← Book details Sanadin Kawa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 3 OF 17

BABI NA GOMA SHA HUDU

Sanadin Kawa Part 1 Complete Hausa Novel · about 13 min read

Duk yanda Fatima ta so hana Husnah su je gidan warce ta kira da kawarta kin saurarenta tayi haka ta tilastata sai da suka hau mota suka dau hanyar gidan kawarta da suka hadu da a IG me suna Sadiya, Allah ya so ta fito da kudin da Umar ya bata daxu da safe, Tafiyar kusan minti talatin da wani abu suka yi kusa da cikin garin Abuja kafin su iso gidan, sun dade bakin gate don sai da mai gadi yaje ya sanar da xuwansu kafin su shiga gidan, tunda Fatima taga irin kallon da yan gidan ke ma Husnah jikinta yyi sanyi kana gani kasan sun gaji da xuwanta, Sadiyar ma sama sama ta kula su bayan ta fito kafin ta kawo masu ruwa da kayan flour, tuni Husnah ta sauka kasa ta fara cin abubuwan dake gabansu, Fatima ta ki cin komai don duk ranta ya gama baci, Sadiya dai na xaune tana kallo a Tv don duk yan gidan da suka tarar a parlor sun bar parlorn, Husnah ta cika baki da cake ta ce "Kawata mun xo neman wata alfarma ne gun ki don Allah...." Sadiya ta kalleta tace "Toh ina ji" Husnah ta kora cake din da drink ta mike tace "Toh ina xa mu je muyi maganan?" Tashi Sadiya tayi ta fita balcony Husnah ta bi ta tana kashe ma Fatima da ta hade rai ido, bayan sun fita nan ta gaya mata abinda yasa suka xo, har da risinawarta tana roko, Sadiya da ta d'an yi jim tace "Har da kaya?" Husnah tace "Hoto kawai xata yi wallahi" Sadiya tace "Shkkn ba matsala" amma kana jin ynda tayi furucin kasan takaici ne ya isheta, dakin mai aikinsu ta kai su, Husnah na rike da hannun fatima da taki sake fuska tana bin ko ina na dakin da kallo tana cewa maa sha Allah, Allah ka bamu irin haka, suna ta xaune dakin sai ga Sadiyar ta shigo da kaya hannunta da abun kwalliya, nan ta mika ma Fatima kaya na Riga da skirt da kayan kwalliya da mayafi, ta juya xata fita Husnah tace "Ki yi hakuri ki d'an ara mana wayar ki xai fi kyan hoton kuma xa mu yi wasu a nan" Sadiyar ta kalleta sannan ta xauna dakin tace "Toh idan kun gama sai in mata" har Husnah ta gama yi ma Fatima kwalliyar kallonsu Sadiya take, a xuciyarta kuma addu'ar shiriya da Allah ya raba su da karya take barin Fatima da ta yi mata kyau sosai, ba laifi Husnah ta iya make up sosai don ba karamin kyau Fatima tayi ba duk da bata yrda ta cika mata kwalliyar ba, Sai washe baki Husnah take ganin yanda ta fito da kawartata, ta juya ta kalli Sadiya tace "Toh dauketa hoton kawata" nan Sadiya ta mike don daukar Fatima hoton, sosai Fatima tayi mata kyau sai dai taki sakin fuska, kusan biyar ta dauketa a daki, Husnah tace "To ya isa haka mu je waje" tana rike da hannun fatima suka fito compound, nan ma sadiya ta dinga mata hotunan, Husnah na nuna masu background, sae jaraba take wai fatima ta tsaya dososo taki murmushi, Fatima ta galla mata harara tace "Ke kar fa ki dameni wannan din da nake fa, ni na ma gaji ki rabu dani" ba shiri Husnah ta ja bakinta tayi shiru, Sadiya dake ta kallonsu ta d'an yi murmushi tace "Toh wannan na karshen dai ki daure ko dariya kiyi xae yi kyau sosai" Fatima bata san lkcn da tayi dariyar ba a haka Sadiya ta dauketa Wanda duk hotunan babu Wanda ya kai sa kyau, Husnah sae murna take, a nan kuma aka gama daukar hotunan suka koma ciki Sadiya ta tura masu duk hotunan a wayar Fatima, Fatima ta mayar da kayanta ta linke na Sadiya ta ajiye tana kallonta tace "Sister nagode sosai" Sadiya tace "A'a ki tafi da su na bar maki" nan Husnah ta canxa fuska sae dae bata ce