Part din goggo aka kai akwatunan..anty Amarya ce ta baro can ta nufi part dinta Dan dubo hydar..
Rikicin Babban Gida Book 1 Complete Hausa Novel · about 37 min read
Ga mamakinta tana shiga ta iske maryam kusa da hydar tana hawaye shiko yana kwance zazzabi ya rufesa..
Abu kamar wasa akadinga shirye2n biki chinchin da su cake dik dai kayan tarkacan ciye2 akai tayi..
Maryam kuwa ko ajikinta ita hankalinta nakan hydar dake kwance..
Yayyunta guda biyu mata da sukayi aure ne suka zo dakin goggo aka jata..kayan ciye2 suka dinga bata suna ta gyarata..kokadan hankalinta be bata komai ba Dan dik abinda aka bata zagewa take taci bama iwa inya mata dadi..
Anty shema'u ce ta kalleta tana fadin
"Gwara kiyita ci ai..aikuwa inna ya kabir ne yakamata yazo yabamu tukwici fa"
Dariya sukayi ita da anty faty..
"Bara na kira Dan banzan"
Abu kamar wasa Anna ta shirin biki hydar kuwa zazzabin ya rufesa sosai amma tsam anty ta hana a fadawa kowa ta rufesa a dakin ta sedai ta shiga ta basa abinci da magani..
*Night*
Zaune maryam take adakin goggo anmata kunshi me kyau ko inna na jikinta kamshi yake ynxu kam abin yabata tsiro tinma ba da aka hanata fita ba zuwa ganin hydar ba..
Gaban madubi take zaune tana kallon kanta.. Irin kyan da tayi kamar daga zama taji anturo qofa..azatonta ya hydar zata gani tayi saurin juyowa..
Ya kabir tagani da sauri ta miqe zata nufi toilet janyota yayi ya hada jikinta da nasa..
"Maryam kin kusa zama tawa"
Kallonta ya farayi ita kuwa tana kiciniyar kwacewa...
.
*Queens online writers👑✍*
[7/5, 1:03 AM] Real Afreen ce💋: 👑👑👑
👸👸👸
*Queens online writers✍*
_Alkalamin Queens_
🍡🍡🍡🍡
🍡🍡🍡🍡🍡
🍇🍇🍇🍇🍇
~Rikicin~
*{Babban gida}*
Wednesday's update 5th July 2017
_Queens online writers muna godiya sosai zuwa ga masoyan mu...Rikicin babban gida littafine da mukeyi domin nishadantar da Ku Kuma Alhmdulh mungani mungode_
*Take note******👍👍
*Plxx kuyi hkr zan canja musu suna*
Maryam- ( _Amra_)
Kabir - _(Arman)_
Episode *11-15*
Yana yin data gansu da safiya ne ya fado mata arai taji wata sabuwar tsanar tasa ta ziyarci zuciyarta Dan haka ta tattaro dikka qarfinta ta kwance kanta daga gareshi tana fadin
"Wallahi bazan taba zama taka ba har a bad a nafi karfinka..."
Murmushin mugunta Arman yayi yasoma matsawa kusa da ita..
Amra kuwa ka da baya ta dingayi harsaida takai jikin bango ..
"Amra meyasa kike gudu na bayan kinkusa zama tawa"
"Wallah Allah ya sau**""
Bata qarasa mgnarta ba sukaji qarar bude qofa..
Arman na ganin anty faty yasoma Sosa qeya..
"Toh sarkin gajen hakuri shine har seka biyota nan ma???"
Kama kame ya farayi Dan hk tanuna masa qofa ficewa yayi sanda yakai qarshen qofa kafin ya juyo ya kashe ma Amara ido..murguda masa baki tayi yana murmushi ya fice...
Yana tafiya ta qara so gun anty faty ta soma kuka
"Antynmu dan Allah kitaimaka min inje inga ya hydar Dan Allah"
Shiru anty faty tayi kafin tace toh tinda gurin ya fara yin duhu jeki dawo ammafa karki Dade..
Tana murna ta nufi koda..
"Kee!! Nisa hijabi mana"
Ammasawa kawai tayi da toh ta suri hijab dinta ta fice..
Ahankali ta tura dakin hydar amma bataga kowa ba Dan HK dakin anty Amarya ta nufa tana kallon anty Amarya ta fita kafin ta tura qofar dakin..
Zaune ta iske hydar ga tilin magunguna agabansa alamun magani ya gamasha..
Da Saudi ta qarasa kusa dashi
"Ya hydar meye hk?"
Ta fada tana duban magungunan dake gabansa..
Yi yayi kamar bemasan ta nayi ba ...
"Ya hydar mgn fa nakema"
"Amra meyasa kika dawo kije kiyi rayuwarki da Wanda kikeso banasanki bansan ganin ki kifice kibarmin daki"
Fashewa da kuka Amra tayi ta duqe
"Ya hydar kai nakeso kainakeso"
Miqewa hydar yayi da nufin fita..
Ta miqe da gudu ta riqo rigarsa
"Ya hydar meyasa kakemin haka kasan kai kadai nakeso"
Dikkansu muryar su rawa takeyi alamun kuka sukeyi
"Amra ki fita ki bar daki nan banaso ganinki kije gun Arman din da kikeso..gobe aurenki Dan HK banga amfanin zamanki anan ba"
Rikicewa Amra tayi muryarta na rawa tana fadin
"Ya hydar wanne irin magana kakeyi hk?kasanfa innasanka meyasa kake fadan HK"
Juyowa hydar yayi idanunsa sunyi jawur furzar da iska yayi tare da goge hancinsa ..riqo ta yayi gam ya tsaya yana kallonta shesheqar kuka kawai takeyi..mgn ya somayi yana fadin
"Amra indai kinasona toh kibi abinda nakeso saboda mu kwatoh syyrmu hkn ne kadai zesa a hkra abarmin ke..kinsan inna sannu ko"
Gyada masa kai tayi alamun eh tare da share hawayen fuskarta...saketa yayi ya juya bayansa
"Amra ki bani kanki itace kawai mafitarmu"
Yafara tare da marairaice fuska ..
Gabanta ne yafadi tafara ja da baya tare da mamakin Kalmar data fitoh daga bakin ya hydar....
Ganin HK yasa ya qara marairaicewa
"Amra Dan Allah kifuba yayinda muke ciki in ban aureki ba zan rasaki arayuwata kitaimakamin"
Hawayene kawai ke zuba a fuskar Amra saboda tariga tayi mutuwar tsaye bata taba tsammanin haka daga ya hydar ba kusa da ita ya matso yafara qoqarin cire hijab dinta...
Can kuwa dakin goggo Arman ne yashigo anty faty ya iske zaune cike da fara'a yake fadin
"Antynmu inna wify ta take"
"Kaga ta fita amma nasan ynxu zata dawo"
"OK bara na jirata dama na zone nayi sallama da ita Dan gobe Anna daura aure xan wuce se nan da 1 ko 2mth zan dawo"
"Meyasa bazaka tafi da ita ba?"
"A'a anty kinsanfa basona take yi ba innaso na koya mata sona kafin na dauki matata"
Murmushi anty faty tayi tana fadin
"Hkn yayi bara naje na dubo ma ita"
Toh ya amsa dashi ita Kuma ta fice daga dakin..anty faty na fita ta tafi wata sabgar gabanta tama manta da Neman Amra ta fitoyi...
Fitar anty faty da minti biyar Arman yaji an banko qofa dasauri ya dubi qifar cike da mamaki ya miqe ganin safiya tsaye se share hawaye takeyi
Dasauri ya miqe tsaye Dan yariga yasan meyasa kawota matsowa kusa da ita ya farayi yana fadin
"Dan Allah safiya kitsaya ki saurare ni"
"Ba abinda zakacemin toh wallahi bazan taba yarda Ku zauna lfy ba"
Shafa kansa yayi tare da shafa gemunsa yana cike Lebensa..
