Part din Sultanate.
Sanin Gaibu Part 1 Complete Hausa Novel · about 34 min read
"Likita baka ce kome ba, tun ɗazun kake kanta, kuma gashi zaka bar gidan." "Allah ya baka nasara, da sauki damuwa ce ta mata yawa, amma ba wani abin da yake damunta." "Tow shikenan" ya fada yana kallon Sultanate da take barcin allura. Domin kwana biyu nan, ita tasan.me take, jikinta kamar ana konata ta cikinta, gashi tana shan ruwa kamar me, haka kuma bata isa ta kwanta ko ta rufe Idanunta ba, Dawlat khatoon zata gani a tsaye a gabanta cikin jini. Firgi zata bude idanunta. abinda ya haifar da haka, saukar da ake da yankan da ake yi, shi yake karya duk wani asirin da aka yi domin rufe bakin mutane da jama'ar masarautar baki daya. Tow addu'ar da ake bata faduwa banza, domin kuwa ya fara bankad'o abubuwan da yawa, a gefen Abdulkarim, wanda ya kashe Mansurah bayan ya mata fyade, kama shi hukumar Saudiya tayi dama duk abin da Hajiya Suhailah tayi domin shi take, tow gashi ya tab'o me tsada a Saudiya har an kama shi..
***
UK....
#Mai_Dambu
[13/07, 10:03 am] usmanlauratu71: 64... UK.
Rike hannunsa tayi tana kallon waje, kafin sauke ajiyar zuciya. Duk da an mata aikin bakin ko zata yi magana, amma har yau shiru babu alamar zata yi magana, idanunta ne ya cika da kwalla. Daga yadda ta razana ya sa shi fahimtar akwai wani abu a ƙasa. "Meke faruwa?" Hawaye ne suka zubo daga idanun ta." Ta girgiza mishi kai tana. "Gaya min wani abu na faruwa ne?" Hawaye ne sharr suka kara zubo mata. Da hannu ta mishi magana ta ce. "Kar ka fita zata zo!" Murmushi yayi sannan ya saka hannu ya rungume ta. "babu abin da zata iya miki, matukar ina raye.!" Ya fadi haka tare da barin ta a wurin ya shiga hada kayanta, domin an sallame ta. Sai da ya gama kome sannan ya fita da kayan da ita suka fita tare ne, bai san me Latifah take bukata ba. Saka yayi a mota, sannan ya koma cikin asibitin. A kofar dakin ya hango ta da yar askar da aje tiyata, tsayawa yayi ya ga ta shiga cikin dakin. Rufa mata baya yayi ya rufe kofar a razane ta juya, domin bata kawo ya fita da Sa'ade ba. Sake askar tayi. "Kakanki ya saka miki mummunar ciwon da ba zaki tab'a warkewa ba, da ace haukar ki ya kai matakin da kika tab'a min yarinyar da nake Bala'in so da kin sha mamaki, ban san me kike so ba, ni dai na ce bana sonki kuma na kara gaya miki bana sonki, wace ce ke da zakina bibiyar matata? Tunda abin ya kai ga haka zan hada ki da hukuma, kuma karshe sai kin rasa aikin ki!" Zubewa tayi akan gwiwanta tana me fashewa da kuka. "Don Allah ka rufa min asiri, wallahi ba zan kuma tab'a ta ba, don Allah." "In one condition, matukar kika shiga harkokin ta, wallahi sai na gayawa Mahaifinki abin da kika aikata " daga haka ya juya abin sa, matukar abuturab ba autar maza ba ne, ta hakura da shi, amma kuma ina zata samu namijin da ya iya sarrafa mace ba tare da ya kai last stage ba. Yana fita wurin motar ya same ta sai zare idanu take, murmushi jibi zasu bar london ya gama kome na shi domin ita, zai karasa sauran a lagos.
Kusan satin ta huɗu a asibitin, koda suka isa a tare suka shiga kitchen, sumbatar wuyarta yayi, suna aikin karshe da suka kusan gamawa ne, ya dauki garin fulawa ya bata mata fuska da shi, ware idanu tayi, ta dauki sauran fulawan ta shafa mishi a jiki ta fita da gudu, ya bi bayanta, suka shiga zaga falon, kamar zasu tashi gidan da dariyar su. Kamota yayi ya mannata da bango, sosai yake tura mata sako masu saukin ɗauka, yana ji wani irin Kaunarta zuciyar shi tana kara narkewa akanta. Definitely ya gama mutuwa akan yarinyan nan, lokaci kadan yake jira su zama daya. Daukarta yayi zuwa cikin bedroom dinsu, wanka suka yi a tare, sannan suka fito. Mini skirt na jeans ta saka, sai hafvest da ta daura pink, gashin kanta ta daura shi bayan ya busar mata da shi. Komawa ban daki tayi, jin shiru shiru yasa shi fahimtar tutu take, toroso. Fita yayi daga dakin, tana gamawa ta kuma gyara ban dakin ta fito. Sai da ya shafe jikinta da turare, sannan ta futo wurin cikin abincin. A tare suka ci abincin, sannan ta tattara kome ya fito musu da popcorn, suna kallo suna ci, har Azhar, a tare suka nufi dakinsu, suka yi alola ya ja su sallah, suna idarwa suka shiga hada kayan su. A hankali suna yi yana mata hira, murmushi kawai take, kafin la'asar sun gama hada kome, sallah suka yi, suka shiga hada ba wajen, suna tsokanar juna, wunin ranar tattara kayan su, suke. The next day suka tashi da aikin cire kome a gidan suna sakawa a kwali, domin ya ce ba zai kuma dawowa london ba. Haka suka yi ta sakawa a kwali ana rufe bakinsa, wurin sha biyun rana babbar motar