auwab sosai, saboda yadda yake tarairayar ta yake bata kulawa,duk lokacin da ya saɓa dawowa bai dawo ba duk sai ta firgice ta yi ta kiran shi a waya

Wani lokacin kuma ya kan ɗauke ta su tafi yawo,duk tambayoyin shiririta da labaran shirmen da take yi masa ba ya gajiya sam,ya na amsa mata da kulawa

A ɗan ƙanƙanin lokaci khairi ta goge ta murje sosai ta yi haske ta yi ƴar ƙiba,yadda take jin Auwab a ran ta abin har mamaki yake ba ta,sau tari ita kaɗai ta kan shiga damuwa idan ta tuna cewa Inaaya za ta dawo,ta zama ta ukun su

Tsawon sati uku suna rayuwar su a haka,yau asabar,babu makaranta,shima Auwab bai fita aiki ba, dukkan su suna parlour kamar yadda suka saba wasu lokutan,waƙar unavailable ta Davido ta kunna ta na ta rawa,a niyyar ta ta koyawa Auwab da ke zaune yana kallon ta,shi kam khairi mamaki take ba shi, yarinya kamar aljana,amma ta na matuƙar burge shi,ya na son komai na ta,shirmen ta,rigimar ta,taɓarar ta,wani lokacin nutsuwar ta da sanin ya kamata ɗin ta

Kallon shi ta yi ta na murmushi ta ce"yaya kaima ka taso mu yi"ya yi ɗan murmushi, daidai lokacin Inaaya ta shigo parlourn,ko kallon su ba ta yi ba ta shige ɗakin ta

Haka kawai Khairi ta ji gaban ta ya buga,jikin ta ya yi sanyi,jiki a saɓule ta miƙe ta wuce ɗakin ta,amma kafin ta yi nisa Auwab ya janyo ta ya na faɗin "Madam ina zuwa kuma?ke da za ki ƙarasa koya min rawa?"ɗan murmushi ta yi kawai,ya ja hannun ta suka nufi ɗakin ta

Kwana uku da faruwar hakan da daddare suna ɗaki suna cin abinci ita da Auwab suna hira,faɗa masa take yi da kallon mai ji da kai take yi masa,ita a ganin ta ya na da girman kai, saboda wulaƙancin da ya taɓa yi mata,har complain ɗin maganganun da ya gaggaya mata ana i saura sati ɗaya bikin su sai da ta yi masa, murmushi kawai yake yi ya na jinjina darun Khairi ,yana matuƙar tausayin ta,ya damu da duk wani abu da ya dame ta,itama dai yanzu ta gane ashe shima ya na da kirki kamar su yaya sulaiman da babban yaya Azad

Inaaya ce ta shigo ɗakin ko sallama Babu,suka ɗaga kai suna kallon ta,ta tsuke cikin wasu matsiyatan ƙananan kaya,ta yi kwalliya sosai,kyan ta ya ƙara fitowa,kai tsaye wajen Auwab ta je ta kama hannun shi ta na kallon tsakiyar idanun shi ta ce"taso muje!"

Babu musu ya miƙe ya bi bayan ta suka fice daga ɗakin, Khairi ta bi bayan su da kallo,haka kawai take jin wani irin abu ya tokare mata wuya,a hankali ta sunkuyar da kanta ta na ƙoƙarin danne abinda take ji,wanda ta rasa dalilin jin shi

Haka ta yi ta zaune ta na jiran dawowar Auwab,amma har wajen sha ɗaya da rabi bai dawo ba,ita ma bata yi bacci ba,ita da ta saba bacci tun ƙarfe tara zuwa da rabi, ta daɗewar duniya ƙarfe goma, saboda soyayyar ta da bacci,kuma shima Auwab ɗin bai hana ta ba,ranar farko da ya kasance da ita ne kawai ta haura wannan lokacin,shima kuma sai da ta rama abin ta

Khairi ba ta taɓa sanin dare ya na da tsawo ba sai yau,don kasa bacci ta yi ta na jiran shigowar Auwab,amma har ta ɓingire da bacci wajen uku da ƴan mintuna bai shigo ba,kuma da ta yi baccin ma mafarkin shi ta yi wai gasu suna hira yadda suka saba,ta na zuba masa sakarci,wani ya yi dariya ya girgiza kai wani ya biye mata

Tana cikin baccin ta mai daɗi sai jin saukar ruwa mai tsananin sanyi ta yi a jikin ta,ta farka a matuƙar firgice ta na rarraba idanu ta na kallon waɗanda suke tsaye a kanta

Auwab da Inaaya ne da ta rungume shi ta na jefa mata wani irin kallo da ta kasa gane ma'anar shi,ta mutstsuke idanu ta na kallon kofin ruwan da yake hannun Auwab,wanda da alama shine ya watsa mata ruwan sanyin da zuwan yanzu ta fara rawar sanyi

"Tashi!munafuka algunguma,karuwa,shaiɗaniya,ba dai da ni kike ba?sai kin gwammace baƙauyiyar uwar ki ba ta haifo ki ba,dalla tashi!"a cewar Inaaya,ita dai Khairi tsananin mamaki da tsoro ya hana ta ko ƙwaƙwƙwaran motsi

Inaaya bata yi wata wata ba ta ɗauke ta da mari ta ƙara mata,sannan ta finciko hannun ta ta faɗo daga kan gadon,zafi ya sa ta fashe da kuka,ta kalli Auwab ta na kuka ta ce"yaya ka ga ta na duka na!ka yi mata magana!"

"Ki tashi ki yi abinda ta saka ki!"ya faɗa da ƴar tsawa

Cak kukan ya tsaya ta na kallon shi,gani take kamar ba Auwab ɗin ta ba wanda suke tare jiya i War haka suna ta shan soyayyar su,a hankali ta furta"zan yi sallah to "

"Ki tashi ki yi abinda aka saka ki"ya faɗa a ɗan zafafe

Cikin sanyin jiki ta miƙe ta fito,kai tsaye ta wuce kitchen don ta san abinda za ta fara yi, zuciyar ta cike da mamakin sauyawar Auwab, Inaaya ta maƙalƙale Auwab suka fito daga ɗakin tana ta narke masa

Khairi kam haka ta gudanar da aikin gidan tana yi ta na kuka cikin baƙin ciki da mamakin abinda take gani,duk bayan ƴan mintuna sai Inaaya da Auwab sun shigo, Inaaya ta yi ta mata masifa har da duka,idan ta nuna ba zata yi wani abu ba ma sai Auwab ya takura ta ta yi

Bata fito daga kitchen ɗin ba ma sai bayan takwas,don ta yi girki ya kai kala biyar Inaaya ta na cewa bai yi ba sai ta sake,ta gaji sosai,don haka ta na shiga ɗakin ta ta wuce banɗaki ta yi wanka ta sanya uniform ta yi sallah ,ko abinci ba ta nema ba ta fice zuwa makaranta

Ba ta dawo ba sai yamma,don gidan su Vanessa da ta kwana biyu bata je ba ta tafi,ta rinƙa rarraba idanu ko zata ga Inaaya a parlour,don mugun tsoron ta take ji yanzu,da ba ta ganta ba ta yi hanzarin shigewa ɗakin ta

A firgice take kallon Inaaya da take zaune a gefen gadon ta ta na cika ta na batsewa,ga wayar ta a hannun ta,a tsorace cikin tashin hankali ta ce"sannu da gida aunty"

"Yauwa sannu annamimiya,wato dama da waya kika zo gidan nan don ki rinƙa kwashe sirrin mu kina Kai wa wasu ko?"

"A'a aunty!ni ban kai wa..."ɗauke ta da mari Inaaya ta yi ta ce"ke ƴar ƙauye!har kin kai darajar da kike jin zaki iya ƙaryata ni? menene wannan?"ta buɗe mata chat ɗin su da sulaiman ta nuna mata

Sai da hantar cikin ta kaɗa saboda tsabar tashin hankali,ba ta taɓa nadamar rashin sakawa waya key ba sai yanzu,a gaban ta Inaaya ta buga wayar ta da mugun ƙarfi a ƙasa, Khairi ta zube gaban wayar da ta yi kwatsa kwatsa ta na fashewa da kuka, Inaaya ta fincike ta suka bar ɗakin

A second parlour suka tarar da Auwab a zaune ya yi shiru, Inaaya ta hankaɗa Khairi gaban shi sannan ta miƙa masa bulala ta ce"so nake ka yi mata dukan munafurcin da ta yi,yadda gobe ba zata sake ba annamimiya!"

Khairi ta kama kallon Auwab a tsorace ganin ya ɗauko bulalar,kafin ta yi wani yunƙuri ya fara sauke mata,a gigice ta fara ihu ta na roƙon shi afuwa,da ta yunƙura za ta miƙe Inaaya ta saka mata ƙafa ta kifa, Auwab ya cigaba da labtar ta

Inaaya ba ta dakatar da Auwab ba sai da taga Khairi ta daina motsi,sannan ta karɓi bulalar ta ja hannun shi suka wuce ɗakin ta, zuciyar ta fari ƙal

Baiwar Allah Khairi kam ba ta dawo hayyacin ta ba sai bayan mintuna goma da wucewar su,ta na dawowa hayyacin ta ta fashe da kuka ta na tunanin wannan wane irin SIRAƊIN UƘUBAr ne kuma Allah ya ƙara jarabtar ta da hawa,yanzu ita ya zata yi da ranta? me yasa bata taɓa samun tsayayyen farin ciki a rayuwar ta bane?duk yadda rayuwa ta juya mata da daɗi bayan ƴan kwanaki sai ta sauya mata ta koma ainihin UMMIYO ɗin ta,ta miƙe cikin kuka da mamakin wai Auwab ne ya yi mata irin wannan dukan,ta miƙe da ƙyar shiga ɗakin ta ta kwanta ta na kuka,bata juma da shiga ba aka banko ƙofar,ta miƙe a firgice, Inaaya da ta shigo ta na jefa mata kallon tsana tace "na san zuwa yanzu kin fara gane kuskuren ki na shiga tsakani na da miji na ko?akan ki ya ɗaga hannu ya mare ni,ke,wai ke,ke dai! tabɗijam!how manage my lovely husband will slap me because of this villager?to wallahi kaɗan kika gani na abubuwan da na tanadar miki na azaba, makaranta kuma da aka saka ki da farko kin daina zuwa daga yau, kuma ba za'a biya ki kuɗin aikin ba,kuma dole kiyi "

Khairi ta sake fashewa da kuka mai tsuma rai ta sauko ta rarrafo gaban Inaaya ta durƙusa ta kama ƙafafuwan ta ta na kuka ta na faɗin "don girman Allah aunty ki taimaka min kar ki hana ni zuwa makaranta,na roƙe ki don Allah,komai kuka ce na yi zan yi,amma....."

Haurin ta da Inaaya ta yi ne ya katse mata sauran zancen ta ta na ta rizgar kuka,ta ɗora da faɗin "kar ki sake taɓa ni da wannan dirty hand ɗin na ki,maza tashi kije ki yi min aiki na"ta faɗa tana fincikar Khairi zuwa waje,ta hankaɗa ta, Khairi ta yi gaba ta faɗi,amma ta yi saurin tashi ta na kuka ta yi hanyar kitchen

Tsawon watanni biyu khairi ta kwashe a wannan hali ta na fuskantar azabtar wa kala kala daga wajen Inaaya da Auwab,haka kawai idan tsanar Khairi ta motsawa Inaaya za ta saka Auwab ya yi mata dukan mutuwa,gashi yanzu an raba ta da wayar ta ballantana ta gaggauta sanar da gida ko za'a kawo mata ɗauki,ita dai da wannan rayuwar wallahi ta gwammace hannun mum,wadda duk tsiya za ta samu ta ci,kuma ba'a jibga mata aiki kamar jaka,kuma ko babu komai akwai masu supporting ɗin ta a gidan,gashi ta na da ƴancin kewaye gidan ma,amma nan kuwa banda duka da azabtar wa babu abinda take ganewa,ta fice hayyacin ta ta fige ta lalace ta zama wata firgitacciya,ita kenan kullum da tsamin jikin duka,ko babu dukan ma saboda jikin ya saba ciwo yakeyi

Lallai Khairi yanzu kika hau SIRAƊIN UƘUBA 😭😭

Kada dai a manta VIP group ₦300 ne kacal

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a

🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee

*Young talented writers association (YOTA)*

Page 56

Dama ita ba ta damu da abinci ba,ta fi damuwa da bacci,to yanzu duka biyun ba ta samu yadda ya kamata,nan da nan kuma sai ga ciwon ciki da ƙirji,duk son khairi da bacci sai dare ya zo ya shuɗe bata yi ba don azaba,ta san Inaaya baza ta taɓa nemar mata lafiya ko ta saka a nemar mata ba,kuma a yadda ta fuskanta in dai a gaban Inaaya ta tambaye Auwab Inaaya sai ta hana,don haka sai da ta bari ya fita zuwa harabar gidan wajen motarshi ta tambaye shi ya kai ta asibiti bata da lafiya

Kallon ta kawai yayi,irin kallon da ta kasa fassara shi,ya ɗauke kai ya na faɗin "ki tambayi matar gidan,za ta sa a kai ki"ya na gama faɗar hakan ya shiga motar shi ya fice daga gidan,ta bi shi da kallo jikin ta a sanyaye,wannan ba wannan Auwab ɗin da ta sani bane watannin baya,wannan Auwab ɗin ne wanda ya gaggaya mata magana,wannan Auwab ɗin wanda yake mata kallon banza,ta goge ƙwallar idanun ta,a sanyaye ta koma kitchen ɗin ta ta zauna,ta san Inaaya baza ta taɓa bari ya kai ta asibiti ba,don haka ta haƙura ma

Gashi kuma abin takaici duk wannan abu dake faruwa babu wanda ya fi yi mata ciwo kamar nisantar ta da Auwab yayi,ba ta da fata da burin da ya wuce ya rungume ta ya lallashe ta kamar yadda ya saba yi mata a ɗan lokacin da sabo ya shiga tsakanin su,so take yi ma ko sau ɗaya ya ce mata"me ya faru ne alkhairi na?ko ba kya son na mayar da ke wajen Daddy? rigima ko alkhairi na?bakin tsiwar ya mutu ne?"ire-iren waɗannan tambayoyin yake yi mata duk sanda ya gan ta cikin damuwa

Idan kuma ta na cikin walwala ya rinƙa tambaya"yau dai alkhairi na labarin albasu nake so ko na Queen's College,yau dai bani labarin me kuka yi a makaranta ke da ƙawayen ki su Vanessa da Matilda?"ire-iren waɗannan abubuwan take yawan tunawa, shi yasa a kowanne lokaci cikin zubar da hawaye take

Babu ruwan su da ta ci abinci?ƙalau take?me yake damun ta? abu ɗaya ke haɗa su,ta tashi ta yi aiki idan ta yi kuskure Inaaya ta dake ta ta saka Auwab ya ƙara mata

Watanni huɗu kenan yanzu,ta rame ta lalace ta sake yin duhu,sai idanu zuru ziri,jikin ta kuwa kusan ko'ina shatin duka ne,a wannan lokacin ne ta ji chanjin yanayi sosai a jikin ta,banda jinyar da ta ɗauki tsawon lokaci tana yi yanzu ta na jin jikin ta nauyi,ga cikin ta da ya ɗaga,a kwanakin nan ta na ganin ɗagawar cikin amma bata taɓa damuwa ba,yanzun ma da ta ji motsi ya na yi mata yawa a cikin bata kawo komai ba,ta ɗauka duk larura ce kawai

A wannan ɗan tsukin tafiya ta kama Auwab zuwa Sweden,kuma shi kaɗai zai tafi,don haka ya tafi ya bar Inaaya da khairi a gidan

Ranar da ya tafi washe gari Inaaya ta bar gidan itama,ya zama saura Khairi kaɗai a gidan

Saboda ciwo Khairi ta daina da yawa daga ayyukan gidan tunda masifaffiyar bata nan,a wannan lokacin ne ma ta samu take ɗan yin baccin da ba ta samu damar yi ba lokacin da ta fara jinyar

Kwanan Inaaya biyu da tafiya Khairi na kwance a parlour bayan ta gama ɗan aikin da bata rasa yi ta ji ƙarar doorbell ɗin parlourn

Gaban ta ya faɗi sosai,don ta san babu mai zuwa daga matar gidan sai mai gidan,don haka ta miƙe zaune,cikin yanayin ciwo ta ce"a buɗe take ƙofar"

Da sallama ya shiga parlourn,cikin tsananin mamaki da gigita ta ɗaga kai ta na kallon wanda ko a mafarki ba ta taɓa tsammanin ganin shi yanzu ba, kallon ɗaurarriyar fuskar shi take yi wadda bata saba da fara'a ba sosai,shima cak ta tsaya na ƙare mata kallo,sam ta manta da wata jinya da take yi ta tafi a guje ta rungume shi da ƙarfi ta na faɗin "yaya AZAD!!!"sai kuma ta fashe da wani matsanancin kuka

Lumshe idanun shi ya yi ya buɗe,a ranshi ya na neman tsarin Allah daga shaiɗan, Sulaiman da ya shigo daga bayan shi ya janye ta cikin sauri,shima dai wannan fuskar ta shi mai cike da fara'a da wasa da dariya a ɗaure, shima ƙanƙame shi ta yi cikin kuka ta na faɗin "yaya Sulaiman ka ga yadda na koma,don Allah ku maida ni gida kar na mutu anan,yaya Auwab ba ya so na, aunty Inaaya ta tsane ni,babu wanda yake so na,sun raba ni da komai,sun hana ni zuwa makaranta,kun gani duk jiki na bulala,aunty Inaaya ta na saka yaya yayi min duka,ya hana ni abinci,bani da lafiya amma sun ƙi kai Ni asibiti,don Allah yaya ku taimaka min kar na mutu anan,yaya Auwab ya tsane ni so yake ya kashe ni,dashi da matar shi"a hankali Azad ya juya ya fice daga parlourn hawaye na wanke masa fuska,khairin shi dai da ya sani, lively khairin shi,mai surutu,mai tsokana, rigimammiya,idan ta juyo kuma akwai hankali da nutsuwar zance,ita ce ta koma haka,duk ta firgice,ta rame,ta yi baƙi,ya samu waje ya zauna ya jinginar da kanshi da bango,bai damu da hawayen da ke zubo masa ba

A hankali sulaiman ya zame ta daga jikin shi duk da ta ƙanƙame masa hannu cikin tashin hankalin kar ya bar ta,ya ja hannun nata zuwa kan sofa ya zaunar da ita,cikin kwantar da murya ya fara magana

"Kinga ki nutsu zamu yi magana,idan ba haka ba zamu yi tafiyar mu ni da babban yaya mu bar ki anan,idan baki daina kukan nan ba zamu tafi,kin ga babban yaya ma ya fita saboda kina kuka"

Kasa haɗiye kukan tabyi duk da ƙoƙarin ta na yin hakan, sulaiman ya haɗe rai ya ce "to na tafi,kuma ba zan dawo ba tunda ba za ki yi shiru ba"cikin tashin hankali mai tsanani ta zube gaban shi ta kama ƙafafuwan shi ta na faɗin "don girman Allah yaya sulaiman ku ji tausayi na,bani da gata sai yadda kuka yi da ni,ina cikin bala'i anan don Allah"

"To na ji little sister!now stop crying sai mu yi magana"

"Yaya na kasa daina wa ne,don Allah ka mayar da ni gida,kar na mutu anan don Allah"sulaiman bai sake magana ba ya kira Azad ya shigo cikin parlourn

Azad na shiga Inaaya da Auwab da suka haɗu a airport suka shigo parlourn,ta na ganin Sulaiman zuciyar ta ta yi baƙiƙirin,shi kam Auwab kallon su yake yi da wani yanayi a fuskar shi mai wuyar ganewa,duk da a cikin su ukun babu wanda ya damu ya gane

"Su waye ku?me ya kawo ku gida na?"a cewar Inaaya cikin yatsina fuska tana yi musu kallon rainin wayo

Azad ko kallon banza bai yi mata ba, sulaiman ne ya watsa mata kallon ƙasƙanci ya ja tsaki sannan ya sake mayar da kallon shi ga khairi da take kyarmar tsoro

Kafin ya yi magana Inaaya ta ja tsaki ta kalli khairi a wulaƙance,a nufin ta ta cusawa su Sulaiman haushi ta ce"ke ƴar ƙauye tashi ki haɗa mana ruwan wanka ni da miji na,mun gaji"

Ga mamakin su sai gani suka yi Khairi ta miƙe tsaye jikin ta na kyarma za ta tafi,Sulaiman ya cafke kafaɗar ta ya kalle ta cikin idanu, fuskar shi a ɗaure ya ce"idan aka sake ce miki ƴar ƙauye kika amsa to zan bar ki a garin nan"

Bisa ga mamakin Sulaiman sai ya ji Auwab ya ce"sulaiman ka ƙyale ta ta yi abinda aka saka ta,ba na son koyawa yaro raina babba,wannan ba tarbiyya bace"

Sulaiman ya yi masa kallon rainin wayo yace"oh haka aka yi?to bari ka ji,ko kai da kake matsayin miji a gare ta baka isa ka sa ta zubawa wata tsohuwar kilaki ruwan wanka ba,kai ko da kai da kake matsayin mijin ta a wannan halin"

Inaaya ta fashe da kukan kissa ta na rungume Auwab ta na complain wai Sulaiman ya ce mata karuwa,a zafafe Auwab ya ce "kar ka cuce ta kasa ta yi ta auren ta,don babu wata ƴa mace da ta isa na aure ta ta raina min mata"

Sulaiman ya yi tsaki ya kalli khairi ya ce"ke!maza ɗauko hijabin ki mu tafi"

Da azama khairi ta miƙe jikin ta har rawa yake yi za ta wuce ɗakin ta, Inaaya da baƙin ciki ya kamata,don bata so Khairi ta samu hutu tun yanzu ba,amma idan sun san wata ai basu san wata ba,don haka ta ce"ya ce fa idan ta fita a bakin auren ta"

Sulaiman ya kalle ta fuska a ɗaure ya ce"kar ki sake saka min baki a magana malama,ba dake nake ba,ki bari mijin na ki ya yi magana idan ya na da zarrar hakan"

"Eh haka na ce"a cewar Auwab

Azad ya kalli Auwab da sauri, Khairi kam ƙamewa ta yi ta kasa wucewa ta ɗauko hijabin, Sulaiman ya jinjina kai ya ce "ka rubuta a rubuce,don yau ko me za'a yi ba zata kwana a wannan gidan naka ba da yake ƙarƙashin mulkin zalunci"Inaaya ta kalle shi a raine ta taɓe baki,ta kalli Auwab da yake jiran decision ɗin ta sannan ta wuce ɗakin ta ta yago paper da biro ta miƙa masa ta na faɗin "ba su gate pass su bar min gida"

Khairi ta fashe da kuka ta na faɗin "yaya sulaiman saki na zai yi fa, don Allah ku ce ya yi haƙuri,don Allah yaya sulaiman"

"Idan kika sake magana a wajen nan sai na mare ki wallahi,shashasha!

Sai me idan ya sake ki?uwar me kika tsinana da gidan na shi?"

"Yaya Sulaiman ka taimaka min don Allah! wayyo Allah na!bani da sa'a a rayuwa ta, kullum a cikin ganin masifa da bala'i nake, rayuwa bata yi min daidai, wayyo Allah na,zan mutu yaya zuciya ta zafi take yi min,kowa ya tsane ni,yaya bani da gata!"ta kama sauke ajiyar zuciya da ƙarfi,daga Sulaiman, Azad har Auwab kallon ta suke yi,sai da tazo nan a maganar ta Sulaiman ya fizge takardar hannun Auwab da ya gama rubutawa sannan ya ɗaga khairi cak,ko hijabin nata bai jira ba suka yi waje, Azad na bin bayan shi ko kallon banza bai sake yiwa Auwab da Inaaya ba da take wani murmushin farin ciki ba

Daga nan wani babban asibiti suka nufa da Khairi a Boston,suna zuwa aka karɓe ta aka shigar da ita,suka zauna suka yi shiru a reception cikin tsananin tashin hankali da rashin madafa

Azad ne ya fara kallon sulaiman ya ce"na kasa gane me yake faruwa da Man, imagine wai Auwab matar shi ke juya shi, I know who is Auwab tun muna yara,bashi da hayaniya amma yana da ra'ayin kan shi,in fact,idan ka tuna ya sha fasa yin wasa ko wata fita idan ba'a bi ra'ayin shi ba,ban taɓa ganin mutum mai tsananin riƙo da ra'ayin shi irin shi ba,amma wai yau sai ga the same Auwab dai wanda na sani wai mace,mace ke juya gidan shi, I'm really confused sulaiman "

Sulaiman ya yi murmushin takaici ya ce"don't mind babban yaya, seems like ba laifin shi bane, whatever, Auwab yana buƙatar addu'ar mu kawai"

Azad ya ɗan yi tsaki ya na girgiza kai kafin ya ce"yanzu yarinyar nan duk yadda za'a yi muyi insisting su Daddy a mayar da ita makaranta,kar a sake yi mata wani aure a wannan tender age ɗin nata,inna sabuwa da ta kawo maganar ma kar ta san auren ya mutu"

Sulaiman ya gyaɗa kai cikin sanyin jiki,dukkan su sun yi jugum jugum zuciyoyin su cike da tashin hankali

Basu koma masaukin su ba sai bayan isha'i, dukkan su su biyun babu wanda ya runtsa saboda tashin hankalin yadda suka ga khairi

Washegari tun sassafe Sulaiman ya tafi asibitin saboda kiran shi da aka yi, shi kuma Azad bai isa ba sai wajen takwas na safe,a reception ya ga sulaiman cikin tashin hankali ya na girgiza kai,Azad ya yi saurin ƙarasawa gaban shi ya riƙe shi ya na faɗin"lafiya dai Sulaiman?"

"Akwai matsala yaya Azad!"gaban Azad ya faɗi,amma cikin dakiya yace"wacce iriyar matsala ce?"

Sulaiman ya ja numfashi ya furzar,ya ce"Ummul khair is twenty weeks pregnant!!!"

To pa🥺🥺🥺🥺murna💃💃💃💃 ko baƙin ciki 😥😥😥

Ko ma dai yaya ne Allah ya raba lafiya

Kada dai a manta VIP group ₦300 ne kacal

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a

🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee
*Young talented writers association (YOTA)*

Page 57

Zuru Azad ya yi masa ya na kallon shi ya kasa cewa komai,kafin a hankali ya ce"wacce Ummul khairi kake magana akai Man?"

"Ummul khairi dai wadda muka kawo nan jiya,matar ƙanin ka,kuma yaya na Auwab!"

Wani jiri ne ya kwashi Azad,ya dafa bango ya na kallon Sulaiman, da a ƙyar ya ƙara faɗin"to yanzu ya za'a yi kenan?"

"Ya za'ayi kuwa?kawai ayi mata treatment,tunda bayan cikin akwai ulcer da ƙarancin jini,idan ta ji sauƙi sai mu mayar da ita gida"

Shiru ya yi ya na kallon Sulaiman,kafin cikin sanyin murya ya ce"ba zai yiwu a cire cikin ba?"da sauri Sulaiman ya kalle shi ya ce"saboda me za kace haka?akan me?"

"Sulaiman mu faɗawa kanmu gaskiya,khairi ta yi ƙanƙanta da haihuwa at her age,baka tsoron kar ta samu wata matsalar?"

"Yara nawa ne suka haihu waɗanda ba su ma kai ta shekaru ba?ka ajiye wannan batun,kawai dai da cikin zamu yi amfani mu yi nasara akan shi da matar shi,bana son wani ya san da batun cikin ma banda iyayen mu"

Azad ya sauke ajiyar zuciya yace "to shikenan, Allah ya dafa mana"

Sulaiman ya amsa da"ameen "

Kwanan ta shida a asibitin ta samu sauƙi sosai,a ƴan kwanakin nan su Sulaiman sun yi matuƙar ƙoƙarin ganin sun mantar da ita damuwar ta sosai,amma abin tashin hankalin da suka fuskanta shine ta kamu da soyayyar Auwab mai tsanani,kuma ta na matuƙar kishin shi,yanzu kuma saboda rabuwar da ya yi da ita a wulaƙance abin ya ƙara yi mata yawa,don haka ta kasa dawowa daidai, kullum cikin kuka da damuwa take

Da ƙyar suka samu ta rage damuwar saboda yawan kwantar mata da hankali da sukeyi,kwanan ta goma sha biyu aka sallame su, washe gari suka hawo jirgi suka dawo gida

Abinda Ya ba su mamaki shine faɗan da Daddy yayi ta musu na cewa sun kashe auren Khairi,ashe wai Auwab ne ya kira waya ya ce Azad da Sulaiman sun je sun dage sai ya saki khairi,ya sake ta shine suka ɗauke ta,gashi kuma ba su dawo gidan ba sai bayan kusan sati biyu da sakin

Daddy yace ba zata zauna a gidan shi ba,a parlourn mum ta zube ta rinƙa gunjin kuka,ya ce baza ta zauna ba saboda ba zai yiwu Azad ya shirya maƙarƙashiya ya kashe auren ɗan uwan shi dake kanta shi ya aure ta ba

Waɗannan kalamai na Daddy sun tayar da hargitsi sosai a family ɗin,daga daddy har Abba ba su shirya saurarar Azad da Sulaiman ba,a cewar su tun da farko sun fahimci shi kanshi Sulaiman ya so Azad ya auri Khairi

Saboda wannan tashin hankalin Khairi ta yanke jiki ta faɗi,wadda ita laifin ta a wajen su Daddy shine sokwancin da tayi har aka kashe mata aure, Azad da Sulaiman ɗin ne suka ɗauke ta zuwa asibitin Dr jameel,aka yi admitting ɗin ta,ta sha baƙar wahala sosai,wannan karon mum da Beely,da ta haihu watanni uku baya ta samu ƴar ta mace sun tausayawa Khairi sosai,don har fakar idanun Daddy suka yi suka je suka ganta a asibiti, Nusra har kuka sai da ta yi da taga yadda khairi ta koma,duk da treatment ɗin da akayi wa khairin a Boston,ga oxygen an saka mata

Da ƙyar da suɗin goshi su Daddy suka yarda suka saurari su Azad,a parlourn Abba aka zauna,Daddy ya tambaye su dalilin su na zuwa gidan Auwab suka tayar da hargitsi,Azad batare da ya yi magana ba ya kunna voice record da ya yi musu tun lokacin da su auwab ɗin suka shiga ba tare da kowa ya ankara ba

Daga Daddy har Abba sun firgita da jin abinda yake faruwa a gidan Auwab,har gwara Abba dama ya san akwai matsala, suka yi shiru na ɗan lokaci kafin Abba yace

"Shikenan, Allah ya kyauta! Umar yarinyar nan babu mai sanin bata da aure sai mu ɗin nan,don inna ba zata bari ta yi karatu cikin salama ba,nan da next three months za'a juya sabon session,kawai ta koma makaranta ta ci gaba da karatun ta kawai, Allah ya bata lafiya"

Kallon juna Azad da Sulaiman suka yi,kafin Sulaiman ya yi gyaran murya ya ce"Abba akwai wani hanzari ba gudu ba"

Abba ya kalle shi ya ce"da wata matsala ne?"

"Abba Khairi tana da juna biyu na watanni biyar, dole zamu jira haihuwar ta kafin mu yanke wani decision game da rayuwar ta"

Daga Abba har Daddy suka sauke ajiyar zuciya a kusan tare,ga abin farin ciki amma babu damar farin ciki, Daddy ne ya fara faɗin "shikenan! Allah ya raba su lafiya ya bada mai albarka"suka amsa da "Ameen"

Daddy ya ci gaba da faɗin "don haka nan za ta dawo,za ta koma asalin part ɗin Auwab na gidan nan ta ci gaba da zama, za'a samar mata mai kula da ita,babu wanda zai san babu auren in sha Allah, ballantana akai ga inna Sabuwa, saboda abubuwan da kan iya zuwa ya dawo"dukkan su sun amince da wannan shawara

Haka taro ya tashi zuciyar kowa babu daɗi,daga Azad har Sulaiman babu wanda ya sanarwa da mahaifiyar shi cikakken abinda ya faru,su dai sun ce Khairi da Auwab sun rabu, Khairi kuma tana da ciki kuma Auwab ɗin bai sani ba

Kwanan Khairi biyar a asibiti aka sallame ta, Daddy da Abba sun je,tana ganin su ta fashe da kuka sosai,da sauri Abba ya rungume ta yana bubbuga bayanta,sun ɗauki lokaci suna lallashin ta da yi mata alƙawura,sun ji tausayin ta sosai,don zuwa yanzu Khairi rigimammiya mai kuka da ihu ta koma wata silent Khairi,sai dai hawaye kawai da ajiyar zuciya da shashsheƙar kuka,gaba ɗaya ta lalace ta sake komawa ƴar firit,dama gashi ba ta iya cin abinci sai Nusra da Surayya dake yawan zuwa mata sun matsa mata take iya ci kaɗan,su kansu cikin jin tsananin tausayin ta suke

Gidan Abba aka maida ita aka samo mata wata babbar mace aunty Hafsa take kula da ita,Ammi da mifra matar Sulaiman sun shiga sun ga jikin ta,har yanzu dai khairi babu baki,ga yawan tunani,rabon ta da wani abu wai shi murmushi kuwa ta manta lokacin

BAYAN WATA ƊAYA

"Little meyasa bakya son zuwa asibiti ne?ba ki san situation ɗin ki ya na buƙatar tsayawar likita ba?ko ba kya so ki haifa mana healthy baby ne?"ya ƙarasa faɗa fuskar shi da ɗan murmushi

Wani banzan kallo ta watsa masa ta ɗauke kai ta na ci gaba da cin yalon da ya kawo mata,dama a kwanakin nan zuciyar ta a kusa take,abin masifa ko kuka ba ya yi mata wahala,ya yi ɗan murmushi sannan ya miƙe yace"to ni dai bari na tafi tunda na yi magana an yi min banza,dama gobe zan koma Australia,shiyasa na zo,kuma cikin rashin sa'a kuma gashi ba'a maraba dani"

Hawaye ya ciko mata idanu,ta kalle shi ta ce"kaima tafiya za kayi ka bar ni Kamar yadda yaya sulaiman ya tafi ya bar ni?"

"Babu mai tafiya ya bar ki little sister!aiki ya kai Sulaiman Lagos kuma zai dawo very soon,ba ki ga matar shi ma bai tafi da ita ba?"

Hararar shi ta yi ta ce"Kai kuma na san idan ka tafi baza ka dawo ba don matar ka ta na can"ɗan zaro idanu ya yi ya na murmushi ya ce"waye ya ce miki ina da mata?"

Kallon ka raina min hankali ta yi sannan ta ci gaba da cin yalon ta,wanda a yanzu bata da kamar shi,ya yi ƴar dariyar rigimar Khairi,gaba ɗaya yanzu ta zama wata masifaffiya,ya ce"ki tambayi Sulaiman ki ji, tuntuni mun rabu da mata ta "

Wannan karon cikin fushi take kallon shi,ta ce"itama rabuwa kayi da ita da ciki ko bayan ka yaudare ta ta yi tunanin ka na son ta ko?"sunkuyar da kai Azad ya yi cikin jin tausayin khairi,har yanzu zuciyar ta bata gama manta abinda Auwab ya yi mata ba,kafin ya ɗago ya kalle ta a sanyaye,sai kuma dariya ta kama shi ganin yadda ta tsatstsare shi da manyan idanun ta, waɗanda a yanzu sun ƙanƙance saboda kumburin fuskar ta,a sanyaye ya ce

"Ita lokacin da ta samu nata cikin ina bata kulawa sosai,kuma ina matuƙar son ɗana,amma ita bata so,don haka sai ta zubar da cikin"ya ɗan yi shiru cikin jimami,har yanzu idan ya tuna wannan asarar da Fadeela ta yi masa sai ya ji wani ɗaci a maƙogwaron shi,yaci gaba"tun daga lokacin muke ta samun matsala,har muka rabu"

Tausayin shi ya kama khairi,amma sai tace"to wai da bata gaya maka bata son haihuwar ba sai da ka aure ta zata zubar maka da ciki?"

"Kin san ni bani nace ina son ta ba,mummy na ce ta bani auren ta,don haka ba auren soyayya muka yi ba,ta bani wahala sosai kafin mu rabu"Khairi ta yi tagumi ta na kallon shi, cikin tausayawa ta ce

"Allah sarki yaya na,kaima ashe ka sha wahala"ya yi murmushi ya ce "akwai wahalar da na sha wadda tafi waccan,amma alhamdulillahi komai ya wuce khairi,yanzu dai na ɗage tafiyar zuwa Australia gobe,zan zo na kai ki asibiti for check up "

Narke fuska ta yi ta ce"to yaya amma ba za su yi min allura ba ko?ni bana son allura"

"A haba!allura ai ta marasa jin magana ce, waɗanda idan aka ce musu suyi sai su ƙiyi"shiru ta yi fuska a narke ta na kallon shi,don ko tantama babu da ita yake,don Khairi kam cikin nan banda rigima da daru har da kafiya ya saka ta,don ma yanzu ta fara cire Auwab a ranta

Murmushi ya yi ganin yadda ta narke fuska ta na son fashewa da kuka,ya ce"haba Dr khair albasu tamu,yanzu idan muka zo kiyi mana allurar haka zaki rinƙa yi mana kuka?"

Ta tura baki gaba ta ce"to ba kaine kake tsokana ta ba?"

"Ni fa ba da ke nake ba,ni ban tsokane ki ba "ita dai dai sai tura baki take yi,ya yi murmushi ya ce"mum tace na kawo miki tuwon dawa da kika ce mata kina so,amma gashi na kawo kin ƙi ci,ko bakya so ne?"nan da nan fuskar ta washe ta ce"ina so mana,man shanu nake jira idan Abba ya zo dashi sai ya bani,ko cikin dare ne sai naci abu na"ya miƙe tsaye ya ce"da kin gaya mata ai da ta saka an kawo Miki,bari na je zan turo Ma'aruf ya kawo Miki yanzu"ta sake washe baki ta na faɗin"na gode yaya na,ka gaida min da mum da aunty,ka ce suma na gode musu"Azad ya yi ɗan murmushi ya fice daga ɗakin

Mama Khairi Allah ya raba lafiya 🤰 🤰🤰🤗😌😊

Kada dai a manta VIP group ₦300 ne kacal

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a

🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee
*Young talented writers association (YOTA)*

Page 58

Kamar yadda Azad ya yi alƙawari khairi ba ta tashi daga inda take zaune ta na cin yalon ba Ma'aruf ya yi sallama a parlourn nata,ta ɗaga kai ta na kallon shi ta na murmushi,shima murmushi yake yi,cikin tausaya mata yace"sannu maman biyu"don cikin nata babu daɗewa da dawowar ta daga US ya fara girma sosai,sai ya yi kama da na ƴan biyu

Ta yi murmushi ta ce "sannu da zuwa yaya Ma'aruf ,ya su mum da aunty?"

"Dukan su lafiya lau,sun ce a gaishe ki,ya jikin?"

"Jiki alhamdulillahi,ya makaranta?"

Ya zauna ya na faɗin "makaranta alhamdulillahi saura kaɗan,na kira wayar ki ba ta shiga,gashi babban yaya ya ce na amso miki man shanu a wajen mum"ya miƙa mata man shanun a wata madaidaiciyar roba

Khairi ta amsa ta na murmushi ta ce"na gode Allah ya saka da Alkhairi,waya ta wani lokacin damu na take yi shi yasa nake kashewa"Ma'aruf ya ce"to Allah ya kyauta, ni zan wuce"Khairi ta ce"to na gode sosai yaya Ma'aruf,ka gaishe su"ya fice ya na amsawa da za su ji

Washe gari wajen ƙarfe tara na safiya Azad ya zo ya kai ta asibiti,sai surutu take ta zuba masa,masu ma'ana da shiririta,kuma idan bai bata amsa ba sai ta nemi saka masa kukan taɓara,dole ya biye mata da bata full attention a labaran shirirtar da babu abinda yake ganewa a ciki

Yanzu khairi ta sake sosai saboda irin kulawa da gatan da take gani har daga wajen mum da ta tsane ta a baya, ba'a maganar su yaya sulaiman,matar shi ce dai sama sama suke da ita, wannan baya damun ta don bata cikin lissafin ta

Regular check up aka yi mata sosai,har yanzu akwai ƙarancin jini a tare da ita,sannan kuma ulcer da take yawan sata ciwon ciki,don haka aka yanke shawarar yi mata allurar ulcer

Ihu ta saka ta kama diddira ƙafa ta na faɗin "yaya na ka ji wai zai yi min allura,ni dai ba na son allura "Azad ya kalle ta da kulawa ya ce"sai mene kike so Dr khairi na? faɗa min yanzu yanzu a musanya miki shi da allura"ta yi raurau da idanu ta ce"gashi kuma bana jin daɗin magani,amai yake saka ni"shi kanshi likitan da ya duba ta Dr Jamil sai da ya yi ƴar dariya ballantana Azad,ta kalle su idanun ta sun yi rau rau,sannan ta juya cikin sanyin jiki za ta fice daga office ɗin, Azad ya janyo hannun ta ya na murmushi ya ce"haba Dr khairi tamu mallakin albasu,waye ya taɓa autar Daddy ne?"ta tura baki hawaye ya na ɓalle mata ta ce"kun mayar da ni mahaukaciya sai dariya kuke yi min "Dr Jamil ya yi murmushi ya ce"ba dariya muka yi miki ba fa,kawai yadda kika faɗa mana gaskiya ne ya burge mu,mun yi dariya ne don farin ciki da alfahari ƙanwar mu ba maƙaryaciya bace,ko?"ta gyaɗa kai ta na ɗan murmushin yaƙe,don dai bata da hujja ne,amma ta san raina mata hankali aka yi

Dr Jamil ya ce"good mother!to yanzu ya kike so ayi?ko a rubuta Miki magani?"shiru ta ɗan yi suna kallon ta,kafin ta gyaɗa kai a sanyaye

Tare suka jero suka fito suna hirar baby idan ya zo yadda za'a tarbe shi,daga wajen karɓar result na scanning suke,an tabbatar da baby boy ne,ta kalli Azad ta na murmushi tace"yaya Azad ka san me?"

Ya kalle ta da kulawa ya ce"a'a sai kin faɗa little sister"

Ta ce"yaya Azad idan na haihu ka san sunan wa zan sakawa baby na?"ya ce "a'a sai kin faɗa "ta yi murmushi ta ce"sunan ka zan saka masa in sha Allah "ya kalle ta ya na ƙoƙarin buɗe motar shi ya ce"wow!amma na ji daɗin wannan karar da akayi min,amma meyasa za'a saka suna na?"

Ta shiga in da ya buɗe mata ta na murmushi,shima ya shiga ya tayar da motar suka nufi gate ɗin asibitin

Khairi ta na kallon shi,a sanyaye ta ce"ka yi min komai a rayuwa,a duk sanda nake cikin matsala you will be there for me,ka nuna min ƙauna da kai da yaya Sulaiman,kun zamar min bango,don haka......"

"Huuuuuuuu! Dr khairi na kuka zata yi,taɓararriyar Daddy kawai,bari kawai na koma asibiti a chanja mana maganin nan da allura,dama na san ba sha za kiyi ba,amma allura kam da kai na zan kai ki ayi miki ko?"ya yi saurin katse ta jin zata karya masa zuciya,don idanun ta har sun fara tara hawaye

Tura baki ta yi ta na hararar shinl,ya yi ɗan murmushi ya na girgiza kai, dama so yake ya mantar da ita maganar da ta fara,ya ce "ni fa da wasa nake yi,sunan babyn mu maimakon a saka suna na idan ana so a burge ni sai a bar ni na zaɓa masa suna"

Ta kalle shi ta ce"to na baka zaɓi"

"Good! thanks very much little sister!idan namiji ne kamar yadda muka gani Abubakar za'a sanya masa,idan mace ce kuma HABIBA!!!"

Sanda Azad yake ambaton Abubakar ta yi murmushi sosai,amma ya na cewa Habiba annurin fuskar ta ya ɓace a take,ta girgiza kai tace"baza'a sanya wa ƴa ta Habiba ba!"

Mamaki ya kama shi,ya ce"saboda me to?"

