← Book details Silar Da Namiji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 5

Sashe 2

Silar Da Namiji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

É—aga masa kai kawai yayi "data farka kwa iya wucewa Amma Asiye waÉ—annan medice's É—in"

Miƙama masa takardar yayi Sale yaƙarɓa shikuwa yanufe cikin ɗakin yanamai jin takaicin rasa Shagalin ligth beb in the world,

Kwance take fuskarta fayau still hijabin najikinta ɗan taɓe baki kawai yayi kafin yakoma gefe ya zauna yana faman zuba tsaki,

A ƙalla sai kusan Awa ɗaya tafarka da salati A bakinta,

Tinda yaji yarda take Ambaton Allah yasa ya maida kallonsa gareta ko ƙyafta idansa bayayi Wannan shine karo nafarka daya ga macce bayan mahaifiyarsa tafalka da Ambaton sunayen Allah,

Saida tagama Addu'o'inta sannan tafara yunƙurin tashi dama buɗe idanuwanta cikin nasa idan nata suka faɗa kallon kallo suka shigayi naɗan wani lokaci ita tanamasa kallon rashin yarda dama waye shi, Shikuwa kallon ma'anoni da dama yake mata haryanajin inama Ace ita ya Aura tinda bisaga dikanku Alamu kamilace ita.

"Sani Yaƙatse musu tinaninsu dacewa sannu ƴammata kin falka? ko zaki iya miƙewa muje gida ƴallaɓai nasauri ne,"

Maida kallonta tayi kan sani Ahankali Tace," meya kawoni nan,? su waye ku,"?

Murmushi yayi yayi kafin yabata labarin dik Abunda yafaru.

Ɗan zabura tayi da sauri ta miƙe tsaye hartana fisge canula ɗin hannunta,

Nawar yamatso da sauri kusa da ita yana mai kama hannunta inda tafisge canula ɗin jini na ɗiga wani bandage dake gurin yaɗauka ya maƙala mata yanajin bugawar zuciyarta daya riƙe hannunta kawai, Ahankali Yace," kada kiyi wasa da lafiyarki dik halinda kika tsince kanki Aciki muje musauke ki gida daganan muwuce muma,"

Kallonsa tayi tare da ɗan kwace hannunta daga nashi tana mai sauke idata ƙasa dan haka kawai taji gabanta nabugawa game dashi, cikin ƙarfin hali Tace," nagode zan iyakai kaina ma,"

Murmushinsa maikyau yayi kafin Yace," mu muka bigeki dan haka muzamu sauke ki gida malama nasan kina tsoro ko? to kada kidamu bamai cutarwa tsakanin nidashi, muje kawai,"

Badan tasoba tabi bayansa tanajin faÉ—uwar gaba,

Saids yatsaya babban phamacy yasaye maganukan da Abincin take Away sannan suka nufe kwatancen nata zuwa gidansu..

Bawanda yayi magana cikinsu harsuka isa saidai dik ta takure kanta gefe, lokaci lokaci yakan É—an murmusa idan yaga yadda tawani takure kamar tahaÉ—u da dodo,

Suna tsaida motar tayi saurin fitowa hakan yayi daidai da fitowar baba daga gidan dan zuwa nemanta, ganinta cikin mota haɗaɗɗiya ba ƙaramin ɗa gamasa hankali yayi ba,

Gurinsa tanufa tanamai durƙusawa tana gaidashi kafin yayi magana Nawar yafito yanufoshi.

Cikin ladabi ya sunkuya yagaidashi yabashi labarin komai,

Baba Yace," to mungode kashiga daga ciki mana,"

"A'a baba ina sauri ne banan ne garin mu ba dik da dai narasa jirgina na yau saigobe zan koma Amma insha Allah kafin nakoma gobe zan dawo yanzu ga magungunnan ta Ajikinsu dik A kwai yarda za'ai Amfani dasu,"

Sallama sukayi Akan gobe zaibiyo sannan yawuce..............

WhatsApp number 07064904617 or call number 07031012948

_BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_
[08/04 12:09 am] 🥰Mujaheedah🥰 (MATAR💖MLM): *SILAR ƊA NAMIJI!!!* *FREE BOOK Page 16&19*

