Sashe 2
Kundin Tsatsuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*** **** A can birnin Sin kuwa, cikin sulusainin dare Ruziyal na kwance cikin dakinsa yana barci, kawai sai ya farka a firgice sakamakon wata irin kara da ya ji mai kama da saukar aradu. Nan take ya mike zumbur ya ruga izuwa ga tagar dakin ya budeta da sauri. Tartsatsin hasken tsawa ne ya bugi fuskarsa, ya ja da baya a tsorace. Cikin karfin halli ya kara lekawa waje. Wannan karon bai ga tsawar ba, sai a can nesa kadan ya ke hango kyallinta. Ruziyal ya dubi sararin samaniya da kyau, ya ga babu ko alamar hadari, sai kirjinsa ya fara dakan uku-uku, don ya tabbatar ba lafiya ba. Take zuciyarsa ta fara wasuwasin shin an ya kuwa ba aljanin nan ba ne ya sake dawowa? Tabbas daga bangaren rijiyar nan mai dauke da Kundin Tsatsuba ya ke hango kyallin walkiyar. Ba tare da bata lokaci ba Ruziyal ya dauki rigarsa ya sa, sannan ya bude kofa ya nufi tsakar gida gadan-gadan. Da zuwansa bakin rijiyar sai ya iske, an dauke wannan katon murin nata an ajiye shi a gefe guda. Cikin tsananin tsoro, Rumyal ya leka cikin rijiyar. Yin haka ke da wuya, ya ji wani abu yai fitar burgu ya doki kansa, sai ga Ruziyal yayi tsalle sama ya fado kasa tini! Ko da ya dago kai sama, sai yai arba da shi. Ba wani ba ne face dansa Jafar bisa wani aljani mai siffar tsuntsu, hannayensa biyu na rungume da littafin KUNDIN TSATSUBA a kirji. Ko da suka yi arba, sai Jafar yai murmushi ga Ruziyal ya ce "Ya kai abbana, ai dama na gaya maka cewa sai na dauko wannan littafin, to ga shi kuwa lailai rana ba ta karya." Cikin tsoro da matukar mamaki da damuwa, Ruziyal ya mike tsaye ya ce "Ya kai dana, ka rufa mini asiri, ka rufawa kanka, ka mayar da wannan littafi inda yake. Idan kuwa ka ki zaka tsokano masifar da ajali ya fita dadi. Ko da jin haka, sai Jafar ya bushe da dariya yа се "Haba abbana, ka manta ko ni waye? Ni ne fa hatsabibi uban hatsabibai. Ni ne likitan kasada, mai binciko bala'i. Ni ne guguwar fitina, mai tada duniya tsaye. Ban so a zauna lafiya, kuma bana son a mutu. Ni da tsoro mun raba gari. Da a ba ni labari, gwara ni na bayar. Abba ka yi hakuri, ni kam na yi gaba, sai wata rana. Idan da rabon mu sake saduwa zan dawo gida, idan kuma babu shi kenan, wannan ga ni ya zamo na Karshe a tsakaninmu." Jafar na gama fadın haka, ya zunguri cikin aljanin da kafafunsa, kawai sai aljanin ya kara yin sama ya luluka cikin gajimare. Shi kuwa Ruziyal sai ya daga kai sama yana mai kallonsa cikin tsananin fargaba da damuwa. Hawayen takaici ya zubo masa, ya ce a ransa "Duk da dai Jafar ne dana kadai a duniya, da shi da gwara babu, domin ga shi yanzu ya janyo mini masifar da babu wanda ya isa ya kare ni." Tafiyar dakika sittin suka yi a sararin samaniya, suka iso wani jeji da ke bayan gari. Aljanin ya sauko kasa gaban wani kogon dutse. Saukarsu ke da wuya, Yelisa ta fito daga cikin kogon, ko da ta ga Kundin Tsatsuba a hannun Jafar, sai fuskarta ta cika da annuri, ta dubi wannan aljani da ya kawo Jafar ta ce "An gaisheka