Part din mai gidan ta ta wuce direct, ta
Safiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 378 min read
bude kofa ta shiga ta tarar da shi yana aiki
akan computer, ya juyo yana kallon ta sai
kuma yayi murmushi tare da daga hannun
sa yace "na daina, na daina" ya san ta
saka dokar cewa dare lokacin iyali ne da
hutawa da kuma ibada, duk wani abu da
za'a yi na neman duniya to ayi shi da rana.
Amma sau da yawa ba bin dokar tata yake
yi ba sai dai in ta kama shi ya bada hakuri.
Bata kula shi ba dan abinda yake ranta ya
fi wannan, sai ta wuce kan lounging chair
din da take dakin ta zauna, yayi wheeling
study chair din tasa zuwa gabanta ya
tsaya yana kallon ta. Da karyayyiyar
murya tace "dazu naji kace Gidado bashi
da lafiya, me yake damun sa?" Abba ya
dan yi mata murmushi "he will be okay
kamar yadda na gaya miki, Rigima ce da
taurin kai da ya dorawa kansa kwanan
nan" ta gyada kai tana kara fuskantar inda
maganar ta saka gaba "akan Safiyya ne
ko?" Abba yace "yes. Kamar sun samu matsala ne I think. He told me wai sun rabu tunda bama so. Ita ma kuma wai babanta baya so. Amma na san fada
kawai yake yi ba wai rabuwar suka yi ba"
ta danyi murmushi, ita taga abinda ta gani
yanzu a dakin sa.
Ya danyi gyaran murya sannan with
serious voice yace "kince zamu yi
magana akan Muhammad. Wacce
magana ce?" Ta danyi ajjiyar zuciya tare
da cewa "kai ma ka fadi haka ai. You first"
ya sauke ajiyar zuciya sannan yace
"yaron nan ba zai hakura da yarinyar can
Safiyya ba. I think we need to look into
other options than rabasu da karfi. A
shawarce zan saka a yi min bincike akan
yarinyar, sannan zan je inga mahaifinta inji
shi menene take dinsa on all this tunda
Gidado yace min shima ya hana yarinyar
haduwa da shi. Ma'ana yasan abinda ake
ciki kenan. Amma sai mun fara bincike
akan yarinyar dan a lot of things don't add
up about her",
Mama ta dan girgiza kanta a hankali tace
'"ba ka bukatar yin bincike, I have got all
the informations we need about yarinyar"
yayi shiru yana kallon ta da mamaki "how?
When?" Ya tambaya dan ya san bata boye
masa komai. Tace "dazu nayi magana da
Safina, akan zancen komawarta gidan mijinta tunda jikin su duk yayi sauki. She told me wadansu maganganu da suka razana ni sosai" ta fada da karyayyiyar zuciya, ya bata rai, baya son bacin ran
matar ta sa ko kadan, yace "wadanne maganganu kenan?" Ta girgiza kai "maganganun basu da muhimmanci. Surikar muce still.
But she is not the right choiceor Gidado."
Ta danyi shiru kamar yadda shima yayi
yana kokarin fahimtar ta, sai kuma ta
cigaba "sanda Hajjo tazo garin nan tazo yi
mana murnar bikin su Muhammad ta ga
pictures she told me ta san Safina, she
told me they are family friends, and dazu
maganar da Safina ta gaya min akan
Safiyya ta daga min hankali har na fara
mummunan tunani akan Gidado so l
called Hajjo and asked her a favor, nace
dan Allah ta gaya min duk abinda ta sani a
kan Safiyya step sister din Safina. Farko
kamar ba zata fada min ba, sai da ta
fahimci hankali na a tashe yake kuma na
gaya mata abinda yake tsakanin Gidado
da Safiyya da kuma abinda Safina tace
min akan safiyyan wanda har ya tayar min
da hankali nake neman gaskiyar lamari,
Sai ta saka nayi mata alkawarin ba zan
gaya wa kowa a duniya ba, har kai, sai da
nayi mata wannan alkawarin sannan ta gaya min komai".
Ga mamakin sa sai yaga hawaye yana bin
fuskarta, ta saka hannu ta share sannan
tace masa "na riga nayi mata alkawari, bana son in karya alkawarin da nayi mata. Amma abinda zan gaya maka shine yarinyar nan Safiyya ta sha wahalar da
ban taba gani ko jin labarin wadda ta sha
irin ta ba. Ta fuskanci kaddara mai zafi. Kaddara kuma irin wadda zata iya fadawa a kan kowacce ya mace" ta danyi shiru still idonta yana kasa sannan ta sake cewa
"ni mace ce, kuma ni uwa ce, watakila ku maza ba lallai ku fahimta ba amma ni na fahimta. Tunda har Allah ya sarke zaren kaddarar Gidado da na Safiyya har yanzu ta zamanto ita ce farin cikin sa, ni na amine kaje ka nema masa auren Safiyya ko dan mu samu ladan yarinyar nan sannan kuma mu samar da farin ciki ga dan mu".
Ya dan girgiza kai cikin mamakin maganar
ta yace "amma ba kya ganin this will be
too much for him? I mean mata biyu at his
young age? Kuma mata biyun ma
makusantan juna? Zai fuskanci crises
sosai a gidan sa" ta danyi murmushi
"wannan kuma zabin sane, zama da su
gabakidaya ko aka sin hakan zabin sa ne, mu namu shine mu sauke nauvin sa da Allah ya dora mana sannan muyi musu addu'a baki daya".
Tana gama fadar haka ta mike ta cire hijab
din jikinta ta rataye tare da hawa kan gado
ta fara gabatar da addu'ar kwanciya
bacci. Ya bita da kallo abubuwa da yawa
suna yawo a cikin ransa. Duk da cewa
shima tun dazu zuciyar sa ta fara karkata
zuwa da wannan barin amma bai dauka
tata zata chanja akala a lokaci daya ba.
Me Safina tace mata? Me kawarta Hajjo
tace mata? Baya son ya matsa mata har
ta gaya masa tunda tace alkawari tayi
cewa ba zata fada wa kowa ba har shi. Shi
kuma zai so matarsa ta kasance mai cika
alkawari.
Sai dai in dai har zai aikata abinda ta
ambata na aurawa Muhammad Safiyya, to
dole ne sai ya san abinda taki gaya masa
din, ko da kuwa ba'a wajenta ba ne ba.
Da maganar ya kwana da ita kuma ya
tashi, Da ita yaje office da ita kuma ya
tashi, Wannan ya sa daga office din bai
tafi gida ba sai ya gayawa driver dinsa ya
kai shi gidan Alhaji Adam Muhammad, Ya
san address din gidan ne sanda yana
bincike game da Safina lokacin auren
Muhammad. Mai gadi ya bude musu cikin sauri saboda gain kamalar sa, sai kuma ya tsaya yana kallon sa bayan ya fito fuskar sa tana nuna alamar ya gane shi,
ko kuma ace ya gane waye shi.
Ya kara gaishe shi cikin girmamawa sai ya
gaya masa cewa gurin mai gidan yazo.
Take ya ga fuskar sa ta dan saura cikin
yanayin jimami sannan yace "baya jin dadi
kam. Bashi da lafiya. Yau kuma kamar jikin
ya matsanta masa dan tun safe babu
wanda aka bari ya shiga gurinsa. Amma
bara in fada a cikin gidan na san zasu san
abinda za'a y" ya fada yana dosar
Hussein da ya fito daga cikin gida da key
din mota a hannun sa daga alama fita zai
yi, suka dan yi magana da Hussain sai
kuma Hussain din ya kalli Abba sannan ya
koma cikin gida da sauri.
Sai Abba yaji babu dadi a ransa, tunda
bashi da lafiya bai kamata ya zo ya dame
shi ba, Wannan ya sa ya sake kiran mai
gadin ya gaya masa "zan koma kawai.
Allah ya bashi lafiya, Zan dawo gobe ko jibi insha Allah" mai gadin ya gyada kai cikin fahimta sannan
cikin girmama wa yace "zan gaya masa
insha Allah, da zarar na samu ganin sa zan gaya masa" driver din Abba ya bude masa kofa ya shiga sannan suka fita daga gidan a nutse kamar yadda suka shigo.
Hussain ya shiga cikin parlour da sauri,
Mommy tana zaune tana waya da sister
dinta da take aure a Kaduna "wallahi har
yanzu bai ce min komai ba Sakina. Na
rasa yadda zanyi. I tried all I can possibly
do amma babu wata amsa. Yau ma
gabakidaya ya kara rikicewa, ya ki ganin
kowa ya hana kowa ganinsa sai Dr
Ma'aruf. Shima kuma duba lafiyar sa kadai
yayi amma bai ce masa komai ba".
Tana cikin maganar Hussain ya shigo, ta
lura magana yake son yayi mata sai tayi
masa alama da hannu cewa ya fadi abinda
yake son fada, yace "baban yaya
Muhammad ne yazo, yana waje wai yana
son ganin Daddy" cikin sauri tace "Sakina
zan kira ki later" ta katse kiran tana kara
kallon Hussain da shima yake tsaye yana
jiran abinda zata ce "baban Muhammad
kace? Wanne Muhammad din?" Ya dan
bata rai "Muhammad din Safina mana,
Shine yazo gashi can a waje yace yana
son ganin Daddy, gashi kuma kinga
Daddy tun safe yace kar wanda ya shiga
gurinsa shine nazo inji me za'a gaya
masa?" Ta mike da sauri kamar zata fita waie sai kuma ta dawo da baya "je ka sake duba Daddyn naku ka ga ko ya bude kofar" ya fita amma bata iya hakura ba sai
ta bi bayansa tana jin dadi a ranta, at last iyayen Muhammad sun yunkuro da niyyar yin maganar da zata gyara auren yayan na su.
Sam bata jin dadin yadda Safina take
zama a gidan mijinta amma kuma ya zata
yi? Dangin mahaifin su Safinan sun yi shakulatin bangaro da su kamar ma basu san da su a duniya ba, babu abinda zata ce sun tsinanawa yaran tunda mahaifin su ya mutu sai auren da suka daura wa
Safina wanda a yanzu ba komai bane ba
illa alakakai.
Hussain ya dawo tun kafin ta karasa fita
yana cewa "ya tafi. Ina jin Baba Ya'u ya
gaya masa Daddy baya jin dadi. Har ya
tafi" ta dan dafe kanta da hannun ta cikin
nuna rashin jin dadin ta, ta so ace mazan
sun zauna sun tattauna, wata kila zaman
nasu ya samar wa da yarta ta mafita.
Ta juya ta koma parlor ta zauna tana sauke ajjiyar zuciya hankalin ta gabakidaya yana kan halin da marayun yayan ta suke ciki. Kwana biyun nan ko bacci bata samu tayi saboda damuwa da take ciki da halin da yayan nata suke ciki, hanya kawai take nema da zata bi dan ta gyara musu rayuwar su ta samar musu da farinciki. Amma bata san wacce hanya
bace ba.
Ta zauna tare da sake sauke ajjiyar zuciya tana tuna maganar da Safiyya ta gaya mata few days ago, maganar tayi mata zafi amma kuma gaskiya ce, cewa auren ta da Adam kawai pretending suke yi but
they are not happy with each other, because they lack the major ingredient of marriage, they lack love.
Ta tuna da yadda auren nasu ya kasance, Hajiya ce ta hada su a ganinta zasu cike wa juna gurbin da suke da shi a rayuwar su. Farko duk sunyi rejecting saboda tunanin auren junan su kamar in amana ne ga marigayiya Safiya, amma kuma a hankali bayan an shekara biyu ana jeka ka dawo akan maganar sai suka amince. Safiyya ce sanadiyyar amincewar ta su duk su biyun, Ita ce a tsakiya.
Tun sanda kasa ta rufe don Safiya bayan
Adam babu wanda Safiyya take yarda
dashi sai Sa'adatu, Tun Adam yana yakice
Safiyya daga jikin Sa'adatu musamman
sanda Hajiya ta fara yi masa maganar
auren sa'adatun har daga baya shi da kansa yake kai ta gurin ta ta dan rike masa ita idan zaije wani meeting mai muhimmancin da ba zai iya tafiya da ita
ba. Ta san cewa ya amince da auren ne ba
wai dan yana son ta ba sai don yana son
ya sama wa Safiyya uwa. Ita kuma a nata
bangaren ta amince masa ne dan ta samarwa nata yayan uba. So it was just a transaction a tsakanin su. Kuma over the years duk kanninsu sunyi iyakacin kokarin su wajen ganin sun sauke nauyin yayan da
yaje wuyan su. Duk d dai sun fuskanci challenges akan hakan dan Adam ya kasance mai matukar nuna soyayya ga Safiyya yadda baya hada ta da kowa baya
hada ta da komai. Hakan ya jawo musu matsaloli da yawa, a hankali kuma ta fahimci cewa sam bai
yarda da ita akan Safiyya ba, komai tayi
mata idon sa yana kai, sannan baya taba
neman shawarar ta idan zai yanke hukuncin duk da ya shafi Safiyya, kusan duk abinda ya shafe ta ma boye mata yake yi baya son ta sani,
Hankalin ta bai gama tashi akan hakan ba
sai da ya fara rashin lafiya, rashin lafiyar
da aka tabbatar musu da cewa bata da
magani. Few months after that sai gashi da theory din cewa kusan duk abinda ya mallaka mallakin Safiyya ne. Hakan ya sa tayi tunanin plan ne ya shirya dan ya
mallaka wa Safiyya komai, ita kuma da
yayan da ta haifa masa (twins) ko oho.
Ballantana kuma agololin da tazo da su gidan.
Tayi iyakacin kokarin ta dan gain an warware wannan kullin, har sai da ta tabbatar da cewa magana tabbas ce babu fashi sannan ta hakura. Amma kuma
wannan sai ya sanya tsoro a ranta, tsoro mai girma, idan har haka ne idan mai kasancewa ta kasance da Adam to ya zata yi da yaya hudu? Biyu ma ta kasa
rikewa a lokacin da take da kuruciva ballantana hudu a lokacin da girma ya riga ya zo mata?
Wannan tunanin shi ya dasa toro a ranta
shi kuma tsoron sai ya dasa wata idea a
ranta, idea din hada auren Safiyya da
Mustapha. Idan aka yi auren tabbas zasu
samu security yadda ko babu ran Adam
ba zasu tagayyara ba. Sai dai tun a bugun
farko Safiyya ta debi kasa ta watsa a
idanunsu tace bata so, Sai dai hakan bai
sage mata guiwar ta ba, kamar yadda
hakan bai hana ta zuwar wa Adam da
maganar saurayin da Safiyya take son
yazo gurinsa ya gaishe shi ba. Sai dai kuma taji dadin yadda yayi rejecting maganar tare da nuna cewa sai Safiyya tayi karatu mai zurfi sannan zata yi aure, a
ganin ta wannan wani hope ne na cewa Safiyya zata iya yarda da auren Mustapha kafin lokacin.
A haka kuma kaddara ta fada wa Safiyya,
ciki ya bayyana a gare ya, wannan
maganar ba karamin tayar mata da
hankali tayi ba, tayi takaici kuma tayi
bakin cikin kasancewar haka akan
Safiyya, ta kuma tausaya mata halin da ta
shiga lokacin da tayi niyyar zubar da cikin.
Sai dai kuma a kasan ranta wannan ya
kara mata hope, cikin Safiyya yana nufin
more chances for Mustapha to marry her.
Amma kuma cikin bai fita ba, sai ta boye
maganar kin fitar cikin daga kowa da
kowa, a ranta tana gayawa kanta cewa
tayi hakan ne dan ta hana Safiyya cutar
da kanta, dan kuma ta hana ta aikata
zunubin zubar da ciki, amma deep inside
of her tana ganin ta kara wa Mustapha
chances of marrying Safiyya. With dan
shege, dole na gida za'a aura mata dan a
rufa mata asiri. And who is better to do
that then Mustapha?
Kuma cikin ikon Allah sai gashi Adam ya karbi maganar, amma Safiyya ta rufe idonta tace bata san zance ba. Har ma daga karshe ta zabi Mukhtar akan Mustapha din, shi kuma Adam as always, ya bi bayan yarsa.
Ta sauke ajjiyar zuciya. Wannan abin ya
kona mata ranta sosai, ta san cewa sun
fahimci dukiyar su take so musamman
yadda suke ta boye mata abubuwa, wai
shekara da shekaru kayan Safiya da
sarkokinta suna cikin gidan amma Adam
bai taba gaya mata ba. Ita ma kuma tasan
ba zata ce ta so Safiyya kamar yadda take
son Safina ba, amma tabbas ta so Safiyya
kuma har gobe tana son ta. Bata taba
cutar da ita ba kuma bata jin ko nan gaba
zata cutar da ita. Amma kuma tana son
yayanta sosai, tana kuma son securing
future din su da tata.
Sai dai yanzu duk abubuwa sun rikice
mata, har bata ma san ta inda zata kamo
zarurrukan rayuwar yayan na ta ba
ballantana ta tabbatar da ingancin sakar
su. Safiyya taki auren Mustapha, ga
Safina can kuma yana shan wahala a
hannun mijinta saboda Safiyya, Safiyya…..
Safiyyan kuma da a yanzu babu abinda
zata iya yi mata dan tun daga ciyarwa har
komai nasu ita da yayan ta ita ce take yi musu.
Ta juya ta kalli hanyar dakin Daddy jin ana
kiraye kirayen sallar magrib, tun jiya da ta
yi masa sallama taje ta kwanta bata kuma
saka shi a idonta ba dan tun asubar fari a
rufe kofar sa ya ce babu wanda yake
bukatar gani a ranar. Hatta Ahmad da
yazo sai juyawa yayi ya koma ba tare da
ya ganshi ba. Hatta yar lelen nasa Safiyya haka ta gama knocking kofa da kiran sunansa ta hakura
ta koma sama ita ma ta rufe kanta.
Ita dai bata san me ya same shi ba, tana
kuma fatan ba wani laifin aka ce wani a
cikin yayanta ko ita sunyi ba. Ya kori
Mustapha yace babu shi babu shi har
abada, saura kuma wa? Saura Safina? Ita
ma yace babu shi babu ita?
Ta mike tayi hanyar dakin tana addu'a a
ranta, ga mamakin ta tana buga wa sau
daya sai gashi ya bude mata shi da kansa,
Ta shigo sai tuka wheelchair dinsa ya
koma ciki ba tare da ya ce mata komai ba,
Ta zauna tana kallon sa, kafin tayi magana
yace "ina Hussain. Yazo ya taimaka min
inyi alwala" ta dauko wayarta da sauri
"bara in kira Hassan, Hussain ya fita" sai kuma ta ajiye wayar "ko inzo invi maka to ni?" Bai ce mata komai ba sai ta wyce ta dauko buta da bowl din da taga suna yi
masa alwalar a ciki, tazo ta fara zuba masa ruwan tana kuma wanke masa gabobin alwalar sa harta gama yi sannan ta mike tana kallon sa.
Tabbas akwai wani abu mai girma da yake
damunsa, amma tana tsoron tambaya kar
yace tazo ta bar masa gida irin yadda
yace ranar da ya kori Mustapha. Ta saka
towel tana rage masa damshin ruwan a
jikinsa yadda ta ga yaran suna yi. "Dazu
kayi bako. Mahaifin Muhammad yazo yana
son ganin ka sai aka ce masa baka jin
dadi" kallon da yayi mata sai ya saka ta
tunanin in akwai abinda ta fada mai zafi,
kamar ba zaiyi magana ba sai kuma yace
"me yace? Da wacce maganar yazo?"
Tace "bai ce komai ba. Amma ina tunanin
maganar Safina ne. Kasan fa har yanzu
tana gidan surukan bata koma gidan ta
ba. Maybe zuwa yayi ya bada hakuri akan
abinda yaron yayi sannan a nemi sulhu a
tsakanin yaran",
Ya juya kujerar sa ya kalli gabas sannan ya
tayar da sallah ba tare da yace komai ba,
Kafin ya idar ta fita, Ya juya yana kallon hanyar da tabi sannan ya daka hannu ya kuma daukan wayarsa da take gefen gadon sa, a hankali ya sake playing video din da ya kalla ya kai sau goma a cikin daren jiya da kuma wunin yau. Ya saka camerar din ne dan Safiyya, dan tana acting weird tana kuma boye masa abubuwa da yawa da yake son sani. Amma kuma bai taba tunanin allura zata tono masa garma ba.
Yayi shiru yana kallon Safiyya da
Muhammad a cikin screen din wayarsa,
yana kallon su kuma yana sauraron
maganganun su, yana kuma sauraron
satin kukan safiyyan da yake ratsa ko'ina
na jikin sa. Babu abinda yake so a duniya
sama da ita. Babu kuma abinda ba zai
bayar ba dan ya samar mata da farin ciki
mai dorewa. Dan ya tabbatar cewa
wannan kukan nata shine na karshe a
rayuwar ta. Amma ya zaiyi....? Abinda take
so din is close to impossible.
Ya fahimci abubuwa da yawa a cikin video
din, ciki kuwa har da cewar Safiyya ba
zata taba samun mijin da zai so ta kamar
Muhammad ba, shi bai ma taba tunanin
akwai soyayya mai karfin irin wadda
wadannan yaran suke yiwa junan su ba.
Babu kuma abinda ba zai iya bayarwa a
yanzu dan yaga sun auri junan nasu, ko
da kuwa sauran numfashin da ya rage masa a duniya ne. Amma auren Muhammad ba zai yiwu ba sai da
amincewar iyayen sa. Iyayensa kuma baya
jin zasu aura masa Safiyya musamman
idan suka ji kaddarar da ta fada mata.
Shi kuma a matsayin sa na uban ta ba zai
je ya roke su ba. In yayi hakan ya karasa
zubar mata da guntun mutuncin ta a idon
su. Zai jira ... Zai kuma yi addu'a. Addu'ar
kuwa yayi yanzun ma, addu'ar Allah ya
zaba wa safiyyan sa abinda yafi mata
alkhairi a rayuwa. Yana shafawa Malam
Ya'u ya shigo, ya gaishe shi sannan ya
tabbatar masa da abinda Sa'adatu ta fada
dazu "baban mijin Safina yazo dazu, na
ga kamar maganace mai muhimmanci
yazo da ita amma na gaya masa ba ka jin
dadi sai yace a rabu da kai amma insha
Allah gobe zai dawo ya ganka in ka ji
dadin jikin ka" ya fada cikin girmamawa.
Daddy ya sauke ajiyar zuciya tare da
dawo da video din baya ya cigaba da sake
kalla sannan a hankali yace "gobe? Allah
ya sa muna da rabon ganin goben. In yazo
goben zan ganshi insha Allah"
Maman maman✍🏻
[07/01, 10:46 pm] +234 906 816 1960: ❤️🩹Safiyya❤️🩹
Episode Fifty Nine : Chosen
Her🧕🏻
Na saki labulen tare da komawa baya a
hankali ina kuma rufe bakina da tafin
hannuna. Tabbas Abban Muhammad ne.
Amma me yazo yi gurin Daddy? Me yazo
vi gidan mu? Me ya sani menene kuma bai
sani ba?
Na koma kan gado na na dauki waya ta
and for uncomfortable time na kira
number din Muhammad. Tana ringing, har
tayi ta katse bai dauka ba. Tun safe haka
nake fama. Nayi kiran nayi message din
amma ya share ni. Jiya haka na kwana
ban vi bacci ba kuma a jiyan wayar ta sa
ma bata shiga sam, yau kuma tun sate
tana shiga amma baya dauka.
Na fahimci fushi yake yi da ni, na kuma
san laifina kuma da mana san ransa zai
baci in ya fahimci abinda nayi amma nayi
wa kaina alkawarin kamar yadda nayi
masa alkawari shima wanna insha Allah
zai zama bacin ran mu na karshe, Bani da
tabbas din plan dina zsi tafi smoothly
amma abinda nake da tabbas akan sa shine addu'ar da nayi a kan lamarin, ina da tabbas din Allah zai amsa kuma zai warware mana komal cikin sauki kamar
yadda ya zaba min Mukhtar sanda na roke
shi kuma daga baya ya warware min
aurena dashi cikin ruwan sauki,
Na bude Whatsapp da sauri na tura masa
message din da nake ganin zai dauki
hankalin sa ya kula ni ko da kuwa bai huce
da ni ba, in dai na samu ya kula ni ni
nasan yadda zanyi ya huce din.
"'Abba yazo gidan mu yanzu. I think gurin
Daddy yazo".
He saw the message kamar yadda ya ga
guda goma sha dayan da na tura masa so
far. Na ga ya fara typing kuma sai ya
daina, sai kuma ya koma offline. Naji wani
takaici ya kara mamaye zuciya ta hawaye
ya kawo a ido na. Nan da nan na fara
kukan kuwa. Ni da me zanji ne wai. Sai
kawai na danna masa recording kukan
nawa nayi tayi kamar karamar yarinya na
tura masa,
Ina kalion sanda message din ya je masa,
ma ga kuma sanda yayi playing, he
started typing again sai kuma ya daina.
Naji kamar in jefar da wayar a kasa dan
takaici. Sal na ajiye ta a kan gado na koma
toilet na wanke fuskata sannan na zo zan wuce in fita daga dakin naga wayar tana blinking, da sauri na dawo da sure ta na bude hoping to see his name sai kuwa naga message daga gare shi.
"Na samu sabon ring tune"
Sai da na dan dora wayar a saman kirjina
cikin nuna jin dadi na tare da lumshe ido
sannan na bude na tura mass reply,
"Ka wujjjiga zuciyata Muhammad. Gabaki
daya na fita daga hayyacina a cikin wuni
daya"
"Let me see"
"See what?"
"The face. Data fita daga hayyacin na ta"
Sai na gyara hijab din jikina tare da danna
masa video call. Bai dauka ba sai yayi
rejecting.
"Can't answer..... Let me call you"
Na rike wayar ina jujjuya ta a hannu na,
wata zuciyar tana gaya min suna tare da
Safina ne shi yasa yaki daukan kira na.
Mintina kadan sai gashi ya kira ni video call
Na jingina wayar tawa a jikin frame din
gado sannan na kwanta ruf da ciki ian
kallon wayar sai na answer. Yana dakin sa
na gidan su a kan kujera, Kallo daya nayi
masa na fahimci shima ya wujijiga kamar
ni. Fatar idonsa tayi ja sannan sides din
don sun tashi kadan. And his lips looked
a bit dry.
Direct nace masa "ba kayi bacci ba jiya
ko" na lura studying dina yake yi shima
sai yace "nayi. For like 3 hours I think.
How are you?" Ban amsa ba nace "3
hours yayi kadan" ya daga kafada "ba laifi
na bane ai. Me laifin ai ta san laifin ta" na
kwabe fuska makar zan cigaba da kukan
"na sani ai. Amma ai na baka hakuri. Dan
Allah ni dai kar ka sake yin fushi da ni kaji?
Gwara kayi min bulala Allah" na karasa ina
jin hawaye yana kawo wa ido na.
Yayi wanj gajeren murmushi da ban gane
ma"anar sa ba kuma naji bana son sani, a
hankali kuma yace "look at you. Kamar da
gaske zaki daina din" nayi sauri cewa
"Allah Yaya Muhammad da gaske nake, na
daina bata maka rai kaji?" Na karashe
cikin lallami, ya danyi shiru fuskarsa tana
nuna har lokacin yana cikin bacin ral yace
"but why do you do it?" Ya tambaya, sai nima na tambaye shi dan in tabbatar da cewa abinda nake tunanin ya bata masa rai din shine da gaske ya bata masa din "me yasa a karshen maganar mu ta jiya na
gaya maka zan rabu da kai?" Ya girgiza kansa idonsa a kasa sai kuma ya dago tace "me yasa tun kafin mu zauna baki gaya min cewa zaki yi recording maganganun mu ba? We promised each other that zamu ke yin everything together a yanzu. You
should have told me dan in san abinda ake ciki, I felt...........used". Ya karasa still da bacin rai a fuskarsa.
Na gyada kai cikin fahimtar sa, amma sai
nace "I promise I will explain everything to
you. Amma yanzu dan Allah kayi hakuri
kaji? Yanzu lokacin sallah yayi and zan
sauka wajen Daddy idan nayi sallah. I will
call you in na dawo daki and I will explain
everything to you" ya gyada kai shina
yana waigawa bayansa kamar wani ne ya
shigo dakin, sai kuna ya juyo yace min
"okay zamuyi magana in an jima" daga
haka ya katse kiran
Na ajiye wayar tare da kife goshi na akan
ta na some seconds sai kuma na mike da
sari yadida naji kiran sallah yana kara tashi a massilatai na shiga toilet. Bayan na 'idar na gabatar da adduoi na sai na sauka kasa kamar yadda na saba na tafi part din Daddy, babu kowa a parlour sai motsin
Esther tana shirya dinner dining. Na wuce
zuwa kofar shiga part din Daddy, tun safe
ban ganshi ba, tun safe bai bari kowa ya
ganshi ba dan haka bani da tabbas din
cewa yanzun ma zan ganshi din. Kowa a
gidan bai san dalilin hakan da Daddy yayi
ba amma ni na sani, duk kowa yana cikin
damuwa amma ni duk nafi kowa damuwa
duk kuwa da cewa ina jin relief a wani
bangare na zuciya ta cewa na gaya masa
gaskiyar komai ba zai mutu da haushi na a
ransa ba amma kuma bani da tabbas din
hukuncin da zai dauka, Sai dai kowanne
hukunci ya dauka na tabbatar ba zai yi
hukuncin da zai zama cutarwa a gare ni
ba.
Na shiga parlour sa na tarar da Hussain a
zaune daga alama daga masallaci va
dawo, ya mike tsaye yana kallona cikin
girmamawa sai nace "ya bude?" Ya dan
gyada kai kadan "ya budewa Mommy da
zu, amma ban sani ba ko ya kuma rufewa"
nace "ba ka gwada shiga ba bayan ta
fito?" Ya girgiza kai yana dan murmushi
"Ke dai je ki gwada, toro nake ji kar ya
sauke fada a kaina" na harare shi nayi
hanyar corridor din da zai sada ka da
bedroom dinsa. Na karasa bakin kofar na taba ta ina addu'ar Allah yasa ya bude, amma kuma ina tsoron facing dinsa after knowing what he heard and what he saw. Na danyi knocking kadan sai kuma na
murda handle din na tura ta, naji ta bude
sal nayi sallama tare da kasa kunnena,
banji ya amsa ba, kuma dama yanzu ba'a
fiya jin amsa sallamarsa ba tunda muryarsa tayi kasa sosai, dan haka kawai sai na shiga.
Yana zaune akan kujerar sa, da wayarsa a
hannun sa, naji gabana ya fadi amma sai
na maze na nuna kamar damuwata gabaki
daya akan halin da yake ciki ce. "Daddy"
na karasa gurin sa da sauri. "Daddy ka hana mu ganin ka tun safe, duk mun damu" na durkusa a gabansa trying so hard not to look at screen din wayarsa. Ya
saka hannu ya kashe hasken screen din
sannan yayi ajjiyar zuciya tare da miko
min hannu, na rike hannun nasa da hannayena duk biyun tare da dora guiwowina a kasa nace "Daddy are you okay? Wani abun yana damunka?" Sal ya danyi min gajeren murmushi, "I am fine Safiyya. Zuciyata tayi min dadi sosai. Ina fatan ke ma watarana zaki ji dadin taki zuciyar" na kara rikon hannun sa nace "a
yanxu ma ina jin dadin zuciya ta Daddy. Knowing that you are happy kadai ya ishe ni farin cikj" a hankali yace "I have made a lot of mistakes Safiyya in raising you, Nayi kurakurai da dama. Addu'a ta kadai a
yanzu ita ce Allah ya kara ara min lokacin
da zan gyara su" na zauna sosai tare da
zame hannu na daga cikin nasa, kai na a
kasa nace "Daddy you did well, kayi iya
kacin kokarin ka. Allah ya saka maka da
alkhairi",.
Muka danyi shiru kadan amma ina jin a
jikina kallo na yake, sai kuma yace "kina
da wani abu da kike so inyi miki? To put a
smile on your gloomy face today? Tunda
bani da tabbas din gobe" na danyi murmushi sai kuma na dago kai nace "Daddy ka dawo da Mustapha gida, he should be with you too, Bashi da wani
gidan sai nan. Bashi da wani uban sai kai.
Ban san laifin da yayi maka ba amma kayi
hakuri". Ya sauke ajiyar zuciya yana kallon gefe
amma bai ce min komai ba, a hankali na
sake cewa "kaji Daddy na?" Ya dan kalle
ni kadan ya sake dauke kai yace "ina
twins? Suna ta nema na ko?" Na danyi
murmushi "Hassan yana parlour, wai
toro yake ji kar kayi masa fada idan ya
shigo* ya danyi murmushi mai sauti yace
Wit a min sh)" na tashi ina jin dadi a raina duk kuwa da naga Daddy bai amsa bukatar da na gabatar masa ba na leka nace "baban Daddy, Daddy yana
magana" ya bude ido sal kuma ya mike da
sauri yana magana a hankali yadda Daddy
ba zal jI ba "shi yasa nace ki shiga, yana
ganin ki zai sauko" nay dariya tare da
talle masa keya, ya shiga yana sosa keyar
na bishi a baya ina jin yana gayawa Daddy
*Daddy ka ga ta dake ni ko?", Daddy ya
mika masa hannu "zo nan babana" na
karasa nima ina dariya. Daga baya sai ga
Hussain ya shigo shima, sai kuma ga
Mommy ta shigo ganin babu wanda yaje
cin abinci, a karshe sai abincin aka hado
aka kawo mana nan muka zauna muka ci
a plate daya mu uku, Daddy yana kalion
mu yana murmushi amma kana ganinsa in
dai ka san shi kasan akwai abinda yake
ransa. Mommy ma haka, tana tayamu
hirar kadan kadan amma ita ma ranta duk
a dagule yake kuma nasan Mustapha take
missing. A lokacin ne kuma naji tana waya
da Safina, Safinan tana gaya mata cewa
a koma gidan mijinta, Ta ajiye wayar tare
da jan tsaki tana kara bata fuska tace da
Daddy "Safina ce. Wai an mayar da ita
gida dazu, an kuma bata wata yar aikin. Ina in maganar komawar tata baban yaron yazo da zu kuy" Daddy ya juya ya kalle ta kadan sal kuma ya dauke kansa al ce komal ba ya cigaba da sauraron musun da ake tafkawa tsakanin Hassan da Hussain akan yan wasan ball.
Duk hirar nan da akeyi Muhammad yana
raina, na sam ya kira waya ta yaji ban
dauka ba amma kuma bana son tashi
saboda ina jin dadin zama da Daddy
musamman idan naga yana wasa da
twins. A haka har mukayi sallar isha muka
cigaba da hirar mu, Mommy kam sai naga
ta kwanta akan kujerar da take dakin ta
rufe idon ta, naji babu dadi a raina, na san
Safina da Mustapha ne a ranta and I felt
bad for her amma sam ban ji regret akan
abinda nayi ba.
Sai da Dr Ma'aruf ya shigo sannan ya
sallame mu yace mu bar Daddy ya huta,
muka tashi muka fita muka bar su sai
Mommy da ta zauna ita ma. Direct dakina
na koma ina addu'ar Allah ya sa
Muhammad bai sake yin wani fushin ba.
Na je na dauki waya ta na kuwa ga missed
calls din sa kusan two hours ago. Har na
zauna na danna kiran sa sai kuma na tuna
da maganar Mommy cewa Safina ta koma
sai na kashe a raina ina gayawa kaina
yana can yana angoncewa. Yes, na
fahimci yaudarar sa tayi ta aure shi amma har yanzu ban manta da zancen cikin da tayi a gidan sa ba. Nayi kwafa na tashi na fara cire kayan jiki na. Sai gashi ya kira ashe wancan kiran nawa ya shiga. Na harari wayar ina gaya wa kaina cewa taimaka masa zanyi by not answering his call dan kar yashiga hakkin matar sa. Amma ni na san kishi ne.
Sai da na shiga nayi wanka na fito sannan
na sake ganin wani missed call din da
kuma message.
"Sarkin kishi"
Na murguda baki kamar yana kallo na
amma kuma ina jin kewar sa a raina ina so
muyi magana dan akwai a lot of unsaid
words a tsakanin mu.
Sai da na gama dukkan shirin kwanciya
bacci na sannan na hau gado nayi addu'a
na rufe ido, so nake inyi bacci da wuri dan
ina da abubuwan yi da yawa washegari
wadanda suka shafi aiki na kuma ina
bukatar clear head. Amma bacci yayi
kaura daga idanuwa, kawai lissafe lissafe
nake tayi,
Nasan Daddy yaga video din can, wanne hukunci zai yanke akai? Me Abba yazo yi gidan nan? Da gaske maganar Safina ce ta kawo shi ko kuma wata maganar daban? Me Muhammad da Safina suke yi yanzu? Nayi tsaki tare da juyi, "Ya Rabbi" na fada a hankali kamar zanyi kuka, Sai kuma na jawo wayata na kunna data ina lura da yadda lokaci ya tura, Messages
suka yi ta shigowa duk ban damu da su
ba sal da naga nasa sannan na bude.
*I called, ba kya kusa. Call me in kin
gama"
Ina gama karantawa na ganshi online.
"Me kike yi baki yi bacci ba?"
*Kar ka dame ni. Go back to your wife"
"Hmmmm"
*Fadi dai abinda yake ranka, kar maganar
ta kumbura maka ciki"
*Ban san me yasa kike nuna kishin ki akan
ta ba, even after I told you yadda abin ya
kasance"
"She is still your wife, And you got her
pregnant"
“Hmmmm"
“Kai ma hmmm”
"Me kike nufi da hmmm din ta ki?"
"Abinda kake nufi da taka hmmmm din shi
nake nufi da tawa hmmm din"
"To ai baki san me tawa hmmm din take
nufi ba"
"Me take nufi kuwa? In banda cewa maza
rigar kaya ne ku?"
"Lo!"
'"Dariya ma kake yi ko?"
"Okay to me kike so nayi? Can I call you
please?"
"Ni ba zanyi waya da mijin aure ba da
daddare. Saurayi na zan kira wanda bashi
da mata"
"Hmmmm"
"Kai ma hmmm"
"Please in kira ki?"
"This user is busy"
“Please minti biyu kawai, So nake kawal
inji muryar ki kince min goodnight baby"
Kaje ta gaya maka baby din, ta goya ka
da zani ma babu ruwa na”
Na tura masa ina jin raina yana kara baci,
ni yadda ya dauk maganar ba koma ba
shi yafi komai bata min rai. Ina ganin sa
yana typing na kashe data ta tare da jetar
da wayar gefe na a kan gadon na ja bargo
na lulube har kaina.
A wannan daren shima da kyar bacci ya
dauice ni. Washegari ina kan system tun
safe ina all dan ko breakfast ban saulia
kasa rayi ba sai dal Esther ta kano min,
ina sane da Muhammad kuma na san ya
kamata muyi magana in warware masa
abubuna amma na cigaba da share shi.
Har sal wajen azahar na kammala na tashi
tsaye nayi mika duk jiina yana ciNio, wai
dan mana samu tunda uncle Ahmad ya
kora bakin aikin sa yana dan dauke min
wasu nauye nauyen.
Sai da na shiga toilet nayi wanka na shirya
sannan na zauna na kunna wayata ina
murmushi, ko babu komai na san jilin sa
-ya gaya masa zuNa yanzu, ba dai shi mai
mata ba? Himmm
Ina kunnawa sai ma hau yan danne danne
na, a haka na shiga Instagram na fara
scrolling through feeds, a lokacin ne naga
wani post a wani blog da naga yaja
hankali na saboda tarin comments din da
akavi akan sa. Sai na samu kaina da
karantawa. Irin yan hide my ID din nan ne,
na karanta labarin tun daga farko har
karshe sannan na sake karantawa sai
kawai na samu kaina da dariya. Mamakin
Safina yana kara kamani.
Tun a karantawar farko na gane ita ce.
Wai tana neman shawara ne agun
malamar blog din da yan comment
section, wai step sister din ta tana neman
raba ta da mijinta. A labarin nata yadda ta
nuna shine a gurin dinner dinta ne muka
hadu da Muhammad, wai tun daga nan na
makale masa shi kuma ya juya mata baya,
babu irin wulakancin da baya yi mata
akaina. Tace a wayarta ma ya dauki
number ta kuma ya gaya mata baki da
baki cewa number ta ya dauka. Sannan
bayan ta samu ciki yace baya so saboda
yana ganin in suka haihu za'a hana shi
aure na, yace sai ta zubar taki shine ya
mare ta ya kuma ture ta da mota ta fadi
cikin ya zube kuma taji ciwuka.
Maganganu dal iri iri,
Ko comment section din ban shiga ba na
wuce na cigaba da abinda yake gaba na.
Mani da lokacin ta ballantana na bloggers Sal na fita ma na koma na Kira mijin nata sai bayan da ya dauka sannan a tuna ashe fushi nake yi dashi, duk kuwa da
cewa ban san abinda yayi wanda yasa
nake yin fushin ba. Da ya dauka kuma si
nayi shiru. Shima daga bangaren sa sai
yay shiru din muk cigaba da sauraron
numfashin juna. A raina nace zanga wanda zai fara sauko wa tsakanin ni da kai,
Shi din ne kuwa ya fara magana "wai ni ya
akayi wanna lamarin ya juye ne? The last
time I checked ni akayi wa laifi nake yin
fushi ana bani hakuri har da yi min kuka.
Yanzu kuma lokaci daya na samu kaina a
mai bada hakuri bayan ban san laifin da
nayi ba kuma ban gama hucewa daga
laifin da aka yi min ba" na murguda baki
*oho. Nima ban sani ba" na kuma yin
shiru, yayi ajjiyar zuciya "to shikenan. Kiyi
hakuri. Whatever it is. I am sorry,
shikenan?*
Nace "shikenan. Kai ma kayi hakuri. Na
san nayi ba dai dai ba amma ina saka ran
dan nayi maka bayani zaka gane insha
Allah* ya danyi shiru sannan yace *why
do jou do it? Why were you recording our conversation kuma meyasa baki gaya min zaki yi hakan ba before you do it”
Na danyi ajiyar zuciya nace "I wasn't
recording.... Yace "then someone was
listening. Maganganun ki na karshe sun
nuna min cewa ba dani kike magana ba,
da wani kike magana. Waye?" Nace
"Daddy" duk muka yi shiru, sai ya
maimaita "Daddy? How?" Sai na bashi
labarin cctvn da Daddy ya saka a ko'ina a
gidan sa da niyyar kamani tunda ya lura
kamar bani da gaskiya ina boye wani abu,
and how I used that to my advantage
wajen warwarewa Daddy duk abinda
nake ganin ya karata ya sani a game da
alakar mu.
Yayi shiru har na kai karshen bayanin
nawa sannan yace "and why didn't you
tell me before? Yadda zamu zauna mu
shirya komai tare?" Na ce "I wanted to do
that. Amma kuma idan na gaya maka your
reactions won't be real, I wanted to show
Daddy the truth and the depth of your
love for me, and I did. Kayi hakuri Baby. I
believe wanna maganganun da Daddy
yaji tsakanin mu su zasu kawo mana
karshen issue din mu with him. Insha
Allah ina ran zai fahimta"

Ya danyi shiru kadan kamar yana tunani akan maganar sannan yace "na fahimce ki, na kuma karbi uzurin ki, but please Piya let this be the last time da zaki boye
min magana. Please" a hankali nace
"insha Allah. Kayi hakuri. Wannan shine
bacin ranka akan wanna maganar na
karshe. Kaji?" "Hmmm" kawai yace, nace
"ka hakura?" Yayi ajiyar zuciya "ya zanyi?
Ya zanyi da ke Piya? Ba na iya fushi da ke
duk yadda naso inyi hakan kuwa. Yanzu
wannan fushin da nayi me ya faru da ni?
Ba gashi nan kuma ni nazo ina bada hakuri ba?" Nace "ai issue din da ka bada hakuri a kansa daban ne ba wannan bane ba. Wannan ai ni na bada hakuri akan sa
tunda nice nayi wannan laifin" yace "okay
ni akan wanne na bada hakurin kenan?"
Na dan bata rai nace "ka sani ai. You are
just refusing to admit it" yace "because I
don't believe abinda nayi laifi ne, but still
na bayar da hakurin ai ko? And one day
insha Allah, I will explain it to you" nace
*One day? What day?" A hankali yace
"idan lokacin yayi you will know" nace
"hmmm" ya danyi dariya "what?" Nace
"kai fa yanzu ka gama yi kin preaching
akan being open to each other da sauran
su. And now you are closing up" ace '"akwai abubuwan da are sensitive...." Nace "sensitive? Abin da zaka fada min ya kal wanda na gaya maka zama
sensitive?" Sal ya sake cewa "hmmm" sannan sal yay kokarin chanja topic yanzu dai kina so kice min duk maganar da muka yi shekaran jiya Daddy yaji? Na fahimci chanja layi yayi Amma ita ma maganar da ya dawo kanta mai muhimmanci ce
Nace “ba ji kadai nayi ba, har gani yayi” muka sake yin shiru sai naji yace “oh my god” dasauri, nace “what?” Ya sake cewa “ya salam” kamar hankalin sa a dan tashe, Nima nawa hankalin ya fara tashi nace “what? Mene ne ya faru?” Yace “kin ce ya ga komai” nace “yes, ya gani, am sure. Menene ya tada hankalin ka? Yace “at a point there. There was a point that we……that we were……”na gane abinda yake magana akai sai na ajiye wayar nima cikin tashin hankali, naji kamar kasa ta tsage in shiga “na shiga uku” na fada a fili, na kuma daukan wayar da niyyar mu tattauna mu nemi mafita sai naji yana dariya, nace “dariya fa kake yi? Ka shigo gidan Daddy har falon sa kayi hugging? Ka san halin Daddy kuwa? Ya dai na dariyar yace “point of correction. His daughter hugged me” da sauri nace “I didn’t. I didn’t” yayi dariya sosai “ko mu karbo video dan daga hannun daddy mu duba?” Nace “a karbo mana, kowa ya gani ai zai gane. It wasn’t…… I wasn’t…..I was trying to stop you” ya cigaba da dariya hankalinsa a kwance, nace "at least nawa
is justified. Na ka kuma fa?* cikin dariya
yace "it is justified too. I was trying to
console you, rarrashin ki nake y'* ya fada
da confidence, nace "okay haka zaka ce
masa ko? To babu ruwana ni dai" muka yi
shiru, sai kuma yace "kin san Allah ne ya
kama mu? We have never done something like that, ranar da mukayi kuma a matsayin kuskure a ranar ne aka kama mu. Maybe dan Allah yana son mu
ne, it is a warning to not do it again". Muna ta yin hira sai ji nayi ana kiran sallar la'asar, dole muka rabu dan amsa kiran ubangijinmu ba wai dan mun gaji da
junanmu ba, na ajiye wayar ina muirmushi,
one thing about soyayyar mu da Muhammad ita ce duk tashin hankalin da muke ciki to as long as we are together sai muji kamar bamu da damuwa ko
kadan, Sai da nayi sallar laasar sannan na
sauka kasa, a lokacin naga mommy tana
zaune a dining tana ta juya cokali a
hannunta, na zauna na gaisheta ina
kalionta yayin da Esther take hidimar zuba
min abinci, Sai da ta gama ta tafi sannan
nayi mata magana "mommy nayi wa
daddy maganar Mustapha, insha allah zai
huce nan bada dadewa ba, Yanzu ma in
na sake korawa gurinsa zan sake yi masa magana. Kuma • ta watsa min wani kalion da yasa na mayar da sauran magana ta cikin cikina na kasa fito da ita.
*kamar yadda kika yi masa magana ya
kore shi?" ta fada a hankali maganar kamar ba daga bakinta ta fito ba, na rufe ido na na bude ina jin babu dadi a zuciyata, idan nace ban son mommy
nayi karya, sam bana jin dadin yadda
alakar mu take komawa, Na dago kaina a
hankali nace mata "wallahi mommy bani
na ce ya kore shi ba. Ta yaya zan ce masa
ya kore shi? Shima nan ai gidan su ne, insha allah.....* "cut it" ta dakatar da ni, "bana son jin komai daga gareki, daga baban naki nake jiran jin bayanin da zai yi
sannan in san wanda nima zanvi" sai ta
tashi ta bar abincin ta ta fita, nima ji nayi
duk abincin ya fita daga kaina. Na jima ina kokarin ganin naci, amma ganin hakan ba zai samu ba sai hakura na tashi zan koma sama dan bana son
cigaba da zama a kasa ballantana mu
sake yin sa'in sa da mommy. Sai dai ina
shiga parlor Hussain ya shigo da saurin sa
*mommy, baban Muhammad ya dawo,
gashi can a waje yace a gayawa daddy
yazo" mommy ta mike daga kwanciyar da
tayi da sauri tare da daukan mayafin ta da
Yake ajiye a gefe, Hussain yace "ba sai kin
tashi ba mommy, ki bari zan shigar da shi,
gaya miki dama kawai zany* ta girgiza
kanta " uhm uhm, barni inje inyi masa bayani sosai, kasan baban naku ya zama a lallaba yanzu” na bita da kallo har ta shiga part din Daddy sai na wuce Hussain da sauri na koma sama naje na daga labule ina kallon Abba, yana tsaye a jikin motarsa looking as majestic and elegant as ever, wani irin kwarjini yana fita daga jikin sa, a gefen sa Haidar ne a tsaye yana ta kalle kallen gidan. Gabana faduwa kawai yake yi da sauri da sauri, shin da gaske maganar Safina yazo yi? Ko wata maganar ta daban? Ko Daddy zai yi masa maganganun mu da Muhammad? Sai na koma cikin dakina na da sauri a lokacin da naga Hussain yazo yayi musu iso suka doshi kofar shiga part din Daddy daga waje. Nayi dialing number din Muhammad ina binsu da kallo har suka shiga sannan ya dauki kiran, tun kafin yayi magana ne “Abba ya dawo yanzu ya shiga gurin Daddy” he sound surprised, “ yanzu?” Nace “yes, yanzu suka shiga. Kasan me ya kawo shi?” Ya danyi shiru, “he mentioned something shekaran jiya akan zaizo gurin Daddy. But ban dauka soon zai zo din ba. Let’s wait and see me zasu ce.” Nace “tsoro nakeji” yace “tsoron me?” Nace “kar Daddy ya nuna masa wannan videon” yace “what about it? In yayi haka ya rage mana aiki shima ko?” Nace “baka gane ba….. there is that part a ciki” ya danyi dariya “that part where you were hugging his son?" naji hankali na ya kara tashi "dole ma in sace wayar daddy".
Ina nan ina gadin hanya ina jiran fitowar
Abba amma shiru, sai daga baya na lura
bada Haidar suka shiga ba, dan naga
alamar shima ya gaji da jira ya dawo waje
ya zauna akan kujera, daga baya ya mike
ya koma cikin mota, Duk abinda ake yi ina
updating Muhammad wanda yake makale
a kunne na. Shima daga gurin aiki ya tashi
yana hanyar sa ta komawa gida. Sai da
aka fara kiran sallar magrib sannan Abba
ya fito, Haidar ya fito daga cikin motar da
sauri ya bude masa kofa ya shiga shi
kuma ya tuka suka fita daga gidan. Na
sauke ajjiyar zuciya sannan na gaya wa
Muhammad, daga nan nay masa sallama
na tafi da shirin yin sallah nima, Ina idarwa
na sauka kasa na zauna a parlor ina ta
baza kunne inji ko wani zaiyi min maganar
baban Muhammad da yazo.
Ashe bani kadal bace ba, mommy ma
baza kunnen take yi dan itama Daddy bai
barta ta zauna tare da su ba, amma daga
Hassan har Hussein babu wanda ya san
komal akan zuwan nasa. Daga baya dai da ta fahimci ba su ji komai ba sai ta tashi ta shiga gurin Daddy da kanta. Ta jima a ciki sannan ta fito fuskarta tana nuna
damuwa, ta dan zauna kadan sai kuma ta tashi ta hau sama tana waya da mustapha. Nima ina son shiga gurin Daddy kamar yadda nake vi duk dare
amma kuma sai na kasa, zucivata cike da fargaba,
A karshe dai na tashi na shiga saboda
nima ina son ganin sa, ba zan iya
kwanciya bacci idan ban ganshi ba. Na
shiga dakin nasa da sallama kamar
kullum, yana kwance nurse dinsa yana
goge masa jikinsa domin vi masa shirin
bacci, ya miko min hannu kamar kullum
yana murmushi, na karaso na saka hannu
na a cikin nasa sai yace "naga baki shigo
ba, da yanzu zan aika a kira ki. Ina so ki
shigo muyi magana kafin inyi bacci" nayi
kneeling a gabansa nace "gani daddy,
akwai abinda kake bukata ne?" ya girgiza
kansa kadan "alhamdulillahi, babu abinda
nake bukata a yanzu. Allah yayi min komai
Alhamdulillah" na gyada kai ina murmushi
nima nace "Alhamdulillah" sai yace "sai
dal akwai abinda nake so in gaya miki" na
hadiye wani abu a kirjina nace "menene
daddy?" yace " kamar yadda kika gaya
min cewa kin hakura da wancan yaron,
kuma kin bani damar in zaba miki mijin da
zaki aura ko wanene, na fitar miki da miji
safiyya, and you are getting married as
soon as possible insha allah"
Maman Maama✍🏻
[07/01, 10:46 pm] +234 906 816 1960: ❤️🩹Safiyya❤️🩹
Episode Sixty: The Reward
Assalamu alaikum, Ina barar addu'a a
gurin ku, na rasa cousin dina shekaran
jiya da daddare. Allah ya ji kanta ya kai
rahama kabarin ta tare da sauran
al'ummar musulmi baki daya. Ameen
Na ji wani abu ya tokare min a
makogwarona, sam ban yi tsammanin
wannan maganar daga gare shi ba a
yanzu, na cigaba da kallon sa ba tare da
na bude baki ba ballantana inyi masa
magana, shima kallon nawa yake yi, sai
kuma naga a hankali ya saki hannuna
sannan ya saka hannu ya goge min fuska
ta, sai a lokacin na fahimci hawaye ne
yake fita daga ido na, nayi sauri na goge
da nawa hannun sai yace "kiyi addu'a" na
gyada kai da sauri sai kuma na tashi nayi
masa sallama na juya da na koma cikin
gida,
Addu'ar da yace inyi ita nayi tayi kuwa.
Zuciyata tayi min wani irin nauyi. Miji?
Aure? Na san yayi min maganar aure kuma na san babban burinsa a yanzu da kullum yake ganin kamar ba zai kara kwana daya a duniya ba shine ya ga nayi
aure, amma ban dauka da kanshi din zai
zabar min ba kamar yadda ni da kaina na
ce masa na amince, musamman ganin
cewa sanda za'a yi min wancan auren ma
na fari kuma ga laifin da yake tunanin nayi
a lokacin amma duk da haka sai da ya
bani zabi. Na dauka wannan karon ma
zabin zai bani amma zai hada da Muhammad a ciki tunda ya fahimci gaskiya yanzu.
Nayi ajiyar zuciya, babu abinda nake son
ji a yanzu sai abinda Daddy da Abba suka
tattauna a zaman da suka yi na fiye da
awannin biyu. Me suka ce? Me sukayi?
Wanne hukunci suka yanke?
Na dauki waya ta ina kalion lokaci, thinking if it is right to call Muhammad a wanna lokacin. Tunanin haka kuma sai yasa kishi ya kara tokare min zuciyata. Ina
tsananin kishin Muhammad dan addu'a ce kawai take kwantar min da zuciya ta a duk lokacin da na tuno cewa yana auren Safina har yanzu, Kuma suna da dukkanin rights din da ma'aurata suke da su for each other. Nayi tsaki tare da ajiye wayar na fara shirin kwanciya duk kuwa da cewa akwai wadansu aiyuka da zanyi kafin in kwanta din.
Ina cikin shirin naji waya ta tayi kara amma
ba Muhammad bane ba, na dauka na
duba naga sunan Mustapha. Har nayi
niyyar ba zan dauka ba sai kuma nayi
tunanin why not? Na dauka da sallama.
"Hankalin ki ya kwanta ko?" Ya fada ba
tare da ya amsa sallamar ta wa ba. Nayi
ajjiyar zuciya sannan na zauna a bakin
gado nace "dama na san you will accuse
me of this" yace "to idan ba ke ba waye?
As far as I know ban taba yi wa Daddy
wani babban laifin da zai ji zafi na har
haka ba. Ko kira na baya amsawa. Wai
waye baya kuskure ne? Me yasa zaki
yafewa Mukhtar ma amma ni ki kasa yafe
min?" Nace "ba lallai ka yarda ba. And
believe me, right now yadda abubuwa
suka cunkushe min, I don't even care ko
ka yarda ko kar ka yarda. Amma ni na yate
maka ba tun yanzu ba, abinda nace kawai
shine ba zan aure ka ba saboda ba zan
iya zaman aure da kai ba. Maganar Daddy
kuma ni da bakina ban je gurinsa na gaya
masa abinda kayi min ba, ballantana har
ince ya kore ka. Kuma bayan ya kore ka
ma naje na roke shi ya dawo da kai, kuma
ban hakura ba zan cigaba, amma ba dan
kai ko dan halin ka ba sal domin shi da
Mommy"
Na katse kiran tare da jan tsaki ina jin
raina yana kara baci. Mutane suna da
saurin judging other people but not
themselves. Kowa yafi jin dadin rufe laifin
sa ya kalli na wani. Sanda muna magana
da Mustapha naji shigowar kira, na kuma
san muhammad ne amma da muka gama
wayar ban duba bama dan bana son va
fahimci ina cikin bacin rai, bana son ya
san abinda yake tsakani na da Mustapha
dan ina fatan nan gaba komai zai wuce
kuma ina fatan zasu samu fahimtar juna
watarana.
Sai bayan da na gama dukkan shirye
shirye na sannan na dauki wayar amma
ban kira shi ba sai na hau online, ina zuwa
na tarar da message dinsa already a can.
"Me Daddy yace?"
Nayi murmushi, he is as much concerned
as lam, "Nima ban sani ba, Bai gaya min
komai ba a kan haduwar su da Abba.
Abba bai ce maka komai ba?" Naga message din yaje masa amma bai bude ba,. Na ajiye wayar ina tunanin ko in Kira shine? Sai kuma na fasa, Maybe yayi bacci, maybe kuma yana tare da matarsa, Nayi tsaki tare da jan bargo na rufe har kaina. Mintuna kadan kuma sai na bude na sake daukan wayar na nemo number
din sa na kira, tayi ta ringing sai kuma naji
an dauka amma kuma ba'a yi magana ba.
A take na fahimci cewa ba shi bane ba,
zuciya ta ta gaya min cewa in katse kiran
amma kafin in katse sai naji tace "waye?
Yana wanka ne, matarsa ce take magana"
Sai na katse kiran na ajiye ina jin kamar
ana gasa masara a kirjina. Jiki na ya bani
ta san nice and she said that to hurt me
kuma tayi nasara. I though she will call
back amma sai naji shiru. Sai da aka jima
sannan na sake jin ya kira ni, na share shi
da na gaji da jin karar wayar ma sai na
saka ta a silent nature ta gefe ina
hawaye.
Da assuba ma ina idar da sallah naji kiran
sa, nayi tsaki, a raina nace "ka koma gurin
matarka kaji duminta kafin rana ta fito.
Munafiki" na sake yin tsaki "namiji!
Namiji!" Na nade kayan sallahta na koma
gado na kwanta, naji shigowar message,
sai kuma na jawo wayar na duba message
din a raina ina tunanin ai ba zai san na
gani ba tunda sms ne,
"Please ki dauki waya. Akwai wani albishir da zan yi miki mai dadi"
Sai kuma ya sake kira, kamar ba zan
dauka ba kuma sai curiosity yayi getting
the better of me, na dauka amma ban ce
komai ba sai yace "albishirin kj' nayi shiru
amma zuciya ta tana bugawa, ko Abba ya
gaya masa wani abu ne? Yace "baki ce
goro ba" a hankali nace "ka fadi abinda
zaka fada ka koma gurin matarka" ya
danyi dariya, wani takaici ya sake kama ni,
wato ya kira nine kawai dan ya yi min
dariya, nan take na fara hawaye "au dama
kira na kayi kayi min dariya ko? Kai ba ka
damu bama da abinda nake ji a raina, you
don't care".
Ya dan gyara muryarsa da take dauke da
alamun bacci yace "one day you will be
here on my bed and I will tell you the
story of what happened yesterday night
and you will laugh too, kinji? Believe me
abin dariya ne ba na damuwa ba. Kinji
sweetling?" Na goge hawaye na da hannu
na nace "to ka gaya min yanzu mana in da
gaske kake yi. Me yasa sai ranar da baka
da tabbas din zuwanta?" Yace "ina ji a jiki
na cewa zata zo mana Piya, Ina ji a jiki na
nan ba da dadewa ba zaki zama mallaki
na" sal ga murmushi yana replacing
hawaye na. "Abba yace maka wani abu ne?” Yace “bai ce min komai ba, nayi ta binshi amma ko maganar baiyi ba min ba sai Haidar naji yana gayawa Mama ita ma sai ta share maganar. Daddy bai ce miki komai ba?”
Na danyi shiru sannan nace “bai ce komai ba akan zuwan Abba. Amma ya gaya min wata maganar daban” yace “wacce maganar? Me yace?” Nace “yace Wai ya zaba min miji, kuma zai daura min aure nan ba da dadewa ba” muka yi shiru gabaki day sai yace “are you thinking what I am thinking?” Na danyi murmushi “yes. yes I am” ya danyi karar murna “yes!” Nayi dariya sosai “zaka tayar da makota daga bacci fa” yace “let them them wake up. Kowa ma ya tashi bacci yakare” Nace “ba lallai ne abinda muke tunani shine ba fa” yace “think positive” na sauke ajiyar zuciya amma still ina jin hankali na bai kwanta ba, sai dai murnanar da yake yi ta sanya ya min rai sosai, yace “su fa sun dauka suna playing din mu ne, basu san mu muka je fa kwallon a field din ba” nayi murmushi “idan suka gane kuwa zasu iya fasa abinda suka fara” yace “ai manyan mutane ne, basa magana biyu, indai har sunce yes din shikenan magana ya kare”.
Mundade muna hira, har sai da gari yayi haske sosai sannan yayi min sallama tunda zai fita gurin aiki, sai a lokacin na tambaye shi "wal wanne albishir ne kace
zaka yi min?" Yace "to ai baki ce goro ba,
shi yasa na fasa gaya mik'" nace "goro"
yace "I love you, Shine albishir din, I love
you so much" na lumshe ido na na bude
ina jin kamar bani da wata damuwa duk
duniya, sai kuma nace "and i love you too
by Baby" sai kuma na katse kiran da sauri
na kife wayar tare da rufe idona ina zabga
murmushi kamar tababbiya, sai kuma na
fara jejjefa kafafuwa irin yadda yara suke
yi in suna murna daga nan kuma sai na
mike tsaye akan gadon na fara tsalle, sai da nayi mai isa ta sannan na fadi na kwanta akan gadon ina
mayar da numfashi na. Wata zuciyar ta
tambaye ni what if ba shi bane zabin
Daddyn? What if Abba da Daddy basu
daidaita ba and Daddy yaji haushi yayi
deciding on someone else? Nayi sauri na
kawar da tunanin tare da maimaita abinda
Muhammad ya gyaa min dazu "think positive".
Na tashi na saka hijab dina akan dogayen
kayan baccin jikina na fita, yau saboda
farin cikin da nake ji ni zan yiwa yan gidan
nan gabakidaya breakfast. A kitchen na
samu Esther har ta fara peeling potatoes, na dauko kajl daga freezer na fara akin su ni kuma, muna yi muna hira da dariya and she mentioned that yau ma that person ne ya kuma saka ni farin ciki, ranar ban
boye mata ba kawai sai na gyada mata kai
amma ban kara komal akan hakan ba
Bayan mun gana mun jera komai a dining sai na koma sama zan shirya ita kuma ta fara hidimar gyaran gida, sanda na kuma saukowa duk mutanen gidan sun tashi,
muka wuce dakin Daddy na fara gaishe
shi tare da kissing cheeks dinsa sannan
na bi su twins duk nayi kissing dinsu na
koma kan Mommy ita ma nayi mata kuma
na rungume ta, ta janye ni tana kallon
fuska ta da alamar tambaya amma sai na
share. A lokacin ma sai da na kara yi wa
Daddy maganar Mustapha, twins suka
taya ni rokon sa and he said he will
consider it. "Zai dawo, amma ba yanxu
ba. Akwai abinda nake jira", Mommy tana
kallon mu bata ce komai ba.