"Saboda mahaifiya ta ta banzatar da ni,ta wulaƙanta ni,ta tafi bata sake waiwaya ta ba,tun ina kukan rashin ta har na haƙura,ban san daɗin uwa ba,ban san daɗin uba ba,mahaifi na ya rasu,ta san da hakan amma ko sau ɗaya bata taɓa zuwa ta ganni ba,na rayu cikin maraici da kaɗaici,da datti da ƙazanta gami da jahilci "ta ɗaga kai ta kalle shi tace"duka ita ce sila,duk wata UƘUBA da na fuskanta a rayuwa ta na san tana da kamasho a ciki"

"Matsalar ki Khairi ba ki da uzuri,kin taɓa bincikar yadda ta bar gidan ku?"Khairi ta ɗago kai fuska a ɗaure ta na kallon shi,ta ce"kai ka taɓa?"

"Inna ce take so ta yi mata auren dole taƙi yarda,shine inna ta ce baza ta tafi dake ba"

"To meyasa bata taɓa zuwa ta ganni ba?"

Ya ɗan yi shiru kafin ya ce"tana da hujjar ta,ya kamata muyi mata uzuri"khairi ta kawar da kai kawai bata sake cewa komai ba

Suna sauka a maimakon ya wuce da ita part ɗin ta sai ya wuce part ɗin Ammi

Da sallama ya shiga,Ammi dake shigowa cikin parlourn itama ta amsa sallama da murmushi a fuskar ta ta na kallon ƴar darun tasu da ta kwaɓe fuska,da alamu wani abun ne bata so amma Azad ɗin zai yi mata, musamman yadda Azad ɗin ya ɗauke kanshi ko kallon arziƙi bai yi mata ba

Waje ya samu ya zauna ya na gaida Ammi ta na amsawa da fara'a, Inaaya da take zaune daga ɗan gefe da duk ba su kula da ita ba sai kallon cikin jikin khairi take yi idanun ta waje saboda tsananin mamaki da kiɗima,ita kam khairi sai kumbure kumburen rigima da taɓara take yi bata san ma da ita a wajen ba

Azad ya na kallon Ammi cikin girmamawa ya ce "Ammi ga magungunan little sister,na san idan na bata baza ta sha ba,yanzu kuma na san mai kula da ita bata nan,don haka Please Ammi gashi na kawo Miki,ki rinƙa tabbatarwa ta sha,idan taƙi zuwa ta sha kawai kiyi min waya,dole na mayar da ita ayi allura"

Diddira ƙafa ta kama yi ta na tura baki tana faɗin "ni dai bana son allura,Ammi kice masa ni kar ya kai ni ayi min allura"

Ammi ta kalle ta sosai tace"idan ba kya son allura sai dai idan za ki rinƙa cin abinci sosai,sannan kuma kizo ki rinƙa shan maganin ki regularly,if not,ni da kaina ma zan mayar dake ayi miki allurar"Azad sai kallon yadda take kwaɓe fuska yake yi kamar zata yi kuka yana ɗan murmushi,daidai nan Auwab ya shigo da sallama

Kamar an yi ruwa an ɗauke haka khairi ta yi ɗif,gaba ɗaya yanayin ta ya sauya,Azad ya kalle ta da ɗaurarriyar fuskar shi,gani ya yi jikin ta ya fara kyarma,a ɗan fusace ya ce"wuce na mayar dake part ɗin ki"babu musu ta wuce ya bi bayan ta ko kallon sashen da Auwab yake bai yi ba suka nufi part ɗin khairi, Auwab ya bi su da kallo kawai

Suna shiga ta fashe da kuka sosai ta zube a ƙasa,da sauri ya ɗago ta ya na kallon ta fuska babu fara'a ya ce"kashe kanki kike so kiyi saboda shi?ba ki gani ba rayuwar farin ciki yake yi shi da matar shi?ke kuma zaki yi ta ƙuntata kan ki a dalilin shi? menene hakan khairi?ko so kike mu da muke ƙaunar ki ki jefa mu cikin damuwa?"

Cikin wani irin kuka ta ce"na kasa mantawa dashi yaya Azad!ya cutar dani,na tsani kaina,na tsani komai na rayuwa,na tsani....."

"Kin ga!wallahi idan baki daina ɗorawa kan ki damuwa akan wanda bai damu dake ba zan ƙyale ki! Khairi nawa kike da zaki bari soyayyar wani ta kassara miki rayuwa? Khairi mun sha wahala sosai kafin mu samo lafiyar ki,amma saboda wanda yana can bai san yadda muka yi fafutuka da lafiyar ki ba za ki sake saka jefa kanki cikin masifa ba, ki koma cikin hankalin ki Khairi,saboda ke fa na ɗage tafiya ta ta Australia da ya kamata na tafi tun last week na zauna duk don mu samu kwanciyar hankalin ki,amma yanzu saboda mutum ɗaya kina so ki mayar mana da aiki baya,why khairi why?"

Allah sarki 🥹 soyayya ba karya ba ce 😥

Kada dai a manta VIP group #300 ne kacal

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a

🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️ Nusy bee

*Young talented writers association (YOTA)*

Page 59

"Yaya ka yi haƙuri don Allah,na daina, wayyo zuciya ta zafi take yi min,zan mutu yaya,don Allah,don Allah......."ya yi sauri toshe mata baki ya zaunar da ita,shi kan shi hankalin shi ya yi masifar tashi

Kallon ta ya yi saurin yi ganin ta yi baya za ta faɗi,yayi saurin taro ta ya na girgiza ta,amma numfashin ya tafi,ya yi saurin kwantar da ita ya ɗauko water bottle ɗin ta ya buɗe ya yayyafa mata,ta sauke ajiyar zuciya ta na lumshe idanu ta na buɗewa

Azad ya ɓata sama da awa ɗaya ya na ƙoƙarin kwantar mata da hankali da bata ƙwarin gwiwa,har sai da ya ga hankalin ta ya kwanta sosai,ta samu nutsuwa ta daina kukan sannan ya yi mata sallama ya tafi, lokacin ma mai kula da ita aunty Hafsa ta zo

Ranar haka khairi ta wuni sukuku gaba ɗaya bata da kuzari,ko da Sulaiman ya dawo yazo wajen ta su gaisa kallo ɗaya ya yi mata ya san ta gamu da Auwab da suka zo shi da matar shi

Shima dai sulaiman ya yi ƙoƙarin ganin ta saki ranta,ganin yadda suka damu da rashin walwalar ta yasa ta danne ta cigaba da harkar gaban ta

Washegari da yamma Inaaya ta na zaune a ɗakin da aka sauke ta a part ɗin Ammi,kamar ance ta leƙa window ta hangi Khairi ta na ɗan zagayen ta na masu ciki,cikin ya fito sosai,duk da bai yi mata muni ba amma kowa ya ganta ya san ciki gare ta,ta yi kwalliyar ta cikin doguwar riga peach colour da ɗan madaidaicin hijabin ta iya ƙugun ta fari wanda ya yi mata kyau,ƴar fuskar da ke fito da tsantsar ƙuruciyar ta ta yi fes da ita babu kwalliya ko ɗaya a fuskar ta, Inaaya wani irin zafi da baƙin ciki ne ya rinƙa taso mata,dama jiya da ƙyar ta iya bacci saboda baƙin cikin ganin ciki a jikin khairi,ta kira Auwab ta yi ta zazzaga masa masifa,amma ya nuna mata shi bai san da wani ciki ba

Ba tare da tunanin komai ba ta faki idanun Ammi ta fito daga ɗakin nata ta fice daga part ɗin zuwa backyard inda khairi ke ta ɗan zagaye tana jin karatun Alqur'ani da Sulaiman yace ta yawaita ji saboda zai rage mata damuwa,kuma alhamdulillahi ya na rage mata damuwar

Ji ta yi an janyo ta baya,ta waigo da sauri ta na kallon Inaaya da bata san ma da ita aka zo ba,sai da gaban ta ya faɗi da ta tuna irin azabtar da ita da ta yi,amma ko a fuska ba ta nuna mata komai ba,sai kallon ta kawai take yi

"Yarinya ƙarama Kamar ke wai kin san namiji a shekarun ki,har da ciki"sai kuma ta kwashe da dariya,ta ci gaba"wato ke yanzu kina ganin kinyi ƙwarin da za ki iya haihuwa har ki goga dani ko ki koma gidan mijin ki ko me?shegiya ƙaramar kilaki"

"Baiwar Allah me na yi Miki za ki saka ni a gaba kina zagi na?ko dai so kike ki janyo wa kanki abinda yafi ƙarfin ki?"Khairi ta faɗa cikin fusata da tsiwa

Tsananin mamaki ya hana Inaaya magana,wai Khairi da take mata magana ta na kyarma ita ce tsaye gabanta ta na yi mata rashin kunya tana gaya mata magana, Khairi bata sake Binta kanta ba ta kewaye ta zata wuce,ba ta ankara ba ta ji Inaaya ta shaƙo ta a fusace ta ɗauke ta da mari,ta na huci ta ce "ke har kin kai darajar da zan rinƙa yi miki Magana amma ki gaya min magana ki wuce,to ban zo ɓata lokaci ba,ba na son sake ganin ki a nan tunda ba gidan ubanki bane,ki tattara komai naki ki koma ƙauye inda......"bata samu ƙarasawa ba saboda dukan da Khairi ta rufe ta dashi, dama khairi tuntuni akwai saurin fushi, ballantana ga cikin nan da abu bai kai na ɓata lokaci ba ma sai ta kwana ta wuni ta na ɓacin rai,masifa kam ta zama ƙawar ta,amma azo har inda take a takale ta?inaaa!!jefar da wayar ta ta yi ba tare da ta sani ba ma ta hau Inaaya da duka kamar ba mai cikin watanni shida ba,da farko Inaaya niyyar ta ta ƙwaci kanta,don gani take ba ƙaramar gazawa ba ce a wajenta khairi ta dake ta,amma khairi ta bata mamaki irin wanda bata taɓa tunani ba,don duka khairi take yi mata kamar an aiko ta

Ganin babu dama ya sa Inaaya ta fara ihu ta na kiran Auwab,kusan lokaci ɗaya suka iso shi da Haidar da ya zo wajen Khairi ya kawo mata gandar da mum ta saka a dafa mata

Auwab ya yi yin duniya Khairi ta saki Inaaya amma ta ƙi,gashi tsoron taɓa ta yake yi kar yayi mata illa,Haidar kuwa da ya tabbatar Inaaya ce a ƙasa sai ya yi saurin ja baya ya na magana"ke Khairi sake ta,ki yi haƙuri ki daina dukan ta,kin ga bake kaɗai....."maganar shi ta ɗauke saboda marin da Auwab ya saukewa Khairi,ta saki Inaaya ta yi taga taga za ta faɗi, Haidar ya yi sauri ya riƙe ta ranshi ya na wani irin ɓaci

Dafe fuskar ta ta yi ta fashe da kuka ta na faɗin "Allah ya isa na mugu kawai,ba zan taɓa yafe maka ba"Auwab dake rungume da Inaaya jikin shi na rawa ya ɗaga kai a sanyaye ya kalli Khairi da haidar ya ɗaga ta ya riƙe mata hannu ya na kallon ta ya ce"Allah ya saka miki, Allah baya zalunci ba ya lamuntar zalunci"ya na kaiwa nan y aja hannun ta a fusace suka bar wajen tana kuka

Kai tsaye parlourn Ammi suka wuce, Ammi da Sulaiman suka bi su da kallo ganin khairi da ta fita ɗazu ta na ta fara'a yanzu kuma gashi ta dawo da kuka,shi kanshi Haidar ɗin fuskar shi a ɗaure

Wajen Sulaiman ta nufa ta na kuka ta nuna masa gefen fuskar ta ta na faɗin "yaya ka gani ya mare ni saboda matar shi,kuma ita ce ta fara tsokana ta"nan da nan ran sulaiman ya ɓaci don ya gane Auwab take nufi,kafin ya kai ga magana sai ga Auwab da Inaaya sun shigo, sai wani narkewa Inaayan take yi ta na kukan shagwaɓa

Ta gaban su suka zo za su wuce,har sun gota su Sulaiman ya miƙe fuska babu yabo babu fallasa ya sha gaban su, Inaaya sai watsa masa wani mugun kallo take yi cike da tsanar shi,don kaf dangin Auwab bata jin akwai wanda ta tsana kamar Sulaiman

"Ban san me Ummul Khairi ta yi maka ka mare ta ba,ban damu da akwai dalili mai ƙarfi ko babu ba, whatever,duk mai hankali da iymani indai ya ga Khairi dole ya tausaya mata,Allah ya ƙaddari auren ta a ƙananun shekarun ta,ya kuma azurta ta da ciki,amma don rashin iymani an gallaza mata sannan an yi mata sakin wulaƙanci,alhakin hakan ya na tafe,ka san shi kwikwiyo ne baya gajiya da bibiyar mai shi, ni ba duk wannan ba,kar ka sake ɗaga hannu ka mari Ummul Khairi ko me tayi,take this as last warning Auwab!I repeat it kar ka sake marin ta,kai ko baƙar magana ko dunguri,babu ruwan ka da rayuwar ta,da kai da matar ka kuyi abinda ya kawo ku ku bar gidan nan babu wanda zai shiga sabgar ku,amma kuma ku kiyaye, otherwise mutuncin ku ya zube a banza!"

Mifra da ta shigo parlourn sai kallon mijin nata take yi da wanda ta san suna ƙaunar junan su fiye da ƙima amma saboda Khairi yake gaggaya masa magana,ta harari Khairi da ke zaune a gefe ammi ta na lallashin ta,wani haushi da kishi ya sake turnuƙe ta ganin Ammi ta na mata raɗa a kunne ta na ta murmushi ta na goge ragowar hawayen fuskar ta,ta san ko ita ba'a nunawa ƙaunar da ake nunawa Khairi a matsayin ta na ƴar uwar Ammi ɗin ma

Auwab ya saki baki ya na kallon Sulaiman har ya gama sannan ya ce"Sulaiman ni kake yiwa warning?ni kake faɗawa magana? Ammi ni yaron nan yake gayawa magana?"

Sulaiman ya ce "whatever!na dai gaya maka,ka sake taɓa ta ka gani"

"Da wannan hayaniyar ai da rama mata ka yi sai na tabbatar da baka da kunya"a cewar Auwab a fusace, Inaaya sai kallon su take yi tana jin daɗin abinda ke faruwa

Sulaiman y ayi ɗan murmushi ya na kallon Ammi da ta kama hannun khairi ta miƙar da ita tsaye suna zaga parlourn,ya mayar da kallon shi ga Auwab ya ɗan sosa ƙeya ya ce"kuma fa ka kawo point"kafin Auwab ɗin ya ankara Sulaiman ya saukewa Inaaya mari,sannan ya kalli Auwab ya ce"idan kana da zarra ka rama mata!"cikin kwanciyar hankali ya juya zai bar parlourn

Ammi,Haidar, Inaaya, Khairi,Mifra da Auwab kowa sai da yayi sak saboda abinda ya yi wa Inaaya,a tsorace Khairi ta kalli Auwab sannan ta kalli Haidar da ya kashe mata ido ya na yi mata murmushi,ta sunkuyar da kai ta na jin yadda Inaaya ta fashe da kuka,Ammi ta na yi wa Sulaiman magana amma tuni ya fice,shima Haidar ya ja hannun Khairi,ya biya ta part ɗin ta ya ɗauko gandar ta suka shiga motar shi suka fice daga gidan,ya na murmushi ya ce yau dai bari ya kai ta wajen su mum da aunty

Yacin Sulaiman ina yin ka💃🥱😆😅✌️😁🤭🤗🫣🙈sai da kai ɗan ƙunar baƙin wake😅😅😎😁🤣🥱

Kada dai a manta VIP group #300 ne kacal

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a

🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee
*Young talented writers association (YOTA)*

Page 60

Sulaiman kuwa ya na shiga part ɗin shi mifra ta biyo bayan shi fuska a ɗaure,kanshi ta zo ta tsaya ta na faɗin "officer menene ma'anar abinda ka yi yanzu?"

Kallon ta ya yi da confused face ya ce"me kenan?"

"Seems like son yarinyar nan kake yi officer,in banda haka menene za ka...."

"Matsalar ku mata akan kishi hauka da rashin tunani!

Khairi matsayin su Surayya gare ta a waje na,kuma hakan ba zai taɓa chanjawa ba,dole na tausaya mata saboda irin gararin rayuwar da ta tsinci kanta ko da ace ita ba jini na ba ce, ballantana har yanzu khairi ta na matsayin matar yaya na Auwab ne saboda ba ta gama iddar shi ba

Kuma ma banda abin ki ko da zan so Khairi ta auri wani ba Auwab ba ai Azad ne,bani ba,ko lokacin da aka rinƙa tashin hankalin nan kin ji an ambaci ina son ta da aure?"a sanyaye mifra ta girgiza kai, sulaiman yace"don haka ni bana daga cikin mazajen da nake sakawa Ummul Khairi rai ta aura, beside,yanzu Ummul Khairi babu batun aure a tsarin ta ma,har yanzu da take shirin haihuwa shekarun ta na haihuwa sha shida ne,kinga ko Nusra da Surayya ta girma ma sha takwas take,to ko Surayya yanzu karatu take ballantana ita,don haka feel free madam, Ummul Khair a yanzu tausayawa take buƙata daga gare mu ba jin haushi ba"

Sosai bayanin Sulaiman ya sauƙaƙawa Mifra ranta,har ta tuna yadda suka dawo da Khairi ɗin,a sanyaye ta ce "to Allah ya sauke ta lafiya, Allah ya bata mai sauƙi"sulaiman ya yi murmushi ya ce"Ameen,ko ke fa?"

Ta yi murmushi ta na kallon jaririyar ta dake kusan sa'ar ƴar Beely wadda ta ci sunan Ammi suke kiran ta da Anam,a sanyaye ta ce"ita ma nan da some months ta na da baby kamar Anam ko?"

Sulaiman ya yi ƴar dariya ya ce"eh mana,ko bata isa bane?"

"Gaskiyar magana ba ta isa ba wallahi, sixteen years fa,wata ma ko secondary school ba ta gama ba ai"

Sulaiman ya yi murmushi cike da takaici ya ce"ita ma daga js2 ta rubuta placement, kawai sai aka yi mata aure"Mifra ta sauke ajiyar zuciya ta ce"to Allah ya ba ta mai albarka "Sulaiman ya amsa da"Ameen"

LUGARD ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA

"Haidar me yasa ka kawo ta?me yasa baka gudun abin magana?kana son mahaifin ku ya yi ta mana faɗa ko?"

Murmushi Haidar ya yi ya na kallon mum da ke jefa masa tambaya ta na tsatstsare shi da idanu,ya ce"matsala aka samu acan gidan Abba,ƴar hatsaniya ta haɗa Khairi da matar Auwab,sai Auwab ya mari khairi,sai........'

"Mari?mari kuma?ka ji abinda kake faɗa kuwa Haidar?yanzu duk wanda ya mari Khairi ya ce ya mari me fisabilillahi in dai ba babu zuciya a ƙirjin mutum ba?"

Murmushin takaici ya yi yace"maybe babu zuciyar ne,kin ga mum,ni ba wannan ba ma,so nake ki kyautata mata yadda ɗanki mafi soyuwa a gare ki zai yi farin ciki,a yanzu na san ya haƙura da Khairi,amma farin cikin ta shine burin shi har yau"

Jikin mum ya yi sanyi sosai,ta kalli Haidar tace"Aliyu na yi nadamar nunawa yarinyar nan ƙiyayya,ba tayi min komai ba sai biyayya,bata da matsala,yanzu gashi na nakasa ɗana saboda..."ta kasa jurewa ta fashe da kuka, Haidar ya yi sauri ya taso zuwa inda take yana bata baki

Ya ce"mum don Allah ki manta baya,ki fuskanci yanzu, Allah ya yi sai Khairi ta fuskanci jarrabawar rayuwa,kuma alhamdulillahi duk da ƙarancin shekarun ta bata gaza ba ta yi nasara,ki yi mata addu'a Allah ya raba ta da cikin jikin ta lafiya"

Mum ta yi murmushi ta ce"Ameen,Allah ya raba su lafiya "ya miƙe ya na murmushi ya fice daga parlourn

KHAIRI

Khairi kam bayan sun gama gaisawa da mum sai ta wuce part ɗin aunty Naja ta na ta mamakin yadda mum ɗin take son ta yanzu,a wajen aunty Naja ta ci abinci ta yi sallar maghriba,sannan ta zauna suna ta hira har wajen tara na dare

Sallar isha'i ta yi sannan ta miƙe gaban ta ya na faɗuwa ta koma part ɗin mum,kai tsaye ɗakin beely ta nufa,inda yarinyar ta mai suna Yusaira take ta faman tsala kuka

Da sallama ta shiga,sai dai ba'a amsa mata ba,don haka ta shiga don ɗaukar Yusaira,don daga jin yadda take kuka ta san babu kowa a ɗakin

Amma ga mamakin ta sai ganin aunty Beely ta yi ta yi tagumi ta lula duniyar tunani, da mamaki ta ƙarasa kusa da ita ta na kiran ta"aunty Beely!aunty Beely!!aunty beeeelyy!!!"

Firgigit ta yi ta na kallon ta,sai kuma ta yi murmushi ta ce"maman unborn,yau ke ce a gidan namu?"

Cikin rawar murya Khairi ta ce "aunty Beely me yasa kike kuka?"Beely ta kasa controlling hawayen ta ta fashe da kuka sosai,itama Khairi kuka take yi ta rungume Beely,sai da Beely ta ji relief ta ɗago Khairi tana faɗin "khairi na yi nadamar abubuwa da yawa a rayuwa ta,na yi nadamar aikata abubuwa,yanzu gashi na girbi abinda na shuka,na kasa gayawa mum"da sauri Khairi ta zauna kusa da ita ta ce"aunty Beely me ya faru?me ya same ki?"

"Khairi ki yafe min abinda na yi miki,yanzu gashi ya na ta bibiya ta,yanzu zancen da nake yi miki ma miji na ya sake ni

Ban sanar da mum ba saboda na yi abinda ba zan iya kallon idanun ta ba, Khairi mum ta hana ni bin boka amma na yi kunnen ƙashi,a ƙarshe miji na ya aiko min da saki tun kafin haihuwar Yusaira amma na kasa sanar da ita,gaba ɗaya rayuwa ta babu farin ciki, yaya zan yi khairi?"

Cikin kuka Khairi ta ce"ki koma ga Allah kiyi ta istigfari,ki roƙi Allah yasa haka ya fi miki Alkhairi, aunty ki daina kuka don Allah,ni ki duba halin da nake ciki,na yi yarinya da ɗaukar ciki,a haka nake duk wani aikin wahala a gidan yaya,kuma haka kawai sai matar shi ta sa ya dake ni ya hana ni abinci,kina gani sakin wulaƙanci yaya ya yi min don matar shi ta saka shi,ke baki fuskanci ko ɗaya daga waɗannan ba,aunty Beely ki godewa Allah ki daina kuka,don Allah ki daina kuka"Beely bata san lokacin da nata kukan ya ɗauke ba ta na kallon Khairi da ta gane har yanzu ta na jin ciwon abinda Auwab ya yi mata,a hankali ta janyo ta ta rungume ta ta ce"na daina kuka Khairi,kema ki daina kuka don Allah"a hankali khairi ta fara rage kukan,kafin ta janye jikin ta ta ɗauko Yusaira da har yanzu kuka take yi

Babyn ta shiga ran Khairi sosai, Beely ta na gama shayar da ita ta amshe ta za ta goya, Beely ta yi wuf ta ɗauke daga bayan ta tana ƴar dariya ta ce"saurin me kike Madam?ki bari Allah ya sauke ki lafiya,idan ya so ko kyauta sai na bar Miki,yanzu dai gata ki ɗauke ta,amma banda goyo"bata yi musu ba ta ɗauki Yusaira ta na ƙare mata kallo ta na murmushi, yarinyar kyakkyawa sosai kamar uwarta,ta na ta kallon Yusaira aunty Naja ta kira ta,babu ja ta gayawa aunty Naja za ta kwana a wajen aunty Beely,aunty Naja bata damu ba ta ce to sai da safe

Yanzu babu wata matsala tsakanin mum ko yaran ta da aunty Naja,don lokacin da beely ta na fama dalaulayi aunty Naja ta kula da ita sosai,hatta da kwadayin masu ciki bata gaza yi mata,hakan ya sauko da zuciyar mum,don ance mai ɗa wawa,daga baya Azad ya shirya tsakanin su, komai ya wuce

Abu ɗaya ke damun mum har yanzu,shine farin cikin ɗanta da dad ya tabbatar muddin ya na raye aure ya haramta tsakanin Azad da Khairi har abada,hakan ya tilasta wa mum haƙuri,don dai ta san ta bar gini tun ran zane

To dama Hajiya mum ai dama sau ɗaya take zuwa a rayuwa,da ta wuce har abada shikenan 🥹

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a

🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee
*Young talented writers association (YOTA)*

Page 61

Wajen ƙarfe uku da rabi da Beely ta farka ta kalli khairi a fusace ta ce"wai ke dole sai kin nunawa mutane yarinya ce ke har yanzu da sauran ki?meye hakan?"khairi ta yi narai narai da idanu ta na kallon Yusaira da ta rungume ta ce"gani na yi ta na motsi za ta tashi shiyasa na tashi na ɗauke ta"ta goge hawayen da ya cika mata idanu

"Ikon Allah!to meye na kukan kuma daga magana?"ba ta amsa mata ba ta ci gaba da goge hawayen, Beely ta zauna sosai ta ce"ki kwantar da ita,gobe da safe sai ki ɗauke ta,kin ga idan ba kya samun bacci akwai damuwa,kin ga halin da kike ciki"babu musu Khairi ta kwantar da ita daidai saitin fuskar ta,idanun ta ƙyar a kanta,sai da Beely ta ɗauke ta ta mayar da ita cikin ɗan gadon ta sannan Khairi ta samu bacci ya ɗauke ta

Washegari mum da su Haidar suna zaune a parlour, ƙoƙarin fara karyawa suke yi gaba ɗaya akan wata ƙatuwar darduma da sukanyi hakan lokaci lokaci,sai ga Khairi ta fito ta na goge idanu

Dukan su bin ta suka yi da kallo,ta na zuwa kusa da mum ta zauna ta na fashewa da kuka,mum ta ajiye serving spoon ɗin hannun ta ta riƙo ta ta na faɗin "me ya faru ne?waye ya taɓa ki?"

Cikin kuka ta ce"aunty Beely ce ta hana ni ɗaukar baby!"

Haidar, Ma'aruf har Nusra sai da suka kalli Khairi da mamakin abinda ta faɗa,abin da mamaki wai Beely ta hana ta ɗaukar ƴar ta,kafin su kai ga magana Beely ta biyo bayan ta hannun ta riƙe da waya ta na ƙoƙarin kira,waje ta samu ta zauna ta na amsa gaisuwar ƙannen nata da kai

"Bilkisu me yasa za ki hana Khairi ɗaukar Yusaira?"mum ta tambaye ta ta na kallon ta

Bata kai ga amsawa ba aka daga wayar, muryar Azad ta cikin speaker ɗin wayar ta fito raɗau"Hello Bilkisu!"

"Good morning big bruh!"ta faɗa ta na kallon khairi da tayi tsuru tsuru

Ya ce"morning beely,ya kwanan baby?"

"Baby yau ta kwana a hannun small mum ɗin ta,small mum ɗin ta ƙi bacci ta na ta yi min rigima tun jiya idan na ce ta ajiye ta,yanzu kuma don na ce ta zo ta ci abinci sai ta kama kuka ta zo tan a haɗa ni da su mum"duk wannan bayanin idanun ta na kan Khairi da ta yi fuskar tausayi ta na kallon ta

Nusra da Ma'aruf suka kama dariya a lokaci ɗaya, Azad ya yi ɗan shiru kafin ya ce"wacce small mum ɗin nata?"

Beely ta ce"Khairi mana!"

"Khairi kuma?yaushe ta zo?"

"Jiya ta zo,sun zo tare da Aliyu"

"Okay gani nan zuwa"ya kashe wayar

Khairi ta kalli mum kamar zata yi kuka,mum ta ce "rabu dasu,matso ki ci abincin ki kinji?ƙyale su"

"Mummy to kice ta bani ita"ta faɗa ta na sake kwaɓe fuska, Nusra har da kusan kifawa ta na dariya,kafin mum ta sake magana hawaye suka zubowa Khairi ta sake cewa"mum kin ga tana yi min dariya"

Mum ta miƙe ta sakarwa Nusra duka a baya, Nusra ta yi ƙara, daidai lokacin Azad ya shiga parlourn da sallama

Ya na shiga Khairi ta gyara zaman ta ta na kallon shi,sai zare idanu take yi, ya kalle ta fuska a haɗe ya ce"taso mu tafi!"

Mum ta kalle shi ta ce"ina za ka kai ta?"

Ya ce "mum alƙawari ne cewa za ta ci abinci ta sha maganin on time,if not zamu koma ayi mata allura "ihu Khairi ta saka ta na faɗin"wallahi mum bana son allura,kice masa don Allah kar ya kai ni ayi min allura"

Mum ta ce"rabu da shi kici abincin ki,babu mai kai ki allura kin ji?"ta tura mata plate ɗin ƙosan ta da ta saka aka yi mata

Ta na ci ta na satar kallon Azad da shima ya zauna ake karyawar da shi, Beely ta na kule da ita ta na ɓoye dariyar ta, Nusra ma yanzu sai dai ta yi a ɓoye tunda ta sha duka

Ranar ma saboda Yusaira a gidan ta kwana, Beely kam mamakin yadda take matukar son yara take yi,har ta gaji ta ce"anya kuwa za ki bamu aron baby idan ya zo kuwa?irin wannan ƙulafuci haka?"ita dai khairi bata sanin ma ta na yi

HAƊEJIA ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA

"Sulaiman ko?"

"Haka sunan yake, idan zaki yi kara kina iya kira na da officer ko abban Anam duk da cewa ni ƙanin mijin ki ne!"ya bata amsa ya na mata wani banzan kallo yana mayar da ƙafar shi kan kujerar simintin da yake zaune ya miƙe ta

Cikin ɗacin rai ta girgiza kai tavna faɗin"kaine ka cire hannu ka mare ni ko?"

"Eh!don ina da tabbacin da ke da mijin ki babu abinda zaku iya akai ne shiyasa "

"Mhm!"ta yi wata ƴar dariya,"ba ka san ni bane,da ka san wacece ni da sai ka gwammace ka yi wasa da wuta da kayi min ko kallon banza ma,ba na barin duk wanda ya ɗaga min yatsa,don babu shakka sai na karya shi"

Sulaiman ya ƙyalƙyale da dariyar rainin hankali ya na kallon Inaaya a wulaƙance ya ce"really?you are mistaken madam!ba kowa asiri yake ci ba,wani sai dai ya warware asirin ba dai asirin ya yi nasara akan shi ba, Kamar yadda na warware wanda kika yi wa mahaifi na!"ya ƙarashe ya na kallon ta a tsanake

Tabbas ya ga razana a fuskar ta,ya yi wani murmushi ya ce"tukunna ma,na fara warware wanda kika yi wa babban yaya,amma ban gama ba,na yi Miki alƙawarin shima sai na warware shi"

A maimakon razani wannan karon dariya Inaaya ta yi sannan ta gimtse fuska ta ce"zan ji tsoron ka san asiri na yi Wa yayan ka ne?"

Yayi saurin cafewa da faɗin"baki ji tsoron mahaliccin ki ba sai ni?"ta yatsina fuska ta ce"whatever!na yi maka alƙawarin sai na raba ku da abinda kuke jin itace farin cikin ku,da ita zan yi amfani na cusa muku baƙin ciki na har abada tunda akan ta aka mare ni"

Sulaiman ya yi murmushi ya ce"fatan Sa'a ƙaramar mushrika!"ya mike da sauri ya bar wajen,don ya fuskanci idan ya cigaba da magana da ita zai iya kai mata duka,shi kuma ba hakan yake buri ba

KHAIRI

Washegari Khairi ta dawo,tunda ta shigo gaida Ammi ta ga Auwab sai ta ji gaban ta ya faɗi,har ma ta yi nadamar dawowa,sama sama suka gaisa da Ammi ta koma sashen ta ta na mamakin irin kallon da yake bin ta dashi,duk da kallo ɗaya ta yi masa ta ɗauke kan ta

Wajen ƙarfe huɗu na yamma ta na kwance a part ɗinta ta ji mutanen gidan suna yiwa su Auwab sallama,sosai ta ji daɗin tafiyar da zasu yi don idan akwai abinda ta tsana bai wuce ta buɗe idanu ta ga Inaaya da Auwab ba,ta na jin driver ɗin gidan ya fice dasu don ya kai su airport ta fito ta wuce parlourn Ammi da tun da Ma'aruf ya dawo da ita bata shiga ta yi mintuna biyar ba

AUWAB

Tun lokacin da ya mari Khairi gaba ɗaya ya rasa nutsuwar shi,ya rasa yadda aka yi har zuciya ta rinjaye shi ya mari abinda yake ji a ranshi fiye da komai,duk wulaƙanci da duka da yake mata yafi ta jin ciwon hakan,ba zai iya ƙirga sau nawa hawayen shi ya zuba ba don kawai ya ga nata ya na zuba,ya rasa yadda aka yi ya chanjawa alkhairin shi da yake jin ta kamar ruhin shi da gangar jikin shi

Ranar da ya mare ta kuwa bai iya bacci ba a ranar, musamman yadda Haidar ya kama hannun ta suka bar gaban shi,sam maganar da haidar ya faɗa masa da rashin kunyar da ta yi masa basu dame shi ba kamar marin da yayi mata

Tsawon kwanaki biyu da ya ƙara a gidan ya shiga damuwa sosai saboda baya ganin gilmawar Khairi,ya so ya yi magana da Sulaiman amma ya ƙi bashi fuska,akan dole ya shirya tafiya US a yau duk da bai so hakan ba,shi fa dabara yayi wa Inaaya suka taho,amma niyyar shi ya gyara tsakanin shi da khairi ko da baya jin mayar da ita

Sai dai kuma har ya siya tickets ɗin jirgi sai ga Khairi ta shigo gaida Ammi,ya ji zafin yadda ko nuna ta san da zaman shi a wajen bata yi ba,ta gama gaida Ammi ta juya ta fice,babu jumawa aunty Hafsa ta zo tana tambayar Ammi magungunan ta,tun daga lokacin yake ta tunanin yadda zai tura Inaaya US ita kaɗai ya gyara tsakanin shi da alkhairin shi

Sai da suka je airport dabara ta faɗo masa,ya ɗaga waya kamar ta gaske,ya na faɗin "inna lillahi wa inna ilayhi rajiun! yaushe?

An kai shi?

To bari na zo,don Allah bari nazo,bamu kai ga tashi ba,yanzu zan dawo"ya kashe wayar cikin tashin hankali yake sanarwa Inaaya cewa wani amininshi ya rasu zai je jana'izar shi yanzu,ta tafi zai biyo ta zuwa gobe

Inaaya bata yi tunanin komai ba ta yi addu'a Allah ya ji ƙan shi,ta yi saurin tafiya layin jirgi ma don kar yace su tafi ta'aziyya tare, saboda bata son hayaniya da damu

Sai da ya tabbatar jirgin su ya tashi sannan ya fito daga airport ɗin, zuciyar shi cike da tunanin yadda zasu kwashe da Khairi

Allah yasa ta gasa maka aya a hannu🥱

Wanda yake tare da ni ya ɗaga hannu🥱

Kada dai a manta VIP group #300 ne kacal

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a

🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee

*Young talented writers association (YOTA)*

Page 62

Napep ya tare don ya kai shi Hadejia road,Ammi ta na zaune a parlourn ta ta na kallon news sai ganin mutum ta yi ya shigo

Da mamaki take kallon shi ta na amsa sallamar shi,ya shigo ya nemi waje ya zauna ya na faɗin "good evening Ammi!"

"Evening!lafiya dai ko?ina matar taka?"

"Lafiya ƙalau, Inaaya ta tafi,sun tashi yanzu"

"To Allah ya kai su lafiya "

"Ameen"Ammi ta cigaba da kallon ta ba tare da ta bi ta kanshi ba,shima ya zauna ya yi jugum ya na ɗan satar kallon ta,can dai ya yi breaking silence da faɗin

"Ammi ina Man?"

"Kasan inda za ka gan shi ai"ta faɗa ba tare da ta sake kallon shi ba

Ya kai kusan mintuna goma a zaune shiru kafin ya miƙe jiki a sanyaye ya fice daga parlourn,ya na fita kai tsaye garden ya nufa ya zauna akan kujerar simintin da ke wajen ya na baza idanu wajen part ɗin shi don jiran fitowar Khairi

Bai tashi daga wajen ba sai da akayi kiran sallar maghriba,a can masallacin ya yi ta zaman shi ya na tufka da warwara har isha'i,da ƙyar ya iya dawowa bayan yayi sallar isha'i,ya na dawowa kuma ba tare da tunanin komai ba ya nufi part ɗin shi inda Khairi take a yanzu

Sai da ya shiga sannan ya ji gaban shi ya na bugawa,ya na jin kunyar haɗa idanu da Khairi saboda shi kan shi ya san ya zalunce ta,ya samu waje akan kujera ya zauna ya na kallon ƙofar ɗakin ta

Ganin zaman ba zai fishshe shi ba sai ya miƙe ya nufi ɗakin kai tsaye,aunty Hafsa bata nan saboda bikin ƴar ƙanwar ta da ta tafi,don haka Khairi ce kawai sai inna talatu ɗaya daga cikin masu aikin gidan da suke leƙo ta lokaci zuwa lokaci

Bata cikin dakin,amma ya ji ƙarar ruwa a banɗaki alamun wanka take yi,ya ɗan lumshe idanu yana tuna ɗan moment da suka yi tare,wani lokacin tare ma suke yin wankan,ya biye mata suyi ta shiririta musamman lokacin da Inaaya bata nan

Motsin buɗe ƙofa ya ji, yayi saurin ɓuya yadda baza ta gans hi ba yana kallon ta tun daga sama har ƙasa

Daga ita sai towel iya cinya,sai wani ɗan ƙarami da ta yafa a kafaɗa,kanta wasu tsofaffin kalaba ne da suka haɗe tsagar su tsabar daɗewa,tun wadda Surayya tayi mata da ƙyar bayan ta dawo daga asibiti,har yanzu kan nata shi da ganin ruwa sai dai shafar alwala,don cikin nan ba ƙaramin tsanar taɓa kai ya saka ta ba

Hankalin ta kwance take shafa lotion ɗin ta ta na waƙar ta, Allah Allah take ta gama don ta san ɗan malelen da Ammi ta aiko mata da shi dole zai yi daɗi,don ya sha manja da yajin tafarnuwa

Waƙar ta maƙale cak ganin Auwab a jikin madubin,a gigice ta juyo har numfashin ta na shirin ɗaukewa ta na kallon shi a matuƙar tsorace,da sauri ya nufe ta,ta ƙwala ihu a firgice,ya yi saurin ƙarasawa kusa da ita ya kama hannun ta ya na faɗin "ki daina jin tsoro nine fa, Auwab ne"

Da ƙarfi ta fizge hannun ta ta na kiran"Ammi! yaya!yaya na!!!yayaaaaa!!!"cikin gigita ya rungume ta da ƙarfi ya na toshe mata baki,daga ita har shi jikin su rawa yakeyi

Gefen gadon ɗakin nata ya ja ta ya zaunar ya na kallon yadda take kallon shi a tsorace,hawaye kam ya daɗe da fara ambaliya a kumburarriyar fuskar ta,ya ƙare mata kallon,daga baya ya tsayar da idanun shi akan cikin nata da yayi mata ɗaf,so da ƙaunar su su duka ya na ratsa ko'ina a jikin shi

A hankali ya zame hannun shi daga kan bakin ta ya na kallon cikin idanun ta,ya girgiza kai a sanyaye ya na share mata hawayen da suke zuba kamar an buɗe famfo,ƙasa ƙasa ya ce"Please Ummul khair ki daina kukan nan,ki saurare ni mu yi magana don Allah,kin ga........"saukar marin da ya ji ta bayan shi ne ya katse shi,da sauri ya waiga ya na kallon Ammi da ke ta huci ta na kallon shi,a hankali ya sunkuyar da kan shi ya na jin yadda Khairi ta sake buɗe murya ta na kuka,Ammi ta ɗago ta a tausashe ta ce"me ya yi miki?"

Cikin ihun kuka ta ce"maƙure ni yayi ya toshe min baki"bai san lokacin da ya ɗago ya ana kallon ta ba da mamaki,Ammi bata kalle shi ba ta kalli Surayya dake bakin ƙofa ta ce"Surayya zo ki kama ta ku wuce ɗaki na,ga hijabin ta can ɗauko ki saka mata"babu musu Surayya ta shigo ta na satar kallon yayan nasu ta yi abinda Ammi ta umarce ta ta kama hannun ta suka fice daga ɗakin,har lokacin kuka Khairi take rizga kamar ƴar ƙaramar yarinya

Aunty Hafsa ma juyawa ta yi a sanyaye ta bar ɗakin ta na nadamar abinda ta yi, ita ce ta tara musu mutane,don da za ta shigo ɗakin ta ji ihun Khairi,kuma da ta leƙa ta ga mutum ya matse ta a jikin shi ya toshe mata baki, bata gane waye ba ta tafi da gudu ta sanarwa Ammi,da ta san Auwab ne da bata yi hakan ba

Ammi ta kalli Auwab fuska a ɗaure ta ce"ka yi hakan ne don saboda part ɗin ka aka kawo ta ko?to yanzu ta bar part ɗin naka,kai ma kuma kar ka sake shigowa nawa part ɗin"ta na kaiwa nan ta juya da nufin ficewa daga ɗakin

Da sauri Auwab ya sha gaban ta ya durƙusa yana faɗin"Please Ammi,don girman Allah ki saurare ni,don......"kafa ta saka ta buge shi ta fice daga ɗakin,ya bi ta da kallo zuciyar shi ta na zafi

Kallon shi ya mayar ga Sulaiman dake tsaye bakin ƙofa ya na kallon shi,a hankali ya sunkuyar da kai saboda wani irin rauni da ya ji ya na taso masa, sulaiman ya tako a hankali ya shigo ɗakin idanun shi akanshi

Hannun shi ya kama ya miƙe tsaye, ba tare da yayi masa magana ba ya ja hannun shi zuwa parlour ya zaunar da shi akan kujera,shima ya samu waje ya zauna

Ya kalle shi cikin tausasawa ya ce"why Auwab?

Meyasa?

Menene dalilin da ya sa zaka yi wannan gangancin?me ya kai ka?kuma yanzu,me ya kawo ka wajen Khairi?"hawaye ya ciko idanun shi,ya yi ƙasa da kan shi ya ce"Nima ban sani ba, I'm just feeling somehow tun ranar da na juya mata baya, kullum zuciya ta zafi take yi min idan na ga tan a kuka,ranar da na sake ta ban iya bacci ba,ranar da na mare ta ji na yi kamar na kashe kaina"ya ɗago hawayen idanun shi suna zubowa kan fuskar shi ya ce"mey asa nake yin hakan sulaiman?"

Duk da sulaiman ya tausaya masa amma sai ya dake,ya ɗaure fuska ya ce"kai zan yi wa wannan tambayar a tunani na,tunda kai ba yaro ƙarami ba ne ko?kuma a tunani na ka san ya kamata"

Lumshe idanun shi ya yi ya ce"Nima ban san me yake faruwa ba Sulaiman,kawai dai wani lokacin kamar umarni ake ba ni na yi abu,kuma sai na ji cewa bani da nutsuwa sai na yi,idan kuma na yi sai ya dame ni"

"Auwab tell me the truth,na san baka son Khairi sanda aka yi auren nan,matar ka Inaaya ita ce komai naka,kuma ban yi mamaki ba da naje gidan ka na ga yadda ta wulaƙance, menene yake faruwa?"