dauke da kwantena tazo ta kwashe kayan. Da kawun sa ya haɗa a waje. "Kana ta shiri kenan?" "Eh Uncle in sha Allah zan tafi gobe." "Allah ya tsare hanya" "Amin Ya Allah" ya fada yana tsaye suna ta zuba mishi kayan a motar, har suka gama sannan yayi cike ciken da zai yi suka tafi shi kuma ya koma cikin gidan, tana kitchen, wando ne a jikinta irin crazy din nan, sai bodyhook, a hankali ya isa bayan ta, sumbatar wuyarta yayi yana faɗin. "Kina kunna min wuta fa" murmushi tayi hannun shi ya kai cinyarta yana shafawa a hankali. "Idan kina irin wannan dress din, zaki hana ni, abin kirki domin nayi ta tunanin wadannan halittun." Juyawa tayi tana kallon shi, sumbatar bakin shi tayi, ya riko ta tsam. Sun kwashi mintina goma sha a haka, don ma Allah ya taimaka abin da ta daura bai zube ba. Dakyar suka yiwa juna a falon, kamar cin wuta haka suke biyar da kansu. Turo kofar falon Latifah tayi, ta hango yadda suke wani abu. Da sauri ta mai da kofar ta rufe, tayiwa kanta alkawarin bata kuma shiga rayuwar su, amma a duk lokacin da ta gansu a wannan yanayin ji take kamar ba zata iya ba. Su kan can suka lula, sai dai yau Abuturab yaso wucewa, ganin yadda jikinta ya dauki rawa da tsoro ya sa shi dole ya kyaleta. Ya koma gefe, yana me rungume ta. "Sorry " ya fada a hankali, domin gaskiya yasan yana kwaruwa, shi yasa yayiwa kansa alƙawarin suna isa kwara, wallahi hakurin sa ya ƙare. Haka suka shiga wanka a tare, koda suka fito sallah suka yi, da yamma suka fita yawo tare da tsaraba, haka tayi ta jidar turare da kimono wa Ummi da wani arab shop ta sayawa Rumaisah da Zakiyyah da Ummy Aymana dogayen riguna, duk da shi ya bata kuɗin, Innar ta da yayunta, atamfar Super exclusive ta sayawa Inna kala biyu, sai Inna Larai ba, Abuturab ya karawa Inna lace mai kyau, sak irin na Inna, sannan ya kaita inda ya sayi kimono yayi ta saya mata, me hade da riga da wando, ko riga da skirt. Takalma kuwa haka yayi ta jida mata. Sannan ya sayawa Malam Aminu shadda me kyau da tsada. Wani gefe suka shiga yaga wani rigar barci lingeria, ya ɗauka yana son first night dinsa da ita shi zata saka, janya yayi suka tafi suka biya kudin kayan, sannan suka bar kasuwar. Koda suka dawo kayan ya zuba a cikin akwatin da ya sayo, bayan sun kwanta yana cikin jikinsa ya ce mata. "Ki shirya domin wallahi bani d'aga miki kafa."kifa kanta tayi a kirjinsa tana dariya.
Ba zata tab'a manta da wannan moment din ba, yana cikin ranta da brain ta ba.
Washi gari, da asuba cab yazo ya dauke su. Suka bar Ingila, akan idanun Latifah suka bar gidan. Basu samu jirgin Lagos ba, sai dai sun samu wanda zai isa dubai,kafin su samu na Lagos. Tafiyar kwana ɗaya da wuni daya. Suka iso Lagos a gaji suka samu jirgin kwara.
Koda suka iso kwara, Ra'is ya je ya dauko su. Sun gaji musamman ita, suna isa bangaren Ummi suka sauka, anan suka ci abinci suka huta. Da gayya Ummi ta dauke ta, shi kuma ya nufi cikin gidan gaida mutane. Ko ba a gaya maka ba, kasan ya samu nutsuwa a auren da yayi, don haka kowa ya gansa sai ya yi magana akan kibar sa. A bangaren Sultanate ya yada zango. "Munafuki me ya dawo da kai?" "Nazo binne ki da ranki ne, sharrin da kika yi su raka ki har makwancinki" yana fadar haka ya bar ta, sallah magariba aka kira ya nufi masallaci, bai dawo ga sai da aka yi sallah isha. Sannan ya dawo ya nufi bangaren Ummi abinci ya ci, kiri-kiri ya saka Sa'adensa a gaba, haka kawai a hana shi matarsa, tun fitarsa Ummi ma gyara mishi matar take, bawai ta rike ba ne. Suna shiga part ɗinsa wanka yayi sannan ya dauko mata doguwar riga da a cikin kayan sa, ta bata ta sauya kaya, alola tayi suka gabatar da sallah nafilla da ma'aurata suke yi a daren su na farko. Bayan sun idar, ya fita ya kawo musu, fita yayi sai gashi dauke da hollandia milk, ya ajiye cup biyu, ya zuba mata daya shima ya zuba daya suka sha. Yana jan ta da hira. A hankali ya dauki kofin ya fita da shi ya dawo, brush yayi itama kuma tayi, kafin ta fito ya ajiye mata rigar barcin. Tana fitowa ta samu baya dakin, daukar kayan tayi ta shige ban daki, ta saka sannan ta fito ta kwanta. Kamar ya sanin ta gama kome ya shigo shima, tunda ya haura gadon, yake kashe ta da al'amarin soyayyarsa, wanda ita kanta ta saba ba wani sabon abu bane, sai dai kuma labarin ya sauya ne a lokacin da ya isa matakin farko ta nasarar zaman su abu daya, lallai ana sha gwagwarmayar a wannan fagen, domin kuwa ita kanta da tasan haka abin yake, da koda wasa ba zata yarda ta bashi yarda da amanar ta ba, domin sai da ya gwangwaje amarcinsa, ya kai matakin da ba zai iya hana kansa gamsuwa ba, ya kyaleta. Ina