Ranar haka na wuni da murmushi a fuska ta Muhammad a makale da ni a waya yana ta yi min nacin yana son gani na amma na gaya masa babu dama, tunda na gaya wa Daddy cewa na rabu da shi bana son yin wani abu ko yaya ne da zai nuna wa Daddyn cewa karya nake yi. Kuma a wani bangaren na zuciya ta har yanzu ina tunanin kallon don Muhammad after maganganun da muka yi ranar nan. Da yamma sai ga Uncle Ahmad, ya shigo ciki muka gaisa sannan ya shiga gurin Daddy suka jima suna magana sannan ya fito shima da murmushi a fuskar sa, "God is really amazing" ya fada a lokacin da yake yi mana sallama. Muka bishi da ido ni da Mommy har ya fita sannan Mommy ta tabe baki "ba dai za'a taba chanjawa tuwo
suna ba, komai gyaran da za'a yi masa kuwa".
Ranar na zo kwanciya bacci sai ga
message from one of my guards
"Mukhtar was seen lurking around this
area. Be careful". Na alive wavar tare da
yin ajiyar zuciya. Mukhtar bashi da hankali
tabbas, yana kuma son ya kure nawa
hankalin. Sun riga sun san abinda zasu yi
in suka kama shi, dan haka ban sake
maimaita musu ba.
Haka kwanaki suka yi ta wucewa, babu
wanda aka cewa komai a cikin mu daga ni
har Muhammad, shi na fahimci hankalin
sa a kwace yake amma ni sam nawa ba'a kwace yake ba except idan muna waya da Muhammad. Gani nake ba Muhammad ne Daddy ya zabar min ba, gani nake yi Muhammad is too good to be true with me dan ni na saba da bad news, bad news na sani tun kafin haihuwa ta dashi na saba dan haka good news din sounds weird to me.
Kwanaki biyar bayan zuwan Abba sai ga
Uncle Sufyan yazo gidan mu, nayi murnar
ganin sa sosai na gaishe shi sai kuma nayi
ta kalion bayan sa ko zan ga Aunty Hajjo
ta shigo, sau yace min "ba tare muka z0
ba aj" sai naji kunya ina fatan ba wai yana
nufin Junior nake nema ba, ni kuma har
ga Allah Aunty Hajjo nake nema,
maimakon ita sai Abdul naga ya shigo da
leda a hannun sa, na gaishe shi shima sai
gaishe da Mommy tare da miko min ledar
hannunsa sa "tsaraba" yace yana
murmushi, na karba nayi masa godiya sai
suka wuce gurin Daddy.
Na bude ledar, kayan ciye ciye ne kawai iri
iri, exotic biscuits and chocolates. Na
mika wa Mommy "gashi Abdul ya kawo
min" ta tabe baki "ni kika ga ya bawa?"
Sal naji babu dadi, na cigaba da tsaiwa da
ledar a hannu na sai tace "abinda vasa
aka kala wa Mustapha wani sharrin kenan
aka kore shi, Abdul ake so a dawo da shi.
Kuma na san wanna duk hadin Ahmad ne, Dan dan sa dan akuya ne ya san ba za'a mayar masa da ke ba shine ya kwaso Abdul. Ai shikenan". Na juya ban ce mata komai ba na koma sama, bana son obsession din Mommy akan hada aure tsakani na da Mustapha,
wannan obsession din shi ya rufe mata
ido gabakidaya. Ya kamata ace ta gane
bana so ne kawai kuma hakan baya nufin
bana son ta ko yayan ta, baya nufin kuma
zan daina kula da su. Auren Mustapha ne
bana so and there is no amount of nagging da zata yi da zai saka in chanja.
Amma kuma bayan na koma daki na bude one of the biscuits ina ci sai wani tunani ya fado min, what if Abinda Mommy ta fada akwai gaskiya a ciki? What if Abdul Daddy ya zaba not Muhammad? Na fito
da biscuits din bakina da sauri na zubar a waste bin sannan naje toilet na wanke bakina ina kallon kaina ta mirror, "Ya Rabbi" na fada a hankali. Tun daga nan
kuma sai hankali na ya tashi,
A gidan suka karasa wunin ranar, har sai da suka ci abincin dare sannan suka tafi. Banji dadin yadda na hadewa Abdul rai ba duk kokarin da yayi na ganin munyi hira sanda na sauka gurin Daddy, na ga kuma
shima bai ji dadin hakan ba a fuskarsa amma kuma I couldn't help it. Ya zanyi idan maganar Mommy ta kasance. Ranar sai da nayi kuka kafin inyi bacci amma
ban yarda na nuna wa Gidado ba duk
kuwa da yaso ya fahimci ina cikin damuwa, Washegari Friday sai ga Uncle Ahmad da sassafe muna breakfast ya shigo da kansa yana tambaya ko akwai
abinda ake bukata na cefane a gidan, yace za'a yi baki ne in an jima bayan sallar juma'a. Mommy ta tambaya su nawa ne vace bai sani ba kawai dai ayi abinci da
yawa kuma na fita kunya. Bata ce masa komai ba amma da aka jima sai gasu sun dawo shi da yaya da ledoji cie da kaji da vegetables ta fruits. Sai kuma kwalayen lemuka na alfarma.
Mommy ta tashi ta shiga gurin Daddy sai
kuma ta fito ranta a bace ta hau sama.
Hakan ya sa na fahimci ba zata yi girkin
ba, dan haka na cire hijab dina muka
shiga kitchen nibda Esther muka kama
aiki, muna cikin aikin Hussain ya shigo
shima na tisa keyarsa zuwa kitchen din na
bashi aiki, Hassan ya shigo shima na jawo
shi, tun suna bata rai har suka saki jiki
muka yi ta aikin muna hira Hassan har da
kunna kida yana rawa. Sai da muka ci
karfin aikin sannan muka sallame su dan
kar su makara masallaci mu kuma muka karasa
Abinci kam munyi shi, friend rice da taji
Kayan hadi da kuma hanta, sai mandi rice
Ita kuma de aka hada ta da gasashshen
naman ragon da yayi laushi sosai, sai
kuma muka yi brown superghetti da kuma
cheese macaroni, sai tuson shinkafa
miyar zogale sannan sakwara da miyar
agushi, Sa peppered chicken da salad,
Sannan fruits. Mun yi aiki kam mun gaji
sosa), dan ma kowanne variety ba wai da
yawa muka yi sosai ba amma munsan zai
isa tunda abubuwan da yawa, Muka gama
juye komal a warmers, muka ware na
abincin gida muka Esther ta kai dining ta
jera ni kuma na fara kokarin hawa sama
sai gata ta dewo tana cewa wai ai bamu
gama ba tunda bamu yi farfesu ba,
*Abinci baya zama complete sai an hada
da pepper soup" na harare ta, ssi kiyi tayi,
ni dai ba inji bace ba kuma na gaji, ke kika
ce ba kya so a kawo miki mai taya ki aik™️"
La dega kafada "indai farfesu ne yanzu
kuwe zanyi, akan sa za'a hada ni da wata? Ai kuwa gwara in kwana ina yin farfesu, kala biyu zanyi ma ko uku. Haka kawai?” ta koma kitchen tana mita ni kuma na girgiza kai kawai na koma daki.
Dana shiga sai na tsiri aikin gyara kayana ina kokarin Cire zuciya ta daga tunanin bakin Daddy, su Waye? Me kuma ya bata ran Mommy haka? Sam bana jin dadin bacin ranta. Sai na fita na tafi dakin ta na tarar da ita a falon ta na sama a zaune tana waya, “wallahi sakina na gaji da halin mutumin nan. Allah hakurin da nakeyi ba kowacce mace zata iya irin sa ba. Sam Sam baya ganin daraja ta da kima ta, dani da babu duk daya. Kawai daga tambayar su Waye bakin da zasu zo sai ya fara neman gayamin magana……” sai na juya na koma ba tare de na karasa shige ba,
Ina komawa dakin sai kawal na cigaba da
gyaran kayan da na fara, amma still zuciya
ta tayi min nauyl, ban gama ba kuma sai
na barshi na shiga toilet nayi wanka na
fito ina tunanin kiran Muhammad ko naji
muryarsa inji dadi amma kuma sal na
tahimel lokacin masallaci ne, dan haka sai
na barshi na shiga closet dina na dauki abaya mai dogon wando na saka ba tare da na yi wata kwalliya ba except for mai da turare, lokacin na san an gama fitowa daga masallaci, Amma still ban kira Muhammad ba sai na tayar da sallah, sai dai banjima da tayar wa ba naji alamun motoci suna shigowa gidan mu, nayi kokarin yin sallah ta a nutse sannan nayi addu'a na shafa sai kuma na mike na daga labulen
tsegumi na na leka waje. Bakin motoci na
gani guda uku, Ban san ko daya daga ciki
ba. Sai motar uncle Ahmad da ta uncle
Sufyan. Na ci gaba da kalion motocin ina
jin faduwar gaba a karshe ma kawai sai na
koma na zauna a bakin gado ina kallon
hoton Ammie rungume da ni. A hankali
nace "Hey Ammie".
Wayata naji tayi kara alamar shigowar
sako, na dauka da sauri ina tunanin ko
Muhammad ne amma sai naga alert ne
daga banki na, personal account dina,
bana expecting wani kudi da zai shiga ciki
dan haka na bude, na tsaya ina kallon
kudin, sannan na kalli sunan wanda ya
turo min kudin "Abbakar Sadiq Abdallah"
ban taba jin sunan ba tun da nake, sai
kuma na kalli caption din "sadaki".
Gaba na yayi wata irin faduwar da sai da
na zamo daga kan gadon na zauna a
kasa, Abbakar Sadiq Abdallah? Waye
wanna kuma ni Safiyya? Na shiga uku.
Kar dal ace Daddy aure na ya daura da
wanna mutumin da ban ma taba jin sunan sa ba.
Karar waya ta ce ta dawo da ni hankali na,
na dan zabura kadan saboda tsoratani da
karar tayi, tun kafin in dauka na san
Muhammad ne, wayyo Muhammad,
innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Amma
kuma sai nayi tunanin bara in dauki kiran
nasa inji yana ina, watakila zan samu wani
bayani daga gare shi.
Na dauka na saka a kunne na ban ce
komai ba sai naji muryarsa fes a kunne na,
kamar ma a hanya yake "hey sweetling.
Kin ganni yau a kafa na tafi masjid saboda
in samu lada" na dan dake nace "kana ina
yanzu?" Yace "ina hanyar komawa gida,
are you okay? You sound not okay" sai
kawai na katse kiran tare da ajiye wayar a
gefe na. Ina jin shi yana cigaba da kira na
amma ban dauka ba. Waye wannan
Abbakar Sadiq din? Menene dalilin Daddy
na hada ni da shi? Da gaske an daura min
aure da shi?
Na cigaba da zama a gurin kamar gunki
har adadin mintuna ko awannin da ban
sani ba, Sal kuma naji anyi knocking kotar
dakina, automatically nace "shigo" ba
tare da nayi tunanin waye ba, kamshin
turaren da naji ya saka na juva, Uncle Ahmad ne, ya ci kwalliyar sa cikin manyan kayan da daga gani sabon dinki yayi ga hular sa ya saka da tayi matching da
kayan sa, fuskarsa kamar gonar auduga,
kallo daya nayi masa na dauke kai, kowa
ma haushi yake bani.
Ya shigo sosai ya zauna akan kujerar da
take dakin tana kallon gadona shima yana
kallona yace "Safiyya" na daga kai na
kalle shi na mayar da kaina kasa, yace
"kinga sako kenan?" Na gyada masa kai
kawai, sai ya sake yin murmushi yace
"yaya ya gaya min cewa kin bashi wuka
da nama, kince kin amine ya zaba miki
koma wanene yake gain shi ya dace da
ke. Ya kuma zaba din, nima kuma na
aminta da zabin na sa bayan yayi min
bayanan dalilin yin zaben. Na shigo ne
yanzu in gaya miki an daura miki aure
yanzun nan" yayi shiru muna jin alamar
fitar motoci daga harabar gidan. Yace
"Allah ya sanya alkhairi ya yi miki albarka"
sai ya mike tsaye, nayi sauri nace "uncle
waye...….???" Sai kuma na kasa karasa
tambayar, ya karasa min "waye angon?
Kar ki damu, zai zo in an jima da daddare
sal ku ga juna, Ina so ki saka a ranki cewa
duk duniya babu wanda yake son ki sama
da Adam kuma ba zai taba zaba miki
abinda zai cutar da ke ba" ya kai bakin kofa na sake tambayar sa "uncle an gaya wa Mommy?" Ya daga kafada "mijin ta ne ya yanke wannan hukuncin, shine kuma zai gaya mata da bakin sa. Ni ba za'a ji
mutuwar sarki a baki na ba". Na bishi da kallo ina kokarin digesting maganar sa. Kiran da ya shigo wayata ya katse min tunanin na dauko wayar ina kallon sunan Muhammad ”pyar💕” sai kawai na katse kiran tare da kashe wayar gabakidaya na ajiye ta sannan na tashi na gabatar da sallar la'asar din da ake tayi a
masallaci, ni dai ba zan iya cewa ga abinda nake ji zuciya ta ba dan wani irin zafi da zugi take yi min.
Da na idar da sallar ma sai na kasa yin
addu'a mai tsaho kamar yadda na kasa
yin kuka, kawai na zame na kwanta a kan
sallayar na lukluba da hijab din jikina ina
jin sanyi yana ratsa kasusuwa na. Anan na
cigaba da kwanciya har aka yi sallar
magrib, babu wanda ya leko gurina nima
kuma babu wanda na nema, naji ina
missing Ammie sosa da sosai, wai aure
aka daura min yau.
-Na tashi duk da sanyin da nake ji na je
nay alwala na dawo nayi sallar magrib
sannan na cigaba da zama akan sallayar
ina ta kiran sunayen ubangiji da niyyar ya kawo min dauki ko ya kawo min sassauci a zuciya ta. Ina nan zaune naji an sake turo kofar an shigo tare da sallama, na juya da sauri jin muryar da nayi kamar
daga sama, Muryar Aunty Hajjo, na bita
da kallo har ta karaso cikin dakin ta kunna
fitila tana kallona da murmushi a fuskar ta
"amarya" na sunkuyar da kaina ina fatan
hawaye zasu zo ido na ko zan samu sanyi
a zuciya ta, na kasa ko da gaishe ta ne, ta
zo gaba na tare da kamo hannuna ta rike
a cikin nata tace "k gaishe ni ba zaki yi
ba? Ke fa kika ce kin ba da zab'" ta fada
cikin tsokana, na bude bakina da niyyar
gaishe ta amma muryar taki fitowa sai na
mayar da kaina kasa, tace "ki tashi ki
shirya ga angwayen can sun zo zapsu
ganki" na sake dago ido da sauri na kalle
ta sake yi min murmushi sai nayi sauri na
girgiza kaina "ni ba zan je ba. Ni bana son
zuwa. Ni ban san shi ba. Ni bana son shi"
sai na ga ita dariya ma abin ya bata. "Ya
akayi kika san ba kya son sa bayan ko
ganin sa baki yi ba?" Ni dai ban ce mata
komai ba amma na san ko waye shi ba
zan so shi ba dan babu wani space a
zuciya ta da Muhammad bai cika ba.
Ta matsa wai lallai sal na tashi na shirya na chanja kaya, na tubure mata taga ina neman inyi mata dan karamin hauka sai ta rabu da ni tun da ta lura kayan jikina ba wai sunyi muni bane ba, amma sai ta
kwaso turare tayi ta fesa min har sai da
naji yayi min yawa a kaina, sai kuma ta
nemi mayafi mai dan girma ta lullube ni da
shi ta kama hannu na muka fita. Muna fita
daga dakina na juya ina kallon hanyar
shiga part din Mommy, a hankali nace da
aunty Hajjo "Mommy fa?" Ta kalli kofar
tace "tana gurin Daddyn ki" daga haka ta
ja hannuna muka sauka kasa. Ni dai ina
kankame da hannunta jikina sai rawa yake
yi kaina a kasa har muka sauka, naji alamar akwai mutane kuma maza a falon saboda maganganun da suke yi kasa kasa amma muna gama saukowa suka yi shiru, ban daga kai na kalle su ba sai ma sake
shigewa jikin Aunty Hajjo na yi wadda ita
naga kamar ma abin dariya yake bata, da
kyar ta jawo ni daga bayanta ta tsayar
dani a gabanta sannan a hankali kamar
mai rada tace min "ta yaya zaki ga angon
naki idan baki daga idon ki ba?",
A hankali na daga idon na nawa, zasu kai
su shida ko bakwai a falon duk da ban
tsaya kirga su ba. Na fara kallon su daya
bayan daya, duk da murmushi akan
fuskokin su, a fuska ta biyu naga Haidar,
yana kallona da murmushi a fuskar sa, najl
zuciya ta ta buga da karfi, a take na bude
luska ta sosal a fara baza idon neman sa, and then I saw him, smiling brightly from ear to ear, hasken hakoransa yayi matching da hasken fararen kayan jikinsa wadanda suke kyalli da sheki kamar
yadda fatar jikinsa take yi. Sai na ga
kamar gabakidayan sa ya zama tamkar
farin wata dan daren goma sha biyar. Ya
mike tsaye idanunsa suna kyalli, reflecting
the love he has for me, sannan a hankali
ya bude min hannayensa.
Na saki hannun aunty Hajjo, ba tare da na
jira komai ba, ba kuma tare da na damu
da tarin mutanen da suke gurin ba, na
wuce straight zuwa kirjinsa sannan ya
mayar da hannayen ya rufe ni a ciki. A
take na saki kukan da nake ta fatan zuwan
sa tun lokacin da aka daura auren.
Ina jin yadda gabakidaya falon ya rude da
hayaniyar da take nuna murna.
Maganganu suke yi hade da dariya
gabakidayan su a lokaci daya amma bana
jin abinda suke fada, bana jin komai sai
sound guda biyu a lokaci daya, daya na
bugun zuciyar shi da nake jin ta kamar a
cikin kunnena take bugawa, dayan kuma
na murmushi mai sauti da yake fitarwa
wanda nake jin sa tamkar a cikin
kwakwalwa ta yake yinsa, sai naji wannan mix na sautuka tamkar shi ya fi kowanne sauti dadin sauraro.
Ya kara matse ni a jikinsa da hannu daya,
sannan ya saka daya hannun a hankali
yana bubbuga baya na dashi alamar
rarrashi, sannan a cikin kunne na yace "it
is okay. Ya isa haka. Muhammad Gidado is
here. You are okay kinji?"
Na daga kai a hankali na kalli fuskar sa
kamar mai tabbatar wa da cewa shi din ne
ba wani ne ba, ya sunkuyo da kansa
shima muka kalli jina cikin ido sai kuma
nayi saurin mayar da tawa fuskar kasa ina
jin kamar numfashi na zai dauke, we have
never been this close, I have never been
this close to any man.
Aunty Hajjo ce tayi gyaran murya, sai naji
kunya ta kama ni kamar zan nutse a kasa,
da sauri na kara jawo mayafin jikina na
kara rufe fuska ta dashi, tace "wanne rufe
fuska kuma zaki yi? Ni da kika manta da ni
ma? Babu komai ai yau na san matsayi
na" mutanen gurin suka yi dariya, nima
nayi tare da kara sunne fuskata a kirjin
Muhammad, tace "babu komai mu hakan
da ma muke fata, Sako ne dama na zo isar muku da shi inji parents din ku. You are a reward to each other for being good kids. Fatan su kawai tare da mu gabaki daya shine ku cigaba da zama yaran kirki. Allah
kuma yayi muku albarka".
Gabakidaya aka ce Ameen, ta juya zata
tafi, na bita da kallo sai idona ya sauka
akan Daddy a can kofar shiga part dinsa,
yana zaune akan wheelchair din sa idonsa
a kaina fuskar sa dauke da murmushi. A
hankali nace masa "thank you" ta hanyar
motsa bakina yadda babu wanda yaji
sound din sai shi da yake kallo na. Ya
gyada kai sannan ya daga hannun sa yayi
min thumbs up sai kuma ya juya ya koma
cikin part dinsa ya rufe kofa.
Maman Maama✍🏻
[07/01, 10:46 pm] +234 906 816 1960: ❤️🩹Safiyya❤️🩹
Episode Sixty One: Selfishness
Not Edited
Him👳🏻♀️
One week ago
Idan yace a cikin nutsuwa yayi wannan
sati to tabbas yayi karya, daga shi har duk
wanda yake tare da shi ya tabbatar cewa
ba'a nutse yake ba. Sau da yawa mutanen
da suke tare da shi sukan tambaye shi
"are you okay?" Sai dai ya gyada musu kai
kawai ya sharar da maganar dan baya son
yin karya kuma baya son yin bayanin
abubuwan da suke damun sa din.
Na farko akwai labaran da Safiyya ta bashi
na gaskiyar abinda ya faru da ita, gaskiyar
abinda ya jawo ta rabu da shi a wancan
karon. Zai iya cewa tunda ya zo duniya bai
ta ba jin abinda ya daga masa hankali ba
irin wannan maganar, wannan tashin
hankalin ya janyo har likita ya gwada jinin
sa kuma ya tabbatar masa da cewa yana
gab da samun cutar hawan jini,
Sai na biyu kuma fahimtar da yayi cewa
duk maganganun da suka yi da Safiyya
Daddyn ta ya gansu kuma ya ji su,
wannan ma ya saka shi cikin damuwa dan
bai san wanne mataki Daddyn zai dauka
akan abinda yaji kuma ya gani ba. Will he
be satisfied cewa ya cancanta ya bashi
yar sa kamar yadda ya fahimci Safiyya
tana saka rai ko kuma zai raba su ne for
the second time. Ian kuma hakan ta
kasance anya kuwa zuciyar sa zata iya
dauka? Anya?
Sai dai kamar yadda Safiyya tayi shima sai
yabi hint dinta, sai ya sanar wa da
iyayensa duk biyun cewa ya hakura da
auren Safiyya tunda basa so, amma kuma
ba wai dan shi baya so ba, ya kuma nuna
musu irin damuwar da wanna hukunci
zai jawo masa, sannan kuma sai ya cigaba
da addu'a ba dare ba rana akan fatan
Allah yay guiding iyayen na sa su zaba
masa abinda yake mai alkhairi a gare shi.
Abu na uku kuma da ya dame shi a cikin
satin shine yadda Mama ta rufe idonta
tace ya tattara matarsa su koma gidan su
ta gama jinyar su. Haka yana ji yana gani
ya dauke ta a mota da kayan ta ya kai
gida. Dadin da yaji a wannan bangaren daya shine yadda Safinan ta dauke mass
wuta gabadaya ko kallon inda yake bata yi
ba tunda ta shiga motar har ta sauka, shi
kam sai yaji hakan yayi masa dadi sosai.
Suna sauka kuwa kowa ya kama gabansa.
Abu daya ne yake kwantar masa da
hankali a duk wadannan al'amuran, shine
waya da Safiyya. In suna waya manta wa
ma yake yi da kowa da komai ballantana
har ya tuna da wasu problems da suke
tattare da kowa da komai din. Duk da son
da yake yi ya ganta amma haka ya hakura
saboda babu dama. Duk kuwa da damuwar da yake ciki haka ya daure ya ke nuna mata bashi da damuwa dan baya son taji damuwar sa tai breaking down.
Shine namiji dan haka shi zai zama
strength din ta
Sanda ta bashi labarin zuwan abban sa
gurin Daddyn ta yayi mamaki dan Abban
bai ce masa komai akan hakan ba. Ranar
ma bayan sun gama waya haka ya tafi
gida yayi ta zama ko zai ji abban ya ce
masa wani abu amma sai yaji shiru babu
bayani. Ranar kuma da ta gaya masa
abinda Daddy yace mata akan ya zabar
mata mijin aure sai ya nuna mata yana
murna, ya nuna mata yana tunanin shine
wanda Daddy din ya zaba, yayi hakan ne
dan va qa alamar zuciyar ta cike take da doubts amma kuma a zahirin gaskiya ta sa zuciyar ta fi tata raunana akan lamarin
Sai ya ga kuma hakan ya yi lifting spirit
dinta sosai ta kuma dan saki jikinta suna
cigaba da faranta wa junan su rai but
kowa a cikin su akwai doubt din shi.
His second major concern aside not
having Piya is what to do with Safina.
Safina have been like a thorn in his heart
tunda ya san ta ya san wacece ita, bai
taba tunanin zai iya wulakanta mutum
kamar yadda ya wulakanta Safina ba, bai
kuma taba tsammanin akwai macen da
zata dauki abinda Safina ta dauka daga
gare shi ba. She did everything she did
saboda tana sonsa, or rather because she
is obsessed with him, dan shi bai yarda
abinda take ji a kansa soyayya ce ba. At
the end kuma, she lost everything.
Wannan shi yasa yake jin tausayin ta a
kasan ransa, musamman bayan tayi
miscarriage, duk da cewa ba da ne ta
haita ta kuma rasa ba amma ya san a
matsayin ta na uwa already ta so abinda
ya zauna a cikin ta, Wannan ya sa yake daga mata kafa yanxu sosai, ya daina yi mata kallon wulakanci
¡ya kuma daina gasa mata bakar magana,
ya kan shiga gurin ta kullum ya dauki kudi
ya bata ya kuma tambaye ta in akwai
abinda take so. Sai kuma ya fahimci ta
fara daukan hakan a matsayin wani abu
daban, har ta dawo da yi masa girki
wanda tun a ranar farko da ta yi masa ya
gaya mata ta daina "ba ci zanyi ba, barnar
abinci kuma babu kyau" hakan ya sosa
mata rai sosai har ta zubar da kwalla ta sa
ya kuma jin tausayin ta but he stood his
ground, any na farko anyi na karshe,
yanxu kaffa kaffa yaje yi da sha ko cin duk
wani abu da yake gidan dan gudun kar a
kuma, kar ta kara samun damar yiwa
rayuwar sa illa. Sai dai kuma Safina wata
halitta ce wadda a duk lokacin da kaji
tausayin ta sai tayi wani abun da zai saka
kaji tausayin kanka for jin tausayin ta. Ya
fahimci rawar kafar da take tayi a kansa
tunda ta fahimci ta fara samun sassauci a
gurinsa, kwalliyar ta dawo, saka matsatstsun kayan sun dawo, amma shi yasan ba zai iya bata abinda take so ba, ba zai iya ba, wannan shi ya sake tuna
masa cewa dole ya san yadda zaiyi ya
rabu da ita as soon as possible dan idan
ba haka ba zata jashi zuwa wuta for not
fulfilling her sexual desires as her husband,
A bangare daya kuma har yanzu bai cire
Mukhtar a ransa ba, Safiyya tace yayi
mata alkawarin ba zai taba shi ba amma
ko a lokacin bai yi alkawarin ba, kuma
baya jin zai iya. Wani irin rage yake ji a
ransa a duk lokacin da ya tuna da shi. Ya
san kuma rage din da yake ji just need a
little push zai yi exploding, push din kuma
might be as little as seeing Mukhtar din.
anar Monday yaje gidan su kamar yadda
ya saba yi duk sanda ya tashi daga aiki,
sai dai tun a waje ya ga motar Uncle Faruk
a harabar gidan su, bai ma san uncle din
nasa ya zo gari ba dan haka ya shiga cikin
gidan da murnar sa dan yayi missing din
shi. Amma sai dai yana shiga ya ga
Mommy (his grandma) a zaune a falo tare
da Abba da Mama da kuma shi uncle
Faruk din. Ya kara fadada murmushin sa,
ba zai iya tuna ranar da yaga Mommy a
gidan su ba, bata zuwa sai dai su je
gurinta,
"Matar" ya fada da murmushi "yau auren
ne ya kawo ki har gidan nan? Ko biko kika
20 dan kinga kwana biyu ban leka kin
ganni ba?" Ta watsa mass harara "ohh
Wali nan kai namiji ne? Namijin da har za'a
y) biko idan yayi yaji?" Uncle Faruk yana dariya yace "maganar gaskiya dai Mommy bikon kika z0, kinga kyakkyawan saurayi kim kasa zama sai da kika biyo shi har gidan su" ta tabe baki "ina abin yake?
Zama kyawawa ai sun kare. Tun da mijina
ya mutu babu wani namiji da zai burge ni
anan duniya".
Gidado ya karasa gaban su yana jinjina
soyayyar Mommy da marigayi Muhammad
Dikko. Babu yadda za'a yi ayi magana da
ita bata saka shi a ciki ba. Ya durkusa ya
gaishe ta amsa tana kare masa kallo daga
kasa har sama, sai kuma ya juya ya gaishe
da Uncle Faruk amma sai uncle din ya
mike ya jawo shi jikin sa ya rungume,
Gidado ya lunshe ido yana jin zuciyar ss
tana yi masa dadi, yana son yan'uwan sa
sosai.
Har ya koma ya zauna Mommy tana bin sa
da kallo, sai da ya zauna sannan ya kalle
ta tare da daga mata kafada "what?" Bata
amsa masa ba sai ta juya gurin Abba
"gashi nan ai abinda na gaya muku tun
ranar nan kuka mayar da magana ta wasa,
jibi yadda matar can ta zuke yaron nan,
kunga yadda ya koma kuwa? Haka
gidadon yake? Yaro ya kare gabakidaya ya
lalace maimakon ace yayi kiba yayi
annurin aure amma shi sai bushewa da
naga yayi * Mama tace "Mommy kin manta bashi da lafiya ne? Accident fa yayi, har yanzu dinkin da aka yi masa a kansa bai gama warke wa ba, daga baya
kuma ya kwanta rashin lafiya again"
Mommy tace "dama haka zaku ce ai. To
waye ya saka yayi accident din? Ai
Maimoon ta gaya min komai abinda ya
faru, kuma waye ya saka ya fara rashin
lafiyar? Ba damuwa aka ce tayi masa
yawa ba? Me zai saka shi damuwa in da
yana samun kwanciyar hankali da iyalin
sa? Gaskiya da sake. Ai na ga ba kwa daukan abin da
muhimmanci shi yasa nace auta ya kawo
ni har gidan naku dan ku fahimci
muhimmancin magana ta" Abba yace
"Mommy rashin lafiya ai daga Allah ne ko?
Ai wani baya saka wa wani rashin lafiya"
ta harare shi tace "Allahu Akbar. Mai
karatu na gaba" ta nuna Mama "ke zaki
dora daga inda ya tsaya? Aya zaki jawo
min ko hadisi?" Mama ta girgiza kai da
sauri sai uncle Faruk ya yi dariya, Mommy
ta juya ta watsa masa harara sai ya dauke
kansa gefe yana kunshe sauran dariyar
sa. Mommy ta cigaba "magana daya ce
nazo da ita, Yaron nan aure za'a sake yi
masa. Ga jikoki nan kyawawa Allah ya hore min su, in ma baya so a cikin su yaje ya zabi wacce yake so a waje ya kawo in dal tayl a aura masa ita. Ba zan zauna ina kallo a cutar min da jika ba wallahi. Haka
kawai ba zai kare yarintar sa cikin wahala
dan ya faranta muku ba".
Abba ya yi gyaran murya ya fara magana
cikin lallami dan ya fahimci sosai
mahaifiyar ta sa ta dauki zafi. "Mommy ki
kwantar da hankalin ki. Mun riga mun
gama magana da ma da Zainab akan
issue din yaron nan. Har ma na yi waya da
Habib da Moon nace mu hadu yau a gidan
ki mu tattauna akan maganar dan mu
tsayar da shawara daya. Amma tunda
kinzo nan din kuma kinzo da maganar ba
ra in kira su kawai sai ince su taho nan
gidan, tunda ga Faruk ma yana gari...
Tace "auren za'a yi masa dai k0?? In ba
wannan maganar bace ba bana son jj"
Mama tace "auren za'a yi masa Mommy.
Insha Allahu in muka yi miki bayani zaki
fahimta" Mommy tayi ajiyar zuciya "zan
saurara inji. Duk wani hukunci da za'a
yanke ina nan zaune zaku yanke shi. Ba
zan barku ku sake daukan wani shirgegen
aikin ku hada shi da shi ba. To me yayi
zali shi ba wuta ba? Haka kawai
santalelen saurayi kamar wannan a tashi a
dabaibaye rayuwar sa a guri daya a hana shi zaben abinda yake so. Ni ba dan Ayaan ya riga yayi maganar Khausar ba da Gidado zan bawa"
Faruk yace "wai ya batun Bassam kuwa?
An gano inda yake?" Abba yace "eh an
samo shi. Yana wani hotel ya kama daki,
Sun rufe masa account din sa dam haka
very soon zai nemi gida da kansa. Ja'irin
yaro mai tsaurin ido" Mommy tace "irin na
ubansa ne ai. Wanne irin tsaurin ido ne
ubansa bai yi ba? Zasu zo su saka yaro a
gaba wai yayi rashin kunya bayan su babu
irin rashin kunyar da ba su yi ba".
Gidado da tunda Mommy ta ambaci
kalmar aure yaji cikin sa ya juya, yana
sane da kallon da Mama take jifansa da
shi da nufin ya tashi ya basu guri amma
yayi kamar baya ganin ta dan so yake yaji
komai a maganar, sai dai kuma sai yaji sun
saki maganar sa sun koma maganar
cousin dinsa Bassam da yake son khausar
ita kuma suna soyayya da Ayaan, wannan
ya sa yayi yaji ya bar gidan Auntyn su
Hafsat bayan yayi mata rashin kunya, ya
koma hotel da zama, yanzu yadda za'a yi
ya dawo gida a hukunta shi ake nema.
Yana jin Abba yayi waya da Mammy da
kuma Uncle Habib yace su zo gidan sa,
sannan suka cigaba da hirarrakin su. Sai da Mama taga dai bashi da niyyar fita sannan ta kira sunan sa direct. "Gidado" ya juyo ya kalle ta "tashi ka tafi" babu
musu ya mike tare da yi musu sallama ya
fita, Sai dai kuma zuciyar sa bugawa take
yi sosai, ya tabbatar tunda Mommy ta
dage akan maganar auren nan to dole sai
anyi shi? Amma kuma da wa? Kar fa aje a
sake daura masa igiyar da zai kasa
kwance wa bayan ga waccan igiyar har
yanzu yana fama da ita.
Haka yaje yayi ta shawagi a gari, yasan in
yahe gidan sa ma wani takaicin zai tarar, a
karshe sai ya tafi gidan Ya Amen ya ci
abinci a can suka kuma tattauna akan
maganar. Ya gaya masa duk abinda ake
ciki, except for abinda ya samu Safiyya,
ya dai nuna masa iyayen ta ne suka matsa
mata suka hada ta aure da Mukhtar,
yanzu kuma da zaman auren yaki yiwuwa
sai suka raba.
Anan ne Al'ameen ya kuma tabbatar wa
da kansa cewa Gidado yana matukar son
Safiyya kuma at this stage abu ne mai
wahala ya rabu da ita. Dan haka ya yanke
shawara a ransa cewa zai je ya gwada
bugar cikin Mammy yaji shawarar da suka
yanke kuma ya nuna mata abinda ya
tahimta da dan uwan nasa, Humaira ta fito sun gaisa, ya karbi Ayman yana yaba wa da yadda yaron yayi girma sosai, a ransa yana fatan ranar da zai ga
nasa dan shima, Sai kuma suka vi hirar
karatun da Humaira zata fara yi very soon
a jami'ar Oxford akan harkar zane zane.
Daga nan suka koma hirar Bassam and
his drama.
Sai da dare yayi sosai sannan ya tashi zai
tafi, Humaira tace ya gaishe da Safina, sai
yaga sun kalli juna ita da Al'ameen sunyi
dariya, ya tambaya "what?" Sai Humaira
tayi saurin girgiza kanta "babu komai fa.
Ka gaishe ta Please" koma menene bata
son ta gaya masa dan ta san tsakanin
mata da miji, kar ya gaya masa shi kuma
ya gaya wa matar tasa.
Sai bayan sun fita sannan Al'ameen ya ke
gaya masa ashe wai drama akayi ranar da
Safina tazo barkan Ayman. An bata jariri
taki karba wai ita bata iya daukan jarirai
ba, ai kuwa aunty Amina tana gurin dan
haka ta wanke ta tas a gaban mutane,
daga baya ta hada da nasiha, shine ta
shiga daki ta zauna ita kadai ta ki yiwa
kowa magana, Mufida ma da tazo tayi
mata magana da niyyar ko zata saki
jikinta, har tana janta akan su shiga
kitchen suyi girki tare sai tace ita ba zata bata kayan ta da kamshin abinci ba, ai kuwa Mufida taji haushi da kyar su Basma suka hana ta kula ta suyi rigima.
Shi dai Muhammad murmushi kawai yake
yi, a ransa hangowa yake yi Safiyya ce,
yana hango yadda zata shiga kitchen din
nan tayi girki, yana hango yadda zata
dauki babyn nan ta rungume, yana
hango..... Sai da Al'ameen ya taba shi
sannan ya lura da murmushin da vake tavi
"wato kai murna ma kake yi matar ka bata
samu karbuwa a family ba k0? Mugu"
Muhammad ya yi dariya kawai ya shiga
mota ya tafi amma ya san rashin samun
karbuwar Safina a family yana nufin
higher chance of samun karbuwar
Safiyya.
Duk da dare yay amma bai hakura ba sai
da ya biya ta gidan su wai ko za'a ce
masa wani abu, ya tarar bakin duk sun tafi
amma kuma daga Mama har Abba babu
wanda yace masa komai. Hakan kuma ya
damu zuciyar sa sosai. Gani yake da ace
maganar Safiyya suka yi ai da zasu gaya
masa ko dan su faranta masa ko?
Babu wanda ya kula shi da niyyar faranta
masa din sal anar Alhamis, ranar ne Abba
yay masa magana casually a harabar
gidan su sanda yaxo yake kokarin shiga, "Uhmm Muhammad, maganar da kaji munayi ranar nan da Mommy akan auren da tace ayi maka. Ka amince ayi?" Ya danyi shiru yana kallon sa ya rasa abin
cewa, gashi kuma abban a tsaye yake
amsa yake jira "aure Abba?" Ya tambaya
muryar sa cike da damuwa. Abba ya bata
rai "ka zama kurma ne?" Ya girgiza kansa,
there is a chance na cewa Safiyya ce
sannan kuma akwai chance na cewa ba
ita bace ba. Risk ne wannan zai dauka,
babban risk. Ya gwada tambaya "Abba
aure da wa?" Sai kawai ya ga Abban yayi
murmushi sannan ya dan daki kafadar sa
kadan yace "some one better than your
wife. We will never repeat the mistake we
did a baya" ya danji sanyi a ransa, tunda
ake maganar Safina sai yau yaji ra'ayin
Abba a kanta. Ya san dai koma menene
iyayensa ba zasu cutar da shi ba and he
trust they will make the best decision for
him. A hankali yace "shikenan Abba na
amince" Abban ya sake murmushi sannan
yace "Allah ya baka ladan biyayya" sai ya
juya ya shiga motarsa driver ya ja suka
fita.
Washegari juma'a ta zagayo amma babu
labarin komai. A juma'ar ne kuma bayan
yaje masallaci ya dawo Safiyya ta kira shi
da tashin hankali a muryarta, tambayar sa
kawai tayi yana ina sannan ta katse kiran ba tare da ta ce komal ba, yayi ta kira bata dauka ba, daga nan ta kashe wayar ta ma gabakidaya. Wannan ya tayar da hankalin sa, a niyyar sa in ya koma gida zai dauki
motarsa ya tafi ya zaga dangi yayi
gaisuwar juma'a kamar adda ya kanyi in
ya samu dama. Amma sai ya fasa, yana
zuwa motar ya dauka kawai ya fita ba tare
da ya ji abinda Safina da ta sha kwalliyar
lace take gaya masa ba.
Hanyar gidan su Safiyya ya dosa, ko bai
shiga ciki ba maybe zai samu wani labari
daga gurin mai gadi duk da dai mai gadin
shima wani kallo yake yi masa kwana
biyun nan. Sai da ya kusa zuwa sannan kiran waya ya
shigo masa daga gurin Mama "kana ina?
Kazo gida yanzu akwai magana mai
muhimmanci" sai yaji a muryarta kamar
farin ciki take yi, a yanayin order din da ta
bashi kuma kamar laifi ne yayi. Ya rasa
menene, amma in dai Mama tayi kira to
babu sauran jira. Sawun giwa ya take na
rakumi. Kan motar ya juya ya chanja titi
zuwa wanda zai kai shi gidan su.
Bayan ya shiga sai ya tsaya a harabar
gidan yana kallon motocin da suke wajen,
kusan duk iyayen sa maza suna nan har da motar uncle dinsa yayan mama dake Kano. Ya fito sai mai gadin su ya karasa da sauri yana watse baki hannun sa rike da goro da alawa yace "ranka ya dade
munji abin alkhairi, Allah ya sanya alkhairi
ya sa abokan arzikin juna ne ku" gabansa
ya fadi, ya kalli fuskar mal gadin ya kuma
kalli goron hannun sa sannan yace " meen" sal ya shige cikin gida da sauri.
Tun daga waje yake jiwo dariyar iyayen
nasa, daga dukkan alama suna cikin
nishadi, yana shiga yaji Mama tace "au
Amir yaje? Dama yana gari? Yaushe rabon
da inga bawan Allahn nan" Abba yace
"nima ban san yana gari ba shi yasa ko
neman sa banyi ba, sai kawai ganin shi
nayi sun zo tare da Sultan. Zan kawo shi
gidan nan kuwa insha Allah kafin ya koma
Kaduna" Habib yace "ai Sultan ne ya biya
sadakj" Mama tace "haba? Ya riga Faruk
kenan" Faruk yayi dariya "ya fini baki ai.
Kin san yayan nawa ba'a kure shi a
magana, Yace lallai wannan aure shine zai
biya sadakin sa, dole na hakura na bar
masa, Amma ina nan zan bawa ango da
amarya gift instead of sadakin da ban
samu bayar wa ba".
A hankali Muhammad yace "sadakin wa?"
Duk suka juyo suna kalion sa, Habib ya
mika masa hannu yayin da Mama ta hade rai "baka iya sallama ba?" Uncle Hamza wan Mama yace "in yayi sallamar ma ai ba za kuji ba kuna ta hira, yau dai daya al a daga wa ango kafa kar ayi masa fada" ya
karasa maganar yana dariya amma
Muhammad kallon sa kawai yake yi. Ya
san za"a daura masa aure amma bai san
cewa za'a daura ba da sanin sa ba.
Ganin duk shi suke kallo dai ya karasa ciki
ya zauna a kasa, a tsakiyar su. Uncle
Habib ne yayi magana, "Kamar yadda
muka shawarta a tsakanin mu, bisa
la'akari da dalilai masu yawa sannan kuma
da amincewar ka, an daura maka aure
Muhammad, da Safiyya Adam Muhammad".
Wani murmushi ne ya taso tun daga
zuciyar Muhammad har zuwa kan
fuskarsa. Wani irin farin ciki yake ji yana
lissafin ina ma shi yaro ne ya tashi yayi ta
zagaye gidan a guje yana tsalle? Instead
sai ya rufe fuskarsa da hannayensa ganin
yadda iyayen nasa already suka fara
tsokanar sa, "Kaga marar kunya ko? Satin
nan gabakidaya a kumbure yayi shi kamar
zai fashe amma ji yadda yake murmushi
ko kunyar mu baya ji" Abba ya fada da
dariya a muryarsa, Daga jin muryasa ka
San farin cikin dan na sa ya saka masa
farin ciki shima, Faruk yace "ai kuwa dai tushi ya kare, ciwo ya kare, hada akwati a gudu daga gida a je a dauke yar mutane ya kare" ya fada yana dan jan kunnen Gidado kadan cikin tsokana. Gidado ya
sake jin sabuwar kunya ta rufe shi. Uncle
Habib yace "nauyi kuma ya karu ba. Ni
tausayin ka nake ji Gidado. Hada mata
biyu musamman masu kusanci da juna
irin wanna sannan kuma wadanda kake
musu mabanbantan soyayya sosai akwai
wahala. Akwai aiki a gaban ka sosai".
Daga nan sai suka koma yi masa nasiha
akan sauke nauyin iyali da kuma kwatanta
adalci. Suka kara nuna masa irin girman
da ya same shi da kuma jaddada masa
cewa suna tare da shi a duk kan
al'amurran sa, duk wata shawara ko wani
taimako zasu bashi in dai suna da hali. Sai
kuma suka gaya masa cewa idan an jima
bayan sallar magrib ya shirya ya kuma
nemi abokan sa su raka shi ya gaishe da
iyayen Safiyya, daga nan kuma su gano
amaryar.
Daga nan ya tashi ya shiga dakin sa. Yana
rufe kofa ya zarce straight yayi sujjada
dan nuna godiyar saga Ubangiji, har sai
da hawaye ya kawo cikin idon sa. Ya na
dagowa ya cigaba da neman Safiyya a
waya, amma still wayarta a kashe. Ya tura
mata message ta Whatsapp duk kuwa da yasan ba zata gani yanzu ba.
"I am yours, and you are mine. Forever"
Daga nan sai ya fada akan gado yana yar
dariyar murna, babu abinda yake son gani
a lokacin sai fuskarta, ya zata ji? Ya zata
yi? Sai kuma ya dauko wayar sa ya kira Ya
Amen, yana dauka yace "kai an daura fa"
Al'ameen yayi dariya "amma yaron nan ka
cika marar kunya wallah, ni ba yayanka
bane ba kake ce min wai an daura"
Gidado yayi dariya cikin nishadi "watanni
ne fa kawai, ko goma basu kai ba"
Al'ameen yace "ko kwana goma ne dai na
girme ka kuma dole ka bani girma na"
Gidado yace "a da kenan, yanzu nine
yayan ka in gaya ma" Al'ameen yace "la
ila. Da gaske yaron nan ka raina ni fa.
Kana gaya min kana da mata biyu ko?
Dole Ayaan yaji maganar nan kuwa" suka
cigaba da hirarrakin su cikin nishadi,
Al'ameen ya gaya masa cewa dama
Mammy ta gaya masa maganar auren
Gidadon amma Abba ya hana a gaya
masa yana son ya gani if he will still do
the biyayya without knowing wadda za'a
aura masa din. Gidado yayi murmushi
kawai suka yi sallama bayan ya sanar
masa maganar zuwa gidan su Safiyya in
an jima,
Sai kuma ya fara lissafin wadanda zai kira
a abokan sa, daga baya kawai sai ya fasa
yace Al'ameen da sauran kannensu na
family sun ishe shi sai abokinsa Usman
wanda already ya san Safiyya. A haka ya
hada team din sa, Al'ameen, abdulshakur
dan aunty Amina, Baffa second child din
Uncle Habib, Haidar, sai kuma Usman.
Al'ameen ne duk ya gaya musu, ai kuwa
nan da nan suka zo gidan suna ta
hayaniya da tsokanar Gidado wai ya girmi
har iyayensa yanzu, ya zama mai mata
biyu. Matan ma sai gasu suna ta zuwa
Allah ya sanya alkhairi, gida ya cika kamar
ana taron biki, Mama kuwa taji dadin
zuwan nasu dan ta samu sun cinye
abincin da ta girka wa yan daurin aure dan
basu ci ba haka suka bar mata kayanta
suka ce sun ci abinci a can. Nan da nan
aka cinye abincin tas har sai da aka dora
wani. Kowa ya kalli Gidado ssi ya tsokane
shi saboda yadda yake washe hakora
kamar gonar auduga, kana kallon sa
kasan cewa yana cikin farin ciki mai tarin
yawa.
Sai da suka yi sallar magrib sannan suka
fara shirin tafiya gidan su Safiyya, ya
shiga toilet yayi wanka, yana fitowa ya ga
Kaya akan gadon sa a ajiye, ya san Mama Ce ta ajiye masa, yaji wani sonta yana karuwa a ransa, ya dauki kayan yana dubava, yadi ne fari kal mai laushi a
hannu da kyalli a ido, anyi masa dinki itin
na zamani da zare off white mai kyalli
wanda ya dace da hula da kuma takalmin
da ya gani a gefe duk size dinsa, sai
karshi suke yi wanda ya san mix ne na
turaruka kala kala, Sai kuma dan karamin
box dauke da agogon rolex sabo fil,
"Mamana" ya fada a hankali yana jin dadi
a ransa.
Ya saka kayan ya shirya tsaf sannan ya
tsaya yana kalion kansa a madubi, ya tuno
maganar Safiyya "You will wear white, You
will look so good in white" yayi murmushi
sannan ya ciro agogon daga cilkin kwalin
sa ya saka, Ya ji an danyi gyaran murya
daga bayan sa, ya juya yaga mama a
tsaye ta jingina da jikin bango, ya danyi
kokarin rage murmushin fuskar sa amma
sai ya kasa instead sai kawai yayi dariya
tare da karasa wa gurin ta da sauri ya
rungume ta har da dan daga ta ya raba ta
da kasa, ta dan dake shi a katada tana
dariya ita ma "ajiye ni kai. Marar kunya*,
¡ajiye ta ta ja dogon hancin sa "kayi kyau sosai Muhammad Gidado" yay kissing
goshinta tare da kama hannun ta ya rike a cikin nasa “thank you Mama. I mean thank you for everything” ta gyada kai "Allah ya baka ikon sauke nauyin da ya
dora maka, Allah yayi muku albarka
gabakidaya", Yace "Ameen" sannan ya
wuce ta ya fita.
Yana fita matan da suke gurin suka fara
rangada guda, shi kuma sai washe baki
yake yi. Aka zo akayi ta daukan pictures
da shi sai da kyar Abdulshakur ya jashi
suka fita. A hanya ma haka suka yi ta raha
har suka je gidan, a lokacin ya kara
tabbatar wa da cewa bayan Ya Amen da
babu wanda ya san alakar da take
tsakanin Safiyya da Safina, tunda basu je
gidan Daddy ba a lokacin auren Safina,
dan haka as far as danginsa are concern
Safina yar Katsina ce kamar yadda ta
tabbatar musu da kanta. A gidan suka samu tarya daga wani mutum mai cikar kamala da kwarjini
wanda daga baya Muhammad ya fahimci
shine Uncle Sufyan din da Safiyya ta gaya
masa, shi ya shigar da su har wajen
Daddy suka gaishe shi, suka same shi
tare da uncle Ahmad, shi dai Muhammad
yana ta sunkuyar da kai baya son hada
ido da Daddy, Daga nan kuma aka dawo dasu parlor suka gaisa da wadda ya gane a matsayin Aunty Hajjo. Sai tace su jira a kawo musu amarya, tun daga nan ya
mayar da hankalinsa kan hanyar da yaga
ta bi. Yana jin sauran samarin wajen suna
ta hirarrakin su amma sam hankalin sa
baya kan su, ita kadai yake so ya gani. Sai
yaga kamar sun dade da yawa, me suke yi
ne wai?
A sanda ya dora idonsa a kanta kuwa ji
yayi babu wani sauran birbishi na damuwa
da ta rage masa a duniya, with Safiyya as
his wife, yana maraba da dukkan
challenges na rayuwa.
Ya lura da kallon da tayi wa Haidar,
sannan a take ta fara neman fuskarsa a
cikin mutanen gurin. Ya fahimci cewa
ganin Haidar da tayi ya saka ta gane da
shi a ka daura. Suna hado ido ya mike
tsaye tare da bude mata hannayensa, not
minding Aunty Hajjo ballantana sauran
samarin da suke gurin, ba ta watsa masa
kasa a ido ba kuwa ta zo ta shige mazaunin ta, cikin kirjinsa and they had their first halal hug, or maybe he should call it their first hug dan wancan na ranar
nan was done a cikin tashin hankali dan
haka babu wani feelings a cikin sa.
Yana jin hayaniyar mutane amma duk
baya jin abinda suke cewa, bugun zuciyar
Safiyya kadai yake saurara, tare da dumin
jikinta da kuma kamshin da yake tashi
daga gare ta. "It is okay. You are okay.
Muhammad Gidado is here" ya fada mata
a cikin kunnen ta. Ta gado da niyyar
kallon fuskarsa yayin da shi kuma yake
kallon kasa a kokarin sa na ganin tata
fuskar wannan ya saka fuskokin su duka
zo dab da juna. Tayi saurin mayar da tata
kasa shi ma ya dauke tasa gefe because a
yadda yake jin zuciyar sa a kanta anything
can happen.
Ya lura tunda tazo gurin ake musu hotuna,
Aunty Hajjo ta fadi sakon da iyayensu
suka bayar sannan ta juya ta tafi ta bar su,
daga nan Safiyya ta fara kokarin janye
jikin ta daga nasa, maybe sai yanzu ta
fara jin kunyar mutanen gurin, ya dan
sake ta kadan sannan ya jata suka zauna,
tana ta kara lullube jikin ta da katon
mayafin da ya kai mata har kasa. Suna
zama ya kara riko hannunta yana kokarin
leka fuskarta, ta dan harare shi da
kumburarrun idanunta, ya fahimci ta
dauka ba dashi aka daura ba, Allah kadai
ya san yawan kukan da tayi , sai yaji ya
hakan yayi masa dadi sosai, it feels so
good to be loved by the person you love
A hankali yayi mata introducing wadanda
suka zo da su, kowa yana tsokanar ta
"yau dai munga Safiyya"
"daga yau dai mun huta da labarin
Safiyya. Daga ina kake Safiyya, ina zaka je
Safiyya, me kake yi Safiyya"
"Har mafarkin Safiyya fa yake yi, cikin
dare zaku ji yana kiran sunan ta"
Muhammad yace "ban da sharri kuma.
Wannan dai kazafi ne"
Abdulshakur yace "a kira Ayaan a
tambaye shi ranar nan a UK idan ba sunan
ta kake kira mana cikin dare ba". Duk suka
yi dariya banda Safiyya da taji kamar zata
nutse a gurin., Haka suka yi ta raha suna
duke dauken pictures yayin da Esther ta
shiga hidimar cika musu gabansu da
snacks da drinks, sam ta kasa rufe bakin
ta tun da taji abinda ya faru saboda
murna. Safiyyah ta lura cewa Abdulshakur
yafi kowa surutu da tsokana, yayin da
Al'ameen yake zaune kawai yana kalion su
yana murmushi, sal jefi jefi zaka ji yayi
magana a hankali, Sai da suka fara shiri
taliya ne Al'ameen din yazo gurin su yace mata "amarya congratulations, Yanzu dai
za'a bar min zucivar dan uwa ta huta" a hankali tace ba tare da ta dago kal ta kalle shi ba "thank you Ya Amen. A gaida Humaira da Mammy" sai yayi murmushi aransa yana jin cewa tabbas dan uwan
nasa ya samu chanji.
Shi ya hada kan kannen nasa ya kora su
waje, ya kuma ce ya bawa Muhammad
minti biyu idan bai fito da zasu tafi su
barshi sai dai amaryar tasa ta kai shi gida. Suna fita Muhammad ya kara karfin rikon da yayi wa hannun ta. Sannan yayi kokarin daho fuskarta da daya hannun. "Amaryar Muhammad" ta kara sunne kanta gefe
tana jin kunyarsa "wai kunya ta kike ji? Ni
fa" ta juya fuskarta dayan gefen, da gaske
kunyar ta sa take ji musamman yanzu da
aka bar su su biyu, Ya danyi dariya "lallai
da rabon yau zan kwana a gidan Daddy
kenan. Ta yaya zan tafi ba tare da na kalli
cikin idon ki ba?" Ya fada yana daga
hannun ta da yake cikin nasa ya kai bacin
sa tare da hura mata iska a fatar hannun.
Tayi kokarin janye hannun amma sai ya
kara rikon su tare da fara kissing knuckles
din ta one after the other. Ta juyo da sauri
ta dora manyan idonta akan sa tace cikin
rada "CCTV" yayi saurin sakin hannun
yana rarraba ido, sai ta mike da sauri ta
bar inda yake tare da cewa "goodnight" yana ta rarraba ido amma da murmushi a
fuskarsa yayi mata alamar tazo su je waje
da hannun sa. Ta makale kafada, ya hade
hannayen sa alamar roko, ta sake makale
wuya. Ya kankantar da idonsa a kanta irin
kallon da yasan yana saka ta jin kunya sai
ta ja mayafin ta ta kara rufe fuskarta.
A lokacin aka bude kofa aka fito daga part
din Daddy. Duk suka juya suna kallon
wadda ta fito din, Mommy ce, fuskar ta
jage jage da hawaye, ta kalli Safiyya da
tayi saurin sunkuyar da kanta kasa sannan
ta kalli Muhammad shima ya janye idonsa
daga nata suna adawa, babu wanda ya
iya gaisheta a cikin su ballantana yace
mata wani abu, ita ma bata ce musu
komai ba sai ta wuce ta hau sama. Suka yi
shiru gabakidaya babu wanda ya sake
magana. Haidar ya dawo yace "Wallahi Ya
Amen yace zamu tafi mu barka" Gidado
ya gyada kai, kafin yace komai Safiyya ta
juya ta bi hanyar da ya ga ta fito daga ciki.
Haka ya tashi ya fita, bai ji dadin ganin
hawaye a idon Mommy ba amma shi kam
yau babu abinda zai saka wa farin cikin sa
shamaki,
Suka shiga motocin da suka zo a cikin su
sannan suka fita cikin nishadi kamar yadda suka shigo.
Daddy...
One week ago....
Ya dago kaga kai yana kalion bakon nasa
wanda shi da kansa ya ce a shigo da shi
har cikin dakin sa. Suna hada ido sai yaga
yanayin bakon nasa ya chanja gabaki
daya, lokaci daya yayi wani irin sanyi
wanda da bai shigo da shi ba. Maybe
kuma hakan yana da dangantaka ne da
yanayin rashin lafiyar da yake ciki da
kuma injinan da suke zagaye da shi.
Yayi masa maraba tare da nuna masa
kujera "bismillah". Abba ya zauna yana
cigaba da kare wa dakin kallo wanda ya fi
masa kama da dakin asibiti. Daddy ya
danyi murmushi yace "forgive all the
medical tarkace, Safiyya ce duk ta cika
min daki da shirgi, ni kuwa na san duk
yawan machines din da zata siya lokaci
yana cika zan tafi"., "Me yake damunka?"
Abba ya tambaya da Hausar sa mai
accent din fulani irin na Muhammad
Gidado, Daddy yace "ALS" sai Abba ya
cigaba da kalion sa da rashin fahimta,
Daddy ace "neuromuscular disease ne
da yake paralysing muscle, thereby
restricting movements. Ba zan cika ka da
medical jargons ba amma already na wuce time din da doctors suka yi tunanin ba zan kai ba" Abba ya girgiza kansa "ba su suke bada rai ba. Ba kuma su zasu
dauka ba" Daddy ya gyada kai "you are
right, I am a living testimony. But I am
sure ba wai kazo dan jin labarin rashin
lafiya ta ba ko? What brings you to me?"
Abba ya danyi shiru yana tattaro tunanin
sa waje daya, ganin Daddy ya taba
zuciyar sa sosai. Muhammad bai taba
gaya masa cewa bashi da lafiya ba. Ya
danyi gyaran murya sannan yace
"hmmm.... I don't know ko kasan ni
waye" Daddy yace "baban Muhammad
ne, mijin Safina. Kuna kama sosaj" Abba
ya dan yi murmushi tare da shafa gefen
fuskarsa sai kuma yace "haka ne. Amma
ba maganar Safina bace ta kawo ni. Nazo
ne farko ina so inji ko kana da masaniya
akan alakar da take tsakanin Muhammad
da Safiyya?".
Daddy ya danyi shiru kamar mai tunani
sannan yace "na jima da sanin cewa
akwai wani yaro da Safiyya take so, in
fact, tayi ta kokarin ganin cewa ta kawo
min shi ya shigar da maganar auren ta ni
kuma na hana ta saboda burin da na dora
akan ganin tayi karatu mai zurfi, saboda
wasu dalilal nawa. Daga baya kaddara ta gifta wadda tayi sanadiyyar rabuwar su. Amma ban san cewa shine Muhammad din da kannen mahaifin Safina suka daura
mata aure da shi ba sai kwanan nan. So your answer is yes, na sani".
Abba ya danyi shiru yana digesting
wanna amsar sannan kuma sai ya sake
yin wata tambayar "and what do you think
about their relationship. Menene
matsayar ka akai" Daddy yace "nace wa
Safiyya no. Na gaya mata cewa ba zan
aura mata shi ba duk kuwa da a fahimci
soyayyar da take yi masa, na hana ta
auren sa saboda kasancewar sa mijin
Safina. I don't know ko kasan relationship
din da yake tsakani na da mahaifiyar
Safina?" Abba ya gyada kai "na sani.
Babu wanda ya gaya mana hakan a
danginta, amma mun binciko hakan sanda
muna bincike akan auren ta".
Daddy yace "good. I raised her like my
daughter. Ba zan ce na so ta kamar yadda
nake son Safiyya ba but I did my best.
Sun tashi kamar sisters. Wannan ne
abinda ya kara bata min rai sanda na hana
Saliyya alaka da Muhammad amma taki
jin magana ta ta cigaba da ganin sa
behind my back. Na tambaye ta kuma
dalili ta kiyi min cikakken bayani illa cewa tana son sa. I got scared, I am a sick father unable to guide and protect his only daughter, Wannan ya saka na saka
cctv a dukkan bangarorin da suke gidan
nan except for bedrooms. Na saka ne dan
ita. Dan in san duk wani move dinta in
kuma yi kokarin discharging fatherly
duties dina. She told me cewa zata rabu
da Muhammad kamar yadda na bukata
tunda ta ga raina baya so. She invited him
in, suka zauna, and they had this conversation" ya fada yana mika wa Abba wayar da take hannun sa. Ya kara da cewa "ka kalla tun daga farko har karshe
sannan sai kai ka gaya min abinda kake
tunani a game da alakar ta su"
Abba ya taso ya karba, fuskar Muhammad
din sa ya gani da ta yarinyar da ya jima da
sanin sunan ta amma sai yau ya fara ganin
tata fuskar. Daddy ya kara da cewa "duk
abinda zaka ji ta fada, gaskiya ne, abinda
ya faru da ita kenan".
Abba yayi shiru yana sauraron
maganganun Muhammad dana Safiyya da
suke fitowa tas ta jikin speaker wayar.
Sanda ya gama gabakidaya a razane
yake. Hankalin sa ya kai makura wajen
tashi. "Ina yake?" Ya tambaya "shi
Mukhtar din ina yake? Da gaske kun
barshi? Kun kyale shi?" Daddy yace "da gaske mun barshi da Allah. Mun kyale shi shida Allah, Muna nan muna jira. A haka ma da muka rufe maganar Safiyya is
about to lose the person she loves very
much, me kake tunanin zai faru da ita idan
muka fito da maganar? Bata aikata laifin
komai ba but most people will run away
from hada zuriyar su da ita....." Abba yace
"then most people da kake magana a kai
a jahilai. Wannan abu ne da jahilai zasu
aikata, Kuma alhamdulillah Alhaji Adam,
dani da iyali na bama cikin jahilai, kamar
yadda na tabbatar kaji a cikin maganganun Muhammad".
Daddy ya dago kai yana kallon sa yace
"me kake nufi?...." Abba yace "ina nufin
ina nemawa dana Muhammad auren
Safiyya a gurin ka. In dai har kana ganin
zaka iya bashi ita duk kuwa da alakar da
take tsakanin ku da matar sa ta yanzu".
Daddy yayi shiru yana kallon sa sannan ya
maimaita masa maganar da ya tabbatar
yaji a cikin hirar su Safiyya "Safiyya ta na
da da, wanda ta haifa ba tare da aure ba.
