sashe na zaki dawo ba da jimawa ba"
Haihuwa-Da-Hanji-Complete Hausa Novel · about 178 min read
Suka yi murmushi ta dubi su Aishatu
"Sai ku zauna nan duk abinda basu fahimta ba za ku iya fahimtar da su da kuma bayani akan
family Dukda sai a hankali za su san kowa"
Suka amsa kan ta miƙe ta fice suna mata sai anjima.
Yadda su Aishatu suka kame haka dukkansu suka kame sai hirar ya koma tsakanin junansu
kawai ita jannah ma waya take da mijinta yayinda Abeeha ke hira da Afeefah suna yar dariya,
kaman daga sama sai ga shi ya shigo. Ko Aisha yau ne suka fara ganin juna dashi face to face,
zama yayi a one seater ya kame yana kallonsu daya bayan É—aya, jannah ta fara gaishe shi ya
amsa ta mishi murnan dawowa cikin family Abeeha ma ta gaishe shi.
Zarah ce ta gaishe shi ya kalleta yana son tuna sunan
"Aammm.."
"Zarah"
"Oh Yeah lafiya ƙalau"
Ya kalli Aisha da ta gaishe shi last itama ya amsa, Afeefah ce ta gaishe shi ya É—an yi shiru kan
ya kalleta sai ya miƙe ya nufi ɗakinshi.
Abeeha ta miƙa hannu ta mistineta, kallon jannah tayi sai jannah ta harareta dole ta miƙe don
sun cika ta da lectures kaman me akan Rayyan tun fitansu gida har hawansu jirgi zuwa
sauƙansu magana ɗaya ake babu abinda basu gaya mata ba akan gidan sarauta sai ta tashi ta
kama mijinta a hannu in ba haka ba ta ji a salansa.
Ruwa ta haÉ—a a tray da cup mai tsananin kyau ta É—auka ta nufi É—akinshi, yana zaune bakin gado
dafe da kanshi dake É—an sarawa ya ji sallamar ta, bai É—auka za ta shigo ba sai kuma ya ganta
unexpected idanunshi masu shiga jikinta ya kafe ta da su yana yawo lungu da saƙo na jikin
nata, tana sanye da doguwar riga peach mai roba ya fitar da duk wani shape É—inta ta É—aura
dankwalin sai ta sako jelar guda É—aya ya sauka har kan kirjinta tayi kyau sossai barin ma lips
É—inta dake shining na lip gloss.
Ruwan ta zo ta ajiye mishi tana ɗan ɓata fuska, fuskar yake ta bi da kallo bayan ta ajiye ta juya
zata tafi karab ya riƙo hannunta ya ɗan ja ta tayi baya baya ta zauna bakin gadon gefenshi har
suna gogan juna ya juyo ya kalleta ba tare da ya saki hannun ba.
"HaÉ—e ran nan fa?"
Yayi magana yana dan É—age gira guda alamun tambaya, lumshe ido tayi don maganan ta ji shi
ne har cikin zuciyarta.
Bata san ta narke ba tayi shiru bata ce komai ba. Kuma sai bai ji haushi ba sai ma kyau da ta
mishi yadda take yi da fuskan itama kuma ta ji daaÉ—i da bai mata ihu ba sai ma Ruwan da ya
É—auka ya sha kaÉ—an ya ajiye yana dafe Goshi da hannunshi É—aya har lokacin É—ayan na cikin
hannunta yana dan motsawa a hankali.
"Ba ka da lafiya ne?"
Ya ji tambayar nata sai ya buÉ—e idanunshi da suka É—an sauya ya kalleta ya É—aga mata gira É—aya
"Sorry"
"Kin san Meyasa ban amsa gaisuwarki ba?"
Ta girgiza kai ashe ya san laifin da ya sakata fushin ma.
"Saboda ba haka ake gaisar da miji ba madam..."
Kan tayi wani magana ya ja hannun nata sai jinta tayi kirjinshi ya rungumeta ta runtse ido tana
jin zuciyarta na chanza bugu, a hankali ta sa hannunta ta riƙe shi yayi baya baya ya jingina da
jikin gadon ya É—an lumshe ido.
"Ya kike?"
Taji maganan daga sama, ita dai ta rasa gane kanshi so yake sai ya zautata ko menene?
"Lafiya ƙalau, ina taya ka murnan reunion ɗinka da family... Na kuma ga naɗi Allah ya taya riƙo"
Ya yi murmushi kaÉ—an kan yace
"Ameen, thanks"
Suka yi shiru, ƙoƙarin Miƙewa take ya matse ta
"Your perfume! Yana da daaÉ—i"
Tayi murmushi
"Thank you, gashi na mata ne da na baka"
Dole ya saka shi dan murmusawa yadda take maganan bilhakki.
Sun dan jima haka kan aka kira azahar ya sake ta ta mayar da kanta ƙasa tana wasa da bakin
gyalen ta shi kuma yana kallonta.
"Kin gama exams lafiya?"
Tana mamakin yadda sai an manta wani abin shi kuma sai lokacin yake magananshi
"Alhamdulillah"
"Meyasa kika shiga toilet da waya kika jefa ruwa?"
Ta É—an zaro ido tana mamakin yadda aka yi ya sani shi kuma idanun yake kallo, haka kawai yaji
baya so su daina maganan Dukda kanshi dake sarawa sai yaji in dai magana da ita ne ko za'a
kwana kaman ba zai gaji ba, sanyin yanayinta, kamshinta, murmushinta da ma maganarta
kashe shi suke.
Bayani take mishi amma Bakinta yake kallo har ta gama bai ji komai ba, jin ana shirin shiga
sallah ya miƙe ya nufi bayi bai ce komai ba, ta girgiza kai ta dauki tray ɗin ta fito dayake
É—akinshi akwai dan hanya tsakanin shi da parlor da hakan yasa tana gab da bayyana parlor ta ji
Zarah na cewa Aisha
"Aisha kina ganin Ya Sameer zai yarda ya aureni? Wlh tun ranar da ya cecemu na kamu da son
shi da na fahimci shine Yaya Sameer wanda nake da alkawarin aure dashi tun yaranta sai na ji
na sake kara sonshi kalleshi kiga yadda yake komai cikin wani irin aji da natsuwa...ba ki ji kishin
da Naji ba da na kalli matarshi"
Aisha tayi dariya
"Zai aureki mana kin taba ganin inda aka yi alkawarin aure aka karya shi a zuri'ar nan? Kuma ai
na ga matar tashi tana da sanyi bare ma dolenta ta ga kishiya har da kwarkwarori ma idan yana
so sarkin gobe fa take aure"
"hakane kam duk kishi na shiyasa nake dannewa sanin a auren sarki iya ruwa ne fidda kai
kowacce ta iya allonta ta wanke ne, yanzu haka ba za'a rasa ma waenda suka nemi haÉ—in aure
dashi ba ta wurin mai martaba daga bayyanar shi zuwa yau"
Sossai maganganunsun ya daki Afeefah, bata san wani irin yanayi ta shiga ba ko motsi bata yi
ba sai da ta ji ya buÉ—e kofa ya fito sai ya tsaya yana kallonta tayi kokarin danne abinda ke taso
mata ta fita parlorn ya bi bayanta ya fice masallaci ita kuma kan ta isa dining ma kuyanginta sun
karɓa...
"Ba Za mu isa kuyi sallah ba?"
Ta tambayesu tana danne yanayinta kwarai da gaske don for the First time a rayuwarta taji
zafin wani duk abubuwan da ake mata a baya tana kokarin shanyewa kuma tana kokarin ta ga
bata tsani kowa ba amma yanzu ji tayi bata son sake kallon Zarah a inda take, har É—aci É—aci
take ji akan harshen ta maganan son da take yiwa Rayyan ke ta kai koma a ranta...
"Kar ki damu yanzu za mu tafi ma ai"
Kai ta gyaɗa suka miƙe suna mata sai anjima tace
"Na gode sai anjima"
Suka fice ta nufi É—akinta ta samu bakin gado ta zauna tana dafa kirjinta dake zafi zafi, duk É—an
farin cikin da ta samu a tare da shi ya kau.
Bata motsa ba sai da aka mata sallama ta ba da izini aka shiga sai ta kalli wata mata ce babbar
mace rike da wani tray a hannunta wata kuyanga na binta a baya da akwati
"Barka da wannan lokaci ranki ya dade"
Nauyi taji na matar tace
"Ina yini?"
Matar ta kalleta lallai wannan ba tashin masarauta ba ce.
"Fulani FaÉ—imatu ce ta aiko mu shirya ki mai martaba na son ganinku gabaÉ—aya"
Kai ta gyaÉ—a matar ta shige bayi ta haÉ—a mata ruwa mai kamshin gaske ta mata iso cikin bayin
ita dai ba don su jannah sun ce mata kar tayi musu a duk abinda ake sakata ba da zata ce
musu ba sai ta yi wanka ba yanzu tayi wani amma kuma da ta shiga ruwan yadda aka hada shi
ya mata daaÉ—i da ta fito kamshi duk motsinta haka yake tashi.
Turaren kolecture suka bata mai bala'in kamshi ta shafa ko ina na jikinta kan ta shafa lotion
É—inta, da kansu suka shirya ta cikin atampha riga da zani da ya zauna mata sossai suka bata
gyale ta yafa bayan sun daura mata dan kwali suka hada gyalen da É—an kwalin suka yi pinning
yadda ba zai dinga zamewa ba kan suka É—ora mata wani cream colour Alkyabba da yayi mata
mugun kyau kaman ka sace ta ka gudu.
Ta kara turaruka Dukda kamshin ma da take ya isheta, kan suka fito gabaÉ—aya ta samu su
Abeeha a parlor
"Masha Allah Kin ga yadda kika yi kyau uwargidan Ciroman fombina kuma Yariman matasan
fombina?"
Sai ta É—an yi murmushi kadan don uwargida da aka ce ya tuna mata kalaman zarah..
Suka fice gabaÉ—aya aka musu jagora har babban parlorn mai martaba sun samu kowa na nan
na kusa kusa dangi da ya kamata a ce sun sani.
Gaisuwa aka yi Mai martaba ya gabatar da Uncle Musa da su Uncle sanusi matsayin dangin
Rayyan tunda su suka rike shi tun barin shi gidan har kawo yanzu, yayi musu godiya marar
iyaka kan ya nuna su Abeeha matsayin 'ya'yanshi don ya ce a yanzu basu da maraba da su
Aisha a wurinshi sai ya nuna Afeefah don Ammi dake gefenshi duk ta nuna mishi su dama
kuma ya riga ya gaisa da su Uncle kan zaman duk Ciroma yayi introducing nasu.
"Ga 'yata Afeefah ita ce matar Ciroma, ina fata za mu cigaba da zama anan cikin zaman lafiya
da haÉ—in kai yadda muke tafiya, ina marabtar ku da shigowa wannan masarauta matsayin 'ya'ya
masu daraja, duk wani abu da kuke so za ku iya zuwa kai tsaye wurina dukkanku matsayin uba
nake a wurin ku kaman yadda na dauke ku duk 'ya'ya na"
Godiya duk suka yi Afeefah dai na matuƙar takure kuma zuciyarta bugawa yake kaman zai fito
tana jin idanu sun mata yawa a jiki amma bata iya ta É—ago ba har sarki ya sallami Matan suka
fice
"Afeefah!"
Ta ji muryarshi ya kira sunanta sai taji wani iri, sunanta a bakinshi daban take jinshi chak ta
tsaya ya matso har tana jin kamshinshi da ma numfashin shi dake fita a hankali...
"Ba na son duk abin da za'a baki a gidan nan ki ci! Idan ma ya baki sha'awa za ki iya fada min
in nemo miki amma kar ki ci komai daga kowani bangare a gidan nan ina fata kin gane?"
Kanta ya ƙulle ta ɗago ta kalleshi amma ganin idanunshi a kanta ya sa ta ɗan gyaɗa kai.
"Ki amsa min da bakinki, bana son jin cewa kuskure ne ko akasin hakan... Ba kuma na so ki
fara tunanin dalili hope am clear?"
"In shaa Allah"
Kai ya gyaÉ—a ya juya ya koma ita kuma tayi gaba ta samu su Jannah, aka fara raka su sashen
Fulani Adama duk inda ta wuce kirari ake mata.
A ƙasa duk suka zauna tana kame cikin kujera suka gaisheta ta amsa tana ɗan murmushi
"Æ´a ta Afeefah sai ga ki gidan sarauta, ina fata za ki ba da haÉ—in kai wurin ganin an zauna cikin
aminci kin ga nan ba kaman normal gidaje ba"
Tayi murmushi tace
"In shaa Allahu Mama"
"Sannan za ki yi haƙuri da tsare tsarenmu anan, duk muma haƙuri muka yi muke zaune lafiya
ina fata in kin ji labarin alkawarin zarah da mijinki ba za ki ji haushin mu ba kar ki ga kaman
daga dawowanshi ne aka bashi mata, kin san mu anan al'adar mu in aka haifi namiji da shekaru
biyu ko uku ko ma biyar daga an haifi mace to za'a yi mishi alkawari wanda sai in mutuwa ce ta
karya, kin ganni nan tun ban yi rarrafe ba nake matsayin matar mai martaba haka ma Uwar shi
Ciroma amma kin ga duk muna zaune ne lafiya cikin amana da kula da juna"
Ta Yi mugun ƙoƙari da ta iya danne hasalan da ranta ke yi tayi murmushi
"Eyyaaa Allah ya ba mu ikon zama lafiya na gode".
Sai kallonta Fulanin take har suka tashi suka fita ta sa aka bi su da kyautarta na maraba a
ƙwarya rufe da faifai...
Su Jannah maimaita maganan suke da damuwa ita dai bata ce musu komai ba har suka shiga
wurin Ammi suka gaisheta
"Afeefah kina lafiya kam?"
Ta gyaÉ—a kai basu jima sossai ba don su Zarah suna wurin suka mata sallama itama kyauta
sossai ta basu a ƙwarya suka nufi wurin Fulani Ameenatou kadaran-hadaran suka gaisa ta basu
kyautarta suka nufi wurin Amarya Fulani Salimah itama suka gaisa kan suka nufi sashensu
alkyabbar kawai take so taji ta cire ta huta gashi ana ta kiran la'asar, suna zuwa kuwa ta zame
kayakin tas ta É—auki karamar riga marar nauyi mai hannun singlet dogo ne sossai silk Brown ta
saka yana da tsagu gefe da gefe har wurin gwiwa ta hau gado ta kwanta kawai bata motsa ba.
Maganganun da ta riska yau kawai a gidan ta ji ya sire mata, bata san ta fashe da kuka ba
zuciyarta na squeezing yana mata zafi ta ma rasa me ke damunta.
Ta Yi kuka har tayi bacci a haka sai Magrib ta farka ta dauki hijabi ta saka bayan ta wanke
fuskanta idanunta dai har lokacin sun dan kumbura kuma sun yi ja ta fito parlor ta samu su
Abeeha suka É—an yi hira ta ci abinci kaÉ—an kan ta ce musu za ta kwanta kanta na ciwo daga
haka ta shige É—aki.
Abeeha tace
"Addah jannah baki kula Afeefah na da damuwa ba?"
Tace
"Na kula Abeeha ko nima ina taya ta damuwa ace daga zuwa yau an fara mata zancen zata yi
haƙuri mijinta aure zai yi, na san zai iya yi probably tunda dama haka tsarin su yake amma
kuma bai kamata ana fada mata ba gaskiya."
"Gaskiya sai Naji da ma bamu zo ba ni da nake murna, ashe abin da za mu tarar kenan ni
haushina ma ko fa gama fahimtar juna basu yi ba."
"Dole mu san abin da za mu yi akan hakan Abeeha, ki ji mana ko mu yi amfani da kishin nata
ne mu ƙara kusanta su?"
Shawara suka fara suna murmushi, Abeeha ta miƙe ta shige ɗaki jannah ta cigaba da zama don
ita ce ma take dan iya magana da Rayyan É—in ba tsoro ba komai tana nan zaune sai gashi kallo
daya zaka mishi ka san ya gaji tiɓis.
"Sannu da dawowa Yaya"
Ya amsa da
"Yauwa"
Zai wuce tace
"Wai da ma kai nake jira ne!"
"Allah ya sa lafiya"
"Da sauƙi dai Yaya Afeefah ce tun ɗazu take kuka wai kanta na ciwo ta sha pcm ma bai sauƙa
ba"
Ya É—an yi jimmm yace
"Meyasa baku kira ni ba? Kun san tana da low BP sai ta fara suma ne za ku yi aiki da hankali?"
Da faɗa ya ƙarasa ta ɗan duƙar da kai
"Ka yi haƙuri"
Ya ja tsaki kan ya juya yayi É—akin Afeefar.
Ta saki murmushi ta juya ta nufi É—akinsu Abeeha na jiranta suka kashe suna dariya har da
kwaikwayon masifar shi, shi kam yana shiga....
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*50*
Kai tsayen bakin gadon ya nufa ya kai hannu ya yaye duvet da take lulluɓe ciki, a hankali ya
sauƙe hannunshi a goshinta hakan ya sa ta ɗan buɗe ido ta kalleshi sai ta mayar ta rufe, ta
sake buÉ—ewa idanunshi a kan wuyanta zuwa kan kirjinta da har saman ke a bayyane, muryarta
yaji tace
"Ya Saraki!"
Sai ta sake mayar da idanun ta rufe, ƙarasa yaye duvet ɗin gabaɗaya yayi ya kai zaune gefenta
yana kai tafin hannunshi ya shafa wuyanta da shima ya É—an yi dumi amma ba zafi ba.
"Kuka kika yi? Me ya sameki?"
Shiru tayi bata buÉ—e idanun ba shi kuma bai daina shafa wuyanta da ya É—auki hankalinshi
sossai ba, jin yana ta da mata da tsikar jiki yasa ta kai hannu ta riƙe hannun nashi cikin wani irin
murya ta sake kiran sunan nashi
"Ya Saraki!"
"Na'am Matar masu sarauta."
Yadda ya amsan sai da ta buÉ—e idanunta, sunan ya shige ta har inda bai kamata ya je ba.
"Mu je ki gayamin dalilin wannan kuka"
Ko motsi bata yi ba, ganin ta ƙi motsawa Ya sanya hannu ya ɗauke ta chadak sai jinta tayi cikin
hannunshi bai sake cewa komai ba ya fice da ita zuwa É—akinshi, a kan shimfidadden gadon shi
ya yi mata masauki zai kalleta don tunda ya É—auketan a bazata kallon fuskanshi take tana jin
soyayyarshi na shiga jini da bargon ta tayi saurin rufe idanu, bai ce komai ba ya miƙe yaje ya
watsa ruwa ya sanya kayan baccin shi ya rage wutan É—akin kan ya zo ya hau gadon ya kwanta.
Duk abinda yake tana jinshi, kwanciyarshi da janyota zuwa jikinshi duk lokaci É—aya hannunshi
zagaye da kwankwasonta ɗayan a haɓarta ya furta
"uhmm faÉ—amin"
Da kyar ta iya samo kalmar
"Mene?"
Ta furta
"Abin da ya saka Matar Saraki kuka har ya ja mata ciwon kai"
Shiru tayi for seconds tsantsin rigar jikinta da kamshin dake fita daga jikinta har gashinta ya
shagaltar dashi a hankali yake É—an bin jikin nata yana shafawa ba tare da ya sake magana ba.
Chan tace
"Wai da gaske ku nan tun yaro na ƙarami ake mishi mata? Da gaske sarki ba zai iya zama da
mace É—aya ba?"
Shiru yayi, chan ya ce
"Wa ya faÉ—a miki wannan magana?"
"Kawai na ji ne a wani labari..."
Murmushi mara sauti yayi kishi ne ya sakata kuka kuma ya san tabbas faÉ—a mata aka yi don
wulakanci daga zuwanta an tarbe ta da abin da zai sakata kuka a banza, kwafa yayi bai ce komi
ba
"Da gaske ne kenan?"
Ya ji muryarta na É—an rawa tayi tambayar.
"Shhhh ki yi bacci, za mu yi maganan wani lokaci"
Dole tayi shiru, hannunshi yake É—an bubbugawa a bayanta kaman mai rarrashin 'yar baby har
tayi bacci ya sauƙe numfashi yana saƙe-sake mai dumbin yawa har bacci ya sure shi shima a
haka.
Washegari ko da ya tashi sallah ya san bata yi so bai tashe ta ba, ya gyara mata kwanciya kan
ya miƙe ya shige toilet yayi alwala ya fice masallaci, daga nan ya tsaya suka gaisa da su Uncle
sun jima suna magana da Saleem da duk yau suke zancen juyawa, sai da gari ma yayi haske
sossai ya dawo bai sameta É—akin ba amma ta gyare tsaf ta saka turare ya tsinci kanshi da
murmushi kaÉ—an kan ya wuce yayi wanka bayan ya shirya yana ma shirin fita ne ya ji sallamar
ta.
Ya amsa yana mayar da idanu kanta sai ya lumshe su ya sake buÉ—ewa, yarinyar tana fusgar
hankalinshi fiye da yadda zai misalta sanye take da wani coffee doguwar riga mai shige da
material amma yana da kauri an tattare kirjin ƙasan a sake wane umbrella suna haɗa idanu ta
kawar da nata don bata iya jure kallon cikin idanunshi barin ma in yana binta da mataccen
kallon nan da ya tsira, gaban kujeran dake dauke da table ta ajiye mishi tray É—in da ta shirya
abincin kaman ka kwace don kyaun da yayi a ido, doya ne dafaffe da sauce na manja kana
ganin kifi nasha nasha a ciki da kuma dafaffen kwai cikin Miyar, sai dafaffen plantain da ta musu
wani yanka mai kyau, da tea mai kauri cikin mug sai da ta ajiye ta É—ago lokacin ya matso dab da
ita.
"Good Morning!"
Ta faÉ—a har lokacin bata wani fara'a don ba wani daaÉ—in zuciyarta take ji ba, hannunshi na
dama ya miƙa mata alamun su yi musabaha sai ta sanya nata ciki a hankali, da sanyawar da
sauya hannun nashi da yayi zuwa hagunshi da fusgarta zuwa kirjinshi da zagaye
kwankwasonta da yayi da hannunshi na daman duk lokaci É—aya, kirjinta da nashi suka haÉ—e ta
zaro idanu tana kallon shi shima cikin idanunta ya zubawa idanu sama da seconds biyu kan ya
furta
"Good Morning Caramel Queen..!"
Ya faɗa yana bin smooth and silky skin ɗinta da wani irin kallo, kanta ta mayar ƙasa.
Ya zame hannunshi dake kwankwasonta ya kai kan fuskarta da ta sako 'yar gashi kaÉ—an gaba
ya É—an shafa gashin da yatsa É—aya yana mayar dasu gefe ya furta
"Ya ciwon kan?"
Ta kalleshi ta kawar
"Alhamdulillah na ji sauƙi"
"Har yanzu fushin ne?"
Tayi shiru, ya ɗago haɓarta ya hura mata iskar bakinshi ta lumshe idanu, tana jin tender nd soft
palms É—in shi na wasa da tafin hannunta.
"Talk!"
Ta sauke nannauyar numfashi tana jin salon shi na kasheta, zamewa tayi tana zare hannunta
"Abincin ka na sanyi"
Haka kawai he doesn't like this silent treatment of hers.
Zama yayi bai ce komai ba ta tura mishi abincin ya fara ci da bismillah ta juya ta fice, bayanta
ya bi da kallo har ta rufo kofar ya sauke numfashi a lokaci daya yana tunanin wanda ya fada
mata batun zarah shi da ko za'a shaƙe shi ma bai san kamannin zarahn a idanunshi ba, salon
kishin ta kuma ya tafi dashi har yana dan murmushi wai ita tana fushi hmmm
Misalin karfe sha É—aya dukkansu suka fito don sallama da su Uncle Musa da zasu koma da
Saleem, ita jannah na nan akwai wani taron Matasa da aka haÉ—awa Yariman na Matasa kuma
Ciroman fombina wanda zallar al'ada suke son fitarwa a wannan gagarumin taron za'a yi shi a
jibi sai gata sai ta wuce itama ta bar Abeeha da har sun fara batun neman transfer don Rayyan
ya rantse ba gidan da zata je ta zauna kuma ba zata zauna hostel ba.
Tun tahowarsu ya zuba mata idanu magana yake da Afeefah matsayin É—an uwa da 'yar uwa
yana kuma bata ƙwarin gwiwar zaman cikin gidan amma tahowar Aisha ya ɗauki hankalinshi
har bai san kuma me yake cewa ba, Afeefah ta juya ta kalli wacce yake kallo haka ta saki
murmushi ta juyo tayi waving
"Ya Saleem ya dai?"
Cike da dariya shima ya É—auke kai ya mayar kanta
"An tafi da ni ne, kanwata za ki taya ni yaƙi"
Dariya tayi lokacin Rayyan ya ƙaraso inda suke har lokacin Afeefah na murmushi yace
"Me yayi muku daaÉ—i haka?"
Idanunshi a kan matar tashi da murmushinta ya tafi dashi ainun.
"Sirri tsakanin yaya da kanwa"
Inji Saleem, ta É—an waro ido ta kalli Saleem tace
"Gwara ka kiyaye aka hana ka babu ruwan Afeefah"
"Da fa gaskiyarki, Yayanmu barka da fitowa"
Ya juya yana miƙawa Rayyan hannu da kaman yanzu ne suka haɗu cikin ladabi.
Murmushi Rayyan yayi yana girgiza kai wanda ya shagaltar da Afeefar a kallonshi don
murmushi ne da bata taɓa gani yayi ba, murmushi na mishi kyau ainun barin ma fararen
hakwaranshi da suka bayyana suka haske fuskar tashi.
Gaisuwar da su Aisha ke musu ya sa ta dawo daga duniyar shagaltuwarta sai dai ganin kallon
da zarahn ke yiwa Rayyan ya sa taji duk mood É—inta ya chanza, shi kam Rayyan ko kallonsu bai
yi ba ya amsa Uncle Musa ke yiwa Saleem magana akan su wuce kafin su yi missing flight dole
duk suka yi wurin motar ya dubi Afeefah
"kanwata za mu yi magana fa"
Ta gyaÉ—a kai kawai suka yi sallama suka fice cikin motocin alfarma wanda da Rayyan suka tafi,
su matan su uku suka yi sashenta suna 'yar hira yayinda Zarah da Aisha suka nufi ɓangaren
Ammi.
Rayyan bai tashi shigowa gidan ba sai yamma sossai, a parlor ya zauna ta kawo mishi ruwa ya
sha hankalinshi duk a na kanta a koyaushe dressing É—inta na kashe shi don yanzu fitted
atampha ne a jikinta tayi É—aurin ture ka ga tsiya da ya zauna mata tana kokarin É—age tray É—in
gabanshi tace
"Abinci fa?"
"No sai anjima am not Hungry"
Kai ta gyaÉ—a ta nufi kitchen shiganta ba jimawa tana ba kuyangin ta umurnin aikin da za su dan
yi mata su yanke yanke na shirya mishi abincin daren bayan ta gama ta nufi fitowa daidai
Gaabɗo ya shigo da wani paper bag ya zube a ƙasa
"Ranka ya daɗe wannan saƙo ne daga Gimbiya zarah tace a baka"
Da wani irin hanzari ya ɗago ya kalli kofan kitchen ɗin, bai taɓa jin tsoron wani ya ga ko yaji
abinda babu daaÉ—i ba irin yanzu da yaji duk duniya tashin hankalinshi shine taji wannan zance.
"Fita dashi, kar ka kara karɓan abu da sunan sako zuwa gareni matukar ba matata bace ko
mahaifina"
"A gafarceni ran..."
"Fita nace!!"
Da É—an karfi yayi maganan da sauri GaabÉ—o ya fice.
Ya tashi shima gabaÉ—aya a parlorn ya wuce É—akinshi a lokacin ita kuma ta fito hawayenta na
zuba, Jannah da Abeeha dake daga chan jikin ƙofan ɗakinsu suka yi dariya.
"Allah ya sa ta ji, don hakan ne kawai zai kawo musu kusanci idan tana kishin nan tana fusgar
hankalinshi ne kanta"
Jannah ta faÉ—a
Abeeha tace
"Amma kam za ki sakata kuka a banza Adda Jannah... Allah ka yafe mana baiwar Allah Zarah"
"Eh gwara tayi kukan ta nemi mafita wa zuciyarta, ita kuma zarah dama kar tayi tunanin samun
matsuguni a ran Ya Rayyan don shi ba namijin da zai iya da soyayya bane muddin Afeefah ta
mishi dabaibayi a zuciya"
Hirarsu suka cigaba da yi cikin nishadi don sun tabbatar ko Afeefah bata nemi Rayyan ba shi a
yanzu ba zai jure nisantarta ba.
Ɗakinta ta koma ta zauna bakin gado babu abin da bata saƙa ba kuma ta hana kanta kuka,
dole ta yi me É—ungurungun wai haihuwa da hanji! Dole taje ta ji shin yana sonta ko da gaske
baya sonta wata zai aura...
Kiran Sallar Magrib ya sa ta miƙe ta gabatar da sallah don ta yi wanka tun rana, kitchen ta nufa
ta haÉ—a mishi macroni da gasashen chicken breast tana cikin yi aka kira isha taje ta gabatar kan
ta dawo ta ƙarasa taje ta shirya mishi a dining a yanzu hijab ne jikinta har ƙasa, daidai yana
shigowa take cewa Sa'ade
"Ki tattare kitchen nan please ban yi shafa'i da wutiri ba bari na gabatar"
Bata ma kula da Shigowar tashi ba don ciki ciki yayi sallama ta wuce É—akinta ya bi bayanta da
kallo hannayenshi zube cikin aljihu, a natse ya ƙarasa dining ɗin daidai Fitowar Abeeha da
Jannah suka mishi sannu suma suka zauna suka shiga cin abincin, ganin ta jima ya sa ya dubi
Abeeha
"ƙira min Afeefah"
Ta miƙe ta nufi ɗakin ta samu ta idar tana zaune ne kawai, jin yana kiranta ta miƙe ta nufi
parlorn zuwa dining.
"Zauna ki ci abinci"
Ganin fuskarshi ba fara'a yasa ta zauna ta zuba abincin kaÉ—an tana ci kaman bata so, karamin
kwalin da bai jiman nan ba GaabÉ—o ya zo ya ajiye mishi ya tura mata.
"Na gode"
Ta faÉ—a tana jan paper bag É—in ta buÉ—e ciki sai ta ga waya ne dall a cikin kwali Iphone 17 Air ce,
bata nuna zumudi ko farin ciki sossai ba sai ma su Abeeha ne ke ta santin wayan ta sake ce
mishi ta gode ya bi fuskarta da kallo.
Bayan sun bar dining É—in su sa'ade suka zo suka tattare wurin tsaff.
ÆŠakinta ta koma ta bar su Abeeha da wayan a parlor suna mata setting ta yi wanka, ta duba
wani orange and Black nigty silk ne mai hannun shimi ya bi jikinta sossai don Black lace É—in ya
kara haske kayan, hijabi ta saka a kai ganin yadda ko motsi tayi komai na jikinta na motsawa
cikin kayan musamman hammatan dake bayyana tudun na shanunta time ta kallah almost nine.
Fitowa tayi Abeeha ta bata wayan don jannah ta gudu waya da mijinta a É—aki, É—akinshi ta nufa
kai tsaye da sallama ta kutsa kai rike da wayan a hannunta don tana so su yi magana.
A tsaye take bisa kanshi yana kishingide cikin tattausan Italian cushion a hankali yake É—an
taune lip É—in shi kaifaffun idanunshi zube bisa kanta
"am...am just fed up, ba na tunanin zan iya cigaba da zama a haka i've had enough na san ba
ka aureni ba ne saboda kana so na, ka aure ni ne out of pity da kuma am... Mammi. Muddin na
cigaba da zama a haka zan iya mutuwa a yanzu bana jin zan iya cigaba da kasancewa
matsayin ma..matar k..."
"It's pretty!"
Ya furta chan ƙasa cikin deep voice ɗin shi da ya sa ta kame, duk maganar da take yi ba
idanunta yake kallo ba lips ɗinta da take motsa su a hankali ya ƙurawa lumsassun idanunshi
yana wani kashe su yana buÉ—ewa...
"W...whatt?"