dalili, shekara nawa yana dakon zama magidanci yanzu da ya samu babu me hana shi, ban daki ya shiga ya gyara jikinsa, sannan ya haɗa mata ruwan zafi, da kansa ya taimaka mata, ya kwashe zanin gadon, ya ajiye. Domin Ummi ta bukaci haka. Lokacin da ya fito da ita daga ban daki, kuka take da rigima dakyar ya lallabata suka kwana, cikin dare zazzaɓi ya rufe ta, haka ya kwana yana rarrashinta, ga shegen raki. Asubar farko ya bugawa Ummi kofa, tana zauna akan abin sallah, ya shigo dakin. Sunkuyar da kai yayi a gabanta. "Na gode da kika bani duk wani tarbiyyar da ta dace, Ummi na gode da taimakon da kika min na zama D'a nagari, Ummi ki saka idanu a kaina da iyalina koda zan kauce hanya" "Allah ya maka albarka, ya Fulaninta take " sunkuyar da kai yayi ya ce. "zan tafi masallaci, ban san me zaku bukata ba" "ka koma gidan su Ra'is zamu kira ka idan muka bukaci wani abu " haka ya mike cike da kunya, a lokacin ta mike tare da nufar wardrobe dinta, ta dauko sabuwar alkyabarta, sannan ta dauki da wasu awarwaro na gold da dan kunne da sarkan su, har da sarkan kafa da bariman hanci, wani shegen lace ne na alfarma ta fito da shi, waya ta dauka ta kira Zuwairah. Can kuwa sai gata a tare dq suka nufi part din Abuturab. Kaya sosai Ummi ta shiga da shi, sai da suka shiga uwar dakin ta hangota cikin bargo a dunkule, nan Ummi tayi ta shafa kanta, har ta bude idanunta, fuskar ta tayi jajjur, sai kuma.ta fashe da kuka. Haka Zuwairah ta hada mata ruwan zafi, ta saka duk abin da ake bukata, sannan Zuwairah ta basu wuri Ummi da kanta, ta rikota tare da mika mata towel, ta taimaka mata har zuwa ban daki, yadda take tafiya sai ta baka tausayi domin baki daya tayi laushi. Haka dai Ummi tayi ta mata bayani, har ta gyara jikinta, sannan ta fito, kiran Zuwairah tayi ta tsaya ta shirya suka wuce ɓangaren Ummin, dauke da zanin gadon da suka yi tarzoma akan sa, aka saka a tire, ana bin part part na gidan nuna musu abin da ya faru daren jiya, don haka duk matar da aka kai.mata, haka zata cire gold ko kudi me yawa ta fanshi zanin gadon da gadon da suka kwana, har wurin Sultanate aka kai, ta fanshi gadon Zuwairah ta ce mata. "baku fansa yadda Umminsa ta fansa ba, ta fansa da gwala-gwalan tire daya, sai kudi miliyan biyu, da mota Land cruise, sai kujeran hajji, da yawon buɗe ido, ku kuma.baku fansa yadda ya da ce ba. Don haka yau akwai walima."
[13/07, 10:03 am] usmanlauratu71: 65... Sosai Sultanate ta kadu, duk da halin da take ciki bai hanata balai ba, amma kuma ciwon da take fama da shi ya ishe ta. Zuwairah sun bar gidan suka tafi bangaren Ummi, kafin kace me yayun Abuturab sun zo suma.sun fanshi zanin gadon, amma ina Ummi ta jima da musu kane-kane akan Ƴaranta, zuwa rana gidan ya cika, zazzabin da ya rufe Sa'ade yasa dole aka d'aga walimar, amma fa anyi karamin biki ko.nace ana kan biki a cikin gidan. Sai dare suka samu zazzabin ya sauka, domin sai da aka saka mata ruwa, a lokacin Abuturab ya zo har dakin Ummin da take kwance, ya shiga. Zama yayi a gefen gadon, yana shafa fuskarta. Bude idanu tayi tana kallon shi, kafin ta dauke kai domin fushi take da shi, "kiyi hakuri" ya fada yana ciro wani karamin box ya ciro mata wani sarkan diamond ya saka mata, sannan ya saka mata zoben, yana mirza hannun. "My love for you is deeper than the deepest ocean
taller than the tallest mountain
hotter than the hottest desert
and denser than the densest of forests
my love for you is truly eternal
I love you." Ya fada mata, hawaye ne ya zubo mata. Yana share hawayen ya cigaba da cewa. "Behind every successful man is a woman ? Whoever said this is 100 percent right. You're the secret behind my success, my dear wife. I love you. ina son ki, ina son ki, zan kuma cigaba da son har numfashina a karshe. Nasan wata rana zan saka ki a cikin damuwa ki min uzuri da kawaici ni ma dan adam ne, zan iya laifi a koda yaushe. Ina son ki lucky." Ya ciro sabon waya ya daura mata a kan hannunta. "Idan na koma zan kira ki Please kar ki kashe wayar, ina sonki" ya sumbaci goshinta, sannan ya mata sai da safe. Ummi tana bakin kofar, tausayi ya bata domin da gasken gaske son Sa'a yake kuma irin mahaukaciyar soyayya ce mara jin rarrashi. Lokacin da ta shiga dakin tana ganin yadda take kokarin boye wayar, sharewa Ummi tayi, irin bata san kome ba, sannan ta shiga ban daki ta hada mata ruwan zafi, ta taimaka mata ta shiga ban daki tayi wanka, tana fitowa ta samu ta ajiye mata tea me zafi da farfesun kazar gida. A hankali take shiryawa, tana gamawa ta fara sha, tana lumshe idanun ta. Sai dai har lokacin bakinta babu dad'i ko.kadan.