Ka tabbatar a haka kake so ka aura wa
danka ita?" Abba ya gyara zama yace "na
tabbatar, dalili na na farko shine ina da ya,
kwanan nan na aurar da ita, na tabbatar
kuma cewa har yau har gobe bata wuce kaddarar da ta fada kan Safiyya ta fada mata ba. Babu wani a cikin mu da ya isa ya wuce jarabawar sa. Dalili na biyu shine
ban taba ganin soyayya irin wannan da na
gani a tsakanin wadannan yaran ba, zan
iya cewa daga ni har kai munyi kuskuren
barin su suyi zurfi irin wannan, Allah ne ya
kare mana su but they are too close. Yarinyar nan ita ce farin cikin Muhammad, a matsayi na kuma na mahaifin sa zan yi iyakacin kokarin gain na samar masa farin ciki in all the halal ways. Tambaya ta
anan ita ce, zaka iya aura wa yarka mijin
step sister din ta?" Daddy yayi shiru yana dan juyi akan wheelchair dinsa, fuskarsa duke da
murmushi kamar mai tunani, sai kuma
yace "ni uba ne. And it is very okay for
parents to be selfish sometimes when it
comes to their kids. Parents have to be
selfish sometimes" Abba yace shima yana
murmushi "not sometimes, parents are
selfish all the times when it comes to their
kids. Haka din kuma dai da ne. As long as
their selfishness bai zamo shiga iyakar
ubangiji ko danne hakkin wani ba. Then it
is okay 1 am ready to be selfish if you are"
Daddy ya mika masa hannu suka yi musa biha, fuskokin su duk da murmushi, wani bond mai karfi yana creating kansa a tsakanin su.
Abba yace "abu daya ne ya saka ba xan
daura wa Muhammad aure da Safiyya a
yanzu ba. Shine mahaifiyata da yan uwa
na. Bama taba yanke wani babban
hukunci ba tare da mun sanar wa da junan
mu ba. Zan je in same su muyi magana,
zan gaya musu iyakacin abinda nake
ganin ya kamata su sani. Zamu tsayar da
rana cikin satin nan zamu dawo a daura
musu aure"
Bayan sun rabi Daddy ya kira Sufyan ya
sanar masa, sannan ya kira Ahmad shima
ya sanar masa da abinda ake ciki, dukkan
su sunyi murna kuma a take Sufyan ya
shirya suka taho Nigeria shida iyalinsa
dan yana son ayi komai da su, musamman
bayan yayi magana da Hajjo kuma ta
tabbatar masa da cewa ta san mahaifiyar
Muhammad din kuma sunyi maganar
Safiyya da ita few days ago. Dasu akayi
shirin komai, Daddy ya roke su akan kar
su fada wa kowa har sai maganar ta
tabbata, baya son attention din mutane
akan maganar, bayan son attention din
mutane akan Safiyya. Bai gayawa Mommy
ba saboda bash da tabbas din yadda
zata vi reacting to maganar. Ya san kuma in dal ta sani to sai Safina ta sani, duk da yasan hakan ba zai hana faruwar auren ba dan babu mai saka wa ko hana wa a cikin su amma ya san hakan zai iya janyo
unwanted attention din da baya so.
Ko a ransa bai ji cewa yayi wa Safina ba
dai dai ba musamman bayan zargin da
yake yi na cewa ita tayi wa Safiyya
kwacen saurayi, plus mugayen karerayin
da ta fada akan Safiyya dan ta bata ta a
grin Muhammad.
Amma kuma a ransa yasan cewa baiyi wa
Sa'adatu dai dai ba na kin fada mata da
yayi. Sai dai ita mutum ce da ba'a gane
kanta, shi kuma a yanzu da yake gab da
cimma burin sa na gyara kurakuren da
yayi akan Safiyya, baya jin zai iya daukan
risk.
Present day…..
Bayan angwayen sun fita daga gabansa
sun koma babban falon gidan, sai Daddy
ya dauki waya ya kira number din Mommy
kamar yadda ya shirya zai yi. Ya gaya
mata ta same shi a dakin sa amma ta biyo
ta barandar sama dan akwai baki a falon
kasa, sai da ta zo ta zauna sannan yace
mata yana zuwa. So yake kawai ya ga
tuskar Safiyya a lokacin da taga Muhammad a matsayin angon ta. Sai da ya gani din kuwa, and murmushin da ya gani a kan fuskar ta was worth all the
risks he took to put it there. She said
"thank you" to him, he gave her a thumbs
up sannan ya koma cikin dakin sa inda
Mommy take zaune tana jiran sa.
Ya shiga ya rufe kofa sannan ya zauna
suna kallon juna na was seconds sannan
tace "kace inzo zamuyi magana. Kace
kuma akwai baki, bayan dazu babu irin
tambayar da banyi maka ba akan bakin da
za'a yi kaki gaya min su waye. Su waye
bakin? Wacce magana zamuyi?" Ya
cigaba da zama a inda yake, a ransa yayi
hakan ne dan kar tace zata fita wajen
bakin ta basu kunya a cikin surukai.
Ya sauke ajiyar zuciya yace "dazu da
yamma. Na daura auren Safiyya da
Muhammad".
Farko zama tayi kawai tana kallon sa
kamar bata fahimci abinda yace ba, sai
kuma da tsananin mamaki tace "what?
Adam me kake cewa ne haka? Wanne
Muhammad din? Mijin Safina?" Ya gyada
kansa a hankali still idon sa a kanta yana
kokarin studying dinta. Shi da whatever zata yi baya son ta fita falon nan,
Amma sai yaga ta cigaba da yin shiru tana
kallon sa, sai kuma a hankali hawaye suka
fara bin ion ta. Ya fara driving kujerar sa
zuwa gare ta sai ta daga masa hannu.
"Don't! Kar kazo nan. Kar ka gaya min
komai. Bana son jin komai. Ka bani hanya
in wuce. Kwana daya ba zan kara a gidan
ka ba. Yau nayi nadamar shekarun da na
bata tate da kai. Dama na riga na san cewa kai mutum ne mai son kanka amma ban tana zaton ka
kai haka ba sai yau" sai kuma ta koma ta
zauna tare da rushewa da kuka mai kona
zuciya.
Bai ce komai din ba ya cigaba da zama a
bakin kofa. Sai da tayi mai isarta sannan
ta dago tana kallon sa ta sake maimaita
abinda ya gaya mata, maybe dan ta kara
tabbatar wa ba wai ji ne bata yi daidai ba.
"Mijin Safina fa kace ka daura wa aure da
Safiyya. Mijin Safina fa. Kana cikin
hayyacin ka kuwa?" A hankali yace "yana
sonta, kuma tana son shi. Sannan ba
haramun bane ba" ta girgiza kai cikin
dacin zuciya "ita kuma duk abinda take so
Sal ta samu kenan, Ko da kuwa abin ba
nata bane ba na wata ne sal ka kwace ka bata kenan. Wannan wanne irin son kai ne?" Sai ya maimaita mata maganar da suka yi da Abba. "Parents are at times
selfish when it comes to their kids. And
thst is okay. In dai har ba'a shiga hakkin
wani ba".
Tace "hakki? Shiga hakki fa kake magana
akai. You just destroyed Safina's marriage
just so that Safiyya can get married to
mijin Safina da ta gani tana so. Kuma kake
min maganar shiga hakki?" Yay driving
kujerar sa zuwa inda take yace cikin
sassanyar murya "kin taba tambayar
Safina yadda suka had da Muhammad?"
Ta goge hawayen fuskarta "menene hadin
wannan da auren da ka hada?" Yace "it
has everything to do with it. Kin taba
tambayar ta?" Yadda taga ya sassauto da
muryar sa ya saka ta baci amsa duk kuwa
da wani irin haushin sa da take ji daga shi
har yar lelen yar tasa. "Na tambaye ta
tunda ni na damu da ita, kai da baka
dauke ta yar ka ba ai ko maganar ba ka yi
mata ba. Da tace min friend request ya
tura mata a social media sai suka zama
abokai daga baya suka fara soyayya, sai
da incident din ranar dinner dinta ya faru
iyayensa suka zo nan sai na fahimci akwai
wata a kasa, dana sake tambayar ta sai ta
gaya min cewa a social media taga hoton sa ta fara son sa, sai tayi cigiyar ko akwai
wanda ya san shi ya hada su, shine
kanwar sa ta hada su" Daddy yayi ajiyar
zuciya yace "bani da tabbas din gaskiyar
haka ko rashin gaskiyar hakan. Abinda
nake da tabbas a kan sa shine
Muhammad shine yaron da Safiyya ta
saka kika yi min maganar sa shekaru biyu
da suka wuce, shine yaron da suke tare a
garin nan sanda tana karatu, shine yaron
da muka dauka shi yayi mata ciki ita kuma
ta ki gaya mana waye shi saboda ta san
ba shi bane ba. Wannan dalilin ne ya saka
ta yanke jiki ta fadi ranar da aka dura wa
Muhammad aure da Safina. Ina kyautata
zaton hoton auren ta gani a waya. He was
Safiyya's before he became Safina's. Dan
baka ba abin Safina na kwace na bawa
Safiyya ba. Yes, I am selfish, amma ban
shiga hakkin Safina ba".
Tayi shiru tana tunani, and she
remembered wani dare a Berlin da Safiyya
ta farka tana ihun kiran sunan
Muhammad. Shine Muhammad din?
Ta dago kai tana kallon Adam, not
knowing what to say or feel, Sai tace "tun
yaushe kasan hakan? And you never think of telling me? Saboda me? Saboda kana ganin bam isa ba dan bani na haifi Saliyya ba? Saboda kana ganin ban isa kayi shawara dani a duk al'amurra da suka
shafi Safiyya ba? Ba ka taba yarda da ni
akan yarinyar nan ba and it hurts me more
than anything. Ba ka taba gaya min komai
da ya shafe ta, ita ma kuma ba ta gaya
min. Me yasa a matsayi na na uwar ta tun
da taga Muhammad din ba zata same ni
ta gaya min ba?"
Yayi shiru yana kallon ta, and she truly
looked hurt, da alama abin yayi mata ciwo
sosai. Jin bai ce komai ba ta cigaba da
amayar da abinda yake ranta "misali
maganar kayan Safiya, wai ace ka ajiye
kaya a gidan nan kusan shekaru ashirin
amma minda nake matar gidan ban san
suna cikin gidan ba. Sannan yaron nan da
ta haifa, da ga kai har ita babu wanda yayi
min maganar yaron nan sai a gidan biki na
ganshi" Sai yace "Safiyya have her own
reasons da yasa ba ta gaya miki magana,
Ni ma kuma ina da nawa daban. This may
hurt you amma na tabbatar kin san
gaskiya ne. Kina da son abin duniya
Sa'adatu. Kina da son kudi sosai ta yadda
har ba kya iya boyewa. Ni da ke duk
munsan dan su kika aure ni. Safiya have told me a lot about son kudin ku jokingly dan haka tun sanda na aure ki na san halin ki" tayi shiru ranta yana kara
baci akan abinda yace, amma kuma a
kasan ran nata ta sam gaskiya ce. A bitter
truth.
Ya cigaba "it is hard to know where a
person stands with people like you. Ba'a
gane soyayyar ku ta gaskiya ko akasin
hakan. Yanzu misali tun ranar da na gaya
miki cewa almost all of my wealth belongs
to Safiyya sai kika tattara ni kika watsar,
duk wata kulawa da da sanda nake
hidimar fita dake kasashen duniya for
vacations kike yi min yanzu kin daina. Ita
dukiya tana da santsi ko da a gurin wanda
bai damu da ita bane ba, yo ina ga wanda
yake son ta ido rufe? Dan me ba zan ke
boye miki abubuwa ba?".
Ta sunkuyar da kanta kasa hawaye suna
cigaba da zuba a idonta tace "na so
Safiya, in kuma son Safiyya" yace
"sannan kuma kina son dukiyar su. And it
is okay kamar yadda na fada wa Safiyya
sanda ina kokarin convincing dinta ta auri
Mustapha, Life is mostly trade by batter.
Maganar Safiyya kuma dalilin da yasa ba
ta gaya miki gaskiyar abubuwan da suka shafe ta shine saboda mentally ta riga ta saka a ranta cewa ko ta gaya miki ba zaki yarda ba" ta dago kai tace "saboda me? Ita tace maka haka?" Ya girgiza kai,
"Kwanan nan na fahimci hakan. Saboda
tun suna yara in ta gaya miki magana ba
kya dauka kin fi yarda da abinda Safina
tace miki a kanta" ta bude ido "kuma kace
ba ita ta gaya maka ba" yace "ba ita ta
gaya min ba. Maganar naji suna vi ita da
Mustapha, bai musa ba kuma, kamar
yadda bai musa cewa yana shiga dakinta
for years yana neman ta ba".
Wata zabura Mommy tayi ta tashi saura
kadan ta fadi sai ta fada kan kujera, ya
zagayo tare da mika mata hannu duk da
ba iya taimaka matan zai yi ba. Nan take
muryar ta ta cigaba da rawa, hawayen
idon ta ya dawo,. Yace "wannan pain din
shi na gudar miki shi yasa na kasa fada
miki. Yanxu ma ina gaya miki ne kawai dan
ki fahimci maganar sosai kar ki fahimce ta
a bai bai ki yi abinda zai raba min kan
iyali" tace "duk wanda ya gaya maka
wannan maganar karya yake yi. Ko
safiyyan ce ta gaya maka karya take yi
masa, so take kawai ka kore shi dan bata
son auren sa. Wallahi sharri take yi masa"
ya girgiza kai yana dan murmushi "kamar yadda na gaya miki, parents are all selfish when it comes to their kids. Already har kin goyi bayan sa, Kuma again kamar
yadda na gaya miki, babu wanda ya gaya
min, ni na gansu suna maganar, na kuma
ji duk abinda suke cewa" ya dauko
wayarsa "kina so ki gani?" Ta bishi da
kallo kawai ta kasa cewa komai sai yace
"na saka cctv a gidan nan ba tare da kowa
ya sani ba, saboda rashin lafiya tayi
limiting yadda zan saka ido tare da kula
da iyali na, Ta haka na gansu suna
maganar, basu san ina jin su kuma ina
ganin su ba, so it's pure truth. Ya jima
yana so ya lalata ta, innkika je dakin ta
kika duba zaki tarar da wukar da ta ajiye
saboda tayi masa barazana dan ya shigar
mata din, wanna shine dalilin kiyayyar ta
gare shi. Wannan shine dalilin kiyayyar ta
ga auren sa. Wannan kuma shine dalilin
da ya sa na kore shi",
Ya fada yana cigaba da mika mata wayar.
Bata karba ba sai ta kife fuskarta a jikin
kujera tana kukan takaicin halin yayan ta,
ya dora hannun sa a bayan ta cikin shigar
lallashi yace "kiyi hakuri, Babu iyayen da
suke perfect. Ni da ke duk munyi
mistakes gurin raising yayan mu. We
should have separate Mustapha from
Safiyya tun sa da suka balaga dan ba
muharraman juna bane ba. We should have listened more to their small complains and act on them, we should have investigate magana idan suka gaya
mana ba wai mu yarda da su blindly be.
Amma lokaci bai kure ba, we are still alive
and we can fix their lives, wannan shine
abinda nayi ga Safiyya. The biggest
mistake I made a rayuwar ta shine not
listening to her sanda ta ce ta samu
wanda take so zata aura. Da tana gidan
mijinta da maybe duk abinda ya faru da
ita bai faru ba". Ta dago kanta "yanzu to ni yaya zanyi, ta ina zan fara? Me zanyi akan Safina?" Yace
"that is where maganar investigate ta
shigo ciki. We will investigate, mu tace
karya daga cikin gaskiya a maganganun
da Safina ta fada yadda mu zamu samu
fahimtar maganar sosai. Sauran kuma ya
rage na mijin ta. Amma ni in kika tambaye
ni zan ce miki chances are very high that
Safina ta san Muhammad shine saurayin
Safiyya. A tunani na hoton da tayi talla
dashi a social media a wayar Safiyya ta
dauka"
Mommy ta fara girgiza kanta sai ya sake
yin murmushi yace "kamar yadda na gaya
miki, parents are naturally selfish when it comes to their kids"
Daga waje yaji karar bude gate sannan
yaji ana shiga motoci, ya san bakin ne
zasu tati, Sai ya sauke ajiyar zuciya ya
tuka kujerar sa zuwa wajen kararrawar
kiran nurse dinsa, it has been a long day,
yana bukatar yayi bacci kuma,
Ganin haka ya sa Mommy ta mike, still not
knowing what to think or do. Zuciyar ta
tana yi mata zafi, abubuwan sun
cunkushe mata a kanta, bata san menene
zata dauka menene ba zata dauka ba.
Bata tashi fahimtar zurfin bacin ranta ba
sai da ta fita falo tayi mugun gain Safiyya
da Muhammad, ba tare da tace musu
komai ba ta wuce su zuwa sama sannan a
tsaya a bakin window tana kallon motocin
da suka fita daga gidan.
Sai dai motocin ba su jima ta fita ba wata
taxi ta tsaya a kofar gidan sannan wata
mata ta fito daga ciki, ssi da ta shigo gate
sannan Mommy ta gane ta Safina, duk ta
fita daga hayyacin ta kamar mahaukaciya
sabon kamu. Da sauri Mommy ta fito daga
dakin ta sa sauko daga stairs din a dai dai
lokacin da Safina ta shigo falon, idanunta
jage jage da hawaye.
"Mommy zuciya ta zata fashe, Mommy
zan mutu, Wayyo Allah na., Wayyo
Muhammad. Wayyo Abba na",
Maman Maama✍🏻
[07/01, 10:46 pm] +234 906 816 1960: ❤️🩹Satiyya❤️🩹
Episode Sixty Two: Unloved
Not Edited…
"Mommy zuciya ta zata fashe, Mommy
zan mutu. Wayyo Allah na. Wayyo
Muhammad. Wayyo Abba na".
Kuka da hun Safina ya cika gidan
gabakidaya. Babu wanda bai ii ba har
Safiyya da Aunty Hajjo da suke dakin
safiyyan. Suka fito da sauri a lokacin da
Mommy ta fito ita ma ta sauka kasa da
sauri. Sai suka tsaya akan barandar suna
kallon yadda Safina ta zube a tsakiyar
falon tana wani irin kuka.
"Yaya za'a yi min haka a gidan nan. Ta
yaya za'a aurawa Safiyya mijina. Mommy
how can vou let them do this to me?
Wannan wanne irin son kai ne? Wannan
wanne irin rashin adalci ne? Ba zan iya
ganin ta da mijina ba, Mutuwa zanyi
Mommy".
Mommy ta karasa gurin da sauri kamar
zata kifa, ta saka hannu daya ta kamo ta
ta dago ta sannan ta sauke mata wani gigitaccen mari da dayan hannun, Kartin marin ya saka Satina ta sake kifewa a wajen tare da rushewa da wani sabon
kukan. Mommy ta sake kamo ta ta kara
sauke mata wani a dayan side din fuskar.
Nan da nan fuskarta ta kara ja saboda
kuka da kuma zafin marukan, Mommy ta
saka kafa ta dake ta, hakan yasa ita kuma
tayi baya saira kadan ta fadi Aunty Hajjo
da tayi saurin saukowa ta rike ta.
"Sa'adatu menene hakan? Zaki ji mata
ciwo ki jiwa kanki ciwo kema"
Mommy ta nuna Safina cikin dacin zuciya
"ba mutuwa taxe zata yi ba? Gwara in
kashe ta da hannu na akan ta mutu
saboda namijin da bai damu da ita ba.
Gwara in kashe ta da hannuna akan bakin
cikin da take kunsa min akan da baya son
ta. Namijin da ta lalata alakar ta da yar
uwarta saboda shi" ta fada tare da
kwacewa daga hannun Aunty Hajjo ta
koma ta damki kunnuwan Safina duk
biyun ta sske dago ta zaune, Safina tayi
karar azaba tana jin kamar zsta ski fitsari
a wando, Mommy tace "dan ubanki ki
gaya min gaskiya, kin san saurayin ta ne
kafin ki kai masa tallan kanki ko baki sani
ba? Shi yasa kika tafi da shi Katsina dan
ba kya son ya ga Daddy ya gane? Dan ubanki ba zak| gaya min gaskiya ba?"
Aunty Hajjo ta banbare hannun Mommy
daga kunnuwan Safina, ita kuma tayi sauri
ta rike kunnuwan tana jin kamar Mommy
ta cire masa su, ta ma daina kukan yanzu
dan abinda take ji a zuciyar ta yati karfin
kuka, the last person da taje tunanin zata
goya mata baya ta debi kasa ta watsa a
idanunta. Wani irin bakin ciki take ji da
take gain gwara mutuwa akan sa. Yanzu
ne ta kara tabbatar wa cewa kaf duniya
babu wanda yake son sa, me ya rage
mata to? Me zata zauna tayi a duniyar
kuma?
People have always love Safiyya more…...
Tun suna yara, hatta Mommyn ta ma da
ba ita ta haife ta ba gani take yi kamar tafi
son Safiyya a kanta. A makaranta ma anfi
son Safiyya duk kuwa da cewa tafi
Safiyyan hakuri da biyayya, Safiyya taurin
kai da tsaurin ido da rashin kunya da
shegen iyayi da manyance wanda Safina
take finding very annoying amma kuma
still an fi son Safiyya. Ko kawa tayi to
kuwa in dai har ta hada su da Safiyya sai
ta ga kawar ta koma ta zama kawar
Safiyya ita ta koma second choice.
Ballantana Daddy da baya boyewa. Daddy
bai taba hada Safiyya da kowa ko komai a
rayuwar sa ba. And that made her crave for a father's love duk kuwa da cewa yana
sauke musu dukkan hakkokin uba amma
tana kwadayin soyayyar da yake yiwa
Satiyya. Sail dai in Safiyya bata ambata ko
kuma ta nuna tana son abu ba to sai ya
samo mata shi sai dai in har abin mai
cutar wane. Wani lokacin Safina har
mamakin audacity din Safiyya take yi,
tana kuma jin haushin iyayen nasu akan
biye mata akan duk abinda ranta yake so,
tana ganin bata ta suke yi. A hankali ta
fara kallon Safiyya a matsayin marar
tarbiyya, ta kuma fara ganin kanta a
matsayin ita ce mai tarbiyya. And she
started wanting people to believe that.
Tun daga lokacin ta fara jingina duk wani
abu marar kyau zuwa da Safiyya, duk
wani abu mai kyau kuma zuwa gare ta.
Like, as the good girl that she is, she
deserves everything good. Mentally kuma
ta saka a ra ta cewa Safiyya will end up
bad, tunda dai tarbiyya bata ishe ta ba. Wannan ya sa duk wani laifi da akayi automatically zata jingina shi ga Safiyya. Ko menene gani take yi tabbas Safiyya
zata iya aikata shi tunda bata da tarbiyya
ba kuma ta tsoron kowa, to tsoron me
zata ji tunda ba hukuntata za'a yi ba? lya kaci Mommy tayi ta mata fada idan Safina
tace tayi wani abu, shima fadan daga
baya saboda rashin tarbiyya in Mommy
tana yi mata shi sai ta saka hannu ta
toshe kunnuwanta ma'ana ba ma zsta j
ba ballantana tayi aiki da shi, ta kuma rufe
idonta ma'ana ba ma zata gani ba
ballantana abin ya dame ta.
Wanna ba karamin bata ran Safina yake
yi ba, tana ganin Safiyya ta raina mata
uwa, wato ta mayar da ita mahaukaciya ko
kuma karyar da zata yi ta haushin ta ita
kadai. Dan haka ta cigaba da jiran that
bad thing da tasan tabbas tana nan
tahowa kan bad girl like Safiyya. And it
eventually happened. Rana daya
Mustapha da Daddy suka dawo da ita
daga Abuja, Mustapha kuma ya sanar
musu ita da Mommy cewa Safiyya ta fara
shaye shaye, wannan maganar ta taba
zuciyar Mommy sosai, it kuma Safina ba
zata ce tayi mamakin hakan ba dan dama
ita ta san karshen alawa kasa, duk kuwa
wanda ya sai rariya ya san zata zubar da
ruwa, a ranta kuma sai ta saka kan cewa
downfall din Safiyya ne ya fara, and more
is coming. Kamar kuma ta fada da bakin
Mala"iku sai gashi ta shiga dakin Safiyya
ranar nan ta ganta kwance male male a
cikin jini da kuma kwalin maganin zubar
da ciki a gee. Lokaci daya ta fahimci
abinda ya faru, Safiyya cikin shege tayi kuma ta zubar da shi.
ita ta fada wa iyayen su, and da kyar ta iya
containing dadin da ya cika zuciyar ta
sanda ta ga Daddy ya dauki belt yana
tafka wa Safiyya, she deserves that, the
spoilt little bitch. And a ranta ta sake
cewa kadan ma kenan, More are coming.
A ranta tayi niyyar sanarwa da duk
kawayensu da suke bawa Safiyya more
importance than her, dan su san cewa
Safiyya is the bad one ita kuma ita ce ta
gari, amma sai Mommy ta kira su har daki
uta da Mustapha ta ja musu kunne da
manya manyan kalmomi akan duk wanda
a cikin su ya fitar da maganar waje to
babu ita babu shi har abada. Ta kuma
sake sealing bakunan su ta hanyar kara
tabbatar musu da kudurin ta na aura wa
Mustapha Safiyya. "Dan haka in kun fitar
da maganar ma nan gaba ku zata shafa
idan akayi auren" "amma Mommy in akayi
haka ba'a yiwa yaya Mustapha adalci ba,
wanna lalatacciyar yarinyar za'a aura
masa? Yarinyar da take shaye shaye ga
kuma cikin shege tayi sai kuma a makala
masa ita?" Mommy ta doke bakinta da
bayan hannun ta "kar in sake ji. Wallahi
Safina ki fita daga ido na, Kar in sake jin
kin fadi wadannan mugayen kalaman a
kan yaruwarki. Kaddara ce ta same ta
kuma babu wanda ya wuce wannan
kaddarar" Sai Safina ta juyar da kai tana hawaye. Me yasa su basa ganin abinda
take gani ne? Me yasa idon su yake
rufewa akan Safiyya ne?
Amma kuma dole tayi shiru din, dan ta
fahimci Mommy da gaske take sai ta
bala'in bata mata rai in dai maganar nan
ta fita tunda daga alama Mustapha ya
karbi maganar auren kuma ba zai fitar da
maganar ba. Dan haka ana jin maganar a
waje Mommy zata gane ita ce.
Amma kuma ta wani bangaren sai taji
dadin maganar auren Safiyya da
Mustapha. Hakan yana nufin a step
toward cikar muradin zuciyarta. Sai kuma
ta samu kanta da murmushi bayan ta
goge hawayen fuskarta. Muhammad will
soon be hers insha Allah.
Tun hutun Safiyya na farko bayan ta fara
MD University ta zo wa da Safina labarin
Muhammad. "Nayi saurayi Safina" ta fada
boldly kamar yadda ta saba yin maganar
ta direct, ko tayi maka dadi ko akasin haka
kai ka sani. "Malam Muhammadu. Malami
ne a MD" Safina tayi dariya, sunan sounds
like sunan tsohon lecturer mai fama da
tsohuwar mota. "Allah ya shire ki Safiyya.
Ke kuma duk iyayin nan naki akan lecturer
zaki kare?" Safiya tayi murmushi "ina son
sa a haka. Shima kuma yana so na sosai. Love is all that matters" ta fada tana juyi
akan gado dramatically. Safina ta girgiza
kai kawai a ranta tana jin downfall din
Safiyya yazo finally dan in dai tace tana
son abu to da wahala idan bata samu ba,
she will end up with tsohon lecturer
maybe ma mai mata da yaya, watakila ma
ya kusa retire.
Yayin da ita kuma Safina zata samu prince
charming dinta. Ta rufe ido tana lissafo
kamannin sa a ranta, dogo, fari tas,
masculine, kyakkyawan gaske with a true
red lips that she so much likes. Mai
matukar sonta kamar ya chine ta. Very
romantic wanda zai ke kashe ta da
kalamai da tarairaya da kulawa. And also
very rich, mai hawa manyan motoci da
saka suturu masu dan karen tsada. Tayi
murmushi, Safiyya can go with her Malam
Muhammadu. Ita kam ta riga ta gama
picturing irin mijin da take so and they will
live happily ever after, while Safiyya's
marriage will probably crumble saboda
rashin tarbiyyar ta.
Wanna buri da ta dora akan irin kalar
mijin da take so shi ya hana ta kula
samari, samari da yawa suna nuna suna
sonta, duk da dai most of them ba sa iya fuska, amma kat cikin su babu wanda yayi
fitting dream husband dinta, Shiga jami'ar
da tayi ita ma anan kano ya kara mata
yawan masu cewa suna sonta, ciki kuwa
ranar nan har da wani malamin
makarantar ta su da har ya bata dariya
ma, ta yaya ma zata kula shi? Sai kace
wata Safiyya. So take ta kere Safiyya a
miji kamar yadda ita kuma ta kere ta a
komai banda tarbiyya.
A haka har Safiyya ta sake dawowa next
hutu, a lokacin ne take gaya mata already
"malam Muhammadu" ya fara yi mata
maganar aure. "Kin san kuma Daddy ya ja
min kunne akan yin soyayya, tsoro na ke
j'"' sai Safina tayi dariya "ke ce fa Safiyya,
da kin yi wa Daddy kuka shikenan zai aura
miki Malam Muhammadun ki" amma sai
Safiyya ta girgiza kai "no, ba zai yi ba. He
is very serious about it". Wannan kuma ya
saka Safina wondering why? Me yasa
Daddy zai hana Safiyya samari amma ita
bai ce mata komai akan hakan ba?
Sai kuma ta samu amsa dinta a ranar 20th
birthday din Safiyya. Ranar da Daddy ya
tara su tare da wadansu mutane da suka
sha suits, ya shirya musu tatsuniyar cewa
kusan duk abinda ya mallaka mallakin
Safiyya ne. Ranar yadda Safina taga rana haka taga dare. How? Why? Ta yaya
Safiyya zata samu wanna abin, she do
not deserve it. Ita ma kamar Mommy,
daga farko ta dauka son zuciya ne kawai
ya saka daddyn fadar haka dan ya san ya
fara rashin lafiyar da bata da magani
kuma in ya mutu gadon Safiyya bashi da
yawa, sauran duk na Mommy ne da twins,
amma daga baya ita ma sai ta fahimci da
gasje maganar haka take. Abin ya kona
mata zuciya sosai. Sannan ya dasa mata
wani abu a zuciyarta game da Safiyya
bayan kiyayya. Hassada.
Bata tashi kara raina kanta ba sai da ta
fahimci '"malam Muhammadu" fa is not
someone she pictured him to be. Ba
tsoho bane ba, and he is far from being
poor. Ba wai ganin shi tayi ba amma daga
yadda suke zama suyi ta waya da Safiyya
da kuma irin kalaman da Safiyya take
furta masa ta cikin wayar a matsayin
amsar maganganun sa ta fara fahimtar
hakan. And then one day she saw a
glimpse of him sanda suna video call da
Safiyya. Sai da ta dafe kirjinta ta shiga
ban daki ta rufe kofa tana mayar da
numfashi. He looks exactly like yadda
take picturing prince charming dinta. And
she fall instantly in love.
Har ta sake fitowa basu gama wayar ba, bata jin me yake cewa saboda ear piece
ne a kunnen Safiyya din amma daga
yadda take ta zabga murmushi tana
lumshe ido ya tabbatar wa da Safina cewa
kalaman da yake gaya mata are exactly
irin kamalan da take so prince charming
dinta ya ke gaya mata.
Ranar har sai da tayi kuka. Wani irin zafi
zuciyar ta take yi mata. How can Safiyya
have that? How can she have everything
that she wanted for her self? As the good
girl that she is, ita ta cancanci everything
good ba wai Safiyyan da babu wanda ya
isa ya gaya mata magana ta ji ba. Sai dai
kuma bata san ta yadda zata bullowa
lamarin ba. Ba ta san me zata yi ba. Daga
nan ta ajiye duk wasu burikan ta a gefe,
dukkan rayuwar ta a gefe ta koma living
and breathing for Muhammad. Hanyar
duk da zata bi ta same shi ita take so.
Har wata rama tayi a cikin kwanaki kadan,
har sai da Mommy ta tambaye ta in akwai
abinda yake damun ta amma tace babu
komai dan tasan Mommy ba zata taba
goya mata baya ba wajen cimma burinta.
Daga nan soyayyar Muhammad ta fara jan
ta, ta fara daukan wayar Safiyya with
every chance that she gets dan ta kalli hotunan Muhammad, and the more she
looks at him the she fall deeper in love
with him.
Komai na shi yayi mata exactly irin yadda
take so, his smile, ya subhanallah! Bata jin
akwai abinda ba zata iya sadaukar wa ba
just to have him look at her and give her
that smile. Or kiss her with those lips. Or
even.…...... Bata jin akwai abinda ko wanda
ba zata iya rabuwa da shi ba to get
Muhammad. Especially Safiyya.
A haka Safiyya ta koma makaranta, taking
all the links to Muhammad with her.
Wannan semester din hauka ne kawai
Safina bata yi ba. Ta yi iyakacin neman da
zata yi masa a social media ta rasa shi. Ko
mai kama da shi bata gani ba. With him a
zuciyarta gani take yi dukkan maza kamar
dodanni ne. Bata da wani abu da ta sani
game da shi sai sunan sa, Malam
Muhammadu, what kind of name is that?
Sai dai bata da wanda zatayi shawara da
shi idan ba zuciyar ta ba. Zuciyar tata
kuma a cike take da soyayyar sa, dan
haka zuciyar tata ta bata shawarar da
take ganin ita zata kai ta ga samun
muradin ta. Wannan yasa Safiyya tana
sake dawowa wani hutun ta dauki wayarta
la nemo number din sa a ciki. “Pyar💕” la ga any saving, ta gane shine amma
ta ga any saving, ta gane shine amma
kuma wani irin kishin safiyyan taji tana ji,
da kyar ta lallashi zuciyarta ta hana kanta
fasa wayar dan takaici. Ta dauki number
din kawai tayi saving a tata wayar da
"Habibie"
Tabbas tana jin labarai iri iri a social
media, labarai akan halin maza da yadida
basu da amana. Sau nawa saurayi yana
soyayya da ya zai fasa ya dawo kan
kanwa? Sau nawa saurayi zai hada
kawaye biyu yayi soyayya da su a lokaci
daya? Sau nawa saurayi zai auri kawa
daga baya yazo ya sake auran aminiyarta?
Dan Muhammad yana soyayya da Safiyya
hakan ba ya nufin cewa ba zai so ta ba ita
ma. Musamman tunda dai itana ta a da
kyawun ta dai dai gwargwado kuma tafi
Safiyya tarbiyya. Har a gurin malamai
kuwa taji cewa maza babu abinda suke so
irin mace mai biyayya. Basa son mai
taurin kai. Safiyya and taurin kai kuwa are
five and six, dan haka kwace saurayi a
hannun ta ba zaiyi mata wahala ba.
Wannan ya kara mata kwarin gwiwa sosai.
Ta kuma yi addu'a akan Allah ya bata
nasara akan sa, sannan ta zauna ta tsara
kalaman da zata gaya masa. Sai da ta
gama duk shirin ta sannan ta shiga daki ta
rule kofa ta kira shi, Bai dauka ba. Sai da tayi masa five missed calls sannan ta
hakura tare da gaya wa kanta cewa yana
wani uzuri ne, sai kuma ta yanke hukuncin
zata rubuta message ta tura masa, amma
kuma tana tsananin, tsananin son jin
muryarsa.
Ga mamakin ta tun kafin ta tashi daga
gurin sai gashi ya kira ta back, sai da
zuciyar ta tayi wata bugawa mai karfi
ganin sunan Habibi yana yawo akan
screen din ta. Ta lumshe ido ta bude tare
da sauke ajiyar zuciya sannan ta dauka.
Tas taji muryarsa ta fito ta cikin wayar,
with his fulani accent, "hello, who is
there?" Ta sake sauke wata ajjiyar zuciyar,
muryar sounded exactly like yadda tayi
tunani, sannan a hankali ta sake tata
muryar kasa ta fara gaishe shi, tun kafin
ta karasa ya katse ta "I missed calls from
this number, wacece? how can I help
you?" Tace "wata zuciya ce da ta kasa
controlling kanta har sai da ta kira ka dan
tayi maka fatan alkhairi tare da shaida
maka cewa tana cike da muradin.......
." Ya
dakatar da ita "thank you for the call and
the care, But I am not interested" and
then a sound na katse kira.
Ta jima da wayar a kunnen ta ta ma kasa
sauke ta kasa, Wani irin daci take ji a ranta, dacin da har sal da ya sauko da hawaye daga idonta zuwa kuncin ta, Shikenan? Just two seconds na muryar sa
shine reward din soyayyar ta?
Zuciyar ta bata sake breaking ba sai
washegari da ta sake gwada kiran sa taji
cewa yayi blocking number dinta. Tana
shiga dakin Safiyya kuma ta tarar da ita
tana ta dariya a waya kuma ta san da
shine. "I miss You too. Soon zan dawo
ai…..." Safina ta juya da sauri zuwa nata
dakin ta fada kan gado ta kama kuka.
Kukan da tayi na farko a kansa, not
knowing it is just the beginning.
To add to her agony, bayan ta kuma
samun damar daukan wayar Safiyya da
niyyar sake dubawa ko zata samu wata
number din sa ko kuma social media
handles dinsa, ko dai wani abu da zai yi
linking dinta da shi, sai ta tarar safiyyan ta
chanja password din watar tata daga
wanda ta sani, tayi ta kokarin guessing
amma ta kasa bude wayar, daga baya ma
sai wayar ta rufe kanta, takaici ya kara
rufe Safina ta tashi ta fita. A haka har
lokacin komawar Safiyya makaranta yayi,
bata samu wani abu da zai sake linking
dinta da shi ba. A lokacin ne kuma ta lura
da hoton da Safiyya ta chanja na kan
screen din ta da shi. Hoton su ne shi da ita a gaban motar ta, motar da aka siya
mata saboda gata duk kuwa da cewa a
hostel take zaune amma ita aka ki siya
mata aka ce ta ringa amfani da motocin
gidan. Daga alama Safiyya ce ta dauki
hoton ta hanyar selfie, yana sanye da
kananan kayan da suka kara fito da kirar
jikin sa, ya dan hade ransa kadan
hannayensa a cikin aljihun wandonsa
yayin da Safiyya take dariyar da take
bayyana kyawawan hakoranta, daga
alama tsokanar sa take yi. Safina taji wani
kishi ya kara sarkafe zuciyarta, ta saka
hannu ta toshe fuskar Safiyya ta bar tasa
shi kadai tana imagining fuskarta a inda ta
safiyyan take. Tabbas ba karamin kyau
zasu yi ba. Tabbas ba karamin dacewa
zasu yi da juna ba.
Sai kuma wani tunani ya zo mata, ta daga
wayarta ta bude camera sannan ta saita
wayar safiyyan ta dauki screen din wayar
a hoto bayan tayi zooming ta tabbatar
yayi clear sosai. Ta ajiye wayar safiyyan
sannan ta koma kan hoton da ta dauka a
wayarta tayi cropping ta cire Safiyya ta
bar shi shi kadai. Sai taga ya kara yi mata
kyau sosai, ta jima tana kallon sa sonsa
yana karuwa a cikin zuciyarta kamar zai
fasa kirjinta ya fito. A take zuciyar tata ta
sake bata wata shawarar, ta dauka ba tare
da musu ba, ta juya zuwa dakinta ta zauna tare da hawa Instagram ta nemo
blog din da ta kanga ana posting irin
abinda take so, ta tura hoton tare da
rubutu kamar haka.
"Salam malama, Hide my ID please. Dan
Allah ina cigiyar wannan bawan Allahn ne.
Allah ya saka min soyayyar sa a cikin
zuciyata kuma na rasa a inda zan same
shi".
Ta tura sannan ta zauna zaman jira. Ranar
da wayarta ta wuni ta kuma kwana a
hannun ta amma malama bata yi posting
ba, washegari ma haka. Daya washegarin
ma haka. A ranar ne kuma Safiyya ta sake
komawa makaranta. Sai a daren ranar ne
ta ga anyi posting request din nata. Nan
da nan aka fara comment, masu fada
mata bakar magana nayi masu zagin ta
nayi, yayin da wasu kuma suka fara
yabawa da halittar gwarzon nata suna
nuna suma suna so. Babu wata
takamaiman amsa dai har bacci ya dauke
ta. Da safe tana yin Sallah kan wayarta ta
koma ko zata ga wani sabon comment, a
lokacin ne kuma ta gani daga wata da ta
kira kanta da kanwar sa "laaah, wannan ai
Hamma ne. Poster kina ruwa".
Babu bata lokaci ta shiga dm din yarinyar da daga baya ta fahimci sunan ta Mufida,
la gaya mata ita ce mai cigiyar wannan
bawan Allahn, tana so ta taimaka mata ta
hada ta dashi. A take Mufida ta gaya mata
ba zal yiwu ba, yana da budurwar da yake
so sosai kuma bayan ita baya kula kowa.
Amma duk da haka bata kyale ta ba, ta
ringa yi mata naci. Kira, message, kira,
roko Allah da Annabi. Daga baya dai ta
bata number din sa tace ta gwada sa'ar
ta. Number din dai data dauka a wajen
Safiyya ce, amma bata gaya wa Mufida
yayi blocking already ba, sai ta sayi wani
sim din musamman ta sake kiran sa da
shi. Wannan karon ko dauka bai yi ba, ta
tura masa message, da aka kwana biyu ta
sake kira sai taji shima yayi blocking. Still
bata hakura ba, ta koma ta ringa bin
followers din Mufida tana nemansa har sai
da gano shi.
"Muhammad Gidado" ta karan ta sunan
shi a fili tana jin sunan ya zauna a dukkan
gurbin zuciyar ta, Sai dai account dinsa
private ne, ta tura masa friend request,
request din da har yau bai amsa ba,
Ta yaya? Ta yaya zai so Safiyya ita kuma
ya ki ta? Me yasa? A zuciyar ta sai take
ganin dan dai kawai bai bata chance bane
ba. Shi namiji ne fa ita macece, kuma ba, Shi namiji ne fa ita macece, kuma
macen da take da komai da maza suke so
a tare da mata. In dai har zata samu
chance with him tabbas zata ya mantar
da shi Safiyya ta kuma kafa kanta a cikin
zuciyarsa. Zata yi amfani da dukkanin
baiwar da Allah yayi mata dan ganin ta
cimma wanna buri na ta.
Kamar amsar addu'ar ta sai ga wannan
kaddara ta saukar wa Safiyya, kuma
kamar yadda Mommy tace, in dai har aure
ya tabbata tsakanin Safiyya da Mustapha
to hakan yana nufin rabuwar Safiyya da
Gidado, hakan yana nufin high chance for
her to get him. In dai har Safiyya tana
gidan mijinta kuma ai dole ya hakura ya
manta da ita.
Sai dai ta cigaba da kiran Mufida da
sunan gaisuwa, dan ta kara tuna mata da
cewa tana nan fa akan burin ta bata
hakura ba. Tana ganin hakan xai kara
pushing luck dinta up. Sai dai bata san
luck din nata zai yi sama sosai ba, bata
taba tsammani ba, kawai ranar nan bayan
Mommy da Daddy sun tafi da Safiyya
Germany zata haihu sai ga kiran wayar
Mufida, wai ana nema wa Muhammad
mata kuma tayi wa iyayen su da shi
maganar ta har kuma ya amince yace a
Kira ta a tambaye ta it she can get married in less than two months.
It was like a wildest dream come true,
Kamar mafarki wanda bata so kuma bata
fatan farkawa daga cikin sa. Abinda bata
taba tsammani ba. Ranar rawa tayi tayi a
cikin dakin ta ita kadai tana murna. Farko
kamar za'a fasa maganar dan da Mufida
kawai suke magana amma shi yaki kira,
lokacin har raba dare take yi tana addu'a
akan Allah ya juyo da hankalinsa gare ta,
ta fahimci he was heartbroken akan
rabuwar sa Safiyya, duk da dai bata san
me safiyyan ta ce masa ba cos she doubt
idan zata iya fitowa ta gaya masa cewa
ciki tayi in dai har ba cikin sa bane ba.
Wannan maganar kuma ita ta daga mata
hankali a lokacin, what if cikin jikin Safiyya
na Muhammad ne? It is very possible.
Amma in ta tuna da dagewar da safiyyan
tayi cewa bana Muhammad bane ba sai
taji sanyi a ranta, saboda ta san idan
nashi ne Safiyya ba zata ki fada ba.
Already ta riga tayi plans dinta na yadda
auren zai tafi ba tare da Safiyya ta sani
ba, ba za ta sani ba har sai an daura
vadda babu yadda zata yi, zuwa lokacin
uma a yadda taji Mommy tana fada zata iya yiyuwa an daura wa Safiyya nata auren
itama,
Rana daya kuma sai gashi ya kira din, dadi
kamar zai kashe ta, duk da dai abinda ya
gaya matan are far from kalaman soyayya
amma ya nuna amincewar sa akan auren.
Daga nan ta tatattara kayan ta sai Katsina
dan gin baban ta, a can take so a daura ta
yadda Muhammad ba zai ga komai da zai
dangantata da Safiyya ba. A can din kuma
ya je ya ganta for the first time, ta yi masa
kwalliya ta gani ta fada, kuma yayi mata
kyau shima a zahiri fiye da yadda yake yi
mata a hoto, amma kuma sai ta fahimci
hankalin sa sam baya kanta, sai kuma ta
fahimci ya fara kokarin dangantata da
Safiyya, wanda a take ta juya maganar ta
bagarar da shi. Kamar yadda ta saka rai, yan uwan
mahaifin ta sunji dadin kai musu miji da
tayi, musamman da suka fahimci cewa
akwai maiko a tare da shi. Ita kuwa ba
kudin sa take yiwa ba. Shi din take so,
kuma zata yi iyakacin kokarin ta taga
cewa ta same shi especially yadda
abubuwa suka kankama lokaci daya.
Taji dadi da Mommy da Mustapha suka
baro su Safiyya suka taho wajenta, amma
kuma bata ji dadin yadda Mommyn ta
dauki auren ba "waye shi? A ina kika samo shiz Shine tat dr da la addabeta da ita, Ita dai Mommy ta san
Salina bata da wani tsayayyen saurayin
da take kulawa, ballantana ace lokaci
daya har auren ta ya tashi da gaggawa
haka. "ni bana son gaggawar nan Wallahi,
Abi maganar nan a hankali a barsu su
fahimci juna muma mu fahimce su" amma
ina, yayan baban su har ya karbi kudin
aure kuma ya karbi ranar da iyayen
Muhammad suka zo da ita.
Dole Mommy tayi shiru, sai dai ta tattara
ta koma Abuja ta zauna a gidan Hajiya
tana cigaba da mita. "Ni hankali na bai
kwanta ba. Sam yaron bai yi min ba".
Amma a haka akayi. A haka aka daura
auren ta da Habibin ta Muhammad. Ranar
kowa ya ganta ya san tana cikin tsantsar
farin ciki dan sam ta kasa rufe bakin ta
tun sanda aka shigo da shi cikin gidan
yayan baban su bayan an daura auren ta
daga ido ta kalle shi taji kuma an tabbatar
mata da cewa shi din nata ne a yanzu,
mijinta, halak malak.
Tana ji still Mommy tana yiwa ya uwanta
mitar yadda angon ko damuwa da ya kebe
da amaryar sa bai nuna ba, "ko kallon kirki
banga yayi mata ba". Amma ita Safina ko
a jikinta, idan bai kalle ta yanzu ba zai kalle ta ne idan sun kebe a cikin gida
daya, daki daya kuma akan gado daya
Kamar yadda take jl a social media, maza
basa taba wuce wannan tayin, basa iya
controlling kansu akan wannan abun. Ita
kuma tayi niyyar bashi wannan abun har
sai ya gode Allah. Wannan niyya ta ta ta
saka tun weeks to bikin take ta lodawa
cikin ta kayan mata, Ita da kanta ta ringa
order daga Instagram vendors tana
dirkawa cikinta, ta shafa na shafawa, ta
goga na gogawa ta turara na turarawa ta
cusa na cusawa. Tayi niyyar Muhammad
sai ya mace a kanta, ba Safiyya ba, zata
mantar da shi wanzuwar kowacce mace a
duniya.
Ta shiga online classes da akeyi na sirrin
rije miji, a can ta koyo irin shugar da ya
kamata take yi masa dan jan hankalin sa,
a can ta koyi irin girkin da zata ke yi masa
dan jan hankalin sa, magana, tafiya,
kwalliya da shi kansa uwa uba bedroom
affairs din duk ta haddace komai a kanta.
Jira take kawai a kata gidan sa. Rayuwa
bata kara yi mata dadi ba sai washegarin
daurin auren ta da Mommy ta sanar mata
an daura auren Safiyya da Mukhtar. Ji tayi
kamar an saka ta a aljanna. Shikenan
Safiyya da Muhammad suny rabuwa ta
har abada, dan ta tabbatar a irin son da ta
san Mukhtar vana vi wa Safivya to auren su mutu ka raba ne takalmin kaza,
o da daga baya Safiyya tayi accusing
dinta of auren tsohon saurayin ta, zata ce
coincidence ne, tunda dai Safiyya bata
taba nuna mata shi ba. Koma bata yarda
ba matsalar ta ce. Ita dai tunda ta samu
Muhammad shikenan.
Sai dai tun ranar dinner din su ta tabbatar
wa kanta akwai jan aiki a gabanta, ta kata
fahimtar girman son da Muhammad yake
yiwa Safiyya, amma kuma ai babu yadda
ya iya, tunda Safiyya dai matar aure ce a
yanzu. Ita bata ma ga dalilin da yasa
Mommy ta dauki zafi a lokacin ba, in ma
ya tafi ai zai dawo ko? Kawai dai dan
Mommy bata son sane tun farko, but she
will learn to love him eventually. Da zarar
ta shiga gidan sa ta kuma shiga dakinsa
komai zai kare. Shi namiji ne ita kuma
mace, zata bashi abinda duk duniya babu
mai bashi irin sa.
Sai dai, tun a ranar da ya dauke ta daga
gidan su da kansa ya kaita gidan sa, tun a
daren ranar ta fahimci kaddarar da ta
kawo ta gidan sa mai wahala ce, ta
fahimci ba zata ci wanna jarabawar da
sauki ba, Mugun kalion da yayi mata a
cikin dakinsa tunda aka haife ta ba'a taba yi mata irin sa ba. Mugayen kalaman da ya
gaya mata tun da aka haife ta bata taba
tsammanin wani zai gaya mata irin su ba.
Jikin na ta da take ji da shi shi yayi wa
kalion banza ya kuma wulakanta, sannan
ya hankada ta waje ya rufe kofa.
Haka taje ta kwanta rungume da pillow a
kirjinta, hawaye kwance a idonta, da kyar
ta samu tayi bacci saboda bakin ciki da
kuma tarin kayan matan da ta dura wa
cikin ta. Wata irin soyayya take yi masa
zazzafa. Wata irin sha'awar sa take ji mai
karfi. A cikin kwanakin da suka biyo bayan
nan ta kara tabbatar da gurbin da ya ajiye
ta, kamar yadda ya fada mata da bakinsa
"you are just a ladder da zanyi amfani da
ita to get to Safiyya" ta kuma kara
fahimtar cewa duk abinda yake yi mata ko
kuma zai yi mata nan gaba saboda
safiyyan ne. Shi gani yake yi kamar ita ta
raba shi da Safiyya, tuhumarta yake yi
kullum bincike ya ringa yi kullum, so yake
lallai sai ya san menene ya faru da
Safiyya,
Ita kuma wannan sai ya kara mata tsanar
Safiyya a zuciyar ta, kuma take amfani da
dukkanin damar da ta samu wajen gaya
wa Safiyya magana a kokarin ta na rage
radadin maganganun da shi yake gasa mata kullum saboda tana yi masa wami
inn son da ba zata iya mayar masa ba shi.
Kullum bakin cikinta shine, ta yaya zai zo
Safiyya soyayya mai zafi irin wannan
sannan ita kuma ya ki ta? Why? Sai kuma
ta sake wani realization din da ya kara
sinking zuciyarta, ba shi kadai ba, dangin
sa ma basa son ta except for yan gidan
su. Ya tabbatar da wannan ne tun ranar
da ya kaita gidan kakannin sa da niyyar ta
gaishe su. Tun daga kallon da kakar ta sa
ta bita da shi ta ji kamar zata rushe da
kuka, kallo ne irin na "wannan kuma fa?
Daga ina?" Daga baya ma kiri kiri ta ce ta
tashi ta bata waje zata yi magana da shi.
Kannen mahaifin sa ma da aka tira ta ta
gaishe su a sama bata ga komai a tare da
su illa rashin acceptance, ita dayar ma da
taji suna kira da Ummee ko amsa
gaisuwar ta bata yi ba, ko daga ido bata yi
bama ballantana ta bata mutuncin kallo,
dayar ce ta dan amsa mata ba yabo ba
fallasa sannan itama tace mata ta sauka
kasa gurin yara.
Su kuwa wadanda aka kira da yara tana
saukowa wajen su suka daina hirar da
suke yi duk suka bata fuska, Daga baya
suka fara zamewa daya bayan daya suna
komawa cikin wani daki, sai ji tayi sun
cigaba da hirar su har da shewa a cikin dakin. Wannan ba karamin kona mata rai
yayi ba har sai da ta shiga toilet tayi kuka.
Amma a karshe ta share hawayen ta tana
jin a ranta cewa ta fahimci dalili6da yasa
suka yi mata haka. An gaya musu ita tayi
wa Muhammad tallan kanta, kuma ta san
wadda ta fada, Mufida ce. Dan haka tun
daga nan ta ce a ranta duk ta san inda
zata ajiye su har munafukar mufidan, su
bari dai kawai ta samu Muhammad a
hannun ta. Sai dai kuma a daren ranar
Muhammad ya gurza mata wani rashin
mutuncin da har yau ta kasa mantawa da
shi. Har gorin agolanci yayi mata.
Wasa wasa abinda take ganin tafi karfin
sa ya juye ya koma cewa ya fi karfin ta.
Duk abinda zata yi dan ta kawo
Muhammad kan gadon ta tayi amma ya
gagara zuwa, duk abinda aka gaya mata
yana jan hankalin namiji tayi amma yaki
jan nasa hankalin. Ta fahimci ma shi
hanyar rabuwa da ita yake nema sai dai
yana gudun fushin iyayensa ne. A lokacin
ne tana scrolling through Instagram taga
post din wata da take neman shawara
akan mijinta baya kula ta ta wannan
bangaren, ta yi iyakacin iyawarta amma
kamar dutse take yi wa, sai ta ji kamar ita
ce tayi rubutun, dan haka ta shiga
comments dan gain ko zata samu mafita
akan tata matsalar, A cikin comments din ne ta ga wata ta bata shawarar da saka
masa desire pills a cikin lemo ta bashi, ko
baya so sal yayi. DM din matar da tayi
comment din ta shiga ta nuna mata kamar
ita ce mai post din ta kuma tambaye ta
inda zata samu maganin da tayi magana
akai, sai matar tace mata tana siyarwa,
dan haka babu bata lokaci ta biya kudin
har da na delivery aka kawo mata har
gida,
Sai dai kuma matsalar shine baya ci ko
shan abincin ta, ko loma daya bai taba yi
ba tunda aka kawo ta, amma duk da haka
ta gwada hada masa sobo ta saka a ciki ta
kai masa, sai dai kamar yadda tayi tunani
yadda ta kai da rana haka ta dauko
kayanta da daddare bayan ya bita da
bakar magana da mugun kallo. Yana
zaune yana juye tea din da ya dafa a cikin
kettle din sa zuwa cikin cup. A take ta
fahimci ta hanyar da zata bi ta bashi. Da
safe da ta dawo gyaran bangaren nasa ta
debi pills din guda biyu ta jefa a cikin
kettle din da already taji akwai ruwa a ciki.
Fatan ta shine ba zai zubar da ruwan ba.
Tana leken sa ta taga taga yayi boiling ya
zuba ya tati cikin bedroom yana sha. Ta
juya ta koma dakin ta, ta kara shanye
sauran maganin matan ta tare da tsala
wanka ta bade kanta da turare, wannan kukan da ake cewa maza suna yi wa
matan su shi take so yau Muhammad yayi
mata, wannan tarairayar da take
karantawa a novels shi take do ayi mata
ita ma yau. She already pictured him
crying and begging for her forgiveness
tare da alkawarirrika marasa adadi.
Sai dai shiru bai zo din ba. Tayi jiran har ta
gaji, ga abubuwan da tasha suna damunta
sosai tana gujewa kanta fada wa halaka,
wannan ya sa ta tashi ta tafi dakin nasa da
kanta, ta bude ta shiga har bedroom ta
ganshi kwance akan gado ya hadawa
kansa ac da fan amma sai gumi ne yaje
karyo masa, tasan baccin wahala yake yi,
ta san kuma bacci ba mai nauyi bane ba
dan haka ta shiga toilet dinsa ta cire
kayanta tare da daura towel ta fito ta dan
buga gado yadda zai tashi, yana tashin
kuwa ta jefar da towel din jikin ta sannan
ta durkusa ta dauka tare da yi masa karya
sannan ta fita. So take taga karyar taurin
kansa.
Ai kam ya biyo ta din, kuma yayi abinda
take fatan zaiyi din, but it was totally
opposite what she expected. Yes, he was
more of a man than she ever expected,
but there is no affection in his actions. All
the kisses, hugs, cuddles and whispering sweet words into her ears that she expected were missing. Bukata ce kawa ta kawo shi, bukatar da ita ta saka masa
kuma ita kadai ya biya without even
looking at her face, yana gamawa kuma
ya ture ta daga jikin sa ya fice daga dakin
tare da buga mata kofa da karfi.
Ranar tayi kukan da sai da ta dauka
hawayen ta zasu kare, gabakidaya hope
dinta ya ruguje a tsakiyar kanta. Da
wannan makamin ta dauka zata ci shi da
yaki amma sai gashi makamin nata yayi
backfiring a kanta. Da safe ko kallon
hanyar dakin ta bai yi ba ya fita, ita ta
tashi ta gyara kanta duk da azabar da
take ji a can, sai dai tana fitowa bayan ta
danji dadin ruwan zafin da ta shiga sai
gashi ya dawo, daga ganinsa sai wani
hope ya ratsa zuciyar ta, maybe it wasn't
all in vain, ya dawo ne dan ya nuna mata
soyayya at last.
Sai dai wata azabar ya sake dandana
mata, wannan karon bayan buga kofa har
da tsarabar takarda ya ajiye mata. Sanda
ta gani sai ta dauka kalamai ne irin na
nuna yabawa da kuma godiya da
alkawarin soyayya har abada, but instead
sai ta samu bayanin cewa yayi tafiya
kuma ita ma zata iya tafiya gidan su. Ta rintse idonta tana jin hawaye masu zafi
suna zubo mata, A ranar, a kuma lokacin
ne tayi nadamar auren sa. Dukkan kayan
yakin ta sun kare, still nasara tayi mata
nisa., Sai dai bata tafi gidan ba kamar
yadda ya bukata, ta cigaba da zama, ta
fahimci abinda yasa yake so ta tafi shine
dan kar iyayensa suce shi ya rabu da ita,
so yake ace ita ce ta rabu da shi. Ko da
kuwa ba dan haka ba tafiyar zata yi mata
matukar wahala a yanzu, dan wannan
abin da ya faru a tsakanin su ya kara mata
zafin soyayyar sa a zuciyarta yadda har
take jin kamar zuciyar tata ba zata iya
daukan sa ba, take jin kamar bata da
lafiya, kamar zata mutu. Daga haka kuma
sai ciwon ya dore, tun tana ganin abin
kamar wasa har ya zama gaske, wasa
wasa sai gashi likita ya tabbatar mata da
ciki ne a jikin ta, cikin Muhammad.
Wanna shine greatest news da ta samu
a rayuwar ta. Ta san wannan cikin yana
nufin kara tamke zaren alakar ta da
Muhammad. Zaiyi wahala yanzu iyayensa
su barshi ya sake ta. Jin labarin cikin ya sa
Mama ta tattaro ta ta dawo da ita gaban
ta dan tayi rainon cikin. Taji dadin hakan
sosal dan ta fahimci da gaske mahaifiyar
Muhammad tana kaunar ta kuma ta san
hakan yana da alaka da son da take wa Muhammad din.
Anan ta zauna ta jira shi har ya dawo daga
tafiyar da yayi bayan wata uku. Sai dai tun
a ranar da ya dawo din ta fahimci cewa
labarin cikin nata bai yi masa dadi ba,
amma ta san duk taurin kan sa in ta haihu
dole zai so abinda zata haifa din kuma
tana saka ran cewa soyayyar abinda zata
haifa zai iya shafar ta watarana. A lokacin
ne kuma mugun labarin mutuwar auren
Safiyya ya risketa. And her world came
crashing on her head. Duk da tasan zaiyi
wahala iyayen su da nasa su amine su
aura masa Safiyya bayan yana auren ta
amma ta san shi ba zai dauke ion sa
daga kan safiyyan ba indai ya san bata da
aure. Tayi kokarin boye masa maganar
amma har gida Mommy tazo ta bashi
labari, a take kuma ya bi Safiyyan.
Wannan ya sa Mommy ta saka ta a gaba
da tambaya akan abinda yake faruwa, sai
ta samu kanta da gaya mata cewa
Muhammad din ya ga Safiyya tun zuwan
da yayi gidan su farkon auren su kuma ya
fara sonta duk kuwa da gaya masa da ita
Safinan tayi cewa Safiyya tana da aure, ta
gaya mata cewa akan Safiyya ne duk
matsalolin da suke samu da Muhammad.
Ita kuma Mommy ta kwantar mata da
hankali da cewa abu ne da ba zai taba yiwuwa ba, babu yadda za'a yi a aura wa
Safiyya mijinta.
Sai dai a abubuwan da suka biyo bayan
nan ta fahimci babu komai a cikin rayuwar
nan sai son kai, duk iyaye yayan su suke
so. Including iyayen Muhammad wadanda
suka shafe idonsu da toka suka ki nunawa
Muhammad kuskurensa akan zubewar
cikin ta, maman da take kallo a matsayin
tana sonta sai ta juya mata baya duk da
abinda ya same ta na rashin link guda
daya da take ganin zai zaunar da ita a
gidan mijinta. A gurin Muhammad kuma ta
dauki wani darasi, darasin kuwa shine ba
zai taba son ta ba ko da kuwa zata ke
yankan naman jikinta ne tana bashi a baki
yana ci, kuma ba zai taba daina son
Safiyya ba ko da kuwa ita Safiyyan zata ke
yankan naman jikin sa tana ci.
Ta fahimci cewa her whole life has been a
lie. Duk abinda ta dauka akan maza da
yadda suke soyayyar su ba haka bane ba.
True love truly exists, kuma soyayyar
namiji ta fi karfi sosai akan ta mace
saboda zuciyar sa tafi ta mace karfi. Idan
namiji yana yi miki soyayya ta gaskiya
babu wani chanji na rayuwa ko kuma
dadewar zamani da zai goge wannan
soyayyar. Zai iya aure ma ya hayayyafa
amma still zuciyar shi tana ga waccan wadda yake so din kuma ko da ace sun
tsufa ne in ya samu dama zai aure ta. Ita
ma kuma Muhammad din ya sha gaya
mata cewa da ace ba ita bace ba, da ace
wata ce daban da bata da hadi da Safiyya
da zaiyi zaman aure da ita har ma in Allah
ya albarkace su da yaya su hayayyafa.
Daga nan sai mission dinta ya chanja
daga neman samun soyayyar Muhammad
zuwa revenge, revenge on muhammad,
revenge for loosing everything to him.
Wannan ya sa ta koma gidan sa ta cigaba
da zama, tana kara gaya wa kanta cewa in
dai tana gidan to ba za'a aura masa
Safiyya ba. Daga Daddy har Mommy har
su ma nasa iyayen ba zasu yi wannan
hadin ba. Ba zasu yarda su hada su kishi
ba.
