← Book details Ig Ajeemal Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 6

Sashe 3

Ig Ajeemal Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

cikin nisha da yamurda matane nayunwa yasa tatuna tunsafe ba abunda tasawa cikinta , hakan yasa tamike tafice tabar fadeelah dake kwance saman bed tana latsa wayarta , nisha direct kitchen tanufa ta tadda barka tana tsaka da aikin da ammi tasata , barka naganin nisha tasaki murmushi, "

yar nan yau koma inakika shiga kolekoni bakiba inata cikiyarki ,murmushi nisha itama tayi tana fadin"

kinsan yanzu papan aheel yace nadaina kawo masa breakfast daga nan sede naje can part dinsa nayimasa girki dana dawo kuma bacci nakomayi shiyasa yau bakijiniba ai , "
.
Kai amma yayankun nan yana wahalar mana dake amma ko bakomai zaki samu lada ai, amma koya kikeji da wannan masifaffiyan matar tashi mai bala'in kishin tsaya duk ita take kore masu mata aiki saboda rashin hankali irin nata , barka tafadi gamida jimami, ,"

Uhm baba barka taimakeni da a binda zansawa acikina because yunwa nakeji sosai tunsafe namance banci komai ba nisha tafadi gamida kaiwar da zancen barka,"

laa ai ammi tafadamin bake a breakfast din dazu sabida bacci kike baki tashiba shiyasama nakillace miki naki breakfast din amma inda wani abunda kikeso kifadi yanzu sena miki shi,"

aa basekin wahalar da kankiba iya wannan dinma yayi ,"

To shikenan kede jekizauna a dining table yanzunan zanfito barka tafadi, bamusu nisha tayi abunda barka tace ba dadewa barka tafito daga kitchen tajerawa nisha plate agabanta plate din Irish and chicken dawani hadin salad agefe se dan madaidaicin kyakykyawan bowl mai daukeda fruit salad wanda yaji madara Yakuma sha sanyi ,bawani tsayawa jira nisha tasoma ci seda taci takoshi takauda yunwar dake tareda ita daga nan tadauki plates din tanufi kitchen, tana shiga ta ajiyesu daga bisani tashiga taya Barka da aikace aikacen da take ,sannu ahankali sunayi suna fira hatsuka kammala daga nan suka shiga jera kayan lunch bisa dining table daga nan Barka takoma kitchen tadauko try din abincin data tanadarwa kamal da matarsa masu lunch din tasuma kokarin ficewa,"

Baba Barka ina kuma zaki bayan gani ? nasan lunch din su ya kamal ne da aunty nabilah please bani nakaimusu na hutar dake ,"

Aa yar nan baza ayi hakaba, tunsafe kika gama bautan yayansu yanzu kuma nabarki kikare Dana kaninsa gaskiya baza ayi haka daniba kibarshi kawai yanzu zanje nadawo "

Please baba Barka kibari nakai mana , nanfa nisha taita mata magiya tareda dagewa Barka wanda yasa dole Barka tahakura tabata try din abincin nisha ta amsa tareda sa kai tafice , nisha nakarisowa door din kamal tashiyin knocking bugu daya zuwa biyu aka bude, koda budewa kuwa nabilah takagani tsaye cikin shirin kananun kaya t shirt da wando skintight wanda yawuce gwiwar kafarta kadan tasakalo sumarta har baya yakwanta lub tayi kyau da ita, murmushi nabilah tasakarwa nisha cikin sanyin murya tace ,"

Please come in! ahankali nisha tasakalo kafarta takariso cikin parlour yayinda nabilah tamaida door tarufe ta dawo kusa da nisha ta tsaya tana cigaba da murmushi, itama nisha murmushi take daga bisani tashiga fadin, "

Am..dam.ma lunch dinku ,"