Tea ɗin ne ta ji daɗin, kara wayar ta ji ta bude. ```The best day in my life was the day I married you
the best thing in my life is you
I cannot imagine a single day without you
i've said it once, and i'll say it again
I love you!!``` murmushi tayi tana jin saukar kalamansa kamar yadda sanyi yake sauka idan babu riga a jikinka, seriously wani bala'in kaunarsa take ji. *Love ... I want to hold you close to me and feel our hearts beat as one … forever ....* ta tura mishi, kashe wutar dakin Ummi tayi, sannan ta fita, ai kamar an basu damar amayar da abin da yake cikin ransu ne. A hankali abubuwan masu yawan gaske suka yi ta kankama a cikin daren nan, soyayyar junan su da suka gaza boyewa. Sai wurin Biyu na dare ta kwanta, Washi gari aka tashi da gaggaumin walima, wayyo Allah. Biki aka yi sosai, kafin zuwa dare an watse aka mai da amarya bangaren. Tunda ya sha ruwa kafin ya fita sallah isha, yake jin kamar ana rike mishi numfashinsa dakyar aka kai raka'ar karshe ya yanki jiki ya fadi yana aman jini. Rungumar shi Ra'is yayi."Abuturab!" Ya fada da ƙarfi dan dole domin sallah da aka yi sallamar shi a gaggauce aka tafi asibiti da shi, kafin kace me labari ya bazu a gidan Abuturab ya faɗa, dole aka yi arrested din duk wani Maid na ɓangaren Ummi domin daga ɓangaren ya wuce masalaci. Ita kanta Ummin asibiti suka nufa da Sa'ade da take kuka sosai, gashi da kyar take takawa, a asibitin suka kwana, Dole Washi gari aka tura su Abuja, jikin Sa'ade yayi sanyi sai kuka take, akwai gidan Sultan anan Abujan anan suka sauka. A can kuwa kwara bincike da yayi bincike ga azaba, dole yasa Jalilah fadar gaskiya ita ta saka mishi guba, domin tace zata fadi gaskiya ne a gaban Sultan domin yace ba zai tafi ba, Ra'is da Ummin. "Waye ya baki guba kika saka mishi.?" "Sarkin Malamai, Alhaji Sani, sai Sultanate, da Hajiya Suhailah, da Dauda Jama'a, da Sanata TJ, Dr Muhammad Ismail, sune suka biya domin sun tabbatar Aliyu zai gaje ka, a hannun shi na karbi kwangilar kashe Maina da Saraki, nice ba taka kan Saraki, nice na kashe Gajiya da jikanta, naso kashe Ummi ammada zaran ka kusancin inda take, ba zaka iya mata kome ba, domin akwai wasu irin mutane da suke kare ta, nice nayi ta bibiyar Aliyu tun yana matashi ina cutar da shi, domin Ummi ta yarda da ni, nice na kai musu hari lokacin da ya kwana gidan Ummyn Aymana." "Duk saboda me kika yi haka!" Dariya tayi sannan ta ce mishi. "Saboda ina sonka Sultan, idan na kashe yaran Ummi da ita shi ne Sultanate zata saka ma aure ni kuma na haifa yarimomin gobe , ai an bani guba na saka maka,amma Zuwairah ta tura sakon har zuwa wurin Ummi, karshe sakon ya fada hannu, na cewa Zuwairah matukar ta tona min asiri, sai na kashe D'anta." Magana marasa dadi, haka tayi ta fada. "Daga baya na fahimci karfin Ummi shi ne Abuturab, shi yasa na saka mishi guba ana bikin zaman shi cikakken ango, yayi murnan a lahira itama matar sa sai na kashe ta babu me kara haihuwar da namiji. Domin na fahimci ummi ko Badi'atul tafi kowacce mace daraja a cikin gidan nan, kamar yadda Uwata ta kare rayuwarta, tana bauta mata haka take son na kare rayuwata ina bauta mata, bayan nasha bibiyar rayuwar auren ku, ina ganin yadda kake haukata ta, tana kuka tana ihu so nake naji haka, sai akayi dacen muradun sauran mutanen yayi daidai da nawa." Shiru tayi kafin ta kwashe da dariya. "Kujeran da kake kai, da jinin matar ka, Dawlat khatoon da Danka Muhammad aka samar maka, sai da aka zuba da jinin mutanen da babu ruwan su, ka tambayi Sultanate, jinin mahaifinka, Jinin Dan uwanka Abdulsamad, jinin matar ka da jinin Yaran ka Maina da saraki, sai.jinin Mansurah domin taji kome, Ubanta Marwan yana jin haushin ka, ya sadaukarwa da yarsa, me kake son sani?".
".ku tafi da ita, sannan duk masu hannu a zakulo su, ita kuma ku b'atar da ita, yadda ba a kuma jin labarin ta ba, idan da hali mazan ma kusan yadda zaku yi da su. Sauran xan ji da su, wannan umarnina ne na bada. Kafin Aliyu ya dawo ina son a share min kowacce kazamta, Suhailah da Sultanate a kyale su." "An gama Sultan "
Kamar yadda ha bada umurnin haka, aka yi ta bin daya biyu ana kama su, tare da tattara su, har lagos. Babu abin da ya fi ciwo a dauke ka a tafi da kai duniyar da baka sani ba, a cikin kwantena aka saka su, Dan majalisar wakilai da na dokokin kasa, sai baffan Ummi, aka dura su a cikin kwantenan, sannan aka saka su a can ƙasar kwantanonin, aka share su da sunan za a kai kaya zuwa China ne.
**
Har dakin Sultanate Sultan ya shiga tana kwance. "me yasa kika sadaukar min da jinin Iyalina? Me yasa jinin Yarana da Matata? Kina haka ne don kar mulkin ya fita hannuna? Umma kin yi kuskure, Aliyu shi zai cigaba da da mulki uwarsa tana gefensa." Yayi magana me zafi, yana kuka kafin ya mike ya fita, wata rayuwar tana bukatar sadaukarwa. Dole ya hakura da kome. Yana fita daga cikin part dinsa, aka rataya mishi igiya, duk yadda yaso ya kwaci kansa, haka suka sakale shi. Suna gama fahimtar ya tashi aiki, jami'an tsaron masarautar suna musu kawanya, tare da haska su, Hajiya Suhailah da Dan uwanta. Kama su akayi, shi kuma Sultan Abdulrahman ya rasu, dama duk rigimar domin shi ne. Kafin kace me labarin ya cika masarautar.