"Ur lips... They are pretty"
Ko kan ta farga ya yunkura ya fusgo hannunta guda ta tafi gabaÉ—aya kanshi tayi masauki a kan
kafafunshi fuskarta ya sauƙa kan wuyanshi a tare suka ɗauke numfashi. A ɗan razane ta shiga
mutsu-mutsun sauƙa ya sa hannunshi na hagun ya zagaye kwankwansonta yayi pinning ɗinta
jikinshi, na daman ya sanya ya zare mata hijabin idanunshi na sauka kan jikinta, ya bi damtsen
hannunta da yatsa biyu cikin wani salo har cikin tafin hannunta kar yayi baya ya riƙe wrist ɗin
hannun ya ɗora saman heart ɗin shi da ke beating very very fast. A take nata ma ke ƙoƙarin
sauya bugu numfashi na neman kwace mata idanunshi a saman fuskarta kaman zai tsagata da
su ya furta
"saƙon zuciya baki ne yake furta wa sai dai kuma wani lokacin yana iya fin ƙarfin harshe ya bar
wa idanu nunawa, Lil angel saurari bugun zuciyata ki kalli tsakiyar kwayar idanuna na tabbatar
sun isa sanar miki da cewa Ryan na ƙaunarki ba zai iya rayuwa babu ke ba, kuma yana
tsananin buƙatar ki, you are like a Light in my darkness. You are not just my wife Afeefah you
are my safe space, my solace...you are the key to my salvation..."
Wani irin birkicewa ta nemi yi saboda nauyin zantukan nashi ga idanunshi masu kaifi da yake
zagaye fuskanta da su yana wani lumshe su, maganar ma har cikin ɓargonta take ji saboda
yadda muryarshi ke fita very deep nd husky.
"A haka kike cewa in rabu da ke? Uhmm? Ki fahimta rashin ki a gareni masifa ne Afeefah"
Ƙuri tayi da idanu kalamanshi suna samu matsuguni daram a cikin zuciyarta, sakinta yayi ta
koma zaune kawai akan kafar tashi, kanta ta mayar ƙasa tana neman dulmiyewa tsabar yadda
kalaman suke zuwa mata a bazata Rayyan ne fa gabanta shine yake fitar da waennan
tsadaddun kalmomin daga cikin bakinshi?
Anya ta ji da kyau? Ko dai yaudararta yake shirin yi ganin irin kallon da yake mata ba tare da ya
sake furta uffan ba, shi ne zai so mace kamarta? Sake É—ago kai tayi ta kalleshi suka hada
idanu. Sarai ya san kokonto take akan kalamanshi kuma hakan bai mishi daaÉ—i ba, ya kai
hannunshi ya kama haɓarta ya ɗago fuskarta yana kallon cikin idanunta cikin karantar yanayinta
bai furta komai ba.
Idanunta ta mayar kasa zuciyarta na bugawa da tsananin karfi har tana jin kaman cikin ko wani
lokaci zuciyarta zai iya yin bindiga ta mutu, amma shi ko a jikinshi kuma fuskar a kame yake
magana idanunshi na yawo bisa jikinta ya
ce
"Idan kuma kin matsa da sai na rabu da ke, zan iya yin hakan ne kawai under 2 conditions
Afeefah sai ki zabi wanda kike gani ya fi miki sauki ni kuma i promise zan rabu da ke!"
A razane ta dago ta zuba mishi idanunta da har sun fara zubar da kwallah lips dinta dake rawa
ya bi da kallo kan ya dauke idanu yana lumshe wa ya bude
Da ma na sani baya so na tunda gashi zai iya rabuwa da ni amma me yasa nake jin zafi?
Meyasa nake jin kaman karshen rayuwata ne ya zo? Abinda take ayyanawa kenan a ranta..
Da kyar ta iya furta
"Menene conditions din?"
Tana ji gwara ta sani gwara ta hakura ta nemi daidai ita.
"It's either ki mayar da lokaci baya ki goge ranar da na fara sanin ki a rayuwarta don daga ranar
ne zuciyata ta fara bugawa da Ƙaunarki ko kuma ki tsaga zuciyata ki sauya min da wata zuciyar
don wannan ta jima tana sakar da jini mai dauke da kaunarki zuwa ko wani sashe na jiki da
jijiyoyina...."
Baki kawai ta saki hawayenta na zuba sossai da sossai, ya kai hannu ya janyota suka samu
kusanci ainun, ya É—ago babbar yatsarshi ya shafa soft lips É—inta dake ta rawa idanunshi na cikin
nata yayi leaning a hankali ya ɗora bakinshi kan nata zuciyoyinsu na amsa baƙon yanayin nasu
da karfin gaske.......
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*Babu lallai ku ji ni da daddare manage this please, and na ga ruwan comments da Adu'o'i na
gode kwarai Allah duk ya faranta mana ya hada mu da masu kaunar mu saboda Allah*
*51*
A hankali ya raba bakin nashi da nata, ya zuba mata idanunshi da suka matukar sauya ko da ta
buɗe idanu sai suka sarke cikin nashin, ya riƙe natan sama da mintuna da suka fi biyu kan ya
saukar da kanshi wuyanta yana goga mata gemunshi zuwa karan hancinshi a gefen kunnenta
cikin wani irin salo da bata san ta mayar da hannayenta biyu bayanshi ta yi grabbing wuyanshi
ba tana sauƙe numfashi.
A hankali yake haurawa numfashinshi na sauka da zafi yana ƙarasa hautsina mata natsuwarta
har ya isa cikin kunnenta cike da wani shauƙi mai dauke da mayen son da ba za ta iya resisting
ba ya shiga whispering into her ears
"Afeefahhh ke ce ta farko a zuciyata, ke kika buÉ—e shafin farko a soyayyata, a kanki jikina da
zuciyata suka fara gamsuwa da cewa ni din namiji ne cikakke kuma ina buƙatar Abokiyar
halitatta, ki amince min mu zama daya, ki yarda na baki ragamar rayuwata! dama É—aya tak nake
so ki ba ni...ni kuma zan killaceki a cikin zuciyata tsawon rayuwata, zan zama bawa a gareki
mai hidimarki tsawon rayuwarmu zan tabbatar wa da duniya ke ce farin ciki na kuma hasken
zuciyata..ina fata ba za ki hanani raɓa daga ni'imarki ba?"
Hawaye ne ke zuba mata na rashin Makama, yanayin ya mata zafi kalaman sun mata tsauri
ainun ta yadda take jin kaman tana duniyar halwa ne na soyayya ba duniyar mutane ba, bata
san ta gyaÉ—a mishi kai ba yayi murmushi mai nauyi wanda sautinshi ya fita kaman numfashi,
bata ankara ba taji ya tashi da ita a hannunshi ya isa ya mayar da hasken É—akin dimmm sossai
kan ya nufi gadon ya shimfiÉ—eta za ta yunkura ya bi bayanta his hands started to move inch by
inch na jikinta, yana squezing É—inta gently bakinshi is slowly kissing her and driving her nuts
especially wuyanta da ya fi ko ina motsa shi, da baki yayi amfani ya saukar da sleeve na riganta
cikin salon da bata taɓa sanin akwai shi ba, heavy breathes ɗin shi na sake birkitata.
cikin natsuwa yake komai, Sai da ya tabbatar tayi laushi shima ya fara rasa kanshi a duniyarta
kan ya nufi yin mai gabaɗaya, a sannan ne ya birkice ya gigice tunaninshi ya ɓace, jinshi yayi
nisa bashi da buri a lokacin illa na ganin sun zama daya ta zama shi shima kuma ya zama ita,
ko da ya ji shi a duniyarta ƙarasa haukace wa yayi a sannan ne ita kuma ido ya raina fata ta
fahimci that pleasure da irin tarin iya sarrafa mace da yake dashi ne ya ruÉ—e ta har ta zaci abin
mai sauki ne, duk irin magiya da roƙon da take mishi haɗe da kuka duk baya ji, idan hannunta
ya sauka jikinshi ma sai yaji kaman zaburarwa ne cikin salonta.
Bai sarara mata ba bai kuma saurara ba don yayi haukacewar da ko sunanshi ka tambaya a
lokacin ba zai iya tunawa ba ita kaÉ—ai ya sani, ita kaÉ—ai kuma yake gani...Tsammmmm haka ya
rukunkumeta yana binne kanshi a wuyanta a sadda ya samu cikakken natsuwa, Dukda irin halin
da take ciki na fitar hayyaci da raɗaɗin azabar da bata taɓa fuskantar irinshi ba a rayuwarta
tana iya jin É—umin hawayenshi dake bin wuyanta, chan kaman daga wani uwa duniya take jin
shaƙaƙiyar muryarshi na furta
"Allah ya gafarta miki Mammi, Allah ya yafe miki kurakuranki Allah ubangiji ya sadaki da
rahamarsa Allah ya jiyar da ke daaÉ—in aljannah fiye da yadda kika yi sanadiyar jin wannan daaÉ—i
nawa na duniya....Thank you! Thank you Mammi"
Sossai yake hawaye har numfashinshi na seizing ya mata riƙon da kaman ya tsaga jikinshi ya
chusata yake ji ko zai samu saukin abinda ke shirin zauta shi, bai iya ya motsa ba kaman yadda
itama bata da kuzarin É—aga ko da yatsar ta ne, yana so ya É—aga ta ya ji lafiyarta yana so ya
gwada buÉ—e baki ko zai iya furta mata tarin irin kaunar da yake mata sai dai ya kasa, ya kasa
sarrafa kanshi bare ya sarrafa jikinshi abu daya ya sani ta gigitashi a duniyarta ta goge mishi
haddar da baya tunanin har abada akwai wacce ta isa ta kaishi inda ta kaishi, ta kashe mishi
duk wani laka na jiki kaman ba tsayayye kuma jarumin sojan nan ba, ƙasusuwanshi sun yi
laushin da ya kasa ko da lankwasa su bare ya sarrafa su har su miƙe a dole ya sake binne ta ya
ja bargo ya rufa musu a haka wani irin bacci ya É—auke shi ba tare da ya san halin da take ciki
ba.
Sautin kuka da turirin zafin dake fita daga jikinta zuwa nashi ne yayi sanadiyar farkawarshi,
gaining courage yayi ya yunkura da ita a jikin nashi har lokacin banda bargon nan babu komai
jikinsu duk su biyu, juyata yayi ta koma kwance yayi pecking goshinta a hankali ya fara ambaton
sunanta
"Afeefah... Bebe!"
Bata amsa ba sai kananun kukan da take na zazzafar zazzabi idanunta a rufe kirib
"Am so sorry...am sorry"
Ya faÉ—a yana sake pecking goshinta kan ya sauka ya nemi wandonshi na bacci ya saka ya nufi
toilet shi karan kanshi kafafunshi rawa suke kanshi ya mishi nauyi ainun, gefen cikinshi ya riƙe
mishi sossai amma sanin dalili tunda shi likita ne bai wani damu ba ya haÉ—a mata ruwa mai zafi,
ya dawo gadon ya É—auketa kaman 'yar baby.
"Matar Saraki..! Afeefah... Kina ji na? Zan saka ki a ruwa compose yourself kar ki ji zafin a
bazata! Am so sorry Ya Saraki bai kyauta ba, Yafam boÉ—É—i am"(ki gafarceni kyakyawata)
Da wani irin sloww tune yake maganan a kunnenta kan ya saukar da ita a hankali cikin ruwan,
wani irin ƙara ta saki tana rirrikeshi za ta tashi ya shiga ciki ya danneta kawai ta kife kanta
kirjinshi tana girgiza wa cikin azaba da kuka mai ratsa zuciya, hautsinannen gashinta da ya
gama wargaza wa yake shafawa zuwa bayanta yana hura mata iska a kunnen yana whispering
"sorry, am so Sorry My love."
Sai da suka yi ruwa uku a tare tana liƙe bisa kirjinshi idanunta a rufe rufff kan ya sakata tayi
niyya suka yi wankan tsarki, a towel fari ƙal yayi wrapping ɗinta ya sake ɗaukar ta zuwa kan
cushion ya ajiye ta, har lokacin bata buÉ—e ido ba kuma bata bar kananun kuka ba shi kuma bai
bar lallashi da ban haƙuri ba, gadon yaje ya chanza musu bedsheets.
A gabanta ya tsuguna bayan ya É—auko magani, bata ma san ya zo ba don har bacci ya fara
fusgarta na wahala kawai taji hannunshi cikin towel É—in ya shafa cikinta ta É—an zabura sbd har
lokacin hannunshi da sanyi ta buÉ—e ido sai suka haÉ—a ido tayi saurin rufewa yayi murmushi
"Tashi ki sha magani 'yar albarka..!"
Bata motsa ba shi ya É—ago ta zata fara kananun kuka ya sanyata jikinshi ya shiga bata tea din
da ya saisaita zafin ta sha sossai kan ta sha maganin, a maimakon tayi shiru ma sai ta sake
fara wani kukan.
"Am sorry My love, har yanzu baki ji sassauci ba?"
Ta gyaÉ—a kai tana hawaye don ita kaÉ—ai ta san me take ji, shima kuma ya san jarumar mace
yake tare da ita tayi matukar ƙoƙari, a hannu ya dauƙeta bai damu da su sa wani kaya ba suka
koma kan gadon ya shimfiÉ—eta bisa kirjinshi
"Sannu Chéri am(My darling) in duba in gani ko kina buƙatar stiches?"
Ta maƙe kafada za ta fara kuka yayi murmushi mai sauti kan ya shiga shafa wet gashinta da
yayi mishi laushin taɓawa saboda bai bushe ba, a kunnenta yayi whispering
"Afeefahh kin san Bugawar zuciya alama ce ta mutum na raye ko? Toh kece bugun Zuciyata
wanda hakan ke nufin idan babu ke a zuciyata babu ni zan iya amsa kowace irin tambaya a
game dake saidai tambaya daya da ba zan iya amsawa ba ita ce wane irin so na ke miki,
wannan tambaya ba zan iya amsata ba domin ni kaina ban san wane irin so nake miki ba abin
da kaÉ—ai na sani game da yadda nake jinki cikin jinina shine ba zan iya cigaba da rayuwa ba
idan har ba'a tare dake ba. Afeefahhh idan har rayuwa ba za ta yiwu babu iska ba haka nima ba
zan iya zama mai rai ba tare da ke ba, ke ce rayuwata Gimbiyata"
Duk giyar soyayyarta ya saka yana jin kome ya faÉ—a mata yayi kadan wurin bayyana abin da
yake ji, kuka take ba na bakin ciki ko ciwo ba kukan farin ciki take, tana kukan alfahari tana
kukan isar ta macen da aka iya macewa a cikin begenta, tana kukan mallakar wannan gwarzo
namijin da bakinshi bai yi nauyi ba wurin shimfide mata sirrukan zuciyarshi, rungumeta ya sake
yi tsamm yana shafata cikin bege
"Allah ubangiji ya kula min da dukkan lamuranki na rayuwa, yadda kika shayar da ni garÉ—i da
zaƙin zumanki ubangiji ya shayar da ke ruwan alkausara... Thank you so much Habeebty a
yanzu you are not just the part of my life you are the owner of my heart, ki yi bacci Habeebty kiyi
bacci cikin salama"
Da wannan kalamai haÉ—e da tarin lallashinshi mai tsadar gaske bacci ya É—auketa. Ya jima
sossai kawai yana kwance in ta motsa sai ya sake shigar da ita jikinshi kaman za'a raba su ne
ya yi pecking tsakiyar kanta, sun so su makara don ƙarshen ta a gida ya ja su sallah bayan ya
kaita tayi alwala, wani baƙin Oman jallabiyarshi mai adon gold ya saka mata sossai ya mata
tsawo ya É—auko mata hijab É—inta ya saka mata shima ya saka jallabiya ya ja su sallah, suna
idarwa ya janyota ta kwanta a kan kafafunshi ya zare hijabin yana shafa gashinta yake musu
azkar duk su biyun don da kyar tayi Sallar saboda bacci da zazzabin da bai gama sake ta ba,
tuni ta yi baccinta peacefully har ya gama ya dauƙeta ya mayar da ita gadon yana kallon pale
fuskarta.
Idanu ya lumshe yana sauke numfashi, a duk sadda zai ganta wani sabon ƙauna da mararinta
yake ji yana kwarara cikin zuciyarshi, hannunta ya riƙo yayi pecking ya sake yi mata peck a
Goshi kan ya miƙe ya fito, hadiman da suke share share da goge goge suka zube ƙasa suna
kwasar gaisuwa, ya É—an shafa kanshi ya ce
"Ammm yau gabaÉ—aya na baku hutu, ina so ku koma sashenku kuyi duk abinda kuke so sai
dare ku dawo"
"Godiya muke Yariman Matasa! Godiya muke Ciroman fombina Allah ya kara girma da arziki
Allah ya biya buƙatu"
Kai kawai ya gyaɗa suka miƙe suka fice shi kuma ya nufi kitchen.
Abeeha da zata fito kenan ta ji yana koran hadimai ta koma ta buga jannah da ke shirin
komawa bacci
"Wallahi barin sashen nan ya kama mu Addah jannah... Me afkuwa ta afku ga Ya Rayyan chan
kitchen zai dorawa gimbiyarshi breakfast "
Da sauri jannah ta miƙe zaune cike da zumuɗi tace
"Keeee Ya Rayyan É—in?"
"Shi fa wallahi, hmmm ai na san jiyan nan ba lallai a wanye ƙalau ba, bawan Allah Saraki a waje
Hadimin Afeefah a gida"
Suka kwashe da dariya jannah na cewa
"Kin ga irin su Yayan nan hmmm ki bar su kawai... Maza shirya bari nima na shirya mu koma
sashen Ammi for today mu bar su su ƙone in sun ga dama"
Abeeha na dariya ta shiga toilet wanka ji take zuciyarta kal kal, basu fi mintuna talatin ba suka
bar sashen abin su.
Shi kam bai ma sani ba yana kitchen, plantain yake frying amma minti minti zai saki murmushi
yana tuna moments É—insu na jiya, ji yake ma yana kewanta a jikinshi daga Fitowar shi É—akin
zuwa yanzu, sai da ya gama ya haÉ—a mata spicy egg sauce mai É—an yawa, ya yi toasting bread
with butter very soft and simple kan ya shirya plate É—in with so much love don burin shi kawai ya
ga tana murmushi burin shi ya ga ta ji daaÉ—i kuma tayi alfahari, clean tray mai kyau garai-garai
ya samu ya ajiye plate É—in ya hada da tissue ko za ta bukata wrapped with cutlaries.
Dube dube ya fara har ya samu wani drawer mai dauke da notepads masu yawa da Pen sbd
specifying objects, rubutu yayi a jiki ya manna a gefen tray É—in ya hada tea mai kauri sossai ya
ajiye kan ya É—auka ya nufi É—akin.
A gefen bedside ya ajiye ya yaye mata duvet É—in har lokacin riganshi ne jikinta, ganin tana
baccinta peacefully ya shafa fuskarta motsi ta fara a hankali har dai ta buÉ—e idanunta da suke
kumbure ta sauke bisa kanshi ya sakar mata kyakyawar murmushi
"Good Morning My Queen, My greatest blessing and the reason i believe in love..."
Duk yadda bata so murmusawa ba sai da yayi escaping ta tsinci zuciyarta da dumbin farin ciki
wane takarda.
Miƙewa tayi zaune tana sauƙe kanta ƙasa haɗe da fara wasa da hannunta tace
"Good Morning"
Bai matsa mata ba ya san kunya ke É—awainiya da ita shi ko a jikinshi ya É—auko tray É—in ya ajiye
mata a kan cinya zai yi magana wayanshi ya shiga ƙira ganin mai martaba ne da kanshi ya sa
yayi picking yana fita daga É—akin don dole zuwa parlor.
Note É—in da yayi rubutun ta É—auka ta shiga karantawa.
"Na shirya miki wannan karin kumallon ne da tarin soyayya, kina da muhimmanci sossai a
rayuwar Ryan. Allah ya albarkaceki da farin ciki da lafiya kullum, Ina ƙaunar ki!"
Zuciyarta ta sa hannu ta dafe, kaunar ya mata yawa ji take ta ma rasa me zata yi sai sake
karantawa take tana murmushi. Adanawa tayi ta dauki fork ta fara cin abincin da ya shirya mata
da hannayenshi, loma biyu tayi sai gashi ya dawo yana zama gefen ta
"Afuwan mai martaba ne ya kira ni ko yau zan samu fita ran gadi da shi"
Kai ta gyaÉ—a tana sakar mishi cokalin bata ce komai ba don ya riga ya sanya hannu cikin nata
ya karɓa ya cigaba da bata cike da kulawa yace
"Kin san me na ce mishi?"
Kai ta girgiza
"Ce mishi nayi yau yini na, magana na da duk wata kulawa tawa naki ne ke kaÉ—ai saboda kin
bani abu mafi daraja a rayuwarki..."
Da sauri ta kalleshi tana zaro idanunta waje gabaÉ—aya ya saki murmushi mai kyau har
hakwaranshi na bayyana tace kaman za ta saki kuka
"Da gaske haka ka faÉ—a mishi?"
Hancinta ya lakace
"Gashi na saka ki kallona da waennan idanun da suke kashe ni, kuma na ji wannan murya taki
mai kaman sarewa..."
Bata san tayi murmushi ba shima ya cigaba da yi har ya gama bata.
"Mu je in miki wanka..!"
Ta zaro ido
"Zan iya wlh"
Tayi saurin faɗa a Shagwaɓe ya kalleta
"Ya daina zafi? Kin tabbatar za ki iya tafiya?"
Kai ta gyaɗa ya dage tray ɗin ta sauƙo tana Miƙewa tsaye ta riƙo shi jin tana shirin faɗuwa wani
Sharp pain na shigarta, ya ajiye tray ɗin yana saɓarta
Duk rigima da Shagwaɓar da tayi ta mishi dole suka yi wankan ta lura ita ce ke mutuwa da
kunya shi ko a gyalen shi tattalin ta yake wane ƙwai, shi ya dubo mata wani kaya ta saka Dukda
ma ba masu nauyi ba a parlor ya ajiye ta ya kunna mata Tv wai tayi kallo bari ya zo, har ya tafi
ya koma yaje ya É—auko mata popcorn ya zo ya bata yayi pecking goshinta kan ya koma É—akin
nashi ta bi bayanshi da kallon ƙauna tana murmushi cike da tarin farin ciki....
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*52*
https://chat.whatsapp.com/HUJI7tg9TOU941grP60r4S?mode=ems_copy_c
Kinaneman group din dazaki ringa sarinkayan kitchen cikin farashin sari...tayadda koda kinje
kasuwa bazakisamu kasa d farashinmuba snn zaki iyazuwa har hargida kisayi dukkan kayan
dakike bukata cikin kwanciyar hankali kokisaya ayimaki delivery zuwa dukkan inda kike afadin
Nigeria da dama makotan kasashenmu kikarbi kayanki cikin farinciki da aminci!!!.....kiyi joining a
mai nono kitchen utensils and household........gaskiya d amana sune takenmu!!!ðŸ‘ðŸ»
*****
Ga mamakinta bai fita É—in ba ya tabbatar mata da gaske yake ya cewa Abeey bata da lafiya ba
zai iya yin nesa da ita ba, kunya ya rufe ta amma shi ko a gyalen shi da kanshi ya gyare É—akin
tsaff ya wanke beddings da suka ɓata kan ya dawo yayi joining ɗinta a parlor hannunshi da mug
yana sipping tea, da kanta ta kai kwance jikinshi ya mayar da hannunshi É—aya bayanta ya
rungumeta suna kallon a tare hasken parlorn a kashe Dukda hantsi ce amma yadda curtains
suke rufe kirib rip hasken duk a kashe sai ya ba da wani yanayi kaman cinema.
Film din ya ƙare amma bata sani ba saboda ta yi nisa cikin tunani, hawaye kuma na bin fuskarta
har take ji kaman zazzabinta zai dawo sabo, kula da hakan da yayi ya É—aga mishi hankali ya
É—ago fuskarta yana kallon ruwan hawayen da take yi
"Afeefah lafiya? Me yasa kike kuka haka?"
Yana maganan ne yana É—auke hawayen da palms É—in shi wasu na gangarowa, a hankali tace
"Twins na cikin film din nan sun tuna min da Suhail da Suhaila ne, ko ya suke? Na san yanzu
sun girma, ko suna maraicin uwa kaman yadda nayi? Ko suna samun farin ciki duk ban sani
ba..."
Fuskarta ya saka cikin tafukan hannunshi guda biyu ya matso sossai har suna shakar
numfashin juna chan ƙasa cikin Muryar rarrashi yace
"Ba kin rabu da su ba kenan har Abada Bebe..! Za mu koma in shaa Allahu za mu je mu gansu
a tare ki daina zubar da hawayen nan, they are priceless to me..."
Yana kai nan yayi leaning tare da fara É—auke hawayen da harshen shi cikin wani salo da ya sa
ta sake ƙanƙameshi, daga nan ya sauƙar da lips dinshi a kan nata da baya gajiya da su, sai da
ta ga yana ƙoƙarin ɗaukar wani hanyar ta zame tare da kwanciya kan jikinshi ya rungumeta
suna sauƙe numfashi a tare.
"I love you...!"
Ya raÉ—a mata a kunne, ta É—an yi murmushi bata ce komai ba.
"Na jima ina son na baki haƙuri kan wani laifi da na miki"
Ta É—an É—ago kanta tana kan jikinshin
"Me kayi min Ya Saraki?"
Ya kai hannunshi É—aya yana wasa da gashinta da ya ki yarda ta saka hula idanunshi na a kan
fuskarta yace
"Ranar da kika fara gani na i scared you alot da har na kan yi sensing tsoron ki a duk sadda
kika ganni ko kika ji muryata, that time i was very upset sai nake ganin kaman idan da akwai
wanda ya fi cancanta da kashe kanshi ni ne but why you? Ƴar karama dake da wannan ɗanyen
hukuncin? Raina ya ɓaci da na yi kwanaki da takaicin da ban san na menene ba, i wanted to go
back to the hospital ko in kira Saleem amma na danne kawai ban yi hakan ba, daga baya i saw
you at saleem's place da yake ba ni labari i was shocked sai dai sanar da ni da yayi yana sonki
ya sa na miki murna a lokacin bcs na san shi mutumin kirki ne ƙwarai sai kuma matsalar
mommy ya yi striking"
Ta É—an yi murmushi har lokacin tana kallon fuskanshi yadda yake magana da ma yadda yake
wasa da gashinta na kara dulmiyar da ita a kaunarshi tace
"Dukda na ji tsoro sossai da reaction É—inka to tell the truth shine yayi sanadiyar gane kuskurena,
reaction É—inka ya fahimtar da ni ba karamin kuskure nayi ba a yunkurin kashe kaina da nayi... A
lokacin bani da yadda zan yi Afeefah Mayya ce kuma annoba ce ba Afeefar yanzu ba"
Yayi murmushi da yayi mishi kyau sossai
"Har yanzu ma ai ke mayyar ce!"
Ido ta zaro, ya kai hannu ya lalace mata hanci
"Eh mana! Gashi kin lashe min zuciya"
Bata san ta saki murmushi mai sauti ba tana É—an hararanshi yayi pecking idanun yana sake
rungumeta.
"Ka san kuma da gaske na riƙe ka? Har ma sunanka marar kirki a zuciyata.."
Ya É—ago ta ta zauna yana kallon fuskarta
"Seriously??"
Ta gyaÉ—a kai
"Na fahimceka ne a sadda Mammi ta sanar da ni wanene kai!"
Shiru yayi, ta sa hannunta ta riƙe nashi biyu
"I hope yadda komai ya wuce a tawa rayuwar kaima za ka bar komai ya zama tarihi Ya Saraki!"
Shiru yayi bai ce komai ba, ta san halin kayanta bata so tayi zurfi a maganan ranshi ya ɓaci
amma ta fahimci yar tsamar da yake yi da mahaifiyarshi kuma rayuwa ba zai taɓa tafiya a haka
ba, dole ne zai bar komai ya wuce kaman ba'a yi ba ta sani ba at once zai chanza ba amma a
hankali dole zai wuce É—in...
Baya baya tayi ta jingina bayanta da jikin hannun kujerar bayan ta saka pillow sai ta wara mishi
hannu, a hankali ya kai kwance kanshi na sauka a kan kirjinta ta saka hannayenta biyu tana
shafa kanshi zuwa bayan wuyanshi shi kuwa ya lumshe ido yana ji kaman ya É—auketa su koma
É—aki don kunna shi take ba tare da ta sani ba.
Sun jima sossai a haka kan ya ce
"Kin san mene?"
Ta ce
"uhm uhm"
Tana cigaba da wasa da gashin keyarshi
"I love hugging you, a duk sadda kika rungumeni sai na ji kaman mu dawwama a haka a tare, I
just wanna lay here on your chest forever"
Sake rungumeshi tayi tana jin kalamanshi masu tsada na sake samun matsuguni a ranta, ita
kanta tana mamakin kanta amma an ce komai wuri yake samu a yanzu da yake nuna mata so
da kauna sai taji she can go any extent don ganin ta faranta mishi itama, tsoron da take mishi
ya kau sai taga kaman ba shine ke bata tsoron nan ba, kaman ba shine take shakkar ko tari a
gangarshi ba.
Suna parlorn har azahar ya fice masallaci ita kuma taje É—aki tayi Sallarta, bata so ya dawo yace
zai yi girki don haka ta wuce kitchen kawai daga É—akin bata cire hijabinta ba don rigar jikinta
wani iri yake sakata ji bashi da maraba da babu, har lokacin ba wai ta dawo daidai bane amma
tana ga responsibilty É—inta ne samar masa abinda zai ci.
Mai ta ɗora a wuta ta kawo ƙoda da ta yanka 'yan daidai ta zuba, suna cikin soyuwa ta fara
yanka sausage suma bayan ta kwashe kodar da ya soyu ta zuba sausage É—in shima sai da yayi
ta kwashe ta zuba shrimps da ta wanke tsaf ta soya su ta kwashe, ta kawo tomato patse ta
zuba cikin man ta fara soyawa a gefe tana markada kayan miya da suke a frigde a gyare
already sai da tomato din ya fara zaƙi kan ta juye kayan miyan a kai ta fara seasoning da su
curry, chicken seasoning da dai duk abinda zata buƙata kan ta kawo soye soyenta na ɗazu ta
zuba cikin sauce É—in ta juya tare da rufewa ta nufi basmati Rice dake kitchen É—in kofi biyu ta
diba ta tafi bakin sink tana cikin zuba ruwa don wanke shinkafar ya shigo.
"Kin yi laifi!"
Ya faÉ—a yana nufarta, ta kalleshi ta saki murmushi
"Tuba nake Ciroman duk duniya!"
Hijabin ya zare mata ya koma ta bayanta yayi hugging É—inta hannunshi É—aya na zagaye
kwankwasonta
"Meyasa kike girki a yau? Ba ki san na haramta ba?"
"Ba wani abu mai wuya bane kuma bashi da yawa, gashi na kusa gamawa!"
Wuyanta yake shunshunawa
"Shi wannan turaren kam kaman a fatarki aka haÉ—a so sweet"
Ganin ya fara bata kisses a wurin ya sa ta É—auki shinkafar da ta gama wankewa
"Ya Saraki abincina zai ƙone"
Bai saketa ba haka suka koma bakin gas din ta juye shinkafar ciki ya lumshe ido yana shakar
kamshin
"Hannunki daban ne a girki do you know that?"
Tana zuba tafasashen ruwa madaidaici ciki tace
"Lokacin da nake yi wa su Inna Larai Talla mutanen kasuwa kan faÉ—i hakan amma wannan
training É—in dai na abincin birni na same shi ne ta sanadiyar Mammi Allah ya gafarta mata"
Ya ce
"Ameen"
Fuskarshi na nuna rashin jin daaɗin halin da ta taɓa tsintar kanta a baya, suna kitchen ɗin har
ruwan shinkafar ya É—an tsotse ta juya kan ta rufe da foil ta rage wuta ya kara 15mins ta juyo
musu a plate ta ɗora kan tray shi ya Karɓa suka koma parlor, shi ya ɗauki spoon ɗin ya shiga
bata yana ba kanshi, a lomar farko ya lumshe ido ya buÉ—e yana taunawa
"Wow My love shi kuma wannan menene sunanshi?"
Tayi murmushin farin cikin ganin yana yabon abinda ta dafa tace
"Supreme Rice sunanshi"
"I love it, Allah yayi miki albarka"
Ta amsa da Ameen suka ci gaba da ci har suka gama ya bata ruwa ta sha kan ya tattare
kwanukan za ta karɓa ya ture hannunta.
"Ya Saraki..."
Ya ma yi gaba bai saurare ta ba ta miƙe ta bishi
"Kar fa a kama ni dumu-dumu da laifin saka Saraki aiki"
Ya ajiye kwanukan yana É—aukatarta gabadayanta
"Girmanki ne hakan, ina so har abada in zama mai hidimta miki har sai na kasance ni ne
ma'anar farin ciki a rayuwarki"
She's just blushing daga jiya zuwa yau bata san matakin da zata É—ora farin cikin dake ratsa
zuciyarta ba hakika tayi dace kwarai da masoyi, kai tsaye kan gadonshi ya shimfiÉ—eta ya zare
rigan shi ya kwanta tare da janyota jikinshi sai ta fara zare idon tsoro.
