← Book details Safiyya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 2 OF 3

Part din sa ya wuce, sai daya bude ya

Safiyya Part 1 Complete Hausa Novel · about 240 min read

shiga sannan ya tuna bai fito da kayansa
daga mota ba, ya juya ya fita ya tarar har
lokacin tana zaune a mota tana kuka. Ya
fito da kayansa ya ajiye ya bar mata nata a
ciki. Mai gadi yazo da sauri ya gaishe shi
ya dauki kayan ya wuce ciki. Sai a lokacin ta fito daga motar, ta tsaya tana kallon sa suna magana da mai gadin, yan aikin ta biyu da cousin dinta da suke gidan suka fito ta bude booth ta basu kayan ta suka
shiga da shi cikin gida.

Sai da ya gama yiwa mai gadi magana ya
juya zai tafi sannan ta kira sunansa
"Muhammad" ya dakata amma bai juyo
ba. Ta karasa bayan sa ta tsaya sannan
tace "I am pregnant" still bai motsa ba
ballantana ya juyo ya kalle ta. Ta cigaba "I
wanted to tell you tun kana can, amma ba
ka daukan waya ta ba ka duba messages
dina. At least idan banci albarkacin
soyayyar da nake yi maka ba ai ya kamata
yanzu in ci albarkacin abinda yake ciki na"

Ya yi gaba, pretending kamar bai ji abinda
ta fada ba amma ransa tafasa yake yi.
Yana zuwa dakinsa ya zauna akan gado
ya dafe kansa da hannayensa guda biyu.
"Ya Salam" ya ambata. Yanzu shi ya zai yi
da wannan yarinyar ne? Ta zame masa
karfen kafa,

Tashin hankalin sa guda uku ne akan
wannan cikin. Na farko ya san yanzu
¡yayen sa sun sani, za kuma su dauki
hakan a matsayin ya karbi auren kenan. Hakan kuma zai kara masu wahalar amincewa idan yace zai rabu da ita. Na biyu kuma he just can't imagine Safiyya
seeing Safina pregnant with his child,
tunda dai tasan yadda aka yi aka samu
cikin, it will break her to pieces. Yasan
cewa Safiyya ma zuwa yanzu akwai
tabbacin tayi irin wanna mu'amalar da
mijinta Mukhtar, amma ai shi bashi da
alaka da Mukhtar but Safina is like a sister
to her. Abu na uku kuma mafi muhimmanci shine ya zai yi da yaron ko yarinyar da zata haifa masa? Anya zai iya son su yadda ya kamata kuwa?
Considering irin tsanar da yayi wa
mahaifiyar su. Baya son ya zama bad
father kamar yadda yake bad husband.

Her🧕🏻

Kamar yadda nace na gama shafe babin
Mukhtar haka nayi, ban kuma ko da tayar
da maganar ba. Sau da yawa Mommy ta
kan saka ni a gaba tana so muyi maganar
and she will be like "yaron nan ya dage
dai shi ba zai yi sakin nan ba. Ai kuwa
¡yayen ne ya kamata su matsa masa.
Maybe ya dauka bluffing kike yi ba da
gaske kike ba maganar court din nan. To in bai sake ki bama in aka rufe shi dole alkali ya raba auren kinga a yayi biyu babu" in tana yin maganar na kan chanja
topic ko kuma in ina da abinyi inyi excusing kai na in tafi inyi.

Twins sun zo da weekends sun gan mu
and I guess Mommy ta gaya musu abinda
yake faruwa, suka zo suka saka ni a gaba
"yanzu Yaya Fiyya ya ma za'a yi ki barshi?
Ai wallahi ki kai shi kara. Make him pay for
what he did. Shege mugu azzalumi" sai
nayi murmushi kawai na rabu da su. Daga
baya suka ce sai sunje har gida sun same
shi, anan ne nayi magana na hana su nace
babu ruwan su a ciki, maganar manya ce
kuma manyan will take care of it.

Har lokacin Mukhtar bai hakura da turo
min messages ba, na safe daban na rana
da ban na dare da ban. And a cikin su all
maganar sa daya ce "ina matukar son ki
Safiyya, dan Allah ki bani dama in gyara
kurakurai na. I want to take care of you
and our son" Or something like that.

Ranar nan kuma har da cewa "duk abinda
ya faru laifin ki ne. Da kin karbi soyayya ta
tun farko da duk haka bata faru ba. We
will have been happily married by now.
Wallahi Safiyya ina son ki"

A lokacin ne na bashi amsa "ta waya zaka
turo divorce note din ko kuma a takarda zaka rubuto? In a waya ne please send it to my email for safe keeping".

To take my mind off things sai na mayar
da hankali kan renovating Oasis, a bawa
wani kamfani contract din gyaran
buildings din ciki har mun zauna mun
gama tsara komai. Na kuma samu
landscape designer shima mun tsara
yadda design din harabar gurin zai
kasance. Duk sun fara aiyukan su already.

Sai na mayar da gurin wajen zuwa na in
debe kewa, wani lokacin mu tafi tare da
Daddy wani lokacin har da Mommy da
Mustapha. Sai na fahimci cewa Daddy
yana jin dadin zaman Abuja yanzu dan ko
maganar komawa Kano baya yi. Ya kan i
min maganar Mukhtar shima sometimes,
yace lokaci ya bawa Uncle Ahmad ya ga
idan zai iya controlling dansa, if not duk
abinda muka yi ba zamu zama mu muka
tozarta familyn ba, cos munyi duk abinda
zamu iya yi.

Ranar nan na tafi Oasis ni kadai, Daddy
yayi baki wani abokinsa da matarsa dan
haka shi da Mommy suna gida, and I
noticed motar Mukhtar tana bina a baya
through my center mirror, Ban kula shi ba
na cigaba da tafiya ta har naje Oasis din
and I told ma'aikatan da suke aiki a gidan cewa someone has been following me,
kar su barshi ya shigo ina zargin mugu ne.
Ai kuwa ina jin su suna hayaniya a bakin
gate, har yan unguwa suka fara taruwa
and I guess he ran away.

A lokacin ne na kira barrister Umar and
told him ina bukatar body guards, like
always, he showed concern amma nace
masa zamuyi maganar later. Bana son in
saka su a cikin maganar har sai Mukhtar
ya zabi one of the options din da na
bashi. Babu bata lokaci ya samo min
guards din manyan gaske su uku, and
they also have military training, nan take
na dauke su aiki, aikin su shine kula da
lafiya ta. Duk inda na je suna bina a baya.
Ba wai a mota daya muke tafiya ba but
suna motar su suna bina a baya ba tare
da ya zama obvious cewa suna bina ba. A
gida ma kuma they keep guard, sun kara
zama another layer of security a gidan.

Na nuna musu pictures din Mukhtar da na
motar sa and I asked them to keep a look
out for him, bana sonsa anywhere close
to me, Ai kuwa ranar nan na sake fita ni
kadai purposefully dan ina son ya bini din,
like I expected, he followed me har Oasis,
na shiga nay packing and my guards
packed after me na gaya musu "in yazo
ku kama shi ku mika wa police shi, in yayi resisting ku dake shi"

Ai kam yaci duka, dan dama na san zai vi
resisting din, sai da suka yi masa laga
laga sannan suka mika shi hannun yan
sanda da sunan yana stalking dina, I
thought zai gaya musu ni matar sa ce but
he didn't, maybe he is not as dumb as I
thought. Sam ban gaya wa Daddy ba sai
da uncle Ahmad ya kira shi ya gaya masa
wai Mukhtar yana hannun police, shima
kuma yace ba zaiyi bail din sa ba. A haka
dai sai da yayi three days sannan wani
kanin umman sa yaje yin bail din sa, a nan
barrister Umar yaje on my behalf kuma ya
nemi a tura su court dan yana son
Mukhtar yay signing restraining order
against me. They went and he signed. A lokacin na
kara fahimtar cika baki yake yi ashe da
kurin banza.

I continued waiting for my divorce paper
and it finally came. Ranar ina daki a zaune
na gama interviewing wan digital
designer da nake son dauka aiki dan yake
zana mana patterns masu kyau na
atampopi da laces, sai ga Mommy ta
shigo da takarda a hannun ta. Ta zauna
tana kallona fuskarta da murmushi sai
kuma ta miko min tace "finally ya rubuta" na karba ina jujjuya takardar a hannuna duk kuwa da cewa a zuciya ta na san ta mecece.

Tace "Ahmad ne da kansa yazo ya kawo
wa Daddyn ki, yace sai da suka saka shi a
gaba shi da mahaifiyarsa suka ce zasu
tsine masa sannan ya rubuta. He kept
hoping cewa zaki chanja mind dinki ki
koma gidan sa" nayi shiru dai ban ce
komai ba. Sai kuma na mayar mata da
takardar "ku zaku rike a hannun ku ai"
tace "ki fara budewa ki karanta. Saki baya
tabbata sai sakon ya isa zuwa ga wadda aka saka".

Na bude na karanta

"Ni Mukhtar Ahmad Muhammad, na saki
matata Safiyya Adam Muhammad saki
daya. Ina fata da kuma saka ran watarana
zata fahimci girman soyayyar da nake yi
mata za kuma ta yafe min mu dawo mu
cigaba da auren mu"

Na ninke ta na mika mata. Ban damu da
adadin sakin da yayi ba in dai yayi din
shikenan, abinda na sani shine ko duniya
zata taru a kaina ba zan koma wa auren
sa ba.

Mommy ta karba ta mayar cikin envelope
din ta tace "to alhamdulillah, Allah ya sa
haka shi yafi alkhairi. Insha Allah ma
hakan shine mafi alkhairi" na sunkuyar da
kaina kasa nace "Amen" ta mike tsaye
tace "sai ki fara lissafin idda kuma" na
girgiza kaina nace "babu iddar sa a kaina"
sai ta fadada murmushin ta "masha Allah.
To magana ta kare kenan. Bara inje in
sanar wa da Adam. Allah ya kawo miki na
gari wanda mutuwa ce kadai zata raba
ku" nace "Amen" a hankali, sai kuma
nabi bayanta da kallo ina tunanin har
yanzu bata hakura da hada aurena da
Mustapha ba. A gurin ta wannan rabuwar
da muka yi da Mukhtar kamar second
chance ne ta samu na hada ni da Mustapha.

Sai da ta fita sannan na sauke wata
katuwar ajiyar zuciya. Free at least. Naji
kamar an dauke min wani katon dutse
daga kaina. Na rufe idona tare da saka
hannayena biyu na rufe fuskata da su
"'alhamdulillah, alhamdulillah,alhamdulillah"

Na jima a haka sannan na bude fuskata na
dauko waya ta na kira barrister Umar
"hello barrister, Ina bukatar gain ka
Please, yaushe kake free?"

And then two days later muka hada case file akan abinda ya faru da ni. Hankalin barrister Umar ya tashi sosai da na gaya masa abinda ya faru da ji. Babu yadda bai yi da ni ba akan in barsu suyi bincike
amma nace su ajiye file din kawai, he even
bluntly told me cewa Mukhtar yake zargi.
"That guy da yake binki ranar nan" na
girgiza kaina "just keep the file in your
firm. Let's wait and see. Duk ranar da ya
ambaci da na a matsayin dansa a ranar
zaku kai shi court ko bani da rai, and
make sure he gets the highest possible
sentence".

A haka na bar case din a hannunsu, legal
firm ne suke da shi dan haka ba wai
barrister Umar ne kadai ba, ko babu shi
akwai wasu, and the case is with them.

And that was another weight off my
shoulders.

Ina komawa gida na hadu da Mustapha.
Ya bini cikin gida yana min magana. Muka
tsaya a gaban stairs. Yace "Mommy ta
gaya min what happened. Allah ya sa
haka shine mafi alkhairi" nace "Ameen,
Nagode" yace "are you now done with
him? Zan iya cin ubansa yanzu?" Nayi
murmushi "be careful, am sure he is
angry yanzu, kar kaje garin fansa a fanso
ka" yayi murmushi "you don't know me, you have no idea what I can do. Will you like to know" na girgiza kaina "no thank you. But just know that na gaya maka
abinda Mukhtar yay because I think you
deserve to know. Duk abinda zai faru a
tsakanin ku babu hannuna a ciki. Ko me
zaka yi masa bani na saka ka ba kuma ba
dan ni kayi ba. Is that clear?" Yace "yes
ma, sound and clear" na wuce shi na fara
hawa stairs and I saw Mommy looking
down at us, sai kuma ta juya kamar ba
kallon mu take yi ba ta koma ciki. Two Days after that ina daki a zaune ta shigo. "Safiyya shirya mana muje mu duba Safina. Bana jin dadin yadda alakar
ku take tafiya wallahi. So nake yau muje
mu wuni a gidan ta" na fara girgiza kaina
"Mommy bana jin dadi" na dafe kaina
"kaina ne yake ciwo" ta saki baki tana
kallona "yanzu fa na ganki kuna ta hira da
Esther a kasa, and suddenly ciwon kai
yazo dan nace muje gidan Safina?" Na
zauna tare da dafe kaina "yanzu bayan na
hau naji kaina ya fara ciwo" tayi ajjiyar
zuciya "ai shikenan, Allah ya sawake"

Tana fita na koma na kwanta ina
daddanna waya ta. I have been thinking
about him a lot, duk da ma dai ina kokarin
keeping kaina busy to stop myself from thinking about him. Dan future din mu together is very blurry ba kuma na son sake saka mu a cikin heartbreak irin
wanda muka shiga a baya, ko kuma ma
more than that.

Na dan jima a haka ina scrolling blindly
through social media, ba na ma gane me
nake karantawa sai kuma a mike na ajiye
wayar na shiga toilet nayi wanka na fito
and I took my time to dress up elegantly.
Very classy but less flashy. Na saka turare
na yafa mayafì na sannan na dauki
glasses dina na saka. I looked at myself in
the mirror and smiled.

Na san ba lallai bane mu hadu da shi a
gidan ba, but at least zuwan nawa da
kuma yadda nake looking plus the fact
that I am now single zai hana Safina bacci
a daren yau. Wannan shine target dina.
But what if muka hadu? Na tambayi kaina
tare da rike kirjina saitin zuciya ta. Naji
kamar in fasa zuwa but wani abu da nake
ta tura wa kasan zuciya ta for months
shine yake taso min. My heart hoped with
every vein and artery in it that my eyes
will see him.

Na bude kofa na fita baranda a dai dai
lokacin da Mommy ita ma ta fito daga
dakin ta. Ta tsaya tana kallona da baki a sake, I smiled at her nace "na shirya Mommy" ta rufe bakin tace "ciwon kan ya warke kenan?" Na sake murmushi sai na
wuce ta na sauka kasa. Ina jinta ta sauko
tana kiran Mustapha, na wuce falo na tafi
gurin Daddy. Ina shiga na cire glasses
dina na rike su a hannu na. Yana zaune
yana kallon news, na gaishe shi and naga
alamar yaji dadin ganina. "you look great"
yace nayi murmushi "Thank you Daddy"
sai kuma na gaya masa inda zamu je and
ask him if he needs anything kafin mu tafi,
duk da dai twins suna gidan kuma ba da
su zamu tafi ba. And akwai yaron da yake
masa errands a part dinsa.

Ya girgiza kai yace "bana bukatar komai.
A dawo lafiya" na mike na mayar da
glasses dina sannan na fita.

Motar Mustapha naga an fito da ita, na
tsaya a gefe ina jiran su fito, Mommy ce ta
fara fitowa tana ta lissafa wa Esther
abubuwan da zata yi kafin mu dawo. Tana
zuwa ta shige bayan motar, na gane
abinda ta shirya, tana so mu zauna tare
da Mustapha a gaba and I didn't care,
Esther ta tsaya tana kallona tace "kinyi
kyau Madam" nayi mata murmushi tare
da thumbs up sannan na wuce na shiga
gidan gaba,

Mustapha ya fito shima da sauri ya shiga.
Muna daukar hanya Mommy ta fara fada
"yaron nan mijin Safina she ya dawo?
Amma ko a ransa bai yi tunanin ya kamata
yazo ya gaishe mu ya duba jikin Daddy
ba. Wannan wanne irin siriki ne Allah ya
hada ni da shi? Ko waya bai yi ya gaishe
mu ya gaya mana cewa ya dawo ba. Ita
kuma munafuka tayi shiru dan bata son
fadar laifin sa dan kar inyi fada..." na jawo
ear piece daga cikin jaka ta na saka a
kunne na sannan na kunna kida a waya ta.
Ina kallon Mustapha yana kallo a tare da
murmushi amma bai ce komai ba.

Muna yin packing a gidan I saw his car, I
saw his two cars, jikina kuma ya bani yana
gidan. Na bude kofa na fita for the first
time ina karewa harabar gidan kallo, naga
motar Mommy a gefe wadda ta bawa
Safina. Ni kaina bani da tabbas din abinda
nake aikatawa but zuciya ta tana ta zuga
ni. Na san a cikin biyu za'a yi daya, ko dai
in breaking heart din Safina ko kuma ni in
kwaso nawa heartbreak din. Zuciya ta
kuma yanzu bana jin tana da karfin karbar
another heartbreak,
Nabi bayan Mommy zuwa part din Safina,
ina shiga naji nadamar zuwa ta sauko min,
wani feeling nake ji na kishi a cikin
zuciyarta. Kishi mai zafi but na daure. Na
samu guri na zauna tare da daukan kafa
daya na dora akan daya. Mustapha ya zauna opposite me tare da kwalla wa Safina kira "kina ina ne wai?" Naji ta amsa daga ciki.

Mommy ta shigo tana mita. "Yana gidan,
Zan ga karyar rashin kunyar sa yau. Zan
gani idan ba zai fito ya zo ya gaishe ni ba"
na gyara zama na. This is a drama worth
watching. Ni na san rikicin Muhammad.
Idan ya rikice tsohuwar mota ma ta fishi
dadin sha'ani. Ba'a controlling dinsa.

Ina nan zaune aka kawo mana drinks aka
ajiye, Mommy ta mayar da mitar ta kan
Safina "ba zata fito bane ba ko me? Lemo
muka z0 sha ne wai? Idan dangin mijin
sunzo suma haka kike musu?" Safina ta
sake amsawa daga ciki sai gata ta fito
tana daura dankwalin. And she startled
when she see me sitting there looking all
pretty and elegant, one leg on top of the other.

Sai da Mommy tayi mata magana "Safiyya
ce kike kallo haka? Ko don ki ya samu
matsala ne?" Ta wuce ta gaba na, jikin ta
yayi matukar sanyi taje gurin Mommy
"Mommy sannu da zuwa, Ban dauka tare
zaku zo ba shi yasa" Mommy ta tabe baki
"kin santa kamar mai aljanu, da tace ba
zata zo ba kuma sai ta chanja shawara" ina jin su ta gaishe da Mustapha sannan ta juyo tana yi min magana, nayi pretending kamar banji ba sai Mustapha
ya dan buga kujerar da nake kai, na kalle
shi sai ya nuna min Safina, na cire ear
piece din da yake kunnena ya yi mata
murmushi brightly nace "hi Safina. Ya
kike? Ya mijin ki? Hope yana gida dai yau
mu gaisa" And she lost all colors, her
white skin became very pale.

Mommy ta dora daga inda na tsaya "nima
ina fatan yana gidan. Dan yau sai na yi
masa wankin babban bargo a gidan
nan......" Na mayar da ear piece dina cikin
kunne na na cigaba da jin waka ta. Sai dai
har cikin bakina daci nake ji. Wani iri nake
ji a raina. Wani irin kishi nake ji a zuciya ta.
Kishin da na jima ina dannewa ranar sai
naji yana kokarin yafi karfina. Mommy ta
tura Safina ta kirawo mata Muhammad.
Bata jima ba ta dawo "Mommy bacci yake
yi" "bacci kuma?" Mommy ta fada "wanne
irin bacci? Kuma ni ina kiransa ba zaki iva
tashi sa ba?" Safina tayi kamar zata yi
kuka, Mommy ta saka salati "wai tsaronsa
kike ji ne ko menene?" Safina ta zauna
akan hannun kujera "Mommy ai ba yanzu
zaku tafi ba. Kafin ku tafi zai tashi" amma
kamar kara zuga Mommy tayi, haka ta
juya ta dake komawa sai gata ta sake
dawowa. "Kofar dakin nasa ma a rufe take" Mommy tace "wanne irin kofa a rufe? A cikin gidan sa in zaiyi barci sai ya rufe kofa? Wanne irin aure kuke yi ne
wai?" Safina bata ce komai ba sai Mommy
ta sake cewa "kinga yadda kika kara
lalacewa kuwa? Da da baya nan kinyi kiba
kinyi kyau amma daga dawowar sa j
yadda kika koma. Gaskiya ba zan iya
cigaba da yin shiru a lamarin nan naku
ba" ta dauko wayarta, Safina tace
"Mommy wa zaki kira?" Mommy tace
"'uwarsa zan kira, ita ta kira shi tace yazo
nan ya same ni ina neman sa tunda ke ba
zaki iya zuwa ba" Safina ta mike tsaye,
obviously distressed.

Sai ta wuce mu tayi hanyar kitchen, sai
kuma ta leko ta kira sunana "Safiyya dan
zo mana ki ga girkin nan, ke ce gwanar
girki" ina jinta amma yanzu ma sai da
Mustapha ya sake taba kujera ta sannan
na cire abin kunne na. Mommy ce tace
min "je ki ga wacce kwamacalar take
hada mana a kitchen din".

Ni nasan babu wani girki da zata nuna
min, but bani da uzurin kin zuwa, na tashi
na tafi yayin da Mommy ta fara waya da
mama Muhammad.

Ina shiga kitchen din ta ja hannuna "I want
you to leave this house right now" na gyara tsayuwa ta nace "or what? Me zai faru idan ban fita ba?" Tace "zan gaya masa. I swear to God idan baki rabu da
shi ba zan gaya masa" nayi tsaki "wa ya
rike ki? Je ki fada masa mana. Matar da
ko bedroom din mijinta bata da ikon shiga
ita take cika wa mutane baki. Please go
and tell him and I assure you zaki farka ne
ki ganki a gadon asibit'" and the look on
her face was almost pitiful, but I didn't
pity her, na je gabanta na tsaya nace "he
is mine. You stole him. I am taking him
back. Na gaya miki tun dadewa, da kafafuwan ki
zaki ruga a guje ki barshi kamar yadda
kika kawo kanki da kafafuwan ki".

Ta danyi murmushi tace "haka ne. Ni na
kawo kaina. And I know he will choose
you over me. But do you think he will
choose you over his child" ta fada tare da
kama hannuna ta dora akan marar ta.

Nayi sauri na janye hannu na ina jin gabaki
daya jinin jiki na yana kafewa, She is
pregnant, Na gaya wa zuciya ta. She is
pregnant with babyn Muhammad. Naji jiri
yana kokarin dibana. Ta kara matsowa
kusa da ni tace "he is mine. Nawa ni kadai. And I will do anything to keep him".Sai kuma ta juya da sauri ta fita daga kitchen din.

Sai da na dafa bango sannan na iya
tsayawa sosai. Wani daci nake ji a cikin
zuciyata. No matter how I tried babu
abinda nake gani a ido ma sai Muhammad
da Safina doing the deed. Har wani baci
nake ji a cikin zuciyata.

Na lallaba na fito bakin kofar kitchen din
ina kallon Mommy suna magana da
Mustapha amma bana jin abinda suke
cewa dan ji nayi kunne na ya toshe gabaki
daya. Na cigaba da bin bango ina tafiya
har nazo tsakiyar falon a dai dai lokacin
da Muhammad ya turo kofa ya shigo.

Yana shigowa idonsa ya sauka a kaina. He
looked startled kamar zai juya ya koma a
guje sai kuma yayi regaining kansa ya
tsaya yana kallona. Jallabiyya ce a jikin sa
ruwan toka mai duhu da ta dace sosai da
fatar jikin sa, sumar kansa da ruwa a jiki
daga alamar daga wanka ya fito dan har
akwai alamun ruwan a jikin jallabiyyar ta
sa, idanunsa da fuskarsa suna nuna
alamar yayi bacci mai nauyi. Sai naga
kamar bai taba yi min kyau irin yau ba.
Kamar ba'a taba yin namiji mai kyawun sa
ba.

It took him a lot of efforts to take his eyes
off me ya mayar da su kan Mommy
sannan ya durkusa a gaban ta yana
gaishe ta. Bata amsa ba ta kama wanke
shi din kamar yadda tayi niyya "wato da
baka yi niyyar fitowa ba sai da na kira
Zainab ko? Ita ce kadai zata yi maka
magana kaji ni ban isa in aika a kira ka
kazo ba ko?" Ya sake dago kai ya kalle ni
sannan yace "ina bacci ne, ban san kunzo
ba, sai yanzu ta kira ni tace kun zo" tace
"na tura matar ka ai tace dakin a rufe.
Wanne irin aure ne wannan. Ni fa ban
ganewa auren ku ba sam. In ba zaka yi ba
babu lallai babu dole ka dawo min da yata
ina son kaya ta. Ga Safiyya nan ma da
auren ta ya mutu babu abinda ya same ta,
ita ma......." "Safiyya?" Ya maimaita tare da
sauri ya dago kai ya kalle ni. Ina cikin
idonsa na karanto abubuwa da yawa. Naji
wani karfi ya zo min na zagaya na dauki
jakata na mayar da glasses dina sannan
cikin sauri na ratsa tsakiyar falon nayi
hanyar waje,

Mommy ta katse maganar da take yi tace
"ina zaki je" ba tare da na tsaya ba nace
"gida zanje, kaina ne yake ciwo" ina wuce
shi ya mike tsaye "Piya!" Ya kira sunan da na manta rabon da inji an kira ni da shi. Sunan da ya kara stirring abubuwa da yawa a cikin zuciya ta. Amma kuma ido na babu abinda yake gani sai shi da Safina,
making a baby. Na wuce shi ba tare da na
kalle shi ba, Safina ta mike tsaye da sauri
a lokacin da shima ya biyo baya na da
sauri "Piya" ya sake kira na amma ban
waigo ba sai ma saurin dana kara nayi
hanyar gate.

A cikin falon muna fita Safina ta juya gurin
Mommy tace "congratulations. You just
ruined my life. Me yasa ba zaki yi shiru
ba?" Sai ta juya da sauri tayi akin ta.
Mommy ta bi hanyar da muka fita ni da
Muhammad da kallo sannan ta bi hanyar
da Safina ta bi ita ma da kallo sai kuma ta
bude hannun ta alamar tambaya "me ya
faru wai? me nace?" Ya juya tana kallon
Mustapha ta sake cewa "me nace?"
Mustapha ya daga kafada alamar shima
bai sani ba.

Maman Maama✍🏻

Longest episode ever ko?😁
I just want to finish this novel but I am
loving it
[07/01, 10:46 pm] +234 906 816 1960: ❤️‍🩹Safiyya❤️‍🩹

Episode Forty Nine : Broken


*Contact Bojuwa HERBAL'S for all your*
*kayan mata for*
*Amarya*
*Uwargida*
*Bazawara*
*Mai jego*

*Saiwowin sanyi gangariya da na dahuwar
kazar sababi har da na tattabaru da
ciccibi all from Chad.*

*Kayan gyara masu kyau da inganci kala
daban daban, special maganin sanyi for
women of class*.

*Contact Surayya HALIN YAU on*
*08032773332*

*. . .

Ina zuwa gate na kama kokawa da kofar
na ma rasa inda zan murda in bude, il
nake yi kamar wuta ce take ci a cikin
zuciyata, Mai gadin su ya taso da sauri ya bude min amma kafin in fita Muhammad ya karaso. Kusan tare muka fita nayi kokarin kara sauri amma sai ya rike jaka
ta, na juyo a fusace na nuna shi. "Sakar
min jaka" naga yanay in sa gabaki daya ya
chanja fuskar sa tana nuna alamomin
tambaya da yawa "Safiyya? Me ya bata
miki rai haka?" Na sakar mass jakar nayi
gaba, dan rainin hankali, wato ni zai raina
wa hankali har yayi min wata tambaya
marar ma'ana.

Ya sha gabana da sauri yana kokarin hada
ido dani, saura kadan muyi karo saboda
saurin da nake yi. "Piya dan Allah ki tsaya
muyi magana" na zagaye shi naci gaba da
tafiya, bana son ganin shi sam, bana
kuma son jin muryarshi dan ji nake yi
kamar in shaki wuyansa, munafiki.

Ya sake rike mayafi na, "Piya Please now.
Me nayi ne wai ni?" Na juyo da sauri ina
kallon sa cike da masifa sai na nuna masa
gidan sa nace "she is pregnant" nan take
naga yanayin fuskar sa ya juye zuwa guilt,
pure guilt. Ya saki mayafin nawa a hankali,
bana bukatar wani dogon bayani kuma na
san ba karya take yi ba, gaskiya ta tada
this time around. Naji abinda ya tokare
min a kirji ya fadje6, wata kila ma tare da
zuciyar tawa suka fashe. Kawai sai wani kuka yazo min, ai kuwa na fashe da kuka. Yayi sauri ya kara matsowa kusa da ni "Piya!" Kuma sai ya kasa cewa komai, yayi attempting magana ya kai sau biyar amma
ya kasa furtawa.

Na juya na barshi anan a tsaye na cigaba
da tafiya ta ina kuma cigaba da kuka na.
Idan ka ganni zaka dauka sakon mutuwa
aka aiko min ko kuma patient ce ni a
psychiatry. Ya cigaba da bina, "Please
Safiyya people are looking, ki daina
wannan kukan, let me get my car and take
you home. We will talk on the way" ba
tare da ma juyo ba nace "I don't care
about people, I don't care about anything,
I don't care about you or your wife or your
baby. Ka juya ka koma gurinta and don't
ever talk to me again. Karma ka kara
nuna ka san ni. I wish ban sanka ba a
rayuwata"

Ya sake zagayowa gaba na, ya tare min
hanya, kokari kawai yake sai na kalle
idonsa ni kuma naki daga kai in kalle "look
at me Safiyya, Let me get the car. We will
talk" na karbi jakata daga hannun sa
sannan na dake shi da ita a kirjinsa, "Get
out of my way, get out of my site, Get out
of my life, Me zaka ce min? Zaka ce min
ba naka bane ba?" Yayi shiru bai ce komai
ba amma tsananin tashin hankali ya bayyana a fuskar sa. Na nuna shi da yatsa na "babu ni babu kai har abada" na sake zagaye shi zan cigaba da tafiya sai va
sake rike jaka. "Piya....... Dan Allah..... Ki
tsaya muyi magana" na sake sakar masa
jakar sai kuma kawai na durkusa a inda
nake dan ji nayi ba zan iya cigaba da
tafiya ba. Na kife kaina akan guiwowina na
cigaba da russ kuka kamar wadda aka ce
Daddy ya mutu.

Ina jin wasu mutane suka zo wucewa suka
yi masa magana ya basu amsa amma
banji abinda suka ce ba sai suka wuce.
Sai naji motsinsa shima ya zauna a kasa a
kusa da ni, ina iya jin kamshin sabulun da
yayi wanka dashi. Ji nake yi a raina tamkar
komai na rayuwata ya tarwatse. Tamkar
zuciya ta ta tarwatse, tamkar duk
achievements dina are nothing because
of this. Kamar ni din kaina is nothing
tunda har Muhammad ya manta da ni
already yayi settling da Safina. Dama haka
kishi yake? Lallai na jinjinawa mata masu
kishiya musamman idan suna son mijin
sosai, Sai da nayi kuka na sosai sannan na dago
kai ina kallon sa, fuskarsa tayi ja kamar shi
yake yin kukan, muna hada ido ya miko
min hankyn daya dauko daga cikin jaka ta da take hannun sa "ya isa haka kar kiyi
ciwo kuma. I promise you it is nothing. It
doesn't mean anything. I don't know how
to explain to you but I promise you zaki
fahimta" na karbi hanky din na goge fuska
ta sannan na mike tsaye ina jin kirjina yayi
min nauyi, ya mike shima sai nace masa in
a much calmer voice "you don't have to
explain anything. Na riga na fahimta. Ni
kadai nake haukana da ma. I ......" Ya
katse ni "Piya haukan da nake yi akan
sonki na tabbatar yafi naki yawa. Yarinyar
can makira ce. She did something. Kuma
dama this is exactly what she wanted.
This is exactly why she did what she did"
na girgiza kaina "I don't want to know
what she did or what you did. It is over
between us again. I am breaking up with
you for the second time" na fada tare da
fara kokarin tare taxi, mai taxin yana
tsayawa Muhammad yace masa "get out
of here, go" mutumin ya bi mu da kallo
sannan ya ja motar yayi gaba.

Muhammad ya juyo kaina "you are not
breaking up with me Safiyya. Never again,
I will never let it happen" ya fada with so
much confidence, Na juya na cigaba da
tafiya tare da cewa "watch me" na cigaba
da kokarin samun abun hawa.

A lokacin mota ta tsaya a gabana, motar
Mustapha, yana zaune a seat din driver
fuskar sa cike da alamomin tambaya ya
kalle ni ya kalli Muhammad da yake tsaye
a kusa da ni hannunsa rike da jaka ta, ya
ambaci sunansa "Muhammad?"
Muhammad yayi kamar bai ji shi ba, sai ya
sake kallo na yace "Mommy tace in biyo ki
in kai ki gida, are you coming or not?"
Kamar ransa a bace yake amma bani da
option dan babu abinda nake so a lokacin
irin inyi nisa da Muhammad.

Na warce jaka ta daga hannun sa da karfi,
karfin da nayi amfani da shi ya sa nayi
baya kamar zan fadi, ya saka hannu daya
ya tare ni sannan ya mikar da ni tsaye
sosai. Ina jin na tsaya nature hannun sa
tare da nuna shi "you hurt my heart, you
hurt my heart really bad. I don't want to
see your face again, ever" sai kuma na
zagaya na bude motar na shiga na zauna.
Mustapha ya ja muka tafi.

Na kwantar da kaina a jikin kujera ina
kokarin hana kaina cigaba da kuka, wata
irin tafasa zuciya ta take yi. Na rufe ido na
ina ta jan numfashi da karfi trying to calm
myself amma sai naji Mustapha ya fara
magana cikin daga murya "what just
happened? What was that? Are you in a
relationship with mijin Safina?".

Na bude ido na juyo ina kallon sa raina
yana kara baci, sai ya cigaba da magana
"wancan munafikin yaron. He have been
giving Safina trouble all along and now
this? Yarinyar nan tana can tana kuka
Mommy ta saka ta a gaba ta kasa gane
kanta ashe uta ta san abinda yake faruwa,
ashe kukan da take yi kenan. What do you
think Mommy and Daddy will think idan
suka ji wannan labarin?"

A hankali nace masa "Mustapha, ko kayi
shiru ka daina min hayaniya a kai ko kuma
ka yi packing in fita. I don't owe you an
explanation. I don't care what you think.
am not going to explain anything to you"
bai yi shiru din ba ya sake cewa "but you
owe our parents explanation na how you
are in a relationship with min sister din
kj" "step sister" na gyara masa tare da
jawo ear piece na saka a kunnuwa na
sannan na kwanta a kujerar na rufe ido
na,

Ban sani ba ko ya cigaba da maganar ko
kuma ya hakura, Sai da naji mun tsaya
sannan na bude ido na na dauki jaka ta na
fito. Shima ya fito yana kallona yace
"yanzu ni what do you want me to do with
this information" nace "whatever you
want. Ko ka wuce ka gaya wa Daddy ko ka
koma ka gaya wa Mommy ko kuma ka shiga gidan radiyo ka fada, ko kuma ka rike a zuciyar ka. I don't care",

Na juya da sauri na shiga gida, kuma har
zuciyar ta wa ban damu ba din. In dai
Muhammad ne Safina ta je na bar mata. In
dai Safina ce Muhammad yaje na bar
masa. Nayi saving Daddy da Mommy
stress din solving wannan issue din. Na shiga cikin gidan da sauri, ina jin Esther tana yi min magana ko kallon ta banyi ba na hau sama na tafi dakina na
shiga na kulle kofa. Kokari nake vi lallai sai
na hana kwakwalwa ta tunanin
Muhammad da matarsa, irin abinda na
kanyi tun da aka yi auren su, amma kuma
yau zuciya ta tayi over powering
kwakwalwar ta karbe ragamar controlling
emotions dina. Dan haka na zauna a kasa
a gaban gado na cigaba da rusar kuka na.
My heart was so broken beyond repairs.
But my brain was trying to tell me the
truth, sai dai zuciyar ta wa taki bata
damar yin magana.

Sai da na gama sannan na tashi na cire
kayan da nayi masa kwalliya da su nayi jita
da su a tsakar dakin sannan na saka kafa
na tattake su. What was I even thinking?
That we will be back together bayan yana auren Safina? Ni kaina na san babu yadda
za'a yi Daddy da Mommy su yarda da
hakan but I love him so much, yanzu
kuma na tsane shi, I hate him so much
amma kuma ina son sa, how is that even
possible?

Him👳🏻‍♀️

Tun da ya dawo baya zama a gida, kamar
yadda Abba ya fada aiki ne dankar a
office yana jiran sa, ga shi kuma yana so
ya fara implementing knowledge din da ya
samu a gurin tarukan da yaje, dan haka
abu ya taru ya cakude masa. Sai da weekend ya zagayo sannan ya samu hutu ya zauna a gida. But he was being careful yanzu a gida yana kiyaye
abinda zai ci ko zai sha ko kuma ma duk
abinda zaiyi amfani da shi. Shi gani yake
yi asiri Safina tayi masa da ya saka shi
acting that way a daren can. Wannan ya
sa kofar part din sa yanzu kullum a rufe
take, yana shiga zai rufe ta ciki, in ya fita
ma kuma ya rufe ya tafi da key din. Yanzu
ko abincin da take ajiye wa kullum ba ta
da damar ajiyewar.

A ranar Saturday din ne ya samu ya
kwanta yayi bacci mai nauyi sosai da
rana. Sai da zuhr ya tashi, ya shiga toilet yana wanka yana gab da fitowa yaji wayarsa tana kara, ya gama ya fito ya duba sai yaga Mama ce ta kira shi. Ya na
kokarin kiran ta kenan sai ga wani kiran ya
shigo, ya dauka ta tambaye shi a ina yake
sai ya gaya mata yana gida, nan take ta
hau shi da fadan wai ana ta nemansa a
gidan ya rufe kofarsa, he tried to explain
to her bacci yake yi amma taki sauraren
sa tace maza ya je ya gaishe da Mommyn
Safina tazo tana neman sa.

Da sauri ya zura riga ko gama drying
jikinsa bai yi ba ya fita dan da gaske ya ji
Mama ta dau zafi. Sai dai yana shiga falon
Safina ya ganta, ba Safina ba Safiyya. She
looked different, more matured but more
beautiful. Amma kuma hankalin ta a tashe
yake, ranta a bace yake, and he was more
concerned about abinda ya bata mata rai
ya tayar mata da hankali haka then fadan
da yaji Mommy ta fara yi masa. Bai ma ji
me take cewa sosai ba, kamar dai she
was showing dissatisfaction akan yanayin
zaman su da Safina har tana magana in
baya son ta su suna sonta, But then he
heard something. "Ga Safiyya nan da
auren ta ya mutu babu abinda ya same
ta" and it caught his attention, a take
kuma ya gane me hakan yake nufi. Auren
Safiyya ya mutu.