komai ba, sai da suka tashi tafiya tace "To ni baki bani kayan ba Sadiya ko na maki wani laifi ne" Sadiya ta yi murmushi tace "Bari in dubo maki to" daga haka ta tafi dakinta ta dauko mata wani kayan ta bata, Husnah ta dinga godiya har da durkusawa tana washe baki, Fatima da takaici ya isheta ta fice daga dakin suna biye da ita, a bakin gate Sadiya ta basu dubu daya kudin mota Fatima ta mata godiya ta fita ta bar Husnah dake ta godiya kamar wata marokiya ta dau hanyar titi, da gudu Husnah ta kamota tace "Kinga masu kirki koh, kuma ace duk sati baxan dinga xuwa nan ba, ko don irin cimarsu ni bbu Wanda ya isa ya hanani xuwa wllh" Fatima dai bata tanka ta ba har suka shiga mota xa su koma Suleja. Sai kusan karfe biyar da rabi suka isa gidansu Husnah, Fatima da duk hankalinta ya gama tashi tace "Kinga baxan shiga ba xan samu adaidaita daga nan in wuce gida nasan Ammi na can tana jirana na dde sosai, sai mun yi waya" Husnah ta rikota tace "Toh amma banda masa bakar magana plss, ki kara editing hotunan ki tura masa masu shegen kyan ciki plsss ki rufa mana asiri mu ma mu faso gari kwanan nan" Fatima tace "Naji ni dai sai mun yi waya" daga haka ta wuce da sauri ba tare da ta damu da dubu dayan da aka basu da Husnah ta boye a jaka tun daxu ba, adaidaita ta samu ya kaita har kofar gida, Ammi dake tuka tuwo tana xaune kan kujera kusa da coal pot bata ko amsa sallamarta ba, a sanyaye ta durkusa nesa da ita tace "Don Allah don annabi Ammi kiyi hakuri nasan na dde sosai, kinga dambu tace in tsaya in koya mata bata iya ba kuma shi xata yi, shine kawai na tsaya na girka mata, kiyi hakuri Ammina" Ammi ta kalleta tace "Toh ni na ce maki wani abu ne Fatima" Fatima tayi shiru bata ce komai ba, Bude ledan da ta shigo da tayi ta fiddo kayan ciki da mayafi tace "Gashi Ammi ta bani, nace ta bari na gode amma ta ki saurarana" Ammi tace "Allah ya saka da alkhairi" Fatima ta sauke ajiyar xuciya a hankali tace "Ameen" sannan ta mike ta shiga cikin dakinsu tana murmushi. Ita ta karasa sauran aikin gidan Ummi na taya ta, suna gamawa ta daura ruwan wanka ta koma daki, sae kusan shidda ta fito tayi wankan ta daura alwala ta shiga daki, Ta gama shafe shafenta ta saka doguwar riga ta dau wayarta ta hau saman gado ta bude data, IG ta shiga ta duba DM dinsu da Elbash taga har lkcn bai ce komai ba, ta d'an yi jim, sai kuma ta tura masa "Are you ready to listen to why I followed you and went ahead to ping you?" Daga haka ta fita ta koma WhatsApp, sai da taji kiran sllh ta kashe data ta mike, tana idar da sllh tayi azkar dinta sannan ta fita xuwa dakin Ammi, Ammi dake xaune Da Ummi da Yusuf suna cin abinci ta kalleta, xaunawa tayi gefen Ummi, Ammi dai bata ce mata komai ba tana jiran ta ji me ya kawota sanin bata shigowa sae idan abu ya kawota, Ita kanta she was uncomfortable can kuma ta mike xatah fita Ammi tace "Kin ci abincin ne?" Fatima ta kalleta tace "Shi xan je in ci ynxu" Ammi dai bata ce mata komai ba har ta fita, ta rasa irin yar tata, bata taba ganin yar da ke kin sakewa da uwarta kamar Fatima ba, Fatima ta debi tuwo kadan da miyar kubewa ta saka cokali ta wuce daki, har ranta ta tsani cin tuwo, ta gama jagwalgwa shi ta tura gefe ta dau wayarta ta bude datan ta, message din Elbash ta gani yace "I am not interested" tsuru tayi tana kallon message din, can tayi murmushi tace "is that so??" ya bude message din yaki cewa komai, bayan kusan minti sha biyar tace "u knw something I already knew about you even before chatting u up?" bayan wani lkci yace "That's ur cup of tea..."