Amma hukuncin nata bai yi wa Mommy
dadi ba, tayi fushi sosai da ita ta kare
mata zagi tas sannan ta kwashe masu
taimaka mata ta bar ta ita kadai ga rashin
lafiya. Duk da haka bata saduda ba. Ta
daura aniyar ba zata bar Safiyya da
Muhammad su samu abinda suke so ba,
junan su. Mama ta aiko aka dauke ta zuwa
gidan ta, hakan yayi mata dadi first dan
maran tana da kirki sosai kuma zata kula
da ita sosal, amma a yan kwanakin da ta
take yi a gidan Maman sal ta fahimci ta chanja mata fuska sosal. Kamar tana
kulawa da ita ne dan dole.
Sal gabanta ya fadi, zuciyar ta ta raunana
sosal. Tsoro ya kama ta, Kar dai Mama ita
ma ta daina son ta, kar dai ita ma Safiyya
take so yanzu. Wannan ya sa ta gaya
mata abinda take tunanin ko da soyayyar
safiyyan ta fara kafuwa a ranta zai rushe
ta tun kafin ginin yayi nisa.
Ranar mama ta shiga dakin da take tayi
mata maganar lokaci yayi da ya kamata su
koma gidan su ita da Muhammad. Sai
kuma ta dora mata da nasiha akan hakuri
da kaddarar miscarriage da ta same ta.
Sai ta dago kai tana kallon ta tace
"Mama" Mama ta juyo tana kallon ta, tace
"kun san kuwa abinda ya hada mu rigima
a gida ranar da accident din nan ya faru?"
Mama ta cigaba da kallon ta bata ce
komai ba sai Safina ta cigaba da cewa
'"akan kanwa ta ne. Wai kanwata yake so.
Yace sai ya aure ta. Ba zaku aura masa ita
ba ko?" Mama ta dawo ta rike hannunta
tace "ki kwantar da hankalin ki. I already
know about it kuma na riga nayi masa
magana" Safina ta gyada kan ta "Nagode.
Nasan dama ba zaku yarda ba. Kawai ina
damuwa ne dan na san halin Safiyya. Ko
kun matsa masa akan rabuwa da ita ba
lallai ne ita ta rabu da shi ba
Zata makale masa Especially not after
what happened" cikin curiosity Mama
tace "what happened? Menene ya faru?"
Safina ta dago kai ta kalle ta sai ta mayar
da kanta kasa tace "she is trying to cover
up her past" ta danyi shiru sannan ta
dago kai ta cigaba "she have a bastard
child. Tazo garin nan karatu ta koma gida
da ciki. Har yau bata fadi waye uban dan
da ta haifa ba. Ina tsoron kar ta makala wa
Muhammad".
Mama ta zare hannunta daga nata
idanunta suna nuna tsantsar tashin
hankali. A razane tace "Safina? Me kike
fada ne? She is like a sister to you" Safina
ta girgiza kanta "she is never my sister.
Bata da tarbiyya ko kadan" mama ta mike
har lokacin hankalin ta a tashe. "Na shiga
uku" ta fada a hankali, ita Safina sai tayi
mamakin tashin hankalin Maman ta bude
baki sai Mama ta daga mata hannu "I
don't want to hear anymore. Wannan
issue din sirri ya kamata a tsakanin ku ku
family dinta. Bai kamata kina fadawa
mutane ba, Ina kuma fatan bayan ni ba
zaki gaya wa kowa ba" sai ta juya da sauri
ta fita daga dakin,
Salina ta bita da kallo cikin mamakin reaction dinta, sai kuma ta daga kafada
cikin nuna ko in kula. Sai dai zuwa dare ta
fara damuwa da reaction din maman
musamman sanda ta aiko a gaya mata ta
hada kayanta gobe zata koma gidan ta.
Ba kuma ta shigo tayi mata sai da safe ba
kamar yadda ta saba. Sai Safina ta samu
kanta da yin kuka, ta sake rasa wata
soyayyar, ta rasa Mama, Abba dama bata
san inda yasa gaba ba. Yanzu Daddy da
Mommy ne kadai suka rage mata, sai
kuwa Mustapha.
Ta koma gidan mijinta still hoping zaman
nata a gidan zai hana Safiyya shigowa,
still thinking iyayen nasu zasu so ta ko da
this ones ne. Amma sai dai sati guda da
yin maganar ta da Mama ta na zaune a
falon ta ita kadai kamar kullum tana jiran
ta ji shigowar motar sa, duk da ba lallai ne
in ya shigo ya leko in da take ba. A zaman
ne ta dauko wayarta tana chatting da
kawayenta, like always, tana ta zuba musu
karya akan Habibin ta, bayan sun gama
hirar ne kamar an ce mata ta duba status
sal ta duba,
Pictures ta ga ana ta saka wa kamar kuma
duk iri daya ne sai changing position. Yan
wwan Muhammad ne suke saka wa, few of
them da take da numbers dinsu, suma kuma ta karba ne tun lokacin bikin su a
gurin Mutida, tun bayan bikin kuma ba
wata magana suke yi ba. Na Mufida ta
fara budewa dan gain da tayi kamar
Muhammad din ta ne a jiki, gabanta yana
muguwar faduwa.
Ai kuwa hoton yana gama budewa sai
ganin ta tayi ta rikito kasa ba tare da
tasan sanda ta fado din ba. Muhammad
ne rungume da Safiyya kamar zai tsaga
kirjinsa ya saka ta ciki. Fuskarsa dauke da
murmushin da bata taba ganin yayi irin sa
ba, ita kuma shegiyar safiyyan ta
kwantarda kanta a kirjin nasa tare da rufe
idonta. A kasa Mufida ta rubuta
"alhamdulillah. I can't contain my joy. My
Hamma is finally happy"
Next kuma dan short video ne na lokacin
da safiyyan ta taho ta shige cikin
budaddun hannun Muhammad shi kuma
ya rufe da ita yana dan bubbuga bayan ta
kadan tare da rada mata wata magana a
cikin kunne. Shi kuma Mufida tayi
captioning da "an daura an daura, Safiyya
is finally Hamma's",
Then another picture da ya saka zuciyar
Satina ta kusan barin kirjinta, still shina a
gurin ne, gurin da yanzu Safina ta gane da
talon gidan Daddy. Suna tsaye dai still ya
unkuyo da fuskarsa ita kuma ta dago tata, fuskokin su dat dana juna, A cikin
idanuwansu kana iya hango tsantsar
soyayyar junan su.
"Shegiya karuwa" Safina ta fada cikin
karaji. "Wayyo Allah na" ta karasa tana yar
da wayar tare da dora hannayen ta duk
biyun a bisa kanta. Ba zata iya kwatanta
abinda take ji a zuciyarta ba kamar yadda
ba zata iya bada labarin yadda ta fita
daga gidan har taje gidan su ba. Burinta
kawai ta ganta a gaban Mommyn ta, the
only person da take ganin ta rage mata a
cikin masu sonta. Tana son Mommyn ta
rarrashe ta ta gaya mata karya ne abinda
ta gani.
"Mommy zuciya ta zata fashe, Mommy
zan mutu. Wayyo Allah na. Wayyo
Muhammad. Wayyo Abba na".
But instead of rarrashi, sai maruka ta
samu daga Mommyn na ta,
Her🧕🏻
Na jima ina kallon Safina ina kuma
sauraron kalaman ta. Abu daya kalaman
nata suke tunamin, ranar da aka daura
auren ta da Muhammad, halin da na shiga a lokacin da naga hotunan su ita da Muhammad. Furucin da muka yi kusan iri daya ne ni da ita sai dai banbancin
Mommy da ta kira ni kuma a kira Daddy.
Na sauke ajjiyar zuciya sannan na juya zuwa dakina, a hankali na furta "Karma is a real bitch"
Maman Maama✍🏻[07/01, 10:46 pm] +234 906 816 1960: ❤️🩹Safiyya❤️🩹
Episode Sixty Three: Sai da na jima a
zaune a daki katin Aunty Hajjo ta dawo, na
lura duk zuciyar ta a dagule take sanda ta
shigo sal kawai ta zauna tana kallo na
sannan tace "Allah ya ji kan Safiya" a
hankali nace "Ameen" sai ta sake yin shiru
sannan tace "ko zaki zo mu tafi gida tare?
Maybe you will feel more comfortable
there" na girgiza kaina ina murmushi a
raina nace, this is my father's house, I am
not going anywhere, in na bar gidan mu to
gidan miji na na nufa.
Ta sake yin ajliyar zuciya "but be careful
kinji? Be kind to Sa'adatu. Kar kuma ki
kula Safina har kuyi hayaniya kinji? Take
very good care of yourself because akwai
wadanda suka damu da ke sosai, your
father, your husband and junior" ta karasa
tana murmushi, nima dan murmushin nayi
sai kuma nayi sauri na daina dan kar ta
gani, ta sake cewa "da kin yarda zaki bini
da kin ganshi ai. Yana nan yana kokarin
fara rarrafe" jin dai ba xan kula ta akan
maganar sa ba sai ta koma nasihar da
take yi min kafin mu fita gurin Safina akan
hakkokin miji akan matarsa da kuma
hanyoyin da zanbi cikin sauki in sauke
wadannan hakkokin har ma da karin kyautatawar da zata kuma kara min martaba a idonsa, Ni kuma a raina ji nake yil can do all that and more to
Muhammad. Bata yi min zan cen zama da
Safina a matsayin kishiya ba ni ma kuma
naji dadin da bata yi min maganar ba cos I
wasn't ready for that. Ranar farinciki na
ce gwara a barni inyi farin cikin without
kishiya talks, kishiyar ma kuma Safina,
Daga baya sai Abdul ya kira ya a waya
yace tazo su tafi gida, tace min "zan tafi,
amma zan dawo gobe muyi maganar
gyaran amarya, duk da basan lokacin da
zasu saka na tariya ba amma bana jin zai
dauki lokaci tunda alhamdulillah akwai
masu maganar a dukkan bangarorin " ta
karashe tana dariya. Murmushi kadai nayi
sannan nayi mata godiya ta kuma raka ta
zuwa bakin kofa na dawo ciki dan bana
son mu hadu da Abdul ya tsokane ni.
Ina komawa daki a fada kan gado na tare
da lumshe idona ina jin dadin silence din,
in assessing tare da accepting situation
dina, Matar aure, matar Muhammad. Na
danyi dariya kadan sai kuma hawaye ya
biyo bayan dariyar, tun suna fitowa kadan
kadan har suka fara fitowa a guje suna
wanke duk wan sauran bakin ciki da
bacin ran da ke zuciyata dangane da issue din Muhammad, Sal na tashi na kara gyara mayafin jikina sannan na yi sujjada a kasa ina godewa Allah tare da cigaba da zubar da hawaye na akan sallaya ta.
Tabbas na dandana rayuwa, na dja wahala
irin wadda ko makiyi na bana yi wa fatan
ya sha irin ta, amma Allah ya kasance a
tare da ni every step of the way, shi ya
rike hannuna yayi guiding dina tare da
haska min hanyar da nabi, shi ya kasance
tare da ji a lokacin da nake tunanin na
rasa komai, shi ya taya ni zabin abinda
yake shine alkhairi a gare ni sannan kuma
ya juya lamari na in the most simplest way
possible. A cikin ikon sa da rahamar sa
yanzu kusan duk abinda na rasa sun dawo
gare ni, abubuwan kuma da ba zasu dawo
ba sai ya saka min hakuri da dangana a
zuciyata tare da fatan hakurin zai zama
kaffara a gare ni.
Na dago zaune daga sujjada ta ina goge
sauran hawaye na, ni na san wannan ba
shine fadan karshe a rayuwa ta ba, ni na
san wannan Mabudi ne kawai na wata
sabuwar chapter a rayuwa ta, ni na san
jarabawa ta bata kare ba for as long as I
am alive, amma kuma bana jin tsoro ko
kadan dan na tabbatar as long as zan
kasance tare da Allah shima zai kasance
tare da ni, zai kuma yi riko da hannayena
ya taya ni fighting battles dina, battles din
na tabbatar zany wining tunda ina tare da
Allah na.
Daga nan kuma sai na tashi na gabatar da
sallar ishain da ban yi ba. Ina cikin sallar
Esther ta shigo ta ajiye min abinci ta
zauna tana jira na har sai da na idar
sannan na juyo ina kallon ta. Fuskar ta
kamar anyi mata albishir da Jesus dinta
ya zo "Madam! Congratulations. Ina cikin
murna sosai. Mijinki mai kyau mai kyau
mai kyau. I cannot tell you how happy I
am for you" nayi murmushi "thank you
Esther.
And I don't know how to say this to you
but just know that kinyi matukar kokari
gurin tabbatuwar wannan maganar" ta
dan bata rai tana tunanin kokarin da tayi
sai kuma ta sake washe baki "the pepper
soups! Guda uku nayi. Da na naman rago,
dana kaji da kuma na kifi"., Nayi murmushi
kawai bance komai ba sai ta sake cewa
"dazu na ban san angwayen zasu zo ba
banyi musu komai ba, sai ga Alhaji Ahmed
nan ya kawo snacks da yawa yace in kai
musu da drinks" na gyada kai kawai "ya
kyauta. Ya kyauta sosai'",. Ta nuna min tray
din da ta shigo dashi "white rice na dafa
miki da sauran fish pepper soup din dazu
Na san kina so. And I made your
timoothie!" Ta fada with excitement. Na dauki cup din a zuka through straw din
da yake saman sa yayin da ita kuma ta
zuba min ido tana kallona har na ajiye
sannan nace "duk kamun kafar ki dai ba
zan tafi da ke ba. Kina nan gidan" ta bata
rai "haba madam haba madam" nayi
dariya "sai abinda Mommy tace, kin san
dai ba zan dauke mata ke ba ko?" Ta
gyara zama "shawara Madam, na yarda a
kawo wasu masu aikin, and then in kin
tashi tafiya I will just say tunda akwai
wasu ni zan biki, kinga ba zata ce komai
ba" nayi shiru bance komai ba sai ta sake
cewa "please!'" Nayi ajjiyar zuciya "okay.
Shikenan. Get them. Guda uku, Sai mu
gwada su mu gani" ta mike da sauri tana
murna "na gode, thank you Madam".
Tana fita na bude abincina na ga yadda ta
kawata white rice din with vegetables.
Pepper soup din ma daga gani ba wai
saura bane ba sabo ne tayi min, duk kuma
na san na kamun kafa ne. Sai na samu
kaina da cin abinci na cikin nishadi,
abubuwa da yawa suna yawo a kaina,
plans nake making iri iri, in saka in
warware in girgiza kai a inyi murmushi
duk ni kadai. Sai a lokacin na tuno da
cewa tun rana waya ta a kashe take, Allah
kadal ya san sau nawa Muhammad ya kira ni a yau din nan, To dama ya lafiyar kura?
Na dauko wayar bayan na gama cin
abincin na kira Esther tazo ta kwashe
kayan. Na kunna, messages suka shigo
min sosai, na sa na fara nema kuma shi na
fara budewa na karanta.
"I am yours, and you are mine. Forever
and ever"
Nayi murmushi na sake karantawa sannan
na kara karantawa. "Ina sonka sosai
Muhammad" na fada a hankali. At a point
na fitar da rai completely da auren
Muhammad. A lokacin da na zabi Mukhtar
da kaina na dauka na rabu da Muhammad
har abada. Na dauka kuma zan zauna da
Mukhtar har abada. Amma ashe Allah
yana nasa plans din.
Naji ina son kiranshi inji muryarshi, for the
first time as his wife, dan na san shi yayi
ta kira na wayar a rufe, amma sai na samu
kaina da kasa yin hakan. So nake ya fara
kirana, ajin nan dai ba zan sake shi ba sai
na ja abina. Sai dai shiru bai kira ba. Har
na tashi na dan motsa jikina saboda
abincin da naci yayi min nauyi na kuma
gyara gurin kwanciyata tare da rage kayan
jikina nayi shirin bacci amma bai kira ba.
Sal na kwanta akan gado a fara karanta sakonnin da aka turo min.
Sal na lura da yawa yan uwan mu na Kano
sun samu labarin daurin aure na ashe,
duk sun turo min sakon taya murna,
Salima da Salim ma sun turo min, salima
ta ce ta kira wayar a kashe amma zata zo
gobe. Sai kuma wani message from
unknown number
'"Ina miki son da ba zan taba iya hakura da
ke ba Safiyya, ina miki son da zan iya taba
bari wani ya same ki ba bayan ni Safiyya.
Especially not him"
Na mike zaune tare da sake karanta
message din. Tabbas na gane wanda ya
turo sakon duk da ba number dinsa bace
ba kuma bai rubuta sunan sa ba. A take
nayi wa security na forwarding message
din tare da number din. Minti biyu suka yi
responding. "An sauke layin. But we will
be at alert. Be careful". Har na ajiye wayar
sai kuma na dauka da kira chief of the
security din nace masa "in kun ganshi
anywhere around this house or around
me, ku harbe shi a kafa ku mika wa police
shi. You still have the restriction order?"
Yace "yes boss, just lock your doors and
windows. We will get you a gun tomorrow"
Na katse kiran tare da dafe kaina ina jin
raina yana matukar baci. It hurts me a lot
idan na tuna da Mukhtar din da na sani,
Mukhtar din da na tashi together with,
sannan kuma na tuno wannan ranar, na
tuno abinda yayi min wannan ranar, Bana
jin da ace wani ne daban abin zaiyi min
ciwo irin haka, ko da kuwa ace Mustapha
ne.
Sai da na tuno da Mustapha sannan na
tuna da cewa naga sunansa as I was
scrolling through messages, amma ban
dauki wayar ba sai na tashi na rufe kofa ta
na kuma tabbatar dukkan tagogin dakin
da kuma na toilet a rufe suke. Na kuma
tabbatar wuka ta tana nan a inda nake
ajiye ta sannan na koma na kwanta.
Mukhtar ba zai kuma taba ni ba, har
abada.
Message din Mustapha na nemo,
"Naji abinda kika yi. Kin kyauta"
Ban bashi amsa ba kawai na fita ina jin
nadamar budewa, suna so su bata min daren farin ciki na. Gashi Muhammad din ma yaki kirana. Amma sai naki bawa kaina damar yin bacin rai, not tonight. Instead, sal na dauko chats din mu da Muhammad nayi ta karantawa ina murmushi tare da dariya at the same time, a haka har bacci ya dauke ni,
Cikin baccin naji wayata tana kara, na bude idona da kyar sannan na lalubota, sai lokacin ma na fahimci ko fitilar dakin ban kashe ba bacci ya dauke ni. Sunan
Muhammad na gani, na duba time naga 12:45, na dauka na dora akan kunne na amma bance komai ba sai yace "kar dai kice min bacci kike yi" na juya idona kamar yana kallo na sannan cikin muryar bacci nace "to me zanyi idan banyi bacci ba? Tunda babu wanda ya damu da ni ballantana ya kira ni yay min hira" ya. danyi dariya "amma kin bani mamaki. Ni da na dauka yau kwana zaki yi kina rawa da murnar farinciki burinki ya cika?" Na san tsokana yake ji da ita nima cikin tsokanar nace "ashe abinda kake yi kenan shi yasa baka kira ba? Kana can kana rawa da murnar burin ka ya cika. Na san fa yadda ka mace a kaina baka ji baka gani" yace "ohh da gaske. In na mutu a soyayyar ki ma ai tare muka mutu ni da ke. Har da kuka fa dazu saboda murna. Murnar kin samu santalelen bafulatani kama ta" nayi dariya ina jin baccin yana barin ido na nace "shi yasa naga ai har nayi baccina amma kai ka kasa bacci sai da ka kira kaji murya ta. Dan in baka ji ba ba zaka iya bacci ba" yace "wannan kuma kin fadi gaskiya. Ba zan iya barci ba sai naji muryar ki. Sai yanzu na shigo gida tun dazu ban samu privacy ba. Ina ta fama da baki. Bayan bakin kuma sun tafi sai muka zauna da Abba da Mama muna ta magana. I told them all about you. But sai na fahimci sun san some parts of the story" na lumshe idona na bude ina jin girmansu yana karuwa a zuciya ta for accepting me the way I am kuma ba tare da wani bata lokaci ko wasu conditions ba.
Ya cigaba "Abba was a bit concerned
about all the ...….. He was concerned
about the..........." Na karasa masa "about
the wealth" yace "yeah, right. But then
daga baya sai Mama ta fahimtar da shi.
Naga alama kin samu fada sosai a gurin
Mama" ya karasa da farinciki a muryar sa,
nace "nima fadarta mai girma ce a wajena" yayi ajjiyar zuciya "ni yanzu damuwata itace naga alamar suna son su la lokaci kafin ki tare wallahi. Abba wants
to renovate the house, wai zai mayar da
Shi up to your standard" na danyi dariya
"menene standard din nawa? I thought it
was built to my taste da mako?" Yace "yes, but yanzu suna ganin wai gidan yayi kadan, ni banga kadan dinsa ba. Nayi magana kuma Mama ta harare ni tace min marar kunya" nayi dariya "inye, rich kid.
Kana zaune ana yi maka komai ko?" Yace
"not anymore. Abba said this will be the
last. Dama sunce in suka yi min aure sun
daina yi min komai. Amma auren ne har
yanzu ba'a gama ba" ya karasa yana
dariya. Nace "uhmm, dan gata" yace "ba
zaki bari ba ko? Please ni dai in sunzo
sunce lokaci mai yawa zasu saka ki ce ke
next weekend kike so" nayi dariya "kar ka damu. Ni gobe ma zan taho. Kawai ka samu daki daya a gidan ka share mana shikenan".
Haka muka ta hira, lokaci yana ta tafiya
bamu sani ba kuma munkan mu ba zamu
ce ga abinda muka tattauna a hirar ba. Sai
jin sanyin gari nayi yana ratsa ni sannan
na kalli agogo, nayi sauri na bude ido.
"shikenan zaka saka gobe in tashi da
kumburarrun idanu. Go and sleep Mr
Man" yace "duk wanda yace miki me yasa
baki yi bacci da daddare ba ki ce masa
nine na hana ki yin baccin, in kika ce haka
zasu kawo ki da wuri" nayi murmushi
kawai "good night" yace "sai dai good
morning kuma yanzu ai. But just one more
thing please, Tambaya ce da n'" nace "Allah yasa na sani" yace "Akwai abinda ya damyi confusion dina, lissafina bai tafi dai dai ba gaskiya, dazu ma muna
maganar da Mama sai naga kamar ta
share maganar bata son y" na danyi shiru
ina jin sa ina tunanin wanne lissafi ne, sai
yace "date din da kika gaya min uncle
Ahmad ya kawo sakon takardar nan. Har
zuwa yanzu a lissafina ba'a yi wata biyu
ba ma ballantana uku. I thought sai kinyi
wata uku tukunna or somewhere close to
that. I know you and Daddy all have the
Islamic knowledge concerning that so
dole akwai explanation" yayi shiru nima
nayi, na gane abinda yake nufi na kuma yi
realizing yadda yake avoiding mentioning
sunan Mukhtar.
Jin nayi shiru sai ya sake cewa "kin gane
abinda nake nufi? I just want to know
why" direct na bashi amsa "saboda banyi
masa idda ba. Babu iddar sa a kaina" ya
danyi shiru kamar bai ji me nace ba amma
na san yaji, sanda yayi magana naji relief
mai yawa a tare da muryar sa "and hakan
yana nufin me kenan?" Nace "ni ma ban
sani ba. Sai dai a tambayo" yace "wa za'a
tambaya? Bayan gaki nan ina tambayar ki
Kawai ki fada min abinda hakan yake nufi
n ban sani ba" nace "to ni ma ban sani ba, Good night" yace "zaki fada ne, Zaki yi min dogon bayani ne in details…..." Na katse shi "good night" sai na katse kiran na ajiye wayar ina murmushi duk kuwa da
cewa kaina yayi min nauyi sosai saboda
baccin da yake cikin sa.
Sai bayan da nayi sallar asuba sannan
nayi bacci mai nauyi, ban tashi ba sai
around 12 shima kuma dan ina son inje
inga Daddy ne tunda jiya ma ban samu
ganin shi da daddare ba. Da sauri nayi
wanka na shirya cikin doguwar rigar
atampa na fito as usual banyi kwalliya ba,
ina fitowa Esther ta shiga ta fara hidimar
gyaran dakin dama jiya duk na hargitsa
closet din.
Dakin Daddy na wuce direct, na tarar da
shi tare da uncle Ahmad suna magana,
ina shiga suka juyo suna kallona suna
murmushi "amarya" uncle Ahmad ya fada,
nayi kamar zan koma da baya dan kunya,
sai Daddy ya miko min hannunsa "come
here" na karasa na saka hannuna cikin
nashi sannan na zauna a kusa dashi tare
da gaishe shi, ya amsa na gaishe da uncle
Ahmad shima ya amsa tare da cewa "ya
shirye shire?" Sai nayi kamar banji ba sai
yace "umman ku zata shigo in anjima ai,
Salima zata zo itama kuyi magana. Duk
abinda kuke bukata sai kuyi magana kinji? Ko ba zaki fada min ba ki fada wa Salima
sal ta gaya min" a gyada kai idona a
kasa, Daddy ya dan matsa hannuna a
cikin nasa na dago ido na kalle shi sai
yace "kin shiga gurin Sa'adatu?" Na
girgiza kai "yanxu na tashi, na fara zuwa
wajen ka ne amma yanzu zanje wajenta"
ya gyada kai "alright ki shiga. And be nice
to her" nace "to" har zan tashi kuma sai
na sake cewa "Daddy kunyi magana da
Hajiya? Ta sani?" Yace "eh, I told her tun
kafin a daura. And I will call her yanzu in
gaya mata an daura din, jiya na manta ne"
uncle Ahmad yace "kar ka dora wa kanka
laifi yaya, ai ba kai ya kamata ka gaya
mata ba, Sa'adatu ce zata gaya mata" ni
dai sai ya zame hannu na na tashi, ina jin
Daddy kamar kar ya saki hannun nawa,
sai naji zuciya ta wani iri, he is already
missing me.
Har na kai bakin kofa kuma sai uncle
Ahmad ya sake kira na, na juyo sai ya
nuna min gurin zama dan haka na dawo
na zauna sai yace "na manta ba muyi
maganar ba. Akwai kayanki na gidan
Mukhtar, naje na gansu an hada komai a
waje daya, na saka yau za'a kwaso su a
kawo su nan gidan, ban sani ba ko akwai
abinda zaki yi amfani da shi a ciki.
Kayan sakawar ki da kika bari a can ma na
saka Salima ta hado miki su, tare da lefen
ki ashe duk baki yi amfani da komai ba, in
anjima in zasu zo zasu taho miki da su",
Na danyi ajiyar zuciya sai kjma naga
kamar ni duke jira suji abinda zance,
Daddy zainiya fadar abinda za'a yi ko ya
gaya min abinda zanyi amma Daddy baya
min haka, baya taba yanke min hukunci
sai dai ya tambaye ni abinda nake tunani
in na fadi abinda ya san ba dai dai bane
ba sai ya gyara min zuwa abinda yake dai
dai ta hanyar bani shawara.
"Ni sam ban saka lissafi da su ba. Banyi
tunanin komai a kansu ba. Abubuwa da
yawa ba'a taba using ba except for kujeru
da aka dan zauna akai. I don't know ko
za'a ajiye wa Salima tunda babu abinda
zasuyi har Allah ya kaimu bikinta. In ma
kuma bata son colours din ko design din
za'a iya siyarwa a siya mata wasu"
Uncle Ahmad ya fara girgiza kai, "kayan
masu tsada ne sosai, abubuwa da yawa
ba sai an sake siya miki ba. Kayan suna da
yawa sosai" ya yi ta fada irin ka rasa abin
cewa din nan. Ni kaina na san kayan masu
tsada ne dan sanda Mommy tayi order din
su sai da na jinjina kudin amma tace su
suka fi dacewa da ni. But there is trauma attached to them and I cannot use them.
Kuma wanna kyautar ina ganin zata kara
bonding zumuncin da ya fara samun
baraka tsakanin mu. Daddy yana
murmushi yace "kai da ba kai aka bawa
ba ina ruwanka? Kanwarta ta bawa ai" jin
hakan sai nasan yayi accepting decision
din nawa, na sake mikewa sai uncle
Ahmad ya sake cewa "at least ki karbi
kayan lefen to. Ni na siya dama ai ba shi
ya siya ba, sai ki kara akan dinkunan da
zaki yi na zuwa can gidan" na gyada kaina
nace "zan karba, Thank you Uncle" na
fada dan bana son inyi jayayya da shi kar
ya dauka wani abun ne daban.
Dakin Mommy na wuce duk kuwa da
yadda Esther take bina da cup din coffee
a hannun ta, bata falon ta, babu kowa a
falon dan haka na wuce bedroom din ta
ina fatan kar mu hadu da Safina a can.
Nayi knocking na tura kofa tare da
sallama ina jin yadda gaba na yaje
faduwa, ina cherishing relationship dina
da Mommy sosai ina kuma kokarin
avoiding abinda zai lalata shi. Tana
kwance akan gadon ta amma idonta biyu,
ta dan juyo ta kalle ni sannan ta mayar da
kanta ta kwantar, na zagaya ta side din da
fuskarta take na zauna akan carpet nace
"good morning mommy" ta bini da kallo
tare da dan motsa bakinta kadan ba tare
da naji abinda tace min ba, Banji dadin yanayin fuskar ta ba dan idanunta sun
nuna bayan kukan da tayi jiya bata yi
cikakken bacci ba. Na cigaba da zama a
gabanta amma bata ce min komai ba har
wajen mintuna goma, ina so muyi magana
dan haka nace "I am sorry Mommy" a
hankali tace "for what? What are you
sorry for?" Na danyi shiru ina tunani,
menene abinda nayi wa Mommy ne? Sai
kawai nace "I am sorry for whatever I did
that made you cry" ta dafa gadon ta mike
zaune tare da jingina bayan ta da
headboard. Tana kallona tace "tell me
something Safiyya. Tunda Allah ya hada ni
da ke akwai abinda na taba yi miki that
made you feel I am not your mother?" Na
danyi tunani kadan, I can mention a few
things but I didn't, sai na girgiza kaina
"babu" ta cigaba "but you still think I am
not good enough to be your mother ko?
Ke ma irin ta mahaifin ki ne ko? Kullum
kina tunanin zan cutar da ke ne ko? Kina
kallona a matsayin kishiyar uwa, bayan
kuma da ace Safiya tana da rai da ba zan
taba zuwa gidan nan ba" na girgiza kai
"ko tana da rai Mommy dole zaki zo ai.
Twins kuma fa?" Tayi shiru tana kallona
"you are always smart, with your words
with your actions and with your choices.
You have no idea how much hard it was to
raise you, especially with idanun babanki
da ko kallon banza aka yi miki sai ya chanja fuska, especially with idanun
mutane akai suga me zanyi, Wannan ba
yar ta bace ba wadancan ne yayanta.
Kuma bana taba yin dal dai. Adam will
criticize, Ahmad will criticize, Hajiya will
always have something to say. But I did
my best, Through it all I did my best. Idan
ku baku gani ba Allah ya gani ai. Ban taba
cutar da ke ba kuma ba zan fara daga yau
ba. Yes naso Mustapha ya aure ki amma
ban tura shi yaje ya ci zarafin ki ba. 12 1d AM
Tabbas ina son Safina amma ba zan goyi
bayan ta rabaki da saurayin ki ta aure shi
ba. Ni bana son yaron ma. Har yanzu ma
da kike matsayin matarsa still bana son
sa. Ban sani ba ko nan gaba zaiyi abinda
zai saka in so shi. Amma ina so daga ke
har Adam ku sani cewa it hurts so much
that you do not trust me after all these
years, that you treat me like an outsider
ba wai uwa ba da ya kamata ace ta fi
kowa kusanci da ku, ba zaku bude baku
ku gaya min magana kuyi min bayani ba."
Ta karasa hawaye yana bin fuskarta. Naji
zuciya ta ta kara karyewa, na tashi na
zauna a bakin gadon nace "kiyi hakuri
Mommy, dan Allah ki daina kuka. I am
sorry, I never meant to hurt you wallahi
ban so na saka ki kuka. Ke kadai ce
uwata, ke kadai na sani uwata kuma ke
zaki cigaba da zama uwata. Dan Allah ki
yale min" ta girgiza kanta "there is nothing to forgive ai. Kawai yana yin
tunanin ki akaina nake so ki gyara. In ma
da akwai na yafe miki. Allah ya ji kan
Safiya" nace "Amen. Nagode Mommy"
sai kuma na zagaye ta da hannayena na
rungume ta ina jin wani iri a raina. Nayi
missing our hugs and kisses. Nayi missing
yadda muke zama muyi hira muyi wasa da
dariya. Nayi missing dinta. Ta zagaye ni
da hannayenta ita ma sannan ta dan buga
bayana kadan sai kuma ta sake ni.
Na tashi na fita daga dakin ina jin nauyin
zuciyata ya dan ragu akan issue din. Ina
gama breakfast a kasa su Umma suna
zuwa tare da Salima da uban lodin
kayana, kayan sakawa ta da kuma
akwatinan lefe na da har yau Allah bai
bani ikon bude su na ga menene a ciki ba.
Aka shigar da su wani daki a ka ajiye su.
Sai a lokacin Mommy ta sauko still kana
ganin ta ka san tana cikin damuwa. Suka
gaisa sama sama da Umma, a raina ina ta
addu'ar kar Umma ta ce zata gaya mata
magana kuma sai naga bata yi din ba.
Daga nan Umma tace uncle Ahmad yace
suyi maganar shire shiryen tariya ta,
amma already Daddy yace baya son biki,
baya son duk wani abu da zai jawo
attention din mutane, nima dama banyi
lissatin yin biki ba, Ina dai tunanin shirya
walima for my friends da sukayi ta mitar na watsar da su tun lokacin wancan bikin,
Nan na gaya musu cewa ni walima kawai
dan shirya for my friends, Umma tace to
suna nasu Mutanen sai su zo walimar
kawai, a take Salima tace ba zai yiwu a
kawo mana tsofaffi cikin walimar mu ba,
suna ta musun su sai ga Aunty Hajjo nan
tazo itama. Na gaishe ta nan take ta shige
cikin maganar itama, ita ta goya wa
Salima baya. "A'a ba zaku shiga walimar
su ba. Kinga Salima, ku chanja wa event
din naku suna daga walima zuwa wani
sunan da zai nuna na yammata ne kawai,
in ba haka ba har da kakanni sai kun
ganj"
Ni dai ban ce musu komai ba. Mommy ma
few words kawai take dan sakawa dan
hankalin ta gabaki daya kamar baya gurin
kawai a zaune take. And I asked myself
again ina Safina take? Ko dai ta koma
gidan Muhammad ne?
Ban samu amsar ba sai da na tafi daki yin
sallar na hadu da Esther sai na tambaye ta
ko taga Safina a gidan? Sai tace "ya da
dare bayan kin taho daki Mustapha yazo
ya dauke ta. Na gyada kai, maybe gidan
Hajiya ta tafi ita ma, Ina yin sallar
maimakon in koma kasa sal na dauki waya
la na kira Muhammad muka sha hira, ya gaya min wai already har sunje da Abba kamfanin da zasu vi musu
Renovating gidan, har sun zabi plan, "kamfanin su Ya
Amen ne fa, they are into construction,
Dama su suka gina gidan tun farko, yanzu
ma kuma su zasu yi aiki a kansa" da ya
fara tsara min yadda suke so ayi wa gidan
sai da naji kana yana neman bugawa "ni
fa ba gane wa nake yi ba wallahi. Ka
barshi kawai in an gama naje sai in gani"
ya dan mararaice "inzo in dauke ki yanzu
muje in nuna miki?" na danyi dariya "me
zaka nuna min tunda ba'a fara komai ba?"
Ya danyi shiru "yeah, right. To wani abu
zan nuna miki daban. Wani abu ne da
nasan kina son gani" nace "dauki hoton
sa a waya ka turo min" yace "it is too big,
ba zai dauku a waya ba. Please inzo
muje?" Nace "ko kazo ma ba zan fito ba.
Wallahi gidan mu a cike yake da iyaye na.
Ba zan wuce su in tafi gurin a ba" yace
"ni fa mijin ki ne.
Maganar wa zaki ji? Tawa ko tasu?" Yadda
ya fadi maganar da authority ya sa na
mararaice "Please Baby, dan ni suka zo
gidan fa, Kuma kawai sai in bika mu fice
mu bar gidan?" Ina maganar Salima ta
bude kofa ta shigo tace min "Fiyya ki zo
ga Hajiya nan tazo" nayi mata alamar ina
zuwa sannan nace masa "kaji ko?" Ya
danyi shiru sannan yace "Hajiya
Maryama?" Nace "yes ita" yayi ajiyar zuciya "hey Piya! How are you coping? I
mean ya kuke ciki da Mommy and her
children?" Na sauke ajjiyar zuciya ina jin
dadin concern dinsa nace "yanzu dai
zanje gurin Hajiya. We will talk about it
later insha Allah" yace "okay. Just take
care of yourself kinji? Kar ki bar komai ya
bata min ranki. And ....... Zan shigo in an
jima da dare idan sun tafi. Kuma babu
zama a falo with the cctv thingy" nayi
dariya "okay. Bye Baby. Love you "
Da sauri na sauka kasa, ban san yadda
Hajiya zata dauki maganar ba kuma tana
daga cikin mutane masu muhimmanci a
rayuwa ta wadanda no matter the
situation ba zan so mu samu sabani ba.
Tana zaune a kan carpet ta mike kafarta,
na sauko reluctantly ina tunanin abinda
zata ce min sai cewa tayi "ina akwatin
kayan ki? Nace wa adamu fa ya gaya miki
ki hada kayan ki tare zamu tafi, wannan
karon ni zanyi gyaran amarya" Aunty Hajjo
tayi saurin cewa "a'a fa. Wannan aikin ai
na iyayen amarya ne ba kakanni ba. Ke dai
zaki iya kawo gudummawar abinda kika
tara" na dan saki raina kadan tare da
karaso wa nace "Adam, Hajiya, ba Adamu
ba" ta jeho min throw pillown da yake
kusa da ita "jaira, Adamu zan ce ba zance
Adam din ba" nace "already ai kin fada". Aka sake yin dariya,
Daga nan suka cigaba da lissafe lissaten
su yayin da ni kuma muka ware da Salima
muke namu. Decisions din mu na kayan
da zan saka ne a event guda daya da
nace zanyi sai kuma na kai amarya. Amma
kuma dai bamu sani ba ko gidan su
Muhammad zasu shirya wani abu. Karshe
dai muka ce zanyi dinkuna na fitar biki set
biyar in case, sai kuma sauran dinkunan
da zanyi. A take na dauko system dina
muka fara neman material, shiga can fita
can da kyar muka samu guda biyu da
suka yi mana, to matsalar kowanne sai an
nemi abun da za'a hada shi da shi. A
karshe dai kawai muka yanke shawarar
neman fashion designer da zata yi mana
komai. A karshe dai Salima kin bin Umma
tayi tace a waje na zata zauna "akwai
abubuwa da yawa da zamuyi kuma bamu
da lokaci" Umma tace "au har kun saka
ranar ne mu bamu sani ba?" Sai akayi
dariya kawal.
Da daddare Muhammad yazo kamar
yadda yace, na san da zuwan na sa dama
dan haka naje nayi wanka na shirya cikin
riga da skirt na atampa na gyara gashina
nayi daurin dankwali mai kyau. Dinkin ya
zsuna das a jikina, na shafa turaruka na
masu dadin kamshi, Salima tana ta
tsokana ta wai sai ta raka ni ta gaya masa ita ta shirya ni ko zai dan miko mata wani
abu. Ban samu lokacin yi masa girki ba
amma na saka Esther tayi masa kuma na
san zata fitar da ni kunya. Amma mutumin
nan yana zuwa sai yayi zaman sa a mota
sannan ya kira ni "ina waje a mota" nace
"waje kuma? Ka shigo mana ga ...." "Not a
chance. Ki same ni a mota" ya katse
kiran.
Na sauke wayar daga kunnena ina hararar
ta. "Kinji wai ba zai shigo ba" na gayawa
Salima da take bina da kallo, tace "to me
yasa? Ciki ba yafi sirri ba?" Na dan yi
murmushi kawai dan nasan rashin sirrin
cikin gidan shi yasa ya zabi zama a waje.
Na dauki mayafi na na yafa ina jin wani iri,
wasa wasa kuma sai zuciyata ta fara
bugawa da karfi. Wata zuciyar tana gaya
min in cire kayan inyi zamana a daki in
kashe wayata. Amma banyi hakan ba dan
nima ina son ganin sa amma ina tsoron
ganin na sa. Muhammad yanzu miji na ne,
kuma ban yarda da wannan neman
privacy din na sa ba,
Haka dai na taka na fita, a raina ina
tunanin wanna shine zuwan Muhammad
gurina gidan mu da niyyar zance na farko
in all the years da muke tare, na bude
karamar kolar gate na fita waje ina neman motarsa. A inda ya saba parking a
tsallaken mu na duba ban gan shi ba, sai
daga baya naga motar tashi a jikin gidan
mu cikin inuwar katangar gidan, Na sake
jin bugun zuciya ta ya karu. Na dan tsaya daga bakin gate din na
dauko waya ta na kira wayarsa, ina jin ta
tana ringing a cikin motar amma bai daga
ba. Na karasa kusa da motar na tsaya
zuciya ta tana kara gaya min in koma cikin
gida, sai naga an bude kofar bayan motar,
na dan tsorata kadan duk da ina kallon
security na a bakin gate sai naji muryar sa
yace "matsoraciya, come in" na kalli
motar, Muhammad bashi da gaskiya,
bayan kin shiga cikin gida da kuma yin
packing a cikin duhu shine ya koma seat
din baya ya zauna nima kuma yake so in
shigo bayan.
Na makale kafada "ni dai ka fito nan" ya
kunna fitilar cikin motar "kin ga fa, kaza
na kawo miki" ya karashe maganar yana
nuna min ledojin da suke gabansa. Sai
kuma ya bini da kallo ta hasken cikin
motar da ya haska ni "wow. You look
good" na dan tabe baki "ni dai ka fito" ya
danyi dariya "kar dai ki ce min ke matsoraciya ce har haka. I just want us to talk in private, shikenan kawai"
Na bishi da kallo, yayi kyau sosai, kamar ma sabon aski da gyaran fuska yayi, kamshin turaren sa da kamshin motar sa suka kara kawata min shi. "magana kadai zamuyi'" na fada ina hade rai. Yace "yes,
haka nace. In ba magana ba me kike
tunanin zamuyi?" Ya fada yana kankance
idonsa, na dauke kana nace "kayi
alkawari?" Ya daga gira "nayi alkawar'"
nace "ka rantse" yayi dariya tare da dafe
kansa "Please Piya, ki shigo mana. Bana
son mutanen waje suna gane min ke
saboda kyan da kika yi. Eh nayi alkawari I
will not do what you think I am here to do"
ya karasa da dariya a muryarsa sannan ya
matsa tare da bani space din shiga.
Sai da na sauke ajjiyar zuciya tare da
karanto addu'ar da ban san ko ta menene
ba sannan na shiga na zauna a dofane
daga bakin kofa. Ya bin da kallo sannan
ya girgiza kai kawai, sai kuma ya zuro
hannunsa ta saman cinyata ya jawo kofar
ya rufe sannan ya kashe fitilar da ya
kunna,
Maman Maama✍🏻
[07/01, 10:46 pm] +234 906 816 1960: ❤️🩹Safiyya❤️🩹
Episode Sixty Four : Fearful
A wannan lokaci da muke ciki na sanvi
kina bugatar abubuwa da zaki ci/ sha
Wanda zai saukar miki da wadatacciyar
niima Kuma ya Kara miki dandano da
kuzari. Akwai abubuwa da dama da muke
amfani da su a cikin gida Wanda in kika
¡ya sarrafa su zasu magance miki matsala
ta oza room musamman ma daukewar
niima da sauransu. To 'yar kuwa me kike
Jira? Kiyi kokari ki shiga wannan aji da
zamu gudanar inda zaki koyi abubuwa
kamar maganin sanyi, maganin Karin
niima, maganin Kara dandano da
sauransu a saukake ba tare da kin sha
wahala ba akan kudi qalilan.
Ga masu bugatar shiga wannan aji zasu
iya Yi mun magana WhatsApp
direct.wa.me/8033308307 ko Kuma kuyi
joining wait-list group dinmu domin Karin
bayani.
https://chat.whatsapp.com/
L1PcrHctun5JIQnBHmOlih
Duhun da na ga ya mamaye idona ne ya
razana ni lokaci daya, yana tuna min da wancan duhun. Na fara kokarin bude kofa
sai ya rike hannuna "Hey! What's wrong"
ya fada with that deep voice of his da
nake finding soothing a baya amma a
yanzu sai na jishi kamar as a reminder to
him being a man.
"Please ka kunna fitila, I
have phobia for darkness" na fada murya
ta tana rawa hawaye already ya fara
taruwa a idona. "Okay okay" ya fada yana
matsa hannuna da yake cikin nasa a
kokarin sa na ganin yayi calming dina
down amma ko kadan banji hankalin nawa
ya kwanta ba.
Ya saki hannuna tare da mikewa ya taba
wani abu a jikin dashboard din motar sai
naga haske ya kawo a jiki, ba wai hasken
da zai haska motar gabaki daya ba but
just enough to let us see each other. Ya
dawo ya zauna tare da juyowa sosai yana
fuskanta ta "shinenan?" Nayi shiru bance
komai ba ina kara takurewa a waje daya
tare da kallon duk wani movement dinsa,
Ya dawo ya zauna sosai yana karewa
fuska ta kallo, Sai ya lura da hawayen da
suke kyalli a cikin ido na yace cikin
mamaki "wai harda kuka? Daga duhu sai
kuka? Kin fiya shagwaba Safiyya" nayi kokarin gogewa tare da turo baki cikin shagwabar nace "ba kai bane ka kashe fitila kuma ni bana son duhu. Allah kar ka
kara kashewa" ya danyi murmushin da
ban gane ma'anar sa ba yace "to menene
abin toro a duhun in banda dai ke
matsoraciya ce, menene zai kama ki
bayan ina nan" na yi magana a can kasa
yadda ba zai ji ba "kai ne ai bana son
zama da kai a cikin duhun" yace "me kika
ce?" Na girgiza kaina da sauri "ni babu
abinda nace" ya bini da wannan kallon da
bana so, nayi saurin duke kaina sai yace
"baki da gaskiya, gulmata kika yi ko?"
Nace "dama mutum yana gulma shi
kadai? Ni da zuciyata muke magana" ya
matso yana kara tsare ni da idanuwansa
da na kasa cigaba da kalla "waye zuciyar
ta ki to? Na dauka nine ai, ta yaya kuma
za'a yi magana da ni ban ji ba" yadda
yake maganar a hankali ya saka nake jinta
tun daga kunnuwana har tafin kafa ta.
Na mikar da hannu na da niyyar yi masa
shamaki kar ya karaso jikina "kayi
alkawari, kar ka manta kayi alkawari, kuma
alkawari abu ne mai girma" sai ya zura
yatsun sa cikin nawa tare da sauke
hannayen namu kasa a tare. Na daga haya
hannun na nuna masa karshen kujerar ta
daya bangaren "ka matsa can ka zauna, ai kace magana zamuyi, amu iya yi kana
can ina nan" ya kalli gurin sannan ya kalle
ni tare da tabe baki sannan sake rike daya
hannun nawa da dayan nasa "too far.... Ba
zamuji maganar juna ba. Ko kinfi son sai
muni amfani da microphone wajen hirar?
Zance fa nazo" ya karasa maganar yana
robbing thumb dinsa a wrist dina. It was
just a simple touch, maybe innocent
maybe not tunda ban ga zuciyar sa ba but
it sent chills down my spine. Nayi sauri na
kwace hannun ina gogewa a jikin skirt
dina "no touching. You promised no
touching" na kwashe dayan hannun shima
tare da boye su duk biyun a baya na. Ya
jingina kansa a jikin kujerar yana kallona
da dariya a fuskar sa, na bata rai "kana
sane wallahi. Tsokana ta kake yi wallahi.
Dama alkawarin ba da gaske kayi ba" ya
daga kafada "da gaske nake mana. Zuwa
nayi kawai muyi hira muci kaza. And we
can't do that while knocking Daddy might
be watching ko?" Nace "to ai ba hirar
kake yi ba. Ta ba ni kake yi.
WhatsApp.com
KAYANMATA CLS WAITLIST
WhatsApp Group Invite
5
10:27
Kuma in kana da gaskiya me yasa ka siyo
kaza?" Yanzu dariya yayi so sai sannan
ace "shikenan yanzu ba zanci kaza ni da
matata ba sai da wata manufa. Maybe
abun yana ranki ne shi yasa har kika
takura kanki haka" na harare shi ban ce
komai ba sai ya sake cewa "ki rantse da
Allah ba abinda yake ranki ba kenan. The
innocent me is just trying to talk" ya fada
yana kara matsowa har jikin mu ya na
haduwa idonsa tar akan fuskata, gani
dama a jikin kofa nake a makale. Na zaro
ido tare da saka hannu na biyu a kirjinsa
na tura shi baya da dukkan karfina. Bai
motsa ba sai hannuna da naji ya sage
"ash" na fada ina rike guiwar hannun,
"sannu" ya fada yana rike inda na rike din
"ciwo kika ji? Bara in yi miki addu'a" sai ya
sunkuyo da fuskarsa dai dai damtsen
hannuna ya ja hannun rigar sama ya fara
hura min iska, sunkuyawar da yayi ya saka
gashin kansa yazo dai dai fuskata da
wuyana. Kamshin sa naji ya wuce ta
hancina ya shige har jijiyoyin jikina, Kuma
dai a ido kamar zai yi laushi in an taba.
Saukar lips dinsa a cinyar hannu na ne ya
saka na dawo daga tunanin gashin kansa,
na tura shi baya da karfi kuma da sauri,
saboda sammatar sa da nayi wannan
karon shi yasa na samu nasarar raba shi
da jikina. Na sake nuna masa karshen
kujerar nace "ko ka koma can ko in koma cikin gida. Wallahi babu gaskiya sam a
lamarin ka yau" ya daga hannu "okay
okay naji. Amma na tabbatar miki babu
abinda ya kawo ni yau sai tarin gaskiya.
Zan koma, amma ta yaya zamu yi hirar
kuma?" Ya fada yana komawa can
karshen kujerar jikin kofa kamar yadda
nima nake. Na sauke ajjiyar zuciya sannan
for the first time tun da a shiga motar na
shaki numfashin da ya karasa min har
cikina.
Na dan daga murya nace "in kayi magana
kamar haka zanji abinda kace" sai dai
kuma sai muryar tawa ta fito da karfi five
da yadda nayi niyya. Ya toshe kunnuwansa da hannayensa "wai! Zaki cire min dodon kunne ai" na harare shi na sake maimaita "ba ka da gaskiya wallahi" amma sai stupid zuciya ta take cigaba da
jaddamin kyawun da yayi mata duk kuwa
da yadda take bugawa da karfi cike da
tsoron sa as a man,
Sai ma ga ya dauko wata leda karama ya
shimfida a tsakanin mu sannan ya dauko
bakar ledar da nake tunanin kazar da ya
ambata ce a ciki ya dora akai ya bude
ledar, wata container ta bayyana transparent, irin wadda ake packaging abinci a fancy eateries. Ya bude
gasashshiyar kaza ta bayyana wadda a
take kamshin ta ya cika motar, ya bude
wasu kananan robobi da suke tare da
robar kazar, daya sauce ce itama da take
tashin kamshi mai dadi dayar kuma yaji ne
irin na masu siyar da suya. Ya sake dauko
robar youghurt ya ajiye tare da dan dube
dube kadan sannan yace "na manta cups.
Zaki iya sha ta bottle din?" Na tabe baki
tare da dauke kaina gefe kamar ban ma
ga kazar ba nace "ni bana sha. Ba zan ci
naman ba ma" yace "ai kuwa da kinyi
missing. Kun iya gashin kaji nake gaya
miki" ya fada yana gyara zaman sa tare da
gutsirar naman da na kara tabbatar da
laushin sa, gashi sai mai ko yake yi a
hannunsa, ya dangwala a cikin sauce din
sannan ya saka a bakinsa ya tauna tare da
lumshe ido "hmmm. Kinji dadin kuwa?"
Na dauke kai kamar ba shi nake kallo ba
tare da tabe baki, "ta yaya zanji dadin
tunda bani nake ci ba?" Ya sake daukan
wata tsokar ya dangwala a cikin yaji ya
kara sakawa a bakin sa yana kallo na yana
murmushi,
Na kara hade rai. "Har abinci na saka aka
yi maka. Amma kaki shiga ciki ballantana
ka ci. Shikenan babu komai" ya hadiye tare da korawa da youghurt din sannan yace "okay let's make a deal. Zaki ci kaza ta ni kuma zan karbi abincin da kika shirya
min, zan tafi da shi gida ko gobe ne sai
inyi warming" na dan kalle shi da alamar
tuhuma. "yau gaba daya alkawari kake yi
kana karyawa. Kar inci kaki karbar abincin" ya miko min hannunsa "mu daura alkawarin to, yadda ba zan iya kuncewa ba" nature hannun nasa tare da hararar
sa '"no touching" sannan na saka hannu
na a cikin naman, dama duk yawu na ya
gama tsinkewa.
Na mika masa hannu "ina nawa youghurt
din?" Ya danyi dube dube yace "sai dai
muyi sharing wannan, na so in taho da
cups da sai mu raba" na dauki robar
amma mai makon in saka bakina akan
inda ya saka din sai na daga ta na tsiyaya
a cikin bakina, saura kadan in kware
saboda kallon da ya bini da shi, irin kallon
kin raina min hankali din nan tare da na
zaki gane kuren ki. Na shaye ina gyaran
murya tare da kunshe dariya ta, yace "ni
ko?" Yana nuna kansa, "wallahi zaki gane
da ni kike" na daga kafada ta ina dariya
kasa kasa cikin tsokana "wa ace ka siyo
daya?" "Zaki sani, I will not forget this" ya
fada yana cigaba da cin kazarsa.
Nima cigaba nayi da ci, dan sosai tayi min
dadi, daga nan kuma sai muka kama hira,
ya sake bani labarin gyaran da za'a yi wa
gidan sa da zamu zauna, na fahimci
fasalin da moons construction company
suka yi proposing yayi masa sosai dan sai
kara yaba tsarin yake yi, sannan ya fada
min already Mama ta bayar da kwangilar
kayan lefe, za'a bawa matar da aka bawa
number ta ta kira ni in gaya mata sizes
tare da sauran bayanai. Ni kuma sai na
bashi labarin dramar da akayi tsakanin
Salima da iyayen mu mata akan walimar
da nace zanyi, na tambaye shi kuma ko
yana ganin zasu yi wani abun da zasu
bukaci inje? Sai ya ce Mama dai kamar ba
zata yi ba "but am not sure about my
aunties, musamman Ummee, kullum
neman uzurin da zai kawo ta Nigeria take
yi" sai kuma ya amince da shawarar inyi
taro na da friends dina kawai dan mufi
bonding sosai, "Friends are very
important in life, sometimes as important
as families" ya danyi shiru sai kuma yace
"as for the rest of the family kuma a
shawarce ranar da zaki tare sai a shirya
musu walima a can gidan, grand walima,
kin san iyaye akwai son zuwa ganin dakin
amarya, sai suje su wuni a can su ga
ko'ina su kuma yi duk abinda suke so.
Kinga shikenan ba zasu ke dawowa daya
bayan daya ganin dakin amarya ba" ya
karashe yana min kallon da bana so.
Na dauke kaina amma kuma naji shawarar
tasa ta kwanta min, amma ban yanke
hukunci ba tunda ina gain ba hurumi na
bane ba sai nace "hakan kuma yayi
ma'ana sosai. Zan bawa Mommy wannan
shawarar inji abinda zata ce" ya gyada kai
"do that. Abinda tace din sai ki gaya min.
Sai inyi wa Mama magana ita ma inta
yarda har suma bangaren su duk sai a
hadu a gidan ranar" sai kuma na dan bata
fuska "kar fa aje a bata min gida" yayi
murmushi "to sarkin tsafta. Akwai
compound da zai dauki kowa ai. Duk cin
abinci sai ayi a waje. Cikin gidan kuma sai
a ajiye masu gyarawa continuously har a
gama"
Na dan yi shiru ina shan youghurt din da
na manta na saka robar akan lips dina, sai
yace "there is another thing kuma da
nake so muyi magana" na dan juyo ina
kallon sa sai yace "what do you think
about zuwa Kura?" Na dan bude ido ina
kallon sa kirjina yana bugawa "Kura?" Na
maimaita cikin mamaki sai ya daga kafada
yace "Kura da kwatarkwashi" na girgiza
kaina. "Ammie tace kar inje" ya sauke
ajjiyar zuciya "haka ne. She was afraid kar
su cutar da ke kamar yadda suka yi niyyar
cutar da ita. But lokaci ya tura da yawa,
zamani ya chanja sosai. I doubt idan
wadancan da suka samu sabani da su
suna da rai har yanzu ko kuma still suna
harboring grudges akan abinda
mahaifinsu yayi shekaru kusan 45 da suka
wuce. And kamar yadda kika ce Daddy ya
gaya miki ranar nan, a ko'ina akwai
mutanen kirki akwai kuma mutanen da
bana kirki ba. A cikin siblings din Ammie
ba zamu rasa na kirkin da zamu jawo jikin
mu ba. Ko da daga nesa nesa ne a fara
zumuncin in mun fahimci hali sannan sai
mu jawo su kusa" na sauke ajjiyar zuciya
ina kallon sa amma bance komai ba, sai
ya cigaba "and about kwatarkwashi, tun
ranar da kika bani labarin iyayen Baba
Hadiza, I thought about it, na san irin
wadannan fulanin mai gari shi yake basu
land su zauna idan sun shigo garin sa,
sannan kuma suna bin the same route ne
a tafiye tafiyen su, so probably ba za'a
rasa descendents dinsu da har yanzu
suke wuce wa ta kwatarkwashi ba, zamu
iya samun record a wajen dagacin garin,
za kuma mu iya bashi cigiyar cewa idan
har sun shigo garin a sanar da mu ko a
basu number waya su kira.
I just want us to do something, I just want
you to have them back in your life. Kinji?"
Na dan goge hawayen da naji ya fara
taruwar min. There is a genuine concern
about yadda yake yi min magana that
touched my heart. Ya cigaba "Please, at
least tell me you will consider it. Ko ba
zaki yi yanzu ba" ya gyada kai da sauri ina
kokarin mayar da hawaye na, ina missing
Ammie sosai and tabbas samun danginta
a kusa da ni zai cike min wani gurbin na
kewarta. "Insha Allah. Zan yi magana da
Daddy akan hakan. Zai ji dadi na sani"
yayi murmushi "ina son Daddy sosai"
nima na dan yi murmushin sai ya fara
tattare containers din da muka ci kazar a
ciki sannan ya dauki wipes ya kama
hannuna ya fara goge min yana kallona,
ban kula shi ba na san neman magana ne
sai na dauki youghurt dina na cigaba da
sha, sai da ya gama ya goge nasa hannun
ya rufe packs din ya mayar cikin ledar tare
da bude kofar ya fita, nima sai na ciri wipe
din na goge yar karamar ledar cin abincin
da ya shinfida duk da ba bashi tayi ba
sannan na nannade ta na mayar inda naga
ya dauko, a lokacin ne na lura da wata
robar youghurt din da take ajiye a kasa.
Ya bude motar ya shigo sai na dago ta ina
hararar sa. Yayi murmushi bai ce komai ba
sai na ce "baka da gaskiya na gaya maka
"yayi yar dariya "ai baki ji nace dama guda
daya na siyo ba ko? So nake in mun
shanye daya sai mu sake shan dayan" na
sake hararar sa tare da mika masa guntun
wanda nake sha na dauke wancan da ba'a
bude ba. Ya ajiye yana gyara fuskar sa
kamar wanda zai yi wata serious magana
yace "akwai sauran abu daya kuma mai
muhimmanci da nake so muyi magana
akai" na nutsu nima ina mayar da hankali
na sosai a kansa, sai ya kama hannuna na
ya rike yana kallon cikin ido na yace "
want to confess something. Kawai dai
kuma bansan me zan ce miki ba. I don't
know how to tell you, ina jin nauyin ki
sosaj" naji gaba na ya fara faduwa,
menene wannan zai gaya min haka. Na
tattaro courage dina nace "menene?" Ya
danyi shiru yana kallon fuskata sannan
yace "youghurt din da muka sha, na
mayar da na baki ciki".
Na zaro ido yayin da ya kyalkyale da
dariya, na dan dake shi a kafada "kai
kazami ne Allah kuwa, ba zan kara cin
abinci da kai ba" dariya sosai ya kama yi,
irin dariyar da ban taba ganin yana yi ba,
nima dariyar na fara taya shi totally
forgetting the tension between us, "Allah
zaka gane kuren ka" na fada cikin dariya,
a cikin dariyar ne kuma na jini a jikin sa, na
sa jawo ni yayi amma ban ji sanda ya jawo
nin ba. Nan take dariya ta ta tsaya, bugun
zuciya ta ya dawo da karfin da yafi na
dazu, na fara kokawar raba jiki na da nasa
ta hanyar saka hannu na daya in tura shi
sai ya rike hannun a cikin nasa hannun
guda daya, dayan hannun kuma ya kara
riko waist dina tare da hade jikin mu sosai.
Idanun sa akan fuskata yana bin kowanne
feature na fuskar da kallo kamar me
neman haddace komai. Babu sauran
dariyar a fuskarsa.
"Ka cika ni" na fada murya can kasa, bana
jin dadin kallon da yake yi min sam, na
sauke ido na kasa a kokari na na daina
kallon cikin idonsa "anki din" ya fada yana
wasa da yatsun hannun sa a cikin nawa,
nayi kokarin kwache hannun sai ya sake
rike shi. "Ka sakar min hannu na" na fada
ina jin abinda yake min a hannu har cikin
tafin kafa ta, "na karfi ne, in kina da karfi
ki kwata" ban ce komai ba kuma bana jin
ko nayi magana muryar zata fito saboda
yadda numfashi na yake yin sama a
lokacin da hannunsa ya bar yatsun
hannuna ya biyo hannun har zuwa
wuyana.
"You promised" na fada a hankali, "I lied"
ya bani amsa a can kasan makogwaronsa
a lokacin da hannunsa ya karaso fuskata,
na dago idona saboda jin iska mai dumi
da nayi a fuskata, idanuna suka sauka a
cikin nasa, hancinsa a saman nawa muna
shakar numfashin juna, kamar yadda yake
futar da numfashi mai zafi na tabbatar
nima haka ne, na rufe idona dan ba zan
iya daukan abin da nake gani a cikin
idonsa ba. And then he kissed me…….
A tsorace na kwace jiki na daga nasa
bayan mintunan da ban san adadin su ba.
Ban san ya akayi ba sai gani na nayi na
tsallaka seat din gaban motar na kuma
dunkule a waje daya jikina yana karkarwa,
acn motar tana sauka a naked fatar
bayana da ba zan iya tuna sanda zip din
rigar ya cire ba ballantana yadda akayi
rigar ta kusa barin jikina completely. Sai
da nayi ta mayar da dogayen numfashi
kafin in dan samu in daidaita tunani na
sannan na fara kokawar yadda zan mayar
da riga ta, sai dai zip din yaki cooperating,
yaki jera kansa ballantana in zuge shi, ko
kuma karkarwar da jiki na yake yi ne? Na
san yadda akayi tafiyar ta fara, amma ban
san yadda akayi tafiyar ta yi nisa sosai ba
sai da naji lips dinsa a inda ban taba tunanin zasuje a yau ba sannan na dawo hayyacina.