Fahimtar hakan don har a jikinta ya ji hakan ya sa yayi murmushi yana shafa kumatunta dake
kan kirjinshi yace
"Bacci za mu yi Gimbiya just stay calm okey ai na san baki warke ba, ko kin warke?"
Kukan Shagwaɓa ta fara ya saki murmushi mai sauti yana shafa bayanta a haka suka yi baccin
kuwa, basu tashi ba sai la'asar yanzu ma da kanshi ya mata wanka duk yadda take dojewa ya
ƙi barin ta, gudu wa tayi ta barshi a bayin don ta kasa natsuwa yayi tashi wankan gabanta sai
take jin kunyar duniya na rufeta.
ÆŠakinta taje ta shirya cikin wata atampha doguwar riga dinkin ya zauna mata tsaff ya fitar da
duk wani sura na jikinta tayi wanka da turare isashe a ranta tana mamakin shine ya kori har su
Adda Abeeha ko su ne suka yi tafiyar su yini guda basa nan, tana kokarin fitowa parlorn taji
sallamar Gaabɗo sai ta koma don yanzu ranshi zai iya ɓaci.
Shi kuwa ya fito ma ganin GaabÉ—o ya sa ya samu wuri ya zauna sai ya koma Sarakinshi ya
É—ora kafa É—aya kan É—aya yana relaxing ba tare da ya kalli GaabÉ—on ba yace
"Menene?"
"Allah ya baka yawan rai kana da baƙo ne babba, na sanar dashi ka ce baka son ganin kowa
yau amma ya dai tabbatar min lallai lallai in ce yana son ganinka"
"Waye?"
Ya tambaya yana kallon GaabÉ—on don bai san wani isashen bane zai ce lallai lallai sai ya
ganshi bayan ya ce baya bukatar ganin kowa a yau.
"Allah ya baka yawan rai ranka ya daÉ—e Ameer ne na gidan Galadima"
Da sauri ya É—ago
"Ameer?"
Kai ya gyaÉ—a cikin tabbaci
"Kwarai da gaske ranka ya dade."
*****
"Fulani kin yi shiru baki ce komai ba, tun da abin nan ya faru muke ta so mu zauna amma baki
ba mu dama ba yau kuma kin kira mu kin yi shiru...! Kar fa mu tsaya kallon ruwa kwado yayi
mana ƙafa shekaru nawa muka ɗauka muna shiri ba zai yiwu lokaci ɗaya komai ya warware ba.
Ba zai yiwu ba"
Ta kalleshi fuskarta babu É—igon walwala tace
"Baka kai ni damuwa ba Yaya, baka kai ni baƙin ciki ba... Ba kuma ka kaini takaicin dawowar
wannan shegen yaron ba mai idanu a tsakar ka, ni kaÉ—ai na san gwagwarmayar da ni tsawon
shekaru ba zan ga kwaba na yana son yin ruwa in ja baya in zuba ido ba, sai dai ba na so mu yi
gaggawa ne komai ya zo ya ƙarasa lalace mana! Dole za mu yi maganin abin"
"A yanzu menene mafita Adda?"
ÆŠayan namijin yayi magana
"Abu É—aya ne tak, dole za mu gabatar da plan É—in mu tun na farko a kanshi... A yanzu
matsalarmu ɗaya ubanshi, amma zan san yadda zan yi dole ya amince da ƙudiri na mu kuma
za mu yi amfani da daman mu salwantar da rayuwarshi da ta iyayenshi gabaÉ—aya don na
tabbatar salwantarshi daidai yake da nasu salwantar don ba za su jure ba..."
Ƙulle ƙullensu suka cigaba da yi sama da awa biyu suna nan zaune kan suka mayar da badda
kamarsu suka fice daban daban kowa yayi hanyarshi.
****
Yinin su Abeeha a sashen Ammi ya musu daaÉ—i don da kanta ma ta tsefewa jannah kai akan za
su yi kitson Fulani tunda gobe akwai taron Matasa na Fuunange, hira suke yi sossai tun Aisha
na É—ari dari da su har suka sake da juna Ammi kam kaman ta mayar da su ciki don kulawa
musamman da suna bata labarin irin kalar rigimar Rayyan da Mammi suna ta raha da dariya.
Ammin na jin kaman ta zama Mammi ko na seconds ne ta samu irin wannan kulawa da kauna
daga yaron nata.
Jin ma mijin jannahn zai zo goben yayiwa Rayyan É—in ma murnan dawowa Ahalinshi sai su
koma jibi yasa ta kira a zo a mata gyaran jiki na musamman, sai yau suka ji kaman sun samu
madadin Mammi don duk abinda Mammi zata iya yi musu gashi Ammi na yi musu, bayan
Azahar da kaÉ—an suna cin abinci ne ma an gama yi wa Abeeha kitson da yayi mata kyau ainun
sai suka ji an turo kofar parlorn.
Aisha ce ta fara kallonshi ta yi tsallen murna tana kwala kiran Ammi
"Ammi! Ammi"
Fitowa daga É—aki Ammin tayi tana cewa
"Aisha bakya rabo da autanci ihun nan fa? Sai idanunta ya sauka a kanshi fara'arta ne ya ninku
a hankali ta isa ta kama hannunshi
"Wa nake gani haka? Ko dai idona ne?"
Yana dariya ya ce
"Sam ba gizo bane nine Ammina, Na same ku lafiya?"
*Kun ga readers marasa cewa thank you ko yin comment nan kuna bani mamaki, na faÉ—a
pages dayawa a baya na nanata Weekdays ina da ayyukan dake gabana sai dare nake posting
amma idan na kai daren nan su masu ma comments É—in ainun da nuna jin daaÉ—insu basa
damuwa kaman Marasa cewa ko ci kanki..Allah ya kyauta*
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*53*

*******
"Ameer! Yaushe rabon da a gana? Ashe za ka zo?"
Ya shafa kanshi yana rike hannun Ammin yace
"Ammi abubuwan mu ne sai a hankali amma kuna raina wlh"
"Da muna ranka ba'a waya kaÉ—ai zaka dinga jin mu ba da kana zuwa shekara nawa rabon da
ka waiwayi gida?"
"Na tuba Ammi yanzu kam zan dinga zuwa, yanzu É—in ma labarin bayyanar Sameer ya saka ni
zuwa dole."
Suka kai zaune, Aisha ta kawo mishi ruwa yayinda jannah ta gaishe shi ya amsa, Abeeha ma ta
gaishe shi ganin shi mutum mai fara'a kwarai da wasa ya burge su.
"Ammi ina kika samu wasu yaran babu labari?"
"Ƙannenka ne, Abeeha da Jannah ga wani yayan naku ɗan wajen babban yayana ne Galadima,
abokin Sameer ne don tare suka tashi kaman 'yan biyu a ɗakin nan ɓacewar Sameer bai sa ya
bar nan ba anan yayi rayuwa har ya gama secondary ya tafi karatu chan kasashen turawa ya
gama da jimawa ya ƙi dawowa"
Sannu da dawowa suka sake yi mishi ya amsa da kulawa.
"Ammi ina Sameer É—in? Wani sashe yake?"
"Ka ci abinci ka dan huta sai kaje yana chan tare da matarsa"
Wara ido yayi
"Har ma aure yayi abin shi"
"Eh ya bar ku da gaurantaka"
Yayi dariya, Abeeha ce ta taya Aisha presenting mishi abinci kan suka koma suka zauna suna
ta jin hirar su da Ammi wanda suke tuna baya tasowarshi da Sameer, hakika zata iya cewa
shine na uku a damuwar rashin Sameer don sai da yayi jinya tunda tun ba'a yaye shi ba ya
yaye kanshi ya dawo wurinta saboda Sameer sun shaku sossai ta zama sanadiyar raba
wannan ƙaunar.
Bayan ya gama sashenshi da bai da nisa da nata ya ƙarasa don ana gyarawa akai akai kuma
zaman cin abincin nan da yayi ta aika wasu hadiman sun sake kakkaɓewa ya tafi yayi wanka
yana fitowa ma yaji ana kiran la'asar don haka sai da yayi sallah ya fita ya tambayi wasu
fadawa suka fada mishi inda sashen na Sameer yake ya nufi wurin.
"Amir Galadima..!"
Rayyan ya faÉ—a fuskarshi É—auke da fara'a shima Amir cike da fara'a ya rungume shi suka raba
hug É—in suka tafa irin na mazan dai da aka manta rabon da a haÉ—u.
"Sameer kana duniya ashe? Baka kyauta mana ba! Ka ɓace babu traces? Hankalinmu ya
matuƙar tashi har ka bayyana ban daina tunaka ba, saƙon bayyanarka na daga cikin news mafi
jin daaɗi da na taɓa ji a duniya"
Murmushi kawai Rayyan yake.
"Mu isa ciki, wannan labari ne mai tsawo and ka san ban da bakin ba dashi"
Suka nufi yana furta
"Har yanzu ana nan da baƙin hali"
Murmushi yayi yana tuna kalmar Afeefah wai ta mishi shaidar Rashin kirki a baya yace
"Tunda matata ma ta faÉ—a hakan don ka faÉ—a ba komai bane"
Dariya sossai Ameer ke yi har suka ƙarasa parlorn suka zauna, nan hira ya fara don Ameer na
daga cikin waenda a bayan ma suka san dariyar Sameer, daga shi har mahaifinshi suna da
muhimmanci sossai a rayuwarshi Dukda tun dawowarshi sau É—aya yaje wurin Galadiman kuma
tun da ya kawo mishi maganan Ammi bai sake komawa ba.
Ita kam Afeefah jin hirar su yasa ta nemi gyale mai girma ta saka ta É—ora wata alkyabba marar
nauyi shara shara a kai ta fito, tayi kyau sossai don ya kasa dauke ido a kanta Dukda bata
shafa komai ba, gaisawa suka yi da Ameer cikin natsuwa da girmamawa kan ta kawo ruwa da
su snacks ta ajiye mishi, ta kalli Rayyan
"Ya Saraki bari na je wurin su Adda Abeeha yanzu za mu dawo"
Bai ce komai ba don baya son abinda ke tsakanin shi da mahaifiyarshi ya shafe su dukkansu.
Ta juya ta fice, tana tafiya ana jefa mata gaisuwa har ta kusa isa sashen suka haÉ—u da Fulani
Adama, ta É—an rusuna ta gaisheta
"Lafiya ƙalau ya baƙunta Afeefah?"
Ta amsa tana ƙare mata kallo ganin yadda ta sake wani kyau da haske.
"Alhamdulillah Mama"
"Masha Allah."
Tana kai nan ta wuce ta itama ta wuce ta nufi wurin Ammin, zaune kuwa ta same su har lokacin
ganinta yasa jannah fara cewa
"Amarsu ta ango"
Murmushi tayi tana sunkuyar da kai saboda Ammi dake wurin ta duƙa ta kwashi gaisuwa.
"Lafiya ƙalau Gimbiya Afeefah, ya zaman baƙunta da rashin sabo?"
"Alhamdulillah Ammi"
"Masha Allah, yanzu kuwa Mamanku ta kawo min ƙararku sai dai na bata uzurin da cewa laifina
ne tunda ku baƙi ne baku wani san tsare-tsaren ba, ni kuma rigimar Sameer ne yasa ban yi
maganan ba"
"Allah ya sa ba laifi muka yi ba Ammi"
"A kan zuwa gaisuwa ne, ya kamata duk safiyar duniya ku bi ku gaida iyayen naku musamman
ke Afeefah da kike matar Ciroma"
"Ayi mana afuwa bamu san da tsarin ba amma za mu gyara in shaa Allah"
Ammi tayi murmushi tana yaba Yadda Afeefar ta iya magana.
"Adda Abeeha kitson nan yayi kyau masha Allah"
"Kin ga nawa ni ma, kitson na da kyau wlh"
Jannah ta faÉ—a tun kan Abeehar ta bada amsa tana nuna mata kanta.
"masha Allah duk sun yi kyau"
"Afeefah zo kema in tsefe miki sai a yi miki tunda duk gobe shigan al'ada za ku yi"
Tace
"Ai Ammi kaina a tsefe ne"
Wacce ta yi musu kitson ta kira aka kawo kayan kitso na musamman itama aka shiga yi mata
kuwa suna hirarsu.
Dab Magrib aka gama yayi kyau ainun ya amshe ta don har a fuskarta zaka san ta chanchada
kitso yadda ya ƙara sheki.
Ana gamawa kuwa sai ga wani hadimi ya nemi a sanar da Fulani Afeefah Ciroma ya aiko a yi
kiranta, Miƙewa tayi ta kalli su Abeeha
"Adda Abeeha ku tashi mu tafi please"
"A'a yi tafiyar ki muna wurin Ammin mu"
Shagwaɓe fuska tayi
"Ni kaÉ—ai za ku bari a chan? Ammi kina jin su?"
"Ba ke kaÉ—ai ba kam, ki faÉ—i tsakaninki da Allah ko sanin mun taho ma kin yi in ba da kika ji
shiru ba?"
Hararar wasa take yiwa Abeehar suka yi dariya har Ammi ganin ta kasa cewa komai yasa ta
juya zata tafi sai ta juyo ta kalli Aisha da itama sun fara sakewa sossai da juna tace
"Ko za mu tafi kawai Aisha?"
Aisha ta zaro ido
"Ni?? Raba ni da shiga shirgin mijinkin nan yanzu su Adda Jannah suka gama labarin rashin
mutuncinshi in je ya zane ni?"
Zaro ido tayi
"Yaya Sarakin ne bai da mutunci? A kunnenshi to!"
Miƙewa suka yi suna ce mata ta tsaya ta ji ta rufa musu asiri su ba haka suke nufi ba tuni tayi
gaba tana dariya suma duk dariyar suke har Ammi, saura ƙiris ta ci karo da Zarah suka tsaya
suna kallon juna, a hankali maganganun Fulani Adama suka shiga dawo mata kaman yanzu
suke yi, barin ma da ta ga kyaun da Afeefar ke ƙarawa ga iya ado kaman sarauniya, ga
kamshin ta da in ka shaka zaka san ka shaka ko ita da ta tashi a masarautar bata irin dressing
da daukar ido haÉ—e da kamshin da Afeefah ke yi, abinda ya sake sa taji kaman da gaskiyar
Adama shine dariyar da ta samu duk suke wanda take da tabbacin yana da alaka da Afeefar
idanunta ta sauke akan Aisha dake tsakiyar su Jannah sai kawai ta juya ta tafi.
"Zarah kin tabbatar za ki iya aikata duk abinda za mu saka ki? Sannan za ki iya riƙe mana sirri?"
"Mama kin raine ni ne akan kafafunki kaman É—iyar da kika haifa da cikin ki, har manta cewa ni
ɗin ɗiyar dan uwanki nake don ban taɓa neman abu na rasa daga wurin ki ba, don na taya ki
yaƙi akan cikar burinki na tsawon shekaru ban faɗi ba sai ma halarci da na mayar. Dukda Na ji
Son Ciroma Sameer a raina hakan ba zai hana na isar da Manufarki yadda ya kamata ba"
"Masha Allah, haka nake son ji yanzu na san ban yi rainon banza ba. Zarah!"
Ta amsa
"Za ki auri Sameer dole sai dai bana so ko kadan zamanku yayi nisa"
Kallonta take da neman karin bayani
"Ba haka aka so ba kuma duk Shigowar wannan Afeefar ne ya ɓata mana komai amma a yanzu
za mu gyara, za ki shiga a mata ta biyu amma ke za ki haihu za mu yi duk yadda za mu yi mu
hana Afeefah haihuwa da Sameer, ke muke so ki sama mana É—a namiji daga nan kuma za mu
shafe Sameer"
"Mama ko da yaron bai girma ba? To waye zai yi sarautar?"
"Mahaifinki shine first cousin na sarki kuma yana da ikon yin sarauta zai iya riƙon ƙwarya har
dan da zaki haifa ya girma ya bashi kin ga kenan Sarautar gabaÉ—aya ta dawo gidan mu kaman
yadda dama tun chan yake a tarihi aka yi mana fin karfi aka hana mu"
Shiru zarah tayi Fulani Adama tace
"Ke kar fa ki tsaya wani kokonto don a sarauta babu kokonto ko tsoro, sannan kar ki bari wani
soyayya yayi tasiri saboda babu wannan a tarihin jajirtaccun da suka yi mulki, ko ni na auri mai
martaba ba don ina so ba sai don burin haifar Sarkin gobe, a yadda ban haihu ba na so kowa
ma ya rasa har shi mai martaban ya mutu a haka dole 'yan uwana su karɓa amma Yarinyar
chan FaÉ—imatu ta lalata min shiri don haka dole ne ta ga ba daidai ba"
WaÉ—an nan sune maganganunsu da Fulani Adama da farko tana wasu-wasi amma yanzu ta ji
lallai zata iya, za ta iya aikata hakan ba ɓata lokaci.
Afeefah na isa ta samu yana zaune a parlor kafanshi É—aya a kan daya yana É—an karkadawa
ganinta bai sa ya saki fuska ba tace
"Barka da hutawa Ya Saraki"
"Sai yanzu?"
Ya faÉ—a yana kallonta, tuna irin kirkin Ammi take da irin damuwar da take ciki ko a murmushinta
za ka iya fahimta hakan yasa ta miƙe daga inda take ta dawo kusa dashi tare da zame alkyabba
da gyalen kanta haɗe da ɗan kwali tace a Shagwaɓe
"Wai fushi ka yi na jima Ya Saraki? Kitso fa nayi kalli ka ga bai yi kyau ba?"
Ya kasa ɗauke ido a kanta ta mishi kyau da Kitson sossai ya riƙo hannunta
"vooÉ—i masin boÉ—É—iyel am"
Dukda bata ji ba ta É—an yi murmushi
"Me ka ce kenan?"
"Mai kitson Fulani bata iya yaren ba?"
"Toh ai bana ji, kaima na yi mamakin yadda na ji kana yi fluently"
Ta É—an kwanta a jikinshi yana sake kallon kitson da ya fidda fatar kanta fesss yace
"Tun daga ranar da na bar gidan nan ban sake yi ba sai da na dawo"
Ta sa hannu ta zagaye cikinshi kanta na a kafaÉ—ar shi duk tausayi suke bata daga shi har
Ammin.
"Toh ka faÉ—a min me ka ce?"
"Ya yi kyau sossai kyakyawata. Abin da na ce kenan"
Tayi murmushi mai sauti tana ƙoƙarin maimaita abinda yace da fulatancin, yadda ta shirmata
dole ta saka shi murmushi har ma ya manta da yana kokarin yin fushi ne ta tafi sashen Ammi
tayi zamanta.
Bayan Magrib ya zo ya ja ta suka fice daga masarautar a wata BMW baƙa ya hana su Gaabɗo
Binshi ta chanza zuwa wani blue Abaya da ya karɓeta sossai, shima navy blue Jean ne jikinshi
da coffee shirt da ya fitar da hasken shi ainun sai ya saka facing cap navy blue saboda mutane
baya so a gane shi a wajen don yanzu sai a fara maganan yana fita da kananun kaya, Sossai
ya zaga da ita hannunta na cikin nashi yana driving da hannu É—aya ba wani hira sossai yake
mata ba amma in tayi magana yana kokarin amsawa bar shi dai da kallonta sai kuma pecking
expecially bayan hannunta dake cikin nashi.
Shopping sossai suka yi suka je suka ci abinci daga nan suka dawo suka sayi popsicle don
tace tana so, sai wuraren 9 suka dawo gida hankalinsu kwance shi yayi sallah already ta shiga
tayi nata kan ta shirya kwanciya, kaman jiya riga da wando ta saka masu yauki na kayan baccin
cream colour da ya amshe ta sossai hannun rigan na singlet ta feshe jikinta yadda ya kamata,
tsoron zuwa É—akinshi take don bata san me zai faru ba kar a yi irin na jiya don ma shi likita ne
yana da tarin sani akan yadda zai bi da ita ko da ta gurzu yayi jinyar kayanshi amma tana
tsoron zafin don har lokacin tana jinta a kumbure.
Gadonta ta hau ta kwanta shiru tana jin kewan jikinshi da har ta fara sabo da hawa, bata yi
mintuna talatin ba ya tura kofan ya shigo ganinta kwance ya saka shi murmusawa ya isa gadon
ya yaye rufan da tayi
"Lallai ma yarinya ni za ki bari kaman gauro?"
Dariya maganan ya bata ta kama murmushi Dukda yadda ta so tayi pretending ta yi bacci dole
ya dauƙeta suka yi nashi ɗakin daga shi sai wani cotton wandon bacci chest dinshi duka a
bayyane haka ya rufeta ciki, yana shafa bayanta yace
"Wasu sun ce zazzafar soyayya tana zuwa ne a bazata! Na yarda BoÉ—É—i saboda a sadda na
fara ganinki ban zaci zan so ki kaman yadda nake jinki a yanzu ba, ban san za ki zama abu
mafi muhimmanci da daraja a rayuwata ba, I just fell in love with you and am still falling even
harder cikin kowani dakika"
Tana tare dashi amma tunaninta yake, tana a jikinshi amma kewanta yake bai taba sanin haka
so yake ba, bai damu da yaji ta Bakinta ba shi dai ya san yana sonta daga shafata da yake ya
nemi zarcewa, za tayi magana ya haÉ—e lips É—insu yana bata wani irin kyakyawar french Kiss da
ya gigitata, tuni rigar ta yayi wani wurin ganin da gaske yake yasa ta kawo kuka ta saka mishi
mai tsuma rai dole ya haura a hankali zuwa wuyanta yana ajiye wet kisses slowly ya isa
kunnenta.
"Am sorry boɗɗiyel am! Ki yi haƙuri kaɗan zan yi ba dayawa ba i promise ba za ki ji zafi ba"
Girgiza kai take sai dai bai bari ta sake wani yunkurin ba ya shiga wasa da harshenshi a
kunnenta, Tsam ta tsume sai da ya tabbatar ta gama rikicewa kan yayi abinda zai yi duk suka
samu natsuwa cike da tarin soyayya da tsantsar kulawa kuma bata ji zafin kaman na farko ba, a
tare suka yi wanka yau ma nade da towel kawai suka shige bargo yana sanya mata albarka a
kunnenta haÉ—e da godiya.
Washegari da safe kaman yadda Fulani Adama ta faÉ—a bayan ta gama mishi abin kari ya ci ya
fita ma wurin mai martaba ta shirya ta nufi wurin Ammi don da gaske su jannah basu kwana
sashen ba, bayan sun gaisa suka dunguma wurin Fulani Adaman suka gaisheta Madarar shanu
ta basu akan su É—uma ciki sabo ne da zafin shi, ita Afeefah bata sha amma don kar su yi laifi
Jannah ta karɓa ta sha, Abeeha ma ta Sha Afeefah na ta wasa dashi har suka ce zasu tafi suka
ajiye mata suka fice, sauran sashen suka je suka miƙa gaisuwa kan ta koma sashenta su
jannah suka koma wurin Ammi.
Bacci tayi sossai sai azahar ta tashi ta shiga shirya mishi abinci inda ta haÉ—a mishi White Rice
da kidney sauce sanin yana son abin sossai, bata ma gama shiryawa ba ya dawo É—akinshi ta
kai ta É—ale kafafunshi yana ci yana bata har suka gama ta fitar da kwanukan. Bayan Magrib aka
zo shirya ta zuwa wurin Taron da Matasan Fulani suka shiryawa Yariman nasu na murna.
Kayan saƙi ne Fari aka bata ta shirya ciki a ƙasan rigan ta saka bodyhug mai dogon hannu fari
ƙal kan ta ɗora rigan ya zauna mata sossai ta ɗaura zanin a ɗan sama kaɗan suka shiga cika
mata kayan adon Fulani bayan an yi mata dauri mai kyau, goshinta, wuya, hannaye har kafa
kayan ado ne irin na al'ada sai aka É—ora mata alkyabba fara kal tayi kyau sossai tana ta kallon
kanta tana murmushi, bayan sun fita tana nan zaune sai gashi ya shigo.
Miƙewa tayi tana kallonshi kaman yadda yake kallonta da tarin ƙauna, farin wando na saƙi
shima shine jikinshi sai wani farin shirt kan rigar sakin har da hula yana rike da sanda yayi kyau
har ta rasa wani irin kyau za ta ce yayi, wayanta da bata taɓa daukar ma hoto ciki ba ta ɗauko
ta ja shi gaban door size mirror ta shiga yi musu mirror selfie, ya biye mata sossai akwai wanda
ya ɗora sandar a wuyanshi ya riƙe da hannu ɗaya ya ɗan karkato ya ɗora hannunshi ɗaya akan
cikinta bayanta na jingine a kirjinshi sossai posture É—in yayi kyau amma bai yi dariya ba sai ta
Shagwaɓe
"Kayi murmushi mana Ya Saraki ka ga fa shiyasa ake cewa baka da kirki"
Bai san yayi murmushin ba ta É—auka duk hakwaransu waje da ya gaji ya ja ta suka fice tana
kallon hotunan nasu na karshe daga ma baya ma shi ta mayar wallpaper wayan ya karɓa yayi
air dropping shima ya mayar nashi wallpaper É—in, sun isa katoton zallar filin taron dake cike da
haske an kawata wurin da kujeru.
Kusan kowa a wurin shirye yake da kayan saƙi na fulani sai a wurin suka haɗu da Jannah da
mijinta shi Rayyan sun haÉ—u tun da ya fita da safe ita ce dai Afeefah sai lokacin ta ganshi, wurin
yayi kyau sossai kujeransu na a haɗe, gefe yan mata da ƙwairen Nono da wasu kananu masu
kyau a tsaftace wanda shine za'a sha a taron
Matasa da yan mata cike da wurin kida da fulatanci na tashi daga wannan ya kare za'a saka
wannan wasu na soyayyarsu yayinda Afeefah ke bin komai dake gudana da kallon burgewa,
wasan kiwo da shanu aka fara inda aka ajiye shanu aka shirya Matasa biyar aga mai dabarar
da zai iya tada shanu tsaye, sossai wasan ya kayatar bayan an gama shi aka yi shaÉ—i sai
wasan Matasa na sanda, aka yi rawa kala daban daban su dai basu tashi ba Dukda ta so ta
tashi amma ganin gogan ya ƙi bada dama sai ta natsu an saka waƙar wani mawakin Camero
Jaamali Na Lara saftata ya waiga ya kalleta tace
"Me ake cewa?"
Ya ce
"Zan fada miki sai mun je gida"
Kai ta gyaɗa amma da aka kira wata mawakiyar Fombina Rukayya aka saka waƙar ta sai ya
waiga ya kalleta
"Akwai inda zan fassara miki amma da sigar namiji zuwa mace"
Kai ta gyaÉ—a.
"kin san me amshin ke cewa?"
Ta girgiza kai
"Ni fa ko zo in kashe ki aka ce ba sani zan ba bare na shirya guduwa"
Murmushi mai kyau yayi hannunshi na cikin nata yana wasa dashi a yadda suke maganan kallo
É—aya zaka musu ka san masoyan Juna ne kuma exchanging kalamai suke don fuskarsu a sake
musamman ita dake ta doka murmushi.
Ya fara yi mata
"Mi É—on yidi ma a anda mi don yiÉ—i ma na? Mi É—on yidi ma Yideyel am nder bernde am.
(Ina sonki baki san ina sonki Ba ne? Ina sonki masoyiyata har cikin zuciyata)"
Sossai take blushing tana jin kidan wakan na mata daaÉ—i barin ma rawan da Matasan suke. Bai
sake magana ba sai da aka zo wani wuri yana wasa da hannunta idanunshi a kan fuskarta yace
"Ki ji! Yiide ma nde nangi am mi warti bumÉ—o!(Sonki da ya kama ni na zama makaho)
Yiide nangi am mi warti ginnaÉ—o..!
(Sonki ya kama ni na zama mahaukaci)
Waru nangam giÉ—É—o am saklare hosi am!
(Zo ki riƙe ni masoyiyata jiri/hajijiya ya kama ni)
Mi É—o numa ma jamma be nange mi nyamataa!
(Kina cikin tunanina dare da rana bana iya cin abinci)
Mi É—o numa ma nange be jamma mi É—anataa!
(ina aikin tunaninki rana da dare bana iya bacci)"
Hannunshi ta sake gimtsewa tana sake faÉ—ada murmushinta ta ce cikin yanayin 'yan koyo
"Mi É—on yidi ma a anda mi É—on yidi ma naa mi É—on yidi ma yideyel am nder bernde am"
(Ina sonka baka san ina sonka bane? Ina sonka masoyina har cikin zuciyata)
"Da gaske ko a waƙa?"
Yayi tambayar yana É—age gira daya cikin salo
Ta saki murmushi
"Da wanne kayi kai?"
"Na taɓa miki wasan ina sonki? To ina sonki Afeefah! idan na kalle ki sai na ga cikakken
kwanciyar hankali zuciyata ta samu natsuwa, kin kasance Abar alfarina!"
A hankali in a whisper tace
"Nima da gaske nake, ina sonka har cikin raina zan kuma zame maka macen da zata baka duk
wani so da kulawar da ba'a taɓa baka irinshi ba, zan zame maka macen da ba zata taɓa ɓata
maka da gangan ba, zan zama mai baka goyon baya a dukkan lamuran rayuwa, zan zama mai
maka uzuri kuma zan kasance haskenka a duk sadda duhu ya nemi mamaye maka hanya, the
girl you never want to argue with but communicate things out, the girl who love you for you ba
don kudi ko mulki ba"
Miƙewa tsamm yayi
"Tashi mu tafi"
Bai jira cewarta ba ya janye ta don tana cigaba da maganganun nan zai iya tafka abin kunya a
bainar nasi duk nema take ta rikita shi ko ta kan Abeeha da ya hanga da Ameer yake so yayi
magana bai bi ba ya buÉ—e mata ta shiga ya zagaya ya shiga aka ja su sai gida.
🖤Gureenjoh 🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*54*

"Duk wanda ka ga ya lashi zumar nasara, to tabbas ya ɗanɗani maɗaciyar haƙuri."
Wannan ɗin wani zance ne na masu hikima. Bahaushe ya ce haƙuri gishirin zaman duniya,
Yayin da ubangiji ya koya mana cewa duk inda abu ya je ya dawo kayi haƙuri! Duk ƙunci ka yi
haƙuri, Duk damuwa ka zama mai haƙuri, Duk mai haƙuri shi ke galaba kuma duk mai haƙuri shi
ke cin riba da wannan aya ta;
"Ista'eenuu billahi wasbiruu" (Ku nemi taimakon Allah kuma ku yi haƙuri).
Haƙiƙa da a shekarun baya za'a iya cewa zata taka wannan matsayi da take kai a yanzu za ta
ce karya ne amma dayake Allah mai jin ƙan bayinsa ne da jiɓantar lamuransu gata a cikin
ni'imarsa marar yankewa. Hakan ya sa cikin waennan watanni uku da suka biyo bayan tariyarta
gidan Sarautar Fombina Bakinta bai taɓa hutawa da godiya ga ubangajinta ba saboda shi ya ce
mana ka gode mishi a dukkan ni'imominsa shi kuma zai ƙara maka.
"Alhamdulillahil lazee bini'imatihi tatimmus salihaat... Alhamdulillah ala kulli haalin...
Alhamdulillah hamdan hamda... Hamdan katsiran dayyiban mubarakan fihi"
Sun kasance kaman ruwan sha a Bakinta, ta samu duk wani gata da zata nema ta uwa irin
Ammi da uba irin mai martaba. Waenda a yanzu suke tabbatar da cewa bata yi kuka da sunan
maraici ba.
Ta samu É—umbin soyayya marar fasaltuwa daga wurin jarumi kuma gwarzon mazanta, a
wannan watanni uku ba zata ce ko kallon banza ya taɓa shiga tsakaninsu ba bayan tattali da
nuna kulawa, bata taɓa neman wani abu ta rasa ba zata iya cewa rayuwar da tayi a gidan na
watannin ukun farko suna daga cikin waenda ba zata taɓa iya shafe su a tarihin rayuwarta ba,
Dukda sau biyu yana tafiya akan aikinshi hakan bai dakile mata dukkannin abinda ya saba ba.