As he was trying to assess the situation
sai ya ga Safiyya ta bar inda take tsaye
tayi hanyar waje da sauri, and bai tsaya
cigaba da jin fadan da ake yi masa ba ya
mike shima da sauri ya bi bayan ta yana
kiran sunan ta.

Har waje ya bita taki kula shi, daga baya
kuma sai ta gaya masa abinda ya bata
mata ran, his worst nightmare, maganar
cikin Safina. Tabbas maganar ta bata
mata rai sosai and she cried like a baby.
She sat down on the floor a bakin titi and
cried. Wannan kukan nata ba karamin
kona zuciyar sa yayi ba. Ya rasa mai ze ce
mata. Yasan zai iya yi mata bayani amma
kuma ba zai iya ba. To me zai ce? Ya rasa
menene ya fi daga masa hankali yanzu,
the fact that matar da baya so is pregnant
for him or the fact that matar da yake so
is crying because of him.

Yayi kokarin yi mata magana ya kasa, yayi
kokarin lallashin ta amma bai san kalaman
da zaiyi amfani da su ba. So he just sat
with her and wished he can cry with her.
A karshe dai ta gaya masa maganganun
da suke nuna zurfin bacin ranta sannan
tace masa "I am breaking up with you
again". Amma duk ba wannan ne damuwar sa ba,
damuwar sa shine Mustapha da yazo ya
dauke ta a mota suka tafi.

Ya tsaya yana bin motar da kallo, and the
first thing that came to his mind was ranar
da suka yi haduwa ta biyu a duniya, ranar
da Mukhtar ya zo ya dauke ta a mota suka
tafi, she later married Mukhtar. Ya girgiza
kansa a hankali yace "no…..no. not this
time. Not again" ya juya da sauri ya koma
cikin gidan sa sannan ya shiga part din sa
da sauri totally forgetting about the
problem with Safina and Mommy. Shi
kawai abinda yake ransa shine Mustapha
da Safiyya a mota. She is broken. She
may even open up to Mustapha and give
him a chance to lallashe ta. Ya sake
girgiza kansa da sauri "uhm uhm" wannan
rarrashin shi zai yi shi tunda shine yayi
wannan laifin. Frantically yake neman key din motar sa, totally forgetting cewa yana kan abinda
aka tanada musamman dan ajiye car keys
a palon sa, sai daga baya kuma ya tuna
sannan ya tafi da sauri ya dauka, Unlike
before yanzu ai ya san gidan su, ya san
har falon Daddy.

Wayar sa ce tayi kara a cikin aljihunsa. Ya
saka hannu ya dauko ta and he saw sunan
Mama. Yaji gabansa ya fadi, sai a lokacin
ya tuna da inlaw dinsa da ta kira shi tana
yi masa fada. Yaji kamar kar ya dauki
wayar. Allah ka dai yasan abinda suka kira
suka gayawa Mama. Wannan wanne irin
kaddararran aure ne?

Amma kuma ba zai iya barin Mama tana
kiran sa bai dauka ba. Tafi karfin haka a
gurin sa. Yayi sliding wayar ya dauki kiran
ya saka a kunnen sa "hello Mama" ya
saurara yaji ta fara yi masa fada amma sai
yaji tace "kaje ka gaishe ta?" Yace "eh
naje, har na fito ma" tace "kana ina
yanzu?" yace "ina daki na" tace "okay ka
2o ka same ni a gidan Mommy" daga nan
ta katse kiran.

Ya rike wayar a hannunsa yana jujjuya ta.
Shi kukan Safiyya kawai yake tunawa. So
yake yaje yace mata "I am sorry" but
sorry for what? Ya kawar da maganar
daga zuciyar sa sannan ya fara kokarin
chanja kayansa, Shi dai ya san indai har
maganar gaskiya za'a bi bai aikata laifin
komai ba ballantana ya bada hakuri,
amma ba maganar gaskiya ake yi ba,
maganar Safiyya ake yi. And as far as magana ce a tsakanin sa da Safiyya then she is always right. Kuma zai bada hakurin ko da kuwa cikin charbi ne.

Ya gama chanja kayan ya dauki key din
mota ya fita, sai da ya kunna motar
sannan ya yi tunanin dolen sa a yanzu
gidan Mommy zai je gurin Mama, sai dai
yana fatan gain maman ba zai dauki
lokaci ba. Ya na tuki yana tunanin
maganganun Safiyya, she said she is
going to break up with him, amma shi dai
ya san dama they broke up already, bai
kuma san sanda suka dawo ba ballantana
har su sake wani breaking up din.

Kukan ta tabbas ya tayar masa da
hankalin amma kuma a wani bangaren ya
kwantar masa da hankali ne saboda ya
tabbatar masa da matsayin sa a gurin ta
and yayi boosting confidence din sa. Ya
tuna kalmomin ta "ashe ni kadai nake
haukana" and he smiled tare da sauke
ajjiyar zuciya. Whether she have been
with Mukhtar or not, shi dai abinda ya
fahimta shine yana cikin zuciyarta kamar
yadda take cikin ta shi. And that is all that
matters.

Sai da ya tsaya yayi sallah a masallacin
kofar gidan sannan ya shiga cikin gidan,
ya ga motar Mammy ya san tana ciki ita ma, dama al'adar su ce sukan je gidan
Mommy duk Saturday su yini tare da ita. A
falo ya tarar da Mammy ita kadai tana
kallon tv, tayi murmushi tana kallon sa
"ubana maganin kuka na" ya yi mata
murmushin shima sannan ya karasa ya
gaishe ta. "Kai yanzu tunda kayi aure
kuma shikenan an daina gain ka, matar
kata boye ka a gida" yayi saurin kare
kansa "Mammy wallahi aiki ne ya sako ni a
gaba. Abba sam baya daga min kafa. Shi
yasa dama tun farko na gudu daga gurin
sa na tafi MD" tace "haka ne. We are all
proud of what you have achieved so far.
Allahu yayi jagora" yace "Ameen" sai ta
nuna masa dakin da yake kusa da gurin
tace "mamanka tana ciki tana Sallah.
Maybe ta idar" ya mike ya shiga dakin da
ta nuna masa. A ciki ya samu Mama ta idar da sallah
tana addu'a. Ya zauna yana jiran ta sai da
ta shafa sannan ta juyo tana kallon sa, ya
gaishe ta "Mama barka da rana" bata
amsa ba sai ta cigaba da kallon sa, ya san
irin wannan kallon and it made him
nervous, sai a karshe tayi magana and
she asked exactly abinda ya san zata
tambaya "me yake damunka?" Ya danyi
dariya nervously "Mama babu abinda
yake damuna fa, stress din aiki ne" ta cigaba da kallon sa "kun yi fada da Safina ne? I don't like the tune of her mother sanda ta kira ni dazu" ya girgiza kai "babu
abinda ya faru Mama. Su suna da
kananan maganganu ne kawai. Dan Allah
kar kike biye mata in ta gaya miki abu har
ki bata ranki" ta dauke idon ta daga kansa
tace "in ba fada kuka yi ba to wani abun
ya faru da ban. Me ya faru?" Ya gyara
zamansa, she will not let the issue go.

Yace "Mama, even if I tell you yanzu ba
zaki gane ba, zaki damu ne kawai. I will
tell you sanda na zama confidence cewa
zaki fahimce ni kuma ranki ba zai baci ba"
ta juyo tana kallon sa tace "okay kai ka
fahimta amma ni ba zan fahimta ba?" Ya
girgiza kansa "ba haka nake nufi ba. Ni
kaina ban san stand dina akan maganar
ba, I just don't want to worry you for
nothing. Nima ban fahimta ba ballantana
in fahimtar da ke" ta dan vi shiru sannan
tace "shikenan. Allah ya jishe mu alkhair'"
yace "Ameen" suka dan yi hirar gida
kadan sannan tace mass yaje ya gaishe
da Mommy (his grandma).

Ya shiga dakin ta ya tarar ita ma ta idar da
Sallah tana kokarin fitowa, sai ta koma ta
zauna tana yi masa murmushi "mai gidan
katako" yace "na karfen dai, Ya Amen ne
na katakon ai" tace "duk daya, Da kai da shi duk babu wanda yake yi min cefane dan haka duk na katako ne a waje na. Na karfe na yana aljanna" ya durkusa a
gaban ta "barka da yamma" ta shafa
kansa tare da amsawa cikin sakin fuska
"ina amaryar ka? Tun da tazo ranar nan ba
ta kuma dawowa ba. Ko ba ka koya mata
zumunci ne?" Yayi murmushi bai ce komai
ba sai ya fara kokarin mikewa, shi duk
hankalin sa yana kan Safiyya, ko ta daina
kukan?

Har ya mike sai Mommy tace "mamanka
ta gaya min ashe Safina jikar Hajiya
Maryama ce, matar Alhaji Nasiru" ya juyo
yana kallon ta yace "ba jikar ta bace ba,
yar kanwar ta ce, but kanwar a hannun ta
ta tashi shi yasa ake dauka jikar ta ce" ya
gyada kai cikin fahimta, har ya sake
juyawa sai tace "har na dauka yar Safiya
ce" yaji gabansa ya fadi, ya juyo yana
kallon ta yace "Safiya?" Tace "eh safiya,
akwai yar Maryama sunan ta Safiya, very
beautiful girl, sun taba zuwa gidan nan
shekaru da yawa da suka wuce tare,
lokacin duk iyayen ka suna makaranta, har
nake cewa ta bani ita in samo mata miji a
Nijar sai tace min an saka ranar ta a
lokacin, da wani mai suna Adam".
Ya juyo da baya kamar wanda ake ja da
igiya ya dawo gabanta "Safiya kika ce Mommy are you sure? Kuma Adam zata aura?" Ta bata rai "me kake nufi ne wai? Na gaya maka sunan yarinyar Safiya kuma zata auri Adam sanda suka zo and you are
still asking me?" yace "I mean shekarun
da yawa, are you sure about the names?
Saboda Hajiya Maryama bata taba
haihuwa ba" ta harare shi "shekaru da
yawa? Ni fa nonon rakumi na sha while
growing up ba processed milk irin wacce
kuke sha yanzu ba. My memory is very
good. Safiya sunan ta. Kuma Maryama
tace min yar ta ce, wanna shine abinda
na sani"

Sanda ya shiga mota ya fara driving sai
yaji ya kasa tantance wanne tunanin ya
kamata yayi yanxu. Safiya matar Adam
will definitely mean mahaifiyar Safiyya. In
dai kuma ba wani babban coincidence ba.
In haka ne akwai dangantaka ta jini kenan
tsakanin Safiyya da Safina? Ya tuna
maigadin gidan su Safiyya ya taba gaya
masa cewa tun mahaifiyar Safiyya na da
rai Mommyn Safina take zuwa gidan gurin
ta amma bai san dangantakar su ba. Are
they related?

Direct gidan su Safiyya ya tafi. Shi yanxu
yasan yana da license din shiga gidan a
matsayin sa na mijin Safina, Sai dai kuma
bai san abinda zai ce ya samu ganin Safiyya ba musamman tunda fushi take yi da shi sosai kuma ba lallai ne ta bashi hadin kai ba. Kuma yana tsoron kar ace Mommy ta dawo gida dan kar ta sake yi
masa hayaniya a tsakiyar ka. And that guy Mustapha ya gansu tare kuma bai san kallon da yayi wa abin ba.
Dan haka dole ya zama careful kar ya
bata goma daya bata gyaru ba.

Mai gadi yana ganin sa ya tafi da niyyar
bude masa kofa amma sai yayi masa
alama da yazo, ya fasa bude kofar ya taho
gurinsa sai ya tambaye shi "Safiyya tana
gida?" Baba Ya'u yace "a'a sun fita da su
Hajiya da farko, sai kuma suka dawo tare
da Mustapha, daga nan kuma sai na ga ta
fita ita kadai, ban san inda taje ba".
Muhammad yaji babu dadi. Ya sake
tambaya ko ita Mommy ta dawo sai mai
gadin ya ce masa bata dawo ba,
Mustapha ma kuma ya sake fita. "Kamar
gidan ka naji ance sun tafi ai",
Daga nan dai sai ya shiga gidan yaje ya
gaishe da Daddy, bai ji dadin gain jikin sa
ba but yaji dadin gaishe shin da yayi da
kuma yar maganar da suka yi, sai dai a
cikin sauri yayi ya gama dan baya son
Mommy ta dawo gidan ta same shi ba tare da ya samu Safiyya sunyi magana ba dan bai san zuwa yanzu abubuwan da Safina ta gaya wa Mommy din ba. Bai
kuma san me zai ce da Daddy ba a yanzu
ba tare da ya yi magana da Safiyya ba.

A haka dai ya hakura ya fita daga gidan
thinking of a way da zai samu ganin
Safiyya ko kuma at least yayi waya da ita.
Yanzu ko number din ta bashi da ita a
wayarsa and even if he is to get the
number ya san tayi blocking dinsa months
ago dan haka ko ya kira ba lallai ta shiga
ba. So he got another sim card just in
case.

Bai koma gida ba sai very late, ya san dai
dole Mommy ta bar gidan a lokacin. Ya
shiga part dinsa ya rufe kofa kamar
kullum sannan ya hada tea ya sha yayi
wanka yayi shirin kwanciya bacci. Ya
kwanta akan gado rigingine yana kallon
ceiling, idanunsa babu bacci ko kadan a
cikin su, babu abinda yake gani a cikin su
din sai fuskar Safiyya tana kuka, babu
kuma abinda yake ji a kunnen sa sai
muryarta tana kuka. Ya jima a haka sai ya
mike tsaye ya dauki wayarsa ya fita da
sauri ya shiga part din Safina. Dakin da
yasan tana kwana a ciki ya dosa kai tsaye,
ya je ya tura kofar ya shiga, har ta kwanta dan dakin da duhu babu fitila.

Ya kunna fitilar dakin. Tana kwance akan
dago ta rufa da bargo, ta juyo da sauri
tana kallon sa, daga alama ta kwanta ne
kawai amma ba bacci take yi ba. Ta mike
zaune da sauri tana kallon sa idanunta
cike da mixed emotions, akwai toro a
cikin su dan har lokacin bata manta da
ranar nan ba, akwai kuma anticipation and
hope din cewa ya dawo ne for more.
Kirjinta yana bayyana cika da kuma
firmness irin na masu ciki. He looked so
manly in his armless rigar bacci mai hade
da gajeren wando iyakacin guiwa.

Ya karasa bakin gadon da take kwance
akai ya dora kafarsa daya akai yana kallon
ta cikin ido yace "bani wayarki" she
looked confused "me zaka yi da waya ta?
Na rantse babu komai a cikin ta. Me aka
ce maka navi kuma?" Ya mika mata
hannun sa '"bani wayarki nace" ta jawo
wayar a gefen pillow din6ta ta mika masa
"wallahi babu komai a ciki. Kuma ka duba
ka gani" ya karba ya jujjuya ta sannan ya
mayar mata da ita yace "bude ta" ta bude
ta sake mika masa with confidence dan
tasan ita dai bata da wani abun boyewa a
cikin wayar. Ya dan jima yana daddanna
wa sai kuma ta ga ya dauko tasa wayar ya
daddanna ita ma, and she realized abinda yayi, and her heart breaks to thousand pieces.

Yana gama wa ya jefa mata wayar kusa da
ita ya juya zai fita, cikin karyayyiyar murya
tace "me kayi? Me ka dauka a cikin wayar
ta wa?" Ya juyo yana kallon ta yace
"number din Safiyya" sannan ya juya ya
fita, ya bar mata kofa a bude fitila a
kunne.

Direct ya koma dakin sa ya dauko sim din
da ya siyo dazu ya saka a cikin wayarsa,
yayi recharging sannan ya koma ya
kwanta yana kallon ceiling kafafuwan sa a
kasa yayi dialing, not even considering
how late it is. Ta shiga, har ta katse bata
dauka ba and he called again, tana cikin
ringing ta dauka kuma daga muryarta ya
san ba bacci take yi ba "hello? Who is
this?" Ya lumshe ido yana jin yadda
zuciyar sa tayi contracting, he so much
misses jin muryarta over the phone and
the memories of all those late night
phone calls just came flooding back to
him,

Ta sake yin magana "hello? Waye wai?"
Yayi magana a can kasan makogwaronsa
"sunana Muhammad Gidado, Please don't
hang up"

Maman Maama✍🏻
[07/01, 10:46 pm] +234 906 816 1960: ❤️‍🩹Safiyya❤️‍🩹

Episode Fifty: Breaking News


Yaji tayi shiru daga can barin, amma kuma
ya san ta ji shi sannan ta gane cewa
shine. Yace "kiyi hakuri na kira ki cikin
dare, but na kasa bacci ne, ba zan iya
bacci ba without at least talking to you. I
tried seeing you ban samu ba. Dan Allah
ki bani dama muyi magana".

Tace cikin dacin murya "babu wata
magana a tsakanin mu Muhammad, kai
mijin yayata Safina ne, kuma ban yayan
ta, wannan shine kawai alakar da take
tsakanin mu. Bayan wannan ban san wata
da har zata hanaka bacci ba" yace "naji.
And ina so ki sani na shirya jin duk abinda
zaki fada min as long as zaki saurare ni
nima. Yanzu dai tambaya daya nake
©️2 neman alfarmar ki amsa min, just one
question, koma menene zai biyo daga
baya" bata ce komai ba amma kuma bata
katse kiran ba, sai yace "dazu naji
Mommy tayi wata magana, tace auren ki
ya mutu, I want to know idan da gaske ne,
I want to make sure dai dai kunne na yaji min ba wai ya gaya min son raina ba ne ba" tayi shiru bata amsa masa ba. Ya sake cewa "Piya, please ba dan hali na ba l want to confirm from you, this is very
important, bana son in dawo da tunanin ki
cikin zuciyata, bana so bakina ya furta
kalaman da suke cikin zuciyata akan ki
alhalin kina matar wani, bana so in yiwa
Allah laifi, dan Allah ki bani amsa".

Ta sake yin shiru, sai da ya kara roka "Piya
Please!" Sannan tace "aure na ya kare da
Mukhtar, but that does not mean
anything. Now this is a warning, kar ka
sake kira na" daga haka ta katse kiran.

Ya dora wayar akan kirjinsa lips dinsa
suna curving into a wide smile,
"alhamdulillah" ya ambata, shi yasan
second chance ne Allah ya bashi at
happiness kuma ba zai taba yin wasa da
wannan chance din ba, zai yi fighting for
his happiness with everything da yake da
shi a duniya, Ya san dai abin ba mai sauki
bane ba, musamman considering
dangantakar matarsa da Safiyya, both
iyayensu ba zasu yarda ba, Safina also
will do everything in her power ta hana
abin kasancewa but ba ita ce damuwar sa
ba. Damuwar sa a yanzu shine yadda zai
yi convincing iyayensa da kuma Daddyn Safiyya.

Yayi ta bitar abubuwan da suka faru a
ranar a cikin kansa, musamman
maganganun Safiyya na dazu da kuma na
yanzu, yasan cewa ranta a bace yake
sosai kuma bai yi blaming dinta ba for
that, amma kuma sam kalamanta basu
bata masa rai ba sai ma sanyaya masa
zuciya da suka yi, saboda dukkan
kalaman nata were screaming "I love you"
shi kuma wannan wan security ne a
wajen sa ya san space dinsa yana nan a
cikin zuciyarta. Abinda ya rage masa
shine ya samu ta huce daga fushin da tayi
and then the battle will begin.

Ya jima a haka yaji karar shigowar
message wayarsa, zuciyarsa ta harba da
sauri, ko bakar magana zata turo masa
indai har ta turo din to wani step ne for
him. Amma yana daga wayar sai yaga
Safina, yayi dan karamin tsaki sai kuma ya
karanta sakon nata.

"Just for the records, ban taba yin
nadamar wani abu ba a rayuwata kamar
yadda nake nadamar auren ka a yanzu.
Ban taba ganin azzalumin mutum, mugu,
wanda bai damu da kowa ba sai kansa ba
a rayuwata irin ka. I have been saying na
yafe mata dukkan abubuwan da kake yi
min da saboda wadannan tsakani na da kai ne, amma wanna ban yafe ba tunda saboda wata ne, ban yafe ba kuma sai Allah ya saka min"

Har ya ajiye wayar ya fara shirin yin bacci
sai kuma ya dauka ya tura mata reply.

"You are mistaken, it has always been
because of her, da ace baki ci amanar ta
ba, da ace baki yi min karya a kanta ba, I
might have been the best thing that
happened to you"

Tun daga lokacin Muhammad ya daura
damarar dawo da matsayin sa a gurin
Safiyya amma abin yana neman ya gagare
shi. Tun ranar da suka yi waya da ya tashi
da safe ya kira ta sai yaji ta rufe sabon
layin nasa shima. Bai hakura ba haka ya
cigaba da siyan layuka tana kuma rufe su
da zarar ta fahimci shine, daga baya kuma
sai ta daina daukan kiran ma kwata kwata,
maybe tayi deciding ta daina daukan new
numbers saboda shi. Messages kuwa babu ta hanyar da bai tura mata su ba har ta e-mail din ta amma
babu reply, bai ma sani ba ko tana gani ko
kuma bata gani amma haka ya cigaba da
tura mata su kullum safe da rana da
daddare kamar shan magani.

Yayi zirga zirga zuwa gidan su yafi adadin
da zai kirga amma baya samun gain ta,
lokuta da dama tun daga gate mai gadi
yake gaya masa bata nan, wani lokacin
kuma ya samu ya shiga sai ya kare da
gaishe da Daddy amma ba zai ga Safiyya
ba. Daga baya ma da yaje sai mai gadin,
wanda zuwa yanzu ya fara yi masa wani
irin kallo saboda yawan tambayar Safiyya
da yake yi, ya gaya masa cewa Safiyya ta
tafi Umrah.

Babu abinda kuma ya rage masa yayi illa
ya jira ta ta dawo, while jiran kuma ya
cigaba da tura mata messages telling her
every detail about his days da kuma halin
da zuciyar sa take ciki akan soyayyar ta.
Duk da bashi da tabbacin tana karantawa
or not. Har da bata sakon tsarabar da
zata taho masa da ita daga Saudiyya,
wani turare da ta taba kawo masa wani
zuwa da tayi lokacin suna tare.

Ya lura cewa Safina ta zama bitter a cikin
yan kwanakin nan, har tsayawa ta kanyi a
waje ta jira shi ya dawo da daddare ta
tambaye shi daga ina yake. Ko kuma in
taga yana waya ta tambaye shi da wa
yake waya, shi har dariya ta kan bashi
idan tayi masa irin wannan tambayar, baya
kuma bata lokacin sa gurin bata amsa. A cikin lokacin ne Humaira matar Al'ameen ta haihu, ta haifi baby boy. Tun a asibitin da ta haihu da shi aka yi komai har aka
sallame ta ta dawo gida sai kuma Mama
ta matsa masa tace ya dauki Safina ya
sayi kayan babies ya bata suje tare ta
kaiwa Humaira.

He did that, duk da cewa zuciyar sa bata
so amma baya tsallake maganar Mama
dan haka yaje ya hado kayan babies masu
kyau ya zo ya dauki Safina a mota suka
tafi gidan Al'ameen. Ya dauka zata yi
masa surutu yauma irin wanda take yi
masa a duk chance din da ta samu amma
sai ya ga ko kallon sa bata yi, wayarta
kawai take danna wa, wannan ya bashi
damar driving din sa hankali kwance har
suka je gidan.

A bakin gate yayi packing, sannan yace
mata "ga kayan barka nan a baya, ki
dauka ki shiga ki kai musu" ta juyo da
sauri tana kallon sa '"ba tare zamu shiga
ba? Mama tace min zaka kaini inyi barka"
ya daga kafada "kuma na kawo ki ba, Ga
gidan nan. Suna ciki. I guess akwai
mutane sosai ma a ciki duk sun sanki har
ita mai jegon in ke baki san su ba. Just
go……. In na gama abinda nake zan zo in
dauke ki".

Ta bude kofar ta fita reluctantly sannan ta
bude baya ta dauki ledojin da ya ajiye a
ciki, yayi murmushi mugunta, ya san tana
avoiding shiga family dinsa tun ranar da
ya kaita gidan kakannin sa and yanzun ma
yasan gidan Al'ameen din a cike yake da
yan barka. Bai dawo daukan ta ba sai
dare, and sanda ya zo daukan ta tana
shiga motar ta fara kuka, ya mika mata
tissue box and she cried har suka je gida.

Her🧕🏻

Ranar da muka je gidan Safina

Bayan na gama kuka na a daki sai kuma
wani tunani ya zo min, na san yadda naga
Muhammad dazu akwai yiyuwar zai iya
biyo ni gida and zai iya yin dabara irin ta
ranar nan yaje wajen Daddy ya saka
Daddy ya kira ni, pretending zai bani sako
or something. Ni kuma idan akwai abinda
bana son yi a yanzu to shine ganin sa.
Wannan ya sa na tashi na share hawaye
na na sake fita na tafi inda a can ne yanzu
na ke samun solace, the oasis, ina fita da
mota naga guards dina sun biyo ni and I
felt safer with them, ko ya biyo ni zasu
hana shi karaso wa inda nake,

A Oasis na wuni ni kadai, har sai da naji an
fara kiran magrib sannan na sake dauko
mota na taho gida, na san Daddy ba zai neme ni ba tunda ya na tunanin muna tare da Mommy a gidan Safina, amma kuma tunani na shine abinda ya faru a gidan Safina din bayan ni da Muhammad mun
fita, me Safina tace wa Mommy? Na dai ji
Mustapha a cikin maganganun sa ya
ambaci cewa Safina tana gida tana kuka,
na kuma san yadda Mommy take son
yayanta zata saka ta a gaba ne da
tambayar abinda ya saka ta kuka, and I
definitely know Safiya will lie and make
my the villain. Ina dawowa gida na tarar har lokacin su
Mommy basu dawo ba, na shiga gida na
wuce dakina nayi alwala na fito kenan zan
tayar da naji shigowar su Mommy, na
tayar da sallah ta, sanda na idar sai na
zauna akan sallaya ta for the first time na
rasa addu'ar da zanyi, gani nake na rasa
Muhammad, and with him na rasa komai
da nake aiming for a rayuwa ta. Duk wani
hope for a brighter future da naji sanda na
rabu da Mukhtar naji ya tarwatse a zuciya
ta.

Ina nan zaune akan sallaya ina aikawa da
annabin tsira salati sai naji an bude kofar
dakina an shigo, na daga kai na ga
Mommy ce da alama ko cire mayafin ta da
ta je gidan Safina da shi bata yi ba. Ta shigo ta zauna akan kujera tana kallona har na shafa addu'a ta sannan nayi mata sannu da zuwa. Tace
"ya ciwon kan naki?" Nace da sauki. Sai ta sake cewa "dazu kuma da kika ji kan ya dame ki maimakon
ki sha magani ki kwanta a can sai kika fito
ke kadai zaki taho gida? Kamar wadda
taje bakon guri? Gidan yar uwarki ne fa,
gidan Safina ne fa" na tashi daga kan
sallayar na fara ninke hijab dina nace
"Mommy nafi relaxing ne a gida, shi yasa"
ta danyi shiru tana kallona sannan tace
"sanda kika fita kun hadu da
Muhammad?" Na dauke kai ina nade
sallaya nace "wanne Muhammad?" Tace
"'kin san muhammad din da nake nufi ai,
mijin Safina" naji ciwon kalmar mijin
Safinan amma na danne nace "a'a, neman
shi ake yi?" Tace "sai naga kamar ke ya bi
sanda kika fita yana kiran sunan ki. Na
dauka zai dawo dake ne yace ki sha
magani ki kwanta kuma naji ku shiru,
shine na tura Mustapha yabi bayan ku in
kin ki dawowa ya dauko ki ya kawo ki gida,
shima kuma da ya koma na tambaye shi
Muhammad din sai yace bai ganshi ba" na
ajiye kayan sallah ta a inda suke na rufe
ban ce mata komai ba,

Sai ta nuna min kusa da ita a kan kujerar
da take tace "zo ki zauna" na je na zauna
kamar yadda tace na sunkuyar da kaina
kasa ina kallon yatsun hannuna. Tace "Safiyya, Yar war ki Safina tana cikin matsala sosai a gidan mijinta. Allah ya jarabce ta da auren mijin da bai san
darajar ta ba ko kadan ballantana ta
iyayen ta. Tun kafin bikin su na fahimci
haka, amma rabon zata sha wahala da
kuma rabon cikin da take dauke da shi a
yanzu ya saka ban yi kokarin tsayar da
auren ba sai nayi tunanin miskili ne kawai
amma zata shawo kan shi. Sai bayan da
aka daura auren sannan take gaya min
gaskiya, ashe a social media ta ga hoton
sa ta kamu da son sa, sai ta nemi kanwar
sa ita kuma ta hada ta da shi. To
coincidentally sai ya kasance a lokacin su
kuma iyayensa suna son yi masa aure,
watakila da ma kokarin fin karfin su suka
ga yana yi shine suke neman yarinyar da
zasu manna wa, ita kuma Safina rabon
shan wahala ya kai ta".

Tayi shiru tana kallona, maybe tana jira ne
in ce wani abu, jin ban ce komai ba sai ta
cigaba "ni abinda yafi bata min rai shine
idan da yasan baya son ta ai da sai ya
fada, tunda na tabbatar iyayensa ba zasu
yi masa dole ba, amma sai ya karbi auren
yarinyar nan, ita kuma Safina munafuka
tunda ta san daga ni har Daddyn ku ba
zamu yarda da irin wanna auren ba shine
ta kai shi Katsina, su kuma wasu
munafukan, dama ba sonta suke yi ba ba damuwa suka yi da ita ba shine basu
à
tsaurara binciken komai ba dan sunga mai
kudi ne suna saka ran zai ke kai musu
wani abu, basu san cewa ita kanta Safina
ba abinda take samu daga gare shi
balantana su, shine suka daura mata aure
da shi" ta sake yin shiru,na dago kai in
kallon ta nace "Mommy why are you
telling me this?" Tace "why not? Me yasa
ba zan gaya miki ba kuwa Safiyya, saboda
yar uwarki ce ita, ina ganin ya kamata ace
kin san halin da take ciki, kuma ai
hausawa sunce ciwon ya mace na ya
mace ne. Na tabbatar ba zaki so Safina ta
kasance cikin kunci a gidan mijinta ba
ko?" Ban amsa tambayar tata ba sai nace
"Mommy yanzu ni me kije so inyi akan
hakan?" Tace "you are very smart Safiyya,
in fact ni ban taba ganin someone as
smart as you ba, kin san Safina bata da
yawo sam, so nake ki saka kanki in her
shoes kiyi tunanin me take ji a zuciyar ta
sannan idan ke ce me zaki yi a kai. Sai ki bata shawara, na tabbatar in tabi shawarar ki zata samu waraka" na cigaba da yin shiru, sai ta mike "kinji kamar har an fara kiran sallar isha, bara in sauri inje
inyi Sallah, just think about it Safiyya, na
san zaki samo mata solution. Tayi kuskure
na sani, amma yanzu it is too late to go
back a gyara kuskuren tunda already har an fara hada zuriya. So nake muyi standing together as a family mu taya ta gyara gidan ta, kamar yadda muka yi
standing together as a family muka rufe
maganar kaddarar data same ki".

Ta juya, har ta kai bakin kofa sai ta kara
tsayawa tace "in kin gama ki sauka muci
abinci tare. Sai mu bawa Daddy labarin
gidan Safina".

Ta fita tare da rufe min kofa. Na bi kofar
da kallo sannan na dawo da hankali na
kan yatsun hannuna naci gaba da kallon
su, na tabbatar Safina ta gayawa Mommy
wani abu a kaina ni da Muhammad, kuma
na tabbatar ba gaskiya ta gaya mata ba.
Dan wadannan maganganun nata a cike
suke da harshen damo, she meant more
than she said. Har da gori a cikin maganar
and I also felt a threat a karshen maganar
ta lokacin da ta ambaci Daddy.

Na tashi na sauka kasa, na tarar Esther
tana ta hidimar shirya dinning sai na taya
ta, nayi kokarin yi mata hira to make up
for dazu dana ni ignoring dinta tana y min
magana, nace "Esther ya kamata a samo
wadda zata ke taya ki aikin gidan nan
gaskiya, aikin yana yi miki yawa, dama
mun barki ke kadai ne saboda ba zama
muke yi a gidan ba yanzu kuwa naga Daddy kamar yafi jin dadin zama a gidan
nan dan haka bansan sanda zamu koma
Kano ba" ta bude ido "wata kuma
Madam? No dai a bar ni ni kadai. Nafi jin
dadin aikina ni kadai bani da wani
problem. Ana kawo Wata zamu fara
competition for your appreciation. Ni ina
da kishi sosai. Idan something nawa ne
nafi son ya zama nawa ni kadai" nayi
murmushi "that makes the two of us
Esther. Tace "I think that makes almost
everyone. Kowa yana da kishi. Maza da
mata. Na wasu ne kawai yafi na wasu,
wasu suna fitowa da shi fili was suna
boyewa. Ya danganta da halin mutum".

Na tayata ta karasawa Daddy soup din da
ta hada masa, saboda yanzu baya iya cin
solid food irin namu, soup ce da aka yi da
shredded chicken, shredded Irish
potatoes and shredded vegetables aka
kuma dafa su sosai yadda ba zasu bawa
cikin sa wahala wajen digesting ba. Shi ya
fara zuwa dining din kuwa a kan
electronic wheelchair dinsa, naje ina
kokarin gyara masa zamansa sai ga
Mommy ta sauko sannan sai ga Mustapha
shima ya shigo, na zauna tare da su muka
ci abincin trying as much as I can inga
cewa na danne abinda yake zuciya ta
amma da kyar nake samo lomar tuwon da
nake ci take wucewa.

I expected Mommy ta bawa Daddy labarin
abinda ya faru a gidan Safina ko tayi
complain akan halin mijin Safina amma sai
naji bata yi ba, sai labarin abincin da
Safina ta dafa musu ta bayar "yarinyar
nan bata iya girki ba. Suma yaran da na
kai mata duk basu iya ba ashe. Nace
wanna wanne irin kwamacala kike baya
mijin naki? Kuma wai a haka ta shiga
online classes na koyon girki, daga videos
din take kalla tana yi".

Mustapha yayi gyaran murya yace "gwara
dai a samo mata wadda zata koya mata
girkin har gida, tun kafin masu iya girki su
kwace mata miji" ya karasa maganar yana
kallona. Daddy da yake jin su yana
murmushi yace"ai kuwa dazu mijin yazo
gidan nan kafin ku dawo" duk muka juya
muna kallon sa, ya cigaba da magana
fuskar sa dauke da murmushi "yaron kirki
ne. Yazo ya gaishe ni. Yace ya ga kunje
amma babu ni shine yace bara shi yazo ya
duba ni" Mommy tace "what? Lallai
munafunci ba'a mata kawai ya tsaya ba"
Daddy ya kalle ta yace"me yasa kika ce
haka?" Ta girgiza kai tare da cigaba da cin
abincin ta amma kana gani kasan ranta ya
baci tace "babu komai, wata maganar ce
daban".

Ranar da daddare ban iya bacci ba kamar
yadda nayi tunani, babu abinda kwakwalwa ta take yi min tunani sai Muhammad da Safina, ko me suke yi
yanzu? Na tabbatar suna manne da juna.
Munafiki, da rana zai wani ringa nuna wa
duniya kamar baya son ta da daddare
kuma yaje yayi mata ciki. Ina nan kwance in da dark, trying to get rid of tunanin Muhammad da matarsa sai
naji wayata tayi kara, na dauka na ga
bakuwar number and the first thing that
came to my mind shine Muhammad ne.
Shine ya saka sabon sim ya kira ni dan
yasan nayi blocking wadancan. Na rike
wayar ina kallon ta har ta katse, amma
kuma ji nake zuciya ta tana bugawa har a
cikin makogwaro na. Nayi missing din sa
sosai, nayi missing our long night calls da
bamu da mu da nisan da dare yayi ba.
Nayi missing listening to his deep calming
voice.

A lokacin wani kiran ya sake shigowa,
kwakwalwa ta tana gaya min inyi ignoring
ko in kashe wayar ma gabakidaya but my
heart wants to listen to his voice again,
And I followed my heart, na dauka,
pretending ban san cewa shine ba "hello,
who is there" yayi shiru, sai kuma naj
haushin kaina, wata kila ma bashi bane
ba, to ya ma za'ayi ya kira ni a wannan daren bayan na san yana can manne da matar sa?

Har zan katse kiran sai kuma naji muryar
sa "sunana Muhammad Gidado, Please
don't hang up" and all the emotions and
the memories came flooding back to me.
He sounded just like when we were free
and without a problem, kamar babu
abinda ya chanja, yet everything has
changed. Misali matar shi da take kwance
maybe ma a kusa da shi a yanzu, watakila
ya gama lallabata ne ta bata hakurin dazu,
tayi bacci shine zai kira ni, watakila ma
satar jiki yayi ya fito daga dakin su yaje
waje ya kira ni. Wadannan thoughts dinne
suka sa na katse kiran bayan na tabbatar
masa da rabuwa ta da Mukhtar kuma na
tabbatar masa da cewa babu sauran
change of something between us.

Ina katse kiran kuma nayi blocking
number din ita ma. Yaje ya karata da
Safinar sa na bar mata shi

A daren na fahimci cewa rayuwa zata
karayi min tsananin a garin Abuja, sai nayi
tunanin alkawarin da nayi wa Hajiya na
zuwa Umrah daga ni sai ita, ina ganin
lokaci yayi da zan cika mata alkawarin ta.

Washegari da naje gaishe da Daddy ma
gaya masa plan dina, ya amince kuma ya
nuna jin dadin sa sosai, nan take kuma ya kira wani agent da zaiyi mana shirin komai. Sai kuma yace "in kun dawo kuma sai mu shirya muje gabakidaya da
Sa'adatu da yara" nayi shiru ban ce komai
ba, sai ya kira sunana "Safiyya" na dago
kai ina kallon sa amma ban amsa ba sai
yace '"koma menene a tsakanin ki da
Sa'adatu da yaranta ki ajiye shi a gefe, na
dauka maganar zargin da kike wa
Mustapha ne ya saka ki ke jan jikin ki daga
gare su, yanzu wancan issue din is over
but har yanzu you seem even more
distant than before. Akwai wani abun ne?"
Na sunkuyar da kaina kasa ina girgiza shi
sannan nace "babu komai" yace "okay.
Bana son a samu komai din, bana son
wani issue tsakanin ku because without
Ahmad, yanzu su ne kadai dangin da kike
da su a duniya".

Na tashi kenan zan fita sai ga Mustapha
nan ya shigo, ya gaishe da Daddy nima
sai na gaishe shi, zan fita kenan yace min
"zaki je Oasis ne yau Fiyya? In zaki je zan
biki. Na kwana biyu ban je ba" na kalli
Daddy sannan na kalle shi nace "Okay" na
juya na fita a raina ina fatan sanda zan tafi
ya manta ko kuma baya gidan, amma sai
dai ina fitowa na ganshi a zaune a rumfar
motoci yana danna waya, ina shiga mota
kuwa yazo ya shiga ya zauna a
passengers seat, naji kamar zan saka
kuka amma a haka na kunna motar muka fita.