ya Gulzum, yau ka yi aiki mai girma." Cikin fara'a ta karbi Kundin Tsatsuba ta dube shi da kyau duba na nutsuwa, sannan ta gyada kai ta ce "Barkanmu da samun wannan litttafi, yanzu sai ku biyo ni zuwa cikin kogon nan, don mu zauna mu yi binciken hanyar da za mu bi mu samo kubar da zata bude shi." Tana gama fadin haka, ta juya ta nufi cikin kogon. Jafar da Gulzum suka bi ta a baya. Bayan 'yar gajeriyar tafiya ne a cikin kogon, suka iso wani fili mai fadin gaske wanda aka kawata shi da ginin lu'u lu'u. Wajen a haskake yake da wani irin haske, wanda ido bai isa ya ga ta inda ya samu ba. Wajen ya kasance wata 'yar karamar fada ce, amma babu komai a wajen face tarkacen kayan tsatsuba iri- iri. Babban abin da ya baiwa Jafar mamaki shi ne, farko sa'adda za su shiga cikin wannan kogo, yana ta lullube wajen kai ka ce fiye da shekaru arba in baya wata halitta ba ta shiga wajen ba. Ko da suka tunkari wajen, sai yanar ta yaye da kanta kamar labule, ta ba su wuri suka wuce, suna wucewa sai ta dawo ta rufe hanyar. Kai tsaye Yelisa ta wuce izawa gaban wani dogon tebur kuma faffada, na bakin karfe man dauke da kayan tarkacen tsafi iri-iri. Da zuwa sai Yelisa ta ajiye Kundin Tsatsuba bisa wannan tebur. Jafar da Gulzum suka tsaya a bayan Yelisa, suna kallon abin da zai faru. Yelisa ta rufe idanunta, ta fora hannayenta biyu bisa wani dutsen tsafi ta fara surutai irin na tsafi. Bayan kamar dakika dari uku da ashirin, sai ga wata karamar guguwa ta bayyana akan wannan tebur tana katantanwa, jim kadan sai guguwar ta rikide ta zama wani siririn aljani wanda kaurin jikinsa bai wuce na silin kara ba, dogo ne zankalele kamar igiya, domin kansa na tabo dutsen saman kogon. Yelisa ta dube shi ta ce "Ya kai Lubumaz, me ka sani dangane da wannan littafin? Ta yaya zamu iya samo kubar Muftahul Zarbil mu bude shi?" Ko da jin wannan tambaya, sai Lubumaz ya kwalla ihu, yai tsalle ya runtuma da kasa, sannan ya dago kai cikin damuwa ya dubi Yelisa ya ce "Kaicona ya shugabata, ki yi sani cewa yau kin yi mini tambayar da nake tsoron amsawa. Ki yi sani cewa, duk duniya babu wata kuba da za ta iya bude Kundin Tsatsuba face Muftahul Zarbil. Ita kuwa Muftahul Zarbil kuba ce da aka gina daga sassa uku, ko wane sashi guda an tafi da shi izuwa bangon karshen duniya, bangaren gabas, kudu da arewa, yau saura kwana arba in cif sashin karshe ya isa bangon arewa. Ya shugabana ki yi sani cewa, babu wani mahaluki daga cikin aljanu ko bil'adama da ya isa ya je wadannan wurare a cikin lokaci kadan, face wani aljani guda daya da ake kira Murkahul Sabus. Yanzu haka shi wannan aljani na can a tsare a eikin fadar sarki Lu'umanu na birnin Teheren, a cikin wani kurkuku da ke Karkashin Kasa, a ɗaɗɗaure da sarkar tsafi a cikin wata battar Ƙarfe, ita kuma battar an sa ta a cikin akwatin bakin karfe, akwatin bakin karfen kuma an kulle shi da katon kwado, wanda ba shi da mabudi sai dai a sare shi da wata takobi da ake kira Sarjis. Ya shugabata, ita kuwa takobin Sarjis mallakar wani tsohon muridi ne da ke