"Haka ne, lokacin da na aure ta ban yi tunanin zan so ta ba,asalima ban ɗauke ta na kai ta gida na a matsayin matar aure ba,amma bayan wani lokaci komai ya sauya,na kamu da soyayyar da ban taɓa tsammanin za ta kama ni ba,na so Khairi irin soyayyar da ban taɓa jin ta akan kowacce mace ba

Ka san wanene Auwab Sulaiman!ina da tausayin mace mai juna biyu ballantana matar aure na,yarinya kamar wannan"ya ɗago a hankali ya kalli Sulaiman da ya zuba masa idanu cike da tausayin shi ya ce"Sulaiman ina son mata ta,ina son abinda ke cikin ta,ka ba ni shawara ya zanbyi?Ammi fushi take yi dani, Daddy da Abba kuma sun ɗauke min wuta ko magana ba sa bani fuskar da zan yi musu,na dawo Nigeria ne da zummar na nemi yafiyar khairi,amma sai gashi na ƙare da ƙara ɓata mata,na rasa yadda zan yi Sulaiman "ya ƙarasa magana ya na runtse idanu

Cikin nutsuwa Sulaiman ya ce"ka na addu'a kuwa Auwab?

Ka na Sallah akan lokaci?

Ka na yawan ambaton Allah?

Amsa ita ce baka yi,ko ka na yi ba sosai ba,don haka ya rage naka ka sake zage damtse ka rage waɗannan ayyukan naka ka yi abinda ya dace ko kuma ka cigaba da fuskantar matsala,a yanzu dai Khairi sai ta haihu za ta koma makaranta,sai ta gama secondary school sannan za'a duba yiyuwar auren ta,kafin wannan lokacin ka wanke kanka a wajen Khairi,shekaru biyu gare ka,ka bi komai a sannu,don ba zan ɓoye maka ba tana cikin tsananin ƙuncin zuciya na abinda ka yi mata,so abinda nake so da kai shine ka bi komai a sannu"cikin sanyin murya Auwab ya ce"yanzu ta tsane ni ko?"

Sulaiman ya girgiza kai ya ce"ba tsanar ka ta yi ba,ta na matuƙar jin haushin ka ne,amma idan ka kyautata mata sai haushin ya koma soyayya,ni zan yi maka ƙoƙari a wajen Abba ya lallaɓa Ammi ta dawo da ita part ɗin naka,amma ina roƙon ka don Allah ka bi komai a hankali,a yanzu ka kwantar da hankalin ka,ka koma bakin aikin ka,idan ta haihu za ka iya dawowa sai asan abinda za'a yi "

Auwab na khairi😅

Kada dai a manta VIP group #300 ne kacal

#Nusy_bee

Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee
*Young talented writers association (YOTA)*

Page 63

A sanyaye Auwab ya ce"thanks brother!in sha Allah zan yi amfani da shawararka, Allah ya sauke ta lafiya ya bamu masu albarka "

"Ameen big bruh!yanzu ya kamata ka siyo komai na kayan haihuwa ka direwa Ammi,na san za ta iya cewa ba'a buƙata,kar ka damu,don kuma na san za ta ji daɗin hakan da za ka yi in sha Allah "

Auwab ya yi ɗan murmushi ya ce"to ni da ba'a taɓa yi min haihuwa ba ta yaya zan san abinda ake buƙata?"sulaiman ya ce"tare za mu tafi ai,tunda a yanzu na ƙwace girman"ya faɗa da sigar tsokana ya na kanne ido

Auwab ya yi murmushi ya na girgiza kai ya ce"ai ka juma da ƙwace girman ai,tun lokacin da kake tare min faɗa a school "Sulaiman ya yi ƴar dariya ya ce"gaskiya ne big bruh!yanzu wanne suna za'a sakawa babyn idan ya zo?"

Girgiza kai ya yi ya ce"ita da wahala da ciki ni kuma da saka suna?na yarje mata ta saka duk sunan da ya yi mata"Sulaiman ya yi murmushi ya ce"husband material and wife material! Auwab da Khairin shi!"

Ƴar dariya Auwab ya yi yana ɗauke kai,kafin su miƙe a tare suna tsokanar juna yadda suka saba kafin abubuwa su lalace,suka jera suka fice daga parlourn

Washegari Sulaiman da Auwab suka je suka yi siyayyar kayan haihuwa,ko shi Sulaiman ɗin ya girgiza da haukan siyayyar da Auwab ya yi,suka fito daga mall ɗin da kaya niƙi-niƙi,aka loda musu a boot da backseat, Sulaiman ya ja motar suka nufi gida ya na ta tsokanar Auwab,wai ba saban ba

A parlourn Ammi suka samu Khairi ta na cin ɗan waken ta har da ɗan kwanon yajin ta a gefe ta na yi ta na ƙarawa,kallo ɗaya ta yi musu ta mayar da kanta ga abinda take ci tana faɗin "sannu da zuwa yaya Sulaiman"

Auwab ya kalle ta,duk da baiiyi mamaki ba,kuma ya tsammaci abinda ya fi haka daga gare ta amma ya ɗan ji babu daɗi, Sulaiman ya ce"sannu hajiyar barkono,ina Ammi?"

Ta yi ƴar dariyar sunan da ya kira ta da shi,ta ce"Ammi da Surayya sun fita gidan biki,not too long"

Sulaiman ya zauna kusa da inda auwab ya zauna ya ce"to da kyau, me yasa ke baki bi su ba?"

Girgiza kai ta yi ta ce"bana son fita sai dole"

Sulaiman ya ce"bakya so ki haihu a gidan biki ko?"ta kalle shi ta yi ƴar dariya ta ce"dama ana haihuwa wata shida?"

Yace"ana haihuwa mana,ƴan baiwa irin ki"

Ta ce"to ai ni ba ƴar baiwa bace"

Sulaiman ya ce"ƴar baiwa ce ke mana,kina da ƙananun shekaru fa kika yi aure, waɗanda suka riga ki aure suka girme ki ma duk ba su haihu ba,amma ke gashi zaki haihu"ya ƙarashe ya na murmushi

Girgiza kai ta yi tana kallon shi,ta kai lomar wani ɗan wake da ba'a gane kamannin shi saboda yadda aka binne shi da yaji,shi dai Auwab kallon ta yake yi kamar idanunshi za su faɗo,duk lokacin da ta kai ɗan waken nan bakin ta sai tsigar jikin shi ta tashi, saboda yajin nan, Khairi ta ce"ni fa ba ƙarama ba ce,a garinmu akwai ƙawaye na da yawa da aka yi musu aure ma tun kafin su kai ni,kuma suka haihu"miƙewa Auwab yayi ya ƙarasa gaban ta ya durƙusa ba tare da ya kalle ta ba,ita kuma kallon shi take yi fuska a ɗaure, sulaiman ma kallon shi yake yi,ya saka hannu ya ɗauke ɗan kwanon yajin da ta ajiye a gaban ta ta na ƙarawa

Ihu ta saka ta na faɗin"wallahi ka bani abu na,ai dai ban kula ka ba ko?yaya sulaiman ka yi masa magana ya bani abu na!!ina ruwan ka dani?don ka ga Ammi bata nan ko?"

Ɗago kai ya yi ya zuba mata idanu ya na kallon ta,a hankali kuma ta daina hayaniyar ta sunkuyar da kai,gaba ɗaya ta ji jikin ta ya yi sanyi,ƙasa ƙasa ya furta"Alkhairi na kin ga ba ke kaɗai ba ce ya kamata ki rinƙa tuna hakan, beside,kina da ulcer,kina son ki rinƙa rashin lafiya ko?"

Murguɗa baki ta yi ta galla masa harara tace"to ina ruwan ka?kuma ni ba alkhairin ka ba ce kar ka sake ce min alkhairin ka"

"To na ji,maman baby na!"

Wani mugun kallo ta watsa matsa ta ce"Allah ya tsare ɗana da zama ɗan ka"Sulaiman da yake kallon drama ɗin har da gyara zama sai da ya kusa fashewa da dariya, Auwab ya ce"okay!to waye uban shi idan ba ni ba?"

Ta cigaba da cin ɗan waken ta ta ce"ni ɗa na bashi da uba"

Da sauri Auwab ya kalle ta,shima Sulaiman kallon ta ya yi amma bai saka musu baki ba, Auwab ya ce"yanzu don kina jin haushi na sai ki sheganta min ɗa?"ta yi masa banza ta cigaba da cin abincin ta, Auwab ya ce"alright!ai dama kin saba yi min rashin kunya,dama......"

Ta fashe da kuka ta ce"ai kai ne ka janyo, ni ban shiga sabgar ka ba amma kai ka shiga tawa,kwanaki haka matar ka ta dake ni,don na rama ka zo kai ma ka dake ni,jiya kuma ka zo har ɗaki na ka maƙure ni ka toshe min baki,yau kuma ka ɗauke min yaji na, wallahi sai na gaya ka da Ammi ta yi min tsakani da kai,ka dame ni"sulaiman ya kasa danne dariya ya miƙe da sauri ya fice daga parlourn,wai Auwab ya maƙure ta!abin ya na ba shi dariya,itama miƙewa tayi da sauri za ta bi Sulaiman amma Auwab ya yi saurin riƙe mata hannu ya zaunar da ita,ta ƙara fashewa da kuka ta na kallon shi,ya ce"ni fa haƙuri na je na baki jiya amma kika tara min jama'a,ni ba maƙure ki na yi ba,gani na yi kin firgita za ki faɗi shine na riƙe ki,toshe miki baki kuma ihu kike ta yi min,amma ƙarshe sai da kika ja Ammi ta ji"

Tayi saurin cewa"wallahi ban yarda ba,kuma ba zan yafe maka ba,mugu kawai,haka kuka yi ta duka na kuna hana ni abinci kai da matar ka, kuka yi ta saka ni aiki mai wahala,gashi kuka hana ni zuwa makaranta "cikin kuka mai ƙarfi take magana,da alamun har yanzu ta na jin ciwon hakan

Shiru ya yi ya na dafe kai,da ta san mikin da take fama masa idan ta na faɗar abubuwan nan da suka wuce ki ta na kuka da bata maimaita hakan ba,da ƙyar ya ɗago ya kalle ta ya ce "to don girman Allah ki yi haƙuri ki yafewa yayan ki, kuskure ne kuma in sha Allah ba zai sake faruwa ba kin ji?, Please Ummul khairi!"

Wani banzan kallo ta watsa masa da jajayen idanun ta ta ce"ko? kuskure?dama haka kuke yi ai,ku yi tsiya ku ce kuskure ne,don Allah ni ka rabu da ni, wallahi idan ba ka fita harka ta ba sai na gayawa Abba,ka dame ni"ta ƙarashe a tsawace tana zare idanu

Girgiza kai kawai ya yi ya na kallon ta, ya ci burin idan Khairi ta na da ciki shi zai kula da ita,ya yi tattalin abar shi,amma da yake komai na bawa muƙaddari ne daga Allah sai ga shi Khairi na ɗauke da ɗanshi,amma ko ƙaunar ace ɗan shi ne ma bata yi

Miƙewa yayi ya fice daga parlourn,amma sai ya tsaya a corridor jin abinda take cewa

"Mtseeeew!yen yen yen chochochochocho!wai kuskure!in yafe masa! baza'a yafe ɗin ba, matsoraci!idan ka isa ka faɗa a gaban matar ka mana,sai a bayan idanun ta"ta sake jan tsaki,ta na duba yajin ta,sai a lokacin ta tuna kamar ya ɗauka,don haka ta miƙe zumbur kamar ba mai ciki ba ta yi waje da sauri

Ta na fita ta ganshi a tsaye ya na kallon ta,sai da ta tsorata,amma sai ta fuske ta ce"ba ni yaji na!"

Fuskar shi a ɗaure ya na kallon ta ya ce"a'a sai kin sake maimaita abinda kika ce yanzu,tunda ke ba matsoraciya ba ce"ta sunkuyar da kai,sai kuma ta juya ta koma parlourn,ya bi ta da kallo ya na murmushi,har yanzu akwai yarinta da ƙuruciya akan Khairi

Sulaiman ne ya damƙawa Ammi kayan da Auwab ya siyo,ta yaba kayan sosai a ranta,amma ba ta nuna ba,asalima cewa ta yi baza ta karɓa ba,sai da Sulaiman ya shawo kanta da ƙyar tukunna

Bayan kwana biyu Auwab ya koma US,a lokacin da ƙyar Abba ya samu ya shawo kan Ammi khairi ta koma sashen Auwab da aka bata,don sai da ya tunatar da ita ba don komai suka yi hakan ba sai don kar inna sabuwa ta ɗago Babu auren


LUGARD ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA

"Shigo mana,nuƙu nuƙun kuma na menene?ko ba ki da gaskiya ne?"Beely da ke shigowa ta yi murmushin yaƙe ta na kallon mum ɗin ta ta yi mata tambayar,ta tsare ta da idanu

Waje ta samu ta zauna kusa da mum ta na kallon ta, ƙasa ƙasa ta ce"good evening mum!"

"Evening,ya jikin Yusaira?kin ba ta magani?"

Beely ta ce"eh, zazzaɓin ma ya sauka,ta yi bacci ma"

"To Allah ya ƙara sauƙi"a cewar mum ta na naɗe dardumar hannun ta, Beely ta amsa da "Ameen"

Sai da mum ta kai dardumar ta ta ajiye sannan ta dawo ta na kallon ta ta ce"ya dai?lafiya na ganki haka?"

Beely ta tattaro nutsuwar ta ta ce"mum magana nake so muyi"

"Wacce maganar ce?"sai da Beely ta aro jarumta sannan tace"mum maganar aure na ne"

"Mhm!babu shi ko?"ta tambaya ta na kallon ta, yanayin damuwa na bayyana akan fuskar ta

Shiru ta yi kan ta a ƙasa kwalla ta na cika idanun ta,kafin ta ɗago ta na kallon mum ta ce"mum ya aka yi kika sani?"

Mum ta yi murmushin baƙin ciki tabna ɗauke ƙwallar da ta tarar mata a idanu,ta kalli Beely ta ce"ni na san babu yadda za'a yi ki ɗauki wannan lokacin a gida da igiyar aure,sannan ina jin kamar sakayya Allah yayi wa Fadeela matar Azad da na saka shi ya sake ta"mum ta ƙarashe ta na goge hawayen ta


Mum fa ta yi nadama da gaske 😥

Kada dai a manta VIP group #300 ne kacal


#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee
*Young talented writers association (YOTA)*

Page 64

Beely ta girgiza kai ta na kallon mum ta ce"ba alhakin Fadeela ba dai,don ni ban yiwa miji na ko da rabin abinda Fadeela tayiwa yaya Azad ba,sai dai mum ina roƙon ki yafe min,kin hana ni aikata abu kuma na aikata"

Mum ta kalle ta, hawaye sun cika idanun ta,ta sunkuyar da kai ta na goge wa,cikin rawar murya ta ce"Bilkisu me kika yi?"

Kuka ya kufcewa Beely ta ce"mum bin bokaye na yi,a ƙarshe gashi hakan bai haifar min da ɗa mai ido ba,mum na yi nadama,don Allah ki yafe min"ta ƙarashe cikin kuka ta na durƙushe wa a gaban mum ɗin

Mum ta share hawayen ta ta ce "ba ni kika saɓa wa ba Bilkisu,ki nemi yafiyar ubangijin ki,shi kika saɓawa,sannan ya na fushi mai tsanani da mushrikai

Don Allah Beely idan kika samu miji kika yi aure kar kiyi irin rayuwa ta a gidan mijin ki, wallahi babu komai a cikin ta sai wahala da nadama, mahaifin ku bai ji daɗin hali na ba ballantana dangin miji na,ɗana mafi soyuwa a gare ni kuma wanda yafi kowa yi min biyayya yafi kowa shan wahala ta, ni kam......"ta kasa ƙarasawa saboda kukan ta da ya tsananta

Itama Beely kuka take yi sosai,ta taso ta rungume mahaifiyar tata zuciyar ta cike da nadamar abubuwan da ta aikata itama,sun ɗan daɗe suna kuka kafin su ji muryar Nusra a parlour, suka yi saurin goge hawayen, Beely ta miƙe jiki Babu ƙwari ta fice daga ɗakin zuwa parlour


HAƊEJIA ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA


Kwanci tashi asarar mai rai,yau da gobe ta wuce wasa,madam Ummul Khairi ta yayyen ta da Auwab ta shiga watan haihuwa,masifa da rashin kunya da tsiwa dai yanzu babu, sai zafin rai da saurin kuka,ta zama wata silent sosai,duk wanda ya ganta sai ta bashi tausayi,dama ita ba wata ƙibar kirki gare ta ba,kuma duk da cikin jikin ta hakan bai ɓoye mata yarintar ta ba,a tsawon watanni ukun Auwab ya zo sau biyu,yanzu bayan haushin abinda ya yi mata har da jin haushin shi duk lokacin da cikin ya hana ta bacci,duk dare haka za ta zauna ta na kuka ta na ja masa Allah ya isa,wani lokacin ma har sai ta saka mai kula da ita aunty Hafsa kuka

A ƴan kwanakin nan ta na ɗan fama da ciwon mara da ciwon baya, Auwab da Azad suna ƙasashen da suke aiki, Sulaiman kuma tafiya ta kama shi zuwa Edo state,ita kuma har yanzu ba wai ta saba da Ammi bane ballantana ta gaya mata damuwar ta,don ma akwai ta da juriyar ciwo

Yau kam tun safe take jin ciwon da bata saba ji ba sosai,don haka bayan ta gaida Ammi ta shige ɗakin ta ta cewa aunty Hafsa kar ta tashe ta bacci take ji, aunty Hafsa ta amsa tare da yi mata fatan tashi lafiya

Itama baccin ta kwanta a parlour,sai wajen sha biyu da rabi ta farka a dalilin sallamar da ta ji

Da fara'a da girmamawa take gaida Auwab da ya shigo parlourn bayan ta amsa masa sallamar,ya amsa da sakin fuska ya tambaye ta Khairi, ta ce "tun ɗazu dai ta ce za ta kwanta bacci,amma bana jin ta fito har yanzu"

Ya ce"da kamar wanne lokaci ne?"

Tace"kamar tara da rabi na safe"ya ɗan yi shiru ya na nazari,khairi ta na son bacci amma ba ta wuce sha ɗaya na safe duk runtsi,don haka ya ce"dubo ta yanzu ko ta tashi"babu musu ta miƙe ta nufi ɗakin

Sai dai a rufe,don haka ta dawo ta shaida masa,ya ɗan yi shiru sannan ya wuce main bedroom ɗin shi dake part ɗin,jim kaɗan ya fito hannun shi riƙe da spare key,da ɗan sauri ya nufi ɗakin khairi ya buɗe

Gaban shi ya faɗi ganin ta a durƙushe a bakin gado,kanta a ƙasa amma ya na iya hango gumin da yake yanko mata,ya ƙarasa da sassarfa ya riƙe ta ya na faɗin "alkhairi na me ya faru ne?me yake faruwa ne?"

Da ƙyar ta ɗago ta kalle shi,idanun ta sai da suka ba shi tsoro,a hankali ta ce"yaya ka taimake ni,mutuwa zan yi,ka yafe min yaya!don Allah yaya ka taimake ni"bai gama sauraren soki burutsun nata ba ya ɗaga ta cak ya yi waje da ita

Allah ne ya kai shi asibiti lafiya saboda yadda ya gigice da ganin halin da take ciki,nan da nan aka karɓe ta,gwajin farko aka gano haihuwa ce,asalima ta kai 6cm,hankalin Auwab dai a matuƙar tashe, addu'a Babu kalar wadda bai yi ba,don baya fatan ko da wasa ya rasa Khairin shi

Ya na nan tsaye ya na Safa da marwa cikin tashin hankali nurse ɗin da take kula da ita ta leƙo ta na faɗin "Madam ta ce tana son ganin yaya"ba tare da ya yi magana ba ya bi bayan ta,ta jagorance shi zuwa ɗakin

Ya yi matuƙar gigicewa ganin halin da Khairi take ciki,gaban ta ya durƙusa ya na kallon ta,jikin shi sai karkarwa yake yi

Kama hannun ta yayi,cikin rawar murya yace"sannu alkhairi na!sannu kin ji?in sha Allahu lafiya za ki haihu kinji?sannu,yanzu za ki haihu kin ji?"ɗaga idanu ta yi da ƙyar ta na kallon shi,a hankali ta ce"yaya!ka yafe min,mutuwa zan yi,idan ka ga mama na ka ce ta yafe min ta yi min addu'a"

Bai san lokacin da ya fashe da kuka ba ya ce "don Allah khairat ki bar wannan maganar,don Allah,in sha Allahu lafiya za ki haihu"ita dai bata sake magana ba, ya yi azamar fita wajen nurse ɗin ya ce"don Allah ku yi mata aiki ku cire mata ɗan,ina son mata ta idan ta mutu ban san yadda zan yi ba"cikin tausayawa nurse ɗin ta ce"in sha Allahu yanzu zata haihu, saboda bata taɓa haihuwa bane ta yi jinkiri haka,amma nan da ɗan lokaci kaɗan za ta haihu"bai ce komai ba sai waje da ya samu ya zauna ya dafe kai,ya na jin wayar shi dake aljihun shi ta na ta ƙara amma ba shi da strength ɗin ɗaga kira yanzu

Kusan awanni biyu ana fama kafin nurse ɗin ta sake fitowa ta na murmushi,ya ɗaga kai ya na kallon ta,shi dai Auwab kallo ɗaya za'a yi masa a gane baya tare da nutsuwar shi,nurse ta ce"congratulations engineer Auwab Usman Saeed,Madam ɗin ka ta sauka lafiya,an samu baby boy"kafin ya kai ga cewa wani abu ma sai ga wata nurse ɗin ta fito nannaɗe da jaririn ta na murmushi,ta miƙa masa

Bai karɓa ba sai da ya ce "to ita Ummul khair ya nata jikin?"

Murmushi ta yi tace"Ummul khairi lafiyar ta ƙalau,yanzu zamu tura ta ɗakin hutu ne,sai zuwa anjuma zaka gan ta"bai sake magana ba ya amshi yaron nashi,ya buɗe fuskar yaron ya ƙura mata idanu,a hankali idanun shi ya ciko da ƙwalla,ya na kallon yaron na shi da basu da maraba a kamanni

Ƙasa da awanni biyu family ɗin su sun cika asibitin,kowa sai murna yake yi Khairi ta haihu lafiya,a ranar aka sanar da Azad da Sulaiman,suma sun yi murna sosai, Nusra ta turawa Azad hoton babyn, Surayya ta turawa Sulaiman, Sulaiman sai tsokanar Auwab yake yi wai ya haifi photocopy ɗin shi,wannan watarana sai an kasa gane ɗan da uban

Lokacin da Khairi ta farka daga baccin da ta yi su Nusra suka kewaye ta suna ta mata sannu kowacce fuskar ta ɗauke da murmushi, Surayya ta ce"congratulations Khairi!babyn ki mai kyau tubarkallah Masha Allah!"Nusra ta ce"kamar ki bar min shi haka na ji da na ganshi,gashi ɗan ƙarami gwanin sha'awa"Surayya ta galla mata harara ta ce"da ƙato kike so a haifa?ko kin manta yau ya zo duniya?"

Nusra ta ce "au! abinka da ba sabam ba,kuma kin ga ko sanda aka haifi Yusaira ai tafi shi girma"ita dai Khairi kallon su kawai take yi,amma ba wannan ne a gaban ta ba,burin ta kawai taga abinda ta haifa

Beely ce ta shigo hannun ta riƙe da jaririn tana murmushi,ta kalli su surayya ta ce"iyayen surutu,to ku fice ku bawa mutane waje,ko ta samu ta huta"babu musu suka miƙe suka yi hanyar fita suna ta murna

Beely ta kalli khairi ta na murmushi,kafin ta yi magana khairi ta ce cikin sanyin murya "sannu da zuwa aunty Beely"

Beely ta zauna ta na murmushi ta ce"ai ke zan yi wa sannu maman baby,yanzu dai karɓe shi,maza kalli kyautar da Allah ya ba ki"babu musu Khairi ta amshe shi cikin sanyin jiki tana ƙarewa showel ɗin da aka naɗe shi a ciki,ko iya showel ɗin ma da gani ya lashe kuɗi ballantana kuma kayan da aka sakawa yaron


Shagaliiiiii 💃💃💃💃💃


Kada dai a manta VIP group #300 ne kacal


#Nusy_bee

Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️ Nusy bee
*Young talented writers association (YOTA)*

Page 65

A hankali ta buɗe fuskar yaron da yake ta shan baccin shi ta na kallon shi,wani irin abu ya tokare ta a moƙoshi ganin yaron babu wani abu na mahaifin shi da ya manta,sai dai ta ji ya shiga ranta fiye da yadda ta yi zato, Beely ta na ankare da reaction ɗin ta,ita kanta Beely tausayin ta take ji,don akwai alamu har yanzu bata gama warkewa daga ciwon da Auwab ya dasa mata ba,a hankali kuma sai ta mayar ta lulluɓe shi ta miƙawa Beely ba tare da ta yi magana ba, Beely ta yi murmushi ta ce"ba ki saka masa albarka ba"a hankali ta ce"Allah ya yi masa albarka"ta koma ta kwanta

A ranar aka sallame ta saboda lafiya ta haihu,duk yadda Auwab yake tarairayar ta da ba ta kulawa banza take yi masa ta na share shi,don ba ƙaramin baƙin ciki ta ji ba ganin ɗanta ya na kama da Auwab

Ƙarin takaici kuma da sulaiman ya dawo da daddare,dukkan su suna zaune a parlourn Ammi,bayan an gaisa aka kawo masa baby,ya na dubawa yace"Masha Allah!big bruh definitely gave to himself! allahumma barik! Allah ya raya"kowa fuskar shi ɗauke da murmushi amma banda khairi da ta ɗauke kai ma

Kwana biyu da yin haihuwar Azad ya dawo,tare da mum suka zo, lokacin ma Auwab ya na tare da su Khairi da Ammi,babyn shi a rungume a hannun shi,shi kuma Sulaiman ya haɗu da su Azad a waje,ya gaida mum a girmame,suka tafa da Azad sannan suka shigo cikin gidan tare,suna ta hira

Da fara'a aka gaisa ana ta raha,ita dai Khairi sai ɗauke kai takyeyi, Azad ne ya fara kula da bata da walwala,yavce"little sister ya dai?ya kamata fa ki kasance cikin farin ciki,duk nan fa don ke muka taru,ko akwai abinda yake damun ki ne?"

A shagwaɓe ta ɗaga kai,da yawan mazauna parlourn suka mayar da hankali gare ta, Sulaiman ya ce"me ya faru?me akayi miki?"

Ta yatsina fuska cikin jin haushi,da ita gaskiyar ta tace"wai duk wahalar da nasha a ciki da haihuwa amma ya rasa da wa zai yi kama sai da....."sai kuma ta yi shiru, parlourn ya yi shiru kowa sai kallon ta yake yi,ba ta damu ba ta ci gaba da magana fuska a ɗaure"ni Allah da na san ba zai yi kama da ni ba ba zan ma fara haifar shi ba"

Hatta da su mum shiru suka yi suna kallon ta,su Beely sai sunkuyar da kai suke yi suna ɓoye dariya, Auwab ya ce"oooookay! sai yanzu na gane dalilin da yasa ake share ni ana wulaƙanta ni,wato dalilin kenan?"kamar jira take ta juya kanshi da masifa

"Kaga ni ban saka ka a cikin magana ta ba babu ruwan ka da ni,tunda na dawo gidan nan sai takala ta kake yi,kai dole sai ka nemi rigima,ai dai ban saka da kai ba ko?akan ɗana nake magana!"ta faɗa a zafafe

Miƙewa tsaye ya yi ya na faɗin "kya ji dashi dai"sannan ya sa kai ya fice daga parlourn

Ɗaga murya ta yi ta ce "ai tun farko laifi na ne da na bar ka kake taɓa min ɗa,amma ka yi na ƙarshe"su dai su Sulaiman kallon ikon Allah kawai suke yi, Khairi sai huci take yi don takaici,don da gaske ta ji haushin kamannin da jaririn ta yayi da Auwab

"Kalle ni nan little sister!"babu musu ta kalli Azad da ya yi maganar,shima fuskar shi a ɗaure,sai ta ɗan tsorata da yanayin shi,bai damu ba ya fara mata magana

"Da ke da Auwab wane ne mai ikon siffanta fuskar jariri?ko kin manta Allah ne ya halicce shi a sigar da ya so?to bana son shirme little sister, Allah ya halicce shi a yadda ya so,idan kika ji haushi kamar kin ƙalubalanci ubangiji ne,kuma ba'a ƙalubalantar Allah a duk abinda ya yi,komai Allah ya yi daidai ne,so ki daina irin wannan shirmen Please,kin ji? Allah ya raya mana shi ya yi masa albarka"jikin ta ya yi sanyi,cikin sanyin murya ta ce"Ameen"

Duk da kasancewar nasihar Azad ta shigi Khairi amma hakan bai hana ta ci gaba da ɗaurewa Auwab fuska ba,gashi shi kuma ko me zata yi masa baya zuciya ya bar kusa da ita

Ana i gobe suna ta na zaune a parlourn ta ta na cin tuwon da aunty Hafsa ta yi mata, Auwab ya na gefen ta ya na ƙarewa babyn shi kallo,babu kalar habaici da bata yi masa ba amma ya yi banza da ita,ƙarshe ma fitowa ta yi ya kalle shi fuska a daure ta ce"wai kai baka da zuciya ne?"

Ya kalle ta ya ɗauke kai,haushi kamar ta yi me don takaici, ta yi ta surutan ta ya yi banza da ita

Shigowar Sulaiman da Azad ne ya katse mata surutan,ta ɗaga kai ta na kallon su ta na amsa sallamar su, Azad ya bawa Auwab hannu suka tafa,sannan suka zauna kusa da shi

Sulaiman ya ce"ba saban ba ɗin fa kenan!kai kamar akan ka aka fara haihuwa,bini bini ka ɗauki ɗa ka riƙe"

Auwab ya watsa masa kallon banza ya ɗauke kai, sulaiman ya yi ƴar dariya,Azad ya ce"bar shi ya ji ɗumin na shi, nima da Allah ya ƙaddara nawa ya taka ƙasa da yanzu muna tare"wani kallo Sulaiman ya yi masa,shi kam Auwab tausayin shi ya ji, Khairi ma haka, Sulaiman ya ce"kai yanzu ba za ka godewa Allah ba da ya nufa baka haihu da wannan yarinyar ba?kai yanzu ka na tunanin ta na da tarbiyyar da zata iya bawa yaran ka?to ya kamata ka gane ko me Allah ya yi akwai hikima a ciki,ko don ka samu ka rayu shine har ka yi saurin manta baya?ka manta lokacin da na zo na same ka a sheme ka na buɗe idanu da ƙyar?"Azad ya kai masa duka ya goce ya na dariya, Auwab ya girgiza kai ya ce"Sulaiman kai dai ka iya sharri wallahi!"

"Ka tambaye shi ka ji idan ƙarya na yi,kwanan shi huɗu bai san a duniya yake ba ko a lahira, saboda yaji dukan mata"

"Kamar yaya dukan mata kamar wani yaro?ni fa ban fahimci komai ba"a cewar Auwab ya na kallon su

Azad ya watsa masa ya na faɗin"kai ma ai munafuki ne,ina ruwan ka da wannan maganar tunda bata shafe ka ba?"Sulaiman ya ce"ai kuwa ta shafe shi,ko kunya kake ji ya san kun yi faɗa da matar ka ta naɗa maka duka ta sumar da kai?"sakin baki Azad ya yi ya na kallon shi jin in da ya kai shi, Khairi dai tana cin tuwon ta ta na kallon su,sai yanzu ta ce"yaya Sulaiman me ya samu yaya na?"

Sulaiman ya fuskance ta ya bata labari a taƙaice,ta yi shiru cike da tausayin Azad, Auwab ma tausayin Azad ya lulluɓe shi, Khairi tace"dama na san masifaffiya ce tunda in dai na kira ta ɗaga sai ta yi ta min masifa,har zagi na take yi "

"Kema ai ba ƙyalle ba ce, ɗaga mata ƙafa kawai kike yi saboda darajar mijin ta,amma wannan Khairin da na sani wallahi ba mai saurara mata bace"

Ta kalle shi ta kalli Azad,fuska a ɓace ta ce"yayana ka yi min iyaka da mutumin nan wallahi, kullum sai ya zo ya liƙe min ya yi ta takala ta faɗa,ina kau da kai bana son mu yi hayaniya amma sai ya ƙure ni,idan na yi magana sai ya yi ta cewa bani da kunya"

Sulaiman kam kasa daurewa ya yi sai da dariya ta ƙwace masa, Auwab ya ce"ina ruwa na dake da zan liƙe miki?ni wajen ɗana mai kama dani nake zuwa,me ya shafe ni da ke?"

Maganar ta yi mata zafi,a zafafe ta ce"to ai Allah ne yayi kamar da kake yiwa mutane gori saboda ita,kuma ni ɗana ba ɗan ka bane,ka je can matar ka ƴar gold ta haifa maka ɗanka"

"To da wacece ta haifa min idan ba mata ta ba?yanzun ma ai matar tawa ce ta haifa min,ko matar ki ce?"

Miƙewa tsaye ta yi ta na kallon shi,cikin masifa ta ce"wacece matar taka?"har da gyara zama ya na kallon ta ya ce"ke mana,har yanzu ke mata ta ce shiyasa kika ga kina zaune a part ɗina baki koma gidan Daddy ba"ihu ta saka cikin takaici, ta fashe da kuka ta na faɗin"sai na gayawa su Daddy su raba ni da part ɗin ka tunda gori kake yi min,dama na san ka zo neman tsokana ta ne"

"Na rasa wa zan tsokana sai ke uwar tsiwa da rashin kunya?"

"Eh ɗin!ina ruwan ka da ni?idan ka yi zuciya kar ka sake zama a inda nake zaune"ta faɗa cikin kuka

"Sai na zauna ɗin tunda ba gidan ki bane gidan Abba ne"

"Eh ai kaima dai ba gidan ka bane"

Azad ya girgiza kai ya ce"enough!Kai Auwab kai ne baka da gaskiya,kar ka sake damun ta ballantana ka tsokane ta!"

Auwab ya kalle shi a kaikaice ya kawar da kai ba tare da ya ce komai ba, Khairi dake kallon shi ta goge hawayen fuskar ta ta ce"yaya ya ji ka ne kawai fa,amma bai ɗauki gargaɗin da ka yi ba,sai wani kallon hadarin kaji yake maka"Auwab ya kalle ta da sauri kamar jira yake ya ce"na kasa dake?ina ruwan ki dani?da yaya na nake magana ba dake ba"ta taɓe baki ta ɗauke kai, Azad ya ce"baza ku daina ba ko?"

Ta yi saurin cewa "yaya shi za ka yiwa magana,ka san ni bana neman tsokana "Sulaiman dai dariyar shi yake sha ya na kallon drama, Azad ya ce"yanzu dai zauna baby sister,gaya min wanne suna kika yanke a sakawa baby,ko a saka masa Abubakar ɗin?"

Murmushi take yi sosai,ta koma ta zauna ta na kallon Azad ta ce"nafi son a saka masa Muhammad!ina son sunan "

Sulaiman ya gyara zama,don ga abin haɗa faɗa ya samu,ya na kallon jaririn da ke rungume a hannun Azad,ya na murmushi ya ce"wow! Masha Allah!abu yayi daɗi,sunan mahaifin shi kenan ko, Muhammad ɗan Muhammad,amma shi me za'a rinƙa kiran shi?ko ace Auwab ɗin kawai?"


Wallahi sulaiman tsaf sai ka kashe aure🤣🤣🤣🤣🤣


Kada dai a manta VIP group #300 ne kacal

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee

Page 66

Shi kan shi Azad sai da dariya ta ƙwace masa ganin yanayin fuskar Khairi,sai wani mugun kallo take watsawa Auwab da ya baje ya na kallon ta ya na ɗan murmushi,a zafafe ta ce"a saka masa Abubakar ɗin shi, Allah ya sauwaƙe na sakawa ɗana sunan wani"

"Ameen!amma ko babu komai sai da aka yi niyyar saka masa sunan wani"yavna faɗin hakan ya yi saurin ficewa daga part ɗin har da ɗan gudun shi ya na ƴar dariya,shi kan shi drama ɗin da suka sha ta yi masa daɗi

Kuka sosai Khairi ta fashe da shi ta na faɗin "yaya ka ji abinda yake yi min ko? kullum sai ya yi ta tsokana ta, ni ba na kula shi amma shi sai ya tsokane ni,ka yi min iyaka da shi"Azad ya kwantar da jaririn hannun shi a hankali a cikin ɗan net ɗin shi, sannan ya ɗakawa Sulaiman duka ya ce"tashi ka fice daga parlourn nan munafuki!duk kai ka haɗa komai"sulaiman ya ce"a haba!ba dai ni ba,ka dai so kaci zali na ne,amma dama faɗan su suke yi na zo na same su"

"Na ji,tashi mu tafi, little sister sai gobe?"

Ta yi murmushi ta ce"to yaya na a gaida min da su mum da aunty"suka fice Azad ya na faɗin zasu ji

Washe gari yaro ya amsa sunan shi Abubakar sadeeq,amma Nusra ta rufe masa da Ajmal, Auwab, sulaiman da Azad ba ƙaramin ɓarnar kuɗi suka yi a sunan nan ba,gashi Khairi tayi farin jini sosai,a kaf family ɗin barrister Umar da na lieutenant general Usman Amra ce kaɗai bata halacci sunan ba, ita ma saboda bata nan ne,ita da mijin ta sun je Wales

Hakan ya ƙarawa Mifra takaicin khairi,don ita bata samun wannan kulawar daga wajen dangin Auwab duk da yadda ta yi iya yin ta ta ja su a jiki su bavsu karɓi hakan ba, musamman Beely,dama ita sabga in dai bata shafe ta ba bata damu da ita ba,daga ita har Azad,ta na da ji da kan ta sosai,shiyasa a yaran mum kaf babu wadda take da ƙarancin jituwa da mutane irin ta

Watan Ajmal biyu aka fara yiwa Khairi cuku cukun komawa makaranta, Khairi sai murna take yi za ta cigaba da karatun da da cire rai da ko
shi daga baya,aunty Hafsa za ta dawo gaba ɗaya saboda kula da Ajmal don Khairi ta samu ta yi karatun ta a nutse

Yau ta na zaune a parlourn Ammi ita da Nusra suna hira,gefen ta Ajmal ne kwance,gama shirya shi da ta yi yanzu kenan,yanzu da kanta take yiwa ɗanta wanka saboda aunty Hafsa ta koya mata,kuma ko a wankan farko bata yi wani kuskure ba,shiyasa ta saki jiki ta cigaba da ba ta

Auwab da Inaaya ne suka yi sallama suka shiga parlourn,kallo ɗaya ta yi musu ta ɗauke kai ba tare da ya amsa sallamar ba ma,rabon da ta saka Auwab a idanun ta tun bayan sati biyu da haihuwar Ajmal,ita kuwa Inaaya tun lokacin da suka yi dambe,cikin Ajmal na da wata shida

Ta na jin Nusra ta na yi musu sannu da zuwa,ita dai wayar ta ta ja tana ta dannawa, fuskar nan babu rahama

Kai tsaye Auwab inda Ajmal ke kwance ya nufa,ya ɗaga shi ya na faɗin "sweetheart!I miss you yaron baban shi,na san ka yi kewar Abban ka ko?"ya miƙe da yaron a hannu ya nufi inda Inaaya take zaune, baƙin ciki kamar ya kashe ta ganin Khairi da ɗa,ya miƙa mata yaron ya na murmushi ya ce "wife ga ɗanki,karɓe shi ki saka masa albarka"

Wani kukan kura Khairi ta yi ta dira a gaban shi tabna masa wani kallo ta ce"me ka ce?ɗanta?ai ka bari ta haifi nata sannan ka kira shi ɗan nata ko?don ka samu fuskar ɗaukar shi shine har za ka bawa wata ƙazama ɗana ta taɓa min ta goga masa datti?to ta haifi nata idan ya so sai ta yi ta ɗauka,wannan nawa ne,kuma ya fi ƙarfin ta!"

Kallon ta kawai Auwab yake yi yadda take ta masifa ta na huci,a hankali ya ce"Ummul khair matsa daga nan wajen!"

Ta yi wata dariyar rainin hankali ta ce"na matsa?da gaske kake?ka ɗauka min yaro kuma ka ce na matsa?to bani ɗana,ni ban damu da kai da rayuwar ku kai da matar ka ba,amma kai baka isa ka shigar da ɗan da na wahala na haifa cikin jagwalgwalon rayuwar ku ba,ka jira ta haifa maka nata,shine naku,amma nawa nawa ne"

"I will give you a hard slap idan ba ki bani waje ba Ummul khair!!!"

Ta yi shewa"heeeeeee!

Wallahi ka na mari na sai na rama akan matar gold ɗin taka,ba ni ɗana"

Inaaya ba ta taɓa jin zafin rashin haihuwa irin na yau ba,idanun ta suka ciko da ƙwalla ta ce"love bata ɗan ta,Nima Allah zai bani nawa,ba fina ta yi a wajen Allah ba na san ya na sane dani"

Khairi ta amshe Ajmal ta na faɗin "eh!aje!idan kin ga dama kifi ƙwarƙwata haihuwa,wannan damuwar ku ce, matsalar ku ce bata Khairi ba,idan kin ga dama ki haifi kano da Kaduna, ra'ayin ki ne,amma ɗana Abubakar Ajmal yafi ƙarfin haɗa hanya da ke, mtseeeew!"ta na kai wa nan ta ja tsaki ta take ƙafar Inaaya ta bangaje Auwab ta wuce ta bar wajen,su kam bin ta suka yi da kallo,don babu wanda ya iya yi mata magana daga Auwab har Inaaya ɗin

Kai tsaye ɗakin Surayya ta wuce inda Surayyan ta shige ta na leƙo su ta window,ta na shigowa ta bawa Khairi hannu suka tafa,ƙasa ƙasa ta ce"gwara da kika yi mata haka,na tsane ta wallahi,tunda yayan mu ya aure ta ya daina kula mu,ya rage zumunci damu,sai fa a dalilin ki ne muke ganin shi akai akai a gidan nan"

Khairi ta zauna a gefen gadon Surayya,ta kwantar da Ajmal a kan gadon,ta kalli Surayya cikin sanyin murya ta ce "Surayya na sha wahala sosai a gidan bayin Allan nan,sun babni wahala,kuma ba wannan ne yabyi min ciwo ba,sai da yaya Auwab ya koya min yadda zan saba dabshi,na shaƙu da shi sosai, lokaci ɗaya ya juya min baya ya yi ta wulaƙanta ni,ban san me yasa sam bani da daraja a wajen mutane da yawa ba"ta goge idanun ta ta kalli Surayya tace"Surayya me yasa mutane ba sa sona? me yasa ake wulaƙanta ni?me yasa bana samun tabbataccen farin ciki?ina da wata nakasa ko aibu ne bayan maraici da ƙauyanci?abinda ya faru tsakani na da yaya Auwab har zuwa yau na kasa cire shi a raina,ina yawaita kukan hakan,ba zan taɓa dainawa ba kuma na san ya yi min nisa ta har abada"ta rufe fuskar ta ta na kuka sosai

Surayya ta rungume ta hawaye na zubo mata,cikin kuka ta ce"ke ɗin ta dabam ce Ummul khairi,ke ɗin ƴar baiwa ce,kuma ko rantsuwa nayi ba zan yi kaffara ba Khairi,mijin ki ya na son ki,kuma ......"da sauri Khairi ta ture ta ta na kallon ta ta ce"so na?shi ya ce miki ya na so na?"