***
Tunda ya farka yake rike da hannun ta, yana faɗin."Ummina ki min addu'a!" Ya fada cikin matsanancin azaba, hawaye na zuba mata ta ce mishi. "Abu Turab naga gawar Abubakar ban yi kuka ba, na ga gawar Umar ban yi kuka ba, Abu turab me yasa nake kuka akan ka? Me yasa nake kuka? Me yasa na rasa kwarin akan ka" fitar da ita nurse suka yi, tana ta kuka. Sa'ade kan, kira tayi daga Sokoto yau da safe aka da Inna suka tafi da ita, domin itama birkicewa tayi bata da lafiya. Babban tashin hankali shi ne dashen huhu za a mishi. Lokacin da za a tafi da Sa'ade, Abdulhakim shima yazo asibitin domin ciwon sa ya ci karfin shi, don haka yazo ganin likita ne yadda yadda ake rike-rike tsakanin Ummi da Sa'ade ba zata tafi ba. Tsayawa yayi ya ga har an saka ta a mota tana ihu. Shiga asibitin yayi ya ga likitansa, sannan ya nime jin matsalar Abuturab. "Ana niman huhun da za a saka mishi nan da awa ashirin da daya, idan babu zai daina jan numfashi ne karshe kuma kasan mutuwa ce!" "Tow ni saura kaso nawa na tsammanin zan rayu?" Bude takardan likitan yayi, ya ce mishi. "Ai kai Ikon Allah yake tare da kai, domin babu wani hope sai na kudirar Allah" murmushi yayi sannan ya ce. "Allah ya jinkirta min mutuwa ne, domin nayi aikin alkhairi, idan aka.cire nawa shi zai tashi!?" "What baka da hankali ne?" "Eh gaskiya bani da shi, a cire min nawa a saka mishi, albarkacin Sa'adatu,ina son ta amma ba zan tab'a ganin tana kuka akan abin da take ba, zan gayawa Iyayena ayi aikin kawai." Kafin kace me Abdul ya kira mahaifinsa ya gaya mishi, ya kuma kira Mahaifiyar sa, ya gaya mata. Domin da farko taki ya ce ko taso ko kar ta so mutuwa zai yi, gara abawa mabukata akan ya tafi haka. Kafin zuwa dare iyayen shi sun iso,yadda yake bayyana musu soyayyar Sa'adatu yasa basu ja ba, koda suka nufi Ummi da al'amarin,shiru tayi ta share hawayenta ta ce mishi. "Abdulhakim,kana da rayuwa bamu san me Allah ya hukunta ba, ka je kayi rayuwarka,ka bar shi idan Allah ya nufa zai tashi shi kenan" "a'a ni na yi niyya, mutuwa xan yi, shima kuma haka.kike son ya mutu? Waye zai saka Sa'ade a farincikin? Tunda ina da damar saka su su rayu dukkan su biyu a cire mishi suyi farincikin rayuwa kawai." Sai da Hajiya Daula ta saka baki, Ummi ta yarda, aka yi aikin, da ya dauki kwana guda ana abu daya, wani ikon Allah ana cire huhun Abdul aka yi wani hatsari, gayen ya mutu ba asan kowa na shi va, likitan Abdul ya nime izinin cire zuciyar gayen aka bashi domin shima ya rasu akan lokaci aka cire zuciyar shi da Huhun aka mai dawa Abdul tare da dashen zuciyar shi, Ko Allah zai saka ya rayu. Haja dukkan su aka turo su. A lokacin likitan ya tara su ya musu bayani, "Allah yana taimakawa masu taimakon al'umma ba tare da sun nime wani abu ba, irin fafutukar da yayi domin ya rayu shi ne naga gara a maida mishi organ dinsa da kuma sabon zuciya, Abdulhakim ua haifu domin ya hakura da farincikin sa yarinyar da yake so ta rayu, bai yi tunanin ya rayu koda wancan mutu ya same ta ba, burin sa suyi farincikin, nima kuma na bashi kwarin gwiwa ya rayu ya taya su farinciki yana da tashi rayuwar shi yasa har Allah ya kawo wancan mamacin domin dukkan su, su rayu shi ne Allah ya dauke rayuwar wancan mamacin Tsarki ya tabbata ga makagin halittun farko da na karshe ........ Shin Allah mun kusan kwashe shirgin mu🙄🤣
[14/07, 9:42 am] usmanlauratu71: 66..... Sosai maganar likitan ya kashewa Ummi jiki, koda yake shi Allah haka yake al'amarinsa. Suna cikin tattaunawar Ra'is ya shigo tare da mahaifinsa. "Sultanah Kwara fa tana ci da wuta!" D'ago kai tayi tana nazarin maganar kafin ta ce. "Ba maza ne a can?" Girgiza kai yayi cikin jimami ya ce mata. "Maza sun fadi." Mikewa tayi, a hankali tare da buga Kirjinta. "Maza sun fadi?" "Abdulrahman Dan Aliyu sulu gambari ya fadi?" Sunkuyar da kai yayi cikin damuwa, "Ra'is ka zauna da Abuturab muje" "Sultanah ai mun zo da jami'an tsaro zasu kula da lafiyar shi, domin sarki ne me jiran gado." Juyawa tayi cikin dauriya kamar zata fasa ihu ta cewa Likitan da su Hajiya Daulah. "Kuyi hakuri mijina kuma sarkin kwara ya rasu ba zan iya zama a nan ba." Gyada kai suka yi tare da mata ta'aziya. Kafin kace me asibitin har ya samu halartar yan jaridu, domin kuwa dayawan su, sun ji labarin rasuwar Sarkin kwara, sannan sun ji labari. Ai anyi dashen huhu a asibitin al'amarin sai ya zama babban al'amari. A private jet suka nufi kwara, kafin su isa manyan mutane da sarakunan daular Uthmaniya sun cika garin. Anyi sallah jana'izar karfe biyu na rana Alhamis. Ummi taci kuka sosai domin ba zaka gane lokacin da tayi kukan ba, sai dare da ta kwanta a lokacin ta nime kowa ya fita mata a daki, a sannan tayi kuka kamar me, tasan iyayenta ta zauna da su, tsawon shekaru sha shida amma sultan ta zauna da zauna na tsawon shekaru arba'in da tara, a wurin shi ta kare yarantarta. Yau kuma a ce babu shi. A bangaren Sultanate kuwa hauka ce bata yi ba, sai dai ta kullace mutane dayawa a ranta domin gani take kamar da gayya Badi'atul Noor ta kashe mata shi. Bayan kuwa tasan ba ita ba ce. Sai da aka yi addu'ar uku sannan, aka fara maganar gaskiya, a lokacin Wazir Dawood ya bayyana kansa, abin ya bawa kowa mamaki, domin koda aka tambaye shi hujjar boye kansa, nan ya shiga basu labarin binciken da yake da barazanar mutuwar da aka masa, sannan ya ce musu. "Zan fita daga ɓangaren Sultanate na hadu da Abdulkarim, yadda ya min ya sani fahimtar zai kashe ni, shi yasa ko da na fito bangaren sai na wuce bangaren Badi'atul Noor, ana na shiga motar Rumaisah aka fitar da ni, nawa motar kuma aka kunnata aka saka karfe a jikin birkin aka fitar da ita daga masarautar. " "Allah ya tsare na gaba, ina Abdulkarim din yake yanzu?" Inji Galadima. "Saudiyya ta kama shi da laifin safara da miyagun kwayoyi, kusan hukuncin kisa ce a can, a nan kuma zan iya cewa za ayi kuri'a ga masu ra'ayin shiga takarar neman kujerar sarautar masarautar nan sai su yi magana, amma ni ina tare da Abuturab ne!" Shiru kowa yayi sannan sauran emirate council suka ce. "Ko akwai me ra'ayin kujeran?" "Babu gaskiya nima ina bayan Abuturab!" Kafin wani lokaci, sun bada goyon bayansu, tare da cewa zasu Yi aiki da shi bilhakki da gaskiya.
