← Book details Majanuni Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 14

Sashe 7

Majanuni Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya tsaya suna gaisawa babu yabo babu fallasa yake kallon mutumin, shima mamakin sauyawarsa yake, kamar bashi ne wannan mahaukacin ba mai yagaggun kaya da kwanciya cikin 'kazanta.

Ya ce." Ai babu damuwa mu je ciki sai ku gaisa sosai tsayuwa a soron bashi da amfani."

Cike da jin dadi ya ce." Na gode sosai Kawu."

Ita kuwa Shahida babu wanda ya kai ta jin dadin ganin yanda Kawu Musa ya saki fuskarsa su gaisa da Masoyinta cikin farin ciki.

Babu yabo babu fallasa ta shimfida masa tabarma ya cire takalminsa ya zauna a nutse ya ke gaisata, ta amsa babu walwala a tare da ita domin dai har yanzu zuciyarta ba tayi na'am dashi ba kawai dai ta hakura ne saboda samun farin cikin yarinyar.

Ita kuwa Saliha a fakaice take kallonsa tana k'unshe dariya, hular kansa da takalminsa soso da ya cire a gefanta su takewa dariya. wanda duk abinda take yana kallonta kuma yana mamakinta a zuciyarsa.

Kawu Musa shi yake masa tambayoyi, cikin nutsuwa yake bashi amsa daidai da tambayar da yayi masa.

Kawu Musa ya ce." To Allah ya tabbatar da alheri a cikin al'amarin. tunda ka riga kayi magana da mahaifin yarinyar ai shikkenan, dama shike iko da 'yarsa, tunda ya baka mu kuma za mu zama masu addua da fatan alheri, amma mun baka amana ka rike ta da kyau, marainiya ce bayan haka kuma ka duba lalurarta.

Ya ce." Nayi alkawarin haka insha Allahu.

Baba Asabe ta ce." Da zai yiwu sai ka kama haya a cikin unguwa ka ajiye ta a kusa, idan yaso ka dinga zuwa daga can abujan.

Ya ce" Hakan ba zai yiwu ba Baba, ni dai buri na ku yarda dani, ku amince cewa zan rik'e amanarku, ni kuma nayi alkawari insha Allahu idan ban rik'e ba Allah ya hukunta ni".

Ta ce." To ai shikkenan Allah ya sa mu dace amin."

Gabadaya suka amsa da "Ameen ameen."

Da zai tafi ya ajiye mata dari biyar, ta ce."A'a zo ka dauki kudinka bawan Allah ka 'kara guziri, kai da za kayi tafiya"

Yayi sauri yasa takalmansa ya kama hanyar fita Shahidan ta bi bayansa da sauri.

'Yar 'karamar waya tacno ya bata ya ce ta ri'ke zai dinga turo mata sak'on gaisuwa, saboda ya san lalurarta, ta kar'ba ta na godiya sai murmushi take ganin yanda aka samu daidaito ta kowane b'angare! a yanzu burinta bai wuce ace sun mallaki juna ba.

****
"Eh ni ne Alhaji Sammani mai leshi kasuwar wambai.'' Ya fad'a yana gyara wayar a kunnansa.

Daga daya 'bangar ya ce." Ma sha Allah. dama na kira ne akan maganarka da Abokinka Jamilu Hujaj."

Ya ce." Eh hakane to ina sauraranka, Allah yasa alheri ne.

Murmushi yayi a nutse ya ce." Alheri ne insha Allahu."

Yayi shuru na second daya kafin ya ce." Nawa ne sauran kud'in naka ne?"

Cike da karsashi da kwarin gwiwa ya ce." Ba saura bane ai domin a miliyan biyu da rabi an bada miliyan daya ka ga kuwa ya wuce saura."

Ya ce." 'Kwarai kuwa, yanzu idan na fahimta cewa kudinka da suka rage a hannun abokinka Miliyan daya da rabi kenan?"

Ya ce." 'Kwarai kuwa." ya fada yana gyara tsayuwarsa a cikin shagon.