"Ka rasa wa zaka aura se Amra qanwace fa gareni"
Ganin be kulata ba yasa ta matsa kusa dashi tayi qasa da murya tana kuka
"Dan Allah ya Arman ka aureni wallahi innasanka inna qaunarka"
"Kiyi hkr kawai safiya"
Tanajin yafadi HK ta miqe da gudu ta fice ranar dakin..
Ajiyar zuciya yasauke tare da komawa yazauna..tunanin me ya tsayar da anty ya farayi
Cankuwa hydar ne yaja Amar yuuu har dakinsa kamar wata sokuwa suna shiga yasa key..
Agun Arman ya kwanta sai barci ya kwashesa... Misalin karfe 1:30 Amra ta turo qofar da layi take tafiya har ta fada gefen gado ..
Shassheqar kukanta ne ya tasa Arman daga barcin da yakeyi tana kwance a dunqule da hijab dinta a hannnu
*Queens online writers*
_Idan kunada comment zaku iya tuntubar kowacce writer din Queens_
[7/8, 12:08 AM] Real Afreen ce💋: 👑👑👑
👸👸👸
*Queens online writers✍*
_Daga Alkalamin Queens_
🍡🍡🍡🍡
🍡🍡🍡🍡🍡
🍇🍇🍇🍇🍇
~Rikicin~
*{Babban gida}*
Saturdays update 8th July 2017
Episode *16-20*
Tana kwance dunqule da hijab dinta a hannu..dasauri ya juya gareta yana tmbyrt meyasameta..Dan jikinsa yayi sanyi atunaninsa zancen aurensu ne dataji
Qin kulasa tayi daga bisani barci ya dauketa..Da asubah tanajin fitar Arman daga dakin ahankali ta miqe daqyar ta kai kanta toilet gawani azababban ciwon kai dake damunta..tafiya take amma hawayene ke bin fuskarta..
Washe gari tinda safe anty faty ta shigo dakin kwance ta iske Amra tana barci ta bata tayi da niyar tashinta firgigit ta miqe har taba anty faty tsoro
"Lafiya Amra meyasameki?"
Dafe kanta tayi tare da sunkuyar da kanta...Zama anty faty tayi kusa da Amra tare da sa hannu ta dago fuskarta..
"Amra meyafaru?dubi yanda idanki yayi ja??kuka kikayi Kuma da rashin barci ko?"
Girgiza kai Amra tayi alamun a'a...
"Hmm baki isa ki boyen komai ba..Amra ko bakyason Arman dole kiyi hkr dashi ahankali zakisoshi "
Acewar anty faty ..
"Anty wai ynxu dgsk Arman zan aura?wallahi ni bana sonshi"
"Kull kar inqaraji kin fada HK..kima tashi kishirya"
Can karshen gado ta rakube ta kifa kai da gwiwa tana kuka anty faty tayi rarrashin duniya amma inna taqi.. kamar tana qara ingizata dik Wanda yashigo seya mata mgn amma taqiji hardai suka gaji suka qyaleta.
Bayan ansauko daga sallar juma'ah ne aka daura auren Maryam(amra) da kabir(arman)..
Gaba daya gidan ya kacame da guda shigowa aka dinga yi ganin Amarya amma Amarya ba abinda takeyi sai aikin kuka ..
Ganin Abun nata banayi bane yasa anty faty tace anemo mata Arman..
Aikuwa ba bata lokaci aka nemosa..Cikin shirinsa na tafiya ya shigo dakin..Amra kuwa nanan kwance har gyangyadi yafara dibanta yana zuwa anty faty tajasa waje ta masa bayanin halin da amra ke ciki..gaba daya hankalinsa tashi yayi jin abayanin anty ko kadan bata ambaci cewar Amra taci abinci ba..
Tafiya anty tayi ta basu wuri..yana shiga dakin ya tsaya gefe yana kallonta alamun barcin na mata dadi..
Gyara mata kwanciya yayi amma firgigit ta miqe tafara kuka..gaba daya hankalinsa ya qara tashi..kusa da ita ya zauna
"Kiyi hkr Amra kibarkuka plxx"
Yana fadan HK yasoma laluba aljihunsa wayarsa yaciro ya kira anty faty akan ta aiko musu da abinci..ba musu aka aiko hanan da abinci ta kawo musu..
Ahankali cikin hikima dararrashi Arman ya jawo Amra jikinsa jiyayi jikinta zafi rau alamun zazzabi ajikinta Anna kawo abincin ya soma bata daqyar yasamu ta qarba ko cin kirki batayi ba sekuma ta dena karba..
Kallonta kawai ya tsaya yi dik tayi wani iri kamar ba ita ba...
Ba shiri ya fasa tafiyarsa aranar wuni yayi a dakin agun yayi sallolinsa Wanda daqyar yake samu taa tashi tayi..
Can bangaran safiya kuwa ba abinda takeyi itama banda kuka da ambaton sunan Arman taci alwashin se Amra ta gane kurenta
Ranar kwana yayi a dakin ita kuwa ta wuni aikin kuka ba mgn..tinda sassafe wayarsa ta tashesa saboda rurin dayaji tanayi daga gurin aikin sa ne akan lallai seya komo aranar..
Anty faty yakira yasanar da ita ya nufi dakinsa ya shiryo yayi wa kowa sallama amma banda matarsa Amra..kin tashinta yayi Dan bayason damunta..
Ahk yayi tafiyarsa tare da barin sallahun waya abata Wanda zasu dinga gaisawa...
Ahankali Amra ta miqe daga kwaciyar dubawa tayi ba kowa a dakin Dan haka ta miqe ta nufi toilet wanka tayi ta gabatar da sallah Wanda ta makarayinsa..
Kayan da tagani saman gadon ne Wanda ykmt tasa tinjiya.. tsaki tayi tasasu ajikinta ko hoda bata sa ba harta juya zata fice ta hango wata takarda saman wani yadi..
Gurin ta nufa tana zuwa ta bude wasiqace..
_Dan Allah mamata ki kulamin da kanki banaso ki cigaba da kuka kuma ga hijab nan kisa kafin kifita innaso idan ndw naganki kina walwala kamar da..bye ki karbi saqona agun anty faty...Luv yuh_
Tsintar kanta tayi dayin murmushi sekuma tayi tsaki daga hijab din tayi harta ajiyeta sekuma ta warwareta tasa..hartakai qofa ta tuna da takardar Dan HK ta daukota ta riqe ahannu ta fice...
Tana fita goggo da anty faty ta tarar a palon..
Anty faty kuwa ba inda Idonta ke kallo se tafiyar Amra daga bisani tayi murmushi tare da fadin Alhmdulh aranta..
Gaidasu tayi dikka tare dayin murmushi suka amsa tsokanarta goggo tadingayi tana fadin
"Haka akeyi kawai jiya seki kwacan mijina?"
"Hmm waye mijin naki?"
"Ahhh kaji fitsara Arrrrmn yake ohm nidai kabiru na iya"
Dariya sukayi dikkansu
"Kedai kika damu dashi goggo"
Tafada tare da ficewarta daga dakin..part dinu ta nufa amynsu ta iske zaune da baqi suna hira gaidasu tayi dikkansu... tanason mgn da amyntata amma takasa Dan HK fita tayi ta tafi dakin anty Amarya tana zuwa bakin qofa ta leqa donganin ko hydar na palon ganin baya palon yasa ta shiga daidai anty Amarya ta fitoh daga kitchen...