Muna fita guards dina suka biyo bayan
mu. Ya juya ya kalle su yace "seriously! I
am here, what more protection do you
want?" Nace "maybe protection from
you" yayi dariya, "you are kidding right? In
zan miki wani abu baa hanya zanyi miki
ba" nayi shiru na rabu da shi dan na san
dama neman magana ne ya saka shi biyo
ni, ni kuma yanzu magana ita ce abinda
bana son yi shi yasa nake barin gidan.

Muka cigaba da tafiya sai yace "Ban gaya
wa Mommy ko Daddy ba" ban kalle shi ba
nace "what?" Yace'"maganar mijin
Safina" nayi shiru na rabu da shi, ya
cigaba"baki tambaye ni dalilin da yasa
ban gaya musu ba" still bance komai ba,
sai yace "dalilin da yasa ban gaya musu
ba shine exactly dalilin da yasa ban gaya
wa Daddy inda kika je ranar nan ba" nace
"and what reason was that?" Yace
"because I care. I care about you and I
want you to trust me. Ina so ki fahimci cewa I am loyal to you.And I am very trustworthy" nayi ajjiyar
zuciya nace "wai dan Allah Mustapha kai
baka da budurwa ne da zaka je ka dama?
Kai ko zancen nan ma ba ka zuwa? At
& least go out and meet people, maybe
zaka samu mai sonka one day" yace
"yammata akwai su mana, su da kansu suke kawo kansu, but the problem is I already have my eyes and heart somewhere. I just want to be seen. I just
want my efforts to be appreciated".

Sai da muka je nayi packing sannan na
juyo ina kalion sa nace "Mustapha, it is
not going to happen. Let it go. Don't drag
please, we have been through this before.
Ka bar maganar dan Allah" na bude kofar
zan fita sai ya kira sunana, na juyo ina
kallon sa sai yace "and neither will you
and Muhammad happen. Daddy ba zai
taba bari ki auri mijin Safina ba".

Na fita daga motar da sauri na shiga dakin
da nake zama a ciki duk sanda na je gidan
na rufe kofa sannan na jingina da jikin
kofar. Ba maganar sa ce ta bata min rai ba
abinda ya bata min shine the fact that he
is right. Daddy will never let it happen.
Idan da ace Daddy zai samu yadda yake
so to zai so in auri wanda yake kusa da ni,
someone like Mustapha, someone da ba
za'a yi bincike ba idan zaa5yi auren.

lyayen Muhammad ma ba zasu barshi ya
aure ni ba considering alaka ta da Safina,
ko zasu bari ma zasu yi bincike, and
chances are high that they will find out
about my fast, I am sure Safina zata basu
labari ko da basu tambaye ta ba, And as righteous as they are, they will never let him marry someone da take da dan shege. So Mustapha is right. It is never
going to happen.

And just as if to rub salt on my wound sai
ga kira nan ya shigo waya ta from an
unknown number, a take na san cewa
shine, and my stupid heart pick up the
call na saka a kunne na, ya sake yin shiru
irin na jiya, nima kuma nayi shirun, sai
daga baya ya kira ni da sunana shi kadai
yake kira na da shi "Piya" na ji hawaye
naya bin fuska ta amma ban amsa ba, ya
cigaba "I know you can hear me, please ki
bani ko da minti biyu ne inyi miki magana,
I just want you to listen to me" and I
listened to him as he try to pour his heart
out to me, sai da naji kuka yana kokarin
kwace min sannan na katse kiran without
saying a word to him. Sannan nayi
blocking number din ita ma.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya mana,
kullum sai Muhammad ya saka sabuwar
number ya kira ni, farko ina dauka ba dan
komai ba sai dan inji muryarsa in samu
sanyi a zuciya ta, daga baya sai na daina
dauka dan na fahimci sauraron nasa was
doing more harm to my heart than good,
Giving me false hope, Da ya ga na daina dauka sai ya koma turo min messages, kamar dosage na magani
haka ya riga feeding dina da soyayyar sa,
safe, rana, dare, har zama nake yi in saka
waya ta a gaba ina jiran shigowar sakon
sa. And when the nights get lonely sai in
zauna inyi ta bitar messages dinsa kamar
mai dorin karatu.

A haka har muka tafi Umrah nibda Hajiya,
naji dadin tafiyar tamu sosai musamman
peace din da na samu a zuciyata sanda
na taka kafa ta a cikin garin Madina, and
the weight da naji any lifting daga
zuciyata sanda nayi kuka a cikin sujjada ta
a gaban ka'aba.

A ranar ne bayan mun koma masauki
Hajiya ta saka ni a gaba da tambaya.
"Kina da wani problem ne Safiyya? Akwai
abinda yake damun ki?" Na girgiza kaina
da sauri laughing nervously, "bani da wani
problem Hajiya, me kika gani?" Tace
"dazu kukan da kika yi a gaban ka'aba is
not normal. Abu biyu zai saka mutum
wannan kukan, ko dai wani babban zunubi
da kayi nadama akan sa kake neman
gafarar ubangiji ko kuma wani problem da
kake da shi kake neman Allah ya baka
mafita" nayi shiru ina niyyar ce mata bani
da problem amma sai hawaye na yayi
betraying dina,

Ta zauna tana kallo na kawai, sai kuma
tace "kin san yanzu da nake kallon ki me
kika tuna min dashi?" Na goge hawaye na
tare da girgiza kaina, sai tace "mahaifiyar
ki. Ganin da na fara yi mata a duniya.
Ranar da Hajiya Kyauta ta kawo min ita
gida na. I have never seen anyone as
broken as she was, she was so sad.
But you know what? She was also
determined. She had a purpose. Aim dinta a lokacin shine tayi all that she can a rayuwa so that zuri'ar ta, ma'ana you, will not be in her situation. Bata da
komai kuma bata iya komai ba a lokacin,
hatta shara sai da aka koya mata dan bata
¡ya irin ta mu ba. But she worked hard,
harder than anyone I have known. She
took risks, risks that even I couldn't. And
all for you. At the end kuma, she gave her
life for yours".

Nayi shiru ina jin ta, wondering if her
words are to make me feel better or
worst. Sai ta cigaba "but yanzu da nake
ganin ki a wannan halin sai na samu kaina
da tambayar kaina, All that your mother
did are for what? Because you are as
broken and devastated as she was
lokacin da ta shigo Abuja. To hakan yana
nufin all her sacrifices have been in vain kenan?"

Na girgiza kaina "Ammie was mistaken.
Money doesn't buy happiness. It only
creates problem. Well at least it did for
me. Gani da kudin dai yanzu but ba zan
¡ya siyan abinda zai saka ni farin ciki ba"
Hajiya ta girgiza kanta "no Safiyya. You
are mistaken not her. Money doesn't buy
all happiness, yes, amma talauci ma haka.
Money can create problems tabbas,
amma talauci ya fi shi creating problems.
Kowa da kaddarar sa, whether you are
talaka ko mai kudi. Safiyya, happiness can
only be found from within, you are the
only one responsible for your happiness
not abinda kike da shi and not mutanen
da kike tare da su. Only you and the
choices you make can make you happy"

Two weeks muka yi a can muka dawo
Nigeria, and sanda muka dawo I felt a lot
better duk da dai har lokacin ban samu
solution to MG problem ba.

Sai dai kuma a ranar da muka dawo din
muna zaune a falo da kowa da kowa har
da twins sai ga waya anyi wa Mommy,
tace Safina ce ta kira ta "maybe zata ce
zata zo miki sannu da zuwa ne" ta fada
sannan ta dauki kiran, amma kuma tana
dauka sai muka ga ta mike tsaye cikin
tashin hankali "accident? Wanne irin accident? Ban gane ba, Safina ce tayi accident ko mijinta? Tare suka yi? Ni fa ban gane ba, suna ina?" Na mike tsaye ina
kallon ta ido na kamar zai fado kasa.

Ta bi mu da kallo, jikinta har rawa yake yi
"'Ramla ce, yarinyar da na kaiwa Safina,
wai mijin Safina ne yayi accident. Ita ma
kuma Safinan wai tayi accident. Ni ban
gane ba. Kuma tace ba tare suka yi ba".

Na juya da gudu nayi waje, sai da na kama
handle din mota ta sannan na tuna ban
dauko key ba, na koma gurin daya motar
da bata bukatar key na bude ta da
fingerprint dina hannuna yana karkarwa
sannan na shiga na tashe ta na fita daga
gidan a guje.

Him👳🏻‍♀️

It has been 3 weeks already yana ta bin
Safiyya amma ya kasa samun ko da
response ne from her, ya zama as
frustrated as anyone can be. Ya zama
kuma very irritable, abu kadan ne yake
bata masa rai, Punching bag dinsa kuwa
tana shan duka dai dai gwargwado, And
he tried as much as he can to avoid
Safina dan yana gain zai iya rufe ta da duka anytime dan koda yaushe zuciyar sa tuna masa take yi cewa Safina ce sila, duk halin da yake ciki a yanzu ita ce ta ja masa.

And then ranar nan, ya dawo daga office
a gajiye ga yunwada yake ji, ya taho da
takeaway din abinci, ya shiga falonsa ya
zauna akan dinning table ya bude abincin
ya fara ci kenan ta shigo. Ya rufe idonsa
yana karanto adduoin samun nutsuwa, ta
karaso inda yake ta ja kujera ta zauna
tana facing dinsa, ya cigaba da cin
abincin pretending as if bai san tana gurin
ba. Tace "sannu da zuwa" ya cigaba da
cin abincin sa, sai ta kalli abincin tace "I
have cooked for you you know? You don't
have to buy food outside" ya dago ido
yana kallon ta, sai kuma ya girgiza kansa
ya cigaba da cin abincin sa, tace "it is still
not too late Muhammad, we can start all
this over again. Idan da zaka manta da
abinda baka da shi kayi concentrating
akan abinda kake da shi, then we can be
happy. Dole mu samu a way out of this life
kafin babyn nan yazo Muhammad, we
cannot bring him into this world a cikin
wannan yanayin" ta fada tana shafa cikin
ta, "he is your blood and he is innocent"
ya ajiye cokalin hannunsa yace "you made
the decision to bring him into this world at
this time Safina not me, dan haka laifin ki ne ba nawa ba.

Take the fault for once".

Ta girgiza kanta,
"how can you say that?
Da ma akwai wanda yake making decision
sanda za'a haifi wani idan ba Allah ba. Kar
kiyayya ta saka ka yin sabo dai" yace "you
know what I mean, and as always kina
kokarin kiyi twisting maganar ne. And
since we are talking about this, I want to
know me kika yi min a ranar nan" ta
girgiza kanta "ni ban yi maka komai ba"
yace "karya kike yi. Ke ma kuma kin san
karya kike yi. Asiri kika yi min ko? Shirka
kika aikata kawai dan ki kaini kan gadon ki
ko? Was that it?" Ta fara hawaye "ni
wallahi ba asiri nayi maka ba. Ta yaya ma
zaka yi kace haka? Ka san abinda ya faru
ai, I went to your room nayi wanka and
bayan na dawo daki na you came da
kanka" yace "yanzu duk toilet din da suke
gidan nan ki rasa a wanne zaki yi wanka
cikin dare sai na bedroom dina? Just
because kin san abinda kika yi and you
wanted to like add more salt to the wound ko?" Ya mike tsaye cikin fada, ya nuna ta "you are going to tell me what you did on way or another because idan har asiri kika yi dole ki bar gidan nan da ba zan cigaba
da zama na mashirikiya ba, you are going
to explain it to Mama, a lokacin zata san
who you really are" ta mike ita ma "ni ban
yi maka asiri ba, me yasa wai duk wani
worst abu kake danganta shi da nine? I
just wanted my husband to love me, I
thought you would love me" ya matsa
kusa da ita yace "and you did what?" Ta
juya tana kallon kettle dinsa da take jone a
socket. Ya kalla shima, sannan ya kalle ta,
"a ciki kika saka asirin?" Tace "ba asiri
bane ba na gaya maka" yace "menene
to?" Ta sunkuyar da kanta kasa tace
"desire pill".

Ya bude baki cikin mamaki sannan ya fara
ja da baya "desire pill?" Ya maimaita
"'yanzu lalacewar ki har ta kai haka dama
Safina? Yanzu abinda na dauko na kawo
gida na kenan?" Ta fara kokarin kare
kanta '"I tried everything I could to get
your attention Muhammad, har abinda
ban taba tunanin zanyi ba a rayuwata nayi
saboda kai, na kaskantar da kaina iya kar
kaskantarwa. I thought...." Sai kuma ta
kasa karasa maganar saboda wani mugun kallo da yake yi mata.

Ya sake taku biyu zuwa gare ta yace
"yanzu ke har kinsan kiyi wa namiji amfani
da irin wannan abun dan ya kwanta da ke?
Maza nawa kika saka wa? Huh? Nawa?
Now am not even sure if that is mine" ya
fada yana nuna cikin ta. Fuskarta ta nuna
bacin rai tace "me kake nufi? You are
crossing a line kuma Muhammad . Kai ne
babban shaida ta cewa kai ne namiji na
farko a gare ni. Kuma kai ne na karshe.
Then how can you accuse me of that?"
Yace "nine shaida? I am not sure of
abinda na tarar ai. Since kinyi wayewar
using desire pill am sure kinyi wayewar
faking abinda kike magana akai. I read
cewa yammata suna iya Watsewar su a
waje su yi na fake su kai gidan miji kuma.
And I am sure you can do that. So wannan
dan in kin haife shi sai anyi masa dna
sannan zan karbe shi".

Ta zame ta zauna akan kujera tana dafe
kirjinta, daga dukkan alama bai taba gaya
mata mai zafin ta yau ba. Tayi shiru ta
kasa magana tana kallonsa, sannan a
hankali tace "i have been good. I kept my
chastity and brought my virginity to my
married home na kuma bawa mijina na
sunna, Ni ba yar iska bace ba
Muhammad. Yan iska suna can a inda suke. Amma ni kake yiwa kazafin zina sannan kake sheganta min dan da na samu cikin sa a dakin auren sunna, dakin
auren ka. Bayan shegun suna can a inda
suke."

Yace "I am not sure about that, sai kin
haihu naji abinda likita yace" tace "na
yarda za'a yi dna din, just dan kar ayi wa
dana tambarin da aka yi wa nata. Just dan
kar ayi min tambarin da aka yi mata" ya
juyo yana kallon ta, ita ma shi take kalla
cikin ido, babu sauran toro a idonta,
kukan ma ya tsaya. Yaji zuciyar sa tayi
contracting yace "ita wa kenan?" Ta mike
tsaye tana kallon cikin idonsa tace
"kasan wadda nake nufi ai" ya karaso ya tsaya a
gabanta cikin kaurin murya yace "say her
name if you dare" tace "Safiyya. Safiyya Adam Muhammad" yayi shiru yana kare mata kallo, not knowing what to think and she helped him clear his doubts "amsar da kayi ta nema kwanan baya ita
ce zan gaya maka yau, cikin da ka gani a
jikin Safiyya last year cikin gaskiya ne.
Kuma na shege ne. She slept with so
many men that she couldn't even name
the father of her unborn baby, Sai da ta
haifa sannan akayi dna. Wannan ya sa
Daddy a kokarin rufe abin kunyar da tayi ya aura mata Mukhtar. Wannan ne dalilin da yasa tayi breaking up with you dan tasan iyayenka ba zasu bari ka auri
someone like her ba. A yanzu haka tana
da dan shege yana nan a raye hiding
somewhere only she knows"

Yayi taku biyu baya yana girgiza kansa
"you are a liar" tayi murmushi, "not this
time, I am not. In baka yarda ba go and
look into her eyes and ask her idan bata yi
cikin shege ba, go ask her idan bata da
dan shege"

"You are lying" ya sake fada, idanunsa
suna juyewa, yana jin jiri yana neman
daukan sa, yes abinda ta fada na ciki
made sense, it answered a lot of
questions. Amma zuciyar sa ba zata iya
daukan gaskiyar ba. Ji yake yi kamar zata
bar kirjinsa. Da baya yake tafiya har ya bar
dining din ya shiga falon sa, wani jiri ya
debe shi ya fadi akan kujera a falon ya
dafe kansa, ta karaso inda yake da sauri
already tana regretting abinda ta gaya
masa, ta rike shi "Muhammad!" Ya mike
tsaye da sauri sannan ya sauke maruka
guda uku akan fuskarta, saboda karfin
marin sai da ta kai har kasa, ya wuce ta da
sauri ya dauki key din motarsa ya fice
daga falon da sauri.

Ta hango fitarsa, abinda ta fara tunani
shine mota zai shiga, ta mike da sauri duk
kuwa da dishi dishin da take gani amma ta
bishi, ta san shi da gudu a mota a halin
lafiya lau ma ballantana a halin da yake
ciki. Ta fita a daidai lokacin da yake yiwa
mota key, ta karasa da sauri "Muhammad.
Dan Allah ka tsaya, kar kayi driving, dan
Allah ka tsaya, tayi kokarin rike motar
yayin da shi kuma ba tare da ya lura da
fitowar ta ba ballantana yaga ta rike mota
ya ja motar a guje, motar ta ja ta da karfi
sannan ta fadi a kan cikin ta a tsakiyar
compound din gidan a daidai lokacin da
Ramla ta fito saboda jin muryarta da tayi
tana magana da karfi.

A guje ya fitar da motar da ga gidan,
wannan ya sa bai kalli titin ba ya hau kai a
guje, motar da ta taho a guje akan titin
itama ta daki side din tasa motar, nan take
motar ta sa ta fara adungure a kan titin,
sai da ta dungura sau uku sannan ta
tsaya,

Maman Maama✍🏻
[07/01, 10:46 pm] +234 906 816 1960: ❤️‍🩹SAFIYYA❤️‍🩹


Episode Fifty Two: Together


Naji wata irin faduwar gaba, "what?" Na
tambaye shi a tsorace, sannan na juya ina
kallon layin mu da muka fito da ga ciki
"Muhammad what are you doing. This will
make things worse, wannan ba zai gyara
komai ba sai dai ya kara batawa. Dan
Allah ka tsaya. Dan Allah ka tsaya muyi
magana you will understand abinda nake
nufi".

Bai ko juyo ya kalle ni ba ya cigaba da
driving dinsa, na sake kokarin yi masa
magana "to ina zaka kaini ma wai? Ina
zamuje?" Bai kalle ni ba yace "I don't
know. But we will figure it out" na girgiza
kaina "I understand ranka ne a bace,
annabi ma ya hana yanke hukunci a cikin
bacin rai. Please park the car and let's
calm down a bit, we will figure things out",
Bai amsa min ba sai ma kara gudun motar
da yayi yana ta wuce motoci, wannan ya
kara tabbatar min da bacin ran da yake
ciki, in dai yana irin wannan driving din to
either ransa a bace yake ko kuma he is
stressed or tired, amma idan yana cikin
farin ciki musamman in muna hira mai dad a mota to a hankali yake driving, most of the times ma dead slow yake tafiya.

Na juya kaina ina kalion motocin da muke
wucewa toro yana kamani, what if wani
abun ya same mu kuma? Na waiga baya
na and I saw my guards following us and I
calmed down a bit, at least someone is on
the look out for us. Na sake juyowa ina
kallon sa, trying to get him to look at me
"Muhammad dan Allah slow down. Please
park the car. Let me drive, I will take us to
duk inda kake son muje" ya dan kalle ni
kadan sannan ya sake mayar da idonsa
kan driving dinsa, na sake cewa "Please
Yay Muhammad".

Ya sha wata kwanar da ta hau da mu kan babban titi, shan kwanar da yayi a guje ya
saka naji faduwar wani abu a seat din
baya, na juya and I saw yar karamar jakar
takardun sa, I have seen it ones and he
told me it contains all the important
documents na rayuwar sa. Na juya da
sauri na dauko ta na bude, making sure
ita din ce, sannan na rufe ina kallon sa
idona cike da hawaye, wato da gaske
yake kenan,

Ya kalle ni shima sannan ya kaill jakar
hannuna yace "We will need them, Dole
zan bukaci neman aiki so that I can take
care of you" naji hawayen sun karasa
gangaro wa, poor Muhammad, neman aiki
yake so yayi dan ya samu kudin da zai
kula da ni, ni Safiyya. How innocent of him,

Ya cigaba da magana. "I have some little
money in my account. We can get you
some clothes with it. And we can also get
a place to stay for a while. And other
necessities, Then I will look for a job. Or
get some business started. Ke kuma sai ki
koma school. Not MD though. We are
going to be Okay. Like you said,
everything is going to be alright".

Na goge hawaye na sannan na rufe jakar
na ajiye ta a gabana. Abinda na fahimta a
lokacin shine the only way to get to him
shine in nuna masa na yarda da abinda
yake lissafawa, that will calmed him down.
In naki he will only get more angry.

Nace "I can work nima. I can get a job da
baya bukatar takardun makaranta. Na iya
girki, zan iya samun aiki a restaurant or
something" ya girgiza kai "no, you will not
work in a restaurant, Sai dai kiyi a gida.
Irin wanda ake yi ana order din nan, I can do the delivery" nayi murmushi tare da kwantar da kaina a jikin kujera ina kallon sa nace "no. Ba zaka yi delivery ba, Haka kawai in mata sunyi order su ringa ganin
ka? We will get a delivery man. Sai a siva
masa abin hawa, Bana son yammata suke
gane min kaj" and I saw his body relaxed,
har rikon da yayi wa wheel din ma karfin
sa ya ragu, his eyes softened, ya juyo ya
kalle ni yace "ohh, and kuma kika ce zaki
yi aiki a restaurant. Kin dauka ni zan barki
kina serving maza?" Na bude ido "hey, ba
fa waitress nace zan zama ba. Just a
coOk, A kitchen zan ke aiki na. Babu
ruwana da customers" yace "still. It may
get crowded. And yadda kika iya girkin
nan someone may say yana son ya ga mai
girkin. Gwara kiyi girkin a gida ni kuma
inyi delivery" nayi murmushi ina kallon
fuskarsa "you will be the cutest delivery
guy ever, that's why ba zan barka ba, Sai
dai in zaka ke saka nikab" and he laughed. Kar karamar dariya but ta chanja yanayin
fuskarsa gabakidaya, ya dan dafe kansa
da hannunsa daya yana cigaba da driving
da daya hannun, zuwa lokacin ya koma
driving slowly.

A hankali nace "sannu, Kan ka ne yake
ciwo? Let me drive" ya girgiza kansa "I am fine" nace "ka san dai | am a better driver than you ko? Look at what your rough driving caused you, Kaje ka fasa kai ka kusa ka jawo min asara" na fada ina nuna
bandage din kan sa, ya dan taba gurin
ciwon tare da bata fuska alamar vana vi
masa zafi sai kuma yace "shi yasa in
muka haihu ke zaki ke driving yara zuwa
school, dan in suna yi min hayaniya a
mota za'a iya samun matsala" nace "to in
ka bani motar da wacce zaka ke zuwa
office?" Yace "kafin nan na sayi wata ai. It
won't take me long to find a job. But ban
san yadda zaki ringa hada makaranta da
catering services da kuma school runs
din yara ba. Sai dai a samo musu driver"
nace "another car kenan fa. Ga kuma
kudin salary din driver. Dole sai mun koyi
managing abubuwa fa" ya juyo yana
kallona da dariya a muryarsa yace "who
are you? Where is Safiyya Adam
Muhammad, the girl that always want to
spend money and buy classy things and
enjoy soft life. Ke ce kike zancen a tattala
kudi kuma yanzu?" Nayi murmushi "to
yaya zanyi? Yana yin rayuwa ne ya chanja.
Dara kudin Daddy nake kashewa yanzu
kuma any kidnapping dina daga gidan
Daddy and I am on a run. Zuwa inda not
even my kidnapper knows. Dole yanayin
tunani na ya chanja zuwa survival instinct".

Muka danyi shiru babu wanda yake
magana for a while muna cigaba da tafiya
a titin barin gari kowa yana lissafi a cikin
zuciyarsa. Waya ta tayi kara, na duba
naga number din one of my body guards
ne, na dauka na saka a kunne na sai va
tambaye ni if I am okay, a hankali nace "I
am fine" sannan na katse kiran. Ya miko
min hannun sa yayi min alamar in bashi
waya ta, nayi ajjiyar zuciya na mika masa
sai ya kashe ta ya ajiye a tsakanin mu
sannan ya dauko ta sa ita ma ya kashe ya ajiye.

Muka cigaba da tafiya sai kuma yace "You
will continue to have the kind of life you
are used to, or even more. I will work hard
kinji" nayi shiru ina kallon sa, imagining
the kind of life da muka gama shiryawa
yanzu a cikin motar nan, just me and him
alone in the world. Sai kuma nace "It
would have been a good life. A great life
in dai da akwai ka a ciki. But it is just a
dream Muhammad. We cannot have that
in reality. We have responsibilities,
Responsibilities to our parents. They love
us, they love us more than anything. They
do not deserve this from us" ya kalle ni
yace "and do you think we deserve what
we are going through? Wanne laifin muka aikata?" Nace "ba muyi laifin korai ba, amma basu sani ba ai. We just need to get them to listen to us and to understand us, na tabbatar ba zasu yanke mana
hukuncin da zai cutar da mu ba. Saboda
sun fi mu san kan mu" yace "aha! And
that is exactly what I am trying to do. To
get them to understand. To understand
that I cannot continue living like this. I
cannot continue living without you".

Na sake cewa "not like this Muhammad.
This will break their hearts. Zasu ga
kamar mun zabi junan mu ne a maimakon
su. Ba zasu ji dadin hakan ba. Muma ba
zamu ji dadin hakan ba. We need to do
this the right way".

Ya juya motar zuwa gefen titi yayi packing
dinta sannan ya juyo yana kallona yace
"then tell me which way is the right way. I
tried explaining things to Mama ta kasa
fahimta kuma banga laifin ta ba saboda
nima ban fahimta ba. All you have been
telling me in this relationship is nothing.
Sometimes it felt as if I am in this
relationship alone. Baki gaya min komai
ba ban san komai akan ki ba, ban gane
komai ba ta yaya zan fahimtar da su? All I
know shine ina son ki and I know you love
me bayan hakan ban san komai ba. Then
ran daya you just appeared like that and told me Wai Kina da aure gashi har Kina


halin damuwar da yake ciki a yanzu ni na
jefa shi a ciki. A hankali nace "I am sorry
Muhammad" ya nuna ni "if you say you
are sorry one more time....."
. " Sal kuma ya mayar da hannun ya ajiye yana kallo na, trying to calm himself down.

Sannan kuma murya can kasa yace "you
have no idea how stubborn your love have
been a cikin zuciyata, You have no idea
how crazy it almost drove me" ya kalli
kansa, with bandages on different parts
of his body yace "hell, I am not sure ma
ko yayi succeeding in making me crazy.
Just look at me. I mean I am literally on a
run from my parents after kidnapping
you" ya karasa maganar yana dariya, nima
dariyar na taya shi, sai kuma yace "I have
tried in ga na cire ki daga raina Safiyya
Adam na kasa, I mean you get stuck in my
head har zama nake yi muyi hira a cikin
kaina wani lokacin muyi fada in baki
hakuri ko da ba nine da laifi ba".

Na rufe fuskata da hannuna ina dariya
sannan na bude nace "dole a bani hakuri
in ba haka ba asha rigima" ya girgiza kai
"piya, you are impossible" muka danyi
shiru, zuwa lokacin gari yayi duhu sosai,
sai kuma on a more serious note nace
masa "na san I have not been a good
girlfriend to you, Babu abinda na kawo
rayuwar ka sai tarin damuwa da emotional torture. Shi ya sa kullum nake baka hakuri, dan bani da abinda zan baka sai hakurin. I mean har a cikin baccina nake
baka hakuri...." Ya katse ni "no, kina da
wani abu da zaki bani bayan hakuri. Zaki
fada min gaskiya, and when I say gaskiya I
mean the entire truth. I want to know
everything." na gyada kai na "na yarda,
You deserve the truth kuma zan gaya
maka truth din, gabakidayan ta, Na kuma
tabbatar zaka fahimce ni in sha Allah. But
Please Muhammad we need to go back
home. Na san by now an fara neman mu,
musamman kai da kake asibiti, Mama da
Abba ba zasu ji dadi ba. And Daddy, ba
zan iya yi wa Daddy haka ba Muhammad,
ya gaya min kaje ka gan shi ranar nan na
tabbatar ka ga yanayin jikin sa, in na tafi
na bi saurayi na barshi bakin ciki na will
kill him, we will figure this thing out while
still under our parents'

Yayi ajjiyar zuciya "you are right. I was
wrong to try taking you away from Daddy.
Zan mayar da ke gida. But I also want you
to promise me two things. Na farko zaki
gaya min gaskiya akan komai ba komai.
Na biyu, from now own, no more hiding
things from each other, we will do
everything together. We will solve the
issue with our parents together. We will overcome all the obstacles together", Na gyada kai "na amince, nayi alkawar'" yace "Okay, then start talking ..... From the
beginning"

Na danyi shiru ina kalion yatsun hannu na
sannan nace "it is a long story
musamman tunda ina so in fara maka tun
daga farko, zan gaya maka kamar yadda
nayi alkawari amma ba yanzu ba. We do
not have time a yanzu, You need to get
back to the hospital. I need to go back
home tun kafin hankalin Daddy ya tashi"
ya gyara zama yace "we have the whole
day..." Daga nesa muka ji ana kiran sallah
a wani masallaci. Yayi shiru yana kallona
sai nace masa "wannan sallar isha ce ba
magrib ba" yayi sauri ya duba agogon
motar and the time was 7:52pm.
Na sake maimaita masa "We need to get
you back to the hospital, and I need to
get back home" ya tayar da motar tare da
cewa "it is a long way ai. You can tell me
in the way",

Muka juya mota muka koma daya hannun
muka dauki hanyar komawa cikin gari,
amu jima muna tafiya ba yayi packing a
gaban wani masallaci ya shiga yayi sallah
nima nayi alwala na dauko sallaya a cikin motarsa nayi sallah, na lura da motar guards dina a dan nesa da mu kadan. Ina idarwa ya dawo ya sake tayar da motar
muka cigaba da tafiya, muna fara tafiyar
ya kalle ni yace "uhun. Ina jin ki. Start
talking" na danyi shiru ina kallon sa,
thinking of where to start from.

Na san yana bukatar ya fahimci komai, tun
daga dalilin da yasa na kasa kai shi gidan
mu a wancan lokacin zuwa uzurin Daddy
na hana yi min samari wanda shine dalilin
da yasa ban kai shi gurin sa din ba, amma
ba zai fahimci duk wannan ba sai ya san
labarin Ammie. Dan haka daga labarin
Ammie ya kamata in fara yi masa, ko
kuma ma ince daga labarin Baba Hadiza.

Na dauki waya ta na bude pictures nayi
scrolling zuwa hoton su Ammie da na
dauka ranar nan a waya ta, na nuna masa
tare da nuna Ammie nace "wannan ita ce
mahaifiyata" ya kalle ta sannan ya kalle ni,
"kuma kama sosa'" nayi murmushi
"Nagode" yace "Allah ya yi mata rahama"
nace "Amen" sai kuma na nuna Baba
Hadiza nace "wannan mahaifiyar ta ce,
sunan ta Baba Hadiza, wadannan kuma
yan'uwan ta ne, uwa daya uba daya" ya
gyada kai cikin fahimta tate da mayar da
hankalinsa kan driving din da yake sai nace "duk sun mutu gabakidaya" yayl sauri ya kalle ni da mamaki "what? Ga baki dayan sup" Na gyada kai "yes,
Ammie ce kadal ta girma a cikin su, ita ce
ta karshen mutuwa" yace "how? Accident
ko menene?" Nace "no they died in
different kind of tragedies" na danyi
murmushi nace "| used to say that
tragedy is another name for my family.
Yanzu kuma zan fahimtar da kai dalili",

Daga nan sal na bashi labari, labarin Baba
Hadiza da iyayenta da yan'uwan ta da
yanayin rayuwar su, sai kuma na bashi
labarin auren ta da Alhaji Haladu da
yanayin zamanta da abokan zamanta har
zuwa mutuwar Alhaji Haladu da kuma
yadda rayuwa da kasance musu bayan
nan. Sannan one by one na bashi labarin
yadda suka mutu, tun daga kan Khadijah
har zuwa kan Sauda, da kuma yadda
Ammie ta gudu dan kar ayi mata irin auren
Baba Hadiza, dan kar ta haife ni in rayu
cikin wahala kamar yadda su suka yi, na
bashi labarin shigowar ta Abuja da
zamanta a gidan Hajiya.

Duk a cikin labarin nawa in dai aka zo kan
abinda bai fahimta ba zai tambaye ni in
sake fahimtar da shi, amma sai na ga
labarin Hajiya ya dauki hankalin sa sosai.
"you mean Hajiya Maryama? Yayar Mommy?" Na gyada kai "eh ita. I guess you already know her" yace "naje gidan ta ones, she said ta san grandma dina, and ranar nan ita ma grandma take ce min ta
san ta and she said she knows her
daughter mai suna Safiya, wai kuma ta
auri wani mai suna Adam. I told her bata
da yaya amma she insisted tana da ya mai
suna Safiya" nayi murmushi ina jin dadi,
nace "haka take cewa, cewa take yi yarta
ce, amma in reality yar aikin ta ce. And
she was so kind to her in ways that I
cannot describe" muka sake yin shiru a
lokacin da muke shigowa unguwar mu. Ya
je yayi packing a kofar gidan mu yana
kallona yace "yanzu cewa zaki yi zaki
shiga gida ki bar ni ko?" Nace "ko zaka zo
mu shiga tare?" Ya kama handle din kofa
"finally za*a kai ni wajen Daddy" nayi
dariya "rufa min asiri. Wasa nake maka fa"
ya langwabe kai "still da'" nace "ka dan
kara min lokaci kadan. I need to prepare
him. I need to find words da zanyi using
to convince him" ya kalli gate din mu yace
"you need the words now" na juya nima
na kalla and I saw Malam Ya'u a tsaye
yana kallon mu sai kuma ya juya ya koma
cikin gidan. Nayi ajjiyar zuciya nace "l
really don't know me zan ce masa, amma
kaima kana bukatar words din da zaka
fada a gida" yayi ajjiyar zuciya "I think we
should just tell them the truth, sai muga abinda zasu yi akai. Kamar yadda kika ce, they love us and will make the right decision for us". Na dauki wayata na rike ina juijuya ta ina kallon sa, feeling reluctant, kamar kar in
fita daga motar, kamar kar in rabu da shi,
but kamar yadda nace, we must face our
reality. Sai kuma nace "good night Malam
Muhammadu" na bude kofa na fita da
sauri sai ya kira sunana "Piya" na juyo ina
kallon sa sai yace "don't get married
again" nayi murmushi "I will, I will get
married. And you will be the groom" sal
kuma naji kunyar kalion da yayi min na yi
cikin gida da sauri. Amma sai na tsava a
jikin gate, ban matsa ba sai da naji alamar
ya tafi sannan na yi hanyar cikin gida ina
harhada kalamai a raina.

A hanya muka hadu da Baba Ya'u yana
fitowa daga bangaren Daddy, nace
"sannu Baba Ya'u" ya bini da kallo yace
"sannu ranki ya dade. An dawo lafiya?"
Nace "lafiya lau" sai ya koma gurin zaman
sa ni kuma na shiga cikin gidan.
Na san dai Mommy tana asibiti wajen
Safina, though ban sani ba ko ta dawo
gida bayan na fita, Mustapha kuma da
twins tunda ban gansu a waje ba kuma
basa falo na san maybe sunyi bacci, amma Daddy na san idonsa biyu tunda yanzu naga Baba Ya'u ya fito daga gurin sa. Ma san kuma ya kamata inje in gan shi
ya ganni, amma kuma ban san me zan ce
masa ba. Kitchen a fara shiga ina neman abinda
zanci dan yunwa nake ji, gwara ko fadan
za'a yi min ayi min da abinci a ciki na kar a
gama yi min fadan kuma in kasa cin
abinci. Na samu abinci na zuba, na hada
smoothie na na sha sannan na tafi part din Daddy.

Yana zaune ya saka tv a gaba amma daga
gani kasan ba ita yake kallo ba. Na shiga
da sallama "Daddy ba ka kwanta ba?" Ya
daga kai ya kalli agogo sannan na juyo
yana kallo na fuskarsa cike da damuwa.
Na karasa gabansa "barka da dare
Daddy" yace "kin dawo? Ya jikin Safinan?"
Na sunkuyar da kaina ban ce komai ba ina
jiran inji ta inda fadan zai fara sauka kaina,
ko kuma at least ya tambaye ni ina naje
amma sai naji yayi shiru bai ce komai ba,
sai dai fuskar sa a cike take fal da
damuwa, Haka na gaji da zama sai nace "Daddy a
kashe maka tvn ka je ka kwanta? It is
getting very late" yace "ki barshi, Ki je ki kwanta" sat nail ban Il dadi ba, bana son
jayi fushi da ni, so hake yayi min tada ya
aye min abinda nayi ba dal dal bane ba
in yaso ni kuma sat inyi masa bayant
Amma kuma ko bayanin ne ina bukatar
hada kalmomin da zanyi bayanin da su.
Dan haka wannan fushin da yayi duk da
dal banji dadin sa ba amma ya bani
chance din shirya case dina, Amma eluk
da haka sal nace "Daddy kayl hakur'" bal
amsa min ba daga farko sal daga baya
yace "akwal abinda kike so kl gaya min
ne? Akwai laifi da kike so kiyi confessing?* Na bude baki sal na mayar na rufe ban ce komal ba, sal yace "tashi kI je ki kwanta" har na tashi zan Ata /lkl a
sanyaye sai ya kira sunana, na juyo sal
yace "abinda ya faru a da ba zai maimaita
kansa ba. Do you understand me?" Na
gyada kai da sauri *yes, Daddy" na fita da sauri,

Daki na na wuce da sauri ina /in babu dad
a raina, Na san dal Baba Ya'u abinda zal
ce masa shine mjin Safina yazo ya dauke
ni a mota, Sannan kuma yanzu zai ce
masa mijin Safina ne ya dawo da ni a
mota, And I thought he will confront me
about menene alaka ta da mijin Safina da
har zai bar asibiti ya taho wajena? Kuma
ina muka je, But he didn't. And only God
knows why.

Ina shiga daki na zauna a favorite spot
dina, kan gado na ina facing my mother's
picture. A raina ina ta saka da warwara ina
so in samo hanyar da zanbi wajen
warware wanna lamarin ba tare da ran
iyayen mu ya baci ba. Kamar yadda
Muhammad ya fada, we will have to make
them understand, Yes, da mun gudu din
da gaske they may understand but in a
hard way, ni kuma so nake mu samu
mafita ba tare da ran su ya baci ba.
Ban samu kwanciya ba sai after two na
dare, and still without a concrete solution.
Sai dai ina kwanciya waya ta tayi kara na
duba naga number din Muhammad, nayi
murmushi, duk damuwa ta tana gushe
wa, na dauka nace "hey Baby" yace "hey,
bulala nawa aka yi miki?" Nace "ko daya.
Kai fa?" Yace "they are giving me a silent
treatment. Ko fadan ma ba'a yi min ba.
Mama da Abba sun gane gurin ki na taho,
but the rest are thinking cewa ba'a cikin
hayyacina na fita ba. Maybe su maman sun reserving fadan ne for later, " nace "to ko dai meeting
suka yi tare da Daddy sanda bama nan?
Shima kamar reserving yake yi for later". but the rest are thinking cewa ba'a cikin hayyacina na fita ba,

Maybe su maman sun reserving fadan
ne for later. " nace "to ko dai meeting
suka yi tare da Daddy sanda bama nan?
Shima kamar reserving yake yi for later".
Yayi dariya, na fahimci he is feeling much
better than sanda ya bar asibitin and naji
dadin hakan sosai. Yace "I guess we will
find out soon enough, Ni dai na san cewa
wannan battle din bamu fara shi dan mu
daina ba. Yanzu problems a side, yaushe
zaki cigaba da bani labarin? I need to
know all the details kafin in ja damarar
yakin" nace "as soon as any discharging
din ka from the hospital. For you to fully
understand the next part of the story, ina
bukatar in nuna maka wani abu" yace
"Okay. Tomorrow zasu sallame ni insha
Allah. Highest next tomorrow" nace
"Okay, baka da lafiya, bara in barka ka
samu bacci sosai, good night" yace
"good night, and don't forget to dream about me".

