← Book details Ruhin Jinn Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 4

Sashe 2

Ruhin Jinn Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

.......Horo Yake bashi sosai ba dare ba Rana Azaba iri iri Yake bashi domin koyar dashi, b'angaren tsafi kuwa take Yayi zarra duk da tsafi ga Addini haramun ne Amma idan zakayi Amfani dashi b'angaren kare Kai to Lalle Addini yabaka dama,

Saida Suka kwashe Sama da Shekara 5 Yana horar Dashi Alokacin ya zama cikin Namiji Mai k'arfin dantse da sihiri Cikin k'ank'anen lokaci ya soma shahara sama da mlm Bukar ma,

A Wad'annan shekarun Abubuwa da yawa sun faru domin *RUHIN JINN* baida shigowa garin Yana kisan gilla wa mutanen garin ba, idanma kace had'a kayanka zakayi domin ka gudu to Lalle Kamar kabada katin gayyata ne wa mutuwarka,

Ganin mutane nayi kowa Yanata gudu sauri sauri Yana shigewa gida Domin b'oye kansa domin kuwa yaune *RUHIN JINN* d'in yake bayyana, Shikuwa tafiya Yake Hankali kwance cike da izza, Sanye Yake cikin kayan Saki Rabin fuskarsa kuwa rufe da k'aton rawanin da ya d'auka, Kirar sadaukan maza ta bayyana jikinsa k'afafunsa sanye da takalmin fata, Abayansa wata k'atuwar takobice sanye cikin kubenta, kallo d'aya zaka masa kasan yakai Jarumin Namiji, duk da fuskarsa rufe take Amma Hakan Bai hanna bayyanar kyawonsa ba, kallon mutane kawai yake suna guje gujensu Amma shikam ko Ajikinsa,

Cikin k'ank'anen lokaci guguwar ta tataso Ahankali har tasoma k'arfi, Yanajin Ihun mutane suna Fad'in "mugudu *RUHIN JINN* d'in ya bayyana tinkan Ya hallakamu,"

Bai juya, cigaba da tafiyarsa Yayi tamkar baiji Abunda suke fad'a,

Y'ar Sarki Yazira tafito rangadi Kan dokinta saiga faruwar wannna Abun dokin nata Ya tsorata jefar da ita yayi tare da zurawa Aguje yabarta k'asa tana Ihun neman taimako inda Sauran Hadimanta ma suka ranta A nakare domin tseratar da ransu,

Gadan gadan guguwar Tayi kanta, tagama sadak'arwa Kan yau k'arshen ta Yazo Domin kallo d'aya zakama guguwar ka fahimce ta Aljanu ce duk wani dabarun tsafinta sun kasa kareta daga wannan guguwar, wani Ihun tasake zabgawa domin k'iris ya rage guguwar ta sameta,

Juyowa yayi Jin Ihun yayi yawa tsayawa yayi cak tareda waiwayo bayansa, ganin guguwar tana daf da illata wannan budurwar yasa yasa Cikin zafin nama Ya ruga da Azababben gudu, cikin k'ank'anen lokaci ya Isa daf dasu lokacin har guguwar tana Neman d'auke ta, Cikin zafin nama ya sureta A Kafad'arshi ya matsar da ita gefe,

Ganin irin yarda wannan bil'Adam Yashiga gabanta Yasa guguwar tsayawa cak,

Fuskartarta gaba da gaba jarumi Jalal yayi kallon kallon suka Fara tsakaninsu Al'amarin da yabawa duk wani mahaluk'i dake wurin mamaki kenan ita kanta Yazira mamaki ya kamata,

Kallon guguwar yake tsayi ne da ita Sosai Wanda Koda mutum zai d'aga kanshi bazaiga k'arshenta ba gata bak'a wulik da munin kallo,

Kansa guguwar Tayi cikin Mugun nufi, Shikuwa Addu'a Yasoma da Anbaton Allah, Wani k'aton marfin kwano Ya d'auko Yayi kariya dashi koda guguwar tazo kansa ta rufeshi, baka Ganin komai yayi duhu, tajima tana zagayarshi yana duk'e da marfin Kafin tayi gaba tabarshi,

Saida komai ya lafa sannan ya mik'e tsaye Yana karkad'e jikinsa, ba Koda Alamun gajiya tare dashi Abun mamaki ma Wai Yafita raye,

Tafiyarsa kawai Yafara baiko waiwaye inda budurwar take ba, duk da kiransa datake hakan baisa ya tsaya ba, Yawuce Abunsa,

Tana zaune gun saiga Sauran Hadimanta sundawo sune suka taimaka Mata tamik'e,

Direct tana Shiga gida fada tawuce cikin tashin Hankali Sarki yake tanbayar ta Ya Akayi ta tsira?