"ahhh Amarya seda angon naki ya tafi tukun zaki fitoh?"
Tabe baki tayi ta gaida anty Amarya ta Amsa zama tayi akan kujera tana jira taji ko zata qara mata zance Arman ...itako so take taji inna ya tafi?
Ta qaraci za manta ta miqe ta fitoh ...dakin goggo ta nufa Dan da alamun can xatafi samun bayani dakyau baseta tmby ba...
Tafiya take cikin sauri tayi cinkaro da mutun tana dubawa taga safiya ce..
Kaucewa tayi amma safiya ta kuma tare hanyar..
"Dan Allah kibarni naje inda zani"
Acewar Amra
Murmushin mugunta Safiya tayi tare da fadin
"Banda lokacin ki ynxu amma zamu hade anjima"
Tana kaiwa nan ta bige kafadar Amra ta wuce abunta..binta da kallo Amra tayi daga bisani tayi tsaki dan tasan dik baze wuce akan ya Arman ba..
Tsaki tayi ta kama gabanta tana shiga dakin goggo tasamu wuri ta zauna...
"Amarya ya akayi ne?"
Acewar anty faty..
Girgiza kai tayi alamun a'a..zama tayi dirshen tana jin hirar goggo da anty faty so take taji inda Ya arman yaje amma bazata iya tmby ba gashi har ynxu anty faty bata bata saqon ba...
"Anty faty wai ba wani labari ne?"
Acewar Amra..
"Bakomai Amra yauwa Arman yaban saqo in baki"
Dadi ne ya cikata tadan juya gefe tayi murmushi tana juyowa taga anty faty na miqo mata kwalin waya dasauri ta karba tana murmushi bata zauna palon ba ta nufi daki ...
Kallo kawai suka bita dashi...
Kan gado ta zauna ta bude wayace sabuwa dal.. Gieoni P5W ...
Murna pall azuciyarta hada wayar tayi tasa sim din data gani aciki ta kunna ta...
Contact ta fara shiga ko zataga nunmbern Arman amma babu.. Tsaki tayi tafara tunanin yazatayi?
Kodai taje ta tmby anty faty..jitayi bazata iya ba Dan HK ta ajiye wayar ta zuba mata ido tana jirankira ..wayar na soma ruri tadauka ta kara akunta abinda taji ne ysa tayi tsaki ta kashe..
"Wa'annan Mtn din yan rainin hankankali ne..ynxu a inna zan samu number ya Arman godiya nakeso in masa fa"
Tsaki tadingayi itakadai adaki ...
*Queens Online writers*
Visit & join our group on Facebook *(Queens Hausa Novels)*
[7/17, 5:21 PM] Real Afreen ce💋: 👑👑👑
👸👸👸
*Queens online writers*
_Alkalamin Queens_
🍡🍡🍡🍡
🍡🍡🍡🍡🍡
🍇🍇🍇🍇🍇
~Rikicin~
*{Babban gida}*
Episode *21-25*
Tsaki tadingayi itakadai adaki daga bisani ta miqe cikin sa'a ta tarar anty faty ta bar palon..
Ahankali ta faki idon goggo ta dauki wayar anty faty ta shige daki..
Cikin sauri tashiga wajan calls din Anty faty can qasa taga ansa bro Arman..
Cikin sauri ta kwafe numbern ya Arman ta tafi ta mayar da wayar.. Dakin ta koma tayi save dinsa da Mr.man..
Tinani ta somayi takirasa karta kira farayi dailing sai kuma ta kashe...
Kasa nutsuwa tayi sai tsaki take tana yawo adakin..
Daga qarshe kwanciya tayi agun barci ya dauketa..
"Ke Amra tashi La'asar tayi fa"
Azabure amra ta miqe Dan ko sallahr azahar batayi ba..
Tana miqewa ta nufi toilet tayo alwalla tana fitowa ta gabatar da SALLAH..
Ahankali ta janyo wayarta 10misd call tagani Abun ya bata mamaki to wayasan numbernta da har aka kirata haka???..
Tana duba taga Mr.man. cike da mamaki tasoma fadin
"Dama ya arman nada numberna cabdijan"
"Bara nakirasa"
Harta dailing numbernsa saikuma ta qara kashewa..
Murmushi tayi ta ajiye wayar ta nufi toilet domin yin wanka...
Daure take da towel ajikinta ta fitoh tana goge jiki ga mamakinta taga mutun a tsaye safiya ce..
Yi tayi kamar bata ganta ba ta cigaba da goge jikinta gaban madubi ta nufa ta bude cream din dake gundan shafawa...
"Ke baki ganni bane?"
"Toh inna ganki fa goyaki zanyi?"
Cije lebe safiya tayi Dan taji zafin zancen Amra Dan HK ta nufi inda take..
"Wallahi Amra saikinyi nadamar auran ya arman saina koyamiki hankali"
Murmushin mugunta Amra tayi tare da fadin
"Ai dama kullun acikin nadamar aurensa nake..kuma da hankalina saidai inkece baki dashi kike bukatar inkoya miqi"
Daga hannu safiya tayi da shirin marin amra da sauri amra ta duqe..
"Wallahi karki kuskura ki mareni..ni kifita anan banida lokacin ki"
Wayar Amra ce ta soma ruri ahankali amra ta juya domin dauko wayar dasauri safiya ta nufi inda wayar take bazatoh ba tsammani taga safiya ta dauki wayar..
"Karki amsa min waya"
Acewar Amra
Kamar ko taqara ingiza safiya ta amsa wayar.. Karawa tayi akunenta..
"Nace karki amsa min waya ko?"
Safiya ko ko ajikinta saurarawa tayi taji ko muryar ya arman ce ..illai ko taji muryarsa..
"Safiya ki ban wayata"
Kamar akunnen ya arman tinani ya farayi meya kawo safiya gun Amra..
Kashe wayar yayi ya soma neman layin Anty faty..
Safiya kuwa tanajin ya kashe tayi dariya mugunta ta jefa wayar kan gado tare da fadin..
"Ki kiyayi haduwarmu ta gaba.."
Ficewa tayi bata jira jin ansar amra ba
Daukar wayar amra tayi kamar ta kira shi amma sai taqi.
Wani irin radadi takeji aranta daga wayar tayi tayi jifa da ita tadaki sip dinta ihu tayi ta kika ta zauna..
Hawayene yafara zuba a fuskarta dasauri ta share hawayen fuskarta ta sa kayanta hartakai qofa ta tuna da wasiqar ya Arman akan tadinga sa hijab cikin sauri ta juya ta nufi wajan sip din harta dau hijab din ta juya taji wayarta ta fara ruri..
Kamar jira take ta nufi gurin da sauri..Daur wayar tayi arman ne dasauri ta amsa ta kara a kunenta amma kasa cewa komai tayi..
Shiru sukayi dikkansu na 'yan mintina jin shirun yayi yawa yasa ya Arman yasoma fadin..
"Meyaa kawo safiya gunki"
"Nima bansani ba"
Ta basa ansa cike da shagwaba kamar zatayi kuka...
Dadi sosai Arman yaji atunaninsa bazata ansasa ba Dan hk ya kuma fadin
"Kiyi hakuri zan mata mgn"
"Toh" kawai ta fada suka kuma yin shiru dikkansu harna yan mintina...
"Kinci abinci kuwa"?
" a'a ynxu xanje inci"
"Tofa jekici xankiraki anjima"
Yana fadan hk ya katse wayar..
Shiru tayi ta cire wayar daga kunenta ta kara a qirjinta murmushi tayi kafin ta miqe tasa hijab din tafice..