***
Sokoto.
Rikice musu Sa'adatu tayi, har da zazzaɓin ta, ana cikin fama da ita ne, aka kira Allah yayiwa surukinta rasu, don ko da aka ce surukinta ya rasu, suma tayi domin gani take boye mata aka yi, bayan tafiyar su Sadeeq, ne Ummu Hafsah tayi ta rarrashinta, amma fir taki shiru dole sai da aka dauko Inna Laminde da suka dawo Umra, ita ta kai ta Maikulki, a can ne suka samu kanta, amma rigima da wanda ya kai kuka da wanda bai kai kuka ba, tow sunan su kuka ne. Tattara shirginta Inna tayi ta watsar, ta cigaba da harkan gabanta. Karshe da ta ishe ta, ta rufe da fada tana cewa. "Na rantse da Allah kika ishe ni sai kin koma can gidanki, domin wallahi ban ciki da rashin mutunci." "A dai tausaya mata, bana son tashin hankali, yarinyar tana cikin damuwa a kara mata da wani." Inji Malam Aminu, domin a duniya ya tsani wanda zai batawa Sa'adatu rai. Tsaki Inna tayi, bata kula shi ba.
***
Bayan sati biyu da musu aiki, Abdul kullum yana wurin Abuturab. Wadanda suka zama kamar abokai, wani abun alkhairin shi ne yadda suka manta da Sa'ade a tsakaninsu. Suka rungume kansu a matsayin musulmai dan uwan Muslim ne, haka ba karamin dadi yayi ba, shi kan Abdul imagine yake da yau gashi ga sarki, domin abin da ban mamaki, yadda rayuwar Abuturab din yake gudar dashi babu mulki babu izza, nutsuwa da mutumtaka. Sannan yadda yake waya da mutane. Musamman Mahaifiyarsa. Cikin girmamawa, tare da bata dukkansa. Shigowar likita yasa shi ajiye wayar da yake. "Dr ina son zuwa ga matata amma baka bani damar haka ba, haka zan ta zama?" "Your highness, muna kokarin ganin mun duba lafiyar ka ne sama da kome." Dariya Abdul yayi ya ce mishi. "Kasan dai ni surukinka ne domin Yayan Sa'ade nake, kana jin kunya ta mana!" Murmushin gefen baki yayi, ya ce mishi. " Tow zan duba yiwuwar na ji kunyar ka." Haka suka yi ta hira. Har likitan ya gama duba shi, ya duba Abdul ya ce musu. "nan da kwana uku zaku tafi!" "Harararsa Abuturab yayi ya ce mata. "I can't wait har kwana uku!" "Idan kaso sai ka tafi ai" dafe kansa yayi ya ce. "ka rena mana sarki fa Ra'is!" Tsaki Ra'is yayi ya ce mishi. "Waye Sarkin? Wannan dan iskan? Tir da samun banzan sarki irinsa " "ka iya bakin ka,domin sai mu hana ka shiga kwara." Abdul ya fada yana dariya, kiran Nazifi yayi ya gaya mishi cewa yana zuwa nan sokoto a tabbatar an kintsa gidansa na Maikulki, ya amsa mishi da tow.
-
Yau Asabar, tana daki kwance. Ta ji muryan Inna Laminde tana faɗin. "Sannu ku da zuwa sannunku" ta shigo daki ta dauki taburma tana faɗin. "Auta fito ga baki nan Kinyi" fitowa tayi tana sake baki, Rahilah da Husnah, da wani irin gudu suka rungume juna, suka kuma shige daki sai kuka da farincikin. Nan dai suka sha kukansu, sannan suka buge da hirar su. Suna cikin hiran Nazifi yazo da sakon Abuturab. Ai kuwa babu shiri su Inna suka tisa keyarta rakiyar Inna Larai, suka tafi gidanta. Ga kayan abinci da Nazif ya kawo. Don haka suka shiga aikin gyara kome har da Inna Larai, suna yi suna taɓa hira, abinci suka yi dake akwai kayan lambu har gidan Mai gari, aka kai. Inna Larai ta wuce da nasu, ita da kawayenta suka naje a falo ana hira. Bayan sun ci abinci sun huta suka shiga zaga cikin gidan. Anan suka ga hoton su. "Dama shi kuma aura?" Murmusawa tayi ta ce musu. "eh shi ne!" "Ina wancan mijin da aka ce kin kashe?" "Yana raye rabuwa muka yi!" "Allah Sarki." Nan suka dawo falo suka baje. Kafin suka kalli lokacin. "Zamu koma gidan Inna mu kwana sai jibi da safe zamu koma." "A'a ga part dina." "Idan mijin ki baya son baki fa?" Hararan su tayi tana faɗin. "Shi din Yarima ne, kin ga babu yadda zai ki baki " a kofar gidan kuwa an saka masu kula da gidan ne, har dare babu al'amar sa, kwanciyar su suka yi abin su, hankali kwance. Ranar lahadi suka kuma tashi da aiki. Domin Nazifi ya tashe shi bayan ya tambaye su me suke bukata, kayan snacks suka rubuta mishi da su dangin zobo. Aikuwa ya amsa ya tafi can sai gashi kaya niki-niki. Sannan ta ce ya kunna musu injin. Cake da Donut suka yi, Rahilah ce keyi tana basu labarin yadda dangin Mahaifiyar ta, suke sonta. Sai dai har lokacin nan, babu me maganar sonta da aure saboda nakasarta. Gara Husnah an tsaya da maganar aurensu, dan uwansa Muhsin zata aura. Sai nan take tambayar su Kubrah, Husnah ta ce tun gama waec basu kuma haduwa ba.