Jannah ta koma sai dai su yi waya, Abeeha ta yi transfer ta dawo nan Fombina da karatun ta
yayinda ta yi kane kane zuciyar Ameer Galadima ta hana shi komawa wurin aiki, a gefe É—aya
kusan duk waenda suke kusanci da Aisha da Saleem sun san cewa sun mato akan son
junansu, daga mommy har su Sadiqa har Umman Sulaiman da ma matarshi su kan kira ta su
gaisa sa'i da lokaci don yadda suka mayar da ita É—aya daga cikinsu itama haka ta É—auke su
tamkar yan uwan da ta rasa, abu ɗaya ta kasa shine ƙarasa shirya tsakanin Rayyan da Ammi,
yana da taurin zuciya irin na Fulanin Asali iyakancinshi da ita idan sun haÉ—u gaisuwa ne amma
bayan nan baya ƙara komai Ameer yayi, mai martaba ya yi, Yaya Maudo(Galadiman Fombina)
shima ya yi itama tana kan yi Dukda duk ranar da tayi maganan sai sun ɗan samu saɓani ya
nuna mata baya so bata taɓa dainawa ba lokaci lokaci.
A gefe ta kan tuna kawu da su inna Larai don an ce jini ko ya yake ya fi ruwa kauri duk abinda
suka yi mata gashi bai katangeta da samun farin ciki ba, sai ma kusanta ta da yayi da farin cikin
mai tarin alkhairai, Result ɗinsu na Waec ya fito kuma ta ci sossai tayi ƙoƙari Dukda shi gogan
nata bai ce komai a kai ba hakan ya sa ta fara sanyawa zuciyarta cewa ba lallai tayi karatu
yadda take so ba, ta sakawa zuciyarta ba komai kake so kake samu ba kila karatun ba alkhairi
bane da haka ta danne ranta bata taɓa yi mishi magana a kan makarantar ba.
Yau ya kama Friday haka kawai take cikin nishadi tun da ya sauƙe mata zallar madarar ƙauna
ya fice da safe sa'i da lokaci ta kan saki murmushin da baya rabo da fuskarta, bayan tayi Sallar
la'asar ta gabatar da duk abinda ta saba kowani juma'a a irin lokacin na karatun suratul kahf da
adu'o'i ta tashi ta nufi kitchen. Ta ɓata lokaci sossai wurin gasa mishi kifi da yake matuƙar jin
daaÉ—in gashin nata ta soya plantain da irish ta shirya table É—inta tsaf kan taje tayi wanka,
kananun kaya ta saka wando ne da bai kai ma gwiwa ba rabin cinya Black sai White Shirt da ta
saka tayi wani irin kyau kaman ka sace ta.
A kwanakin ita kanta ta san ta sake chanzawa ta yi kubul kubul fatarta yayi fresh kaman mai
wanka da madara, ita kaÉ—ai ce don tun gama taya ta aiki ta tura su Sa'ade sashen baya da ya
sa aka gyara musu na cikin ɓangaren nata saboda shi ba mutum bane da yake son takura a
sadda yake tare da iyalinshi, Abeeha ta jima da komawa wurin Ammi wai in ta cigaba da zama
za su iya makantata cikin ko wani dakika don haka tayi ta kanta. fitowa tayi kai tsaye zuwa
kitchen tana tuna wani haÉ—i na musamman da aka koya mata tun kafin aurenta dashi yau kam
ta yi niyyar gwadawa, ayaba ta ɓare guda huɗu ta dauki tafarnuwa guda ɗaya ɗan daidai ta
haÉ—a ta zuba a blender ta markade ta juye a cup, zumarta na asali ta zuba a kai tana jin
haushin rashin kankanrar matar da bata dashi amma ko a haka ta san emergency ne mai kyau
kaman yadda matar ta yabe shi, shanye wa tayi a tsaye a kitchen É—in kan ta koma É—akinta tayi
ruf da ciki tana danna waya.
Shigowar shi gidan jin bai ji motsinta ba yasa ya nufi É—akin nata, sanye yake da khakinshi full
don wani aiki ya fita akan tsaro tun safiyar yana tafiya yana ɓalle botiran ji yake kayan sun ishe
shi, tura kofar É—akin da kafewarshi a wurin lokaci É—aya don ji yayi ruwan jikinshi na neman
tsiyayewa, surar jikinta na neman zauta shi kafafunta zuwa cinyar ta dake a bayyane suka tasar
da mazan dake jikinshi a lokaci guda, harshenshi ya fidda ya ɗan jiƙa lebanshi da yake ji sun
bushe kan ya nufi gadon, ya ajiye kayan hannunshi ya kai zaune bakin gadon ya É—ora
hannunshi kan cinyarta, tun shigowanshi kamshin turarenshi ya gaya mata wanene da gayya ta
ƙi juyawan, ganin har lokacin bata juya ba ya sa ya saki murmushi mai sauti.
Hannun ya É—ago ya kai kan rigan ta ya yaye ya kai fuskarshi yayi kissing fatar bayan yana
shafawa a hankali, kan ya ɗan kwantar da kanshi yana jin yadda ta sauƙe ajiyar zuciya, bai yi
magana ba ya cigaba da goga mata gashin gemunshi a bayan yana shafawa da hannunshi tuni
ta kasa natsuwa ta juyo sai yayi mata rumfa yana haÉ—e goshinta da nashi ya lumshe idanu yana
shakar daddadan kamshin turarenta dake ƙara hautsina shi.
"Debbo boÉ—É—o am! Fushi kika yi?" (Kyakyawar matata)
Yayi magana yana dan hura mata iska a idanun da ta rufe.
"Shi ne ka je kayi zamanka ka manta da ni tun safe ko waya baka yi min ba.. Kuma ai ka ce za
ka dawo da wuri amma sai yanzu? Kwalliyana har ya goge"
"Ya subhallah...!"
Ya ambata a chan ƙasan makogoronshin, peck yayiwa bakin Shagwaɓar ta sanya hannu akan
dantsenshi dake bayyane don daga shi sai vest ya zame rigar ta riƙe shi da kyau.
"Na isa in manta da bugun zuciyata? Ko kin san mintuna biyu a nesa dake kaman shekara biyu
ne a gareni yayinda shekara biyu a tare da ke zai zama tamkar mintuna biyu? Sam bana sanin
gudun lokaci idan ina kusa dake Matar masu sarauta"
Murmushi mai sauti kaÉ—an ta sake da ta sake motsa zuciyarshi.
"Ni ce addiction É—inka yanzu kenan?"
Tayi maganan tana ɗan yawo da hannunta slowly a kan damtsenshi zuwa ƙirjinshi, ya ɗan
taune lip.
"Yes you really are my dear.. Craving É—inki nake kaman mai ciki"
Dariya ta É—an yi, ya kama lips É—in da nashi yana kissing slowly kan ya saki ta É—an yi murmushi
"Always remember that zan iya gajiya da komai a wannan duniyar amma banda ke, even when
am tired all i want is you.."
Hannayenta ta mayar bayan ƙeyarshi tana mishi susa ita kanta ta san tana yin hakan ta gama
kunnashi, tuni hannunshi ya kai ga kwankwasonta yana yin sama da rigar bakinshi is kissing
her like his life depend on that, ba zai iya haƙuri sai dare ba he just want to feel her bukatarta
kullum sabo yake zama mishi, kaman yadda mutum ba zai iya rayuwa babu iska ba haka yake
jin ba zai iya rayuwa babu ita a gangarshi ba.
Ya kuwa É—anÉ—ani abin da ba zai iya janyewa cikin lokaci kankani ba, rikice mata yayi sai da ta
fara dana sanin shan abinda ta sha da yamman don bai barta ba sai da ta fara mishi kukan
gaske, ya rungumeta yana sanya mata albarka.
Tayi lub a ƙirjinshi suna sauƙe numfashi a hankali hankali, wayanshi ya duba sai ya ga dab ake
da kiran sallah dole ya miƙe da ita zuwa bayi suka yi wanka duk jikinta a mace suka fito daure
da alwala, bai iya ya je masallaci ba don an fara kiraye kiraye kan ya isa ma za'a iya idar wa
jallabiya ya saka ya ja su suka idar, ya waigo yaga sai ɓata fuska take ya janyota jikinshi ta
kwanta suka yi azkar a haka kan yana shafa fuskarta yace
"Raguwata zan ga ranar da zaki gama sabo da jaruminki"
A Shagwaɓe tace
"Ni dai a'a na yi fushi!"
Murmushi ya saki ta kalleshi
"Murmushi na yi maka kyau kar ka daina kwata kwata ka ji Ya Saraki?"
Yana shafa girarta yace
"Yau jinki nake na musamman Boɗɗi garɗinki wane zuma farar saƙa don haka dole ma in yi ta
miki har sai kin gaji. Tashi ki ga wani abu"
Miƙewa tayi ya tashi yaje ya dawo manyan paper bags da ya shigo da su ya ajiye ya koma ya
zauna, buɗewa yayi ya ɗauko wasu papers ya miƙa mata.
"Congratulations wannan admission naki ne"
Hannu ta sa ta rufe bakinta tana zaro idanu fuskarta cike da wani irin tarin expression tace
"No..No you can't be Serious! Don Allah da gaske kake ko wasa? It can't be..."
Ta ma rasa me zata faÉ—a tsabar farin ciki and ganin irin wannan tarin farin cikin da shine
sanadin ya saka ya ji shima zuciyarshi ta yalwata da farin ciki, ta ajiye papers É—in ta rungumeshi
tana hawaye
"Ban zaci za ka barni nayi karatu ba, har na cire rai ashe kana chan kana nema min thank you
My love! Thank you so so much rabin raina"
Ya rungumeta shima har ta gama farin cikin kan ya ɗago ta ya riƙe hannunta.
"Maganan gaskiya Afeefah ina matuƙar kishinki, ina jin zafi idan na ga idanun wani namiji ya
kalleki ko da da second guda ne, don ke É—in tawa ce! don ni kaÉ—ai aka halliceki kaman yadda
aka halliceni don ke! At First ban yi niyyar bari kiyi karatu ba ko ba don kishi na ba sai don
kasancewarki Matar Ciroma mai jiran gado, ba Girmanki bane chakuduwa da maza don neman
ilimi hakan yasa na nema miki Open university"
Sakin hannunta yayi ya buɗe jakar Apple Mac book ne da Apple Ipad ya fiddosu a kwali ya miƙa
mata
"za ki yi amfani da waennan kiyi karatunki daga kan gado i promise to help you in all the
process exams kaɗai zai kai ki makaranta. Ina fata hakan bai ɓata miki ba?"
Ts saki murmushi hawaye na zuba mata tace
"Har wacece ni da zan ce hakan bai min ba? Ciroma ne fa gabana kuma Sarakin Fombina..! Ni
din ban kai wannan matsayi ba kuma ko da na kai ba zan taɓa kin amincewa ba don ni'imace
hakan da ban tsammata ba Allah ya bani, wasu na chan ma suna neman yadda za su yi
karatun bai samu ba, wasu na chan suna yawo lectures cikin rana, zafi da ruwa ai ni daaÉ—ina
ma na samu miji mai gatanta ni... Allah ya saka maka da alkhairi na gode sossai na gode
kwarai, na...."
Bakinta yayi saurin rufewa da nashi ya bata deep Kiss da ya sa take jin sanyin na sauka har
cikin zuciyarta.
"Babu wannan tsakaninmu girmanki ne Sarauniyata"
Tayi murmushi tana sake godewa Allah.
Janshi tayi suka je ya ci abinci yana bata cike da kulawa har suka gama suka zo suka gabatar
da isha kan suka shige cikin bargo yana yi mata setting na system da ipad É—in yana koya mata
yadda zata yi amfani da su tana daga kwance nashe nashe akan kirjinshi.
Washegari da misalin ƙarfe goma ta fito cikin wani Apiligue lace peach da yayi mugun amsarta
ta ɗora gyale mai girma a kai tare da alkyabba marar nauyi ta nufi sashen Ammi don miƙa
gaisuwa, ta isa parlorn babu kowa don haka kai tsaye É—akin Ammin ta nufa ta saka hannu zata
bude ta ji Ammin na cewa
"Yaya Maudo ni dai ban goyi bayan wani auren Zarah da Sameer ba Dukda na san alkawari ne
amma Meyasa Mai martaba zai fara matsawa a yi shi yanzu? Shi kanshi Sameer É—in ba son
maganan yake ba sai kwana- kwana yake ya fi sati biyu mai martaba na Binshi da wannan
magana... Ba wai bana son zarah bane amma yaushe har suka dawo suka gama sabo da nan
É—in? Kwata kwata aurenshi ma da Afeefar bai fi watanni takwas ba don Allah ka bashi shawarar
a jinkirta ba dai sati biyu masu zuwa kaman yadda yace ba..."
Wani irin faÉ—uwa gabanta yayi har tana ganin jiri, Dukda tana jin Ammin na cigaba da magana
bata iya ta tsaya sauraronta ba don mugun jin da tayi ya daki zuciyarta fiye da zato ko
tsammani, a gigice ta juya ta nufi sashensu don gaisuwar ba zata iya shi ba cikin wannan hali ta
tabbatar da za'a bincika jininta yayi mugun hawa ko ya zuƙe tas yayi ƙasa tsabar tashin hankali
Yana zaune kawai ya ga faÉ—owarta don yau din Asabar ne bai fita ko ina ba da kyar ma ya
kyaleta ta fita gaisuwar, ganin halin da ta shigo ya sa yayi saurin Miƙewa yana rike kafaɗunta.
"Afeefah! Afeefah menene? Me ya faru?"
Ta kasa magana ma, girgizata yayi
"Me ya sameki? Afeefah!!!"
Da ƙarfi yayi maganan yana bin jikinta da kallo sai dai bai ga komai ba.
"A wurin Ammie ne aka ɓata miki rai? Ko wurin Mama ne? Me ya faru kika shiga cikin wannan
yanayin? Ki yi min magana mana!"
Kuka mai sauti ta fashe dashi kaman wacce aka rufe da duka sai ta sake É—aga mishi hankali ya
juya da sauri zai fita ya tambayo uban da ya taɓa ta tayi saurin riƙo hannunshi tana kukan
sossai duk ta ruÉ—a shi.
"Sakeni in ba zaki faÉ—a min abinda aka yi miki ba Afeefah, Sakeni nace in je in ji dalilin da
kaina...!"
Da tsawa yayi maganan yana kokarin fusge hannunshi tayi saurin rungumeshi kamkam tana
cigaba da kukan da ya ƙarasa cire mishi natsuwa.
"I thought ina da muhimmanci a rayuwarka, a zatona duk wani abu da ya shafeka ya shafe ni
Meyasa zaka min hakan? Meyasa Ya Saraki?"
Sakinta yayi yana riƙo fuskarta idanunshi cikin nata
"wa yace miki ba ki da muhimmanci a rayuwata? Kin kuwa san yadda nake jinki Afeefah?
Meyasa za ki yi irin wannan tunanin?"
"Ba gashi ba, idan har ka daukeni da muhimmanci ba zaka binne ni ba, ashe aure zaka yi nan
da sati biyu? Aure Ya Saraki irin wannan baka iya ka sanar min ba?"
Kukan da take na shaketa ta ƙarasa, sossai fuskarshi yayi Red ainun jijiyoyin kanshi duk suka
miƙe kukanta tamkar saukar tafasashen ruwa ne a zuciyarshi shi kadai ya san irin abinda yake
ji, a ina ta ji? Zai yi magana ta ture hannayenshi ta nufi É—aki da gudu tana cigaba da kukan ya
riƙe kanshi yana ambaton sunan Allah, bayanta ya bi da sauri sai dai ya tarar ta rufe kofan da
makulli hankalinshi ya sake tashi ya shiga bubbugawa yana kiran sunanta cikin damuwa...
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*55*

********
Yayi yayi ta buɗe kofar ta ƙi, har spare key ya ɗauko sai dai dayake ta bar key jikin ƙofan ya ƙi
shiga, cike da damuwa ya koma ya zauna a kan kujera hannunshi dafe da goshinshi sama da
mintuna goma yana nan shiru kan ya miƙe ya tafi ɗakinshi yayi wanka ya shirya cikin wani
jumpha baƙi dinkin zamani, ya saka hula da half cover duk baƙake ya fito kai tsaye ya nufi
motarshi su Gaabɗo na miƙa gaisuwa ma babu wanda ya amsawa ganin yanayinshi yasa basu
nuna za su bishi ba don kallo É—aya ya musu suka koma suka natsu.
Tafiya ba mai nisa ba sossai ya kai shi shiyyar da Galadima yake duk a cikin masarautar,
parking yayi ya sauka ya nufi ciki hadiman ɓangaren na ta miƙa gaisuwa bai amsawa ko ɗaya
ba ya isa babban parlorn Galadiman, ya kuwa same shi zaune suna ma tattaunawa ne da
Ameer, ganinshi ya sa duk fuskokin su suka cika da fara'a
"A'ah yau ɓatan kai ka yi ne Ciroma?"
Da kyar ya É—an sake fuskan ya zauna
"Baba Barka da rana"
"Barka dai, ya iyalin naka?"
"Alhamdulillah"
Miƙawa Ameer hannu yayi suka gaisa kan ya dubi Baba.
"Baba dama na zo ne akan maganan Zarah da mai martaba ya tayar, idan da hali ina so ka
mishi magana Baba a dakatar da maganan nan zuwa gaba duk yadda zan mishi bayani ya kasa
fahimtata, na amince mishi ne kawai saboda na san girman alkawarin wannan masarauta kuma
ba na so ko kadan a ga gazawarshi ka san yadda su Makama suke... Na ji na amince amma ba
yanzu ba kaman yadda suke so"
Galadima ya sauƙe numfashi ya ce
"Sameer da safen nan muka gama wannan magana da mahaifiyarka, ta kirani akan a ja
maganan ba yanzu ba duba da baka ma wani jima da dawowa ba abubuwa dayawa baka gama
sabo dasu ba, ga matarka da bata rufa shekara ba Dukda ba hujja bace tunda anan muna
aurawa namiji ma mata biyu a rana É—aya amma abin a duba ne zancen naku, Mahaifiyarka ba
iya jayayya take da mai martaba ba a wanchan ɓangare kuma akwai Fulani da 'yan uwanta har
biyu suna uzzura mishi duba da yarinyar ta isa auren shiyasa abin ya zo a hagunce. Zan gwada
yi mishi magana idan ya amince sai a bar maganan for now amma da kamar wuya wai gurguwa
da auren nesa"
Idanunshi ya runtse ya san dama aikin su Fulani Adama ne they will be on his fathers neck har
sai sun ga sun samu abinda suke so, shi wlh ba ma zai iya wassafa yadda zarahn take ba
Dukda bata dameshi ba amma tashin Hankalin Afeefah shine abinda ba zai iya jurar gani ba a
abinda ya shafi auren.
"Baba don Allah a yi min wannan ƙoƙarin, mai martaba yayi rantsuwar ba zai karɓi wani uzuri
daga gareni ba muddin ba mai ƙarfin da zai iya haramta auren bane a yanzu duk abinda zan
fada mishi gani zai yi excuse nake kawowa na watsa mishi ƙasa a idanu"
"Hakane. Dukkanmu ba za mu so ganin an yi ƙaranta ba don ba girman wannan masarauta
bane, zan gwada mu gani"
"Na gode sossai Baba bari na koma"
Ya miƙe Ameer ma ya miƙe suka fito a tare a jikin motan shi suka tsaya yayi shiru.
"Lafiya dai kam Sameer? Ko duk maganan auren ne ya saka ka cikin damuwa?"
Numfashi ya sauke yana fesar da iska daga bakinshi
"Ameer damuwana É—aya ne tak tashin hankalin Afeefah, bana son zancen auren nan kwata
kwata don na san ba zata ji daaÉ—i ba wace macece ce zata so a mata kishiya? Irin wannan kam
ma Gani zata yi kaman don ita ba yar cikin gidan nan bane za'a ware ta ko a ba ni zarah,
tunanin sakata a damuwan ya sa ban iya na yi mata maganan ba amma sai gashi ta ji a wani
wuri yanzu haka tana chan tun dazu tana kuka ban san ya zan yi ba!"
Cike da damuwa ya ƙarasa maganan.
KafaÉ—ar shi ya dafa
"Ban taɓa sanin haka rauninka yake ba sai akan Afeefah, kuma gaskiya baka kyauta ba ya
kamata duk abinda yake faruwa ta fara sani daga wurin ka zata iya fahimtarka ba wai taji a wani
wuri ba da ake maganan kila saura sati biyu...! Yanzu kai za ka kwantar da kai kayi rarrashin ta
hanyar da zata fahimceka ko don gaba duba da kaine magajin wannan jaha ta mu ko a rana
É—aya ana iya baka mata a É—aura bambancinta kawai zai iya zama kana sonta fiye da kowa
kuma hakan ma wani makami ne a gareta"
"Dole na Ameer don ba zan samu natsuwa ba muddin tana cikin damuwa, bari na je. Na gode"
Da kallo Ameer ke Binshi har ya shiga motar ya bar wurin, murmushi yayi lallai So So ne hmm
idan ba son ba wani abu ne zai taɓa zuciyar Sameer haka? Juyawa yayi ya koma ciki don basu
gama tattaunawarsu da Mahaifin nashi ba.
Sai da yayi azahar ya dawo ɓangaren ga mamakin shi ya samu abincinshi jere a kan dining
kuma ya san bata taɓa bari hadimai su mishi girki ba kenan ita ta fito tayi, ɗakin ya nufa ya
murda handle É—in sai dai a rufe still goshinshi ya dafe bai taba sanin tana da fushi haka ba, ya
san kalar haƙurinta lallai ya kaita maƙura.
Dakinshi ya nufa don abincin ba zai shiga ba ya rage kayan jikinshi ya kai zaune yana lissafi.
Wasa wasa har dare ta ƙi bude kofan, ko da ya fita Magrib da isha kan ya dawo ya samu ta
É—auke abincin dazu ta ajiye wani daban, shima bai bi ta kanshi ba ya sake komawa kofar É—akin
yana kiran sunanta amma ta ƙi ta buɗe daren tea ya sha daga ita har shi baccin su rabi da rabi
don tunda suka shirya basu taɓa kwana ba tare da juna ba cikin bargo ɗaya skin to skin sai
ranar.
Æangaren Afeefah Da asuba bayan ta yi sallah ta É—an yi azkar kan ta miÆ™e ta saka wani silk
fabric gown ta É—aura dankwalin fuskarta har lokacin da alamun kuka don kukan da ta jima bata
yi ba tayi shi a jiya a ƙarshe ta yi finalizing solution ɗinta, ta sakawa zuciyarta haƙuri da juriya
don ba zata taɓa hana shi ba idan Allah ya rubuta, haka ba zata saka ya ƙi bin umurnin
iyayenshi ba ta riga ta sakawa zuciyarta cewa ko ba jima ko da bai auri zarah ba zai iya yin
wani auren don haka za tayi Adu'a Allah ya kawo wacce za su zauna lafiya, za ta kuma yi iya
kokarinta na ganin ta cigaba da zama ta farko a zuciyarshi har abada sai dai ba zata É—auki ya
dinga binne ta a komai ba, don yawan fushin nata ma na rashin faÉ—a mata akan lokaci ne.
Ta zubawa dining ɗin idanu ganin bai taɓa komai ba ta tattare ta nufi kitchen ta saka a
microwave don bai lalace ba, kokarin É—ora mishi wani abin take don ta san shi kam ba zai ci
wanchan ba kawai ta ji an rungumeta ta baya, daga ita har shi sai da suka sauƙe wani
nannauyan numfashi, shiru tayi bata ce komai ba ta cigaba da kokarin aikinta ya É—aga ta chak
yayi ɗakinshi da ita ya sauketa a kan gado yana zama ya riƙo hannayenta duk biyu.
"BoÉ—É—i am...!"
Idanunta ta kawar yayi murmushi mai sauti ya ce
"Na tuba ki yafe ni Afeefah, ba zan iya jure fushinki ba Allah kaÉ—ai ya san wani hali kika jefa ni
daga jiya zuwa yanzu... Please lets talk kin ji?"
Idanunta suka cika da kwallah bai ankara ba ya ji ta fashe mishi da sabon kuka a fili ya furta
"Yaaa Salaam Afeefah...."
Rungumeshi da tayi ya saka maganan yankewa, ya rufeta cikin jikinshi yana shafa bayanta
idanunshi a rufe yana jin zafin kukan nata har ranshi.
"Ki yi haƙuri na saka ki cikin wannan hali, it wasn't intentional ban san yadda zan iya fuskantarki
da maganan bane but am sorry kin ji?"
"Promise me Ya Saraki, ka min alkawarin cewa ba za ka taɓa juya min baya ba, ka yi min
alkawari cewa ba zaka sake ɓoye min duk wani abu da ya shafe mu gabaɗaya ba, i felt hurt
zuciyana ya kwana yana zafi da raÉ—aÉ—in jin zancen aurenka ba tare da na sani ba"
ÆŠago fuskarta yayi yana share mata hawayen da hannayenshi biyu cikin karyayyen murya yace
"I promise Afeefah, na miki alkawari in shaa Allahu. Ki yi haƙuri i didnt meant to hurt you that
badly dubi fuskar ki yadda yayi looking so tired and pale sbd zubar da hawaye"
Wani hawayen ne ya gangaro sai ya runtse ido yayi shiruu.
Shesheka ta ja ta sa bayan hannunta ta share wani ya sake zuba ta sake sharewa looking cute
nd sad at the same moment.
"Ka yi haƙuri i couldnt control my emotions ba laifina ba ne, am jealous kishi nake ji in na tuna
nan da kwanaki kadan zan raba ka da wata, za ka shaki kamshinta ba nawa ba, za ka hada jiki
da ita.... Am sorry"
Duk ta rasa yadda zata yi bata san tana da irin wannan kishin ba kuma ruwan kaunar da ya
zuba mata ya sa take jin shigo da wata duniyar su zai yanke mata wannan ƙauna.
Jikinshi ya janyota zuciyarshi na tsananta zafi ya kasa magana, ita kuma ta zaci shirun da yayi
ita ce take ɓata ranshi cikin kuka tace
"ka taya ni Adu'a Allah ya sassauta min abin da nake ji Ya Saraki, am just jealous because I
love you, angry because all i care about is you a lokaci guda kuma am scared because am
afraid of losing you"
ÆŠagota kawai yayi ya haÉ—e bakinsu don kukan ya gama hawa kanshi, wani irin deep Kiss yake
yi mata da tun bata amshi signal É—in ba har ta amsa, a iya romance ya tsaya sai da ya tabbatar
jikinta yayi laushi ainun fatarshi da nata na a manne da juna yana shafa bayanta a hankali suna
sauƙe numfashi zai yi magana ta riga shi muryarta chan ƙasa tace
"I wanted to be the only one to tells you I love you, wacce za ta haÉ—a miyaun baki da kai,
touches your skin and feel you inside me sai dai kash! kana naka ne Allah na nashi, Kana da
damar auren mata har huÉ—u tunda kana da halin hakan kuma kana da lafiya, abu daya zan roka
daga gareka Ya Saraki kar ka daina so na don Allah zuciyata fashewa zata yi".
Yana shafata tana sake yin lub jikinshi ya shiga furta
"Afeefah ki yarda da ni, babu wata kishiya da zuciyar Ryan zata iya yi miki a soyayya domin ke
É—aya jal ta sani kuma ke kaÉ—ai ta aminta da ki ja ta duk inda kike so, da ke kaÉ—ai ta aminta a
matsayin Abokiyar rayuwa ba ni da yadda zan yi ne da babu dalilin da zai sa in amince da batun
zarah amma ba zan iya watsawa mahaifina ƙasa a ido ba alkawari ne da aka yi tun ban san
kaina ba, amma in har za ki cigaba da wannan kukan komai zan iya yi ciki har da barin wannan
gid..."
ÆŠagowa tayi ta haÉ—e lips É—insu da kanta sai da ta bashi kyakyawar Kiss kan ta kalli idanunshi
hannunta na a fuskarshi shima idanunshi zube cikin nata da suke a rine tace
"Kar ka ce komai, ni da kai duka karkashin ikon mai martaba muke dukkanmu uba ne shi a gare
mu da magana kawai zai yi mu cika, sannan aure ba haramun bane idan yana cikin ƙaddararmu
ina roƙon Allah ya ba ni haƙuri da juriya ya kuma kawo mana ta gari wacce za mu haɗe kai mu
zauna mu kula da kai gabaÉ—aya, don haka Allah ya nuna mana lokaci ya bamu zaman lafiya
gabaÉ—ayanmu"
Ta ƙarasa tana komawa kan kirjinshi ta kwantar da kanta tana mayar da hawayen da suka cika
mata ido.
Matseta yayi a jikinshi kawai bai ce komai ba, sun jima a haka don bacci ne ma ya É—auketa shi
kam bai iya yayi baccin ba damuwar da ta shiga ya tsaya mishi ainun ya san ba komai bane sai
zallar soyayyar da take mishi, lumshe ido yayi kawai sai ranar da take ba Mammi da Abeeha
labarinta ya faÉ—o mishi the way she was deeply hurt nd depressed anya ta chanchanci raba
farin cikinta guda É—aya jal da wata? Yayi adalci kenan idan ya iya haÉ—a jiki da wata mace ba ita
ba? Numfashi ya sauke mai nauyi ya mirginata kwance ya ja mata bargo kan ya sauka ya dauki
shirt ya saka ya nufi kitchen.
Breakfast ya samar mata bayan ya gama ya kai har kan gado ya ajiye kan ya shiga shafa kanta
zuwa fuskarta cikin tattali da kulawa har ta buÉ—e ido, murmushi ta mishi ya mayar mata
"Tashi ki ci abinci BoÉ—É—i"
Miƙewa tayi zaune tace
"Brush tukuna bakina babu daaÉ—i"
"Ba dole ba na tabbatar through out jiya baki ci komai ba"
"kaima ai na ajiye maka baka ci ba i was disturbed"
"Toh ba fushi kika yi da Sarakinki ba..!"
Yayi maganan cikin muryarta ta saki dariya ya É—auketa zuwa bayi tare suka yi brush suka dawo
tana bashi yana bata har suka koshi.
Wanka ma tare suka yi abin su yana ta takalarta tana ture shi, suka fito ta shirya shi kan suka je
É—akinta ya taya ta shiryawa.
"Bari na je nayi gaisuwa na dawo"
"Ki bar gaisuwan nan babu inda zaki a sake bata miki rai a banza"
Idanu ta ware
"An taɓa fushi da iyaye ne Ya Saraki? Iyaye musamman uwa ita kaɗai ce take mantawa da
kanta yayin da take yiwa danta Adu'a ita a wurinta idan danta yayi nasara itama ta yi, Na san ka
rasa Mammi ka kuma tabbatar babu zafi da ciwon da ya kai na rashin mahaifiya. Ciwo ne da
baya taɓa goguwa har abada, zaka yi fata za ka yi adu'ar ko da ganinta sau ɗaya ne a yayinda
kasa ya rufe idanunta a sannan kuma babu halin hakan, Uwa garkuwa ce ga dan da ta haifa,
Ya Saraki in na ce maka ga kalar kukan da nayi na maraici ba zaka yarda ba, duk raÉ—aÉ—in da
zan fada maka akwai ba zaka fahimta ba wani lokacin Allah ya sanya albarka daga bakinsu
kawai kake nema ba zaka samu ba, Allah ya umurcemu da kyautata musu iya iyawa a sadda
suke raye ni ka ga ban samu wannan damar ba, ko sanin su ban yi ba tsakanina da su Adu'a
ashe ba zaka amfani wannan damar ba? Don Allah Ya Saraki ka sake tunani akan hukuncin da
zuciyarka ke aikatawa, Allah ya sasanta tsakaninku cikin sauƙi"
Shiru yayi ganin kaman zata ɓata mishi rai ta tashi ta fice tana ce mishi sai ta dawo ya bita da
kallo kawai bai ce komai ba.
Sashen Ammi ta fara zuwa suka gaisa ta É—an jima suna hira da Zarah da Aisha kan ta wuce
sashen Fulani Adama.
"Barka da safiya Mama!"
Tana hakimce ta amsa idanunta na scanning Afeefar ciki da bai kallon da ya sa taji duk ta
tsargu kan ta amsa.
"Lafiya ƙalau, shi mijin naki kam isar shi ta kai ya share sama da watanni a Masarautar nan bai
taɓa zuwa inda muke ba sai dai mun haɗu a hanya ko? Uhm ko da shike ba ke ya kamata na
yiwa zancen ba mai martaba ne ya É—aure mishi kugu dole"
Shiru tayi don bata san me zata ce ba, kiran hadimarta tayi
"Ke Rahane kawo mata abin taɓawa"
"Ai mama da ta barshi yanzu na karya kenan na fito"
"Dama na lura baki taɓa cin komai na ɓangaren nan ba, ashe kema baki daukeni uwa ba
kenan... ai shikenan sai gaisuwar ma a barta kawai Allahn da bai bamu 'ya'yan ba yana sane da
mu, na ji labarin babu abinda bakya ci a sashen FaÉ—imatu nan ne ba zaki ci komai ba? Yayi
kyau"
Bata san Meyasa take mata maganganu haka ba, duk sai ta rikice ma tana tuna gargaÉ—in
Rayyan akan kar ta ci komai na gidan kuma dai tana cin na Ammi, wani zuciyar yace ta
gudarwa kanta matsalar Fulani Adama ta ci kawai ai Rayyan ba zai sani ba kuma ma kindirmon
da aka kawo mata fari tas kwance a ƙwarya yayi matukar bata sha'awa don haka ta janyo ta
dauki ludayi ta shiga sha, sai da ta sha dayawa ta ture tayi godiya kan ta miƙe ta bar sashen.