Hannuna har ya kage saboda kokarin
gyara rigar amma taki gyaruwa, kamar
zanyi kuka. Na kuma kasa daga idona
ballantana in kalle shi. Ina dai jin sa jera
numfashi a baya, maybe trying to calm
himself down kamar ni. Ni bana jin ma zan
iya kallon sa a yau dai kam. Naji muryarsa
kamar wanda yake magana daga can
nesa "Hey! Tsaya in gyara miki kar kiji wa
kanki ciwo" na kara takurewa a kasan
kujerar tare da rufe fuskata da hannayena
biyu "ya Rabbi" na fada a hankali. Naji
motsinsa ya taso sai na kara makurewa
kamar zan shige karkashin kujerar "ki
tsaya, rigar zan gyara miki" ya fada still
not sounding like himself. Na kife fuskarsa
a kan seat din kujerar ban kalle shi ba
kuma banyi magana ba. Naji ya sake
sauke wata ajjiyar zuciyar sannan ya bude
kofar motar ya fita sai kuma naji ya bude
seat din driver ya shiga sannan naji
hannun sa a baya na ya mayar min da bra
strap, duk da naji bai saka dai dai ba banyi
complain ba sai kuma ya hada zip din
rigar ya zuge. Ban ce komai ba sai na
dago hannuna daya na mika masa, yar
dariya yayi kadan sannan naji ya saka min
dankwalina a cikin hannun, ban kalle shi
ba na daura, daurin da na tabbatar bashi
da maraba dana tababbu, sai na kuma
mika masa hannu na sai ya saka min mayafina, na lulluba a jikina ba tare da na kalli mayafin ba ballantana in ga ko na saka dai dai ko akasin haka, ina jin sa yana dariya kasa kasa amma a raina nayi
kwafa ban ce komai ba dan ba zan iya
cewa komai ba. Na bude kofar motar ba
tare da nace komai ko na kalle shi ba na
fita, sai da naji kafata ta taka duwatsu a
kasa sannan na koma na zauna akan
kujerar tare da cewa "auch!" Yayi saurin
cewa "menene?" Ban amsa ba sai na
kuma mika masa hannu na, bai gane
abinda nake nema ba sai da ya kuna fitila
ya duba baya sannan ya miko min takalma
na yana dariya. Nayi kwafa a fili na saka
takalman sannan na karasa fita na bar
masa kofa a bude.
Na jishi ya fito daga motar ya biyo bayana
yana dariya kasa kasa, ya danyi kokarin
gyara min mayafina sannan yace "ga
wayarki, ko kin barmin" na mika masa
hannu bance komai ba sai ya saka min ita
a cikin hanun, daga nan na kara sauri har
na je gate, ya bude min kofa na shiga sai
ya rike mayafina "Please look at me
mana" na girgiza masa kai da sauri sai ya
saki mayafin yace cikin tsokana "sai na
sawo gobe" ban ce masa komai ba na
kara sauri zuwa ciki, sai da na shiga
sannan naji motsin rufe kofar gate.
Shirun da naji gidan yayi ya saka na
fahimci kowa a gidan yayi bacci, na sauke
ajjiyar zuciya cikin jin dadin hakan dan
gani nake yi kamar duk wanda ya kalle ni
zai fahimci abinda ya faru, musamman in
aka ga lips dina. Na saka hannu ina
goggoge su ina jin yadda suka zama
puffy, Allah kadai ya san lokacin da na
bata a cikin motar nan tare da mutumin
nan. Nayi kwafa. Da ni yake maganar. Har
da wani cewa sai ya dawo gobe ko? Zai
ga gobe ganin idon sa. Har lokacin jiki na
rawa yake yi. Na zauna akan kujera trying
to get the scene and the feelings out of
my head. Karar waya ta ya saka na dan
zabura kadan. Na duba naga sunan sa, he
must be kidding me, me zai ce min kuma?
Sai kuma nayi tunanin o wani abun na
manta mai muhimmanci, a dauka na
saka a kunne na ban ce komai ba sai yace
"abinci na.
Ki kawo min abinci na" bance komai ba na
katse kiran, Ni ina zanga abinci a gidan
nan yanzu? Amma duk da haka sai na
duba kitchen, cikin ikon Allah na samu
warmers kanana a jere a gefe, na bude na
tabbatar abincin da Esther ta hada mishi
ne, na dauko basket na jera na bude fridge
naga drink din da nake tunanin shi ta hada
wa sannan na rufe basket din.
Sai dai ni nasan ba zan iya komawa waje
gurin sa ba. Na hau sama dakina na tarar
da Salima tana kallo a tv tana ta kyalkyala
dariya. Ina shiga ta dago kai tana kallo na
sai kuma ta kwashe da dariya, "wannan
daurin fa?" Na taba kaina sannan nace
cikin muryar da naji kamar ba tawa ba
"yanzu dankwalin ya kunce a kitchen, ban
ma san ya daura shi ba". Cikin tsokana
tace "ai na dauka sai dai a aika miki da
kayan ki" ban kula ta ba na cire mayafin
da dankwalin sai kuma nayi sauri na duba
a madubi dan bana son ta ga wani abu
kuma again, casually nace mata "dan
Allah Salima ko zaki kai masa abinci waje?
Yana mota" ta mike zaune "au bai ci
abincin ba? Esther tayi ta sintiri tana
neman ki ai, na dauka an kai masa" nace
"bai ci ba. Wai tafiya zai yi da shi. In na
fita kuma tsayar da ni zai kuma yi. Dan
Allah ki kai masa. Gashi can a kitchen" ta
sauka daga kan gadon ta fita tana
maganar da banji abinda tace ba.
Tana fita na zauna akan kujera tare da
dafe kaina. Wannan aure anya kuwa?
Wannan mutum ya zanyi da shi? Ina son
sa sosai amma Allah ya sani ina matukar
tsoron abinda aure ya kunsa, abinda
kuma na tabbatar ba zai iya daga min kafa
akai ba. Da dai kuma ace irin na yau ne
kadai za'a ke yi ana bari da da sauki sauki.
Na rufe idona tare da kwanciya akan
kujerar ina kokarin daidaita tunani na. A
haka Salima ta dawo ta same ni bakin ta
har kunne, ta daga min rafar sabbin kudi
da aka bata tana rawa, sai kuma ta zauna
tare da cewa "an bani amanar ki. Ance in
kula da ke sosaj" na dan yi mata murmushi
kadan. Ta sake cewa "I thought
ba zai sakar min fuska ba saboda Yaya
Mukhtar. Amma yayi min fara'a kuma har
ya bani kudi " na mike nace mata "ke ba
Mukhtar ba ce ba kuma Mukhtar ba ke
bane ba" daga haka na shiga toilet dan
bana son ta kara ambatar sunan Mukhtar
especially not now da nake cikin tunanin
yadda zan iya fuskantar aure na saboda
abinda yayi min.
A toilet na kimtsa jiki na nayi alwala na fito
zan yi sallah sai take gaya min twins ma
sun shigo nema na. Na jinjina kai kawai,
tunda akayi daurin auren nan bamu yi
magana da su ba kuma a zuciya ta ina
son muyi magana dan mu samu fahimtar
juna.
Sai da na idar da sallar sannan na sake
fita na duba Daddy na tabbatar yana baccinsa peacefully sannan a duba Mommy ita kuma
na ga bata yi bacci ba tana kallo kuma tana
waya, na fahimci da Safina suke wayar sai
nayi mata sai da safe na koma dakina nayi shirin bacci. Ina jin waya ta tana kara da sound din
Muhammad sai na dauka sannan na saka
ta a silence, haka yayi ta kira na, ina kallon
sunan na sa ina murmushi amma ban
dauka ba. Sai kuma ya turo min message
"Please come online" sai da na ja aji na
kadan sannan na hau.
"Yanzu ba zakiyi min magana ba? So nake
fa kawai inji muryar ki. Dan Allah ki dan yi
min magana mana ko ba kya so inyi bacci
yau"
"Uhmm"
"Yanzu anan ma ba zaki yi min magana
ba? Wai laifin me nayi ne?"
"Karya alkawari"
"Dama sanda nayi alkawarin ba har
zuciyata ba ne ba. Allah ma ya san ba har
zuciyata bane ba. Though ban dauka
cewa I will take it that far ba. But you are
very beautiful and sweet. I lost control"
Na danyi murmushi bance komai ba.
Ya sake turo wani
"Can we meet tomorrow? Maybe at the
Oasis?"
“Nooo”
“😂. I promise magana kadai zamuyi. I
will not touch you"
"Goodnight Baby"
"Good night. And I love you"
"I love you too"
Na tura masa tare da lumshe ido ina jin
sonsa tare da wani sabon feeling daban
da ban san shi ba, mai hade da tsoro suna
gauraye zuciyata.
Washegari nayi maganar walimar da
Gidado ya bani shawara tare da Mommy,
ta amince cewa hakan din dai dai ne,
amma direct ta gaya min cewa babu
wanda zata gayyata daga side din ta
except Hajiya da take dole. Na fahimci
haka kuma banji komai a raina ba dan
nasan it's for the best. Sai kuma naji na
sake jin kewar dan gin Ammie. Hakan ya
saka ina zuwa gurin Daddy na gaya masa
maganar da muka yi da Muhammad jiya.
Sai naga yaji dadin maganar sosai
musamman maganar dangin Baba
Hadiza. "Yaron nan yana da hankali sosai.
Amma a shawarce ku bari sai bayan bikin
ku in hankali ya kwanta sai kuje".
Sai na sake yi masa maganar Mustapha
"Daddy yaushe zaka dawo da
Mustapha?" Ya dan kalle ni yace "sai kin
bar gidan. Zai dawo, amma sai kin tafi
gidan mijinki".
Da yamma Aunty Hajjo ta dawo gidan
kamar yadda tayi alkawari. A tare da ita
akwai another guest. A little human being.
Ta miko min shi "rike min wannan yaron
Safiyya ki huta. Ya zama kato duk ya
gajiyar da ni" na mika hannu zan karbe shi
sai ya makale kafada yana kara rike
rigarta. Na daga kai na kalle ta sai tayi
murmushi "kyuiya fa yake yi dama. But in
kika dauke shi zai hakura" na sake mika
hannu na dauke shi ina jin yadda yayi
nauyi. Yayi ta bin fuskata da kallo sai
kuma ya turo baki yana jera ajiyar zuciya.
Ya kumbura fam kamar zai fashe. Aunty
Hajjo tayi dariya "in kina da sweet je ki
bashi. Amma ba me zaki sosai ba" Salima
da ake yi a gabanta ta zo ta shafa kansa
tace "cute boy" ai kuwa a take ya fashe,
ya kwarara hun da ya cika gidan
gabakidaya, sai ga mutane sun fara
fitowa, Mommy ta sauko daga sama sai
na mika mata shi kamar zanyi kuka, ta
karba ta jefa shi sama ta chafe sai ya kara
sound din kukan. Sai ga Hassan nan ya
shigo shima ya karbe shi "Mommy dan
waye wannan?" Mommy ta kalli Aunty
Hajjo tace "dan Hajjo ne" Hassan yayi
murmushi '"ban taba ganin baby a gidan
nan ba".
Farko da Hassan ya karbe shi sai yayi
shiru, Aunty Hajjo tace ya dauka Abdul
ne, amma kuma sai yake ta kokarin leka
fuskar Hassan din, suna hada ido kuwa ya
sake wage baki da kukan da yafi na baya
karfi. Hussain shima yazo ya gwada tasa
basirar amma Junior yaki, sai ga Daddy ya
aiko wai waye ya cika masa gida da
hayaniya? A kai masa shi. Na sunkuyar da
kaina kasa dan na san ya fahimci waye,
tunda Aunty Hajjo tace tare suke da uncle
Sufyan kuma yana wajen Daddy din, sai
Hassan ya dauke shi ya tafi da shi can. Sai
kuma muka ji shiru.
[07/01, 10:46 pm] +234 906 816 1960: Da yamma Aunty Hajjo ta dawo gidan

Daga nan Aunty Hajjo suka cigaba da
maganganun su da Mommy. Ranar lissafin
siyayyar kayan daki suka fara, Mommy
tayi min maganar kaya na na gidan
Mukhtar sai na gaya mata abinda nayi da
su, ta tsaya kawai tana kallona sai kuma ta
girgiza kanta suka cigaba da maganar su.
Har Mommy ta dauko takarda zata fara
list na kayan da za'a siya sai Aunty Hajjo
ta bada shawarar a bada kwangila kawai,
a samu kamfanin da suke interior design a
basu kwangilar komai, za'a hada ni da su
yadda zan ke gaya musu duk abinda nake
so su kuma suna taimaka min wajen zabe
da kuma siyowa "in muka yi haka mun
huta, kuma tunda aikin sune hardly su
manta wani abu".
Mommy ta amince da shawarar ta.
Ni dai na barsu da wannan na koma sama
zanyi sallar azahar. Ban sauko ba har
akayi la'asar nayi na shiga toilet nayi
wanka ina fitowa sai naga Junior shi kadai
a zaune a kan gado na. Na sam Aunty
Hajjo ce ta kawo min shi. Na durkusa a
gaban gadon ina kallon sa yanata wasa da
toy dinsa, sai kuma ya juyo yana kare kin
kallo, a karshe yay deciding cewa bai
sanni ba sai ya turo baki ya fara ajjiyar
zuciya idonsa ya ciko da hawaye.
A hankali nace "hey there! Remember
me?" Ya cigaba da kallo na nima sai na
samu damar are masa kallo. Yayi fari
sosai yayi kiba kamar zai fashe, fatarsa
kamar zaka taba jini ya fito, komai a
jikinsa yana nuni da yadda yake cikin
kwanciyar hankali. Idonsa yana nan irin na
ubansa amma sauran features din sa ba
zaka kalla direct kace nawa bane ba sai
dai in kallon kurilla zaka yi masa.
Sai na tuna da chocolate din da Abdul ya
kawo min ranar nan naki sha na dauka shi
za'a aura min, na bude inda na ajiye su na
dauko na nuna masa ya miko min hannu
da sauri tare da yin gwarancin da ban
gane ba "acici, har yanzu kana nan da cin
ka ashe Adam" na karasa na bude masa
na mika masa, garin karba ya hantsula
baya ya kwanta, sai na jashi na tare shi da
pillow, sai ya fasa kukan ya kama shan
sweet.
Mun jima tare ina ta vi masa hira shi kuma
yana ta shan sweets dinsa, har labarin
aure na sai da na bashi da kuma yadda
nake son angon, ya bata jikinsa gabaki
daya ya kuma bata bedsheet din, sannan
daga baya ya rarrafo jikina nima ya bata ni
da chocolate din.
Aunty Hajjo ta shigo tan kallon mu, yana
ganin ta ya fara mika mata hannu yana
murna, ya rike haba "oh Allah, haka dama
ake renon Safiyya" nayi murmushi bance
komai ba. Ta mika hannu ta dauke shi tayi
toilet da shi da sauri tana cewa "ni dai ba
zaka bata min jiki ba. A toilet naji su suna
ta babbaka dariya sannan suka fito ta
gyara masa jikinsa tas. Na mika masa
hannu sai ya makale, tayi dariya,
"sweet
din ki ta kare aj" nayi hanyar fita tana
cewa "mu zamu tafi. Ba lallai mu dawo
gobe ba sai dai idan da akawai wani abu
mayi waya" har ta kai bakin kofa na ce
mata "Aunty Hajjo" ta juyo tana kallona
nace mata
"thank you" ina kallon Junior
da yake ta kara shigewa jikinta yana
tunanin daukan sa zanyi. Tayi murmushi
tana shafa kansa tace
"no. Thank you.
Mune da godiya. He is nothing but a
blessing to us".
Bayan sun fita sai na bisu a baya, ina jin
kamar in ie ince ta bani dana amma na
san hakan shine dai dai a gare shi. Ina
tsaye akan barandar naga Abdul ya
shigo, daga inda nake na hango yadda
Junior yake murna da gain sa, shima
cikin murnar ya karbe shi tare da kissing
Cheeks dinsa sannan suka fita.
Salima kamshin take yi.
An kawo lefe. Maza ne suka kawo kamar
yadda Daddy ya bukata, muma anan
mazan ne suka karba anan falon Daddy,
suka kuma saka tariyar ta kasance sati
daya bayan kawo lefen. Sai da suka yafi
sannan aka shigo dasu cikin gida mata
suka gani. Ni kam na san kusan komai da
yake ciki dan da yawa daga cikin kayan ni
na zaba tare da taimakon wadda suka
bawa kwangilar. Komai na lefen yayi min
kamar yadda komai yayi min a cikin kayan
da designers din gidana suke siya. Duk da
ba'a gama aikin gidan ba amma na basu
plans din gidan sun san yawn dakunan
da kuma sizes din su da komai, dan haka
ta haka suke siyayyar su.
A lokacin problems dina guda biyu ne
kawai. Na farko jikin Daddy da yake kara
lalacewa kullum, gashi kuma wai zan tafi
in barshi a cikin wannan halin. Sai na bivu
angon nawa da yake kara rikice min
kullum. Har sai da nace ina ma ba'a daura
auren nan ba an bari sai an gama shirin
tukunna? Zuwa lokacin har cikin raina
tsoron kebewa da shi nake vi. Hakan
kuma ya kara min tsoron abinda zai
kasance a cikin auren namu. Ko ya na
tuno abin sai toro ya kamani. Har tashi
nake yi cikin dare in roki Allah ya yaye min
tsoron mijina da na fara.
Ba wai shi nake tsoro ba, ina son sa sosai
kuma na yarda har cikin raina ba zai cutar
da ni ba, amma ko yaya nay imagining
kasancewa da shi a matsavin mata da mili
sai na tuna ranar nan, ranar da tafi
kowacce rana baki a rayuwata. Sai na
tuno pain din, sai na tuno darkness din.
Sai kuma na tuno fear din. And it kept me
up at night,
Maman Maama✍🏻
[07/01, 10:46 pm] +234 906 816 1960: ❤️🩹Safiyya❤️🩹
Episode Sixty Five: The Wedding
Tunda satin bikin ya shigo abubuwa suka
kara rikice min. Duk da dai aunty Hajjo
tana taimaka min da abubuwa sosai dan
Mommy ta zama very moody a cikin
kwanakin nan, ta daina fadan ta ma daina
magana sosai and it broke my heart to
see her like that amma sai in taushi kaina
da gayawa kaina cewa bani na saka ta a
cikin damuwa ba. Ina dai iyakacin kokarin
ganin nayi involving dinta a komai ko da
kuwa ta hanyar bata update ne akan duk
abinda ake ciki, in ta bada shawara kuma
ina kokarin gain nabi dan in faranta mata
ko yaya ne. Amma na san zuciyar ta tana
wajen yayan ta.
Bata taba yi min maganar Safina ba nima
ban taba yi mata ba, haka Muhammad,
bai taba yi min maganar ta ba nima ban
tambaye shi ya suke ciki ba,
At a point da abubuwa suka yi min yawa
sai da na gayawa Muhammad ko za'a kara
sati daya ne? Dan har lokacin masu gini
ba su gama finishing ba ga masu saka
kaya suna jira, ai kuwa a take yaje ya saka
Ya Amen a gaba ya hana shi shakar
numfashi mai kyau har sai da suka gama
komai in two days sannan ya bar shi ya
huta. Sai masu kaya suka fara aikin su,
saboda kurewar lokaci haka suka yi aikin
nan day and night, na tattara twins na
tura su gidan dan su tabbatar anyi komai
yadda ya kamata. Da suna can din ma ban
kyale su ba ko da yaushe muna waya ina
jin abubuwan da aka kawo da kuma a inda
aka saka komai, sai kuma su yi min video
su turo min in gani dan in tabbatar da
cewa abinda na ce ayi ne kuma an saka
shi a inda ya dace. Kuma interior
designers din sunyi kokari sosai gaskiya.
Few things ne naga an samu kuskure
akai dan haka banyi dragging ba sai kawai
na barsu tunda dan Adam tara yake bai
cika goma ba.
Aunty Hajjo ma kullum sai taje gidan taga
progress din aikin, in da gyara tayi musu,
at a point uncle Ahmad ma yaje ya ga
komai kuma ya bada nasa shawarwarin.
Sosai kuma nake jin dadin yadda komai
yake turning out, sosai kuma nake kara
investing in making my home as luxurious
as I can dan a raina ina ganin nan ne gidan da zanyi mafi yawa daga cikin
rayuwata a ciki, gidan da zan haifa kuma
in reni yayana. Gidan da zan kira gida na.
In three days suma suka gama saka komai
da jera komai sannan aka gyara gidan tas
aka rufe.
Ranar da aka gam aikin, ranar Alhamis
kenan, twins suka dawo gida da rana suka
tarar da ni tare da Muhammad a harabar
gidan mu amma daga side muna zaune
akan kujeru sai suka karaso suka gaishe
da Muhammad sannan suka gaya mana
cewa wai sun kama daki a gidan, yanzu
ma kayan su suka zo dauka. Muka yi
dariya Muhammad ya ce "to Allah ya sa
ba dakin Haidar kuka kama ba dan tun
dadewa yace shima ya kama daki"
Hassan yace "ko dakin sane tunda mu
biyu ne shi kuma shi kadai dole ya hakura
ya bar mana, in ba haka ba kuma sai a
gwada karfi aga wanda zai kayar da wani"
aka sake dariya suka shige, sai nabi bayan
su da kallo ina jin dadin yadda suka yiwa
Muhammad magana, they have been
quite about the whole issue kuma na san
an saka su a tsakiya ne, though ni ban
taba zama na tambaye su ra'ayin su ba
kawai ina involving dinsu ne a cikin
abubuwa. Bayan sun wuce Muhammad ya yi clicking
fingers dinsa a kusa da fuskata, wannan
ya dawo da ni hayyacina na juyo ina kallon
sa sai yace "ina kika tafi?" Nayi murmushi
"ina nan" yace "a'a, kin bi twins dai kun
shige gida kun barni anan" na sake
murmushi kawai. Tunda satin ya kama na
koma shiru sosai. Magana ma kadan
kadan nake yin ta dan abubuwa ne da
yawa a raina. Ina son muhammad ina son
auren sa amma kuma ina tsoron auren
sosai, kuma bana son rabuwa da Daddy.
Sannan kuma ga missing Ammie da nake
kara yi sosai a kwanakin nan, duk da cewa
uwa uku nake da ita a yanzu amma babu
wanda zai iya replacing gurbin uwa a
zuciyar yarta.
Muhammad tun yana tsokana ta yanzu
har ya bari, tunda in ya tsokane ni ma ba
kula shi nake yi ba. Sai dai ya shigo mu
zauna yayi ta min hira ina amsa masa
sama sama,
An gama tsara komai na yadda bikin zai
kasance, kamar yadda Daddy ya bukata
ya kuma cigaba da insisting, baya son duk
wani abu da zai jawo attention din
mutane, ina ganin kuma hakan da yayi ta fada ne ya saka suma gidan su
Muhammad ba su shirya wani shagali
babba ba. Ya dai ce min zasu yi wuni a
gidan kakannin sa ranar friday. Ni ma
kuma a ranar Friday din ne zanyi taron da
na shiryawa friends dina "Fiyya's Sourie"
na kira taron, Muhammad ne ya kama
mana inda zamu yi taron ya kuma biya
komai, Mufida kuma ta aiko min da
gudummawar sovenniers masu tsada da
za'a raba wa mutane, da ma na karbi
number dinta a hannun Muhammad tun a
week to taron muni magana kuma na
aika mata da cards guda ashirin nace ita
da cousins din su mata. Salima ma tayi
wadansu sovenniers din.
Daga taro na kuma sai walima da za'a yi
ranar Saturday, ranar da za'a kai ni gidan
Muhammad. Ita kuma walimar a gidan na
wa za'a yi ta a harabar gidan, both family
na da na Muhammad zasu yi attending a
lokacin ne kuma danginsa zasu ganni,
kowa kuma zai samu damar ganin gidan
amarya.
Muhammad ne ya kawo shawarar kuma
aka karba, amma kullum in muna maganar
sai nayi masa mitar zai saka a bata min
gida, Dan sosai nake ji da gidan nan nawa shima kuma ya sani. Ya kance "ni kam in
aka bata gidan nan ina jin ba za'a barni in
vi bacci ba"
Na dago kai na sake kallon sa dan jin da
nayi a jikina cewa kallona yake tayi, muna
hada ido na sake mayar da kaina kasa ina
yin murmushi sai yace "Please Piya. Ki
rufa min asiri ki dawo dai dai. Ni ban saba
da wannan ba gaskiya" nace "zaka saba
da ita ne ai a hankali" ya girgiza kai "no.
Ba zan saba da ita ba. Zan dai dawo da
Piya ta ko da karfi ne. Allah dai ya kaimu
jibi" a haka ya gaji da shiru shiru na ya yi
min sallama ya tafi amma ace zai sake
dawowa da dare ya kawo min sako.
Na tashi na koma gida. Already gidan mu
ya fara cika da yan'uwan mu da suka fara
zuwa daga Kano. Cousin din su Daddy da
muke kira da gwoggo Hauwa tazo tare da
yayanta uku da kuma surikarta. Matan
kanin baban su Daddy ma sunzo su biyu.
Kanwar babarsa ma wadda take kamar
kaka a wajen mu a yanzu ita ma haka ta
matsa sai da aka taho da ita tare da
matan yayan ta su uku tunda ita yayan ta
duk maza ne, Sauran yan'uwa kuma sai
washegari muke saka ran zuwan su,
Ina shiga tun a falo suka dasa tsokana ta, "'Amarya wanna sheki haka da kike yi
duk na amarcin ne?" "Amma kuma ta
rame fa" "tsoron auren kike ji?" "To ko dai
a fasa ne?" Na juya ya zabga wa wadda ta
fadi haka harara, abokiyar wasan mu ce
da ma, tayi dariya tare da fadawa goggo
Hauwa da take zaune a gefe "harara ta
tayi, wallahi goggo harara ta tayi" na
sunkuyar da kai kamar ba ni nayi ba na
zauna a gefen gwoggo nace "sharri zaki
yi min? Ai Allah yana kallo kuma zai saka
min" Hasina tace "ni ma na ga hararar fa.
Kuma yanzu ma daga gurin angon take, ai
na hango su sanda naje ba da sako waje"
goggo Hauwa tace "kika je bada sako ko
kika je tsegumi?" Ta juyo tana kallona
tace "wai so take ta ga wanda yafi
Mukhtar da har kika rabu da Mukhtar kika
aure shi" Salima da take kwance a gefe ta
tashi tace "ai kam dai in kyau ne yafi Yaya,
kuma yana da kirki sosai, ga kudi, baku ga
motar da yake hawa ba" Hasina ta saki
baki tace "lahh ka ga yarinya mai gudun
dangi? Nawa ya baki?" Suka sake yin
dariya sai gwoggo tace "ni kam ba zance
nafi son sa akan Mukhtar da yake da na
ba. Amma ina musu fatan alkhairi. Allah ya
sa albarka a gidan auren su ya sa mutu ka
raba" a hankali nace "Amen" Hasina ta
sake cewa "aah gwoggo wallahi Ameen
ta ce, ba zaki bari mu mu amsa ba?" Haka muka cigaba da zama a tare muna
ta hira, naji suna ta tambaya akan Safina
wai basu ganta ba ko sai gobe zata
shigo? Su a gain su tunda a garin take
aure ai ya kamata a ganta actively a cikin
shire shiryen bikin ba wai sai ranar taron
zata zo ba. A lokacin na kara fahimtar
cewa ba su san waye na aura ba kuma
bana jin ko sun ganshi zasu gane shi in
dai ba fada musu akayi ba. Watakila zasu
sani nan gaba. Watakila kuma akasin
haka.
Wata kila idan suka sani zasu san
complete labarin kuma su goyi bayana,
watakila kuma ba zasu fahimta ba zasu
zage ni. But in whatever case, I don't
care.
Anan muka ci abincin dare tare, wadanda
basa kusa ma duk suka dawo falon aka
hadu aka ci abincin tare, Esther wadda
already ta hada kayanta kamar ita za'a
yiwa auren ta na ta hidima da mu tare da
sababbin yan aikin da aka kawo su uku,
Bayan mun gana cin abincin na kira
Salima da Hasina da Hafsat muka tafi
dakina nace su taya ni hada kayana, Ko
kuma ince su hada min kayana, Dan zama
nayi kawai ina kallon su suna hadawa ina jin babu dadi a raina, dan lokacin auren
Mukhtar babu abinda na dauka a cikin
kayana dan ban ma yi tunanin zan yi
dadewar da nayi a gidan sa ba. Kayan
gurin Ammie gabakidaya na dauka dan ba
zan iya bayar da ko daya daga ciki ba.
Kayana kuma na dauki wadansu da nake
so sauran kuma gabaki daya nace
bayarwa zanyi. Ai kuwa su da suke gurin
su suka fara zaba, nace "idan kuka dauki
da yawa to babu ku a wadancan kayan"
Hafsat tace "wadanne kayan?" Nace "ba
zan fada ba, amma in dai kuka dauka da
yawa babu ku a wadancan" sai suka
rarrage, daga nan nace su fifftar su raba
wa dangi dan sun fi ni sanin dangin.
Ai kuwa haka suka sha rabo, gida gida,
duk wadda kaya na zasu iya yi mata sai da
ta samu. Sai na bar su suna rabon kayan
na tafi gurin Mommy na gaya mata kudiri
na "Mommy kayan can na lefe da aka
kawo daga gidan uncle Ahmad, ki rabar
wa da mutane, duk yan'uwa a raba a
bawa kowa, komai da komai, har
akwatunan" ta tsaya tana kallona sai na
daga kafada nace "babu abinda zanyi da
su Mommy, ga wannan lefen da aka kawo,
ga dinkunan da nayi, ga kuma kayan da
already nake da su". Ta gyada kai tace "shikenan, za'a bayar", Itama haka ta
zauna ta rabar da kayan tas, dangin uwa
da dangin baban Daddy kowa sai da ya
samu, ma'aikatan gidan mu both Kano da
Abuja, hatta masu gadi da drivers sai da
Mommy ta basu wani abu a ciki. Amma
bata bayar da kayan kwalliyar ba sai yace
in tafi da su gidan Muhammad saboda
baki yan uwansa in sun zo. Na amince da
abinda tace, sai ta hada da kayan
kwalliyar da kayan lefen da aka kawo daga
gidan su Muhammad da kuma kayana da
na hada na gida wadanda zan tafi da su ta
bawa su Salima Hassan ya kai su suka kai
min gidan Muhammad.
Ni dai tunda muka yi maganar kaya da
Mommy ban kuma bin ta kan su ba, sai
dai duk wanda yazo yayi min godiya sai
inyi masa murmushi kawai. Da dare
Muhammad ya dawo kamar yadda yace
zai dawo. Ina tare da Daddy ya kira ni
yace yazo yana waje a mota. Na dan j
faduwar gaba amma na danne na saka
hijab dina na fita. A motar na tarar da shi
a zaune a seat din driver sai na zagaya na
zauna a gefen sa, na gaishe shi yayi shiru
bai amsa ba sai na dago kai muka hada
ido na sake mayar da kaina kasa, ya kira
sunana "Safiyya" na dago kai da sauri dan
ba zan iya tuna ranar da ya kira sunana
haka ba. Sai ya juyo ya kama hannayena duk biyun ya rike "look at me" na sake
dago kai muna kallon juna "me yake
damun ki?" Na dan kirkiri murmushi "ni
kuma? Nothing fa. Kawai abubuwa ne dai
suka dan yi min yawa" ya girgiza kai "ban
yarda ba. Ba zaki fada min ba?" Na sake
mayar da ido na kasa ina jin kamar zanyi
kuka.
"Ba kya son rabuwa da Daddy? Shine
damuwar ki" nayi saurin gyada masa kai
tunda hakan yana cikin damuwata. Yayi
ajiyar zuciya "ba zaki rabu da Daddy ba
kinji? Insha Allah kullum zamu ke zuwa
muna gaishe shi. Nayi miki wannan
alkawarin. Ki saki ranki ki daina damuwa
kinji?" Na sake gyada masa kai sai yace
'to kiyi min hira. I really miss the sound of
your voice " na danyi murmushi nace "to
me zance? Dazu ma ba muni magana
ba" yace "nayi magana dai. Ni kadai nayi
magana ta dazun ma. Kuma na san gobe
ba lallai in samu ganin ki ba. Ko inzo in kai
ku gurin gyaran gashin?" Na girgiza kai
"muna da yawa ai, ba zaka ji dadin shiga
cikin mu ba. Hassan sai ya kaimu ko mu
dauki driver" ya dan yi murmushi "ko dai
kina kishin kar a gane miki miji?" Na
harare shi tare da kwace hannuna in
kishin nake yi ma ai babu laifi
Miji na mai kyau ne kuma ina son sa" yaji
dadi sosai sai ya saka dan yatsa ya dago
haba ta yana kallon cikin ido na for some
seconds sannan yace "kina da kyau sosai
Piya. Ina son ki sosai",. Na danyi murmushi
sai yace "I am glad ba za'a yi taron da
maza ba, yadda kike ta kara kyau din nan
bana so maza su ganki ballantana ace
kinyi kyalliya" na dan yi dariya "ohh and
you are calling me sarkin kishi ko?" Ya
daga kafada "I wasn't complaining ai. Ina
son kishin ki sosai. Yana kara kin
confirming kina so na" nace "to yanzu su
friends din naka babu abinda zaka shirya
musu kenan?" Yace
"kamar kin san da zu
muka gama rigima. Sunce wai ban
gayyace su daurin aure na ba ballantana
in shirya musu reception and I told them
ni ma ba'a gayyaceni daurin auren na wa
ba. Haka suka zauna suka tsuye ni wai
nayi musu karya nace kin mutu" na bude
ido "what! Yaushe kace musu na mutu?"
Yayi dariya "lokacin wancan daurin auren
ne suka dame ni da tambayar ya akayi ba
ke zan aura ba, and su ba su san irin
heartbreak din da nake going through ba
a lokacin, Ni kuma nace musu kin mutu"
dariya nayi sosai sai ya tsaya yana kallona
kawai yana murmushi. Sai kuma naga yayi
sauri ya dauko wata leda a baya ya miko min "Har na kusa mantawa, I bought you
chocolate slurry, irin wadda kike so" na
dan bude ido kadan sannan na bude ledar
na dauko dan karamin cup din ina kallon
sa sannan na kalli Muhammad "a hana ni
sha fa, kai fa kace min in ban daina sha ba
zan zama katuwa" ya dan daga kafada
"yau dai kadai. Daga yau ba zaki kara sha
ba" na bude cup din na dauko dan
karamin spoon din da yake makale a jikin
cup din na diba na saka a bakina ina jin
dadin narkakkiyar chocolate din da aka
chakuda da madara kuma ba'a saka sugar
ba, na kwantar da kaina a jikin motar tare
da lumshe ido na memories din rayuwata
da Muhammad yana dawomin kaina. Na
bude ido naga idon sa yana kaina, na sake
diba da spoon din na kuma sha sai yace
"babu tavi ko?" Ban ce komai ba na dibo a
spoon din na mika zuwa bakinsa. Mai
makon ya sha sai ya kama hannu na ya
dawo da shi baya ya mayar da spoon din
cikin cup din sannan ya saka dogon dan
yatsa na a cikin chocolate din ya
dangwalo sannan ya kai bakin sa, na
lumshe ido ina jin wani irin feeling na
yadda yake yi wa finger din nawa a cikin
bakinsa, nayi kokarin karbe wa amma yaki
saki, sai ya sake mayar da shi ya kuma
dangwalo wa ya sake mayarwa bakin sa,
"hmmm" yace "chocolate din nan akwai dadi fa" ya sake kokarin mayar da yatsan
nawa cikin cup din for the third time sai na
janye cup din, "zaka shanye min ai'" na
fada trying to make him stop, yace "rowa
ko? To shikenan, ki rike taki chocolate din
in rike tawa" ya fada tare da mayar da
hannuna zuwa bakinsa. Sai da yabi
fingers din daya bayan daya kamar wanda
ya samu sweet din gaske, sannan ya juya
hannuna ya manna min kiss a tsakiyar
tafin hannun. Nayi saurin janye hannuna
tare da boye shi a bayana trying to hide
yadda yake saka ni nake ji. Ya sake cewa
"rowa ko?" Na mika masa cup din gaba
daya,
"gashi na bar maka" yace "taki ce
wannan ai, ki bani nawa kawai" na girgiza
kai sai yace "okay to bana son wannan
din, ki sha kayar ki kawaj" na dauki spoon
din na cigaba da sha da sauri da sauri, ina
son in rage wa zuciya ta bugawar da take
yi. Sai da nayi nisa da sha sannan ya
karbe cup din daga hannu na da hannun
sa daya, daya hannun kuma ya kamo
fuska ta ya juyo dani gare shi and
unexpectedly ya hade bakin mu guri daya.
Sanda ya sake ni babu sauran taste din
chocolate a bakina, ya shanye tas, abinda
ya rage min a bakin kawai taste din sa ne,
wanda nake jin sa kamar ba'a iyakacin
bakina kadai ya tsaya ba, kamar dukkan
jijiyoyin jikina ya zagaya. Na bude idanuwa na da suka yi min nauyi na ssuke su a
kansa, har lokacin fuskarsa tana kusa da
tawa, idanun sa a cikin nawa, murmushi
mai fadi akan fuskar ta sa yace "nima na
sha tawa" sannan ya daga min gira yace
"and mine is sweeter" na tura baki tare da
saka hannu ina goge lips dina nace "kai
kazami ne Allah kuwa" ya danyi dariya
"kar ki damu, da sannu zan jaki zuwa
class dina, watakila ma ki fini kwarewa"
na murguda baki ina magana kasa kasa
sannan na
bude kofar motar na fita nace masa "kayi
wa kanka, na fasa yin hirar da kaj" na rufe
kofar sai kuma na sake budewa na dauki
cup din chocolate dina nace
"kuma ba
zan bar maka chocolate dina ba" yayi
murmushi "na sha tawa ai" har zan rufe
kofar sai yace "hey Piya" na tsaya sai
yace "I love you" na danyi murmushi ina
jin har na huce nace "I love you too Baby".
Na rufe masa kofar amma sai ya cigaba
da zama a motar har na shiga cikin gida
sannan ya tafi,
Na danyi kokarin calming kaina down a
compound amma shima da mutane dan
haka na wuce cikin gida, ina shiga sai nayi
sauri na wuce kitchen na wanke fuskata gabaki daya dan duk dankon chocolate
take yi, sai kuma na zauna a kitchen din
na cigaba da shan chocolate dina ina ta
zabga murmushi ni kadai.
Washegari da sassafe muka tashi muka
shirya zamu tafi gurin gyaran gashi, na
shiga yiwa Mommy sallama na tarar har
lokacin rabon kaya take tayi, har zan fita
sai ta kira ni "Safiyya, ni kuwa yaron nan
bai yi miki maganar yadda yake ciki akan
Safina ba?" Na danyi shiru ina kallon ta,
trying so hard kar in nuna bacin rai na, sai
kuma kawai na girgiza mata kai nace "a'a.
Bai ce min komai ba" sai nayi sauri na fita
daga dakin kar ta sake yi min wata
maganar. Ni bana son jin duk wani abu
daya shafi Safina da Muhammad, bai taba
yi min maganar ta ba nima kuma ban taba
tambayar sa ba. Duk wani hukunci da ya
yanke ko zai yanke a kanta abinda ya
shafe su ne bana son shiga ciki kuma
bana son a shigar da ni.
Muka je tare da Salima aka yi mana
gyaran gashi, sannan aka yi min pedicure
da manicure, aka kuma yi min teeth
whitening sannan saloon din suka yi min
massage for free a matsayin wedding gift din su. Daga nan muka dawo gida muka
tarar mai kunshi har tazo, nan da nan na
zauna aka fara rangada min jan lalle,
bayan an gama akayi baki shima amma
kadan as adon jan, sai ya fito yayi kyau
sosai, har yamma bamu gama ba. Tun da
rana kawayena na kano suka karaso, naji
dadin zuwan su sosai dan akwai da yawa
daga cikin su da mukayi shekaru rabon da
muyi magana sai da bikin nan ya tashi na
neme su kuma sai gasu sun zo. Ko dan
nima na san I was quite popular a
makaranta kuma da yawa kawayena suna
sona.
Lokacin yan gidan mu suna ta shirye-
shiryen zuwa gidan su Muhammad wunin
da aka gayyace su, sai a lokacin na lura
ashe tare da garar da akayi min zasu tafi
su kai musu, ni kuma ana gama min na
shiga wanka nayi da special man wankan
da mai gyaran jiki na ta bani, ina fitowa ta
zo ta kuma turarani da turaren ta mai
kamshi da kama dukkan sassan jiki, cikin
sauri na saka rigar da na tanada for
today's occasion sannan nay sallar
magrib din da ake yi a lokacin sannan
muka zauna zaman kwalliya,
Sanda aka gama kwalliyar ni kaina zaman
kallon kaina nayi a gaban madubi, lallai da
gaske Muhammad yake da yace yana murna babu maza a bikin, dan ni kaina sai
nayi kishin nunawa mazan da ba nawa ba
wannan kwalliyar da kyan da nayi. Sai
kuma naji ina son ya gani shi, ba wai a
hoto ba, dan haka na dauki waya na kira
shi "hey baby" duk yammatan gurin suka
juyo suna kallona, nay musu fari da ido
bayan naji ya amsa "kana ina?" Yace "ina
gidan ki. Kin san ni yau nake tarewa. I am
here busy arranging ny things" nace
"zaka iya zuwa nan yanzu?" Ya danyi
shiru "is everything okay?" Nace "komai
lafiya. Nayi kwalliya ne nayi kyau, and I
want you to see me" ya danyi murmushi
mai sauti. "I won't miss this for a thing.
Zan ajiye komai in taho. Sai in kaiki gurin
taron. Ki ce suyi gaba zamu taho tare"
nace "okay, sai kazo" na katse kiran ina
kallon kawayena da suke bina da kallo,
Nan da nan suka kama surutu "ba tun yau
ba na fada, mijin Fiyya zai sha iyayi"
"wannan soyayyar in da ace kina da
kishiya ai sai ta hadiyi zuciya ta mutu" "ni
kam zan so inje gidan ki watarana in ga
yadda za'a ci wannan soyayya " "in dai
mijin bai yi a hankali ba Safiyya will have
him licking at her fingers" na sake juya
idona nace "na nawa kuma? An wuce
wanna gurin ai". Haka suna ji suna gani suka shiga motoci
suka tafi nace ba zan tafi da su ba, Salima
ma data makale sai ta bini wai ai ba'a
barin amarya ita kadai haka na kora ta
nace in dai bata tafi tare da su ba sai dai
ta tafi ita kadai dan ba zata shiga motar
mijina ba. Sauran mutanen gidan ma babu
wanda bai yaba da kyan da nayi ba dan a
lokacin suke dawowa daga event din
gidan su Muhammad hannunsu cike da
abin arziki. Suka yi ta daukan hotuna da ni
har sai da Muhammad yace yazo sannan
twins suka raka ni na fita wajensa.
Bridal gown na saka fara sal, silky material
a ciki mai karamin hannu sai kuma aka
dora lacy material a sama shi kuma da
dogon hannu, aka kuma yi dogon trail
yana jan kasa sosai a baya na. A dai dai
waist din rigar kuma anyi ago da flowers
different colors an zagaye ni da su, sai
kuma gashi na da aka gyara aka zubo min
da shi ta side din kunnen hagu na sannan
ya sauka har kafadar hagun ya kuma
nannade a bayana, Anyi wa gashin ado da
pins masu different colors kamar na
flowers din jikin rigata. Sannan aka lullube
gashin nawa da farin lacy veil, Takalmi da
jakar hannu na duk sunyi matching da flowers din jikin rigata. Ya fito daga motar
yana kallona baki a sake. Daga kallon
kawai a san kwalliya ta biya kudin
sabulu.
[07/01, 10:48 pm] +234 906 816 1960: ❤️🩹Safiyya❤️🩹
Episode Sixty Six : Avenged
Not completely edited 😁 I am tired as always.
Tun daga fitar Aunty Hajjo sai na koma
nayi shiru, tun kawayena suna tsokana ta
har suka ga ina neman saka musu kuka
sai suka rabu dani suka cigaba da
hirarrakin su da shewa, suna ta labarin
gida na da yadda komai na gidan yayi
kyau ya kuma da ce da inda aka ajiye shi.
A lokacin naji Farida tana tambayar "ku
wai da gaske wadancan sababbin
motocin da muka gani da bow a jiki gifts
ne aka kawo mata?" Salima tace "eh fa.
Kanin baban sane ya kawo musu ita da
angon as wedding gift" Hasina tace
"gaskiya mutanen nan suna da Naira, Kin
san kuwa tsadar motar nan? Guda biyu
just like that wai wedding gift?" Salima ta
dan tabe baki tace "in dai kudi ne gidan
su suka zo" sai muka hada ido na girgiza
mata kaina, dan ni idan akwai abinda bana
so shine bragging da arziki, in ka sani kawai
ka sani in kuma ba ka sani ba bana
bukatar ka sani sai dai in ta kama dole.
Suna nan dai har suka yi sallar isha' i,
kawayena da suka zo min from outside of
Abuja duk gidan mu zasu koma su sake
kwana sannan washegari su koma gidajen
su. Around 8:30 sai ga kiran Muhammad,
ban dauka ba sai na mika wa Salima, a
zuciya ta ina tuna cewa tun safe rabon da
inji muryar sa, da ta dauka sai naga tana
murmushi tana kallona sannan tace "ba
ita ba ce ba. Salima ce. Kunya take ji wai
ba zata dauki wayar ba" sai kuma tayi
dariya, sannan tace "okay, gamu nan
zuwa" ta miko min tana murmushi "yace
suna first floor, mu sauka mu same su".
Muka tashi gabaki daya, suka sake gyara
min laffaya ta suka rufe min koina har kafa
ta, sannan suka kara min turare suka
kama hannu na muka sauka zuwa falon da
yake a hawa na biyu. Ni dai jana kawai
suke har suka kaini kan kujera suka ajiye
ni. Sai da na zauna sannan na fahimci a
kusa da mutum aka zaunar da ni. Sai
kuma naji muryar Ya Amen yana amsa
gaisuwar da kawayena suke yi musu, tare
da muryar wasu mazan amma kamar basu
da yawa ba zasu fi su uku ko hudu ba.
Daga nan kuma aka gabatar da addu'a
aka shafa sannan Farida kawata tun
primary school sarkin surutu ta fara zuba,
har da yin speech akan wai sun bawa
Muhammad amana ta, sai tazo ta kama
hannuna ta dora akan nasa tana lissafa
masa irin kyawawan halaye na, ta kara da
cewa "amma fa sai kayi hakuri, akwai iyayi
da taurin kai" ina jin Muhammad yana
dariya. Sai kuma Usman abokin sa shima
ya gode wa kawayena for hidimar da suka
sha a lokacin bikin, ya kuma koda abokin
na su da lissafa irin kyawawan halayen sa
shima, sannan ya tabbatar wa da
kawayena cewa abokin su zai rike amanar
da suka bashi.
Daga nan kuma sai aka fara cinikin
fuskata, kawayena suka dan ware gefe
daya suka yi meeting sannan suka yanki
kudi mai tsoka suka fada, abokan ango
suka fara jayayya, sun jima suna to and
fro sannan suka daidaita akan price din da
kawayen suka ki sauka daga kansa, daga
nan abokai suka ce a bayar da account
details din da za'a basu kudin, suka fadi
account aka tura musu, sai da kudin ya
shiga sannan naji kawayena sun hau
shewa da hun murna, kudin da aka basu
har yafi wanda suka tambaya da farko.
Daga nan Salima tazo zata bude fuska ta
ango ya hana, kiri kiri yace babu wanda
zai ga fuska ta a cikin abokansa a ranar, ai
kuwa nan rigima ta kaure tsakanin sa da
su, suka yi masa gorin dama babu abinda
ya shirya musu a bikin nasa, kuma fuskar
amaryar ma yanzu ya hana su gani. Anan
na jawo shi na rada masa cewa ya gaya
musu ina gayyatar su cin taliyar amarya
nan da kwana uku, amma da Muhammad
ya tashi fada sai yace next week.
Haka dai aka gama komai cikin raha da
walwala sannan suka tashi suka yi min
sallama suka tafi, duk wadda ta leka
fuskata sai inji kamar in rike ta in hana ta
tafiya amma ina ji ina gani suka tafi suka
barni. Ni ko rakiyar ma banyi musu ba,
Muhammad dai ya sauka ya raka
abokansa ya kuma sake yiwa kawayena
godiya, Sai da suka tafi sannan ya dawo. Har ya
dawo ina zaune a inda ya barni. Naji
shigowar sa amma sai naji shi shiru, ina
nan dai zaune a inda ya barni. Ina jin a jiki
na cewa kallo na yake yi, sai kuma naji yayi
gyaran murya.
"inzo in gani ni?" Ban yi magana ba sai
naji shi ya karaso gaba na ya tsaya yace
"ko nima sai na sayi fuskar amaryar ne?"
Still bance komai ba sai ya durkusa a
gaba na ina jin kamshin da yake tashi
daga jikin sa, ya dan daga laffayar ya leka
fuskata muka hada ido sai nayi sauri na
rufe ido na, yayi murmushi mai sauti
sannan ya daga laffayar ya bude ta
gabakidaya ya sauke ta akan kafada ta
yana karewa fuska ta kallo. Na daga idona
muka hada ido yayi min murmushi "kinyi
kyau sosai. Yau gabakidaya ban ganki ba"
shima yayi kyau kwarai da gaske, yana
sanye da riga da wando na yadi dark blue
da akayi wa dinki mai kyau kuma suka fito
da kyan fatarsa sosai. Hularsa ta zauna
sosai a kansa kamar dan kan aka halicce
ta. Amma sai na kasa ce masa yayi kyau.
Sai naji bakina yayi min nauyi, na sake
mayar da idona kasa sai ya zauna a kusa
dani tare da rike hannuna yace "kinyi kuka
k0? Ance min kinyi kuka a gurin Daddy
ko?" Na gyada masa kai ban ce komai ba,
ya saka yatsun sa guda biyu ya dago
fuska ta ya juyo ta tana kallon sa, na sake
daga ido na na saka a cikin nasa, sai yace
"yanzu ma kamar kin sake wani kukan. Su
Salima kika yiwa? o kukan Daddy da
Mommyn ne har yanzu?" Ban amsa ba sai
naji kamar zan sake yin wani kukan. Yayi
ajiyar zuciya "thank you Piya. I cant thank
you enough for your love and sacrifices.
Ko barin gida da kika yi kika yarda kika
taho nan zaki zauna da ni ni kadai is a
very big sacrifice. Wannan abu ne da ba
zan taba mantawa ba insha Allah. Na yi
miki alkawarin in Allah ya yarda ba zaki yi
nadamar zaba ta out of all the men in the
world ba" a hankali nace "nima insha
Allah ba zaka yi nadamar zaba ta out of all
the women in this world ba" yayi
murmushi. "Finally! Na sayi bakin".
Ya mike tsaye ya mika min hannun sa
"come, let's take a tour of our house" na
saka hannu na a cikin nasa ya jani na mike
tsaye, amma maimakon mu tafi sai naga
ya fara kokarin kunce min laffayar jikina
"akwai stairs, kar ki fad;" ya fada da yaga
ina kokarin hana shi. Sai da ya warware ta
sannan ya ajiye akan kujera yana kallona,
naji kunya ta kama ni sosai, ban taba
tsayawa a gaban sa haka babu mayafi ko
hijab ba, gashi kuma dinkin jikina babu
laifi ya fitar da shape din jiki na sosai.
Shape din da ni kaina ina matukar ji da shi.
Ganin kallon ya ki karewa ya saka na yi
kokarin sake daukan laffaya ta duk kuwa
da cewa ba iya daurawa zanyi ba, ya
karbe daga hannu na yana dariya
"'shikenan, na daina kallon ki" na harare
shi, ashe ma ya na sane kenan. Ya zagaye
waist dina da hannun sa ya jani zuwa
jikinsa "you are just so beautiful, I still
can't believe you are mine. Thank you for
being mine" ban amsa masa ba dan
harshena gabakidaya yayi nauyi, zuciyata
tana bugawa da karfin da har nake jin ta
cikin kunnuwana.
Sai ya sauke fuskarsa akan kafadata
sannan ya fara bin wuyana yana
shanshanawa tare da goga min gashin
sajensa. Na yi taku biyu baya da sauri
wanda hakan ya sa jiki na ya rabu da nasa
ina kallon sa, sai na ga ya fara dariya a
hankali "kinga idonki kuwa Piya? Kamar
an yi shaking rat a cikin kettle" na harare
shi "kana sane ma kake tsokana ta
wallahi. Allah Malam Muhammadu duk sai
ma rama abubuwan da kake yi min
kwanan nan" yace "ai haka nake so da ma
n ai, so nake ki rama" na danyi murmushi
ina kallon kasa sannan nace "wai yaushe
table din yayi turning ne? Ni dai na san a da nice mai tsokanar ka kai kuma mai jin
kunya amma yanzu kawai sai naga munyi
chanjin positions" yayi ajjiyar zuciya tare e
da yin taku biyu zuwa gaba na yace "a lot
of things have happened, a lot of things
have changed" na gyada kai na cikin
amincewa sai ya jera dani yace "but
nothing matters now tunda we are
together ko?" Na zura hannuna ta cikin
nasa da ya miko min ina kallon fuskar sa
kamar yadda shima yake kallon tawa da
murmushi sannan nace "let's take a look
at our home".
Gidan hawa biyu ne, ta kasa muka fara.
Akwai katon falo a kasa, wanda shine
kusan ya chine rabin ground floor din.
Yana hade da dinning room mai girma
shima, daga falon har dining din anyi sune
kawai for occasions da za'a tara mutane
da yawa. Bayan su kuma sai kananan
faluka guda biyu iri daya at different sides
of babban, daya nawa dayan na
Muhammad, kowanne da two bedrooms
da toilets a ciki, saboda baki,
Daga nan kuma sai first floor, ana iya
hawa ta falon Muhammad ana kuma iva
hawa ta falo na. Shi kuma akwai
madaidaicin falo wanda muka zauna dazu, akwai kitchen kato shima tare da
store sai kuma madaidaicin dinning room
a hade da falon. Daga nan kuma sai gym,
wanda Muhammad ya cika da kayayyakin
motsa jiki masu yawan da har sai da na
tambaye shi idan gasar wrestling ta WWE
yake so ya fara shiga. Daga nan kuma sai
bangaren swimming pool, da muka shiga
sai da na rike baki na cikin mamaki tare da
jinjinawa Kamfanin su Ya Amen akan iya
aikin su, gurin yayi kyau sosai kuma
gabaki daya a zagaye yake da glass din
da kai da kake ciki zaka ke ganin kowa a
waje amma babu wanda zai iya hango ka
daga waje. Katon swimming fool ne a
tsakiyar gurin blue tiles din da aka shafe
jikinsa da su suna chanja color zuwa
different shades of blue saboda fitulun da
aka saka musu. Akwai grin yin shower da
kuma changing room a cikin gurin sai
kuma kujeru guda biyar. Instead of tiles,
grass carpet ne a lullube a kasan gurin.
Daga yadda na nuna Muhammad ya
fahimci bayan kitchen nan ne favorite
spot dina a gidan, Daga nan kuma sai
sama ta biyu. Da akwai stairs daga gym
da zasu kai ka saman akwai kuma wasu
daga falo,
A sama ta biyun kuma bedrooms ne
kawai. Bedroom dina da na Muhammad iri daya ne exactly. Girman da komai daya
ne. Ni ba bedroom din ko kayan cikin sa
na fi so ba na fi son closet din. Daga
bedroom din zaka shiga kofa, a hannun
dama akwai toilet, a hannun hagu kuma
closet. Zan iya cewa kusan girman su
daya da bedrooms din dan ni nawa bayan
lockers din da aka zagaye bangon su da
su har kujera na saka a tsakiyar closet
din, irin katuwar kujerar nan wacce ake iva
mayar wa gado, a gaban kujerar kuma
katon mirror ne, both sides of mirror din
kuma kananan drawers ne da zaka iya
ajjyar kayan kwalliya. Daga hannun daman
ka in ka shigo closet din kuma study table
aka saka, anyi masa dukkan tsare tsaren
da zan iya yin aikin office dina ko karatu
ko whatever nake bukata a gurin, lokokin
gurin takardun aiki da duk was littattafai
zan saka. Hannun hagun kofar kuma gurin
yin sallar ne, an shimfida praying mat
sannan anyi provision for gurin ajiye
Alqur'ani a lokacin karanta shi, lokokin
wajen kuma zan zuba littattafan addini ne
a ciki. Zan iya shiga cikin closet dina in
wuni ba tare da na bukaci fitowa ba, sai
dai a kai min abinci, Komai na bedroom
dina fari ne tas, sai da Aunty Hajjo ta dage
sannan na bari aka sirka farin kadan da
light ash. Daga dakunan mu kuma sai dakunan da
akayi su a matsayin extra bedrooms guda
biyu iri daya, ni kuma a raina sai na lissafa
su a matsayin dakunan yara idan Allah ya
bamu nan gaba.
Sai da muka gama da nawa muka yi
hanyar nasa sai ya tare kofa yana shafa
kai, na tsaya ina kallon sa nace "ba ka da
gaskiya" ya danyi murmushi "it is kind of
messy" na harere shi "kazanta ko?" Ya
daga kafada "ba laifi na bane ba ai. Ke
kika hana ni zama in gyara jiya kuma
sanda na dawo na gaji. Yau kuma tun safe
Mama bata barni na zauna ba ina ta zirga
zirga" na dan sunkuyar da kaina kasa
nace "anan ka kwana?" Ya danyi
murmushi "a ina to zan kwana idan ba'a
gida na ba?" Ban ja maganar ba dan bana
son yin maganar sai na cire hannun da ya
tare kofar nace "saí naga abinda kayi a
dakin" na shige da sauri kafin ya sake tare
ni.
Ina shiga dakin na sa sai naji kamar ya
kwace wa kitchen matsayi a waje na.
Maimakon nawa da yayi haske saboda
white color da akayi using, shi nashi royal
blue ne da sirkin golden. Wannan ya sa dakin yayi duhu and it looks very cozy.
Na lumshe ido na ina shakar kamshin sa
da dakin yake yi, sai ya zagayo ta bayana
ya rungume ni ta baya "to ya? Bulala nawa
za'a yi min ta bata daki da nayi ban gyara
ba?" Babu wani hargitsewa da dakin yayi,
dagon dai ba'a gyare yake ba beddings
din duk a cukurkude, sai kayan sa kamar
set biyu a ajiye akan side drawers din
gefen gadon daga gani cire su yayi bai
adana ba, ga kuma takalma suma kafa
biyu a watse a tsakar dakin. Daga can
kasan window kuma akwatinan kayansa
ne ko shigar da su closet bai yi ba
ballantana ya jera. Nayi kokarin juyo wa in
kalle shi amma sai ya kara matse ni da
jikinsa shinshinar bayan kunne na
"'hmmm, kamshin ki dadi" ya saka hannu
ya ture dankwalin kaina sannan ya zare
ribbom din dana nannade gashi na dashi,
gashin ya zubo har saman kafadu na sai
kuma ya saka fuskarsa a cikin gashin tare
da kara sauke wata ajjiyar zuciyar,. Nayi
kokarin bambare hannunsa da ya zagaye
ciki na shi amma sai ya kara matse ni a
jikinsa yana shafa dogon gashina da
dayan hannun na sa, nace "kana
wayencewa ne kawai dan kana jin kunyar messiness of your room" ya danyi dariya
kadan, "zan gyara, amma bara in gama
wannan gyaran tukunna" na juyo da sauri
amma bai barni na bar jikinsa ba sai ya
sake hade jikin mu muna fuskantar juna
idanun sa akan lips dina, na dan ja fuskata
baya na kara distance a tsakanin lips din
mu "na ga dakin ka, yayi kyau. Now let's
go '" ya danyi dariya a cikin kirjinsa yana
biyo fuskata da tashi "let's go where? Ai
nan ne final destination din. Ko baki san
nan ne turakar mijin ki ba" nayi shiru ban
ce komai ba ina cigaba da kokarin hana
shi hade bakin mu, ina jin yayan hanjina
suna karkarwa. Ya cigaba da magana, ina
jin motsin lips dinsa akan nawa "kin san
me akeyi a turaka?" Ban amsa ba dan
banajin zan iya amsawar, numfashin sa
kawai nake shaka. "in gaya miki? In nuna
miki?" Na girgiza kaina da sauri "bana son
gani. Bana son ji. Ni dakina zan tafi" yace
"hmmm" tare da kissing hancina da kuma
haba ta, cikin dauriya nace masa "kai ma
hmmm" sai yayi dariya, "ba kin ce kina
son sanin ma'anar hmmm dina ba?" Nace
"bana so, na yafe, Ka rike ma'anar
abinka" dariya ya danyi tare da goga min
sajensa a gefen fuskata "ko ba kya son
sani yau sai na sanar da ke" ya fada yana
sake dawo da bakinsa kusa da nawa. Na
matse lips dina na shigar da su cikin bakina sai ya sake yin dariya tare da
mintsini na a cheek dina, na dan yi kara
"har da mugunta kuma? Daddy ya ....
Ban gama ba ya mayar da maganar tawa
ciki ta hanyar hade bakin mu.
Sai da yayi mai isar sa sannan ya janye
bakinsa, ya tsaya yana kallona idanuwana
a lumshe, sai ya mayar da bakin sa kunne
na yace min "I have got a favorite thing to
do yanzu. Kissing you is now my favorite
thing to do" na bude ido na ina kallon sa
sai ya kama hannuna "come, na siyo miki
kaji, kar ki ce nayi miki rowa".
Ya jani ya zaunar da ni akan
hargitsatstsen gadon sa, sannan yace
"ina zuwa, minti biyu, kar fa ki gudu" duk
da halin da zuciya ta take ciki sai da na
danyi dariya. Ya fita da sauri ni kuma na
cigaba da zama ina karanto dukkan
adduoin da na ke ganin zasu vani kwarin
guiwar fuskantar mijina. Kullum in ana
bayanin toro in aka ce mutum yana jin
kayan cikin sa suna rawa bana iya gane
wa, amma yanzu na gane, yanzu nima
nawan rawa suke yi sosai, hatta hakora na
karkarwa suke yi, Babu abinda yake yawo
a kaina sai azabar da Mukhtar ya ganar da
ni, sai irin tsoron da naji a lokacin da yake
gana min azabar. Na sani cewa Muhammad ba Mukhtar ba ne ba, na
kuma yarda cewa ba zai cutar da ni ba.
Amma kuma na kasa cire tsoron daga
zuciyata.
Ya dawo hannayen sa dauke da ledoji
manya guda uku, ya ajiye su a gefe na
yana kallon dakin yace
"gaskiya naji
kunya da yawa" sai ya sunkuyo kawai naji
ya daga na chak, na bude ido da sauri ina
kallon sa sai naga ya ajiye ni akan kujera
sannan ya juya ya fara gyara gadon, ina
kallon sa har da dauko turare ya fesa a
beddings din, gyaran na shi dai daga gani
ba iyawa yayi sosai ba irin yadda nake so,
amma dai ya gyara.
Sai kuma ya kwashe tarkashen kayan sa
ya shiga da su ciki, ya fito yana sake
kallon dakin sannan ya kalle ni yace "yayi
ko?" Ban amsa masa ba sai ya karaso
gaba na yace "sallah ko kaza?", A hankali
nace "ni sallah zanyi. Ni ba zan ci kaza ba,
Nina koshi" ya danyi dariya
"kwadayayyiya, ranar nan ma haka kika ce
ai, sai gashi har kin fi ni ci" na dan harare
shi kadan. Sai ya wuce zuwa toilet dinsa
yayi alwala, ni ma yana fitowa na tashi na
shiga, na jima a cikin toilet din ina kokarin calming kaina down sannan nayi alwalar
nima na fito. Na tarar da shi ya shinfida
mana wani karamin carpet akan carpet
din da yake dakin already, naji kamshin
dakin ya chanja kamar ya kara wani
turaren na daban mai dadin kamshi, "bani
da hijab" na ce masa, "bara inje daki in
dauko" ya girgiza min hannun sa "uhm
uhm. Ki zauna anan inje in dauko miki" na
bude hannu na, "to ai baka san inda yake
ba" da kyar ya yarda muka tafi tare, ban
sani ba ko tunani yake yi zan gudu idan na
tafi ni kadai?