Dakin amynta ta nufa cike da shagwaba ta kwanta akan qafar amynta wacce ke zaune a Palo..
"Kekuma har ynxu bakisan kingirma bane?"
"Anmyta wai inna ya Arman ya tafi ne?"
"Oho aiki ya tafi mana.."
Murmushi kawai Amra tayi tare dayin shiru tana tinanin meyasa ya Arman be tafi da ita ba..
Washe gari
Zaune Amra take zaune apalon anty Amarya tana kallo .hydar ne yashigo palon tsayawa yayi yana kallonta ahankali ta juyo ganin shine yasa tayi tsaki ta ta miqe zata shige dakin anty Amarya dasauri ya riqota.
"Kasakeni ka qyaleni"
"Meyasa bakyason mu hadu ynxu meyasa kike gudu na?kodai Arman ya hire miki kunene"
"Inkana surutanka karka kuskura kasa mijina aciki Dan ba sa'aryinka bane..ka qyaleni innasan mijina"
Sake baki hydar yayi yana kallon Amra da mamakin abinda take fada
"Amra ni kike fadawa kinason wani bani ba?"
Share hawayen dake fuskarta tayi kafin ta soma fadin
"Ya hydar nasoka ada lokacin danayi tunanin kana sona..ka cuci rayuwata bana qaunarka banason ganinka ka matsamin"
Tana kaiwananta fashe da kuka..
Muryar anty Amarya sukajiyo tanafadin
"Mexan gani haka iye hydar"!!!!
*Queens online writers*
[7/21, 4:17 PM] Real Afreen ce💋: 👑👑👑
👸👸👸
*Queens Online Writers*
_Daga Alkalamin Queens_
*Saqon gaisuwa mai tarin yawa zuwa ga masoyan mu mungode sosai da qauna Allah ya bar xumunci*😍
🍡🍡🍡🍡
🍡🍡🍡🍡🍡
🍇🍇🍇🍇🍇
~Rikicin~
*{Babban gida}*
Episode *26-30*
"Mexan gani haka iye hydar"!!
Ja dabaya hydar ya farayi yana Sosa qeya kunya ce ta rufesu dikka bama kamar Amra da ce ta tsani ya hydar...
" umma Ku tsaya kiji"
Acewar hydar
Daga masa hannu tayi tare da fadin
"Ya isa hk banason jin dog on bayani...kasan cewa Amra ynxu tanada aure atanta kokunqi ko kunso dole Ku hakura da junanku..Dan hk inna gaisuwa ba banaso inqara ganin haka"
Gabadayansu ajiyar xuciya suka dauke bama kamar amra wacece dik tabi ta tsargu...
Ficewa tayi daga palon bata jira cewar su ba.. Yana fita momy ta fara masa fada akan batason taqara ganin sun kebe da amra saboda inshi akama haka bazeji dadi ba..
Kallan anty Amarya ne suka ratsa jikinsa gabadaya yayi sanyi sai a ynxu ya fara danasanin abinda ya ma amra...
Godiya yama umman tasa kafin yashige daki...
Amra kuwa tana fita da side din anty Amarya part dinsu Arman ta nufa kasancewar yasu taxi daya da safeena watoh qanwar Arman...
Tanazuwa bata iske kowa a Palo ba dan haka ta wuce tanufi dakin su safeena...
Kamwance ta iske safeena akan gado tana karanta novel awayarta mai suna (Tamishi illah) Na Fadeela lamido
Duka Amra takaima safeena..
"Kefa banxace wallahi kiyitafaman aikin karanta novel"
Tsaki safeena tayi tare da miqewa zaune tana fadin
"Ynxu xakizo kidameni"
"Dallah dan ma nazo tayaki hira"
"Au yi hakuri Ashe yanxufa matar yayace"
Tsaki Amra tayi tare da fadin
"Bara bason haka"
Dariya safeena tayi tare da fadin
"Haba Amra yadai kamata ace ki hakura kiso mijinki tinda haka Allah ya qaddara miki..kuma nasan ya Arman baze taba cutar dake ba"
"Hmm kawai amra tace"
Safeena ce hango wayar dake hannun Amra
"Laaa Amra waya kikayi shine bazaki fadamin ba"
"Yi hakuri dan Allah yayanki ne ya bayar abani"
zaro ido safeena tayi tare da fadin
"Ke ba yayanki bane?
Ohhh nagane mijinkine shi".
Duka Amra yakaima safeena nanfa suka fara hira har safeena ta budewa Amra watsapp...
Sunan Mr.man ne ya appear a contact list dinta kawai...
Nanfa safeena tasa mata numbern ta bayar ajasata a groups...
Ba ita ta bar gun safeena ba sai 10...
Part dinsu ta nufa yau bata da niyar kwana a dakin goggo..dakin ta ta shiga direct ...caji ta sa wayarta kafin ta shiga toilet wanka tayi kafin ta nufi kitchen domin diban abinci saboda wata iriyar yinwa da takeji...
Indomie ta dafo ta dawo daki..zama tayi kangado tadauko wayarta ..kunna data dinta tayi...prfle din ya arman ta nufa hoton dake kan dp dinsa ta bude tana kallo...
Ya Arman ne yasha kakinan nasa na sojoji gabindigarsa a hannu murmushi yayi ahoton Wanda ba qaramin kyau yayi ba zuba masa ido tayi nanfa ta tsinci kanta da yin murmushi...
Message taga yashigo Mr.man dasauri ta bar gun prfle din nasa ta nufi gun message tana budewa taga ya rubutoh mata
_😡Kaii baby waya bude miki watsapp baki fadamin ba plxx banso ki kula wani_ I miss u
Murmushi kawai ta dingayi tama rasa mezata rubuta masa
Nanfa suka dinga hira kamar me...
Akwana atashi yau sati biyu da bikinsu... Waya suke Sosai tana zuba masa shagwaba..shiko ya arman ganin ynxu Amra ta sake dashi yasa ya fara tunanin yadawo ya tafi da matarsa kawai...
Kullun sai tayi hoton ta tura masa haka shima sai ya turo mata...
Yau ta kama ranar juma'ah
Zaune Amra da safeena suke suna kwalliya..wayar Amra ce ta fara ruri dasauri Amra ta dauko tare day in murmushi ta kara a kunne...
Sallamar da ta masa ma ita kanta cike da shagwaba tayi ta safeena kuwa kallon Amra kawai takeyi yanda ta zage tana zubawa ya Arman shagwaba...
Abinda yafi bata mamaki ma dataji tace masa my hero...
Nanfa suka dinga soyy a waya abinsu suna hira sai dariya suke...
"My hero wai yaushe xaka dawo ne"
Dadine ya shika Arman dayaji tamasa wanan tam bayar murmushi yayi sosai kafin ya soma fadin
"Dole indawo intafi da matata cox am missing her a lot"
Dariya sosai Amra amtayi tare da jin dadin abin da ya Arman ya fada.. Rufe fuska tayi kamar yana kallon ta itadai safeena na gefe ta zuba mata ido...
Nanfa suka shirya akan xexo daya samu Hutu agun aiki..
3weeks later**
Akwanakinan Amra ciye2 kawai takeyi harda su goro kowa tsiya yake mata...yaukam da masanancin ciwonciki Amra ta tashi..
Kowa gigicewa yayi agidan haka aka sunkuceta sai asibiti nanfa aka mata yan gwaje gwaje aka gane tana dauke da juna biyu...
Kowa mamaki ya farayi amma anty faty ko sanar dasu cewar tayi ai ran da aka daura aure adakin goggo suka kwana shida ita....
Nanfa daga mamaki aka koma murna...