Ya ce" Babu matsala ka tura min account number zan sa maka insha Allahu."

Mamaki ya rufe shi! ya bud'e baki kenan zai yi magana sai ya ji wayar ta tsinke! ya dinga kallon fuskarsa wayar yana mamakin in da Alhaji Jamilu ya samu wannan hanyar, shin waye wannan mutumin? amma bari ya tura account din ya gani, domin bai gama amincewa da maganar mutumin ba, ya na so ya tabbatar ne kawai.

Ko minti biyar bai yi da tura account d'in ba ya ji alert kudi sun shigo, yana dubawa ya ga kud'insa cif miliyan biyu da rabi!

Cikin tsantsar mamaki! ya nemi guri ya zauna jikinsa sai kyarma yake dama Jamilu ya sha sheda masa cewa shi ba 'karamin mutum bane.

Text ne ya shigo wayarsa ya bude yana dubawa.

Sai jikinsa ya 'kara mutuwa karanta abinda yake k'unshe.

_"Ga kud'inka nan Alhaji, ka mayar masa da miliyan dayan da ya baka Allah ya kiyaye faruwar hakan anan gaba."_

Hannu na rawa ya fara kokarin kiran wayar sai dai sai kash a kashe take, ya kira ya kai sau bakwai bata shiga ba, sai ya hakura ya fara laluben lambar abokin nasa domin fada masa halin da ake ciki.

" Na san da hakan, domin kafin a tura maka kudink'a sai da aka sheda min, Yau ka tabbatar da cewa ni din ba 'karamin mutum bane ko?" ya fada cike da izzah da ginshera!

Alhaji Sammani ya ce." Wai don Allah ina ka samo wannan mutumin domin daga jin muryarsa bai yi kama da abokanan hurd'ar mu ba."

Murmushi yayi kafin ya ce." Haihuwa ce tayi min rana saboda haka mu bar maganar kawai, kai kayi nufin tozarta ni Allah bai nufa, sai ka tura min abinda yayi saura nawa dake hannunka, daga haka ala'karmu ta yanke."
Ya na gama maganarsa ya kashe wayar yana jan tsaki, account number ya tura masa yana jiran ya ji alert.

Cike da kwarin gwiwa ya fito daga d'akinsa! ya bankad'a labulan dakin yana kiran sunanta.

Ba ta amsa ba sai ido kawai da ta zuba masa.

Ya ja mugun tsaki kafin ya ce." Na yarda ke ce ki ka karya ni, ba tun yau ba malamina ke sheda min hakan, rabon wad'annan yaran nake zaune dake, amma ki sani, Mariya ta fiye min ke duk da bata raye ina alfahari da ita, domin ta haifa min yarinyar da ta share min hawaye, ba zan ga ji da sheda miki cewa ke da yaranki baku da amfani a guri na ba."
Yana gama maganarsa ya saki labulan ya kama hanya yayi ficewarsa zuciyarsa fes! gabadaya duk wani damuwa da lalure-lalure da yake sun tafi sakamakon shigowar kud'i, a maimakon ya je ya mayar wa da dillali kudin ya bashi takardar gidansa, kawai sai ya cigaba da fantamawa da kud'in, ya gwammace ya zauna a matsayin d'an haya a gidan, domin zuwa yayi ya bashi kudin hayar shekara biyu dubu dari biyu da ashirin, yasa abinda ya rage a aljihunsa ya cigaba da buga barikinsa.

Baba Asabe tayi-tayi dashi kan cewa a je ayi binkice a can garin nasu amma fafur! ya'ki a lokacin har ya so yayi mata rashin kunya! Kawu Musa ya ce kawai ta kyaleshi kamar yanda ya fad'a mata cewa uwarsa da ubansa ne kawai za su fad'a masa magana ya ji akan wannan al'amari to tunda basa raye babu wanda ya isa domin dai yarinya 'yarsa ce shi yake da iko da ita!