And I did dreamt of him, Muna ta hira
muna dariya, And it was the best dream
da na vi a cikin shekaru.

Him👳🏻‍♀️

Sai da ya tabbatar ta shiga gida sannan
ya tayar da motar yana murmushi, ya tuno
kalaman ta na karshe sai ya girgiza kansa
cikin jin dadi, sai kuma yayi sauri ya dafe
kan "ouch!" Ya fada vana jin zafin ciwon
da yake kan nasa, shi da har ya manta da
shi, lokacin da suke tare kamar ciwon ya
warke, kamar ma bai ji ciwon ba, yanzu
kuwa sai yaji ciwon ya dawo. Maybe dama
ita ce maganin,

Ya fara tunanin abinda yake gabansa,
yadda zai fuskaci iyayensa dan ya
tabbatar zuwa yanzu sun san me yayi,
gashi ya kashe wayarsa dan haka sun yi ta
neman sa a waya ma basu same shi ba.
Ya yarda Safiyya ta fi shi gaskiya, their
parents do not deserve this. But he just love her a lot.

Yayi tunanin zuwa gida saboda ya san by
now sun bar asibitin sun koma gida amma
kuma cion da kansa yake yi masa ya
saka ya chanja shawara ya juya zuwa
hanyar asibiti, ga shoulder dinsa ma sai
yanzu ya tuna da ciwo a wajen, and
maybe driving din da yayi ne ya saka take
masa zugin azabar zafi. Kafin ya karasa
asibitin ya hada gumi, yana zuwa yayi packing sannan ya shiga reception, yana shiga Wata nurse ta ganshi ta ce "ga patient din da ake nema ya dawo". Ya
karasa kan kanta yace da attending nurse
*just give me something for the pain* sal
wani doctor yazo ya kama shi yace "let
me take you to your room, and then we
will see what we will do about the pain",

Aka mayar da shi dakin da va gudu daga
ciki aka kwantar da shi a kan dawo
sannan aka mayar masa da drip din da ya
cire, ya kwanta ya rufe idonsa yana jin
likitocin suna ta zirga zirga a kan sa, a
hakan ya fahimci cewa su Mama sunyi ta
neman sa anan asibitin sai suka yi waya
gida aka ce musu yaje can shine suka tafi
neman sa can din, maybe har gidajen
yan'uwa an zagaya neman sa.

Ai kam sanda suka zo kungiya guda suka
Zo, with all his uncles and aunties, yana jin
mamie tana maganar zata nemi asibitin
suyi referring dinsa zuwa asibitin ta, she
is a neurosurgeon kuma wai suna tunanin
buguwar da yay aka ce ta saka shi ya fita
ba tare da ya san ya fita din ba.

Kowa sai lallaba shi yake yi, tun daga kan
ma'aikatan asibitin har zuwa kan family
dinsa, a cikin yan duba shin yaji har da
muryar Mommyn Safina, amma sai ya cigaba de pretending kamar bace/ yake yI har sai da ta fita, amma daya bude Ido ya kalli Mama sa yasan cewa ta san yana sane ya fita, kuma tasan inda yaje. And
she looks very disappointed in him, Sal
dai bata ce masa komai ba. Ranar Abba
ne da kansa yace zai kwana a gurinsa a
asibiti instead of Haidar da yake kwana
da, Sai bayan da kowa ya tafi Abba kuma
yayi alwala ya tayar da sallah sannan
Muhammad ya mike ya dauki wayarsa ya
cire drip din hannunsa ya shiga toilet
kamar zai kama ruwa and he called her.
She answered immediately with "hey Baby".

And ranar yayi baccin da ya jima bai yi
mai dadi irin sa ba. Ba wai problem din ne
babu ba, but with her by his side, yasan
they can overcome any obstacle together,

Maman Maama✍🏻[07/01, 10:46 pm] +234 906 816 1960: ❤️‍🩹Satiyya❤️‍🩹

Episode Fifty Three: A Forever Thing 2


Washegari da safe ma yayl bacel sosal
bayan ya koma ya kwanta after subh,
Maganganun Mamie da Mama ne suka
tashe shi, "Wannan yaron fa babu abinda
yake damunsa ina gaya miki Moon, ki rabu
da shi kawal, tsabar rashin Jin magana ne
a cikin kansa ba elwo ba" Mamie tace
"amma ya kamata muy) confirming first
kafin muce babu komal, Ni sam bana jin
dadin ganin sa a haka wallahi, KI bari in
tafi da shi can asibitin koma menene sal
mu tabbatar a can" Mama tace "kashi ina
baki kina kin karba, Yana sane ta yake
komal in gaya miki. Wal yaron nan jlya fa
shirin guduwa yayl, har da zuwa gida ya
hada kaya akwati guda, har da daukan
takardun makaranta ya zuba a mota ya
tafi, Kamar irin yammatan nan na da da
suke guduwa daga gida su shige duniya
idan za'a yi musu auren dole", Mamie ta
yara dariya "kal Zainab, gidadon ne zal
gudu daga gida, Salihin yaro irin wannan.
A cikin yaran mu fa Allah Gidado yana
daga cikin nutsatstsun cikin su. To saboda me zai gudu? Mama tayi kwafa yanzu kike cewa nutsatstse, yaron nan fa duk inda kike tunani ya wuce nan. Wai
dan nayi masa fada ne fa shine ya je ya
hada kaya zai gudu, ko gidan war wa zai
je?" Mamie tace "amma akan menene
kika yi masa fadan? Let's start from there,
nina san ruwa baya tsami banza babana
ba mutumin banza bane ba" Mama tace
"ai dama bayan sa zaki bi. An kusa a fara
lissafa shi a cikin mutanen banzan ai in
dai bai chanja halin sa ba. Duk wanda zai
bijirewa maganar iyayensa menene shi?"
Mamie tace "ni dai ki gaya min Please,
akan menene?" Mama tace "to wadannan
yaran suna da wani problem ne da ya
wuce guda daya?akan wata yarinya ce.
Akan wata tsi....." Sai kuma tayi shiru sannan tace "bana son in tsine mata kar ta dawo ta karasa tarwatsa rayuwar yaron nan" sannan sai ta bawa Mamie labarin abunda ta sani game da Safiyya.

Duk, maganar da suke yi Muhammad yana
jin su, amma sai ya cigaba da pretending
kamar bacci yake yi, a ransa yana lissafin
cewa wannan ranar is going to be a long
day, dan haka bai shirya fara ta yanzu ba.

Yana nan kwance har suka gama
maganganun su, Mamie ta fahimci point
of view din Mama, kuma ta fahimci
damuwarta a matsayin ta na uwa, Amma
kuma sai ta bata shawara. "Sai mun bi abin a hankali, tunda har yaron nan duk soyayyar da yake yi muku da mu bakidaya ya iya hada kaya zai bar gida to gaskiya
sai mun hada da dabara. He loves her
deeply. Kuma love either make a person
or breaks him. Ya kamata mu bashi
listening ear, muji mu kuna saka ido sai
mu bashi shawara. Amma kar muyi
kokarin forcing din sa in ba haka ba zamu
tura shi bango, a karshe kuma zamu iya rasa shi".

Mama tace "to wanne irin tura wa zuwa
bango ne ya wuce hada kayansa da yayi
zai shiga duniya?" Mamie ta sake yin
dariya sannan tace "to ba gashi nan ya
dawo ba? Yadda ya tafi da kafafuwansa
haka ya dawo da kafafuwan sa. So let's
start from there. Mu fara tambayar sa
dalilin tafiyarsa da kuma dalilin dawowar sa sai muji"

Sun jima suna hirar su sannan Mamie tayi
wa Mama sallama ta tafi, dama kamar
office zata wuce ta biyo. Ya cigaba da
kwanciya, duk kuwa da cewa jikinsa ciwo
yake yi saboda dadewar da yayi a kwance
amma kuma baya son ya tashi yayi facing
Mama. Yana nan kwance yaji tace "na san
idonka biyu ai. Ka tashi ka ci abinci ka sha magani"

Ya tashi zaune yana shafa kai, shi Mama
kullum mamaki take bashi akan yadda ba
sa iya boye mata komai daga shi har
yan'"uwan sa, ko tari suka yi ta san
ma'anar sa. Ta bata fuska tace "ta je kayi
wanka kayi brush ka zo ka ci abinci" ya
mike kamar wani karamin yaro yaje yayi
abinda tace ya dawo ya zauna ta zuba
masa abinci ta ajiye masa akan table a
gaban gadon tace "oya eat". Automatically ya fara saka loma a bakin sa, ita kuma ta zauna opposite dinsa ta zuba masa ido, ya rasa inda zai saka
kansa, da kyar abincin yake wucewa. Jira
yake yi ta fara magana amma taki farawar
har sai da ya cinye abincin da ta zuba tas
sannan ta zuba ruwa ta miko masa tare da
magani, ya karba ya sha ya mika mata
kofin ya cigaba da zama kansa a kasa.

Sai kuma tace "tunda har ka iya daukan
kafa ka fita kaje gida ka hada kaya ka
gudu ai tabbas zaka iya zuwa ka duba
matarka da take kwance bata da lafiya
k0? Matarka da tayi miscarriage din
danka, ko ka manta da ita? Na san maybe
ka manta ma kana da aure ko?"

Ya dago kai yace "Mama...." Sai kuma yayi shiru saboda wata harara da ta watsa masa, ya sake sunkuyar da kansa, tace "me zaka gaya min ne ni wai? Har kana tunanin zaka zabi budurwa akai na? Akan
mu?" Ya girgiza kai "ba haka bane ba
Mama. I was just trying to make you
understand. To make you listen to me"
tace "to I am listening ai yanzu. Fada min?
Da ka dauki kayan ina ka tafi? Gidan su
kaje ka ce su baka daki? I quess sun hana
ka dakin ne shi yasa ka dawo ko?".

A hankali yace "gidan su naje, amma ba
cewa nayi su bani daki ba. Cewa nayi ta
zo mu tafi ........" Sai kuma yayi shiru, ya
san maganar ta kara bata ran Mama
amma kuma so yake ya gaya mata
gaskiyar komai, ta jima sannan tace "ta zo
ku tafi ina? Ku shiga duniyar tare?" Yace
"nima ban san inda zamu tafi ba. I just
took her daga gidan su and we drove out
of town. She convinced me to change my
mind. Ita ta sa muka dawo. I took her back
home ni kuma na dawo nan".

Ta danyi shiru sannan tace "in summary,
ta fika hankali kenan" ya dago kai ya kalle
ta sai kuma ya sake mayar da kansa kasa
yace "kiyi hakuri Mama. I am sorry". Ta
mike tsaye tayi hanyar waje tana cewa "ka
tashi muje ka duba matar ka, ka kuma
bata hakurin marinta da kayi, sannan kayi mata jajen barin da tay!" ya mike sannan ya bita a baya. A ransa yana tunanin yadda a cikin laifukan sa bata lissata da
ture Safina da mota ba, hakan yana nufin
bata yarda ya aikata hakan ba, and
wannan realization din ya saka yaji sauki a
cikin zuciyarsa.

Suka fita daga bangaren da yake suka
shiga wanni bangaren daban, sai kuma
suka shiga wani daki. Mama ta tura kofar
da sallama, Mommy suka tarar a zaune
akan kujera tana shan wanj abu a cikin
kofi, Safina kuma tana kwance akan gado
fuskarta tana kallon daya side din.
Mommy da Mama suka gaisa tare da
tambayar jikin marasa lafiyan, sai kuma
Muhammad ya durkusa ya gaishe da
Mommy, ta amsa masa ciki ciki, daga
dukkan alama tana fushin abinda take
tunanin yayi wa yarta ne.

Ya mike tsaye ya tsaya yana kallon Safina
da bashi da tabbas din bacci take ko
idonta biyu, sai yaga Mama ta fita sannan
Mommy ma ta ajiye cup din hannun ta ta
bita a baya, Ya zauna a gefen gadon yana
kokarin ganin fuskar Safina, sai ya danyi
gyaran murya yace "ya jikin?" Ta bude ido
tare da juyowa tana kallon sa, He saw
yadda idanunta suka fada ciki suka yi ja,
sannan kuma side din fuskar ta da ya Mara tayi baki. Daga alama sai marin ya bar mata tabo. Sai yaji babu dadi, ko a mafarki bai taba hango a namiji mai dukan mata ba, ya sake cewa. “ya jikin” ta dauke kai tana kallon gefe tace “as if you care” yace “tunda na tambaya it means I care” tace “mama dai ta saka ka agaba tace kazo kacemin ya jiki. You don’t care ko na mutu ko nayi rai, kawai kana following your mother’s order ne “. Yayi ajiyar zuciya ya mike tsaye yana kallon ta yace you are right, ita tace nazo. But I am truly sorry for that ….’ Yafada yana nuna gurin daya mareta .

Ta shafa gurin tace “ I will aware it like a badge of honor, maybe it will serve as a reminder to me, a reminder of how heartless you are” ya tsaya kawai yana kallon ta, aransa yana jin nadamar tausayinta dayaji farkon shigowar sa dakin. Sai ta cigaba “Nasan kayi farin ciki dakaji labarin cewa burinka ya cika the baby is gone. Amma duk kinsa dakayi bazaka chanja wa tuwo suna ba, naka ne” yadaga kafada yace “well, contrary ce what you said, I felt bad da aka gayamin, amma kuma sai na fahimci Allah yana hikimar data saka hakan yakasace, and then, dama ke kika kulla sanadiyyar samuwar sa, yanzu kuma ke kika yi sanadiyyar rashin sa , and I warned you karkiyi kokarin hadani da iyaye na but you didn't listen, yanzun zaki tabbatar cewa sun san abinda zanyi sun kuma san
abinda ba zan yi ba". Ya juya zai fita sal ta kira sunansa, har yayi niyyar share ta sai kuma ya tsaya,
wata kila a maganganun ta zai samu wani
information din da zai kawo masa saukin
lamura. Tace "jiya Mommy ta gaya min
wai an neme ka ba'a gan ka ba, an aika
gida kuma sai mai gadi yace ka zo ka
dauki mota a fita, tun a jiyan na gaya wa
Mommy cewa gurin Safiyya ka tafi amma
taki yarda, har waya ta kira gida aka
tabbatar mata da Safiyya bata gida amma
bata varda ba. Ni kuma na san can ka je"
ya juyo sosai yana kallon ta yace "idan
can naje din kuma fa? What will happen?"
Tace "nothing. A cikin kwanakin nan,
especially yesterday da ka tafi gurin ta, I
learnt one of the greatest lessons of my
life, that ba zaka taba so na ba, ko ma me
zanyi ba zaka so ni ba. Dan haka ba zan
sake kokarin komai akan hakan ba. Amma
kuma akwai wani abu da na tabbatar
shine sakayyar da Allah zaiyi min akan
zaluncin da kayi min" tayi shiru tana
kallon sa, ya tako ya dawo zuwa gabanta
ya tsaya yace "and what is that?" Sai tayi
murmushi tace "You will never marry Safiyya. Har abada. Sai dai kuyi ta kallon juna a haka, But you will never be husband and wife" sai shima yayi
murmushi yace "and why do you think
hakan ne zai faru?" Tace "because our
parents will never allow it. Ba ka san halin
Daddy ba, ba zai taba aura maka Safiyya
ba as long as lam alive. Babban burinsa
shine hadin kan gidan sa, ba zai taba bari
ka tarwatsa masa gida ba. And your
parents too will never allow you to marry
kanwar matarka, musamman in suma
suka san who she really is and what she did".

Ta tsaya suna kallon juna shida ita, tana
jiran tajj ya hau masifa or worst. Amma sai
taga yayi murmushi. "Tell them please, ki
gaya musu. Watakila a lokacin zaki kuma
daukan wani darasin, Watakila darasin da
zai zama sanadiyyar gyaran rayuwar ki".

Ya juya ya fita.

Bayan ya koma daki bai jima ba doctor din
da yake duba shi yazo yace dama Abba
ya nemi a sallame su da safe kafin ya fita,
a sake dudduba Muhammad sannan ya
rubuta musu sallama, Ya daura shoulder
brace a kafadarsa ta hagu inda ya samu
dislocation, ya kuma yi warning dinsa
against any physical activity da zai saka yayi amfani da yawa da hannun har zuwa nan da two weeks. Suna gamawa Haidar ya zo zai dauke su su tati gida. Mama taje ta gaya wa Mommy sannan bayan ta
dawo ta saka Muhammad da Haidar suka
je tare suka yi musu sallama sannan duka
Zo suka tafi gida,

Sai da suka je gida ya samu yayi excusing
kansa ya shiga daki sannan ya samu
damar kiran Safiyya. "Hey sweetling"
"Hey Baby. I have been wanting to call
you tun dazu ina toro" ta danyi dariya.
Yace "nima. Tun safe ban samu privacy
ba sai yanzu. How have you been, Daddy
yayi wata magana ne?" Tace "lafiya lau.
Just missing you. Ya jikin ka? Hope ba
kaje ka sake balla wani kashin ba" yayi
dariya "won't do it again ai. Except maybe
if I want your attention kuma kin ki bani.
Dan na fahimci ciwon nan has been a
bliss to me, tun da kinyi fushi da ni yanzu
kin sauko" tace "wa yace maka na sauko?
1 just pity you kar ciwon yay maka yawa,
but kana warke wa zan cigaba da fushi
na" yace "naji na kuma amince. Ni dai in
dai za'a bani damar yin rarrashi ko anyi
fushin bani da matsala, I know my ways
around you" tace "really? What are the
ways? Fada min nima in sani" yace "no.....
It is my little secret, Ba zan gaya miki ba,
Yanzu ma na samu wata sabuwar hanyar, duk sanda kika yi fushi da ni sal in fara rashin lafiya kawal so that you will come running 'Wayyo Yaya Muhammad, i am
sorry'™️' ya fada yana kwaikwayon ta, ta
fara dariya sai yayi shiru yana sauraron
dariyar tata da murmushi kwance akan
fuskarsa sannan yace "hey Piya" ta yi
shiru tace "yes" yace "I missed you" tace
"I missed you too Yaya Muhammad".

Sun jima suna hira, sai kuma take gaya
masa in an jima zasu fito ita da Daddy
zasu je asibiti. Bata ambaci sunan Safina
ba amma ya fahimci duba Safinan zasu je
yi, tunda suka shirya basu taba ambatar
sunan Safina ba, they act as if ba ta yi
existing a rayuwar su ba. Ballantana
Mukhtar da har yanzu ba su ma bude babin sa ba. He then asked her yaushe zasu kuma haduwa? Yaushe zasu cigaba da maganar da suka fara. She said anytime ya samu damar fitowa daga gida yayi mata
magana. Akwai wani abu da take son nuna masa,

Daga haka suka yi sallama kamar ba zasu
rabu ba sai dan lokacin sallar la'asar da
yayi. Sannan kuma Daddy yana jiran ta
zasu fita. Bayan ya tashi yayi sallah ne Mama ta jira shi ya sake komawa palo ya ci abinci sal kawai yayi zaman sa a falon yana kallon tv. A lokacin Mufida tazo
dama kullum sai sunje asibiti ita da
mijinta, ta zo ta saka shi a gaba da sannu
har sai da ta fara bashi dariya. Sai ta
zauna tana ta tattaba ciwukan jikin sa wai
zata ga wanne ne yafi yi masa ciwo
wanne ne kuma ya kusa warkewa. Ya ga
alamar kamar fita zasu sake yi ita da Mama.

Sai dai a lokacin da Mama ta fito da
mayafin ta a jiki sai suka ji sallama an
shigo falon, yana daga kai suka hada ido
da Safiyya da Mommy. Sai da ya dan
tsorata amma sai ya maze ya amsa
sallamar kawai ya dauke kai. Zuciyar sa
tana tambaya "me ya kawo su?"

Mama tayi musu sannu da zuwa, Mommy
ta zauna akan kujera Safiyya kuma ta
zauna a kasa a gaban ta, daga ganinta
kasan she is very uncomfortable. Sam ta
kasa hada ido da kowa a cikin falon
musamman Mama da kullum in ta ganta
gani take kamar zata zo ta kwada mata
mari. Sai da suka zauna sannan ta gaishe
da Mama "Mama barka da yamma" mama
ta amsa mata da "sannun ki"., Sai ta koma
ta zauna tana jin kamar ta fashe da kuka,
ta kasa gaishe da Muhammad ma. And to add to that sal Mommy tace "Safiyya ba ku gaisa da Muhammad ba, kin duba shi ma kuwa?" Safiyya ta dago kai tace masa "sannu., ya jikip" Ya danyi gyaran murya,
she looked so sad that it breaks his heart
"jiki da sauki, Thank you"

Sai kuma aka yi shiru ana kallon kallo,
kusan kowa a falon so yake yaji dalilin
wannan zivarar a vanzu, except for
Mommy, dan haka ita ta fara magana,
"Afuwan Hajiya Zainab mun zo muku kai
tsaye, na ga ma kamar fita zaku y" Mama
tace "dama grin ku zamu je mu sake
duba jikin Safina" Mommy tace "haka ne,
kuna kokari kam wajen duba ta. Amma ni
in magana tana damuna a rai na bana iva
yin shiru akan ta sai na yi ta shi ya sa na
kasa hakuri nace da Safiyya tazo ta rako
ni inzo muyi maganar kawai kowa ya huta"
Mama tayi gyaran murya tace "wacce
maganar kenan Hajiya Sa'adatu? Ina fatan
dai lafiya ba jikin Safina bane? Wani abun
likitocin suka ce?" Mommy tace "a'a jikin
Safina da sauki, ai dazu ma kum ganta,
tsagewar kashin ce ma matsalar da tuni
sun sallame ta ita ma" ta danyi shiru
sannan tace "akan Safina din ne dai, akan
kuma jikin na ta. Nace bara inzo inji
wanne mataki kuka dauka ko kuma zaku
dauka akan sa" ta fada tana nuna
Muhammad "naga alamar fa Hajiya Zainab ko fadan kirki ba ku yi masa ba, Ni kuma ba zan iya ja baya inyi shiru ina kallon sa bayan ga abinda yayi wa yarinya
ta ba, Gashi shi har an sallame shi daga
asibiti zai cigaba da rayuwar sa ita kuma
tana can tana fama da tarin injuries da
kuma bakin ciki a zuciyarta, Ko hakuri ma
fa bana jin yaron nan ya bata. Na san kun
dauki nauyin hospital bills da komai har
abinci da ruwan da zamu sha a asibiti
kunyi providing but still she needs justice.
In ba'a yi masa hukunci ba nan gaba
abinda yafi haka zaiyi mata. Watakila
gawar ta za'a kawo min nan gaba".

Mama tace "Hajiya Sa'adatu. Da kin san wannan maganar zamuyi ai da mun sallami yara sai muyi ta mu kadai ko kuma da shi Muhammad din, amma wadannan kannen sane bai kamata ake maganar
matsalar auren sa a gaban su ba" Mama
tace "Safiyya ta san komai ai. Ina sane na
taho da ita zuwa gaban sa dan ta kara
sanin komai, so nake ta san duk irin halin
kuncin da yar uwarta take ciki akan sa.
Dan ta kama kanta ta guje wa aikata irin
kuskuren da yar uwar ta tayi ta san irin
mijin da zata kawo in ta tashi aure".

Mufida ta take zaune a gefen Mama tace
"Mommy Yaya Muhammad is the best mij
da kowacce mace zata samu, Mij ne irin wadda kowacce mace take mafarkin samun irin sa. Dan Allah Mommy kar ki fadi maganar da za'a mayar miki".
Mommy tace "gashi nan al kina mayarwar.
Ni dai ban gani ba, Babu abinda Safina ta samu a gidan auren ta sai bakin ciki da bacin rai. Kun kalle ta
kunga yadda ta koma kuwa? A haka take
sanda aka yi auren?"

Mama ta juya tana kallon Mufida, sai
Mufida ta dauki wayarta ta mike tayi ciki,
Safiyya ma sai ta mike zata yi waje, amma
sai Mommy ta dawo da ita, "dawo ki
zauna. Ina sane na taho da ke ai. Darasi
nake so ki dauka." Safiyya ta koma ta
zauna hawaye ya fara taruwa a idonta.
Muhammad da da yake adan kwance a
jikin kujera sai ya mike ya zauna dai dai,
Mama tayi sauri ta kalle shi "kar kayi. Kar
inji muryar ka" sai ya koma yadda yake ya
zuba wa Safiyya ido.

Sai Mama ta dauko wayarta tayi kira tace
"Haruna driver kana kusa? Eh, dan Allah
dan je gidan Gidado, eh inda matarsa
take, akwai kanwar matar Ramla a gidan,
ka dauka min ita dan Allah yanxu ka kawo
min ita gidan nan, da sauri Please. Na
gode" sai tayi gyaran murya tace "Okay,
Hajiya Sa'adatu. Bara muyi maganar. Tabbas nayi wa Muhammad fada, har yanzu kuma fushi nake yi da shi bamu shirya ba kuma nayi niyyar sai ya gyara
halinsa sannan zamu shirya. Amma fadan
da nayi masa nayi masa shine akan
abinda yayi. Ba wai akan abinda bai yi ba.
Muhammad ya mari matarsa tabbas,
kuma haka din babban laifi ne wanda ban
taba tsammanin zai aikata ba and I am
very much disappointed in him, amma bai
ture ta da mota ba" Mommy tace "Okay
abinda ya gaya miki kenan ko? Abinda ya
gaya miki kenan ke kuma kika goyi bayan
sa. Bayan kuma kinyi min alkawarin
zamuyi bincike zaku gano gaskiyar lamari.
To idan bai ture ta ba ta yaya taji raunukan
da suke jikin ta a yanzu, ta yaya cikin
jikinta ya zube? Ita ta yiwa kanta?".

Mama tace "ba zan ce ita tayi wa kanta ba
amma bashi yayi mata ba. Ni na haifi
Muhammad, kuma na san halinsa ciki da
bai. Na san baya karya. Ban ce wai baya
karya completely ba amma bai iya ba, ta
yadda indai yayi in dai ka san shi sai ka
gane karya yake yi. Na tabbatar kuma
tunda ke kika haifi Safina, I am sure kema
kin san dukkan halayen ta da suke
bayyanannu tunda ni kaina da na dan
zauna da ita a lokacin da Muhammad
baya nan na san wasu daga cikin
halayenta, Safina tana da karya. Na
tabbatar kuma kin sani. She is defensive. Duk wani laifi da tayi ko kuma wan abu da take tunanin cewa laifi ne sai tayi karya dan ta kare kanta. Ko da kuwa abin dan
karami ne as simple as waye ya bar tukunyar miya a bude, ballantana something as big as this".

Mommy tace "okay, to kawai dan tayi wa
Muhammad karya sai ta zubar da cikin
ta?" Mama tace "bani da amsar wannan.
Mu dan dakata kadan yarinyar can Ramla
tazo. Ita ta kira ni a waya sanda abin va
faru, ke ma kuma kince ita kuma ta kira ki.
Dan haka ina saka ran cewa a gabanta
abin ya faru. Sannan kuma yar'uwar Safina, so it's for Safina's advantage, bana jin zata yi mata karya" suka yi shiru gabaki daya, daga dukkan alama jikin Mommy ya fara sanyi.

Suna nan zaune kowa yana magana da
zuciyar sa suna jiran a kawo Ramlah sai
Mommy ta nemi shiga toilet, Mama ta
nuna mata ta tafi, sai kuma ta cigaba da
zama tana kallon Safiyya da Muhammad.
Safiyya tana zaune a kasa, kanta a kasa
tana jujjuya wayar hannun ta, Muhammad
kuma yana zaune akan kujera a kusa da
Mama opposite din Safiyya ya zuba mata
ido. And there is a sadness in his eyes
that disturbed Mama,

Tayi gyaran murya sai yay sauri ya dauke
idonsa daga kan Safiyya, Tace "Safiyya"
sal Safiyya ta dago kai ta kalle ta and
immediately suna hada ido ta mayar da
kanta kasa tace "na'am" sai Mama tace
"akwai wani saurayi da na sani, iyayensa
suka raba shi da wata budurwa da yake
so dan suna tunanin zata cutar da shi, sai
ya hada kayansa ya je ya dauke ta wai
zasu gudu suje suyi aure a wani guri.
Ma'ana ya zabe ta akan iyayen na sa. Me
zaki iya cewa akan wannan saurayin?".

Safiyya tayi shiru, daga alama ta rasa abin
da zata ce, sai kuma daga baya tace
"bamu yi dai dai ba Mama, Kiyi hakuri.
Mun kuma gane kuskuren mu, Ba zamu
sake ba" Mama tace "amma me kike
tunanin ya saka shi yin hakan in the first
place?" Safiyya ta sake yin shiru sannan
tace "yarinta ce". Bayan Mommy ta dawo sai ga Ramla ta shigo da sallamar ta, fuskar ta cike da
mamakin kiran da akayi mata. Ta gaishe
su sannan Mama tace mata "yauwa
Ramlah. Ina ta so ne dama in tambaye ki
yadda akayi Safina taji ciwo. Muhammad dai mun san a mota ya fadi, Safina fa?" Ramia ta gyara zama tace "faduwa tay'" Mommy tace "kamar ya faduwa? A ina ta fadi?" Ramla tace "muna falon ta muna
kallo tare sai muka ji shigowar sa gidan,
sai ta tashi ta tafi bangaren sa, daga baya
kuma sai naji ya fito ya tayar da mota ita
kuma ssi naji tana ta kiran sa da karfi
shine hankali na ya tashi sai na fito da
sauri, sanda na fito sai na ga yana cikin
mota ita kuma tana kokarin yi masa
magana, kamar tana cewa kar ya fita, sai
ta rike karfen bayan motar shi kuma sai ya
ja mota da karfi shine ta fadi a wajen".

Suka yi shiru gabakidaya sai Mama tace
"da ta rike karfen ya juyo ya kalle ta, kin
ga alamar ya san ta rike?" Ramla tace
"gaskiya Mama ban sani ba. Motar akwai
tint kuma glasses din a rufe suke dan
haka ban ga fuskarsa ba" Mama ta sake
tambaya "da ta fadi kuma bai tsaya ba"
Ramla "bai tsaya ba, da gudu ya ja motar
ai. Yana fita kuma naji karar motar a waje
yay accident".

Suka sake yin shiru sai Mama tace
"shikenan Ramlah,. Shiga ciki ga su Aisha
can kawar ki a kitchen, in kuma gida zaki
koma kije sai Haruna ya mayar da ke"
Ramla ta tashi da sauri ta shiga ciki.

Mama ta juya tana kallon Mommy tace
"tsautsayi ne ya faru amma ya hadu da
ganganci. Ta yaya zata yi tunanin zata iya
rike mota? Wannan dai ya wuce Allah ya
basu lafiya baki daya, Allah kuma ya
mayar musu da mafi alkhairin abinda suka
rasa. Maganar mari kuma ya bata hakuri,
kuma insha Allah nayi miki alkawarin
makamancin hakan ma ba zai kuma
faruwa ba, Kiyi hakuri"

Ranar har dare Muhammad yana ta kiran
wayar Safiyya amma bai samu ba. Ya tura
messages ma amma babu response yana
tashi da safe ma ita ya cigaba da kira
amma still shiru, zuwa azahar ya kai
matukar damuwa, sanda suka yi sallar
la'asar ma kuwa daga Abba har Mama
sun fahimci akwai abinda yake damunsa
amma babu wanda yace masa komai sai
ma maganar yaje ya duba Safina Mama
tayi masa. Duk kuwa da cewa ita din taje
da safe ta duba ta. Ya samu ya tafi
bangaren sa kamar zai shirya ne zuwa
asibitin sai ya sake kiran wayar Safiyya,
bata dauka ba ya tura mata message

"Please Safiyya don't do this, in ma nayi
laifi ki hukunta ni da komai amma kar ki
hana min jin muryarki"

Shi gani yake yi maganar sa da Safina da
akayi jiya a gabanta ce ta saka tayi fushi
da shi.

Sai ya sake kira. And she picked. Yayi
ajiyar zuciya "na kusa in zama gawa..
This punishment is to severe for me Piya.
Gwara ki saka ni inyi ta frog jump daga
nan har Kaduna" sai yaji Muryar ta can
kasa tace "I am sorry Baby, na kasa kiran
ka ko amsa wayarka. I was sooo....." Sai
kuma tayi shiru, yaji zuciyarsa tana
bugawa da karfi, kamar kuka take yi, ya
mike zaune daga kwancen da yake
"Piya?.... Are you crying? Me ya faru?" Ta
dan sai ta muryarta tace "I have been
depressed tun jiya. I want to see you, can
you come over please?"

Tun kafin ta gama maganar ma ya mike
"gani nan zuwa, kina gida?" Tace "eh.
And Baby kana ji na? Please drive safely
kaji? Ka taho a hankali. I can't take it in
wani abu ya same ka, I cannot loose you
too"., Yayi kokarin rage damuwar sa "naji.
Zan taho a hankali, Just stop crying, We
will talk about it idan na karaso". Ya cire kayansa tare da adjusting shoulder brace din da take ciki sannan ya saka kananan kaya saboda a waje akwai sauran
rana, Cikin sauri ya shirya ya fita, a
parlour ya tarar da Mama ace mata zai
fita tace a dawo lafiya, ita tunanin ta
asibiti zai je, yana fita ya dau hanyar gidan
su Safiyya zuciyarsa cike da wasiwasin
abinda ya faru da har ya saka ta serious
kuka, dan yasan ita gwanar kukan
shagwaba ce amma wannan bana
shagwabar ba ne ba, Ranar ma bai shiga gidan ba a waje ya tsaya and he called her yace mata yana
waje, ita ma bata ce ya shigo ba sai gata
ta fito bayan yan mintuna, and he saw
Malam Ya'u ranar ma a tsaye yana kallon
su har tazo ta bude gaban motar ta shiga.
Bai bi ta kan Malam Ya'u ba sai ya mayar
da hankali kanta. Fuskarta tayi fari tas
idonta ya kumbura. Yaji damuwar sa ta karu,

"Piya? Lafiya? What happened?" Ta fara
kokarin hana kanta cigaba da kuka tace
"'jikin Daddy ya kara matsawa. Yau da safe
ya kasa numfashi, sai da aka kaishi asibiti.
They intubated him. Sai dazu muka samu
ya fara numfashi, Ya dawo gida yanzu
amma the doctor is with him for a 24 hours monitoring".

Gidado yaji zuciyar shi tana breaking for
her, ya san how much she loves her
daddy. Ya fara bata hakuri "ya Salam, I am
so sorry Safiyya. I am sorry you are going
through all this, Allah ya bashi lafiya,
Insha Allah zai samu lafiya kinji? Ki daina
damuwa. Am sure shima ba zai so ya
ganki cikin damuwa ba" ta goge hawayen
da ya fara fitowa tace "kana gaya min
hakan ne kawai dan ka kwantar min da
hankali. But he is not getting better.
Ciwon sa ba mai warkewa bane ba. Babu
magani. Duk yawan kudin da nake dashi
babu magani ballantana in siya masa. I
have to stand back and watch him die a
little bit at a time" bai gama gane
maganar ta ba amma ya cigaba da
kokarin kwantar mata da hankali. "Babu
ciwon da bashi da magani Safiyya. Allah
dai bai bawa likitoci samun maganin ALS
ba for now amma hakan ba yana nufin
babu maganin ba, and God can work
miracle on him. Addu'a babu abinda bata
magani kinji? We will pray for him. Allah
zai bashi lafiya".

Ta gyada kai kawai sai tayi shiru. Zuwa
jimawa yace "do you think it is okay for
me to go in and see him? Ina so inga jikin
na sa" tayi sauri ta girgiza kai. "jiya da daddare bayan na dawo gida ya kira ni yayi min maganar ka" ta juya tana kallon sa "ya san abinda yake tsakanin mu, Ya
kuma ce min in rabu da kai, Yace ba zai
aura min kai ba. Yace bai yarda inje gurin
wani ya aura min kai ba, Yace kuma in fito
da miji inyi aure in the shortest time possible".

Gidado yaji kamar duniyar sa ta ruguzo a
saman kan sa. Shi da ya dauka Daddy zai
fi musu sauki akan Mama da Abba, ta ina
zasu fara kenan yanzu? And issue din
Daddy is more sensitive saboda rashin lafiyar sa.

Yayi shiru kawai yana kallon ta, yawun
bakin sa gabakidaya ya kafe ballantana ya
samu yayi mata magana. Sai ta kifa kanta
akan dashboard din motar ta cigaba da
kukan ta. Sun jima a haka tana kuka shi
kuma yana kallon ta, sannan kuma a
hankali ya dauko their forever rose da ya
ajiye ranar nan a cikin motar, ya rike ta
hannun sa yana juyawa yana karanta
rubutun jiki sannan ya kamo hannun
Safiyya ya saka mata ita a ciki ya hada da
hannun sa ya rike.

Ta dago fuskarta tana kallon sa, sannan ta
kalli hannayen su and the rose in the
middle, Tana ganin ta ta gane ta. Ta saka daya hannun ta share hawayen ta tace "you kept it" ya kirkiro murmushi duk da zuciyar sa a rikice take but he had to be the strong one yace "of cause I did, I
cannot let go of it. I cannot let go of your
love, I cannot let go of you. Kamar yadda
kika ce, the love between us is a forever
thing. It is stronger than anything da zai
shiga tsakanin mu. We have dealt with
enemies Safiyya, duk da har yanzu ban
san details din battles din da kika yi
fighting for to come back to me ba, amma
na san cewa the worst is over. Na san
cewa wadanda zamu fuskanta yanzu are
the people that love us the most, and
they want the best for us, kawai suna
bukatar su fahimci cewa we are the best
for each other. And that's what we will do.
We will convince them. Ta cikin lumana
dan bama son mu rasa albarkar su. We
will show them how much we love and
care for each other".

Ta danyi shiru tana kallon shi and he saw
yadda damuwar fuskar ta take washewa,
and then a hankali tace "CCTV" ya dan
bata fuska yace "what?" Sai ta girgiza
kanta tace "nothing" amma kuma ya ga
kamar 50% na damuwar ta ta tafi. Sai
tace "there is something I want to show
you. Something I want to tell you. Just drive I will direct you zuwa gurin" ya kunna motar tare da kallon gate din gidan "are you sure? Baba Ya'u zsi gaya wa
Daddy mun sake fita, bana son Daddy
yayi fushi da ke" tace "zai iya gaya masa
amma ba yanzu ba. Yanxu ba zai samu
ganin sa ba. And I want him to tell him" ya
sake kallonta cikin rashin fahimta "why?"
Ta danyi murmushi and in that smile he
saw the stubborn Safiyya da ya jima bai gani ba.