Yinin ranar suna tare da Rayyan yana sake nuna mata ita kaÉ—ai ce tauraruwar zuciyarshi yana
cika ta da kauna don ko girkin rana da dare ma ba ita tayi ba, bayan sun gama cin abincin dare
tana kwance kanta akan kafafunshi suna ma kallon wani movie ne yana wasa da gashinta ya
shiga jin hannunshi na jikewa musamman in ya kai ga goshinta, shafa goshinta yayi yana kiran
sunanta ta amsa
"Lafiya kike zufa haka? Duk irin Ac dake aiki a parlorn nan?"
Tace
"Nima ban sani ba kawai dai cikina ke dan murda min kadan kadan ba sossai ba"
"Mp ne? Amma ai bakya ciwon cikin priod pain tashi mu gani ko mu tafi asibiti?"
Ta girgiza kai
"Ba wani sosai bane ba fa zai daina Yaya"
Ganin ta ƙi tashi ya sa ya kai hannunshi yana shafa mata cikin a hankali.
Mutsu mutsu ta fara duk ta kasa kwanciya wuri guda ita kaÉ—ai ta san azabar da take ji wanda
rashin son tada mishi hankali yasa take ta daurewa, yana kula da motsinta sai gani tayi ya
É—agata ya kai hannu ya kunna hasken parlorn tarrr, ganin idanunta ya tabbatar mishi da ba
ciwon wasa take ji ba.
"Tashi mu tafi Asibiti"
Ya miƙe yana riƙo ta bata yi musu ba ta miƙe tsaye sai dai abin da taji yana bin kafan ta ne yasa
tayi saurin kallon wurin shima ganin yadda ta razana sai ya kai idanunshi wurin.
"Jini??"
Yayi maganan a É—an rikice kaman kuwa ana jira su gani cikin nata ya shiga kartar da bai yi ba
da farko, damke hannunshi tayi tana jin azabar na shirin kasheta tuni ta fita hayyacinta a rikice
ya É—auketa suka fice daga parlorn da gudu GaabÉ—o ya je ya buÉ—e mishi mota ganin yadda suka
fito ko tukin ba zai iya ba yana rike da ita a baya yana shafa cikin yana mata sannu sai juye juye
take tana zub da hawayen da bata san suna ma zuwa ba, hankalinshi ba karamin tashi yayi ba
jinin da bai san daga ina ba kuma na me na ta wanke su sai sannu yake maimaita mata kaman
ya taya ta kukan a haka suka isa asibiti aka yi emergency da ita don har ta fara sumewa.
A masarauta kuwa Ammi na zaune da su Aisha aka kawo musu labarin dukkansu hankalinsu ya
tashi suka miƙe tsaye suna tambayar
"Me ya sameta?"
Babu wanda ya san amsar sai kiran me martaba da Ammi tayi tuni ya bata umarnin tafiya suka
fito a ruÉ—e sai ga Ameer tare da shi da wasu securities suka bi bayan su Afeefar cike da adu'ar
Allah ya sassauta koma menene ya bata lafiya cikin gaggawa..
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*Don Allah ku yi min uzuri na so in bi comments in amsa kowanne amma na kasa, bana jin
daaÉ—i ne kar ku yi expecting biyu gobe in na iya na yi É—ayan ma Alhamdulillah!*
*56*
Afeefah ta matuƙar jiggata kan aka samu aka shawo kanta da kyar, shi dai ba zai ce ga abin da
yake yi musu a ɗakin ba yana tsaye ne kawai saboda matsayin shi na likita kuma mai muƙami
da ba zasu iya kora ba, hannunshi na rike da nata yana tsaye kyamm idanunshi na zube kan
fuskarta wani irin ciwo ne wannan lokaci É—aya? Me ya sameta? Babu kalar sake saken da bai yi
ba.
Kalaman da ya ji likitocin suke yi cikin harshen turanci cike da ƙwarewar aiki ya ƙara daure
mishi kai ya jefa shi cikin tunani da damuwa lokaci É—aya.
"Sir da ka je ka sauya wannan kaya saboda duk sun yi stains, za tayi bacci sossai kila sai zuwa
midnight ta farka sai a sake running wasu tests"
Wani likitan ya faÉ—a bayan ya dafa kafaÉ—ar Rayyan da ya jima cikin duniyar tsoro, mamaki da
kaÉ—uwa.
Hannunta ya zame yana kallon kayan da aka kawo za'a sauya mata da wasu towels da za'a
goge mata jikin da ya ɓaci Dukda mata ne karɓa yayi suka fita, shi ya goge mata jikin tas ya
sanya mata kayan asibitin riga da wando ne kan ya gyara mata kwanciya ya duba tafiyar ruwan
har lokacin fuskarshi Jajazir, kwakwalwarshi ya ƙi hutawa da saƙe saƙe a haka ya fito daga
É—akin sai ya tsaya chak yana kallon Ammi da take kallonshi itama a zaune.
Jikinshi ya bi da kallo yana tuna jinin É—an shi ne nan ko É—iyar shi, wani irin zafi da bai san ya zai
fasalta ba na taso mishi a cikin zuciya bai san ya nufi Ammin ba ya samu wuri a gefenta dab ya
zauna bai ce komai ba kanshi a ƙasa, dukkansu sun yi mamaki har ita kanta amma ta danne
tace
"Sameer ya jikin Afeefahn?"
Ya yi shiru na seconds yana hadiye wani irin miyau ya ce
"Da sauƙi tana bacci"
Wannan ne karo na farko da maganan da ba gaisuwa ba ya shiga tsakaninsu hakan ya faranta
mata kwarai amma damuwar halin da Afeefah take ciki bai barta ta nuna ba.
"Me ya sameta haka?"
"Ammi Afeefah ta ci wani abu a sashenku da safe?"
Abeeha da har hawaye tayi ta zubarwa tace
"A'a Yaya ko ruwa bata sha ba tace ta ci abinci kenan ta fito"
"Me ya faru da ita haka?"
Ameer da Ammi suka tambaya a tare, haƙorinshi ya sa ya datse lip dinshi na ƙasa kan ya saki
zuciyarshi na tafarfasa yace
"Æari tayi... Zubar da shi aka yi! ta yi misscarrage ba tare da duk mun san akwai ma É—an ba.."
"Innalillahi wainna ilaihi rajiun..."
Abinda duk suka faÉ—a a tare kenan, Ammi ta sanya hannunta ta kama nashi sai ya kalleta
"Ammie ɓari biyar kika yi?"
Ta gyaÉ—a kai bata ce komai ba
"Duk wannan azabar da Afeefah ta sha haka kika sha?"
Ta sauke numfashi tace
"Na sha wanda ya fi shi ma Sameer, shi ina mai tabbatar maka azabarshi zai iya É—ara na
haihuwa. Ka je ka sauya kayan nan haka kar ƙarnin jinin ya zauna maka a jiki"
Idanunshi ya É—aga sama yana mayar da emotions dake taso mishi ya kalli jinin
"ÆŠanki É—an watanni biyar ma kin rasa shi ko Ammi?"
Nan ma ta gyaÉ—a mishi kai.
"Haka zafin yake?"
Bata danne ba tayi murmushi mai ciwo tace
"Duk wanda za ka ji daban yake da na uwa Sameer, uwa ce kaÉ—ai za ta iya fasalta wannan
zafin... Idan har ka ji zafin fitan É—an da baka ma san da zamanshi ba ka fasalta da Aliyu da na
rasa sai da na raini cikinshi na watanni tara na haife shi na shayar dashi na ga haƙorinshi na
farko, na ga murmushinshi na farko na ga zamanshi kan Allah ya karɓi abin shi..."
Hawaye ne ya zuba mata a lokaci ɗaya da Ryan, shi likita ne amma bai taɓa kula da abinda ya
shafi ciki ko haihuwa ba don duk abu da mata a baya ba kaunarshi yake ba, cikin jannah da
Abeeha duk ba zai ce ga yadda Mammi tayi ba, idan wannan bari ya saka shi jin irin wannan
zafin ya Ammi ta ji?
Bayan duk wahalar kuma aka yi ta yunkurin kashe shi mahaifinshi bai É—auki kwakwaran mataki
da zai sa hankalin uwar tashi kwanciya ba, motsin da suka ji yasa duk suka É—ago sai ya ga mai
martaba ne da dogarai biyu don ya kasa zama dole ya biyo bayansu. Shima kuma a yanzu ya
fahimce shi dole ba zai so rabuwa da É—an shi guda da Allah ya bashi bayan tsawon shekarun
da ya É—auka babu haihuwa ba.
Dukkansu basu da laifi, uwar da ta zama distressed ta haɗa baƙin ciki, damuwa da wahala duk
lokaci guda zai ga laifinta ko uban da baya so ya ga yayi nisa da gudan jinin da yake mararin
samu? A yanzu ya fahimci damuwar Ammi ta sanadiyar Afeefah ya ji a ranshi zai mata uzuri ya
ji a ranshi kaman Allah ya riga da ya rubuta ne Mammi ce zai yi rayuwa da ita har mutuwar ta
ba Ammi ba, kaman yana ji a ranshi cewa Adu'ar Ammi ce Allah ya karɓa ya tura mishi Mammi.
Ta wani ɓangaren he's grateful na barin shi masarautar don da bai bari ba da bai san Mammi
ba idan kuma bai santa ba da bai samu Afeefah ba the 2 most important persons da Allah ya
bashi su as his greatest gift.
Ƙasa ya kai ya riƙe hannun Ammi ya ɗora fuskarshi a kai ya ce a hankali
"Ammie ki yafe min, ki yi haƙuri na tuba!"
ÆŠumin hawayenshi suna sauka ne da nata, kuka take sossai na farin ciki Allah ya amshi adu'ar
ta, Allah ya karkato mata da hankalinshi cikin sauƙi. Ɗago shi tayi ta miƙe tsaye kawai ta
rungumeshi Dukda tsawon da ya fita, duƙawa yayi suka rungume juna yana jin dumin
mahaifiyar tashi na ƙara karya zuciyarshi, da kyar ya danne kukan da ke taso mishi.
Mai martaba ya dafa shi yana dan buga kafaÉ—ar shi zuciyarshi fari tas na ganin abinda ya jima
yana fata shima, komai ya wuce don Ammie É—ago shi tayi ta ce
"Sameer na yafe maka duniya da lahira baka yi min komai ba, ni ya kamata ma in nemi
yafiyarka da wahalan da na saka ka... Haƙiƙa na yi kuskure mai girma wanda Allah ne ya dube
ni ya raya min kai kan tafarki amma da ban san da wani ido zan isa ga mahallici na ba da
rayuwarka ya salwanta. Ka yi haƙuri"
Kai ya gyaÉ—a.
Mai martaba ya ce
"Ya mai jikin yanzu?"
Cike da girmamawa Ammie tace
"Alhamdulillah Taƙawa tana bacci ne sai dai mun rasa ɗan cikin"
"ɓari tayi? How?"
Juyawa Ryan yayi ya fita Ameer ya bishi, Ammi ce ta mishi bayanin suma basu sani ba amma
da yake asibitin kuÉ—i ne kuma kwararrun likitoci ne suka duba ta a bincikensu sun tabbatar da
abu ta sha yayi sanadiyar zuban cikin.
"Tirƙashi! Kar fa tarihi ya maimaita kanshi!"
Shiru Ammi tayi ba zata so wa Afeefah wannan wahalar ba, Amma Allah ubangiji ya sa lokacin
tonon asirinsu ne yayi haƙiƙa adu'ar da take ta tabbatar ba zai faɗi ba Allah sai ya bi mata
hakkin cutar da ita da aka yi.
Suna nan zaune sai ga Ameer da Ryan sun dawo ya sauya kaya zuwa riga da wando english
wears hannunsu rike da ledoji manya da alama ba gida ya je ba, ya dubi mai martaba.
"Abieey ya kamata duk ku je ku huta da safe Ammie sai ta dawo"
Sun amince don a yadda yake sun san ko me zai faru ba zai amince wani ya kwanan mishi da
mata ba don haka bayan Ameer ya miƙa mishi ledar suka yi sallama har Abieey ya juya Ryan
ya ce
"Abieey"
Sai ya juyo
"Abieyy ina so ka min wani alƙawari guda ɗaya"
Kai ya gyaÉ—a
"Abeey ka min alkawarin duk wani mai hannu a matsalar da Afeefah ta shiga zai biya
kwatankwacin wahalar da ta sha kuma ba zaka hana ni yanke hukunci akan hakan ba! Idan
kuwa har link É—in wannan laifi ya haÉ—u da na mahaifiyata wanda yayi sanadiyar nesanta ni da ku
gabaÉ—aya....."
Sai ya danne haƙorinshi da ƙarfin gaske yana dunkule hannu alamar bai ma san me zai iya
aikatawa ba.
Numfashi mai martaba ya sauke
"In shaa Allahu za'a yi duk abin da ya kamata ai wanda ya kashe mutum ba shi da sauran
alfarma, amma yanzu ka yi focusing kan lafiyarta tukun"
Juyawa kawai yayi ya nufi É—akin don ya faÉ—a ne ma kar mai martaba yayi yunkurin hana shi
daukar mataki idan har abinda yake zargi ne.
Wuraren karfe É—aya na dare ta farka, yana zaune hannunshi É—aya a cikin nata idanunshi zube a
kanta ta buÉ—e idanu, ta lumshe ta sake buÉ—ewa a hankali yace
"BoÉ—É—i kin tashi? Sannu!"
Ta lumshe ido alamun amsawa duk jikinta ba kwari a hankali tace
"Me ya same ni? Cikina bai taba irin wannan ciwo ba na É—auka mutuwa zan yi Ya Saraki..."
Goshinta yayi pecking ya É—ago yana shafa kanta yace
"Ba yanzu ba Afeefah, ba za ki mutu ki bar ni ba"
Za tayi magana sai ga Dr da wasu nurses sun shigo, bai motsa ba har suka iso kanta likitan
yayi ta mata tambayoyi tana amsawa kan nurses É—in suka dibi jininta suka mishi sai da safe
suka fice.
Tsabar kyaun asibitin da tsarin shi ba zaka ce É—akin asibit suke ba don ya fi yanayi da É—akin
Hotel É—aukar ta yayi gabadayanta yaje ya mata wanka suka dawo É—akin, tea ya hada mata ya
hau gadon yana bata a hankali har ta ce ya isheta ta sha wasu magunguna kan ya dube ta
"GabaÉ—aya yau me kika ci da ban sani ba?"
Tunani ta tafi amma dai ta san duk abinda ta ci a ranar shi ne ya girka, gabanta ne ya faÉ—i ta
ɗago tana kallonshi ganin kallon da yake mata na son fahimtar yanayinta ya sa ta kasa ɓoye
abin da ta so ɓoyewan muryarta na ɗan cracking tace
"Na sha kindirmo a sashen Mam..."
"Afeefah Ban gargaÉ—eki akan cin komai a gidan chan ba?"
Calmly yayi maganan trying really Hard to control his self sanin ita karan kanta ta jiggata amma
tana fara cewa
"Ka yi haƙuri maganganunta ne suka...."
"To hell with the maganganun Afeefahhh"
Ya katse ta da wani irin tsawa.
"Raina ni kika yi ko kin dauka ban san me nake ba ne da zan ce kar ki yi abu kiyi? Kin fini sanin
me nake yi ne? Ke ga ki mai sanyin zuciya ko? Toh sai ki zuba ruwa a ƙasa ki sha tunda kin
yiwa kanki asarar É—an da ko sanin zamanshi ba mu yi ba, kuma kar ki zaci alhakin akan waenda
suka aikata hakan ne har ke tunda na gargaÉ—eki..."
A razane take kallonshi bata san hawaye sun fara cika idanunta ba sai zubowar su taji ta kai
hannu ta dafa cikinta muryarta na rawa sossai ta ce
"Æ..É“ari na yi?"
Ganin yayi shiru ta sake cewa
"Da gaske ɓari na yi Yaya? Wlh ban sani ba! Ban san akwai shi ba da ban sha ba, kawai
kindirmon ya...ya ba ni sha..."
"Kin yi min shiru ko sai na tsinka miki mari Afeefah???"
Baya ta matsa don yadda ya harzuko É—in nan duka ne kawai ya saura bai kai mata ba jikinta sai
ya fara rawa, kuka take yi sossai ya cigaba da masifa cike da bacin rai
"Ban gaya miki duk abinda kika ji ya baki sha'awa ki sanar da ni ko menene ko a ina ne zan
samo miki ba? Ko ban faɗa miki ba??? Amma da yake kunnen ƙashi ne da ke ga abin da kika
janyo...."
Cikin kuka da rashin madafa take furta
"Am sorry...! Ka yi haƙuri na yi kuskure... Ban sani ba ne.."
Bai tanka ba sai ficewa da yayi daga É—akin gabaÉ—aya don ya cigaba da tsayuwa ma karya mishi
zuciya zata yi.
Kuka ta fashe dashi tana ambaton sunan Allah, wato ana cewa gidan sarauta na da kunne ashe
ba kunne ba kadai har da ido? Cikin da ko su iyayen basu sani ba wasu sun hanga har sun
cutar musu da shi? Laifinta ne wlh laifinta ne ta yi kuka har baccin wahala ya É—auketa tunda a
magungunan akwai na saka bacci bata ga Shigowar shi ba, shi ko yana zaune a reception ya
jingina bayanshi kanshi a jikin gini kafafunshi a harde yana saƙe saƙe don abin nan ba zai taɓa
tashi a banza ba.
Washegari ko da Afeefah ta farka bata ganshi asibitin ba sai su Ammie Aisha da Adda Abeeha
da kuma wasu hadimai, yanayinta duk ba daaÉ—i suka raka ta bayi suka fito tayi wanka suka
taimaka mata ta shirya kan suka zuba mata abin kari bata da wani apetite in ta tuna haukan da
tayi sai taji hawaye na zubo mata, Ammi ce tayi ta bata baki dai har take jin zuciyarta yayi sanyi.
Abin mamaki ta ƙara kwana biyu a kwance har wankin cikin aka yi Ryan bai dawo asibitin ba ko
ma ya dawo bata sani ba don idanunta dai basu ganshi ba hakan ke nuni da cewa ba fushin
wasa yayi ba, dare haka zata yi kukanta har tayi bacci da safe ayi ta tambayar me ya samu
fuskarta tace babu komai a kwana na uku aka sallame ta suka dawo masarautan kai tsaye
sashenta suka kaita nan ma baya nan.
Wata elderly woman Ammi ta turo tana kula da ita musamman cimarta don tana bukatar
abubuwan da za su dawo mata da kuzari da kuma karfin jiki, ita dai duk abin da ta bata ci take
kuma tana kiyaye dokokin matar tunda har Ammi ta ce mata da sanin Ryan ta turo matar sai
bata ɗaga hankali ba, Dakon dawowanshi tayi tayi a daren sai dai abin mamaki har wurin ƙarfe
1 na dare ya shigo sashen É—an kallonta yayi ya É—auke kai tana sanye da riga da zani sai É—an
kwalin da tayi simple dauri da ya bayyana gashinta ta baya bayan dan kunne babu wani
accesories da ta tula, bata ji sallamar shi ba kenan ciki ciki yayi abin shi ganin zai wuce ta miƙe
tsaye
"Ya Saraki...!"
Chak ya tsaya, ta tako a hankali ta dawo bayanshi muryarta na rawa ta ce
"Don Allah ka yi haƙuri, ba zan iya cigaba da jurar fushinka ba. Ka gafarceni na san na yi
kuskure don Allah ka yafe min"
Idanunshi ya runtse na seconds kan ya buÉ—e ya cigaba da tafiya bai ce mata komai ba,
bayanshi ta bi tana kuka mai sautin dugunzuma hankali, share ta yayi ya cire kayanshi tsaf ya
É—aura towel ya shige bayi yayi wanka yana fitowa ya ganta tsaye again har lokacin bata bar
kukan ba, zuciyarshi ne ya karye yana jin kukan har cikin kanshi.
Gaban mirror yaje yana goge jikinshi da ƙaramin towel ya ɗauki bodyspray ya feshe kirjinshi
dake bayyane dashi yana ƙoƙarin Juyowa kenan yaji ta kwanta a bayanshi ta saka hannayenta
a kugunshi tana kuka still har hawayenta na É—iga a fatar bayanshi, kasa controlling kanshi yayi
ya juyo gabaÉ—aya ya bata kyakyawar runguma.
"Kayi haƙuri ba zan sake kuskuren tsallake maganarka ba, fushinka na sake ɗaga min hankali
don Allah ka y...."
Fuskarta kawai ta ji ya É—ago ya haÉ—e lips É—insu yana bata sumba mai zurfi baya baya yake yi da
ita har jikin gini, ta sanya hannayenta biyu ta zagaye wuyanshi tana bashi support, sai da ya gaji
don kanshi ya raba bakin nasu suna jan numfashi a hankali hankali ya haÉ—e goshinta da nashi
yayi pecking lips ɗin still don baya taɓa gajiya da su a hankali yace
"Kar na ƙara ganin kin zubar da hawayenki wanda kika yi a baya sun isa, Allahn da ya bamu ba
tare da sani ko shawarar mu ba zai bamu wani. Mu sa a ran mu haka ya kaddara wannan É—in
ba mai zuwa ba ne"
Kai ta gyaÉ—a mishi ya ja ta bakin gadon ya taya ta cire kayanta tas ya É—aura mata towel don su
sun fi gane kwana a haka, ya ja ta suka kwanta hannunshi na yawo jikinta cike da kulawa a
haka suka yi bacci dukkansu kowa da abinda yake saƙawa.
Washegari da safe kan ma su tashi An shirya musu abinci wanda daga sashen Ammie ne,
kuma ta yi mamakin ganin ya zauna suka ci tare don duk zamanta a asibiti Ammi ke mishi girki
da kanta, bayan sun gama suka fito a tare gaisuwa yana sanye da wani Beige yard mai taushi
da kyaun shi ya bayyana tsurar tsadarshi tana sanye da straight skirt and blouse da aka yi rigar
da wani yadi mai sulɓi green za ka zaci fitted gown ne mai combination da lace idan baka sani
ba saboda yadda ya zauna mata, alkyabbarta mai kauri ne hakan ya sa bata damu ba kuma
akwai gyale Kasar shi hannunshi na riƙe da nata suka nufi sashen na Ammi, sai mamaki take
da tunanin yaushe suka shirya kuma? Amma a gefe É—aya farin ciki ne ya cika mata zuciya da
har ta kasa boyewa sai murmushi take zabgawa yana kallonta bai ce komai ba har suka shiga.
Sun samu Ammi zaune cikin kujera Abeeha da Aisha na karyawa yayinda Ameer ke zaune
yake jan su da hira da wasa, ganin su ya sa fuskar Ammi cika da fara'a, kai tsaye gangarta yaje
ya zauna Afeefah ta samu wuri a ƙasa ta zauna tana ta murmushi Allah ya gani shiryawarsu
wani abu ne mai muhimmanci a gareta da bata taɓa saka goshinta kasa ba tare da ta yi mishi
adu'a ba kuma Alhamdulillah ko a yanzu waninsu zai faÉ—i ya mutu ta tabbatar ba za su bar abin
nadama ba.
Gaisuwa suka yi tana tambayarta jikinta tace da sauƙi, suka gaisa da su Abeeha yayinda duk
suka gaishe shi ya amsa cike da izzarshi ta jinin sarauta don fuskar a kame take tun abin da ya
faru bai wani sake ba, sun jima anan kan yace ta tashi su tafi.
Babu musu ta miƙe suka fice yana riƙe da hannunta da dumbin mammakinta sai ta ga ya nufi
hanyar Sashen Fulani Adama, gabanta ne ya shiga dokawa amma ganin babu fuska ya sa bata
yi magana ba har suka isa. Tana zaune a parlornta ta yi zurfi cikin tunani sai ganinsu tayi ita
kanta ganin Rayyan mammakinta ya kasa ɓoyuwa har bata san ta miƙe tsaye ba sai da yayi
murmushi ya ce
"Mama barka dai mun zo ba sanarwa dole ki ji mamaki"
Yana maganan yana zama, itama komawa tayi ta zauna tana kakaro murmushi
"Gaskiya kam na yi mamaki ashe baka manta hanyar sashen nan ba?"
"Ɗa bai taɓa mantawa da uwa ba ai Mama, Fatan kina lafiya?"
Idanunta ta kawar don wallahi kallon da ta ga yana mata a take ya saukar mata da wani irin
faÉ—uwar gaba har tana jin zufa na keto mata amma ta dake.
"Lafiya Ƙalau, ashe kuma abin da ya faru kenan? Allah ya mayar da alkhairi"
Afeefah da itama karon na biyu bayan zarah ta ji ta tsani matar ta gaisheta da kyar, ta amsa
basu jima ba ya miƙe har sun nufi fita ya juyo ya sake kallonta ya saki murmushin da ya sake
kaÉ—a mata yar hanji.
Jeka ka dawo ta shiga yi hannunta da waya tana ta danna kira sai dai karo na sama da É—ari da
wani abu kenan daga jiya zuwa yau bata samu Layin ba, yaraf ta koma ta zube tana dafe
goshinta dake sara mata...
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*57*
*Ƙarshen Alewa...*
Satin da ya biyo bayan faruwar ɓarin ba zata ce bata ji daaɗinshi ba sai dai ta kula tarin
soyayyar da yake nuna mata ya ragu da kaso talatin cikin É—ari wani sa'in ma sai ta ga kaman ya
koma mata asalin Rayyan É—in shi na baya da ta sani, Dukda bai rage ta a komai ba na kulawa
sai dai tana ji a jikinta har yanzu bai gama sauƙa ba wanda ita kanta in ta tuna sai ta yi kuka, ta
fara lectures online kuma yana bata taimako yadda ya kamata ta ɓangaren, ta zuba idanu ta ga
sun koma yadda suka faro amma ta kula shi bai san zuru ba dole ta sake shirin bashi haƙuri.
Sannan a kwanakin ya kan daÉ—e a waje wani har ma tayi bacci bai dawo ba sai dai ta farka ta
sameta kwance jikinshi, a yau ta yi niyyar sake tunkararshi ta sake bashi hakuri don bata
kaunar wannan silent treatment É—in nashi ko kaÉ—an, karfe goma ta fito wanka ta zauna ta É—auki
lokaci kwarai wurin sake gyare jikinta tsaf ta haÉ—a wani magani da wannan mata da Ammi ta
turo mata take bata da madara ta sha, dama ta dafa mata goron tula ta zuba zuma shima ta sha
kan taje ta fara neman abinda za ta saka, wani farin strapless lace bra mai haÉ—e da wando
wanda ma kai tsaye zaka iya kiranshi bumshort ta saka ta É—ora rigar saman da ya bayyana
duka fatar jikinta don bashi da maraba da raga.
Gashinta ta gyare tsaf ta fito ta nufi kitchen, a yadda dare yayin nan ta san ko ya dawo ba sake
cin komai zai yi ba sai ta haÉ—a fruit salad ta cika mishi madarar ruwa ta saka a frigde ta fita ta
kara karfin Ac ta sake kunna turarukan wuta a duka burners dake kusurwan gidan sai da ta ba
kowanne mintuna biyar taje ta kashe kamshin na fita a hankali ba tare da wani hayaƙi ba, tana
shirin nufar É—aki ta ji ya turo kofar parlorn sai ta tsaye nan tana kallonshi.
Numfashinshi ne ya so barin shi na wucin gadi idanunshi manne da jikinta yana bin ta da wani
irin kallo da ya sakata sakin murmushi ta nufo shi a yangace, gani yayi in ta cigaba da tafiyar
kan ta iso za ta iya sumar dashi yasa ya yunkura kawai ya nufeta sai janta kawai yayi ya
rungume yana sauke fuskanshi cikin wuyanta da wani irin salo ya sauke numfashin relief,
ƙanƙameshi tayi kaman yadda shima yake sake riƙe ta cikin kirjinshi hannayenshi na sake
matse ta.
"you are driving me crazy My Love"
Murmushi mai sauti tayi, ta raba hug É—in tana sunne kai wai ita a dole kunya hakan kuma na
sake tsuma shi tace
"You are welcome My king, ka bar ni ina ta kewa"
Ya saki murmushi
"Daga yau in shaa Allah na gama barinki da kewata mu je ki taya ni wanka"
Ya riƙe hannunta tace
"Ba ka jin yunwa?"
Yayi pecking bayan hannun nata yana sake bin jikinta da kallon dake rikitata ya furta
"Ke kaɗai nake buƙata a yanzu idan na sameki na ƙoshi"
Tayi murmushi a kunyace ta bi bayanshi zuwa É—aki, a tsakiyar É—akin ta tsaya chak ya waigo ya
kalleta
"Menene?"
"Na tuna! ba fushi kake yi da ni ba har yanzu...Na baka haƙuri na baka haƙuri amma ka ƙi ka
haƙura"
Da wani irin salon Shagwaɓa da sanyi tayi maganan, ya lumshe ido yarinyar tana shirin zauta
shi a tsaye da sauri ya buÉ—e idon jin motsinta sai ya ga ta juya zata fita da hanzari ya saka
hannunshi ta cikinta ya dawo da ita baya har kan kirjinshi bayanta ya sauƙa ya sauƙe kanshi
cikin wuyanta yana bata wet kisses da suka sa ta fara kunnuwa don ya mugun sanin weak point
É—inta yace
"wa ya ce ban haƙura ba Boɗɗi? Ai na haƙura..."
A cikin kunnenta yayi maganan chan ƙasa muryarshi na sarkewa. Ba zai iya jurewa har yayi
wanka ba hakan yasa ya chusa hannunshi cikin yare yaren rigar yana shafa duk inda hannunshi
ya sauka a fatarta har lokacin kuma yana wasa da wuyanta da harshenshi.
Cikin whisper yake jefa mata magana a cikin kunne bata ma jin me yake cewa don yadda ya
rikice haka ya rikitata abinda ta iya tsinta shine
"lets make another baby my Queen..."
Kai ta gyaÉ—a ya zura harshen cikin kunnenta daga haka basu ma san sun isa gado ba, sossai
yayi kewanta rabon da ya ji shi a gajimare tun kan tayi ɓari sai ya ji kaman an sauya ta ne,
kaman an kara mata zuma ta haukatashi ta gigitashi a duniyarta sai gashi yana sambatun da
bai ma san abinda yake cewa ba ta bashi gudumawa sossai don itama ta yi kewar shi ƙwarai
basu sarara ba sai da ya tabbatar bayan ya samu natsuwa itama ta samu ya rungumeta cikin
kirjinshi yana sanya mata albarka.
Ta sake shige wa jikin nashi tana murmushin kunya, chadak ya É—auketa suka je suka yi wanka
suka fito cikinta ta shafa
"Yunwa nake ji"
"Afuwan duk na yashe abincin, bari na samo miki wani abu"
Ya faɗa yana kokarin saketa ta riƙe hannunshi
"Just sit bari na É—auko mana fruit salad da na haÉ—a É—azu"
Kai ya gyaɗa ta fice chan ta dawo da bowl mai girma dauke da spoon ciki, hannu ya miƙa mata
ta bashi ya ajiye bedside kan ya janyo hannunta ta zauna kan kafafunshi bayanshi jingine da
jikin gado ya shiga bata a baki sai da ta É—auke kai ya mayar da spoon É—in ta É—auka ta dibo tace
"Haaa"
Murmushi ya saki ya buɗe bakin ta shiga bashi sai da ta kai spoon na ƙarshe ya kai hannu ya
sauƙe towel ɗinta daga sama ɗan tsorata da tayi ya sa ta ɓata mishi lips sai ta Shagwaɓe fuska
yayi murmushi, ta juyo gabaÉ—aya ta raba kafafunta tsakanin nashi tace
"oops lemme help clean your mouth"
Lumshe ido yayi ta kai bakinta ta sude madarar tas za ta janye yace bata isa ba nan suka sake
fara ƙoƙarin komawa ruwa ita ta janye tana dariya.
"Ke ko?"
"Me na yi? Ba kai ne ka ja na ɓata maka bakin ba kuma daga taimako sai sai a nemi zarcewa"
Ya janyota ta dawo jikinshi yana murmushi tace
"Yau saura sati É—aya aurenka ko?"