Surayya ta yi murmushi ta na riƙe hannunta ta ce"tabbas yayan mu ya na son ki,ya na matuƙar son ki,ki kwantar da hankalin ki ki ƙwaci mijin ki daga hannun waccan shaiɗaniyar,ku yi rayuwar ku cikin farin ciki da mijin ki da ɗanku"

Khairi ta yi ɗan murmushi ta ce"rabu da su Surayya,ni a yanzu so nake na gina rayuwa ta,babu aure ko soyayya a ciki,har yanzu yaya Auwab ya na son matar shi fiye da yadda yake son komai na rayuwar shi, sauƙin ta kawai ya na matuƙar son ɗan shi, banda haka "ta yi murmushi kawai

Surayya ta kwantar da murya ta ce"ke fa mace ce Khairi"

"Ita ma mace ce ai Surayya,kuma masoyiyar mijin ta,Kin ga bar ni da wannan zancen,bari na je na duba na ga ko aunty Hafsa ta gama girki,yunwa nake ji"bata sake sauraren Surayya ba ta sungumi Ajmal ta yi waje, Surayya ta bita da kallo zuciyar ta cike da tausayin ta

Da yamma Khairi ta na wanka Ajmal ya farka daga barci ya fara ƙananun kuka, lokacin aunty Hafsa ta leƙa wajen masu aikin Ammi da take ɗan zuwa jefi jefi, Auwab da ya shigo part ɗin ya na ganin Ajmal a kwance a kan gado ya na ƙananun kuka ya ɗauki abin shi ya dawo parlourn ya na masa hira kamar wani babba ya na murmushi

Ji ya yi an taho da gudu,kafin ya ankara Khairi ta fizge ɗanta ta na huci,sai wani mugun kallo take watsa masa,bata ce komai ba ta juya ta koma cikin ɗakin ta ta na ƙwafa, Auwab har da tagumi ya na bin ta da kallo

Kwanansu Auwab uku a garin suka koma US,duk yadda Auwab ya so ya shawo kan Khairi a ɓoye hakan ya ci tura,ƙarshe ma a parlourn Ammi a gaban Inaaya take gayawa Ammi ta ja masa kunne ya daina damun ta

A ranar Auwab da Inaaya sai da suka samu matsala,da ƙyar ya shawo kanta washe gari kuma suka yi musu sallama suka bar ƙasar


Khairi masifaffiya ce yacin😡

Kada dai a manta VIP group #300 ne kacal

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee
*Young talented writers association (YOTA)*

Page 67

Wata tsadaddiyar private school Sulaiman ya kai ta,wannan karon day zata yi ko don Ajmal, ba tare da ɓata lokaci ba kuma Abba ya siya mata mota ya bayar a fara koya mata

Murna iya murna Khairi tayi ta,ga makaranta ga mota,kuma saboda ta saka ranta cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ta fara iyawa

A makaranta ss2 ɗin ta aka saka ta, science class,don da gaske khairi take na ƙaunar zama likita,har yanzu da nauyin Ajmal ya hau kanta burin ta bai chanja ba

Kwanci tashi babu wuya wajen Allah, Khairi ta kammala ss2 za ta tafi ss3,shima dai result ɗin ta ya yi kyau sosai, a tsawon watannin da ta ɗauka ta na karatu sau ɗaya Auwab ya zo, ya kwana ɗaya ya koma,yanzu ma ba wani fuska yake gani a wajen ta ba,don duk wata hanya ma da za ta kusanta shi da Ajmal ta toshe ta

Sulaiman kam ya zama babban abokin ta, musamman ma yadda yake ɗebe mata kewa da shiririta da barkwancin shi,hakan ya ƙara rashin jituwa tsakanin ta da Mifra,tun ta na damuwa har ta watsar,sai ma idan ta gaya mata magana ita ma ta mayar mata

Sun shiga ss3 lafiya,inda karatun su ya ɗauki zafi fiye da koyaushe kasancewar SSCE ta sako su a gaba,ga JAMB,yau ba ta dawo ba sai wajen la'asar,an tashi su wajen ƙarfe uku,motar ta ta bata matsala a hanya sai da aka gyara,ga yunwa ga gajiya,ta na shiga Ajmal da a yanzu zai kai shekara ɗaya amma ya na yawon shi ko'ina,ya taho da gudu ya ɗane ta ya na gwaranci ya na kiran umma da shi kaɗai ya iya,ta rungume shi sosai ta na kissing kumatun shi,ta na murmushi ta ce "I miss you best friend,na same ka lafiya?"shi dai babu baki sai gwaranci,ta dire shi ta na murmushi ta kama ɗan hannun shi suka nufi ɗakin ta

Sallamar Sulaiman ta ji,ta waiga da murmushi ta na kallon bakin ƙofar,ganin tare suke da Auwab da ta manta da shi ma a duniyar ta sa fara'ar ta ta ragu,ta na murmushi ta ce "sannu da zuwa yaya Sulaiman"

"Yauwa sannu maman Ajmal!ya makaranta?da alamu ma yanzu kika dawo ko?"

Ta ce"dawowa ta kenan wallahi,na gaji,ga mota ta na ta bani matsala a hanya"sulaiman yace "Allah ya kyauta"Auwab kam ƙare mata kallo yake yi a cikin uniform ɗin makarantar,farar riga da straight skirt ash color,sai baby hijab wanda bai wuce ƙirji ba shima fari kamar rigar, Auwab ya ce"a haka kike zuwa makarantar?"

Wani banzan kallo ta watsa masa ta ce"kana da matsala da hakan ne?"

"Yeah of course,kar ki sake fita ba tare da kin sanya babban hijabi ba,wannan ba mutuncin ki bane, saboda ko babu komai kya kama kanki don darajar ɗanki ko?"

"To kai menene naka?me ya shafe ka da rayuwa ta da ta ɗana?"ya faɗa a harzuƙe

Auwab ya kalli Sulaiman da ya zauna ya na gyara zama ya na kallon su,ya yi murmushi ya na girgiza kai ya ƙarasa gaban Khairi ya kama hannun Ajmal, bai yi tsammanin Khairi za ta sakar masa Ajmal ba,ta juya da nufin shigewa ɗakin aunty Hafsa da take sallah har lokacin

Jiyo Auwab ta yi ya na faɗin "na yi missing ɗin ka yaron maman shi,da tuni yanzu sunan ka ɗaya da abban ka kamar yadda kuke kama ɗaya,kaga munafukin da ya janyo hakan bai faru ba"ya faɗa yana nuna sulaiman da yake ta dariya,ita ma Khairi sai da ta ji abin ya bata dariya musamman da ta tuna abinda ya faru a lokacin, Sulaiman ya na dariya ya ce"kai dai gaya masa gaskiya, babu ruwan Sulaiman"Auwab ya yi ɗan murmushi kawai ya ɗauki Ajmal suka yi waje, sulaiman ya bi bayan shi

Bayan maghriba aunty Hafsa ta na wajen inna Sa'a, ɗaya daga cikin masu aikin gidan,ita kuma Khairi ta kunna waƙar my Shayla ta juma jux ta na ta rawa, don rawa da waƙa a wajen Khairi yanzu an samu cigaba fiye da baya,ta yi wayayyun ƙawayen da suka mayar da ita ruwa tsundum,ta saka Ajmal a gaba ta na rera masa baitukan waƙar

"I will be there for you today and tomorrow 🥰

I just want you to know 😊

You are my Shayla 💃

You are my everything 🥰

Oh my radar 🤩O ti shey di e sin

My bebe,my bebe kanife,you are my bae😘

You'll be my Shayla,and my everything 💃💃💃!!"

Ta na bin waƙar da ta kunna a TV ta na rawa ta na rungume ɗan ta da yake ɓangale baki, Auwab ya shiga ya ɗauke Ajmal da ta ɗan ajiye shi a kan kujera,duk a cikin rawar,ya na kallon ta ya ce"ɗan nawa za'a koyawa shaiɗanci kuma?to gaskiya ba zan lamunci hakan ba"

"Na sha gaya maka ka fita a harka ta kaƙi,amma ka iya cewa ba ni da kunya,to ka cigaba da tsokana ta wallahi zan fara ramawa"

Ya ɗauke Ajmal ya nufi hanyar fita ya na faɗin "fara ramawa zaki yi dama?"

Ɗaga murya ta yi ta ce"ai ko me na yi maka kai ka ja, kai ne ka shiga harka ta"

Sulaiman da ya shigo ya na dariya ya kama hannun shi suka koma cikin part ɗin ya na kallon Khairi ya ce"zuwa yanzu ya kamata ayi wa yaya na afuwa a yafe masa,ya sha wahala sosai fa"

Taɓe baki ta yi ta ɗauke kai ta ce

"Shi ya ga zai iya ai,ni ina da abin yi"ta shige ɗakin ta ta bar su Sulaiman ya na ta yi wa Auwab shaƙiyanci

Ƴan mintuna da ficewar Auwab da Sulaiman Khairi ta ji sallama,ta fito ta na kallon Mifra da ta haɗe girar sama da ƙasa ta na kallon khairi

"Me mijina yake yi a wannan part ɗin? me yake kawo shi nan ɗin?"

Khairi ta ɗan yamutsa fuska ta ce"I can't get you,ban gane me kike nufi ba"

"Ina nufin me kika yiwa miji na ya liƙe miki babu dare babu rana? wace ce ke a cikin mata da mijina yake gaya min magana a duk lokacin da na nemi kar ya zo wajen ki?tukunna ma,ke macen gida ce ko karuwa?ki bi yaya ki bi ƙani,ki bi wasu ma dabam,to bari ki ji,duk wani abu da kike taƙama dashi na fiki,last time nayi Miki magana na ja miki kunne amma kika manna min hauka saboda kina tashe ko?to ina Miki gargaɗi da babbar murya ki fita harkar miji na,don shi ɗin ba property ɗin ballagazazzu irin ki bane,ki kama mutuncin ki ki riƙe darajar ɗanki sannan ki cigaba da yaƙi da jahilcin kanki,ko Kya zama mutum,amma ni ba zan iya bin bagidajiya irin ki ba muna gasa,don haka,idan kin ji gargaɗi na kinyi wa kanki,idan baki ji ba to za ki gani akan ki, shashasha kawai"tana kai wa nan ta juya a fusace ta fice daga parlourn ta na jan tsaki,ta bar khairi da bin ta da kallo kamar an dasa ta

Har dare ya raba khairi bata yi bacci ba,bata taɓa jin ta tsani kanta kamar yau ba,kowa baya son ta, komai baya yi mata daɗi,don haka gwara ta nisanci waɗannan bayin Allah ko za ta ji salama a ranta,ta waiga ta kalli inda take kwantar da Ajmal,baya nan ya na wajen mahaifinsa,ta goge hawayen idanun ta,tun a yanzu ta fara kewar gudan jinin nata wanda take ji a duniya bata da kamar shi,shima bashi da kamar ta

Ana fita sallar asuba Khairi ta saka hijabi ta faki idanun mai gadi ta fice daga gidan,gaba ɗaya garin ma ji take ya yi mata zafi ballantana gidan,ji take idan bata nisanci mutanen gidan ba ma za ta iya mutuwa,don haka ko waiwaye bata yi sai da ta bar area ɗin gaba ɗaya sannan ta fara tunanin inda ya kamata taje

To pa!anya Khairi ta yi dabara???

Kada dai a manta VIP group #300 ne kacal


#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee
*Young talented writers association (YOTA)*

Page 68

Napep ta tsare kai tsaye ta ce ya kai ta tasha, lokacin da ta isa can wajen ƙarfe shida saura ƴan mintuna,ta yi Sa'a motar Kaduna ta na lodi, ba tare da tunanin komai ba ta shige,dama ta fito da kuɗi,amma banda kuɗi ba ta fito da komai ba

Sam ba ta kula ba an gama lodin ba ma sai da ta ji motar ta tashi, saboda lulawa da ta yi duniyar tunani,ta rufe fuskar ta da hijabin ta hawaye ya na ta wanke mata fuska

Bata san ina za ta je ba,ba ta san dalilin da ya sa ta tsani gida ba,ita dai gwara ta yi nisa da gidan, wataƙila ta daina jin baƙin ciki da ƙuncin da take ciki

Ajmal!shine yake ta zuwa ranta,hawaye masu zafi suka zubo mata,ta kasa gane dalilin ta na tsallake yaron ta ɗan shekara ɗaya da wata ɗaya ta shiga duniya ko me aka yi mata kuwa,ta sani Ajmal baya cin abinci,madara ma idan bai ga dama ba baya sha,shi dai ya fi gane ta shayar dashi kawai,kuma yadda suka shaƙu ba ta san yadda zai yi ba idan ba ta nan,ta ci gaba da kuka har bacci ya yi awon gaba da ita


HAƊEJIA ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA

Wajen ƙarfe bakwai na safe aunty Hafsa ta gama gyara gidan ta yi girki,ta yi mamaki sosai da Khairi bata leƙo ta gaishe ta ba,amma sai ta yi tunanin ko ta makara ne, saboda idan makara ta yi ba ta tashi da wuri ba sai ta gama duk shirin ta sannan ta fito

Har wajen bakwai da rabi aunty Hafsa ba ta ji motsin Khairi ba,da sauri ta fice daga ɗakin ta ta nufi ɗakin Khairi don ganin ko lafiya

Sai dai ta yi ta sallama har sau uku amma shiru,da sauri ta shiga don ganin ko lafiya,amma sai ta ga wayam

Mamaki ya kama ta,to ina Khairi ta je?jiya dai ta tabbatar ta yi mata sallama ta shiga ɗaki tun da wuri amma ba ta ga lokacin fitar ta ba,amma haka ta nufi part ɗin Ammi don ganin ko tana can

A bakin ƙofar suka haɗu da Auwab riƙe da Ajmal da yake ta ƙananun kukan rigima,da alamu dai so yake ya ga maman shi, aunty Hafsa ta rissina ta na gaishe shi

Da sauri ya miƙa mata Ajmal ya ce"yauwa!gashi kai mata shi,ya na farkawa ya fara kuka,ina ga yunwa yake ji"

Tsumu ta tsaya ta na kallon shi,ya ce"ki amshe ki kai mata shi maza,kar haƙurin shi ya ƙare ya kama kuka sosai"

Cikin mamaki ta ce"to ai duba ta na zo yi anan,bata can ɓangaren ta,na ɗauka ta zo nan shine na biyo ta"

Shiru ya yi kafin ya ce"Ummul khair ba ta zo ba,ki dai sake dubawa,ko ta tafi makaranta ne?"

Aunty Hafsa ta girgiza kai ta ce"Khairi duk saurin da take yi ba ta fita daga gidan nan sai ta shayar da ɗan ta ta yi masa wanka da kanta,ko da ba'a wajen ta ya kwana ba"Auwab bai sake magana ba ya juya da sauri ya koma sashen Ammi

Abu kamar wasa ƙaramar magana ya zama babba,tun suna neman ta su biyu har suka gaji suka sanar da Ammi dake bacci, Surayya ma ta fito ta kira layin Khairi,ta yi ta ringing amma ba'a ɗaga ba

Haka suka yi ta gwada number ɗin ta,a ƙarshe Sulaiman ma da ya zo part ɗin yanzu ya shiga cikin su aka yi ta gwada kiran Khairi amma ba ta shiga

Cikin sarewa Sulaiman ya ce"ku daina kiran ta a waya,ba ta tare da wayar ta,da zuwa yanzu ta kashe ta"

"Me kake nufi ne Sulaiman?"a cewar Ammi da ta firgice lokaci ɗaya

"Khairi ba ta ignoring kira,sai dai ta kashe wayar baki ɗaya,don haka a san wani abin yi ɗin kawai"

Kafin azahar gaba ɗaya mazauna gidan sun san Khairi ba ta nan, Mifra ta tsorata sosai,don ta sani kai tsaye za ta iya barin gidan ko don maganganun da ta gaya mata,Abba dai ya yi wa Ammi faɗa sosai don a ganin ta kamar da sakacin ta Khairi ta ɓata ba'a sani ba

Cikin kwanaki biyu gaba ɗaya gidajen biyu ya hargitse babu nutsuwa a cikin su,su Nusra sai koke koke suke yi,mum kam dama bata da lafiya tun kwanciyar Azad,to yanzu abin ya fara dawowa,Azad ne kawai bai sani ba,don su Abba sun hana a sanar masa

Auwab kuwa gaba ɗaya ya fita a hayyacin shi daga shi har Ajmal,wanda ya rame sosai saboda bai saba da abinci ba,madara kuma sai ta kama dole yake sha,ya saba da shayarwar mahaifiyar shi da take yi masa a ƙalla sau uku a rana,a yanzu kuwa yayen dole ya kama shi, kullum ya na hannun Auwab yayi jugum,ko kuma ya na kuka yabna kiran umma!da shi kaɗai ya iya faɗa


KADUNA STATE

A tashar da khairi ta sauka ta haɗu da wata mata mai abinci, abinci ta siya ta ci,sannan ta samu waje gefen da matar take ta zauna ta na tunanin inda za taje

Matar ta kalli khairi ta ce"lafiya dai ko?na ga kin zauna kin yi tagumi"Khairi ta sauke ajiyar zuciya ta ce"ba komai"

"A'a ki faɗi abinda yake damun ki,ba komai kika zauna a tasha?"

"Kawai dai,ban san kowa a garin nan bane"shiru matar ta yi ta na kallon ta da mamaki,kafin ta ce"to me kika zo yi nan ɗin?kina matsayin mace?kuma yarinya?kar dai ki lalata rayuwar ki da bariki don Allah, wallahi babu ranar da take yi sai dai ayi nadama"

A sanyaye khairi ta girgiza kai ta ce"ba bariki na zo yi ba,na rasa iyaye na ne,kuma bani da kowa,shi yasa na zo nan,ban san inda zan je bane"


Shiru matar ta yi tana kallon ta da tausayawa,don ta ga gaskiya a idanunta,kafin tace"yaya sunan ki?"

"Suna na Amina"

"Ashe ma uwa ta ce,ai ko don wannan sunan ba zan bar ki anan ba,za ki bi ni gida na ki rinƙa taya ni aikin abinci ina biyan ki?"

Murmushi Khairi ta yi ta ce"in sha Allah,na gode "

Matar tace"babu komai,ni dai fata na don Allah ki riƙe amana"

Khairi ta ce"in sha Allah "

Tare suka ƙare siyar da abincin, Khairi ta wanke kwanukan suka wuce gidan matar,har lokacin Khairi jin zuciyar ta take yi kamar zata fashe,banda tunanin Ajmal babu abinda take yi,ta kasa gane dalilin ta na barin gida irin haka

Gida ne maidaidaici mai ɗakuna uku,matar da ta gabatar da kanta a wajen Khairi da mama Hajara ta bawa Khairi ɗaki ɗaya,khairi ta shiga ɗakin ta na ƙare masa kallo

Akwai ƴar yaloluwar katifa a ɗakin,sannan akwai wani tsohon cupboard irin na da,da fanka sai ledar tsakar ɗaki,dama ta ci abinci ba ta jin yunwa,ta fita tsakar gida ta yi alwala kasancewar babu banɗaki a ɗakin nata,ta gabatar da sallar la'asar sannan ta zauna ta yi shiru ta faɗa duniyar tunani

Mama Hajara ita kaɗai ce a gidan take rayuwar ta,ƴar ta ɗaya kuma ta na ƙasar Kamaru tana aure, shi yasa ta ji daɗin samun Khairi,sai take jin ta kamar ƴar ta


BOSTON, MASSACHUSETTS, USA.

"Weldon Shukra,a wannan karon na ji daɗin aikin ki fiye da koyaushe, don haka zan tura Miki kuɗin da kika ce,amma bayan nan Please ba na son ki sake damu na da batun kuɗi,ke kenan baki da aiki sai na tambayar kuɗi"

Shukra ta yiwa Inaaya wani banzan kallo ta ce"dole na nemi kuɗi saboda kema kin sani kuma kin shaida kuɗi sune komai,ba don kuɗi ba da baki kai inda kika kai ba,da baki juya wanda kika ga dama ba"

"Then,so?ko kina tunanin ko babu kuɗi kilaki kamar ki ta kai darajar da za ta kai darajar mace iri na har ta yi tunanin zata juya wani?to bari kiji,ishashshiyar mace ita ce wadda take gaban iyayen ta, kuma gidan mijin ta,ba wadda ta bar gidan su ta shiga yawon bariki ba!"

Maganar ta yi wa Shukra zafi,amma ta yi ƴar dariya ta na kallon inaaya tace"bariki dai bariki dai!!kin manta ita ce ta haɗa mu?kina yi ina yi?"

"Kema kin san ba saboda kuɗi nake yi ba, kin san nafi ƙarfin in fita neman kuɗi wajen wasu,kuma kin san ko a bariki aji aji ne,kin san nawa yana sama,so calm down,ki kwantar da kai kawai ki mori arziƙi Madam!"

Shukra bata sake magana ba sai bin Inaaya take da idanu,a ranta kuwa ita kaɗai ta san me take ayyanawa,Inaaya bata damu ba ta tura mata 5m da ta yi mata alƙawari,ta kalle ta fuska babu yabo babu fallasa ta ce"na tura Miki kuɗin aikin ki,ya kamata ki tafi kar ki rasa Flight"

Shukra ta ɗan bi ta da kallo kafin tace "ba tare zamu tafi ba?ba kin ce za ki Nigeria ba?"

"No tafi kawai,daga baya zan biyo ki"

Shukra ba ta so hakan ba,don budget ɗinta zai tarwatse, don haka ta ce"why not mu tafi yanzu?kin san da zafi zafi ake dukan ƙarfe"

"Shukra! ba'a bani command ko kin manta ne?"

"I'm sorry ma'am!"

"Gwara ki tafi kar ki rasa Flight "ta faɗa ta na ɗauke kai

Shukra ta miƙe ta na faɗin "alright!sai kin zo"Inaaya bata yi magana ba ta miƙe ta shiga ɗakin ta, Shukra kuma ta fice daga gidan


HAƊEJIA ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA

Yau kwana shida kenan da ɓacewar Khairi,babu irin nema da cigiyar da ba'a yi ba amma an rasa ta,gaba ɗaya gidan lieutenant general da gidan barrister kowa ka kalla a firgice yake, Daddy da Abba sun baza kuɗaɗe a masallatai da makarantu da gidajen marayu kan Allah ya bayyana ta ya tsare ta a duk inda take

Yau tun safe da ƙyar Auwab ya sha tea,har yanzu da ake maganar ƙarfe uku na yamma babu abinda ya iya sakawa a bakin shi,shi kam Ajmal zuwa yanzu ya fara sabawa da madara, Allah ya saka masa dangana, yanzu bai cika kiran umman shi ba,yanzu ya na hannun Ammi,sai abban na shi da yake ɗaukar shi lokaci lokaci


Gaskiya masoyan Azad a wannan karon ko ba ku tausayawa Auwab ba ai ya kamata ku tausayawa ɗanshi😭

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee

Page 69

Yau ma ya na zaune a parlourn,gefen shi Surayya ce da ta yi jugum ta na ta kallon Ajmal da yake ta ƴan wasannin shi na yara

Sallamar da suka ji ne ta sa suka yi saurin ɗaga kai suna kallon mai shigowa, Inaaya ce,sanye cikin baƙar abaya,ta sanya baƙin spec da ya cinye rabin fuskar ta,hannun ta riƙe da ƴar jaka, fuskar nan a ɗaure babu rahama

Ta na shigowa Auwab ya miƙe da sauri,ta ƙaraso ta ɗan rungume shi,sannan ta kalle shi ta na murmushi ta ce"tafiya zamu yi fa,babu time"babu musu ya miƙe tsaye ya ce mata"okay let's go"

Mamaki ya kama Surayya ta bi su da kallo,daidai lokacin da Ammi ta fito daga ɗakin ta, itama bin su ta yi da kallo,suna daf da fita ta yi ƙarfin halin cewa"ina zaku tafi? Auwab ina zuwa kuma?"

Inaaya ce ya juyo ta na kallon su da murmushi akan fuskar ta ta ce

"Sannu mama,ina kwana ina gajiya,na jira shi ne bai dawo ba,shiyasa na ga gwara na zo na saka shi a gaba mu tafi"

"Bai gaya miki ƙanwar shi kuma matar shi ce ta ɓata ba?"Ammi ta faɗa a zafafe

Maganar ta daki Inaaya,amma sai ta yi murmushi ta ce"oh ɓata ta yi?to Allah ya bayyana ta,amma sai nake ganin kamar babu amfanin zaman shi ko?tunda dai na ga ba nemo ta zai yi ba ko?kuma ba saurin bayyana za tayi ba idan yabna nan ko?"

Da mamaki suka bi ta da kallo,ganin za ta sake jan hannun shi ya sa Ammi ta buga masa tsawa"Auwab dawo!babu inda za kaje sai an ga Khairi!"

Inaaya ta kalle shi ta mayar da hankali ga Ammi ta ce"sai haƙuri fa mama,amma tafiya dole muyi ta"Ammi ta jinjina rashin kunyar Inaaya,amma sai ta ce"Hajiya ba dake nake ba,da ɗana nake ko?"

Wata ƴar dariya Inaaya ta yi ta kalle shi ta ce "to kai ka ji!"

Auwab kanshi a ƙasa ya ɗan girgiza kai ya ce "Ammi ya kamata na tafi Please,don Allah ki yi haƙuri,ba girman ki bane jayayya da sirikar ki!"

Sakin baki Ammi ta yi da tsananin mamaki ta na kallon Auwab, Inaaya ta kalli Ammi ta na wani miskilin murmushi ta ce"to Ammi,sai in ce sai anjuma ko?"ta ja hannun Auwab suka nufi ƙofa

"Auwab!ni?ni kake zaɓar matar ka a kaina? inna lillahi wa inna ilayhi rajiun!"sai ta fashe da kuka,itama Surayya tuni ta fashe da nata kukan

Sulaiman da ya shigo ya ƙaraso da sauri ya na faɗin"menene haka Ammi?don Allah ki daina kukan nan,ki ƙyale shi ya tafi,ai zai dawo,ana neman shi ma sosai a wajen aiki wai za su fitar da wasu motoci,don Allah ki ƙyale shi "ya waiga ya kalli Auwab ya ce"big bruh Allah ya kiyaye hanya,ku tafi kawai kar kuyi missing flight"Inaaya dai tsananin mamaki ya hana ta magana,don ta na shigowa Sulaiman ya shigo,ta na murmushi take faɗin"ya haƙuri?na ji ance ƴar Gold ta shiga duniya ko?"

Haka kawai ya ji maganar tata ta hau da wani tunani da yayi,ya yi murmushi ya ce"ƙwarai kuwa,yanzu sakamako kawai ya rage"

Ta yi ƴar dariya tace"shima wanda kuke taƙama dashi ɗin zuwa na yi na janye shi mu tafi,idan ya so sai na ga kai kuma me za ka iya?"ya yi murmushi again ya ce"fatan Sa'a!"

Jan hannun ta da Auwab yayi ne ya sa ta dawo daga tunanin da ta tafi,sai taji duk gwiwar ta ta sage,don ta san Sulaiman zai iya aikata mata abinda bata yi tsammani ba,don haka ta ƙudurce a ranta zata zama cikin shiri

Suna fita Ammi ta fashe da kuka sosai ta na faɗin"ta raba ni da ɗana, Sulaiman a gaban ka ta ja hannun ɗan uwan ka suka tafi sun bar ni!"

Cikin kwantar da murya ya ce"Ammi tunda kika ga na yi hakan akwai abinda na shiryawa ne,ke dai kawai ki bi mu da addu'a kawai,kar ki damu,in sha Allah da Khairi da Auwab duk za su dawo,su sasanta kansu su ƙara haifa Miki kyawawan jikoki ƙannen Ajmal "duk da damuwar da take ciki sai da ta yi ɗan murmushi, sulaiman ya fice zuwa sashen shi

Mifra ba ta parlour sai Anam da ke ta wasannin ta,bai kula ta ba saboda yana cikin damuwa ya wuce ɗakin mifra

Jin maganar ta ya yi ta na waya,sai ya ɗan dakata don ya jira ta gama,sai ya ji ta na faɗin

"Ni wallahi na yi mamaki,ban taɓa tsammanin maganganun da na yaɓa mata za su saka ta bar gidan nan ba,kuma don hauka har da dire jaririn ɗanta,to dai har yanzu ƙoƙarin neman ta suke yi amma shiru,duk Abban Anam ba ya hayyacin shi"

Ɗan shiru ta yi kafin ta ce"ke dai bari aunty Laila,da farko yarinyar tausayi take bani,amma sai makirci da kissa ƴar ƙarama da ita,da farko da na tuntuɓi abban Anam ce min yayi wai kamar su Surayya take a wajen shi"


Ta yi ƴar dariya bayan ta gama sauraren mai mata magana ta ce"munafukai ɗaya aunty Laila?kuma baki na ƙanin ƙafata na yi gum,babu wanda na gayawa ni na kore ta a gidan nan,shegiya mai ...."

Maganar ta maƙale a lokacin da ta buɗe labulen ta ga sulaiman a tsaye a bakin ƙofar ɗakin yana jifan ta da wani irin kallo mai firgitarwa,da alamu duk abinda take faɗa ya na jin ta

kai ya juya ya fice daga ɗakin,ya fice daga part ɗin baki ɗaya

Tuni Mifra ta zube a ɗakin ta ɗora hannu aka ta na faɗin "na shiga uku,yanzu me zai faru?me zai yi min?ya Allah na tuba,ka ceci aure na!"


LUGARD ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA

Da mamaki take kallon shi,shima kallon na ta yake yi,da ƙyar ta furta "welcome big bruh!"

"Weldon Bilkisu!na same ku lafiya?"

"Lafiya ƙalau,ya hanya?"

"Hanya alhamdulillahi,ina mum?"ɗan murmushi ta yi tace

"Mum ta na ciki ɗan mummyn shi,ta ɗan sha magani ne shine ta kwanta"

Zaunawa ya yi yana kallon ta,ba tare da ya kula da tsokanar shi da take yi ba ya ce"dama bata da lafiya shine ba'a gaya min ba?"

Girgiza kai ta yi tace"a'a,ka san dai tun lokacin da ka kwanta jinya itama sai ta kwanta,to shine har yanzu take karɓar medication,ka san kafin ka dawo ta ƙi yarda likita ya yi attending ɗin ta,to abin ya ɗan yi worst shine har zuwa yanzu ake duba ta"

Shiru ya ɗan yi kafin ya ce cikin sanyin murya "to Allah ya bata lafiya,kema kin yi jinya ne?"

Ta girgiza kai ta ce "a'a,me ka gani?"

"Kin rame sosai, lafiya dai ko?"

"Mhmmm!Abubuwa sun yi yawa yaya,kai dai ka ci abinci ka huta kawai,akwai labari"babu musu ya miƙe ya fice zuwa part ɗin shi,so yake ya samu ya leƙa Khairi,don kwana biyu ba ya samun ta a waya

Bai dawo part ɗin mum ba sai bayan awanni biyu, lokacin mum ta farka,ya gaishe ta da girmamawa,ta amsa ta na faɗin"zuwa babu sanarwa Azad?"

Ɗan murmushi ya yi ya ce"nayi missing ɗin ku mummy na, Bilkisu ina Yusaira ne?"

Beely ta ce"Yusaira ta na ɗaki ta na bacci,yanzu ta gama rigima ta shiga ta kwanta"

Ɗan murmushi ya yi ya ce"na yi missing ɗin su ita da ƙanin ta,gwara ita three days back na ji ɗuriyar ta,amma Ajmal rabo na da jin shi ten days kenan"

Kallon kallo aka fara tsakanin mum da Beely,Azad da mamaki yake kallon su,kafin ya yi magana Beely cikin rawar murya ta ce "yaya Khairi ta ɓata, ba'a san inda taje ba"

"What!ɓata? Khairin?are you listening to yourself ma kuwa Bilkisu?"

Hawaye suka ciko idanun ta,ta ce"yaya Khairi ta ɓata, wallahi ko sama ko ƙasa an neme ta an rasa,babu irin cigiyar da ba'a yi mata ba an rasa ta,bata tafi da yaron ta ba ballantana wayar ta"

Shiru Azad ya yi ya na jinjina kai a hankali,bai yi Magana ba ya miƙe ya fice daga parlourn,kai tsaye ya faɗa mota ya wuce Hadejia road,wani irin tashin hankali yake ji,sai dai ya yi ƙoƙarin saita nutsuwar shi ya na ta ambaton"inna lillahi wa inna ilayhi rajiun!"


Kada dai a manta VIP group #300 ne kacal

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee
*Young talented writers association (YOTA)*

Page 70

Allah ne ya kai shi gidan lafiya,kai tsaye cikin gidan ya nufa gabanshi ya na faɗuwa

Da sallama ya shiga parlourn,da mamaki yake bin occupants ɗin dake parlourn da kallo,Ammi ta na zaune a gefe, Surayya ta na gefen ta,sun zubawa Mifra dake durƙushe a gaban Sulaiman ta na kuka idanu, Azad ya mayar da hankalin shi kan Sulaiman da yake zaune ya na danna waya,ko kallo biyu bai yi wa Mifra ba

"Sulaiman me yake faruwa ne?mene ne haka kuma?"

Sulaiman ya ɗago ya na ɗan murmushi da za'a iya kiran shi na yaƙe ya ce"welcome big bruh!ya hanya?"

Azad ya ce"alhamdulillahi,amsa min tambaya ta Sulaiman!"

Sulaiman ya girgiza kai ya ce"ka tambaye ta,nima ban san me take yiwa ba,sai dai ta yi mana bayani baki ɗaya"Azad ya mayar da hankali ga Mifra, cikin kwantar da murya ya ce "maman Anam samu waje ki zauna mu yi magana"babu musu Mifra ta zauna ta na share hawaye ta na shashsheƙar kuka

"Me yake faruwa ne?me ya same ki kike kuka?"ya tambaye ta

Cikin gunjin kuka ta ce"don girman Allah ka ce masa yayi haƙuri,na san ya ji abinda nake cewa a waya,na yi nadama don Allah ya yi haƙuri "

Azad ya kalli Sulaiman, Sulaiman ya ce"ta maimaita maka abinda na ji ta na cewa,don ni babu ruwa na da ita wallahi"Azad ya mayar da hankalinsa kan Mifra,a hankali ya ce"Madam me ya faru?wayar me ya ji kina yi?"

Da ƙyar ta iya faɗin"a...a...a kan batun Khairi ne"

Sai da gaban shi ya faɗi,ya ce"me ya samu khairin?"

Cikin kuka da rawar murya ta fara bayani"wallahi sharrin shaiɗan ne,ranar da baban Ajmal ya dawo mun samu saɓani ne,na taɓa yi mata magana tun kafin lokacin cewa ta fita harkar miji na,amma sai ta ce shi da na isa dashi shi zanyi wa magana,dalilin haka sai raina ya ɓaci, shine lokacin da na ga ya shiga bangaren ta tare da abban Ajmal ɗin na je na same ta na gaggaya mata magana,ban san me ya faru ba washe gari kawai na ji an ce ba'a ganta ba"

"Ƙarya kike munafuka!ki faɗi abinda kika yi mata dai,don kin taɓa yi min maganar na rabu da ita nace ba zan rabu da ita ba,me kika ce min a ranar?cewa kika yi in dai kina raye sai gani na ya gagare ta,ko ba haka aka yi ba?

Nayi Miki bayani a baya cewa babu soyayyar aure a tsakanin mu kin ƙi yarda,don haka yadda gani na ya gagare ta,kema ki tattara naki kayan ki wuce gidan ku sai na neme ki,kar kiyi min wata magiya,don wallahi kaɗan daga aiki na na datse igiyar aure na dake,tashi ki bani waje"

Faɗar irin tashin hankalin da Mifra ta samu kanta a ciki ma ɓata lokaci ne,Ammi da Nusra dai sai kallon Mifra suke yi da matsanancin mamaki,suna kallo ta miƙe ta fice daga parlourn ta na gunjin kuka

Azad ya kalle shi cikin sanyin murya yace "anya hukuncin nan yayi daidai Sulaiman,ina ganin....."

"Don Allah yaya Azad ka bar ni kawai na hora ta,idan kuma kuka matsa min zata yi tafiyar da babu dawowa "shiru Azad yayi bai sake magana ba, Ammi kam dama bata yi magana ba,don sun san halin Sulaiman sarai,indai aka ƙure shi bai iya fushi ba

Sai a lokacin Azad da Ammi suka gaisa sosai, sannan suka jajanta abin, Azad ya ce"ina yaron nata da aka ce bata tafi dashi ba?"

Ammi tace"ya na wajen mai kula dashi, Hafsa,bai juma da barin nan ba"

Azad ya yi shiru cike da jimami,kafin ya ce"in sha Allah za'a ganta, Allah ya bayyana ta"

Suka amsa da"Ameen"

Bai juma ba ya tafi,amma kafin ya tafi sai da aka ɗauko masa Ajmal yayi masa wasa sosai,kafin ya tafi


HAYIN RIGASA, KADUNA STATE, NIGERIA


Sati biyu kenan Khairi ta na rayuwa a gidan mama Hajara,matar mutuniyar kirki sam bata da mugunta,kuma abin hannun ta bai rufe mata idanu ba,hakan ya ƙara wa Khairi ƙwarin gwiwa,ta sake zage damtse take mata aiki tsakanin ta da Allah,ita kuma bata fashin biyan ta kuɗin ta akan kari

Yau Khairi tana zaune ta na yanka alayyahun da zasu yi taushe dashi,mama ta kalle ta tace

"Ni kuwa uwa ta ga shawara mana"

Khairi ta kalle ta tace"ina jin ki mama"

Mama Hajara ta ce"akwai wata Hajiya, uwar ɗakina ce,a shekarun baya ta taɓa sanya wa a kawo mata ƴar aiki,sai na kai mata ƴata mardiyya, wallahi ba ki ga yadda ta kyautata mata ba,har makaranta ta saka ta,ta dai kula da ita kamar ƴar ta,to bayan auren mardiyya mun kai mata wata yarinya,sai dai cin zalin yaran ta take yi,ga sace sace kamar ɓera, wannan dalilin yasa suka gaji suka sallame ta,yanzu haka suna kan neman yarinyar da zata yi musu aiki ne,kuma suna biya mai kyau,akwai abinci mai kyau da wajen kwana mai kyau,mai zai hana ki jarraba uwa ta?"

Khairi ta ajiye wuƙar hannun ta ta ce"ni fa tsoron gidajen masu hannu da shunin nan nake mama,don bana son wulaƙanci, wa ya sani ma waccan yarinyar yaran rashin kunya suke mata shiyasa take dukan su?ko kuma ba sa bata abinci Shiyasa take musu sata?"

Ɗan murmushi mama Hajara ta yi ta ce"na gaya miki mardiyya fa ta yi aiki a gidan,wai don ta ji daɗin gidan ne yasa nake miki kwaɗayi,Kin ga ke marainiya ce zan so ki zama wani abu a rayuwar ki,wannan sayar da abincin duk wahala ne,ga ki matashiyar yarinya,amma menene shawarar ki?"

Khairi ta ɗan yi shiru kafin ta ce"to Allah ya zaɓa abinda yafi alkhairi,zan gwada zuwa,idan naga da matsala sai na dawo gida"

"Yauwa shikenan ma,jibi idan Allah ya kai mu sai muje in sha Allah, Allah yayi niki albarka "khairi ta yi murmushi kawai

Bayan kwana biyu Mama Hajara da Khairi suka tsari abin hawa tun daga rigasa zuwa malali,bayan sun sauka mama ta biya mai abin hawa kuɗin shi,suka nufi bakin gate ɗin mama ta ƙwankwasa ƙaramin gate

Mai gadi ya leƙo,ya na ganin ta ya rissina ya na gaida ta,ta amsa da fara'a suka shiga cikin gidan,dama sun yi waya da hajiyar

A parlourn gidan mama da Khairi suka zauna akan carpet, Khairi sai kalle kalle take yi,gidan Daddy da Abba yana ta dawo mata a rai

Kusan mintuna goma suka ji hayaniyar yara da maman su ta na yi musu magana,tuni Khairi ta gyara zama tana rarraba idanu don ganin waɗanda zasu sauko

Da kamar seconds goma matar da yaran ta suka bayyana,babbar mace ce da ba zata wuce shekaru talatin da biyar ba, kyakkyawar mace ce fara tas,yaran ta ma haka suke,farare ne kyawawa masu kama da ita,yaran ƴan biyu ne mace da namiji, waɗanda ba za su wuce shekaru uku da haihuwa ba

Da fara'a ta shigo parlourn ta na faɗin "Barka da zuwa mama,ya hanya,ya kasuwa kuma?"

Mama ta ɗan rissina ta ce"Barka da fitowa Hajiya!"

"Barka dai mama,ya hanya?"

"Hanya alhamdulillahi!yau dai na ce bari na cika miki alƙawarin ki,ga mai taya ki aiki nan na samo miki,akwai aiki babu ƙyuya,ga tsafta"

Matar ta zauna sosai ta na mayar da kai ga Khairi da ta ɗan rissina ta na gaishe ta,ta amsa cike da fara'a ta ce "sannun ki ƴan mata,yaya sunan ki?"

"Amina"ta bata amsa,matar ta ce"to da kyau Amina,ina fatan zamu zauna lafiya da ke"

Khairi ta ce "in sha Allahu bazaki same ni da wata matsala ba"

Matar ta ce"haka ake so,yanzu dai aikin ki shine shara,da gyara min gida,sai yara na ga su nan za ki kular min da su,abincin su da tsaftar su, abincin gida kuma ba sai kin yi ba,akwai cook na musamman da yake kula da wannan ɓangaren,ina fatan za ki iya?"

A sanyaye Khairi ta gyaɗa kai da ta tuna nata da ta bari a gidan su,a hankali hawaye ya cika mata idanu,matar bata kula ba ta cigaba da bayani

"Zan rinƙa biyan ki dubu talatin, idan kika ƙara ƙwazo sai na ƙara miki in sha Allah "

Khairi ta ce"to Hajiya na gode"matar ta ce "yauwa, ga yara na nan, ƴan biyu ne,sunan su Ashraf da Ashfa,don Allah ki ja su a jiki kamar ƙannen ki"

Khairi ta ce"in sha Allahu zan kula da su sosai Hajiya "

Daga nan Hajiya tayi wa mama alkhairi sosai,mama ta yi ta godiya,tayi wa Khairi sallama ta tafi

Hajiyar da kanta ta nunawa Khairi ɗakin ta, khairi ta ɗauki jakar kayan gwanjon da mama ta siya mata ta nufi ɗakin


Khairi a matsayin ƴar aiki😥

Kada dai a manta VIP group #300 ne kacal

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee
*Young talented writers association (YOTA)*

Page 71

A kwanaki biyu da khairi ta yi a gidan Hajiya ta fahimci halayen ta da yanayin rayuwar ta,mace ce mai sauƙin kai,akwai kirki da son hira,ta na da son gayu da kwalliya,ga son tsafta,don zuwa yanzu ta bawa Khairi kaya kusan kala biyar,ta na matuƙar jin daɗin yadda khairi take jan yaran ta a jiki,ita kuwa Khairi ta na jin yaran a ranta fiye da kowanne yara idan aka cire ɗanta Abubakar Ajmal,suma yaran kuma suna matuƙar ƙaunar ta

Ta na fita aiki da safe,ta kan dawo wajen ƙarfe uku na yamma, Khairi ce take zama da su Ashraf da suke kiran ta da aunty Meena, kamar yadda maman su ta koya musu

Lokaci ɗaya Khairi ta chanja ta yi kyau, matsalar ta ɗaya ta kasa cire yaron ta a ranta,duk lokacin da ta ga yadda Mamie,kamar yadda yaran suke kiran ta tana tarairayar yaranta,ko ta dawo aiki suka tafi da gudu suka rungume ta suna bata labari sai Ajmal ya faɗo ranta,sai ta yi kuka sosai a ɓoye


LUGARD ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA

A ƴan kwanakin nan gaba ɗaya Azad babya cikin nutsuwar shi,ƙarfin hali kawai yake yi,jikin mum gaba ɗaya ya rikice,kuma ta ƙi yarda a kwantar da ita s asibiti, har yanzu sai dai likita yazo ya duba ta ya tafi

Ga kuma ɓatan Khairi wadda har zuwa yanzu ba'a samu ko alamu na inda take ba,gaba ɗaya ya gigice,ko abinci baya iya ci sosai

Yau ma ya na part ɗin shi ya na zaune,wayar shi ce take ta ruri,kamfanin da yake yiwa aiki a Melbourne ne suke ta faman neman shi amma ya ƙi ɗaga wayar,to yanzu ma idan ya ce zai je ya yi aiki a can me zai iya yi?mata biyu da yake so fiye da rayuwar shi, ɗaya ta na kwance bata da lafiya, ɗaya kuma ma bai san a wanne hali take ciki ba ma,ya goge hawayen idanun shi a sanyaye,dama shi Azad akwai saurin karyewar zuciya

Sallamar aunty Naja ya ji,ya ɗaga kai ya na kallon ta gami da amsawa a sanyaye,ta ƙaraso ta na kallon shi cikin tausayawa,ya ɗan saki fuskar shi ya na faɗin "sannu da shigowa aunty!"

Ɗan murmushi ta yi itama,ta ce"sannu Azad,ya mai jikin?"