Suna fara tafiya ya ga ta juya ta kalli
bayansu sannan ta dauki wayarta tayi kira
"it is okay. You can go back. No babu
damuwa. Yes I am sure" ta karasa
maganar da authority. Ya sake kallon ta
yace "da wa kike magana" direct tace
masa "my body guards" da mamaki yace
"body what?" Ta danyi murmushi "I will
explain in a bit" sai kuma cikin damuwa
tace "just promise me that koma me na
gaya maka it won't change anything. Dan
Allah" yayi ajiyar zuciya "I just told you
that what I feel for you is a forever thing
didn't I?" Ta dan kwanta a jikin kujerar
tana kallon sa tace "I am just insecure ne
kawai. I have been this insecure tun da
nasan gaskiyar magana a kai na. Gani
nake in na gaya maka gaskiya you will run away from me, Shi yasa tun lokacin na kasa gaya maka" ya danyi murmushi *wacce irl ce gaskiyar magana a akan ki
din? That you are an alien from another
planet, ko kuma ke jinsin aljanu ce ba
mutane ba?" Ta dan yi dariya, yaji dadin
yadda ta fara sakin jikinta amma kuma
yana jin tsoron abinda zata gaya masa
din, yace "I missed the way you smile and
laugh" ta sake yin murmushi tare da rufe
side din fuskar ta da hannu daya, yace "I
like your finger and your nails" sai ta ja
mayafin ta ta rufe fuskarta gaba daya ta
kuma boye hannayenta a cikin mayafin.

Yace "to in baki bude fuskarki ba ta yaya
zaki nuna min hanyar da zamu bi?" Tace
"ina gani ai a haka" yace "I like the sound
of your voice too" ta fara buga kafar ta a
kasa cikin shagwaba "ni ka bari, Allah"
yayi dariya, trying to loosen the
atmosphere more. A haka ta ringa nuna
masa hanya har suka shiga wata unguwa
sai kuma suka je gaban wani babban gida
suka yi tsaya, gurin yayi kama da gidan
gona saboda bishiyoyi da ya hango a ciki,
and it also looked newly renovated dan
tun daga waje yana jin kamshin pent and
even the outside walls are newly painted.
A saman gate din anyi rubutu da karafunan da akayi wa ado da fitulu an rubuta "The Oasis".

Suka tsaya kawai basu ce komai ba, sai ta
mika hannu ta danna horn din motar, wani
mutum ya bude karamar kofa ya leko yana
kallon motar, sai kuma ya fito ya rufe kofar
ya taho inda suke, ta sauke window din
side dinta sannan ta daga wa mutumin
hannu, ya kalle ta sai ya koma ciki har da
gudun sa sannan ya bude gate din ta ciki.
A hankali Muhammad ya ja motar suka
shiga ciki, yayi packing yana kare wa
gurin kallo "wow, this looks amazing" tayi
murmushi tace "thank you, let me show
you around". Sai ta bude kofa ta fita shima haka. Shi
duk a lokacin tunanin sa gurin Daddy ne,
amma tana fitowa sai yaga ma'aikatan
gurin sun taho suna ta gaishe ta sannan
su gaishe shi, still ya cigaba da tunanin a
matsayin ta na yar oga ne, sai kuma yaji
wani da yaxo ya gaishe ta yana yi mata
maganar abubuwan da za'a siya da kuma
abubuwan da suka rage da za'a yi, kamar
yana bata update, sai tayi kokarin dakatar
da shi tare da ce masa zasu yi maganar later.

Daga nan suka fara tafiya a cikin gurin shi
da ita side by side, iskar gurin mai dad
tana kada su, tsuntsaye suna yin wakokin su a saman bishiyoyin gurin. Suna tafiya tana yi masa bayanin ko ina da kuma abinda za'a yi a gurin, ya fahimci duk an
gama gyaran sai abinda ba'a rasa ba, sai
kuma dabbobin ne suka rage ba'a kawo ba,

Suna tafiya suka zo wajen wata bukka, irin
traditional bukka akayi but in a modern
way aka saka flowers suka zagaye ta
sannan aka saka kujeru a ciki, suka shiga
suka zauna sai tayi shiru, kamar duk
hankalin ta a tashe yake, yana kallon ta
yace "uhum, ina jin ki. Kince zaki nuna
min wani abu kuma zaki gaya min wani abu, what is it?" Ta nuna gurin da hannunta tace "this is it. This farm is what I wanted to show you" sai kuma tayi shiru, yace "it is good, gurin yayi kyau sosai and the business will be lucrative" ta sake yin shiru sai yace
"menene kuma zaki gaya min?" Tace
"abinda zan gaya maka shine it belongs
to me. It is mine" ya bude ido cikin
mamaki "WOw. Daddy ne ya baki" ta
girgiza kai "not Daddy, but Ammie"
"Ammie?" Ya fada cikin mamaki, ta gyada
kai "yes, her. And wannan bashi kadai
bane ba. It is not even among the most
important. She….... She had ...." Sai kuma tayi shiru ta cigaba da jujjuya wayar hannun ta

Ya jawo kujerar da yake kai closer to her
yana leka fuskar ta yace "hey, it is me.
Muhammad. You can tell me anything.
What are you afraid of?" Ta dago kai tana
kallon sa tace "am afraid you will leave
me in ka sanj" ya girgiza mata kai "never.
Kina jina? I will leave you no matter what"
ta gyada kai sannan ta gyara zama. "A ina
na tsaya maka a labarin da nake baka?"
Yace "Ammie ta shigo Abuja ta sauka
gidan Hajiya Maryama, Ita kuma ta dauketa a matsayin yarta" tace "okay, yanzu zamu cigaba...…”

And then she told him labarin Safiya
Haladu, irin fadi tashin da tayi da
shekarun da ta dauka tana businesses
daban daban har zuwa sanda ta koma
Safiya Khalid and haduwar ta da Adam
Muhammad da kuma risk din da ta dauka
with the gold company and how it turned
out. Zuwa shekarun da suka yi suna kafa
business na hadin gwiwa da daukarkar da
Allah yayi musu a cikin shekarun, problem
din haihuwa da suka samu, her problem
with her half siblings, haihuwar ta and her
decision to gift her everything.

Maman Maama✍🏻
[07/01, 10:46 pm] +234 906 816 1960: ❤️‍🩹Safiyya❤️‍🩹

Episode Fifty Four: The Legacy 2


Not Edited….


Her🧕🏻

Two days ago...
"good night, and don't forget to dream
about me".

And I did dreamt of him. Muna ta hira
muna dariya. And it was the best dream
da na yi a cikin shekaru,

Washegari ban tashi da wuri ba sal around 12 na safe, Ina tashi da Muhammad na tashi a raina. Zuciya ta cike da tunanin sa, fuska ta dauke da murmushi. Da sauri sauri na shirya na sauka kasa dan inje in ga Daddy, duk da dai na san shima yanzu ba ya tashi da wuri. Ban ma tsaya yin breakfast ba, duk kuwa da Esther da take ta bina a baya tana gaya min ta shirya min favorite dina, Nayi mata godiya kawai na shige part din daddy, A raina ina tubanin ko ya huce? Ko yau zaiyi min maganar Muhammad? Ko kuma dai ni infara yimasa maganar?

Ina shiga na ganshi tare da nurse din da yake zama dashi, sunayin maganganu a hankali amma suna gani na sai suka daina, kamar wata magana sukeyi da basa so inji, muka gaisa da nurse din na tambaye shi jikin daddy yace min da sauki, sai ya fita nikuma nazauna a gaban daddy tare da dafa guiwoyinsa ina kallon fuskarsa da murmushi a tawa fuskar, “good morning Daddy na” na fahimci yana kokarin cigaba da yin fushi
da nine amma kuma ya kasa, ya dauke
Kansa gefe yana Kallon tv yace "how are
you?" Na dawo da fuskata inda tvn take
nace "I am good, Ya jikinka ka?* yayi shiru
bai ce komal ba sai ma ya fara kokarin daukan wayarsa da take gefensa. Na dauko masa wayar na bashi, sannan na tashi na dauko wani support machine da ake daura masa tun daga kafadar sa zuwa fingers dinshi wanda yake taimaka masa yayi amfani da hannun sa sosai, Na saka ma, still bai kuka ni ba sai yafara daddana wayarsa daga baya sai naga ya sakata a kunne yafara magana, najima a zaune a gurin ina jinsa yana ta waya da abokan sa, daga sun gama da wannan su koma yi da yi da wancan har dai nahakura ba tashi na fita

Bayan nayi breakfast sai na sake komawa
gurin Daddy, na tarar da shi tare da twins
suna ta hira suna dariya, sai kawai na
tsaya ina kallon su ina jin dadi a raina,
Hassan yana ta zuba musu zance, ina
shiga nima suka jani cikin hirar ta su, na
karasa na zauna a gaban Daddy na dauki
kafarsa daya daga kan karfen kujerarsa na
dora akan cinyata ina shashshafa masa ita
tare da jan yatsun kafar, sai muka fara
maganar karatun twins, su wai sunfi son
su dawo nan Abuja suyi karatun. Hassan
yace "wallahi yaya bama jin dadin kanon
yanzu tunda ba kwa nan, tunda kun ki
komawa gwara mu dawo nan din muma.
Gidan empty babu kowa" Daddy yace "in
kun dawo nan aikin ku kuma fa waye zai yi
muku?" Hussain yace "ni nayi retire" duk
sai da muka yi dariya, nace "ya kuka fara
karaya ne tun yanzu? Kamar ba maza ba?
Ni plan dina shine a sama muku jami'a a
kasar waje, sai ku ajiye akin ku tafi in kun
dawo sai ku cigaba" Hassan ya fara
murna "ni America zaki kaini yaya. Kuma
kar ki hada ni makaranta daya da Hussain
kar yaje yake ta min wa'azi a can".

Daddy ya bude ido "au baka son wa'azi
babana? To kayi wa kanka, a Kano zaka yi
karatun" Hussein yace "yauwa Daddy, ka gano shi. Ni kam a kaini makarantar King Fahad a Saudiyya" Hassan yace "Allahu Akbar! Ya Sheikh ustaz Malam Ahmadu" Har Daddy sai da yayi dariya. Muka yi ta
hira mai dadi kamar bamu da problem, sai
daga baya yace min inje in shirya in an
jima zamu fita ni da shi da twins muje mu
duba Safina. Duk da dama su twins sunje
da safe kafin in tashi daga bacci. Ban
musa ba nace masa to.

Daga nan na tashi na koma dakina, a
lokacin ne naga kiran Muhammad, muka
zauna muka yi hirar mu mai dadi na gaya
masa zan fita zuwa asibiti. Daga nan na
shirya da sauri dan kar in sake yin wani
laifin a wajen Daddy, nayi sallar la 'asar
sannan na fita.

Hassan ne ya tuka mu a motar Daddy
wadda take ajiye baya hawa, dama twins
ne suke hawan ta yanzu idan sun zo gari,
Hussain yana gefensa ni da Daddy muna
baya, muna tafiya muna hira, and Daddy
used the opportunity to talk to us about
hadin kai da kuma son juna. "Be each
other's keepers" he said.

"ku kar kuga ita macece ku raina ta, ku yi
mata biyayya kamar ni kuke bi, duk
abinda zakuyi ku nemi shawarar ta. She is strong and she will take care of you, bani da shakka akan wannan. Ke kuma kar kiga su kanana ne ki raina su, ki saka su a cikin dukkan al'amuran ki, kiyi shawara da su a
kan dukkan abinda ya shafe ki. In kinyi
haka you will be enough for each other".
Na kama hannun shi a rike da hannayena
biyu ina jin wani nauyi a kirjina. He looked
at me and smiled.

Muna zuwa asibitin suka dauko kujerar
Daddy a bayan motar suka dora shi akai
sannan suka tura muka shiga ciki. Muna
shiga dakin da Safina take muka tarar da
wasu kawayen ta sunzo dubata, da suka
gan mu sai suka yi mata sallama suka tafi.
Na samu guri akan kujerar two sitters da
take gefe a akin na zauna bayan na
gaishe da Mommy, ina zama Mustapha ya
shigo, ya je ya gaishe da Daddy sannan
ya dawo ya zauna a kusa da ni, nayi
kamar ban ganshi ba na dauko waya ta na
fara daddanna wa.

Daddy yaje har gaban gadon Safina ya
duba ta, ta tashi zaune ta gaishe shi. Ya
duba hannun ta da kafarta da taji ciwo
sannan Mommy ta zo tana nuna masa
fuskarta "ka ga marin da yayi mata? Ka ga
irin cin mutuncin da yayi mata? Ko mu
bamu taba dukan ta ba amma wani kato a can ya kusa ya kal ta lahira, Wannan yaron ba mutumin kirki bane ba Daddyn Mustapha. Wallahi ba mutumin kirki ba ne
ba. Na tabbatar da kai ka bada auren
Safina ba zaka ba shi ita ba. Na tabbatar
da kai ne zaka yi bincike kuma zaka san
halin sa. Ita dai Safina iyayen ta sun cuce
ta, ita ma kuma ta cuci kanta tunda ita ta
kai kanta gurin su. Amma yanzu ba zamu
kuma irin wancan kuskuren ba".

Duk mukayi shiru babu wanda yace
komai. Safina ta fara kuka kasa kasa,
Daddy ya dora hannunsa akan kafadar ta
a hankali cikin muryar sa ta rashin lafiya
ya fara rarrashin ta. "kiyi hakuri Safina
kinji? Kaddarar ki ce haka. Amma za'a
dauki mataki akan abinda ya far, zamu
tabbatar haka ba ta sake faruwa da ke ba
ko kuma da wani daga cikin yayan mu ba."
Mustapha yace "wallahi dan Mommy ta
hana nine amma da yaron nan dazu ba
zai bar asibitin nan ba dan sai na karya
masa hannu ko kafa" Daddy ya juyo yana
kallonsa yace "ban amince ba. Kar ka
taba shi. In ka taba shi kai ma ka zama irin
sa kenan" Mommy tace "ai na gaya masa
kar ya taba shi, matakin shari' a zamu
dauka akan sa. Da dai iyayen sunce min
zasu dauki mataki shi yasa nayi shiru na
saka musu ido, amma yanzu naga basu
da niyyar daukan wani mataki a kai dan haka mu zamu dauka" Daddy ya girgiza kai "'a ba za'a yi karar sa ba. Akwal martabar aure al a tsakanin su. A fara
kokarin sasanta maganar a gida tukunna,
sai in anga abin ya gagara tukunna sai a
shigar da sharia ciki. Tunda duka da
kuma ture wa da mota ai domestic
violence ne".

Ina jin su ni dai ban ce komai ba, A lokacin
kuma na kara zargin daga Daddy har
Mommy sun san tsakani na da
Muhammad kuma suna fada min magana
ne a fakaice. Suka cigaba da maganganun
su Safina kuma ta cigaba da kukan ta sai
kuma kawai naga Mommy ta mike, tace
"ni in abu yana cina bana iya zama
wallahi, Safiyya zo ki raka ni gidan su
yaron nan, Mustapha zo ka kai mu. Gwara
inje inji inda binciken nasu ya tsaya dan in
san abunyi a akan maganar nan".

Na dago kai da sauri ina kallon ta sai
kuma na girgiza kai and ban san sanda
nace "no Mommy, I don't want to go
there" wani kallo da Daddy yayi min shi ya
sa na mike na fita ba tare da na sake yiwa
kowa magana ba amma ji nake kamar in
ruga da gudu in samu mota in koma gida,
like why? Me yasa zata je dani gidan du
Muhammad akan rigimar sa da Safina? Al
wannan maganar manya ce and I am not manyan Satina duk kuwa da cewa ni nayi mata kayan daki.

Ina jin su suka fito ita da Mustapha suna
maganganun su, yana bude motar nayi
sauri na shige baya na zauna. Suka shiga
gaba tana cigaba da mita tare da fadar
maganganu akan Muhammad, sai na saka
hannayena biyu na toshe kunnuwana na
jingina kaina a jikin kofa. A haka muka je
gidan raina a matukar bace, ni ban taba
zuwa gidan su Muhammad ba sai ranar. Muna yin packing ta juyo tace min fito muje, na sake girgiza kai na kamar zanyi kuka "Mommy I rather stay in the car"
tace "da a motar zan barki ki zauna ai da
ba zan taho da ke ba. Ina sane na taho da
ke din ai'". A dole na fito daga motar ina ji
ina gani ta tusa keya ta zuwa cikin gidan,
my mind was telling me to call one of my
guards da na tabbatar suna waje ya zo ya
kwace ni daga hannun Mommy ya mayar da ni gida.

Muka shiga ciki, and I saw Muhammad da
wata da na fahimci Mufida ce, sai kuma
ga Mama ita ma ta shigo. Haka naje na
zauna and I was literally forced to listen to
maganganun su akan rigimar Safina da
Muhammad har daga baya aka kira shaida ta kuma tabbatar da cewa Safina ce mai
laifi concerning zubewar cikin da kuma
raunukan da ta samu not Muhammad.
Amma dai tabbas Muhammad ya mare ta.
But that doesn't made me feel better dan
kirikiri nake ganin kiyayya ta a idon Mama.

Haka Mommy ta gama borin kunyar ta ta
tashi muka fito, da zamu fito ta saka aka
kira mata Ramla tace tazo mu tafi tare.
Muka sake komawa mota muka juya zuwa
asibiti. Mustapha yana ta tambayar yadda
aka kare, Mommy ta fara "sun goyi bayan
dan su. Wai ba da sanin sa bane ba. Har
da kuma cewa wai marin da vavi mata ma ai ya bata hakuri. Kuma ta gaya min bai bata hakuri ba sai ma maganar banza da ya ke gaya mata".

Na nemo ear piece na toshe kunnuwana
har muka je asibitin, zuwa lokacin ana ta
kiraye kirayen sallar magrib, muna zuwa
muka tarar Daddy yana jiran mu na dauka
juya wa kawai zamuyi mu tafi but he said
"Safiyya kiyi wa Safina sallama" na ji
kamar zan fashe da kuka, na je gaban
gadon nace "zamu wuce. Allah ya kara
miki lafiya" tace "Amen. Thank you" sai
na wuce na fita da sauri ina jin alamar duk
yan dakin ni suke kallo.

ina zuwa mota sal gain Mommy nayi ta
biyo mu, wai gida zata je ta kwana shi
yasa ta taho da Ramiah ta kwana a wajen
Safina. Ni dal har muka je gida ban sake
magana ba, Muna zuwa na wuce dakina
da sauri na kuma rufe kofa ta sannan na
shiga toilet nayi alwala na fito nayi sallah,
na rufe kofar ne saboda na san Mommy
zata iya cewa zata shigo ta sake yi min
irin maganar ranar nan ni kuma raina a
matukar bace yake ina tsoron kar in gaya
mata bakar magana.

Ina jin ta tana taba handle din kofar amma
nayi kamar bana kusa na cigaba da zama
na akan sallaya. Ni na san har lokacin my
mental health is not okay, in dai har zata
zauna tana zagin Muhammad a gaba na
anything can happen. Na tuna sanda
Mukhtar ya zage shi a mota na bude kofa
zan fita. Ina nan zaune har akayi sallar
isha na tashi nayi sannan aka sake
knocking kofa ta sai kuma naji muryar
Esther. "Madam Daddy yana kira".

Na ajiye charbin hannuna sannan na tashi
na bude kofar na fita, na wuce Esther na
sauka kasa. A dinning room na same su
gabaki daya suna cin abinci, ina shiga
Mommy tace "ina sane nace da Esther tace miki Daddy ne yake kira ai, gashi nan kin sauko, Tun dazu nake hawa ina miki magana amma o amsa baki bani ba" nace mata "ina sallah ne" sal kuma na
juya gurin Daddy nace "Daddy ganj" ya
nuna min kujera "ki zauna ki ci abinci tare
da yan'uwan kj" na girgiza kai nace "na
koshi" yace "ki zauna ki ci abinci nace"
sai na ja kujera na zauna na zuba abinci a
plate na fara ci kamar yadda ya umarce ni.

Mustapha yana kallo na yace "wai ke me
yake damun ki ne?" Mommy tace "fushi
take yi, dan dazu na matsa mata ta shiga
gidan surukan Safina" Hussein vace
"Mommy to me yasa za'a matsa mata?
Tun da ta nuna bata so ai da sai abarta
ko" ta zabga masa harara tace "to uban
iyawa, ka fi mu santa ne ko kuma ka fi mu
sanin abinda yake dai dai. It was for her own good" Hassan yace "we just don't like seeing her sad. She have been through a lot. She should be happy" sai naji abincin da nake ci ya tokare a makogwarona, Hassan is right, I should be happy. But I am not. Ban kuma san ranar da zanyi farin cikin ba.

Haka na cuccusa abincin, ina jin shi
gabakidaya yana tsayawa a kirjina baya
wuce wa ciki na, sal da na ga kamar zanyi
wa kaina illa sannan a daina nci na
cigaba da zama akan kujera ina kallon su
har suka gama, Ina jin twins suna bawa
Mommy labarin nace zan kai su kasar
waje karatu, a take naji tana yiwa
Mustapha maganar ya zauna da su ya
taya su zabar makarantar da ta dace da
fannin da kowa a cikin su yake son
karanta. Daddy ne ya fara cewa zai shiga
ciki ya kwanta, Mustapha ya tashi ya
taimaka masa ya shiga dashi cikin part
dinsa, ina ganin sun wuce na mike da
sauri na fita nima na hau sama zuwa
dakina. A hanya na hadu da Esther, sai na
ga ta bini a baya amma bata ce min komai
ba har na shiga dakina sai ta shigo ita ma
sannan ta rufe kofa tana kallo na.

Na tsaya ina kallon ta da alamar tambaya
sai ta fara magana cikin inda inda "uhmm
Madam, dama wani abu nake so in gaya
miki" na zauna ina kallon ta with serious
face nace "what? Wani abu ya faru ne?"
Tace "I am not sure, but I just want you to
be careful" na ji gaba na ya fadi, nace
"careful about what?" Sai ta shigo ciki
sosai ta zauna akan gado tana kallona
tace "da akwai wani ex boyfriend dina, to
yana ta so mu shirya ni kuma naki yarda"
na cigaba da sauraron ta duk kuwa da cewa bani da interest in her relationship
with her ex boyfriend, Ta cigabe "sal
dazu, na ganshi a gidan nan bayan na
dawo daga aiken da Daddy yay min,
lokacin ba kwa nan kuna asibit!, I asked
him me yake yi anan farko sal ya ki fada
min yace it is confidential, Sal na cigaba
da insisting sal naji. And in his attempt to
get back to me sal ya gaya min" na gyara
zama nace "ya gaya miki me?" Tace
"dama yana aikin saka CCTV ne. To wal
Daddy ne ya saka shi ya saka a ko'ina a
gidan nan. Kamar Daddy yana zargin
something us happening amma ba'a gaya
masa, yana son sanin komal da yake
faruwa a cikin gidan nan. Shine dazu ya
fita da ku gabakidaya ni kuma ya aike ni
dan ya bawa mai aikin damar yin aikin ba
tare da kowa ya sani ba. He told me ya
saka small cameras da ba za'a gani easily
ba a koina a gidan nan except for bedrooms and toilets. Sannan yayl connecting komai zuwa wayar Daddy, duk abinda za'ayi yanzu a gidan nan Daddy
zai gani kuma zai ji".

Nayi shiru ban ce komai ba sai ta sake
cewa "na gaya miki ne so that you should
be careful in da akwai wani abu da ba kya
so Daddy ya gani ko ya ji. Ni ma yanzu
dole in rage saka kida a kitchen in ina
aik™️" ta karasa tana dariya, Nayi mata
murmushi "Okay Esther, Nagode sosal for this. I won't forget your kindness" tayi murmushi ita ma tace "you deserve it" har ta kai bakin kofa sai ta juyo tace "bazan gaya wa kowa ba bayan ke. And I wish
Daddy zai kama duk me laifi a gidan nan".

Bayan ta fita na jima a zaune ina juya
maganar a raina sai kuma na tashi a kalli
agogo sannan na fita na sauka kasa da
sauri na tafi bangaren Daddy. Na tarar har
an gama yi masa shirin kwanciya yana
zaune akan gado da dan karamin
Alqur'ani a hannun sa yana karantawa, sai
na zauna a bakin gadon ina kallon sa har
ya gama ya shafa, Da dauki Alqur'anin na ajiye a inda ake ajiyewa sannan na dawo na zauna

Yana kaliona yace "Safiyya, akwai
maganar da kike son gaya min ne?" Na
sunkuyar da kaina sannan ace "Daddy
fushi kake yi da ni ko?" Yace "akwai
abinda kika yi wanda zai saka inyi fushi da
ke?" nace "I am sorry Daddy, jiya nayi
maka karya, nace zan je asibiti kuma ban
je ba" ya daga hannun sa a hankali ya
dago fuskata yace "tunda kin yarda baki
je asibitin ba, ina kika je?" Na sunkuyar da
ido na kasa ina wasa da hannu na, ya kira
sunana "Safiyya" na dago kai muka hada
ido sai na sake mayar da kaina kasa, yace * understand life has been hard, and
cruel to you, I understand I haven't been
as good a father as I planned to be for
you, But you must put the past behind
you and face your future. Na san cewa
yanzu is too early in fara yi miki maganar
aure, but I do not have time Safiyya. And I
so much want to see you married and
happy before I go, Ina so ki samu mutumin kirki mai hankali
wanda zai soki kuma ya rike ki tsakani da
Allah, wanda zai zame miki gata bayan
babu ni ki aura, dan Allah Safiyya" nayi
sauri na dago kai tare da rike hannunsa
"Daddy don't beg me, abinda duk kake so
shi zanyi, If you want me to get married I
will get married, Ni dai so nake ka daina
fushi da ni dan Allah, Na kwanta na kasa
bacci. Ina cikin damuwa Daddy" na fada
murya ta tana karyewa, yace "menene
damuwar ki? Dan ina yin fushi da ke ko
kuma akwai wata damuwar da ban?" Nayi
ta kokarin fitar da maganar amma na
kasa, sai daga baya sannan a hankali nace
"Muhammad" yayi shiru yana kaliona
sannan yace "wanne Muhammad din?"
Sai naji na kasa kiran sa da sunan mijin
Safina kamar yadda suke kiran sa da shi,
Sal na gyara maganar "wanda muka je
gidan su dazu" yayi ajjiyar zuciya, "mijin Safina?" ya fadi sunan da bana so din.

Nayi shiru ban amsa wannan ba, sai ya
sake tambaya "what about him? Me kike
so ki gaya min akan sa?" Nace "uhmm,
dama ..... Jiya da banje asibitin ba, muna
tare da shi" yace "I know. Malam Ya'u ya
gaya min. Abinda nake so inji shine
menene a tsakanin ku da har zai bar
asibiti a halin rashin lafiya, ya tsallake
matar sa da iyayensa ya taho wajen ki?"
Na cigaba da kallon yatsun hannu na
sannan nace "Daddy, Muhammad
shine ....... Shinake........Wannan
maganar........." "Shi kike so zaki aura" yayi
summarizing duk maganganun da nayi
niyyar yi masa. Nayi shiru bance komai ba
ina jin yadda zuciya ta take bugawa a
kirjina. "Haka ne?" Ya tambaya, na gyada
kai na ba tare da na kalle shi ba.

Ya jima shiru yana kallona sannan yace
"out of the billions of maza da suke
duniyar nan Safiyya babu wanda yayi miki
sai mijin da Safina take aure?" Naji
hawaye ya fara taruwa a idona. "ba
haramun bane ba tunda ku ba sisters
bane ba, zai iya auren ku ya hada ku ku
biyo Safiyya but common........ You are
smarter than this Safiyya you are above
this. Ta yaya ma hakan zata yiyu? Ta yaya
ma kike tunanin zan aikata hakan?"

Na dago kai ina kallon shi hawayen ido na
yana karasa gangarowa kan kuncina,
"Daddy shi nake so. I don't know anything
else, I don't know yadda za'a yi ko kuma
me hakan xai jawo I just know that I love
him" ya dakatar da ni yace "and that is
where you are wrong. Very wrong, Love is
just not enough. Just because you love
him and you think he loves you saboda
yana dukan matarsa da wulakanta ta
saboda ke doesn't make him the right
choice. He is all shades of wrong for you.
And ni ba zan aura miki shi ba".

Na fara girgiza kaina hawaye na suna
karuwa, "Daddy...." Ya daga min hannu,
"dalilai uku ne ya saka ba zan aura miki
shi ba kuma ban amince ko da ace gobe
na tashi babu rai ki aure shi ba. Na farko
saboda yana auren Safina, Safina tamkar
yaya take a gare ki mahaifiyar ta ita take
amsa sunan uwa a gare ki, Tun daga kan
Sa'adatu har kan Hussain babu wanda zai
amince da wanna shirmen da kike
shiryawa and if you insist you will loose
them just like you lost Ahmad, Dalili na
biyu shine Muhammad ba mijin kirki bane
ba, bana miki fatan ki auri miji mai irin
halin sa, ance idan zaka aura wa yarka mill
mai mata ka bincika kaga yadda yake treating matar sa ta gida saboda exact treatment zai yiwa second matar, Watarana kuma hannu zai daga ya mare ki
" you provoked him, Dalili na blyu shine iyayensa, if you insist on marrying him har iyaye suka shige maganar they will dig and they may find out, abinda muka yi
sacrificing a lot to bury, Gidan su kuma babban gida ne, How do you think they will treat you? How do you think, they will look at you?",

Na rufe fuska ta da hannayena ina cigaba
da kuka kasa kasa, Ya kamo hannun ya
rike, naji yadda nasa hannun suka yi zafi
yace "Safiyya, in daí na isa da ke ki
hakura da yaron nan. Kiyi addu'a, nima
zan yi miki addua, Allah ya baki wanda ya
fishi, Sa'adatu is still insisting on Mustapha but I told her like I did before that ba zan matsa miki ba, But you should think about that too", Na karbe hannuna
ina girgiza kai na tare da jin duk duniyar
tayi min kunci, ji nake kamar numfashi na
zai bar jiki na, Na zame zuwa kasan gadon na zauna sai kuma na mike nayi hanyar waje da sauri,
ina jin shi yana kira na da muryarsa da
take fita da kyar amma ban juya ba, ina zuwa dakina na tarar da missed calls din Muhammad a waya ta. Sai na zauna na rungume wayar a kirjina ina ta rusar kuka, gani nake yi babu abinda yayi min saura kuma a duniya. Babu wani sauran farinciki daya ragemin a duniya. Muhammad shine farin ciki na. Shi nake so

Ranar kwana nayi ina aikin kuka. Kaina ya
toshe na kasa yin tunanin komai
ballantana in hango wa kaina hanyar da
zata bulle da ni. Da assuba bayan nayi
sallah ina zaune akan sallaya ta naji ana
buga min kofa da karfi, sai da ma dan
firgita sannan naji muryar Mommy tana
kire na cikin tashin hankali, ban jira komai
ba dan Daddy ne ya fara fado min a rai, na
mike a razane na bude kofar, kallo daya
nayi mata na san babu lafiya dan haka na
wuce ta a guje ina harhada stairs na
sauka kasa a dal dai lokacin da naga
Mustapha yana turo shi akan kujerar sa
zuwa waje, na karasa gurinsu a guje
*Daddy!'" Na kira sunan sa da karfi ina
jüliga shi amma baya motsi, a lokacin
twins suka fito suma suna kokarin yin karo
da juna, ina jin Mommy tana janye ni daga
jikin sa amma kuka nake ina kiran sunan
se "Daddy 1 am sorry" na fada a lokacin
da ake saka shi a mota,

Gabaki dayan mu haka muka dunguma zuwa asibitin, sai da muka ji sannan suka gaya mana cewa da sauran ransa numfashin sa yayi kasa yayi kasa sosai har yayi loosing consciousness, sai suka fara kokarin daidaita masa numfashin amma abin ya gagara, kamar hanyar da iska take bi zuwa lungs dinsa ne tazama weak takasa shigar da iskar, saida suka sake masa tube directly zuwa lungs dinsa sannan sukayi pumping oxygen ciki, a hakan ne numfashin nasa ya dawo, but they also kept him under sedative dan a samu numfashin ya dai daita kafin asan abinyi next

Ranar naga tashin hankali, Dan ba zanma iya cewa ga a inda hankali na yake ba, bazan ma iya cewa ga abunda ake cewa ko akeyi ba nidai ina zaune a kusa dashi hannuna rike da nashi a gaba na akayi komai, sai bayan da aka gama ne sai ga uncle Ahmad ya shigo hankalin sa a matukar tashe, wannan shine gani na dashi tun ranar daya ajiye min takardar barni aiki. Na daki hannun Daddy na tashi na rungume shi, shima ya rungume ni hankalinsa yana kan Daddy sannan kuma ya sakeni ya karasa gaban sa yana shafa gashin Kansa, sai kuma ya tashi ya fice idanun sa cike da hawaye, sai wajen azahar Daddy ya fara farfadowa suka cire masa tube din sannan suka cigaba da
monitoring breathing dinsa har sai da
suka ga ya dawo dal dal sai abinda ba
za'a rasa ba, Yayi kokarin yin magana
amma ya kasa, doctors din suka sake
saka shi ya koma bacci dan ya daina
stressing kansa akan sai yay magana ko
wani motsi. Daga haka doctor din mu yace a bamu shi
mu tafi gida shi zai zauna da shi a gidan,
dama kuma akwai nurses guda biyu da na
dauka suke zama dashi tare da taimaka
masa yin abubuwa, Mustapha ma kuma
yana iyakacin kokarin sa. Sai bayan da
muka taho a hanya sannan na fahimci
menene ya faru, the nurse that was supposed to stay with him that night shine Mommy tace ya tafi zata zauna da Daddy, wai ita kuma sai bacci ya dauke ta
a dakin ta sai da assuba sannan ta tashi,
shi kuma ana tunanin tun cikin dare ya
samu breathing issue din amma babu
wanda yake kusa da zai taimaka masa a
haka har yay loosing consciousness, sai
da asuba Mommy ta shiga ta ganshi a haka,

Sai naji na tsane su gaba ki daya, na tsani
kaina nima. Ya za'a yi a bar shi shi kadai? How terrible must have felt sanda ya tashi yana neman taimako kuma babu wanda zai bashi?

A gidan ma bacci aka barshi yayi, aka hana kowa shiga gurin sa sai doctor ma’aruf wanda yayi mana alkawarin yana tashi Indai ya fahimci babu matsala zai sanar damu muzo mu ganshi, sai alokacin na koma dakina, Esther tana ta bina tana rokona naci abinci tunda tasan ko breakfast banyi ba, nace takawo min daki sannan nashiga toilet nayi alwala nafito nayi sallar la’asar, na cigaba da kuka na agaban ubangiji, a lokacin ne naji karar waya ta, ni namanta ma ina da waya, nadauko ta a kusa dani

pillow na tun inda na aliye ta jiya da
deddare kafin iny/i bacci, anan na tarar da
jerin missed calls din Muhammad da
kuma messages din sa, na fatimei yay
tunanin nayi fushi da shi ne akan zuwan
de mukayi gidan su liya, Sal na Kira sti,
aji dadin jin muryarsa amma kuma at the
me time muryar ta sa ta tuna min da
magangianun mu Daddy wya da dare, sai
na nomi yazo in ganshi, yazo muyi magana.

Babu jimawa yazo, ni kuma nayi amfani da lokacin jiran nasa wajen cin abinci da Esther sannan nayi wanka
tunda kayan bacci ne ma a jiki na da hijab
din sallah, na chanja kaya amma banyi
kwalliya ba face turaren da na dan saka
kadan, ko mai ban shafa a jiki na ba. Yana
kira na yace yazo na fita da sauri amma
sai na fara shiga gurin Daddy na tarar har lokacin yana bacci Dr tare da Hussein suna zaune a tare da shi. Sai na wuce na fita waje.

A waje na same shi and I told him everything, yayi kokarin rarrashina tare da kwantar min da hankali duk kuwa da cewa shima na fahimci cewa nasa hankalin ya
tashi. And I decided to continue with story ne da nake bashi. I decided to take him to the oasis and tell him the story of Ammie and her legacy.

A Oasis din na bashi labarin, har zuwa kyautar da Ammie tayi min na kuma lissafa masa maya daga cikin abubuwan da ta bani.

Na tsaya ina kallon expression din fuskarsa ina cigaba da jin faduwar gaba. Tun ranar da Daddy ya gaya min yawan abubuwan da na mallaka a duniya nake
lissafin gaya wa Muhammad, har Allah yayi rabuwar mu ban samu courage din gaya masa ba, yanzu gashi mun sake dawowa. Ina tsoron kar ya guje ni saboda
haka, dan nasan maza, musamman maza masu ji da mazantaka irin ta sa ba kowa ne zai so ace matarsa ta fishi arziki da daukaka ba.

Yayi shiru yana kallona sannan ya girgiza
kai "wait... Wait.... wait..... Just wait" nayi
shiru duk da dama ba magana nake yi ba,
ya cigaba da kallo na amma daga alama
bani yake kallo ba hankalin sa yana yawo
ne trying to get the clear picture of abinda nagama yi masa bayani. Zuwa can kuma vace "what?" Cikin mamaki. Na rufe idona na bude "I am sorry Muhammad. I never want to drag you into this. Nima
duk ban san da wannan maganar ba sai
daga baya. Kuma na rasa yadda zanyi in
gaya maka. I was afraid you will leave me
because of it. I am still afraid" na fada
murya ta can kasa, ya dawo da hankalin
sa gare ni, sannan na sunkuyar da fuskar
sa kasa yana kokarin hada idon sa da
nawa da na sauke kasa. "Hey sweetling,
don't say that. Look at me" na dago ido
muka hada ido da shi sai yace "I will never
leave you kinji? Not because if this, not
because of anything. In kinga na rabu da
ke to sai dai in ke ce kika ce ba kya so na
kuma" naji hankali na ya fara kwanciya, but still there is more to my news. But that will have to wait for another day, dan already na riga na yi plan din how to break that news to him.

Na dan kirkiri murmushi nace "thank you.
Nagode da soyayyar ka gare ni Yaya
Muhammad" ya mayar min da murmushin
sa mai kyau sai kuma ya daga kai yana
hura iska ta bakin sa, he still looked
shocked akan labarin nawa. But there is
still more to that sai na cigaba. "It has
been 22 years since the gift, it has been
20 years since her death, and things have
changed since then. Everything have
multiply" ya dawo da idonsa kaina yana
kallo na na gyada masa kai "I now own
almost everything da yake a sunan ta ita
da Daddy. I own wealth that even I cannot
comprehend. Sole ownership of two fully functional companies and a share in a lot of others. Including a hefty share in the gold company. And cash, lots and lots of cash".

Ya sunkuyar da kansa yana kallon
hannunsa sai ya dago yana kallona da
murmushi a fuskarsa yace "tun ranar da
na fara ganin ki, I have been calling you a
rich kid, not knowing you really are a rich
kid Safiyya" a danyi murmushi tare da
girgiza kaina nace "I didn't know then.
Har yanzu kuma ni kaina ban gama
accepting maganar ba, Da ace za'a dawo da rayuwa baya ace kuma zasu tambayi ra'ayi na kafin suyi abinda suka yi I wouldn't have accept it, I don't want it, Nauyi ne beyond dukkan understanding
dina, dukiya jarabawa ce and I have been through test often test tun kafin ma in San ina da dukiyar" nayi shiru sannan nace "Har yanzu a cikin jarabawar nake.
And I don't know if I can pass this last one. I don't think I can lose you and Daddy at the same time".

