← Book details Jikar Iya Delu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 7

Sashe 1

Jikar Iya Delu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*JIKAR IYA DELU*

Page 13 & 14

"Yasauka akan cikakkiyar halittarshi mebawa duk wata cikakkiyar mace tsoro. Ido hajja tawaro Dama tasan minene namuji tinda ak'auye tataso komai ba boyewa sukeyiba Hakan yasa takurma Wani irin ihu tana fad'ar wayyo allah iyanaa nayi mugun Gani yau wlh naga macijin ya Ahmad wayyyoo..arazane M. Ahmad yajiyo Yana duban inda yakejin sautin muryarta aikodai ita d'in ce cikin hanzari yafigi towel d'inshi yad'aura tareda komawa bathroom d'in cikin takaici kamar yakashe kanshi Dan haushi..itako tasowa tayi aguje zatabar d'akin cikin sauri yadanna Wani remote aiko k'ofar tadatse gam domin yaji motsinta zata gudu

Itako turus tayi Ganin k'ofar tarufe domin tasan waye ya Ahmad da rashin mutincinshi Hakan yasa tayi tsaye tana rabon Ido...shiko yafi minti 30 acikin bathroom d'in Yana tunanin wata zuciyar tace to idan Bata fitaba tayaya zaka shirya har Kaci ubanta Hakan yasa yabud'e k'ofar daga cikin bathroom d'in...aiko hajja nagani k'ofa tabud'e tayi wuff tafice kamar walk'iya sedai kafun takaiga k'ofar general parlor itako tarufe tayi yadda zatayi k'ofar tak'i buduwa.

Shiko Dagan gan yarufe k'ofar lokacinda yabud'e ta bedroom d'in,, fitowa yayi yashiga shirinshi hankali kwance kamar yadda yasaba sedai duk ranshi adagule yake a office sameera tab'ata mishi Rai yanzu Kuma ga wannan fitsararriyar tana mishi nata iskancin waitaga macijin shi ko uban waye yace mata macijine Kuma inatasan abun oho, ahakan dai har yagama shirinshi kana yazauna bakin gadon tareda janyo laptop d'inshi yashiga Wani aikin.

Itako hajja kala tana cikin tsoro harta Dena jinshi Takoma tsakiyar parlor tana mishi burkuce tajanyo wannan ta tab'a wancan,,harta gaji Takoma tazauna Amma befitoba Kuma k'ofar Bata Bud'eba Hakan yasa tafarajin haushi tashiga dukan k'ofar kota Ina Amma k'ofa tak'i bud'uwa.

Afannin Al'ameen kuwa kod'a yasamu maah a kitchen abunci yakarb'awa yaya nazeeru kana yakoma part d'inshi yasamu ya nazeeru yafito daga wanka harya Saka kayanda ya ajiye mishi, k'arasowa yayi cikin d'akin yad'auki kayanda ya nazeeru yacire yafito dasu yajefar kana yak'ara dawowa...zama yayi kusanshi yace ya nazeer Kaci abunci mana. "Humm baradai nayi sallah Al'ameen ko sallar asuba yau banyiba wlh..Ido Al'ameen yawaro Yana fad'ar Mee? Sallar asuba fa tab d'ijam Kai kuwa miyahanaka sallar asuba? Koda yakedai Yi sallar tukunnah kamun kayimun bayanin ma yadda akayi Abba yaje garinku har iya ta yadda tabi yoshi..Humm kaide bari kawai nayi sallar ai abun ba,amagana allah dai ya kyauta gaba kawai. "To shikenan barana jiraka yafad'a Yana cire kayanshi Shima Domin yayi wankan..shiko ya nazeer yashiga jero sallolinda ake binshi

Acan part d'in M. Ahmad kuwa gabaki d'aya hajja tashak'a iya shak'a domin yanzu taso tabar part d'in kamarme yunwa takeji sosai Kuma tanaso taje Taga iyarta Amma k'ofa tak'i bud'uwa anan tazube bakin k'ofar tana mayarda numfashi bayan tagama dukan k'ofar...shikuwa ahankali yake saukowa cikin tafiyarsa ta k'ak'k'arfan namuji seda yasauko parlor ne yaganta tukunnah yatinada ita domin shi wlh harga allah yamantama da ita,,cikin tsare gida yak'araso tsakiyar parlor yazauna Yana danna wayarsa batareda ya Kalli ko inda takeba.