Nanfa anty faty ta kira arman
"Hello Soja Dan gayu...ka taho gida Abban ka na bukatar ganinka emergency"
"Anty faty lafiya?"
"Kaidai kazo kar yayi fushi tam baruwana"
Kashe wayar tayi shiko masa nutsuwa yayi yafara tunanin yadda sedai excuse yasamu ya tafi...
Koda labari ya iske hydar hankalinsa tashi yayi gumi ya dinga hadawa ya kasan nutsuwa...
Safiya kuka tadingayi tare day in alwashin saita zubda ciki nan bazata yarda Amra tahaihu da ya Arman ba Dan Arman nata ne itakadai...
Amra kuwa tinda safeena ta fada mata take kuka ko abinci yaqi ci..hankalin kowa a tashe yake dan ji ake da cikin dake jikinta bama isa yan dakinsu Arman din kamar su goyata itako abinduniya uabi ya isheta...
Inya Arman yazo yazatayi???😭
Kucigaba da kasancewa damu...yazata kasance a episode din gaba?..
Ynxu idan Arman yasan tana ciki yazata kasance????
*Queens online writers*
[7/22, 4:02 PM] Real Afreen ce💋: 👑👑👑
👸👸👸
*Queens online writers*
_Daga Alkalamin Queens_
*Asallamu'alaikum naga comments dinku toh ataqaice star din littafin daga farko itace muka maida mata _AMRA_ shikuma kabir ya koma _ARMAN_*
_Masu batun ciki na Arman ne ko ba nashi bane?Toh Ku qara tariyo baya saboda ciki bana Arman bane na hydar ne_
Godiya me tarin yawa ga masoyan mu Queens😍👍mun gode Allah yabar zumunci
🍡🍡🍡🍡
🍡🍡🍡🍡🍡
🍇🍇🍇🍇🍇
~Rikicin~
*{Babban gida}*
Episode *31-35*
Washe gari tinda safe kowa ya hallara kowa da sallon girikin da akawa Amra ba Wanda baya farinciki da cikinan inba hydar da safiya da ita kanta ba... Dan cikinan babban tashin hankali ne agaresu bama kamar Amra wacce ba abinda takeyi banda kuka komai taqi yarda taci..
"Hello Arman kanajina"
"Eh anty faty innajinki meyafaru"
"Arman gafa Amra bata da lafiya kuna taqi cin komai fa"
Hankalin Arman ne yaqara tashi sosai Dan hk cikin rawar murya yace abama amra wayar sa mata akayi akunne amma ba abinda yakeyi banda kuka Dan dik atunaninta sunriga sunfada masa cewar tanada ciki...
"My baby kukan me kikeyi karki manta bakida lafiya fa plxxx kici abinci kinji ko"
Shiru amra tayi tana sauraron sa tsananin mamaki ne ya kama amra me ya arman ke nufi ze karbi cikin kenan koda ba bashi bane?
Muryarsa ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin da take ciki..
"Kici abinci kinji baby inba hk ba ko nazo bazan tafi dake ba kuka nima rashin lafiya zanyi"
Soma share hawayen ta tafarayi sai aynxu tasamu damar yin mgn..
"Zanci... Yaushe zaka zo?"
"Gobe ko jibi insha Allah"
Addua ta masa kafin sukai sallama akan anjima ze qara kira yaji ko taci abinci...
Nanfa akasamu amra taci amma kusan Rabin abinda taci dik ta amayar dashi...
Daddare Aka sallamosu suka koma gida dakin goggo ta sauka saboda goggo ta takura sai dai ita zata kula da Amra ba ai mata musu ba aka barta...
Dakin nan data fara kwana nan aka sauketa aka ta....
Dik abinda tace tana buqata suna mata amma har yau bata dena kuka nan ba kowa na mamakinta...
Washe gari da safe Amra na kwance ta rufe ido kamar tana barci amma idonta biyu..ji tayi an turo qofa ahankali ta bude fuskarta da mamakinta sai ganin safiya tayi...
da sauri ta miqe zaune tabi safiya da ido...ahankali safiya ta soma tafiya har saida takai inda Amra take..
"Murna nazo tayani da kuna baqincikin abinda ze faru dake kwanan insha Allah"
Gaban Amra ne yafadi da jin zancen safiya tinani ta farayi kardai ace safiya yasan sirrin da take biyewa? Toh taya za ayi yasani inbadai ya hydar ne ya fada mata ba...toh ai kuna mgn kirki bata hadasu da hydar...
Qarar bude qofar dataji ne ya dawo da ita hayyacinta..ganin safiya tayi tana qoqarin fita kaikuma ta juyo tana fadin
"Farinciki shin samun cikin baqin cikin kuna shine nixanxama ajalin cikinan sai ya zube ya Arman nawane"..
Sai alokacin Amra tasamu qarfin yin magana Dan taji ba abinda take zargi bane..
" ya isheki haka..mijina yafi qarfinki idan kinacin qasa ki kiyayi ta shiru..ciki kuwa in kinga dama kixubar dashi ynxu ynxunan...ya arman kuwa ya miki nisa"
"Wallahi zaki sha mamaki ne amra ni kike fadawa wa'anan kalaman ko"
Tsaki Amr@ tayi tayi ta koma ta kwanta safiya kuwa ficewa tayi tare da buga qofa bummm...
Yautake ranar da Arman XE dawo dik inda hankalin Amra yake yayi dubu a tashi yake SBD har ynxu a tsorace take ..
Misalin qarfe 11:45am arman ya iso yana isowa akafara mai sannu da zuwa...
Anty faty ce ta jashi sukai part din goggo a Palo ta tsyar dashi ...
Wani Elgmnt din hoto babba takawo masa wanan nade yake...
Ahankali yana murmushi ya bude Dan ganin meye wanan...
Hoton baby ya gani ajiki..
"anty ai wannan hoton jariri ne..me kukeci na baka na zuba insha Allah kun kusa samun jika"
Murmushi anty faty tayi tana fadin...
"Ai munsamu qaramin Soja Dan Amra nada ciki"
Dariya Arman yafara yi itama anty faty sai wangale baki takeyi Dan dik a tunanin ta. Murnace...
"Kaiii anty faty Abun naki harda zolaya kuma ynxu dai inna amra"
"Tana cikin dakin mana dgsk fa nayi Arman"..
Murmushi ya kum ayi yashige dakin Anty faty tabi bayan sa...
Yana ganin amra sukayiwa junansu murmushi
" baby kinji fa anty faty sosuke mu basu baby"
Shiru amra tayi jikinta yafara rawa alamun bemasan tanada cikin ba..
"Wanne ciki kuna banda Wanda ke jikinta"
Shiru arman yayi ahankali fara'a mr dake fuskarsa ta dauke ya juyo yana kallon anty faty..itako gyada kai tayi tana murmushi
"Eh Arman kakusa kazama abba"
"Yuh mean Amra Nada ciki?"
"Eh Arman ciki ne da ita 1month"
Kallon Amra yayi ya fara nunata da yatsa yafara ja da baya har saida yakai qarshen bango kafin smya silale qasa ya zaune dabas...
Anty faty kallon su ta tsayayi Amra yayi amra kuwa kuka tafara harda shesheqa tasa hanunta ta rufe bakinta..
Kusa dashi tafara matsowa dasauri ya daga mata hannu alamun ta tsaya..
"Wai meye haka meke faruwa ne?"
Acewar anty faty wacce ta tsaya kallonsu da mamakin abinda taga sunayi..kuka amra keyi kamar ranta zefita tana fadin
"Kayafemin kayafemin"!!!
