Sashe 3
Kanwar Shehu Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
Comment section👇🏼
https://chat.whatsapp.com/DrrHAf8xE7P56YCUZkhGlG
بسم الله الرحمن الرحيم
Kamar kullum tun ƙarfe 6 na asuba basu koma barci ba sai gyaran gidan ake yi "Inno ta ce Jawahir kinga yanzu an kusa komawa makaranta ko? To abincin kawai zamu rinƙa yi a gida ne ana zuwa sai ki daina tallar kawai kinga ba lokaci to!''
Inno kuma kina ga za'a zo a siya kada fa mu kwana ciki?
A'a in Sha Allah za'a siya ma ki kwantar da hankalin ki, daga yau zamu fara a cikin gidan in Sha Allah zamu yi nasara haba Dr jawahir ya da sarewa haka a'a Allah na tare damu in Sha Allah...
Allah yasa mu dace ta faɗa, karfe 8 dai-dai suka gama aikin su aka shinfida tabarma domin ƙari tana gamawa kuma suka huta inno ta daura abincin ita kuma kwanon da suka bata ta wanke su...
Ƙarfe 12 dai-dai inno ta gama abincin inda can kasuwar ana ta jiran "Jawahir" ta kawo abinci amma shiru saboda inno tana gyara kayan ta, ita kuma mai saidawa ga tsafta komi nata tsaf take tafiya dashi, sallama aka fara cikin gidan abada abinci cikin kan kanin lokaci sai gashi har nema ake babu, inno ta ce kinga ni ai yanzu shikenan munyi dabara daga yau a gida zamu rinƙa komi kawai bazan iya wannan tallar ba kullum gaskiya!..
Wallahi kam anyi dubara kinga wanda ya siya yau zai faɗa gobe a gida aka yi ya saya ...
Tabbas haka ne mudai Allah ya dafa mana!
Suna zaune majociyar su ta shigo da sallama a bakin ta, suka gaisa da Inno ta ce don Allah tana san "Jawahir ta raka ta birni saro kaya ita yar ta bata da lafiya ne!''
Inno ta ce har ina zaki je haka? Ashe rabii ba lafiya ubangiji Allah ya bata lafiya to!!
Amen ya Allah zanje Kano ne in Sha Allah..
Ubangiji Allah ya kai mu lokacin badamuwa!
Godiya tai mata tare da tafiya.... Sai da ta tafi ne inno ta ce wai lafiya na daina ganin" rabi ne gidan nan?''
Bata rai tai tare da faɗin inno mun bata da ita fa..
Kai innalilahi wa'inna ilahir raji'un shiyasa nadaina gani