Labarin Komai tabasa amma Kuma Bata ga fuskar Jarumin ba ,

Shela Sarki yasa Kan koma waye ya bayyana kansa kuma zai Masa Kyauta Mai tsoka Amma hakan baisa Jalal bayyana kansa ba,

"Naji Abunda yafaru Kuma Inada tabbacin Kaine kaceci ginbiya Yazira Amma Meyasa baka bayyana kanka ba," cewar wani tsoho dake tare dashi

"Abba Ni bana neman komai Kawai nayi Dan Allah ne, bana buk'atar komai nasu"

"D'an kayi k'ok'ari Amma kuma halwar tsafi na gawadamin Akwai gagarumin Aiki gabanka domin kuwa ba Ai nahin *RUHIN JINN* d'in bane kukayi wannan Karon kuma inada tabbacin bazai barka ba, sannan bakada k'arfin iya YAK'I dashi, dama ace zai bayyana A Asalin siffar sane ta hakan kawai Za'a iya illatashi"

"Amma Abba taya Za'a iya sa Yadawo Asalin siffar sa? Kuma taya Zan gano ko mamana tana Raye,"?

"Abunda madubin tsafi YAK'I nunawa kenan Amma dai Tabbas tana raye Bai kashe taba, Samun siffarsa Abune Mai matik'ar Wuya kuma Koda Yadawo siffar sa ba Lalle bane kayi nasarar hallkashi saidai A hallka wannan *RUHIN JINN* d'in nashi"

"Ta Ina zanga wannan *RUHIN JINN* Abba,"?

"Bansani ba bangano ba Amma Zan k'ara bincikawa, kaidai Koda yaushe kazama Cikin Shiri,".

Faruwar wannan Abun ba k'aramin Bata ran Aljani mardus, Yayi ba zaune yake cikin wani irin k'asum gumun daji Ank'awata fadarsa da Abuvuwan Alfarma

"Tuba nake ya shuga bana, wannan ba k'aramin hatsabibin Yaron bil'adama bane shine ya Hana na d'auko Yarinyar Kuma nakasa cutar Dashi, Danayi Yun k'urin ganin na hallakashi sai yazama na nine yake neman halakawa dawasu kalmomi da yake Fad'i,"

"Rufamin baki, banza ba gasharen Aljani Kawai k'aramin Yaron Bil'adama shine zai hanaka Aiwatar da aikina? Kasan me mutanen garin sukami? Jinjina Yarona durus Suka Yanka Suka barni da jininsa kawai Wanda sama da Shekara 50 yanzu Ruhin sa kawai ya ragemun, Kuma Muddin ban yanka wannan Yarinyar Yazira ba nayi Amfani da jininta d'aya bazai tab'a tashi ba, Da RUHIN sa kawai nakeda k'arfin tsafi Domin tin Yana ciki nagama mallakasa komai Indai ba Ruhin sa ba bazan tab'a iya yak'ar wad'an Nan bil'Adam d'in ba, Magana ta K'arshe kota yaya Akawo min Yarinyar Kuma shima Yaron A hallkashi, kuje da kamannu iri iri cikin garin domin halkasu,"

"Angama ya Shuga," bat wasu daga Cikin Aljanun suka B'ata,......

_BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_

WhatsApp number 07064904617

*RUHIN JINN☠️💀😈*

_PAID BOOK #300 ONLY_

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK...(24) RUHIN JINN PAID BOOK
loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝```

_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *RUHIN JINN💀☠️😈👹 PAID BOOK 300 ONLY*
_Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._

_Wednesday 30/8/2023_

*Free 🅿️ 16 to 20*

........Safa da marwa Sarki Aruf yake zufa sai faman tsatstsafo Masa take, kallo d'aya zaka masa kasan Tabbas yana cikin tsantsar tashin hanakali,

"Yanzu meye mafita mlm"?

