← Book details Sawun Giwa Part 7 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 6

Sashe 6

Sawun Giwa Part 7 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Dukkansu kallonta sukayi acikin mamakin sauyawarta lokaci ɗaya,,,itakuwa hadima fuwa dasauri tafito daga kitchen ɗin tana amsa kiran da maisoon tayi mata. Wani mugun kallo ta watsa mata kafin tace "fuwa waye yataɓa abincinnan bayan nabar kitchen? Ta tambaya idonta ƙuri akanta. Cikin mamaki da tsoro hadima fuwa tace "bawanda yataɓa ranki yadaɗe nice kawai na ɗauko nakawosu nan Allah dai yasa ba laifi nayiba? Shiru maisoon tayi tanabinta da ido ko ƙiftawa babu kafin tanisa tace "waye yashigo kafin su basam? Kuma ina hadima juwaira? Tasake jefa mata tambayar. "Bawanda yashigo ranki yadaɗe kuma juwaira tunda taɗauki abincin memartaba bata dawoba...kai kawai maisoon yajikinta kana tace "kin tabbata? "Eh ranki yadaɗe. Shikenan jeka. "Godiya nake Allah yaƙara miki lafiya, cewar hadima fuwa tana barin wurin hartakusan shiga kitchen sekuma tadawo dasauri tana faɗar "tuba nakeyi uwar gijiyata tabbas aɗazu ina kitchen naji motsi a parlor sedai koda nafito bayan gimbiya kursum kawai nagani tafita daga parlor, taƙarasa zancen kanta aƙasa. Ido suka zaro atare, ita kuwa maisoon kafeta kawai tayi da ido kafin tayi saurin riƙe Hannun junaid dayaje saka abincin abakinshi. Cikin faɗuwar gaba suke kallonta, ita kuwa cikin bada umurni tace kowa yadakatarda cin abincin nan, kana tajuya zuwa ƙofar fita parlor cikin sauri kamar zata tashi sama,,,,dukkansu da kallon mamaki suka bita amma ba wanda yayi yunƙurin binta.

Tana fita bata zarce ko inaba se pert ɗin gimbiya zaitun, tareda nufar bedroom ɗin gimbiya kursum kaitsaye sedai tun kafin taƙarasa ciki sukaci karo da ita abakin ƙofar, kallon kallo aka tsayayi tsakaninsu kafin maisoon tace "yah sheikh yace nakiraki, tafaɗa cikin basarwa. Wani malalacin murmushi kursum tayi aranta tana faɗar "lallai aikin wannan bokan shine ake kirada yankan wuƙa. Afili kuma setace "muje tayi gaba cikin ƙarairaya hadiman dasuka rakota suna take mata baya har pert ɗin sheikh sudais, tana shiga parlor Maisoon ta dakatarda hadiman abakin ƙofa kana itama taƙarasa ciki....kursum kuwa su yarima basam takebi da kallon wulaƙanci ganin yadda suka zuba mata ido...Maisoon tana ƙarasowa wurinta tace "bisimillah zauna kafin yafito tayi maganar kamar ba komai. Seda kursum taɗan yamutsa fuska kana taja kujera tazauna tana ɗan jujjju idonta ranta wasai musamman dataga black tea ɗin da maisoon tazubo a cup setayi tunanin shine yasha yarage.

Ƙarasowa maisoon tayi wurinta kana tace "kitaɓa wani abin mana tayi maganar tana ɗauko black tea ɗin data zuba a cup taƙara wani sa'annan tamiƙawa kursum....wani ɗan iskan kallo tabita dashi na bakida hankali kafin taja tsaki cikin tsiwa tace "nayi Miki kamada wadda zataci banzan abin hannunki ne? kawai kije kisamarwa yah sheikh zuwana koni naje nasameshi dakaina, taƙarasa zancen tana bankawa maisoon harara..gira ɗaya maisoon ta ɗage mata kana tayi murmushi tace "au haba Ashe dai zaki iya samunshi? Humm to nidai duk ba wannan ba kawai ki karɓa domin shine abinda zebaki damar ganinshi, taƙarasa zancen tana ƙoƙarin kai mata cup ɗin bakinta. Cikin ɗan firgici kursum taja baya tana bankawa maisoon wata muguwar harara"wlh bazan shaba ina ruwanki dasenasha wani abu anan gidan nasani kowani mugun abin kika sakamin aciki, tayi maganar cikin firgici tana ƙoƙarin barin parlor....wata muguwar ɗamƙa maisoon tayi mata tana hiyo da Ita, kafin tahaɗe girar masa da kasa tace "ƙarbi kisha tun muna sheda juna nidake domin wlh ko sama da ƙasa zasu haɗe sekinsha wannan tea ɗin zakibar pert ɗinnan.