Itako yanzu haushi yafara kamata domin Dama zumud'in Ganin nashine kawai takeyi Amma tatsani halayyarsa ta banzatarda mutane acewarta, dudda gajiya datayi da zama part d'in Amma Hakan besa tayimishi maganaba tunowada abunda tagani yanzu a bedroom d'inshi Wani irin tsorone yarufeta domin Gani takeyi kamar k'ara Ganin abun zatai atake kuwa jikinta yad'auki rawa Domin Hajja allah yayi mata tsoro Amma fa akwai muguwar tsokana da tsiwa harta sayarwa.....seda yagama sham k'amshinshi kana yad'ago blue eyes d'inshi ahankali tareda watsa matasu nad'an Wani lokaci kamun yabud'e Baki cikin cool voice d'inshi yace "Kee zonan, yafad'a kamar bashine yayi maganarba...itako tajishi Amma setaga Kuma kamarba magana yayiba kartazo Kuma tajazawa kanta Wani laifin Hakan yasa tayi kamar batajiba...sake d'agowa yayi Yana kallanta yadda tayi ko oho Amma kallo d'aya zaka mata kasan cewa atakure take. Lips d'inshi nak'asa yad'an ciza ahankali kamun yak'ara cewa waibada ke nake magana bane?

"Na'am ni ya Ahmad?? "Aa ni yafad'a Yana doka mata harara... mik'ewa tayi ahankali tazo wurinshi aranta se addu'a takeyi allah yasa karya daketa, tana zuwa tazauna kusan k'afarshi tana fad'ar Gani. "Okay zama ma zakiyi kenan oya tashi Maza kiyi nilldown anan...aiko cikin sauri tamik'e batareda yace komaiba.

Nisawa yayi ahankali yace "miyakawoki bedroom d'ina batareda nasaniba? Yayimaganar kamar ba'a Bakinshi tafitaba...shiru tayi batace komaiba Hakan yasa yak'ara tambayarta ahasale. Aiko tatura Baki gaba kafun tace "toba ganinka nazoyiba. "Au ganina ni bak'onkine? Ko Ganin nawane harse anje bedroom d'ina duk wannan parlor be ishekiba? Yafad'a cikin Jin haushi tunowada abunda tayi mishi...itako shiru tayi kawai tana kallanshi yadda Bakinshi kejuyawa Yana magana ga idonga nashi sewani lumshewa sukeyi suna bud'ewa Hakan yasa tashaga da kallanshi. Shiko Jin tayi shiru seya d'ago Yana kalanta Amma seyaga gabaki d'aya hankalinta na kanshi Amma bashi take saurareba aiko yak'ara Jin haushi sosai domin duk seyaga dantaga girmanshi ne takeson renamai wayo, cikin tsawa yace "waiba tambayarki nakeyiba? Okay ko abunda kike fad'a shine Dama kikaje Ganin inda kin iya iskanci acan kauyen naku mima kikace? Majici kome? To ainama kikisan wani abun maciji kodama kallan privide part d'in namuji ne kawai aikinki acan? Kinzama Yar iska bamusamibako? Yak'arasa zancen kamar anmasa dole tareda kafeta da blue eyes d'inshi masu razanata.

Itako arazanen kuwa ta d'ago tana fad'ar y'ar iska Kuma ya Ahmad wlh ni ba Yar iska bace yawwa sedai idan Kaine Dan iska kaida kefidda abun fitsarinka awaje ko kunya bakaji gashi katoto kamar macij...kuf tayida bakinta Saka makon saukar b'allarda bakin yaji seda tayi saurita dafeshi tana matsar k'wallah.

"Cikin Jin haushi M. Ahmad yace au watoma kinsamu Bakin maganar dazakimun rashin kunyako? Yayi Miki,, Dan shiru yayi Yana lumshe kyawawan idanuwanshi kamun yabud'esu tarrr akanta yace "mima kikace? Ninenayi mene? Yatamba idonshi tarr akanta. Hakan yasa tasha jinin jikinta tana girgiza mishi Kai cikin tsoro. "Humm yy kyau zakisan kuwa banajin kunya yafad'a Yana shafa kwantacciyar sumar fuskarshi...itako girgiza kanta tafarayi tana matsar k'wallah tareda bud'e Baki zatayi magana yayi saurin d'aga mata hannu yace "karki soma yimun magana yanzu domin bazan saurarekiba kawai kitashi kifara tsalle kwad'o Kuma daganan har kizagaye parlor Nan yak'arasa zancen Yana nuna mata inda zata fara...Ido tazaro tana fad'ar Dan Allah ya Ahmad kayi hak'uri wlh baza..cikin sauri yadakatarda ita tahanyar fad'ar dakin k'ara magana tinanina ze canja akanki nafara Baki horonda yadace da haukarki.

Gum tayi cikin kuka tafara tsallen kwad'o daga inda yanuna mata tanayi tana sharar k'wallah...shikuwa mayarda hankalinshi yayi kan wayarshi dayake dannawa kamar besanda allah yayi mutin awurinba, kusan awa d'aya hajja na Abu d'aya Amma yayi biris da ita kala tanayi cikin kukan takaicin yasakata harta farayi cikin kukan jigata..