Ya ja ajiyar zuciya ya sauke ya ce"mai jiki da sauƙi"bata sake magana ba ta ajiye basket ɗin hannun ta ta fara ƙoƙarin zuba masa abinci

A sanyaye ya ce"aunty ki bar shi ba na jin yunwa"ba ta kula shi ba sai da ta gama zubawa ta miƙa masa plate ɗin ta na faɗin"maza karɓi,ka bani plate ɗina,yanzu gaba ɗaya baka cin abinci,duk ka rame,gashi kuma na zage na yi maka abincin da ka fi so,maza karɓi"jiki s sanyaye ya karɓa,ya fara turawa,duk son da yake yiwa pounded yam da miyar egusi ɗin sai yaji shi kamar magani

Sai da ta tabbatar yaci sosai sannan ta yi ta masa nasiha cikin hikima ta na bashi ƙwarin gwiwa har ya ji sauƙin ƙuncin da yake ji,daga baya ta yi masa sallama,ya yi mata godiya ta kwashe kayan ta ta tafi


BOSTON, MASSACHUSETTS, USA


Yau Inaaya kwanan ta biyu ba ta nan,ta yi tafiya zuwa ƙasar Canada,a cewar ta wani aiki zata yi makaranta sun tura su

Daga jiya zuwa yau gaba ɗaya zuciyar shi a sake yake jin ta,gaba ɗaya sai yake jin kanshi kamar wani prisoner da aka ɗaure tsawon shekaru yau aka sallame shi,sai dai gaba ɗaya kewar gida ta dame shi,don haka yau bai dawo daga aiki ba sai da ya sallami abokan aikin shi don ya na so ya je Nigeria ya ɗan kwana biyu

Harabar gidan ya fito ya zauna ya na kallon flowers ɗin da suka ƙawata gidan,daidai nan aka buɗe gate aka shigo

Kallo ɗaya yayi wa matar ya ɗauke kanshi, bai yi mamakin irin shigar da ya ganta da ita ba saboda yanayin society ɗin,ko nace yanayin ƙasar,yana nan zaune ta ƙaraso kusa da shi ta na faɗin "hye!"sannan ta nemi waje kusa dashi ta zauna

"Good morning Mr charming!"ta faɗa tana kallon fuskar shi ta na ɗan murmushi

Bai amsa ba sai gyaɗa mata kai da ya yi, fuskar shi a ɗaure ya na kallon ta,bata damu ba ta ce"idan babu damuwa ina son ka bani wasu ko da thirty minutes ne,wata magana mai muhimmanci zamu yi "shi dai bai ce mata uffan ba, ba ta damu ba ta Ciro wayar ta ta buɗo wani hoto ta ɗaga wayar ta ta na nuna masa ta ce"ka san wannan?"

Kallon ta kawai yake yi ba tare da ya ce uffan ba,ta yi ɗan murmushi ta ce"ba abin mamaki bane ka santa ko kar ka santa, sunanta INAAYA MUKHTAR,ita ɗin matar ka ce, abinda ya sa nace bai zama lallai ka santa ba shine saboda sai da ta juyar maka da hankali sannan har ka yarda ka aure ta

Kar na kai ka da nisa,ni dai suna na Shukra ne, asali na ƴar garin Yobe ce,amma na rabu da iyaye na,mun haɗu da Inaaya a Kano,iyayen Inaaya suna da matuƙar wadata,kuma ita kaɗai ce ƴar su, rayuwa suke yi cike da ƴanci da rufewar idanu,a dalilin haka Inaaya take abinda ta ga dama

Na liƙewa Inaaya ne saboda na ga zan samu maiƙo,na yaudare ta na janyo ta ƙungiyar mu,ta koyi lesbian,har ma da homo sex,dama tun sanda na ganta ta saba bin maza,sai dai ba kowanne namiji take bi ba, kasancewar ta kyakkyawar mace sosai,sannan kuma ita ba baƙuwar kuɗi bace,bugu da ƙari kuma tana da gadara da nuna isa,ta na da girman kai da taƙama,hakan ya jefa min ƙyashin ta shekara da shekaru,amma hakan baya hana ni na yi mata aiki don ina damfarar ta kuɗaɗe masu yawa, Shiyasa ban so komai ya ruguje ba amma babu yadda na iya,dole na kawo ƙarshen jin kan ta

Duk abinda zan faɗa maka a yanzu ina da hujja,akwai voice da video record da na yi mana lokacin da muke ƙulla tsiyar mu,don haka zan kunna maka

Da farko dai Inaaya asiri ta yi maka ka faɗa soyayya da ita, kai ne namiji na farko da ya fara burge Inaaya har ya ji sha'awar aure,amma abin takaici wancan karon da ta yi maka magana har sau biyu a nufin ta fara neman hanyar shiga sai ka wulakanta ta,asalima ko kallon arziƙi bata ishe ka ba,hakan ya taɓa mata ji kumarta,ni da kaina na kai ta gun wani hatsabibin boka,muka yi Sa'a kai ɗin ba mai damuwa da addini bane sosai,don haka aikin mu yayi nasara sosai

A wancan lokacin ta yi maka asirin da yasa ka tsani dangin ka ka daina shiga cikin su,ciki har da aminin ka,kuma ɗan uwan ka sulaiman, hujjar ta ita ce bata son takura da yawan bibiya irin na wasu mutane,kuma ta san danginka zasu iya aikata hakan

Tayi wa mahaifin ka asiri ya kwanta jinya na tsawon lokaci saboda ya zo har nan garin don ganin lafiyar ka

Ta yi maka asirin da ya sa kake jin zaka iya bijirewa iyayen ka akan duk abinda bata so,ka tuna matar ka Ummul Khairi?to tayi maka asirin da yasa ka tsane ta,a ƙarshe ka yi mata sakin wulaƙanci,a ƙarshe dai, Inaaya tayi wa Ummul Khairi asirin da ta shiga duniya aka neme ta aka rasa,yanzu kuma shirin ta shine ayi wa ɗan ka ɗaya tilo asirin da zai bar duniyar baki ɗaya!!!"

Yadda ya zuba mata idanu cike da tsananin mamaki ya na kallon ta har ta gama bayanin ta bai iya sake ko motsi ba, Shukra ta yi wani murmushi ta kama danna wayar ta,sai ga voice kala kala na Inaaya,na irin makircin da ta shirya masa da family ɗin shi da sunan soyayya

Jikin shi ya kama rawa, amma ya gagara furta komai, Shukra ta miƙe ta na murmushi ta ce"ga su nan da voices da videos ɗin duka na tura maka ta Whatsapp,idan matar taka ta dawo ka ce ta rage ji da kai da alfahari da nuna isa,ta na saurin kai mutum ta baro"ta miƙe tsaye ta na ɗaukar jakar ta,daidai lokacin Inaaya ta shigo gidan riƙe da ɗan ƙaramin akwatin ta

Wani matsiyacin kallo ta fara watsawa Shukra,wadda take wani murmushin rainin hankali ta na kallon ta,cikin kwanciyar hankali ta ce"Barka da dawowa matafiya,ya hanya,ina Safwan ɗin?"

Gaban Inaaya ya buga,amma maimakon ta amsa mata sai tac e"uban me kuke yi ke da miji na?kin san dai ba zan lamunci cin amana ba ko?"

"Kin san dama an ce wanzami baya son jarfa,ke kina can kuna raƙashewa da mazan waje shi kin hana shi sakat,daga ya bar gari ga sana'ar shi kema za ki bar gari ga yawan dadiron ki,kar ki wahalar da kanki,na kwance masa komai na sirri,kafin nan kuma na lalata dukkan aikin da na yi miki"

Cikin wata kalar gigicewa Inaaya ta ɗora hannu akai ta na faɗin "har da baƙin aiki???"

Shukra ta yi wata dariyar rainin hankali ta ce"ai ta kanshi ma na fara,yo idan ban warware baƙin aiki ba me akayi kenan?duk tsiya in dai ya na son ki sai dai ya hukunta ki kawai,amma yanzu na san buri na zai cika,za ki wulaƙanta ki ƙasƙanta,zuwa yanzu ina fatan kin gane iya bariki ake buƙata a wajen karuwa ba kuɗi da isa ba"ta na kai wa nan ta yi hanyar gate ta fice tna jiyo ihun Inaaya ta na murmushi

"Wayyo Allah na bani na lalace!na shiga uku!! Shukra kin cuce ni, Shukra kin kashe ni,kin tona min asiri!me na yi miki!! don Allah Auwab ka saurare ni, wallahi soyayyar ka ta janyo na yi maka haka,na rasa yadda zan yi ne,ina tsananin son ka,don girman Allah ka yi haƙuri ka yi min uzuri, wallahi idan ka ƙaurace min zan iya mutuwa,ka tausaya min Auwab"tana ta haukan ta cikin nutsuwar shi ya wuce gidan ya ɗebo abinda zai ɗebo ya fito goye da backpack ya zo ya bi ta gaban ta,ta miƙe a haukace ta nufo shi,ya watsa mata wani mugun kallo da ya sa hantar cikin ta kaɗawa,ya juya don ya fice,kafin ya ankara ta riƙe masa kafafu cikin tashin hankali,kafin ta kai ga cewa komai cikin zafin nama ya wancakalar da ita ya fice daga gidan

Sai da ya shiga taxi sannan ya kira sulaiman,ya na jin muryar Sulaiman sai ya fashe da kuka sosai,mamaki da tsoro ya kama sulaiman,cikin gigita ya ce"ya dai big bruh?lafiya kuwa?"

Da ƙyar ya daidaita nutsuwar shi ya ce"Sulaiman ka na gida?"

Da sauri ya ce"eh ina nan,ga ni ga Aahir ma,ga su Ammi,me ya faru?"

"Okay" kawai ya ce ya kashe wayar baki ɗaya ya dafe kanshi,hawaye na yi masa zarya a fuska,bai taɓa riskar kanshi cikin tashin hankali ko da makamancin wanda yake ciki ba,ya rasa takaimaimai ma tunanin da zai yi,sai yanzu wasu abubuwan suke haskawa a kanshi,mace ta yi ta gara rayuwar shi kamar ƙwallo,ta shiga tsakanin shi da Abban shi,ammin shi da Sulaiman,ya yi saurin girgiza kai,a fili ya furta "impossible!!not me Auwab!"


MALALI,KADUNA STATE, NIGERIA


"Amina kin yi bacci ne?"

Khairi ta yi saurin zama sosai ta ce"a'a ban yi bacci ba,akwai abinda za'a yi ne?"

Mamie ta girgiza kai ta ce"a'a,dama na manta ne ban gaya miki ba, gobe yara na za su dawo,manyan ƴaƴa na da suke karatu a Cairo,don Allah zamu tashi da wuri mu shirya musu abin motsa baki,yau aiki ya yi min yawa ne,gashi na dawo da ciwon kai shiyasa ban yi miki maganar ba"

"Ayya!sannu Mamie, Allah ya ƙara sauƙi,babu matsala, Allah ya kai mu goben"Mamie ta yi murmushi ta ce"Ameen, mu kwana lafiya"ta fice daga ɗakin


Finally dai alkadarin Inaaya ya karye, Auwab ya dawo a Muhammad Auwab ɗin shi, readers yanzu na san zaku ji sanyi ko😅

Kada dai a manta VIP group #300 ne kacal


#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee
*Young talented writers association (YOTA)*

Page 72

Washegari tun da sassafe suka fara gyaran gidan da yin abinda ya kamata don taryar baƙin,ba su gama ba sai wajen azahar,daga khairi har Mamie kowacce ɗaki ta nufa don ta yi wanka ta yi sallah ta huta

Ita khairi ma bayan ta idar da Sallah ta haye kan gadon ta ta kama bacci,ta ɗan juma ta na baccin kafin ta farka,ta ɗauki hijabin ta ta fita zuwa parlour,in da take jin hayaniya na tashi,sai ta ji ma kamar akanta suke magana

Ɗaya daga cikin ƴan matan ta ji ta na bayani"Mamie Allah ya sa dai ba irin Barira ba ce,kin san har yanzu wannan watch ɗin nawa da yaya ya siya min?sai dai tashin zance?"

Muryar wata budurwar ta ji ya ƙyalƙyale da dariya ta ce"auntie Beela dama ke ce mai jin tausayin ta kina hana ni dukanta,amma ni tunda ta yi min rashin kunya na don na mata magana ta daina dukan su Ashraf na tsane ta"Khairi ta taɓe baki ta kutsa kai cikin parlourn

Da sallama ta shiga parlourn kan ta a ƙasa, tuni mutanen parlourn suka yi shiru suka waigo suna kallon ta,bata ko kalle su ba ta ce"sannun ku da dawowa,ina wunin ku?"

"KHAIR ALBASU!!! Is it you?"

Da tsananin mamaki ta ɗago tana kallon mai maganar,sai ta yi karo da wadda ko a mafarki kamannin ta ba zasu taɓa ɓace mata ba, NABEELA SALEH, ɗaya cikin ƙawayen ta na amana waɗanda suka yi Queen's College tare,cikin tsananin mamaki ta ce"Nabeela! Nabeela,ke..ke..ce .."sai ta fashe da kuka ta durƙushe a wajen

Nabeela ta ruga da gudu ta rungume ta suka cigaba da kukan tare,su dai jama'ar dake zaune a parlourn kallon su suke yi kawai basa fahimtar komai


Nabeela ce ta fara tashi ta na goge hawayen ta,ta kama Khairi ta miƙar da ita tsaye ta kalli Mamie ta ce"Mamie wannan ce Khairi albasu,ƙawa ta da nake baku labari,mun fara junior secondary school da ita a Queen's College lokacin da na yi karatu a Kano,to ita ta zana placement tana js2,daga nan bamu sake jin ɗuriyar ta ba ni da Amra,Nima kuma ina kammala js3 Daddy yace sai dai na dawo Kaduna na cigaba da makaranta,har zuwa yau muna zumunci da Amra,amma ban sake samun Khair ba, Mamie ina kika samo min ita?"ta ƙarashe magana ta na kama hannun Mamie da ta zubawa Khairi idanu kamar za su fito,ita kuwa Khairi kanta a ƙasa saboda tsananin fargaba da kunya

"Kenan yaudara ta kika yi?menene mission ɗin ki a gare ni da za ki zo gida na ko sunan ki ki kasa gaya min?waye ya aiko ki?"

Shiru ragowar mutanen parlourn suka yi suna kallon khairi,hatta Nabeela da mamaki take kallon su duka biyun,cikin kuka sosai khairi ta ce"wallahi ban yaudare ki ba,kuma bana fatan na yaudare ki,tabbas dake da mama ban kyauta muku ba amma bani da zaɓi ne kiyi haƙuri

Suna na kamar yadda kika ji ta faɗa Ummul Khairi ne, labari na kuwa ......"ta kwashe komai ta gaya musu,ta ƙarasa da faɗin "ni kaina har yanzu ban san dalilin da yasa na bar gida kai tsaye ba tare da wani dalili ba,don alwashi na ɗauka washegari sai na samu matar yaya Sulaiman na gaggaya mata maganar da zata ƙona mata rai,sannan na gaya wa mijin ta yayi mana iyaka,amma kafin washegari gari na ji ba zan iya jure zaman gidan ba,shiyasa kawai na bar gidan washegari kafin kowa ya fito,har yanzu ban san dalili na na barin yaro na wanda yake karɓar shayarwa ba,har kullum zuciya ta ciwo take yi,a duk lokacin da na ga kin dawo daga aiki yaran ki sun tafi da gudu sun rungume ki suna murna sai na tuna Ajmal ɗina,haka yake yi min duk sanda na dawo daga makaranta,na ɗauka zan yi farin ciki idan na nisanci gida,ashe a banza,babu abinda hakan ya ƙara min sai ƙuncin zuciya "

Sai yanzu mutanen parlourn suka kula da irin kukan da Mamie take yi hannun ta dafe da kanta, Khairi na zuwa nan Mamie ta ƙaraso ta rungume ta da ƙarfi,ta kalli Nabeela, Hisham da fadwa,har ma da su Ashraf dake zaune suna kallon su tace cikin kuka"yau wacce rana ce a gare ni?farin ciki zan yi ko baƙin ciki?ƴa ta UMMIYO da na rabu da ita shekara da shekaru ta dawo gare ni,ya Allah na gode maka da ka tsare min ita,ya Allah na gode maka da ka bata ikon haye SIRAƊIN UƘUBAr rayuwar da ta yi karo dashi!"

Gaba ɗaya parlourn ya yi shiru,kukan Khairi ya tsaya cak,ta ɗago a hankali ta na kallon Mamie,kafin ta zame jikin ta ta matsa baya,dukan su kallon ta suke yi,sai da ta fara ɗaga kai ta ƙarewa ko'ina na parlourn kallo sannan ta mayar da idanun ta ga Mamie da ke kallon ta jikin ta ya na ta rawa,cikin wata iriyar murya mai cike da baƙin ciki ta ce

"Umma na! kece??kin haife ni a albasu,da mahaifi na,ku biyu gare ni kawai, Allah ya ɗauki rayuwarshi,ke kuma kika tsallake kika tafi kika bar ni,kika zo nan kika auri irin mijin da ya dace da ke,gashi nan kun haifi yara irin waɗanda suka fi dacewa su samu kulawa,ni kuma kin tsallake ni tun ban fi su ba kin barni batare da kowacce kulawa ba,su kuma kin nemo musu wadda zata kula da su ko bakya nan!"ta yi wani murmushi ta ce"da kyau!zuwa yanzu na san bakya buƙata ta ne saboda mahaifi na ya yi Miki tsufa lokacin da kika aure shi,kuma baƙauye ne,amma yanzu kin auri ɗan birni kuma wataƙila baku da ratar shekaru ba kamar Abba na ba,don haka nima bana buƙatar ki!! tsawon lokaci yadda mahaifi na ya rasu kawai na yarda kema kin bi shi ne,don haka a yau in sha Allah,a yanzu zan bar Miki gidanki,da yardar Allah ko awa ɗaya ba zan ƙara a garin Kaduna ba ma ballantana a gidan ki"ta na kai wa nan ta miƙe a zafafe ta nufi hanyar waje


HAƊEJIA ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA


Ɗaga kai ta yi ta na kallon su gami da amsa sallamar da suka yi,cikin sanyin murya ta ce"sannun ku da zuwa,kun ƙaraso?"

Sulaiman yace"eh Ammi, sannu da gida, lokacin da na je ma sun ɗan juma da sauka"Ammi bata sake magana ba idanun ta kan Auwab da yayi wani iri,shima kallon ta ya yi,suna haɗa idanu ya fashe da kuka ya ƙarasa kusa da ita da sauri ya rungume ta da ƙarfi

Ɗago kanshi ta yi ta na faɗin"please Auwab kar ka karya min zuciya,me yake faruwa ne?ka na ɗaga min hankali idan naga kana kukan nan,don Allah ka yi min bayanin me yake faruwa?"da ƙyar ya daidaita nutsuwar shi ya ce

"Ammi ki yafe min don Allah!na san na ɓata miki, Please Ammi na"

"Na yafe maka,don Allah ka gaya min me yake faruwa,ka ɗaga min hankali "jikin shi na rawa ya zaro wayar shi,ya kunna musu duka record ɗin da ya yi saving,har da videos,cikin rawar murya ya ƙara musu da bayanin da Shukra ta yi masa na komai

Hankalin Ammi ya yi masifar tashi,ta fashe da kuka, Sulaiman ya yi ɗan murmushi ya juya harshen su na shuwa yace"dama na san za'a yi haka,amma ban taɓa tsammanin tun farkon maganar auren ba'a hayyacin ka kake ba,amma tun sanda ka saki Khairi na san akwai wata a ƙasa, Muhammad Auwab dai da na sani matarshi ta yi kaɗan ta bashi command ya karɓa,na san wanene shi ciki da waje,Shiyasa Ammi lokacin da ta zo ta ce ya bi ta su koma na ce ki yarje masa kawai"Auwab shima cikin Yaren shuwa yace"don Allah ka best friend ka taimake ni,ka nemo min Ummul khairi na idan ba haka ba zuciya ta zata buga, Please and please bruh"

Sulaiman cikin kwantar da murya ya ce"in sha Allah zan nemo maka ita,shima babban yaya ya zo ya na ƙoƙarin shi,in sha Allah zamu ganta,ka kwantar da hankalin ka ka ji"da ƙyar suka samu suka lallashe shi, Surayya dake tsaye ta na kallon su ta juya ta koma ɗakin ta ta na share hawayen da suke zubo mata,a ranta ta na tsinewa Inaaya


MALALI, KADUNA STATE, NIGERIA


Ɗaga kai tayi ta na kallon ƙofar da ake ƙoƙarin buɗewa,sai kallon Hisham take yi da ya shigo cikin ɗakin fuskarshi babu walwala,a bayanshi kuma Nabeela ce da fadwa,dukkan su idanun su jajir,da alamu kuka su kayi suka godewa Allah

Kusa da ita Hisham ya zauna,ɗan kallon shi ta yi ta ɗauke kai,shima ba zai wuce sa'an Auwab ba,fari ne ƙal kamar Nabeela da fadwa,sai dai shi babu alamun shiru shiru ne,don ɗazu da ya yi ta lallaɓa ta taƙi yarda ta dage sai ta fita bai tsaya wata wata ba ya ɗauko ta ya kawo ta ɗakinshi ya datse ta a ciki,sannan ya koma ya tambayi Mamie labarin komai,cikin kuka Mamie ta zayyane masa komai,ya ji tausayin su gaba ɗaya,amma bai buɗe Khairi ba don lokacin buge buge take ta na ihu,har sai da ta gaji ta daina,aka samu wajen hour ɗaya sannan ya je ya buɗe ɗakin,su fadwa suka bi bayan shi

Ya kalle ta ya ce"Ummul khairi,ya kamata ki saurari mahaifiyar ki,don baki fi ta jin zafin haihuwa ba,ta tsallake ki saboda dalili mai ƙarfi ta nisance ki hawaye ya na zubar mata,ke kuma har yanzu bamu san dalilin ki na tsallake yaron da yake shan mama kika shiga duniya ba,amma mun yi miki uzuri ko don hawayen idanunki,don haka kiyi wa Mamie adalci,kema sai ki samu sassauci"jikin ta ya yi sanyi sosai,ta miƙe cikin mutuwar jiki,ya saka ta a gaba suka nufi parlourn Mamie inda take zaune,idanunta sun kaɗa sunyi jajir saboda kuka,ta na ƙarasawa ta zube kusa da ita kanta a ƙasa

Ita ma Mamie ƙasa ta sauko,ta rungume Khairi,cikin shashsheƙar kuka ta ce "ki yafe min Ummul khairi!tabbas na yi kuskure,amma ya kamata ki duba uzuri na,ke uwa ce wadda ta rabu da tilon ɗanta,na san zaki ji zafin,to ki raya a ranki ina jin ninkin naki sau goma,kuma na rayu dashi a haka,ko babu komai ke kewar ɗanki kawai take damun ki,kina da yaƙinin zai ci ya sha, za'a kula dashi, amma ni kuma ina da tabbacin duk hakan baza ki samu ba,kuma gashi hasashe na ya tabbata,a haka na rayu da wannan ciwon tsawon shekaru goma sha uku"to goge hawayen ta,khairi ma kuka take yi, jikin ta ya ƙara sanyi, Mamie ta kalle ta ta fara

"Na auri mahaifin ki ina da ƙarancin shekaru,a lokacin ina hannun ƙanin mahaifi na ne da bai taɓa haihuwa ba, mahaifi na ya bashi ni don tausayawa,amma matar shi ta tsane ni,ta wahalar da ni sosai,a ƙarshe ta saka ya aurar dani ga dattijo mai yawan shekaru,kuma baƙauye, duk da ƙarancin shekaru na a wancan lokacin sai da na yi kukan baƙin cikin wannan aure, mahaifiya ta kuwa duk da kasancewa ta autar ta bata nuna damuwa ba,sai ta bi ni da fatan alkhairi kawai

Sai dai kuka na ya sauya lokacin da na shiga gidan mahaifin ki a matsayin matar aure,ya shagwaɓa ni sosai,ya nuna min soyayya da kulawar da na ji a duniya babu wata mace da ta kai ni dacen miji,na rayu a gidan shi tamkar sarauniya, saboda gata da tattalin da yake yi min, sanadiyyar haka duk wata ƙiyayya da nake masa ta kau

A haka na haife ki, mahaifin ki da kanshi ya bani zaɓin suna,na sanya miki sunan wata ƙawa ta da ta rasu tun muna yara,duk da ƙalubalen da nake fuskanta daga mahaifiyar mijina da faccaloli na ko a jiki na,don a lokacin ko an ɓata min rai na zo ina kuka miji na ya dawo akwai waƙar da yake yi min irin ta yara,ba na sanin lokacin da nake yin dariya ma idan yana yi min, raino na dai sosai yake yi,har zuwa lokacin da muka same ki sai muka zama tamkar yara biyu a gaban uba na gari"Mamie ta goge hawayen ta cikin jimami, kafin ta cigaba

"Rasuwar mahaifin ki itace ta tarwatsa komai,na yi kuka sosai,na yi baƙin ciki,wai a wannan zafin mutuwar ne mahaifiyar shi da ban ji daɗin ta ba ko kaɗan take roƙo na wai na auri ƙanin miji na, saboda matar shi bata da kirki,har tana kwaɗaita min shi ɗin ɗan birni ne,matarshi bata da kirki,amma idan na shiga na daidaita mata zama, ni kuma nace ba zan aure shi ba

A dalilin haka bata bar ni na gama takaba lafiya ba,ranar da zan tafi na so tafiya dake,amma tace ban isa ba,na yi kuka sosai,amma ƙarshe sai na zama abar zagi,a gaban idanu na aka ɗauke ki aka kai ki ajiya,na ƙaraci kuka na da tashin hankali na tafi Malumfashi garin mu

Kullum ina cikin damuwa da tashin hankalin rasa ki,duk da na koma hannun mahaifiya ta, dalilin haka babban yaya na Alhaji aƙilu ya tafi dani Sokoto,ya mayar dani makaranta,matar shi aunty Aliya kuma ta saka ni na fara business,wai don duk na daina damuwa, Ummul khairi ɗa na dabam ne a zuciyar iyayen shi, musamman wanda yake cikin halin da kike ciki,daga baya dai bayan na gama diploma ta a ƴan shekaru baya Alhaji Saleh ya aure ni ya kawo ni Kaduna,ya damƙa min yaran shi suka zama yara na,ya mayar dani makaranta na haɗa degree na,ko lokacin da na haifi ƴan biyu sai da na yi kuka don na tuna ki,duk wani ɗa da zan rungume a bayan ki yake Ummul khairi,akanki na san daɗin ɗa,akan ki na san zafin rabuwa da ɗa,don haka ina roƙon ki don girman Allah ki yafe min,ba laifi na bane,amma bana son ki ƙullace ni please Ummul khairi "ta ƙarashe cikin rushewa da matsanancin kuka

Khairi ma kukan take yi,ta rungume ta sosai ta kasa magana,su Nabeela ma da suke kallon su kukan suke yi,kowa cikin su jikin shi a sanyaye


Tsakanin maman Khairi da Khairi waye ya fi abin tausayi 😭

Kada dai a manta VIP group #300 ne kacal

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee

Page 73

Ranar dai gidan haka aka wuni sukuku, Mamie da kanta ta kira mama Hajara ta gaya mata cewa Khairi ƴar ta ce,mama kam ta yi matuƙar farin ciki,amma ta shaidawa Mamie cewa yanzu bata nan,ta je gidan ƙanwar ta a Zaria,idan ta dawo za ta shigo, Mamie dai ta yi mata godiya sosai

Washegari ganin halin da suke ciki ya sa Hisham ya kwashi su Khairi suka tafi yawo,a mota sai tsokanar su yake har suka saki jiki suna tsokanar shi suma

Ba su dawo ba sai bayan maghriba,dukkan su a gajiye suke,Fadwa ta wuce ɗakin ta,ita kuma Nabeela ta ja Khairi zuwa ɗakinta

A can suka yi ta hirar makaranta, Nabeela ta kira Amra video call,da ita kuma take ƙasar India tana karantar medicine,ihun murna suka yi ta yi suna ta shaftar su yadda suka saba suna makaranta, suka yi hirar malaman su da class members,daga baya Khairi ta ba ta labarin halin da ta tsinci kanta a ciki bayan ta bar makaranta,sosai Amra ta tausaya mata,har kuka ta yi mata, Amra ta ce "na tausaya miki sosai khair,amma na taya ki murnar zama uwa, in sha Allah very soon zan ga ɗanmu"Khairi ta yi ƴar dariya,suka cigaba da hirar su har dare ya raba ma basu sani ba


HAƊEJIA ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA


Ya na kwance akan doguwar kujera Three sitter dake parlourn Ammi ya yi zuru ya na kallon Ajmal da yau ya tashi da kewar mahaifiyar shi,bini bini sai ya kama kiran "umma!ummaaaa!!"gaba ɗaya ya sanyaya masa jiki,ya rasa yadda zai yi da shi,sai dai ya saka shi a gaba ya na ta kallo

Ammi ce ta shigo parlourn da sallama, sam bai san ta shigo ba,sai kallon yaron shi da yake ta faman kiran umma yake ya na ƴan wasannin shi,ta girgiza kai cike da tausayi ta samu waje ta zauna ta na kallon shi ganin bai ma san ta shigo ba

"Auwab!"a ɗan firgice ya juyo ya na kallon ta,a sanyaye ya ce "sannu Ammi"

"Sannu Auwab,ya jikin?"

"Jiki ya yi sauƙi alhamdulillah,ina Man?"

Ta ce"Sulaiman ya tafi aiki,da wata matsala ne?"

Ɗan shiru ya yi kafin ya ce"Ammi ki ce masa ya dawo da matar shi,ba ta da laifin komai,magana ta fatar baki ta yi kawai don ta na kishin mijinta,kuma na tabbatar banda wannan ƙaddarar da ta faru Khairi ba zata ƙyale ta ba,sai ta ce sai ta rama "

Ammi ta ce"to sai ya dawo,sai ka yi masa magana,me ya faru ne na ganka wani iri haka?"zama ya yi sosai ya na kallon Ajmal da har yanzu ya na ta wasan shi ya na kiran umma,ya ce

"Ammi yaron nan kamar kewar maman shi ya tashi da ita yau,tunda na shigo parlourn nan nake jin ya na ta kiran umman shi, gaba ɗaya wani iri nake ji"

Ammi ta yi shiru ta na kallon Ajmal da har yanzu yake ta wasannin shi,duk ya rame sosai,har yanzu ba wani cin abinci yake yi sosai ba,madarar da ake bashi ma ba sosai yake karɓa ba sai ya ji yunwa,ga ƴan kwanakin nan haƙori ya sako shi a gaba,a yanzu yawan kuka da yawan kiran umma kawai ya rage,shima idan ta juyo masa ya na yi,gaba ɗaya dai gidan ya na nan sukuku saboda halin da Ajmal yake ciki

Kafin Ammi ta yi magana suka ji sallama,da sauri Auwab ya zauna ba tare da ya san ya yi hakan ba yana kallon ƙofar, Inaaya ta shigo ta na ƙara yin wata sallamar muryar ta na rawa, Ammi ce ta amsa, Auwab kam sai kallon ta yake yi,ta sha dogon hijabi,idanunta sun kaɗa sun yi jajir,farar fuskar ta ta kumbura sosai,da alamu ta sha kuka,ta shigo ta ƙarasa gaban Ammi ta durƙusa ta ce"sannu da gida Ammi,ina kwana!"

"Lafiya!sannu!!"ammi ta faɗa ta na kallon ta

Juyawa ta yi ga Auwab tace"ina kwana"

Bai amsa ba, sai ma ɗauke kai da ya yi ya na wani murmushi ya na cije leɓen shi na ƙasa, ta yi ɗan murmushin yaƙe ta nufi wajen da Ajmal yake ta wasannin shi,ta na faɗin "my boy!ya kake? ina......"da kallo ta bi Auwab da ya yi caraf ya ɗauke ɗanshi ba tare da ya kalle ta ba ya koma kujerar da yake kwance ya zauna, Ajmal kam ya firgita da yadda Auwab ya fizge shi,ai kuwa ya fashe da kuka yana sake kiran "ummaaaa!!"Auwab ya fara lallashin shi ya na dannar zuciyar shi,don ji yake kamar ya rufe Inaaya da duka ko ya ji sauƙin baƙin cikin da yake ciki, shiyasa ya zaɓi ya share ta kawai,don ya san idan ya ce zai yi mata magana ma lamarin ba zai yi daɗi ba

Kuka Inaaya ta saka ta na faɗin "don girman Allah ka yi haƙuri,ka yafe min,wallahi sharrin shaiɗan ne ya hade min da soyayyar ka, wallahi ba hali na bane!na rasa yadda zan yi ne,ina tsananin son ka ne, please ka yafe min Auwab"

"Au haba!da gaske dai ba halin ki ba ne?kuma yafiya kike nema?"da mamaki suka waiga suna kallon Sulaiman da yake sanye cikin baƙar designer suit da ta yi masa kyau sosai,idanun shi akan Inaaya,ya na wani murmushi da shi kaɗai ya san ma'anar kayan shi

Cikin gunjin kuka ta kama faɗin "don girman Allah ku taimaka min,ku roƙe shi ya yi min duk hukuncin da zai yi min amma kar ya sake ni,ina son shi wallahi,na yi alƙawarin duk abinda aka ce na yi zan yi,amma don Allah ku taimaka kar aure na ya mutu na roƙe ku"

Sulaiman ya yi wata dariyar rainin hankali ya ce"Au Allah?ke ta auren ki ma kike?an gaida tattabara!"ya yi ɗan murmushi ya nemi waje ya zauna ya kalle ta yace"mu ta ƴar uwar mu muke yi da kika ɓatar ta shiga duniya ba tayi miki laifin komai ba,don zalunci da a mugunta da ƙeta kika raba mu da ita,kika raba ta ɗan ta da take shayarwa saboda ke baki san zafin ɗa ba ko?to ya yi kyau,dama ko ba ki zo ba Boston ba baƙo na bane,zan je har can na ɗauko ki na dawo dake Nigeria don ki girbi abinda kika shuka, dama kafin nan ina da cikin ki, lokacin haifo ki kawai nake jira,kuma gashi ya yi,ba a haifi wata kilaki da ta isa ta zo ta tsaya a gaba na ta na gaya min magana ta na shan alwashi ba sannan ta ci banza ba,ke wawiya ce,baki san waye ɗan sanda ba,da ba kiyi wannan wautar ba"ya ciro wayar shi ya kunna voice ɗin maganar da ta taɓa yi masa har tana cin alwashin sai ta ɓatar da wadda suke taƙama da ita

Bayan ya ƙare ta kalle ta ya ga yadda ta yi tsuru,ya yi murmushi ya ce"wannan voice ɗin zai zama hujja a kanki, don haka,men!"ya ɗaga murya,sai ga ƴan sanda sun shigo,ya nuna Inaaya da ta daskare a durƙushe ya ce"ku tafi da ita,ku tambaye ta har sai ta faɗi inda ta kai min ƙanwa"babu musu suka yi waje da ita ta na ihu ta na kiran Auwab,wanda hankalin shi ke kan Ajmal da ya samu ya yi shiru yake ta ƙoƙarin yin Bacci


LUGARD ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA

"Yaya!yaya!!yaya zo ka ga mummy,mummyn mu mutuwa zata yi,zo ka ga abinda take yi!!!"a gigice ya jefar da laptop ɗin hannun shi ya fice a guje don ganin halin da mum take ciki, Nusra ma ta bi shi a guje

Yayi matuƙar tsorata ganin mum tana Aman jini

A matuƙar tsorace ya ƙarasa ya riƙe ta ya na faɗin "mum!me ya same ki? inna lillahi wa inna ilayhi rajiun!mum dole mu je asibiti please"bai saurari abinda take cewa ba ya yi azamar yin waje ya kira driver,sannan ya kama ta ya yi waje da ita, Nusra sai kuka take yi,ya ce ta koma ciki,idan aunty Naja da Beely suka dawo ta gaya musu sun je asibiti

Asibitin Dr Mahfouz ya kai ta,anan bayan an duba ta ya sanar masa da cewar ciwon zuciyar ta ne ya yi tsanani,don haka dole a kwantar da ita

Shi dai Azad gashi gashi nan ne dai kawai,gaba ɗaya jin shi yake yi dama zai mutu ya huta da tashin hankalin duniya,daga wannan sai wannan

Daddy ya fara kira ya sanarwa,a lokacin ma ya na Lagos, amma ya ce zai yi boarding next flight,in sha Allahu zai taho Kano, bai juma da yin waya da Daddy ba aunty Naja da Beely suka shigo asibitin

Kallon su kawai yake yi lokacin da suke tambayar shi me yake faruwa a gigice,daga baya ya girgiza kai a sanyaye ya ce"mu yi mata addu'a kawai aunty, Allah ya bata lafiya"daga nan dukkan su ba su sake magana ba, Beely sai karantar shi take yi cikin tashin hankali

A ranar daddy ya iso,a lokacin mum ta dawo hayyacin ta,shi kaɗai aka bari ya shiga wajen ta,ya yi mamakin yadda ta rame ta lalace,ya ƙarasa da sauri ya riƙo hannun ta ya ce"sannu Salma!ya jikin naki?"

A hankali ta ɗaga idanu ta kalle shi ta ce"sannu da zuwa barrister!"

"Sannu Salma,garin yaya kika bari ciwo ya ci jikin ki haka kika ƙi gaya mana?"

Wani murmushi kawai ta yi ta ce "barrister komai ya ƙare min,gaba ɗaya rayuwar ma ta fita a kaina,na kasa tuna wani mutum ɗaya da ya ji daɗin rayuwa dani,ko kai,ko ƴaƴana,ko waɗanda zama ya haɗa mu, rayuwa ta gaba ɗaya ba ta da wani amfani,yanzu gashi na nakasa ɗana da yafi yi min biyayya akan kowa,yake ƙauna ta fiye da kowa, saboda son zuciya ta,bana jin zan yafewa kaina"Daddy ya goge mata hawayen da yake zubo mata,cikin kwantar da murya da lallash ya ce"meyasa zaki ce haka?waye ya ce miki ba mu ji daɗin zama dake ba?don Allah Salma ki daina irin wannan maganar,za ki warke in sha Allah,za ki koma cikin yaran ki ku cigaba da rayuwa cikin farin ciki,don Allah ki daina irin waɗannan maganganun Salma"

Ɗan murmushi ta yi kawai sannan tace"kayya barrister! alƙalami ya riga ya bushe

Amma ina roƙon ka ka yi min wata alfarma barrister!"

"Ina jin ki Salma! faɗi ko menene in sha Allah zan yi miki"

"Don Allah so nake ko bayan raina idan Allah ya bayyana Khairi ka aura mata Azad,ban taɓa aikata abinda ya yi min tsaye a rai kamar hana wannan auren ba,har yanzu ina jin magiyar ɗana mafi soyuwa a gare ni a kunne na ya na roƙo na na bar shi ya auri yarinyar da bata yi laifin min komai ba,amma naƙi,har yau ina iya tuna sanda yake kallo na yace na zaɓa masa wadda ta dace da rayuwar shi,amma shima yana da wadda yake so,na yarda na zaɓa masa wadda nake so amma na hana shi zaɓar wadda yake so, barrister na sani Azad ba zai taɓa yafe min ba"ta ƙarasa faɗa cikin matsanancin kuka

Cikin gigicewa Daddy ya ce"trust me Salma, wallahi wannan maganar ta wuce,amma tunda kin ce a aura masa Khairi idan ta bayyana in sha Allahu za'a yi hakan,da kanki ma zaki kai ta ɗakin ta in sha Allahu,ki daina wannan maganar"mum ta yi ɗan murmushi,bata sake magana ba ta lumshe idanu kawai


Wai yau nice na tausayawa mum😭😭😭😭

Kada dai a manta VIP group #300 ne kacal


#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️ Nusy bee
*Young talented writers association (YOTA)*

Page 74

Zuwa yamma su Sulaiman suka ƙaraso tare da su Ammi,anan ma bayan sun fito reception sun ƙara tattauna batun ɓatan Khairi sosai,da yadda ake ta faman wahalar nema amma har yanzu shiru,shi dai Daddy ya ƙara bada shawarar a zage sosai da addu'a da sadaka,kuma sun yi na'am da wannan shawara,amma Daddy ko da wasa bai sanar da su maganar da mum ta faɗa masa ba, don shi ya ɗauki hakan a zafin ciwo kawai

Sai dare su Ammi suka koma gida,ran kowa babu daɗi,ga Ajmal ya ta da rigima sosai ya na kiran umma, hakan ya sa Auwab zazzaɓin da yake fama dashi aka samu yayi sauƙi ya dawo,daga ƙarshe dai shima asibiti ya kwana a ranar, Sulaiman ya ɗauki Ajmal daga Wajen Auwab ɗin,shima gobe in sha Allah zai wuce Maiduguri don dawo da Mifra ɗakinta


MALALI, KADUNA STATE, NIGERIA

Kasancewar an rufe biyan kuɗin WAEC dole ya sa sai iya NECO aka biyawa Khairi a wata tsadaddiyar private school,a wannan lokacin damuwa ta yi mata yawa, saboda kewar ɗanta da ta dawo mata sabuwa fil,don har Hisham,da yanzu yake yawan jan ta a jiki ta roƙa ya samo mata dabara ta je gidan Abba ta ɗauko Ajmal,ya tabbatar mata babu yadda za'a yi a neme ta a rasa su kuma suyi sake da yaron ta jariri,don haka ta yi haƙuri kawai,bayan ta gama exam da kanshi zai kai su ita da Mamie su gaisa da su Abba sai ta ɗauko ɗan ta

A yanzu ƙuncin zuciyar da take ji ya ragu sosai,su Nabeela da Fadwa kam sun zamar mata ƴan uwa,dama can Nabeela tata ce,to yanzu abin sai ya yi gaba kuma

Alaƙarta da Hisham kuwa,tun ta na ɗaukar ta a matsayin ƴan uwan taka har ta gane shi ba wannan ya ɗauka ba,a lokacin ta ɗan tsorata,don bata yi tsammanin a matsayin shi na saurayin da bai taɓa aure ba zai iya aurar bazawara ba, dalilin haka ya fara avoiding ɗin shi

Nabeela ya samu yake tambayar ta dalilin da ya sa Khairi take gudun shi,ta ce ita ma bata sani ba amma za ta tambayi Khairin

Da daddare suna ɗaki,khairi ta na kwance akan gado ta na danne danne a sabuwar wayar ta da Mamie ta siya mata, Nabeela dake zaune akan study table ta na duba wani littafi ta kalle ta ta ce"Khairi an aiko ni,ko nace ance na tambaye ki"

Khairi ta kalle ta ta ce"wacce tambaya ce?"

Nabeela ta ce "meyasa kike gudun yayana?ko ya na da wani aibu ne da ya cancanta ki guje shi?"Khairi ta yi ƴar dariya ta ce"me ya kawo wannan maganar kuma Nabeela?babu wani aibu,kawai dai...."sai kuma ta yi shiru ta kasa ƙarasawa

Nabeela ta taso ta dawo kusa da ita ta zauna ta na kallon ta ta na murmushi ta ce"Khairi kenan, I know kin san yayana ya na sonki, right?why baza ki ba shi dama ba,yayana is very nice person fa"

Khairi ta yi murmushi ta na ɗan girgiza kai ta ce"will that be possible?yayanki saurayi ne bai taɓa aure ba,ni kuma bazawara ce har na haihu,ko kun manta da hakan?"

