← Book details Majanuni Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 14

Sashe 5

Majanuni Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gefin magriba ya sauko 'kasa yana sanye da farin yadi dinkin tazarce, yadin mai taushi ne wanda kallo d'aya zaka san mai tsada ne, kansa sanye da hulu zannar bukar mai adon bakin zare da ja! kafarsa sanye da bakin takalmin mai gidan yatsa. bai yarda ya fito haka ba sai da ya sakaye idonsa da farin gilashi.

Da sauri Sule ya je ya bud'e masa mota! tunda ya ga ya fito ya san fita za su yi.

Duk saurin Sule sai da wasu daga cikin mutanan dake gurin suka ganshi. Kafin ki ce kwabo sun yanyame! motar! wani za'kwa'kuri a cikinsu ya 'bude murya sosai dan da alama maro'ki ne ya fara yi masa kirari. "Damuna uwar albarka." Alhaji Saddiku mai dubun nasara! kai ne 'ki gudu sa gudu mazan fama! Allah yayi maka arziki muna amfana dashi! Allah ya 'kara suturtaka *'DAN GASKE!* 'Dan da aka haifa da kyakykyawar Aniya."

Da murmushi a fuskarsa yake d'aga musu hannu cikin nuna alamun jin dad'in addu'onin da suke masa! Sule da Labaran suna ta k'ok'arin ganin sun kori mutanan da sukeyi dafifi a jikin motar, da 'kyar suka matsa sannan ya samu ya shiga motar ya zauna amma duk da haka hannu yake daga musu cike da jin dadin adduarsu.

Motar tana daf da fita ya hangi dattijuwar matar da ba zai ta'ba mance fuskarta ba. tana tsaye ita ce a kusan 'karshen layi.

Baba Asabe ganin yana kallon gurin da suke da sauri ta daga masa hannu tana fadin." Alhaji Allah yayi maka albarka hakika kana aikata alheri muna rokon Allah ya kai mizani, Allah ya yi wa dukiyarka Albarka."

Ya amsa da "Ameen ya rabbi." Ya kalli Laraban da fadin." Ka fita ka samu daya daga cikin yaran dake wannan aikin, cewa su ware Dattijawa maza da mata a sallame su duba da raunin da suke da shi."

"An gama ranka ya d'ad'e."

Da sauri ya fita daga motar ya je ya cika umarni ya dawo ya zauna a mazauninsa, Sule ya ja motar suka fita.

Sai da suka hau titi sosai sannan ya ce." Ranka ya dad'e "Gadon 'kaya za mu nufa ne?"

Ya ce." A'a Adakawa za mu je."

Gabad'aya sukayi shuru babu wanda ya sake magana, sai dai Labaran da Sule cikin tunani suke! a duk lokacin da suka shigo garin KANO maigidan nasu sai ya je unguwar Adakawa kuma baya yarda su shiga dashi cikin unguwar a bakin titi yake sauka ya ce su tafi zai dawo gida da kansa. Wannan abu na nasu mamaki mutu'ka!
[12/7, 8:06 PM] Bintu: 45&46
"Wai ana sallama da Shahida." Yaron ya fad'a yana wasa da garegaran dake hannunsa. Saliha dake zaune a tsakar gidan tana kula da masu shige da fice domin sayan abinci ta hararin yaron tana shirin magana sai ga Shahidan ta fito daga daki. Sai tayi shuru tana yi mata wani mugun kallo.

Yaron ya ce." Yawwa Shahida ki zo ana kiran ki a waje." Da dan 'karfi yayi maganar. saboda ya san lalurarta.

Da sauri ta ce." Ka je ka ce gani nan zuwa." Yaron ya juya ya fita cike da wasa a tare dashi.

Dama tayi wankata tsaf ta shirya cikin atamfah mai sauki kudin, sai kawai ta fesa turare mai dadin 'kamshi ta sa hijabi a jikinta, ta fito cike da farin ciki a tare da ita.

Saliha ta bi ta da harara da fadin." Shashasha! mara hankali kawai."