_Tofa anfara rikicin babban gida_
*Queens online writers*
[7/27, 2:20 PM] Real Afreen ce💋: 👑👑👑
👸👸👸
*Queens online writers*
_Daga Alkalamin Queens_
Note:
*Plxxx munada yar matsala atafiyarmu a novel dinan..a musulunce hukuncin matar auren da tayi zina shine a gefeta..idan muka cigaba da tafiya ahaka toh qarshe jefeta za ayi kuma bamason kashe star din novel din ynxu saboda munada sauran tafiya agaba...Dan haka muncanja salon akan ana gobe daurin auren ne taje gun hydar*
_plxxx kowacce ta karanta abinda ke sama👆kar qarshe nazo Anna kawo mana complain akan ga abinda ya kamata plxx_
🍡🍡🍡🍡
🍡🍡🍡🍡🍡
🍇🍇🍇🍇🍇
~Rikicin~
*{Babban gida}*
Episode *36-40*
Acewar anty faty wacce ta tsaya kallon su da mamakin abinda taga senayi...kuka amra kayi kamar ranta zefita tana fadin
"Kayafemin kayafemin"
Kasa magana yayi wasu guntayen hawayene suka zubo masa a fuska dan hk yamiqe cikin zafin nama yanufi qofar fita anty faty kiransa takeyi amma kamar tana magana da dutse...
Itako amra silalewa tayi qasa tana rusa uban kuka..har yakai qofa ya bude ze fita ya juyo yana kallon amra sekuma ya fice daga dakin...
Karasawa gurin ta anty faty tayi tana fadin
"Meye haka ne? Kunqi fadamin abinda ke faruwa kunsani a duhu"
Qinmagana amra tayi sai kuka takeyi itakuwa ganin kukan nata bana qarewa bane yasa anty faty ta miqe ta fice daga dakin abunta tanazuwa gun ammyn amra ta sanar mata abinda ke faruwa cikin sauri suka nufi inda take harda goggo wacce aynxu suka tarar a dakin...
Cikin sauri ammynta ta qarasa..
"Amra meke faruwa ne?kibar kuka nan haka karfa kimanta da yanayin dakike kifadamana meya hadaku..
Cikin kuka ta rungume ammynta tana fadin
" Ammyna Dan Allah Ku yafemin wallahi bahaka bane"
Qara rikitasu tayi sukayi sukayi ta fada abinda ke faruwa amma taqi yarda tafa...
Yaukam safiya batasan meke faruwa ba agidan tayi shirinta tsaf na tafiya gun yayansu dake aure Mina...
Arman kuwa tinda ya tafi dakinsa ya shige ya kulle qofa banda kuka ba abinda yakeyi ..tinani ya farayi toh cikin waye?yama za ayi ace Amra tayi zina bazema taba yiyuwa ba..
Wani sabon kukan ne ya kufce masa ya rasa yanda zeyi..
Anty faty kuwa hankalinta kasa kwanciya yayi Dan haka kiran Abban Arman tayi ta sanar masa abinda ke faruwa..
Kankace me antarasu a dakin goggo amma arman yaqi zuwa daqyar mumy tasamu yafi toh ya taho..
"Kaii Arman meyaa faru ne?banason shashanci fa"
"Daddy bansan meyafaru ba kuta tmbyt"
"Inna maka mgn kana cemin atmbyt ya kuke Neman maida mutane mahauka tane?"
Mumy ce tayi caraf da fadin
"Haba Dan Allah abisa ahankali mana"
"Banaso kiqara mgn kinajina ko?"
Acewar dady
Tabe baki tayi shiru..
Amra kuwa nadaga gefe ba abinda takeyi banda kuku
Kallon Amra dady yayi yana fadin
"Bazakiyi mgn bane kema"
Kukan nata qaruwa yayi sosai ran Abban ta kuwa harya soma baci..miqewa yayi cikin sauri gadan gadan yayi kanta..ganin haka yasa arman ya tsorata kar a illatata cikin sauri yasoma mgn
"Kayi hakuri Abba zan fada"
Cikin sauri amra ta dago kanta ta kalli arman ta girgiza kai dubawa tayi kaf gurinan hydar bayagun..
Dady ne yana abba hkr akan yadawo yazauna..
Goggo ce ta kalli arman wacce se aynxu ta tanka tana fadin
"Kai muke sauraro"
Cikin 'in'ina yasoma mgn..Dan hk amra ta qara sautin Ku kanta
"Ba baba".
" ba ba meye?" Acewar mumy
Rufe idanunsa yayi tare dauke ajiyar zuwa yana fadin
"Ba cikina bane"
Sallati akahau raftakawa apalon kowa na kallon amra wacce ta dunqule kanta a gwowowinta...
"Arman kana da hankali kuwa"
Acewar mumy
"Lafiya ta lau momy.."
Sai kuma ya fashe da kuka yana fadin
"Bacikina bane bansan dashi ba ta yaudareni.."
"Mumy dik sonda nake ma amra tamin haka"
Magana yake yana kuka wani Abun nasa ma basa gane me yake fada jijiyoyin kansa dik sun tashi..
"Mumy dik abinda nake mata be isheta ba..nabarta agida saboda banason quntata mata har sena soni amma zata min haka"
"Mumy mena ma amra mumy ki tambayayeta laifi na mat*****ta**AAA"
Qarar saukan marin da sukaji ne yasa sukayi saurin juyawa ..Abban amra ne ya mareta..
"Amra irin tarbiyar dana baki kenan?watoh gsky ne shiyasa kika qasa qaryata zancen sa"
Ammynta dake gefe tana hawaye ta soma fadin
"Me muka rageki dashi meyasa zaki mana haka?cikin waye amra"
Kasa jurewa arman yayi ya miqe ya fice..ita kanta goggo hawaye yakeyi tama kasan fadan komai..anty faty kuwa mutuwar zaune tayi..
Kuka kawai amra keyi abba ne yaqara kai mata duka
"Bazaki yi mgn ba"
Dady ne ya soma fadin
"Kubita ahankali wannan hayagagar qara furgita zakuyi"
Abban Amra kuwa kamar an qara ingiza sa wayar wutar dake jikin socket ya zaro... Kiran sunansa akeyi Anna fadin a a.. Amma inna yaqi kan amra ya nufa cikin zafin nama..ganin dgsk yake yasa ta miqe..
"Xan fada abba wallahi ya hydar ne"
Cakkkk Abban nata ya tsaya jikin kowa yayi sanyi..anty Amarya dake gefe tana sharar hawaye saboda tausayin amra tayi saurin miqewa cikin tashin hankali
"Wanne hydar din hydar nawa?"""""😱😱😱😱
Mahaifin hydar dake gefe ya gyda kai yana fadin
" hydar nawane agidan kuma kinsan bazata masa sharri ba"
Jikin Abban amra ne ya mutu besan sadda wayar wutan ta sulale ahanunsa ba.. Samun guri yayi yazauna yana salati..
Cikin zafin nama Abban hydar ya miqe tafita yana qwalawa hydar kira..
Ammyn amra kuwa ba abinda take fadi banda
"Amra kiban kunya ..amra bansanki ba"
Mgn take tana kuka..amra ke gefe har shesheqar kuka takeyi tana fadin
"Dan Allah Ku yafemin"
Afusace abbanta ya dago .
"Zakici ubanki keda yafi yar"
"Wa'iyazubillah habba haba kar hankalinka ya gushe mana saboda bacin rai"
Hydar ke kwance yana shaqar barcin sa bemasan meke faruwa ba baki qofar da yaji anyi ne yasa ya juyo kan ya Ankara yaji saukar wayar wuta ajikinsa da gudu ya dita ya nufi qofar fita kan kace me ya isa tsakar gida muryar Abban sa na rawa yana fadin
"Hydar nixaka kunyata kayiwa matar wanka ciki nixaka kunyata?hydar tsinema zanyi bazan xauna da mazina ci ba"
Su kuwa suna jin hk suka fitoh..