Al'ameen kuwa tinda ya nazeer yagama sallah yashiga bashi lbrn abunda yafaru Wanda yasani tindaga farko har k'arshe...cikin mmki da tsoro Al'ameen yace "ya nazeer wai dagaske hajjar ce kekomawa jinjirar kodai wasu shedanune kesan tsorataku? "To nimadai bansaniba Al'ameen Amma dai wannan lamarin akwai tashin hankali acikinshi.. gaskiya kam Amma Koma minene aizamu Gani insha allah..kamun ya nazeer yak'arayin magana wayar Al'ameen tayi k'ara, d'auka yayi tareda karawa akunnenshi yace hello Abba. Bansan mi abban yace mashiba sedai kawai naji yace okay Abba tareda yanke wayar Yana kallan nazeeru yace barana kirawa iya delu ya Ahmad nadawo. "To shikenan sekadawo cewar ya nazeer,,,shiko Al'ameen yamik'e yafita.

Hajja nanan tana famada tsallen kwad'o Al'ameen yaturo k'ofar parlor yashigo batareda yak'arasa shigowa dukaba yacewa ya Ahmad Abba nakiranshi.. okay kawai yace tareda yad'ago ba, shiko Al'ameen yakoma warshi.

Mik'ewa yayi ahankali zefice idonshi yasauka akan hajja datake tsallen kwad'o komai na jikinta na tsallen kamar yadda takeyi, saurin d'auke kanshi yayi kamar begantaba yafice warshi. Aharabar gidan yakira captain basheer da wasu sojoji ukku yace su tsaremai hajja Kuma karta zaune kotayi Wani abun batareda yadawoba. "Okay Sr suka had'a Baki wurin fad'a kana shiko yanufi part d'in iyayen nashi..!

Autar alher ✍️

*JIKAR IYA DELU*

Page 15 & 16

"Dasallama akan labbansa yashigo parlor,,, dukkansu suna zaune akan dining har iya....Abba ne yace babana shigo mana kadawo? Ga iya tind'azu take tambayarka. "Murmushi maah tayi itama tace babana y aikin? Dukkansu bece musu komaiba seda yak'araso inda suke kana yace good evening Abba and maah how was yours day? Atare suka had'a Baki wurin fad'ar good son alhmdllh.

"Ahh ni delu Ina Ganin iKon allah 🤔 ayi mutin se bakin Hali da d'abi'ar yahudawa,, yanzu ace iyayen nakama sune suke haba haba dakai Amma Kai ko ajikinka sema Wani murtik'e fuska dakakeyi kana Wani kallan mutane shek'ek'e kamar wasu sa'anninka kana kawani mak'ile kamar anshak'e ashawo kana fad'ar Wani gudu'gudu attani abba, bawallah gudu attaniba gudu talata aikin banza aikin wofi. Iya tak'arasa zancen tana dallawa M. Ahmad harara.

Daga Abba har maah dariya kecinsu kamar me Amma bame halinyi...shikuwa gogan ko ajikinshi Sema zamada yayi agefen kojerarta Yana yamutsar fuskarshi...itako Ameena da fitowarta kenan taji iya na wannan lissafin taketa k'unshe dariyarta gudun kada tayi ya Ahmad yaci ubanta Amma da bahakaba da se cikinta yayi ciwo wurin dariya...tana k'arasowa wurin itama tace good evening all my lovely family tafad'a tareda mannawa ya Ahmad kiss ahannunshi Dake ajiye akan dining d'in....harara Abba ya Gallamata domin yagano bakin iyane take nema,,shiko ya Ahmad ahankali yad'ago yana kallanta kamun yabud'e Baki cikin sweet voice d'inshi yace "bro yasaka angyara Miki motarki? "Eh ya Ahmad...daga Hakan bek'ara cewa kimaiba yacigabada dannq wayarshi.

Itako seyanzu tad'ago tareda cewa "oyoyo oyoyo iya delun hajja oyoyo I miss you so much tafad'a lokacinda ta manna mata kiss a kumatu..laaa'haula fisha'atillahi yau nashiga aljannah da izinin uban giji wannan yarinyar zata kasheni da kirfa kwanana Basu k'areba wannan wanne irin Muna funcine? Dacan bakisan kimun oyoyo d'in ba seyanzu bayan kingama tsotsewa wannan yayan naki me bak'in Hali hannu kana Kiwanizo kinamun Wani oyoyo Nima tsotsar kumatamun nawa zakiyi kenan kina kiramun Wani misisi Toni magece ko mazuru? Dazakimun kiransu akunne iyee? Kajimun Yarada bakantar banza data wofi.
Chapter 1 · 0% Book details