← Book details Kundin Tsatsuba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 3

Sashe 1

Kundin Tsatsuba Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

KUNDIN TSATSUBA
Rubuta Labari
Abdul’aziz Sani Madakin Gini
Shekarar Rubutu
2008
Ɗaukar Nauyi
Mansur Usman Sufi
08137237071

Shekara goma sha, ba don siffar gafobin jikina ha. Yana da baiwa ta rashın gashi, da yanayin tsufa. Kuma har yanzu ya kasance ƙaƙƙarfa, ga ƙoshin lafiya. A tarihin rayuwarsa, bai taɓa rashin laliya ba ko da kuwa ciwon kai
Wata rana da sassafe Gimbiya Sima ta aika aka kirawo ƙaddaru, Da yake ba a yi masa iso gareta, sai kawai ya wuce izuwa cikin ƙuryar turakarta, inda ya iske ta a cikin bahon wanka mai cike da kumfar sabulu, kayangi na cuɗa ta
Ko da ya ganta a cikin wannan hali, sai ya sunkuiya da kansa kas cikin sauri ya ce "Kaicona da cin amanar gidan nan, lallai ba zan iya kallon tsiraiciinki ba. Ranki ya daɗe ki gafarce ni, ban san zan riske ki a wannan hali ba na shigo."
Ko da jin haka, sai Sima tayi murmushi ga Ƙaddaru ta ce “ka yi sani cewa, ban kirawo ka nan ba sai domin idanunka su ga kyakkyawar surar jikina guda daya. Don haka ina umartar ka ɗaga kai ka ƙare mini kallo daga sama har ƙasa, sannan daga bisani zan yi maka wata tambaya.
Na rantse da kabarin mahaifina, idan ka ƙi bin umarni na zan kashe kaina, kuma na ɗora alhakin raina akanka. Ka yi sani cewa tuni na gama shirya komai, tare da wadannan kuyangi
Sima na gama faɗın haka suka, sai Kaddaru ya ga kuyangi su goma sha ɗaya sun firfito daga inda aka ɓuya sun rufe ƙofofin fita daga wannan taraka sun bar guda ɗaya jal. Cikin tsananin razana, Ƙaddaru ya ɗago kai dubi Gimbiya Sima jikinsa na karkarwa.
A wanan lokacin ta mike tsaye daga cikin bahon wanka, kumfar sabulu na manne a jikinta. Take wata kuyanga tasa wani kyakkyawan farin kyalle ta goge surar jikin Sima ta bayyana ƙarar tumbur babu wani hijabi.
Gashin kanta bakl sidik mai ƙyalli-ƙyalli ya zuba har Kasan mararta, Cikinta a shafe yake kamar ba ta taɓa cin komai ba. Ƙugunta kuwa a tsuke yake, daga baya ya fashe yai doro kamar a ɗora kofin lemo akai ya zauna. Fatar jikinta ja ce subul-sumul, ko digon kwarzane guda babu a ko ina. Tana da siriri wuya kamar na barewa. Sima doguwa ce mai kaurin jiki. Tana da manyan cinyoyi, da zara- Zaran yan yatsun hannu da ƙafa. Batun ido, hanci, da baki kuwa, kamar kwararren mai zane ne ya zana su bisa takarda dai-dai yadda take bukata. Idan tayi murmushi, mutum na iya jin kamar an zare masa cutar ajali wadda aka sha fama shekara da shekaru.
Ya yin da waziri Ƙaddaru yayi arba da wannan kyakkyawar sura, sai ya ja dogon gwauron numfashi ya ce "Ranki ya dade, na rantse da girman abin bautarmu, ban taɓa ganin wani abu mai kyau ba a doron ƙasa tamkar ki ba. Inda na san haka kike, da tuni na mutu wajen neman kyakkyawan mijin da ya dace da ke, domin sai ne a kawo miki wanda babu mai kyawunsa a duniya."
Ko da jin wannan lafazi, sai Sima ta kyalkyale da dariya ta ce "Ka fara hawa kan turbar da nake so. Ya Ƙaddaru kayi sani cewa, a rayuwata ta duniya babu abin da nake so face tafiye-tafiye, don ganin abubuwan al'ajabi cikin duniya. Ka sani cewa ina da kyau, mulki
babu abin da na nema na rasa, face abokin rayuwa da ya dace da ni.