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

```RUBUTA LABARI DA TSARAWA 🥰MUJAHEEDAH🥰 (MATAR 💖 MALAM) HEEDAH HAYDAR OSTHMAN..... AMMYN KHAUSAR CEEE....```

*BESIDE IN TRUE LIVE STORY,...... SHOURT STORY*

_Inama ɗaukacin dukan jama'ar musulmai barkda shanruwa Allah yaƙarɓe Ayukanmu nagari marasa kyau Allah ka yafemuna RAMADAN MOUBARK_

Gidan Gwamna ya koma suka zauna da najib ɗansa harzuwa goben dama Akwai sanayya tsakaninsu kusan tare sukayi karatu A ƙasar Ustrilli'a saidai basu cika sanun jutuwa ba saboda halinsu ba iri ɗa yabane,

Wayarsa Najib ya miƙa masa Yace," kai lazy kanaji wayarka na ringing ka barta Mommy ce fa,"

Yana ɗan tura baki yaƙarɓe wayar saboda harya fara bacci da gangan yamaida wayar silent ɗazun sai yanzu yacire dan yasan indai zai barta da ringing km kunne to ba ƙaramin Takurawa rayuwarsa za'ayi ba da kira,

Kara wayar kawai yayi A kunnensa batare da yace komai ba,

Mommy dajin numfashinsa Alamar yana ƙalau dai yasa hankalinta ya kwanta Tace," Haba Nawar meke damunka, wai meka ɗau duniya ne? Shin ka manta nice Uwarka nice nasha wahala kanka Amma kullum cikin sani ɓacin rai kake taya zakaga haske A kan lamarin ka? Nawar da bahaka kake ba, tabbas miyagun Abokai dakake bibiya suka lalatamun kai," Kuka tasa daga bisani ta tsinke kiran.

Dik maganar da Mommy ke faÉ—i Najib yaji komai dan dama yana É—an duba wasu file ne,

Aje file ɗin yayi ya fuskance Nawar tareda naɗamasa duka Abaya da ƙarfi,

Miƙewa zaune yayi bashi Yana mutsitstsika ido cikin masifa Yace," me haka najib yazaka shiga rayuwata bakasan idan inajin bacci ko inayi ba'a tadani ba ko Ahanani ba,"

Cikin takaici Najib Yace," Wannan kuma kai tashafa malam Wllh kaji tsoron Allah Uwa Uwa ce wani nacan Uwarda zata masa faɗa Akan gaskiya wllh yarasa wani yanada ita saidai ita kanta batasan gaskiyar ba balantana ta ɗaura ɗan nata ko dan taguji ɓacin ransa taƙi gaya mai wllh Nawar kaji tsoron Allah Akan Abinda kakema Mommyn ka wllh sai Wutar Allah tacika,"

Tsaki yayi yamiƙe daniyar banmasa ɗakin dan yaɓata masa rai sosai,

Saurin riƙo hannunsa Nawar yayi Yace," Kada kayi fushi zankirata nabata haƙuri kuma daga yau na daina insha Allh,"

Murmushi Najib yayi Yace," ko kaifa yanzu ma shirya ai,"

:::::::::::;;;;;;;;;;;;;;

*BAYAN WASU KWANAKI* Abubuwa da yawa sunfaru daga ciki harda saka ranar Auren Nawar da Deeyam inda Neera Ake shirin gudanar da nata bikin itada Kamal,

Kamal bawani bane face ɗan kasuwa rufin Asiri ne kawai dashi yataɓa Aure Amma yasaki matarsa saboda matsala dasuka samu..

Gidan nu Neera yacika sosai Su deeyam sungama rabon katin dan yau ne É—aurin wankin Amarya,

Takurata suke Akan tatashi taje tayi wanka da kwalliya Amma kota kansu bata biba, babbar wayarta Smath 8 take charting Abunta tana murmushi lokaci lokaci.

Ganin sam batada niyar tashi yasa deeyam ƙwace wayar Tace," Haba malama kedawa haka? idanma Angon ne ai saiyajira dika kwanaki nawa suka rage ne,"?

TafaÉ—a cikin sigar zolaya.

Miƙewa zaune Neera tayi Tace," Wllh kunfaye takura waima wacece Amaryar dama Angon? Shirme fa kawai kuke, Mtswwww Allah yakyauta nayi charting da wannan matsiyacin, dalla ban wayata," tafisge wayar tacigaba da charting ɗinta.

Mamaki ne yakama dika sauran ƙwayen dake wurin musamman deeyama "Kina hankalinki kuwa Neera mijinki zaki kira da matsiyaci,"?

"Miji!!!? ni wllh banda miji kuma banyi miji ba Amma son zanyi badai yanzu ba, kai bari kugani dan nagaji da wannan Abun naku wllh,"

Wayar taÉ—aga tasaka wata number kira ringing 2 Ana 3 Aka É—aga,

Muryar wata Æ´ar matashiyar budurwa naji tanacewa," Laaah Aunty Amarya kece dakanki kika kirani yau? Ai munana zuwa wankin Amarya yanzu haka shirin tahowar muke,"

"Ke dallah malama banason surutun banza da uwarku nakeson magana tana kusa kibata kawai,"

"Aunty kina cikin hayyacinki kuwa? zaginmu zakiyi,"?

"Shin zaki bata wayar ne ko a'a nasake neman wani layin da za'a haÉ—ani da ita,"

Kan nafi tayi magana Mamansu taƙarɓe wayar takara Akunnenta dik wata maganar Neera Mama taji, Tace," Ai uwarsu ɗince faɗi dik Abinda kikeson faɗe inajinki,"

"Masha Allah dama zangaya miki ne wllh wllh wllh kigayawa wannan matsiyacin ɗan naki Yazo yaƙarɓe dik wata tsiyarsa ni nafasa Auransa dan ni ba'ajinsa bace wllh, idan kuma kikayi taurin kan hanashi ko shi yayi wllh wllh wllh randa Zantare gidansa wllh saina kashe shi...................

