Sashe 10
Majanuni Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jin yunwa na nema ta halaka ta yasa babu shiri ta dauki fitila ta nemi hanyar kicin ta je tana laluben abinci, aikuwa ta samu fulas cike da dambun shinkafa wanda yaji kayan had'i! ga ledojin ruwa nan pure water ta dauka ta fito da fulas din abincin a hannunta.
[12/12, 1:06 PM] Bintu: 53&54
A ta'kaice dai Shahida ita kad'ai ta kwana, domin tun da yayi fitar nan, bai dawo ba, tun tana jin tsoro har ta hak'ura ta barwa Allah al'amarin, sai dai bakinta bai daina addu'a ba har san da bacci 'barawo ya sace ta.
Motsin shigowarsa da asubah ya tashe ta, sai ta mik'e zaune da sauri tana laluben fitilar da gurin bacci ta fad'i a gurin, batiran duk suka watse
Shigowarsa yayi daidai da lokacin da ta gama gyara fitilar haske ya mamaye falon.
Ya kalle ta babu walwala a tattare dashi ya ce." A nan ki ka kwanta ne?"
Kanta ta daga masa alamar ."Eh." ya kama hanyar d'akinsa ba tare da ya sake wata magana ba, wannan ya sake tabbatar mata da cewa ba a gidan ya kwana ba.
Jiki a sanyaye tayi alwala ta fito anan falon dai ta gabatar da sallah, ta jima tana addu'a tana kuka sosai take neman sassauci a gurin mai duka domin ba ta ta'ba tunanin cewa zata fuskanci irin wannan matsala ba.
Sai da gari ya waye sosai ya fito cikin shiri ya d'ora rigar sanyi babbah da sabuwar hula irin sanyi ya rufe kunnuwansa sannan ya rufe idonsa da gilashi b'aki, tsira masa ido tayi domin gani tayi kamar yayi haske ba kamar can baya ba sai dai har yanzu wannan k'asumbar tana nan duguzaza! tare da tsalli-tsallin furfura.
Ganin yanda take kallonsa sai ya sha kunu! ya ce." Na zama tibi ne?"
Ba ta ji abinda ya fad'a ba amma yanayin yanda yayi maganar yana tsatstare ta da ido ta fahimci cewa ransa a 'bace! sai ta d'auke kanta tana mamakinsa a cikin zuciyarta.
Gyaran murya yayi sosai ya bud'e ta domin ta ji abinda zai fad'a mata.
"Zan tafi can kudu wani aiki kamar yanda maigidana ya umarce ni, don haka za ki cigaba da zama anan babu wata matsala tunda akwai ci dasha saboda haka ki kwantar da hankalinki, amma ban amince ki je ko'ina na ba, abinda na aminta dashi zuwa gaishe da kakar maigidan kamar yanda na fad'a miki da farko.
Tsoro ta cire a ranta ta kalle shi sosai kafin ta ce." Shi maigidan naka bai san cewa kai ango bane zai tura ka wata uwa duniya, kada fa ka manta amana ka d'auko ni a gaban iyaye na mai yasa tun kafin tafiya tayi nisa ka sauya hali, wallahi ban yi tunanin haka daga gare ka ba."
Hannu ya d'aga mata da fad'in." Za kiyi min rashin kunya ne?" ta girgiza kanta. ya cigaba da cewa; idan na zauna a gidan me zanyi miki da har ki ke wannan maganar."
Sunkuyar da kanta tayi tana mamakinsa.
Ya cigaba da cewa'' Ai ban ta'ba ganin makwad'aicin uba irin naki ba, wanda bai san k'ima da mutumcin 'ya'yansa ba. domin ya ba ni auranki ne a matsayin fansa a gare shi, ke da bakinki kuma ki kayi al'kawarin girmama maigidana saboda alherin da yayi miki keda mahaifinki, amma har kina da bakin fad'in wata magana a kansa, to ki iya bakinki idan ba haka ba ranki zai yi mummunan 'baci!