Haka suka cigaba da hira, bayan sun gama suka tafi wanka, dawowa tayi kitchen din daure da towel, domin ita ta bar musu dakinta ne, ta koma dakinsa tayi tayi wanka. Bata san da zuwansa ba, sai ji tayi yayi sama da ita. Ajiyar zuciya ta sauke tare da dafa hannun shi tana dariya. Bai tsaya da ita ko ina ba, sai dakinsa. Cikin wani irin kewarta yake tafiyar da ita. Kamar ya mai da ita cikinsa sai gashi daga ita har shi kuka suke, wani irin so yake mata, har ya samu nutsuwa, suka yi wanka a tare, yana goge wurin ciwonsa da ya dauko warkewa. Shafa wurin take tana kallon shi. "Kin ga aikin yayi kyau! Kin san waye ya bani huhunsa? Abdulhakim Sharif Hamidu." Tura kanta tayi gefen da babu ciwo tana murmushi. Haka suka shirya. A can main falo har da Abdul, wanda ya zauna kamar mara gaskiya, can sai Rahilah. Cike da mamaki suka yi ta kallon su, kafin suka shiga kitchen suna gulmar su. Basu ga Sa'ade ba, shi da kansa ya fito ya nufi dakin ta, ya dauke mata kaya masu kyau da babban mayafi, ya kawo mata ta shirya. Sannan suka fito a tare, kitchen ta shiga suka fara fito da abinci, Rahilah tana zolayarta. "Husnah ji yarinyar nan ashe shigewa suka yi wurin ita da mijinta" "da dai kun daina wannan maganar domin, Hammayo yana jin Yaren mu" zaro idanu suka yi. "Allah yasa ban ce kome ba" kallon Ra'is yayi cikin yarbanci ya ce. "Kasan yaran nan gulmar Lucky suke take gaya musu ina jin Yaren su." Kallon su yayi yana murmusawa, nan ya gayawa Abdul abin da yake faruwa da turanci. "Kai haba. " Nan suka gama shirya musu abinci, sannan suka bar wurin itama suka ci nasu a dakin su, sai murmushi take tana cin abincin. Kasa kasa Rahilah ya tab'a Husnah. Dariya suka mata, haka suka yi ta hira har suka gama da su Abdul zasu bar garin ne su fita da su Rahilah da Husnah, bayan Abuturab ya masu shatara na arzikn, nan gidan ya rage iya su biyu, da dare kuwa gidan su Inna suka nufa, basu dawo ba, sai dare. Suna dawowa suka wuce dakinsa. Anan suka yi wanka a tare. A wannan daren, sun gurji amarcinsu. Kamar me kafin suka kwanta.
Sai da suka shafe sati daya, sannan suka wuce Umra daga sokoton, Ummi tasan dalilin sa na guje guje sarautar ce baya kauna, kuma dan kaniyar shi dole haka zasu koma yaje ya amsa. Daga Umra yawon buɗe ido suka yi ta yi, sai da Sultanah Badi'atul Noor ta mishi barazanar matukar bai dawo ba, wallahi sai ta kwace Sa'ade idan ya dawo. Haka ya hakura suka koma gidan, manyan fadar ne suka hadu, aka yi meeting. Sai bayan sun gama meeting din sannan suka nufi Badi'atul Noor da zancen. "Mun yanke shawarar akan Abdulrashid, zamu bashi sarautar dan masanin kwara, sannan an bashi auren Latifah yar gidan Khamal, mun samu Sahalewan haka ne daga Sultan Aliyu Abdulrahman Dan Aliyu sulu gambari. Ita kuma Saratu mun bada ita ga Ra'is Dawood, mahaifinsa ya maida shi mishi muƙaminsa na Waziri." "Masha Allah Ubangiji ya taya su riko. An yi haka da kwana biyu, Abuturab ya dawo. Yana dawowa Ummi ta amshi Sa'ade ta ce zaka yi ta ganawa da manyan mutane na tsawon kwanaki ita kuma zaka bar min ita. Murmusawa yayi ya ce. "Duk abinda kika ce Queen Mother " daga nan suka ajiye zancen ta mishi tass akan maganar bada auren yan matan da yayi ba da izinin iyayen su ba. "Haka kawai su nime yi min katsalandar cikin rayuwar aurena " "dama akan waec din Sa'ade na biya mata za a mata, kana ganin zata iya karatu da renon ciki?" "Kai Ummina me ya kawo zancen cikin nan?" "Ai na gani ne, shi yasa. Me yasa baka damu da zancen mutuwar mahaifinka ba?" Murmushi yayi me ciwo. "Ummina, naga mutuwan yayu na biyu akan Idanuna, sannan duk sun mutu ne domin Abba, idan nace ban damu ba nayi karya. Amma idan na barwa Allah zai gafarta musu, rike abin da aka maka bai janyo kome sai gaba da kullatar juna, shi yasa naki damuwa da mutuwar, Allah ya mishi rahama." "Amin Ya Allah, Ubangiji yasa mu dace."
Bayan sati Uku aka yi bikin bashi sarauta, mutane dayawa sun zo har da su Inna. Dake basu san ana boye cikin Sa'aden ba ne Inna take tambayarta dama ciki da ita, shiru tayi, kafin kace me ai kuwa labarin ya karade ko ina, sai dai kuma a daren ranar zazzaɓi ya rufe ta, sai da aka saka mata ruwa. Tun daga ranar ta fara laulayi, don har su Inna suka bar garin bata cikin hayacinta. Haka har lokacin zana Jamb yayi, shima Alfarman aka nima mata, mijinta sarki kuma ya tafi da kansa ya zana mata, domin tausayin matarsa. Kaf dangi aka daurawa cikin nan kauna, Addu'a da rubutu babu wanda Ummi bata ba, har saukar Alqur'ani tasa aka mata akan cikin, da wahala ya ishe ta, sai ta Sa'ade na kuka wiwi,.ita a cire cikin wata biyar ta gaji wallahi. Dakyar Ummi suke lallabata. Kullum Zakiyyah da Rumaisah tare da Ummyn Aymana suna hanya, sai da ta cika wata bakwai cif ta daina laulayi, wanda yayi dai-dai da bikin Abdul da Rahilah, yaushe aka kulla, amma tabbas sun je har sokoto aka daura auren, aka dauko amarya daga yola, hannu bibbiyu Hajiya Ita amshi surukarta. A bakin Hajiya Daulah take jin labarin rabuwar Abdul da Sophia, tana can canada. An sha biki sosai. Kafin su bar garin Abuturab ya samu Dr Sharif inda ya nemi Alfarman ya dawo da Hajiya Daula, kuma be ki ba, haka ya dawo da ita..