Nabeela ta galla mata harara ta ce"and so?tunda nake da yaya na ban taɓa jin ya ce ya na son wata a rayuwar shi ba sai ke,na yi farin ciki da hakan sosai,kin san menene so kuwa?to shi so babu ruwan shi da budurwa, bazawara ko tsohuwa ce ma,ko ƴaƴa dubu kika haifa indai da soyayya sai kiga an yi aure kuma an zauna lafiya,kuma soyayyar ta cigaba, ballantana Khairi dududu nawa kike har yanzun ma?kuma ɗanki ai ɗan yaya Hisham ɗina ne,Malama ki yarda kawai ayi ƴar gida,kina gama exam a ɗaura,mu wuce Egypt gaba ɗayan mu,kuna honeymoon muna karatun mu"ta ƙarashe ta na ɗan dukan kafaɗar ta

Murmushi kawai Khairi ta yi, Nabeela ta dungure mata kai tace"ko baki amince ba yacin ni na amince,yayana dai ya kai a bashi dama,don ya na da class dai kin sani"khairi ta harare ta tace"na ji,kar ki dame ni,idan kika bani haushi kuma sai na fasa"Nabeela ta washe baki tace "a'a ni babu ruwana da shiga tsakanin masoya, Allah ya bar ƙauna"Khairi ta yi mata banza ta cigaba da danne dannen wayar ta

Wasa wasa sai ga soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakanin Khairi da Hisham, Mamie kam kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha saboda farin ciki,ta na matuƙar farin cikin ƴar ta gudan jinin ta za ta auri Hisham,wanda ta yarda ta tarbiyya da kirkin shi

Hisham da kanshi ya samu Mamie ya shaida mata bayan Khairi ta gama rubuta NECO da kanshi zai mayar da ita dangin mahaifinta,sannan ya nemi auren ta,Mamie ta yi farin ciki gami da fatan alkhairi


HAƊEJIA ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA


"Abban Anam ga abinci da na jera maka a dinning area,ka ƙyale yaran nan ka fara cin abinci "banza ya yi mata ya cigaba da biyewa Anam da Ajmal da ke ta faman zuba shiririta, bata yi zuciya ba,don ta san laifin ta,ta ce"abban Anam ga abinci fa"ya kalle ta cikin idanu,cikin Yaren shuwa ya ce"naci a wajen mahaifiya ta!"

Shiru ta yi jikin ta a sanyaye,ta samu waje ta zauna idanun ta suka tara ƙwalla, kafin ta kai ga magana wayar shi ta yi ruri,ya ɗauka ya ɗaga

Ji ta yi ya ce"okay shikenan, I'm on my way right now"bai ko kalli sashen da take ba ya miƙe ya fice daga parlourn

A bakin gate ɗin gidan ya tsaya ya na kallon asalin tsadaddiyar motar da ta yi parking, driver ɗin motar ya fito ya buɗe gidan baya,mamallakin motar ya fito ya na taku ɗaiɗai ya na ƙarewa Sulaiman kallo a wulaƙance

Sulaiman bai wani nuna masa damuwa ba,ya na ƙarasowa ya miƙa masa hannu,shima bai ja ba ya ba shi suka yi musabaha,sannan alhajin ya fara magana cikin isa

"Suna na Alhaji mukhtar,tsohon ministern kuɗi, kuma ɗaya daga cikin manyan attajiran Nigeria,na san ko baka sanni a fuska ba zaka san sunana a Wajen mutane ko?"

Sulaiman ya ce"eh to maybe,Amma abin ka da ba na damuwa da abinda bashi da muhimmanci a waje na, shiyasa bai zama lallai in tunaka ba, anyway,barka da zuwa,can we get in?"

Alhaji mukhtar da maganar sulaiman ta fusata shi ya ce"kai yaro!baka da inda ka isa ka ajiye ni a wannan kangon gidan naku,zuwa na yi na bika ta lalama ka sakar min yarinya ta da ka kama,ko na saka ka rasa aikin ka"

Yatsina fuska Sulaiman yayi, yace"wacece yarinyar taka da na kama?don ban san wacce ce daga cikin su ba,don ni banga mai kama da kai ba a cikin waɗanda na kama ɗin ba"

"Wadda na aurawa sakaran yayan ka!"Sulaiman ya yi dariyar rainin hankali ya ce"ikon Allah!wannan abu bai yi ba,ita dai wannan ƴa taka bata da sa'a a rayuwa,ga ta sakarya daga sakaran uba zuwa sakaran miji,to...."a fusace driver ɗin Alhaji mukhtar ya kaiwa Sulaiman mari, Sulaiman ya riƙe hannun shi ya ce"kai yaro!ba da kai nake ba,da ubangidan ka nake,ko kaima baka samu tarbiyyar bane?"ya yarfar da hannun driver ɗin ya kalli Alhaji mukhtar ya ce"na san kana da sanayya a sama,to idan ka isa ka fito da ita mu gani, ni kuma daga ranar na bar aikin ɗan sanda!"ya na kai wa nan ya juya ta shige cikin gida

Duk yadda Alhaji mukhtar ya yi don ganin Sulaiman ya saki Inaaya ya zama a banza,ya yi duk yadda zai yi da manyan da ya sani amma abin kamar baya yi,ya ɓarnatar da maƙudan kuɗaɗe amma shiru,dole ya fara neman Sulaiman don sulhu, Sulaiman kuwa ya ƙi ba shi haɗin kai,sai ya koma neman Abba,amma Abba ya ce yarinyar da ake case akanta amanar shi ce,idan ya ganta za'a saki Inaaya

A ƙarshe dai sai da Inaaya ta samu sati uku a kulle sannan Sulaiman ya amince aka fito da ita,gaba ɗaya ta lalace ta jeme kamar ba ita ba

Kai tsaye gidan su ta je, mahaifiyar ta ta na zaune ta yi jugum ta faɗo parlourn,da matuƙar azama ta miƙe tsaye cike da mamaki da farin ciki ta na kallon ta,amma kafin ta yi magana Inaaya ta yanke jiki ta faɗi,ai kuwa ya gigice ta fara ihu,masu aikin gidan ne suka taimaka suka fitar da ita,aka saka ta a mota aka nufi asibiti da ita


Kada dai a manta VIP group #300 ne kacal


#Nusy_bee


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


__Free_book_

✍️Nusy bee
*Young talented writers association (YOTA)*

Page 75


Wani ƙarin tashin hankalin bayan likitoci sun yi gwaje gwaje sun gano ta na dauke da Cutar AIDS,sannan ta na ɗauke da Cancer ta dubura da ta mahaifa,ta na ɗauke da ciwon ƙoda da hanta saboda shan giya da take yi,take mummyn ta ta yanke jiki ta faɗi saboda tsananin tashin hankali da ruɗani,itama dai cikin gaggawa aka shiga da ita don duba ta

A ƙasa da kwana biyu Inaaya ta lalace ta zama wata ƙwarangal,ga ƙananan tsutsotsi da suka fara fitowa ta duburar ta,wari kam ta na yin shi har babu mai so ya kusanta kanshi da ita, mahaifiyar ta dai tuni ta dawo hayyacin ta,amma banda kukan tashin hankali babu abinda take yi, Alhaji mukhtar ne ya yanke shawarar fita da ita zuwa ƙasar India don duba lafiyar ta


MALALI, KADUNA STATE, NIGERIA


Su Hajiya khairi hankali ya kwanta,yanzu gaba ɗaya ta mayar da hankali sosai ga karatun ta,wani lokacin har tsokanar ta Nabeela take yi, musamman idan ta tuna baya yadda take da naci da son karatu

Yau ma ta na zaune ta na karatu akan study table dake ɗakin nasu Nabeela ta shigo,ta amsa mata sallamar ta ta na kallon ta, Nabeela ta na dariya ta ce"an gaida babbar likita ta garin albasu"

Ɗan murmushi ta yi ta ce"Allah sarki yayana da yaya sulaiman, sune suke yi min wannan kirarin,yanzu ko a wanne hali suke oho?".

Nabeela ta matsa kusa da ita sosai ta ce"seriously Khair yayyen nan naki are very nice,more especially wannan classic one ɗin, Azad,komai nashi mai kyau ne wallahi,hatta da maganar shi,ya na burge ni over"Khairi ta yi ƴar dariya ta ce"kuma Kinga ba shi da mata dama,ƴar shawalwala yake nema "Nabeela ta haɗe rai ta ce"me kike nufi da bashi da mata,ƴar shawalwala yake nema kuma?"

Khair ta yi gatsine ta ɗauke kai ta ce"babu komai,kawai gaya Miki na yi auren shi ya mutu"sai ta yi tagumi ta ce"wallahi tausayi yake ba ni,ya sha wahalar aure,yanzu ma tsoron auren yake ji"a takaice ta bawa Nabeela labari,itama Nabeela sai ta yi shiru cike da tausayin shi,zuwa can tace"Allah sarki! Allah ya mayar masa da alkhairi "Khairi ta ce"Ameen "

Nabeela ta miƙe tsaye ta na faɗin"gobe fa da safe yaya Hisham zai koma Cairo kin sani,don haka mu da kanmu zamu je mu siyo sarƙar nan,ya tura min kuɗin gaba ɗaya "Khairi tace"to Allah ya kai mu,an gode Allah ya ƙara buɗi"

Nabeela ta ce"a'a bani zaki yiwa godiya ba,ki bari idan ku kayi waya sai ki yi masa"khairi ta galla mata harara, Nabeela ta yi dariya ta juya ta fice daga ɗakin ta na rera waƙar masoya, Khairi ta yi ɗan murmushi kawai ta na girgiza kai,ta cigaba da karatunta

Washegari da safe suka raka Hisham airport don komawa ƙasar Egypt cikin babban birnin ta Cairo,shi ɗin ƙwararren likitan ƙashi ne(orthopedic),acan yake aiki,inda fadwa da Nabeela suke karatu kuma suke zaune a gidanshi,amma su anyi musu hutu shiyasa ya rako su gida

Har dama su Nabeela suka bashi shi da khairi suka yi sallama,daga inda suke tsaye suna iya hango yadda Khairi take ta narkewa ta na zuba masa shagwaɓa da shagwaɓa,ai kuwa bayan ya wuce sai da suka kusa saka Khairi kuka saboda tsokana

Da yamma suka shirya fes da su, Fadwa bata nan a lokacin,don basu juma da dawowa daga airport ba ta tafi gidan ƙanwar maman su a Zaria, Khairi ta shirya cikin wani uban sun lace light blue da aka yiwa ɗinkin half bubu,da ratsin maroon flowers,ita kuma Nabeela ta sanya atamfa blue Black,dukan su suka sanye fararen medium veils, Nabeela ta ɗauki makullin mota suka fita

Kai tsaye wani katafaren shagon sayar da sarƙoƙi suka nufa, Nabeela ce ta zaɓar musu masu tsananin kyau da tsada, kowacce sai da ta gwada tata,ta yi mata kyau sosai sannan suka fito cike da farin ciki,wannan karon khairi ce ta amshi driving ɗin

Sai dai bisa tsautsayi suna tafiya a motar wani mutum ya tura su suka faɗa wani rami a gefen titi,mutumin ya fito daga motar shi ya na yi musu masifa, Allah yasa a gaban mutane ya tura su,suka samu aka shigar musu,sai dai tayar motar ta yi faci,gashi basu da spare,dole suka kulle motar bayan sun kwashe kayan su suka nufi gida,duk da akwai ƴar tazara tsakanin su da gida


** ** **


"To yanzu maman Abeed sai yaushe?tunda kuka yi aure fa daga ke har oga baku zauna a Nigeria na wata uku ba fa"wadda aka kira da maman Abeed ta yi ƴar dariya ta ce"kamawa ta yi aunty zee,amma in sha Allah mun kusa dawowa baki ɗaya,nima ina son na ganni kusa da gida, kin san tunda aka yi aurena sau uku kawai na je gida,an yi sabgogi da yawa bana nan, dole ina buƙatar zuwa gida"wadda aka kira da aunty zee ta ce"kema dai kya faɗa, amma nisan nan duk sai kaji ka da kewa"

Maman Abeed ta buɗe baki da zummar yin magana su Khairi suka zo wucewa,dukkan su a gajiye suke,sai masifa Nabeela take yi ta na jawa mutumin da ya janyo musu wannan wahalar Allah ya isa, Khairi ta gaji ta ce"Nabeela wallahi kin dame ni da mita,ki bar ni na ji da ɗaya mana, haba!"

"Oho dai ke kika sani ƴar rainin hankali kawai"ita dai khairi bata sake magana ba suka cigaba da tafiya Nabeela ta na cigaba da sababi

Maman Abeed ta kalli aunty zee ta ce"aunty Zee waɗannan ƴan matan a ina suke?"

Aunty zee ta kalle su cikin rashin damuwa tace"kamar na san farar,amma ita baƙar ban ma taɓa ganin ta ba sai yau"

"Kayya!ni baƙar nake so na san inda take ba farar ba ma"

Aunty zee ta ce"farar kamar a gidan Hajiya Habiba take,gidan ya na ƙarshen layin nan namu,maybe idan kika yi magana da ita ta haɗa ki da sister ɗin tata,amma meyasa kike son ki san inda take?"

Ajiyar zuciya ta sauke ta na kallon aunty zee ta ce"ita ɗin matar yayana ce,ko na ce tsohuwar matar yayana,ta ɓace lokaci ɗaya aka neme ta aka rasa,abin tausayin ta na da jaririn da bai kai yaye ba ta tsallake shi ta tafi,sai daga baya muka gano ashe asiri co wife ɗin ta ta yi mata,to yanzu kuma asirin ma ya karye,amma ba ta koma gida ba,ban san dalilinta ba,kuma ban san a inda take zaune ba,ko in ce bamu sani ba ma"aunty Zee ta jinjina kai ta na ƙara kallon hanyar da su Khairi suka bi,wadda zuwa yanzu sun ɓacewa ganin su

A take maman Abeed ta Ciro wayar ta daga jakar ta ta kira Auwab,ya na ɗagawa ta ce"yaya Auwab kana Nigeria?"

"Cikin sanyin murya ya ce"to ina za ni Amra?ai indai ban ga Khairi ba bana jin zan iya zuwa ko'ina"

"To albishirin ka big bruh, Allah ya sauƙaƙa maka,don gata na ganta anan Kaduna da navzo wajen ƙanwar abban Abeed,amma ita bata ganni ba"

Shiru Auwab ya yi kafin yace"Amra are you sure of what you are saying?"

Amra ta ce"I'm very sure yaya, wallahi ita na gani,na san ta fa sosai ko ka manta ne?"

"Ki tura min address ɗin wajen "abinda ya sake cewa kenan,ta ce"okay!"bai sake magana ba ya kashe wayar


HAƊEJIA ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA

Tunda Amra ta kira shi ta shaida masa labarin ta ga Khairi ya rasa nutsuwar shi,gaba ɗaya ya sake fita hayyacin shi,ranar haka ya kwana, washegari ya wuni ko abincin kirki baya ci,tunanin yadda zai ga Khairinshi ya dame komai, Ammi dai bata ba tayi masa magana ba,don ta san halin da yake ciki

Sulaiman ya bawa takardar sakin Inaaya uku da ya rubuta don ya kai mata,shi kuma ya gaya wa Ammi cewa zai je Zaria ɗaurin auren wani abokinshi,amma yau zai dawo

Ammi ta kalle shi cike da kulawa ta ce "kai da baka da lafiya Auwab?yaushe aka sallamo ka daga asibiti?"ya yi ɗan murmushi ya ce"na ji sauƙi fa Ammi,idan na fitan ma sai nafi jin ƙwarin jikina"

Ammi ta yi masa fatan alkhairi,da ta nemi ya bari su tafi tare da Sulaiman ya ce kawai ta ƙyale shi, wataƙila ma hidimar ayyuka sunyi masa yawa,ya na buƙatar hutu


To Mr Auwab Allah ya kiyaye hanya,amma ina tausaya maka 😥

Kada dai a manta VIP group #300 ne kacal

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

✍️Nusy bee
*Young talented writers association (YOTA)*

Page 76


MALALI, KADUNA STATE, NIGERIA

Yau da safe khairi bata tashi da wuri ba saboda gajiyar jiya,ta na idar da Sallah ta sake mayar da kai ta cigaba da bacci, Nabeela ce dai ta tashi da wuri,ita ma dai gidan ba wani daɗi yake yi mata ba, Fadwa har yanzu ta na Zaria,yaya Hisham kuma ya koma Cairo, Mamie kuma ta yi sammakon fita aiki,sai twins ne kawai dake zaune a parlour suna ta wasan su

Ita ma cikin su ta shiga ta na tsokanar su aunty Meena ba ta tashi daga bacci ba, kasancewar har yanzu sun kasa sabawa da sabon sunan mai rainon nasu aunty Khairi,sai dai aunty Meena,da ta nuna bata so Mamie ta ce"haka za ki amsa shi kuwa,tunda ke ce kika janyo,ke kika raɗawa kanki "haka zata yi ta kumbure kumbure su Nabeela suna mata dariya

Mai gadin ne ya yi sallama daga bakin parlour,amsawa ta yi ta ɗauko ɗan mayafi ta ɗora akan dogon gashin ta da bata saka masa ɗan kwali ba,ta leƙa ta na faɗin "baba Ina kwana!"

Ya amsa shima ya na rissinawa,sannan ya ce"dama Hajiya Ummul khairi ake nema"

Ɗan yatsina fuska ta yi ta ce"waye haka da safiyar Allah?"don lokacin bai fi sha ɗaya da ƴan mintuna ba

Baba mai gadi ya ce"Nima ban sani ba,amma wani saurayi ne"take annurin fuskar Nabeela ya ɗauke,saurayi? lallai,ai kuwa bari taje ta karta masa rashin mutunci yadda ko a gaba aka ce ya sake zuwa inda take ba zai sake wannan gangancin ba

Kallon baba ta yi ta ce"ka kai shi parlourn baƙi yanzu,ana zuwa"daga haka ta juya ta koma cikin ɗakin ta ta na ta masifa ita kaɗai,ta dubi Khairi da ke ta baccin ta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ba ta san ma ta na yi ba,ta yi ƙwafa ta na hararar ta,ta ce"ko ke ce kika ba shi dama yau sai ya gwammace bai sanki ba"ta sanya hijabi tayi waje,kai tsaye ta nufi parlourn baƙin gidan

Sai da ta shiga parlourn sannan ta yi sallama,da farko bata yi niyyar sallama ba don rashin mutunci kawai zata yi ta koma,amma kwarjinin da guy ɗin ya yi mata ya sany ta yin sallamar ta na ƙare wa farar fuskar shi kallo

Ɗagowa ya yi da ɗan murmushi kan fuskar shi ya ce"sannu!ko zan iya ganin Ummul khair Please?"

Duk yadda ta so yin masifa sai ta kasa,saurayin ya na yi mata kama wani da wanda ta sani,ko kuma ta sanshi,amma ta manta a ina,kuma waye?don haka sai ta samu kanta da faɗin"bacci take yi "

Ɗan murmushi ya yi ya ce"I will wait ta tashi,na gode"ba ta sake magana ba ta fice daga parlourn ta na tunanin inda tasan wannan guy ɗin

Ta na shiga ɗaki sai ta samu Khairi har ta tashi za ta shiga wanka,Khairi ta dakata tana kallon ta, Nabeela ta samu waje ta zauna ta na hararar ta

Khairi ta ce"ke fa idan kika tashi rikici ko matacciyar mota albarka,yanzu me na yi miki da za ki zo ki saka ni a gaba kina harara ta?"

Nabeela ta taɓe baki ta ce"wani saurayi ne yake kiran ki"

"Kira na!ni kuma?"

A fusace Nabeela ta ce"ƙarya na yi miki!kin san na saba"Khairi ta kalle ta a ɗage ta shige toilet ta na jiyo ta ta na faɗin "wallahi duk wanda ya yi ƙoƙarin shiga hurumin yayana sai ya gane kuren shi"Khairi tana banɗaki sai da ta yi dariya,don dama tasan abinda Nabeelan take yi wa fushi

Da kamar rabin awa Khairi ta shirya cikin doguwar rigar atamfa,a gurguje ta ɗan sha tea da Nabeela ta haɗa mata,wai duk don su ƙara ɓatawa saurayin lokaci ya gaji ya tafi,ta ɗauki dogon jilbab ɗin ta ta sanya, Nabeela ma ta sanya hijabin,ta rufa mata baya,a cewarta babu wanda ya isa ya shiga gonar yayan ta ta na tsaye ta na kallon shi, wallahi sai ta dakatar da shi

Da sallama Khairi ta shiga parlourn ta na raba idanu, ragowar sallamar ta maƙale, idanu waje take kallon saurayin da aka ce yake kiran ta, tsananin mamaki da firgici suka wanzu a fuskar ta,magana take son yi amma ta ƙi fitowa, Nabeela da ta biyo ta don ganin yadda za'a yi sai ta zama ƴar kallo, da ƙyar ta furta

"Yaya AUWAB!"

Miƙewa ya yi ya na ɗan murmushi ya nufo inda ta ke ya na faɗin "yeah! Alkhairi na!!"

"Kar ka ƙaraso inda nake AUWAB!mugu!! azzalumi!!!na fita a rayuwarku don Allah ku bar ni haka!!! wahalar rayuwar ta ishe ni haka,ka fita a rayuwata,ka nisanci inda nake,na bar maka komai naka,na bar maka hatta da ɗanka,don Allah nima ka barni,ka bar ni na samu farin ciki,don girman Allah Auwab!!!"cikin tsananin kuka da hargowa Khairi ke faɗar Wannan maganar

Sam babu alamar fushi ko damuwa akan fuskarshi,sai dai ya tsaya cak ya na kallon ta,ita ma Nabeela tsayawa ta yi ta na kallon Auwab,zuwa yanzu ta gane waye,ta gane shine tsohon mijin ta,kuma dalilin da ya sa take ganin kamar ta san shi saboda kamar da suka yi da ƙanin shi Sulaiman ne

Ganin Auwab ba shi da niyyar fita ya sa Khairi ta janyo wani flower vase cikin fitar hayyaci ta kwaɗa masa a kai ta na ihu,take kuwa jini ya ratsa lallausar sumar shi ya wanke masa fuska, Nabeela ta yi ƴar ƙara a firgice ta kama jan Khairi da ƙarfi,amma cikin wani irin ƙarfi da yake taso mata ta hankaɗe ta ta fara ɗaga duk abinda ya zo hannun ta ta na saukewa akan Auwab, wanda ya lumshe idanun shi kawai ya na sauraren ikon Allah

Cikin ƙaraji Nabeela ta fara faɗin "ka gudu!ka gudu kar ta illata ka, Please!!!"amma ko gezau bai yi ba,ganin haka ya sa Nabeela ta nufi cikin gida ta na ihu ta na kiran Mamie

Mamie ba ta cikin gidan,cikin tashin hankali ta kira ta a waya ta shaida mata ga Khairi nan za ta kashe wani, mamie ba ta wani gama gane bayanin ba ta ce gata nan,ta kashe wayar ta

Da hanzari Nabeela ta koma wajen Khairi da Auwab,zuwa yanzu ya zauna ya dafe kanshi,ita kuma ta gaji ta koma gefe ta na gunjin kuka ta na sambatu

"Me ka zo yi inda nake?kai macuci ne,ka ce tun farko ka fi ƙarfin aure na,kuma ka aure ni ka yaudare ni ka koya min sonka da sabo da kai,a ƙarshe ka wulaƙanta ni,hakan bai yi maka ba sai da ka ƙara min da sakin wulaƙanci,ka tuna?ka tuna maganganun da ka gaggaya min lokacin da ya rage sati guda auren mu?na san zuwa yanzu ka manta,ni ban manta ba,kuma duk zaluncin da ka yi min ba zan yafe maka ba"haka ta cigaba da sambatu, Nabeela da ta dawo ta yi tsumu ta na kallon Khairi da take ta kuka cikin jin ciwon abinda Auwab ya yi mata,ita dai Nabeela sai dai ta kalli Khairi ta kalli Auwab,wanda ya dafe kanshi da hannu bibbiyu,ko fuskar shi ba'a iya gani

A gigice Mamie ta shigo parlourn,gabanta ya faɗi ganin yadda Khairi ta raunata Auwab,cikin gigita ta ce"baki da hankali dama? menene haka?wanne irin rashin hankali ne wannan?kashe shi kike so kiyi?"

"Eh!so nake na kashe shi!Mamie idan na kashe shi na kashe masifar da ta gallabi rayuwa ta,na san zuciya ta zata huta da ganin abinda yake saka ta baƙin ciki, Mamie ki kore shi na tsane shi,na tsani ganin shi, Mamie ba na ƙaunar shi!"a fusace Ammi ta ɗauke ta da mari,wannan marin ne ya sa Auwab ya ɗago a firgice, Khairi ta saka ihu ta nufi cikin gidan da kururuwar kuka, Nabeela ma ta bi bayanta ta na kuka, Auwab da Mamie suka bi su da kallo


Kada dai a manta VIP group #300 ne kacal

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

✍️Nusy bee
*Young talented writers association (YOTA)*

Page 77


Mamie ta kalli Auwab cikin kulawa ta ce"ka yi haƙuri da halin Khairi don Allah!"Auwab ya yi ɗan murmushi ya ce"ba laifinta bane, an yi mata laifi ne Mamie!"

Daga nan family doctor ɗin su ta kira ya duba Auwab ya yi masa treatment,ta saka aka kawo masa abin taɓawa,sai dai ya kasa saka komai a bakinshi ko da ruwa ne

Bayan an nutsu ya gaida Mamie,ko wacece wannan a wajan Khairi tana da alaƙa da ita duba da tsananin kamanni,ta samu waje ta zauna a parlourn ta fuskance shi sosai ta ce

"Nice mahaifiyar Ummul khairi,na bar ta tun tana ƙarama, abubuwa kala kala sun faru,masu daɗi da akasin haka,sai dai ga dukkan alamu ta na jin zafin rabuwar da ka yi da ita har yanzu? menene gaskiyar maganar?"

Bai yi mamakin jin cewa ita mahaifiyar Khairi bace,amma ya yi mamakin inda suka haɗu da juna,sai dai bai nuna mata ba,ya ce"duk abinda Khairi ta faɗa miki haka ne,sai dai akwai dalili "ya ba ta labarin komai daga shigowar Inaaya rayuwar shi har zuwa yanzu da ta fita a rayuwar shi,irin ɓarnar da ta yi masa da irin cutar da ta saka shi ya rinƙa yiwa Khairi,yadda ta saka shi ya saki Khairi da cikin da bai san dashi ba,da yadda ya rinƙa ƙoƙarin ganin ya daidaita tsakanin su amma Khairi tana gwasale shi,har zuwa lokacin da aka neme ta aka rasa babu abinda ya bari bai gaya wa Mamie ba

Shiru Mamie ta yi ta na kallonshi,don ya fi bata tausayi ma fiye da Khairin,a hankali ta ce"to ina yaron nata?"

Cikin sanyin murya ya ce"yana nan,Ammina ta ɗauke shi"

Mamie ta sake yin shiru kafin ta ce "zai yiwu ka kawo shi ko da zuwa nan da ranar Sunday ne?don Yanzu ina bakin aiki aka kira ni ina so mu yi magana sosai"ya gyaɗa kai ya na faɗin "in sha Allahu zan kawo shi,sai dai Mamie ina roƙon wata alfarma"

"Ina jin ka!"ta bashi amsa

Da ƙyar ya iya tattaro nutsuwar shi ya ce"don Allah Mamie a bata haƙuri,komai ya faru ba laifi na bane,ta taimaka ko don darajar ɗanta Ajmal ta dawo ɗaki na,mu cigaba da riƙon shi tare,ko don duba da har yanzu shi jariri ne,kuma bai yi laifin komai ba"

Shiru ta yi cike da rashin jin daɗi,kafin ta ce "haka ne maganar ka,amma ba zan iya cewa komai ba har sai na yi magana da ita,don zancen da nake yi maka zuwa yanzu sun daidaita da ɗan miji na Hisham,jira yake ta zana exam ɗin ta ta NECO su je kano ya tambayi aurenta"

Har wasu taurari Auwab ya gani suna giftawa a idanun shi,ya ɗanyi shiru kafin ya aro jarumta ya ce"to shikenan, Allah ya dafa mana"Mamie ba ta iya amsawa ba saboda tausayinshi da ta ji,ya yi mata sallama ya miƙe ya fice daga parlourn, Mamie ta bishi da kallo cike da tausayin shi


** ** **


Khairi kuwa tana shiga ɗakin su ta zube a ƙasa tana mayar da numfashi, Nabeela da ta shigo daga baya ta ɗaga ta zaune,suka rungume juna suna kuka,sun kwashi seconds a haka kafin khairi ta janye jikin ta tana kallon Nabeela, Cikin sanyin murya ta fara magana

"Nabeela ina ji kamar zaman gidan nan ya fara fin ƙarfina,don shigowar Auwab cikinshi tamkar na bar shi ne!"

"Baza ki bar gidan nan saboda shi ba, amma tabbas shi ba zai sake taka koda ƙofar gidan nan ba,ki kwantar da hankalin ki Khairi"

Cikin gunjin kuka tace"meyasa zan kwantar da hankali na? Nabeela ni kaɗai na san masifar da na gani a gidan Auwab,ya bani wahala da shi da matar shi,in dai na tuna wannan abin yana yi min ciwo"

"Na sani,amma zuwa yanzu ya kamata ace kin wuce ki zauna kina kuka saboda Auwab,You have to move on khair,kowa yana cigaba kema ya kamata ki cigaba,ko har yanzu da soyayyar tashi a ranki?"da sauri Khairi ta girgiza kai tana faɗin"Allah ya sauwaƙe na so shi,naso me a tare da shi?"

Da ƙyar Nabeela ta danne dariya, wataƙila Khairi ta manta ta ji lokacin da take faɗar sai da ya koya mata son shi sannan ya guje ta,amma sai ta basar ta ce"don haka just erase him in your mind,ki cigaba da rayuwar ki cikin farin ciki"Khairi ta gyaɗa kai ta na jin ƙwarin gwiwa na shigarta,da haka Nabeela ta samu ta mantar da khairi damuwar ta


** ** **


Auwab kuwa yana fita daga gidan ya buɗe motar shi ya kifa kanshi akan steering yana sauke numfashi,ya ɗauki lokaci a haka kafin ya buɗe motar ya rufe komai,ya taka har bakin titi a ƙafa,ya tsari napep yace ya kai shi tasha

Kai tsaye motar Kano ya hau,har aka zo Kano baya cikin hankalinshi har sai da aka sanar da shi,kamar kazar da ƙwai ya fashe wa a ciki ya fice,ya sake samun napep zuwa gida

Ammi tana zaune a ɗakin lta,wanka tayi wa Ajmal tana cikin shirya shi sai ga Auwab ya faɗo ɗakin a firgice,sai da ta tsorata,yana zuwa ya faɗa jikin ta ya rungume ta da ƙarfi,sai ya fashe da wani matsanancin kuka

Jikin Ammi har rawa yake yi wajen tambayar "me ya faru Auwab?me ya same ka?waye ya rasu?don girman Allah Auwab ka sanar dani don ka ɗaga min hankali"

"Ammi nine zan mutu,ki taimake ni, mutuwa zan yi idan na rasa ta,Ammi ina son ta, Ammi ba laifi na bane,don girman Allah ki gaya mata,ta tsane ni,Ammi wani zata aura bani ba, Please Ammi na help me, I can't endure it anymore please Ammi "

"Wai wacece?akan wa kake magana ne?don Allah ka yi min bayani,ka ɗaga min hankali "ta faɗa itama ta na fashewa da kuka

A hankali ya fara daidaita nutsuwar shi ya na kallon Ajmal da tuni ya daɗe da fara kukan,yana kallon Ammi cikin rawar murya ya ce"Ammi Ummul Khair ce,wai wani take so ni ta bar ni,ta ce bata so na"

Sulaiman da ke tsaye bakin ƙofar yana kallon yayan nashi ya taho da sauri ya kamo shi ya zaunar dashi da ƙarfi ya ce"a ina ka ganta?meyasa baka dawo da ita ba? meyasa ka barta?"ya daidaita nutsuwar shi sannan ya gaya musu duk abinda ya faru,ya rufe da faɗin "ni yanzu idan tayi aure ta bar ni ban san yadda zan yi ba,ina tsananin son ta fiye da yadda nake son kaina, Ammi don Allah ki bata haƙuri kar ta guje ni,ta yafe min don Allah,ta aure ni ko bata so na,na ci albarkacin Ajmal Please Ammi, Man don Allah ku taimaka min"ya ƙarashe maganar yana riƙe hannun sulaiman,wanda mamaki da tausayin yayan nashi ya rufe shi

Sulaiman ne ya kwantar da murya yace"kar ka damu bruh, in sha Allah babu mai aurar maka mata,yanzu nan da ranar Sunday zamu je Kadunan tare,na san yadda zan yi,in sha Allah kaine zaka samu Khairi,yanzu ka ajiye wannan damuwar a gefe ka zo mu je mu duba mum, ɗazu mun yi waya da babban yaya ya ce an sallame ta tana gida,duk ka yi wani iri kamar ba jarumin yaya na ba mai taurin kai da kafiyar nan,mai shariyar man,kar ka bani kunya mana best friend,ko da yake khairi ta yi maka dukan ƙauna shiyasa duk jikin ya yi sanyi ko?"Auwab ya yi ɗan murmushi yana girgiza kai,in dai Sulaiman yana gefen shi baya taɓa yarda ya bar shi cikin damuwa,Shiyasa bashi da aminin da ya wuce Sulaiman a duniya

Da yamma tare suka je lugard road a motar sulaiman,don motar Auwab dai tana Kaduna,anan bayan sun gaida mum suka zauna da Azad suka gaya masa komai da ake ciki,ya yi farin cikin bayyanar khairi sosai,sai dai shima ya ji haushi jin cewa za ta auri wani,koda ya so ta so mai tsanani ya yi ƙoƙarin yaƙi da shaiɗan don kar ya dasa masa tsanar ɗan uwan nashi,kuma alhamdulillahi ya yi nasara,sai dai baya jin zai iya yaƙi da shaiɗan akan wani bare can,don haka ko shi dole zai san duk yadda zai yi Khairi ta koma ɗakin ta

Don haka ya dafa kafaɗar Auwab cikin sanyin murya ya ce"kar ka damu bruh,in dai Ummul khairi tamu ce babu wani wanda ya isa ya same ta sai mijin ta Muhammad Auwab,ka kwantar da hankalin ka"Auwab cikin raunin murya ya ce"sure babban yaya?kar na saka rai kuma hakan ya gagara,a hannun mahaifiyarta take fa,kuma wanda ake maganar zata aura mahaifiyar ta ta amince dashi fa"

Allah sarki rayuwa 😭yau dai ga Azad yana karfafawa Auwab alƙawarin samar masa auren Khairi 🥺salute to pure Love ❤️

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

✍️Nusy bee
*Young talented writers association (YOTA)*

Page 78

Azad ya yi murmushin ba shi ƙwarin gwiwa,ya dafa kafaɗarshi ya ce"ni fa na ce ka bar komai a hannu na,ko ka manta wanene Sa'eed ne?"

Auwab ya girgiza kai ya na murmushi ya ce "ban manta ba,na gode sosai big bruh, Allah ya bawa mummy lafiya"

Azad da Sulaiman suka amsa da "Ameen"shi dai sulaiman yau babu tsokana,don dukkansu su biyu tausayi suke ba shi,ya san Azad ƙarfin hali kawai yake yi, amma har yanzu ya na son Khairi

Dukansu su su ukun suka tsara tafiyar zuwa ranar Sunday,nan da kwana biyu kenan, Auwab kamar ya janyo ranar haka yake ji,duk da cewa ya na fargabar yadda za su kwashe da ƴar rigimar tashi a karo na biyu


MALALI, KADUNA STATE, NIGERIA


Kwana ɗaya da faruwar hakan sai ga Hisham ya dawo,ashe Nabeela ce ta kira shi a ɓoye ta sanar da shi cewa tsohon mijin Khairi ya zo gidan,don haka nan da nan ya yi azamar zuwa

Da Mamie ya zauna,ta yi masa bayanin komai a nutse,duk da ya ji tausayin Auwab ɗin amma baya jin zai iya bar masa Khairi,ya ce Allah ya kawo shi lafiya

Ai kuwa washe gari ta kama Monday,da yamma wajen ƙarfe uku, Khairi ta na ɗaki ta na game a wayar ta, Nabeela kuma ta na zaune akan study table ta na kallo a laptop ɗin ta,sai ga kiran Mamie ta ce ta fito

Doguwar riga ce a jikin ta ash color,ta ɗauki mayafin rigar da ke gefenta ta yafa ta nufi ƙofa, Nabeela da ta bi ta da kallo ta miƙe ta na faɗin "ina zuwa?"

"Mamie ce ke kira na,idan za ki je taho mu tafi"babu musu Nabeela ta bi bayan Khairi suka nufi parlourn Mamie

Da sallama suka shiga,dukkan su suka ƙame da mamaki suna kallon mutanen dake zaune a parlourn, Khairi ta saki murmushi ta na faɗin "yaya na!yaya Sulaiman!!sannun ku da zuwa,na yi kewar ku sosai"

Azad ya kalle ta ya na murmushi, Sulaiman ya ce"ba wani nan,gashi nan kin yi ƙiba abin ki, kin bar mu da jimami?"ta yi murmushi,ta buɗe baki da zummar sake magana sauti mafi soyuwa a gare ta ya ratsa dodon kunnen ta

"Umma! ummaaaa!!!!"

Jikin ta har rawa yake yi ta na dariya da ɗan hawaye,ya taho da gudu ya ɗafe ta,ta rungume shi sosai,take ta ji zuciyar ta ta karye,take ta fashe da kuka sosai,da ƙyar ta iya ɗago shi daga ƙirjin ta ta fara masa magana kamar wani babba

"Ashe ba ka manta ni ba baba na?na yi kewar ka,na yi kewar ka,na yi kukan rashin ka,kai ne duniya ta,kaine farin ciki na,ka yafewa ummanka kaji?ba a son raina na tafi na bar ka ba,in sha Allahu yanzu ba zamu sake rabuwa ba ka ji? ka ji best friend??"ta ɗago idanun ta cike da hawaye ta na kallon Nabeela da tayi sakare tana kallonta cikin tausayawata ce"Nabeela ga yaro na Ajmal,wanda muka rabu da shi watanni biyu da ƴan kwanaki baya,gashi ga sake dawowa gare ni"Nabeela da ƙwallar tausayin Khairi ta cika idanun ta ta ƙaraso ta kama Ajmal ta ɗauke shi, Khairi ta goge idanun ta ta na kallon Sulaiman ta ce"yaya Sulaiman ya yi jinya ne?"

Sulaiman ya ce"ya rame ko?"

Khairi ta ce"ya rame haka,amma sai ya yi wani iri"ya ce"kin san baya cin abinci,madara ma ba kowacce yake amsa ba,kuma sai yunwa ta matsa masa,gashi ya saka ƙulafucin ki a ranshi,kwana biyun nan ne ya rage koke koke da kiran ki"hawaye suka zubo mata,cikin raunin murya ta ce"na zalunce shi ko yaya?"

Azad da tausayinta ya kama shi ya ce"ba ki zalunce shi ba Khairi, Allah shine shaida, jarrabawa ce ta same shi,amma alhamdulillahi tunda komai ya wuce"Khairi ta ce"yanzu zan iya cigaba da shayar da shi?kaga har yanzu jariri ne"

Mamie ta kalle ta cike da takaici da kunya, Azad ya ce"tunda yanzu ya manta kuma ya fara sabawa da madarar ina ga bar shi a yayen kawai, Allah ya raya mana shi"ta yi ɗan murmushi ta na zuciyar ta cike da jin daɗi da farin cikin dawowar cute baby boy ɗin nata,sai kuma ta gaida Azad da Sulaiman,har da Hisham ma da ya tarbo su suka yi gaisuwar mutunci suka shigo

Ta juya zata tafi Mamie tace"Khairi koma ki gaida yayan ki!"

Juyowa ta yi tana yatsina fuska ta ce "Mamie wane yayan nawa?duk na gaida su fa"wani mugun kallo ta watsa mata,babu shiri ta juya tana kallon Auwab, wanda duk abinda take yi ya na zaune ya na kallonta,ta watsa masa harara ta ce "Sannu!"tayi wuf ta fice daga parlourn tana ƙunƙuni

Mamie da su Sulaiman sun ɗan daɗe suna tattaunawa kafin su yi mata sallama suna ta yi musu godiya ita da Hisham, ta ce babu komai ai an zama ɗaya, Sulaiman ya ce a kira khairi suyi sallama,sai gashi sun fito ita da Nabeela

Sai a lokacin suka gaisa sosai da Nabeela,Khairi tana murmushi take faɗin "yaya Sulaiman,yaya Azad kun tuna ta?ƙawa ta ce fa,tare muka yi Queen's College,ajin mu ɗaya,ikon Allah ashe wai ƴar uwa ta ce!"

"Allah sarki!ashe kune kuka bata shawara,ko na ce kuka zuga ta ta rinƙa shan maganin dakatar da menstruation ko?"

A fusace ta kalle shi kamar dama jira take,tace"malam tunda ka zo ka ji na yi maka magana?"

Shima da sauri yace"kinji nima na yi Miki magana,ni ba dake nake ba"Nabeela dai kunya ta rufe ta, Khairi ta yunƙura za ta sake magana Nabeela ta ce "Malama ba dake yake ba fa,almasifatu!"ai kuwa ta koma kanta da masifa,sai da Mamie ta yi mata tsawa sannan ta yi shiru tana huci

Cike da takaici Mamie ke faɗin "ashe haka kike yi wa mijin naki rashin kunya Khairi?"

Zumɓura baki ta yi tana faɗin "ni fa ba miji na bane"

"Zan kwaɗe ki anan wajen idan baki yi min shiru ba"Sulaiman da yaji takaicin dakatawar wannan drama ya ce"Mamie faɗan ƙauna ne fa, ba'a dakatar dashi,irin wannan faɗan ƙara danƙon soyayya yake yi"gaba ɗaya sai da suka yi dariya banda Khairi da ta cika tayi fam,hatta da Hisham da ya yi dariya sai da ta ji haushin shi, ba'a maganar Nabeela, ballantana kuma Sulaiman da Azad,kankat kuwa uban tafiya,wato Auwab

Sai da aka gama raha sannan Sulaiman ta ce "Khairi yaushe za ki zo dubiyar mum?"

"Bata da lafiya ne?"ta faɗa yanayin ta yana sauyawa

Azad yace"ai ta juma ta na jinya"take tashin hankali ya bayyana a fuskar ta,ta ce"zan bi ku na ga jikin ta"

Azad ya ce"yanzu? ki bari sai next time,Kin ga yanzu lokaci ya ƙure,zamu iya yin dare a hanya"ta fashe da kuka tana faɗin"don girman Allah ka kaini naga mummy,don Allah!"Azad ya ce"to ki tambayi Mamie,idan ta amince sai mu tafi "Mamie tace"na amince, Allah ya tsare hanya,daga nan sai ku kai ta wajen kakar ta su gaisa "da sauri khairi ta ce"wacce kakar tawa?"

Mamie tace"inna sabuwa, mahaifiyar baban ki"

"Allah ya sauwaƙe,idan banda ƙaddara ma me zai mayar dani wajen wannan matar? wallahi ko garin naje ba wajen ta na je ba"dariya kawai suka yi, Azad ya ce yana murmushi"kema Mamie naji an ce ta gwada yi miki kama karya zata yi miki auren dole,kika gudu "Mamie ta yi ƴar dariya ta ce"ai barrister aka ce na aura,wai na gyarawa mummy zama,na ce ni zaman aure ya kawo ni ba gyara zama ba,kuma miji na ya rasu, shine fa ta kore ni ta raba ni da ƴa ta"

Duk da ta yi ƙoƙarin dannewa amma sun karanci abin ya taɓa mata rai, Sulaiman ne Sarkin zolaya yace"a'a Mamie,kin dai guji Daddy,kin nuna bakya yin mu kawai"suka yi dariya, Hisham ya ce"Daddy dai sai dai ya yi haƙuri,amma Mamie ta abban mu ce,daga ita babu ƙari "haka dai suka yi ta tsokanar juna, Nabeela na kallon su suna burge ta,kafin Khairi ta fito, Nabeela ma ta ce zata bi su

Da aka zo shiga mota Khairi ta ce baza ta shiga ta Auwab ba,kuma babu wanda zai shiga tsakanin Azad da Sulaiman,shi dai Hisham da ya ga rigima ta ƙi ƙarewa sai ya kalli khairi cikin kwantar da murya yace "Khairi ya kamata ki rinƙa tunawa Auwab yayan ki ne,jinin ki ne,kuma uba ga ɗan ki,har yanzu yana da damar sake zama miji a gare ki,don Allah ko bai ci albarkacin komai ba yaci na ɗanshi,ki nunawa Ajmal soyayya ta hanyar martaba mahaifin shi, Please Ummul khair"jikin ta ya yi sanyi, batare da ta sake magana ba ta buɗe baya a motar Auwab ta shiga, itama Nabeela ta shiga, Auwab ya shiga gaba ya tayar,suka ɗagawa Hisham hannu suka fice, Sulaiman da Azad suka biyo bayan su


Shagaliiiiii 😂

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

✍️ Nusy bee
*Young talented writers association (YOTA)*

Page 79

Suna tafiya a hanya Khairi tana yadawa Auwab habaici tana farfaɗa masa maganganu,ko kallonta bai yi ba, driving ɗin shi kawai yake yi,ƙarshe Nabeela ce ta gaji ta ce"wai ke Khairi menene haka?tunda muka shigo kike ta yada habaici, lafiya....?"