Wani irin tsorone yamamaye kursum lokaci ɗaya gumi yafara wanke mata fuska. Sukuwa su yarima junaid ido kawai suka zuba musu suna kallon ikon Allah domin suma a ɗarɗare suke zukatansu fal da tsoro kar Ace har abincinda suka riga sukaci akwai wani mugun abin aciki. Jabaya kursum tafarayi tana neman wurin guduwa, cikin sauri tajuya zata gudu, cikin zafin nama maisoon tasaka mata kafa tafaɗi yarab, sa'annan ta ɗauketa da wasu gigitattun matuka har biyu Seda duka parlor ya amsa, Ita kuwa kursum ta buga wata muguwar ƙara domin sosai marin yashigeta wanda ya haddasa mata ɗaukewar ji da gani lokaci ɗaya, ido yarima junaid yawaro yayinda yarima basam yasaki murmushi....ƙafa Maisoon tasaka ta danneta da guywarta kana taɗauki cup ɗin taɗora akan bakinta tareda saka hannun ɗaya ta toshe mata hanci wanda yasaka dole tabuɗe bakinta babu shiri,,,juye mata Black tea ɗin tashigayi tana haɗiyewa dole, seda tashanye ganin wani yazube ƙasa yasa Maisoon kallon yarima junaid da idonta dasuka koma red sharr tace "zubamin wani, tafaɗa cikin wata irin murya me mugun amshi...dudda cewar yarima junaid yaso kin zubomata amma yanayinta ba ƙaramin tsoro yabashiba Hakan yasa yaɗauko cikin sauri yazuba mata har seda yacika cup ɗin...Hakan taƙara juyewa kursum shi kana ta ɗagata tana banka mata wani mugun kallo, ganin tana yunƙurin ami ne yasa Maisoon yimata wata muguwar shaƙa cikin ɗaga murya tace "narantse da sarkin dake busa numfashi idan kikayimin amai anan Sena fidda miki maƙoshi waje, yafaɗa tana sauke mata wasu zafafan marukan..atake idon kursum suka firfito waje kamar zata sheƙa barzahu sekakari takeyi cikin galabaita da azaba...wasu marukan Maisoon taƙara sauke mata tana faɗar "uban waye yabaki damar shigowa parlor na? mikika zubamin a abinci? Wakikeson cutarwa? Ni MIJINA? Ko ƙanenshi? Wlh idan bakiyi maganaba Sena kasheki shigiya marar imani uban me kika zubamin nace? Tafaɗa cikin daga murya wanda yayi Dede da shigowar sheikh sudais parlor cikin kamala da sallama ɗauke a bakinshi,,,sedai abinda yagani yayi bala'in bashi tsoro da mamaki, dasauri yaƙarasa wurinsu yana faɗar "subhanallah butti Mike faruwa ne? saketa plesse, yafaɗa yana ƙoƙarin raba maisoon da kursum sedai abin yaci tura ganin yadda takafe wuri ɗaya kamar dutse, seda yayi da gaske yasamu ya ɓanɓareta daga jikinta, atake kursum tazube awurin sumammiya..betsaya komaiba kawai ya saɓa maisoon akafaɗa yanufi bedroom ɗinshi da Ita, yana watsawa su yarima basam harara ganin yadda suka zuba ido kawai suna kallon matsrshi zatayi kisan kai ga dukkan alamu suma atsorace suke. Ɗauke kansu sukayi dasauri daga kallonshi harya shige bedroom ɗin.

"Haba yah sheikh wannan hararar taka ai sedai kayi waye ze tunkari Anty gimbiya awannan yanayi tahaɗa dashi, cewar yarima junaid..shidai yarima basam bece komaiba se hadimanta dayakira wanda suke abakin kofa suna rawar ɗari babu halin shiga dudda sunajin ihunta tunda Maisoon ta hana, kuma idan suka barta zasuci abinsu agun gimbiya saudat, sunajin kiran yarima basam cikinsu ƙara durar ruwa, cikin bada umurni yace susaka mata ruwa kana sunɗauketa daga nan su kaiwa uwarta kafin me gidan tafito domin idan tagantanan ƙarasata zatayi...aiko cikin sauri suka aiwatar da abinda yace..sukuwa pert ɗinsu suka nufa suna tafe yarima junaid na faɗar"tab dijam dama Ashe Anty gimbiya Hakan take Ashe tamafi ƙarfin yadda muke tunaninta tab lallai akwai dambarwar fitina agidannan zanga ya Anty saudat zatayi...shi dai yarima basam bece mishi komaiba seda suka shiga parlor su kana yace "wannan hukuncin datayi mata shine Dede domin bamusan watayi nufin cutarwa ba kuma kila mu muringada munshiga tarkonta tunda munci abincin sedai kawai Allah yakaremu...ameem ameen amma da Anty gimbiya ta huce zanje na ɗauko abinnan nakaishi abincika ko akwai wani abu aciki, cewar yarima junaid..humm kawai yarima basam yace yana shigewa bathroom ɗinsh

Sheikh sudais kuwa yana shiga ya ajiye akan bed ɗinshi amma se wutsil wutsil takeyi nason kwacewa tafito sam taƙi yadda ta zauna..ganin taƙi yadda ta zauna ne yasa yayi saurin....!

Autar alheri ✍️
Chapter 6 · 0% Book details