---
Jingine da allon gado take, kafaffunta sun kumbura, kallon cikin wata takwas din da yayi turtsitsi yayi ya shafa cikin yana kallon yadda cikin ke motsi kamar zasu fito. "Sannu kinji" tun a scanner ake cewa biyu ne, kuma duk maza ne. Juyar da kai tayi tana jin azaba kawai. Gyara kafarta tayi zata sauka ya rike ta, "shaaaaaa!" Ruwa ya faso mata, komawa tayi ta zauna a jikin gadon. A rude ya riko hannunta. Zare hannunta tayi, tana nuna mishi waya ya kira Ummi. Ai bai kula waya ba, ya fita da sauri. A wannan yanayin ita kawai tasan ba su zasu cire mata ciwon ba, amma kuma kiran ummin zai taimaka mata. Yadda take zaune kamar ance ta ware kafarta, sai ga kan Yaro ya sako kai. Rike gadon tayi, Allah da ikonsa ya bata sa'ar Nishi sai ga ɗan kamar an zaro shi. Daidai shigowar su, "bani kayan haihuwar " Ummi ta fada, tana sauke Babyn tana mishi Addu'a. Sannan ta ajiye shi. Sake wani yunkurin tayi, sai ga Babyn nan ya kuma fitowa da mabiyansa, shima dauka tayi ta nema mishi tsarin shaidan. Sannan ta ajiye babyn, yanke cibiyar tayi ta nad'e su. Sake yunkurin tayi wani babyn ya fado yar karama da ita. "Allah sarki sun mata wayo" ta dauke babyn ta mata Addu'oin itama. Sannan ta jijjiga cikin sa'aden jini ya zuba, kafin ta kaita banɗaki ta zaunar da ita ta kuma zubar jini. Tana fitowa ta samu yana ta kiran su Ummyn. Tana zuwa domin tana Asibitin da take aiki da su alluran. Ummi ta gyara Uwar da yaran baki ɗaya, Ummyn Aymana da wata Dr suka zo, aka mata allura aka duba lafiyar yaran, Ummi ya kwashe su sai part dinta, can ɗakinta ta kaita, bayan ta sake mata wanka domin wanka sosai ta mata, Zuwairah ta kawo mata kunun kanwa da farfesun Bindin saniya. Tasha ta kwanta.
Kafin wani lokaci labarin haihuwar ya karade ko ina, sai gashi, ana ta zuwa Barka.
Inna daga Maikulki suka zo, ana jibi suna. Da yayun sa'ade, an yi hidima sosai irinta .manyan mutane, Yaran sun ci sunan Abubakar (Hassan sun bar mishi maina) Umar(Hussain sun bar mishi saraki) Dawlat khatoon (Gambo suna kiranta Amira) an sha hidima sosai. Domin jegon har da Sultan Abuturab ake yinsa domin cewa yake shima ya haihu ne, satin Inna Laminde biyu ta koma don duk sun tafi sun barta. A wannan aikin hajjin Bana Abdul iya biyawa Inna da Malam Aminu aikin hajji, domin yayi alƙawari ne ya sauke. Watan su Sa'ade uku ta koma bangarenta bayan Ummi ta gyara ta ciki da waje. Zo kusa rawan kai da rawan jiki. Sai da suka cika wata hudu har sun fara zama suka tafi Sokoto wanda yazo daidai da bikin Husnah. Anyi bikin da sati daya Rahilah ta haihu, Abin mamaki sunan Sultanah Badi'atul Noor aka saka. Takanas tazo sunan da kayan takwaran ta.
Sai bikin Yusuf da aka yi a lokacin Allah ya bawa Aunty Ummi ciki.
-----
A can kwara ma buki aka yi sosai, sannan aka bawa Kowa sarautar da ta dace da shi, Ra'is da Abdulrashid. Sultanate tana kwance babu abinda ba a mata, sai dai tana wulakance domin tana gani babu yadda ta ita, sai takaici da bakin ciki.
Badi'atul Noor ita ta amshi kome abin da yake tsoro, gashi ya faru sauran matan Sultan Abdulrahman, tunda aka raba gado kowa ta kama gabanta. Yaran su Abuturab ya dauke nauyin su har da na Yayunsa.
****
Bayan shekara biyar, bikin Yaye daliban babban Jami'ar Jos take, a cikin har da Fulani Sa'adatu Aminu,matar Sultan Aliyu, cikin ikon Allah ta fito da First class, a bangaren Jarida, sai tafa mata ake, idan ja ganta sai ta burge ka, yarinya me ji da kuruciya ga Yaranta nan biyar ta kuma haihuwar wasu Yara biyu. Bayan an gama raba musu kyautattaka. Suka bar makarantar. Har zuwa lokacin Allah ya bai bude mata baki ba, Ƴaranta da ta haifa na baya mace da namiji. Macen sunan Innarta ce ana kiranta da Qurratul Ayn, namijin Amir ake kiransa. Tunda suka shiga private jet, Abuturab sai Binta da idanun yake. Karshe da ta zauna kusa da shi ya ce mata.."Kin san Allah, london zamu wuce na dasa miki Ummina, domin naga sai wani Yanga kike min" juya kanta tayi tana dariya.
***
Malam Aminu duniya sabuwa, sai gashi har da karo aure, inda ya hadu da wata munafukan bazawara, ta hada shi da cutar sanyi. Dama can Inna ta yafe shi. Ai haka ya hana kowa sakat, abin haushin da dariya ya gogawa Inna Larai, haka suke ta jinya a tare. "Allah ya tsinewa, Jummala, munafuka na gode da ba sida ta saka.min ba"
"Babu tsinuwar da zai ka mata, kwadayi da jarabarka"
**
Husnah ta haihu da namiji, haka ma Aunty Ummy ta haihu itama da namiji, Matar Yusuf kuma Y'a mace, lokacin Sa'ade suna London ganin likitan kunne ko za a dace. Amma har zuwa lokacin ba A dace ba.
ALHAMDULILLAHI.
(Kun gane ba kome kake so zaka samu ba, Matsalar sa'ade na bar shi a haka ne, tana ji tana gani magana ce Allah bai nufa tayi ba, idan muka ce lallai sai tayi magana tow kuwa mun ja da ikon Allah, Don Allah ayi hakuri Haka na tsara labarin ba zata tab'a magana ba, sai dai kuma she achieve more successful abubuwa, ta samu miji me sonta, Dangin mijin nasonta Mahaifiyar miji na sonta. Alhamdulillahi, Don haka idan kuna da interesting kuyi following din Karfe dukka karfe ne, Na gode taku har kullum Ramlat Abdulrahman Manga Mai_Dambun gayu.)