A É—an sanyaye tayi maganan, yayi pecking goshinta yana kallon idanunta yace
"Ai ina da aure ni"
Tayi murmushi
"Ba nawa auren ba ina magana kan amaryar ka Zarah
"Wace hakan?"
Ta É—an Harare shi da fararen idanunta da ya saka shi sakin kyakyawar murmushi tace
"Ka fa san wacce nake nufi ko baka san sunanta ba?"
"What name? Afeefahhh ita kaÉ—ai na sani, Afeefah kamal Its the only name i learned nd i call.."
Yayi maganan yana lakace hancinta idanunshi na tabbatar mata da sunanta kaÉ—ai shi ya sani a
duniyarshi.
Za Ta sake magana ya haÉ—e bakinsu sai da ya tabbatar ta manta da maganan wata zarah kan
ya zare bakin yana rungume da ita suka yi bacci cikin natsuwa da tarin ƙauna.
Washegari da safe shi yayi mata breakfast don da asuba ma bai barta ba duk jikinta ya mata
laushi, bayan ta karya yayi wanka ya shirya cikin wasu fararen kaya da suka amshe shi ƙwarai
da gaske ga mamakin ta ta ga ya É—auko wani alkyabba silver ya saka da yayi mugun yi mishi
kyau, baki ta saki tana kallonshi sai ya É—auko wani takalmi shima silver da ya fi yanayi da na
saurata ya saka ya saka hula kan ya zauna ya naÉ—a rawani.
"Tabarakallah Masha Allah!"
Ta ambata tana sauƙe numfashi idan ba Allah ba waye? Waye ya isa kera irin wannan jarumi,
santalale kuma kyakyawar namiji haka mai zati da kwarjini? Bayan nan kuma ya É—auka ya bata
matsayin miji! Alhamdulillah ta sake ambata bata san ya iso ba sai hura mata iska da ta ji yayi a
fuska ta lumshe idanu tana sake buÉ—ewa a kanshi hannu ta É—aga a dunkule ta shiga furta mishi
kirari.
"Ado da kanshi ya sara maka ɗawisu...Barden maza in ka fito yaƙi ya kare, mari babban kifi
maganin hadamammu...bangon duniya sun yi iya yinsu sun kasa Huda ka, Allah ya bar mini kai
jarumin jarumaina...!
Mai sarauta da halin girma.
Tauraron sarakai jigon Afeefah
Saraki kai gaba kai musu nisa kamo ka sam sam ba su iyawa sarakai duk suna a bayan ka..!
Allah ya ja da zamanin Ciroman duk duniya Yariman matasan Fombina...kare ka angon
Afeefah"
Sossai yake murmushin da ya sake tafiya da ita ya duƙa yayi pecking goshinta yace
"Duka wannan kirari nawa ni kaÉ—ai Matar masu sarauta?"
"Duk kirarin da zan ma ka wuce nan Sarakina! Allah ya bar mini kai har aljannah"
Ya shafa fuskarta yana kallonta har lokacin cikin towel take ya shafa idanunta da suka sake
haske da sheki zuwa lips É—inta da ya mayar da su cherry Red tsabar yadda ya fitine su ya furta
"Zan fita, ki kula min da kanki har zuwa dawowata kar kuma ki manta da cewa Saraki na ƙaunar
ki... Your eyes, your voice, your smile kai komai da komai i just love everything about you"
Ta sauƙo tana gyara towel ɗin ta ɗauko turare ta sake fesa mishi tana murmushi tace
"I love you more takecare, sai ka dawo"
Kaman kar ya tafi haka ya fice ta koma ta zauna tana murmushi.
Yana fita kai tsaye Fada yayi fuskarshi a haÉ—e ya shiga dogarai suka fara mishi kirarin isowa,
karon farko da ya zo fadan tun naÉ—inshi shi karan kanshi Abeey ya ji mamakin ganinshi haka, a
gaban mai martaba ya duƙa
"Barka da safiya Your majesty..."
Sarkin dogarai zai amsa sarki ya É—aga mishi hannu
"Barka dai Ciroma, ina Fatan lafiya don da ganinka akwai magana fal a bakinka"
"kwarai kuwa Adalin sarki, na zo ne zuwa na musamman a yau... Na zo ne in shigar da ƙara ina
kuma fata wannan sarki mai adalci zai yi mana hukunci daidai da tsarin addini bisa adalci irin
nashi"
Gaban mai martaba ne ya faÉ—i, ya riga ya san binciken da Sameer ke yi amma baya so ko ma
menene a kawo shi gaban fada shi kuma Saraki Yana so ne duniya ta shaida ta yadda kunyar
duniya da mutanen cikinsa kaÉ—ai ya ishe su kan su gamu da na lahira, yana sane yayi hakan
kar ma Mai martaba yayi tunanin Afuwa saboda zumunci ko wani abu...
"Na zo ne in shigar da ƙarar Makama, Madaki da Fulani Adama bisa laifin zamba cikin aminci,
yaudarar masarauta, cin amana, zalunci da kuma kisan kai... Sun cutar da wannan masarauta
kuma sun cutar da sarki tsawon shekaru a yanzu kuma sun cutar da abinda bai kamata su cutar
ba... A Yanzu kan shari'a tayi nisa nake shaida cewa na yanke alkawarin aure dake tsakaninmu
da zuri'arsu don zuri'arsu basu da nagartar amsa sunan sarauta har abada"
Kallon kallo aka shiga yi cike da dumbin mamaki yayinda Makama da Madaki zufa ya shiga yi
musu wanka, gabansu ke faÉ—uwa amma Makama ya dake ya ce
"Wani irin zance kake yi Ciroma? Kar fa ka manta waenda kake zargi da waennan muggan
ayyukan ba tsaranka bane kuma iyaye muke a gareka... Daga dawowarka zuwa yanzu har ka
isa shiga lamuran da baka sani ba? Ka kiyaye don ba za mu yafe sharri ba ko daga waye
kuwa.."
Yayi murmushi ya ce
"Sanin kun taka matsayin iyayen nawa shi yasa na kawo zancen inda za'a yanke hukunci da
wasu ne chan. Hmmmm...."
Mai martaba ya katse shi
"Mecece hujjarka na wannan zargi Ciroma?"
"Ina da tarin hujjoji amma kan nan ina so a gurfanar da Fulani Adama gaban fada a kuma
gayyaci duka matan LaamiÉ—o don duk ya shafe su"
Sarkin gida Mai martaba ya kalla tuni ya fice, duk fadan ana zaune shiru kowa da abin da yake
saƙawa yayinda su Makama ke zare idanu suna kuma haɗa gumi da tsoron abinda wannan
karamin alhakin zai iya yi musu.
"Kaman yadda kuka sani gabaÉ—aya bana É—aga kafa a zalunci kuma ko wanene muddin na
same shi da zalunci na kan hukunta shi ne daidai da laifin da ya aikata ban cire kowa ba,
Ciroma ya shigar da karar Makama, Madaki da kuma Fulani Adama bisa zargin cutar da
iyayenshi da matar shi za mu so jin hujjojinshi don yin hukunci daidai da laifukansu idan kuma
muka same shi da son bata suna ko wasa da hankalin wannan fada shima za mu yanke mishi
hukunci daidai da laifinshi. Muna sauraronka Ciroma"
Gaabɗo ya kalla sai ya miƙe da sauri ya fita, idanu Fulani Adama ta zuba mishi tana jin wani irin
tashin hankali na rufe ta, da alama kallon biri take yi mishi shi kuma yana mata kallon Ayaba, a
zaton ta ta toshe duk wani hanyar da zai iya sunce mata zani a kasuwa sai ya ke kokarin nuna
mata shi É—in mai zamani ne dole ta kiyaye shi. bata gama tsurewa ba sai da ta ga wasu sojoji
mata biyu sun shigo da rahane da aka chanza mata kamanni ko tsayuwa bata iya yi suka
gurfanar da ita, zabura tayi sai kuma ta koma yaraf ganin An sake shigo da wani mutumi an yi
mishi É—aurin huhun goro Dukda shekarunshi, azaba duk ya ishe shi ko motsi baya iya yi mai
kyau....
"Kai!!!"
Rayyan ya daka wa tsohon tsawa da sauri ya zube ƙasa yana roƙon yafiya cikin kuka.
"Menene alaƙarka da waenchan???"
Ya É—aga kai ya kalli su Fulani Adama ya ce
"Tsawon shekaru arba'in kenan ina yi musu aiki ba na asiri bane, ina ba su wani magani ne da
ya shafi lalata mahaifa, hana É—aukar ciki da ma zubar da shi idan ya samu... Sai G...gu..ba. A
gafarceni Ranka ya daÉ—e da farko ban so aikatawa ba suka min barazana da 'ya'yana daga
baya son zuciya da kudin da suke cika min ya ja ni har na zalunci Sarkin mu mai adalci.... Don
Allah a yi min aikin gafara na tuba na bi Allah na bi ku ku yafe min..."
Tsaki Rayyan ya ja ya kalli Rahane
"FaÉ—i bayanin da kika yi min..."
Cikin kuka da tarin nadama marar amfani ta shiga cewa
"Sunana Rahane, ni ce amintacciyar Fulani Adama tun da jimawa amma ba ni na fara yi mata
wannan aiki ba mahaifiyata ce da Allah ya yiwa rasuwa, ta bani labari kan rasuwar ta irin son
mulki da izza irin na fulani Adama, ta tabbatar min akan mulki babu abinda Adama ba zata yi
ba, ta iya makirci kala kala kuma bata bar kowa ba har mai martaba, da fari bayan aurenta da
mai martaba ta zaci zata haihu plan É—in ta kuma tana haihuwa za ta yi sanadiyar mutuwar shi
danta ya zama mai jiran gado sai Allah bai kawo haihuwar ba har ya auri Fulani Aminatou anan
ta yanke hukuncin muddin bata haihu ba babu mai haihuwa a wannan masarauta har mai
martaba kuwa don haka ta yanke hukuncin yin mai gabaÉ—aya Wai Haihuwa da hanji da
taimakon yayanta da ƙaninta suka samu wannan mai maganin sadidan yake bata maganin
hana É—aukar ciki..
A kowani sashe na matan sarki tana da amintacciyar baiwa da take biyan su makudan kudi
suke yi mata aikin zuba maganin nan a abinci kowace mace da mai martaba ya aura, tun Fulani
Aminatou bata shekara uku ba ta gama da mahaifarta yayinda a fili take nuna tausayi da neman
taimako ga mai martaba wanda hakan ya bata matsayi mai girma a idanunshi, Shigowar Fulani
FaÉ—imatu ya zame mata barazana don bata yarda hadimai su mata girki ba kuma idan tana yi
bata nisa da bakin murhunta hakan yake bata damar É—aukar ciki tunda duk abinda ta girkawa
mai martaba ma babu maganin, duk ta É—auka Fulani Adama kan san yadda tayi ta sha wannan
magani da take karɓo wa cikin ya ɓare. ko da ta samu cikin farko na yarima Aliyu ta gudu
Mambila babu yadda basu yi ba su sayi hadimarta mai rasuwa Hanne ta zuba musu maganin ta
ƙi har alkawarin kasheta suka yi amma ta ƙi amincewa bayan sun dawo masarauta suka samu
nasarar ba wa yarima Aliyu guba ya ci ya mutu fahimtar za ta iya tona musu asiri itama suka yi
ajalin ta.
Cikin Ciroma Sameer ne ya zo musu bazata don ita kanta mahaifiyar bata san da ciki ba sai da
ya girma, sun yi duk yadda za su yi sai dai Zakaran da Allah ya nufa da chara ko ana muzuru
ana shaho sai yayi dole ya zo duniya, sun so kashe shi yadda suka yi wa Yarima Aliyu amma
shi ɗin murucin kan dutse ne bai fita ba sai da ya shirya ya zame musu kabewar kan ƙabari
bakin cikin mai taushe, daga karshe dole suka sa mahaifiyarshi ta rabu dashi ala dole don babu
yadda ta iya tana so wa danta rayuwa.
Fulani Adama ta fi tsanar Fulani FaÉ—imatu akan duka matan sarki don Cikin lokaci kankani ta
lalata wa Fulani Salimah ma mahaifarta ita ce ta zame mata gagara badau bisa kariyar Allah, a
farkon aikinta babu asiri babu tsubbu don duk ta fi gane kirsa da makirci amma Makama da ya fi
kowa son mulkin yana ganin kaman ko ba jima Ciroma Sameer zai dawo sai ya je yayi mishi
asirin da zai saka ya manta komai da kowa, ya mishi asirin da zai ji ko sunan iyayenshi ba zai
iya ambata akan harshenshi ba, ya saka mishi tsanar masarauta da sarautar gabaÉ—aya,
Kwatsam sai ga shi ya ɓullo kaman huduwar rana tafin hannu yayi kaɗan ya kare shi sun shiga
tashin hankali don basu taba zato ko tsammanin bayyanuwar shi ba tunda an tabbatar wa
Makama cewa asirin ba mai karyewa bane don kogi aka jefa aka ba wa tsuntsu wani ya fire sai
gashi ya dawo kuma da wata mace.
Anan suka yanke hukuncin aura mishi zarah da haÉ—in Bakinta na daga ta aure shi sarki yayi
murabus za su kashe shi su kashe sarkin sai su karbi sarautar har dan Zarah ya girma,
kwatsam ta fahimci Fulani Afeefah na da juna biyu, hankalinta ya tashi ta aikeni wurin mai
maganinsu inda ya bani magani na kawo sai dai duk abinda aka bata bata ci har sai da Fulani
ta yi mata wasu maganganu da suka raunata zuciyarta ta sha fura, a cewar mai maganin sai
bayan sati ma zata yi ɓari kar ma a zarge ta tunda da wayon ta ba zata bari a lokaci ɗaya ta
zubar da cikin ba dayake Allah ba azzalumin bawan shi ba akwai rabon kamatan dumu dumu
bisa laifukanta sai cikin ya ɓare a ranar dole aka san me ta ci kuma a ina ta ci inda daga ranar
Ciroma Sameer bai bar su sun shaki iska ba.
Ya kama ni aka dinga min horo iri iri bai bar ni ba sai da na faÉ—i komai na kuma kaishi wurin mai
maganin aka kama shi... Ku yafemin don Allah ku yafe min na tuba wallahi umarni kawai nake
bi don tsira da rayuwata"
Cikin kuka mai tsuma zuciya ta ƙarasa.
"Innalillahi wainna ilaihi rajiun..! Innalillahi wainna ilaihi rajiun"
Abinda ke tashi kenan a fadar duka matan sarki kuka suke yi mai tada hankali yayinda mai
martaba ya runtse ido yana jin hawaye na sulmiyo mishi, ashe kashe mishi yaro suke niyyar yi
shiyasa take kanainaye shi da kissa da komai take cusa mishi son auren Zarah da Sameer? Ya
gode Allah da ba'a yi auren ba da ba zai yafe wa kanshi ba.
"Wallahi na yi nadama tun ba yanzu ba amma tsoron hukuncin Fulani Adama ya sa na kasa
daina basu magani, yarana sun mutu duk a gobara na auri mata sama da biyar duk suna gudu
su bar ni don na kasa basu haihuwa, tun mutuwar yarana na yi nadama amma ban san yadda
zan yi ba a gafarceni"
Tsohon ke fada. Fulani Aminatou tace
"Allah ya isa! Allah ya isa tsanina da ku duka wallahi Allah ko da ni kaÉ—ai ce zan yafe muku ku
shiga aljannah ba zan taɓa yafe wa ba"
Fulani Salima ma Allah ya isa take jerawa cikin kuka mai ciwo, mai martaba hawaye kawai yake
yi haka Ammi dake jin mutuwar yaronta ya dawo mata sabo.
"Babu aure tsakaninka da Zarah har Abada Ciroma, ku kuma wannan kaÉ—ai ya ishe ku tsoron
Allah, wannan kaÉ—ai ya kamata ya ishe ku ishara.... A tube musu duk wani rawanin zuri'arsu ku
kuma shaida na yanke igiyar aurena da Adama a dibe su a kaisu kurkuru mafi azabtarwa na
wannan masarauta kan a yanke musu hukuncinsu.... A tabbatar basu samu natsuwa ko
kwanciyar hankali ba"
"An gama ranka ya dade"
Sarkin dogarai ya zube ya amsa kan wasu majiya karfin suka shigo suka saɓesu ko damar
magana ba'a basu ba, kunya da dana sani marar amfani na rufe Adama komai ya kare mata a
lokacin da bata yi tsammani ba.
Rayyan ya dubi Afeefah dake kuka ya girgiza mata kai a hankali yace
"Na gode Afeefah. Na gode kwarai ta sanadiyarki asirinsu ya karye idan baki manta ba duk
ayoyin da kike yi wa Saleem a tare muke sha Dukda ban san da zaman wani asiri a jikina ba,
Kin ba ni babban dama ta sanadiyarki na samu faÉ—a wa Mammi abinda ta jima tana son ji na
wanene ni kafin mutuwarta. Ba zan taɓa manta wannan taimako naki ba na gode"
Ammi ta rungumeta tana kuka. A haka aka watse zaman fadan mai martaba sai riƙe shi aka yi
zuwa sashenshi tuni Rayyan ya maƙala mishi ruwa don ba karamin hawa jinin shi yayi ba.
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*58*
Alhamdulillah komai ya cigaba da tafiya normal bayan nan, ta cigaba da lectures É—inta cikin
kwanciyar hankali kuma tana samun duk wani kyautatawa daga zuri'ar na mijin nata kaman
yadda shima yake kara samun kusanci da iyayenshi, Mai martaba ya sha jinya kan ya warke ya
tara matan yayi ta basu haƙuri a ganinshi komai ya faru ne sanadin aurenshi da suka yi, sun
nuna haka ƙaddarar su take sai dai Fatan Allah yayi musu sakayya akan Adama, Zarah da bata
san komai ba sai da aka warware daga farko ji tayi duniyar yayi mata zafi damuwa yayi mata
yawa ta tattara ta koma wurin mahaifiyarta da dukkansu har yan uwanta kunyar abinda
mahaifinsu ya aikata ya sa ba sa iya ko fitowa, Ammi bata neme ta ba haka Aisha don tunda
har ta yi niyyar auren Rayyan ne don ta cutar dashi su ma suka ji ba za su iya cigaba da hulda
da ita ba amma Aisha tayi kuka kaman ta mutu, ta É—auki zarah kaman 'yan biyunta ne bata zaci
hakan daga gareta ba.
Maganan yanke hukunci sai da suka yi wata biyu suna cikin na uku garƙame cikin azabtarwa
kan aka yankewa Fulani Adama hukuncin kisa ta hanyar rataya, Makama da asirinshi ya dawo
mishi ya haukace damuwarshi kawai a barshi yayi ta tafiya ji yake kaman kwakwalwarshi zai
fashe idan bai shiga duniya ba dukan da yake yiwa Madaki yasa aka raba musu É—aki, shi
Madaki da sauran hadiman an yanke musu life imprisoment iyalan su sun yi kuka kaman ba
gobe amma bahaushe ya ce tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan yi wa dukan tsiya.
Soyayya tsakanin Saleem da Aisha yayi nisa don har ya turo mai martaba yace za su yi fixing
rana sai a haÉ—a da na Ameer da ya kasa komawa da Abeeha dake shirin gama makaranta,
Jiddah dai da tayi mugun kewan su sai dai a haÉ—u a yi ta waya. Yau ya kama ana ya gobe
Afeefah za ta gama First semester examination É—inta kuma Rayyan ya tabbatar mata a satin za
su fara shirin tafiya Kaduna don ta matsa mishi sossai akan komawa ga su Suhail da kuma su
kawu Dukda shi baƙin cikin kawun bai taɓa wankuwa mishi a rai ba sai dai bai hanata ba don
haka mai lalle ta nema Ammie ta turo mata har sashenta.
Tana zaune da dogon wando da wani shirt Black na ma Rayyan É—in ne daga ganin girman da
yayi mata amma ta fi jinta comfortable ciki, ta É—aura Black dan kwali a kanta an gama lallen kafa
da hannun duk an saka leda su Aisha na gefe suna ta hirar su da ta shafi rayuwa har jan ya
kama aka cire mata sai aka zana mata baƙi a bayan hannun don ta ce jan kawai ya isa a
kafafun yarinyar kwararriya ce kuma lallen ya mugun kamawa yayi maroon sharrr kaman ka
sace kafafun in ka gani, Rayyan ne yayi sallama ya shigo duk suka mishi sannu da dawowa
daidai an gama baƙin kenan ya tsaya yana kallon hannun kan ya ce
"Wai tunda na bar ku kina nan wurin zaune?"
Ta karkata kai fuska a ɗan Shagwaɓe tace
"Kwalliyar kenan sai wahala duk yunwa ma nake ji babu hannun cin"
Ya kalli hannun nata sai ya nufi kitchen, Aisha da Abeeha suka kwashe da dariya suna tafawa
"Sai da ke Matar mijinta"
Aisha ta faÉ—a tana dariya.
Abeeha tace
"Ku tashi mu tafi yanzu bai wuci abinda zata ci ya je nema mata ba kan ya dawo ya kora mu ko
su makanta mu gwara mun yi ta kanmu salin alin"
Afeefah na ce musu su tsaya ko ta kanta basu bi ba suka tarkata suka tafi sai gashi ya dawo
hannunshi rike da wani plate.
"Duk ka kora min 'yan hirar Ya Saraki..."
"Dama wani amfani suke dashi a gareki idan ina nan? Babu so Haaa ki ci abinci"
Murmushi ta saki tana bude baki ya saka mata Nan-bread guda biyu da ya sanyo a plate É—in da
curry chicken da ya zuba a gefe, da hannunshi yake bata yana tabbatar da bai ɓata mata jiki ba
har ta ƙoshi ya bata ruwa ta sha kan ya shiga duba lallen.
"Kin yi wa lallen nan kyau ainun BoÉ—É—i na"
Tayi murmushi tana sake kallon lallen
"Ko kuma shi ya min kyau dai ko Ya Saraki?".
"Wai dama baki sani ba?"
"Mene?"
"Ado biyayya yake miki, Kwalliyar da kanshi ke kike mishi kyau ba shi yake miki kyau ba.."
She's just blushing don bata gajiya da sauraron dadadan kalamanshi yana É—an wuya ya sake
bakin don haka idan ya sake yana zubowar tana amfani da damar ta adana a cikin zuciyarta ta
yadda ko baya nan in ta tuna fuskarta kan zama ya cika da tarin murmushi.
Washegari kuwa aka kai ta paper yadda aka saba motoci biyu har gaban exams hall su jira ta
gama a dawo da ita gida, yau ko da ta fito bata gansu ba, daga jikin hall É—in ta tsaya sai ta ga
call nashi tayi picking ya ce mata ta taho yana kallonta fuskarta cike da fara'a ta nufi motar
nashi don a yau da kanshi ya zo É—aukar ta.
Idanunshi da ya zura mata tun tahowarta ya lumshe a sadda ta yi masauki gaban motar
kamshinta mai sanyi da natsuwa na ratsa shi
"Hey Assalamu Alaikum"
Ta furta a hankali tare da miƙa mishi hannunta ya ɗan murmusa kan ya miƙa nashi ya shigar
cikin nata yana kallon tsakiyar idanunta ya furta
"Wa'alaikissalam warahmatullah"
Cire hannunta ta so yi sai ya gimtse yana mata kallon baki isa ba kuma ai dariya ta É—an yi, ya
miƙa hannu gefenshi ya zaro wani rose Red nd green dake fidda sassanyar kamshi ya miƙa
mata.
Da hannu ɗaya ta karɓa ta kai hancinta tana lumshe ido fuskanta ɗauke da murmushi tace
"and this?"
"I am bribing you a ban dama in fitar dake outingâ€
Dariya ne ya É—an kufce mata
"seriously? Ai na zaci saurayi da buduruwa ne ke fita date ba mata da miji ba"
Tayi tambayar tana wara fararen idanunta a kanshi ya kai hannunshi É—aya kan kumatunta ya
shafa
"Babu laifi a hakan.... Afeefah ki na da kyau fiye da duk wani abu mai kyau, kina da daraja fiye
da duk wani abu mai daraja a kullum soyayyarki ƙara yawa take a zuciyar Ryan, I will always
love you again and again...kullum sabunta kanshi soyayyar ki ke yi so i have to be very caution"
Tayi murmushi mai cike da tarin alfahari tana sake shinshuna kyawawar furen dake hannunta.
Motar ya ja suka fice daga makarantar.
"Kin ce za ki yi sayayyar su Suhail should we start with the shopping ko mu je ki sha ice
cream?"
Tayi murmushi tana sake jin alfahari zuciyarta fal godiyar Allah tace
"Lets start with the shopping"
Kai tsaye shopping din ya kaita a tare suke tafiya hannunshi rike da nata É—ayan yana tura chart
na shopping din ita kuma tana duba abinda zata É—auka.
Tsaye yake sai dai bayanshi a jingine da stall É—in kayayyaki inda suke babu wasu yawaitar
mutane, ita ke sayayya shi ya zuba mata idanu yana aikin kallo, sanye yake da full Black Jean
nd top ya saka facing cap da ya zauna mishi sossai saboda mutane kar su gane shi, takalman
kafafunshi ma bakake ne, hannayenshi duka a zube a aljihu... Don tun dazu suke tsaye wurin
choculates É—in tana ta rawan ido.
Ta É—auko wani choculates tana dubawa sai kuma ta É—an É—ago karab suka haÉ—a idanu kusan
karo na biyar kenan a take ta Shagwaɓe fuska tana kallonshi ya ɗan saki smile yana ɗage mata
gira guda
"ya dai? Na miki ne?"
Ya ƙarshe da wani kayataccen murmushi...
"Ni ya kamata in ce haka ai tun da ni ake ƙarewa kallo.. Ni Allah watarana har muni na sai ka
binciko"
Ta faÉ—a cikin yanayin da ya saka shi faÉ—aÉ—a murmushin shi, choculates na hannunta ta É—aga
sama
"Ina son picking wa su suhail wannan yayi ko? Ko me kake tunani?"
Very naughty yana ɗan lashe lip ɗin shi na ƙasa ya furta
"I am thinking of kissing you..."
Hannu ta saka ta rufe baki tana zazzaro ido ya saki dariya mai sauti kan ya yunkura ya nufe ta,
kalle kalle ta fara kan ta yunkura kuwa da gaske yayi pecking lips É—in nata hannunshi na É—an
manna ta da jikinshi.
"Ya Saraki waje fa muke"
"Ina ruwana"
Ganin yana ta kallon fuskarta ta san zai iya aikata abinda ma ya fi haka don haka ta janye ta
saka choculates É—in tace su tafi ita kam ta gama, sai murmushi yake mata don ta bashi dariya
yadda take zare ido kaman yayi komai ne gaban mutanen, shi ya biya kuÉ—in suka fice.
Sossai suka zazzaga ya kashe ta da tarin soyayya wai murnar kamallah exams sai dare suka
koma masarautan, a sayayyanta har su Ammie ta yiwa don haka tana idar da isha ta fito
hadimarta tayi saurin karbar manyan ledojin hannunta suka nufi sashen Ammin don shi bai
shigo ba tukuna, ta shiga sashen Ammin da sallama sai idanunta suka sauƙa kan zarah dake
tsugune ƙasa sanye da hijabi tana kuka sossai.
Gefe ta samu ta zauna bata ce komai ba har zarahn ta gaji da kukan ta fara roƙon su yafiya duk
ta rame tayi duhu. Ammi ta sauke numfashi tace
"Zarah ki daina kukan nan haka ni kam na yafe miki, wlh ban taɓa bambanta ki da Aisha ba
Dukda na ji mamakin ƙudirinki a kaina amma tunda kin gane kuskuren ki Allah ubangiji ya yafe
mana gabaÉ—aya"
Aisha ma tace ai ya wuce. Ta kalli Afeefah zata yi magana Afeefah tace
"Ni dai baki min komai ba wlh zarah. Allah ubangiji ya cigaba da É—ora mu duka bisa turban
gaskiya"
Suka amsa da Ameen kan ta miƙe ta fice suka bi ta da kallo.
Afeefah ta gaishe da Ammie ta amsa cike da kulawa tana tambayarta exams
"Alhamdulillah Ammie mun gama lafiya"
"Allah ya ba da sakamako na alkhairi, yanzu sai shirye shiryen tafiya Kaduna ko?"
Kai ta gyaÉ—a Ammie tace
"Masha Allah, Allah ya nuna mana. Akwai saƙo zuwa da safe za'a kawo miki sai ki duba ki ga
idan akwai abinda kike son ƙari ko chanji duk sai a yi"
Godiya tayi sossai kan ta miƙawa Ammie ledar hannunta daidai Rayyan ya shigo kenan tana
cewa
"Ammi mun je shopping ne sai na É—auka muku da Abeey"
Ta miƙawa Aisha nasu.
Ammie ta buÉ—e ledar Dukda duk wani kyauta da za'a yi mata tana da halin yin fiye dashi amma
kyautatawa abu ne mai daaɗi kwarai kuma ta ji daaɗi har ƙasan ranta Leshi ne mai tsadar
gaske sai turare shima designer na Abeey, Abeeha da Zarah dogayen riguna ne egypt Abaya
sai yan abun ciye ciye tarin choculates. Shi karan kanshi Rayyan fuskanshi ya nuna jin daaÉ—i
ainun Dukda tare suka Saya amma ko kusa bai san har da su Ammie ta yi wa sayayyar ba sai
darajar ta ya ƙaru a idanunshi barin ma da ya ji adu'o'in da Ammie ke yi mata anan ya fahimci
duk kudin iyaye kyautata musu na saka su farin ciki kuma hakan Allah ne kadai ya san irin ladar
da zai baka bisa wannan murmushi da ka sanya su aiko ya ƙudiri aniyar cigaba da ganin
wannan murmushi na Ammie, Sai kusan goma suka bar sashen.
Bayan kwana biyu da gama exams É—inta suka fito a shirye tsaff cikin shiga na alfarma, tafiyar
har da Abeeha da Aisha don duk sun gama exams motoci shida ne ya kaisu Airport yana riƙe
da hannunta cike da kulawa da so da kauna har suka sauƙa a filin tashi da saukar jirgi na
Abuja, anan ma motocin alfarma bakaken prado sai sheki suke da securities ne suka zo É—aukar
su ya san aikin mai martaba ne don haka babu wani dogon nazari suka shiga zuwa gida, sun
samu gidan a cike su Saleem da sisters É—in shi ga Sulaiman da matarshi da Twins su fauza ga
jidda an shirya musu abinciccika iri daban daban kasancewar tafiyar mintuna 40 ne ba wani
gajiya suka yi ba nan Sulaiman da Saleem da kuma Rayyan suka zauna sitting room yayinda
'yan matan suke ta hira a parlor babu wani nuna bakunta ko rashin sanayya kaman 'yan uwa.
Sai wuraren isha duk bakin suka tafi Aisha ta sauƙa ɗakin Afeefah na ɓangaren Mammi yayinda
su Afeefah suka sauƙa sashensu.
Washegari da safe suka fito a shirye tsaff suka shiga wannan motocin nan a jere suka Lula sai
Anchau Shigowar su Layin su Aunty zee suka jera gabaÉ—aya securities É—in suka fiffito aka buÉ—e
musu kofa za ta sauƙa ya riƙe hannunta yana kallon gidan da ya fara ganinta ciki a sadda ta
sallamar da Rayuwa, ita kanta tana tuna ranar da aka yi yunkurin kashe ta a wannan gida, tana
tuna rayuwarsu da Aunty zee tana iya tuna ranar da ya fara tare ta a cikin jikinshi lokacin da ta
yanke yin mai Dungurun gum da rayuwarta Wai HAIHUWA DA HANJI a sadda ta sallamar cewa
barin ta duniyar shine maslaharta idan har ta tafi ai shikenan babu mai kallonta bare yayi mata
sharrin maita ko zama annoba.
Idanunta cike da hawaye ta kalleshi ya lumshe nashi cikin su fuskarshi babu walwala yace
"Kin ga dalilin da ya sa bana so ki zo ko?"
Ta mayar da kanta ƙasa ta san kuka kam sai ta yi shi kuma abinda baya so kenan sam.
"Ki min alkawari ba za ki yi kuka ba"
Tayi shiru bata ce komai ba, ya zame hannunshi yana sauke numfashi sai ta juya ta sauƙa ta
nufi kofar kyauren gidan da ya tsufa mata ainun kaman ba gidan Aunty zee ba da yake fes fes,
jama'ar unguwa dayawa sun fita suna kallon wanda ya zo don jiniyar masu take musu baya ya
ja hankalinsu sossai.