Na dauko hijab dina na hada da kayan
bacci na da sauran abubuwan da nake
bukata idan zanyi shirin kwanciya. Kamar
wadda zanyi hijira zuwa wani garin. Muka
koma dakin nasa na ajiye kayan da na
debo sannan na saka hijab dina muka
tayar da Sallah. Bayan mun idar shi yayi
mana adduoin masu tsaho, nayi mamakin
yadda ya juya bakinsa yana jero mana
adduoi cikin karshen larabci, sai naji
kamar yaren sa ne, muka shafa sai ya
tambaye ni idan ina da wata addu'a da
zanyi mana sai na daga hannu na a zuciya
ta na roki Allah ya yaye min wannan
tsoron da nake ji sannan na shafa, ya
shafa shima sannan ya yambaye ni "mai kika roka mana?" Na girgiza kaina "shirri
ne" ya bude ido sirri? A tsakanin mu da
ma akwai sauran secret?" Na sunkuyar da
kaina ban ce komai ba. Ina jin sa yana
cigaba da kallo na sai na dago kaina na
kalle shi cikin ido nace "Yaya Muhammad"
bai amsa ma amma gabakidaya attention
dinsa yana kaina, a hankali cikin karyewar
murya nace "tsoro nake ji, I am scared
Yaya Muhammad" bai ce min komai ba sai
naga ya sunkuyar da kansa yana kallon
kan cinyata, nima na kalli inda yake kalla
sai na ga hannayena da suke kan chinyar
sun karkarwa kamar wadda take jin
tsananin sanyi, nayi sauri na rike su da
junansu sai ya matso ya dora nasa
hannayen akan nawa ya rike gam har sai
da suka daina karkarwar sannan yace "I
know. Na san kina jin tsoro Safiyya, sai dai
kuma bayan haka na san wani abu daban,
na san kina sona kamar yadda nima nake
son ki" ya gara zaman sa sosai sannan ya
cigaba "kin san wani abu? ranar da kika je
office dina a MD kika gaya min cewar kina
da aure, I was devastated a lokacin,
maybe tashin hankalin da na shiga shi ya
hana ni ganin gaskiya, amma bayan na
koma gida, bayan na nutsu nayi tunani sai
na tuno da fuskar ki a lokacin da kike yi
min maganar, na kuma tuno da yadda kika furta kalaman, sai kawai naji na fahimci
wani abu, na fahimci kina so na sosai,
wannan son kuma shine abinda ya bani
hope, shi ya rike ni ya hana ni hakura da
ke inyi moving on, ya hana ni giving up.
Tun daga lokacin kuma har zuwa yanzu
soyayyar ki ita ce take jagoranta ta a
dukkan decision dina, yanzu ma kuma ita
ce hope dina. You have fear, Yes, but you
also have love".
Ya mike tsaye tare da mikar da ni tsaye
nima sannan ya zaunar da ni a bakin gado
sai ya tafi gurin ledojin da ya shigo da su
ya dauko wata karama ya dawo kusa da ni
ya zauna ya bude ta ya dauki wasu boxes
guda biyu kanana tare da wasu takardu,
ya ajiye takardun sannan ya bude box din
farko ya nuna min "look at this beauty" na
kalli abinda yake ciki, a take na bude baki,
ya danyu dariya yana jin dadain yabawa
abinsa da nayi. Zo be ne na diamond, anyi
mass rings din sirara guda uku amma
saman su an hade shi da dunkulallen
diamond mai shape din heart. Ya fito da
shi sannan ya kama hannuna ya saka min,
yayi dai dai a danyatsa na kamar an
gwada, kamar ya san me nake tunani sai
yace "na karbi measurement dinki ne a
wajen matar da ta hada lefe. Do you like it?" Na sauri nace "like it? I love it Baby.
Thank you" na fada tare da daga shi ina
kallon sa sosai, a cikin heart din anyi
design din rose flower, petals dinta
different colors kuma na lura kamar
colours din nasu yana chanja shade idan
aka haska shi, yayi murmushi ya sake
kama hannun nawa yana shafa yatsun
yana kallon ring din sannan ya kai shi
bakinsa ya sumbata yace "I may not have
a gold company and all the rest, but I do
have love and I am today giving you all of
my heart together with all of my love, as
far as love between couple is concern. I
want to share my parents, my siblings and
all of my family with you. I want to share
my life with you. And I promise you that I
will work hard to give you all that you
deserve. And I promise you, insha Allah,
that you will never shade sad tears again,
sai dai in abinda yafi karfina, and ko da
yafi karfin nawa ma, I promise you that we
will cry together, wipe away each other's
tears, and pick up each other. We will
walk through the journey of this life
together. You will never be alone again",
Na fara sheshshekar kuka ina kallon sa "Muhammad……Yaya Muhammad.......
have been through a lot a rayuwata, zan
iya cewa tun kafin a san za'a haife ni
rayuwa ta take dabaibaye da tragedies iri
iri. At a point na dauka cewa ny family is
cursed. Amma yanzu.... Yanzu da nake
ganin ka a gaba na..... Sai na fahimci cewa
kai ne sakamakon da Allah yayi min a
duniya for all that I went through. Kai ne
light din da ta jira ni at the end of the
tunnel. Yanzu na fahimci duk abinda ya
same ni Allah yana jaraba nine dan yaga
idan na cancanci ya bani kai. Thank you.
Thank you for loving me. I love you so
much Baby na".
Na fada kirjin sa ina cigaba da kuka na.
Sai da ya bar ni na danyi kadan sannan ya
dago ni yana kallon fuskata yace "next
year by now, babyn mu yana kuka ke ma
kina kuka. Da ana bayar da sarautar kuka
da na nada ki" na harare shi tare da magana
kasa kasa "ni sai na yi kuka na wallahi",.
Ya kalli daya box din da take ajiye yace
"baki saka min nawa ring din ba fa"
na dauka da sauri na bude ina kallon
nashi zoben, irin nawa be sak sai dal shi
nashi anyi da azurfa ne ba diamond ba,
Sannan instead of rings duda uku nashi
mai kauri ne guda daya, kuma rose din
cikin nashi bata colours kamar tawa. Na
kama hannunsa na hagu na cire zoben da
yake jikin danyatsansa na hudu na saka
masa zoben, yayi mass kyau sosai ya kara
haska hannun. Ya miko min hannun tare
da hade rai "and now you kiss it". Na
makale kafada "kai komai kiss komai kiss"
yace "au haka kika ce? To wallahi sai kinyi"
ya taso kaina kamar zai hau jiki na sai na
yi sauri na kama hannun nayi kissing na
mayar masa da kayan sa, yace "Allah ya
taimake ki yarinya".
Ya mike tsaye "yanzu kuma saura in baki
kaza ki ci." Na makale kafada "ni fa na gaya
maka ba zan ci ba" ya wani table ya kawo
gaba na "to shikenan, ba zaki ci ba ni zan
baki a baki" ya dauko another leda ya bude,
kaji ne a ciki ba zan iya cewa ga adadin su
ba saboda anyi pieces da su, ashe har da
guzurin plate din sa a cikin ledar, ya zuba a
cikin plate din sannan ya dora akan table din
sau kuma ya fito da wani drink da ban taba
gain irinsa ba ya zuba a cup ya ajiye a kusa
da plate din sai kuma ya bude daya ledar, na
lura fruits ne a ciki, sai yace "na manta ban
dauko wuka ba" nace masa "ni fa ba ci zanyi
ba" bai nuna yaji abinda nace ba sai ya durkusa
a gaba na ya dauki tsokar naman guda daya ya
kawo baki na "bude. Bude mana" na bude a
hankali ya tura min a ciki "sai kinci naman nan
yau ko dura zanyi miki. Kin san dadin sa kuwa?
To wannan yafi na ranar nan dadi" naji dadin
masa kuwa, amma ni yanzu ba ta nama nake
yi ba. Kalamansa su sassauta min toro na amma fa
yana nan babu inda yaje, sannan kuma a cikin kalaman na sa banji inda ya am bata cewa ba
zaiyi ba, sai ma zancen Baby da ya yi min. Haka
ya ringa cusa min naman nan, sannan ya dauko
drink din ya kawo bakina "sha wannan. I bet duk yawon kasashen ki baki taba shan wannan
ba" na kurba, yayi dadi sosai, na karba na kara
sha yace "kinji da dadi ko?" Sai na gyada kai na
zuba wani na mika masa. "'yayi dadi. Na gode. Na koshi. Kai ma ka sha" ya karba ya shanye
sannan ya ajiye cup din tare da mike wa.
yace "yau yaki za'a yi in gaya miki,
between your fear and my love. Zamu ga
wanda zai ci nasara. Ni kuma na san nine
da nasara, Tunda na san love is the greatest weapon of all. Da mana jima ina share hanya, yanzu filin yaki kawai zan shiga ko a mutu ko a yi raj" yadda yayi
maganar sai ya bani dariya, amma kuma ban dara din ba dan babu dariya a tare da ni.
A dai dai lokacin ne kuma abin ya faru.
Ina zaune akan gado ina facing kofar
shigowa, shi kuma yana tsaye a gaba na
yana kallona ya juya wa kofa baya. Idona
yana sunkuye a kasa, amma duk da haka
sai na ga kamar kofa ta motsa duk kuwa
da cewa babu kara. Nayi sauri na dago
kaina and I saw him, a tsaye a bakin kofar,
muna hada ido ya karasa shigowa ciki da
sauri sannan ya ja kofar ya rufe ya murda
key din sannan ya zare key din ya saka a
aljihu. Mukhtar.
Kusan abinda ya faru ya faru ne in
seconds, a take na kwalla kara muryata
da fuskata cike da toro, dukkan tsoron
da nake kokarin dannewa ya ninninka
kansa sau babu adadi. Muhammad ya
juya da sauri saboda ganin inda nake kallo
da kuma razananniyar karar da nayi. Cikin
bazata Mukhtar ya damki wuyansa
sannan ya hankada shi da karfi ya buga
shi a jikin bangon dakin, Kansa ya bugu a
jikin bangon, dama gashi bai jima da jin
ciwo a ka ba, ya dafe kan yana kokarin
regaining kansa, wannan ya bawa
Mukhtar damar binsa ya kuma damkar
makogwaronsa tare da matse shi a jikin
bango da dukkan karfin sa.
Muhammad yana da girma, dai dai girman
da namiji matashi mai irin shekarunsa ya
kamata ya samu, Mukhtar ba sa'an sa
bane ba, sannan kuma Mukhtar kato ne,
tun yana yaro dama Mukhtar ba karami
bane ba dan haka yanzu za'a iya kiran sa
da katon mutum. Na sake kurma wani
hun tare da yin tsalle na tsallake table din
gaba na nayi kan Mukhtar ina dukan sa da
dukkan karfin da Allah ya bani. "Ka sake
shi.…. Ka sake shi ....." Na cigaba da ihun
a yayin da Muhammad ya samu ya
banbare hannun Mukhtar da kyar daga
makogwaronsa. "Run........" Yace min "ki
shiga toilet ki rufe kofa" ya kara fada a
lokacin da Mukhtar ya murde masa
hannun sa zuwa bayan sa sannan ya sake
hada shi da jikin bangon kansa yana sake
buguwa".
Tsoron Mukhtar da nake ji ya rinjaye ni da
farko, na ruga toilet da gudu kamar yadda
Muhammad yace min amma kuma sai
soyayyar Muhammad ta hana ni shiga
toilet din, In na shiga na tsira dan na
kofofin gidan suna da kyan da Mukhtar ba
zai iya balla su ba, Amma kuma
Muhammad fa? Zai iya yi masa komai
musamman idan ya kasa samu na, sai na
juyo a guje kamar yadda na tafi a gujen
amma sai na fara bude window nayi ihun
neman taimako sannan na dawo na fara
daukan duk abinda zan iya dukan Mukhtar
da shi ina kwada masa.
Dakin babu wani tarkace a ciki, dan haka
sam babu wani abu da zan kira makami.
Naji ina missing wukar da take kasan
gado na a gidan Daddy, na kuma jinjina
hikimar Annabi da ya shawarce mu mu
ringa ajiye makami a dakunan mu. "Run
nace miki. Take my phone and lock
yourself in the toilet. Then call someone"
na girgiza kai ina jan hannun Mukhtar da
dukkan karfina "gurina na kazo. a sake
shi. Don't hurt him. Ni kai min duk abinda
zaka yi min ka rabu da shi" na fada ina
hada masa da duka da yakushi da duk
abinda zan iya, na lura a jike yake da
gumi, na lura har wan wari yake yi. Ya
saka hannu daya ya ture ni na fadi kasa,
Muhammad ya zaburo "don't touch her!"
Ya fada a zuciye, Mukhtar ya sake mayar
da shi ya buga a jikin bango "or what? In
na taba tan me zakayi? Mama's boy. In na
taba tan babu abinda zaka iya sai dai ka
ruga gida da gudu kana kuka kaje ka fada
wa maman ka. Stupid, Shashasha, Ban
taba ganin sakarai irin ka ba. Duk
shekarun da kuke tare, duk kyawun nan
na ta, na dauka you already had her ashe
kai sakarai ne, wata kila ma baka iya ba.
Maybe kana jira sai an koya maka ne a
gida"
Muhammad yace "say whatever you want
to say, maganar dai guda daya ce, ba ta
son ka ni take so, shine kuma abinda yake
damunka. Shine abinda duk ya jawo maka
halin da kake ciki" ran Mukhtar ya sake
baci "karya kake yi, tana so na. Ni ta zaba.
Da kanta ta zabe ni tace ni zata aura. laifi
ne kawai nayi mata. Fushi ne kawai take
yi. She is mine, mine, mine, ni kadai. And I
am here to take her. Zan tafi da ita in bata
hakuri mu cigaba da zaman mu"
"delusional" shine abinda naji Muhammad
ya fada masa.
Ya sake shi ya matsa baya da sauri, daga
gani kasan ba'a cikin cikakken hankalin sa
yake ba. Muhammad ya durkusa yana
mayar da numfashi. Sai kuma Mukhtar ya
juyo yana kallona da irin kallon da na saba
gani a idonsa sanda ina gidan sa, kallon
sha'awa "or maybe I should have her
here" na mike tsaye da sauri, ya juya yana
kallon Muhammad yace "I will have her
here a gaban ka inga abinda zaka yi a kai".
Bacin ran da na gani a fuskar Muhammad
ban taba gain irin sa ba a duniya, ban
taba tunanin yana da irin sa ba. A fusace
yayo kan Mukhtar, Mukhtar ya rike
hannun da ya kai masa duka da shi ya
hana shi zuwa jikin sa, nan take suka
cigaba da gumurzu. Na dauki wayar
Muhammad a kan table kuma sai na rasa
wa zan kira, wa zan tayarwa da hankali.
Na sake lekawa da taga na cigaba da ihun
neman taimako, na tabbatar security na
suna waje, na kuma tabbatar sun ji ni,
amma tashin hankali na daya shine tun
sanda muka sauka kasa da niyyar kallon
gida Muhammad ya rufe kofa, duk kuma
inda muka shiga muka fito sai ya rufe
kofa. Dan haka kofa nawa zasu bude kafin
su shigo inda muke. Na kuma tabbatar
sun kira duk wanda ya kamata su kira,
maybe sun kira police ma already. Na
tuna bindigar da suka bani, tana can
dakina a cikin safe din gwala-gwalai na na
wajen Ammie,
Amma kuma sai naga Muhammad ya fara
bani mamaki a fadan nasu, a da in za'a ce
min za'a yi fada tsakanin Muhammad da
Mukhtar ba zan dauka cewa Muhammad
zai lasting minti biyu a hannun Mukhtar
ba, amma sai naga yana neman ya gagare
shi. Na fahimci Mukhtar kokari yake yi ya
hada hannayen Muhammad ya rike da
hannu daya dan ya samu damar shake
mass wuya da daya hannun, so yake ya
sumar da shi, may be a lissafinsa sai ya
dauke ni ya gudu da ni. Amma
Muhammad ya hana shi wannan damar.
Daga wancan bangon su koma wannan
bangon har suka fadi a kasa, Mukhtar
yana saman Muhammad yana ta kokarin
kama makogwaronsa, a lokacin naji
alamar an shigo cikin gidan, sai dai ban
san a wanne floor suke ba, na ga wani
frame a cikin bango na hau kan table na
ciro shi na buga wa Mukhtar a ka amma
ko gezau bai yi ba.
A lokacin na lura da abinda Muhammad
yake yi, kafafuwan sa da suke free yayi
amfani da su ya bude kafafuwan Mukhtar,
sannan cikin dabara da karfin da na kara
fahimtar yanzu yana da shi ya dake shi da
karfi da guiwar sa a tsakanin kafafuwan
sa.
Mukhtar ya sake shi sannan yayi baya
yana rike inda ya dake shi din, cikin zafin
nama Muhammad ya tashi ya kara masa
wani kyakyawan dukan a gurin again.
Mukhtar yayi kara ya fadi tare da hade
kafafuwan sa a waje daya cikin nuna
ciwon dukan da yaji, amma Muhammad
sai ya saka kafa ya sake bude kafafun ya
kuma take gurin da karfi da takalmin
kafarsa, Mukhtar ya saki karar azaba,
kamar an cire masa dukkan karfin jikin sa,
Muhammad ya sake duka, again and
again and again. Har tsalle yake yi sannan
ya taka gurin ya murje ya kuma takawa,
ban taba ganin ran Muhammad a bace irin
haka ba kuma bana fatan sake gani har
abada. Jinin da naga yana bin wandon
Mukhtar ne ya saka na fara kokarin rike
Muhammad amma yaki rikuwa, a dai dai
lokacin da aka fara kokarin bude kofar
dakin da muke ciki ne na ga ya bar shi, na
dauka da gaske barin na sa yayi, sai kawai
na ga yaje a kinkimo wata flower vase da
take kofar toilet dinsa, ya zo ya daga ta ya
sakar wa Mukhtar ita a tsakanin
kafafuwan sa,
Ta daki gurin sannan ta tarwatse. A dai-
dai lokacin da security din suka shigo
dakin da muke hannayen su rike da
bindigogi. Nayi sauri na rungume
Muhammad, ina jin yadda jikinsa yake
karkarwa, ina jin yadda zuciyar sa take
bugawa, ina jin yadda numfashin sa yake
fita sama sama. Chief security din ya kalli
Mukhtar da yake yashe a kasa yana fitar
da numfashi sama sama, ya saka kafa ya
shure shi dan ya tabbatar babu sauran
fada a tare da shi sannan Chief security
din ya tambaye ni "are you okay?" na
gyada masa kai kawai. Su biyu suka kama
hannayen Mukhtar suka ja shi a kasa suka
fita da shi. Na bishi da kallo, remembering
everything that happened, and I thought
"What a glorious God I have".
Ni na tabbatar ta Mukhtar ta kare, abin
nan dai ba zai kuma amfani da shi ba har
abada, ba a kaina ba, ba'a kan kowa ba.
Na kuma san Muhammad ya daki banza,
ko shari'a za'a yi Mukhtar ne a kasa,
sannan knowing irin gatan Muhammad,
bana jin ma za'a yi shari'ar.
Hukuncin da addinin musulunci ya tanada
for rape, shine Mukhtar ya kawo kansa
har gida Muhammad ya yanke masa.
Na kara rungume Muhammad, jiki na
gabaki daya yana karkarwa. A hankali ya
fara sauke ajjiyar zuciya sannan ya dago
fuskata daga kirjinsa yana kallo na yana
shafa fuskar yace "Hey. It is okay. It is
over. He will never touch you again. He
will never touch any woman again".
Maman Maama✍🏻
[07/01, 10:48 pm] +234 906 816 1960: ❤️🩹Safiyya❤️🩹
Episode Sixty Eight: Detached
Not Edited
Him👳🏻♀️
Washegari ma bacci suka yi sosai da safe,
basu tashi ba sai around 12, ita ta fara
tashi ta gudu dakin ta ta barshi, rashin jin
duminta ya saka shi tashi shima. Yau ma
kamar jiya Mama ta aiko musu da abinci
sannan Esther ma da take gidan tayi, suna
vin breakfast suka sake dawowa sama. A
wanna ranar sunyi abubuwa da dama,
most of which includes exploring their
bodies, aside that sunyi arranging and
rearranging dakin sa. Daga cewa tazo ta
taya shi shirya kayan sa a closet dinsa sai
ta tsiri rearranging bedroom din nasa ma
gabaki daya bayan sun gama da closet
din, da kyar ya samu ta bar masa gadon
sa a inda yake shima dan ya ce mata ba
zai iya kunche shi bane ba, but kujerun
sai da ta saka shi chanja musu guri daga
inda yake so zuwa inda take so duk kuwa
da cewa dakin sane kuma kujerun sa
amma haka ya juya su da kansa zuwa
ra'ayin ta, bayan ta zama satisfied with
the arrangement kuma ta matsa masa
lallai shima sai ya amince cewa kujerun
sunfi dacewa a inda ta mayar da su, da
yaki fada sai tayi fushi, dole ya fadi abinda
take so din sannan kuma ya bata hakuri
for not saying it a sanda takeso.
Shi dama ya san ya debo wa kansa rigima
with auren Safiyya but he was so looking
forward to it and he knows yana da
hanyar controlling dinta a gurin da take
bukatar control din, but for other petty
things like this, zai barta to have it her
ways. Shima kuma sai ya taya ta gyaran
tata closet din, a nan ya sha iyayi har sai
da ya gode Allah, hatta folding kayan da
ba'a dinka ba sai da ta nuna masa yadda
zaivi, ballantana wadanda suke dinkakku,
daga baya sai ya ce zai yi hanging abayas
da English wears tunda su ba folding
dinsu za'ayi ba, amma nan ma sai da ta zo
ta nuna masa yadda ake saka veil din
kowacce abaya tare da abayar a jikin
hanger dinta, haka da suka zo kan
takalma da jakankuna suma, wai kowanne
takalmi sai an nemo jakarsa an ajiye su
adjacent to each other, a shirya kayan
kwalliya ne gayyar ta watse, suka bar aikin
kuma suka koma wasa wai shine makeup
artist ita kuma client dinsa, haka ta zauna
akan kujera yayi ta shafa mata abubuwa a
fuska, wani abin ma duk da ya karanta
description dinsa amma baya gane
amfaninsa dan haka ba'a gurin da ya
kamata a saka shi ya saka shi ba, a karshe
sai gata ta fito kamar mahaukaciya sabon
kamu, ya saka ta a gaba ya ringa
kyalkyala mata dariya, wannan dariyar da
yayi ce ta saka tace wallahi sai ta rama, ya
yi kokarin gudu ta kamo shi ta dawo da
shi ta zaunar da shi shima ta tsara masa
kyalliya tas a fuskarsa sannan ta rama
dariyar da yayi mata. Haka suka zauna
suna kallon junansu suna tuntsira dariya,
a karshe dai suka gaji dan kansu suka
zauna suka goge wa kansu kwalliyar.
Da rana ma Mama ta aiko musu da abinci.
Yau ma kamar jiya, sun fita sun je duba
Daddy bayan sallar magrib kamar yadda
yayi mata alkawari, bayan sun gaishe da
Daddyn sai ta shiga ta gaishe da Mommy
tunda ta lura yan kano sun koma. Da sauri
ta shiga ta fito saboda yana jiranta, suka
tafi.
Wasa wasa sai gashi wankin hula yana
neman ya kai Muhammad dare, love din
da yake ikrarin zaiyi fighting fear amma
sai ya kasa, sai dai kuma ya fahimci cewa
fadan was no longer between love and
fear but between love and love. Tana jin
toro sosai, shi kuma yana sonta sosai,
dan haka ya kasa takura mata dan yana jin
tausayin ta sosai. She would let him kiss
her, touch her, carry her and fly away with
her in to the sky, zasu yi souring har su
tarar da cloud eleven but she wouldn't let
him do the do, da zarar ta ga ya dauki
wannan hanyar zata rikice ta zare jikinta
daga nasa jiki yana karkarwa, idanu suna
fitar da hawaye, a haka dole zai hakura,
and then she would ask him to hug her
and sleep with her wai toro take ji.
"Baby I'm scared" haka ta kan fada cikin
shagwabar ta da take kara rikita masa
tunani.
A haka kwanaki uku na farkon auren su
suka zo masa, Duk da cewa abubuwa ba
su zo masa a yadda ya tsara su ba but he
wouldn't change a thing idan da ace za'a
bashi damar chanjawar, har zuwan
Mukhtar ma ba zai chanja ba, dan zuwan
na shi ya bashi damar hadiye wani abu da
ya tsaya masa a makogwaronsa tun sanda
Safiyya ta bashi labarin abinda Mukhtar
din yayi mata,
Abinda ya fahimta da ita shine ba wai bata
son abin bane ba, ya fahimci tana so, just
that wancan memory yana sakata tana jin
toro sosai, maybe tana gain kamar
abinda ta ji a wancan karon shi zata sake
ji a wannan karon, duk kuwa da cewa a
zuciyarta ta san ba haka bane ba amma
kwakwalwarta taki karbar gaskiya, the
trauma is still with her and she panics at
the slightest thought of it. Wannan ya
kara masa jin tausayinta da kuma
lallabata. Washegari, maana ranar da suka kwana
na uku together, bayan sun yi sallar asuba
sai suka koma bacci kamar yadda suka
saba yi kullum, ya rungume ta a jikinsa ya
lullube su nan take bacci mai nauyi ya
dauke su, sun jima suna yin baccin
sannan karar wayarsa ta tashe shi, cikin
bacci ya jawo wayar and sunan da ya gani
a jikin screen din ya bata masa mood
dinsa, ya katse kiran sannan ya saka
wayar a silent, ya koma da niyyar cigaba
da baccin sa amma sai yaji baccin yaki
zuwa, reality din situation dinsa yana
lullube shi, kafin ya gama analyzing
situation din nasa yaji wayar Safiyya ta
dauki kara itama, kasancewar tana
bangaren ta sai ta riga shi dauka and cikin
bacci ba tare da ta duba sunan wanda ya
kira ta ba ta amsa ta saka a kunnen ta
tare da cewa "hello" cikin muryar bacci,
kusancin da suke da juna ya saka yaji
muryar da kuma abinda ya fito daga cikin
wayar ta ta, muryar Safina "na kira wayar
sa bai dauka ba, na san kuna tare, ki gaya
masa ko ince ki tuna masa cewa yau
kwanan ku uku tare, hakan yana nufin yau
kwana na ne tun da dai ke bazawara ce
ba budurwa ba......" ya saka hannu ya zare
wayar da ga kunnen ta sannan ya katse
kiran ya ajiye tare da rintse idonsa yana jin
zafin maganar kamar shi aka gayawa, sai
kuma ya sake juyawa wajen Safiyya,
kasancewar ta juya masa baya ne sai
hakan ya hana shi ganin fuskarta. "Piya"
ya kira sunan ta yana kokarin juyo da ita
ta fuskance shi amma sai taki, "safiyya ta"
ya fada with that deep voice of his wanda
ya kara zama deeper saboda baccin da
yayi, tare da zura hannunsa a kasan
cikinta yana kara jawo ta zuwa gare shi.
Ta raba hannunsa da jikinta sannan ta
mike da sauri, har tana vi kamar zata fadi
ta shige toilet dinsa, ya dafe kansa da
hannunsa daya tare da rufe idonsa for
some seconds sai kuma ya tashi ya sauka
daga gadon, ya duba agogo yaga some
minutes to 12, dama jiya ma sai kusan
hakan suka tashi, ya juya ya kalli toilet din,
yana jin karar ruwa amma kuma sai jikinsa
yake bashi cewa ba wanka take yi ba kuka
take yi, ya mike ya bita toilet din, duk
sanda ta shiga toilet takan rufe ne saboda
ya san takura mata yace sai sun shiga
tare, amma sai ya tarar yau a bude, ya
tura ya shiga sai ya ji shower ce a kunne a
dakin shower, ya karasa gurin ya tura
kofar, kamar yadda yayi tunani kuwa a
zaune take dirshen a kasa ta kunna
shower din tana zubowa a kanta duk
kuwa da cewa kayan baccin ta still suna
jikinta, fuskarta a boye a tsakanin
kafafuwanta, duk da baya ganin fuskar
amma ya san kuka take yi.
Yaji wani abu ya tsaya masa a kirjinsa, just
3 days ago ya zauna ya gama tsara mata
alkawarin cewa ba zai barta ta sake yin
kuka ba and she is already doing it. Ya
shiga cikin shower din shima da kayan sa
a jikinsa ya zauna a kusa da ita sannan ya
jawo ta jikinsa. "Babe" Sai dai kuma sai ya
rasa kalaman da zai yi amfani da su wajen
rarrashin, "Babe please ki daina kuka
mana" ya fada yana dago fuskarta tare da
kissing idanunta da ya lura cewa hawaye
ne yake fita daga ciki duk kuwa da cewa
ruwan da yake zubowa a kan su yana
wanke hawayen.
Ta kwace fuskarta ta mike tsaye,
forgetting cewa a jike jikinta yake, "ni ka
rabu dani, bana son jin komai, a tashi ka
tafi gurinta". Ruwan da ya jika ta ya saka
kayan baccin ta marasa nauyi suka
mammanne a jikinta suna bayyanar masa
da dukkan surar ta, abinda ya gani ya
rikirkita tunanin sa gabakidaya. Ya mike
tsaye shima tare da jawo ta ya manna ta a
jikinsa ruwan yana cigaba da sauka a
kansu, a kunnen ta ya rada mata "am
sorry Babe, I promise you, ba zaki kara
kuka akan wannan issue din ba kinji?
Please ki daina" ta fara kokarin kwatar
kanta daga gare shi da niyyar cigaba da
fushin ta, ya ki sakin ta da niyyar cigaba
da lallashi, sai dai kuma a hankali sai
lallashin ya chanja salo daga na kalamai
ya koma na gangar jiki, jin ya fara daukan
wata hanyar ta da ban ya saka ta cigaba
da ture shi "ni ka rabu da ni, ka tafi gurin
ta, kar ka kara zuwa guri na, kar ka kara yi
min magana ma, kar ka ....... " Ya jawo
fuskarta gare shi tare da hade bakin su
cikin kiss mai cike da bayyana mata halin
da zuciyar shi da gangar jikinsa suke ciki
a kanta, tun tana kokarin kwatar kanta har
ya samu nasarar zare dukkan wata laka
da take jikinta, tun tana kokarin resisting
kisses and touches din sa har ta fara
mayar masa da martani ba tare da ta sani
ba. A haka rarrashin yayi leading to
something else wanda a karshe har sai da
ya wajabtar da wanka akan su duk su
biyun duk kuwa da cewa Gidado bai kai
ga destination din sa ba yet. Amma a
ransa ya san cewa ya kusa, kadan ya rage
masa ya je din, ko a yanzu ma da ya
takura da zata barshi ya je amma baya
son ya takura din, baya son ta kuma
alakanta wannan abin da feeling of being
forced, ya fi son duk ranar da zai samu ya
kasance da kanta ta bude masa kofa
kuma ta gayyace shi.
Ya kara karfin shower din tare da fara
gabatar da wankan da ya wajaba a gare
shi, ya juya yana kallon ta, ta dunkule a
can karshe ta rufe fuskarta da hannayenta
biyu da suka sha lalle, shi ya san ko ya ce
ta taso suyi wankan tare ba zata taso ba
dan kunyar sa take ji sosai, kunyar ce ma
ta saka ta dunkulewa a guri daya kamar
ball, sai dai, through all the kunya and all
the rufe fuska yana iya hango murmushin
da yake kwance akan fuskar ta, wannan
murmushin kuma kadai ya ishe shi
payment na hard work dinsa.
Kunyar da yasan tana ji bata hana shi
tsokanar ta ba, yayi directing ruwan
shower din towards har ya fesa mata. Ta
danyi kara tare da tare ruwan da
hannayenta ta bude idonta kadan, sai
kuma ta mayar ta rufe da sauri saboda
abinda ta gani "na shiga uku. Menene
haka ne? Wai kai ba ka jin kunya? Dan
Allah ka saka kayanka ko kuma ka fita"
yayi dariya "toilet dina ne, in kin isa ki
tashi ki fita ke" amma kuma ya san ba
zata iya tashi ba. Ko me zai yi mata ba
zata iya tashi tsaye a gabansa a yadda
take ba. "Dan Allah ka bari.... Dan Allah
ka fita" ta cigaba da rokon sa a lokacin da
ya cigaba da fesa mata ruwan avoiding
her face dan kar ya hana ta numfashi,
yace "ki taso muyi wanka to" ta girgiza
kanta tana kara rintse idonta "I can't. Dan
Allah kayi hakurj" yayi dariya, wai ita ce
mai bashi hakuri, "ki kara bani hakuri to"
"Allah ya baka hakuri, Allah ya huci
zuciyar ka" "kice min Baby" "Baby na dan
Allah kayi hakuri ka fita, ba zan kara
tsokanar ka ba" yayi kwafa sannan ya
mayar da ruwan kansa ya sake wankan da
ya fara daga farko trying not to look at her
dan kar ya koma ruwa, ya san yana
bukatar concentration for abunda yake da
niyyar yi yau.
Ya gama wankansa sannan ya fita ya bar
mata toilet din, ya shirya cikin sauri dan
ya kusa makara masallacin sallar azahar,
har ya fita daga dakin bata fito daga toilet
din ba kuma ya san ta gama kunyar fitowa
kawai take ji, da ya dawo daga masallaci
ma bai same ta a dining ba kamar jiya da
shekaran jiya, wannan ya sa ya debi
abincin ya hau mata da shi har zuwa dakin
ta, ya tarar da ita tana ta kokarin daura
dankwali sai kamshi take, tana ganin sa ta
warware dankwalin ta rufe fuskarta da shi,
ya ajiye abincin tare da karasawa ya jawo
ta jikinsa, ta fara ture shi yace "ko ki bude
fuskar nan ko kuma ni kadai na san me
zanyi miki" ya rada mata a kunne.
Ta yi masa chakulkulin da ya saka ya sake
ta da sauri, ta dauki abincin da ya ajiye ta
ruga da gudu ta shige closet ta rufe kofa.
Ya jima yana kallon kofar yana murmushi
sannan ya fita.
Shi kadai ya ci abincin sa a kasa yana jin
kewarta, amma kuma bai matsa mata da
sai ta fito sunci tare ba dan yana bukatar
concentrating, ita kuma indai tana guri to
dukkan tunanin sa a kanta yake tsayawa.
And now he needs to think about
something else. Wayarsa da take haske
ya kalla, Safina ce dai, kira na kusan biyar
kenan tayi masa a yau. Wannan ma barin
sa yayi har ya katse da kansa bai dauka
ba. Ya samu ya gama cuccusa abincin da
kyar sannan ya shanye tea dinsa ya mike
ya fita. Sai da ya zauna a sabuwar
motarsa sannan ya dauko wayarsa ya tura
wa Safiyya message "hey Babe, a fita.
We will talk about it later".
Yana tura mata ya tashi motar ya fita daga
gidan zuciyar sa cike da tunane tunane.
Hanyar daya gidan nasa ya dauka inda
Safina take. Rabonsa da gidan tun ranar
da za'a kawo Safiyya, ranar asabar. Dama
tun ranar juma'a Mama ta kira shi tayi
masa fada tas akan kin gaya mata da yayi
cewa Safina bata gida tun ranar da aka
daura auren sa da Safiyya. Shi dama tun
ranar da aka daura auren bayan ya bar
gidan su very late ya koma gida mai gadi
yake gaya masa cewa ta fita daga gidan
cikin tashin hankali, mai gadin was
concerned cewa ko mutuwa aka Vi ko
wani mugun abun da ban, sai ya fahimci
cewa ta san abinda ya faru shine ta tafi
gida.
Tun daga nan kawai ya cigaba da harkokin
sa bai neme ta ba bai kuma gayawa
iyayensa ba ballantana su neme ta, amma
a ransa yana ta jira yaji an kira shi ance
Safina ko iyayen Satina sun ce ya sake ta,
amma shiru babu wannan sakon, sal
fadan Mama ne ya biyo baya tare da
sanar masa da tayi cewa ta saka an dawo
da Safina gidan ta. "ya kamata ka san
halin da kake ciki akan yarinyar nan tun
kafin ka daukar wa kanka nauyin da ba
zaka iya saukewa ba" Mama ta fada a
karshen fadan nata.
Ya san abubuwa da yawa maganar
maman take nufi, a ciki har da approval
dinta na abinda ta san cewa yana ransa
tun farkon auren na sa da Safina.
Tabbas, tun ranar dinner din bikin su,
ranar da ya fahimci dangantakar Safina da
Safiyya, a ranar ya san cewa auren sa da
Safina ba mai dore wa bane ba, ya san
cewa zaman su tare wani abu ne da duk
su biyun ba zasu ji dadin sa ba. Amma
kuma ya kasa datse igiyar auren na su ne
saboda iyayensa, saboda gudun bacin
ransu, sai ya fara neman hujjar da zai
basu dan su fahimce shi, aside her being
related to Safiyya dan a lokacin yana
ganin ba zasu dauki hakan a matsayin
huja ba. Amma bai samu ba har abinda va
faru tsakaninsa da Safina ya faru, sai
kuma ga issue din cikinta, wannan duk ya
kara hana shi rabuwa da ita.
Yanzu kuma tun sanda cikinta ya zube
tausayinta yake ji, duk da yasan ita din ba
abar tausayi ba ce ba, gani yake ta rasa
komai saboda soyayyar sa. Gani yake
kuma idan bata yafe masa akan yanayin
zaman da suke yi ba sai Allah ya kama shi
da hakkin ta. Amma kuma ya sani, the
more da ya cigaba da zama da ita the
more alhakin ta da zai dauka ya dora wa
kansa, wannan kuma shine maganar da
Mama take yi masa. Sai dai kuma yana
son rabuwar tasu ta zo da dadi yadda
maybe zata iya yafe masa ko da ba yanzu
ba, yana kuma bukatar dalilin da zai gaya
wa kansa da kuma ita sannan da iyayen
su a matsayin dalilin rabuwar aside her
being Safiyya's step sister.
Wannan ya sa ranar asabar din da za'a
kawo Safiyya ya bi umarnin Mama yaje ya
yi wa Safina siyayya, akwati guda uku ya
cika mata da kayan sawa masu kyau da
sauran kayayyakin amfanin mata, sannan
ya biya ta gurin siyar da mota ya siya
mata mota yar daidai misali aka biyo shi
da ita zuwa gidan,
Yana shiga ya saka mai gadi ya shiga da
kayan cikin falonta ya ajiye, sannan ya
shiga, bata falo, amma yaji motsinta a
cikin dakin ta, ya je kofar dakin ya tsaya a
bakin kofa yana kallon ta, hannayensa a
cikin aljihunsa. Ta hargitsa dakin gabaki
daya, ya kasa gane gyarawa take yi ko
hargitsawa take kara yi. Ita kanta a
hargitsen take. Ta juyo tana kallon sa,
fuskarta gabaki daya kamar ba tata ba,
har wani duhu ya ga tayi.
"ango" tace tana yi masa wani murmushi
da shi kansa ya san ba na gaskiya ba ne
ba. "miji na kuma mijin kanwa ta. Wannan
shine kirarin da zan ringa yi maka daga
yau" ya juya kansa gefe yana kokarin
hana kansa gaya mata wadda zata hana
ta bacci yau. Ta cigaba "ita kuma daga
yau sunanta kanwata kuma kishiya ta.
Maciya amana, daga kai har ita".
Ya danyi murmushi yace "daga mu har ke
mun san cewa she didn't marry your
husband, you married her boyfriend.
Wannan shine cin amana" ta matso
gabansa "really? Kuna da shaidar da zaku
nuna min kan cewa na san kai saurayin ta
ne sanda na aure ka? Kuna da shaida?"
Bai amsa ba sai yace "me yasa kika
dawo?" Ta danyi murmushi mai ciwo tace
"me ya sa ba zan dawo ba? Ka manta kai
mil na ne Habibi?" Ta fada tana kai hannu
fuskar sa ta shafa sajensa ya danyi taku
daya baya sai tace "kai miji na ne kuma
ina son ka. No matter how much you hate
me hakan ba zai cire min sunan matarka
ba har sai ka sake ni da kanka. And you
cannot do that saboda iyayen ka, shi yasa
kaji dadi da na tafì gida ko ta kaina baka
sake bi ba, a ranka kana murnar cewa na
tafi na baku guri zaku ci amarcin ku son
ranku ko? Ni kuma shi yasa na dawo, dan
a raba amarcin da ni. Kar ka manta kwana
uku ne, bazawara ce, dan ma dai at least
ka dandana budurwar kaji dan haka yanzu
zaka fi banbancewa sosai, zaka ware aya
daga cikin tsakuwa, in ka gama kwana
ukun sai ka dawo dakina, watakila zuwa
lokacin ka fahimci gaskiya, in ma kuma
baka fahimta ba ina bukatar ka dawo din
ko kallonka ne in saka ka a gaba inyi tayi".
Bai amsa duk wadannan maganganun
nata ba sai ya juya ya koma falo yace "ki
zo ina son magana da ke". A gaban kayan
da mai gadi ya ajiye ya tsaya, ta fito sai ta
tsaya itama tana kallon kayan tana kuma
kallon sa, ya nuna mata kayan da hannun
sa. "ga kaya nan. Mama tace ana yi a
al'ada" ya ciro key din motar ya dora akan
kayan "ga wannan, it is a gift from me to
you. I know we have been on a wrong foot
throughout our days together amma ina
fatan maybe watarana we will forgive
each other". Ya daga kai yana kalion ta, ga
mamakin sa sai yaga hawaye suna bin
fuskar ta, ya danyi gyaran murya yace
"akwai abinda kike bukata?" Ta dago kai
tana kallon sa tace "abinda nake bukata?
Kamar me fa?" Ya dan daga kafada
"foodstuff, cleaning things, anything dai"
ya juya kanta tace "what of mijina? Idan
miji na nake bukata kuma fa?" Ya sauke
ajjiyar zuciya bai ce komai ba, ta tako
zuwa inda yake "ba'a kawo ta ba ai, dan
haka yanzu ma a dakina kake, me zaka yi
idan nace kai nake bukata a yanzu?".
Ya zaro ATM card ya ajiye a kusa da key
din motar yace "dan kina bukatar wani
abu ki cira kudi ki siya, 2728 shine pin
din". Daga haka ya juya ya fita ya bar
gidan, bai sake kuma waiwayar gidan ba
duk kuwa da kiran da take ta zabga masa
a waya kullum sai yau, three days later.
Yana shiga gidan yayi packing yana amsa
gaísuwar da maigadi yake yi masa sannan
ya fita ya shiga bangaren sa, ya tsaya
yana karewa dakin na sa kallo, thinking
about a lot of things, thinking about
abinda ya kamata ya dauka a dakin da
kuma wanda baya bukata. Sai dai bai
dauki komai din ba, ko zai dauka ba yanxu
ba. Ya zauna akan study yabl6din da yake
dakin ya dauko wata takarda sannan ya
dauki biro yayi rubutu a cike sai ya ninke
ya saka a cikin aljihunsa sannan ya dauki
wayarsa ya kira number din Abba suka
danyi magana kadan sai ya kashe ya mike
ya tafi bangaren ta.
Ya tarar da ita tana ta gyara gyare, da
alama deep cleaning take yi wa gidan, ya
yi sallama sannan ya tsaya a bakin kofa ya
saka hannayensa a cikin aljihu, mai aikin
ta ta gaishe shi sannan ta shiga ciki da
sauri, ba'a jima ba Safina ta fito tana
gyara dankwalin kanta. Yayi mata
murmushi, sai yaga mamaki ya bayyana a
fuskar ta. Maybe bai taba yi mata
murmushin gaskiya ba.
"Sannu da zuwa" ta fada indicisively, "I
thought ba zaka z0 ba. Nayi ta kira baka
dauka ba" ya daga kafada, "You didn't
need to keep calling" ta karasa shigowa
tana kallon fuskar sa da take dauke da
murmushi da kuma annurin da ya kasa
boyewa, kowa ya kalle shi sai yaga
annurin angonci a tare da shi,
"I thought ba zaka zo ba shi yasa nayi ta
kiran ka. I thought I need to involve our
parents…." "Cut the threats" ya fada,
"sit. Magana na zo zamuyi" ta zauna
kamar yadda ya bukata akan kujerar
zaman mutum biyu tana kallon sa,
yanayin da ta fuskanci yana ciki shine
abinda tayi burin samu a rayuwar auren
su, shine kadai abinda take son samu,
not mota ko kudi.... Was it too much to
ask?
Sai ya karaso, and ga mamakin ta sai ta
ga ya zauna akan kujerar da take zaune
akai, it was the closest they get tun da
aka daura musu aure except for that
night. And to top it all sai ta ga ya kama
hannun ta ya rike a cikin nasa, still with
that smile on his face yace "Safina,
Magana nake so muyi. Please ina bukatar
attention dinki. Ina son muyi first
reasonable magana as a couple. Ina son
mu samu understanding, Ina so mu samu
matsaya a auren mu" ta daga kai ta saka
idonta a cikin nasa, within the first second
ta gana narkewa, duk wasu makaman
yakinta suka zube daga hannun ta suka
barta ita kadai, daga ita sai zuciyarta sai
kuma wadannan idanuwan nasa da yake
kallonta da su.
"Can we talk, please" ya fada a kokarin
dawo da ita cikin nutsuwar ta. Ta saka
daya hannun nata ta kara rike hannun sa
da ya rike nata da shi, ji take kamar za'a
saka hannu a zare mata shi, ji take kamar
in ta sake shi zai bace ya barta ta cigaba
da miserable zaman da take vi ita kadai a
rayuwar da ko kallo bata ishe shi ba. Ta
gyada kan ta da sauri gain still jiran
amsar ta yake yi.
Yayi ajjiyar zuciya "Okay. Here is the
thing. We have started on a totally wrong
foot a cikin auren mu, kuma akan wrong
feet muka yi ta tafiya har yau kuma akai
muke. I want to change our relationship.
Dan wannan da muke kai babu inda zai vi
leading din mu to sai destruction. Haka
ne?"
Ta sake gyada kai tana jin kamar a cikin
kwakwalwar ta yake yi mata maganar,
kowacce kalma ta sa tana samun guri
tana zama a cikin kanta, Ya cigaba "okay,
Tunda mun amine muna bukatar chanji
then next thing shine thing shine mu yi
letting go of the one we have tunda mun
fahimci babu inda zai kai mu sai wahala.
But before that, ni dai personally, ina so in
gaya miki cewa duk abubuwan da kika yi
min, wanda na sani da wanda ban sani ba
idan da akwai, na yafe miki. Duniya da
lahira. Kuma on the other hand, ina
neman yafiyar ki ta abinda ni navi miki
intentionally ko unintentionally" ya sake
fadada murmushin sa,"na san navi miki
abubuwa da yawa, some of them I am
even ashame of them. Ina fatan zaki yate
min, ko da ba yau ba, ko watarana ne" ta
danyi shiru tana studying, ta kasa placing
kalamansa at the exact spot da ya kamata
ta saka su. Abinda dai is clear to her shine
Muhammad ne, Habibin ta, a zaune a
gabanta hannunsa rike da nata da kuma
murmushi akan fuskar sa yana rokon ta
gafara akan abinda yayi mata, that is
more than abinda take roka a cikin
addu'arta.
Ta yi masa murmushi "a lot of things have
happened. Most of which nice na jawo
su. Kuma ko a lokacin ma in ka tuna ai ina
gaya maka cewa na yafe maka, saboda
ina sonka, na sha gaya maka ba zan iya
rikon ka a raina ba dan bana son Allah ya
kama ka a kaina" ta fada tana shafa gefen
fuskarsa da hannun ta daya, dayan still
yana rike da hannunsa. Yace "yes, da
farko kenan. Amma daga baya nayi
manyan laifuka ai, avoiding your bed,
slapping you, and the baby......... Na san it
wasn't entirely my fault but da ace ban
bari emotions dina sun rufe idona ba
maybe the accident wouldn't have
happened. Kiyi hakur'" ta sunkuyar da
kanta tana jin hawaye yana taruwa a cikin
idonta, taso cikinta kamar ranta, rashin
cikin nan was the saddest thing that has
happened to her a rayuwar ta. Ta daga kai
ta kalle shi tace"Allah bai yi da ma zai zo
duniya ba. But yanzu ka yarda cewa naka
ne? Ka yarda kai kadai na sani ban san
kowa ba?" Ya gyada kansa yana jin
zuciyar sa tana breaking ace "Na yarda.
Ko a lokacin ma na yarda. Na fadi
maganganun ne cikin bacin rai.
Kiyi hakuri" ta yi murmushi, a ranta tana
kara tabbatar wa da kanta abinda zuciyar
ta ta gaya mata tun farkon shigowar sa, ya
banbance tsakanin aya da tsakuwa, ya
gama chasing tsakuwar ya dawo gurin
ayar "na hakura" ta fada tare da ajjiyar
zuciya, tabbas komai yayi farko zai yi
karshe. "Na hakura, Allah ya bamu wasu
masu albarka" yayi murmushi yace
"Nagode sosai. This really means a lot
kuma ba zan taba mantawa ba". Suka yi
shiru suna kallon juna kowa da abinda
yake zuciyar sa, sai ta daga kanta tana
kokarin hade bakin su.
Ya dan matsa kadan sannan ya mike
tsaye. "Get your veil. Zamu je wani guri
yanzu" ta mike tana kallon sa, gabanta
yana faduwa amma bata gane ina yake
nufi ba. Basu taba fita outing as a couple
ba, maybe wani guri zai kai ta, maybe
kasuwa suyi siyayya, maybe gidan abokin
sa, maybe...…. Alot of maybes.
Sai kuma ya kalli agogon sa yace "bara
inje inyi Sallah, Ki same ni a mota", Itama
sallar tayi. Amma hankalin ta baya tare da
ita. Babu abinda take yi sai juya
maganganun sa a ranta, Amma zuciyar ta
taki barin kwakwalwar ta tayi digesting
maganganun ballantana ta fitar da amsa.
Tarin soyayyar sa ta rufe reasons a
tunanin ta.
Tana gamawa ta kara gyara jikinta sannan
ta saka mayafin ta ta gayawa mai aikin ta
cewa zata je unguwa ta dawo. A mota ta
same shi yana waya. Tana shigowa ya
karasa wayar sannan ya tayar da motar
suka tafi. Ga mamakin ta sai taji yana
mata hira a hanya, yana nuna mata gurare
da kuma bata labarin da ya shafi gurin,
har da dariya yayi mata. Sai da suka yi
nisa sannan ta gane inda suka dosa,
gidan Daddy. "Me zamuyi a gidan
Daddy?" Ta tambaye shi "zamu hadu da
iyayen mu ne muyi magana akan
relationship din mu" tayi shiru tana
digesting maganar "I thought mun gama
maganar dazu" yace
"yes, but they need
to know, ko ba haka ba?" Ta girgiza kai
"we are not kids. Bama bukatar gayawa
kowa komai akan auren mu. Besides,
Daddy ba babana bane ba. Ni baba na ya
mutu" ya juyo da sauri ya kalle ta sai ta
dauke kai gefe, bai kara cewa komai ba
dan bayan gudun kar ta fadi wata mai zafi
akan Daddy har ya kai ga mayar mata ya
bata duk shirin da yayi,
Jin bai yi magana ba sai ita ta cigaba
"baya so na, Ya zabi yarsa a kaina, Idan ya
dauke ni ya babu ta yadda za' ayi ya aura
maka Safiyya. Ya kori yaya Mustapha ma
daga gidansa after all the years da ya
dauka yana bauta masa. Bai damu da
bacin ran Mommy ba. Bai damu da mu
ba" ta karasa tana dan daga murya. Still
bai ce komai ba, har suka je suka yi
packing, kamar yadda yayi tsammani, ya
ga motar Daddy a gurin shima. Ya fito
yace mata tazo su je, ya lura gabakidaya
ta rasa composure din da ta samu sanda
suka yi magana a gida, amma sai ta samu
kanta da binsa suka shiga ta kofar waje
zuwa falon Daddy, ta ga Abba a gurin
sannan Mommy, ko kallon ta Mommy bata
yi ba, dama tunda ta koma gidan
Muhammad ko ta kanta bata bi ba ko ta
kira ta a waya bata dauka, a gurin Safina
sai take gain fushine kawai Mommy tayi
zata huce ne daga baya.
A bangaren Mommy kuwa tun ranar da
Hajiya ta gaya mata Maman Muhammad
ta turo da yan'uwan ta sun bada hakuri
sun kuma gaya mata cewa su basu san
cewa Safina tana gida ba, Muhammad bai
fada musu ba, sannan kuma sun nemi
tafiya da Safina, Hajiya taso ta hana
Safinan komawa, taso a bari a gama bikin
Safiyya sannan iyaye su hadu aji makomar
auren Safinan amma sai Safina ta dauki
mayafi ta ce ita komawa zata yi. Mommy
tayi niyyar binta a ranar ta jawo ta ko da
kuwa a kasa ne ta raba ta da gidan, amma
daddy ya hana ta, a cewar sa Safina
needs to learn on her own, idan suka
tirsasa mata rabuwa da Muhammad zata
ce su suka raba ta da shi dan basa son ta
sun fi son Safiyya. Dan haka ta ja gefe
take jira, kamar yadda sauran iyayen
suma suke jira, sai yau da Daddy yace
mata abban Muhammad yace zasu zauna
akan maganar Safina da Muhammad
sannan ta zo ta zauna din dan taga yadda
lamarin zai kare.
Muhammad ya gaishe su daya bayan
daya, sai Safina ita ma tayi haka. Daga
Muhammad din har Safinan Mommy ba ta
amsa musu ba. Suka zauna a kasa yayin
da iyayen suke akan kujeru. Sai kuma
Muhammad yaji ya rasa me zai ce har sai
da Abba yayi magana "kace mu zo kuma
kayi shiru" Muhammad yayi dan gyaran
murya yace "uhmm. Dama muni magana
ne da Safina, Mun samu fahimtar juna
kuma mun yafe wa juna duk abubuwan da
suka faru a baya, Muna so mu sake bawa
relationship din mu second chance mu ga
yadda Allah zaiyi da mu. Shine muka z0
mu gaya muku",
Sal ya ga kowa ya saki baki yana kallon
sa, har ita kanta Safinan, dan da taga
sunzo nan har ta fara sarewa akan abinda
yake shiryawa. Abba yace "Muhammad,
Look at me. Are you sure? Duk maganar
da muka yanke yanzu anan ita ce final. Ka
fahimta?" Muhammad ya gyada kai "na
fahimta Abba. Nima ba zan kira ku ba idan
har ban tabbatar da decision dina ba" ya
juya yana kallon Safina da take ta zabga
murmushi kanta a kasa.
Sai kuma ya cigaba "a ganina everyone
deserves a second chance, I mean Safina
tayi laifuka kamar yadda nima nayi, idan
har zata iya yafemin nima me zai hana ba
zan yafe mata ba? A bisa alkawarin cewa
ba zamu sake maimaita laifukan mu ba.
Misali, ni yanzu nayi alkawarin cewa ba
zan sake wulakanta Safina ba, ita kuma
tayi alkawarin cewa ba zata sake yin karya
da kazafi da munafunci ba" ya fadi haka
yana kallon Safina da ta dago tana kallon
sa ita ma yace "ko?" Ta kalli iyayen su da
suke kallon ta sai ta gyada kai, amma
hakan bai ishe shi ba sai ya sake
maimaitawa yace "kinyi alkawarin ba zaki
sake yin karya, ko kazafi, ko munafunci a
cikin auren mu ba?". Jikinta ya bata cewa
something is wrong, amma ya nannade ta
da jijiyoyin jikinta dan haka tace "eh. Nayi
alkawari" yayi murmushi "shikenan. Muna
neman a saka mana albarka mu koma
gida. But before that I just need to ask
Safina one question. Safina, did you or
did you not know cewa ni saurayin Safiyya
ne kafin ki tura picture dina blog?".
Tambayar ta zo mata a bazata, and her
whole world came crashing down on her
head. Ta dago kai tana kallon sa "what?"
Ta tambaya, a take ya maimaita mata
tambayar "did you or did you not know
cewa ni saurayin Safiyya ne kafin ki tura
picture dina blog?".
Tayi shiru tana kallon sa sannan ta fara
bin iyayen su da kallo, interestingly
gabakidaya ita suke kallo suna jiran amsar
ta, a take ta fahimci trap Muhammad ya
haka mata, already kuma ta fada a ciki,
yanzu so far bai sake ta ba saboda bashi
da wani laifin da zai makala mata yace
shine dalili, shine yake so ya binciko
wannan maganar a gaban iyayensu a
kuma sake ta saboda ita, ita kuma ba zata
bar hakan ta faru ba. Never. And she
automatically gets into her defensive
mode.
"Muna jin ki" Mommy ta fada, maganar ta
ta farko tun da suka shigo, maybe yanzu
da ta fahimci cewa sakin ta za'a yi shine
ta fara murna. Safina ta kalle ta sannan ta
kalli Abba tana girgiza kai, ta san shine
way out dinta a wajen tunda Mama bata
zo ba, ta san muhammad baya taba
kaucewa maganar iyayen sa "ni wallahi
ban san saurayin ta bane. wallahi bata
taba nuna min shi ba. Bata taba hada mu
ba" Muhammad yace "nasan wannan. Ita
kanta Piya......
.. Uhmm I mean Safiyya ta
gaya min bata taba nuna miki ni ba, kawai
dai tambayar ki nake yi ko kin taba ganin
hoto na a wayarta, ko kin dauki hoto na a
wayarta. Or something like that?"
Direct ta amsa "wallahi ban taba ganin
hoton ka a wayar ta ba. Wallahi....
"Ya
daga mata hannu, "Magana ta kare, bani
wayarki" ta juya ta kalli Mommy sannan ta
kalle shi, "waya ta kuma? Me zaka yi da
wayata?" Ta fada cikin mamaki, bai amsa
mata ba sai ya miko mata hannu, ta dauko
wayar daga cikin jakarta ta bude ta mika
masa, a ranta tana lissafin cewa in dai laifi
yake nema ya makala mata ba zai samu
ba, dan babu wani abun laifi a cikin
wayarta.
Muhammad ya fara scrolling through
tarkacen hotunan da suke cikin wayar, ba
shi da tabbas din me yake nema amma a
ransa yana jin cewa zai samu, bai san
wanne hoton bane ba and it has been
more than two years but a yasan how
obsessed Safina is with him, baya jin zata
¡ya rabuwa da hotonsa a cikin
wayarta.
Ya jima gana scrolling, yayin da su kuma
suka cigaba da kallon sa suna jiran suga
abinda yake nema. And he saw it bayan
har ya fara fitar da rai. His picture, a tsaye
a jikin motar Safiyya a cikin makaranta,
hannayensa a cikin aljihunsa. Ya na ganin
hoton ya tuna shi. Safiyya ce ta dauke su
selfie tare shi da ita. Yayi murmushi yana
tuno da yadda ta so hoton a lokacin, ya
tuna har saka shi tayi a matsayin screen
saver din wayarta for a while. Sai kuma ya
kara kallon hoton and he realized
something, hoton ya nuna cewa an dauke
shine a jikin screen din wata wayar
sannan aka yi cropping, akayi cropping
out Safiyya from the picture.
Ya girgiza kansa sannan ya mika wa
iyayen su hoton. Kamar yadda ya gane
suma haka suka gane, har da date da
time gashi nan ya fito a jikin hoton. A
hankali yace "like I said. She didn't marry
your husband, you married her boyfriend"
ta sunkuyar da kanta kasa tana jin hawaye
yana bin fuskar ta sai ya dauko takardar
da take cikin aljihunsa ya ajiye mata a
gabanta sannan yace "this is not because
of Safiyya. It is because of you, halin ki da
yanzu duk muka tabbatar ba zaki daina
ba, ba zan iya zabawa yaya na uwa mai
hali irin naki ba. Ina yi miki fatan alkhairi".
Ta daga kai ta kalle shi, yayin da shi kuma
ya mike tare da yiwa iyayensu sallama ya
fita. Babu wanda ya tsayar da shi a cikin
iyayen nasu ballantana har su hana shi vin
abinda ta tabbatar ya riga ya aikata. Abba
ne ta tashi ya dauki takardar da take
gabanta ya karanta sannan ya mika wa
Daddy sannan yayi musu sallama tare da
fatan alkhairi sannan ya fita shima kamar
yadda dan na sa yayi.
Daddy ne ya sake mika mata takardar, ta
bude ta karanta rubutu kamar haka.
"Ni Muhammad Lawan Muhammad. Na
saki matata Safina Ibrahim saki daya. Ina
yi mata fatan alkhairi".
Maman Maama✍🏻
[07/01, 10:48 pm] +234 906 816 1960: Assalamu alaikum
Gaisuwa tare da fatan alkhairi.
Naga a lot of complains din ku akan kuna
son a kara tsahon labarin Safiyya. My
initial plan was to conclude the book in
the next three episodes. A yanzu dai bana
jin zan iya kara episodes, sai dai idan zan
dauki break of like two weeks in kammala
da was muhimman abubuwan da suke
jira na idan na gama Safiyya, in yaso in na
gama su sai in dawo mu cigaba.
So, kamar kowanne littafi na, wannan
karon ma zan bawa readers damar voting
yadda karshen labarin zai kasance.
1- in cigaba bisa yadda na tsara in
kammala in 3 episodes
2- in kara jan labarin a kara yawan
episodes amma zan dauki break din two
weeks.
Ya kuka gani????
Idan 1 kika zaba kiyi reacting 👍
Idan 2 kika zaba kiyi reacting 🙏
Any other emoji is invalid vote 😀
Za'a gama voting in two days.
[07/01, 10:48 pm] +234 906 816 1960: Safiyya……
Falon yayi shiru bayan fitar Muhammad da
Abba. A hankali kuma sai sheshshekar
kukan Safina ya fara mamaye shirun.
Daddy ya sunkuyo da kansa yana kalion
ta, tana zaune kanta a kasa hawayen ta
yana diga akan farar takardar da take
hannun ta, takardar da ta yanke dukkan
alakar da take tsakanin ta da Muhammad.
Ya daga kansa yana kallon Mommy wadda
har lokacin kofar da Muhammad da
babansa suka fita daga ciki take kalla.
Fuskarta da wan irin yanayin da ya kasa
placing.
Sai kuma ta juyo a fusace tana kallon
Safina tace "zaki yi min shiru a gurin nan
ko sai nazo na shake ki kin daina
numfashi?" Bata yi shirun ba kuma bata
ce komai ba, sai ma kukan nata da ya
karu. Mommy ta mike da sauri tayi kanta
duk kuwa da maganar da Daddy yake yi
mata akan ta dakata, ta kai mata mari sai
Safina ta sunkuyar da kanta dan haka
marin ya sauka a saman kanta, sai ta
kwanta a gurin tare da kara sautin kukan
ta "dama haka kuke so ai. Gabakidayan
ku haka kuke so. Babu wanda yake so na.
Babu wanda yake son farin ciki na.
innaliliahi wa inna llaihir rajiun" Mommy ta
saka kata ta dake ta cikin dacin zuciya sal
kuma ta rike kafar tana cije baki "Daddy
ya dan daga murya cikin kokarin ganin
Mommy ta saurare shi "Sa'adatu. Kar ki
dake ta. Da me zata ji?" Mommy ta dawo
ta zauna tana rike kafarta yayin da Safina
ta cigaba da kukan ta, Mommy ta kama
fada, first time da tayi fada in days "ba ma
son ki din, na ce bama son ki din. Ya za'a
yi mu so ki alhalin ke ba kya son kanki? Ya
za'a yi mu damu dake bayan ke baki
damu da kanki ba? Da kina son kanki da
babu yadda za'a yi tun farko ki dama wa
kanki wannan salalar tsiyar. Da ba zaki
gina foundation din auren ki akan karya
da yaudara ba, da ba zaki zubar da
mutumcin ki da kimar ki a idon mijin da
zaki aura da kuma yan uwansa ba. Me
yasa ba zai sake ki ba? Me yasa iyayen sa
ba zasu goyi bayan ya sake ki ba? Me
yasa ba zai ki zabar ki a matsayin uwar
yayansa ba? Waye zai so mace mai irin
halin ki ta tarbiyyan tar da yayan sa?"