"Munafuka!ina ruwan ki?dake nake?kar ki sake saka min baki a magana!"

"Na saka ɗin! haba!kin dame ni!!sai masifa kike yi kina ta jaraba duk kin gallabi mutane"daga nan Khairi da Nabeela suka kama hayaniya,dama sun saba,har hakan ya tashi Ajmal ya fara yunkurin kuka,ci kanku Auwab bai ce musu ba,hakan ya sake fusata Khairi,ta kalle shi a kufule t ace"malam tsaya ka ajiye ni, baza'a je a motar taka ba!"

Banza ya yi mata kamar bai ji ta ba,ta sake cika ta ce"malam magana nake yi,ka sauke ni ko?"

Nan ma dai kamar tana magana da motar,daidai nan aka zo danger,a fusace ta fara yunƙurin ficewa daga motar,ita dai Nabeela sai ta zama ƴar kallo

Ta yi ta kiki-kikin buɗe ƙofar,ganin baza ta buɗu ba sai ta kalle shi a fusace ta ce"Malam buɗe min na fita"nan ma kamar ta na magana da dutse,dariya ta kufcewa Nabeela,baƙin cikin haka ya sa Khairi fashewa da kuka,dama Ajmal ya na ta kuka ko saurarenshi basu yi ba,sai Nabeela ce take ɗan rarrashin shi

Sai yanzu Auwab ya juyo ya kalle ta,cikin kwantar da murya ya ce "Ummul khairi,na haɗa ki da girman Allah ki yi haƙuri ki bari mu kai kano lafiya,idan ya so duk hukuncin da za kiyi min da faɗan da za kiyi min zan karɓa,amma wannan faɗan da kike ta yi babu abinda yake saka ni sai rasa nutsuwa ta,kuma gamu a babban titi, Please Ummul khairi ba don ni ba"Khairi dai bata ce komai ba,sai goge idanunta da ta fara yi fuska a murtuke,ya ja mota suka cigaba da tafiya,suma dai babu wadda ta sake magana

Basu isa Kano ba sai da isha'i,kai tsaye lugard road suka wuce,a bakin gate ya yi parking kusa da inda sulaiman ya yi parking tashi motar,ya wuce masallaci su kuma matan suka wuce gida

Da sallama Khairi ta shiga main parlour na ɓangaren mum,Nusra ta ɗago ta na amsawa,ta na tabbatar da ganin khairi ta yi ihun murna ta rungume ta, Beely ma da ke fitowa daga ɗaki ta zo ta rungume ta cikin farin ciki

Babu wadda ta yi mata maganar meyasa ta tafi da inda ta tafi, ballantana ayi mata faɗa kasancewar sun san komai, Nusra da rawar jiki ta kawo musu ababen motsa baki kala kala,amma ita ta ce mum take so ta fara gani

Beely ta ce"mum tana ɗaki,ta ji sauƙi ma,yau ne jikin yake son rikicewa,kuma ba ki gabatar mana da ƙawar taki ba"

Da Khairi da Nabeela duk murmushi suka yi, Khairi ta ce "Aminiya ta ce,kuma ƴa a wajen mahaifiya ta,don ƴar mijinta ce"Nusra tace"wow!ya sunan ta?

Khairi ta ce"Nabeela "

"Wow! nice to meet you Nabeela "a cewar Beely,ita dai Nabeela Babu baki sai murmushi kawai

Kasancewar mum ta kwanta sai su Beely suka bawa Khairi shawara ta bari sai gobe sai su gaisa,khairi ta ce"ita ko yaya ne ta na son ta ganta,babu musu suka bar ta ta shiga ita kaɗai,don Nabeela ma ta ce yau da gobe duk ɗaya ne,za ta bari sai goben sai su gaisa

Da sallama ta shiga ɗakin mum,bata ciki ta shiga banɗaki,amma Khairi ta na iya jiyo sautin amai,don haka da sauri ta ƙarasa banɗakin tana faɗin "sannu mum,jikin ne ya...."

Maganar ta maƙale ganin mum ta na Aman jini,take ta gigice ta riƙo hannun ta ta na faɗin "inna lillahi wa inna ilayhi rajiun!mum bari in gayawa yaya ya kai ki asibiti,mum...."da sauri mum ta riƙe mata hannu,cikin ƙarfin hali ta fara ƙoƙarin wanke wajen, Khairi ta taya ta jikin ta ya na kyarma,ta taimaka mata suka fito daga ɗakin ta zaunar da ita a bakin gado

Gaskiyar bahaushe da ya ce abinda ya baka tsoro watarana zai ba ka tausayi,yau dai ga Khairi a gaban mum ta na zubar da hawaye,amma hawayen tausayinta

Cikin ƙarfin hali mum ta riƙo hannun ta tana murmushin ƙarfin hali ta ce"khairi ke ce?sannu da zuwa,ina yaron naki?"

Khairi ta girgiza kai ta ce"mum kina buƙatar zuwa asibiti don Allah,aman jini ga kika yi yanzu"cike da ƙarfin hali mum ya gogewa Khairi hawaye ta ce"kar ki damu,idan na sha magani ne nake yin hakan,cuta ce take fita,zauna,dama ina so mu yi magana da ke"

Babu musu Khairi ta zauna a gefen mum jikinta na rawa,mum ta ce "komai na rayuwa mujarrabi ne daga Allah, Allah yana jarabta bawa da abubuwa kala kala,babu jarrabawa mafi ciwo irin Allah ya jarabci mutum da mahaifiya,irin abinda ya samu yayan ki Azad kenan"kuka ya ƙwacewa mum,ita ma Khairi ta ƙara sautin kukanta,mum ta cigaba"a kaf ƴaƴana babu wanda ya yi min biyayya ko da kwatankwacin wadda Azad ya yi min,babu wanda ya so ni da alkhairi kwatankwacin yadda Azad ya so ni,babu wanda yake ƙaunar farin cikina ko da kwatankwacin yadda Azad ya so farin ciki na,amma ban yi masa adalci ba,na raba shi da abinda ya fi so fiye da komai a duniya,na liƙa masa wanda baya so,na cutar da ɗana,na nakasa shi da hannu na,na yi nadama,ki yafe min Khairi!"cikin matsanancin kuka ta ƙarashe maganar

Khairi tana kuka ta ce "mum ban taɓa ƙullatar ki ba wallahi,ke uwa ce a gare ni,kin amfanar da ni tarin alkhairi,ko da ace kin yi min kuskure na yafe miki,kema ki yafe min"mum ta yi ɗan murmushi tana kallon Khairi da ta rungume ta,ta ce"na gode sosai Ummul khairi,zan iya roƙon ki alfarma,wadda ta kasance ta farko, kuma ta ƙarshe da zan roƙe ki?"

"Mum ki ba ni umarni kawai zan bi, in sha Allah zan bi"mum ta yi ɗan murmushi ta ce

"Na gode Khairi!ina roƙon ki ki taimaka ki auri ɗana AZAD! Azad ya so ki son da bai taɓa yiwa ko da kan shi ba,ni na hana ya aure ki,a dalilin haka ɗana ya kamu da ciwon zuciya bayan ciwon athma da yake da shi,a dalilin kuskure na ɗana mafi soyuwa a gare ni sai da ya yi watanni a doguwar suma,don Allah khairi kiyi min alƙawarin auren shi "

Gaba ɗaya jikin Khairi ya yi wani irin sanyi, Azad? Azad dai da ta sani? dole ta gasgata mum,amma da ace a bakin wani ta ji wannan maganar baza ta yarda ba,a sanyaye ta amsa"na yi miki alƙawari mum!"

Mum ta yi murmushi sosai,tace"Allah na gode maka da ka bani ikon gyara kuskure na kafin ƙasa ta rufe idanuna, Khairi bari na kwanta, lokacin bacci na ya yi,da safe zamu gaisa sosai"ta kwanta,khairi ta ja mata bargo ta yi mata addu'a ta tofa mata sannan ta fice daga parlourn cikin sanyin jiki

Ta na shiga main parlour su Azad suka shigo da sallama,ta ɗaga kai ta na kallon shi,shima kallonta yake yi saboda chanjawar yanayin ta,a hankali ta ce"yaya na!"Muryar ta na rawa,sai hawaye ya fara zubo mata sharrrr,gaba ɗaya mutanen parlourn suka zabura da mamakin dalilin kukan nata,ta fice a hankali daga part ɗin,Azad ya bi bayan ta,don yaga ko menene ya na da alaƙa dashi

A bakin part ɗin aunty Naja,wadda bata nan,ta je albasu saboda ƴarta rabi ta haihu amma babu ɗan,ga rabin babu lafiya,a bakin part ɗin nata Khairi ta tsaya ta na kallon Azad da ya ƙaraso ya na tambayar lafiya? Khairi cikin kuka ta fara faɗin "why yaya na?why? meyasa ka ɓoye min soyayyar ka a gare ni?meyasa ka cutu ta dalili na?yaya na laifi na ne? meyasa......?"

"Waye ya gaya miki?"ya tambaya yana kallon ta cikin mamaki ƙarara akan fuskarshi

"Mummy,har ma ta roƙe ni na aure ka"

Ɗan buɗe idanu yayi ya ce"really?to me kika ce mata?"

Ta ce"na amsa,na yarda zan aure ka yaya!"

Azad ya yi ɗan murmushi,kallo ɗaya za'a yi masa a gane mai ciwo ne,ya ɗan nisa kafin ya ce"komai na rayuwa ya na tafiya bisa doron ƙaddara Ummul khairi, ƙaddarata ce zan so ki,son da ban taɓa jin irin shi ba, sai dai kuma jarrabawata ce rashin samun samun ki,kuma na karɓi hakan da hannu bibbiyu ina fatan Allah ya musanya min da mafificin alkhairi a rayuwa ta

Khair a Yanzu kin yi min nisa,nisan da ba zan taɓa iya kamo ki ba,don haka waccan maganar na binne ta a raina, kema ki binne ta,mum zafin ciwo kawai ya sa take roƙon ki ki aure ni,amma a yanzu babu wanda kika dace ki zama matar shi sama da mijin ki uban ɗanki Auwab

Shi da sulaiman bani da ƴan uwan da suka fiye min su,ba zan yadda mace ta raba mu ba, musamman wadda mu duka take matsayin ƙanwa a gare mu

Da ace Auwab bai aure ki ba,ko kuma na ce babu soyayyar ki a ranshi tabbas Khairi zan aure ki,amma a yanzu idan na ce zan aure ki zan jefa shi cikin mawuyacin hali fiye da wanda na shiga a baya, please Ummul khair......"

Khairi ta fashe da kuka sosai ta ce"na gane yaya Azad,a Yanzu baka so na,baka ra'ayi na,maybe ka samu wadda tafi ni komai ne, idan ka gaya min hakan ba kayi laifi ba,zan bi ka da fatan alkhairi,amma wani jingina min Auwab da kake yi me kake nufi?inace da kai da yaya sulaiman kuka je har gidan shi kuka ɗauko ni a wulaƙance a ƙasƙance?har ka manta?to ko ban aure ka ba ina da wanda ya fiye min wani Auwab can"tana gama faɗar hakan ta bar wajen a fusace tana kuka,ya bi ta da kallo ya na ɗan murmushi,Khairi dai har yanzu da yarinta akanta sosai


Khairi daru 😆


#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

✍️ Nusy bee
*Young talented writers association (YOTA)*

Page 80


Ko da khairi ta koma cikin gidan ta shiga cikin su Beely suka yi ta hira,har su Auwab suka yi musu sallama shi da sulaiman suka tafi bai ga fuskar magana a wajen Khairi ba,shima kanshi Azad ɗin sai ta ɗauke masa wuta,sai dai shi bai damu ba,sai ya nuna kamar bai san ma tana yi ba, saɓanin Auwab da ya nuna rashin jin daɗin shi

Wajen ƙarfe biyu da rabi Azad ya farka a firgice,da sunan Allah a bakinshi,a hankali ya janyo wayar shi ya na duba lokaci,daidai lokacin kira ya sake shigowa wayar tashi,my world shine sunan da yake ta yawo akan screen ɗin wayar, ba kowa ba ce sai mum,ya yi azamar ɗaga wayar da sallama

Bai ji abinda take cewa ba saboda yadda maganar ba ta fita,cikin azama ya sanya jallabiyar shi ya yi waje,da azama ya nufi ɗakin mum

Hankalin shi ne ya yi masifar tashi ganin halin da take ciki,da sauri ya ƙarasa ya ɗago ta ya na faɗin "sannu mum,jikin ne?"

Ƙasa ƙasa yake jin Muryar ta tana faɗin"Azad ka yafe min ka ji? Allah ya yi maka albarka, Allah ya yi muku albarka gaba ɗaya da kai da ƙannenka,kuma na yafe muku duniya da lahira,ka roƙar min daddyn ku da Naja'atu suma su yafe min"

"Noooo mum, don Allah ki daina irin wannan maganar,za ki bani tsoro mum,bari yanzu mu koma asibiti, haba mum, please "tana ta magana bai saurare ta ba ya yi azamar yiwa driver Magana ya dawo ɗakin,ya sunkuce ta ya yi azamar ɗaga ta ya fice da ita ya sanya ta a mota,driver ya ja suka nufi asibiti

Ba zai iya ƙirga awannin da ya kwashe ya na zaman jiran tsammani daga likitocin da suka shiga da mum ICU ba,kuma har zuwa lokacin bai sanar da ko Daddy da ya koma bakin aikin shi shekaranjiya ba, ballantana sauran jama'ar gidan

Ƙarfe huɗu da mintuna goma daidai,ya fara jin kiraye kirayen farko na sallar asuba,gaban shi ya buga,daidai da sarawar kanshi,ya dafe kan ya na ambaton Allah,ya ɗan ɗago ya na kallon likitoci biyu da suka shiga da mum ICU suna fitowa, fuskokin su cike da alhini

Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke,ya miƙe tsaye jikinshi ya na ƴar rawa ya ƙarasa gaban su ya na faɗin "yaya mum take?"

Ba su kalle shi ba,ɗaya daga cikin su ya ce"ta samu bacci"don duk Wanda ya san Azad ya san yadda yake masifar ƙaunar mum ɗin shi,ya na kallo suka wuce shi,ba shi da zaɓi sama da ya koma gefe ya cigaba da zama

Likita na ƙarshe da ya fito Azad ya sha gaban shi yana kallon shi,da wata iriyar murya ya ce"Dr me ya samu mummy na?ka gaya min,ni musulmi ne,na yarda da ƙaddara,duk abinda ya faru I will accept it with good faith,ni dai ka gaya min,me ya samu mum?"

"I'm sorry Mr Saeed, Allah ya amshi mum,sai dai mu yi fatan Allah ya ji ƙanta ya yi mata rahama"yana faɗin haka ya gaggauta barin wajen da sauri,ko iya kallon fuskar Azad ɗin bai yi ba

Tabbas mutuwa gaskiya ce! gaskiya mai ɗaci,wadda ko wane ɗan adam zai ɗanɗane ta, rayuwar duniya mai ƙarewa ce,wadda take shagaltar da wawayen cikin mu,mum dai tashi,wadda ƴan awanni baya ya yi magana da ita a yau ita ce ake gaya masa ba zai sake ji daga gare ta ba,ya koma inda yake zaune ya zauna ya na bin mutane da kallo ya na sauke ajiyar zuciya lokaci lokaci

Wajen ƙarfe takwas na safe ambulance dake ɗauke da gawar mum ta iso bakin gate ɗin gidan barrister,mai gadi ya buɗe gate motar ta shiga,motar sulaiman dake ɗauke da Auwab da Azad ta bi bayan ta

Babu wanda Azad ya sanarwa rasuwar mum sai Sulaiman,shima bai sanarwa kowa ba sai Auwab,sun jijjiga da mutuwar mum,kuma dukan su sun tausayawa Azad,sun sha matuƙar mamaki ma da har ya iya ɗaga waya ya kira Sulaiman ya shaida masa,shine suka shirya suka wuce asibitin,acan ma da suka gan shi a nutse yake,duk da akwai bayyanar tashin hankali da ruɗani akan fuskar shi,tare da su aka yi komai aka basu mum suka taho gida

Su Beely basu ma san abinda ya faru ba, Nusra ce ta fara gano ambulance ta tseguntawa su Beely da suke zaune a ɗakinta gaba ɗayan su, Ajmal ya tashi da ɗan zazzaɓi, Yusaira kuma ta tashi tana kukan yayen da Beely ta yi mata jiya jiya,a cewar ta tunda aka yaye ƙanin ta itama ta yayu

Nusra tana shigowa tace"aunty Beely Kinga ambulance a gidan nan"sai da gaban su ya faɗi,dama sun yi mamakin rashin fitowar mum ɗin da wuri,amma da yake wani lokacin tana hakan sai basu wani damu ba

Beely ce ta miƙe ta nufi ɗakin mum ɗin don ta duba ta,sai dai a kulle,ta juyo ta dawo parlour sai ga wasu mutane including Azad, Auwab da Sulaiman a cikin su suna ƙoƙarin shigo da gawa

Jikin ta ne ya kama kyarma,da hanzari ta furta"inna lillahi wa inna ilayhi rajiun!waye wannan?wa kuka kawo yaya?"

Bai amsa ta ba sai da suka shigo da mum tsakiyar parlourn, Auwab ya shimfiɗa tabarma suka kwantar da ita sannan Azad ya kalle ta cikin wani irin sanyi ya ce"Allan da ya bamu mahaifiya,ya ƙaddari muka rayu da ita har muka mallaki hankalin mu,ba don munfi marayun da yake rabawa da tasu tun suna jinin haihuwa ba,a yau ya nufe ta da komawa gare shi,a yanzu babu abinda take buƙata daga gare mu sai addu'a"ya na gama faɗin haka ya nufi ƙofar fita daga parlourn ya na ƙoƙarin ɗaga kiran daddy da yake hanyar zuwa

Kafin azahar gida ya cika da mutane,an yiwa mum sutura an kai ta gidan gaskiya,kowa ya jinjina wa Azad,don ko ɗigon hawaye har yanzu bai zubar ba,ammie da aunty Naja suka yi mata wanka,suka shirya ta, Haidar da Ma'aruf kam sai da aka rufe su a ɗaki,don kamar ɗan ƙaramin hauka za suyi, Azad kuwa dashi aka kama makarar,dashi aka sanya ta a kabarin ta,amma ko ɗigon hawaye babu a fuskar shi,Auwab da sulaiman dai sun yi matuƙar firgita da wannan rashin kuka na Azad,don ko su sun zubar da hawaye,Feena ma kamar zata yi hauka saboda tashin hankali da kuka,Daddy ma gigicewa yayi,abin mamaki Azad ne mai kwantar masa da hankali,su Beely kam ba'a magana,don suman ta biyu, su Khairi ma dai hatta da su Nabeela,wadda ta yi nadamar rashin bin Khairi ta gaisa da mum jiya,ashe babu rabon ganawa tsakanin su

Bayan isha'i Azad yana zaune a lambun gidan ya lumshe idanun shi,shi kaɗai ya san me yake ji,ƙarfin hali da dangana kawai Allah ya bashi,amma ya san ba don haka ba rasuwar mum tana iya yin silar tashi rasuwar,gaba ɗaya duniyar ta yi masa ƙunci,jin shi yake yi kamar marayan da ya rasa komai a rayuwar shi

Sallama yabji cikin sanyin murya, da sauri ya buɗe idanu ya na kallon matashiyar yarinyar da suka zo tare jiya,ya gyara zama yana amsa sallamar,ta durƙusa tabna gaishe shi,ya amsa da sakin fuska,ta ajiye masa tray ɗin hannun ta tana faɗin

"Yau tun safe baka saka komai a bakinka ba, shine aunty tace na kawo maka"murmushi ya yi yana faɗin "na gode,amma bana jin yunwa ne"tabce "to don Allah kaci ko kaɗan ne,kaga ba zata ji daɗi ba idan na mayar mata baka ci ba"da haka ta samu ta lallaɓa shi da ƙyar ya ci mara yawa

Washegari Mamie ta zo da mai gidan ta Alhaji Saleh,wanda ya kasance aboki ga barrister Umar,sai su Hisham da fadwa da ƴan biyu,sun samu tarba mai kyau babu laifi,a ranar inna sabuwa ta zo,sai kuka take yi sosai tana faɗin Salma ta yafe mata,kuma tana faɗar kyawawan halayen Salma ɗin da ta sani,su dai waɗanda suka san tsakanin su sai bin ta da kallo suke yi,ciki kuwa har da Ammi

Bayan kwana uku da rasuwar mutane sun ɗan ragu,har lokacin Azad ƙarfin hali kawai yake yi,don ciwon shi na zuciya ne yake cin shi a hankali a hankali, Hisham ne ya fara matsa masa su je asibiti,suna zuwa kuma akayi admitting ɗin shi

Ita dai Mamie ta tafi,amma su Khairi suna nan,washegari a kwana na huɗu,a lokacin hatta su Beely sun ɗauki dangana,tana ɗaki tana bawa Yusaira da Ajmal Custard ɗin da ta dama musu Nusra ta leƙo ta ce"aunty Beely kin yi baƙi"

"To ina zuwa"abinda ta ce kenan,don ta san baza ta rabu da ƴan zuwa gaisuwa ba

Miƙewa ta yi bayan ta gama ba su Custard ɗin, ta sanya hijabinta ta kama hannayen su suka nufi main parlour

Tsaye ta yi da mamaki tana kallon Samha, wadda ke rungume da ɗan jaririn da bai fi watanni uku ba tabna yi mata murmushi

Itama Beely murmushin ƙarfin hali ta yi mata tana faɗin "sannu da zuwa"ta ƙarasa ta amshi babyn,shima kyakkyawa kamar Aman,tace"Masha Allah!ashe haihuwa kika yi!"

Samha ta ce "haihuwa nabyi,watanni uku baya,an samu Haisam,wannan ita ce ƴar tamu ko?"ta faɗa tana zama

Beely ta ce"ita ce"Samha tabce"I see!kamar ku ɗaya,wannan fa?"ta nuna Ajmal

Murmushi Beely ta yi ta ce"ɗan Khairi ne"

Wata zabura Samha ta yi ta ce"wacce khairin kike magana akai?"

Beely ta yi ƴar dariya ta ce"Khairi dai tamu, Ita ce ta yi aure har ta haihu,ga albarkar auren nan a gaban ki ma"Samha ta yi mamaki sosai,kafin su gaisa kamar babu abinda ya faru tsakanin su, Samha ta yi mata ta'aziyya sannan ta ce ta kira mata khairin

Tare suka ƙaraso wajen,ta na ganin ta ta gane ta,ta yi murmushi ta rissina ta gaishe ta, Samha ta amsa da fara'a tana faɗin "sannu maman boy"Khairi ta yi murmushi bata ce komai ba, Samha ta ce"Allah Sarki!ashe aure kika yi!na ga yaro, Allah ya raya shi"Khairi ta na murmushi ta ce"aure na yi,amma yanzu ma na koma makaranta ne"Samha ta ce"to Allah ya albarkaci rayuwar ku ke da shi"Khairi ta ce"Ameen na gode "daga bisani ta yi mata sallama ta koma cikin ɗakin ta na gidan inda suke tare da Nabeela da Nusra

Samha ta dubi Beely ta na faɗin "Bilkisu Umar,is already time for you ki koma ɗakinki Please,mu gina zaman ibada,mun san halin juna,kuma kafin komai ya faru mu ɗin masu son farin cikin juna ne,to bai kamata ace mun raba gari irin haka ba,bai kamata mu bawa shaiɗan ƙofar da zai shiga tsakaninmu ba,don Allah ki dawo ɗakin ki,na san Dr ya nemi ki dawo amma kin ƙi,amma ban san dalilin ki ba"

Beely ta girgiza kai,kai tsaye ta ce"na gama auren mijinki har abada Samha,bani da buƙatar ƙarar da rayuwata a wajen aikata abubuwan da za su kaini ga dana sani,da ace tun farko na san Dr Salis mijinki ne da ban aure shi ba,to ban sani ba sai da abu ya zo daf,kuma a wannan lokacin idanu na a rufe suke kawai na yi aure na huta da maganganun mutane,a ƙarshe sai gashi na jefa kaina a halaka,har ƙarshe ta kaini ga nadama

Zan zauna jiran zuwan nawa mijin da Allah ya zaɓa min, idan kuma bani da rabon sake aure zan rungumi yarinya ta ɗaya da Allah ya bani,da ƙanne na huɗu da nake da su,na gode masa a duk yadda ya tsara min rayuwata kawai"ta kasa tsayar da zafafan hawayen da suka zubo mata

"A'a Beely,za ki haramta abinda Allah ya halatta,ba mijina bane ni kaɗai,har da ke,bakya ganin Allah ya zaɓa miki Salis ne a matsayin miji shiyasa komai ya tafi a ɓoye har daf da bikin,kin yi kuskure nima nayi,mu taru mu gyara kawai,yanzu idan kika ce bazaiki koma gidan mijin ki ba bana jin kinyi wa babyn ki adalci,don.......

"Rashin adalci ai na gama yi mata tun lokacin da na auri mahaifinta, saboda......"

"Baki da wani dalili Beely!baki da wani abu da za ki ce,kinga mu bar wannan chapter ɗin,mu je Dr yana bakin gate,ya gamu da ƙannen ki maza mun yi musu gaisuwa,kije yayi Miki,ina yaya Azad?"

"Bashi da lafiya,ya na asibiti "ta bata amsa tana miƙewa tana goge hawayen idanunta

"Allah sarki,dama sai da ya zo raina,don na tuna yadda kike bamu labarin ya shaƙu da mum, Allah ya yi mata rahama ya baku dangana gaba ɗaya "Beely ta amsa da Ameen, sannan suka miƙe suka nufi gate,inda Salis ke jiran su

Su Beely da samha manya🫢

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

✍️ Nusy bee
*Young talented writers association (YOTA)*

Page 81


Tun daga nesa Dr Salis ya zuba musu idanu ya na kallon su har suka ƙaraso suna ta ƴan hirarrakin su,suna ƙarasowa ta rissina ta gaishe shi,ya amsa tare da yi mata gaisuwa ya na son haɗa idanu da ita,amma ta yi ƙasa da kanta sannan ta amsa, Samha ta ce"bari na baku waje"bata jira amsar su ba ta ja hannayen Ajmal da Yusaira suka koma cikin gidan

"Bilkisu!ayi min afuwa Please,da laifin da na yi,da Wanda ban yi ba,da ina sane ko bana sane,don Allah ayi min afuwa hakanan, lokaci ya yi da ya kamata ki bani haɗin kai mu gyara tsakaninmu,hatta Samha a wannan karon ta bani cikakken goyon baya don na mayar dake ɗakinki,amma me kika ce?"

"Samha Hussain aminiyata ce tun muna secondary, tafiya ta turkey inda na karatun tertiary institution tsawon shekaru shida bai sauya komai na amintarmu ba,tsawon wannan lokacin ni da ita kowa hanyar da zai farantawa kowa yakeyi,amma unfortunately sai gashi na zamo abinda Aminiyata ta tsana,wato kishiya a gare ta

Wancan karon da na aure ka don ban san kai ne mijin aminiyata ba,a lokacin da na sani kuma babu abinda zan iya,daga baya kuma son zuciya ya rufe min idanu ya kai ni ga ɓacin zuciya,a yanzu kuwa na farka daga baccin da na yi,ba zan iya auren mijin ƙawa ta ba ina sani,ko da babu ƙawancenmu na yarda a karo na ƙarshe na sadaukar mata da abinda dama can nata ne, Allah yayi zan aure ka na haifi Yusaira,to Allah ya sa mata albarka"kallon ta kawai yake yi,don a fakaice sai goge hawaye take yi, kuma har yanzu taƙi yarda su haɗa idanu,cikin kwantar da murya ya fara magana

"Aure ibada ne Bilkisu, tun farko dalilin da ya sa aka yi ta samun matsala kenan, Saboda bamu ɗauke shi ibada ɗin ba,da ni da ke da samhan baki ɗaya,amma yanzu in sha Allah na san baza'a samu matsala kamar baya ba,ki yi haquri ki koma ɗakin ki,komai ya wuce Please "

Shiru tayi bata sake magana ba,sai ɗan murmushi kawai da ta yi,ya ce"kiyi min magana da Samha zamu wuce gida,ga wannan"ya miƙa mata abu a leda,ya ce"ki bawa yarinya ta da ban sauke kowanne haƙƙi akan ta ba a matsayi na na uba"Beely ta yi ɗan murmushi ta karɓa ta yi masa godiya, ta yi masa sallama ta shiga cikin gidan

Bayan kwana biyu aka sallami Azad daga asibiti,ya rame sosai ya yi fari kamar mara jini a jiki,a ranar Hisham da su Nabeela suka koma Kaduna

Ita ma inna sabuwa har ɗaki ta je ta ga jikin nashi ta yi masa sannu,ya amsa ya na mamakin halin wannan tsohuwa,har da zama ta na yi masa hira ta na ɓare masa gyaɗa marau da yake kyautata zaton da abar ta ta zo,shi dai babu bakin tambaya,sai ta miƙa masa ya amsa ya ci,duk da ba daɗin ta yake ji ba

Ita ma washegari ta tattara ya nata ya nata ta koma albasu,kafin cikar kwana goma da rasuwar dai gidan ya koma sai ƴan gidan kawai,sai kuma khairi,da yanzu ta dawo nan ɗin da zama ita da ɗanta, Feena ma tuni ta koma gidanta

Azad ya na zaune a part din shi,waya ya gama amsawa daga Melbourne inda abokan aikinsa ke cigaba da yi masa ta'aziyya, sallamar Beely ta ratsa dodon kunnenshi

Ɗaga kai ya yi ya na kallonta,hijabi ta sanya dogo har ƙasa kalar baby pink,ya yiwa farar fuskarta kyau sosai,ta ƙaraso ta samu waje ta zauna ta na faɗin

"Good evening big bruh"

"Evening Bilkisu,ya yaran?"

Ta ce"alhamdulillahi ya jikin?"Azad ya ce"mun gode Allah, I hope all is well"

Yatsina fuska ta yi ta ce"so nake ka roƙar min Daddy please,Ina son komawa makaranta na yi PhD na Please,kuma idan na gama ina son wannan karon Daddy ya barni nima na yi aiki Please"

Kallonta kawai yake yi har ta gama magana, sannan ya ce "Bilkisu yanzu kina jin daɗin zaman da kike yi a gidan nan?"

Da confused face ta kalle shi ta ce"I can't get you bruh!"

"Bilkisu instead of komawa makaranta da kike magana da aiki why not ki koma ɗakin mijinki?ko kin ɗauka daddy ya na jin daɗin ganinki a haka?"

Hawaye ya ciko idanunta,ta ce"yaya Allah bai kawo min bane,nima ai zan so na yi auren na zauna a ɗaki na,amma ba zan iya komawa gidan mijina na baya ba,babu komai a cikin cin amana sai taɓewa da da na sani"

Ɗan murmushi Azad ya yi ya ce"ita ƙawar taki da kike magana ita ce ta fara roƙo na akan na yi miki magana ki koma ɗakinki,da farko nima sharewa na yi,amma da mijin naki ya zo sai na ga ya dace ki koma Bilkisu,zaman ki hakan ba mai yiyuwa ba ne, babu daɗi ace Feena ta na ɗakin mijinta,da ta zo a rasuwar nan kowa maganar ta yake yi,amma ke kin guji aure,kin saka an zagi mum ta na raye,don Allah ki bar ta ta kwanta a kabarinta lafiya"kuka ya kufce mata da ƙarfi,ta faɗa jikin shi ta na kuka sosai,shima take zuciyar shi ta karye,ya fashe da kuka sosai,sai gashi ita ce take lallashin shi,don kukan da bai yi a baya ba ne yake yi yanzu,sai da nauyin zuciyar shi ya ragu sannan ya ce"tashi ki je Bilkisu,don Allah kar ki watsar da maganata"

"Yaya kenan mum fushi take yi dani ko?"ta tambaya muryarta rawa

"Ba haka bane,don mum da bakinta ta ce ta yafewa kowa a cikin yaran ta,itama su yafe mata"Beely ta yi shiru,kafin ta miƙe cikin sanyin jiki ta koma part ɗin mum

Kwana uku da faruwar hakan Khairi ta samu Azad a parlour,cikin damuwa take faɗin "yaya Azad me ya samu yaya Hisham ne?idan nabyi masa magana baya yi min reply, idan na kira ba ya ɗaga min waya"kallon ta ya yi a nutse sannan ya ce"zauna mu yi wata magana little sister"babu musu ta zauna

Ya fuskance ta sosai ya ce"a da ban so na sanar da ke ba saboda wasu dalilai,kamar na exam ɗin ki da sauran matsaloli,amma ko don inna sabuwa dole na sanar dake

Khairi kin tuna ranar da muka je gidan ku na Kaduna?da ni,da Auwab da Sulaiman?har muka taho da ke?"gyaɗa kai tayi ba tare da ta yi magana ba,ya ce"yauwa, to tun a lokacin aka mayar da auren ki Auwab,ni na karɓi auren naki a wancan lokacin,kuma har yanzu sadakinki ya na hannu na, mahaifiyarki ce ta bayar da shawarar hakan,shima Hisham ɗin ya bada goyon bayan hakan,idan kin tuna a ranar mum ta yi miki maganar ki aure ni na ce kin yi min nisa,irin nisan da nake nufi kenan

Babu wanda ya dace da auren ki kamar Auwab Khairi,yadda kika wahala a rayuwa shima ya sha wahala,ya na matuƙar son ki,ya na ƙaunar ki, da ni da Dr Hisham mun duba abubuwa masu yawa da suka tabbatar da cancantar Auwab ya koma a matsayin mijin ki kafin mu yanke shawarar mayar masa da ke,in sha Allah baza kiyi nadamar hakan ba, mahaifiyarki, mahaifiyarshi da mahaifanmu maza duka sun yi amanna da batun,amma kiyi haƙuri idan mun yi miki ba daidai ba"

Shiru ta yi bata ce uffan ba,sai da yace"idan kina da magana feel free "ta girgiza kai kawai,ta miƙe ta wuce cikin gida,ya bita da kallo

Tana shiga ɗakinta ta zube a ƙasa ta na fashewa da kuka,irin azabar da ta sha a gidan Auwab kawai take hangowa, tsoron karo da matarshi kawai take yi, don ita fa har yanzu bata san Auwab ba ya tare da Inaaya ba

Anan ɗakin ta zauna ta na saƙa da warwara,bayan azahar ta faki idanun mutane ta zuba kayanta da na ɗan ta a Boot ɗin motar ta,wadda tuntuni Auwab ya kawo mata,a ranar ma babu kalar masifar da bata yi masa ba don ya taɓa mata mota,kuma ta amshe key ɗin ta

A hankali ta saci jiki ta ɗauki ɗanta suka fice,ta shige mota ta tayar ta bar gidan, zuciyar ta cike da baƙin ciki,a ganinta kawai an yi taron dangi ne har da mahaifiyarta an aura mata mutumin da bai dace da rayuwar ta ba

Babu inda tayi wa kanta masauki sai garin albasu,ranar ma kuwa anyi sa'a Nadiya ta zo kwana mijinta baya nan

Ai kuwa sun sha farin cikin ganin juna sosai, Nadiya da kanta ta dafa mata alala da ta san ta na matuƙar so,sai da ta ci ta ƙoshi sannan suka zagaya ɗakunan kakarta da matan kawunnan ta suka gaisa,mutanen gidan sai mamakin ganin yadda ta chanja suke yi

A ɗakin inna talatu suka kwana,sai da suka suka kusan raba dare sannan suka kwanta

A can gida kuwa, Nusra ce ta fara ankara babu Khairi, don ta duba ta kaf part ɗin mum bata nan,ta duba na aunty Naja,har ma na yaya Azad da na su Haidar,ganin haka ta sanar wa Beely

Wasa wasa suka yi ta neman ta har a waya,amma a kashe, hankalin su ya tashi sosai, Azad ba ya raba ɗayan biyu cewa maganar da ya yi mata ce ta sa ta ta gudu,don wannan karon tabbas guduwa ta yi,don ta kwashe kayan da za ta buƙata,sannan ta ɗauke ɗanta,ya kira Auwab da Sulaiman ya sanar musu

A ranar suka zo, Nusra sai kuka take yi, Azad ya yi musu bayanin komai, Sulaiman ya yi dariya ya ce"gobe mu shirya muje albasu,don bana raba ɗayan biyu can ta tafi"da mamaki suka kalle shi, Sulaiman yace"har yanzu Khairi yarinya ce ƙarama, tunanin yara ne da ita,ita yanzu gani take dukkan mu mun yi mata laifi,daga mu har mahaifiyarta, shiyasa ta koma inda babu wanda ya yi mata laifi,wato albasu "

Gaba ɗaya maganar ta saka su dariya, Beely ta ce"gaskiya Khairi akwai shirme, Allah ya sa can ta tafi ɗin"suka amsa da ameen, Haidar ya ce"Khairi tana da zuciya gaskiya,akwai saurin fushi, ni Allah ya sa ma bata ƙullace ni ba abubuwan da na yi mata a baya "Auwab ya ce"bata ƙullace ka ba,da ta ƙullace ka da tabbas sai ta rama"Azad ya kalle shi ya ce"ka uzzurawa baiwar Allan nan, ka cika damun ta da tsokanar ta"Auwab ya yi dariya ya ce"baza ka gane wannan ƙanwar taka bane,ta cika tsiwa da rashin kunya,ga masifar babu gaira babu dalili,tun a Massachusetts ta ɗana min halin sosai,ba don wasu dalilai ba ni na san babu wanda ya isa ya saki Khairi ya ce ya daki banza"haka suka yi ta tsokanar juna suna dariya

Washegari suka ɗau hanya zuwa albasu,zuciyoyin su cike da fatan dacewa,suna tafiya a mota suna hira,amma Auwab ya yi shiru kamar ba ya motar

Ai kuwa sun yi ƙatuwar Sa'a,suna zuwa suka hango motar ta a bakin gidan, Auwab kamar ya yi me don farin ciki,don nunawa ne kawai bai yi ba,amma cikin zullumi ya kwana jiya

Khairi kam washegari sakawa ta yi a gyara mata ɗakinta,aka liƙe ramukan dakin, aka yi plaster,ta saka aka siyo mata kayayyakin da zata yi amfani dasu,don ita ta saka a ranta ta dawo albasu kenan da zama tunda babu mai son farin cikin ta,har Mamie ɗinta

Tana zaune suna hira da aminiyar ta Nadiya ta na gyarawa yar Nadiyan gashi sai ga sallamar su Auwab,sai da gaban ta ya faɗi,amma ta yi fuska,tana jin mutanen gidan suna gaisawa da su Auwab da zata ce bata taɓa ganin shi a garin ba ma,amma ko ɗaga kai ta kalle su ba ta yi ba

Sulaiman ne ya zo ya zauna kusa da ita ya ce"ayi mana afuwa matar babban yaya,mun tuba,sannan kuma mun zo biko"murmushin yaƙe kawai ta yi bata yi magana ba, ballantana ta gaida wani a cikin su

Shiga suka yi suka gaida mutanen gidan,da yawan su suna ƙarawa da yiwa Azad gaisuwa

Ba su tashi sanin rigimar Khairi ba sai da suka tashi tafiya,juyin duniya ta ce babu inda zata je,Auwab ya nemi waje ya zauna ya kalle su ya ce"ku tafi kawai,duk lokacin da ta huce sai mu dawo gida"

Tsananin mamaki ya kama su,suka kama kallon juna,hatta da khairin sai da abin ya bata mamaki,wai Auwab zai kwana a albasu,mutumin da sau ɗaya ya taɓa zuwa, lokacin rasuwar mahaifinta,kuma shima a lokacin bai kwana a garin ba,amma yau saboda khairi ya zaɓi zaman garin gaba ɗaya

Azad ne ya fara faɗin "Auwab think twice, kar ka yi abinda zaka zo kana regretting,nan albasu ce ba Massachusetts, Boston ko Texas ba"

Auwab ya girgiza kai yace "na ce ku tafi, I will never regret being with my wife,in sha Allah"sun tausaya masa sosai,ita dai Khairi ko a jikin ta, suka yi musu sallama suka tafi

Saleh babban ɗan baban Jamila shine ya rinƙa jan Auwab ɗin a jiki,ya ja shi suka shiga garin yawo,kuma sai gashi garin ya burge Auwab sosai

Da daddare Saleh har ƙofar ɗakin khairi da aka gyara ya raka Auwab, Auwab ya yi masa godiya ya shiga ɗakin ya na kallon Khairi da ta kunna fitilar wayarta ta na shimfiɗa sabon zanin gado akan Sabuwar katifarta,ya samu waje ya zauna ya na faɗin "sannu da aiki Madam"

Ta yi masa banza,bai damu ba ya zauna ya na kallonta ta na gama shimfiɗa wa ta ɗauki Ajmal dake gefe ya na ta bacci ta ɗora shi akan katifar,ita ma ta hau ta yi kwanciyar ta

Ta na jin Auwab zai kwanta shima sai ta karkace yadda ba zai samu waje ba,ganin haka ya ce"to Nima a bani inda zan kwanta Please"ta yi masa banza,sai ma ta ɗauke wayar ta ta kashe fitila,ganin haka ya kunna tashi wayar ya haska ya ɗauko darduma ya shimfiɗa ya kwanta,ya na jin ta ta na ta masifar ya ɗaga mata darduma amma ya yi mata banza

Khairi daru Khairi rigima 😅😅

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

✍️ Nusy bee
*Young talented writers association (YOTA)*

Page 82

A ranar bai iya bacci cikin daɗin rai ba saboda bai saba da bacci irin haka ba,ita kuwa khairi bacci ta sha ta godewa Allah,sau biyu ya na farkawa ya na haska fuskar ta,a ranshi ya na faɗin"sleeping beauty"

A karo na uku kam zama ya yi ya na kallonta,wani moment da suka yi spending tare ne a Boston yake dawowa kanshi,ya yi ɗan murmushi tuna lokacin da take masa rigimar ya mayar da ita wajen Daddy,ya tuna lokacin da take yi masa tsiwa akan layi da lokacin da ya kaita asibiti,ya tuna lokacin da suka zama abu ɗaya, lokacin da take son koya masa rawa,sai da ƴar dariya ta kubce masa,ya na cikin tunane tunane ya ji kiran sallar farko na asuba,ya duba agogo,ƙarfe huɗu da mintuna biyu,ya miƙe ya ɗauki pure water ɗaya a cikin waɗanda khairi ta siyo jiya,ya fice daga ɗakin ya nufi tsakar gida

Ganin duhu ya sa ya kunna fitilar wayar shi ya ajiye ya na alwala ya na ƙarewa tsakar gidan kallo ya na jinjina buwayar Allah,mutane ne suke rayuwa a nan,kuma cikin farin ciki da walwala, wataƙila ma suna farin ciki fiye da waɗanda suke rayuwa a irin gidajensu

Bayan ya idar da alwalar ɗaki ya koma ya tayar da Sallah akan dardumar da ya kwanta ya yi bacci,bayan ya yi Sallah raka'a biyu ya zauna ya na ta istigfari,sosai yaji nutsuwa a ranshi,kafin lokacin sallar asuba ya shiga,aka yi kiran sallah na biyu,wanda ya tashi Khairi

Sau ɗaya ta kalle shi ta ɗauke kai,a ranta ta na mamakin ganin shi ya na sallar dare,don shi kam banda sallar farilla bai damu da dukkan wata ibada ba, bata san Auwab ɗin baya ba irin na yanzu bane,tunda ya zo masa a bayyane cewa Inaaya sihiri ta yi masa ta raba shi da komai nashi ya sa ya dage ya koma ga Allah,ya daina wasa da ibada,ya daina wasa da azkar

Tare suka fita Masallaci da Saleh,ita kuma Khairi ta tayar da tata sallar akan dardumar da ya tashi akai,ta na idarwa ta yi azkar ɗinta ta kwanta akan dardumar,har bacci ya ɗauke ta

Shima Auwab bayan ya dawo gida bacci ya ji a idanunshi sosai, saboda jiyan bai samu wani bacci ba,amma ganin Khairi akan dardumar da ya kwanta ya sa ya haye katifarta ya kwanta a gefe,ko da za ta nemi ta kwanta sai ya bata waje,ba kamar yadda tayi masa ba

Har baccinshi ya fara nisa ya ji ana shurin ƙafar shi da ƙarfi,a ɗan firgice ya farka ya na kallon Khairi dake tsaye akan shi ta na girgiza,bai ce mata uffan ba ya zauna ya na kallon ta ya na sauraren ta

"Sauko min daga kan katifa"abinda ta ce kenan a tsiwace

Babu musu ya sauko,ya kalle ta ya ce"ina dardumar?"ta ce"ka shimfiɗa taka,wannan tawa ce"ta koma ta yi kwanciyar ta

Ta na ji ya ce"to shikenan"ya yi kwanciyar shi kan simintin ɗakin,da yake bacci ne akan shi tuni ya fara fizgar shi

Khairi ta tashi zaune ta na kallon shi,sai kuma ta ji ya bata tausayi,idan zata yi masa adalci duk wahalar da ta sha a gidan shi bai taɓa hana ta wajen kwana mai kyau ba,don haka a fusace ta ce"ka tashi to ga dardumar"tuni bacci yayi awon gaba dashi ma bai san tana yi ba,ta kuwa sanya ƙafa ta fara zungurin ƙafarshi da ƙarfi,ya buɗe idanun shi a hankali,ya zauna ya na runtse idanun shi jin yadda kan shi yake sara masa,bata damu ba ta ce"ga dardumar ka kwanta a kai"

Buɗe idanunshi ya yi, waɗanda suka kaɗa suka yi ja saboda suna buƙatar bacci,ya kalle ta yace"Ummul khairi jiya ban yi bacci ba,don Allah ki bar ni na yi bacci kinji,na roƙe ki don Allah,ko don Ajmal ɗin mu"

Shiru ta yi bata ce komai ba,ganin ya na ƙoƙarin komawa ya kwanta a ƙasa sai ta yi azamar cewa"to ka kwanta kan katifar,kusa da Ajmal"bai yi mata musu ba ya koma kan katifar,ita kuma ta yi kwanciyar ta kan dardumar da ta ɗauko don ta ba shi

Ba shi ya farka ba sai wajen karfe tara da rabi na safe,bai yi mamakin irin baccin da ya sha ba kasancewar jiya da dare ya san bai yi bacci ba,ya kalli inda Ajmal ke kwance,wayam baya nan,ya miƙe a hankali ya leƙa waje,mutanen gidan kowa harkar shi yake yi,iya leƙe-leƙen shi bai hango Khairi ba ballantana Ajmal,gashi so yake ya shiga banɗaki ya yi wanka,amma baya jin ma zai iya amfani da banɗakinsu

Zuwa can ya ga ta shigo ita da wata da bai san wacece ba,sai hira suke yi suna dariya,zogale ne da yawa a hannun su,da alama ɗebowa sukayi,waccan matashiyar ta janyo tabarma ta shimfiɗa,suka zube zogalen, Khairi ta sauke Ajmal da ta goya ta rungumo shi ta nufo ɗakinta

Da sallama ta shiga ɗakin ta na sake ɗaure fuska,bai damu ba ya ce"good morning Khair!"