Yana tsaye a soron gidan ya shirya babu laifi doguwar jallabiya ce a jikinsa ruwan madara amma ta kod'e sosai, da ba'kar hula mai raga-raga a kansa, kafarsa sanye da takalmi d'an madina kore sai hannunsa dake makale da carbi mai madannai! yayi mata kyau sosai, ta tsuguna har 'kasa tana gaishe shi.

Ya amsa yana mata wani irin duba mai tattare da abubuwa da yawa.

Cikin nutsuwa ya ce." Ki tashi mana."

Ta mi'ke tsaye tana murmushi, a hankali ta ce." Yau kafi koda yaushe kyau."

Murmushin farin ciki yayi ya ce." Na gode sosai Gimbiyata."

Tana wasa da yatsun hannunta ta ce." Baba Asabe ta je unguwa ya za ayi kenan?"

Ya ce." Hakan ba matsala ba ce idan babu damuwa sai mu je can gidan naku nayi magana da mahaifinki."

Ta ce." Shikkenan hakan yayi."

Suna fitowa kofar gidan. adaidaita sahu yana sauke Baba Asabe da 'katon buhun shinkafarta.

Ta fito da kudi ta bawa direban da fadin." Don Allah ka taimaka ka shigar min dashi gida."

Ya ce."To babu matsala Baba."

Tana juyowa ta gan su a tsaye.

Gabanta yayi mummunar fad'uwa!

Wani irin kallo take musu fuskarta babu annuri ko kadan.

A sanyaye ta ce."Baba sannu da zuwa."

A dakile ta amsa tana kokarin shiga gidan, ya zube gwiwa a 'kasa yana gaishe ta. wuce shi tayi ba tare da ta amsa gaisuwarsa ba.

Sosai ya ji babu dad'i amma sai ya danne! ya tashi tsaye yana buge rigarsa!

Shahida kuwa idonta sun ciko da ruwan hawaye ta ji ciwon wulakancin da tayi masa.

"Kayi hakuri don Allah." Ta fada tana kokarin mayar da hawayen dake kokarin kwace mata.

Ya ce." Babu komai kada ki damu. zubar hawayenki shine damuwa ta, saboda haka kiyi kokarin hana su zuba."

Ta daure tana kokarin mayar da hawayen ta ce." Bari na je na sanar da ita."

Ya ce." To babu matsala.

Gidan ta shiga ta same su suna mayar da magana. Baban tana cewa." Ai mutumin nan yana da kirki sosai wallahi shine ya bada umarnin cewa a sallami dattijai irinmu saboda raunin da muke dashi, da ba don haka ba da tuni ina can cikin 'kila wa 'kala."

Saliha ta ce." Ai ya taimaka wallahi ban yi tsammanin zaki samu ba."

Tana kokarin magana Shahidan ta katseta ta hanyar fadin." Baba wannan fa ba rayuwa ba ce, tunda ubangiji ya girmama dan adam babu wanda ya isa ya wulakanta shi, a matsayinki na mai hankali bai kamata kiyi masa haka ba, ban ji dadi ba wallahi." ta kai karshen maganar cikin rawar murya.

Ta ce." Rashin kunya za kiyi min Shahida?"

Ta girgiza kai "A'a ni ba nufi na kenan ba, kawai kuskuran ki nake nuna miki."

Ta ce." Ai ba tun yau ki ka saba nuna min kusukura na ba Shahida ki cigaba da yi min abinda ranki yake so.

Ta share hawayen da ya soma fita ta ce." Allah ya baki hakuri! dama zan fada miki ne cewa. Za muje can gurin Babana tare dashi."

Ba tare da ta kalle ta ba ta ce." Sai kun dawo."

Ga mamakinta sai ta ga ta juya ta fita.

Suka kalli juna ita da Saliha ta ce." Gatse fa nayi mata."

Saliha ta ce." Don girman Allah Baba ki kyale 'yar iskar yarinyar nan da mahaukacin mutumin nan jiki magayi."

Baban ta shiga girgiza kanta tana tu'ajibun al'amarin.