Hakuri aka dinga bama Abban hydar amma ko ajinka..hydar ma kuka yake yana na tuba...
Cikin sauri Abban amra yace dole arman yasaki amra hydar ya aureta shine kwanciyar hankalin mu..
Cikin sauri Amra ta zube gaban ammynta tana fadin
"Kutaimaki rayuwata wallahi banason ya hydar na tsaneshi"
Hakadeta ammynta ta tayi Dan haka ta nufi gurin mumyn arman tana fadin
"Mumy kice kar su rabani da ya Arman wallahi innason mijina "
Kuka takeyi kamar ranta ze fita..
*Queens writers*
[8/7, 2:39 PM] Real Afreen ce💋: 👑👑👑
👸👸👸
*Queens Online writers*
_Daga Alkalamin Queens_
_(Home for wisdom & perfect online writers🖌)_
*(Q.O.W)👑*
🍡🍡🍡🍡
🍡🍡🍡🍡🍡
🍇🍇🍇🍇🍇
~Rikicin~
*{Babban gida}*
Monday's update 7th August 2017
Episode *41-45*
"Mumy kice karsu rabani da ya Arman Wallahi innason mijina"
Kuka takeyi kamar ranta ze fita....
Ya Arman dake daki yana jiyo zancen su saurinfitowa yayinda kanshi kesara masa sosai idanunsa sunyi jawuri...
Hydar kuwa farinciki yake can cikin ransa ynxu xe kasance da Amra farincikinsa
Isowar ya Arman ne yasa dik hankalinsu ya karkata garesa..
Fuskarsa ba alamun fara'a..
Binsa sukayi da kallo harsaida ya isa gurinda amra take ..kowanensu jikinsa yayi sanyi sutsaya kallon me Arman zema Amra rawar jiki ita kanta tafarayi dan dik ta tsorata...
Ruqo kafadunta yayi ya tsaya kallonta na yan mintina daga bisani ya rungumota jikinsa yayinda hawaye ke xuba afuskarsa..
Wani irin kuka tafashe dashi kamar dama jira takeyi..
Shiru kowa yayi suka tsaya kallon Arman da mamaki..
"Ba Wanda ze rabani da Amra inna son matata"
Acewar arman
Magana yake yana hararar Hydar dake tsaye yana kallonsu ya cika yayi fammm..ita kanta amra yayi mamakin zancen sa sands ta dago ta kallesa..komawa yayi ta lafe kan qirjinsa
"Kaiiii Arman kanada hankali kuwa"
Acewar Abban Arman..
"Abba da hankalina innasan matata ya za ayi arabani da ita kuma Wanda zaku bata bata sanshi"
Kowa agun kasa magana yayi sai Abban Amra ne yake qoqarin amsa shi..
"Arman nima mahaifine gareka bazan yarda kazauna da ita ba..ta bata ma suna ba"
Yana fadan haka be jira amsar da Arman ze bashi ba ya finciki Amra da ga jikin Arman
"Karka kuskura kace komai kuma karka biyoni inhar na isa dakai"
Abban Amra ya fada ..kuka sosai takeyi tana kiran sunan Arman tana bama abba hakuri amma inna janta yakeyi Arman miqa hannu yakeyi yana hawaye..
Kowa agun zubar da hawaye yakeyi..ammynta kuwa kasa daurewa tayi dan haka tabi bayansa tana fadin
"Haba Abban husna kamata ahankali mana karka illatata"
Binsa sukeyi suna basa hakuri amma ita yariga ya zuciya...dakinta ya bude ya jefata har sanda goshinta ya bugi gado ..ihun da tafi ne yasa Arman ya nufi inda suke cikin sauri amma kan ya qarasa abba yasa ma qifar key yana isowa ya sulale bakin qofar yana kuka...
Mumy ce ta tsugunna ta rungume Arman ta baya daqyar tasamu Arman yabar gurin..Abba kuwa tinda yasama dakin key yabar gurin ya nufi dakinsa...
Amra kuwa kukanta tavi me isarta har barci ya dauketa..
Arman kuwa dakinsa mumy ta rakasa saman qafarta ya kwantar da kansa ya sulale qasa itako tana zaune saman gado..
"Mumy dan Allah ki musu magana su dawo min da matata"
"Haba Arman ka hakura da amra ciki ne fa da ita..gsky bazan goyi bayan ka cigaba da zama da ita ba"
Cikin sauri ya dago jajayen idanunsa ya kalli mumy
"Haba mumy!! Itace farinciki na dan Allah karku rabani da ita"
Hawayen fuskarta mumy ta share dan gabadaya tausayin Arman yakamata...
"Kayi hakuri Arman ga safiya itama ai sanka takeyi kuma tafisonka akan Amra"
"Mumy banaso matata nakeso abani"
Shiru mumy tayi na yan mintina...
Taba jikinsa tayi taji harya dau zafi rauu...
Kan gadon tasashi ya koma ta lullubesa ya kwanta yana mata magiya ahk barci ya daukesa
*Washe gari*
"Haba Abban husna ya za ayi kace haka?"
"Nidai nafada dik Wanda ya bata abinci ban yafe ba harsai randa Arman ya hakura da ita dan bazan yarda na basa ita ba kuma itama sai ta yarda zata aure hydar din"
"Haba dan Allah komai fa ahankali ake binsa karka uzura musu dayawa"
"Kifa bar bata bakinki saboda bazan dau wannan shashancin ba"
Shiru ammynta tayi daga bisani ta miqe ta isa Palo da mamakinta Arman ta gani ya kusa qarasa wa qofar dakin amra..
Juyawa tayi ta kalli dakin abba kafin tayi saurin qarsawa
"Arman me kakeyi anan"
"Ammy dan Allah kubari inga matata dan Allah"
Shiru ammy tayi ta rasa mezatace dan tausayin Arman ya ratsata..
Ganin abba na qoqarin bude qofar dakinta yasa ammy tayi saurin boye Arman abayan qofa..Lamarin ba qaramin mamaki ya bama Arman ba..
"Toh meyasa ammy zata boyesa dan Abba ze fitoh"
Yana cikin tunanin yaji ammy na ambaton sunansa..
"Ammy dan Allah kitaimaka kibari naga amra"
"Arman kataimaki kanka ka taimaka amra kataimakeni ka bar nan karka qara dawowa"
"Ammy dan Allah karki min haka laifin me namiki dan Allah kitaimakamin"
Shiru ammy tayi daga bisani tace
"Kajirani inna zuwa"
Juyawa tayi ta nufi dakin abba saman sip ta fara dubawa cikin ikon Allah ta riqo key din dakin..
Jikinta na rawa ta fitoh daga dakin ta nufi dakin amra...
Tsaye taiske arman..tana zuwa suka fara qoqarin bude qofar..
Kwance shame shame suka iske Amra.. Nanfa suka qara rikicewa..taimakon gaggawa suka soma bata dik ta jigata..daqyar suka samu ta farfado idanunta sunyi manya tsabar kuka..
Rungumeta Arman yayi ya roqi ammy data kawo abinci abama Amra...
Batayi wata wata ba yaje ta kawo dan acewar ta bazata iya kashe yarta ba...
Bayan sungama ne ammy ta tattare plates din tana fitowa tayi cikaro da Abba nantake plates din suka zube akasa ...