Banza ta yi masa, bai yi zuciya ba ya ce"Please wanka nake so na yi,Ina son banɗaki"

Nan ma bata kula shi ba,ta janyo kokon da ta kawo tun ɗazu ta fara ƙoƙarin saka sugar da ta siyo,ta ɗiba a ɗan cup, ragowar ta ɗauka ta dangwarar a gaban Auwab

Bin ta yayi da kallo yadda take bawa Ajmal,ta na yi masa wasa ta na murmushi,ya jingina kan shi da bango ya na kallonta,har ta gama ta gyarawa Ajmal ɗin baki ta sake ɗaukar shi ta goya ta fice daga ɗakin bata ko kalle shi ba

Bin ta ya yi da kallo gwiwar shi ta na sagewa,zuwa yanzu ya fara yarda khairi bata son shi,shima jikin shi a mace ya miƙe ya fice daga ɗakin

Allah ya taimake shi ya na fita suka haɗu da Saleh,suka gaisa, Saleh ya ja shi zuwa part ɗin shi da ya gina a cikin gidan,amma daga can gefe,gini yayi kamar na birni, kasancewar shi ɗan boko shima,sai dai har yanzu bai yi aure ba tukunna,amma anan yake kwana,anan Auwab ɗin ya yi wanka,Saleh ya bashi wasu sababbin kayan shi masu kyau,ya saka,ya kawo masa breakfast,amma sai ya ji bazai iya ci alhalin matar shi da ɗanshi basu ci ba

Don haka ya cewa Saleh ya gode,ya karya, Saleh bai matsa masa ba,ya yi masa godiya ya koma ɗakin Khairi

Yini guda ya na zaune,sai dai ya danna wayar shi,gashi tunda ta dungura masa kokon bata sake kawo masa komai ba,asalima bai sake ganin ta a gidan ba sai bayan maghriba

A kaikaice ta kalle shi bayan ta kunna fitilar wayar ta,gaba ɗaya ya yi zuru zuru,amma ya yi fuska saboda ƙarfin hali,wayar shi ma yake dannawa

Bata ce masa uffan ba,ta fita ta tafi wajen baba hari ta karɓo masa shinkafa da miya,girkin yayi kyau sosai,kuma don neman waje baba hari ta zuba a wani food warmer ɗinta mai kyau,ta ɗora warmers ɗin akan wani tray na silver,ta na zuwa ta dangwarar masa da kwanukan,ta juya ta yi ficewar ta

Hanyar da ta bi ya bi da kallo,kafin ya cigaba da abinda yake yi,ya na jin yunwa tabbas,amma a yanzu wannan shariyar da take yi masa tafi damun shi,bata dawo ɗakin ba sai bayan sallar isha'i, lokacin ya lallaɓa ya tafi masallaci,bai dawo ba har ta shigo ta samu ko taɓa warmers ɗin bai yi ba

Ta ɗan razana,amma sai ta dake,tayi wa Ajmal wanka,bayan ya ci abinci ta goya shi

Tana ta faman zagaye da Ajmal ɗin a bayanta ya shigo,ya sake neman waje ya zauna,ta dube shi ta ce "na baka koko ɗazu,shine ka wulaƙanta min kaƙi sha,yanzu ma na kawo maka abinci kaƙi ci,me kake nufi?"ta ƙarashe da ƴar tsawa

"Ba zan ci ba!"ya bata amsa ya na kwanciya akan dardumar da ya san yau ma akan ta zai kwana

"Malam ka tashi ka ci abinci!baza ka zo ka lanjare min idan wani abu ya same ka ba!,ji tun yanzu ma duk ka yi laushi"maganar sai ta bashi dariya ma,ya yi ɗan murmushi sannan ya tashi zaune,ya kalle ta ya ce"to kawo min ruwan zafi,kin ga tun safe ban saka komai a bakina ba"ya na kallo sai da ta galla masa harara sannan ta fice daga ɗakin,ya yi ɗan murmushi ya koma ya kwanta

Da kamar mintuna goma sai ga ta da ruwan lipton a jug,sai madara da milo na sachet,ta haɗa masa tea ta miƙa masa,ya amsa ya na faɗin "thanks alkhairi na!"da murmushi a fuskar shi

"I warned you times without number ka daina gaya min wannan sunan amma kaƙi ko?"ya na sipping tea ɗin a hankali ya yi murmushi ya ce

"Ke alkhairi na ce Ummul khair!a sanadiyyar ki na san daɗin aure,a sanadin ki na samu ɗan da nake alfahari da shi,a sanadin ki....."sai kuma ya yi ƴar dariya ganin irin kallon da khairin take jefa masa,kafin ta buga ƙwafa ta miƙe a fusace ta fice daga ɗakin,ta na jin ya raina mata hankali ma,wai bai san daɗin aure ba sai a kanta,wato yaudarar da ya yi mata a baya ita yake tunanin maimaita mata a yanzu?shi bai san wannan khairin ba wadda ta rayu a gidanshi kusan shekaru uku baya bane?ta ja tsaki cike da baƙin ciki ta na goge ƙwallar da ta kawo idanunta ta wuce inda aka saba zaman hira a gidan,ta shige cikin su suka cigaba da hira

Bata koma ɗaki ba sai wajen sha ɗaya na dare,a kwance ta ga Auwab,ta ɗan kalli sashenshi,bai ji daɗin kwanciyar ba saboda babu pillow,ta ɗauki pillow ɗin ta ɗaya ta zagaya inda kanshi yake a hankali ta ɗaga ta ɗora akan pillow,ga mamakinta sai ta ga ya saka hannu ya ture pillow ɗin ya ce"ki bar ni,idan ina buƙata zan ɗauka"

Haushi da takaici da kunya suka tirniƙe ta,cikin masifa ta ce"ai dama ba'a yi maka gwaninta,ai sai ka yi ta yin yadda kake so ɗin,idan wani abu ya same ka wa ya damu?"

Ya ɗaga idanu ya na kallonta ya ce"ke mana,na tabbatar sai kin damu "

Da hargagi ta ce"saboda kai?kai dai zan damu?a matsayin ka na wa?"

" A matsayi na na mijinki,yayanki,kuma uban ɗanki da upcoming ƴaƴanki in sha Allah "

Ta ja wani dogon tsaki ta ce"ashe zaka dawwama a garin nan indai wannan ne mafarkinka"

"Babu matsala,nan ɗin ma ai gida ne,in dai ina tare da alkhairina everything is fine"ta yi masa Banza ta yi kwanciyarta

A ranar ma bai iya bacci ba,ganin juye juyen ba zai masa ba ya miƙe ya fito tsakar gidan ya samu waje ya zauna ya na chatting da mr Johnson Philip

"A'a! engineer ya dai?"ya ji Muryar Saleh

Da murmushi ya kalli Saleh ya na faɗin "ka shigo?You are welcome"ya bashi hannu suka yi musabaha

Da tsokana Saleh yace"hala Madam ce ta koro ka nan ka zo ka zauna cikin sauro?"Auwab ya yi ɗan murmushi kawai, Saleh yace"na san rigimar ummiyo ai,za ta aikata abinda ya fi haka"Auwab yace "gashi nan ta zaunar damu a garin nan, ta ƙi yarda mu tafi"Saleh ya ce"wai dama wannan zaman ba na daɗi bane kuke yi? I thought Hutu kuka zo"

Auwab ya yi ɗan murmushi kawai, Saleh ya ja hannunshi suka nufi sashenshi,suna shiga ya kunna solar ɗin ɗakin, Auwab ya zauna ya na ƙarewa ɗakin kallo,a ranshi yana jin inama shi da alkhairin shi ne a ɗakin

Saleh ya zauna a gefen shi,cikin kwantar da murya ya ce "saɓani kuka samu da ita ne?kar ka damu ka gaya min,in Sha Allah zan samo maka mafita,bai kamata ka cigaba da biye mata ta na ta zuba shirme ba


Har zan ce Saleh munafiki ne sai kuma na yi tunani na fasa😆


#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

✍️Nusy bee

Page 83

Cikin sanyin murya Auwab ya ce"ba saɓani muka samu ba, matsala aka samu tun daga farko"a nutse ya warware masa komai tun daga aurenshi da Khairin,yadda al'amura suka rincaɓe har zuwa yanzu,ya ƙara da faɗin "ni yanzu babu abinda ke ɗaga min hankali sai tabbacin da na samu cewar Khairi bata so na,dama can na yaudari kaina da na yi tunanin za ta so ni ne, maybe don yarinya ce a lokacin, whatever, abubuwa sun yi min yawa wallahi "ya ƙarasa faɗa ya na dafe kanshi

Tausayin su gaba ɗaya ya kama Saleh,ya dafa kafaɗarshi ya na faɗin"kar ka damu engineer,matarka ta na sonka,kuma ni a yadda na fahimce ta ba wai haushin abinda aka yi mata ke damun ta ba,kishi ne,ko ka gaya mata kun rabu da matar ka?"ɗan shiru ya yi,kafin ya girgiza kai ya ce"gaskiya a'a,amma wataƙila ta ji a wajen mutane"Saleh ya ce"to kai ya kamata ka sanar mata,amma kafin nan ya kamata ka samu tabbacin soyayyar da take yi maka"daga nan ya yi ta bashi shawarwari, waɗanda suka farantawa Auwab ɗin,kuma suka kwantar masa da hankali

Ranar a ɗakin Saleh ya kwana bayan sun gama hirarrakin su da shawarwarin su kan yadda za su ɓullowa lamarin Khairi,tunda Auwab ya zo albasu yau ne ranar farko da ya kwana babu alamun damuwa a ranshi

Washegari ma anan ya yi wanka ya shirya da wasu sababbin kayan Saleh ɗin,yau kam da Saleh ya buƙaci ya karya kai tsaye ya shaida masa ba zai iya cin abinda Khairi bata ci ba,Saleh ya yi ta dariya ya na tsokanar shi da miji na gari, sannan ya ɗaukar masa kayan kalacin da ya siya masa zuwa ɗakin Khairi

Ita kuwa Khairi tunda ta tashi sallar asuba ta yi jugum ganin bata ga Auwab ba,ɗan baccin da take komawa bayan sallar asuba yau bai zo ba ma,haka ta yi zaune ta rafka tagumi har wajen ƙarfe takwas na safe, lokacin da ta ji sallamar Auwab

Zumbur ta mike ta na rarraba idanu,suna haɗa idanu ta sakar masa harara ta ce"daga ina kake?"

Murmushi ya yi,kafin ya ce komai Saleh ya shigo da sallama,ta amsa ta na gaishe shi,ya amsa ya na murmushi, ya ce "ayi mana afuwa,nine na janye shi,amma yanzu ga abin ki na dawo miki dashi,sai dai anjuma zai raka ni unguwa Please"Khairi ta yi ɗan murmushi,kunya ta kama ta,da gaske hankalinta ya tashi saboda rashin ganin Auwab, bata yi tsammanin za ta damu da rashin ganin shi har haka ba, Saleh ya dire musu ledar bread da ƙwai da ya siyowa Auwab, Auwab ya dire jug ɗin Black tea da ledar kayan shayin ya na kallon fuskarta, Saleh dai tuni ya fice daga ɗakin ya na faɗin "engineer kar ka manta fa zamu fita"

Mayar da hankalin shi ya yi kanta sosai,murya ƙasa ƙasa ya ce"good morning ummu Ajmal!"

Jikinta ya yi sanyi jin sunan da ya kira ta da shi, ba ta amsa ba ta fara haɗa masa tea ɗin,kafin ta haɗawa kanta sai da ta fara zubawa Ajmal sugar a koko,don wani abin Allah ya na shan koko sosai,shi zuwan shi garin ma har ƙiba ya ƙara saboda ya na jin daɗin cimar garin, saɓanin iyayen nashi da suka rame, saboda rashin mayar da hankali ga abinci,da kuma damuwa da ke ɗawainiya da su

Karo na farko kenan da suka zauna suka ci abinci tare tun zaman su a Boston,sun yi shiru kowa da tunanin da yake yi,suna satar kallon juna lokaci lokaci,idan sun haɗa idanu kowa sai ya basar,ganin bawa Ajmal koko zai hana ta karyawa ya sa ya karɓi bashi kokon,bata ja ba ta sakar masa

Bayan kamar rabin awa ya miƙe ya na faɗin "Khairi na zan fita"ta yi masa banza,ya yi murmushi ya ce "kin san mutuwa ake yi fa,kika sani ko ba zan dawo ba?"

Sai ta ji gabanta ya faɗi,ya yi ɗan murmushi ya na kallon yadda reaction ɗin ta ya chanja,a hankali ta ɗago ta kalle shi,sai dai bata yi magana ba ta cigaba da tattare inda suka ci abincin

Murmushi ya yi ya juya ya tafi,duk taurin kan ta da ɗauke kai ya karanci ta damu dashi ko da babu yawa,shi hakan ma ya ishe shi

A ranar dai Khairi maganganun Auwab sun kashe mata jiki sosai, gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi sosai,duk ayyukan da take yi ta yi sukuku

Da azahar bayan ta idar da Sallah ta na zaune ta fara jin tashin magana a tsakar gida

Zumbur ta yi ta miƙe jin ana ambaton kar a gayawa ummiyo,mijin ta ne,babu wanda ya san ta fito daga ɗakin ta,ta tsaya ta na kallon kowa,suna ganinta suka yi shiru,har da masu sunkuyar da kai,cikin tashin hankali da firgici da bata san ta shiga ba ta ce"me ya samu yayan?ya na ina?"

Shiru babu wanda ya bata amsa,cikin tsananin tashin hankali ta janyo Safara'u ƙanwar lubabatu ta ce"Safara'u kiyi wa Allah ki gaya min,me ya samu mijin nawa?don girman Allah,don Allah ko gaya min"

Cikin tausayawa ta ce"sun je gewayar gonar yaya Saleh ne maciji ya sare shi!"

Bata san ta yi zaman ƴan bori a tsakar gidan ba,hannun ta akai ta na faɗin"inna lillahi wa inna ilayhi rajiun!hasbunallahu wa ni'imal wakeel!!ya Allah ka taimake ni kar miji na ya mutu ya bar ni! wayyo abban Ajmal!!!"sai kuma ta yi zumbur ta miƙe ta na faɗin"don Allah ku taimaka ku gaya min ya na ina yanzu?don Allah!"baba Atine ce ta dube ta cikin tausayawa ta ce"an ce an kai shi Wajen magaji mai magani,ki yi haƙuri har su dawo"wani irin kuka ya ƙwace mata ta ce"don Allah baba ku barni naje wajen shi,ba zan iya jure zama ba bana son yaya ya mutu"

Inna talatu ce ta ce"a'a ummiyo,kema fa kin san mata ba sa zuwa wajen magaji mai magani,ki dai yi haƙuri ki bari a kawo shi,ki kwantar da hankalin ki in sha Allahu amma ba zai yiwu ko je ba kema kin san tsarin Magaji"Khairi bata sake magana ba ta koma gefe ta zauna ta na goge hawaye,sai addu'a take Allah ya kuɓutar mata da mijin ta a cikin ranta

Bata tashi daga wajen ba sai da aka kira la'asar,ta kasa cin abincin rana, Ajmal ma tuni Nadiya ta ɗauke shi ta tafi dashi gidanta ganin halin da khairin take ciki bayan ta bata baki da bata ƙwarin gwiwa

Har maghriba shiru, isha'i shiru,babu Auwab babu dalilin shi,hatta da Saleh da wani yayansu Auwal da aka tabbatar musu suna wajen Auwab ɗin babu wanda ya dawo gida,zuwa lokacin Khairi ta fice daga hayyacinta saboda tsabar tashin hankali da fargaba,ta kwanta akan dardumar da ta yi Sallah hawaye suna mata zarya,zuwa yanzu gaba ɗaya ta rasa hope,ji take yi ma ta rasa Auwab ɗin ta kawai

Tashi ta yi zaune ta jingina kanta da bango ta na shashsheƙar kuka,babu abinda ya dawo mata kanta sai ɗazu da safe da zai fita, maganar da ya yi mata akan mutuwa,take kukan ta ya ƙaru,a fili ta fara faɗin "don Allah yaya ka dawo,kar ka tafi ka bar ni,don girman Allah!"

Ji ta yi kamar ana ta jera sannu,ta ɗan saurara,sai ta ji muryar Saleh ya na faɗin "mu wuce dashi wajena,ya samu ya huta"

Da gudu ta fito daga ɗakin nata,gaba ɗaya ta firgice a yinin,garin gudu ma ƴar hular da ta sakawa kan ta ta faɗi,amma ta na zuwa gaban Auwab ta ci birki ta na kallon ƙafarshi da aka naɗe da tsumma,da alamu ita macijin ya sara

Da ƙarfi ta rungume shi ta na sake fashewa da kuka,ya ɗan bubbuga bayan ta ba tare da ya ce komai ba,Saleh ya ce"Madam sake shi ya yi wanka ya kimtsa ko?"babu musu ta sake shi,amma ta riƙe masa hannu gam,suka tafi zuwa part ɗin Saleh

Ƙarshe dai Saleh barin part ɗin ya yi tare da ƴan dubiya, don yau ɗin nan dai ya ga alamu Khairi baza ta bari ya kwana a part ɗin ba

Ita ce ta saka masa ruwan zafi,bayan ya yi wanka ta ɗauko masa kayanshi na ciki ya saka,dama ya yi Sallah ya ci abinci,ya haye gadon Saleh da yake tsaf da zanin gado sabo mai tsafta, Khairi ma ta haye kan gadon ba tare da tunanin komai ba,ta rungume shi ta baya tsam kamar za su haɗe

Auwab ya na jin ta ya na ɗan murmushi,ya lumshe idanu soyayyar matarshi ta na sake shiga ranshi ta na ratsa ko'ina na jikinshi,so yake ya tambaye ta Ajmal amma ya fasa,a ranar dai ya yi kwanan farin ciki sosai,wanda rabon da ya yi irin shi ya manta lokacin,ko ma ya ce shekarun,sau biyu ya na farkawa ya ga ta na taɓa masa ƙirji ko ta kai hannunta wajen hancin shi don jin ko ya na numfashi,a na uku dai cikin taushin murya ya ce"kar ki damu alkhairi na,ki kwanta ki yi bacci,ki daina tashin hankalin ki haka,kin ji?"babu musu ta koma ta kwanta ta na sake shigewa jikin shi,ya rungume ta sosai yana kissing goshinta

Da asuba motsin tashin ta ne ya tashe shi daga bacci,tare suka yi alwala ya ja su Sallah,suna idarwa ya koma ya kwanta,ta kwanta a jikin shi ta ƙanƙame shi, ƙasa-ƙasa ta ji ya furta"ina kika kai min yaro ne?"


Shagali🤣🤣🤣🤣

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️ Nusy bee
*Young talented writers association (YOTA)*

Page 84

Cikin sanyin murya ta ce"ya na gidan ƙawata Nadiya,ta ɗauke shi tun jiya"bai sake magana ba sai rungume ta da ya yi sosai a jikinshi

Yau da wuri suka karya saboda yadda Khairi take jin yunwa sosai,don rabonta da abinci tun shayin jiya na safe,bayan sun gama karyawar ta kalle shi ta ce"yaya ka shirya mu tafi gida,baza mu sake kwana a garin nan ba!"

Kallon ta ya yi a nutse ya ce"just like that Khairi?mu ɗan ƙara kwana biyu mana"ta maƙale kafaɗa ta ce "yau zamu tafi gaskiya,tunda ka na da ciwo sai na yi driving ɗin"ya ce "gaskiya ni babu inda zanje yau,don Saleh ya bani gona ma,so nake sai na nome amfanin gonar sai mu tafi"

Shiru ta yi ta na kallon shi idanun ta cike da hawaye,ya ɗauke kai don kar ma ta ba shi tausayi,cikin sanyin jiki ta miƙe ta fice daga ɗakin ta nufi nata,wayarta dake Flight mode tunda ta zo ta cire a flight mode,ta danna kiran layin Azad

Bugu biyu ya ɗaga yana faɗin "little sister!yau kin tuna damu kenan"

Fashewa ta yi da kuka sosai,Azad ya ce"subhanallahi!me yake faruwa ne?ina Auwab ɗin?"

"Yaya jiya maciji ne ya sare shi,na ce mu dawo gida amma ya ƙi"

Azad yace"inna lillahi wa inna ilayhi rajiun!amma an ba shi magani ko?"ta na kuka ta ce"an bashi magani,amma ya ce ba zai dawo ba,kuma har yanzu jikinshi babu ƙwari,yaya gaba ɗaya ya rame,ya yi wani iri,baya cin abinci,duk a takure yake,ko bacci baya iyawa,don Allah ka ce masa ya yarda mu koma gida,don Allah yaya"Azad ya girgiza kai kawai ya na ɗan murmushi kafin ya ce"kar ki damu, I'm on my way kin ji?ki kwantar da hankalin ki,ki daina kukan nan Please Ummul khair"

Ta goge hawayen ta ta na faɗin "to yaya na daina, Allah ya kawo ka lafiya"ya amsa da Ameen ya kashe wayar

Khairi ɗakin Saleh inda Auwab ke zaune ta koma,da sallama ta shiga ta na kallonshi,ya amsa ya na ƙare mata kallo,a hankali ya ce"Alkhairina kuka kika yi?"

Hawaye suka zubo mata ta girgiza kai kawai,ya miƙa mata hannu, bata yi musu ba ta ƙarasa wajenshi,ta faɗa jikinshi ta na kuka, bai yi mata magana ba sai bubbuga bayan ta da yake yi cikin sigar lallashi

Har wajen azahar ta na zuba idanun ganin ta inda Azad zai ɓullo,gaba ɗaya ta fara sarewa ma,yanzun ma Auwab ya yi alwala ya ja su Sallah a ɗaki, inna sabuwa da ta dawo daga tafiya da ta yi ƙauyen kusa da su ta shigo ɗakin ta na mamaki,sau ɗaya ya daga kai ya kalle ta ya ɗauke kai ya na faɗin"sannu da zuwa inna!"

"Ikon Allah!ashe dai da gaske ne,babban ɗan Usumanu ya zo ya tare nan saboda Ummiyo,kai yanzu saboda Allah ba ka ji kunya ba?ace baka zo garin nan ko na wuni ba saboda zumunci amma ka zo ka yi kwanaki ka tare a gindin mace?anya kuwa?"ko ɗaga kai ya kalle ta bai yi ba, Khairi baƙin ciki kamar ta yi me,dama ta sani ita kanta kwanakin da ta yi cikin walwala don bata nan ne,don dama tun kafin khairin ta zo ta yi tafiya,amma yanzu ko shakka bata yi sai zaman gidan ya gundure su su duka

Inna Sabuwa bata damu da yadda ya yi kamar bai ji ta ba,ta taɓe baki ta ce"to Allah ya sauwaƙe,ina ɗan nawa?ya kuka baro shi?"Auwab ya ce"lafiya lau,ya na wajen aiki"ta ce"aiki dai? gaskiya wannan abu da sake,zuwa yanzu ya kamata ya zauna ya huta ku ku kula da gidan"nan ma Auwab bai ba ta amsa ba, bambancinshi kenan da Sulaiman,ba komai yake ɗauka da zafi ba ballantana har ya kula

Inna sabuwa ta sake cewa "kuma kun dawo nan ɗin da zama ne?"Khairi da ta ƙule ta ce"yau zamu tafi"Auwab ya ɗan kalle ta, inna Sabuwa tace"a'a zaku ƙara kwanaki dai,daga zuwana sai ku ce za ku tafi?da can don munafurci ba ku tafi ba sai yau?"Auwab ya yi ƴar dariya mara sauti,muryar Sulaiman ta ratsa ɗakin ya na ƴar dariya"gaya musu dai inna,a bamu hanya zamu wuce"Khairi ta miƙe tsaye da murna,inna ta matsa ta na faɗin"a'a!Sulaimanu ku ke tafe?"Sulaiman ya shiga ya na faɗin"mune a hanya inna,mun same ku lafiya?"ta washe baki ta ce"lafiya lau Sulaimanu,kuna ina wannan yayan naka ya zo ya tare mana anan saboda shi ya fi kowa iya soyayya? salon matar tashi ma ta raina shi?"Azad ya kalle ta kawai,sai kuma ya ce"sannu inna,ina wuni"

Sheƙeƙe ta kalle shi ta watsar, Khairi ta ce a kufule"inna yaya ya na gaishe ki!"

Kallon ta ta yi ta na faɗin"to rasa kunya ɓeran tanka,na ji ai,amsawa ce ban yi niyya ba"Khairi ta fice daga ɗakin a fusace, Azad ya bita da kallo ya na ƴar dariya

Sulaiman ya ce"a'a inna,ayi haƙuri a amsawa babban yaya,tuba yake yi "ta ce"to albarkacinka na amsa masa,lafiya ƙalau,ya gidan ya iyalin kuma?"Azad ya yi mata banza, Sulaiman ya ce"kowa lafiya inna "inna ta ce"shi bashi da baki?sai kai uban ƴan shishshigi?"gum Sulaiman ya yi ya na kallon Azad,da ko niyyar ɗaga kai daga wayarshi bashi da shi ballantana a saka rai zai amsa,a hankali sulaiman ya ce"respond her please,I don't want her to create issue "

"Ta daɗe bata yi creating issue ɗin ba!bani da lokacin wani rikicinta da jan maganarta"ya amsa bai ko kalli sashen Sulaiman ba,ba iya Sulaiman ba,hatta Auwab sai da ya kalle shi da mamaki ya na jinjina halin Azad,inna sabuwa dai ta ƙare ɗiban albarkarta,har ta juya za ta fita sai ta juyo ta ce"wai ku bakwa riƙo tsaraba ne idan zaku taho?"

Zuru suka yi mata su duka ukun, Azad ya fito da kuɗin da bai san adadin su ba ya miƙe ya damƙa mata ya ce "mu kuwa muka riƙo tsaraba"ya koma ya zauna

Tuni inna sabuwa ta fara washe baki ta na faɗin"kaji ɗan albarka,irin albarka, arziƙi daga Allah, Allah ya ƙara albarka,ka ga yadda ake yi sulaimanu! Allah ya ƙara albarka da arziƙi "ta sa kai ta fice tana ta roƙon ta

Sulaiman ya kalli Auwab da yake ta dariya,ya kalli sashen da Azad yake, fuskarshi babu alamun wani expression,ya girgiza kai yace"dole ka yi min dariya ai,ka warke ne"daidai nan Khairi ta dawo ɗakin ta na cika ta na batsewa

Ɗif Auwab ya daina dariyar ya koma ya kwanta lamo, Khairi ta gaida yayyen nata cikin damuwa, suka amsa, Azad ya ce"little sister daga ke har bruh kun rame sosai kamar ba ku ba,me yake faruwa ne?"

Khairi ta fashe da kuka tac e"don Allah yaya mu bar garin nan,maciji ne ya sare shi,kuma ya ce ba zai tafi ba,wai yaya Saleh ya bashi gona sai ya yi noma"Azad ya yi shiru ya na kallonsu, Sulaiman ya ce"kar ki damu,zai tafi,ina Ajmal?"ta goge hawayen ta tace"yana gidan ƙawa ta"

Azad ya ce"ɗauko shi to"babu musu ta miƙe ta na gyara hijabin ta ta yi waje,ta na fita Auwab ya diro daga kan gadon da yake ya leƙa ta window,har ya ga ta ɓace,sannan ya ƙaraso ya basu hannu,da mamaki suke kallon shi,ya zauna sosai ya na kallonsu yace"seriously wannan ƙanwar taku ta bani wahala,sai wulaƙanta ni take yi,ga masifa,ga shariya,gashi ni ba daɗin zaman garin nan nake ji ba,amma ita kamar wadda ake sake cusa mata son garin,haba!"

Azad ya ce"you mean ƙarya kake yi kenan,babu wani maciji da ya sare ka,rainawa ƙanwata hankali kake yi kawai?"

"Nima haka take ta tayar min da hankali ai, ni ramawa kawai na yi,duk ta mayar dani wani firgitacce,ba ta kula ni,ko magana na yi mata sai ya share ni,kuma wallahi ita ma ba daɗin zaman take ji ba,amma saboda rigima......"jin muryar khairi khairi da kamar muryar wata ya sa ya koma ya kwanta lamo kamar yadda yake ɗazu,suka bi shi da kallo,kafin wani cikin su ya ce wani abu sai ga su Khairin sun shigo da sallama

Suka amsa musu, baƙuwar ta rissina ta gaida Azad da Sulaiman,tayi wa Auwab sannu, Khairi ta ce"Nadiya kenan,ƙawata kuma ƴar uwata,a hannun ta Ajmal ya kwana yau"Sulaiman ya ce"very nice,sannu Nadiya,ya gidan ya yaran?"ta ce"kowa lafiya,ya mai jiki?"ya ce "mai jiki da sauƙi,ke zo nan!"ya kira ƴar ta da bata fi shekara biyu ba,babu musu yarinyar ta tafi,ya dauki kuɗin da yayi niyyar bawa inna sabuwa,sun kai 50k ya bawa yarinyar ya ce"maza kai wa mama ta siya Miki alawa"shima Azad ya damƙa mata kuɗi, Nadiya ta yi ta godiya, khiairi ma sai murmushi take yi sosai,ta ji daɗin irin karamcin da suka yiwa Nadiya,Nadiya ta ja yarinyar ta mai suna Fatima ta yi waje, Khairi ta na yi mata godiya

Khairi ta na shirin zama Azad ya ce"Ummul khair,can we discuss outside?"babu musu ta bi shi waje,suka nufi wajen wata bishiya kai tsaye suka zauna

Ya dube ta ya ce"Ummul khair me ya chanja mana ke?me yake faruwa ne? me yasa yanzu kika daina uzuri kika daina yafiya ne?a iya sani na Ummul khairin mu ba haka take ba,so what changed you now our feature doctor?"a sanyaye ta ɗaga kai ta na kallonshi,gaba ɗaya bata gane me yake nufi ba,ya ce"kan batun mijin ki nake magana, meyasa baza ki saurare shi ba? me yasa bazaki yi masa afuwa ba?ya na ta shan wahala a dalilin ki, menene matsalar ne?"

Hawaye suka zubo mata ta ce"yaya ina tsoron komawa gidan yaya,matarshi bata da iymani bata da tausayi,za ta iya kashe ni wallahi"Azad ya girgiza kai ya na murmushi yace"baki san komai ba kenan,to listen to me"a hankali ya warware mata komai na irin halin da Inaaya ta jefa Auwab da duk wanda ya raɓe shi ma,ya ƙara da faɗin "yadda ta azabtar da Auwab da sunan soyayya ke ko rabin hakan ba tayi Miki ba,mafi girman wahalar da ta so jaza miki ita ce ɓatar dake da tayi,amma sai gashi ya zame miki alkhairi kin haɗu da mahaifiyarki,don haka don Allah Ummul khair ina roƙonki ki tausayawa Auwab,shi ɗin abin tausayi ne,ki sauko ki daina fushin nan ku gina kyakkyawar rayuwa, riƙon nan bashi da amfani"Khairi ta goge hawayen tausayin Auwab ta ce"na yi maka alƙawarin zan daidaita dashi in sha Allah,amma don Allah ka roƙe shi ya yarda mu koma gida Please"Azad ya ce"kar ki damu da wannan,zai koma,tashi mu tafi"babu musu ta mike jikin ta babu ƙwari suka koma ɗakin da Auwab da Sulaiman suke ta hirar su cikin Yaren Ammi na shuwa

Suna shigowa suka zuba mata idanu,kai tsaye wajen Auwab ta ƙarasa ta zube a gabanshi,cikin kuka take faɗin "don Allah yaya ka yafe min,ban kyauta maka ba, Please Abu Ajmal!"ɗaga kai ya yi ya na kallon Azad, Azad ya jinjina masa kai,a hankali ya riƙo hannunta ya ɗago ta ya na faɗin "stop crying alkhairina kin ji?komai ya wuce"

Cikin kuka ta ce "bai wuce ba yaya,a sila ta fa maciji ya sare ka fa! Please kar ka tafi ka bar ni,bana son rasa ka yaya"ɗan murmushi ya yi ya ce"ai na samu lafiya, c'mon ki daina wannan kukan,ko kyau baya yi miki,gaba ɗaya ni nayi missing alkhairina mai surutun nan,mai tsiwar nan,amma this cry cry Khairi is sooo annoying...."sai Kuma ya yi ɗan murmushi ganin yadda take harararshi ta na tura baki,ta miƙe tsaye ta kalli su Sulaiman da yake kallon su ya na wani murmushi da shi kaɗai ya san ma'anar kayan mshi ta ce"bari na kawo muku abinci yaya"kafin su yi magana ma ta yi wuf ta fice

Sulaiman ya miƙe kafa ya na gyara zama ya ce"yauwaaaa!bari in yi tsiya!"


Ka daɗe bakayi tsiya ba Malam sulaimanu 😆😆😆😆

#Nusy_bee


Follow this link to join my Whatsapp channel 👇


https://whatsapp.com/channel/0029VaAzdl5BKfhxNYEdIu2a


🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

✍️Nusy bee

Page 85

Azad ya kalli Sulaiman ya ce"Sulaiman na haɗa ka da girman Allah kar ka yi mana haɗin husumar taka da ka saba,ka bar mu mu koma inda muka fito lafiya"

Auwab ya ce"bar shi ya ya yi tsiyar,ai akan shi zata ƙare ma in sha Allah "

Sulaiman yana dariya yace"saboda kana kurin an wanke ka a wajen matar ka?sai na mayar da kai ruwa ma, kuma ka ce ba haka ba ka sha mamaki "Auwab ya yatsina fuska ya ce"har abin mamaki ne idan ka aikata rashin mutunci,amma na gaya maka idan ka yi kanka zai dawo"daidai nan Khairi ta dawo riƙe da manyan warmers,ta yi serving ɗin su duka suka fara cin abincin

Bayan la'asar shirin su na barin garin ya kammala,a lokacin Saleh ya dawo sun gaisa sosai da su Azad, Auwab yay i masa kyautar motar Khairi,da ya ga yanayinta sai ya raɗa mata cewa"zan biya ki fa,kin manta waye Auwab ɗin naki, c'mon cheer up wife"bata yi magana ba ta san tunda ya ce zai biya ta to zai biya ta ɗin, Saleh ya yi mamaki sosai,ya yi matuƙar farin ciki,yay i ta masa godiya

Rabon kuɗi ya yi sosai a gidan, Nadiya kam 500k ya turawa Saleh ya ce ya bata,sannan ya ce tayi wa mijin ta albishir ya ba su gida a cikin garin Kano,sannan kuma zata koma makaranta ta cigaba da karatun ta,Nadiya ta yi farin ciki irin wanda bata taɓa yi ba,daga ita har mahaifiyar lta inna talatu rasa bakin godiya suka yi

A motar Azad suka taho gaba ɗaya, Azad da Sulaiman da ya rungume Ajmal suna gaba, Auwab da khairi suna gidan baya,ta maƙalƙale shi sosai kamar wadda aka ce za'a raba su,shima ya rungume ta sosai,sulaiman sai dariya yake yi,sai da Azad ya gaji ya ce"Sulaiman,ka rufa min asiri ka daina dariyar nan ko na tsaya ka sauka wallahi,ba zaka ka mana rigimar Khairi ba"ƙasa-ƙasa ya yi maganar,don su Khairi basu jiyo shi ba, Sulaiman ya yi ƙasa da murya ya na dariya ya ce"tuba nake babban yaya!"

Yana kallon yadda sulaiman yake leƙen su Khairi ta madubi yana dariya,kwata-kwata Khairi bata kula ba,amma Auwab yana sane dashi sai kallon banza yake aikawa Sulaiman ɗin

Kai tsaye Hadejia road suka yada zango, Ammi da farin ciki ta zo tana tarbar sirikar tata, wadda ta cika da kunyar abinda tayi wa ɗan nata,Ammi ta ja hannunta suka nufi part ɗin ammin

A can suka samu Mifra a zaune, gefenta Anam ce,ta na ganin khairi ta fara murmushin yaƙe ta na faɗin "sannun ku da zuwa,ya hanya?"Khairi ta kalle ta sheƙeƙe ta ɗauke kai,sai su Auwab ne suka amsa mata,ita kuma ta bi Khairi da kallo jikinta a sanyaye

Da yake lokacin sallar maghriba ya kawo kai ya sa mazan suka yi alwala suka fice, matan kuma suka yi alwala suka shiga sallah

A ɗakin Surayya Khairi ta kwanta tana huce gajiya, Surayyan bata nan taje Maiduguri, Khairi ta buɗe data tana chatting da Nabeela da take shirye shiryen komawa Egypt makaranta

Sai bayan isha'i suka haɗu a dinning area,har Azad da Ammi ta hana shi tafiya, Sulaiman sai surutu yake yana tsokanar mutane,babu wanda ya kula shi dai,sai Mifra da Khairi da suke dariya,ganin hakan bai yi masa ba sai ya dubi Ammi ya ce"Ammi kin san me ya kai mu albasu yau kuwa?"Ammi ta girgiza kai ta ce"kace dai Azad ya ce zaku je amma banda haka ai baka gaya min komai ba"Sulaiman ya gyara zama ya ce"to matsala aka samu, maciji ne ya sari ɗanki,shine matar shi ta kira mu tana kuka tace a taimaka musu a zo a raba su da garin"abincin bakin Ammi yaƙi tafiya,ta tsaya cikin tashin hankali tana kallon Sulaiman da ya cigaba da cin abincin shi a nutse cikin kwanciyar hankali,Ammi ta kalli Azad da yake ɗan murmushi ya na girgiza kai, ta ce"Azad me yake faruwa ne? maciji kuma?"Azad ya ce"Ammi ki kwantar da hankalin ki,babu wani maciji da ya sari Auwab,kawai ya gaji da zaman garin ne,ita kuma Khairi taƙi bashi fuska su daidaita,shine suka shirya plan shi da Saleh,babban ɗan baffa kamilu"

Hatta da khairida Mifra sai da suka kalli Azad da mamaki, Auwab kam ganin asirin shi ya tonu ya cigaba da cin abincin shi a nutse,yana ɗan satar kallon Khairi khairi dake jefo masa wani mugun kallo

Ammi ta kalli Auwab ta ce"wannan wane irin rashin hankali ne Auwab?kawai ka ɗorawa kanka masifa saboda abinda kai ka janyo wa kanka?"cikin Yaren shuwa yace"dama abinda sulaiman yake so kenan,kuma ya samu,so yake ya ja min....." Cikin faɗa Ammi ta ce cikin harshen Hausa"to me ya kai ka ɗorawa kanka wannan masifar?"shi dai bai sake magana ba,yana jin yadda Sulaiman yake ta dariya

Khairi part ɗin Auwab ta koma cike da takaicin abinda ya yi mata,ta na nan zaune ta ji sallamar Mifra,ta ɗaure fuska ta na amsawa,ta kama danna wayar ta, Mifra ta shigo ta na murmushin yaƙe ta samu waje ta zauna ta na faɗin "sannu da dawowa maman Ajmal"

"Yauwa,sannu!"khairi ta amsa tana cigaba da ɗan gyaran part ɗin, shiru ya ratsa parlourn kafin Mifra ta ce"dama zuwa na yi na baki haƙuri akan maganar da na gaya miki,don......"

"Ya wuce!"Khairi ta katse ta ba tare da ta kalli shashen da take ba

Shiru ya sake ratsa parlourn,babu jumawa suka ji sallamar Auwab

Sake tsuke fuska Khairi ta yi, Mifra ta gaida Auwab cikin girmamawa,ya amsa da sakin fuska yana tambayar ta Anam,ta amsa sannan ta yi musu sallama ta fice

Ya dubi Khairi ya ce"yaya Azad yana son ganin ki,gobe zai koma Australia"bata kalle shi ba ta miƙe ta fice, Auwab ya bita da kallo yana murmushi yana jinjina darunta a ranshi

A harabar gidan ta samu Azad tsaye jikin motar shi,tana ganin shi ta washe baki tana faɗin "yaya tafiyar kenan?sai yaushe kuma?"

Yayi ɗan murmushi ya ce "sai na zo watarana, maybe ma sai kin haifa mana baby"ƴar dariya tayi tace"to yaya,amma kai baka so ka haifa mana babyn?"sai kuma ta yi serious face ta ce"yaya na ya kamata kai ma ka yi aure,zaka fi jin nutsuwa kuma kaima da daɗi ace kana da zuriya kamar na brothers ɗin ka,duk da cewa na san aure da haihuwar duka lokaci ne,amma yaya ya kamata ka samu nagartacciyar mace kamar kai,ka aura,wadda zata haifar mana yara kyawawa kamar abbansu"ta ƙarashe ta na murmushi

Shima murmushin yake yi,ya ce"ki nemo min mata,na yi miki alƙawarin duk macen da kika zaɓa min zan aure ta"ta yi murmushi ta ce"are you sure idan na nemo maka mata zaka aura?"ya ce"I'm very sure Khairi "ta yi murmushi ta ce"in sha Allahu ka bani just a week,zan samo maka mata ta gari"ya ce "to godiya nake Ummul Khair,sai mun yi waya"ta ɗaga masa hannu ta na murmushi,ya ja motar shi ya fice daga gidan
Chapter 1 · 0% Book details