Sai ya kara matso da kujerar sa ya kama hannuna cikin rarrashi, na zame hannun ina goge hawayen da ya fara sauko min, yace "look at me Safiyya. Daddy will live
longer than we have have ever dreamt of, and together we will convince him akan maganar auren mu kuma zai amine kinji. Na tabbatar miki da haka. Ki daina damuwa dan Allah".

Na dan gyara fuskata ina jin dadin
concern dinsa a gare ni nace "thank you
Baby" yayi murmushi "wai ke waye ya
kowa miki babyn nan ne?" Nace "ba ka
so?" Yace "so kai... It makes me feel...... don't know how to explain it" na danyi dariya tare da juya idona "try..." Ya rage idonsa a kaina, na san irin kallon sai na rufe fuskata da hannu na yace "I will explain. Ki dan jira in gama yaki da Daddy da Abba da Mama, Sal inyi miki bayani dalla dalla, da manyan bakake" nace "na
daina fada to" ya danyi dariya "ko kin daina yanzu I will make sure kin cigaba" na mike tsaye ina son ya daina min irin wannan kallon da yake yi min nace
"come, let me show you something".

Ya tashi ya biyo baya na muka sake jerawa
muka cigaba da tafiya a gidan, kowa
zuciyar sa cike da tunani, and I took him
to the reservoir. Na durkusa a gabanta
tare da dora hannu na akan murfin sannan ba tare da na kalle shi ba nace"she died here" va durkusa a kusa dani cikin confusion yace "who?" Na juyo ina
kallon sa nace "Ammie" ya bude ido cikin
mamaki sannan ya kalli reservoir din ya kuma kallo na, and I told him yadda mutuwar tata ta kasance.
Har na gama bai ce komai ba. Jikinsa yayi
matukar yin sanyi dan da kyar yake daga
kafarsa yana jerawa da ni muna tafiya,
Daga zuciyar sa har jikinsa duk sunyi sanyi matuka, Muka sake dawowa inda motarsa take sai nace "I need to get back home yanzu. Bana son Daddy ya farka ya
ga bana kusa har kuma ya gane cewa na fita tare da kai" ya gyada kai da sauri cikin fahimta, Sannan ya bude motar muka shiga tare muka bar gidan gonar.

Komawa gidan kusan in silence muka yi
ta, lost in our thoughts, Na san dama
maganar dukiyar ta dole zata buge shi
kuma zai bukaci lokaci yay digesting
maganar and comes to term with it, duk
da dai maganganun sa sun karfafa min
gwuiwa da kuka nina min cewa ba zai gudu ba,

A kofar gida ya ajiye ni muka rabu tare da
alkawarin zamuyi waya. Bayan ya kara yi
min was kalaman kwantar da hankalin.
Ana ta kiraye kirayen sallar magrib na
shiga cikin gidan, direct part din Daddy
na wuce na tarar Hassan yana yi masa
alwala. Na karasa da sauri gaban sa
"Daddy" na kira sunansa, ya danyi gyaran
murya yana kokarin yin magana sai na
girgiza masa kai tare da saka dan yatsa na
a kan lebe na alamar yayi shiru, ya danyi
min gajeren murmushi sannan ya kammala alwalar sa, na fita a lokacin da yake kokarin tayar da sallar daga kwance. Nima daki na na shiga nayi sallar tare da
jero adduoin neman zabin Allah akan
lamura na, daga nan sai na kuma komawa
grin Daddy na zauna ina kalion nurses
din suna saka masa drip wanda zai yi
serving a matsayin abinci tunda a yanzu
ba zai iya cin abinci ba., Bayan sun gama
sun bamu guri sai muka zauna a tare da
shi har Mommy muna ta yi masa hira, duk
da baya bamu amsa amma yana ta bin mu
da ido har daga baya bacci ya sake dauke shi.

Sai bayan yayi bacci na koma dakina na
tarar da missed calls daga gurin Muhammad da kuma gurin Aunty Hajjo, aunty Hajo na fara kira sai tace "ke ba kya kiran mu sai mun kira ki ko Fiyya?"
Nayi murmushi kawai. Kusan kullum sai
tayi min wannan mitar, ni kuma ina jin
nauyin kiran ta ne kawai. Na gaishe ta
tace "dama wani abu zan nuna miki" sai
na katse kiran a kira ta video call duk
kuwa da already na san abinda zata nina
min din. Tana dauka kuwa shi na gani,
Yana zaune a cikin play pen dinsa kayan
wasa sun zagaye shi, Na bude baki cikin mamaki, ya zama katoto, yana ta mika hannu zai kamo wata
ball mai kyalli da take makale a saman
pen din, Nace "aunty Hajjo har kun kafa
zama ashe?" Tace "muna koya daj" tana
fada kuwa ya tafi da baya ya fada kan kayan wasan na sa. A tare muka yi dariya ni da Aunty Hajjo, shi kuwa ko a jikin sa sal ya cigaba da mika hannu still zai kamo ball din da yanzu ta kara yi masa nisa.

Ta kai wayar kusa da fuskar sa, nace
masa "hey", ya dan juyo yana kallona sai
kuma yayi sauri ya kai wa wayar wawura
yana kamata kuwa ya danna a baki, sai
gani a cikin bakin sa. Da kyar Aunty Hajjo
ta kwace, sannan ta matsar da wayar
daga kusa da shi, ina ta murmushi nace
"in ka lalatawa Aunty wayar ta sai ka biya ta" tace "mun saba fada akan waya ai" na tsaya ina kallon sa nace "wannan yaron Aunty kumatun sa kamar bread " tayi dariya "duk sanda kuka hadu idan kika
dauke shi kuma zaki ce kamar block, irin
12 inches din nan". Sai kuma ta koma ta
zauna a gefe muka cigaba da hirar mu. Ta riga ta san labarin Mukhtar da abinda ya faru, sai kuma na bata labarin rashin lafiyar Daddy da abinda ya faru dashi yau, ta jajanta sosai ta kuma kwantar min da hankali tare da alkawarin zata gayawa uncle Sufyan.

Bayan mun gama waya sai na kira yallaban da already ya kara yi min two missed calls sanda muke waya da aunty Hajo. Yana dauka yace "hey" nace "hey
you too" yayi dariya "yau babu babyn?" Nace “ nadaina ai” yace “ please, Dan allah, natuba” nace “ to sai kayi alkawarin kadaina tsokanata” yace “nayi, nayi alkawarin komai ma. Please kifada inji” nace “ to zan fada yanzu. Ka shirya?” Yace “ yes, say it please m” nadanyi murmushi kamar yana kallo na nace “Malam Muhammadu dan fillo”.

Maman Maama✍🏻
[07/01, 10:46 pm] +234 906 816 1960: ❤️‍🩹Safiyya❤️‍🩹


Episode Fifty Five: The Green Snake 2


Ina jinsa yana dariya nima na kife kaina a cikin pillow ina dariyar sai da ya gama yace "wallahi kinyi da dan halak, sai na rama. Zaki hadu da ni" na daidaita murya ta nace "sai dai ka rame ba dai ka rama ba. Haka kawai ka baro riga ka taho birni kazo ka takurawa zuciya ta" ya dan yi shiru kuma sai yace "you have been calling me dan fillo, ashe kema fillon ce. Shine kika boye min dan kar in rama" na girgiza kaina nace "| am not. I have never think of myself as fulani. Ko kalmar zo ban sani da fulatanci ba" yace "war.." sai
kuma yayi shiru for sometimes sannan yace "na bawa kaina aikin koya miki fulatanci daga yau. We hardly speak hausa at home. And Mama zata ji dadi sosai idan taji kina fulatanci dan tana so sosai. Zata san cewa jikokin ta zasu iya" na danyi shiru sannan nace "you know as much as I do, ba iya fulatanci ko rashin iya wane zai saka mama ta so ni ko akasin hakan ba, So it doesn't matter" yayi ajjiyar zuciya "haka ne. But to ne yanzu the biggest issue is with Daddy. Because nasan case din is sensitive, dole mu ringa kiyaye abinda zamu ke fada ko kuma abinda zamu ke yi a gaban sa dan gudun bacin ransa. Any idea on how we can change his mind?" Na danyi murmushi dan already I have few ideas da a fara jan zaren sakarsu already. Amma ba zan gaya masa yanzu ba. Nace "not yet. Working on it. Yace "okay da kin samu idea tell me so that we can talk about it, a bangaren Mama da Abba I think I can change their mind, zan dai dan bukaci lokaci ne kawai. Weakness din Mama shine mu yayanta, like she can and will do anything for our happiness. I only need to convince her that you are my happiness shikenan magana ta kare" nace "inye dan gatan Mama. But what about Abba?" Yace "sai dai in Mama bata yi masa magana ba. Abba fa mijin ta ce ne" duk mukayi dariya nace "kamar ka fada a kunnen sa. Sai na gaya masa" yace "I am looking forward to ranar da zaki gaya masa din, I am looking forward to ranar da zaki zama free with them. They will love you, tunda na hadu da ke I always picture you as their in-law, and always picture yadda Mama zata ke pampering din ki with love kina yi mata shagwaba" na dan bude idona na na rufe a hankali nace "I can't wait either"

Mun jima muna hirar iyayen mu sai mukayl sallama. Yace "about that baby thing, ni ta ban hakura ba. Ko ki fada ko kuma yau ba zanyl bacci ba kuma ba zan barki kiy| ba dan kiranki zan yi tayl a waya" nace "sal in kashe wayata al" yace "sai in taho inyi ta buga muku gate kuma ba zan tafi ba har sai kin fito kin ce min baby" nace "bismillah. My windows are sound proof, ko zaka kwana kana bugawa ba zan ji ka ba" ya langwabe murya "please, just say it" na makale kafada kamar yana kallo na nace "naki din" yayi a)jiyar zuciya
"shikenan al. Na san matsayi na yau, Good night" nace "sweet dreams my Baby",

Sai na kashe wayar da sauri ina murmushi, Da akwai wani magic a cikin soyayyar muni da Muhammad, no matter the trouble da muke ciki in dai muna tare sai muji kamar an dauke mana dukkan damuwa, in dai muna tare to everything else feels like a background noise. Nayi ajiyar zuciya ina kallon wayar sannan na dora ta akan kirjina na dora pillow akan ta na rungume ina cigaba da murmushi, Nayi bitar maganganun mu da muka yi and I understand dalilin da yasa yake ganin zai iya convincing Mama cikin sauki, saboda bai san maganar Mukhtar da

amma yana motsa bakin sa da alama azkar yake yi. Na kama hannun sa na kai bakina nayi kissing sai ya bude ido ya kalle ni "good morning Daddy" a fada a hankali, ya gyada min kai kawai, nace "ya jikin?" Ya mayar da idonss ya rufe bai ce min komai ba sai na mayar masa da hannunsa kan cinyarsa a tashi ina tambayar nurse din ya yake ganin jikin daddyn. Yace "da sauki sosai Madam. But we will need a breathing machines on standby dan gudun kar a kuma samun irin
wancan attack din." na gyada kai da sauri '"dr Ma'aruf yayi min magana jiya a asibiti, har na bashi go ahead to order it, yace guda biyu za'a siya ko?" yace "yes, abinda ya kamata kenan, akwai bipap machine, shi kamar mask ne da za'a ke saka masa kullum danbya taimaka masa wajen jan enough air, sai kuma mechanical ventilator da za'a ajiye just in case of another attack" nace "za'a kawo su insha Allah" yace "okay. Sai kuma maganar abinci, baya iya hadiye abincin da zai wadace shi yanzu, dole a fara feeding dinsa through a feeding tube. But zainiya cigaba da gwada ci da kansa din amma kuma sai muke supplementing through a tube dan kar yake zama da yunwa" na gyada kai duk da hawayen da yake kawowa idona, a raina nace "a feeding tube it is, dan my father will not die hungry",

Na juya ina tafiya yana bina a baya yana cigaba da yi min bayanin yadda zasu ke Needing din nasa da kuma duk abinda suke bukata. Sai da muka kai parlour sannan na dakata har ya gama sai nace *kuyi magana da Dr Ma'aruf in ya shigo. Kace nace ayi duk abinda ya kamata" ya gyada kai "okay ma'am" gar na juya zan tafi kuma sai na dawo da baya ina kallon sa nace "will there be pain? Zai ji ciwo sosai?" Ya girgiza kai "no, Just discomfort kafin ya saba. The whole thing about ALS is that it is painless. Babu pain ko kadan" na gyada kai sannan nayi masa godiya na koma ciki,

A dakina bayan na koma na kwanta nake lissafa wanna shine kusan machine na goma da za'a siya wa Daddy to help him with the most basic things that healthy mutum yaje yi cikin sauki. Health is truly wealth, Bayan power wheelchair dinsa da take taimaka masa wajen tafiya automatically ba tare da an tura shi ba, tana kuma ina yin kwana sannan ta hau karamin tudu kamar na bakin kofa da sauran abubuwan da normal wheelchair bata yi, akwai machine din da yake taimaka masa wajen transferring dinsa from the wheel chair to the bed da daddare and back to the wheelchair da safe, akwai wanda ake daura masa a hannu wanda yake taimaka masa wajen aiki da hannun kamar cin abinci da operating wayarsa da sauran basic amfanin hannu, Da akwai wani a toilet da
yake taimaka masa wajen hawa toilet seat din da kuma sauka, da kuma tsaftace jikin sa in ya gama, da akwai na exercise, wanda ake dora shi kullum ya motsa dukkan jikin sa to avoid yankwanewa da nannadewar da jiki yake yi idan ba'a amfani da shi. Da akwai wani ma da muka yi order last week, wanda zai taimaka wajen amplifying voice dinsa yadda za'a ke jinsa sosai tunda yanzu maganar ta sa tayi kasa sosai, akwai wanda yake taimaka masa wajen yin tari ya kuma yi clearing airways dinsa tunda bashi da karfin yin hakan da kansa. Wadannan duk abubuwa ne da healthy mutane suke yin su kullum ba tare da sun biya ko kwandala ba. Ban iya komawa bacci ba, na jima akan gado ina saka da warwara, gabaki daya zuciya ta a dagule, daga baya sai na dauko wayata dan inga ko ina da meeting ko wani abu da zai dauke min hankali na and keep me sane, Sai naga sakon barka da tashi daga Muhammad "morning sweetling. Just want to put on a smile on your beautiful lips, with an assurance that today is going to be a good day insha Allah kinji? No matter what is going on in life I will always be by your side sharing the joy and the sorrow,
Forever and ever. With lots of love from your Baby". Nayi murmushi sannan nayi dariya ni kadai kamar tababbiya. Sai kuma nayi masa reply "hey Baby. Ya jikin? Thank you for the smile, really needed it. Sending
lots of love from a stupid heart crazily in love with you".

Daga nan sai naji na samu karfin fuskantar ranar. Na tashi a shiga wanka na dauki lokaci ina wanke jikina da
mayukan wanka na da suke karawa fata ta kyalli, laushi da santsi, Na fito daga shower na tsaya a gaban mirror din cikin toilet din ina goge jikina ina kuma kare wa kaina kallo, har yanzu ba zance na dawo yadda nake ada ba but na chanja sosai from yadda nake sanda na dawo daga Berlin, fata ta ta dawo color dinta na ainihi sai kyalli take tana daukan ido amma har yanzu ban mayar da kiba ta ba saboda har yanzun hakalina ba'a kwance yake ba, na tsaya ina kallon fuska ta da yadda tsarin komai yake a cikin ta, sai na sauke ajiyar zuciya ina godiya ga Ubangijin da ya halicce ta dan ko ni idan nibaka bawa ikon halittar kaina bana jin zan yi wa kaina kirar da tafi wadda nake da ita a yanzu. Na dan ja da baya ina kallon gurin da aka yanka a ciki na aka fito da Junior, na saka hannua hankali na taba gurin, ya danyi taurin da in ka taba zaka ji shi a hannunka amma a ido it is barely showing sai dai in kasan da shi dama and you are looking for it shine zaka gani, and it has been just 5 months, hakan ya sa na kara jinjinawa likitocin a bisa kwarewar aikinsu sannan kuma na kara tabbatar da abinda suka ce akan aikinsu baya barin scar. Cikina ma kuma bai nuna alamar cewa dan mutum ya zauna a ciki ba, ko dan bai karasa girma ba aka cire shi? Dan ko wata bakwai cikin Junior bai karasa ba sanda aka yi min aiki. Sai kawai naji ina jin tausayin sa, bai gama jin dumin cikin mahaifiyarsa ba bai kuma ji dumin ta a ranakun farkon rayuwar sa ba. Sai naji ina son ganin sa, just to hug him I little and assure him that I love him and that everything will be okay.

Amma kuma na san zuwa na Berlin a yanzu wani abu ne da zan iya cewa is close to impossible, babu yadda za'a yi in iya tafiya in bar Daddy kamar yadda babu yadda za'a yi in iya daukan Daddy a halin da yake ciki in tafi da shi. Na sake sauke ajiyar zuciya sannan a hankali nace "I am sorry Adam, You are going to be okay", A daki na zauna na shirya cikin doguwar riga marar nauyi bayan na shafe jikina da mayukan da suke kara gyara fata ta, sai kuma na jawo system dina na koma kan study table dina na bude na fara going through abubuwan da ya kamata inyi a yau. Na ga cewa ina da meetings har guda biyu daya da rana 12 daya kuma da yamma 4pm. Sai kuma na mayar da
hankali grin karanta wani breakdown da aka turo min na retailers dín kayan mu da yawan kayan da kowa yake siya a wata daga kamfani. Ina so ne zan yi musu kyauta ta bajinta dan in kara rike su gam a hannuna, Na gama dubawa sannan nayi deciding abinda zany musu a rubuta na tura wa marketing department, Ina cikin aikin Esther ta shigo ta gaishe ni tace "Madam breakfast fa yana kasa tun dazu, ko a kawo miki sama ne?" Na dan girgiza kai "kawo min coffee kawa'" ta bata rai "Madam, in ba kya cin abinci zaki fadi watarana" na daga ido ina kallon ta sai tace "so nake ki zama katuwa" na bata rai "I don't want to be katuwa" sal tayi dariyar yadda nake yatsuna fuska tace "to ki dal ci abinci please, Breakfast is the most important meal of the day. Ki samu ki ci protein sosai da breakfast, it will help you go through the day, ko da ace kin zama too busy to eat a complete meal to ba zaki rasa energy ba, Kuma breakfast baya saka kibar da ba kya so, tunda shi You will burn it down during the day ba karar dinner da ake ci a kwanta ba" na yi
murmushi "thank you for the lecture. Now, bring my coffee" ta dan bata rai ta juya tana magana kasa kasa, da alama mita take yi. Na bi bayanta da kallo ima murmushi sai kuma wani tunani ya zo min na mike na rufe system din tare da na da karamin mayafi a kaina na fita. A stairs na wuce ta da sauri ina hada
bibbiyu, ta biyo ni a baya tana haki, na juya nayi mata gwalo "idan da baki hada wannan kibar ba ba zaki yi haki for just coming down the stairs ba" ta bata rai tace "nima dai slimming din nan zan yi", A dining table na zauna tazo ta fara zuba min abinci tana cigaba da yi min lecture akan nutrition, "Idan kin ci da yawa ma you can always go to the gym and turn the fat into muscles" na bata rai "I don't want to have muscle" na fara cin abinci na ta zauna ita ma tana kallo na tana ta zabga murmushi. Ma juya ina kalion ta tare da yi mata alamar tambaya da hannuna sai ta girgiza kai "nothing
Madam. I am just happy that you are in a good mood today. Kwana biyu baya duk fuskarki babu smile" nayi murmushi "someone put a smile on my lips early this morning, and I am going to hold on to it har dare" ta danyi dariya tana tafa hannu "wonderful. I am so glad madam. Zanyi zaman daki. Please take me with you" na bude ido "I said someone, ya akayi kika san namiji ne?" Tace "I know love when I see it, and you madam are in love"., Nayi murmushi kawai bance komai ba.

A lokacin naji alamar wani ya shigo gurin, naga kuma Esther ta gyara fuskarta sannan ta tashi tsaye tana gaishe da wanda ya shigo din. Na juya na ga Mustapha sai na dawo da ido na kan abinci na na cigaba da ci. Ya karaso ya zauna Esther ta fara hidimar zuba masa abinci, ya kalle ni na dago kai nace "goodmorning" yace "how are you?" Ban amsa ba na cigaba da cin abinci na amma ina jin idonsa still a kaina sai yace "ci ba kiba dai inji hausawa sun ce asarar abinci ne" dariya ta kusa ta kwace min sai na mayar da ita, hakan ya sa na kusa kwarewa, Esther ta bar shi ya dawo gurina ya zuba min ruwa ta miko min, na karba na sha nagode mata nacigaba da cin abincin still ba tare da nace masa komai ba.

Yana cigaba da kallo na yace “why are you laughing?” Na danyi kokarin bata rai nace “dariya kuma? Waye yake dariya” yabata rai “wai da” nakara kokarin danne dariya ta na cigaba da cin abinci na. Esther tagama zuba masa ta juya ta fita ta barmu mu kadai. Yafara cin abincin sa yana kallo na har lokacin sai kuma yace “akwai maganar da nake so muyi dama fiyya. I have been thinking of a way to get you alone Amma na rasa, kin san yanda kike yanzu, kin zama hukuma sai lallashi” na gyara zama na tare da daukan cup din coffee na ina karasa shanye abinda yake ciki, na daga gira nace “wacce maganar ce knan ?” Yayi ajiyar zuciya “maganar ai guda daya ce. It is about us. I don’t know why you are still shying away from the truth, chasing a dream that will mever come true” na ajiye cup din ina jin raina yana baci nace “haryanzu dai ban gane maganar ba. Kace about us. Wacce magana ce about us” yayi shiru yana noticing changing yanayin fuska ta yace “kin sani ai” na mike tsaye nace “akwai maganganu da yawa da na sani about us Mustapha, maganar sanda kake cin zalina a bayan mutane sanda muna yara idan na kai kara kuma Safina tayi karya ta kare ka? Ko maganar sanda kayi ta trying to sexually assault me in then threatened me cewa idan na fada sai kayi da gaske?" Ya mike tsaye, jikinsa gabakidaya yana rawa idonsa kamar zai fado kasa dan tsoro yana kalion hanyar shigowa gurin "shishsh, me kike cewa Safiyya? Me ya kaio wanna maganar kuma?" Nace "ban gama ba ai, akwai wata maganar kuma, maganar sanda bayan mun girma kake shiga dakina a dukkan opportunity da ka samu and begging me to let you do
it ko da sau daya ne" ya tako da sauri zuwa gabana yay kokarin rufe min baki da hannunsa, fuskarsa cike da toro, na matsa baya da sauri na kuma cigaba da magana, "you told me babu wanda zai sani, you told me ko na fada babu wanda zai yarda, I had to find a way to protect myself from you Mustapha, Saboda kai
komawa nay kamar yar daba, duk dakin da na zauna ina ajjye da wuka a gefe saboda kai, har yau akwai wuka a dakina saboda in kare kaina daga sharrin ka. You traumatized my childhood, and you traumatized my nights at my teenage Na kasa gaya wa Daddy saboda maganar tayi min nauyi, na kasa gayawa Mommy dan mahalfiyar ka ce kuma ba lallai ta yarda ba kamar yadda kace. But maybe this is the right time to tell them, Maybe in na fada musu a yanzu
zasu fahimci dalilin da yasa na zarge ka akan abinda ya same ni. Kuma zasu fahimci dalilin da yasa nace bana son auren ka" ya sake kokarin rufe min baki, na juya da sauri na dauki wuka a cikin set din kanana wukaren da suke jere a cikin shelf din da take bangon dining room din "the next time you touch me will be the
last time you have a hand".

Ya yi taku biyu baya yana kara lekawa cikin parlour sannan ya juyo yana kallona. '"na riga na baki hakuri ai Safiyya. Me kike so in yi miki ne kuma? Kuskure ne da rudin kuruciya da kuma sharrin shaidan kuma babu wanda yake above mistake. Kuma ai banyi ba ko? To me yasa ba zaki yafe ki manta maganar ba? What do you want from me?" Nace "kaje ka gaya wa Mommy da Daddy cewa ka janye maganar aure na. In baka fada ba ni kuma zan gaya musu dalilin da yasa ba zan aure
ka ba" ya fara jujuya kansa "Safiyya. Wannan maganar ai ba ta kai wadda za'a fasa aure saboda ita ba. I promise you ban taba yi ba, a kanki ma kuskure ne da rudin shaidan, I mean you are very beautiful and we live together and I was young and hot blooded. But that doesn’t mean….” Na katse shi “I don’t care about shaidan and all his sharri stuff. Kai kayi min laifi kuma kai nake hukunta wa by not marrying you. I may forgive you but I can't marry you. Make them understand that or I will”.

Yayi shiru muka cigaba da tsayuwa muna Kallon juna. A lokacin ne muka ji shigowar Mommy, tun kafin ta shigo parlour muryarta ta karade gidan da Fada, Ya juyo yana kallona da sauri yace "I will do it, just don't talk about this again" ya fita da sauri ya taffi gurin ta. Nima fitowa nayi daga dinning din na tsaya akan steps din da ake takawa daga parlour kafin a shiga dinning din ina kalion kofar shigowa pariaur.

Mommy ta shigo mayafin ta a hannu tana zazzaga fada "ban taba ganin mahaukaciya, marar zuciya a duniya irin wanna yarinyar ba. Da ace bata kama da
ni tsaf zance chanja min ita akayi a asibiti. Ta yaya za'a yi ni yadda nake da wanna zuciyar amma ace ita tata kare ya dauke?" Mustapiha da yake kokarin
daidaita yanayin fuskarsa yace "Mommy lafiya? Ke da waye haka?" Hassan daya biyo ta a baya da jakarta yace a hankali “ita da yaya Safina”.

lta kuma Mommy tace "ni da wa kuma in banda waccan shashashar kanwar ta ka? Wai yarinyar nan ance za'a sallame ta yau na tashi da sassafe na tafi dan mu taho gida tare amma budar bakin ta wai ita
gidan mijinta zata koma, Ko a ina mijin yake? Dan wancan fitsararren yaron dai ba miji bane ba. Kuma wallahi ni da ita ne" ran Mustapha ya baci "kuma Mommy kika barta ta tafi baki babballata a asibitin ba?" Mommy tace "bar ni da ita. Bar mishi aikin
nayi. Jira nake yi yayi gunduwa gunduwa da ita ya watso ta waje kuma na gaya mata wallahi ba zan koma asibiti zaman jinyar ta ba sai dai ta tafi Katsina wadanda suka aura mata shi suyi jinyar ta a can.
Haka kawai yara suna nema su haukata ni. Wannan yaron ya zamar min annoba a cikin gidan nan wallahi. Ya mayar min duk yaran sun zama mahaukata. Daga safinan har Safiyya da nake ganin kamar tana da hankali".

Jin ta ambaci sunana sai nayi saurin yin baya zan koma inda na fito. Ban san ta ganni ba sai ji nayi tace "ina zaki je? Dawo nan" na juyo na dawo cikin falon na
gaisheta "good morning mommy" tace "wanne morning din? Wacce Mommy din? Yaushe rabon da ki gaishe ni a gidan nan?” Nace "Mommy al ba kya nan ne shi….” Tace kin san bana nan ne? Na tabbatar baki sani ba kuma baki neme ni ba saboda ke yanzu kin zama yar kanki ko? Ba'a isa ayi miki fada ba sai ki dauki fushi da mutane. Ina daukan ki me hankali
ashe kema shashasha ce irin Safina. To wallahi bari kiji in gaya miki, abinda kike nema will never happen. Babu ta yadda za'a yi miciji ya sare ni a kafa daya kuma
in sake mika masa daya kafar. In zaki dawo hankalin ki ma ki dawo tun kafin lokaci ya kure miki. Shashasha". Sai na juya nayi hanyar stairs. Tace "ai ba ce miki nayi na gama ba" na juyo na dawo amma sai na zamu guri na zauna danna fahimci ba yanzu zata gama fadan ba. Ta kuwa cigaba yin abinta. Ni dai na zauna
kaina a kasa, ina yi ina kallon agogo ina lissafin lokacin meeting dina yayin da ita kuma ta cigaba da juye fadan ta a akaina.

Allah ya taimake ni sai ga Dr Ma'aruf ya shigo, shigowar sa ce ta saka tayi shiru ta amsa gaishe ta da yake yi sannan ya zauna ya miko min wata takarda yana yi min bayanin bills ne na dukkan expenses din da aka kashe a wanna karon da kuma kudin machines din da akayi order. Na dudduba tare da sauke ajiyar zuciya nace "same account da wanda na tuna muku last month?" Yace "eh" Na mike nace okay, zan hado maka da salaries dinku for this month, shikenan sai mu gama dasu. Yayi murmushi "that will be good. Thank you"

A haka na samu na zame na hau sama kamar zuwa zany in yi transfer din amma kawai sai na ajiye takardar nayi kwanciya ta na rufe idona. I knew I have achieved something with Mustapha amma kuma
maganar komawar Safina gidan Muhammad tana neman dagula lamari na. Ba wai na saka ran ba zata koma ba ne ba amma kawai da najinta koma din sai naji kishin ya motsa. Ni kaina ban san yadda
za'a yi wannan lamarin ba. Na dai san kawai cewa ina son Muhammad. Ban kuma saukowa ba sai da na gama dukkan meetings dina da na gabatar online. Ina gama wa na rubuta wata takarda na tura e-mail din Uncle Ahmad sannan nayi refreshing na saka riga da
skirt na atampa na daura dankwalin atampar sannan na saka mayafi na kuma feshe jikina da turaruka masu tsada na fito.

Dakin Daddy na fara shiga. A zaune na same shi Dr yana ta yi masa wasu bayanai shi kuma yana gyada kal alamar fahimta, Na zauna sai da suka gama sannan na karaso na gaishe shi, Ya amsa min, yanzu
muryar ta fito amma can kasa, Nayi murmushi, Dr yace "jiki alhamdulillah, Kar ki damu kinji?" Na gyada kaí tare da kara matsawa kusa da Daddy na rike hannunsa nace "Daddy zan fita, Zanje gidan uncle
Ahmad. Yanzu zan dawo insha Allah", A idonsa naga alamar yaji dadin magana ta, sai ya danyi mun murmushi kadan, Ina fita daga parlourn a na dauko shades a cikin jaka ta na saka a idona, Ina fita
harabar gidan naga guards dina sun tashi zasu tafi gurin motasu sai na kira su da hannu na, suka karasa and I said "I don't feel like driving today" da sauri daya ya koma ya kawo motarsu zuwa inda nake,
daya kuma ya bude min baya na shiga sai ya zagaya ya shiga gaba kusa da dan uwansa muka tafi, A hanya na gaya musu address din inda zamuje, gidan uncle Ahmad, Na dauko waya ta na a duba naga missed calls from Muhammad amma sai na share shi,
Haushin sa nake ji duk da bai yi min komai ba. Amma kuma sai nayi amfani da lokacin wajen saving number din sa da sunan da yake kai tun da "Pyar💕”na kuma bata lokaci wajen zaban hoton sa a cikin hotunan sa da nayi retrieving na saka akan number din sa, na kuma zabi ring tune mai dadi mai cike da kalaman
soyayya na saka masa, sai dai still da ya Kira ni ban dauka ba. A raina nace *kaje Matarka tana gida tana jiran ka*.

A kofar gidan uncle Ahmad muka tsaya muka yi horn aka bude gate muka shiga, amma sai na zauna a mota nace su tambaya suji ko mukhtar yana ciki, suka
dawo suka ce baya nan sai na fita sannan nace musu idan ya dawo kar su barshi ya shiga ciki har sai na gama na fito.

Ina shiga cilkin parlour da sallama naga Umma ta fito daga Kitchen. Sai kawai ta tsaya tana kallona. Na cire shades din idona na durkusa na gaishe ta. Ta amsa still fuskar ta da mamakin ganina sai nace "Umma ina su Salima, ina Uncle?" Sai ta kalli dakin Salima sannan ta juya ta kalli hanyar part din uncle Ahmad amma still
bata de komai ba. Sai na mike tsaye nace *Umma uncle din yana kusa? Zan iya ganin sa?" Ta dan gyara fuskarta tana kokarin cire mamaki daga cikin ta tace
"bara inyi masa magana. Salima tana cilki zaki iya shiga" nace "zan shiga, bara in ga uncle tikunna".

Sai ta juya ta shiga part din uncle Ahmad da sauri, Ina nan zaune sai ga Yaya ya shigo, nay kokarin gaishe shi sai naga yayi min kallon banza ya wuce yana cewa
*dama ke kika ajiye mana wannan bakar motar da wadannan bakaken mutanen a kofar gida kenan" ban ce masa komai ba sai ya shige dakin Salima. Yana shiga sai ga ta ta fito, ta tsaya a bakin kofa tana
kallona kamar yadda nima nake kallon ta. *Fiyya" ta fada a hankali. Na dan yi mata murmushi "hello Salima" ta karaso cikin falon tana murmushi itama. Kafin ta zauna uncle Ahmad ya fito tare da Umma. Na
mike tsaye cikin girmamawa sai da ya zauna sannan na zauna nima a kasa, Umma ta zauna a gefensa tana kallo na fuskarta da expression din self pity. Na
gaishe da uncle, ya amsa min idonsa a kasa sai nace "'Uncle dama zuwa nayi in tuna maka da cewa Daddy ba shi da lafiya. You should be with him. He misses
you. Na san kuma kaima kana missing dinsa" yayi shiru sai kuma yayi magana muryarsa tana rawa "me zance masa idan naje?" Nayi sauri nace masa "kace masa ya jiki? Sai kuma ku cigaba da maganganun ku yadda kuka saba" duk muka yi shiru sai na sake cewa "tun kafin ku san zaku same mu kuke tare, you shouldn't be apart because of us" Umma tace "haka ne. Nima na gaya masa, Kin gan shi nan kullum yana kwance a daki cikin damuwa. Amma insha Allah zai je in an jima* nayi murmushi nace "ke ma ya kamata kije Umma, Kera ai kanwar Daddy ce. Ya kamata kema ki je ki ga jikin sa zaiji dadi.

Ban jima sosai ba saboda babu abin magana sosai., Sun kasa sakin jiki suyi min magana sai na mike nace zan tafi, amma sal na kalli Salima nace "ki zo mu tafi tare Salima. In sun je in an jima sai ku taho tare" ta juya ta kalli Umma sannan sai ta koma dal da sauri ta dauko mayafin ta ta fito. Sai da zan fita nace da uncle Ahmad "uncle na tura maka sako email dinka. I will appreciate a response as soon as possible. The management misses you.

Tare muka koma gida da Salima. Muna ta hira sama sama sai dai daga dukkan alama ita ma tsintar kalimomi take yi wajen yi min magana, Mostly akan lafiyar Daddy take min tambaya ina amsa mata. Tayi magana akan wayata da take ta hasken kiran da Muhammad yake ta jera min. ana ta kiran ki fa* na kalli wayar "share shi kawai" "shi?" Tace tana murmushi, nayi murmushi kawai bance komai ba sai ta dau wayar tawa da wani kiran ya shigo ta amsa ta saka a kunnen ta, na dago kai tare da bude ido ina kallon ta cikin mamaki. Sai naga tayi dariya tana rufe bakin ta da hannun ta sannan tace ba ita bace ba. Kanwar ta ce" eh muna hanya ne, naga kamar kayi laifi ne kana ta
Kira ank dauka shine na taimaka maka na dauka* *okay to gamu nan karasowa" ta fada dai dai lokacin da muka sha kwanar shiga layin mu. A take na hango motar Muhammad a tsallaken gidan mu. Na juya
ido na sannan na dauko shades dina na mayar dasu ido na nace da driver din ya tsaya a waje, muna tsayawa Muhammad ya bude motarsa ya fito ya tsaya a gaban ta tare da saka hannayensa a cikin aljihun
sa. Na cigaba da zama a motar ina kallon sa, yayi kyau sosai cikin dinkin shadda ruwan toka mai duhu, rigar mai kananan hannaye ce wadda ta fito da damatsen hannunsa da naga sun kara girma fiye da
yadda na san su, Fatarsa tana kyalli, iska tana kada yalwataccen gyararren gashin kansa. Salima ta taba ni sannan tace min a hankali "he is hot" nayi murmushi
sannan na bude kofa na fita, a tare security din suka fito sai nace musu su wuce ciki kawai,

I purposely cat walked toward him. Irin tafiyar da na tabbatar ta karasa susuta sauran tunaninsa. Sai dai yadda ya zuba min ido ya saka naji ina kamar zan fadi
amma na samu da kyar na karasa inda yake. Ya danyi gyaran murya yace "you look stunningly beautiful. You took my breath away", Sai na daga gira na dauke
kai gefe daya. Ya zagaya side din da na juya fuska ta tare da hade hannayensa a guri daya yace "ban san laifin da nayi ba. Whatever it is. Na dauki laifin 100 percent and I am sorry" na murguda masa baki sannan na sake dauke kaina "ni gida zan shiga yanzu" yace "not until you tell me me nayi" nace "ya kamata kai ma ka koma gida, Matarka tana jiran ka., Gwara kaje da wuri kar ka yi laifi" and I saw him smiled har sai da hakoran sa suka bayyana "my sweet Piya" ya fada a
hankali. Na juya ba tare da nace masa komai ba zan tsallaka in shiga gida sai ya biyo ni ya sha gaba na sannan ya saka hannu na cire shades din idona "there is no way da zan koma gida ba tare da na kalli idon ki ba" na watsa masa harara trying so hard not to smile and kamar ya sani sai cewa yayi "now smile" and my
stupid heart obeyed her master and I smiled at him, har da lumshe ido da budewa. A hankali yace “much better” sannan ya mayar min da shades dina yace “now I can go home and eat” yajuya yana tafiya da baya da baya yana kallo na har sai da bayansa ya taba motarsa sannan ya juya ya shiga ciki, blew me a kiss.

Maman Maama ✍🏻
[07/01, 10:46 pm] +234 906 816 1960: ❤️‍🩹SAFIYYA ❤️‍🩹


Episode Fifty Six: The Talk

Har na shiga gida da murmushi a fuskata, ina jin sansa a raina sosai sannan kuma at the same time ina jin haushinsa saboda komawar matarsa gidan sa, sai dai ni kaina nasan kishi ne ya saka ni jin haushin ba komai ba, and I asked myself "idan auren ya tabbata, am I ready to share him with Safina?" nayi sauri na kawar da wanna tunanin daga raina sannan nayi replacing dinsa da tunanin ciwon Daddy. Part din sa na wuce, na tarar yana zaune akan gado an saka masa pillows a bayan sa yana kallon tv yana sauraron karatun Alqur'anin da yake fitowa daga ciki, a hankali bakinsa yana motsawa alamar yana bin karatun. Na zauna a kasa a gabansa nima na cigaba da binsu. Sai kuma na tuna da Salima da muka zo tare, na dauki waya ta na tura mata message na gaya mata inda nake na kuma gaya mata zata iya shigowa. Ba'a jima ba sai gata nan ta shigo, ita ma ta samu guri ta zauna a gefe na ta cigaba da bin karatun kamar yadda ta tarar muna yi.