Baba Asabe har kuka tayi saboda tsabar 'bacin rai tana jin takaicin abinda mutumin yake mata, wato ita ta gama yi masa wahala yana nuna mata iko. kawai sai ta barwa Allah al'amarin, ta tsananta da addua.

'Bangaran masoyan kuwa sun sha'ku sosai ta waya domin kalaman soyayya suke aikawa da junansu babu dare babu rana.

Ranar juma'a 20/3/2021 aka d'aura auran, babu laifi d'aurin auran ya tara mutane, amma duk yawancinsu mutanan Hujaj din ne, sai wakilan ango guda biyu da suka bada sadaki, kuma suka kar'bi auran bisa yarjewar addinin musulunci.
[12/10, 9:53 AM] Bintu: 49&50
'Yan Allah ya sanya alhari da 'yan gulma sai shige da fice suke a gidan, ita dai Baba Asabe kallonsu kawai ta keyi saboda ta san mafi akasarinsu, ba alheri ne ya shigo dasu ba, domin da kunnanta ta ji wasu mata suna maganar cewa; ai auran kawai aka d'aura amma babu lefe babu komai, asali ma angon yana da matsalar k'wak'walwa sannan ba shi da wani cikakken asali. ire-iren wannan zantukan jama'a suka ke'be guri guda suna yi.

Amarya kuwa sam ba ta sanya damuwar komai a cikin ranta ba, ta na ji ko babu lefe za ta iya zama da masoyinta burinta ya cika za su rayu cikin inuwa d'aya.

Kitso akayi mata 'kananu irin na bare-bare sai k'unshin salatif da makociyarsu tayi mata, ta sanya sabuwar atamfa wacce ya kawo mata a din'ke da mayafi da takalmi, Rabi makociyarsu wacce tayi mata k'unshi itace tayi mata kwaliyya dai-dai gwargwado tayi kyau tana ta murmushi, mutane na ta'ba ta suna mata Allah ya sanya alheri.

Can gidan Hujaj kuwa Talatu kamar ta zuba ruwa a kasa tasha ganin yanda al'amarin auran ya kasance, babu lefe babu wata hidima da ango yake wa amarya. babban farin cikin ta da ta samun labari cewa ai angon ma bashi da hankali asalinsa mahaukaci ne kawai ya d'an samu sau'ki ne! wannan al'amari yayi mata dadi sosai, kawai sai ta kwantar da hankalinta ta cigaba da sabgoginta, ko gidan bikin ba ta je ba, Jamila ce kawai tayi wanka ta shirya ta tafi. ita da sauran yaran suna gida duk wanda ya shigo sai sun labarta masa abinda yake faruwa.

Da magariba Hujaj ya shigo gidan; kalau dashi cikin sabuwar shadda babba riga da 'yar ciki, komai sabo ne a jikinsa sai walwala yake kamar bai ta'ba shiga wani rikici ba.

A tsiyace! ta kalleshi kafin ta ce." 'Karya banza da wofi ina zaune labarin komai ya same ni da har kake wani fuffuka kana murna ka dauki 'yarka ka bawa mahaukaci wanda ba a san asalinsa ba."

Ya ce." Ai gwara ita akan ke da 'ya'yanki, Talatu daf ki ke da ki bar gidan nan, ki rubuta wannan ki ajiye mutsiyaciya kawai duk kin tsiyata ni, zan dai auro wacce take dai-dai da arziki na."

Ta buga cinya da fad'in" Ai wallahi 'karya kake Jamilu, ai na ci gida ko ka sake ni ba zan fita ba ina nan daram dam."

Ya ce." Tunda gidan ubanki ne ai sai ki zauna sakarai shashasha! kawai."

'Kwallah ta ciko idonta tana rawar murya ta ce. " Shashasha ba, ai ka santa.

A sukwane ya gaura mata mari! wanda sai da ta ga gilmawar taurari! ya nuna ta da yatsa da fadin." Wallahi ki ka sake wata magana a bakin auranki domin dama na ga ji da zama da ke mahaukaciya kawai."
Chapter 7 · 0% Book details