Kuka take sosai! ta ce." Yanzu mai ya kawo wannan maganar? wato ka naso ka nuna min cewa maigidan ka ya fi ni kenan, kada fa kamanta bani da kowa a wannan gari sai kai, ban san ko'ina ba, sannan akwai rashin sabo wannan shine dalilina na fad'in wannan maganar amma bada cin mutunci ba.
Tsaye ya mi'ke tare da fad'in" Ni dai na fad'a miki ki kiyaye! kuma ki iya bakin ki, maigidana ya fi kowa daraja a guri na ciki kuwa har dake, mutukar kina so na shirya dake to ki girmama shi kuma ki san irin maganar da zaki dinga fad'a a kansa.
Cikin shashshe'kar kuka ta ce." Kayi hakuri zan kiyaye insha Allah, yanzu kwana nawa za kayi?"
Ya ce."Sati biyu zanyi." a sanyaye ta ce." To Allah ya kiyaye hanya ya bada abinda aka je nema."
Ya amsa da amen kafin ya d'ora da fadin." Akwai komai na bukata, idan wani abu ya 'kare to kiyi wa Sule magana wanda ya kawo ki nan, abokina ne zai yi miki komai kafin na dawo"
Ta ce." To shikkenan.'' hanyar fita ya nufa, sai ta mi'ke domin yi masa rakiya ya dakatar da ita da fadin." Koma ki zauna bana bukata."
Ta koma ta zauna tana kallo ya bud'e kofa ya fita tayi saurin zuwa ta bud'e labule tana le'kansa, juyo wa yayi suka had'a ido, sai tayi saurin sauke labulan gabanta na cigaba bugawa.
Kamar yanda ya sanar mata da cewa akwai komai na bu'kata hakane. koda ta duba kicin din komai da komai da akwai, sai ta kunna karamin gas din da ta gani a ajiye. ta d'ora ruwan shayi, sannan ta feraye dankalin hausa ta soya dai-dai cikinta, a kicin d'in ta had'a shayin ta zauna tana sha tare da had'awa da dankalin da ta soya.
Tunani ne yayi mata yawa, gabad'aya ta rasa a ina zata ajiye wannan al'amari! ashe Baban-baba mayaudari ne ba ta sani ba? ita dai har ga Allah ta ke k'aunarsa take kuma yi masa kallon mutum mai mutunci da amana, ashe kallon kitse takewa rogo, tun ba aje ko'ina ba ya fara gwada mata wasu dabi'u marasa kyau! hawaye ta share! tana tunanin Baba Asabe, watakila dama abinda take ta guje mata kenan shiyasa hankalinta bai kwanta da al'amarin ba, tabbas duk abinda ya fad'a akan mahaifinta gaskiya ne, beyi masa sharri ba, domin ita kanta ta san ba suyi sa'ar uba ba, sai yanzu take sake gazgata maganarsa, domin duk uban arziki mai kishin 'ya'yansa ba zai dauki aure ya baiwa irinsu Baban-baba wad'anda basu da asali ma'ana ba a san daga inda suke ba.
Sosai ta ci kuka ta koshi a kicin din, ta ajiye al'amarin a matsayin kaddararta, domin a yanzu duk abinda za ta fito ta fad'a a banza babu wanda zai saurare ta.
Wanka tayi ta shirya cikin atamfah riga da siket daga cikin kayan da ya kawo mata jiya, tasa hijabi a jikinta ta kama hanyar fita, tana so ne ta je ta gaisa da masu gidan kamar yanda ya umarce ta kafin ya tafi.
Sai da tayi tafiya sosai sannan ta fito harabar gidan, nan taga mutane rukuni-rukuni a wata rumfa yawanci maza ne matan basu da yawa, suna zazzaune, daga can bakin gate kuma ma'aikata ne masu tsaro sun kai bakwai harda masu bindigu a hannu.