Hussain ne ya shigo, ya sanar mana da cewa lokacin sallah yayi sannan ya dauko bowl yazo ya fara yiwa Daddy alwala, daga nan muka koma cikin gida muka tafi dakina tare mukayi alwala muka yi sallah, Bayan mun idar ne Salima ta tashi tana ninke sallayar da tayi using tace "wai safiyya da gaske wancan gayen kike jawa aji?" na danyi murmushi nace "shi waye da ba za'a ja masa aji ba?" Tace "ya hadu, nake gaya miki ya hadu, most girls will sell their kidney to have him look at them" nayi dariyar yadda tayi maganar nace "Allah ya basu sa'a, now forget about him mu sauka kasa mu ci abinci. I am hungry" muka sauko muka zauna a dining amma still bata daina maganar sa ba "dan kuka
yi aure wato za'a ga kyawawan yaya" nayi murmushi kawai bance komai ba dan bana son yin maganar anan sai ta sake cewa "I wanted auren ki da Yaya Mukhtar ya dore, I was even picturing the nephews and nieces da zaki haifa min, amma Allah ya fi mu sanin dai dai. I wish you happiness, where ever and with who
ever" naji dadin maganar ta nace "ameen, thank you", Na fahimci siblings din Mukhtar basu san gaskiyar abinda ya raba mu ba, ban san me iyayen suka gaya
musu ya faru ma. Maybe shi yasa na fahimci yaya yana jin haushina dan shine ya tarar da yadda na daure yayansa tsirara akan gado.

Da sauri muka ci abincin muka koma wajen Daddy, muka tarar Mustapha yana bashi abinci sai na zauna a gefen gadon ina kallon su har yace ya ishe shi aka ajiye bowl din. Salima ta gaishe shi ya amsa mata tare da mika mata hannu yana murmushi, taje ta saka hannunta a cikin nasa ya tambaye ta ina Salim sai tace
yana school, da yake boarding yake yi a Lagos, sai ta kama yiwa Daddy hirar Salim din da irin dramar da suke sha idan yazo hutu, yana shekarar sa ta karshe ne yanzu. Daddy yana ta murmushi amma baya iya yi mata doguwar magana sai ita ce take tayi.

Fahimtar da nayi cewa yau surutu take ji sai na fara tsoron kar ta bawa Daddy labarin hadadden gayen da yazo gurina dazu, Allah ya taimake ni dai bata bashi labarin ba har su uncle Ahmad suka shigo tare da Umma, bisa jagorancin Hassan. Suna shigowa Mustapha ya gaishe su ya fita. Na sauko kasa nima na barwa uncle Ahmad kusa da dan wan sa ya zauna ya
gaishe shi, Daddy ya hade rai ya amsa sannan ya dauke kansa gefe, Umma ma ta galshe shi tare da duba jikin sa ya amsa mata itama babu yabo babu fallasa. Uncle Ahmad ya fara inda indar bashi hakuri dan ya fahimci fushi yake yi, Umma tana kokarin taya shi. Daddy yace "sai da Safiyya taje tayi maka magana sannan zaka zo ka duba ni?" Umma tace "yaje asibiti ai, lokacin baka sani ba", Daddy yace "bai san gida na ba kenan sai asibiti ya sani? Ke ma baki san gida na ba?" suka cigaba da bashi hakuri mu dai sai muka tashi muka koma cikin gida.

A parlor muka zauna, su Mommy duk suna zaune banda Mustapha, na gaya wa Mommy zancen zuwan su uncle amma sai naga ta dauke kai tana bata fuska tare da magana kasa kasa. Muka cigaba da zama muna hirar mu da Salima tana bani labarin ita ma shirye shirye graduation dinsu da suke tayi, sai
na samu kaina da tunanin nima fa da yanzu ina shekarar karshe a jami'a, ko zan koma watarana? Na samu kaina da tunanin kawayen da nayi a MD wadanda yanzu duk na watsar da su saboda yawan
tambaya ta dalilin barin makaranta ta da suke yi da kuma tambayata ranar da zan dawo. Nayi ajiyar zuciya ina tuna shekaru bitu da yan watannin da nayi a makarantar, they were the most carefree days of my life,

Muna nan zaune sai ga Mustapha ya shigo, yana zama sai naga ramla cousin din Safina da take gidan ta ta shigo itama tare da wadansu mata da na lura yan aikin Safina ne, na cigaba da baza idon ganin Safina sai naga bata shigo ba, na mayar da hankali na kan Mustapha sai naji yana. ce da Mommy, "gasu nan na dauko su, jikin ta zai gaya mata ai" Mommy ta bisu da kallo suna gaisheta tana amsawa dai dai sai ta kira Esther tace ta kaisu dakin da zasu zauna, tace da Ramlah ita kuma ta kai kayanta sama inda suke sauka in sun zo. Sai da suka tafi sannan tayi kwafa tace "zata san da ni take yi ne. Bani na kai mata yan aikin ba? To na dauke kayana, sai inga yadda zata kula da gidan da kuma kanta da hannu daya da kafa daya" Hassan da yake gefe yayi dariya "Allah sarki yaya Safina, yau ta taro match da Mommy" Mustapha yace "ita ta ja wa kanta ai, ni bana tausayin ta, har da
hawayen ta kuwa da nace nazo daukan su, nace mata tazo mu taho tare amma yarinyar nan ta ki" Mommy tayi kwafa "ba zata zo ba ai, babu yadda banyi da ita ba nima fa, Dazu ma sal da na kira ta a waya na kare mata zagi tas amma kamar da dutse nake"

Sai na koma kan kujera na kwanta na rufe har kafafuwana da hijab din jikina, jikina ya bani dalilin komawar Safina gidan Muhammad ba wai dan shi ko dan ita bane ba, ta koma ne dan ni, dan ta san hakan zai bata min rai kuma tana ganin cewa in dai ta fito to zata rage mana wahalar convincing iyayen mu akan
maganar mu, zaman ta a gidan zai karawa shiga ta gidan wahala. Mommy dai ta jera tsaki da kwafa sun kai cikin charbi, aka jima tace "kuma wannan dan iskan yaron ba taimaka mata zai yi da komai ba wallahi, Allah ya sa ma ya zauna a gidan" babu wanda yace komai sai kuma tace "Hussain ka shirya ka je ka kwana a gurinta, yau dai kadai kafin gobe in san yadda zanyi da ita" Hussain ya bude ido da sauri "mommy ni kuma? Yanzu fa kika aika aka dauko su Ramlah sai kuma ki ce ni inje? Ni me zan iya yi mata a gidan?" Mommy ta hau shi da fada "eh kai din nace kaje, ko ba zaka je ba? Ai ba aiki nace kayi mata ba, kawai kwana zaka taya ta zuwa gobe mu ganj" Hussain ya tura baki yana magana kasa kasa tace "wallahi idan ba ka mayar da bakin nan dai dai ba sai nazo na fasa shi. Marar kunya fitsararre", Ya mike ba tare da yayi wa
kowa sallama ba ya fita, sai Hassan ya tashi ya bishi, ta harari bayan Hassan din tace "na ga kashin awaki ma karewar hadin kai".

Shigowar Umma ce ta katse mata maganar ta, ta kara hade rai, Umma ta zauna suka gaisa sama sama ta tambayeta jikin Daddy sai ta tashi tace Salima ta zo su tafi, nima na tashi na raka su waje har zuwa bakin mota nayi musu godiyar zuwan da suka yi, uncle Ahmad yace min ya ga sakona kuma ya gode, zamu karasa maganar ta waya, na gyada kai kawai suka tafi ni kuma a koma cikin gida. Amma sai na koma part din daddy, na tarar shi kadai ne, yana duba wani abu a wayar sa amma yana gani na sai naga yayi sauri ya kife fuskar wayar a kasa sannan ya bata rai kamar babu abinda yake yi, nayi kamar ban gani ba nima sai na zauna a gabansa na tambaye shi saukin jikinsa ya amsa min da cewa yaji sauki sosai, muka danyi maganar feeding tube din da za'a saka masa da kuma
breathing machines din da za'a siyo. Sai kuma yace "Ahmad ya ce min kin mayar masa da aikin sa" na sunkuyar da kaina sannan na dago nace "I never
wanted to take it. Na fadi maganar ne cikin bacin rai sanda na fahimci yana kokarin goyon bayan Mukhtar.but aikin sa nasa ne except idan shine da
[07/01, 10:46 pm] +234 906 816 1960: ❤️‍🩹SAFIYYA ❤️‍🩹


Episode Fifty Six: The Talk

Har na shiga gida da murmushi a fuskata, ina jin sansa a raina sosai sannan kuma at the same time ina jin haushinsa saboda komawar matarsa gidan sa, sai dai ni kaina nasan kishi ne ya saka ni jin haushin ba komai ba, and I asked myself "idan auren ya tabbata, am I ready to share him with Safina?" nayi sauri na kawar da wanna tunanin daga raina sannan nayi replacing dinsa da tunanin ciwon Daddy. Part din sa na wuce, na tarar yana zaune akan gado an saka masa pillows a bayan sa yana kallon tv yana sauraron karatun Alqur'anin da yake fitowa daga ciki, a hankali bakinsa yana motsawa alamar yana bin karatun. Na zauna a kasa a gabansa nima na cigaba da binsu. Sai kuma na tuna da Salima da muka zo tare, na dauki waya ta na tura mata message na gaya mata inda nake na kuma gaya mata zata iya shigowa. Ba'a jima ba sai gata nan ta shigo, ita ma ta samu guri ta zauna a gefe na ta cigaba da bin karatun kamar yadda ta tarar muna yi.

Hussain ne ya shigo, ya sanar mana da cewa lokacin sallah yayi sannan ya dauko bowl yazo ya fara yiwa Daddy alwala, daga nan muka koma cikin gida muka tafi dakina tare mukayi alwala muka yi sallah, Bayan mun idar ne Salima ta tashi tana ninke sallayar da tayi using tace "wai safiyya da gaske wancan gayen kike jawa aji?" na danyi murmushi nace "shi waye da ba za'a ja masa aji ba?" Tace "ya hadu, nake gaya miki ya hadu, most girls will sell their kidney to have him look at them" nayi dariyar yadda tayi maganar nace "Allah ya basu sa'a, now forget about him mu sauka kasa mu ci abinci. I am hungry" muka sauko muka zauna a dining amma still bata daina maganar sa ba "dan kuka
yi aure wato za'a ga kyawawan yaya" nayi murmushi kawai bance komai ba dan bana son yin maganar anan sai ta sake cewa "I wanted auren ki da Yaya Mukhtar ya dore, I was even picturing the nephews and nieces da zaki haifa min, amma Allah ya fi mu sanin dai dai. I wish you happiness, where ever and with who
ever" naji dadin maganar ta nace "ameen, thank you", Na fahimci siblings din Mukhtar basu san gaskiyar abinda ya raba mu ba, ban san me iyayen suka gaya
musu ya faru ma. Maybe shi yasa na fahimci yaya yana jin haushina dan shine ya tarar da yadda na daure yayansa tsirara akan gado.

Da sauri muka ci abincin muka koma wajen Daddy, muka tarar Mustapha yana bashi abinci sai na zauna a gefen gadon ina kallon su har yace ya ishe shi aka ajiye bowl din. Salima ta gaishe shi ya amsa mata tare da mika mata hannu yana murmushi, taje ta saka hannunta a cikin nasa ya tambaye ta ina Salim sai tace
yana school, da yake boarding yake yi a Lagos, sai ta kama yiwa Daddy hirar Salim din da irin dramar da suke sha idan yazo hutu, yana shekarar sa ta karshe ne yanzu. Daddy yana ta murmushi amma baya iya yi mata doguwar magana sai ita ce take tayi.

Fahimtar da nayi cewa yau surutu take ji sai na fara tsoron kar ta bawa Daddy labarin hadadden gayen da yazo gurina dazu, Allah ya taimake ni dai bata bashi labarin ba har su uncle Ahmad suka shigo tare da Umma, bisa jagorancin Hassan. Suna shigowa Mustapha ya gaishe su ya fita. Na sauko kasa nima na barwa uncle Ahmad kusa da dan wan sa ya zauna ya
gaishe shi, Daddy ya hade rai ya amsa sannan ya dauke kansa gefe, Umma ma ta galshe shi tare da duba jikin sa ya amsa mata itama babu yabo babu fallasa. Uncle Ahmad ya fara inda indar bashi hakuri dan ya fahimci fushi yake yi, Umma tana kokarin taya shi. Daddy yace "sai da Safiyya taje tayi maka magana sannan zaka zo ka duba ni?" Umma tace "yaje asibiti ai, lokacin baka sani ba", Daddy yace "bai san gida na ba kenan sai asibiti ya sani? Ke ma baki san gida na ba?" suka cigaba da bashi hakuri mu dai sai muka tashi muka koma cikin gida.

A parlor muka zauna, su Mommy duk suna zaune banda Mustapha, na gaya wa Mommy zancen zuwan su uncle amma sai naga ta dauke kai tana bata fuska tare da magana kasa kasa. Muka cigaba da zama muna hirar mu da Salima tana bani labarin ita ma shirye shirye graduation dinsu da suke tayi, sai
na samu kaina da tunanin nima fa da yanzu ina shekarar karshe a jami'a, ko zan koma watarana? Na samu kaina da tunanin kawayen da nayi a MD wadanda yanzu duk na watsar da su saboda yawan
tambaya ta dalilin barin makaranta ta da suke yi da kuma tambayata ranar da zan dawo. Nayi ajiyar zuciya ina tuna shekaru bitu da yan watannin da nayi a makarantar, they were the most carefree days of my life,

Muna nan zaune sai ga Mustapha ya shigo, yana zama sai naga ramla cousin din Safina da take gidan ta ta shigo itama tare da wadansu mata da na lura yan aikin Safina ne, na cigaba da baza idon ganin Safina sai naga bata shigo ba, na mayar da hankali na kan Mustapha sai naji yana. ce da Mommy, "gasu nan na dauko su, jikin ta zai gaya mata ai" Mommy ta bisu da kallo suna gaisheta tana amsawa dai dai sai ta kira Esther tace ta kaisu dakin da zasu zauna, tace da Ramlah ita kuma ta kai kayanta sama inda suke sauka in sun zo. Sai da suka tafi sannan tayi kwafa tace "zata san da ni take yi ne. Bani na kai mata yan aikin ba? To na dauke kayana, sai inga yadda zata kula da gidan da kuma kanta da hannu daya da kafa daya" Hassan da yake gefe yayi dariya "Allah sarki yaya Safina, yau ta taro match da Mommy" Mustapha yace "ita ta ja wa kanta ai, ni bana tausayin ta, har da
hawayen ta kuwa da nace nazo daukan su, nace mata tazo mu taho tare amma yarinyar nan ta ki" Mommy tayi kwafa "ba zata zo ba ai, babu yadda banyi da ita ba nima fa, Dazu ma sal da na kira ta a waya na kare mata zagi tas amma kamar da dutse nake"

Sai na koma kan kujera na kwanta na rufe har kafafuwana da hijab din jikina, jikina ya bani dalilin komawar Safina gidan Muhammad ba wai dan shi ko dan ita bane ba, ta koma ne dan ni, dan ta san hakan zai bata min rai kuma tana ganin cewa in dai ta fito to zata rage mana wahalar convincing iyayen mu akan
maganar mu, zaman ta a gidan zai karawa shiga ta gidan wahala. Mommy dai ta jera tsaki da kwafa sun kai cikin charbi, aka jima tace "kuma wannan dan iskan yaron ba taimaka mata zai yi da komai ba wallahi, Allah ya sa ma ya zauna a gidan" babu wanda yace komai sai kuma tace "Hussain ka shirya ka je ka kwana a gurinta, yau dai kadai kafin gobe in san yadda zanyi da ita" Hussain ya bude ido da sauri "mommy ni kuma? Yanzu fa kika aika aka dauko su Ramlah sai kuma ki ce ni inje? Ni me zan iya yi mata a gidan?" Mommy ta hau shi da fada "eh kai din nace kaje, ko ba zaka je ba? Ai ba aiki nace kayi mata ba, kawai kwana zaka taya ta zuwa gobe mu ganj" Hussain ya tura baki yana magana kasa kasa tace "wallahi idan ba ka mayar da bakin nan dai dai ba sai nazo na fasa shi. Marar kunya fitsararre", Ya mike ba tare da yayi wa
kowa sallama ba ya fita, sai Hassan ya tashi ya bishi, ta harari bayan Hassan din tace "na ga kashin awaki ma karewar hadin kai".

Shigowar Umma ce ta katse mata maganar ta, ta kara hade rai, Umma ta zauna suka gaisa sama sama ta tambayeta jikin Daddy sai ta tashi tace Salima ta zo su tafi, nima na tashi na raka su waje har zuwa bakin mota nayi musu godiyar zuwan da suka yi, uncle Ahmad yace min ya ga sakona kuma ya gode, zamu karasa maganar ta waya, na gyada kai kawai suka tafi ni kuma a koma cikin gida. Amma sai na koma part din daddy, na tarar shi kadai ne, yana duba wani abu a wayar sa amma yana gani na sai naga yayi sauri ya kife fuskar wayar a kasa sannan ya bata rai kamar babu abinda yake yi, nayi kamar ban gani ba nima sai na zauna a gabansa na tambaye shi saukin jikinsa ya amsa min da cewa yaji sauki sosai, muka danyi maganar feeding tube din da za'a saka masa da kuma
breathing machines din da za'a siyo. Sai kuma yace "Ahmad ya ce min kin mayar masa da aikin sa" na sunkuyar da kaina sannan na dago nace "I never
wanted to take it. Na fadi maganar ne cikin bacin rai sanda na fahimci yana kokarin goyon bayan Mukhtar.but aikin sa nasa ne except idan shine da
[07/01, 10:46 pm] +234 906 816 1960: ❤️‍🩹Safiyya❤️‍🩹


Episode Fifty Seven; The Talk 2


Not completely edited, my tire is tired 😂


He sat like a stone as I told him all that has happened to me tun ranar birthday dinsa da muka je cin abinci restaurant, na bashi labarin gaskiyar abinda ya faru da ni a ranar da kuma duk abubuwan da suka biyo bayan hakan, nayi amfani da kalmomin da nasan zai fahimci abinda nake nufi ba tare kuma dana bayyana abubuwa masu nauyi ba. Sai da na dangane har ga labarin yadda naji maganar aurensa da Safina da kuma haihuwar Junior sannan da dawowata Nigeria.

Na bashi labarin zargin Mukhtar da na fara yi, aurena da shi da kuma tabbatar da zargin nawa da nayi bayan auren zuwa rabuwar mu da conditions din da na dora Mukhtar din a kai dan kare martaba ta da ta Junior.

Har na gama maganganun nawa bai ce komai ba. Ni ma kuma ban iya daga kai na kalle shi ba har sai da na kai aya dan bana jin zan iya hada ido da shi a yanzu, bana jin zan iya sake hada ido da shi ma
gabakidaya.

Jin ya cigaba da yin shiru tsahon lokaci bayan na gama magana sai na mika hannu a hankali na kama hannun sa da nake gani ta cikin hawaye na, na kuma yi
kokarin kiran sunan sa, "Muhammad.......?." Naji hannun sa yayi zafi kamar na wanda yake cikin zazzafan zazzabi, Sai ya zame hannun na sa daga
cikin nawa da sauri sannan kuma ya mike da sauri kamar wanda aka watsa wa wuta yayi hanyar fita daga falon. Na mike nima da saurin ina jin wani irin tashin hankali da fargaba suna mamaye zuciya ta. Na mike rigarsa tare da kiran sunansa cikin karyayyiyar zuciya "Muhammad……….." Ya kwace rigarsa da karfi sannan cikin wata irin muryar da ban san shi da ita ba ya fara magana "I will kill him.... I will kill him.….. I will kill him...." Na fahimci wa yake nufi da him din, hakan kuma ya kara tayar da hankali na, na sake shan gabansa da sauri ina kuka sosai a lokacin,"Muhammad dan Allah ka tsaya, Muhammad Gidado..." Na fada ina
kokarin ganin ya kalle ni amma sai ya ture ni gefe daya ya saka hannu zai bude kofar sai na zagaye shi da hannayena na dora kaina a bayansa na kama kuka mai ratsa zuciya,

Ya tsaya first, sai kuma ya dauke hannunsa daga jikin handle din kofar tare da kife kansa a jikin kofar, ina jin yadda dukkan jikin sa yake karkarwa da wata irin
zuciya da ban san yana da irin ta ba. Mun jima a haka sai kuma ya juyo da sauri ya zagaye ni da nasa hannayen tare da kife fuskarsa a saman kaina ya kama kuka. Nima nawa kukan na cigaba, ban san adadin lokacin da muka dauka a haka ba,amma mun ci kukan mu mun gode Allah. Sai kuma ya sake ni ya zare hannuna daga jikin sa ya koma cikin falon ya zauna tare da juya fuskar sa gefe. Na fahimci baya son inga kukan sa ne, wai shi namiji, ni kuwa babu abinda ya dame ni in kuka yazo min a tsakiyar titi ma zan iya zama inyi kuka na in gama in tashi in tafi, wanda ya gani matsalar sa ce ba tawa ba.

Na koma nima na zauna a gefensa, sai dai har lokacin yaki yarda mu hada ido nima kuma ban shirya yin hakan ba dan haka ban kalli fuskarsa ba nace "Please
Muhammad, promise me one thing, dan Allah kayi min alkawarin ba zaka ko kalli inda Mukhtar yake ba. Please, wannan ita kadai ce alfarmar da nake nema a wajenka" ya goge fuskarsa yana girgiza Kai, sannan yayi ajiyar zuciya yace *I can't. I can't make a promise that I cannot keep" na zamo daga kan kujerar na sauko kasa gabansa "you can. Dan Allah. I went through a lot to keep you clean and away from all these. Please don't go and get your hands dirty by touching him. Daukan doka a hannun mu ba zata jawo mana komai ba sai......" Ya katse ni cikin fada tare da sake mikewa tsaye "kina nufin shikenan? Yayi a banza kenan? Kin barshi saboda kina da sayin zuciya and family dinki sun goya miki baya just because dan uwa ne shikenan kuma magana ta kare? Shikenan babu abinda aka yi masa babu kuma abinda za'a yi masa?" Na mike nima "akwai abinda nayi masa Muhammad. Na kai shi kara grin alkalin alkalai na kuma tabbatar zai saka min. Ina zaune ne kawai ina jira. Sakayyar da Allah zai yi min ta fi hukuncin da kowanne irin alkali zai yanke a cikin alkalan duniyar nan. In ka taba shi yanzu hukunci zai dawo kanka ne kai kuma. Saboda baka da wani ground na shari'a da ya baka damar daukan hukunci akan abinda aka yi min. Please Muhammad, yadida na bar maganar nan ka barta kai ma. Idan da ace da akwai wata hanyar da zan bi mu wuce wannan level din ba tare da na gaya maka maganar nan ba Wlh ita zan bi. Idan da ace xan iya cire maka zafin da kake jl a zuciyar ka da na cire maka shi. You have no idea courage din da nayi amfani da shi wajen zama inyi maka wanna maganar"

Sai ya zauna a kasa a inda yake tare da dafe kansa da hannaye biyu a hankali ya ambaci "my God!" Nima sai na koma na zauna. Ya jima a haka yana rocking in one
place sannan ya dago kai yana kallona yace "you know what hurt me the most in all this? It is the fact that you went through all these ke kadai, without telling me Safiyya, You went through all that alone" ya karasa cikin karyayyiyar murya. Nayi shiru ina jin sabbin hawaye suna zubo min, ya cigaba "You should have
told me. You should have told me the moment it happened. You should have at least share all that burden with me but you chose to carry it alone. Saboda me? Saboda kina tunanin zan guje ki in naji
abinda ya faru ko kuma kina ganin ban kai matsayin da zaki gaya min bane ba?" Ya karasa tambayar cikin fada,

Na dago ina kallon sa, muka hada ido for the first time, idanunsa sunyi ja sun kumbura kamar zasu fado kasa, a hankali nace "i didn't tell you because I know exactly what you would do idan da kaji maganar" yace "and what is that?" Na lankwasa kai ina kallon sa hawaye yana bin fuskata nace "cewa zaka yi cikin ka ne. It would break you up to pieces but cewa zaka yi kai ne, cewa zaka yi naka ne Zaka yi hakan dan ka bani kariya kuma dan kayi forcing iyayen mu su bar mu tare".

Yace "then why didn't you let me do that? Yes, that's exactly what I would have done. Da kin barni nayi hakan da duk bamu zo wannan matsayin ba. Da magana ta wuce tuntuni" nace "da kuma iyayen ka har yanzu suna kallon ka da abin. Zasu yarda muyi auren but they will be very disappointed in you maybe har karshen rayuwar su akan abinda baka aikata ba. Yan'uwan ka, abokan ka, abokan aikin ka duk wanda ya sani ba zai kuma yi maka kallon mutumin kirki ba. Sunan ka zai baci akan abinda baka yi ba. And that's
something da ba zan taba yi maka ba a rayuwa"

Ya rufe idonsa tare da kwantar da kansa baya ya jingina shi a jikin kujerar da take bayan sa. Sannan a hankali yace "so you chose to lie to me. You chose to tell me that kina da aure. "I am married and I love my husband very much" ya karashe maganar cikin dacin rai, sai kuma ya juyo da kansa yana kallona yace "do you have any idea how much that hurt me?" Na girgiza kaina "it wasn't the best decision I know, But I wasn't thinking clearly. Tun daga samun cikin nan har zuwa haihuwar sa bana cikin hayyacina, Babu wani decision da nayi making a cikin lokacin da yake mai kyau ne except not telling you the truth, I mean, I tried to give up the innocent child for a close adoption a kasar da bama ta musulmai ba" na sunkuyar da kai na sannan na dago nace "I tried killing myself, twice" ya bude ido
sosai sannan ya gyara zaman sa yace "you told me kinyi kokarin cire cikin ko da a bakin ranki ne. Wannan ne second time din?" Na daga kafada nace "sanda kaje gidan mu ka gan ni tare da Mukhtar a mota, ya fita da motar, yana gudu a motar sosai and he said some bad words akan ka and I opened the door zan fita daga cikin motar".

Ya zaro ido sosai tare da rufe bakin sa da hannayensa, Fuskarsa cike da tashin hankali. Nace "na gaya maka wannan ne kawai dan ka fahimta kuma ka yafe min
maganganun da na gaya maka to break your heart dan ka rabu da ni" ya rike hannuna da sauri "ba maganar in yafe miki ake yi ba yanzu Safiyya. Promise me that you will never do something like that again" na gyada kai na "insha Allah", Sai kuma muka yi shiru for sometimes, kamar ya danyi calming down a little kuma ya dan fahimta duk da nasan sai yaje ya zauna ya tattauna da zuciyar sa sannan zai fahimta sosai ya kuma gane what he is getting himself into. Daga nan
kuma zai gane abinda ya kamata ya gaya wa iyayen sa, daga nan kuma zai san idan iyayen na sa zasu yarda da auren na mu or not, tunda shi ya sansu ya san abinda zasu dauka da wanda ba zasu dauka ba.

Mun jima a haka sannan ya ambaci sunana cikin sanyin murya "Safiyya" na dago kai na kalle shi sai na mayar da kaina kasa dan ba zan iya cigaba da kallon
jajayen idonsa ba. "I am sorry all this happened to you. Duk da har yanzu ban yarda cewa rashin gayamin was the best decision ba amma na fahimci girman soyayyar ki gare ni and na fahimci kin yi making that decision ne with my wellbeing in your mind, and I really appreciate that. And I will never take your love, understanding and care for granted. Kinji? Amma ina so kiyi min alkawari
saboda nan gaba, promise me you will never hide anything again from me. Through thick and thin, through joy and sorrow, for better or for worst, promise me we will always be together and look out for each other, Kiyi min wannan alkawarin kinji?"

Naji wata soyayyar sa tana karuwa a cikin zuciyata, shi a gurin sa wannan abin da na gaya masa bai ma kai abinda zai saka yayi considering rabuwa da ni ba. Shi kara jaddada min soyayyar sa yake yi a gare ni. Dama kuma na riga na san haka. But I want someone else to know. Dan haka na sake tambayar sa cikin karyayyiyar murya "Muhammad kamar kana manta wani abu. Ina da da. Dan da na haifa ba tare da aure ba. Wannan dan will always be attached to me and to yayan da zan iya haifa nan gaba. In kace zaka aure ni hakan yana
nufin abin zai shafe ka kai da yayan da zamu haifa nan gaba. Are you sure you want to........." Ya katse ni "I am more sure now than I have ever been. Babu abinda ya faru wanda yake laifin ki ko laifin shi yaron, kaddarar ku ce haka. Nima kuma soyayyar ki ita ce tawa kaddarar, kaddarar ki kuma ba ta rage ko kadan daga cikin tawa kaddarar ba sai ma karuwa da tayi. All I want to do now is to take care of you in tabbatar cewa ba ki sake zubar da hawaye ba sai na farin ciki" ,.

Na goge hawayen da suke bin fuskata, wadanda already na farin cikin ne ma. Ya sake matsowa kusa da ni. Yace "I want to marry you Safiyya. Will you marry me?" Na daga kai muka hada ido, murmushi yaso ya kubce min amma sai nayi sauri na rufe fuskata da hannuna na gyara mood dina sannan na bude fuskata a hankali nace "no".

Yayi shiru yana kallona fuskar sa cike da alamomin tambaya iri iri sai nace "I am sorry Muhammad. I am very sorry. This is the last part of maganar da zamu yi yau. And your answer is no. I love you so much, fiye da yadda kalmomin bakina zasu iya furtawa. Ba ni kuma da shakka akan son da kake yi min musamman yau
da ka sake tabbatar min. But I cannot marry you"

Ya koma da baya har sai da ya jingina da jikin kujera sannan ya zauna. Emotions dinsa mixed up. "Why?" Ya tambaya at last. Na fara kuka "saboda Daddy yace in
rabu da kai. Yace ba zai aura min kai ba. Ya kuma ce ko bayan ransa bai yarda in aure ka ba. Ba zan iya bujirewa maganar sa ba. He went through a lot a kaina, Ina so nima in faranta masa rai in yi masa
biyayya ko da kuwa hakan yana nufin zan rasa abu mafi soyuwa a gare ni. Dan Allah Muhammad kayi hakuri...…”.

Sai ya dafa kujera ya mike bai ce min komai ba, sai kuma jiri ya debe shi ya tafi zai fada kan kujura, na tafi gurinsa da sauri kamar zan rike shi sai ya daga mun hannu amma sai ya zauna akan kujerar, Na cigaba da kokarin yi masa magana Gidado, Iyayen mu sun fi koma muhimmanci a gare mu. Mama da Abba ba sa so. Daddy baya so. Both our families ba sa so. Soyayyar da muke yiwa junan mu is not enough especially in zata bata musu rai dan farin cilkin su yafi namu muhimmanci. Dan Allah ka fahimta." Ya dago kansa ya dafe da hannun sa yace "are you telling me inje in cigaba da zama da Safina kenan? Makaryaciya, mayaudariya munafuka? Ita kike so in zauna da ita ta haifa min yaya? And you? Who are you going to marry? Ko akwai wani ne dama da ban sani ba?

Na girgiza kaina tare da kneeling down a gabansa. “Babu kowa Muhammadu. Babu kowa a zuciya ta sai kai. Nima ban san wanda zan aura ba. Na yanke hukuncin zan bawa Daddy zabi ne kawai, duk wanda yaga ya dace sai ya aura min in dai hakan zai saka shi farin ciki. Dan Allah kai ma kayi haka. Ka bawa su Abba zabi”.

Ya mike tare da daukan key din sa sai na mike na kwace "dan Allah kar kayi fushi da ni Muhammad, It hurts me a lot to make this decision amma dole ne. Kai ne farin ciki na, amma farin cikin Daddy yafi nawa muhimmanci a gare ni. Dan Allah Muhammad kayi hakurj" ya miko min hannu, still expression dinsa unreadable '"bani key dina" na matsa baya ina girgiza
kai "ba zan barka kayi driving a wannan yanayin ba" cikin fada yace "you don't care. Don't pretend that you do" nace "but I do, more than you know" ya tako ya dawo gaba na ya tsaya yace "do you truly love me?" Na gyada kai na da sauri "fiye da yadda kake tunani" sai yace "then I will not give up. Ke kiyi abinda kike tunanin shine dai dai, nima zanyi abinda nake tunanin shine dai dai. Kamar yadda nace, soyayyar ki kaddara ta ce, then there is no turning back".

Ya juya ya sake yin hanyar fita nace "key din ka yana hannuna, I will not let you drive" yace "ki rike. Zan shiga ta haya".

Daga haka ya fita. Na koma na zauna akan kujera tare da dafe kaina ita share sauran hawayen fuska ta sai kuma na mike da sauri na bi bayansa, Sanda na hango shi har ya kusa kai wa bakin gate,. Tun daga tafiyar sa ma zaka gane cewa hankalin sa ba'a tare da shi yake ba, na ga Malam Ya'u ya bude masa kofa yana bin sa da kallo har ya fita ya rufe kofar sannan ya juyo muka hada ido, ya jima yana kallona nima sai kuma ya
koma gurin zamansa ya zauna.

Na sauke ajjiyar zuciya sannan na juya zuwa cikin gida cikin sauri mai hade da sassarfa. Na san next stop din Malam Ya'u shine gurin Daddy, a matsayin sa na loyal maaikacin Daddy da ya dauki shekara da shekaru suna tare, yana taya shi looking out for his family ne a lokacin da shi Daddyn yake kwance babu lafiya. Ni kuma haka nake so dama. Ina sane na bar shi ya ga komai. Babu kowa a parlour saboda an fara kiraye kirayen sallar magrib dan haka na wuce sama zuwa dakina na shiga na rufe kofa. A bakin gado na zauna tare da dafe kaina ina kokarin bitar maganganun mu da Muhammad amma na kasa saboda kaina gabaki daya ya toshe ya cunkushe. Hankali na gabakidaya yana kansa, Fatan kawai da nake yi shine ya fahimci
message din da na tura masa, ya fahimci ba da gaske nake ba cewar da nayi ba zan aure shi ba,

Na je window na bude labule amma bana iya hango shi. Ko ya samu abin hawa? Na hango Baba Ya'u a bakin gate yana alwala, na danyi murmushi kadan, na san yana yin sallah zai tafi gurin Daddy ya kai rahoton zuwan Muhammad kuma ya gaya masa inda muka zauna ni da shi. Ina sane nake barinsa yana ganin mu, ina sane kuma na zabi inda zamu hadu da Muhammad din dan ina so Baba Ya'u ya ga shigar mu. Dan ina so ya gaya wa Daddy exactly inda muka zauna.

Na fahimci cewa it took Daddy long to see maganganun mu da Mustapha saboda cameras din suna da yawa shi kuma bashi da isasshen lokaci, kuma bai san wacce Camerar zai duba ya samu wani abun kirki ba. Yanzu kuwa Baba Ya'u zai gaya masa exact camera din da zai duba da kuma exact time din da muka zauna. And he will see and hear everything.

And then he will know gaskiya akan komai da komai. Ni kuma nawa yanxu shine inyi folding arms dina in jira matakin da zai dauka. Na koma bakin gado ina shafa idanuna da suka kumbura saboda kukan da na sha yau, na dauki wayata na gwada number din Muhammad amma har ta gama ringing dinta bai dauka ba. Na sake jin hankali na ya tashi a kansa, na kara kira

still shiru sai na tura mass text

"Baby please call me as soon as you see
this. I need to explain things"

Na dan jira kadan sai kuma na tashi na shiga toilet nayi alwala ina gaya wa kaina maybe shima ya tsaya sallah ne ko kuma har yanzu yana hanya. Sai da na idar da sallah na gama adduoi na sannan na sake daukan wayar na duba amma babu call dinsa kuma bai yi replying message dina ba. A lokacin iya kololuwar tashin hankali na shige ta, na zauna akan gado na dafe kaina "ya Rabbi" na ambata a hankali.
Kamar daga sama naji ana buga kofar dakina, na tashi na bude na ga Hassan a tsaye yana kallona yace "Yaya ki zo inji Daddy" sai da naji kamar dan karamin
fitsari zai fito, na dafe kofa ina kallon Hassan da shima yake kallona da alamar tambaya yace "are you okay" na gyada masa kai da sauri sannan na koma cikin
dakin tare da rufe kofar na jingina da jikinta. Hankali na duk ya rabu gida biyu, ban yi tsammanin samun kira daga Daddy yanzu ba, sannan kuma ina tunanin halin
da Muhammad yake ciki.

Sai da na shiga toilet na dan watsa wa fuska ta ruwa duk kuwa da cewa babu abinda tayi sannan na fita da waya ta a hannu still expecting a call from Muhammad, Ina zuwa zan shiga part din Daddy muka hadu da Baba Ya'u yana fitowa, Ya bani hanya na wuce sannan ya bini da kallo. Sai na sauke ajjiyar zuciya tare da bismillah sannan nayi sallama na shiga,

Yana zaune akan kujerar sa. Kallo daya zaka yi masa kasan yana cikin damuwa mai yawa. Na zauna a kasa ina addu'ar wannan damuwar da zan saka shi a ciki ta
zama ta karshe, nace "Daddy ganj" ya kalle ni ya dauke kai, kamar ba zaiyi magana ba sai kuma yace "waye yazo gurin ki da zu?" Nayi shiru bance komai
ba. Ya sake cewa cikin karyewar murya "ba kya jin magana Safiyya. Me yasa ba kya jin magana ne wai? Yanzu idan Sa'adatu ta ga mijin Safina yazo gurin ki zance kina ganin zata ji dadi?" Nace "Daddy kayi hakuri, na kira shi ne na gaya masa abinda kace. Na gaya masa ba zan aure shi ba. Ba zan kara bata maka rai ba insha Allah Daddy. Duk abinda ka ce shi zany" yayi shiru yana studying dina sannan ya sake cewa "me motarsa take yi a gidan?" Nace "he couldn't drive after I told him that. Shine ya bar ta anan. Zai aiko a dauka" Daddy yay dan murmushi ace "lies........ He wants you to believe that. He wants you to think he care" nayi shiru ban ce komai ba sai ya ce "ki dauko key din motar Ki bayar a kai Bana son yayi amfani da wani uzuri ya sake dawowa gurin kj" na gyada kai sannan na mike zan fita yace "Safiyya" na juyo yace "you did good. Allah yayi miki albarka" a hankali nace "'Ameen ya Rabbi".

Sama na koma na dauko key din, ban sauko ba sai da na sake kiran number din Muhammad, amma yanzu bata ma shiga, na sauka da key din na bawa one of my
guards na bashi address din da zai kai. Duk zirga-zirgar da nake yi Mommy tana parlour tana kallona bata ce min komai ba kuma bata tambaye ni komai ba. Dama yanzu ta ja baya sosai da yi min magana tun akan issue din Mustapha, a fahimta ta kamar tana zargin ina da hannu akan korar Mustapha da Daddy yayi dan a rushe maganar auren mu.