Sanye take da wani dakakken purple lace mai shegen tsada an yi mata dinkin Borno style
straight skirt da bubu da yayi mugun kyau ta zuba accesories gold ne daga wuyanta zuwa
hannunta mayafinta ya zauna mata sossai hannunta rike da wani sabon designer bag da ta
dauka cikin kayan aurenta da har lokacin suke gidansu na Kaduna don bata tattare ba, sai
takalmin ta mai É—an tudu wannan vibe É—in na manyan mata kuma hajiyoyi yan gatan mazajensu
shi take bayarwa har ta tura kofan gidan ta sanya kai da sallama.
Wasu yara biyu ta gani suna wasa sanye da wasu kaya da suka fi yanayi da tsumma sun yi
dukun dukun macen gashinta kaman wanda yayi shekara bai ga ruwa ba, kafafunsu babu
takalmi, ganin ta yasa suka tsaya suna kallonta kamannin fuskokin su yasa taji tayi bursting to
tears, gabanta na tsananin faÉ—uwa ta ce
"Suhail...! Suhailaah???".
Abeeha ce ta dafa ta ganin tana ƙoƙarin faɗuwa saboda jirin da ta ji ya ɗauketa a lokacin da
suka amsa, waennan su ne yaran Aunty zee? Su Suhail ne haka? Innalillahi wainna ilaihi rajiun
"Ina Babanku?"
Cikin maganansu suka ce
"Yana É—aki kwance ba shi da lafiya"
Da sauri ta nufi É—akin da yake kwancen babu komai cikin É—akin sai tantagaryan siminti, me ya
faru? Ta fara tambayar kanta kan ta isa inda yake kwance kan taburma idanunshi a buÉ—e yana
kallonta ta duka gangarshi
"Uncle Usman!!"
Hawaye na zubo mata babu kakkautawa a hankali yace
"Afeefah?? Ke ce??"
Hannayenta ta sa ta toshe Bakinta tana sakin kuka da gaske su É—in ne cikin wannan hali?
"Uncle me ya faru? Ina Hamdiyya? Me ya samu aikinka baka da lafiya ne?"
Duk ta rasa ma me zata tambaya shima yana kuka yace
"Ki yafe min Afeefah don Allah ki yafe min na cutar da ke, na kasa rike amanar da zainabu ta
tafi ta bar mini ki gafarceni AFEEFAH"
"Baka yi min komai ba uncle wlh baka yi min komai ba hasali ma ka rike ni da amana tsawon
shekara da nayi a gidan nan baka taɓa hantara ta ba, wlh baka min komai ba ni ban ga laifinka
ba ko da ka zarge ni saboda ina da tambarin tun farko manne a goshina"
"Na kasa amincewa da cewa Allah ne me kashewa kuma mai raya wa, hankali na ya tashi ainun
don bayan mun binne zainab kin dawo mun kore ki sai muka muka je asibiti da su Suhail za'a yi
musu riga kafi a kuma ba mu madarar da ya kamata su cigaba da sha anan ne likitan ya ji
maganan da muke yi da Hamdiyya da maiyya ce ta kashe zainabu yayi saurin taka mana birki
ya kuma shiga yi mana bayanin abinda ya faru da zainabu wanda bamu sani ba, ya ce mata
dayawa suna samun wannan matsala na Postpertum ko a samu taɓuwar mu'amala ko irin
ciwon cikin wasu kam ma har a zaci sun haukace ne, ciwon cikin nata bamu farga da wuri ba
sai da ya mata illah kwarai muka koma a sannan babu abinda za su iya ta rasu. Hamdiyya
kuma dama ta jima tana yi mata hassada tana jin haushin yadda ta samu ciki ita tana zaune
hakika ta yi yunkurin illa ta cikin tun kan su zo duniya Allah na kare su har ta haihu tana ganin
kaman za ku haÉ—u ku kwashe dan abinda na mallaka da ke da zainabu ga yarana da farin cikin
samuwar su bai ɓoya mini kuma dama ta jima tana sanyawa ranta ba sonta nake ba na aureta
ne kawai don in haihuwa a yanzu da bata haihu ba matata ta haihu ta gama amfani kenan zan
iya sakarta kowani lokaci hakan yasa ta ƙarfafa hassadarta a kanku musamman ke tana amfani
da baƙanta miki tana kuntatawa Zainabu.
A ƙarshe tayi sanadin da kika bar gidan nan anan ta fara rainon azaba ga yarana ba tare da na
sani ba, duka zagi tun basu san kansu ba, ta bar su da yunwa ta bar su cikin ruwan wanka duka
don ba ita ta haife su ba Allah ne ke kare su ban sani ba, a ranan da na san duk abinda take
kullawa na shiga masifar tashin hankali marar misaltuwa musamman in na tuna abinda na yi
miki daga nan jinina ya hau na samu matsalar shanyewan jiki, a takaice Hamdiyya ta tattara
komai ta sayar akan ba zata iya zama da ni ba ga jinya, ga rainon Æ´aÆ´an da ba nata ba kuma
bata da damar haihuwa, ko sati ba'a yi ba na samu labarin mota ta kaÉ—e ta ta rasa kafafunta ta
kuma rasa rabin fuskarta duk kudin yana tafiya a jinyar da har yau bata warke ba. KuÉ—in da
Zainabu tayi ta ajiye miki a asusu da su na tsira sai waenda abokan arziki kan kawo da shi nake
aika yaran nan su sayi abinci su ci ko makota su basu, bana iya yi musu komai ko wanka sai dai
su je su watsa"
Sossai Afeefah ke kuka, Allah sarki rayuwa amma Hamdiyya ta cika azzalumar matar uba kuma
ko a yanzu ta ga ishara, Rayyan Aisha ta kira don Afeefah ta kasa daina kuka hankalinta ba
karamin tashi yayi ba shi ya kira aka dauki uncle Usman yace a koma cikin Kaduna dashi a
kaishi asibiti zai kira Sulaiman kan su juyo.
Su Suhail na rungume da Afeefah suka fito zuwa mota yan unguwar na zuwa su gaisheta suna
ta mamaki har wasu na tambayar ko Afeefahn Aunty zee ce ta gyaÉ—a musu kai, Rayyan ya
zubar da dukiya don duk wanda ya nuna ya gane ta aka gaisa sai ya mishi kyauta daga nan
suka nufi Dutsen-wai.
"Afeefah!"
Ta kalleshi ya riƙe hannunta ya sa hannu yana share mata fuska yace
"kuka sam bai kamace ki ba, ko don zafin da nake ji a nan ya kamata ki sassauta"
Ya ƙarasa yana nuna zuciyarshi. Ta gyaɗa kai ya ce
"Na san burinki shi ne ki yi kuÉ—i, ba kuma don wani abu ba sai don ki tallafawa al'umma
musamman na ƙauye irin cikin kauyen ku da ake rayuwa kara zube babu neman ilimi, babu
sana'a ana rayuwa irin rayuwar dabobbi ko zamanin da chan baya, ina so in sanar miki cewa na
ba da wannan gudumawa na buÉ—e miki Center na farko ina fata ya zama farkon buduwar tarin
alkhairanki... Ina adu'a Allah ya sanyawa gidauniyarki daga na farko har na karshe albarka ya
dafa miki ya kuma isar miki da ladan... Akwai Center da aka gama buÉ—ewa a Dutsen-wai da
Sunanki a yau za'a yi taron kaddamarwa a cikin wannan plaza akwai kayan aiki da malamai na
Musamman da zasu ke koyawa mata sana'o'in dogaro da kai kaman su É—inki da sauransu
akwai kuma makaranta islamiyya da malaman da muka yi hiring na musulunci da za su tsaya
tsayin daka wurin ganin sun koyawa matan wannan kauye da ma mazan addini akwai kuma
babban masallacin juma'a a kusa da wannan plaza shi kam na Mammi ne ina Fatan duk Sallar
da za'a yi ciki ladar ya isa gareta. Ba ni da alaka da kula da wurin daga yau duk naki ne ga
takardun da ma komai da komai na plaza É—in kyauta ne na musamman zuwa gareki"
Jikinshi kawai ta faÉ—a don ta gigice ta rasa ma wani irin abu zata yi, kuka kawai ta saka mishi
yana ta aikin rarrashi za tayi godiya ya manne Bakinta da nashi yana kissing passionatly sai da
ya tabbatar ta daina hawayen kan ya saki yayi pecking goshinta
"Anything for you my baby girl ki sani wannan É—in mafarin nasararki kenan a rayuwa, duk wanda
ya baƙanta miki a da a yanzu yana a karkashin kafafunki, na ji daaɗi da kika nufi saka musu da
alkhairi bayan sun bi ki da sharri amma ki sani wannan yunkuri naki na basu ilimi makami ne
mai girman gaske a duniyarsu ladar ki sai a wurin ubangiji"
Daidai nan suka isa cikin Dutsen-wai ita ke kwatanta musu har kofan Gidan Kawu Labaran.
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
"Last Page na zuwa anjima in shaa Allah. Wlh jiya na yi gajiyar da ban san adadi ba ina buÉ—e
ido da niyyar typing idon na rufuwa ganin ba zan iya ba yasa nayi bacci and yau ma same thing
zan lallaɓa in ba ku shafin karshe in shaa Allah. Na gode da haƙuri da ni*
*59*
A gaban gidan ta tsaya ta ƙura mishi idanu kaman yanzu ne komai ke faruwa da ita, tana tuna
baƙar wuyar da ta ci daki-daki cikin wannan gida, hawaye ne suka cika mata idanu shaidan na
raya mata ta juya ta koma kawai don basu chanchacanci duk wata alfarma daga gareta ba, da
kyar ta hadiye wani abu da ya tsaya mata a wuya tana tuna ni'imomin Allah a gareta sai ta furta
Alhamdulillah don ko daga fasalin gidan zaka san cewa rayuwa ya ƙara taɓarɓare musu wane
wane don daga inda take tana kallon har kofofin dakunan gidan saboda rushewar ginin ƙasan
dake zagaye da gidan, yunkura wa tayi zata shiga sai ta ga Fitowar wani dattijo a yanayin shiga
da fuskarshi ya nuna kamilalle ne wanda kai tsaye bata kawo ko kusa Kawu Labaran bane sai
da suka haɗa idanu, Chakk ya tsaya yana ƙare mata kallo kaman yadda ita ma take ƙare mishi
kallo.
Sanye yake da jallabiya baƙa har da hula taɓani ka ji hadisi da chasbi riƙe a hannunshi sai wani
littafi da ya nuna mata na addini ne, ya rame kam gabaÉ—aya ya lalace, shi karan kanshi bai
gane ta ba sai da yaga kallon da take mishi da hawayen dake zuba mata don kaman an yi mata
wankin inji ne, kaman bata taɓa sanin menene wahala ba a rayuwarta, muryarta na rawa tace
"Ka..kawu"
Tana tuna ranar da ta zo da Saleem yayi mata kora irin ta miyagun aljannu da kayan tsubbu da
komai.
"Af...Afee..fah??? Ke ce Afeefah? Da gaske ke c..e?"
Cikin wani irin karyayyen murya yake maganan, ta É—aga kai sai gani tayi ya iso gabanta ya zube
gwiwowinshi ƙasa da sauri itama ta durkusa yadda yayi suka saki kuka a tare, nata dai bata san
me take ji ba don abubuwa ne suka haÉ—e mata shaidan na tuno mata duk wani minti da tayi a
gidan cikin azabtarwa yana tuna mata irin muggan kalaman kawu a kanta da rayuwarta yana
nuna mata basu chanchanci komai na alkhairi daga gareta ba ta wani ɓangaren tana jin babu
daaÉ—in yadda ta zo ta ga inda suke rayuwa da kuma lalacewar da kawun yayi kaman kuÉ—in
guzuri.
Shi kuwa nadama ce, nadama da kunyar kasa riƙe amana da zumuncin ɗan uwanshi yake yi wa
kuka, kunya mai tsanani da ba zai iya cewa ya taɓa jin irin shi ba yake ji na ɗiyar cikinshi.
"Afeefah idan na ce ki yafe min na so kaina dayawa, na san na yi miki abubuwa masu yawa na
zalunce ki, na ci amanar zumunci, na cutar da rayuwarki fiye da ƙima, na wargaza natsuwarki
har ya kai na kore ki da kaina daga kusa na bisa tarin jahilci da baƙar zuciyata... Ina kallo
matana kowacce take abinda ta so da rayuwarki ana gara ki kaman kwallo, na dauke ki da
kaina na jefawa hukuma ke don kawai ina ganin kin zame min Ƙashin kifi, an zo neman aurenki
har nan na lalata komai saboda kawai wani zargi wanda babu wanda ya tabbatar, saboda son
zuciya irin tamu... A ƙarshe na aurar dake ba tare da na ko yi binciken wanene za ki aura ba,
mecece sana'ar shi, su waye danginshi don kawai sun cika ni da kuÉ—i sun kuma nemi auren
kawai suke so, tun bayan aurenki da kaddara ta faÉ—a min bisa neman zuwa wurin ki da nayi na
ci arziki na faÉ—a hannun 'yan shan jini a ranar na san cewa ke ba Mayya ba ce yadda muke
faÉ—a, a ranar na tabbatar harkar shan jini da maita ya fi karfin kwakwalwarki nadama mai yawa
ya rufe ni a kullum Adu'a ta shi ne yadda zan ganki kafin ƙasa ya rufe min idanu Afeefah...."
Sossai yake kuka ta mayar da kanta ƙasa tana cigaba da hawaye, hatta Aisha da Abeeha
hawaye suke shi kuwa Rayyan kanshi ya kawar yana jin zuciyarshi na jagulewa.
"Ashe za ki zo inda muke Afeefah? Ashe za ki neme mu?"
Zuwa lokacin makota duk ana maƙale ana kallon me ke wakana Larai da Asabe da ma wasu
yaransu dake gida duk sun fito sai dai ita bata kai hankalinta kansu ba yayinda duk suke kuka.
Hannun kawu ta riƙe tana jin yadda zuciyarta ke kakkaryewa tace
"Dole na nemeku kawu dole duk inda zan shiga ku ne nawa, ko me za ku yi min ku ne dole na
duk duniya ba ni da waenda suka fi ku. Tsoro nake ji... Tsoro nake ji kar ku ƙi karɓa ta.."
"Ko a ya kika zo Afeefah wallahi ba zan ki karbarki ba a yanzu, na tuba na yi nadama mai tarin
yawa, na roki Allah a salloli dayawa akan ya waiwayo mana dake ya sa ki tuna da mu. Don
Allah, Don darajar Allah ki dubi girman shi ki yafe min Afeefah ki yafe min don Allah"
Kai take gyaÉ—a wa ta kai hannu ta share mishi fuska
"Na yafe maka kawu wlh duk na yafe muku Allah ya yafe mana gabaÉ—aya"
Inna Asabe ta rarrafo
"Afeefah don Allah ki yafe mana don Allah"
Ta kallesu sai ta ga inna Larai na ja da duwawu kafa É—aya kam babu gabaÉ—aya kuma ba sanda
bare wheelchair zubewa tayi tana neman yafiyarta duk ta yafe musu, Rayyan da ya gaji da
kukan ya taho ya É—aga ta tsaye yana kallon cikin idanunta ya fidda hanky fari tas mai cike da
kamshi ya fara É—auke mata hawayen fuskarshi babu É—igon walwala.
"Am sorry"
Ta faÉ—a a hankali.
Iso aka yi musu sai dai duk gidan an rasa ma taburma mai haske da za'a iya shimfida musu su
zauna, Rayyan take kallo ta juya ta kalli kawu ta sake kallon Rayyan.
"Ko za ka tafi mota ka zauna Ya Saraki?"
Ya harareta ya samu wani dutse ya zauna a kai ta mayar da kanta ƙasa ko wannan kaɗai ya isa
ta yafe musu, wa zai ce Rayyan zai iya zama a irin wurin nan saboda ita? Saboda kawai tana
wurin idan ba don haka ba me haÉ—in kifi da kaska?
Rayuwar mutanen gidan sossai ya chanza mata ko da ta ji irin neman ilimin da kawu ke yi tun
daga sanadiyar yan shan jini da suka kama shi Allah ya nufe shi da shiriya ta tabbatar da gidan
sun rabauta don ilimi shi ne ginshikin rayuwa, yaranshi duk sun dawo kan hanya sai talauci da
yayi musu matuƙar yawa don Allah ya jarabcesu da babu tun bayan tuban shi abinda za'a ci ma
wahala yake sai dai basu daina neman ilimi ba kuma dayake tuban gaskiya suka yi yana iya
yinshi ya ga an ci wani abu ko da sau É—aya ne a yini, tayi kuka har sai da Rayyan ya fara yi
mata faɗa ganin da gaske ranshi ya ɓaci ya sa ta daina, ta basu labarin duk abinda ya faru da
ita har kawo yau
"Allahu Akbar... Allahu Akbar kabiran lallai shi mahakurci mawadaci ne kuma mai haƙuri shi
yake dafa dutse... Yanzu Afeefah har 'ya'yan sarki mai tarin daraja biyu ne a gidana ta
sanadiyar ki? Ashe ke ce kike gina wannan tamfatsatsen gini da masallacin juma'ar da babu
irinshi a wannan gari? Allah mai girma Allah mai yadda ya so"
Kawu ke magana cikin hawaye da tabbatar da girman zatin ubangiji.
Kallon Inna Larai tayi tace
"Kawu me ya sameta?"
"Maciji ne ya sare ta mun yi gargajiya har mun gaji kafan ya rube dole muka nemi taimako dai
da kyar muka hada kudi aka yanke kafar sai dai babu kudin ko sanda ne bare kujeran guragu a
dole take yawo a haka da ja da duwawu"
Lokaci Ryan ya kalla ya mata umurnin su tafi ana jiran su wurin taron da suka gayyata, kawu da
iyalan shi duk suka tafi dasu wurin taron kusan duka jama'ar garin suna É—akin taron barin ma
fankoki dake kaÉ—a su ya sa sai nishadi suke.
Mai gari ne ya fara yin bayani da kuma godiya ga wacce ta dubi garin ta zaɓi inganta rayuwarsu
ta hanyar ba su ilimi wanda ta wannan hanyar ta riga ta gama musu komai, da ya zo wurin kiran
suna sai ya ce
"Wannan É—in ba kowa ba ce illa mata ga Ciroma Sameer, Ciroma mai jiran gado kuma Yariman
Matasa na ƙasar Fombina Afeefa..h Afeefah kamal??"
Sai yayi saurin kallon matar da ake cewa ita ce Afeefahn, duk yan garin ido suka zuba mata
suna mamaki da ikon Allah, wasu kunya na rufe su a yayinda tayi murmushi ta miƙe ta haura
podium ɗin ta karɓi mic
"Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata
ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga
sharrin kawukanmu da munanan ayyukanmu.
Wanda Allah ya shiryar babu mai ɓatar da
shi, wanda kuma ya ɓatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta
da gaskiya sai Allah, shi kaÉ—ai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi
Muhammad bawansa ne manzonsa
ne. Bayan nan ina yi mana Sallama irin ta addinin musulunci shi ne Assalamu Alaikum
warahmatullah"
Duk suka amsa, ta É—an sauke numfashi
"Ba gixo ba kuma ba mafarki ba haƙiƙa ni din ce Afeefah kamal wacce kuka fi sani da Annoba
ko kuma Mayya a wannan gari, haƙiƙa na jure abubuwa dayawa daga gare ku 'yan uwana,
yayyena, Ƙannene na da kuma iyayena. A baya na zama mujiya cikin tsuntsaye Abar kyamata
da gudu. Abar tozarta wa da wulaƙanta wa, Abar muzantawa a cikin al'umma saɓanin a yanzu
da nake da miji nagartacce nake kuma da surakan girma waenda suka taka rawar gani bisa
inganta rayuwata daga Wacce ta sallamar da farin ciki ta sallamar da jin daaÉ—i zuwa wacce ta
zama mai cike da buri da alfahari. Da na zauna nayi nazari da tunanin Meyasa nawa iyalan
kuma dangina suka yi min abinda suka yi a baya sai na fahimci babu wani abunda ke damun
ahalin wannan gari na mu sai rashin ilimi da sanin daidai. Na fahimci mun samu tawaya da
koma baya a wannan ɓangaren iyayen babu bare su tarbiyatar da yara akan daidai, a sadda na
sake zurfafa tunanin me zan yi na taimaki al'ummata sai na ga babu abinda ya fi dacewa irin in
wayar mana da kai in taka rawa wurin ganin mun samu ilimi har ma muna aiki dashi, in ga cewa
wata mace ko wani yaro bai É—anÉ—ani irin É—acin da na É—anÉ—ana ba, in ga cewa yadda rayuwata
ta inganta kowa ma a yankina rayuwarshi ta inganta gobenmu mu samu tsatson da za mu yi
alfahari da su daga wannan gari namu.
Ya ku 'yan uwana musulmai ku sani cewa
addinin musulunci addini ne na ilimi. Umarni
da neman ilimi shi ne farkon abin da Allah
MaÉ—aukakin Sarki ya umarci Annabinsa
(S.A.W) da shi, yayin da ya saukar masa da
faÉ—insa :
‫)اْقَر ْا ÙØ¨Ø§Ù’س ÙÙ… َر Ùّبَك Ø§ÙŽÙ‘Ù„ÙØ°ÙŠ ÙŽØ® ÙŽÙ„ÙŽÙ‚! ÙŽØ® ÙŽÙ„ÙŽÙ‚ Ø§ÙØ¥Ù’لْنَس اَن Ùمْن‬
‫َأْل‬
‫ َعَلَم‬4 ‫ Ø§ÙŽÙ‘Ù„ÙØ°ÙŠ ÙŽØ¹ÙŽÙ‘Ù„ÙŽÙ… ÙØ¨Ø§Ù’Ù„ÙŽÙ‚ÙŽÙ„Ùم‬3 ‫ اْقَر ْا َوَر Ùّبَك ا ْكَر Ùم‬2 ‫َعَلÙق‬
.[Ù¡ - Ù¥ :‫( ]العلق‬5 â€«Ø§ÙØ¥Ù’لْنَس اَن َما َلْم َيْعَلْم‬
Ma'ana : (Ka yi karatu da sunan Ubangijinka
da ya yi halitta. Wanda ya halicci mutum daga gudan jini. Ka yi karatu kuma Ubangijinka shi ne
mafi karamci. Wanda ya sanar da alqalami. Ya sanar da mutum abin da bai sani ba). (Alaq : 1 -
5)
Addinin musulunci ya kwaÉ—aitar da mabiyansa akan neman ilimi, domin ba zai yiwu mutum ya
bauta wa Allah ba sai da ilimi. Allah madaukakin Sarki yana cewa :
)28‫] (ÙØ¥ÙŽÙ‘نَما َيْخ ÙŽØ´ Ù‰ الَّل Ùمْن ÙØ¹ ÙŽØ¨Ø§ÙØ¯ÙÙ‡ Ø§Ù’Ù„ÙØ¹ÙŽÙ„ÙŽÙ…Ø§ÙØ¡â€¬:â€«ÙØ§Ø·Ø±â€¬
TA].
Ma'ana : (KaÉ—ai waÉ—anda suke jin tsoron Allah daga cikin bayinsa su ne masu ilimi)
Idan na ce zan kawo muku faÉ—ar Allah da kuma hadisan da suka yi magana akan ilimi da
amfaninsa gare mu za mu kwana bamu ƙare ba amma tabbas da akwai ilimi da duk ban
fuskanci abinda ya faru da ni a wannan kauyen namu ba, Ajalin mahaifina ya same shi ba tare
da na zo duniya ba, mahaifiyata ta rasu bisa rashin kula da rashin zuwa asibiti a yayin daukar
ciki zuwa haihuwan gida, kakata shekarun ta ya ja ƙwarai wacce dole a yi mata tsammanin
mutuwa a sadda ta tafi haka Goggona ta tafi bisa sakaci da zaman jahilci da dabbanci da ake yi
a cikin gidanta, bamu san kan mu ba bare mu nemi sanin hakkoƙin da suka rataya mana,
hakkoƙin matayenmu, hakkoƙin iyayenmu bare hakkoƙin 'ya'yayenmu wanda duka sai ta hanyar
ilimi za mu sani, na koma wurin Aunty zainabu ta gamu da postpertum wanda ciwo ne da ake
samun shi bayan haihuwa duba da bata taɓa ba ga yawan shekaru babu wanda ya fahimci
hakan sai da lokaci ya ƙure ta tafi duk ba mu dubi ajalin su ne yayi ba, mun manta Allah ya ce
ba zai taɓa jinkirta ajalin dayanmu ba idan ya zo dole za mu tafi. ku sani na yafewa kowannenku
da wanda yayi min na sani da wanda ban sani ba duk na yafe muku, a wannan gidauniya tawa
tafiyar duk na neman ilimi ne da kuma tsayuwa akan kafafunmu don Allah ina roƙon mazaje da
ku bar matayenku da ma ku karan kanku ku nemi ilimi don Allah ba ya ƙarbar uzurin bawa akan
rashin sani saboda ya mana umurnin nema.
Akwai ma'aikata da za su koyar da sana'o'i ga yara da matayenku su ma ku bar su don zai
amfani wannan al'umma tamu, duk lokacin yaye É—alibai idan yayi zan zo kuma idan Allah ya
amince za mu dinga raba kyaututtuka da suka shafi sana'ar da mutum ya koya don ya cigaba
daga inda ya tsaya ina Fatan ganin chanji daga gare mu bakidaya na gode"
Wasu hawaye suke yi suna tuna abinda suka mata amma dayake tana da zuciya mai kyau dubi
Alkhairin da ta nufe su dashi, kawu ta miƙawa mic ɗin don ya taso yana son yin magana, a
gaban tarin al'ummar yana kuka ya ba da duk labarin abinda yayi mata da wanda aka mishi ta
sanadiyar son zuciyarshi da yadda ilimi ya sauya shi daga mummuna zuwa kyakyawa har ya
kara da
"An karɓo daga Kasir ɗan Qaisi ya ce, ina
zaune tare da Abud Darda'i a masallacin
Dimashqa, sai wani mutum ya zo wajensa ya ce masa, Ya Abud Darda' i na zo wajenka ne
daga Madinar Manzon Allah (S.A. W) saboda
wani hadisi da aka ce min kana faÉ—a daga Manzon Allah (S.A. W), kuma babu wata buqata da
ta kawo ni nan sai wannan. (wato jin wannan hadisin) Sai Abud Dar' da'i ya ce,
"Na ji Manzon Allah (S.A. W) yana cewa :
"Duk wanda ya bi wata hanya yana neman ilimi a cikinta, to Allah zai sanya shi akan hanya
daga cikin hanyoyin Aljannah, kuma haqiqa Mala'iku suna sanya fika - fikansu ga É—aliban ilimi,
don yarda da abin da yake nema, sannan duk wanda yake sama da qasa yana nema wa
malami gafara, har ma da
kifayen da suke cikin ruwa. Falalar malami a
kan mai bauta kamar falalar wata ne a daren
goma sha hudu a kan sauran taurari, kuma haqiqa malamai magada Annabawa ne,
Annabawa kuwa ba su bar gadon dinari ko dirhami ba, kaÉ—ai sun bar gadon ilimi ne don haka
don Allah kar mu raja'a akan boko don shi iya na duniya ne mu nemi lahira kuma mu koyar
komin kankartarsa, ko uwa malama ce akan yayanta kar mu saka finafinai ko waƙa gaba mu ta
rawa da nishadi da yara mu koya musu abinda zai amfanesu a gaba. Ni a karan kaina misali ne
kuma Aya ne ubangiji ya nuna min akan Afeefah"
Duk jikin mutanen wurin yayi sanyi kuma sun gamsu É—ari bisa É—ari da lallai suna da nakasu ta
wannan fannin dole rayuwarsu ya tafi a jiɓance, Afeefah da manyan gari a gefenta mijinta ne da
ya bata support É—ari bisa dari suka zaga wurin tassss ta yabi kyau da tsarin komai na wurin
kuma duk abin bukata akwai.
Kawu ta damƙawa wurin ta ce ta bashi amana ya riƙe mata ya kula da komai yadda ya kamata
bisa tsari shi dai babu bakin magana don ya rasa me zai ce.
Cikin jami'an tsaro masu kula da taron kawai idanunta ya sauƙa kanshi, da sauri ta nufe shi
tana kallonshi shima ita yake kallo a hankali ta nuna shi "Sa'adu? Sa'adu Rabi'u kai ne?"
Kai ya gyaÉ—a yana murmushi ya gane ta amma bai zaci zata nuna ta sanshi ba ta juya ta kalli
Rayyan ya matso
"Ka tuna shi Ya Saraki?"
"Wannan police da ya ceceki daga sharrin gurbatattun 'yan uwansa"
Za Ta cire zobenta na gwal ya miƙa hannu ya riƙe nata, ya zari kati daga aljihunshi ya miƙa
mishi
"Ka ƙira ni in shaa Allah kyautarka ya fi karfin kuɗi za'a mayar da kai cikin Kaduna da matsayi
mai kyau"
Hawayen murna ya fara yana godiya.
Ko da aka watse taron suka koma gidan Kawu akan za'a saka date na fara daukar É—aliban da
suka kamata za kuma ta turo waenda za su taimaka mishi wurin fahimtar komai da komai kan a
sakar mishi, a tsakar gidan suka samu an jibge kayan abinci babu abinda babu wanda za su iya
ma watanni goma zuwa ashirin basu nemi kayan abinci ba, a gefe crouches ne da wheelchair
na inna Larai Afeefah tayi saurin kallon Rayyan ya girgiza mata kai yana dan É—age kafada sai
ya juya ya fice ta bi bayanshi
Za tayi magana jiri ya ɗan dibeta da sauri ya riƙo ta
"BoÉ—É—i menene? Ba kin ga illar kukan da kika dinga yi ba duk yau kin tarawa kanki damuwa!
Kan na ciwo ne?"
Ya kai tafin hannunshi yana dafe goshinta hawayen ta sake farawa
"Ban san da wani baki zan fara maka godiya ba Ya Saraki... Ko baka faÉ—a ba na san aikinka ne
Allah ya biya ka ya saka maka da alkhairi ka yi min komai Ya Sa..."
Hannunshi ya sa ya rufe mata baki yana dan É—auke hawayen da take zubarwa yace
"Kin chanchanci fiye da haka a gareni Afeefah don haka ba komai ba ne, na so ko gidan haya
ne mu kama a gyara wannan amma bai samu ba idan ba damuwa za su dan koma Kaduna ko
ma su je ganin É—akin ki a Fombina kan su dawo sai a gyare nan É—in"
Rungume shi kawai tayi ya sa hannu yana dan shafa bayanta kan ta É—ago sai ta sake jin jirin
yamutsa fuska tayi, ya shiga mota don bai kula ba itama ta zaci ma stress ne don haka ta koma
ta musu bayanin za su je Fombina ko sati biyu su yi za'a É—an gyare nan É—in kuka kam kawu har
ya rasa hawaye ya rasa bakin godiya a haka suka É—auki duk abinda za su É—auka aka adana
kayan abincinsu a daki guda suka É—auki duk wani abu mai muhimmanci, yaranshi maza
manyan uku da mata shidda na Inna Asabe uku na Inna Larai biyar suka bar garin zuwa
Kaduna.
Kai tsaye gidan Mammi suka yi masauki jannah ta turo abinci ko da Abeeha ta gaya mata da
baƙi suke ta turo daga restuarant, a masaukin baki aka sauke su suna ta mamaki da santin
gidan, Ita dai Afeefah su Suhaila ta ja zuwa É—akinta ta musu wanka ta duba cikin tsarabarsu da
ta musu na musamman ta fidda kaya ta saka musu suka haÉ—e babban parlor aka ci aka sha kan
kowa ya nemi makwanci don sun gaji, sai da ta tabbatar sun yi bacci ta watsa ruwa ta shirya
cikin wani Red kayan bacci da yayi mata kyau sossai marabarshi da babu kaÉ—an ne ta nufi
É—akinshi...