Gidan duhu sosai! babu haske. dukkaninsu suna rumfa a zaune yunwa na sasakarsu! yau Talatu dai ta ranste tace kowa ya ci aljihunsa! domin ta gaji yawon cin bashi gashi babu mai ko anini a cikinsu, tunda ba sana'a suke ba, bahaushe ya ce duk lalacewar mutum yana da rana. Talatu tana iyakar bakin ko'kari a kansu, yau dai ta gaji! 'kokari take ma ta biya bashin da ta ci a baya wanda kullum ta Allah ake mata sallama ba dare ba rana.

Motsin shigowarta gidan ya sa Hadiza tayi saurin kunna fitilar wayarta tana fadin." Waye?" Ta ce." Ni ce Shahida." Talatu tayi karaf ta ce" Wa ce Shahida kuma. ba dai kurmar yarinyar nan ba, domin na ji kamar muryarta."

Hadiza ta ja tsaki mai tsayi ta tashi ta shiga daki ta kwanta. tunanin yanda za a yi ta samu abinci kawai take, tana ganin saurayinta kawai zata kira a waya ta fad'a masa halin da take ciki.

A wulakance ta kalle ta kafin ta ce." Ke kuma daga ina da wannan daran?"

"Da ga gida nake." tafada a takaice.

Ta ce." Ayyo! to ina fatan dai lafiya?"

"Gurin Babanmu na zo tare da wanda zan aura za su yi magana."

Gabanta ya yanke ya fad'i! ta ce" Waye wanda zaki aura din? wane sakarai! asararran ne mara mafad'i."

Jamila ta ce."Haba Talatu abinda ki ke fa bai dace ba, kefe uwa ce idan ba zaki fadi alheri ba to kiyi shuru."

"Rufe min baki ba'kar munafuka algunguma." ta katse ta a zafafe!

Jamila ta mik'e ranta duk a 'bace ta kama hannunta suka fita tsakar gidan.

"Don Allah Aunty Shahida kiyi hakuri da abinda Talatu take miki wallahi ba na jin dad'i."

A jiyar zuciya ta sauke ta ce."Jamila Mahaifiyarku ba ta k'aunata ban san abinda nayi mata ba. amma ki sani wallahi ta na cin albarkacin ki, da ba don haka ba da tuni na dauki mataki a kanta."

Ta ce.'' Ki cigaba da hakuri watarana sai labari yanzu ina mutumin da ku ka zo tare?"

Ta ce." Yana can waje a tsaye kuma wallahi da gaske ya ke aure na zai yi."

Ta ce.''Amma na ji dadi wallahi. mu je na gaishe shi kafin Baban ya dawo"

Tare su ka fita suka same shi a tsaye a jikin bango (garu) yana danna 'karamar waya nokia da aka d'aure ta da kyaure.

Jamila wani irin kallo take masa a tsorace! kwata-kwata mutumin bai kwanta mata a rai ba, ganinsa wani iri babu sutturar arziki gashi tsoho gemunsa da tsalli-tsallin furfura!

"Ina wuni." Ta fada tana dan sunkuyar da kanta.

Ya amsa fuskarsa a sake yana dan tsokanarta.

Tana 'yar dariya ta ce." Ga aunty na nan; don Allah ka rike mana amanarta! kaga tana da lalura ta rashin ji a kula mana da ita.

Murmushi yayi ya ce." Kada ki damu 'kanwata zan ri'ke amana insha Allahu; yanzu ina so ne nayi magana da babanku domin da gaske na ke."

Tana k'okarin magana Hujaj ya k'araso gurin! kallonsa yayi sama da 'kasa da fadin." Malam menene? ka tsaya min a kofar gida tare da yara na."

Ya d'an rusuna da fadin." Barka da dare Baba." A takaice ya amsa da "Barka dai"

Gurin yayi shuru dukkaninsu jikinsu yayi sanyi!

Ya kalli Shahidan da fad'in."Waye wannan ki ka kawo min?"
Chapter 5 · 0% Book details