cikin karshen jejin Kalkim, jejın da saboda tsananin masifar wannan maridi da akewa lakabi da Magulus. Masana tarihi sun kiyasta shekarun Magulus da cewa a kalla za su kai dari uku da talatin da uku, duk shekara yana haihuwar 'ya'ya dubu uku. A halin yanzu jejin Kalkim a cike yake da iyalansa, ko ina su ne babu masaka tsinke. Duk duniya babu wanda ya san yadda za a yi a kiyaye dokokin shiga wannan jeji a fita lafiya, face mahaitinki Boka Jinshan. Saboda haka ina mai shawartarku da ki kai wannan bukata ga mahaifinki, shi kadai ne zai iya taimakawa ku mallaki aljani Markahul Ko da Lubumaz ya zo nan a zancensa, sai Yelisa da Jafar suka kawo gwauron numtashi suka ajiye. Yelisa ta kara duban sa ta ce "Ya kai Lubamaz, ina son ka gaya mini dalilin da ya sa aka kulle aljani Markahul Sabus a cikin akwatin Karfe?" Ko da jin wannan tambaya, sai Lubumaz ya nisa ya ce "Ya shugabata, kin yi mini tambayar labari mai tsawo, to amma zan yi kokari na gajaree miki labarin a cikin ko da sa'a biyar ne. Sai ku saurara don ku ji wani labari mai cike da al'ajabi. "Fiye da shekaru goma sha biyar baya, sarkı Lu'umanu na birnin Teheren na da wata zabgegıyar kyakkyawar mace da ake kira Fatisa, saboda tsananin kyanta ake zaton cewa ba mutum ba ce zalla. Wasu sun ce ruwa biyu ce, ana zaton ubanta mutum ne, uwarta aljana. Wasu kuma sun ce a'a, ubanta ne aljani, uwarta mutum. Har yau dai babu wanda ya tabbatar da gaskiyar al'amarin. Bayan sarki Lu'umanu ya auri Fatisa tsawon shekara hudu ba su sami haihuwa ba, sai al'amarin duniya suke cabe masa, domin ba shi da burin da ya fi na samun magaji. Yayın da tunani da bakin ciki su kai masa yawa, sai ya tara dukkanín bokayensa ya sanar da su halin da ya ke ciki, kuma ya nemi da su share masa hawaye. Gaba daya bokayen aka rasa wanda zai ce wani abu a wajen tsawon dan lokaci. Daga can sarkin bokayen ya ce "Ya sarkin duniya, hakika ka zo mana da babban al' amari, amma abin da nake so da kai shi ne ka ba mu kwana uku mu je mu yi naziri, lallai ba zamu dawo nan ba sai da hanyar biyan bukata." Ko da jin haka, sai fuskar sarki Lu'umanu ta fadada da murmushi ya ce "To shike nan, ku tafi na sallame ku, zan kasance mai sauraronku nan da kwana ukun." Nan take suka watse suka bar sarki zaune shi kadai a turakarsa, yana nazarin al'amarin a ransa. Da kwanaki uku suka cika, sai sarkin bokaye da tawagarsa suka dawo ga sarki. Bayan sun kwashi gaisuwa, sai sarkin bokaye ya ce "Ya mai duniya, gaba dayanmu mun dukufa wajen bincike bisa samun biyan bukatarka, amma ba mu kai ga samun malita ba, face abu guda." Sarki Lu'umanu va gyara zama ya ce "Ina sauraro, maza ka fadi malitar na ju "Idan har kana so ka samu biyan bukata, sai any kogon Zuhurum an samo tsumin dodo Kirayanu, ka sha sannan matarka zata sami juna biyu. Ya kai wannan sarki, ka yi sani cewa daga nan zuwa kogon Zuhurum tafiya ce ta shekara darı da goma sha biyu ga basamudan gwarzon saurayın aljani mai takama da karfi da samartaka. Haka kuma ka sani cewa, shi dodo Kirayanu shiryayye