[9/18, 8:37 AM] Abue Saleh Kurami: KUNDIN HASKE
Haske Writer's Association
(Home of Experts and perfect Writer's)
*SANADIN K'AWA*
*khaleesat Haiydar*
"And yours also" ta mayar masa tana murguda baki, har xata kashe data ranta a bace sai ga wani message din nasa "Where did you leave" xaro ido tayi, can tayi murmushi tace "Abuja" yace "Where in Abuja" dariya tayi ta tura masa da cewa "That's my cup of tea alone" ga mamakinta sai yace "Hmm" ta lumshe ido ta bude a hankali ta rasa abinda xata ce masa, can tace "Though it won't be of any use to you I live at Maitama, bye.... catch ya later, I've gat to do better things now" daga haka ta kashe data ta jona wayarta da caji ta fita tayi alwala ta dawo tayi isha ta kwanta ranta fari fes. Washegari tana idar da sllhn asuba ta fita don hura charcoal, ta daura ma su Ummi ruwan wanka, kafin karfe bakwai kaninta sun bar gidan xuwa islamiyya, Tana wanke kwanukan da aka yi amfani da su Ammi da ta fito daga daki rike da tsintsiyar da ta share dakinta tace "Yau baxa ki islamiyyar bane ke?" Ta hade rai tace "Ammi baxan je ba, ko na je malam Suraj cewa xai yi sai na koyar yau" Ammi bata ce komai ba ta kwashe kayan su Yusuf dake kan igiya ta wuce daki, Fatima ta gama wanke wanken ta shiga wanka bayan ta daura ruwan da ta daura a coal, doguwar Riga ta sa ta saka hula, duk da hali na rashi dake tare da su hakan bai hanata tsafta ba, ko da yake kusan gun Amminsu suka gado tsaftar, Komai na gidan xaka gansa tsaf tsaf, sutirarsu kuwa ko wasu masu kudin sai haka don tsaf xaka gani, Fatima bata taba sa kayan da bai da guga hakan yasa ko ina taje ake sha'awarta ta fi da yawa daga kawayen da take bi nesa ba kusa ba, shayi ta sha bata kalli bread din ba sbda bata damu da shi ba, ta dau wayarta ta hau net, murmushi tayi ta kwanta saman gado tana kallon message din Elbash "I won't ask for this again, can I see u facially" gun tura photo tayi tap ta shiga gallery dinta daya daga hotunan da Sadiya tayi mata ta xaba, tsaye take kusa da flowers a gefen parking space, full tayi mata hoton Wanda hakan ya fito da ainahin shape dinta da tsayinta, I don't want to waste time describing Fatima but just get this, she is a damsel, she's more den beautiful, komai na mahafiyarta da dauka, tsayin haske kyau, gashi beauty point, tsayin hanci lips masu daukar hankali, infact everything, ga shegen farin jini sai dai kasancewar locality din arean da suke ba lallai a gano value din kyan nata ba, shi yasa Umar ke bala'in sonta, emojin love tayi amfani da ta rufe fuskarta ta tura masa hoton, har xata ajiye wayar ta fita da cup din da ta sha tea sai ga message dinsa yace "What's this?" Ta mayar masa da cewa "What u asked for" yace "I asked to see you facially, I don't get d shape u are showing me" dariya sosai tayi tace "Ohh nan hankalinka ya tafi kenan, anyway that's d least I can do, I can't send less or more than this take it or leave it" yace "Ok" tace "Yeah" yace "Send me ur digit" wani uban tsalle ta doka hannunta na rawa tace "Send urs..." Turo mata special digits dinsa yyi, ta wara ido tana kallon special number din tace "I will giv u a call when am done with what I am doing" daga haka ta k
ashe datan ta, tana dariya tace "Alhmdllh" sai can kusan karfe sha daya tayi dialing numbers bayan ta fita ta siya card din dari biyar da sauran kudin da Umar ya bata, wayar na fara ring gabanta ya fadi sosai tana jiran jin kalan muryar da xata ji, sai da ya kusan katse wa taji an daga, tsit tayi xuciyarta na bugawa, daga daya bangaren cikin wani sanyayyen murya taji ance "Who is on the line?" Da kyar tayi gathering courage tace "Who you gave ur digit" katse wayar taji yyi ta kalli screen din da sauri, sai ga kiransa ya shigo, ta fashe da dariya tayi mai isarta sannan tayi