"Mafita d'aya ce A gaggauta hallaka wannan RUHIN JINN d'in domin Muddin Ruhin Yana Nan tofa saiya Hallaka Y'ar ka,"

"Kodai mu shirya runduna muje Yak'ar wannan *RUHIN JINN*,"

"Bawanda Yasan inda wannan RUHIN Yake, kuma Koda Wanda Yasani tofa Akwai Gagarumin bala'i da masifu ciki,"

"Koda Raina zai salwanta Zan iya kare Rayuwar Y'ata itace Kawai gareni Zan iya yin komai saboda ita,"

"Ashirya tafiyar Amma Kan Aje Ayi gangami domin Aje da manyan Jarumai, musamman wannan Jarumin daya ceci Y'ar ka,"

"Amma Ina zamu ganshi,"

"Bansani ba Nima domin Koda yaushe fuskarsa rufe take ba Wanda ya sanshi, Amma Inada Yak'inin zaije idan Kayi gayyatar domin Kai Sarki ne dole talakawanka Suma biyayya,"

"Magatakarda Aje Ayi shela Ace Inason ganin kowa da kowa dake wannan garin musamman maza,"

Cikin k'ank'anen Lokaci kuwa mutane suka taru k'ofar fad'a, harda Jalal

"Abunda Yasa na taraku Anan Shine, Zamuje neman *RUHIN JINN* Domin halakkashi ko masamu zaman lafiya da kwanciyar Hankali Acikin garinmu, dawa dawa Cikin Jarumanmu zasuyi wannan tafiyar,"?

Kowa shuru yayi mutane sai magana suke k'asa k'asa bawanda zai iya saka kansa cikin wanna masifar

Har sarki yacire Rai da Samun Wanda zaije, kawai saiyaga wani mutum fuska rufe da Rawani Yad'aga Hannu Alamar zashi,

Kowa kallonsa yake da mamakinsa Amma shi ko Ajikinsa

Can dai daga baya Aka sake Samun manyan matsafa da Jarumai 5

Kowa ya watse Ana mamakin wannan Sabon Jarumin,

Kowa yashirya tsaf Domin gudanar da tafiyar daga Ciki harda Yazaira domin tace saitaje,

Ak'alla Ansamu mutane sama da 100 Domin mafi yawansu Jaruman sarki ne, Jarumi Jalal ne Kawai bare, shikuwa dalilin Yarda yabisu domin Yasami damar gano mahaifiyar sa,

Tinda Aka fara tafiyar bisa dawakai Aka nufe cikin manyan dazuka boka Harus shike Nuna musu hanya domin Acikin halwar tsafinsa tana Nuna Masa inda Ruhin yake Adajin, tinda suka fara tafiyar Basu had'u da Komai na cutarwa hakan yasa suka saki jiki,,...

"Wad'annan bil'Adam d'in sun nufomu Ya Shuga kuma da niyar k'ona Ruhin d'anka sukazo muje musamesu mu hallakasu ne Yashugaba,"

"RUHIN baya ta wannan Dajin Tabbas nasan sunsan da Hakan Dan haka kuje ku Hallakasu ku kawomin Yarinyar"

"Angama Shugaba"

Firrr Aljanun Suka watse

...............

Suna cikin tafiya sukaga wasu manyan karnuka manya manya suntare gabansu ko wanne kare d'aya d'auke da Kai 7 Hak'oran su kuwa zago zago halshensu har tab'a k'asa yake,
Dukansu sun razana Amma Banda Jalal domin Yasaba Arba da Irin wad'an nan

Tsayawa sukayi Aka Soma kallon kallo tsakaninsu,

Takobbansu suka zare tareda sakin linzamin dawakansu suka nufe karnukan cikin zafin nama,

Ganin Hakan Yasa Suma karnukan Sukayo Kansu Cikin mugun nufi.............................

_BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_

WhatsApp number 07064904617

*RUHIN JINN☠️💀😈*

_PAID BOOK #300 ONLY_

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._
Chapter 2 · 0% Book details