Ayya thanks you so much nabilah tafadi gamida karban try din abincin takarisa dashi saman table ta ajiye ganin haka yasa cikin hanzari nisha tace,"

se anjima daga haka tajuya tafice tabar nabilah tsaye tana binta daga kallo hartafice , nisha nafita tundaga nisa ta hangi ajmal hanunsa dauke da na aheel se kamal da Daddy wanda yanzu dawowarsu daga masallaci sunjero suna tafiya gwanin sha'awa da burgewa kamal daga nesa ya hangi nisha tafito daga part dinshi amma kafin su iso harta shige bangaransu cikin sauri, direct ajmal yanufi side dinshi shida dansa hakama Daddy yanufi nashi sashin , daga nan kamal shima yakarisa nashi part din,
Da dare guraren karfe 9:pm gabaki daya ahalin abubakar modibbo bature sun hade guri guda suna gudanar da kayataccen dinner, dining table medauke da gurin zaman mutum 12 kowanne acikinsu yakasance daga daya daga ciki wasu suna facing din wasu gwanin burgewa da ban sha'awa harda heelah wacce ajmal ya gayyatota badan komai because Daddy yace yana bukatan kowa yakasance gurin dinner, heelah batasan da dawowarsu kamal ba kwata kwata seyanzu da tashigo ta ganewa idonta wanda hakan ba karamin mamaki tayiba ,

Nisha kuwa tayi tsayuwar daka wajan taya Barka kawo abinci anajerewa wanda komai tare suka gudanar dashi seda suka kammala jera komai Barka tajuya takoma ciki nisha kuma tasamu daman zama kamar yadda kowa yazauna ,daga nanfa kowannensu yashiga serving din kanshi da abunda yakeso yana zubawa a plate, banda ajmal dako motsi baiyiba bayida kuma niyar motsawaa "

yade kowa yadibi abunda yakeso yana ci kaikuwa kasa phone agaba kana dannawa? Daddy ke tambayan ajmal dayayi sunkuye da kayi yana latsa phone dinsa, dan dago kai yayi ba tareda yace komai ba ya ajiye phone din gefe daga bisani yagyara zama ya kallo nisha wacce idonta ke kanshi because kujerunsu yana facing najuna, yanda yakora mata ido tasan serving dinshi yakeso tayi amma ita kuma nisha setashiga kallon heelah wacce takecin abinci tana yamutsa fiska kamar wacce akasa dole ko kallon inda sukema batayi, nan kuma taimada kallonta ga ajmal wanda ya hade rai yabata fiska wani kallon da yakuma watsa matane yasa nisha mikewa tsulum wanda hakan yayi sanadin dawowada hankalim ahalin guresu,

daga hajia Daddy suwa ammi suka shiga murmusawa ganin yanda nisha ke serving din ajmal gwanin shaawa da burgewa duk da dama sunsan ajmal inde tawannan fanninne to komai se amsa abincin ma inda zaisamu adinga bashi abaki ajiye spoon zaiyi , Goggo rabi bakinta kamar zai taba kumatu tsabar murmushin jin dadi, kamal kuwa da mamaki yake kallon nisha ganin bani na iya irin na yarinyar dayin abunda ba asataba gaba daya yarinyar tanasun bawa kanta wahala , taban garan heelah nunawa tayi ko ajikinta amma cikin zuciya allah kadai tasan kunar zunda take gaba daya nisha Rana shigar mata hanci amma ba dadewa zata facuta,

Nisha harta gama serving din ajmal takoma tazauna kamal kebinta da kallo , nabilah kuwa duk motsin mijinta idonta nakansa , abincin dake gabanta bawani ci sosai takeba kawai tsakura take tana juya spoon ajmal kuwa nisha nagama serving dinshi yashiga gunar da nashi cin abincin, Jim kadan ta bangaran nabilah tafarajin kanta na bala'in sarawa, jitayi duniyar najuya mata ahankali ta ajiye spoon din hanunta adan dafe tamike daniyar tashi ,"

Bade harkin kammalaba ammi ta tsareta da tambaya , nabilah bude baki tayi daniyar magana sekuma takasa because wani yunkurin amai dayataso mata aiko cikin hanzari ta toshe bakinta tawatsa aguje tafice daga parlourn,
gabaki dayansu se bin bayanta da kallo suka shigayi harta fice banda kamal dayayi yunkurin tashi yabita, "

mekatsaya hira dakasa bin bayan matarka kamata yayi kabita idan da wani abunda yaci karfinku sekazo kayi magana hajia tafad'i tana kallon kamal wanda keta zare ido shibai zaunaba baikuma tsayaba but jin abunda hajia tafad'i yasashi jin karfin gwaiwar bin bayan matarshi dan haka cikin hanzari yabi bayanta, "