Safina ta mike zaune tace "Saboda
Safiyya ne Mommy, Wannan duk excuses
ne yake creating amma saboda Safiyya
ne, Ita ta saka shi ya sake ni.Shi ya gaya
min da bakin sa yace komai yake yi
saboda Safiyya yake y". Mommy tace
"idan ya sake ki saboda Safiyya sai me?
Ke saboda me kika aure shi? Ba saboda
Safiyya ba ne ba?" Satina ta fara girgiza
kai "ba zan iya rabuwa da shi ba Mommy,
Nina hakura zan zauna da Safiyya kuma
ba zan kara ce mata bazawara ba. Na san
akan hakan ta saka shi ya zo ya yaudare
ni ya saka nace na yafe masa sannan ya
sake ni. To wallahi ban yafe ba. Allah ya
isa na, Sai Allah ya saka min. Kuma wallahi
sai ya mayar da ni .....”.
Kuka take daga dukkan alama ma vata
cikin hayyacin ta, Mommy bata san sanda
ta mike ta sake rufe ta da duka ba. Sai da
Daddy ya danna intercom ya kira Hassan
da yake kusa sannan ya zo ya rike
Mommy wadda take ta fada a jikace, daga
ganin ta zaka gane ranta a matukar bace
yake, fadan ma da kyar take yi tana rike
kirjinta "so kike ki kashe ni Safina? So kike
in mutu ki huta tunda dama kince ba na
son ki ai. To wallahi gidan nan zaki bari. Ki
tattara ki koma gurin wadanda suka daura
miki auren tunda sune masu son ki sai su
mayar miki da auren tunda kin ce sai kin
koma, Sai in gani idan igiyar auren a
hannun su take ko a hannun ki ballantana
ku mayar da shi. Kuma wallahi kinji na
rantse, ko da yaron nan ya dawo da
kansa, in kika sake kika koma gidan sa
babu ni babu ke har abada sai dai ki nemi
wata uwar ba ni ba, kinga sai ki kara
tabbatar wa da cewa bana son ki,.…”
Hassan yayi ta kokarin rarrashin Mommy,
Yadda duk ta tayar da hankalin ta sai yake
jin nashi hankalin ya tashi. Dama daga shi
har Hussein tun ranar da Daddy ya zaunar
da su yayi musu magana akan auren da ya
daura wa Safiyya, mijin da ya daura mata
auren da shi da kuma dalilin da yasa yayi
haka suka san cewa wannan ranar zata
zo. And su babbar damuwar su da zuwan
anar shine mahaifiyarsu, suna sonta
sosai ba sa son bacin ranta kuma sun san
dole abinda ya shafi Safina ya shafe ta, su
ma kuma ya shafe su.
Cikin gida ya kama Safina ya shiga da ita
tana ta kuka da farar takarda a hannun ta.
Yana tafiya Daddy ua jawo kujerar sa
wajen Mommy yana kokarin kwantar mata
da hankali, ta girgiza kai "ba zan iya da
wannan abin kunyar na Safina ba. Katsina
zan mayar da ita gurin wadanda suka
daura mata aure ba tare da bincike ba. In
na barta a gidan nan watarana zan kashe
ta ko kuma ita ta kashe ni da bakin cikin
ta*. Ya girgiza mata kai "in kin mayar da
ita Katsina ta yaya zamuyi gyaran
tarbiyyar ta? Kina tunanin su zasu gyara
ta? Kina gani dai a gaban mu yaron nan
yay mana proving cewa akwai matsala a
tarbiyyar da muka bata. It is not too late.
We can help her" ta sake girgiza kai "ba
azo stage din da zamu taimaka matan ba
ai., A yanzu tana bukatar rayuwata fara
koya mata darasi kafin mu mu dora daga
inda rayuwar ta tsaya, The way she is
obsessed with yaron can zata iya daukan
mayafin ta ta koma gidan sa tace ta mayar
da kanta. Gwara tayi nesa da mu. Gwara
tayi nesa da shi".
Daga haka ta mike ta yi cikin gidan, ya
bita da kallo har ta shige yana jin tausayin
ta a ransa. Sunyi mistakes, gabakidayan
su sunyi mistakes, sai dai yana rokon
Allah ya basu ikon gyara mistakes din su
akan Safina da Mustapha kamar yadda ya
bashi ikon yi akan Safiyya.
Amma kuma a ransa bai ji komai ba gane
da sakin Safina da Muhammad yayi,
yanajin cewa hakan shine mafi alkhairi a
gare su baki daya. Zama da wanda ba ka
so ba karamin ciwo ne da shi ba, and
zama da wanda baya son ka is even more
painful.
Sai ya dauki wayarsa, yana lura da yadda
numfashi yake kara yi masa nauyi a cikin
kwanakin nan, and for the first time in
weeks yay dialing number din Mustapha.
Yayi nazari sosai akan case din Mustapha
da Safiyya, ya fahimci cewa Mustapha
yana da laifi kamar yadda su ma shi da
Sa'adatu suke da laifi a cikin lamarin.
Bata jima tana ringing ba Mustaphan ya
dauka, a hankali yace "Daddy" sai kuma
yayi shiru, Daddy ma yayi shirun, har
lokacin yana jin zafin abinda Mustaphan
yayi kokarin yiwa tilon yarsa, amma kuma
shima Mustaphan yana jin sa a ransa
kamar shi ya haife shi. "Ka zo gida...
Daddy ya fada "kazo gida akwai maganar
da zamu y". Daga haka ya katse kiran.
Sai bayan da yayi sallar magrib aka bashi
abinci yaci sannan Mustapha ya zo gidan.
Yayi sallama ya shigo dakin amma sai ya
tsaya a bakin kofa kansa a kasa yana
kallon kafafuwansa. Daddy ya bishi da
kallo, yayi baki, duk ya kara bushewa, duk
babu gayu da daukan wankan nan.
"Zo nan" Daddy ya fada masa with
authority, half expecting him to turn
around ya koma shima yace ai Daddyn ba
babansa ba ne ba kamar yadda Safina ta
fada dazu, amma sal ya ga ya taho din, ya
2o ya zauna a gabansa a kasa sannan
yace "Daddy barka da yamma" Daddy
yayi shiru yana studying dinsa. Tun yana
shekaru goma yake hannunsa, yanzu
gashi yana neman cike shekaru talatin a
duniya, and through all those years, ba
zai ce baya yi masa laifi ba tunda ya san
ko yayan da ya haifa suna yi masa laifi,
amma abinda ya sani shine yana yi masa
biyayya.
"Ina so muyi magana da kai. Ina so kuma
in na gama maganar ka bani amsar abinda
ka fahimta a maganar tawa da kuma
abinda kake tunanin zaka yi a matsayin ka
na babban da a gidan nan".
Sai ya bashi labarin komai akan alakar da
take tsakanin Safina, Safiyya, da
Muhammad. Ya ga alamar ran Mustapha
ya baci "ni ba haka ta ce min ba Daddy,
ba haka Safina ta gaya min ba. Cewa tayi
min a gurin dinner dinta suka hadu kuma
tun daga nan suke in a relationship, tace a
wayar ta ma Muhammad din ya dauki
number din Safiyya" Daddy ya daga
kafada yace "karya ta yi maka.
Tana da karya sosai tun yarinta har karyar
ta zama habit din ta, Yanzu ma akan halin
ta na karya ne mijin ta ya sake ta" suka yi
shiru sai Daddy ya kara da cewa "me kake
tunanin za'a yi akan lamarin ta?"
Mustapha ya danyi tunani sannan yace
"ta ce kowa baya son ta har Mommy. A
barta ta je Katsina ta kwana biyu sai ta
gane ma'anar so din, zata dawo da
kafafuwan ta za kuma ta gane gata ake yi
mata. Yanzu idon ta ya rufe da soyayya ba
zata ji reasons ba. Sannan aje a kwashe
kayanta daga gidan Muhammad as soon
as possible, dan a tabbatar mata da cewa
ba zata koma ba. Duk randa Allah ya sa ta
dawo daga Katsinan ta kuma gane
gaskiya sai ayi mata afuwa a karbe ta, a
kuma mayar da ita makaranta ta karasa
karatun ta. Hakan zai taimaka mata wajen
moving on. Hakan kuma zai bude mata
kofar wasu chances din".
Daddy yayi shiru yana kallon sa. Sai kuma
yayi ajiyar zuciya. Shi bai fiya son
tarbiyya ta hanyar horo ba, ya fi gane
tarbiyya ta hanyar soyayya da kuma jan
yaro a jiki. Amma kuma kamar sun fi shi
gaskiya. She needs to learn her mistakes
by herself. Amma kuma yana tsoron kar a
hure mata kunne a can, kar maimakon
gyaruwa ta kara lalacewa a can. Amma sai
kawai ya hakura, "Okay. Shikenan. Allah
yasa hakan shi ya fi alkhairi. Ta shi kaje".
Sal dal kuma sai Mustaphan ya kasa tashi
ballantana ya tafi din. Ya cigaba da zama
idanunsa a kasa, "Daddy " ya ambata tare
da dago kai yana kalion Daddy, "Daddy
ban san abinda nayi ba. Ban san abinda
aka ce nayi ba, Daddy ko me nayi dan
Allah kayi hakuri",. Daddy ya sake yin
shiru, ya riga ya yafe wa Mustapha abinda
yayi din, amma har yanzu yana jin zafin a
ransa musamman idan ya tuna cewa da
ace Safiyya ta yarda, maybe da matarsa
kawai zai mayar da ita a gidan har sai
randa asiri ya tonu. Ya dauko wayarsa
yana danne danne har ya binciko video
din da ya riga yayi saving. Sai ya juya
wayar ya nuna wa Mustapha. "Dan taya ni
ganin wanna video din".
Mustapha ya karba a ransa yana tunanin
ko menene, sai yaga abinda bai taba
tsammani ba, ya kuma ji abinda bai taba
tsammani ba. Cikin sauri ya danna power
din wayar ya katse videon tare da kashe
wayar gabakidaya, as if yin hakan zai
goge maganar daga memory din Daddy.
Sai kuma suka yi shiru, Mustapha yana
fatan kasa zata tsage ya shige cikin ta.
Daddy yayi magana "ka bani mamaki
Mustapha. Har bragging nake yi cewa ba
ni da matsala da kai. Har kokarin tursasa
yarinyar nan ta aure ka nayi ina ganin
kamar kai ne kafi kowa dacewa da ita. Ka
gaya min idan da akwai wani laifi da nayi
maka da zaka yi min wanna cin mutuncin
a cikin gida na. Ka gaya min" ya karasa
yana kokarin daga muryarsa da bata
fitowa sosai. Mustapha ya san da Daddyn
da ne da yanzu maybe jikinsa yayi tsami,
Amma sai ya kasa daga ido ya kalle shi, to
da wanne idon zai kalle shi ma? Instead
sai ya fara girgiza kansa, amma kuma
bakin ma ya kasa yin motsi ballantana ya
bada hakuri, to mai zai ce masa? Wannan
wanne irin abin kunya ne haka. Ya lura da
video din cctv ne, ya kuma fahimci cewa
ba Safiyya ce ta tona masa asiri ba.
Kamar yadda ya fahimci cewa ba kwace
mijin Safina tayi ba. Ya fahimci Safiyya
bata da laifi, sai ma tarin kaddarori da
suka yi ta saukar mata one after the other.
And he didn't do anything to help her
matters at all.
Daddy ya cigaba da magana "ita Safiyyan
da kayi kokarin zalinta, ita ce mai roko na
kullum akan in yafe maka in dawo da kai
gidana, tace ba ka da wani gida sai
wannan. Yace nan ne gidan ku. Amma kai
ba ka dauke ta kanwa ba. Da ka dauke ta
kanwa da ba zakayi niyyar aikata mata
wanna mummunan abin ba" Mustapha
yayi magana at last "Daddy ba yanzu ba
ne ba wallahi. Wallahi ba yanzu bane ba.
Dan Allah ka fahimta Daddy. Ban san me
zance maka ka fahimta ba. Wallahi nayi
nadama tun dadewa, Dan Allah Daddy
kayi hakuri" shiru Daddy yayi sannan yace
"a hakura ai, Da ace ban hakura ba da ko
gate din gidan nan ba zaka sake gani ba.
Yanzu ka debo kayanka ka dawo dakin ka.
Sannan ka ajiye wannan girman kan ka je
ka karbi aikin da Safiyya ta baka. Ka kuma
hada kan kannenka ka rike su ka gyara
tsakanin su. Sannan ka kula da mahaifiyar
ka. Tashi ka tafi".
Mustapha ya mike, not knowing what to
think, ya kusa fita Daddy ya kira sunan sa,
ya juyo amma still bai kalli Daddyn ba sai
yace "kuma ka samo mata kayi aure. As
soon as possible".
A bangaren Muhammad tun sanda ya fita
daga gidan sai ya dauki hanyar gidan su,
ya san dole yana bukatar suyi maganar
shida iyayen sa, amma kuma hankalin sa
gabakidaya yana kan Safiyya da ya bari a
gida. Bai jima da yin packing a gidan ba
Abba ya shigo shima. Sai ya jira shi yayi
packing sannan suka shiga cikin gidan a
tare, Kamar yadda suka yi tunani Mama
tana ta akin jera musu abincin dare, tayi
wa mijin nata sannu da zuwa sannan ta
juya ta na kalion Muhammad da ya
sunkuyar da kansa kasa yana shafa
gashin kan sa, ta san akwai magana. Ya
gaishe ta amsa tare da tambayar sa
lafiyar Safiyya da kuma Safina "lafiya lau"
kawai ya amsa mata yabi bayan Abba
suka fara shirin alwalar sallar magrib.
Bayan ya gama alwalar ya kira wayar
Safiyya, tana ta ringing bata dauka ba.
"damn it" ya dan fada a hankali. Sai ya
tura mata message "Babe ......... call me
please" sannan ya bi bayan Abba suka
tafi masallaci. Suna fita waje Haidar yana
shigowa, shima sai yabi bayansu suka tafi
tare.
Bayan sunyi Sallah ya dauka zaman ba zai
yi tsaho ba, amma sai yaji magana ta
mika, Abba ne yayi wa Mama bayanin
abinda ya far da kuma hukuncin da
Muhammad din ya yanke, "Allah ya sa
haka shi yafi alkhair'" kawai tace tare da
tashi ta fara zubawa mijin na ta abinci. A
ranta tana jin feelings dinta blank akan
abinda ya far, a wani bangaren ma
godiya tayi ga ubangiji da yasa babu rabo
a tsakani, tana kuma fatan wannan ya
zamo karshen wahalar dan nata a
bangaren aure, ya samu nutsuwa shima
ya samu farin ciki, ko burinta zai cika na
ganin ya zama abin alfahari ga kowa.
Ta zubawa Muhammad abincin shima, ya
dauka ya fara ci yana ta kallon agogon
hannunsa, da sauri ya cinye abincin yana
son yayi musu sallama sai yaji sun dauko
wata maganar kuma. Maganar sabon aikin
da ake nemawa Haidar da kuma filin da
aka siya masa za'a fara gina nasa gida,
Abba so yake Muhammad ya tsaya akan
abin sosai dan shi ba zai samu dama ba.
Sai kuma maganar tafiyar da Abba da
Mama zasu yi Abudabi nan da next week
dan su huta saboda sun sha hidima
kwana biyu sun gaji. Haidar ya fara
tsokanar su cewa da shi zasu yafi, wai a
hannun wa suka barshi? Tunda
Muhammad da Mufida suna gidajensu.
Har yana cewa wai honeymoon su Mama
zasu tafi. Mama ta rankwashe shi akai "ka
koma gidan su Baffa idan ba zaka zauna
anan ba" ya girgiza kai yana kallon
Muhammad "ni na san inda zanje"
Muhammad ya bude ido "kar kace gida
na. Bani da space" Abba yayi dariya "kaji
fa Haidar. Wato wasa tare ci banban. Yar
shinkafar da zasu sammaka a gidan su ita
ce zai yi maka rowa" Haidar ya kai lomar
abinci yace "kuma ni ba ma cin abinci ne
dani sosai ba. Dan kadan ya ishe ni"
Mama tayi dariya "wa yaga rijiya gaba
dubu. Ai ina bayan Gidado, a cikin sati sai
ka talauta su. Duk kayan garar nan sai ka
cinye tas" Haidar ya bata rai "dama ai na
san matsayina a gurin Mama, dadin ta ma
Abba yati so na" Muhammad yace "a'a,
Abba yafi son Mufida", Dariya suka cigaba
da yi suna hirar su, a karshe dai bayan
Haidar yayi kamun kafa da Mama sai aka
yarda cewa zai je gidan Muhammad din,
Sai bayan sallar isha sannan Muhammad
ya samu ya zame daga gurin family dinsa
ya dauki hanyar gida, ya kira number din
Safiyya yafi sau adadin da zai tuna amma
taki dauka, babu irin abinda baya saka wa
a ransa, zuciyar sa kuma tana gaya masa
cewa tana can tana kuka tana tunanin ya
tafi gurin Safina ne. Ai kuwa abinda ya
tarar kenan sanda ya shiga gidan ya kuma
wuce directly har bedroom dinta.
Tana zaune akan gadon ta ta juyawa kofa
baya ta kifa kanta akan cinyoyin ta. Ya
tsaya a bakin kofa yana kallon ta, ya san
tana da kishi sosai, shi kuma kishin nata
burgeshi yake yi most of the times, yana
kara tabbatar masa da soyayyar ta a gare
shi, amma kuma baya son wannan kukan.
Ya danyi gyaran murya sai ta dago kai da
sauri ta juyo ta kalle shi. Ya ga relief a
fuskar ta sosai.
Amma kuma sai ta sake juya fuska ta
daina kallon sa, jan aji, ajin Safiyya yana
daga cikin abinda yake kara masa sonta a
kullum, Ya karasa gabanta ya tsaya yana
kallon ta da murmushi a fuskar sa, idanun
ta har sun kumbura saboda kuka, yanzun
ma kuma hawayen ne yake kara bin
fuskarsa
Wani abu da Safiyya take kara burgeshi
da shi shine tun da suke bata taba yi
masa maganar Safina ba tun zaman da
suka yi suka yi maganganu, duk kuwa da
cewa ta san tana da power akan sa, tana
da power din da in ta matsa zai iya sakin
Safinan ko da kuwa bai yi niyya ba.
Musamman yanzu da yake kara susucewa
akan ta. Ya san da ace table din a juye
yake, da ace Safina ce take da power din
Safiyya, da baya jin zasu yi kwana daya a
matsayin kishiyoyi. "Piyyyya" ya kira
sunanta da wani yanayi "wai kukan
menene kuma haka. Kin san yadda
hawayen ki suke yin zafi a cikin zuciya ta
kuwa?" Ya durkusa a gabanta yana
kokarin kallon cikin idon ta. Ta sake dauke
kai gefe "ni ka rabu da ni" ta fada cikin
shagwaba, "Ni ba zan rabu da ke ba" ya
fada yana kwaikwayon ta. Ta watsa masa
harara da kumburarrun idanunta, Yayi
dariya sannan ya zauna a gefen gadon a
kusa da ita yana kokarin rike hannun ta, ta
hana shi tana kokarin tashi tsaye still
hawaye yana bin fuskarta. "Wait Babe…
Ki tsaya muyi magana mana, Ki tsaya inyi
miki bayani, ki tsaya in gaya miki abinda
ya faru a can din da naje" ta juyo a fusace
cikin kuka "bana son jin abinda ya faru a
can. Bana son jin abinda kuka yi a can"
sal abin ya bashi dariya.
Ga mamakin sa sai gani yayi ta dawo
kansa ta tura shi baya da karfi ya fada kan
gadon a rigingine, ta kama kokawa da
tazugen wandon sa "abinda ya faru a can
shi zai faru anan ma. Ni ma ai zan iya. Duk
abinda tayi maka nima zan iya yi maka"
dariyar yake yi sosai yana kokarin rike
wandonsa amma sai da ta cire masa ta
zare shi daga jikinsa ta bar shi da gajeren
wando, sai kuma ta haye kan cinyoyin sa
ta zauna sannan ta fara kokawar cire tata
rigar "nima ina da shi ai, duk abinda take
da shi ina da shi. Kuma zan iya. Zan koya
nima' ta cire shirt din jikinta ta jefar, ta
bar jikinta daga ita sai lacy brar da ta kan
saka idan zata yi bacci.
Shi dai dariya yake yi "wait Piya, what are
doing ne wai? Ki tsaya in gaya miki abinda
ya far" ta jawo hannayen sa ta dora su
akan kirjinta "abinda ya faru a can shi zai
faru anan ma" ya dan rage dariyar sa tare
da kokarin mikewa zaune, sai kuma
sauran dariyar ta tsaya a kirjinsa ganin her
almost naked flesh a kusa da fuskar sa,
she looked very breathtaking with
gashinta a hargitse ya sauko gefen
fuskarta, idanunta a kumbure, fuskarta
tayi ja, bata damu da kalion da yake mata
ba ta fara balle buttons din rigarsa sai
kuma ta fara jan rigar da niyyar cirewa, ya
rike hannunta yana kokarin saisaita
numfashin sa da emotions dinsa, still da
sauran dariya a muryar sa "ki bari mana
Babe. Nothing happened na rantse miki"
"ban yarda ba" ta fada tana cigaba da jan
rigar tasa daga kasansa amma ta kasa
"Allah ban yarda ba" ganin ba zata tsaya
ta saurare shi ba sai ya kamo fuskarta da
hannu daya ya hade bakin su.
Hannayen ta da ta daga da niyyar cigaba
da jan rigar su ta sauke a hankali akan
kafadarsa tare da zagaye kafadar da su
tana kara jawo shi jikinta tare da sauke
ajiyar zuciya. Ya danyi murmushi a ransa,
ita ce mai ce masa wai shi ya fiya son kiss
amma kuma a cikin kwanakin da suka fara
learning the art of kiss ya fahimci tana so
ita ma sosai, kawai dai tana jan aji ne shi
yasa bata fada.
Sai da ya tabbatar ya dawo da nutsuwar
ta gare ta sannan ya raba bakin sa da
nata, yabi lips din nata da kallo yana ganin
yadida suka kara yin ja sannan suka kara
zama fresh, baya gajiya da kallon su
kamar yadda a yanzu yake kara tabbatar
wa da kansa cewa baya gajiya da tasting
din su,. Ya daga idanunsa a hankali ya
sauke su akan nata da har lokacin suke a
lumshe, ta bude su a hankali a cikin nasa,
sun jima suna kallon juna sannan yace
"nothing like this happened between me
and her. Nothing like this ever happened
between me and her.
I couldn't do it, because I love you, and
because she is related to you" a idonta ya
ga alamar ta yarda da abinda yace, duk
da dai akwai alamar tambaya, ya san
kuma tambayar dan haka ya bata amsa
"she put desire pills in my tea kettle one
night, that was how she got pregnant, ba
wai da son raina ba ne ba" ya cigaba da
kallon cikin idanuwanta, ya ga relief sosai,
more than yadda ma yayi tunani, ya
fahimci abin have been weighing on her
mind kawai dai soyayyar sa ce ta danne
komai. Sai kuma ta rungume shi da sauri
tare da kife fuskar ta a kan kafadar sa, ya
saka hannun sa daya yana shafa gashin
kanta dayan kuma yana shafa naked
bayan ta down to the rim of her skirt. "I
love you" ta fada a hankali da karyayyiyar
murya, "I love you so much" ta kara fada
da muryar daya tabbatar tare da hawaye
ta fito,
Ya danyi murmushi tare da lumshe ido
yana Jin kamar zuciyar sa tana kumbura a
kirjinsa da soyayyar ta, "I love you too" ya
tada a hankali. Sun dan jima a haka
sannan a hankali ya fada mata cikin
kunnen ta "I divorce her" yaji ta rike
numfashin amma bata dago ba, ya kara
maimaita mata "I divorce her. Na sake ta.
That was what happened da na fita.
Abinda naje nayi kenan" ta dago kai daga
kafadar sa tana kallon sa da budaddun
idanunta, ya saka hannu yana kara gyara
gashin ta da ya yi framing fuskarta. "I am
no longer married to her",. Still ta cigaba
da kalion sa bata ce komai ba. Ya saka
hannu ya rike habarta yace "now smile".
Ai kam a take murmushi ya bayyana a
fuskar ta, sai taji kunya kuma ta kara cusa
fuskar ta a kasan wuyansa, dariya yayi
itama sai tayi dariyar sannan ya jata suka
yi baya suka fada kan gadon shi yana
kasa ita tana kwance akan kirjinsa. Ya
mintsini gefen cikin ta, ta fara kokarin
zame wa sai ya kara rike ta "Babe ko
kunya babu? Babu dan kawaicin nan ma
shine kike dariya ko?" Ta juyo tana kallon
sa fuskarta dauke da annuri, duk tarin
damuwar da ya gani a tare da ita sanda ya
shigo ta gushe, ta juya idonta "ba zanyi
alkunyar ba, Is it a crime dan bana son
raba mijina da kowa? Musamman da
wadda nake kalla a matsayin yayata?
I Wish her well, duk kuwa da abubuwan da
tayi min bani da nufin sharri a gare ta, ina
yi mata fatan alkhairi, ina yi mata fatan
samun miji na gari wanda zai so ta ya kula
da ita, but not my husband. Not at the
expense of my own happiness"
Yayi murmushi yana shafa fuskarta, tare
da jin cewa ita matar rufin asiri ce, matar
da zata iya danne damuwarta dan farin
cikin mijinta. Amma shi baya fatan saka ta
damuwar ko da nan gaba ne.
Ta shagalta da kallon sa bata san sanda
ya saka hannu ta bayanta ya balle hook
din brar da take a jikin ta ba. Ta danyi kara
tare da zaro ido tana kallon sa, yayi juyi ya
mayar da ita kasa sannan ya tashi tsaye
yana karasa cire rigar da ta fara cire masa
"let's finish what you started. Dama kince
kin iya ko?" Ta fara girgiza kanta tana
dariya "ni ba haka nace ba, baka ji dai dai
ba" ya cije lips dinsa yana jan skirt din
jikinta irin yadda tayi masa "naji komai,
har da cire min wando ko? In ma banji ba
yanzu zaki maimaita min inji" ta mike
zaune da sauri tana kokarin rike skirt
dinta, hakan ya bayyanar da kirjinta sai ta
koma ta kwanta da sauri tana rufe kirjin
da hannayen ta tana dariya sosai "ka
bari...…. Allah ka bari ......" Bai bari ba sai
da ya zare skirt din yayi jifa da shi irin
yadda tayi wa wandonsa. Lacy pant dinta
ya bayyana dan uwan brar, ta kifa da sauri
ta koma rub da ciki a kokarin ta na boye
jikinta, tana dariya tana bubbuga
kafafuwan ta a kan gadon "Dan Allah ka
bari Yay Muhammad".
Bai bari ba, dan abinda ya gani ba zai
barshi ya bari din ba, He thought her
some lessons, kamar yadda shima ya koyi
wadansu daga gare ta. Kamar dazu da
safe, sun yi yawo sosai tare da junan su a
sararin samaniya, kuma kamar dazun,
bata gayyace shi zuwa duniyar ma'aurata
ba shima kuma bai matsa mata ba duk
kuwa da matsuwar da yay da son kai
ziyara can din. Sai dai ya fahimci wani
abu, kusan kashi saba'in na tsoron abin
da take ji ya ragu.
Sai da suka tsarkake jikin su har ta saka
kayan baccin ta sannan ya jefa mata hijab
dinta, ta juyo tana kallon sa ta ga jallabiya
ce a jikinsa da dogon wando, "gurin
Daddy zamu je" tayi sauri ta kalli agogo,
15 minutes after 9, tunda taga isha tayi ba
su je ba sai ta saka a ranta cewa yau ba
zasu je ba, Ya daga kafada "munyi
alkawarin zuwa kullum. Maybe ma yana
can ya kasa kwanciya yana saka ran
zuwan mu", Cikin murna ta saka hijab din
akan kayan baccin ta suka tafi. Yana daga
cikin abinda yake kara mata son
Muhammad, yadda yake damuwa da duk
abinda ya shafe ta. Da yake dare ne babu
traffic dan haka basu jima ba suka je.
A zaune kuwa suka tarar da shi akan
kujerar sa, har kayan bacci an saka masa
amma bai kwanta ba, idonsa akan hanya.
Tana shiga murmushi ya bayyana akan
tuskarsa ya mika mata hannu, ta karasa
da sauri ta rike hannunsa sannan tayi
kissing cheeks dinsa "daddyna" ta fada
cikin shagwaba. Muhammad ya cigaba da
tsaiwa a bakin kofa yana kallon su,
fuskarsa dauke da murmushi…....
Daddy ne da kansa ya ce mata kar ta
shiga cikin gidan a ranar ta bari sai gobe
tukunna, maganar da Muhammad ya gaya
mata dazu ya saka ta fahimci Safina tana
ciki kuma Daddy baya son su hadu a
yanzu. Kafin ta fita dai daga gidan taga
twins, su suka raka su har mota sannan
suka gaya mata maganar da ta saka ta
farin ciki "Yaya Mustapha ya dawo dazu.
Daddy ne ya dawo dashi, Yanzu ma yana
dakin sa yana gyara kayansa". Amma
basu yi mata maganar Safina ba kamar
yadda ita ma bata yi musu ba.
Her🧕🏻
Washegari da safe na tashi ina jin zuciya
ta fara kal, haka kawai nake jina cikin
nishadi, Ranar da wuri na tashi ban yi
dogon baccin da na saba yi kwanan nan
ba. Muhammad tun da ya fita da assuba
bai dawo dakin ba da na kira shi a waya
sai yace min yana gym. Ban sani ba ko
rashin jin dumin jikin sa a tare da nine ya
saka na kasa baccin? Na dauko waya ta
na tura wa mutane message din godiya
da ban gajiyar biki. Wadansu kuma na kira
su, musamman kawayena da suka zo
daga nesa, na kira matar Abdul ita ma, ita
ce take gaya min cewa washegari zasu
koma Berlin, Amma sai na kasa kiran
Aunty Hajjo, sai na tura mata message
kawai,
Na kira Mommy itama, muka gaísa sai
take ce min zata je Katsina, ban tambaye
ta me zata je yi ba sai nayi mata fatan
alkhairi tare da tambayar ta ko tana
bukatar wan abu, bata nuna min tana
bukatar komai ba amma muna gama
wayar na tura mata kudi. On impulse sai
na tura wa Mustapha message shima
nace masa job offer dinsa tana nan a duk
lokacin da yake bukatar ta, Ba'a jima ba
yayi min reply "zan je Katsina, in na dawo
we will talk about it" nay murmushi kawal
Sai kuma na kira Hajiya, anan muka jima
muna hira har kyalkyala dariya nake yi,
tana ta tsokana ta wai aure ya saka murya
ta ta kara zaki, wai ko sukari mijin yake
bani ina sha kullum,. Sai kuma ta sake yi
min doguwar nasiha akan zaman gidan
miji, kula da mijin da yan'uwansa da kuma
kula da addini, ta kuma gaya min xewa
Mommy ta gaya mata abinda ya faru da
Safina, sai ta ja kunne na "babu ruwanki.
Tsakanin ki da mijinki daban tsakanin ki da
su Sa'adatu daban. Kar ki tofa albarkacin
bakin ki. Kiyi ta addu'a Allah ya daidaita
lamarin" ta bani shawarwari masu kyau
kuma na saka a raina cewa zan dauka. A
karshe nace mata "Hajiya ina ma zaki
yarda ki dawo gidan nan. Tunda can din
da kike babu kowa sai ke kada'" tayi
murmushi tace "ban taba zama ni kadai
ba Fiyya. Yara uku ne yanzu haka a gaba
na. A hakan ma na gode da kulawar ki
gare ni. Kawai dai ki ringa zagayowa
lokaci zuwa lokaci muna gaisawa. Kuma
duk abinda kike bukata ki kira ni ki gaya
min baki da shamaki", nayi mata godiya
sai kuma na tuna da zancen yan akin da
nake so dan haka nayi mata, na gaya
mata guda biyu ko uku nake so masu
hankali, sai kuma maza guda biyu, tace
min mazan in yiwa Muhammad magana
shi ya kamata ya samo mana, idan kuma
ace ta samo shikenan already akwai
wasu da 2tace min nan da next week
za’a kawo minkwararrun da zasu yi
keeping min gida spotlessly clean,
Har nayi niyyar kiran Umma sal na fasa,
na dau tura wa Salima message tare da
sauran kawayena. Daga haka na tashi na
gyara dakin Muhammad tas na kunna
turaren wuta na gyara toilet din shima, sai
na koma nawa dakin na gyara shi shima
na saka turaren wuta tare da different
varieties of room fresheners sannan na
shiga toilet nayi wanka na fito na shafa
mai ina lura da yadda fata ta take kara
wani sheki na musamman da ba zan tya
cewa ko na menene ba, na saka wata
doguwar rigar da aka dinka min da
atampa amma tsahonta da kadan ya wuce
guiwa ta, ta kuma bude sosai daga waist,
armless ce bata da hannu sai kafada
kawai. Na gyara fuska ta nayi kwalliya mai
kyau, sai nay packing gashina a tsakiyar
kaina da dankwalin atampar na barshi ya
sauko zuwa wuya. Na feshe jiki na da
turare sosai sannan na fito daga dakin na
sauka zuwa first floor, na shiga gym din
Muhammad na tarar da shi yana kokarin
fitowa, kida yana tashi kadan kadan a
cikin gurin. Na tsaya ina kallon sa cikin
fararen track suit masu black strips. Yayi
min murmushi yana bina da kallon
appreciation yace "you look like a Barbie"
na danyi juyi a gabansa tare da bowing
irin gaisuwar turawan ingila nace "good
morning" ya karaso inda nake yana goge
fuskar sa da hanky yace "Baby..... Good
morning Baby zaki ce" na juya ido na
"naki din" ya langwabe kai "Please" sai na
lakuce masa hanci na wuce shi ina
dudduba kayan wajen. Ya biyo ni a baya
"wanne zaki fara using?" Na bude ido
"Allah ya tsayi gatari da saran shuka, so
kake inyi irin wannan?" Na fada ina nuna
arms din sa da suke a mummurde, yayi
murmushi "no, you will not. In dai har ba
extreme kike ba. In dai ba lifting weights
kike yi ba ba zaki yi muscles ba, kawai
treadmill zaki ke hawa, zai kara miki lafiya
ya cire miki kasala, ya yi improving mood
din ki, ya saka ki bacci mai dadi, ya......" Na
saka hannu na rufe masa baki "thank you
coach, but I am not interested" ya dan ciji
hannun nawa nayi sauri na cire "ouch" sai
ya matso ya rungume ni ta baya ya rada
min a kunne na "zai kuma hana ki yin
kiba" na dago kai ina kallon sa sai ya
kashe min ido, ya san lago na, tun a
makaranta ya san bana son kiba amma
kuma ina son cin abinci, na juyo ina
fuskarta sa nace "okay you win. Zan ke
zuwa ones a week" yace "three times a
week" nace "two times a week" yace
"deal, Now let's start" nayi sauri na zame
nayi gaba "ba yau ba fa. Sai dai gobe" ya
biyo ni ya jawo ni jikin sa yana shanshana
gashin kaina "hmmm. ba ki da gaskiya.
Guduwa zaki yi ko?" Na juyo ina kallon sa
sai ya mayar da fuskarsa wuyana "hmmm.
Kamshin ki dad" na ture shi ina dariya "ka
tafi ka je kayi wanka" ya sake jawo ni yana
langwabe kai "ki zo kiyi min" na bude ido
"ka ga girman ka kuwa?" Yace "sai in
sunkuya" na bude hannu na "a nawa zan
yi maka wankan?" Ya kama hannun tare
da kissing tsakiyar tafin hannun Yace
"anything. Zan biya price mai kyau". Na
kama hannunsa "okay. Muje in yi maka"
muna fita na saki hannun na tafi a guje na
shige kitchen na rufe kofa. Ina jin sa yana
dariya sannan naji ya hau sama.
Na dan jima ina kallon kitchen din nawa
ina jin dadi a raina. Na shafa worktop din
tare da deciding cewa ranar zan fara girki
a gidan. Sai dai ban san yadda zan
gayawa Mama cewa ta daina aiki mana da
abinci ba. Na san haka alama ce ta
soyayya amma nima ina son in fara girki a
gida na
Na fita na tafi dinning, already kuwa har
an kawo abincin Esther ta gyara gurin ta
jera, na bude sai na ga kosai, naji dadi
sosai dan na dade ban ci kosal ba. Sai
kunun madara da akayi thickening da
plumbs, Daga nan kuma sai farfesun
kayan ciki, ina bude shi naji kamshi mai
dadi sai nayi deciding zan ci, dan ni in ba
ni nayi farfesun kayan ciki ba bana iya ci
amma wannan zan ci. Na ga Esther kuma
tai mana nan bread din da zaiyi going
well with the pepper soup.
Komawa nayi kitchen na dafa mana tea,
nazo na zauna na cigaba da replying
congratulatory messages din da ban
samu damar budewa ba har Muhammad
ya gama ya fito, muka ci abincin tare ina
mamakin yadda ya ci kosan sosa dan ban
taba tunanin yana ci ba, sai kuma na fara
tsokanar sa da cewa dan fillo ne shi.
Nayi masa maganar ko zai gayawa Mama
ta huta da yi mana girki haka sai yace
babu ruwansa sai dai ni in gaya mata, sai
na bar maganar nima, Amma a raina nayi
deciding abinda zanyi,
Ranar ma a gida muka wuni. Sai magrib
muka fita muka je gaishe da Daddy, Na
tarar Mommy da Mustapha da Safina sun
tafi Katsina, sal twins ne a tare da Daddy,
Naji kamar in zauna sal ya gaya min
washegari zasu dawo, kwana daya suka
ce zasu yi, In almost total silence muka
koma gida, ban san me yasa muka yi shiru
din ba bayan kuma shiru shine last thing
da mu kan yi idan muna tare, haka yayi
driving da hannu daya, hannun sa dayan
rike da nawa, ki da yana tashi kasa kasa a
motar. And I found myself thinking "why
not tonight?" Amma kuma zuciyata tana
karkarwa with the thought,
Haka muka je gida, haka kuma muka
shiga ciki muka hau har second floor, in
silence but hand in hand. Sai da muka
gama hawa muka tsaya a dan corridor din
da ya raba dakin sa da dakuna na sannan
ya juyi da ni yana kallon cikin ido na yace
"you will come, right?" Na dan gyada kai
na kadan amma ban kalle shi ba sai ya yi
kissing hannuna yace "I will wait" sannan
ya juya ya tafi dakin sa.
Nawa dakin na shiga na ciye kayan jikina
na shiga toilet nayi wanka tare da duk
sauran shirye-shiryen bacci, na fito nayi
sallar, asking God for courage and
strength din da na san bani da su sannan
na rufe dakina na tafi na sa.
A kwance na tarar da shi a kan gado
sanye da kayan bacci, ya kashe fitila
except for the bedside lamp din da ta
haska min shi. Na cigaba da tafiya a
hankali wat zuciyar already tana gaya
min in juya in koma dakina in rufe kofa,
Amma ban biye mata ba sai na je na
zauna a gefen sa kafafuwa na a kasa ina
kalion sa. Na fahimci ba bacci yake yi ba,
idon sa biyu, amma bai bude idon ba ya
cigaba da kwanciya a haka.
Na saka hannu na na dama a hankali na
shafa sumar kansa ina jin laushin ta a
hannu na idanuna akan fuskarsa, fuskarsa
doguwa ce amma ba sosai ba, tana da
dan fadi kadan, wanda ya kara mata cika
da kwarjini. Na jawo hannun da ga cikin
gashin kan zuwa sajen da ya zagaye ya
kuma kawata fuskar, a hankali ya bude
idanunsa ya sauke su a kaina. Muka
cigaba da kallon juna through the dim
light of the coloured bedside lamp. Na
matso da fuskata dai dai ta sa sannan na
lumshe ido na na dora lips dina akan nasa
a hankali kamar mai tsoron ta ba wuta.
it started lightly kamar an kunna ashana,
and then grow like a wildfire da ta fara cin
bodies din mu baki daya. Hannu daya ya
saka ya daga ni ya hawo dani kan gadon
sosai sannan ya juye ya mayar da ni zuwa
¡kasan sa. Sanda na kara sanin inda nake a
lokacin na fahimci na rasa kayan jikina.
lokacin da ya raba jikin sa da nawa na
some seconds, da ya dawo sai na fahimci
ya rasa shima nasa kayan. A lokacin ne
kuma fear din ta dawo, the memory of
that night, the pain, the fear, the….... Na
fara ture shi cikin kuka. "No. ..... Stop.....
Dan Allah....... Please........." Gabakidaya
jiki na karkarwa yake yi.
Farko kamar bai ji me nake cewa na, daga
baya kuma sai ya sake ni sannan ya
kwanta a gurin yayi shiru yayin da ni kuma
na ja jikina zuwa karshen gado na takure
ina karkarwa tare da sheshshekar kuka.
Mun dan jima a haka sai ya mike zaune
sannan ya fara kokarin tashi. Sai dai
yanayin sa ya taba zuciya ta sosai,
fuskarsa ta nuna zuciyar sa tana cikin
damuwa and that was something da tawa
zuciyar ba zata iya dauka ba.
Na saka hannun dama na na riko na
hagunsa, ya juyo muka hada do through
the dim light, a take aka samu magana
aka kuma samu fahimtar juna a tsakanin
zuciyoyin mu. Ya sarkafe yan yatsunsa
cikin nawa, na kuwa rike su kam kam
trying to draw strength from him. A
hankali ya juyo ya dawo position din sa,
still idanuwan mu a cikin na juna, ya kama
¡hannuna na hagu a cikin na daman sa yayi
kasa dasu a tare zuwa ga abinda nake
tsoron, na kankame jiki na tare da rintse
idona a lokacin da naji yana karanto
addu'ar saduwa da iyali.
I waited feverishly for the pain. It came,
but just a little. But then something came
too. Something that took us away from
this world and into another. A world that
we never knew existed before. Duniyar da
mu biyu ne kadai a cikin ta, mu biyu, jiki
biyu, ruhi biyu, zuciya biyu but all merged
together as one.
Maman Maama✍🏻[07/01, 10:48 pm] +234 906 816 1960: ❤️🩹Safiyya❤️🩹
Episode Seventy : One Family
A cikin kai na naji karar alarm dina na
sallar asuba, na dan bide idona cikin
nauyin bacci tare da jawo wayar na saka
alarm din a snooze, sai kuma kwakwalwa
ta ta tuna min cewa wannan shine second
snooze da na saka wa alarm din dan haka
na tabbatar daga ni har Muhammad muna
gab da makara sallar asuba. Daga nesa
ina jin ana ta kiraye kirayen sallah.
Na danyi murmushi ina jin saukar
numfashin Muhammad a bayan wuyana,
hannayen sa a zagaye a cikina, kafafuwan
sa a sarkafe da nawa. Na lumshe ido na
bude ina kokarin rage nauyin baccin da
yake ido na tun kafin ya ci karfina. Idan
ban da kiran Allah na san babu abinda zai
tashe ni daga wanna kwanciyar. Sam
daren jiya Muhammad bai bar idona ya
rintsa ba, kamar yadda bai bar jikina ya
huta ba. Sai da ya karar da dukkan karfin
da yake jikina sannan ya rabu da ni to
have just few hours of sleep. Shima kuma
gashi nan ai zai makara masallaci.
Na mika hannu na kuna bedside lamp
din da take bangare na. Na yi juyi ina jin
yadda jikina gabakidaya yake amsawa,
musamman kafafuwana da nake jin su
kamar ba nawa ba. Na sauke nauyayyun
idanuna akan fuskar Muhammad da yake
bacci, ya dan motsa yana kokarin sake
jawo ni jikinsa. Na shafa fuskar sa, a
hankali nace "assalatu khairun minal
bacci" ya dan motsa idon sa kadan, na
shafa kunnen sa tare da jan fatar kunnen
"ka tashi fa. Ana can ana samiallahu liman
hamidan a masallaci" ya dan bude
idanunsa da suke cike da bacci yana
kallona, and then his face lit up with a
smile "hey Babe" ya fada yana kara jawo
ni jikin sa, "sallah" na fada ina yanje
fuskata tare da kare bakina da hannu na.
Ya cire hannun nawa tare da saka
fuskarsa a cikin wuyana yace "bacci"
nace "kaje kayi sallah sai kazo kayi" ya
dago kai yana min wanna kalion na sa
yace "inyi ko? Okay, bara inyi sallar you
will get your wish" na bude ido "bacci fa
nake nufi, kayi bacci nake nufi. Kai kace
bacci bai ishe ka ba" ya janye jikin sa tare
da sauka daga kan gadon ganin cewa da
gaske zai makara masallacin "kar ki
chanja magana yarinya. Zan je in dawo.
Zan zo kuma inyi din kamar yadda kika
ce".
Da sauri ya shiga toilet, bai jima sosai ba
ya fito da jallabiya, ya kunna min fitilal
dakin cikin tsokana ya juyo yayi min qwalo
ni kuma na harare shi a dai-dai lokacin da
aka fara tayar da ikama a masallacin da
yake zuwa ya juya da sauri ya fita ni kuma
ina yi masa dariya. Sai da ya fita sannan
na yaye abun rufata tare da kalion rigar
baccin Muhammad da take jiki na ina
murmushi. Na tuna jiya da daddare da ya
boye nawa a kasan gado sanda nake
kokarin zuwa toilet dan gyara jiina yace
wai shi bai gansu ba, ko a tunanin sa zan
tashi a haka in shiga toilet din ne oho?
Nayi nayi ya shiga toilet ya dauko min ko
da bathrobe ce amma yaki, a karshe sai
na yaye bedsheet din kan gadon na
nannadashi a jiki na na tashi yana ta min
dariya, ai kuwa ina tashi na tafi zan fadi
saboda kafafuwana da naji babu karfi ko
kadan a jikin su, sai dauka na yayi da
sunan zai taimaka min amma ashe
taimakon na mugunta ne, a karshe sai da
ya cire min bedsheet din, wankan ma
kuma bai barni nayi sa cikin salama ba sai
da ya kara min wani dalilin yin wankan.
Na mike tsaye a gaban gadon ina dan
bubbuga kafafuna a kasa ko zan samu inji
sun dawo dai dai, nayi kwafa a raina, duk
kokari na na ganin nayi wanka cikin daren
dan kar inyi da assuba amma yanzun ma
sal nayi wani, takanas yaje kitchen ya
hado min abinci cikin daren bayan munyi
wanka ya kawo min har kan gado wai dan
in dan samu karfin da nayi masa complain
ya karar min, ashe kan sa yake yi wa
tanadin karfin, dan abincin ko gama
digesting bai yi ba ya sake tara min wata
gajiyar.
Jin ana kokarin idar da sallah a masallaci
ya sa nayi saurin shiga toilet nayi wanka
sannan na goge jikina na daure gashina a
cikin karamin towel na saka riga da hijab
din da na ajiye a dakin sa domin sallah na
tayar da sallah. Ina cikin yin sallar ya
shigo, ina jin sa yana gyara gadon har na
idar sannan ya zo kashe fitila ya kuma
rufe blinds din windows sannan ya
kwanta,
Sai da nayi azkar dina na gama sannan na
cire hijab din na karasa drying gashina da
towel din sannan na tafi na kashe bedside
lamp na kwanta nima, a tunani na saboda
dadewar da yayi a kwance da kuma
baccin da na san yana ji, yayi bacci, sai
dai ina kwanciya ya jawo ni "me kika ce da
zan fita? In dawo inyi ko?" Na danyi dariya
tare da juyawa ina fuskantar sa "ka san
abinda nake nufi ai. Kawai kana son ka
juya min magana ne" ya fara kissing
wuyana "say whatever you want to say. Ni
dal abinda naji shi nake amtani da shi" na
dago kansa ina kokarin kallon fuskar sa
cikin duhun da yake dakin "hey! Are you
not tired?" Ya danyi dariya "menene tired?
lam just getting started". Na danyi
murmushi tare da kara shigewa jikinsa
kamar zan shige cikin jikin nace "ni dai
bacci zanyi, Allah kuma kar ka tashe ni
daga bacci na" ya danyi dariya tare da
gyara kwanciyar sa ya dora ni a jikinsa
yana shafa bayana ta cikin rigar jikina
yace "Okay, let sleep. Only dan kar kiji
toro ki hada kaya ki gudu",
Na danyi murmushi tare da kara narkewa
a jikin sa ina kokarin komawa bacci,
Hancina yana shakar kamshin jikinsa,
kunnuwana sun sauraren bugun zuciyar
sa, jikina yana exchanging dumi da nasa
jikin, ga hannun sa yana shafa bayana, sai
naji kamar ban taba jin comport irin
wannan ba. Bacci ya fara daukana kenan
naji muryarsa, "Hey Babe!" Cikin bacci
nace "uhmm?" yace "you know I love you,
right?" Na gyada kai na a kirjinsa nace "I
know" yace "good. And now I want to
update you on the love. Ya karu, ya kara
girman da nake jin har ban san inda zan
saka shi ba dan ya cika zuciyar
gabakidayan ta, har yabi jini ya zagaye
dukkan organs na jiki na. Yanzu ba
zuciyar kike controlling kadai ba, gabaki
daya jikin naki ne. And I also want you to
know that these days da muke tare are
the best days of my life, I will never forget
yesterday's night. I enjoyed every second
of every minute of it".
Na dan daga fuska ta nayi kissing adam's
apple dinsa "I love you too Baby. Ban san
yadda kake jin so na a zuciyar ka ba,
amma ni na san yadda nake jin naka, Na
kuma tabbatar yafi nawa girma, da ace
zan iya fito maka da shi ka gani na san kai
ma da zaka yarda da hakan. But ba zan
iya yin hakan ba, amma nayi alkawarin
cigaba da nuna maka ina son ka every
second of every minute of my life. Forever
and ever" na mayar da kaina na kwantar a
kirjinsa sannan nace a hankali ina shafa
gashin kirjinsa "and I also enjoyed the
night" ya danyi dariya tare da kara
rungume ni yana cewa "na gaya miki this
is only the beginning, enjoyment yana
gaba idan mun iya, yanzu koya mu ke yi".
Ranar sai alarm din sallar azahar ne ya
tashe mu. Da sauri yayi alwala ya fita
masallaci ni kuma na tashi na gyara dakin
sa kamar yadda nake yi kullum duk kuwa
da cewa da gaske jikina yana yi min ciwo,
sal da na tabbatar ko ina kamshi yake yi a
dakin sa sannan a koma nawa dakin na
hada ruwa mai zafi sosai a bathtub na
zuba sinadaran rage ciwon jiki da na
kamshi sannan na shiga na kwanta na
dauki waya ta nayi ta replying messages
tare da scrolling through social media, a
lokacin ne naga reply din Salima, a
Maganar ta na fahimci wanna karon ma
iyayen nasu sun boye musu abinda ya
faru, ta dai gaya min cewa Umma bata da
lafiya hawan jinin ta ya tashi tana asibiti
amma da sauki, sai kuma tace min zasu
zo ita da Salim very soon, har da cewa in
ajiye musu kazar amarci. Sai kuma na ga
message da ga Safina, bana son abinda
zai bata min rai dan haka ban ma bude ba
nayi deleting na kuma yi blocking dinta,
ina fatan wata rana abubuwa su daidaita a
tsakanin mu ko dan Mommy da twins,
amma na san ba yanzu ba. Tunanin
Mommy ya sa na kira ta a waya, na gaishe
ta sai ta ce min suna airport yanzu zasu
baro Katsina ita da Mustapha, har
Mustapha ya ce ta bani wayar, muka gaisa
ya tambaye ni ina ango na, nayi murmushi
kawai ban ce komai ba sai yace zai shigo
gobe "zan zo in ba shi amanar kanwata,
kin san na gaya miki zan fasa bakin duk
wanda ya taba min ke ko?" Nan ma
murmushi kawai nayi sannan nayi musu
fatan zuwa gida lafiya,
Da yake tub din mai keeping temperature
din ruwa ne han haka har a gama abinda
nake yi ruwan bai huce ba, sannan nayi
wanka da sabulun wanka na mai kamshi
na fito.
Riga da skirt na saka designers masu dan
banzan kyau, rigar da kyar take rufe
cibiyata da nayi motsi kuma sai ta fito.
Skirt din kuma irin yadin nan ne mai rawa
a duk sanda mutum ya motsa, na gyara
gashina na shafa masa mai nayi drying
dinsa sosai ina tunanin dole in je inyi kitso
tun kafin Muhammad ya saka gashina ya
lalace saboda yawan wankewa. Sai kuma
na dora hijab akan kayan nayi sallah,
amma da na idar sai na kasa cire hijab din
dan ina jin kunyar kayan jikina.
Kamar yadda nayi tunani a dinning na
same shi yana jira na yana waya, ina
shigowa yayi min alamar "what?" Da
hannun sa, na daga kafada nima alamar
tambaya sai ya nuna min hijab din jikina,
na tura baki kawai na jawo warmers din
Mama na fara zuba mana faten irish din
da tayi mana wanda ya sha
dagargajajjiyan naman kaza, a hankali ya
janye wayar da ga bakin sa ya kare mic
din sannan yace "ba ki da gaskiya" na
harare shi "ina da gaskiya ta, haka kawai
mutum ba zai saka hijab ba sai a ce bashi
da gaskiya?" Ya cigaba da wayarsa ni
kuma na fara hada masa tea na tura masa
gabansa na fara hada nawa. Na fahimci
da Mutida suke wayar sai naji ina
sha'awar closeness din su, sai hirar su
suke yi suna dariya, sai da ya fara saka ni
a cikin maganar sannan tace ya bani, na
karba nima na tsokane ta akan zaman
gwaurancin da take yi, tace ai yanzu ma
shiri take yi zata je gidan Mama ta sake
yin kwana biyu kafin su maman suyi
tafiya, kafin nan kuma take saka ran mijin
ta zai dawo. Sai kuma ta tambaye ni wai
menene sirrin? Wai rabon da taji yayanta
cikin wannan nishadin tun kafin waccan
rabuwar ta mu. Nace in tana son sanin
sirrin ta zo gidana zan gaya mata. Muka yi
sallama.
Na ajiye wayar ina jin idon Muhammad a
kaina. "Zaki cire ko sai nazo na cire miki?"
Na juya ido na tare da zuba syrup akan
pancakes din da Esther ta hada mana. Ya
jawo ni na fado kan cinyarsa yana kokarin
saka kansa a wuyana sai kuma hijab din
ya tare, ya daga ni ya zare hijab din, "na
biya sadaki fa, ko baki sani ba?" Nayi
sauri na koma na zauna akan cinyar sa
tare da boye jikina a jikinsa "ni ban sani
ba…….. Yaushe ka biya?" Ya dago ni daga
jikin sa na sake komawa tare da cusa kai
na a wuyansa, ya saka hannunsa yana
shafa fatar cikina yace "na gaya miki baki
da gaskiya, Ga kuma toro" na dago tare
da hararar sa "tsoron wa zanji? Ba dai kai
ba ko?" Yace "in ba tsoro ba ki tashi mana
in ga kwalliyar. Kika sani ko in bayar da
tukuici?" Na daure duk kuwa da kunyar da
nake ji din na tashi tsaye a gabansa "see?
Ya ka gani?" Ya bini da kallon appreciation
yace "kinyi kyau, Sosai. Na gani kuma na
yaba" na juya ido na "dama dan ka yaba
aka yi. Saura tukuici" na mika masa
hannu, ya kama hannun ya jawo ni dab da
shi sannan yayi kissing fatar cikina da ta
bayyana. Na danyi flinching tare da ja da
baya. Sai ya sake jawo ni na dawo kan
cinyar sa, gashina da ban daure ba ya
zubo akan fuskarsa, ya lumshe ido yana
shakar kamshin da yake fitowa daga jiki
na, ya bude idon ya bini da kallon da na
riga na san ma'anar sa, gain irin kallon
da yake yi min ya sa nace a hankali
"abinci. Na riga na zuba. Zai huce" ya
hade goshinsa da nawa, idonsa akan lips
dina yace "sai a zuba wani".
Sai wain kuwa aka zuba............
Sai da muka samu cin abincin sannan na
tambaye shi "wai abincin me muke ci ne?
Breakfast ko lunch?" Ya daga kadafa
"don't know. Don't care" sai da muka
gana ci sannan na gaya masa plan dina
"ina son zanyi girki muje da shi gidan
Abba muyi dinner a can tare da su. Maybe
in nayi haka Mama zata daina wahalar yi
nana abinci kullum" ya danyi shiru yana
tunani sai kuma yace "good idea, She will
like it. Amma zaki iya cin abinci a gaban
su?" Nace "an gaya maka kowa dan fillo
ne irin ka" yayi dariya "me and you, za'a
banbance waye dan fillo a cikin mu yau.
But let's call her mu gaya mata" ya fada
yana dauko wayar sa, ya nemo number
dinta ya miko min, ina daga kan cinyarsa
na karba naga yadda yayi saving number
din "my love" amma ban kira ba sai na
dauko wayata na saka number nayi saving
as "our love" ya danyi murmushi tare da
kissing gefen wuyana.
Nayi dialing ina lissafin yadda zanyi
introducing kaina a wajenta. Tana fara
ringing ta dauka da sallama, Muhammad
ya kara matso da kansa yana jin abinda
take cewa, na amsa sallamar sannan na
gaishe ta, ta amsa da "kun tashi lafiya
Safiyya?" Naji dadi, ta karbi number ta
kenan. Na amsa "lafiya lau. Ya Haidar?"
Ta amsa da "yana wajen aiki. How are
you? Ya bakunta?" ace "alhamdulillah"
sai kuma nayi shiru, ta danyi shiru itama
sai kuma tace min "ina fatan babu abinda
kuke bukata ko?" Nace "babu komai
Mama….... Dama…..... Dama cewa nay!"
Muhammad yace "Mama dama cewa tayi
wal yau." Na janye wayar da ga kusa
da shi tare da toshe masa baki a zare
masa ido, sai kuma na tashi daga kan
cinyarsa na matsa gefe nace "Mama
dama cewa nayi yau kar kuyi cooking
dinner. I want to cook for you. Sai inyi
anan mu taho dashi mu ci tare da ku" naji
murmushi a muryar ta "are you sure
Safiyya? Ke da kike hutawa kin sha
wahalar biki?" Na dan girgiza kai na "babu
gajiya ai Mama. Na huta sosai, I just want
to cook for you kafin ku tafi ance zakuyi
tafiya" tace "Okay. Shikenan. Lallai yau
Haidar da murna kenan. Dama yace gurin
ku zai daw idan muka tafi", Muka danyi
hirar Haidar kadan sai tace in bata
Muhammad. Na mika masa ya karba suka
dan yi magana sannan ya katse yana
kallona "da me zan taya ki aikin?" Na
girgiza kaina "na gode. Dan Allah ka tafi
daki ko hanyar kitchen bana son ka je.
Kana zuwa ba zaka barni inyi aikin ba".
Esther na kira a waya nace ta zo kitchen
muyi aiki. Muhammad kuma ya koma
sama. Tana zuwa na gaya mata abinda
zamuyi ta fara lissafi, "Zamuyi traditional
dish daya. Sai muyi Arabian daya. Sannan
English daya, Sai snacks.… And salad ....
And pepper soup" Nayi dariya "Esther
and pepper soup" tayi dariya itama.
A take muka fara plans a abinda zamuyi,
muka duba abinda bamu da shi muka yi
ordering online sannan na tafi yin sallah
na barta tana marinating nama da sauran
preparations, ban biye wa Muhammad ya
tsayar da ni ba dan haka ina idar da sallar
la'asar na koma muka fara aiki.
Babu bata lokaci muka kammala, sai da
na tabbatar komai ya zama set saura
finishing sai na bar mata na koma daki na
na shiga wanka. Cikin sauri na fito lokacin
already ana kiran sallar magrib, na shirya
cikin doguwar rigar atampa wadda akayi
wa simple yet classy dinki wanda bai
kama min jiki ba, na saka one of my
mother's pendent sannan nayi simple
kwalliya na shafa turare. Lokacin
Muhammad ya shigo yace min zai je
masallaci, idan ya dawo zai jira ni a waje,
nima sallar nayi sannan na karasa
shiryawa na yafa mayafi na na fito.
Already na tarar Esther har ta shirya
abincin a baskets ta sauka da su kasa,
mai gadi ya taya ta dauka suka zuba a
motar da Muhammad ya fito da ita sannan
muka tafi.
Ni nayi driving, Muhammad yana zaune a
gefe yana ta min labarin dramas din da
akanyi a gidan su akan wanda akafi so da
wanda ba'a so. Haidar ne wai kullum mai
complain cewa Mama bata son shi duk
kuwa da cewa shine mai sunan babanta
A hakan kuma yake yaudarar ta ya saka ta
tayi masa abu tunda idan bata yi ba zai ce
bata son sa, Wannan kuma shi yake sa
kullum suna rigima da Mufida ita kuma
saboda ita kadai ce mace kuma ita ce
karama.
Da muka je gidan shi ya taimaka min
muka fara shiga da kayan cikin gidan.
Bayan mun shiga mun shiga Muhammad
ya aiko aka shiga da sauran kayan. Babu
kowa a parlourn, a zauna sai Muhammad
yazo ya zauna kusa da ni, na dan harare
shi, "ka tashi daga nan" ya daga kafada
"saboda me?" Nace "ni dai ko ka tashi ko
kuma ni in tashi, so kake a fito a gan mu a
haka?" Yana murmushi yace "to menene?
Ba su suka daura mana auren ba?" Nace
"ni dai ka tashi" sai ya rada min a kunne
na "ki zo muje in nuna miki dakina" na
bude ido tare da girgiza kai, yace "kafin
su fito mun dawo fa.
Nuna miki kawai zan y" nace "kayi
alkawari nuna min kawai zaka yi?" Ya miko
min karamin danyatsansa "na yi alkawari"
na saka nawa a ciki muka daura sai nace
"a ina dakin yake?" Ya juya yana nuna min
bayan mu "a can.…….." Sai kuma maganar
to tsaya bai karasa ba. Na kalli inda yake
nuna min sai muka hada ido da Mama,
tana tsaye a hanyar da na bi ranar nan na
je dakin ta da kyakkyawan murmushi a
kwance akan kyakkyawar fuskarta.
idanunta a akan mu. Mufida tana tsaye a
bayanta.
Nayi sauri na zare dan yatsa na daga cikin
nasa ina rarraba ido, ya mike tsaye
sannan ya durkusa ya gaishe ta nima nayi
yadda naga yayi, sai dai shi da fulatanci
yayi ni kuma nayi da hausa, kamar hadin
baki sai ga Abba da Haidar nan sun shigo
daga waje, take Abba ya fara tsokana ta
wai mun wuce su a hanya ina ta gudu a
mota, Mama kuma ta fara kare min wai
Muhammad ne ya koya min gudu da
mota. Haidar yace "yau dai finally an
samu wadda Mama take karewa against
Hamma" na harare shi ina so inyi masa
korafin bai zo gidan mu ba tunda na tare
sai kuma na kasa cewa komai, ina jin
Muhammad yayi magana da fulatanci
yana dariya sai Mufida tace min "wallahi
gulmar ki yake yi. Wai kin gama cika baki
amma muna shigowa kinyi shiru" na dago
kai na harari Muhammad din shima amma
still ban ce komai ba. Bai rabu da ni ba ya
cigaba da tsakana ta wai kullum ina
tsokanar sa wai yana da kunyar fulani,
gashi nan yanzu nice na zama
bafulatanar tunda na kasa yin magana
ma. Na dauki waya ta na tura masa
message "zan kama ka ne, wallahi zaka
gane kuren ka".