Gaba dayansu sun tsorata dan fuskar abba atamke take babu alamun fara'a
*Queens Online writers*
*(Q.O.W)*👑
[8/13, 12:31 PM] Real Afreen ce💋: 👑👑👑
👸👸👸
*Queens online writers*
_Daga Alkalamin Queens_
*👑Queens online writers*
*(Q.O.W)👑*
_(Home for wisdom & excellent writers)_
🍡🍡🍡🍡
🍡🍡🍡🍡🍡
🍇🍇🍇🍇🍇
~Rikicin~
*{Babban gida}*
Saturday's update 12th August 2017
Episode *46-50*
Gaba dayansu sun tsorata dan fuskarta abba atamke take babu alamun fa'a...wani irin miyau me daci ammynta hadiye...cikin sanyin jiki Arman ya miqe yana fadin
"Abba kayi hakuri laifinane"
Cikin sauri ammy tace
"A'a ba laifinsa bane Nina bude"
Ammy tafada tana girgiza kai..bude baki Arman yayi da niyar mgnda sauri abba ya karbesa da fadin
"Banason dogon surutu danace kar abudeta shine kika budeta ko"
Shiru yayi kafin ya cigaba da fadin
"Kuma kai Arman indai harkanason Amra ta fitoh anan seka hkr da ita ta auri hydar din"
Wani iri Arman yaji baze taba yarda amra ta auri hydar ba..kallon amra abba yayi cike da takaici ya nunata da yatsa
"ke nixaki toxarta ki fita zakka acikin yan uwanki ko?toh in har kinason zaman lafiya tohki auri hydar"
Kuka tafarayi sosai tana fadin
"Dangirman Allah abba kayi hkr kayafemin dan Allah"
"kufita Ku bani wuri ki kulle kofarkimaidamin key din ..dik Wanda ya sake daukowa ransa seya baci..."
Riqe Arman tayi gam tana kuka mecin rai...
Arman kuwa yariga yagama fusata dan haka yasa hanunsa ya cire hanun amra daga ruqon da ta mishi harya kai qofa sai ya juyo ya kalleta kafin yayi wuuff ya fice daga part din...
Side din goggo ya nufa zaune ya sameta shiru ita kadai..
Sallama yayi cikin ruwan sanyi yasamu wuri a qasa kusa da goggo ya zauna..
"Arman ya akayine"
"Goggo dik sun birkitamin tinanina da wanne sukeso inji ne?da abinda amra tamin kokuma da rabani da ita dasukesonyi"
"Arman kati hkr ka sallama mata tabi umarninsu tinda ita ta bata musu..batan tanasonka ba ta bari hydar din yashiga rayuwarta"
"Haba goggo a tunanina ke kadai zankawowa kukana dik fadin gidanan ki fahimceni amma segashi kema kina qoqarin qin taimaka min goggo sun hanata fita sun hanatacin abincin abba so yake ya kasheta"
Shiru goggo tayi kafin ta soma fadin
"Kayi hkr zan aika akiramin Abban nata kaji kayi hkr"
Kasa cewa komai yayi sema qara zamewa da yayi ya sulale qasa ya kwanta...
_Bayan kwana biyu_
*Night*
Cikin sanda Arman yake hawan ladar dayasa jikin bangon dazesadasa da window din dakin da amra take..
Ahankali ya taka harya isa window din..zaune take kan sallaya ta idar da sallah tana sharar hawaye kamar daga sama ta jiyo muryar Arman yana kiran ta..
"Baby!!"
Kalle kalle tafarayi can ta hangosa jikin window ...kofa ta kalla kafin ta qarasa gunsa da sauri ta riqe hanunsa guda daya dake riqe da qarfen window din dayan hanunsa ya miqa mata da leda karba tayi ta bude..
Take away din abinci ne da hollandia dink da fruit.. Kallonsa tayi zatayi mgn yasa hannu akan lebenta yana fadin
"Shhh banason mgn kije kici dik kin rame baby ji bakinki dik ya bushe...ki ajiye leden kar abba ya gani zan karba gobe"
Gyda masa kai tayi kafin ta koma ta zauna gefen gado tafara bude ledar.. Fried rice ce taji salad da nama dan take away din kuma tuwo ne..
Shiko sauka yayi ita kuma ta fara cin tuwon tacinye Tass tasha drink din anan barci ya dauketa...
Tinda sassafe kuwa ta ci shinkafar dik da tayi sanyi sosai amma bayanda ta iya sbd jitayi kamar bataci komai ba daddaren..
Arman kuwa yana jikin window yaga shigar abba part din goggo dan hk yayi saurin fita dan ya roqi ammy ta budemasa yabama amra abin kari..
Dai dai yafitoh kenan sukai cinkaro da hydar wani irin takaicine yacikssa
"Watoh shi hydar yanaan yana sha'aninsa ko ajikinsa..."
Cikin sauri Arman ya qarasa gun hydar..hydar na ganinsa ya fara qoqarin guduwa..
Dasauri Arman yaqara sa..
"Nadade innason haduwarmu..hydar nixakawa hk ko?"
Acewar Arman turo baki hydar yayi ya fara qoqarin yin wani zancen banza dan hk ran arman ya baci..duka ya kaima hydar abaki aikuwa ya fasa masa baki ...sakesa hydar yayi dan hk zaro ido hydar ya farayi yana taba inda jini ke fita...
Rai bace Arman yace
"Kadan ka gani"
Yajuya ya nufi part din su amra hydar kuwa ya sake baki yakasa cewa komai
*Queens online writers*👑
[8/15, 4:16 PM] Real Afreen ce💋: 👑👑👑
👸👸👸
*Queens online writers*
_Daga tsakar Queens_
*👑Queens online writers*
*(Q.O.W)👑*
_(Home for wisdom & excellent writers)_
🍡🍡🍡🍡
🍡🍡🍡🍡🍡
🍇🍇🍇🍇🍇
~Rikicin~
*{Babban gida}*
Monday's update 14th August 2017
Episode *51-55*
Part din su ya koma anty Amarya na zaune tanaganin shigowarsa harta kauda ganinta daga garesa sbd ya bata mata rai akan abinda ya aikata sekuma taga jini a bakinsa..
"Meyasa meka?"
Kusa da ita ya qarasa ya zauna
"Ya Arman ne haka kurin fa nazo wucewa ya bugammin baki"
"Kodai wani Abun kace masa hydar"
"A a umma bada abinda kace masa"
Wani irin qululu anty Amarya taji yazo mata..toh meyasa ze dakin mata da,..
Shiru tayi daga bisani ta miqe ranta abace ta nufi toilet ruwa ta debo a bowl da towel tazo tana goge masa gun..
Badai tace komai ba dan daga bisa allamu ranta ya baci..shiko hydar dadi yaji sosai dan dama so yake umman tasa yadawo goyan bayansa harse anbasa Amra...
Shiko Arman part dinsu amra ya nufa zaune ya samu ammy hanan na gefenta suna assignment...
Sallama yayi dik suka amsa masa ya tsugnna har qasa yagaida ta..fuskarta Sam ba fara'a take amsa wa..
"Ammy dan Allah so nake adan budemin amra naga halin da take ciki tinda abba ya fita"
"Kaiiii Arman ka kyale amra ka hakura da ita ta auri Wanda mahaifin ta yakeson bata tinda ita tajawa kanta..ynxu bakasan qin hakura da ita ba kanasata acikin wani hali bane..tinda mutun ya wuni arana so daya ake basa abinci kuma abincin ma can qasa da kwano"
Ammy na kaiwa nan ta fashe da kuka mecin rai..bude baki yayi zeyi mgn ta daga mata hannu da sauri
"Karka cemin komai ka tashi kafita ka tashi nace!!!!"
Ba musu ya miqe ya fice yana waigensu har ynxu ammy na sharar hawaye afuskarta..