Ban zauna a parlourn ba sai na koma dakina. Na zauna akan kujera ina jujjuya wayata hankali na a tashe. Nayi ajjiyar zuciya tare da lumshe ido na ina bitar maganganun mu da Muhammad. Tabbas maganar da ya fada min akan Safina ta taba zuciya ta sosai, fiye da yadda nayi tunanin zata taba ni din. All my life ba zan iya tuna wani abu da nayi mata da nayi deserving abinda tayi min ba. At least ta gaya masa gaskiya mana? Ko da gaskiyar ta gaya masa ba ta kyauta min ba ballantana wanna irin karya haka. Wato
ita duk halin da na shiga da abin da ya same ni bata ji tausayi na ba ma sam, maybe ma murna tayi da faruwar komai, Nayi tunanin labarin da ya bani na yadda taje social media tana cigiyar sa. Yace Mufida tace kusan shekaru biyu da suka wuce ne. Lokacin ma muna tare da Muhammad, lokacin muna tsakiya da kafa soyayyar mu, wato tun a lokacin tayi niyyar raba mu, kamar yadda Muhammad ya fada zata iya yiwuwa tun a lokacin ta dauki number dinsa a waya ta ta kira shi tayi masa tayin soyayyar ta yayi rejecting shi kuma, Shi yasa ta cigaba da yi min bincike with any opportunity da ta samu, looking for something that will link her to him.

Na sake kiran number din Muhammad, still a kashe, ji nake yi a kamar in zauna inyi ta kuka. Sosai nake so inji muryarsa. So nake inyi masa bayanin plan dina da
kumaoutcome din da nake saka rai. So nake in kwantar masa da hankali in kuma jaddada masa soyayyar sa da take cike a zuciya ta.[07/01, 10:46 pm] +234 906 816 1960: Na sake kiran number din Muhammad, still a kashe, ji nake yi a kamar in zauna inyi ta kuka. Sosai nake so inji muryarsa. So nake inyi masa bayanin plan dina da
kumaoutcome din da nake saka rai. So nake in kwantar masa da hankali in kuma jaddada masa soyayyar sa da take cike a zuciya ta.

Him👳🏻‍♀️

The last few weeks have been a rollercoaster of emotions for him. Daga wancan sai wancan sai wancan., And abubuwan ba Wai suna zuwa ne one after the other ba, suna zuwa ne wani issue din a cikin wani kuma har yanzu babu wanda ya samu yayi solving, dan duk issues din are linked to one thing, to one person, Safiyya.

Bai gama warkewa daga shock din karairayin da Safina ta gaya masa ba, wadanda ya san cewa Karya ce amma kuma still akwai something in them da yake son jin gaskiyar sa daga bakin Safiyya, Sai dai sanda ya samu Safiyya kuma har tayi alkawarth fada masa gaskiyar komai akan ta sai ta fara da labarin mahaifiyar ta da yadda ta rasa kowa nata. Labarin ya tabashi sosai ya kuma saka masa tausayin Safiyyan a cikin zuciyar sa, knowing bata da kowa a bangaren uwa. And then a zaman su na biyu sai ta bashi labarin da yafi wancan ruguza tunanin sa, labarin kasan cewar ta mai kudi fiye da tunanin sa. A Daren kusan kwana yayi bai yi bacci ba yana jujjuya maganar a cikin kansa wannan wani abu ne dabai taba tunani ba.

A matsayin sa na namiji, plans dinsa was always been to be a provider to his family, to work hard and take care of his wife and kids and treat them like queen,princes and princesses kamar yadda yaga Abban sa yana yi, amma yanzu knowing Safiyya bata ma cikin class dinsa a kudi sai abin yazo masa bazata, shi bamai kudi bane ba. Iyayen sa dai suna da kudi amma yanzu ne kokarin kafa roots dinsa da tallafin iyayen na sa.

Amma soyayyar da yake mata sai ta saka ya hadiye wannan fear din, ya rarrashi kansa da cewa tana son shi kuma ba zata ke raina abinda zai ke providing mata ba, hakan kuma sai ya kara masa zeal din doubling efforts dinsa na neman kudi to meet up with her.

Amma kuma a ransa ya son Cewa Wannan
maganar ba ita ce wadda yake anticipation din ba, yasan cewa the worst is yet to come. Duk da zullumin da zuciyar sa take ciki hakan bai hana shi cigaba da gaya mata yana son suyi maganar ba, dan yasan dole sai sunyi sannan sannan zasu samu fahimtar juna. A gefe daya kuma ga issue din Safina da ta zame masa karfen kafa, dan yanzu ma tana gidan su tana cigaba da jinya acan tunda taki tafiya gidan su, ko kuma yace gidan su Safiyya. Su kuma iyayenta sunyi fushi sun kwashe mata masu kula da ita.

A daya bangaren kuma ga iyayensa da har yanzu suke fushi da shi akan dukan Safina da yayi, da kuma soyayya da suka san cewa yanayi da kanwar matar sa, Yayi yayi su bashi damar yi musu bayani amma sunki, su a nasu ganin wannan fushin da suke yi da shi shine punishment dinsa kuma shi zai saka ya dawo cikin hayyacin sa ya fahimci abínda yake yi ba dai dai bane ba.

Su a ganin su Safiyya ta kashe auren ta ne dan ta ga ya auri yayarta, shine ta dawo ba wai dan tana son sa ba sai don ta kashe masa aure, and they fear she will
break his heart again. Wannan yasa duk kokarin bayanin da yake yi musu ba sa ganewa, su a gurin su blind love yake yiwa Safiyya dan haka baya gane aibun ta baya ganin laifinta sam.

Dan breakthrough din da ya samu kawai shine kasancewar Mama yanzu ta gane Safina makaryaciya ce, kuma ranta ya kara baci akan hakan sanda Safina tayi masa sharrin kade ta da mota, in fact yanzu ya fahimci Mama tana yiwa Safina abubuwa ne kawai out of the goodness of her heart kuma saboda matsayin matar sa da take dashi amma ba Wai dan tana son ta kamar da ba. And a ransa yasa cewa ta wannan bangaren ne zai samu waraka daga wannan virus din mai suna Safina da ya dabaibaye shi,

And then one day Safiyya called him to their house tace zasu yi maganar da yake ta dreading, Tun kafin yaje gabansa yake faduwa, ya tabbatar zai ji abubuwan da zasu taba masa zuciya har bama ya son
yayi hasashen abinda zai ji din, but he tried to get as ready as he can, Ya shirya gaya mata dukkan gaskiyar sa, ya kuma yi fatan itama zata gaya masa ba tare da ta boye wani abu ba,

Sai dal yana packing a cikin gidan nasu ya ga sakon ta, wai zata gaya masa gaskiyar komal amma kuma maganar ta ta karshe ba gaskiya bace ba, And that destabilized him, Wacece maganar karshe din? And
why?

Amma bai ga fuska da space din tambayar ta ba, ita ma ya ga tsoro da tashin hankali a fuskar ta sanda ta fito, and more than anything, ya ga soyayyar sa. Wannan kuma shine zaren da yake rike da hope dinsa, as long as yana ganin soyayyar sa a cikin idonta, he will never give up

They talked, he told her everything kamar yadida yayi wa kansa alkawari, maganar karshe akan abinda Safina ta fada a kanta ta taba ta sosai har sai da yay nadamar gaya mata, wannan kuma ya sake
tabbatar masa da cewa Safina karya take yi. But then kamar yadda yayi tunani, there is something there, Wannan something din kuma shine abinda yayi finding out when she told him her own side of the story.

She was raped. And kuma a yanzu haka tana da da, alive and healthy.

Wanna labarin is one of the worst news da Muhammad ya taba samu a rayuwar sa ta duniya. But what was more terrifying is what she went through. Shi bai tana jin wannan tashin hankalin ba. She went through hell on earth ba tare kuma da tayi laifin komai ba. And she went through it alone, And she went through part of that to protect him from taking blame for something he didn't do.

Wanna labarin ya ruguza dukkan tunanin sa, ya rusa dukkan katangar da ya zagaye emotions dinsa da ita and he cried with her. Sai dai kuma labarin ya kara masa soyayyar ta a cikin zuciyarsa, if that is
possible, dan dama zuciyar a cike take da soyayyar ta ta. Ya kuma kara fahimtar kyawun zuciyar ta da har ta iya rabuwa da Mukhtar yake cigaba da yawo freely a
gari. Ya dauki aniyar sai Mukhtar ya yi nadamar abinda yayi mata, ita kuma tayi kokarin dakatar da shi kuma ya dakata din amma kuma ba wai ya bar maganar bane ba, ya tsaya ne dan su samu damar kammala maganar su, su kuma samu damar rarrashin juna.

Hakan kuwa suka yi. After re-pledging their eternal love for each other, sai ya sake tabbatar mata da kudirin sa na son auren ta but to his biggest surprise sai tayi rejecting, tace wannan ita ce last maganar da zasuyi. Ta kuma ce rabuwa ma zata yi dashi dan yin biyayya ga mahaifinta.

Wannan maganar tata ce ta saka ya tuna da sakon da ta tura masa kafin ta fito wajensa, and a take ya fahimci abinda yake faruwa, someone was watching
them, probably Daddy,

Wannan tunanin ya kara daga masa hankali, yaji babu abinda yake so irin ya fita daga wajen tun kafin kansa ya buga sabada rudanin da yake ciki, amma sai ta
karbe key dinsa ta cigaba da kokarin gayawa wanda yake jin su cewa she was breaking up with him. He told her tayi abinda take ganin dai dai ne shima zai yi
abinda yake ganin dai dai ne.

Sanda ya fito daga gidan jiri ne kawai yake diban sa, maganganu ne kawai suke
overlapping a cikin kansa ya ma rasa wacce zai dauka yayi tunani akai. Wani bangaren a zuciyarsa haushin Safiyya yake ji, me yasa ba zata gaya masa cewa
wani yana jin su ba? Haushin kowa ma yake j, including shi kansa. Tabbas, soyayyar Safiyya ita ce babbar jarabawar sa a rayuwa.

Taxi ya samu ya shiga sannan ya bawa driver din address din gidan sa, gidan da ya gina da sunan Safiyya, shi yasan ba zai iya zuwa gida a cikin wanna halin da yake ciki ba, dan kallo daya Mama zata yi
masa ta saka shi a gaba da tambayar me ya same shi, daga ya ambaci sunan Safiyya kuwa shikenan lamari ya lalace dan zata iya cewa ma Safiyya ta lashe mata kurwar da. Plus in yaga Safina a yanzu zai iya shaketa har sai ta daina numfashi.

Gidan nashi aka kai shi kamar yadda ya bukata, sai dai shi kansa drivern ya fahimci ba'a cikin hayyacin sa yake ba, ya tambaye shi ko bashi da lafiya amma bai
amsa masa ba, Da kyar ya dauko kudi ya sallami driver din sannan ya juya cikin hada hanya ya karasa gate yay knocking. Mai gadi da yake shirin tafiya masallaci ya bude, sannan ya tsaya yana kallon sa cikin damuwa "ranka ya dade baka da lafiya ne? Ko jikin ne?" Bai amsa masa ba shima ya wuce shi yayi hanyar shiga cikin gidan, sai dai kafin ya karasa kofa ya yanke jiki
ya fadi a gurin,

Mai gadin ya karaso kansa da sauri yana girgiza shi tare da karanto duk adduoin da suka zo bakin sa. Sama sama Muhammad yake jinsa, ya fara kokarin sake tashi amma sai yaga kamar mai gadin ya zama
mutum hudu duk masu kama daya, ma'ana hudu hudu yake gani, ya tabbatar kuma yana sake tashi faduwa zai yi. Ya tuno da maganar Piya ranar da ya taho gidan da niyyar zai kwana shi kadai "in wani abun ya same ka fa?"

Ya mayar da idonsa ya rufe sannan ya cewa mal gadin "kirawo min Abba na"., A cikin kan sa yaji wayarsa tana ringing da kidan da ya sakawa Safiyya. Bai fito da wayar ba ma ballantana ya dauka Ya tuno maganar da ya gaya mata ta karshe, tayi abinda take ganin dai dal ne shima zai yi abinda yake ganin dai dai ne. She definitely had a talk with him and Daddy at the same time, shima yanzu he is going to have a talk with Abba.

Yana jin mai gadin ya gama waya da Abba yana gaya masa halin da yake ciki, sai ya fara kokarin mikewa mai gadin ya taimaka masa, sannan ya bude masa daki mafi kusa da su ya saka shi a ciki. Babu komai a dakin sai carpet, akan carpet din Muhammad ya kwanta tare da rufe idonsa, yaji Safiyya ta sake kiran sa amma bai dauka ba, Ba wai fushi yake yi da ita ba, amma dai baya son yin magana da ita a yanzu, baya son yin magana da kowa.

Sai da kiran ya katse sannan ya jawo wayar ya kashe ta ya ajiye a gefe, ya cigaba da kwanciya yana sauraron yadda kansa yake sarawa da karfi kamar zai
tsage.

Abba ya fito daga masallaci zai shiga gida kenan mai gadin ya kira shi. Daga yadda yaji muryarsa ya san babu lafiya, sai ya gaya masa Muhammad ne gashi ya je gidan kuma kamar bashi da lafiya ya kuma ce a kira sama shi. Wannan ya saka ya fasa shiga gidan sai dai bai gayawa haidar dalili ba dan yasan halin Maman su in dai akan yaya ne yanzu zata tayar da hankalin ta. Sal ya ce masa kawal zai je wani guri ya dawo. Sal dai yana kokarin shiga motar sane yaga shigowar motar
Muhammad gidan, amma maimakon ya ga Muhammad din ya fito sal ya ga wani wanda bai sani ba, wani mai kama da kuma shiga irin da security officers, Har
ya fara tunanin ko wani laifi Muhammad din yayi sai mutumin ya gaishe shi ya ba shi key din motar yace "from my boss, Safiyya Adam, tace a kawo wa Muhammad na gidan nan motarsa, ya barta a gidan su sanda ya je" Abba ya karbi key din yana maimaita wa "boss? Safiyya Adam? Gidan su?" Amma security din bai amsa ba kuma Abba ya san ba zai amsa ba, haka training din su yake, abinda aka saka su shi kadai suke yi basa interfering ko asking ko answering personal questions.

Sai kawai ya saka key din a aljihu ya shiga motar sa ya tafi inda Muhammad din yake. Tabbas, ya san komai ba ake ciki dangane da matsayin Safiyya tsohuwar
budurwar Muhammad a gurin Safina matar Muhammad. Tun daga sanda ya san hakan sai ya fahimci cewa trouble dey

Muhammad yana kwance yaji shigowar Abba, Ya bude idonsa kadan sai yayi sauri ya mayar da shi ya rufe saboda jiri da yaji ya cigaba da fiban sa duk kuwa da cewa a kwance yake. Abba ya durkusa a gabansa
tare da dora hanunsa akan goshinsa da kuwa wuyan sa. Sai kuma ya mike ya dauko wayarsa ya kira likitan su ya fada masa inda zai zo ya same su. Daga nan ya
saka mai gadi ya dauko wa Muhammad din katifa da kayan shinfida a cikin gidan yazo ya saka masa anan dakin, yayin da shi kuma ya taimaka masa yayi alwala yayi sallah sannan ya kwanta a dai dai lokacin da Dr ya shigo. Duba shi yayi, a take yayi concluding "bp dinsa yayi sama gaskiya. We will have to watch it kar ya zame masa matsala" Abba ya runtse ido cikin jin zafin maganar, ko shi ba shi da hawan jini ballantana dan jaririn dan sa. Dr ya gama duba shi ya fita ya siyo duk abinda yake bukata sannan yazo ya daura masa ruwa yayi masa allurai a cikin ruwan sai yayi wa Abba
sallama ya ce sai da safe zai dawo ya sake duba shi.

Bayan ya fita Abba ya zauna a kusa da kan Muhammad yana kallon yadda gumi yake karyo masa alamar zazzabin da ya rufe shi ya sauka, ya shafa kansa a hankali tare da kiran sunan sa “Gidado….. ko zamu koma gida ka kwanta a can?” Muhammad yadan bude idonsa kadan ya kalle shi sannan ya girgiza kansa yace “no Abba. Anan zan zauna. Bana son zuwa gida” cikin kokarin bugar cikin sa Abba yace “ saboda me” Gidado yace “mama zata tayar da hankalin ta in taga bani da lafiya. Kuma bana son ganin Safina” Abba ya sauke ajiyar zuciya yana cigaba da kallon fuskar Muhammad, daga yadda fatar idonsa ta kumbura ya san yayi kuka, shi ba zai iya tuna rabon da yaga dan nasa yayi kuka ba, wannan kuma yakara tayar masa da hankali, ya sake tambayar sa “daga ina kake? me ya same ka?” Muhammad yasake bude idonsa, tambayar dayake so yayi masa kenan, tambayar daya sa aka kira masa shi dan yayi masa kenan, dan haka direct ya bashi amsa “daga gidan su Safiyya……. We broke up again……. Daddyn ta yace ba zai aura mata ni ba. Kuma kunce ba zan aure ta ba”.

Daga haka ya juya wa Abba baya, ya gama maganar sa saura ya jira amsa daga mahalfinsa, kamar yadda Safiyya itama ta gama tata maganar take jiran amsa daga nata mahaifin.

Maman Maama ✍🏻
[07/01, 10:46 pm] +234 906 816 1960: ❤️‍🩹Safiyya❤️‍🩹


Episode Fifty Eight: Parenthood


Not Edited

Abba ya sauke ajiyar zuciya yana kalion
sa, shi bai san a inda yaron nan ya koyo
taurin kai ba, yaro ne shi mai biyayya, ba'a
taba ce masa yes yace no ba. Amma
yanzu yana nema ya birkice musu. Yasan
duk abinda suke ciki amma bai yi magana
a kai ba saboda ya fi son ya san komai a
kan maganar first kafin yayi magana,
yadda in yace no zata tsaya a no din haka
zalika in yace yes.

Amma kuma duk da haka already shi da
mama sun san abinda dan nasu ya ke so
abu ne mai wahalar tabbatuwa, bayan
kasancewar yarinyar nan step sister din
matarsa akwai abubuwa da yawa da suke
cukurkude a cikin lamarin yarinyar wadanda suke bukatar warwarewa. Misali dazu wani katon mutun mai fuskar marasa mani yazo ya kawo masa key din motar
Muhammad kuma yace inji boss din sa sannan ya ambaci sunan safiyyan as boss din nasa, How?

But high bp? Muhammad? Saboda sun
rabu? Ko kuma yace saboda sun ce zasu
rabu dan yadda yake ganin dan nasa da
kuma yadda yayi masa magana bai nuna
alamar da gaske zai rabu da yarinyar ba.
Meaning high bp yanzu ya fara shi kenan.

Ya sake saka hannun sa a wuyansa da
goshin sa yana jin yadda jikinsa yake kara
yin sanyi sannan ya mike tsaye yana
kallon sa tare da sauke ajjiyar zuciya, ya
san ba bacci yake vi ba, wannan juya
masa bayan da yayi ma'ana fushi yake yi
da shi kenan, fushi yake yi da su shi da
maman sa dan sun hana shi abinda suke
ganin cutarwa ne a gare shi.

A hankali yayi magana "zan koma gida
Muhammad. Kar maman ka taji ban shigo
ba ta fara damuwa and bana son ta san
baka da lafiya, bana son ta san kana
neman dora wa kanka ciwon da Allah bai
dora maka ba. I will discuss it with her a
hankali. Ka kwantar da hankalin ka, zan
saka ayi min bincike akan yarinyar, in ta
kama zan je har gidan su inga mahaifinta
inji in yana da masaniya akan abinda yake
faruwa or not", Muhammad bai ce komai
ba amma Abba ya san ya jishi. Sai ya juya
ya bar gidan bayan ya gaya wa mai gadi
yayi keeping eye on Muhammad din kafin ya dawo ko ya aiko a dauke shi.

A hanya ma maganar yake ta juyawa a
ransa, shi bai san wannan wacce irin
yarinya ba ce ba mai shegen nacin da ta
ki bar masa zuciyar da ta huta, bai san
kuma dalilin da shima Muhammad ya
nace mata ba kamar babu sauran mata a
duniya. Shi ya san dan sa da farin jinin
yammata kamar yadda shima yayi a
lokacin samartakar sa, shi da kansa da
yake namiji iyaye a family sun sha yi masa
tayin a hada Muhammad din da yayansu
dan a kara karfin zumunci, Mama ma haka
ta kan samu daga gurin yan'uwa da
kawaye, shima kuma Muhammad din duk
da baya fada amma sun san yammatan
suna cire kunyarsu at times suyi mass
tayin soyayyar su, hakan yana nufin idan
guda hudu yake so to tabbas zai samu da
gudu, but why her? Why this Safiyya?
Mama ta gaya masa cewa yarinyar tana
da kyau amma wannan kadai bai isa dalilin
makale mata ba, dan ya tabbatar ba za'a
ce tafi kowa kyau ba.

Amma dole zasu zauna akan issue din
nan shi da Zainab, dole zasu samarwa dan nasu mafita akan maganar nan tun kafin tayi masa Illawarra da baza su iya magance masa ba. Amma hakan baya nufin zasu tunkuda shi ga halaka dan su faranta masa, idan Safiyya ba yarinyar kirki bace ba kamar yadda suke tsammani hada ta da dan su da yake yaron kirki ba. Ba zasu bari ta karasa kashe musu shi ba.

Ya shiga gida yayi packing ya fito yana
kalion motar Muhammad din, a ransa ya
danyi tunanin maybe a new car will cheer
him up tunda dama yaje ya lalata waccan
saura wannan. Ya shiga cikin gidan, Mama
bata parlour, wannan ya bashi mamaki
dan ya san yanzu lokacin zamanta ne a
parlour har sai duk sunci abincin dare ta
tabbatar kowa baya bukatar komai sannan
zata koma ciki, Ya zauna yana kallon
hanyar dakin da matar Muhammad take
ciki tana jinya, jinyar ciwon da tace shi yaji
mata amma kuma bincike ya tabbatar
musu ba da sanin sa bane ba, in fact zai
iya cewa yarinyar ce ta jawo faruwar abin.
But Muhammad ya mare ta, wannan shi
da kansa bai musa hakan ba. Wannan ya sa dole suke tausayawa yarinyar duk kuwa da sharrin da ta nemi
makalawa dan na su, abinda suka sani
thine matar Muhammad ce kuma tana
son sa sosal da sosai, and she carried
their grandchild for a while kafin su rasa
phi. Sun kuma san cewa ba karamin
takaici Muhammad yake cusa mata ba a cikin auren su musamman yadda yake soyayya da step sister din ta.

Wannan kuma shine gurin da Abba ya
sake diga ayar tambaya. How? Ta yaya
suka zama step sisters? Ta yaya kuma
babu wanda ya san step sisters din ne sai
yanzu?

Ya sake mikewa ganin har yanzu Zainab
bata fito ba ballantana ta bashi abinci
kamar yadda ta saba. Yana son kuma suyi
wannan maganar da ita. Yana son ya
samu amsar da zai bawa Muhammad dan
ya kwantar masa da hankali. A lokacin
Haidar ya shigo, shima ya fara baza ido a
parlour daga dukkan alamu mahaifiyar ta
sa yake nema shima. Sai kuma yace da
Abba "Abba barka da dawowa. Ina
Mama?" Abba yace "yanzu na shigo. Bata
fito ba tun dazu?" Haidar yace "tun sanda
na shigo na ga ta fito daga dakin Safina
sai kuma ta shiga ciki, ina jin dakin ta ta
tafi, na gaji da jiran ta na sake fita sai
yanzu na dawo".

Ba tare da Abba yace masa komai ba ya
tafi dakin nata, zuciyar sa tana gaya masa
something is wrong with her, dan babu
yadda za'a yi la shiga daki ta zauna ita kadai a wannan lokacin. Shi ya dauka ma tana nan ta ishi kowa da tambayar ina ya tafi? Kuma ina Muhammad?
Ya tura kofar dakin nata a hankali yana jin
sanyi da kamshin dakin, sai kuma ya tsaya
a bakin kofar yana kalion ta a zaune akan
gado da wayarta a hannun ta fuskarta a
kasa. Ya tabbatar taji shigowar sa amma
bata dago kai ta kalle shi ba, damuwar sa
ta kara yawa, dalili biyu ne zai saka tayi
haka, ko dai yayi mata laiti tana fushi da
shi ko kuma kuka take yi bata son ya gani.
Ya karasa shiga dakin tare da rufe kofar,
sannan ya taka a hankali zuwa gabanta ya
tsaya, sai ya ga ta kara boye fuskarta tare
da saka hannunta tana goge fuskar,
wannan ya tabbatar masa da cewa kuka
take, hawayen take share wa. Wannan
kuma ya tayar da hankalin sa sosai. Ya
durkusa a gaban ta tare da saka hannu ya
juyo fuskarta gare shi. Ta kale shi din
kamar yadda ya bukata, idonsa ya sauka
akan nata da suke nuna alamun kuka duk
kuwa da cewa ta goge hawayen.

Ya mayar da idonsa kan cinyarta ya ga
wayarta a ajjiye, wannan ya tabbatar masa
da cewa koma menene ya saka ta kukan a
waya aka gaya mata shi. "Waye ya mutu?" Tambayar da ya fara yi mata kenan cikin fulatanci. Tayi saurin
girgiza kanta tare da yin gyaran murya kadan tace "babu wanda ya mutu. Sannu da zuwa" ya mike tsaye sannan ya zauna a kan gadon kusa da ita yace "menene ya saka maman Muhammad kuka?" Ta dan yi
murmushi, babu halin da zata shiga a
ambaci dan nata ba tate da ta murmusa
ba. Duk da cewa a kwanakin nan shine
silar shigarta damuwa sosai. Wannan
kukan ma nasa ne. Ta dalilin sa ne.

Ya saka hannu ya dauki wayar tata yace
"bara in gani, waye ya saka min matata
kuka? Tabbas zan dauki mataki akan ko
waye, sai inda karfi na ya kare" ta sake yin
wani murmushi wanda yafi wancan girma
sannan ta saka dan yatsa ta dauke
hawayen da ya sake makalewa a gefen
idonta. "Hajjo" taji ya ambata a hankali
yana danna wayar ta, sannan ya sake
cewa "allai tafiya Germany ta same ni
kenan. Sai naje naji me Hajjo ta gaya wa
matata da ya saka ta zubda hawaye. Let
me quickly get flight tickets" ta kamo
hannun sa tana cigaba da murmushi tare
da kwantar da kanta a kafadarsa tace "in
ka tambayi matar ta ka zata gaya maka ai,
ba sai ka sha wahalar neman bayani ba"
yace "gwara dai in tafi neman bayanin,
dan a gane girman damuwata" sai kuma
ya kara da tambayar "me ya faru?" Ta
dago kai tana kalion sa, annurin fuskarta
yana gushewa, ta kuma tina da alkawarin da tayi wa Hajjo yanzu a waya, sai ta sunkuyar da kanta kasa sannan tace "ina so zamuyi magana, akan Gidado, akan yarinyar da yake so Safiyya. Amma muje
ka fara cin abinci tukunna" ya kalle ta da
mamaki "Safiyya? Nima da shirin yi miki
magana akan ta na shigo. Me ya faru?" Ta
mike tsaye tare da kama hannun sa tana
kokarin dawo da annurin fuskarta tace
"muje muci abinci tukunna. Kar Haidar yaji mu shiru ya damu. Ina Muhammad?" Tayi tambayar da dama ya
tabbatar zata yi masa, sai ya mike yana
cewa "ya kira ni yace akwai abinda ya rike
shi sai anjima zai dawo gida".

Daga haka suka juya suka fita tare. Cin
abincin nasu ya kasance cikin shiru, kowa
yana juya maganganu da yawa a ransa
har suka gama. Haidar kan sa ya fahimci
akwai wani abu da yake damn iyayen
nasa, yayi kokarin ya ga sun saki ransu
kamar kullum amma ganin hakan yaki
yiyuwa sai ya bar maganar shima kawai
yaci abincin sa, Sai da suka gama sannan
Abba ya danyi gyaran murya yace wa
Haidar din "kaje gidan Gidado na...........
Yana can a kwance bashi da lafiya. Idan
ruwan da aka saka masa ya kare sai ka
taho dashi ku dawo gida" "bashi da lafiya?" Mama ta fada tana zaro ido, Abba ya daga kafada "dana gaya miki da ba zaki ci abinci ba. Duk da yanzun ma ba
sosai kika ci ba. Bashi da lafiya but he will be okay" Haidar ya mike amma shima yana jin babu dadi a ransa, yayan na sa yana ta shiga damuwa iri iri a kwanakin nan,

Daga nan basu sake maganar ba sai ya
mike ya tafi gabatar da sallar ishar da ya
rasa ta a jam'i lokacin yana hanyar
dawowa daga gidan Muhammad, ita kuma
ta kira ma'aikatan gidan suka fara hidimar
gyaran gurin sannan ta shiga sauran
hidimomin da ta saba yi duk dare a gidan
dan tabbatar da komai is in order. Sai da
ta gama sannan ta tsaya tana kallon dakin
da Safina take ciki tana jin wani iri a
zuciyar ta, ba zata iya shiga dakin ba yau
kamar yadda ta saba shiga kullum da dare
kafin ta kwanta. Sai ta juya tana kallon yar
aikin ta mai suna A'isha wadda yanzu ita
take taya Safina kwana, tace "A'isha shiga
ki tambayi Safina in akwai abinda take
bukata, kin kai mata abinci taci?" A'isha
tace "na kai mata abinci tun dazu, amma
bara in koma in tambaye ta ko tana son
wan abu"

Ta shiga dakin, bata jima ba ta fito yanayin fuskarta babu dadi, hannun ta dauke da tray din abinci ta ajiye shi akan cabinet din kitchen din tace "bata ci abincin ba Mama. Kuma tace min bata bukatar komai" Mama ta cigaba da kallon ta fuskarta da alamar tambaya amma bata yi tambayar ba sai A'isha ta amsa "kuka
na tarar ta na yi. Maybe ko hannun ne yake yi mata civo" Mama ta gyada kai tace "maybe" sai kuma ta cigaba da al'amuran gaban ta.

Sai data gama ta shiga dakin ta ta cire
kayanta tayi wanka tare da alwala tazo
tayi sallar shafa"i, bata yi wutiri ba dan
tana da niyyar tashi cikin dare tayi sallah
kamar kullum, sai ta dauko Alqur'anin ta
ta fara karatun suratul mulk kamar yadda
take yi duk dare kafin ta kwanta. A lokacin
ne yayi sallama ya turo kofar a hankali, jin
karatun ta ne ya saka ya karasa shigowa
tunda ya tabbatar a suturce take sai ya
zauna acan gefe yana kallon ta. Bata dago kai ba duk kuwa da zuciyar ta tana son gain sa musamman tunda an gaya mata bashi da lafiya. Haka suke yi
yanzu, tunda aka sallamo shi daga asibiti
take yin fushi da shi akan laifin dukan
matarsa da yayi, amma kuma zuciyarta
tana matukar tausaya masa halin kuncin
da tasa zuciyar take ciki kuma tana neman hanya mai kyaun da zata bi ta saka dan lelen nata a farin ciki in dai hanyar ba haramun bace ba kuma ba zata cutar da shi in the future ba. Sai dai ta cigaba da
tsare gida ne dan jikinsa ya gaya masa ya
san cewa abinda yayi ba dai dai bane ba
kuma ya bata musu rai sosai saboda ya
kiyayi gaba. Plan dinta shine sai yayi
laushi sosai ya bada hakuri sannan ta
saka shi a gaba yaje ya bawa Safina
hakuri a gabanta sai kuma ta hada su su
koma gida tunda alhamdulillah jikin su duk
su biyun yayi sauki sai abinda ba'a rasa
ba. In yaso ita sai da daukarwa safinan
yan aiki tunda Mommyn ta tayi fushi ta
kwashe nata. Kuma ita ta fahimci
Mommyn sosai, dan idan ita ce in her
shoes aka yi wa Mufida abinda akayi wa
Safina ta tabbatar sai tayi abinda yafi
wanda Mommyn tayi. Sai dai kuma ba ta
jin zata kasance in her shoes din, dan
halin Safiya da na Mufida ba daya ba ne
ba. Sannan yanayin auren Mufida da na
Safina ba iri daya bane ba. Amma kuma yau duk plans din na ta sun ruguje…..... She is no longer sure about
what to do, Not after what Safina told her
da yamman nan and also what Hajjo told her

"Mama" Muhammad ya kira sunan ta a
hankali bayan ta kai karshen surar da take
karantawa. Ta dago kai ta kalle shi,
gabanta ya fadi tayi sauri ta dauke kanta
ta kalli gefe, kuka yayi, maybe tun dazu
ne yayi ba yanzu ba but yau yayi kuka, Ba
zata iya tuna ranar da taga dan nata yana
kuka ba tun bayan girmansa. Wannan
kam shine limit dinta, Already kullum
zuciyar ta a karye take in ta ganshi cikin
dakuwa ballantana kuma ace wai yana
kuka? Muhammad Gidado? She can walk
to the end of the earth to prevent that.
She can walk to the end of the earth to
put a smile on his face.

"Mama" ya sake kiran sunan ta. "Mama
dan Allah ki daina fushi da ni. Kiyi hakuri.
In dai akan Safiyya ne na riga na gaya wa
Abba cewa na hakura da ita. Tunda ba
kwa so shikenan. I will accept duk abinda
kuke so. Ni dai dan Allah ku daina wannan
fushin" ta dawo da dubanta gare shi, ta
sauke idonta akan abin karin ruwan da
yake makale a hannun sa, yayi kokarin
boye hannun, ta dauke kanta tace a
hankali "kayi sallah?" Yace "eh nay)" yana
mamakin yadda har yau bata daina yi
masa irin wannan tambayar ba. Tace "kaje
kaci abinci. Me zaka ci? Akwai tuwo kana
so" ya dan bata rai, shi yadda yake jin
makogwaronsa a rue baya jin ruwa ma zai wuce ta cikin sa ballantana tuwo, Ya girgiza kansa "na koshi" ta dauke idonta daga kansa sannan tace "ta shi ka je" ya mike ya fita yana hada hanya, amma a
ransa yasan maganar bata kare anan ba.

Ta bi bayansa da kallo har ya fita sannan
ta sauke ajiyar zuciya. Kowa da irin
kaddarar sa. This is not what they had
planned for him, aure suka so suyi masa
na gata, a lissafin su auren da wuri zai
saka shi ya kara zama responsible mutum
kuma ya kara masa himma gurin kafa
roots din sa ya yi nasa family din and live
happily ever after. Amma plans din su
gabakidaya ya rushe sanda suka fahimci
yarinyar da suka jima da sanin yana
matukar so ta yaudare shi. A lokacin ne
suka yanke shawarar samun wata su aura
masa dan gyara barakar da suke ganin
Safiyya tayi wa rayuwar sa, not knowing
jefa su sukayi a cikin ramin da har yanzu
ya kasa fito da kan shi. Amma yanzu ta
dauri aniyar ganin ta saka igiya ta jawo
kayanta da kanta, ko da kuwa duniya zata
vi mata tofin ana tsine akan hakan.

Sai da ta gama duk abinda zata yi sannan
ta saka kayan baccin ta ta dora dogon
hijab akai ta tafi kitchen, da kanta ta hada
masa abinci marar nauyin da take ganin
zai ya ci, noodles irin dahuwar da yake
so, sannan ta hada masa hot chocolate yana tiriri. A’isha da ta tayata yanka vegetables din tana murmushi tace “Gaskiya zance da yaya karami (haidar) shima yayi rashin lafiya dan ake hada mashi wannan delicious din” murmushi kawai mama tayi bata ce komai ba sai kuma tace mata ta dauka ta kai mata kofar dakin Muhammad din. Ita kuma ta bita a baya.

Sai da A’isha ta ajiye ta juya sannan Mama tayi knocking kofar, shiru ba’a yi magana ba, ta sake knocking shima shiru sai ta tura kofar ta shiga da sallama da tunanin ko yana toilet ne amma sai ta ganshi a zaune akan study table din sa da laptop a bude a gabansa. Hankalin sa gabaki daya yana kan screen din laptop din. Kasacewar ya juya mata baya ne ya saka itama ta tayashi kallon abinda yake kalla.

Safiyya ce akan screen din, kamar video ne yayi mata tana zaune akan swing shi kuma yana tsaye a gefen ta yana dan tura ta da hannun sa kadan. Daga dukkan alama hira yake yi mata mai dadi dan sai murmushi take yi Amma Mama bata jin abinda yake cewa daga inda take tsaye. Yayi zooming fuskarta a lokacin da ta dan kwantar da kanta jikin igiyar swing din tare da lumshe idonta alamar hiran yana mata dadi. Sai a lokacin Mama ta kara tabbatar kyawun halittar Safiyya
[07/01, 10:46 pm] +234 906 816 1960: Safiyya ce akan screen din, kamar video
ne yayi mata tana zaune a kan swing shi
kuma yana tsaye a gefenta yana dan tura
ta da hannun sa kadan kadan. Daga
dukkan alama hira yake yi mata mai dadi
dan sai murmushi take yi amma Mama
bata jin abinda yake cewa daga inda take
tsaye. Yayi zooming fuskar ta a lokacin da
ta dan kwantar da kanta a jikin igiyar
swing din tare da lumshe idonta alamar
lilon yana yi mata dadì. Sai a lokacin
Mama ta kara tabbatar da kawun halittar
Safiyya. Kyakkyawa ce ajin farko and she
has a unique kind of eyes masu melting
zuciyar duk wanda ya hada ido da ita, and
her smile is contagious, da wahala tayi
murmushi wanda yake tare da ita bai taya
ta yi ba. Ya jima a haka yana kallon
fuskarta Mama da take bayansa tana taya
shi. Sai dai a cikin videon without warning sai
Gidado ya tura swing din da karfi, ta dan
yi karamar kara tare da bude ido cikin
toro, ta kuma kankame igiyar a lokacin
da lilon yayi sama da ita. Daga inda Mama take tana iya jiyo dariyar Gidado daga cikin laptop din, dariyar da ta jima bata ji yayi irin ta ba.

Ta danyi gyaran murya, yayi sauri ya kife
fuskar laptop din amma kuma bai juyo ba
dan ya tabbatar ta gani. Sai data kira
sunansa "Gidado" ya juyo da kujerar da
yake kai amma bai daga ido ya kalle ta ba.
Tace "kazo ka dauki abinci gashi nan a
bakin kofa" ya taso ba tare da yace komai
ba ya zo ya dauka ya koma kan kujerar ya
zauna yana kallon abincin tare da jin
soyayya mahaifiyarsa tana karuwa a
ransa, "ka tabbatar ka cinye kuma ka sha
maganin ka. Zan dawo in gani" yace "to"
da murmushi a fuskarsa, yana mamaki
kuma yana son yadda Mama take bashi
umarni tare da treating dinsa kamar dan
primary.

Har ta juya sai kuma ta tsaya ta yi masa
tambayar da dazu ta manta bata yi wa
Hajjo ba "how did Safiyya's mother die?"
Tambayar ta zo masa a bazata. Ya daga
kai yana kallon ta amma kuma bai ga
alamar wasa a fuskar ta ba. Sai a amsa, a
ransa yana yiwa Safiyya godiya da ta gaya
masa komai "she drawn" ya fada, sai
kuma ya yi tunanin kara mata bayani
"Safiyya ce ta fada cikin water reservoir
when she was 2 years old, Her mother jumped in to save her. Ta fito da ita, ita kuma ta mutu a ciki",. Ta cigaba da kallon sa kamar ba ta fahimci abinda yace ba, amma ya fahimci maganar ta taba zuciyar
ta sosai. Ta juya masa baya da sauri,
maybe trying to hide her tears, sai kuma
ta ce "goodnight" sannan ta fita.
Chapter 2 · 0% Book details