Masha allah , ikon allah kai allah abin godiya, tsarabar Canada har gida kai alhamdulillahi Goggo rabi tafadi tana daga hannuwa sama, hajia da ammi farinciki harsun kasa cewa komai , Daddy kuwa kai kasa se murmushi yake heelah se hararo Goggo rabi take wacce keta kwararo godiya ga ubangiji",

dama kinbar wannan godiyar dakike dan abunda kuke tunani insha allahu zubewa zaiyi bade tahaifeshi cikin gidan nanba heelah ke maganar zuci , gefe kuwasu reeda ne ke magana kasa kasa tsakaninsu,"

Awwwn nabilah fa kamar cikine gareta ko fadeelah tafadi ahankali,

bakamar bane cikinema reeda tabata amsa yayinda sukacigaba da cin abincinsu kamar basu suka gama kuskus yanzuba, duk abunda suka gama tattaunawa tsakaninsu nisha najinsu se murmushi take gefe gefe aheel zaisamu kani zasu samu little baby, shikuwa gogan ko ajikinshi tamkar baisan me akecikiba abincinsa yakeci cikin kwanciyar hankali,

Kamal nakarisawa part dinsu koda yashigo parlour ba nabilah aciki hakan yabashi daman karisawa cikin bedroom nan yaci karo da sautin nabilah cikin toilet tanata faman zabga amai cikin hanzari yakarisa baking toilet din ya tsaya harseda ta gamayin aman tawanke bakinta tafito ta tararda kamal bakin door yana jiranta, "

sannu! meyake damunkine kamal ya tambaya gamida tallafota suka karisa bakin bed suka zauna, "

Please tell me what's wrong ? Kamal yakuma tambaya, "

bakomai nabilah tafadi gamida sunnar dakai kasa ,cikin hanzari kamal yadauki phone dinshi yasuma lalubar wata number, "

Wait! what are you doing? Nabilah ta tambaya gamida rike hanunshi, "

doctor fu'ad zankira yanzo ya dubaki yafadamin meke damunki kamal yabata amsa cikin damuwa nabilah karban wayar tayi ta ajiye gefe daga bisani takalleshi yana fad'in, "

bakasan me yake damunaba? gyada mata kai kawai kamal yayi daga nan nabilah tadauki hand din shi tadaura saman cikinta tacigaba da fad'in,"

Babynmune yake zuwa very soon zan koma mummy kaikuma zaka dawo Daddy

🌴🌴 *IG AJEEMAL*🌴🌴

* _STORY AND WRITING_*
By
*_OUM AMREESH_*�
_khaleeseart Raeeys_

........ *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*
(J.W.A)
_masu aiki da zallan fikira da fusaha tareda jajircewa wajan sarrafa alkhalamin wajan ilmantarwa fadakarwa tareda nishad'a tarda al'umma_

بسم ا لله الر حمن الر حيم

.................*_Free book_*😍
.....page51

Cikin murna da farinciki gamida d'auki kamal ke kallon nabilah, "

Oh god waiyanzu ciki gareki ? d'an g'yad'a kai nabilah tayi tasunnar dakai tana murmushi, "

Oh Allah nagode maka zanzama Daddy yanzu nakara girma nima kamal yafad'i tareda rungumo nabilah yana cigaba da fad'in, "

Nagode Allah yamiki albarka ya kareki keda babyna , daga nan nabilah tarungumishi cikin tsatsan so da kauna tana fad'in "

Ameen sannu ahankali suka suma lulawa duniyar maaurata cikin shauki da begen juna , ....

Abangaransu Daddy koda sukajira suga dowowar kamal sukaji shiru hakan ya tabbar musu lapiar kenan da haka suka cigaba da gudanar da dinner d insu , koda suka kammala daga nan kowa yashiga watsewa don yau ba tsayawa dugun hira kasancewa dare yayi sosai , dama ajmal baitsaya wani dugun cin abinciba yatashi yafice, matarshima tarufa masa baya tareda aheel daketa rigima shi bazai mom dinsaba gurin auntynsa zai kasance , daker heelah tasamu tayakiceshi daga jikin nisha suka fice ,
Chapter 3 · 0% Book details