Yana jingine da gado yana jiranta suna haɗa ido suka Sakarwa juna murmushi mai ƙayatarwa,
yanga tayi ta mishi Dukda kunya dake É—awainiya da ita barin killer looks da yake binta da su har
ta iso gadon ya fusgo hannunta ya manna ta kirjinshi yana matse ta a lokaci ɗaya suna sauƙe
ajiyar zuciya a tare
A kunnenta ya raÉ—a mata
"Kina kashe ni da raina Gimbiyata"
Ta É—an É—ago bai tsammata ba ta haÉ—e lips É—insu kaman jira kuwa ya mirginata kasanshi ya
mata rumfa yana bata wasu kisses da suka sake matar da ita a kaunarshi hannunta na yawo
bisa bayanshi zuwa keyarshi tana mishi susa, gasping air yayi ya raba lips É—in suka yi murmushi
mai sauti ya sake mayar da lips É—in yayi mata kyakyawar Kiss
Ta raba fuskansu tana shafa kanshi hancinsu haÉ—e da juna suna musayar numfashi ta ce
"Na gode sossai Na gode kwarai haƙiƙa Allah ya wanke min zuciya ya ba ni mijin marainiya, ya
ba ni kai ba tare da wayo ko dabara ta ba a koyaushe ba ni da abin faÉ—a a gareshi sai
Alhamdulillah. Ina roƙon Allah akan duk ranar da za ka haɗu da shi, Fuskarka ya zama mai
annuri da sheki fiye da yadda yake a yanzu, ya rabautaka da karɓar kyawawan sakamakonka a
cikin tafin hannunka na dama sannan ya ce
"I am pleased with you" ya haÉ—a mu gabaÉ—aya a aljannah madaukakiya ya ba ni dama da ikon
Zama shubagar matayenka a aljannah. Ina ƙaunarka Ya Sameer...Ina ƙaunarka Ya Rayyan ina
matukar sonka Ya Saraki"
Hawayen dake zuba mata yake bi a hankali da harshen shi yana É—aukewa cikin wani salo
zuciyarshi ƙal yayi fixing gaze ɗin shi cikin idanunta
"I love you. love you more than anything Afeefah, ban taɓa jin son wani abu yadda nake jin naki
ba, I love you more than myself. I will always love you. I will love you till the end of my time. No
words can express how much love i have for you. I will alwavs be here for you no matter what
kin ji? Babu abinda zan miki da zan ji yayi yawa you are my favorite girl nd my only blessing"
Daga nan ta dafa chest dinshi sai ya koma kwance ta dane jikinshi da kanta ta shiga gigitashi
abinda bata taɓa sakewa tayi ba ta yi shi a ranar ta goge mishi hadda sai gashi yau ma yana yi
mata kuka don ta gama da rayuwarshi in dai ta fannin ne.
Washegari sun tashi da mummunan labari don Uncle Usman ya rasu labarin ya kaÉ—a ta don
faÉ—uwarta kawai suka ji hankalinsu ba karamin tashi yayi ba barin ma Rayyan a hannunshi ya
É—auketa suka tafi asibiti don duk abinda za su yi sun yi matsayin shi na likita ya kasa farkar da
ita yana jin panic akan ciwon Mammi amma bai san Meyasa duk abinda ya shafi Afeefah na
fitar da ragwantakanshi a fili ba, tsoro da fargaba ya sa ya manta yadda ma ake aikin likitacin
sai a asibitin ne aka samu ta farfado nan suke samun labarin tana da shigar ciki kuma razanar
da tayi har ya fara barazana ga É—an cikin nan ya saka aka yi mata allurar bacci don ta huta
sossai.
'Yan uwanshi sun yi rawan gani da su Sulaiman aka sallaci uncle Usman aka kai shi
makwancinshi dogon takarda da ya roki sulaiman rubuta mishi ya ba Rayyan akan idan ta dawo
daidai sai a bata.
Kwanan ta biyu kan ta dawo cikin hayyacinta tayiwa su Suhail kuka ba na wasa ba don maraici
babu daaÉ—i ta kuma yi alkawarin rike su fiye da Æ´aÆ´an cikinta har illa masha Allah.
A kwana na huÉ—un suka juya Fombina, anan ne Kawu suka san basu ga komai ba baki sake
suke bin irin girma, tsaruwa da ma kyaun masarautar irin mulkin da ake shimfidawa ko a
mafarki basu taɓa mafarkin halartar irin wannan wuri ba sai gashi wacce suka raina ta zama
sanadiyar da ake zube musu, sun yi kuka kaman me don sashe na musamman aka sauke su
mai martaba da Ammi suka tura ake musu hidima wane wasu masu kuÉ—i.
Ammi da mai martaba kaman su hadiye Afeefah jin labarin cikinta, soyayyar mijinta kuwa ya
ninku fiye da yadda yake jinta a da su Suhail sun zama 'yan gata don a take aka tsara musu
dakunansu Mai martaba ya sa aka cike musu wardrobes da kaya Ammi ma ba'a barta a baya
ba don abinda za ta yiwa jikokinta shi take musu har ma sun Fara ƙiran Afeefah da Ammah
Ryan kuma Abbu, school na musamman ya saka su masu musu hidima ma daban aka ware
don Afeefah laulayi mai wahalarwa take.
Satin su Kawu uku suka koma bayan Rayyan ya saya mishi babban waya an hada su da goma
sha tara na arziki suka koma, gidan su ya zama daga cikin gidajen da suka fi kowanne kyau a
garin É—an daidai kuma a kayace sai ya tuna akurkin da suka warewa Afeefah take rayuwa lallai
Allah ya nuna musu ikonshi sun tuba har sun rasa bakin tuba, a kuma satin da suka koma aka
fara gudanar da aikin gidauniyarta.
Sai ga kujerar Umura da Rayyan ya biya musu har da su Mai martaba za su tafi da su Abeeha,
sun yi murna barin Afeefah da bata taɓa zuwa ba za dai tayi kewan yaranta cikinta na wata
huɗu suna gama second semester exams suka chale ƙasa mai tsarki ranar da ta fara ganin
ka'aba tayi kukan da sai da tayi zazzabi bata taɓa ganin abu me kyau da natsuwa ba irin shi
duk rayuwarta, ta zube wurin ta yiwa iyayenta da yan uwanta da ta rasa Adu'a har sai da
miyaun Bakinta ya kafe, sun yi sati uku chan sayayyan baby kuwa kowa yi yake ba Ryan ba ba
Ammi ba ba su jannah ba, daga Saudi sun tsaya kaÉ—an a Turkey sun yi sayan kayan É—akin su
Aisha ana dawowa Nigeria Aka fara hidimar bikin su.
🖤Gureenjoh🖤
HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)
Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)
Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh
ADABI WRITERS ASSOCIATION
*FREE BOOK*
*Wannan shafin naki ne Uwar Ɗakin Damisa namu angon Nyla Ƙani ga Didi kuma Uban Didi.
Nana Halima ko na ce Leemar's delicious mai abincin 'yan gayu...Allah ubangiji ya ƙara miki
basira da hazaƙa ina godiya ƙwarai🥰*
*FINAL PAGE*
*60*
Zaune suke a cikin ƙayataccen hall ɗin da ake shan hidimar bikin Autan Mammi da Autar Ammi
waenda duk yanzu suka zama shalelen Ammi kuma angwayen ma duka 'ya'yanta, Ryan na
zaune bisa wani table riƙe da hannun Afeefah sun yi azabbaben kyau cikin outfit ɗinsu na Soire
party wanda english party ne duk mazan shigar suite suka yi matan english dress, Farin suite
ne jikinshi da baƙin shirt daga ciki bakin takalmi da baƙin hankey da ya ɗan leƙa bakinshi daga
aljihun, gashin shi ya sha gyara ainun fuskarshi sheki yake kowa ya ganshi ya ga cikakken
namijin da yake cikin kwanciyar hankali da jin dadi.
Tana sanye da wani doguwar riga na tsadadden sugar lace da ya bayyana cikinta da ya taso
yayi mata kyau ainun, ta saka gyale da ya tafi da kayan tayi wrapping kanta ta sha make up da
ya matuƙar zama mata wanda mijin nata ke ta bacin rai akanshi don kishi ya sa ko motsi tunda
suka zauna basu yi ba su Saleem sun ta kiranshi ya ƙi zuwa sai Sulaiman ne yake representing
É—in shi, gabansu Suhail da Suhaila ne shigan ryan shine irin na Suhail haka Suhaila ma irin na
Afeefah sai suka ba da wani kyau mai ma'ana.
Zarah ce da yanzu ta sake saboda janta da su Abeeha ke yi a jiki kuma tayi tuban gaskiya ta zo
ta ja su Suhaila don tana kaunarsu su ma kuma sun sonta, Afeefah ta kalli Ryan
"Ya Saraki..!"
A Shagwaɓe tayi maganan ya kalleta
"Matar Masu Sarauta ya aka yi?"
Yayi maganan yana É—age mata gira tace
"Eyyaa dubi ana yi wa Adda Abeeha barin kudi in je in manna kaÉ—an mu yi hoto?"
"Wanda kuka yi kan ku zo nan ya isa ba za ki shiga cikin maza ba"
Ta ɗan ɓata rai har ma nadamar Kwalliyar take ji yadda ya kasa ya tsare dama bikin duk ya
hanata wani hidima yadda ta so cin uwar sabada sai dai ta ga su Samha na yi don duk Fombina
suka zo har Sadiqa da ake hidimar aurensu tare sun zabi su zo nan in za'a É—aura aurenta sai ta
koma tunda sai an É—aura na Saleem an kai mishi matarshi zai ba da nata.
Har su kawu sun zo bikin da Inna Asabe sun bar inna Larai a gida, kawu ya sauya ƙwarai
natsuwa ta shige shi haka Inna Asabe da inna Larai babu wannan rawan kan da son zuciyar
sam sam sam.
A bikin ne ma take samun labarin Sabrina da iyayenta inda ta kwaso HIV da ya kasa warkewa
ga talauci da yayi musu katutu ita Gaje garin zuwa boka nema mata waraka ta faÉ—o daga tsauni
sai gawa aka É—auka Yaya ne ya zo neman tuba wurin mommy kuma ta yafe musu.
"Assalamu Alaikum warahmatullah"
Wata ƙawar Aisha ce ta yi musu sallama, Afeefah ta kalleta da mamaki don ta kula yarinyar na ji
da uban ta wani ne tun fara bikin sai rawar kai take bata zaci Rayyan zai wani kula ta ba sai ta ji
ya amsa, a take wani abu ya taso mata zuwa wuya wato ita ce bata da kishi shi ya hanata tashi
saboda maza ita kuma tana kallonshi yana magana da wata macen.
"Yayanmu barka dai, mun jima muna kallon irin kokarin ka akan rayuwar matasanmu a
koyaushe His Excerllency ba shi da zance sai taka gaskiya samun shugaba irinka abin alfahari
ne in kuwa da irin ku rayuwar matasanmu ba zai taɓarɓare ba"
Ya san mahaifinta Gomna ne mai ci a yanzu don haka yana martaba gidansu sai ya É—an
murmusa
"Thank you"
"idan ba damuwa ga wannan na jima ina so na baka ban samu ganinka ba Its a small gift don
Allah kar ka ce a'a"
Ta ajiye wani karamin paper bag tayi murmushi ta juya ta wuce.
Kaman an ce ya kalli Afeefah ta haÉ—a gabas da yamma kudu da arewa, idanunta har shekin
kwalla su ke, hannunshi dake cikin nata ya É—an murza don ta kalleshi amma ta É—auke kai sai ma
ta miƙe chadak ta nufi waje, da sauri ya bi bayanta yana dan kiranta amma bata waiga ba dab
wurin mota ya riƙo damtsen hannunta a hankali ya janyota bayanta ya sauƙa kan kirjinshi yana
dan lekan fuskanta yace
"Tsaya mana BoÉ—É—i fushi kika yi?"
Fuskarta babu walwala ta janye tare da Juyowa ta kalleshi
"No, Meyasa zan yi fushi?"
"Me yasa kika fito to ina ta magana kin ki kulani?"
Ta kalleshi
"Gashi na kula ka, ina jinka"
Numfashi ya sauke
"It seems kin gaji mu tafi gida"
Ta juya ta nufi motarshi bata ce komai ba, numfashi ya sauke yana É—an shafa gira ya nufi motar
tuni ta buɗe ta zauna ya shiga shima drivern shi ya ja suka nufi ɓangaren su tunda akwai tafiya
sossai, hannunta ya riƙe ta zame tare da juyawa tana kallon Window.
"Akwai abinda ya faru ne? Ko na miki ba daidai bane?"
"Babu, me kuwa zai faru?"
"Ta ya zan sani Afeefah na ga kina fushi"
Ta É—an bashi side eye tana sake juyawa
"Ni ba fushi nake ba"
Lip dinshi na kasa ya É—an lasa har ga Allah bai zaci wai kishi take ba a hankali yace
"Ok"
Ya kalleta sai ya ga ta sake haɗa rai ya sauke numfashi har suka isa ta sauƙa tun kan ya
zagayo ya buÉ—e mata.
Ɗakinshi kai tsaye suka nufa don suna shiga parlorn ya riƙo hannunta, bata ga amfanin make
up É—in ba bayan hotunan da suka yi musamman nata dashi da yayi kyau ainun hannunshi kan
cikinta yana murmushi yalwatacce ita kuma tana kallon hannun nashi tana murmushi wanda har
ta mayar wallpaper to bayan shi bata ga amfanin adon ba.
Wanka ta shiga bayan ta goge Kwalliyar shima ya kwaɓe ya bi bayanta, tana tsaye shower ta ji
ya manne da ita yana bin wuyanta da tafiyar tsutsa, zamewa take har ta gama É—auraye jikinta ta
fice ta bar shi ya bi bayanta da kallo, bata wani tsaya drying kanta ba ta duba shirt din shi ta
saka don tana jin daaÉ—insu sossai ta zame towel É—in tana bottuning shirt É—in da iyakarshi rabin
cinyarta ya fito É—aure da towel a kugunshi da wani irin kallo yake binta ganin ta nufi bakin gado
ya isa ya kama hannunta
"Kina so ki yi mura ko?"
Bata tanka ba yaje ya ajiye ta gaban madubi ya zaro hand drayer ya shiga busar mata da
gashin cikin kulawa.
Miyau take hadiyewa tana bin ginannen jikinshi dake bayyane da kallo, ganin zai kalleta ta
ɗauke kai yayi murmushi ajiye drayer ɗin yayi ya duƙa sossai yana shunshunar wuyanta da
baya rabo da kamshin da yake masifar so, a yanzu har da lips É—in shi yake goga mata zuwa
sajenshi da ya sa duk numfashi na kwace musu barin ma shi da yake a kunne, hannunshi ya
mayar ta gaban rigar nashi dake jikinta ya fara unbottuning saman shirt É—in yana sauke
wahalallen numfashi mai rikitarwa.
"Ya Saraki ka bari, bacc..."
Hannun da ya tura cikin rigar ya sa ta É—auke numfashi ganin zaunen ba zai kai su ba ya É—agata
chadak zuwa gado yana ƙarasa unbottuning shirt ɗin, tun tana resisting har ta sallamar suka
rikice a duniyar masoya sai da komai ya kamallah ta zame za ta sauƙa ya dawo da ita yana
shafa lallausar Fatan bayanta
"Kika cigaba da fushin nan zuciyata za ta iya shiga matsala Ya Alami" (Duniyata)
Yana cigaba da shafata a natse ya cigaba
"A faÉ—a laifina in yi gaggawar tuba kin san Sameer mai biyayya ne a fadarki"
Ta É—an yi murmushi ta isa? Sarkin gobe ya zama bawan ta?
"Shine har da yiwa wata murmushi a gabana har da karɓar gift ɗinta"
"O'ooo am very sorry ban san dalilin fushin ba kenan, kin fa san babu macen da take da daraja
ko kima a idanuna bayan ke da Ammi, Afeefah ke ce mahadina daga ke kuma Ryan ya gama
kallon 'yanmata"
Wani sanyi ne ke kwarara mata yana mata son da bata san adadin shi ba, É—agowa tayi ta
mayar da kanta kan pillown da yake sai ya juyo suna kallon juna tace
"Na sani ba zaka taɓa zama da mace daya ba amma na rasa Meyasa duk sadda wata macen
ta kallar min kai sai in ji mutuwa ne kawai ya saura mini tsabar zafin zuciya"
Yayi murmushi yana riƙo hannunta a tsakiyarsu
"Wa yace miki hakan?"
"An ce sarakai ba sa zama da mace É—aya"
"Za'a fara a kan Sameer Muhammad Modibbo don daga ke na rufe kofa a gidana"
Soyayyarsu suka cigaba da sha yana bata duk kulawarshi ta so ta tafi Kd ya hana don haka ta
mayar da hankali kan lectures É—inta da kulawa da shi da kuma cikinta har Allah ya kawo ta
watan haihuwa, wani ranar Alhamis da dare labour ya saka su nufar asibiti babu shiri a safiyar
juma'a ta santalo katoton É—an ta fari tas mai kama sak da mahaifinshi wanda a ranar BOÆŠEJO
ta sha kuka ganguna da kalangu sun yini dokawa kowa ya gifta Masarautar Fombina sai ya san
ana cikin alkhairi dumu-dumu.
Yaro ya zo da tarin alkhairi don Mai martaba ji yake kaman ranar ne ya fara riƙe Sameer a
hannunshi tuni lungu da saƙo sun samu labari hotunan kuwa har ya je Kaduna uwar jego ta sha
ƙauna iri iri, ko da suka dawo masarauta sashenta take wata dattijuwa ta shiga hidimar kula da
ita da bata cikakken kulawa na masu jegon gargajiya, ranar suna an yi bidiri Aisha ta zo da
cikinta kuwa haka sulaimi ma ta zo da nata tamfatsatsen cikin Haihuwa yau ko gobe sai Jannah
da take shirin zuwa amma labour ya hanata itama a ranar sunan ta haifi danta namiji, Abeeha
ma na fama da laulayi aka yi hidimar suna na ji da gani kuwa yaro ya ci suna Muhammad
Sameer Modibbo.
A daren sunan Rayyan ya tafi Kaduna don da Jannah ya yini, Ammi ma da kanta ta tafi da wasu
hadimai duk basu dawo ba sai da aka yi suna suka bar mata hadimar da zata kula da ita mai
martaba ya aika sha tara na arziki inda yaro ya ci sunan Rayyan.
Bayan sunan Muhammad da suke cewa Arham Sulaimi ta koma da sati biyu itama nakuda ya
tashi mata sai dai she didnt survive bayan ta haihu Allah ya karbi ranta sun shiga tashin hankali
dole Afeefah suka tafi Kadunan duk sun yi jimamin mutuwar ba kadan ba, inda Sameera ta
samu Saleem ta roƙe shi ko don 'yar da ummu sulaimi ta bari tana so ta auri Sulaiman ta shayar
da yarinyar kaman na ta.
Kan Sulaiman ya amince Umman shi ta amince aka daura musu aure kuwa babu wanda ya
hanata shan kwayoyin da ruwan nono ya zo ta shiga kula da ummu sulaimi ƙarama don
soyayyar da take yiwa Sulaiman shi ya dawo kan yarinyar kuma tana haƙuri don auren mijin
matacciya wanda yake son matarshi sai a hankali. Baaba jummai da Afeefah kaman jiƙa da
kaka don kusan kullum suna tare a waya kuma Daga ita har Rayyan da su Ammi su kan yi mata
sha tara na arziki don kaman uwa take har a gidansu Sulaiman É—in ba 'yar aiki ba.
Rayuwa ya cigaba da juyawa ba za'a ce ba'a saɓawa ba sai dai duk abu da fahimtar juna ba
karamin lasting yake yi ba, sossai rayuwar Afeefah yake kan saiti har aka wayi gari ta gama
karatu inda ranar da ta gama last paper ɗinta ta shigo masarautar ta sauƙa a sashensu kawai ta
ga wata hadaddiyar tsadaddiyar Maybaach Ash Color an yi mata ado da furanni, Rayyan ta gani
ya fito cikin kyakyawar shiga fuskarshi É—auke da smile yace
"Congratulations Allah ya albarkaci abinda kika karanta My baby mama"
Tsallen murna tayi fuskarta dauke da fara'a ainun ta karbi keyn ta buÉ—e motar sai taga balloons
na zubowa kaloli daban daban Juyowa tayi rungumeshi cike da farin ciki take cewa
"Thank you so much My love, My best friend, My for ever, My safe space. Thank you for being
you and choosing me everyday.."
kan yayi wani motsi ko magana sai ta fara jin tashin trumpet ana yi mata congratulations tana
juyawa ta ga abokan arziki na kusa da na nesa ta ma rasa yaushe suka zo kuma ta yaya?
Ameer da Abeeha sanye cikin shiga iri daya Abeeha na rungume da É—iyarta mai sunan Mammi
ana kiranta Mamah bata wuce shekara da wata biyu ba, Jannah da Rayyan É—inta da yake ma
wurin shekara uku da wani cikin a jikinta, Saleem da Aisha da suke riƙe da wani Rayyan ɗin dan
wata huÉ—u kacal, Sameera na tura ciki ga Ummu sulaimi da tayi wayo sossai gefen ta Sulaiman,
ga Samha Amarya wacce bikin ta ne next suke ta planning don abin bai zo da wuri ba, sossai
take murmushi tana kallonsu yayyenta ne, Ƙawayenta ne kuma 'yan uwanta ne... Hawaye taji
ma tana ji a daidai sadda su Suhail su uku cikin shiga iri daya na kananun kaya suka zo suka
rungume ta.
"Congratulations Ammah"
Ta É—aga Arham ta na dariya sossai take cewa
"Thank you love, na gode sossai"
Rayyan ya matso yana dauke mata hawayen farin cikin da take, nan suka isa parlor abincicikka
da cakes iri daban daban an ci an sha an yi hira kaman ba gobe, Rayyan dai baya cewa komai
sai murmushi dama sun riga sun san hali Afeefah ce mai shan maganarshi idan ta ciyo shi.
Sai dare suka watse ta fito cikin shirin kananun ƙaya wani half gown purple da ya amshe ta ya
fitar da duk wani sura na jikinta, parlorn su kaman ba shine dazu kaca kaca ba hadimai sun
gyare tsaff an cika turarukan wuta, É—akinshi ta nufa bayan ta duba yaran sun yi bacci yana yana
operating Phone É—in shi hankalinshi ya É—an dauku a chan jikinshi ba riga, tana isa ta sa hannu
ta zame wayan ya É—ago ta jefa wayan kan gado tana murmushi sai ya saki baki yana kallon
rigar na jikinta da ya fito da full chest É—inta daga sama, rabin cinyanta duk a waje gashinta a
É—aure wuri guda sai sheki yake tana ta zuba kamshi bakinta da ta sa wani lilac lip gloss sai
sheki yake, hannu ya wara mata ta kuwa tafi a slow suka yi baya baya tana kwanciya nashe
nashe akan jikinshi don babu inda ya taɓa katifa a nata jikin, da hannunta take wasa da kirjinshi
idanunshi a lumshe ya ce
"BoÉ—É—i"
"uhmm BoÉ—É—in BoÉ—É—i"
Idanunshi da suke ta lumshe wa a mayen ƙaunarta ya buɗe don sunan ya mishi daaɗi
'kyakyawan mai kyau'
"I love the name"
"kai wani suna ne baka so?"
Yayi murmushi mai sauti
"Ai duk sunayen ne daga kin faÉ—a sai sun motsa zuciyar maza"
Tayi murmushi tana tuna lokacin da yake mata masifa in ta kirashi Saraki ta ce
"Shiyasa baka son na ce Ya Saraki?"
Ya ja iska kadan yana furta
"Aouchhh sunan ya fi taɓa ni but sincerely wani irin fusgata yake zuwa gareki in kika faɗa cikin
wannan voice din naki mai daaÉ—i"
Tayi murmushi yana zame ribbon É—inta ya cusa hannunshi cikin gashinta ya ce
"FaÉ—amin abu mai daaÉ—i"
"I love you"
Ya tsinci kanshi da lumshe ido yana jin kalmar straight to his heart.
"FaÉ—i wani"
"Ina sonka!"
Tayi maganan tana wasa da sajenshi cikin susa mai daaÉ—i.
"Sake faÉ—amin"
"wani waƙa Naji da ya dace da kai in rera maka?"
Gira ya É—aga ta gyara kwanciyar ta akan jikinshi ta shiga mishi wakan
"ka sace zuciyata!
Kana kai mini gatah!
Mata nai musu rata..
Ka ce in je in hutaaa..
Ga mijina mai tsafta
Mai halin girma na sarauta
Zama da kai sam babu wahalta..!
Cikin mazaje ka cire tutaaa
Mai adalci da nagarta..!
Fushinka shi ke sa ni É—imautaaa
Mai haƙuri shi ke dafa dutsseee!!"
Numfashi ya sauke muryarta wane sarewa haka ya buÉ—e idanunshi da suka mace a so yana
kallonta a hankali yace
"hakane kam mai haƙuri shi ke dafa dutse, nima na cire tuta tunda na same ki"
Tayi dariya mai yanayi da giggle ya juya ta yana shunshunar wuyanta ta zura hannunta gashin
shi tana É—an kame jikinta tace
"Toh ai ban gama waƙar ba fa Boɗɗin Boɗɗi"
Ɗagowa yayi yayi pecking lips ɗinta chan ƙasa yace
"Toh ƙarasa Babylove"
"Kaine tsanina...maqabulina!!
Kai ne rabin raina... Makasudina!!
Kaine muradina.. Kai ne
Farin cikin raina... Kai ne
Al'amari babba... Kai ne
Abin da duk zan ma.. So ne
Murmushi in kai kyau neeee"
Ya kuwa doka murmushin yana rasa wani baiti ne ma ya fi daaÉ—i, bakinsu ya haÉ—e ya shiga aika
mata zazzafar Kiss cikin kiss É—in ya É—an zame yace
"Nima ke ce farin cikin raina, ke ce muradina kuma ke ce rabin raina My Hayateee... Help me
mu samu Mammin mu a daren nan"
Kaman jira kuwa ta sakalo wuyanshi tana mayar da Bakinta cikin nashi.
*BAYAN TSAWON LOKACI*
Afeefah ce ke saukowa jirgi hannayenta rike da wasu 'yan mata kyawawa biyu, bayanta Suhail
ne da Suhaila da za su yi shekara shidda zuwa bakwai sai Arham da yake huÉ—u da 'yan kai
bayansu wasu hadimai ne guda biyu da suke taimakonta da yaran har zuwa wani prado baƙi
wuluk a jere motocin huÉ—u suka fice daga airport É—in sai fadar Fombina wanda a yanzu LaamiÉ—o
Sameer Muhammad Modibbo ne ke kan mulki, Ƙashin bayan matasan Fombina, jagoran
al'umma kuma jarumin Afeefah uba ga Ciroma Arham da 'yan uwanshi Garkuwa Fulanin duk
Nijeriya.
Isarsu tamfatsatsen sashen na Fulani Afeefah ana ta baza gaisuwa da ban girma tana amsawa
cikin kulawa da kaunar al'ummar nasu kaman yadda suke masifar ƙaunarta, Ɗaya daga
kyawawan yaran nan mace tace
"Ammah mun dawo mu je wurin Abbu? I Miss himmmm?"
Girgiza kai Afeefah tayi
"Abbu na cikin taro Alhan, ki bari anjima idan ya dawo sai ki ganshi ko Mammin Abbu?"
Ta É—an tura lips
ÆŠayar tace
"Ammah to mu je wurin Jadda?"
"Ku fara yin wanka Ahlam sai ku je na san ta yi missing surutunku"
Da gudu suka yi É—akinsu daman yan mazan sun jima da wuce wa yanzu haka bai wuce sauri
suke suyi wanka su tafi wurin Abeey ba dake ji da su.
ÆŠakinsu ta wuce ita da mijinta don bai wani yarda da raba sashe ba tunda har yau bai yarda ya
karbi auren wata ba duk kuwa da tallar da ake mishi tun kan Abeey yayi murabus ya bashi har
yau, ya ce duk abinda zai nema ya samu a wurinta to na me zai sake aure? Me kuma zata
bashi banda ta nemi daga mai hankali? Afeefah na iya kokarinta wurin ganin ta bashi Kulawa,
soyayya da lokacinta bata aikin komai banda gidauniyarta kuma duk ba ita ke kula da komai ba
sai in ya kama don haka tana da lokacinshi full kuma bai taba neman ta ta ƙi ba a koyaushe
burin ta ta faranta mishi ko da har ranta bata so.
Tana zame kayanta ta É—aura towel zata shiga wanka kawai taji an yi hugging É—inta kamshinshi
da numfashin shi ya sanar mata waye, fuskarta washe da murmushi tace
"Sarakina"
"Matar sarki, barka da dawowa ga masoyinki"
Ta waigo tana Shagwaɓe mishi
"Ba wani bayan ka gudu ka baro mu Abuja"
"Kin san ba da son raina bane hakan da a sona na ne da kowa ya tafi ya bar mu mu biyu a
duniyar nan"
Dariya tayi
Yace
"Ya taron na ganku a Tv i hope komai ya tafi lafiya?"
"Alhamdulillah wannan kam ya ƙare saura na Lagos"
Girgiza kai yayi
"Babu inda za ki je, ki wakilta wata ko wani su je miki"
Karkata wuya tayi
"Har kaduna? Ka ga fa akwai sunan ÆŠan Samha ga yaye É—alibai da za'a yi a gidauniyarmu na
Dutsen-wai karo na wurin bakwai akwai kuma taron buÉ—e wani a Anchau"
Girgiza kai yayi
"Ba zan juri nisa dake ba, wai har ma gidauniyar nan nawa za ki buÉ—e ne?"
Tayi dariya yana daukar ta chak suka nufi toilet don yayi mata wanka yana tambayarta Ammi da
Mamminshi fa tace sun tafi sashen Jaddansu(Ammin)
Suka shige cikin bahon wanka suna cika juna da kauna, tana daga cikin matan manya da ake ji
dasu saboda taimako, iya ado da shigar kamalarta, haƙuri da iya maganar ta don duk tayi
magana a taro sai ya kwana biyu yana circulating platforms, karama ce mai halin girma kaman
yadda mijinta yake ƙarami cikin sarakunan yankunan Arewa sai dai akwai zuciya da kwarjini,
idan suna tafiya a tare za ka zaci É—awisu ne yana baza ado gaban 'yar budurwar É—awisunshi,
komai ya wuce a rayuwar Afeefah da har in ta tuna baya sai dai tayi murmushi su kawu na chan
Dutsen-wai har yau sai dai ta kai musu ziyara ta dawo. Dafa ita har Rayyan sun yi sadakatul
jariya da sunan iyayenta da Mammi har basu san adadi ba.
Ta samu akallah gidauniya 10 da ake bata taimako daga masarautu zuwa gomnatin jaha har na
tarayya sun san da zamanta, kasancewar gidauniyarta dake tallafawa mata da yara akan
neman ilimi, sana'o'i da tsayuwa akan kafafunsu kuma dama babban burin ta kenan mutane su
samu ilimi kuma suna samu daidai gwargwado Alhamdulillah.
ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH!! ALHAMDULILLAH!!! ANAN NA KAWO KARSHEN
WANNAN LITTAFI NA HAIHUWA DA HANJI ABINDA MUKA RUBUTA DAIDAI ALLAH
UBANGIJI YA BA MU LADA WANDA MUKA KUSKURE ALLAH UBANGIJI YA YAFE MANA.
HAKIKA TAFIYAR NAN NA DAGA CIKIN TAFIYAR DA YA MATUƘAR YI MIN DAAƊI BISA
GOYON BAYANKU DA COMMENTS NAKU, BAKI BA ZAI FASALTA MUKU IRIN DAAÆŠIN DA
NAJI BA DA KALAR SOYAYYAR DA KUKA NUNA MIN NA GODE NA GODE KWARAI DA
GASKE.
HASSANA SALLAU(MAMAN MUNIFA): DOLE NA AMBACEKI DON KINA ÆŠAYA DAGA CIKIN
WACCE TA BA NI GOYON BAYA A WANNAN TAFIYA ÆŠARI BISA ÆŠARI BAN TAÆA YIN
PAGE DA BABU COMMENT NAKI BA NA GODE KWARAI ALLAH YA RAYA ZURI'A YA BAR
ƘAUNA TSAKANIN KI DA ABBAN MUNIFA.
FATIMA A MUHAMMAD: SIRIKA KUMA AMINIYAR ANGO INA GODIYA DA GUDUMAWARKI
KWARAI DA GASKE. ALLAH YA BAR ZUMUNCI YA NUNA MANA RANAR DA ZA MU ZO
SHAGALI KADUNA.
SIS NANAHALIMA KWARAI NA GODE DA GUDUMAWARKI ALLAH YA BAR ZUMUNCI.
HANIFA MUHAMMAD GURIN: YAYATA KUMA AMINIYATA KAWAR CIN MUSHE NA. MY
SHAYLAAA%% MY RIDE OR DIE🥰🥰NA GODE DA TAKI GUDUMAWAR DA SHAWARWARI
AKAN KO WANI PAGE DA ZAN RUBUTA.
SAFIYA GALADANCHI: ƘAWATA MATAR HAMMANMU FATAN ALKHAIRI ALLAH YA KAWO
MANA KE KASAR FOMBINA💃💃
OUM AMEER: MASOYIYATA KWARAI NA GODE DA ƘARFAFA GWIWA ALLAH YA BAR
ƘAUNA YA RAYA MANA SU AMEER YA KAWO WASU 'YAN UKU SAU UKU☺ï¸
DA MA DUK WAENDA BAN KIRA SUNA BA NA GODE SOSSAI DA SOSSAI, TAKU HAR
KULLUM
🖤GUREENJOH🖤