shiru ta daga kiran ta kai kunne, kafin yace komai tace "I dont want you to burn ur airtime?" Yace "Did I tell u I don't have airtime" tace "Of course that was why u gave me ur digit I guess" yace "Where did u stay at maitama?" Ta langwabar da kai tace "A stranger I met on media is asking where I live, And foolishly I will then go ahead to tell him, sorry I have sense Mr stranger..." Yace "Happy you are not foolish" tace "So where do u live also?" yace "Abuja" xaro ido tayi tace "Really" yyi shiru, tace "Ok, where in Abuja?" Yace "Baki kai wannan matsayin ba a duniya" yar dariya tayi tace "Ohk then, I have important things to do now Elbasheer, bye" daga haka ta katse wayar. Can yamma tana gyaran daki wayarta ya fara ring ta nufi gun wayar da sauri taga Umar ne, hade rai tayi sosai da kamar baxata dauka ba sai kuma ta dauka, ta xauna gefen katifa ta amsa sallamarsa, yace "How you feeling Fatima?" Tace "Na ji sauki" yace "I called daxu baki kusa koh?" Tace "Eh" yace "Ohk, dama kan maganar da muka yi was it a month ago ne?" Tace "Wani magana?" Yace "Magabata na da xan turo, Ammi tayi ma su kawu Jibril magana koh?" Mikewa tayi da sauri tace "Ni nace maka basa nan fa, wai saurin me kke ne haka, Toh ba su dawo ba, da sun dawo ai zan sanar maka" shiru ya d'an yi kafin yace "Toh shkkn" ta murguda baki ta koma ta xauna, yace "Shkkn, anjima xa mu yi waya dear" tace "tohm" daga haka ta katse wayar ta jefar kan katifar ta ci gaba da abinda take, gaba daya taji ko daura mata Umar aka yi a kafa Ita baxa ta iya aurensa sa ba, har ranta ta tsane sa, fita tayi bayan ta gama duk da ranan bata yi niyyar girki ba amma haka Ammi tayi instructing dinta tayi, tana kumbure kumbure take ta aiki har ta gama kusan karfe shidda tayi wanka da alwala ta shiga daki, ta gama shiryawa ta dau wayarta sakin baki tayi ganin miss call din Elbash, murmushi tayi ta shiga kiransa, bai daga ba. Ta idar da sllhn Magrib wayarta ya fara ring ta mike ta dauka, kiran Elbash ta gani, ta daga a hankali ta kai kunne, sallama tayi ya amsa daga daya bangaren, ta langwabar da kai tace "I saw ur miss call" yace "I want to meet with you tomorrow" xaro ido tayi tace "Why?" Yace "Yeah" tayi murmushi tace "That's awful, hw will I meet with a stranger" yace "Am I still a stranger?" Mamaki ne ya cikata tace "Sure, we met just the day before yesterday" yace "Just send me ur address" yar dariya tayi tace "Noo of course nasan ko d'an yankan kai ne kai ko kidnapper" yace "Ni din?" Tace "Ehh" yace "Ok" daga haka ya katse wayar, tsura ma wayar ido tayi ta xauna gefen gado jikinta yyi sanyi, is this not an opportunity, da kansa fa yyi requesting su hadu, but why all of a sudden bayan har ynxu ko jituwa basu fara ba, duk tayi confuse, number Husnah tayi dialing bbu bata lkci da daga, bata jira ta fara mata surutun ta mara kai ba ta fara mata bayanin komai, Husnah tace "what? Gani nan tahowa yanxun nn" daga haka ta katse wayar, Fatima da ta kasa rufe baki a xuciyarta tace ji min yarinyar nan, da daddaren nan, da sauri ta sake kiranta don bata son Ammi ta xargi komai, tana dagawa tace "Ke idan kin xo plss ki kirani in fito kinsan halin Ammi" Husnah tace "Toh" ta katse wayar, Ko minti biyar ba ayi ba sai ga kiran Umar, Fatima ta tsuke fuska, Sai da ya kusa katsewa ta daga, bayan sun gaisa kamr ana tilastata yace "Xan taho ne ya sa na kira ki dear" da sauri tace "Ni wllh tun yamma nake aiki Allah ma ya gani na gaji" a hankali yace "Plss dear... Ba ddewa zan yi ba, sako xan baki in wuce" ta tabe baki tace "Allah ya kai mu" daga haka ta katse wayar ta ja tsaki.
[9/18, 8:37 AM] Abue Saleh Kurami: KUNDIN HASKE
Haske Writer's Association
(Home of Experts and perfect Writer's)
*SANADIN K'AWA*
*khaleesat Haiydar*
Chapter 3 · 0% Book details