```Tirƙashi kunji wata sabuwa kuma, lalle Neera ta iya tada ƙura ran bikin farko Tawargazashi da kanta ko meye silanyin hakan??????????
MuhaÉ—u A next page kawai dan sanin meye dalilinta dama me zaifaru............... Kitaimaka idan kingani kimun sharing koda baki karanta ba dan Allh...```

WhatsApp number 07064904617 or call number 07031012948

_BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_
[08/04 12:12 pm] 🥰Mujaheedah🥰 (MATAR💖MLM): *SILAR ƊA NAMIJI!!!* *FREE BOOK Page 20&29*

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

```RUBUTA LABARI DA TSARAWA 🥰MUJAHEEDAH🥰 (MATAR 💖 MALAM) HEEDAH HAYDAR OSTHMAN..... AMMYN KHAUSAR CEEE....```

*BESIDE IN TRUE LIVE STORY,...... SHOURT STORY*

*TSARABAR RAMADAN*

Tana maganar cikin É—aga murya da nuna gaskiyarta muraran Akan zata iya Aikata Abunda Tace,

Hakan yafara janyo hankalin mutane zuwa É—akin hatta Abba saida Aka kirashi da yake waje,

Fisge waryar Deeyam tayi takatse kiran cikin takaici Tace,"Kina hankalinki kuwa wannan wane irin kunyatawa ne da tozarci? kinsan bakisonsa meyasa kika bari suka kawo kayansu, kuma har Akazo biki,"?

"Ni bance inasonai ba kuma ni bance Aƙarɓe kayansu dan haka wllh koda sama da ƙasa taza game narantse bazan Aure shi, ba"

Tasssss Abba ya wanketa dawasu zafafab maruka Cikin baƙinci da tozarci irin wanda tamasa Yace," wllh baki isaba Neera ni na haifeki bawai ke kika haifan ba, dan haka Auran nan ba fashi,"

"Dawa bakoda wannan tsinanniyar mara kunyar ba, Ai wllh ko itaÉ—aice macce to saidai ya tabbata ba Aura kanajin Tana furta kalmar kisa kace dole É—ana ya Aure ta? wllh bazai yuba Akai kasuwa munyafe," FaÉ—ar Maman kamal dake cikin fushi.

Mama ƙarama Tace," A'a baza ayi hakaba dan Allah kuyi haƙuri Azauna Akan lamarin nan,"

"Wane zama ke kuwa munafuka waya sawo bakinki? idan kinji haushi saiki bashi Æ´arki nidai bazan Aura ba wllh," tafaÉ—a cike da rashin kunya tana wani tura baki.

Niyar dukanta Abba yaso Aka dakatar dashi Mama kuwa itama tahau bakinta ,"Bafa zaiyu kowa yasawa ƴata baki ba tace batayi Ai magana taƙare da hanka kowa yakama gabansa shikuwa Gobe a'aika masa da kayansa,"

Cikin takaici Abba yace," kiÉ—auki Æ´ar taki kubar min gidana na sakeki saki É—aya,"

Yana gama faɗin hakan yabar ɗakin cikin ɓacin rai, Zuciyarsa natafasa Akan wannan Abun baiyi baiyi Aune ba yafaɗi yana mai dafe satin zuciyar sa,

Sosai mama taƙaɗu da sakin dan bata zaci haka ba jiki ba ƙwari ita da Neera sukabar gidan Amma Neera ko Ajikinta dan Ayanzu batajin zata sauya.

Haka kowa ya watse ba daɗi sauran dangi kuwa suka ɗunguma zuwa Asibiti da Abba, likita ya tabbatar musu yariga yasami ciwon sashen ɓaren jiki ma'ana Paralysed dik rabin jikinsa bazai sake Amfanuwa ba.

Sosai Mama tatsorata dajin hakan itakanta Neera ta tsorata Tanbayar kanta take to metayi kenan *SILAR ÆŠA NAMIJI* Abbanta ya nakasa Auren Mamanta ya mutu, da zasusan Ainahin dalilin faruwar hakan datasan saki Uku Abba zaima Mama itakuwa cireta zaiyi daga Æ´aÆ´ansa ma gaba É—aya,.

Sosai mama tadamu dason takoma dan dik Abunda yadameta saidai dik yarda taso Abba yaƙi maidata da ƙyar Akasamu yamaidata yabari Neera tadawo itama,
Chapter 2 · 0% Book details