To ka sanı, ni Sima na rantse da darajar tsafin da na gada a wajen iyaye da kakanni, ba zan auri wani da namiji ba face wanda ya fi ni kyau, mulki da dukiya. Na yi bincike a cikin madubin tsafina na gano cewa akwai wani littafi da ake kira KUNDIN TSATSUBA, shi wannan littafi ya Kunshi manyan abubuwan al’ajabi guda dubu. Lallai idan na mallake shi, na sami ikon karanta shi, zan yi ɗaukakar da babu wani mahaluki da ya taba yi, walau yanzu, ko da, ko nan gaba. Na yi iya ƙoƙarina akan na gano inda wannan littafi yake na kasa. Ya kai Ƙaddaru ka yi sani cewa, bincike na ya nuna mini cewa ba zan taɓa haduwa da namijin da zai dace da ni ba, har sai na karanta wani shafi daga cikin shafukan Kundin Tsatsuba. Yanzu ina neman shawara gareka?"
Lokacin da Gimbiya Sima ta zo nan a zancenta, sat hankalin Ƙaddaru ya dugunzuma ya kasa cewa komai, ya yi shiru yana tunani. Wata kuyanga ta zo da wani babban shuɗin mayafi ta lulluɓawa Sima. Sima ta matsa kusa da Kaddaru ta hai bannu don dafa kafaɗunsa, sai yai sauri ya matsa baya.
Cikin firgici ta dube shi ta ce "Lafiya, me ya faru gareka
Kaddaru ya numfasa ya ce "Ranki ya daɗe, ai ina ishi ne a ce wannan hannun naki ya taɓa jikin wani da mijin da bai dace da ke ba. Na rantse da darajar gidan nan. a sani na tun daga ranar da mahaifiyarki ta haife ki kawo i yanzu namiji bai taɓa taɓa ki ba, har shi kansa mahaifinki kuwa. Kuma shi ne da kansa ya kafa dokar, duk namijın da ya taɓa jikinki a sare kansa, ba don komai ya sa wannan doka ba, sai don gain tsananin kyawunki.
Har yau wannan doka na aiki. kuma muna kiyayewa da ita."
Sima tayı murmushi ta ce "To na ji batunka, zauna ka saurari nawa.
Kaddaru ya zauna nesa kadan da ita, ya sunkui da kai kas, yana mai sauraro cikin biyayya.
"Abin da nake so da kai shi ne, ka kai ni wajen bokan da ya fi kowa ne boka isa a kasar nan, domin ya bincika mini inda Kundin Tsatsuba ya ke, kuma ya taimaka mini na isa wajen, har na mallake shi."
Yayin da Kaddaru ya ji haka, sai ya kara yin shira sawon yan dakiku kadan, sannan ya dago kai ya dubi Sima ya ce "Ranki ya dade, ai kaf kasar nan babu wanda zai iya wannan arki face Boka Sulbaini Ibn Barzuk. Ki yi saní cewa, a halin yanzu yana can jejin Falwas ya shiga kogon Ruhim don yin doguwar halwar tsafi ta kwana arba in da daya, saboda wata muhimmiyar bukata tasa. Ina jin tsoron mu je mu katse masa aiki, fushinsa ya tabbata a kaina."
Yayin da Gimbiya Sima ta ji haka, sai ta dakawa Kaddaru tsawa ta ce "Kai waziri! Ai sawun giwa ya take na rakumi. Bukatarsa ce a saman ta mu, ko kuwa ta mu ee a saman tasa? A she ba ni ke mulkin kasar Laharim ba? Duk mahalukin da ke zaune a wannan kasa yana Karkashin iko na ne Lallai Boka Sulbaini bawan mu ne, ubansa ma yayi baute a gıdan nan, dole ne ya bi umarninmu
"Haka ya ke ranki ya dade, zancenki dutse ne yafe ni."
Da jin haka, sai Gimbiya Sima tayi murmushi tace "Ya kai Kaddaru na umarce ka da ka hanzarta komawa gida don ka yi sallama da iyalanka, ka dawo nan bayan magariba. Yau din nan zamu tafi jejin Falwas don mu sadu da Boka Sulbaini."
Cikin biyayya Kaddaru yai sujjada ga Sima, ya ce "An gama, ranki ya dade."
Nan da nan ya fice daga wannan turaka, zuciyarsa cike da damuwa, domin bai san abin da ka iya faruwa ba ga rayuwarsa. Tabbas ya san cewa gimbiya ta tsokano al'amarin da ba zai taba yiwuwa ba, domin ya taba jin labarin Kundin Tsatsuba a wajen Boka Sulbaini, kuma ya gaya masa cewa babu wanda ya san inda ya ke bare a san wanda ke da mallakinsa.
Chapter 1 · 0% Book details