Daga nan sai Abba ya fara tambayar sa
maganar zuwan mu Kura, Muhammad ya
gaya masa cewa next weekend yake son
muje lokacin munyi two weeks, da yaso
muje bayan daurin aure kafin biki amma
sai Daddy ya nuna yafi son sai bayan bikin
tukunna. Sai Abba yace already ya samo
contact din wani mutumin kura mai suna
Alhaji Basiru, ya kuma yi masa maganar
zuwan mu da abinda zai kawo mu, dan
haka idan munje gurin sa zamu sauka shi
zai yi guiding din mu har mu samu abinda
muke so. Ya karasa maganar da cewa
"kiyi ta addu'a kinji Safiyya? Komai ya
kusa wucewa da yardar Allah".
Na gyada kai na kawai ina jin kamar zanyi
kuka. Na san na jima ina kuka a gaban
ubangiji na ina neman mafita da kuma
sakamako na alkhairi, amma yanxu da
alkhairin ya zo sai nake jin cewa it is more
than I have ever asked for. Mama ce tace
muje mu shirya dining table ni da Mufida,
sai da muka bar gurin su Abba sannan na
fara magana ina kallon dan karamin cikin
jikin Mufida, "ki zauna tun kafin baban
baby ya zo yace na wahalar ma sa da
babyn da" na karasa ina ja mata kujera a
dining set din. Ta fara bude warmers din
da na fara ajiye wa a saman table din "wai
duk ke kika yi wannan girkin? Ke kadai?"
Nace "no. Ba ni kadai bace ba. Akwai mai
aiki na ta taimaka min sosaj" tace "still...
Kinyi kokari sosai" nace "ina son girki ne.
Bana gajiya da shi"
Muka cigaba da setting table din muna
hira, ita ta nuna min inda kowa yake zama
sannan na saka masa abinda zai bukata.
Sai dauka gama ta koma tace musu mun
gama. Suna shigowa kuma sai naji na
kuma takuwa, na zauna kawai Mufida ta
bude abincin tana tambayar kowa abinda
zai ci, Mama tayi mamaki "wai da yawa
kika yi abincin Safiyya" nace "babu yawa
sosai Mama. Kawai dai ban san wanda
zaku fi so ba shi yasa nayi varieties".
Abba tuwon da nayi na markadaddiyar
shinkafa da miyar danyar kubewa yace a
zuba masa, yana fara ci yace a dibar
masa wanda za'a dumama masa da safe
dan kar Haidar ya cinye. Naji dadin hakan
a raina, na fahimci yabawa ce. Sai kuma
na yiwa Haidar dariyar yadda yayi da
fuskarsa "wallahi idan kuka cigaba da
takura min a gidan nan in na koma gidan
Hamma ba zan dawo ba" ya fada yana
cika bakin sa da nama kaza, Mufida ta kal
lomar coconut rice ta kuma kurbi lemon
pineapple gannan tace "dama yaushe
zaka dawo? Ai da kansu zasu dawo da kai
in ka ishe su", Mama tana cin salad din da
aka zuba mata tana kallona tace "a ina
kika koyi girki Safiyya?" Na dago na kalle
ta sai tayi min murmushi, nace "ina so ne
kawai. Ina yi a gida sosai.
Kuma duk cook din da za'a kawo mana
gida na kan zauna tare da ita a kitchen in
koyi irin abubuwan da ta iya. Sannan in
munje vacations duk abubuwan da muka
ci a kasashen da muka je in naji yayi min
dadi na kan nemi recife din in ringa
gwadawa a gida" Abba ya nuna tuwon
gabansa yace "tuwon nan yayi dadi sosai.
Na menene? A ido kamar fulawa a baki
kuma kamar shinkafa" Haidar yayi gyaran
murya suka hada ido da Muhammad suka
yi dariya, na fahimci tsokanar Abba suke
yi amma ban kula su ba sai na bashi amsa
cikin ladabi "shinkafa ce Abba, markada
ta ake yi kamar za'a yi wainar shinkafa
amma sai a tafasa ruwa da mai a ciki a
ringa zuba paste din ana tukawa, Daddy
yana so sanda yana iya cin abinci" Abba
ya gyada kai "nima yayi min dadi sosai,
Miyar ma tayi dadi " na sunkuyar da kai
"na gode Abba" Mama tace "wannan
salad din fa? Ban taba cin hadin salad irin
sa ba" na danyi murmushi "Italian ne
Mama, I Italy na fara cin irinsa shine nake
mimicking, though I couldn't get all the
veggies da suke using, amma da akwai
wani na Morocco, yafi wannan daci
sosai...." Sai kuma nayi shiru ina jin a
raina kamar na saki lay ina ta surutu da
yawa, ban fiye son magana akan abinda
nake da shi ko abinda na iya ba sai in ga
kamar show up ne.
Haidar ya kalli Mufida yace "ke kuma
salad din wacce kasa kika iya?" Tace "ina
ruwan ka? Kai na wacce kasa ka iya?" Ya
matso da kujerar sa kusa da ni "duk
abinda yaya ta ta iya na iya nima, in kin isa
ke ma ki hada kayan ki ki koma wajen ta"
daga nan sai musun wanda yafi kusan ci
da ni ya kaure a tsakanin su. Mama ta
zuba soup a bowl ta dara sha, na fahimci
kamar ba ta son cin abinci mai nauyi da
daddare. Ta dago tana kallon yadda nake
ta juya shinkafa na kasa sakin jikina in ci
duk kuwa da cewa ina jin yunwar, tace
"Hajjo ta bani labarin mahaifiyar ki sosal.
She was an incredible woman and I
believe you are too. I wish I had the
privilege of meeting her amma Allah bai yi
ba, but na samu privilege na meeting you.
Ina so ki sauke ni a matsayin ta, duk
abinda kike tunanin zata iya yi miki idan
da ace tana da rai nima zanyi miki shi
insha Allah, Duk abinda kike tunanin zaki
¡ya zama ki gaya mata nima zaki iya zama
ki gaya min. Kar kiyi considering Gidado a
cikin relationship din mu ballantana har ki
dauke ni a matsayin in-law. Ina so ki
dauke ni a matsayin uwa kamar yadda ni
mana dauke ki a matsayin ya" Abba ya
ajiye spoon din hannunsa yana karbar
bowl din da Mufida da zuba masa fruit
salad yace "that goes for the rest of the
family" ya shafa kan Gidado da yake
gefensa yana cin abincin sa duk abinda
ake bai ce komai ba yace "Gidado is just a
bridge da yayi leading din ki to us. But
you are now a daughter to us kamar
yadda Mufida take. In kin kauce hanya we
will guide you. In kinyi dai da we will
celebrate you and cheer you up." Nayi
murmushi "thank you Abba" ina jin
Muhammad yana zunguri na da kafarsa ta
kasan table din amma ban nuna na san
yana yi ba.
Bayan mun gama su Muhammad suka fita
masallaci sallar isha mu kuma muka shiga
ciki muka yi. Dakin Mufida na shiga nayi
sallar a can ina kallon dakin yadda yake
kamar ba ta yi aure ba, komai na ta yana
nan yadda duk sanda tazo gidan she is
welcome, Hakan akin Muhammad ma,
kafin mu tati sai da ya ja ni ya nuna min
dakin sa and I saw his old pictures har na
dauki guda daya na boye a jaka ta. Muka
yiwa su Mama sallama Mufida ta raka mu
¿har mota sannan muka tafi da niyyar
zamu fito jibi mu raka su airport.
Muhammad ne ya karbi driving din. Muna
daukan hanya na kama hannun sa na
matse tare da zare masa ido nace "wa na
kama? Shine kake tsokana ta ko?" Ya
kama dariya "kinga idon ki kuwa a gaban
Abba? You looked like beran da aka ajiye
a gaban cat" na nuna kaina "ni ko? Ni ce
beran ko? Wai kai waye ya koya maka
hausa ne da har ka ke bakar magana?" ya
juyo yana kallona yace "zama da
madaukin kanwa. Ke kika koya min".
Gidan Daddy muka wuce. A hanya na
nemi shawarar Muhammad akan wani abu
da yake damuna a raina, maganar
Mommy. Ina son yi mata wani abu na
kyautata wa da zata ji dadi. Na fahimci
duk issues din da na samu da ita sun fara
ne tun sanda ta fahimci nice mai kudin
gidan ba Daddy ba, na kuma fahimci tsoro
ne ya saka ta yin koma me tayi, tsoron
rashin madafa idan babu Daddy. Sai na
tambaye shi yana gain inyi mata kyautar
kudi masu tsoka haka ko kuma in siya
mata wata kadara wadda zata saka ta
fahimci ko babu Daddy ba zan rabu da ita
ba. Sal ya bani shawarar da tafi duk
wannan. Kuma sosai nayi na'am da
shawarar ta sa na kuma ji dadi.
A gidan na tarar Mommy ta dawo kamar
yadda tayi min alkawari. A wajen Daddy
na same su ita da Mustapha suna
magana, Na lura maganar Safina suke yi
dan haka ban saka baki ba sai na gaishe
su bayan na gaishe da Daddy tare da
tambayar su hanya. Ga mamaki na sai naji
Mustapha yana tsokana ta wai an gaya
masa ina missing din su kullum sai nazo
gida, Muna cikin maganar Muhammad ya
shigo, ya gaishe da Daddy sannan ya
gaishe da Mommy, ta amsa masa a ciki ba
tare da ta kalle shi ba sannan ta dauki
jakarta ta shiga cikin gida. Ya mika wa
Mustapha hannu suka gaisa babu yabo
babu fallasa sai shima Mustaphan ya fita.
Bayan sun fita ne na gayawa Daddy
shawarar da Muhammad ya bani dazu a
mota "Daddy ina so zan bawa Mommy
five percent share in one of my
companies" ya danyi shiru yana kaliona
amma na ga jin dadi a fuskar sa sannan
yace "why? Menene dalilin ki nayin
hakan?" Nace "kawai ina jin babu dadi ne,
bata da wata kadara in her name, bata da
wani source of income, duk wata bukata
da zata taso mata sal dai ayi mata. She
deserves better. Shine nake gain idan na
bata share din zata samu source of
security sannan zata ke samun wani abu
yana shigo mata yadda ba zata dogara da
sai anyi mata wasu kananan abubuwan
ba. Na san in na bata kudi zata kashe su
ne, in na bata wani abu ma zata iya
siyarwa. Amma hannun jari will be there
kuma zata ji a ranta cewa ita ma da ita a
cikin dukiyar nan. Amma sai abinda kace"
ya danyi murmushi ya kalli Muhammad
duk kuwa da ban gaya masa Muhammad
din ne ya bada shawarar ba, sannan ya
gyada kai cikin amincewa "hakan tunani
ne mai kyau. Allah yayi muku albarka.
Aikin Mustapha fa?" nayi murmushin jin
dadin amincewar sa sai nace "aikin
Mustapha yana nan kamar yadda na gaya
masa, duk sanda yake so za'a bashi list of
all available positions ya zabi wanda yake
so a ciki, Kuma munyi magana yace zai
zo. Maganar Mommy kuma I will ask
barrister Umar to take care of all the
paperwork sai mu kawo maka kai kuma ka
bata".
Maman Maama ✍🏻
[07/01, 10:48 pm] +234 906 816 1960: ❤️🩹Safiyya❤️🩹
Episode Seventy One: The Travelers
Afuwan. Network ya rike min komai tun
jiya. Mun dai kusa gamawa. One more
episode to go. ..........
Please masu tambayar document, like I
said kafin in fara typing paid episodes din
Safiyya, babu document. In mun gama l
will arrange the episodes in the group
yadda zai yiwa kowa dadin maimaici.
Insha Allah.
Muna fitowa muka had da Dr Ma'aruf zai
shiga, sai muka tsaya muka gaisa ya sake
taya mu murnar auren mu sannan ya bani
update akan lafiyar Daddy, as I expected,
ba update bane mai dadi, amma yayi
amfani da kalamai masu kwantar da
hankali kawai dai ya nuna mana we should
expect anything at any moment.
A mota I was feeling down sai Muhammad
ya dan fara yi min hira yaji bana amsawa
sai ya barni. A hanya muka tsaya a wani
fast food joint ya shiga ya lodo mana
kayan ciye ciye wai ya ga ban ci abinci
sosai ba dazu, ya dauko min different
varieties of ice cream saboda ya san ina
so, daga baya ya kwaso chocolates na
dairymilk duk dan ya ga na dawo da fara'a
ta, i tried appreciating him duk da dai still
hankali na yana kan Daddy da yadda yake
jin jiki.
Bayan mun sake hawa titi sai ya kunna
kida kasa kasa muna tafiya muna ji, daga
baya kuma sai ya fara bi with that deep
voice of his, na dan juyo ina kallon sa ina
jin yadda yake bin wakar kamar shine ya
rubuta ta for me, lyrics din tas a bakin sa
🎶🎶I took an arrow to the heart
I never kissed a mouth that tastes like
yours
Strawberries and somethin' more
Ooh yeah, I want it all🎶🎶
🎶🎶Mm, you got me feelin' like
I wanna be that guy, I wanna kiss your
eyes
I wanna drink that smile, I wanna feel like
I'm
Like my soul's on fire, I wanna stay up all
day and all night
Yeah, you got me singin' like🎶🎶
Ganin ina kalion sa sai yayi murmushi tare
da sarkafe hannun sa cikin nawa yayi
kissing ya cigaba da bin wakar,
🎶🎶Ooh, I love it when you do it like
that
And when you're close up, give me the
shivers
Oh baby, you wanna dance "til the
sunlight cracks
And when they say the party's over, then
we'll bring it right back
And we'll say, ooh,🎶🎶…….
nima sai na samu kai na da bive masa na
fara bi nima,
🎶🎶Into the car
On the backseat in the moonlit dark
Wrap me up between your legs and arms
Ooh, I can't get enough
You know you could tear me apart (ooh)
Put me back together and take my heart
I never thought that I could love this hard
Ooh, I can't get enough
Mm, you got me feeling like🎶🎶
🎶🎶I wanna be that guy, I wanna kiss
your eyes
I wanna drink that smile, I wanna feel like
I'm
Like my soul's on fire, I wanna stay up all
day and all night
Yeah, you got me singin' like🎶🎶…..
tun muna yi a hankali har muka fara
raising voices din mu ina using hannun sa
as microphone shima yana using nawa,
wakar ta kare sai wakar "shape of you" ta
fara, muka cigaba da bi cikin nishadi har
ta kai karshe itama sai aka fara "south of
the border"
🎶🎶She got the, mmm, brown eyes,
caramel thighs
Long hair, no wedding ring, hey
I saw you lookin' from across the way
And now I really wanna know your name
She got the, mmm, white dress, but when
she's wearin' less
Man, you know that she drives me crazy
The, mmm, brown eyes, beautiful smile
You know I love watching you do your
thing
I love her hips, curves, lips say the words
Te amo, mami, ah, te amo, mami
1 kiss her, this love is like a dream🎶🎶
🎶🎶So join me in this bed that I'm in
Push up on me and sweat, darling
So I'm gonna put my time in
I won't stop until the angels sing
Jump in that water, be free
Come south of the border with me🎶🎶
🎶🎶He got that, mmm, green eyes,
givin' me signs
That he really wants to know my name,
hey
I saw you lookin' from across the way
And suddenly, I'm glad I came, ay!
Ven para acá quiero bailar, toma mi mano
Quiero sentir tu cuerpo en mi, estás
temblando
Mmm, green eyes, takin' your time
Now we know we'll never be the
same........🎶🎶
Muhammad ya fara bin ta ni kuma ban iya
lyrics din ba amma naki hakura sai nayi ta
zuba shirme na, ai kuwa ya kama min
dariya amma na maze naki dainawa na
cigaba da fadar duk abinda yazo bakina a
dole wakar nake bi, dariya sosai yake yi
sam ya manta ma da driving yake yi, dan
ma a hankali yake tafiya. Allah ne dai
kawai ya kai mu gida lafiya, a gidan ma a
tsakiyar compound yay packing muka
cigaba da bin wakar "wild thoughts" da ta
fara a lokacin, itama ban iya ba, haka
muka fito kan compound din muna bin
waka muna dariya, in ka ganmu zaka
dauka a buge muke saboda yadda muke
dariya muna magana muna waka at the
same time, kofofin motar ma duk biyun a
bude muka bar su, wakar ta dauke sai na
fara wakar kidz Daniel ta "marhaba",
Muhammad bai iya ba amma sai ya dage
ya fara bi, ni dai ina jin har da fulatanci,
larabci da gwaranci ya hada a cikin wakar
nan, dariyar da nayi har sai da na kai kasa
na zauna dirshan ina dariya kamar ciki na
zaiyi ciwo, kuma bai daina ba, na tabbatar
shi kansa bai san me yake cewa ba. Sai
da ya hakura dan kansa sannan ya bari, ya
mika min hannu na kama ya jani na tashi
tsaye still ina rike da cikina saboda dariya,
sai kuma yace "let's see who will be the
first to reach the top!" Muka kwasa a
guje, na wuce shi a waje amma muna
shiga ciki yayi overtaking dina, na rike
rigar sa na jawo shi baya muka fadi a
wajen, ya sake mike wa da gudu nima na
bishi sai dai a kasan stairs na tsaya ina
haki saboda already dariya ta cinye min
duk karfina, amma shi da gudu ya haye
saman stairs, sai da ya kai karshe sannan
ya juyo yayi min gwalo, na daga murya
"wallahi ban yarda ba, ai ban shirya ba.
This is cheating" yace "cheating ya wuce
rike nin da kika yi? Was that not
cheating?". Na zubar da takalma na da
jaka ta a wajen na kwanta a kasa "Ni
wallahi ban yarda ba wayo kayi min, Allah
sal ka dawo an sake" na fada ina bubbuga
kafa a kasa, Sai da ya dawo kuwa, amma
da ya davo ba racing din aka sake ba
sunkuyawa yayi na hau bayansa ya hau
dani saman dan cewa nayi na gaji ba zan
iya hawa ba.
A falon sama ya ajiye ni, sai a lokacin
muka tuna da ledojin da muka siyo, ya
koma mota ya dauko ya dawo muka baje
anan falon muka ci abinda zamu iya ci
sauran ya kwashe ya kai fridge, ni kuma
na gyara gurin na saka turaren wuta to
get rid of kamshin abinci sannan na bishi
kitchen na tarar yana dafa tea sal na zuba
masa spices din da nake using for tea ya
sake re-boiling, sai dai kuma tunda ya
juyo kaina muka manta da tea, sanda
muka tuna da tea din already har ya sake
hucewa dan haka muka sake boiling for
the third time. Bayan tafasa ta ukun ma
bamu sha ba dan sanda ya tafasa ya
kashe kansa bama duniyar nan, muna can
a ta ma'aurata muna shawagi.
Washegari da safe a dakina muka farka.
Mun jima a kwance idon mu biyu amma
kowa da tunanin da yake zuciyar sa, na
fahimci ya farka ne kawai saboda ji da
nayi ya kara matsowa jiki na hannun sa a
ciki na yana shafa fatar cikin, ni tunanin
Daddy nake yi ina lissafin hanyar da zanyi
easing rayuwa for him, Mun jima a haka
tannan naji dan yatsansa yana tracing
scar din da take cikina, na bude ido na da
yake rute amma bana ganin sa tunda a
baya na yake, sai naji ya danyi gyaran
murya sannan a hankali yace "yana ina?"
Na mayar da idanuna na rufe ina jin zuciya
ta tayi nauyi, na sani cewa it takes a lot of
courage and love for Muhammad to ask
me about Junior. Na san dole zasu hadu
watarana kuma dole zasu y interacting in
one way or the other amma banyi niyyar
matsawa Muhammad ya kula Junior ba,
Junior da na ne, ni kadai.
Na bude ido ban ce komai ba sai ya sake
ja na jikinsa ya dora fuskar sa akan tawa
duk muna kallon side daya ya sake cewa
"where is he?" Na danyi tunani sannan a
hankali nace "maybe at uncle Sufyan's.
Or on the road. Or at the airport. Or on
the plane. I am not sure. Na san dai yau
zasu tafi Berlin".
Ya danyi kissing gefen wuyana sannan
yace "call them. In basu tafi ba we will go
and see them up" nayi sauri na juyo ina
kallon sa amma bai kalle ni ba sai ya mike
ya sauka daga kan gadon ya shiga toilet.
Kitchen na tafi, na jima a tsaye ina dafe da
worktop ina jin effects din daren jiya a
jikina, sal na samu kaina da tambayar
kaina haka duk amare suke ji? Amma na
san a hankali jikin nawa zai saba da auren.
Na girgiza kaina da murmushi a fuska ta
trying not to think of the night dan in
samu in yi functioning properly.
Stool na jawo na zauna akai sannan na
kira Daddy a gaishe shi na duba jikinsa,
na san karfin hali yake yi dan har da
tsokana ta yayi, sai kuma na kira Abdul,
half expecting cewa kiran ba zai shiga ba
dan ina tunanin already suna cikin jirgi
amma sai naji ya shiga, ya dauka
"amarya" nayi murmushi "na'am ango"
sai yayi dariya "ai mun girma mu, mun bar
muku wannan title din" nace "na karba da
hannu bibbiyu" yace "ohh da gaske? Ko
alkunya babu?" Ban amsa ba sai nace "ya
kake? Ya Hafsa?" Yace "Lafiya lau, gashi
nan muna shirye shiryen bar muku
wanna kasar ta ku mai dan karen zafi"
nace "karfe nawa jirgin zai tashi?" Yace
"2, that's idan bamu samu delay ba" na
gyada kai ina duba agogo nace "okay. In
sha Allah zamu zo airport din muyi muku
bankwana" ya danyi shiru sannan yace
"ohh. Okay. To shikenan. I will see you
there" daga haka muka yi sallama.
Banana smoothie na fara hadawa sannan
na fara shirya mana breakfast ina yi ina
shan abi na, Muhammad ya shigo
smelling and looking fresh, ya dauke min
smoothie na ya shanye sannan ya sake
re-boiling tea din mu na jiya for the forth
time, ni kuma na hada mana sandwich irin
wanda na san yana so tun ina school
sannan na soya samosas a cikin wadanda
Hajiya ta yo min. Anan kitchen muka yi
breakfast din, muna hirar abinda yake
raina, hirar Daddy. Sai da muka gama
sannan ya tambaye ni "karfe nawa zasu
tafi?" Na gaya masa sai ya mike "okay, ki
shirya sai muje" daga haka ya fita.
Daki na koma na shirya kamar yadda ya
bukata, a raina ina hasko fidkar Junior
kuma ina tunanin ko zai gane ni? Ko zai
yarda yazo gurina? Ko kuma zai turo baki
¡va saka kuka kamar ranar nan? Ina gama
shiryawa Muhammad ya kira ni yace zai je
masjid in na yi sallar in same shi a mota,
hakan ya sa nima nayi alwala nayi sallah
sannan na kara gyara fuska ta na saka
shades dina na yafa mayafi na fita.
A gaban mota na same shi rana tana kara
haske min shi, sai nayi murmushi na tsaya
a bakin kofa ina kallon sa, na rasa dalilin
da yasa kullum nake ganin yana kara min
kyau, kullum na kalle shi sai nayi tasbihi
ga Ubangijin da ya halicce shi. Duk kuwa
da cewa idanunsa a cikin glasses suke sai
da na gane shima ni yake kallo kuma ya
san kalion sa nake yi, yayi murmushi tare
da yi min alamar "what?" Da hannun sa, ni
kuma nayi masa alamar "kayi kyau" tare
da blowing masa kiss. Sai ya tako ya
karaso inda nake tsaye, na langwabe kai
gefe nace "you look so handsome" and I
saw his face turned red, sannan ya mika
min hannun sa na kama muka taka zuwa
inda motar take ya bude min na shiga ya
rufe sannan ya zagaya ya shiga gurin
driver. Ina kallon security suka shiga tasu
motar, sannan ya tayar muka fita. Tun da
muka fita yaki kallon titi completely,
hankalin sa duk yana kaina, a karshe dai
sai ya ja motar zuwa gefe yayi packing, na
juyo zan yi mishi magana sai naga ya cire
glasses din idonsa ya kamo fuska ta zuwa
ta sa ya fara kissing dina, sai da yayi mai
isarsa sannan ya sake ni, na bude ido da
mamaki ina kallon sa sai naga ya kara
fadada murmushin fuskarsa sannan yace
"much better" na bata rai nace "what? A
titi fa muke" ya daga kafada "I don't care"
sai kuma ya ja motar muka yi gaba. Ya
dan juyo ya kalle ni yace "those lips are a
bomb even without a lipstick" na yi sauri
na taba lips dina sannan na jawo mirror na
kalli fuska ta, Ya goge min lipstick tas, Na
bata rai tare da hararar sa yayi dariya, "ko
gobe kika kara sakawa in zamu fita sai na
goge shi" nima sai nayi dariya ina kallon
tasa fuskar, ya bata rai tare da tambayar
"what?" Na nuna masa mirror, ya jawo ya
duba sai na kara yin dariya, lipstick din da
ya goge daga nawa bakin duk ya koma
nasa, nace "dama ai mugunta fitsarin fako
ce" ya bata fuska yace "menene fitsarin
fako?" Na yu masa bayanin karin maganar
da kuma ma'anar ta, ya tura baki irin
yadda nake
yi yana kallon kansa a madubi sai na kara
yin dariya, na jawo tissue na mika masa
sai ya juyo min da fuskar na goge masa
sannan na gyara tawa fuskar.
Sai da muka je airport sannan na kara
fahimtar dalilin goge min lipstick dina,
Abdul yake kishi, ni sai a lokacin ma na
tuna da na gaya masa har da shi aka yi
kokarin hada ni aure, amma ai bance
masa yana so na ko kuma ni ina son sa ba
sai dai kiri kiri ya hana ni tsayawa muyi
magana da Abdul din.
Da ma muna zuwa suma suna zuwa,
Abdul ne ya fara zuwa wajen motar mu da
niyyar mu gaisa amma Muhammad ya
zagayo side din kofa ta yayi bake bake ya
hana ni magana, dole Abdul ya juya ya tafi
yana shigar musu da kaya ciki. Na juya ina
kalion Muhammad sai ya daga katada
sannan ya bude min kofa na fito "babu
dad fa haka. Abdul yana da kirki sosai.
Kuma shima ai yana da matarsa" yace
"ina ruwa na da matarsa, Ya tafi gurin
matar ta sa mana waye yace yazo gurin
tawa matar?" Murmushi kawai nayi dan na
fahimci ba zai fahimta ba. Na tafi wajen
Aunty Hajjo da uncle Sufyan a gaishe su
cikin jin kunya. Muhammad shima ya
karaso ya gaishe su. Ban ga Junior a
hannun su ba kuma ban tambaye su shi
ba. Muka danyi maganar jikin Daddy da
Uncle Sufyan sai shima ya shige ciki, a
lokacin ne Hafsa ta karaso inda muke
hannun ta rike da Junior.
Ta tsaya muka gaisa tana tsokana ta wai
ina kyallin goshi irin na amare, ta koma
kan Muhammad shima wai tun da muka
zo gurin ni yake kallo kamar ba tare muka
taho ba. Junior ne ya ja sarkar wuyanta da
karfi, ta dan yi kara ni kuma nayi saurin
rike hannunsa "Hey! Baka ji ko?" Na fara
kokarin cire sarkar daga hannun amma ya
dintse hannun, tace "karfi ne fa da
wannan yaron da kike ganin sa" na kasa
cire sarkar daga hannun sai na balle mata
sarkar daga wuyanta, ai kuwa yana ganin
mun cire sarkar sai ya saka daya hannun
ya kama dan kunnen ta guda daya har
yana dariya. Na kama hannun a dan daka
kadan tare da zare masa ido "let it go!"
Na fada ina kalion sa cikin ido, sai ya
kyalkyale da dariya yana bayyana hakoran
sa guda biyu. Hafsa ta zaro ido "kar ki
yarda Mama ta ganki kina dukan bundle
of joy din ta" Aunty Hajjo da take gefen
mu tayi gyaran murya tace "ina kallon ta
aj" na danyi murmushi ban ce komai ba,
dan kunnen na cire daga kunnen Hafsa,
Junior ya koma hannu daya sarka hannu
daya dan kunne. Ya juyo yana kallona sai
na harare shi sai ji nayi yace "ehh!" Kamar
me cewa "hey" irin yadda nake ce masa,
sai kuma va saki sarka da dan kunnen
suka zube a kasa ya miko min hannu.
Hafsa cikin mamaki tace "what? Yaron
nan fa baya zuwa gurin kowa" Na dan fara
ja da baya "kwadayayye ne. Ya tuna ina
bashi sweet" sai ta miko min shi "hold
him. Bara in duba kaya" na karbe shi
"ehh!" Ya kara fada yana nuna min
hannunsa "bani da sweet" na fada ina
kallon sa "ban zo da sweet ba".
Muhammad ya karaso kusa da mu. Sai a
lokacin na fahimci mu kadai ne a wajen
Aunty Hajjo ma ta zagaya wajen kayan su
da ake shiga dasu ciki. Na daga kai ina
kalion sa sai naga yana kallon Junior,
expression din fuskarsa unreadable. Ya
ciwon hannayen sa da suke aljihu ya mika
masa "come" nan take Junior ya bata rai
ya turo baki idonsa ya cicciko da kwalla.
Muhammad ya bude ido "me nayi maka?
Shari zaka yi min?" Ai kam nan take ya
balle da kuka, sai naga Muhammad yana
dariya sannan ya lakuce masa hanci
'"shagwaba irin ta gado". Na harare shi
amma bance komai ba.
Sai ya karbe shi daga hannuna ta karfi
yace "tunda kayi min sharri sai na dauke
ka" ya cigaba da kukan sa Muhammad
yana jijiga shi sai kuma ya bar gurin da
shi, har Hafsa ta dawo basu dawo ba, sai
muka shiga ciki tare da ita muka tarar an
gama auna musu kayansu ana clearing
din su, Abdul ne ya tambayi inda Junior
yake babu wanda ya bashi amsa sai yayi
shiru, sai can daga baya kuma sai ga su
nan sun taho, na bisu da kallo har suka
karaso, hannayen Junior biyu rike da
sweet ga kuma leda a hannun
Muhammad. Da yazo kuma sai ya rasa
wanda zai mika wa shi, sai ya mika wa
Abdul.
Da murnar sa yaje gurin Abdul din amma
sai ya juyo yana kallona yace "ehh!" Sai
ya mika min sweet din hannunsa, naji
kunya ta kamani amma ganin kowa yana
kallo na sai na saka hannu na karba tare
da cewa "thank you" ya gyada kai kamar
ya gane abinda nace sannan ya bude tasa
sweet din ya saka a baki,
Aka kira sunan jirgin su sai muka yi musu
salama suka shige. Abdul ne na karshen
shiga, ya dago hannun Junior da yake
rungume da ledar kayan dadin sa yayi
mana bye bye. Muhammad ne ya daga
musu hannu ni kuma sai a bisu da
murmushi kawai. Na bisu da kallo kawai
wandering what life might have in store
for Junior and for us.
Kamar yadida Mustapha yay min alkawari,
ranar suka zo tare da twins bayan mun
koma gida. Suka taho min da motoci na
na gidan Daddy. Lokacin Muhammad ya
fita yaje gida, sai na saka hijab na sauka
kasa gurin su. Anan suka ci abincin rana, I
gave him list of job vacancies din da
muke dasu kuma ya zaba a take kuma na
rubuta masa offer na tura masa zuwa e-
mail din sa tare da tura wa uncle Ahmad a
matsayin sa na chief of staff dina dan ya
sani kuma yayi referring Mustapha zuwa
department dinsa. Sai kuma a ce da
Mustapha "be nice to uncle Ahmad. Na
san halinka. Kar kayi masa rashin kunya
ku zo kuna rigima dan Allah, Babana ne
shi and you have no idea what he is going
through" murmushi kawai yayi ya kalli
twins da suke gurin yace "ba zan yi masa
ba. Na girma ai yanzu" dariya muka yi
gabakidaya,
Sai ya bani labarin maganar auren da
Daddy yace masa yayi, naji dadi nace "ina
yammatan da ka ce min suna ta bin ka?"
Ya bata rai "wasa nake miki fa. Ni bani da
wata budurwa. Ki nemo min" murmushi
kawai nayi na bar maganar.
Daga nan muka yi maganar tafiyar twins
karatu, komai ya kammala zuwa karshen
watan nan zasu tafi insha Allah. Duk da
dai na fahimci kamar basa son tafiya su
bar Daddy amma kuma Daddyn ne mai
matsawa akan tafiyar ta su yace baya son
ciwon sa ya tsayar da rayuwar mu a guri
daya.
Ban tambaye su labarin Safina ba suma
kuma basu yi min ba. Sai da suka zo tafiya
sannan Hassan yake ce min "gobe za'a je
a kwashe kayan yaya Safina a kai mata
Katsina, tare da sabuwar motar da Yaya
Muhammad ya siya mata, har kayan ta da
suke gidan mu ma tace duk a kwashe su a
kai mata Katsina" Hussein yace "Mommy
bata ji dadin hakan ba, Daddy ma haka.
Amma sun ce a barta for now ta huce da
kanta ta gane gaskiya" Hassan yayi ajiyar
zuciya yace "maybe it is for the best" ban
ce komai ba, su ma kuma babu wanda ya
sake cewa komai, Sal da suka zo tafiya na
rako su waje sannan Mustapha yace min
"about that son of hellfire. Ban manta da
shi ba fa. Abubuwa ne suka yi min yawa
kwana biyu shi yasa na ajiye shi a gefe,
amma zan waiwaye shi very soon" na
fahimci zancen Mukhtar yake yi sai nayi
murmushi nace "bana jin akwai abinda
yayi saura a tattare da shi da zaka dauka,
And if I am to advise you zan baka
shawara akan ribar barin komai a hannun
Allah, Sakayya sa tafi duk abinda kake
tunani girma" sai yayi murmushi tare da
gyada kai yace "I will think about that".
Sai da suka shiga mota sannan yace min
"congratulations fa, Allah ya sanya
alkhairi" nayi murmushi "Amen ya Rabbi.
Allah ya nuna mana na yan baya".
Washegari da wuri muka shirya muka tafi
gidan Abba, muka tarar already har sun
shirya abu kadan ya rage musu, naji dadin
yadda Mama tayi involving dina a gyaran
gida tace in shirya mata bedroom dinta in
rufe komai in adana komai yadda zai
zauna as it is har su dawo, I did the best
that I can. Daga nan muka hadu gabaki
daya a ….…….din gidan. Ni da Mufida ne a
can baya, Abba da Mama a tsakiya sai
Muhammad a gaba Haidar kuma yana
driving, Wasa da dariya kawai ake yi a
cikin motar, Haidar ya dage wal su Mama
honeymoon zasu je, Abba yace ina ruwan
sa matar sa ce ko ta sa? Ni dal bana
magana sal an saka ni a ciki kuma na lura
sosai suna kokarin saka ni a cikin magana
in suna yi, Muhammad ne ma bai fiya yi
min magana directly ba, na kuma lura
suna kokarin yin turanci da few hausa
words duk dan saboda ni amma idan su
kadai ne sun fi yin fulatanci,
Bayan munje airport Mama da Abba took
their time to hug each and every one of
their kids, Mama ta zo kaina and she
hugged me too, sai na samu kaina nima
da rungumar ta ina murmushi. Na dago
kaina muka hada ido da Muhammad naga
yana murmushi fuskarsa dauke da farin
ciki, it was like a dream come true for him.
Abba bai rungume ni ba duk da da cewa
yanzun shi muharrami na ne, sai dai he
smiled at me and told me to take care of
myself, ya kuma kara da cewa "idan
Gidado ya dame ki ki kira ni ki gaya min".
Murmushi kawai nayi na sunkuyar da kai.
Sai da suka shiga ciki sannan muka koma,
kiri kiri Muhammad ya kwacewa Mufida
guri ya dawo baya wajena dan ya dame ni,
ita kuma ta koma gaba, Muna barin
airport din Haidar yace "Fiyya, wallahi kar
ki yarda, ki ga Abba ya tafi da Mama
honeymoon amma ke naki angon airport
kawai ya kawo ki? Gaskiya da sake"
Muhammad ya daga murya yace "idan na
tafi da ita kai zaka rasa kwanon abinci. Ai
dama mugunta fitsarin fako ce" Haidar ya
juyo ya kalle mu yace "menene fitsayin
fako?" Dariya muka yi ni da Muhammad
sannan na lakuce masa hanci nace "you
are a very good student Malam
Muhammadu" shima ya rama ace "you
are a very good teacher Safiyya Adam"
daga nan muka kama hirar irin
maganganun hausa da na koya masa,
muka tuna sanda na fara koya masa cewa
mutum karyarsa bata sallah, ranar yayi
dariya kamar me ..….
Gidan Mufida muka fara zuwa dan mu
ajiye ta, amma sai ta jamu muka shiga ciki
wai dama ban taba zuwa gidan ta ba, sai
da muka zagaya ko'ina a gidan, yayi kyau
sosai kuma an zuba naira ba kyar kadan
ba a gidan. A lokacin ne kuma ta bani
shawarar tunda ina koyawa Muhammad
hausa to shima ya kamata ya fara koya
min fulatanci, na kuma amince sannan na
Kara jaddada masa sunan Malam
Muhammad dan fillo,
Ranar kam na dauki darasi sosai na
fulatanci, ya koya min kalmomi da yawa,
na kuma rike su, amma sanda ya gaya min
ma'anar kalmomin da ya koya min sai da
na toshe kunnuwana dan sunyi min girma
a saurare ma ballantana a fade "Allah ya
shirye ka" a fada ina kallon sa yana yi
min dariyar mugunta. Allah ya so ni banje
ina fada a cikin mutane ba. Ya sake jawo
ni, "mun gama lesson one, come, let's
start lesson two" a fara kokarin zamewa
ina dariya "babu wani lesson.….na hakura
da koyon fulatancin tunda ba kalmomin
kirki kake koya min ba" amma sai da ya
jawo ni na karbi darasin dalla dalla na
kuma yi bita sannan nayi hadda.
Washegari Monday Muhammad ya koma
aikin sa, dama hutun sati daya Abba ya
bashi, kuma kasancewar abban yayi tafiya
ya saka bai karawa kansa hutun ba duk
kuwa da yadda yaso yin hakan. Nima
kuma a ranar ne na koma nawa aikin
wanda office dina yake a cikin closet dina.
Sai dai hakan ba wai raba yayi ba sai ma
kara mana dokin gain juna kullum da
yamma, da ranar ma kuma muna makale
da juna almost all through, In ya dawo da
daddare kuma kullum zamu je mu duba
Daddy mu ga idan akwai wani abu da
yake bukata sannan mu dawo gida.
Kamar yadda Muhammad yay alkawari,
da weekend muka tafi Kura local
government, zamfara state. A mota muka
yi deciding yin tafiyar saboda muna son
ganin hanya and have the experience of
being on a road trip together. Ba muyi
niyyar kwana ba amma sai na hada mana
kayan mu set bibbiyu just in case. A ranar
ne kuma na fara using sabuwar mota ta
wadda sai a ranar Muhammad ya bare ta
daga cikin ledar ta. We both dress light
sannan Esther ta cika mana basket da
abinci da sauran kayan ciye ciye, ta kuma
zubawa security suma dan Daddy ya
dage tare zamu tafi da su. Muna yin sallar
asuba muka dauki hanya. Wannan tafiyar
was one of the best memories of our lives
dan mun samu nishadi, nasara da
experience sosai a cikin ta.
Tun kafin mu tafi dama Muhammad ya
kira wanda Abba ya hada mu da shi ya
gaya masa zamu taho, sai kuma ya gaya
min cewa yana da surprise for me a can.
Hakan da naji sai ya saka ni cikin
anticipation and kept me moody a farkon
tafiyar ta mu, amma Muhammad knows
his ways around me dan haka bamu jima
on the road ba na manta da komai sai shi
sai kuma abinda nake ji a zuciya ta game
da shi din.
Munyi hira, munyi dariya, munyi fada mun
kuma mori soyayya, we had to park at one
time a cikin inuwar wata katuwar bishiya
muka danyi uzuri sannan muka muka
cigaba da tafiya muna dariya akan
audacity din mu to do that on the road.
"Baby da wani yazo yayi knocking fa ya
dauka motar ce ta lalace or something?"
"Ai kuwa da sai na cire masa idanu. And
the security won't let anyone come near
us" "idan kuma barayi ne fa?" "Tun muna
ciki ake yi mana addu'a Babe, none of
that will happen insha Allah",
Da muka sake gajiya kuma sai muka sake
tsayawa a wani guri mai kyau da muka
gani muka shimfida carpet din da Esther
ta sako mana a mota muka zauna muka
huta muka ci abinci muka yi sallar. A
wannan lokacin ne muka yi mani major
discovery a rayuwar mu, muka kuma
yanke wani major decision. Mun fahimci
cewa we both have a huge fashion for
travelling, sannan muka yanke shawarar
cewa no matter how long it will take us,
zamu kai ziyara each and every one of the
195 countries of this world. A take na fara
rubuta sunayen countries din da a taba
zuwa ni kadai da kuma wadanda ya taba
zuwa shi kadai sannan da wadanda muke
so mu fara zuwa a tare. A lokacin ne ya
gaya min wani abu da ban sani ba, "I
planned our honeymoon tun sanda na
fara tunanin za'a daura mana aure. I
booked and paid everything bayan an
daura auren an kuma saka ranar biki. Idan
zaki tuna first night din mu together akwai
wasu takardu da na fito da su tare da
rings din nan" na tuna ganin takardun
amma abinda ya faru ranar ya mantar da
ni bibiyar su,
na bude ido cikin mamaki "then why are
we still here?" Ya dan sosa kan sa sannan
yace "I saw jikin Daddy, and I know you
won't want to be away from him in that
condition. Sai na fasa. I cancelled
everything. Yanzu ba gashi muna
honeymoon din mu ba anan?" Ya fada
yana nuna gurin da muke, nayi dariya
amma kuma maganar sa ta taba min
zuciya ta sosai kuma ta kara masa kima
da daraja a cikin zuciya ta. Ina matukar jin
dadin yadda yake da damuwa akan duk
abinda ya dame ni.
Wadannan delays din da kuma
kasancewar ba gudu muke yi ba ya saka
ba mu je Kura ba sai la'asar. Sai da muka
je garin sannan jiki na yayi sanyi,
Muhammad ya kira Alhaji Abubakar ya
gaya masa mun shigo gari shi kuma yayi
guiding din mu zuwa gidan sa. Gida ne
mai kyau, shima kuma babban mutum ne
mai karamci, iyalansa ma haka. Anan
muka samu tarba mai kyau, ga abinci ga
nama da fura da nono. Bama jin yunwa
amma sai da na dan ci kadan duk kuwa da
girgiza min mai da Muhammad yake yi wai
ba'a cin abinci a bakon guri, ni kuma na ci
ne dan suji dadi.
Albishir din da suka yi min shine tun kafin
mu z0 Muhammad ya bawa Alhaji
information din da ya samu daga Daddy,
shi kuma already yayi bincike kuma ya
gane wanne Alhaji Haladu ake magana
akan sa.
"Ban san mahaifiyar ki ba amma na san
yayan sa da yawa, na san shi marigayi
Malam Jamilu (yaya Malam), na san kanin
sa Dauda wanda yayi ajalinsa. Na kuma
san marigayi Alhaji Balarabe, na san da
yawa daga cikin yayansa maza. Da yawa
daga cikin su sun rasu, amma a yanzu dai
akwai mutum uku da na sani wadanda
suke raye a mazan ban sani ba ko bayan
su akwai wani. A matan kuma wadda na
sani ita ce Fatsima" na dago kai ina kallon
sa dan ban san Fatsiman da yake magana
a kanta ba, ban taba jin an ambace ta a
yan'uwan Ammie ba.
[07/01, 10:48 pm] +234 906 816 1960: "Ban san mahaifiyar ki ba amma na san

Sai yace min "Fatima kawar yayar mai
daki na ce, Ita ce karama a cikin yayan
Alhaji Haladu kafin a haifi yayan amaryar
sa da suka rasu. Sanda na gane gidan da
Kuke nema sal na saka ita mai daki na ta
je har gida ta gaya mata labarin ki da
kuma labarin zuwan ki. Matar nan har
kuka tayi na murnar zata gan ki. Na
tabbatar kuma ke ma zaki ji dadin ganin ta
idan kuka je".
Mai dakin na sa ita ta yafa mayafin ta duk
kuwa da girman ta suka rakamu ita da yar
autar yar ta. A fadar ta cewa tayi inda
zamu je babu nisa ba sai mun shiga mota
ba, dan haka muka bar motocin mu a
kofar gidan muka bisu a baya Muhammad
yana rike da hannu na yara da sauran yan
gari suna kallon mu kamar wasu aliens
musamman saboda security din da suka
yi bake bake a bayan mu.
Dan wulakancin Muhammad wai har da
cewa idanun mutanen garin mu zai saka
mishi allergic reaction. Ai kuwa na ce sai
na rama duk sanda muka je yalleman.
Sai da na fahimci kokarin kwantar min da
hankali yake yi yana bani assurance cewa
yana tare da ni, ni kuma tunani na yana
kan wannan Fatsiman da aka ce yayar
Ammie ce, ban taba ganin wani dan uwan
Ammie ba tunda nake a duniya. Gurin da
dan nisa, dan ni kam har sal da na gaji da
taliya amma ban gaji da ganin gari ba, Na
bude ido sosal ina ta kallon titinan su da
layukan su in imagining Baba Hadiza
yadda take yawon tallan abinci, nayi
imagining Ammie da sisters din ta suna
tafiya makaranta, musamman da muka zo
muka wuce ta gaban wata primary sai
matar ta gaya mana wanna makarantar
Ammie na tayi. Jin hakan ya saka na bude
ido sosai ina kallon ta nace "kin san ta?"
Sai tayi murmushi tace "seat din mu daya
a primary one".
Daga nan sai ta fara bamu labarin abinda
zata iya tunawa na Ammie, "tana da wayo
sosai kamar ba yar fari ba. Tana da dogon
gashi. Ina tuna wa da yadda take tsananin
son kanwarta Sauda wadda suke zuwa
makaranta tare, da yadda saudan take
makale mata" sai naji hawaye yana taruwa
a ido na.
A hanya na kira Daddy na gaya masa
abinda muke ciki, dama tunda muka taho
muke waya da shi. Sai ace ya kira Alhaji
Jamil dan Hajiya Kyauta marigayiya
wanda har yanzu sun communicating da
Daddy musamman akan maintenance na
masallaci da boreholes din da aka yi wa
Baba Hadiza a garin, Ya turo mana
number din sa yace mu kira shi idan muna
bukatar wan abu.
Bayan mun wuce primary din ne muka je
gidan, Gidan kasa ne wanda dakunan ne
kawal na kasa amma an zagaye shine da
kara, muna zuwa zamu shiga sal nace da
Muhammad ya tsaya a waje amma sai ya
rike hannuna ya tsare ni da ido kamar
wanda aka cewa in na shiga ba zan fito
ba, a dole muka shiga tare. Guards din ne
suka tsaya a waje da kyar. Matar tana
zaune akan yar baranda a kofar dakin ta
tana tankaden garin tuwo, gefe kuma ga
murhu nan an hada wuta an dora tukunya,
muka shiga da sallama. Ta amsa mana
sannan ta bi yar rakiyar tamu da kallo
"Hajiya Hajara?" Sai kuma ta kalle mu,
idonta ya tsaya a kaina, ina kallon sanda
idanuwan suka bude cikin mamaki sannan
ta mike da sauri kamar zata fadi. Na saki
hannun Muhammad na karasa gare ta ina
kokarin durkusawa in gaishe ta sai ta jawo
ni jikinta hawaye suna bin idonta "safiya!
Jama'a ga Safiya! Ashe ina da rabon
ganin ki kafin in bar duniya Safiya?" Ta
sake ni tana sake kallo na, nima fuskar
tata nake bi da kallo, ba zan ce suna kama
da Ammie ba amma suna yanayi, ina
ganin Ammie a fuskar ta, ta sake mayar
da ni jikin ta ta rungume ni ma sai na
samu kaina da rungume ta ina jin hawayen
da nake rikewa tun dazu suna gangaro
min,
Ta sake ni ta fara zagaye gidan "mai gida!
Mai gida! Harisu! Saminu! Ke Hannatu! Ku
fito ga yata nan tazo! Ku fito ga diyar
Safiya ta zo".
A take mutane suka fara shigowa gidan
nata, wannan ya sa guards dina suka
shigo suma idanunsu a kaina suna
observing duk wanda zai taba ni, ina
kallon Muhammad a tsaye a gefe hannun
sa a cikin aljihunsa yana kallona.
Wadanda ta kira suka firfito daga
dakunan su suna ta kallo na kawai. Sai da
ta nutsu sannan ta gaya min samarin
yayanta ne, magidancin kuma mijinta ne,
yar budurwar da ta kira da Hannatu kuma
ita ce autarta sauran duk ta aurar da su.
Sai da ta gama murnar ta, muka gama
kukan mu ni da ita, sannan ta dauki
tabarma ta shimfida wa Muhammad ya
zauna muma duk muka zauna.
A lokacin take bamu labari "sanda Baba
ya auri Baba Hadiza nice auta a gidan,
dan haka daga ni sai safiya. A shekaru da
kadan Baba Hadiza ta girme min dan ina
da shekaru sha biyu ita kuma tana da sha
hudu sanda Baba ya aure ta. Wannan
yasa a gidan nice zan ce mun saba da ita
dan nice kusan sa'ar ta, tare muka ringa
shiriritar kuruciyar mu, kuma ina nan
gidan ta haifi dukkan yayanta guda uku,
sai bayan haifuwar Khadijah ne aka yi min
aure kafin rasuwar Baba. Dan haka ni nati
kowa sabawa da Safiya. Amma kuma ni
karama ce a cikin yan'uwa na muryata
bata da karfin da zan saka ko kuma in
hana yin wani abu a gidan mu.
Duk abinda akayi musu bana jin dadi sai
dai bani da bakin magana, iyakaci in mun
ware da yan'uwa na inyi mita shima da
zarar sun yi kaina da fada dole in yi shiru.
Mutuwar sauda da batan Safiya suna
daga cikin tashin hankalin da ba zan taba
mantawa da shi a rayuwata ba. Tun daga
nan kuma na fara kukan yin shiru da nake
yi. Na fara neman yadda zanyi in samu
Safiya. Amma ni bani da hali. Mijina bashi
da karfi. Lokacin da labari yazo min cewa
safiya tazo garin nan har taje gidan mu
ranar ko takalmi babu haka naje har gida
amma na tarar ta tafi. Aka ce tayi kudi. A
kace dan yankan kai ta aura. A ka zo aka
ce ita ce mai yankan kan ma. Babu irin
sharrin da ba'a yi mata ba amma babu
yadda zanyi akai. Sanda aka nemo inda
take naso a tafi da ni amma aka ki aka ce
zan bata shiri ne. Daga nan ba na ma
sanin sanda suke zuwa. Sai labarin
mutuwar safiya naji. Nayi kuka sosai,
wannan ya sa aka tafi da ni a lokacin
amma abinda yan uwa na suka yi a gidan
gaisuwar ya sa nayi nadamar zuwa. Na
ganki a lokacin kina karama, kina ta kuka,
amma wadanda suke rike da ke ba zasu
bani ke in rike ba dan basu yarda da mu
ba kuma ban ga laifin su ba. Tun daga nan
duk zuwan da suke yi ban sake komawa
ba dan ina gudun abin kunyar da suke
zuwa yi a can. A karshe dai suka samo
kudin da yayi ajalin biyu daga cikin mu, da
babban yayan mu da kuma autan gidan a
maza, Dauda, wanda shi nake bi. Tun
daga nan sauran yan'uwa suka ce dukiyar
dama ta mutuwa ce, babu wanda ya kara
bi ta kan neman ki ni kuma ban san komai
a kan ki ba ba kuma zan iya mayar da
kaina zuwa gidan ku ba. Na sani a raina
kina raye, na kuma saka raina cewa
watarana zaki zo har nan gidan ki same ni.
Gashi kuma yau Allah ya cika min burina"
Sai da ta gama jawabin sannan tace "ya
sunan kip?" "Safiyya" na amsa murya ta
can kasa "suna na Safiyya".
And that was how I found an Aunt.
Muna gurin ta akayi sallar magrib, ta tuka
mana tuwo ta zubo mana, ina kallon
Muhammad ya dauki cokali yayi loma
daya daga ita kuma bai kara ba. Sai daga
baya na samu yin magana da Muhammad
*kwana ya kama mu, Allah ya sa na taho
mana da kaya" ya gyada kai yana kallon
surrounding din "anan zaki kwana?" Na
daga kai "yes" yayl ajjiyar zuciya, nace
*kai kuma better ka koma gidan Alhaji
Abubakar, na ga masaukin da yayi mana
is decent, zaka iya kwana a can" ya sake
kallon gidan fatsima yace "zaki iya kwana
anan?" Nayi murmushi "zata ji dadi" ya
dan kalli cikin gidan, "just be careful. Your
security will be here with you. Kina da
charge a wayarki?" Nace "eh" na rike
hannunsa "I will miss you, Baby" ina jin
kewarsa a raina tun kafin ya bar kusa da
ni, yayi murmushi "ba yanzu zan bar ki ba
ai. Let's go explore the town muga yadda
yake da daddare".
And it was a good idea, da farko we tried
to mingle with the town people amma
securityn mu suka hana mu sakewa, daga
baya sai muka yi musu wayo muka dawo
ta gidan fatsima muka tambayi Hannatu
ko akwai inda zamu iya fita banda inda
muka shigo? ta nuna mana wata kofa ta
baya da aka rufe da kara muka bi muka
gudu muka barsu suna gadin bakin kofa.
Yawo muka yi sosai hand in hand, muka
zauna a dandali muka sayi awara muka ci,
ko ince naci, dan Muhammad daga guda
daya sai yaki karawa nima da na cinye
guda biyar sai ya hanani karawa ya bayar
da sauran sannan muka sayi rake da
gyada, Muhammad ya zuba mana gyadar
a aljihunsa, muna tafiya a titi muna shan
raken mu muna hira har muka shanve
sannan muka fara in gyadar.
Munyi yawo har sai da kafafuwan mu suka
gaji, babu haske sosai dan haka babu
wanda yake gane mu baki ne. A lokacin
ne muka zo masallacin Baba Hadiza, ina
ganin sa na gane shi dan ina ganin
hotunan shi a wajen Daddy. Sai naga yafi
min girma a ido akan a hotunan. Na tsaya
ina kallon sa, Muhammad ma sai ya gane
shine dan haka ya tsaya. "it is big and
beautiful" ya fada, nima na gyada kai cikin
amincewa "yes it is", sai na cigaba da
kallon masallacin ina mamakin wai da
gaske nan shine asalin gidan kakanni na,
anan aka haifi Ammie, Muhammad kalle ni
'"muyi sallah anan. Dama bamuyi isha ba".
Muka je muka yi alwala a pumps din da
suke a jere a gefe, na lura ana kula da
masallacin sosai dan komai a gyare yake,
na shiga bangaren mata shi kuma ya
shiga na maza mukayi sallah. Na samu
kaina da yin dogayen adduoin ga kakanni
na da iyalin su har da su inna gaje da inna
saade.
Sai da na gama sannan na fito na tarar
Muhammad yana jirana a waje, na lura
mai gadin masallacin jajirtacce ne dan
babu wanda yake bari ya shigo in dai har
ba ibada zaka yi ba dan Muhammad ma
da zai jira ni hana shi tsayawa yayi a
harabar sai da ya fita waje sannan ya jira,
naji kuma voices din yara suna ta karatun
Alkur'ani, sai naji dadi sosai, a raina nayi
niyyar inganta makarantar tare da yiwa
mai gain abun alkhairi.
Ina fitowa Muhammad ya kama hannuna
muka cigaba da tafiya, sai kuma muka
fahimci mun bata dan bamu san hanyar
da zamu bi mu koma gidan fatsima ko
gidan Alhaji Abubakar ba, a lokacin ne
kuma muka lura da security mu suna bin
mu a baya amma sun dan bada distance a
tsakanin mu, Muhammad ne ya gansu ya
nuna min su, na juya na kalle su sai chief
securityn ya daga min hannu, dariya muka
yi, bamu san ya akayi suka nemo mu ba
kuma bamu san tun yaushe suke bin mu
ba.
Wani mutum muka samu muka tambaya,
da kyar ya gane Alhaji Abubakar din da
muke magana akai tunda mu bamu san
wata inkiya ta shi ba ko kuma sunan wani
dan sa, sai yace "ko kune bakin da kuka
2o gidan da zu?" Sai muka yi mamaki
amma Muhammad ya amsa masa da eh
sal yayi mana kwatance. Gidan muka
koma muka dauki motar mu sannan
Muhammad ya mayar da ni gidan fatsima
da already hankalin ta ya fara tashi tana
neman mu. A mota muka yi sallama,
kamar ba zai barni in shiga ba. Yace "take
care" yafi a kirga.
Ina shiga cikin gidan kuwa waya ta tayi
kara naga sunansa sai na saka bluetooth
a kunne na dan na san wayar ba me
karewa ba ce ba.
Ranar mun kusa kwana hira da fatsima da
iyalinta, ni sai naji ina jin nauyin ce mata
fatsima duk kuwa da cewa yayanta ma
haka suke ce mata, sai na fara ce mata
Aunty, suka yi ta min dariya amma naki
dainawa har dai ta fara amsawa. Tayi min
hirarrakin Ammie sosai. Ta kuma bani
labarikan family din mu da abubuwan da
suka faru, tace su uku suka rage a mata,
maza ma su uku ne. Sai jikoki wadanda
suma duk sun girma sun manyanta tunda
dama wadansu jikokin sun girmi Ammie
ma ballantana ni. Itama da take karama
yayanta gabaki daya Hannatu kadai na
girma, Nima na basu Labarin abubuwan
da nake ganin ya kamata su sani kamar
matsayin Muhammad a gurina, amma ban
bude cikina nayi magana sosai ba kamar
yadda Daddy ya gargade ni, duk da dai
banga alamar cutarwa a tare da su ba but
time will tell.
Ta saka aka dauki katifar ta ta kan gado
aka yi min shimfida anan tsakar gida
saboda basu da wuta a gidan, ala daura
min net, na shiga na kwanta ina jin dadin
iskar da take kada ni. Amma kuma dai
baccin banyi wani mai nisa ba saboda
kukan kwari da kuma yanayin chanjin
bakon guri ga kuma sararin samaniya
tarwai a kaina, Duk da haka da safe na
tashi fresh saboda fresh air din da na sha.
A niyyar mu da wuri zamu wuce
kwatarkwashi amma taki yarda, sai da tayi
ta yawo dani gidajen yan'uwa, duk sauran
yan'uwan su sai da ta kaini wajen su, naga
murna a idon wadansu, na ga mamaki a
na wasu, sannan naga mixed feelings a
gurin wadansu, sai dai ban damu ba, bana
nufin kowa da sharri kuma ina addu'ar
kariya daga sharrin kowa. Muhammad ya
bude bakin aljihu da kudin da ban san ma
ya taho da su ba ya ringa raba musu. Ai
kam da yawa ya saye su da wanna kudin.
Da kyar muka samu muka kwace bayan
azahar muka bar garin bayan ta saka nayi
mata alkawari tare da rantsuwa cewa zan
dawo. Ni dariya ma na ringa yi. Tace ta
zata sati daya zanyi. Na tabbatar mata
zuwa nayi kawai gain guri amma tunda
na gansu har sai sun gaji da ni.
Daga nan Alhaji Abubakar ya hada mu da
wani yaron sa muka tafi kwatarkwashi.....
Bani da hope din ganin kowa nawa a can
duk kuwa da cewa Alhaji Abubakar ya
gaya min yana da another surprise for me,
amma abinda na tarar yafi wanda na gani
a Kura faranta min rai, Yayun Baba Hadiza
guda biyu Jabiru da Audu suna garin a
lokacin, Shi Jabiru shekaru ne suka yi
masa yawa and he chose to spend the
last of his days a inda iyayensa suka rasu.
Shi kuma Audu wanda shine Baba Hadiza
take bi ashe tun zagayowar sa garin ta
farko wadda yayi musamman dan kanwar
ta sa sai kuma yazo ya tarar da munanan
labarai a jere, babu Hadiza kanwarsa
babu yayanta. An dai ce babbar
haukacewa tayi ta bi duniya saboda
tashin hankalin abinda ya faru. Wannan
shine last labarin Ammie da yaji. Ya kuma
yi kuka tare da takaici mai yawa akan
hakan dan yana son kanwarsa Hadiza
sosai kasancewar ita kadai ce yar war sa
mace, Daga nan bai kara barin gari ba,
Dagaci ya bashi guri a bayan gari ya kafa
ruga suka zauna shi da iyalinsa yana fatan
watarana Safiya zata dawo kuma zata z0
ta neme su. Lokaci zuwa lokaci ya kan je
Kura ko zal samu labari, amma babu
labar in komai kuma shi bal ma san gurin
wanda zai nemi labarin ba. Bai san kowa
ba sai Alhaji Haladu sai kuma wani kanin
sa. Shima kuma kanin ba'a jima ba ya
rasu.
Daga baya ma sai ya tarar babu gidan
Alhaji Haladu an rushe anyi masallaci. Ya
kan shiga masallacin duk sa da yaje yayi
sallah ya fito amma bai san komai gane da
masallacin ba. Shima ya manyanta, amma
da kwarinsa kuma da yake jikin fulani ne
babu kiba sai ya kasance girman bai kama
shi sosai ba.
Nayi kukan ganin su, kamar yadda suka yi
nawa. Jabiru har sai da na tausaya masa
na koma ni nake bashi hakuri, duk ya
dauki laifin abinda ya samu Baba Hadiza
ya dora akan sa, gani yake laifin sa ne
tunda yazo gari lokacin mutuwar Alhaji
Haladu. Amma ya tafi ya barta da kananan
yara bayan ya san bata da mataimaki sai
Allah,
Sai da aka gana koke koke kuma aka fara
murna. Fulatanci suke yi suma sai hausa
jefi jefi, a lokacin na fahimci fulatanci
dialect daban daban ne dan nasu ya
banbanta sosai da na Muhammad. Suna
gane juna amma ba sosai ba, Sai an dan
hada da hausa wani lokacin kuma sai an
kara bayani, shi kuma sai yayi min bayanin
abinda ban fahimta ba. A haka akayi
communication din. Sai inno matar Audu
ta saka ni a gaba da tsokana wai
maimakon ni zan ke fassarawa mijina
tunda gidan mu aka zo amma shi yake
fassara min. Sai kuma ta tafi wani abu da
ya saka shi murmushi tare da yi min
gwalo. Na harare shi sannan na tambaye
shi abinda tace sai yace cewa tayi ya fi ni
kyau. Ai kuwa na dage nace kishi take yi
tunda ni jika ce a wajen ta tana son ta
kwace min miji.
Sai a fahimci Muhammad yafi sakewa da
su akan a Kura. Nan da nan aka yanka kaji
aka soya mana su aka dama mana kunun
nono, kunun yayi min dadi sosai har sai da
na tambayi Khadija autar Baba Audu ta
koya min yadda ake yi. Muka ci sosai
muka koshi. Muhammad da kansa ya ce
wa dan rakiyar mu ya koma anan zamu
kwana, naji dadin hakan sosai, suma
kuma mun raba dare da su muna hira. Sai
naji nafi sakin jiki da su, na basu labaran
duk abinda ya faru da kuma rasuwar
Ammie na tare da matsayina a yanzu.
Sunyi mamaki sosai sun kuma yi jimami
tare da godiya ga Allah. Sai na basu
labarin Daddy na da halin da yake ciki na
rashin lafiya. Baba Audu yayi shiru sannan
ya tambaye ni abinda yake damunsa, na yi
masa bayanin cutar duk da bansan sunan
ta da hausa ba ballantana da fulatanci. Sai
yace "dan zaku tafi zan bi ku in ganshi.
Zamu warkar da shi da ayar Allah tare da
sauyoyin mu na daji"