Da sauri ta d'auke kanta. tana jin fad'uwar gaba, lallai duk yadda akayi wani abu ne zai faru a gurin, da alamar suna jiran fitowar maigidan ne.
Wata hanya ta bi duk da cewa bata san ina za ta shiga ba kawai dai tayi hasashen nan ne hanyar da zata shiga cikin gidan.
Wani lafiyayyan k'amshin turare ya daki hancinta. da sauri ta d'ago kanta tana kallon hanyar lokacin da suka fito tare da escort dinshi guda biyu. ido suka had'a da saurin gaske tayi kasa da kanta jikinta yayi bala'in mutuwa! ganinsa. cikakken mutum kamili mai halin dattako! yana sanye da farar shadda kal dinkin tazarce da jar dara a kansa as'usul kamar koda yaushe idonsa sakaye da farin gilashi, yayi kyau sosai ba'a magana domin gabad'aya shekarunsa sun 'buya sakamakon gyaran fuskar da akayi masa wanda ya sake k'ayata fuskarsa, gemu kad'an ya bari wanda ya kwanta luf da furfura kad'an-kad'an.
Duk sai ta dabarbace! domin wani irin kwarjini yayi mata, tun kafin ya karaso gurin da take ta zube 'kasa tana gaida shi da yanayin maganarta.
Bai amsa ba sai dai yayi mata alama da hannunsa ma'ana ta tashi, kasa mi'kewa tayi kanta yana 'kasa tana kallon kyakykyawar kafarsa cikin ba'kin takalmi maigidan yatsa.
Ganin ta kasa tashi yasa ya wuce ya bar ta a gurin, yaransa suka rufa masa baya.
Tashi tayi tana buge jikinta zaninta duk ya kwashi datti! a sanyaye ta juya tana kallon bayansu har suka 'kurewa ganinta, ta sauke ajiyar zuciya mai zafin gaske.
A hankali ta tura kofar falon wacce ta kasance ta gilas. sallama tayi a nutse da yanayin maganarta.
Hajiya Saude tayi saurin kallon bakin k'ofar tare da amsa sallamar. kallon rashin sani take mata, ita kuma duk sai ta daburce! ganin kallon da matar take mata.
A sanyaye ta isa har gurin da take ta zube 'kasa tana gaishe ta,
Cikin wani irin yanayi ta amsa gaisuwar tana mamakin daga ina yarinyar take, domin ita duk a tunaninta irin nakasassun da suke zuwa gidan neman taimako ne, da jin yanayin maganarta ta kurame ba sosai take fita ba.
Ta sauke ajiyar zuciya cike da d'an tausayin yarinyar a tare da ita ta ce." Ai yanzu maigidan ya fita idan taimako ki ka zo nema yana waje can zaki tsaya."
Ganin tayi shuru ba ta amsa ba, yasa ta bud'e muryarta ta sake maimaita maganarta .
Cikin jin nauyi ta ce." Sunana Shahida ni ce matar Baban-baba."
Jim tayi kafin ta ce." Ayyo! amaryar Sule ce ashe. sai tasa dariya da fad'in ai jiya nan yake sheda min cewa ya k'ara aure har maigidan ya bashi gurin zama a cikin gidanan Allah ya sanya alheri ai mu nan da Sule muke kiransa."
Murmushi tayi ba tace komai ba, sai dai cikin zuciyarta take ta auna maganganun matar ashe dama sunansa Sule na gaskiya.
Hajiyan ta cigaba da cewa." Ai Sule mutumin kirki ne sosai ki ri'ke shi da kyau sosai! kuma ki zauna da kishiyarki lafiya."
Gabanta ya fad'i jin maganar kishiya, ta dinga kallonta lokacin da take jaddada mata nagarta da kyawun halinsa, sai ta ji wasu zafafan! hawaye suna nema su kufce mata.
Da k'yar! ta iya danne damuwarta, ta ce." Hajiya ko da akwai wani abu da zanyi miki?"